Shamaki ya numfasa tare da faɗin Allah ka bamu mafita. Cike da sarewar gwiwa da kuma addu'a Allah ya fidda shi. Ya nufi gida. Kafin ya kai an kira Isha'i ya isa suna raka'ar ƙarshe, ya shiga ya suka ƙarasa sannan ya ɗora, ya fito ya tarar da mutane suna kjranshi kamar kullum. Ya na ta sallamar su har Buhari masinjan Ofishin A'isha Maman Afra ya miƙo mishi takardun masu kayan ɗaki. Ya amsa ya ce Malam Buhari zan duba a gida. Gobe sai kamin bayani. Malam Buhari ya ce akwai na Ujila a ciki wannan na saman tace ba su bi ƙa'idar kawowa ba, amma mabuƙata ne in da hali ka saka hannu kai da Hajiya ita dai ta saka. Yace to ba damuwa zamu yi magana da Hajiyar. Ya gama sallamar kowa sannan ya nufi gurin Hajiyar. tana jan carbi ya zauna gefe kafin ta kammala. Ya ɗauki takardar saman da aka ce ta gaggawa ce yana dubawa. Zai iya taimakon Yarinyar ko dan sunan Babynsa da take da shi, ya ɗarsa hakan a zuciyar sa. Maimaita Rabi Abubakar, bai san sunan mahaifin ta ba, amma yasan da wahala su zo neman taimako domin ya kula cewa mahaifin Baby mutum ne mai wadatar zuci. zuciyar shi ta kasa nutsuwa ya gangara can ƙasa gurin lambar waya ya duba lambobin da kyau, gaban shi ya faɗi, ya ciro yawa yana soma saka lambar sai ga sunan da ya sawa Baby ya fito. Soyayyata. Baya buƙatar sake sanin wata hujja iya wannan ta wadatar. Ya zare takardar ya aje gefe domin gagarumar matsala ce in har Hajiya ta ga wannan takardar, sannan ya ci gaba da duba sauran. Hajiya ta katse shi da faɗin "An shigo?" Ya dube ta da sauri na shigo sannunku da gida, ya gaishe ta cikin girmamawa ta amsa tare da tambayar kasuwa, ya ce Alhamdulillah. Sai kurum ya ji kamar daga sama ta ce "Ya kabaro 'yan uwannaka?" Ya zaro ido tare da faɗin na'am. Ta share zance da kallon takardun hannunsa, "Waɗannan kuma na menene?" Ya Kalli takardun cikin sanyin jiki tare da zargin wata cikin yan uwan nasa kenan harta sanar da Hajiya ko kuwa dai Hajiyar ce da kanta ta gano cewa sun yi zaman to ta yaya zata gano hakan. Yace, na masu buƙatar kayan ɗaki ne. "Wancan fa da ka aje gefe?" Yawun bakinsa ya tsaya cak, ya hura iska tare da ajiyar zuciya, takardar wasu ne da Maman Afra ta ce ba su cike ƙa'ida ba, na sakasu a gefe ne domin sai mun kammala da waɗannan. Ta tsura mishi ido. Wace number ka ɗauka a takardar?" Zufa ta karyo mishi cikin sauri yace ta Maman Afra Anty A'isha. ,ta ce in kirata inji Malam Buhari da ya kawo saƙon,to naji ƙiwar in tsaya binciko lambar ta a waya ta sai na ɗauka a nan. Ta saki ɗan murmushi mai sauti. "Kenan ita bata samu zuwa zaman ba?" A ina? Ya tambaya da sauri. dai dai lokacin da Juma ta shigo da sallama. Hajiyar ce ta amsa domin shi ya suma da mamaki gami da fargaba. "Juma tana gaida kai tunanin me kake yi ne?" Ta katse shi. Banji ba ne Juma sannu da ƙoƙari. Juma tace ina amsawa, hidima ta zo ai dole abubuwa sun yi yawa. Yace Ummm haka ne. Ya soma kiran layin A'isha. Ta ɗaga. Ya ce Maman Afra kina jina kuna lafiya? Tace lafiya lau,yace Malam Buhari ya kawo saƙo ya ce min kin sako wani Form na Ujila kuma kince muyi waya. Tace "Haka ne." To amma kinsan dai abin nan komai a tsare yake, zan maido miki ki aje shi su jira kamar yadda sauran mutanen suke bin layi, inhar muka fara irin haka za su iya sanar da wasu cewa mun basu agajin gaggawa kuma sai ki ga mutane sun fara zuwa irin wannan roƙon,ke kanki sai su ɓata miki tsari. Tace haka ne, kuma suma mutanen basu dawo ba, munyi da su zasu zo da mahaifin yarinyar yau amma shiru. Domin masu kawo takardar sunce marainiya ce, ita kuma takardar ta nuna cewa marasa ƙarfi ne. In sunzo sai a faɗa musu su jira, sai a saka su a jerin wani watan ko?" Yace haka ya yi suka yi sallama ya ɗago kai ya kalli Hajiya wadda ke faɗawa Azima abinda zata zuba mata daga jerin abincin da Juma ta jere. Yace Naman Afra tace a gaishe ku. "Muna amsawa, ta faɗa ba tare da ta kalli gurin da yake ba. Azima tace Yaya Shamaki me za a zuba maka?" Barshi Azima sai anjima bani dai robar ruwan can. Ta miƙo masa tare da faɗin "Kamar ya yi sanyi da yawa." Hajiya tace Kije ki ci abinci zai fi buƙatar mai sanyin domin naga kamar ya yi zufa. Shamaki yace ai kuma yau ba zafi kuma ga AC ma. Tayi murmushi mai sauti. Ya san wannan murmushin na Hajiya na tuhuma ne. Ya soma tunanin yadda zai ƙoƙarta a bagarar da maganar, ya san Hajiya tana son ƙure shine. Ya miƙe bari inje inɗan watsa ruwa. Tace to babu laifi. Ya kwashi fayal fayal ɗin. Sai tace "Ajiye su zan duba." Duk da faɗuwar da gaban shi yayi sai yace to,ya ɗan sake su kan ya kai ƙasa suka tarwatse, sai ya tattara ya haɗa su ya saka na su Baby a tsakiya.
Ya tafi yana shiga ɗaki ya soma faɗin Innalillahi wa'inna ilaihirra un. Ya zauna bakin gado ya ɗauki waya da sauri ya kira layin Maman Umar yace maman Umar wai in tambaye ki. Tace "Injinka." Waya sanar da Hajiya mun zauna Meeting? " Tasani! Na shiga uku?" Ta tambaya cikin gaggawa kuma atsorace. Yace yanzu na zillo daga falon nata kuma taƙi faɗa min ya akayi ta sani,na ruɗe fa ko dai acikin su Maman Nana akwai wadda ta yi subul da baki? Maman Umar ta ce babu,duk cikinmu Maman Afra ce kawai ta tafi, su gasunan kuma itama wallahi baza ta sanar da Hajiya ba. Yace to yanzu me zance mata tunda dole in koma yanzu dan akwai wata damuwar wadda tafi wannan ɗaga hankali. "Wacece ?" Ta tambaya cikin sauri. Baya buƙatar su sani dan haka ya ce ki share kawai, amma wallahi kamar in nutse bana cikin natsuwa yanzu haka. Tace kawai ka nutsu in zaka koma ka tanaji wata.maganar ko labari ɗankko mata zancan masoyinta wannan zai ɗauke mata hankali har mu tattauna yadda a kayi ta sani. Yace shike nan. Ya watsa ruwa cikin ƙarfin hali, ya saka Jallabiya mai gajeren hannu sanan ya fita zuwa gurin. Hajiya ta gama cin abinci tana shan shayi ya zauna idanun shi suna kan fayal ɗin, har yanzu suna inda ya barsu. Ya ɗarsa a zuciyarsa cewa har Hajiya ta gama dubawa ne ta ajiye ko kuwa dai dama shine ya ke tsorata kansa.
Na gama tsifar kai na ce Jamila don Allah ki je gidansu Anty mai Saloon ki ce zan zo wankin kai, kuma ina son aja min gashi ance ɗari huɗu ne. Jamila ta kalli Umma ta ce Umma a tambayo? Umma tace dan Allah ku rabu da ni, ki ɗauka a cikin dubu ukunki da saurayin naki ya baki ta walima nace Umma zanyi girki walima da cincin tunda ga lemo. Jamila tace Meat pie ake yi fa ko dounot. Umma tace, duk abinda zata yi ma dai ga su can ta ɗauka, amma ki sani dai baza a yi girki ba, ana ta neman yadda za a yi a samu shi kafar a abinci biki za a haɗa a samu a fita kunya. Ga maganar kayan ɗaki Abbanku ya ƙi sam ya rubure ga maƙota sun saka ido suga nuni kunya a samu na yarda min magana. Nace Umma tunda Abba baya so kawai a haƙura da maganar Neman taimakon nan, tunda ai shi Yayan yace baya
da matsala dan ba a min kayan ɗaki ba. Umma tace, " Aike sam baki da hankali musamman yanzu tunda ki ka samu wannan saurayin tashe rashin kunyar ki ta bayyana damuwar ki a kai ki, za a kai ki ba dai namiji ba. Kuma ki kasa kunne ki jini sosai wannan zaƙuwar da kike nunawa in baƙi suka zo 'yan biki ki ka sake ki ka yimin wannan giggiwar sai na saɓa miki, kayan ɗaki kuma inma ba a yi ba koda naji haushi na banza ke za a yiwa gori. Nace to Umma kiyi haƙuri Allah ya bamu mafita. Jamila ta fita domin ta tambayo min gurin wankin kai. Matar nan daƙyar ta amshi ɗari biyar wai gashina yana da cika da tsawo. Na yi mamakin ganin gashina har gadon baya matar tace wai dan ba mai na sa ba da sai ya fi haka tsawo. Nace zanzo da bikina ta sa min. Naje gidansu Umman Amina ina tambayar inda zan samu wadda ta iya Meat pie. Tace Amina ta rakani gidan wata amarya tana yi. Nan dai mukaje tace saidai taimin kwaɓi inje gidanmu in murza in soya domin mijinta zai dawo yamma ta yi. Na siyo abubuwan da ta faɗa na kwaɓi ta kwaɓamin na ɗauka mukaje Amina da Zuhra da Jamila suka tayani, na kifi ne da kayan miya dan kuɗin bazai kai insai nama ba. Muka soye shi raƙayau wai domin kar ya lalace. Na basu su 'yan tayin aiki sukace ya yi daɗi sannan na kaiwa Umma nace gashi ta ɗiba ita da Abbanmu sai a ƙulla sauran. Tace to shi saurayin naki kin ɗibar masa? Nace anan za a ɗibar masa . Umma tace "To a bari sai da sassafe yanzu dai in je in rufe.
Na yi wanka na shiga ɗaki na kwanta ina ta tunanin banji muryar Mijina ba,kuma har yanzu bai ɗaga kirana ba,duk da ɗazu da safe yamin text ya ce fatan ina lafiya kuma in gaida su Umma. Na ce bari in sake kiranshi ko zai ɗaga. Jamila tace mayya sai ki yi tayi. Nace ai ko tara bata yi ba. Na danna kiran layin gabana yana faɗuwa tsabar son da nake masa ko sunan dana sa mishi a wayar na kalla sai inji tsigar jikina tana tashi. Muryata ta soma rawa lokacin da sautin muryarsa ta doki dodon kunnena. Baby Ya ku ke? Lafiya lau Yaya lafiya baka zo ba,kuma baka min waya ba, na shiga damuwa da banjika ba. Yace ayyuka na Baby suna da dama kiyi haƙuri zan zo ba na faɗa miki ba rannan nace bazan ke samun zuwa akan lokaci ba?" Nace Kasan dai alƙawari kaya ne ko? Yace "E." Na ce to ka san dai ka yi alkawarin zuwa filin saukar karatunmu domin kaga karatuna ko? Yace "Haka ne." Na ce to gobe ne da ƙarfe goma na safe za a fara, dan Allah kazo ka ga karatuna. "Wai dama gobe ne?" Ya tambaya da sauri. Nace e mana. "To kuwa gara da kika tuna min gobe Lahadi insha Allah zan samu in zo. Cikin Farin ciki nace to ka gaida Hajiya da su Anisa,kuma ina gaida su Anty su duka. Yace duk zan faɗa musu. Nace to sai da safe yace to mu kwana lafiya.
Jamila ta lalle ni bayan na gama waya tace wai ke Yaya Baby har wani canza murya ki ke yi ba in zakiyi waya da Ya'yan nan, sanan wannan wayar taki ba a saka mata kati ne? Tunda aka baki ban taɓa jin kice a siyo miki kati ba, kuma rannan har Baabar Kurna ki ka kirawa Umma, sun jima suna magana. Sai lokacin na kula da haka na ce taɓ tun katin da ya kawo a kwalin wayar kuma ai katin ɗari biyar ne. Jamila tace duba Balance ɗinki mu gani, na tsurawa lambobin ido baya na danna bangane adadin kuɗin ba. Na furta ina kallon Jamila. Tace, mu gani tace kamar ɗari takwas ko dubu takwas. Nace ko dai naira takwas ba. Muka sa dariya. Nace duk tsiyarsu ko nawa ne dai sai sun ƙare domin kirana zantayi ƙila kuma ina cikin wani tsari ne wanda suke bada bananza. Jamila Tace 'hakane ma. Na sauke ajiyar zuciya na ce Allah na gode maka Ubangiji kamin komai.
Jamila tace Yaya Baby kina bani mamaki har cikin dare ina jinki kina yiwa Allah irin wannan godiyar, wallahi ba su Umma ba ko ni ina jin haushin yadda kika koma mara kunya lokaci guda. Na tausasa Murya yanzu wannan rashin kunya ce Jamila yi wa Allah godiya? Tace "Ai ba iyaka godiyar zaki tsaya ba, da banyi magana ba cewa zakiyi da ya baƙi miji kamar Yaya Aliyu a dai-dai wannan lokacin." Nace to Jamila meye laifin hakan kar ki manta a da fa ko kare bai ce yana sona ba har tsegumina ake a layi yanzu kuwa an dawo masu zaginma sai shige min suke yi. Jamila tace to ai shigewar ta munafirci ce, in kin yarda, ɗazu da Umma tace in amshi rariyar da Umman su Nabila suka ara a gidan na samu Umman su Fati mai awwara,tun daga soro naji suna cewa wai ba'a san asalin Yaya Aliyu ba,babu bincike daga zuwa an ɗau yarinya za a bashi. Wai ƙilama ba ɗan ƙasa bane ƙarshe sai kin tara 'ya'ya ya gudu ya barki. Umman Fati ce da wannan dogon jawabin. Umman Nabila kuwa tace su suka sani dubi uban kayan lefe gashi sun saka aure da gaggawa kamar suna da wata tsiya ma ji ma gani dai mu 'yan rakiya ne har gidan ango muga abinda zasu kai mata." Nace Muna fukai ina son mijina haka, ko daga sama ya faɗo, kinsa Allah da nice naje sai na zage su, nifa Jamila akan Aliyu iyayena ne kawai suka fimin shi sai ku ƙanne na. Jamila tace shiga nayi da sallama sai suka hau borin kunya na amso na dawo ko Umma ban faɗa mata ba. Nace Yawwa gara kar ki faɗa mata dama, cikin damuwa take. Ai basu kaɗaiba ko gidansu Zuhra da suke 'yan uwanmu ai suna nuna baƙin cikin su. Kuma suma suna munafircin Yaya Aliyu na maganar bincike shiyasa ban so aka ƙara sati ɗayan nan ba wallahi. Domin gani nake wani zai iya zuga su Umma su ce sun fasa bashi ni. Jamila ta ja tsaki ta kwanta tare da faɗin ni fatana Allah ya sa yana miki irin son da ki ke masa." Nace yanzu har Kinji haushi kenan? Ta ce "Zakewar taki ce tana yawa, kuma kisan Allah Umma da Abba abin yana basu takaici kyazo kija wa kanki suce sun fasa mugani ko zaki bishi ba aure. Na ɗora kaina a gadon bayanta ina faɗin bazan bishi ba Jamila, amma na tabbatar zan mutu. Dakin yayi tsit Jamila haushi ya hana ta bani amsa. Ni kuma na faɗa tunani wai ace an fasa. Da sauri naga Jamila ta tashi zaune tasa hannu biyu ta tallafi fuskata wai ashe hawayena ne suke sauka a gefen cikinta. Tace Kuka ki ke Yaya Baby, me akayi na kuka?" Na sauke ajiyar zuciya cikin rawar murya nace wallahi ban sani ba Jamila, amma na samu kaina a matsananci son Yaya Aliyu iya tunanin sa in na zurfafa sai na yi wannan kukan. Kuma na kasa gane dalili. Kimin fatan Allah ya sa shima yana sona. Jamila ta shiga lallashina tana share min hawaye tana faɗa min cewa tabbas ya na sona, kuma aure babu fashi kuma za a yi komai cikin rufin asiri. Muka kwanta cikin saƙe saƙen zukata. Sai Muryar Abba muka ji yace "Ke Baby zo nan.'.. Muka tashi da sauri zaune nace Jamila me yafaru? Ta yarfa hannuwa alamun bata sani ba. Jikina ya soma ɓari, na ce kodai ya ji zantukamu ko kuma wasu sun shigo shi akan maganar binciken Aliyu ya fasa aura min shi. "Ina ki ke?" Muryar shi ta ƙara ratsowa. Jamila cikin sauri tace kije mana amma komai zai ce ki yi shiru. Na miƙe na fita yana zaune kan tabarma inda sukan zauna da Umma.
Shamaki ya buɗe flas ɗin abinci ya soma zuba farar shinkafa, idanun Hajiya suna kansa har ya gama sannan ya zauna ya fara ci yana son tuno wane labari ne Hajiyar ta fi maida hankali sosai. Kodai labarin mahaifin su,ko kuma dai labarin kasuwancin su daidai lokacin wayar shi ta soma ruri, ya kalla Soyayyata . Ya ɗago ido ya kalli Hajiya ta tsare shi da kallon tuhuma dole ya yi wayar a gabanta domin fidda kansa. Ya yi ɗan murmushi bayan ya gama wayar ya tauna abincin da ya zuba a bakinsa zai yi magana,sai ta ɗaga masa hannu, gama cin abinci, ka fi kowa sanin cewa bana son ana magana lokacin cin abinci, ka gama sai kamin bayani kamar haka..
Duk saboda son yarinyar ne ka soma munafurta ta har ka shirya zama da 'yan uwanka saboda ni? Sannan ka ciro min fayal ɗin da kake ɓoyewa da hannunka har kana zubar da su dan kawai in rasa gane wanene ka aje gefe. Sannan ka min bayanin dalilin yin duk wannan alamun na rashin gaskiya da kake yi tun da ka shigo gida, kuma ka faɗa min da wa ka yi waya da ka shiga ɗaki! Cokalin da ke hannun Shamaki ya faɗi abincin ya zube masa a riga. Yawun bakinsa ya ƙafe sannan ya tsaida idanun sa akan Hajiya cikin tsananin firgici.
🖊️🖊️🖊
️*HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 12*
Na isa gaban Abba cikin tsoro na zauna, duk jikina babu inda baya rawa, ina da tabbacin da "Abba zai ce an fasa ba Yaya Aliyu ni, bana ko shakka zan iya faɗuwa a gurin sumammiya. Sai naji ya tausasa murya ya ce "Baby" Cikin rawar murya na ce na'amm Abba. Yace "Kina ganin baki da wata damuwa in har aka ɗaura auren nan aka kai ki gidan yaron nan a haka babu kaya ko kuwa kina ga akwai wata damuwa in roƙe shi ya ɗan ƙara mana lokaci muga abinda Allah zai yi?" Na sauke wata wawiyar ajiyar zuciya. Sannan nace Abba ba ni da wata damuwa akan haka, ai munyi maganar da shi ya ce ai duk al'ada ce, kuma ya ce min zai siya in ya samu kuɗi. Abba ya daka min tsawa "Ke! ni ban tambaye ki dogon labari ba, abin da na tambaye ki kawai shine, zaki zauna da mijinki lafiya ko da ba mu samu munyi miki kayan ɗaki ba?" Zan zauna. Na bashi amsa da sauri kamar ina jiran tambayar. Umma ta fito daga ɗaki tace Sannu Baban Babu nifa gaskiya bazan iya kai yarinyar nan gidan miji babu kayan ɗaki ba, kodai ka je ka ciyo ko bashi, ko kuma ka yarda muje ka saka hannu a wancan na tallafin a karɓo, baka da shi, to menene naka na yin girman kai? Abba ya miƙe "Salamatu" ya nuna Umma da yatsa cikin tsananin fushi wanda ban taɓa gani ba, yace ki shiga hankalin ki da ni, in ba haka ba kuma zan yi matuƙar baki mamaki domin zaki tafi gidanku ki haihu a can , ni kuma in aurar da 'yata cikin kwanciyar hankali. Jamila ta fito da sauri ta nufi gurin Umma ta riƙe mata hannu ta na cewa "Umma kiyi shiru: don Allah. Ni kuma kuka ne ya suɓuce min na kasa furta komai, saboda ni iyayena suna sa in sa abinda ban taɓa gani ba tunda na ta so. Kamata ya yi ince su yi haƙuri na fasa auren ma gaba daya, amma yadda nake ji koda tafiya Umman zata yi ba zan iya furta hakan ba, shin dama haka son yake ? Da numfashi yake kamar wani bala'i ko kuwa nawa son ne ya zo a haka? Muryar Umma ta katseni. Lallai Abubakar Allah ya kawo mu lokacin zaka faɗi haka tsakanin ni da kai, to ni kuma da inga aure nan a haka gara ayin bana gidan nan, na yarda da haka. Amma in ka tashi ka bani saki uku ras yadda ba sai na dawo ba.. Da sauri nace Umma kuyi haƙuri saboda ni ba zaku rabu ba. Ni gaba ɗaya ma na fasa au! au!! Sai na samu kaina da kokowa da numfashi na matsawar na furta kalmar zan iya mutuwa. Jina nayi na kai ƙasa ina wani irin numfashi, ina ta kuma ƙoƙarain furta na fasa auren kuma ina jin salatin iyayena kamar daga can nesa, sannan ga muryar Jamila
0 comments:
Post a Comment