️Ya ce "Kamar yaya kenan? Nace ashe ina ta magana da ƙarfi maimakon ka faɗa min sai ka ci gaba da sauraron a haka sai da Hajiya ta nusar da ni a yau, don Allah ka yi haƙuri, kuma daga yau na saukar da muryata ni ma. Nayi ya yi shiru, can ya ce. "Karki takura kanki zuwa yanzu ni na saba da maganar ki." Ya canza maganar da faɗin "Fatan ki na cikin ƙoshin lafiya."
Nace lafiya lau ya kasuwa? Allah ya taimaka. Yace "Ameen.
To yauma rana ta uku haka na fuska sai ƙarfe shabiyu ya shigo, ni kuma na yi kwanciya ta na kulle ɗaki, banji bugun sa ba sam. Ban farka ba sai kiran sallar asuba, da na farka na ganni a ɗakina take naji fargaba, ko yaya wannan bawan Allahn zai ɗauki bin oho. Cikin sauri na ɗakko wayata na duba bai kira ni ba, na shiga banɗaki na yi alwala na fito naji ana ƙwanƙwasa min ƙofa. Da sauri naje na buɗe, shine a tsaye zashi massalaci yace " Ashe kin tashi ma toshi kenan na tafi masallaci." Babu wata alama ta damuwa data nuna a fuskar sa. Nace to, dama ka yi ta kirana ne baccin ne mai nauyi banji ba. Ya yi murmushi "Kada ki damu, ban kira wayarki ba ma,saboda zata tashe ki bacci kuma kinga kanki zai yi ciwo yanzu kije ki yi salla nima kada in makara.
Na idar da salla na zauna kan sallaya ina tunanin ta ina zan ɓullowa wannan al'amari. Yanzu ma nasan sai zai tafi kasuwa zai shigo ya shirya.
Na ɗakko ƙur'ani na zauna ina ta karatu har ƙarfe bakwai, na tashi da sake wani salon dabarar na shiga na fesa wanka na gyara fuska ta na zuba kwalliya na saka Atamfa doguwar riga na ɗaura ɗankwani bayan na saki gashina a kafaɗa. Na fesa turaruka mayafi na yafa kamar mai zuwa unguwa na nufi gaida Hajiya. Suna zaune kamar kullum suna zantuka ƙasa-ƙasa.
Nayi sallama can ƙasan maƙogwaro suka amsa na durƙusa na gaida Hajiya ta amsa fuska a sake, sannan na juya na gaida shi ya amsa yana ta kallona, na ɗan zauna jim,sai na dubi Hajiya zan iya zuwa in taya su Juma aiki? Duk suka Kalle ni, ya kalli Hajiya da sauri. Tace "Menene dalilin ki na so shiga kuxin?" Na ƙasa ƙasa da murya, dama dai ina son in koyi wasu abubuwanne waɗanda ban taɓa ya ba. Tace "To sai ki rubuto min abinda baki iya ɗinba kinga sai in sa a koya miki."
Na koma gefe na zauna ina kallon su,sai satar kallona ya ke yi da mun haɗa ido sai ya faki idon Hajiya ja ɗaga min gira. Can Hajiya tace. "Kinga tashi jeki iciki kin raba mana hankali muna magana. Na yi mata sallama cikin ladabi sannan na tafi.
Ina ta kai kawo a cikin ɗaki ina neman shawarar da zan yanke. Hajiya bazata yarda in zauna kusa da su ba kuma bazata bari in raɓi su Juma ba,ga mijina munyi nesa dole dai in samawa kaina farin ciki na nufi gefen sa ma jiya Rahin da yara ana shirin makaranta,na zarce gurinsu. Ta taga na ke kallon yadda suke shirin, sai na shiga na ƙara gyara musu. Mubina tace "Momy saboda ke momy ce shine ki ke saka mana kayanmu?" Nace e mana ai ita Momy ta son taga yaranta sunyi kyau sosai sun fi kowane yara. Meema tace Zainab ƙawata tace su Momynsu ta ke yi musu Homework mu kuma sai dai Anty lesson take mana. Nace wacece kuma Anty Lesson Rahin ta ce wadda ke zuwa gida tana ƙara musu karatu. Nace au, to ina kuma Azima ta ke? Rahin ta nuna min ɗayan dakin da hannu ta ce ita ga ɗakinta can.
Na tashi na nufi ɗakin tana zaune bakin gadon ta tana saka safa, ɗakine sosai irin na mace da komai a ciki. Ta bini da kallo nima dai ita nike kallo zancan gaskiya kuma yarinyar tana da kyau sosai. Nace Azima baki zo ɗakina ba Ni gashi na zo naki, ko bakya son mu saba ne? Taɗan taɓa baki. "Ni bana da ra'ayin sabawa da kowa sai Hajiya kawai." Nace haka ne. Ni kuma nafi sabawa da Shamaki. Ta kalleni da sauri sai kuma ta sunkuyar da kai ta ci gaba da abinda take yi. Nace bari in tafi,in kin dawo zaki zo ɗakina? Tagirgiza kai tare da furta 'a'a.
Na tafi ina mamakin 'yar ƙaramar yarinya ta iya kishi haka. Ɗakinsa na koma na shiga gyarawa har na gama bai zo ba, na fito Juma ta dawo daga kai min abinci nace a kawo turaren gefena tace to, har zan tafi sai nace bari injirata domin inyi amfani da damar in ji wani abu a gurin Juma.
Ta kawo turare, ta ake zata tafi, nace ni ko Baba Juma dan Allah ina da tambaya, sai naga ta juya da sauri tamkar bata jini ba. Na cika da mamaki na kama hanya na yi ɗakina. Kaina gaba ɗaya ya kulle,sai naji an ƙwaƙwasa ƙofa, ina buɗewa sai naga Juma da turaren gefena tace ai 'yannan na jiki ɗazu kiyi hankali ba ko ina ake magana a gidan nan ba domin cike yake da kyamarori. Na zaro ido tace zan samu wani dalili da zan shigo ɗakin baccin ki a ciki ne ba a saka kyamara. Bata jira jin me zance ba ta wuce.
Na koma na zauna daɓas akan kujera, ina tunanin wace irin kyamara, a zuciyarsa nace ƙila irin ta gidan Ya Umar Soja wadda ya sawa Asmy a littafin da na taɓa karantawa na fuska biyu. Ashe dai akwai shi a gaske kenan. To in Yaya Umar Faruk ya saka wa Asmy kyamara domin ya ga abinda take yi in baya nan ko tsoron karya na ƙarta kawo masa namiji gida su kuma nan gidan saboda me suka saka? Dole akwai buƙatar in shiga taitayina sosai, tunda shi kanshi da yake iƙrarin sona bai sanar da ni cewa in kula akwai kyamara ba.
Laf na yi a cikin ɗaki a saman gadona, hatta karin na kasa yi, can naji an buɗe ƙofar falona an shigo. Nasan shine domin naji ƙamahinsa. Na tashi zaune yace "Wai har an yaye ni ne?" Nace kamar yaya? Yace baza a zaɓa min kayan ba? Nace to ai kai nake jira, ga mamakina sai yace "To ba sai a ciro a ajiye min ba tunda an gyara min ɗakin." Na miƙe to muje in baka. Ya kamoni zuwa jikinsa, yace "Baby sai inga kamar kina guduna ne, jiya ki ka ƙi zuwa ɗakin mijin ki." Nace Barci ne ya kwashe ni. Ya ɗago fuskata ya haɗa tsinin hancinmu yace "Ba sai kije can ki yi bacci ba?" Na kumshe ido nace yau zan yi haka.
A ɗakinsa duk da nayi wanka sai da muka sake yi tare domin sai da ya ja dalilin haka, gaskiya na yarda da son da yake min domin ya nuna min zallar hakan sannan ya iya tafiyar da mace cikin sati ɗaya na amarci bani da bakin magana. Damuwata shine ƙaranci lokacin da muke yi da shi. Duk dare sai nayi bacci yake shigowa, ba bu haduwar asbashi, sai da safe kurum muke soyayyar da bata fi ta minti talaatin ko arba'in ba. Ba hira sam, Lokaci dai da zamu zauna mu yi hira babu shi, ko ya fita kasuwa sai dai in masa text na miƙa gaisuwa amma fa in na jiraci amsa to ni ce zanji haushi, ɗan lokacin da ya kan samu ya kira ni ma ba kullum ba.
Ranar da na cika kwana goma sai na tashi da mura da zai fita ya sanar da Hajiya. Tace assha sai an kira likita ne ko kokuwa dai akai mata magani?Yace Ina ganin kawai akai mata magani tunda ta yi aiki ma. Hajiya tace Allah ya sawaƙa.
Ina kwance akan gado naji sallamar Juma nace ta shigo ciki, ta kawo min magani muta tace "Hajiya tace ayi miji sannu." Nace ina amsawa. Tace to tace ayi miki sannu in kinji ba wani sauƙi sai a kira likita. Nace ba komai.
Tace kwanaki kin ce zaki tambaye ni wani abu." Nace e ta ce "To ga shawara duk wani bayani da za ki so ji in kin kwantar da hankalinki zaki same shi, amma in kin fi son ki tambaye ni to kina iya tambaya amma zance ka iya tasowa in faɗawa Hajiya cewa kin tambaye ni abu kaza, bansanta ba amma hakan ka iya shafar jarabawarki. Ta ƙara matsawa kusa ba a banza ki ka ga na kwashe shekaru a gidannan ba, 'yar amanar gidance dan na yaba da halinki ba shine zai sa in zaɓe ki in buɗe musu sirri ba. Na ɗan taɓaki ne domin ku lura da zaman gidan ba wai domin ni da ke mu zama munafukan Hajiya ba." Tuni na yi mutuwar zaune, amma sai na dake nace, Allah sarki Baba Juma waccan ranar dama zan tambaye ki ne ko zan iya zuwa kicin inke tayaku aiki saboda in koyi wanda ban iya ba, to kuma na riga ma na tambayi Hajiya tace in rubuta abinda zan koya sai ta sa a koya min. Juma ta ce "Allah Sarki to ai Hajiya baza ta yarda ki shiga kicin ba, domin Hajiya bata yarda ɗanta ya ci abincin wata matarsa ba. Amfanin ki ɗaya ki biya wa ɗanta buƙata ki haifa masa 'ya'ya. Na danne tsoron da ya taso min nace, to ita matar aure ai bata da yadda zata yi sai abinda mijinta yace. Juma ta juya ta ce ashe dai kin gano." Na bi bayanta da kallo a fili nace akwai aiki.
.....
Na koma na kwanta ina tunani, kullum in na kalli sauƙi ta nan sai ya zama tsuri, na tabbatar wa kai na Juma tana sanar da ni ne cewar bata da sirri sam. Ga gida cike da na'urorin ɗaukar hoto. Yawata ta soma ruri, na duba lambar Umma ce, na ɗaga Jamila ce, cikin rawar murya ta ce Yaya Baby Umma ba lafiya gamu zamu tafi asibiti haihuwa ce tun jiya jini ne ya ɓalle mata da sauri na diro daga gado ina faɗin wane Asibitin ne gani nan zuwa. Tace Murtala zamuje. Da gudu na ja hijabi na saka na sa takalmi har na fita daga falo sai wata zuciyar ta tambaye ni da cewa,kin tambayi mijinki? Na ciri wayar a jaka na yita kiran wayarsa amma bai ɗaga ba. Na nufi gurin Hajiya na tsugunna a gaban ta idanuna sun ciko da hawaye. Tace "Jikin ne?" Nace a a ko maganin ban kai ga sha ba, aka kira Ni daga gida Ummanmu za akai asibiti jini ya ɓalle mata. Tace Ya Salam! To yanzu ya akayi? Nace zanje ne. Tace kin faɗawa mijinki? Na dubeta bai ɗauki wayata ba. Tace to kiyi haƙuri ki koma har sai kin samu izni daga gare shi. Na sake rusunawa nace Hajiya ko ku zaku kirashi wallahi bata cikin hayyacita. Hajiya tace "Samu nutsuwa mana Rabi'atu, ki koma ɗakinki ki jira mijinki ya dawo ko ya ɗaga wayarki, ko kinje baki da wani taimako da zaki iya yi mata bayan addu'a ki koma ciki ki yi mata.
Na miƙe a hankali hawaye suna tsiyaya daga idanuna, na nufi ciki a hankali kamar kazar da ƙwai ya fashe mata na nufi sashe na.
Ina shiga na cire hijabi kaina nayi jifa dashi na na zube nan a ƙasa ina rera sabon kuka tare da kiran dukkan layukan Shamaki amma babu wanda ya ɗaga. Na kira wayar Umma itama Jamilan bata ɗaga ba. Na kira ta Abba shima sai a kira na uku ya ɗauka, cikin kuka nace Abba ta haihu? Yace "Kash waya faɗa miki ba na hana kowa ya sanar da ke ba!" Nace Abba saboda me? Yazun ma saboda baya nan ne shiyasa ban taho ba,amma ya jikin nata? Yace "To a ci gaba da addu'a sun dai shiga da ita ciki har yanzu ba su fito sun ce mana komai ba, sai faɗa suke wai anbarta a gida ta galabaita. Su kuma kowa yasan cewa in ba kuɗi baza su taɓa taɓa mara lafiya ina ta buga bugar neman kuɗinne bansamu na kirki ba gara a gurinta an samu dubu tara."
Nace Abba ka turo Jamila ina da dubu goma ta kawo maka su. Yace "Ina ki ka samu karfa kice zaki taɓa kuɗin mijinki." Nace nawa ne abokan sa suka bani Jamilan ma tasan ina da kuɗin tunda agaban su ne aka bani.
Yace "To zan turo ta yanzu daga nan Asibitin Murtala sannan karki sake ki fito ba tare da sanin mijinki ba." na. Cikin kuka nace to Abba.
Muna aje waya na ɗora sabon kuka ina addu'a. Kamar minti arba'in sai wata wayar tarho da ke maƙale jiki bangon ɗakina kusa da gado ta shiga tsuwa, ni har na tsorata zan fita da gudu na jiyo tsuwa a ɗakin bacci tunda ban taɓa ji ba. Na leƙa na kalli inda nake jin ƙarar sai naga ashe gurin wayar ne, naje na ciro na saka a kunne, muryar Hajiya naji tana cewa "Kece ki ke da baƙuwa a gate? Nace e ni ce ƙanwata ce Jamila. Tace koma waye ba ƙanwarki ba, kamata ya yi ki sanar a faɗawa mutanen da ke gate in ba haka ba baza su barta ta shigo ba.
Cikin dasashiyar muryar da na sha kuka nace zan kiyaye gaba insha Allahu Hajiya tace shike nan. Jamila tana shigowa muka rungume juna muka ɗora sabon kuka,kunsan minti uku sannan na lallasheta na ɗakko kuɗin na bata, nace su da waye a asibitin tace Umman Amina ce da Umman su Zuhra, sai Abba.
Na rakota zuwa falon Hajiya ta yi wa Hajiya sallama Hajiya tace "Har zata wuce to kin bata ruwa ta sha kuwa?" Nace na shafa'a sauri take daga asibiti ta ke. Jamila na fita zan juya Hajiya tace "To me tazo yi kenan haka?" Nace saƙo na bata. Tace "Amma banga komai a hannun ta ba?" Har zan ɓoye sai na tuna da maganar Juma da ta Shamaki, game da faɗan gaskiya, sai nace kuɗi ne na bata zata kai wa .Abbanmu asibiti. "Ina kika same su?" Ta jeho min tambaya da sauri. Nace abokan shi suka bani ranar da aka kawo ni. Tace "Kin ce abokan shi, shi wa?" Na fara gajiya da tambayoyin ga halin da nake ciki sai na soma hawaye cikin rawar murya nace Shamaki. Ɗa gyaɗa kai tare da faɗin "To na gane, shi kuma kukan na menene?" Na share hawaye tare da girgiza kai nace ba komai. Ta maida kallon ta ga TV na wuce ciki zuciyata fal da takaici.
Haka azahar da la'asar suka riske ni a gurin ba wani labari a halin na faɗawa Jamila zan ke kira ina samun labarin halin da Umma take ciki amma kona kira bata ɗagawa. Shima Abba shiru, shikuwa mijina fushi ma nayi ban ƙara gwada wa ba. Addu'o'in dai ba irin wadda bana yi.
Sautin wayata ya sa na tashi da gudu na nufi ɗalkota ina dubawa Shamaki ne, na zauna a ƙasa ina kallon wayar harta yanke, ya sake kira har lokacin ban ɗaga ba. Gani nake babu wani amfani ko na ɗaga. Karan da wayar ta addabe ni da shi ya ci gaba da kirai shi ya sa dole na ɗaga amma ban iya magana ba na kara a kunne Yace "Baby Ina meeting a Abuja lokacin da ki ka kirani yanzu ina filin jirgi nan da minti talatin ina Kano me ya faru?" Na saki sabon kuka, cikin muryar da na yi kuka na gaji nace Umma ta mutu ina ta kiranka baka ɗaga ba ƙilama yanzu an kaita. Yace "Wace Umma?" Nace Ummanmu na kashe wayar na ɗora sabon kuka.Ni na gama yanke wa tunda suka ƙi ɗaga wayata bashakka Umma ta mutu na rasa ta har abada.
Shamaki ya yi tsam a filin jirgi ya ɗaga waya ya kira Number Abba. Abba ya ɗaga Shamaki ya gaida shi cikin girmamawa, sannan yace "Yarinyar nan ce ta kira ni tana min kuka
"Wai da gaske ne Allah ya yi wa Umma Rasuwa?" Abba yace Baby akwai ruɗaɗɗiyar yarinya, shiyasa ban so Jamila ta faɗa mata ba. Kuma shine dalilin da ya sa nace karsu ɗaga kiranta.Ummansu addu'a take buƙata, bata rasu ba yanzu dai sun ce mu tafi asibitin Malam Aminu Kano. Aiki ne za'ayi mata. Shamaki yace Abba ina ganin ku tafi asibitin Zeena Hospital zan sanar da likitan kafin kuje ya ɓuɗe mata fayal.
Abba yace alhamdulillah na gode Aliyu Allah ya sa a mizani. Yace ba komai sai munzo asibitin.
Ban kuma ji daga kowa ba har magariba.In
Kwance inda nayi salla. Juma ta shigo da abinci ta ga na rana yana nan. Tace "yannan ki daure ki ɗan taɓa mana." Nace Baba Juma karki aje haɗa duka bazan iya ci ba. Tace "Banga laifin ki ba yarnan Uwa ta wuce wasa. Kuyi addu'a Allah ya fisshe ta. Nace Ameen. Yau ce ranar farko da na ganshi ya shigo a irin wannan lokacin.
Ban Ko ɗago ba bare in dune shi. Ya tsugunna a gaba ya sa hannu ya ɗago ni fuska ta ta yi suntum yace "Subhanallah Baby kinga fuskar ki kuwa? Na soma sabon kuka ya rungume ni ki samu natsuwa, ki shirya muje Asibitin mu duba ta. Nace bata mutu ba?
Yace ta samu sauƙi muje
ki tabbatar Na tashi da sauri na shiga ciki na wanko fuska na saka Hijabi yace "A' a ki canza shiga mai kyau, sannan ki ci wani abu naji tace haka ki ka yini.
Nace zan canza shigar amma abinci kam ka min afwa sai na ga jikin.
A falon Hajiya mun rusuna ya sanar da ita cewa mun fito. Tace Juma ta haɗa abincin da za'a kai asibitin.
Muka fita tana cewa mu yi mata sannu.
Muna baya Bala direba ya na jan mota muna baya ya sarƙe
hannuwanshi cikin nawa har muka kai Zeena Hospital. Nace
ba Murtala aka ce ba ? Yace "Ƙila daga can aka turo su nan." Muka shiga ni dai da kyar nake cire ƙafa, ban damu da gaisuwar girmamawar da Nurse ɗin ke yiwa Shamaki in mun haɗu da su jifa jifa ba. Ya kira yaawar wani yana tambayar sa da turanci lambar ɗakin. Ya faɗa masa har mun ɗan wuce sai muka dawo baya. Abba na zaune bakin gadon da Umma ke bacci ya riƙe mata hannu da ake yi mata ƙarin jini.Kan tabarma kuma Jamila ce da Umman su Amina.
Da sauri naje na riƙe mata hannu Abba ya ce ai bata farka ba ,bayan anyi aikin. Na dubi Abba da sauri nace wai dama aiki aka mata. Ya ce "aiki aka yi mata 'yan ta wahala kukan ta ɗaya da aka ciro ta ta koma ga Allah." Allahu akbar, ina take Abba. Yace "An rufe ta ɗazu nan kafin magriba ita kuma sai mu yi fata Allah ya bata lafiya." Muka amsa Shamaki suka gaida da Abba ya masa ya maijiki daga nan yace zaije ya duba wani ya dawo,ya fita .
Abba ya ce ki bi mijinki sau da ƙafa dubi abinda ya yi mana banda shi da sai dai Ummanku ta mutu domin bani da kuɗin da za a yi mata aiki. Na dubi Abba shine ya biya? Abba yace komai da komai. Bala direba ya shigo da kayan abinci Jamila ta amsa ta na yi masa sannu, suka gaida da Abba ya tambayi mai jiki sannan ya fita. Shamaki suka shigo da likitan na gaida shi. Likitan ya yi bayanin cewa saura minti arba'in ta farka anyi aikin cikin nasara kuma zata tashi lafiya lau. Sai yanzu na haɗiye wani tarin abu da ya maƙale min a wuya. A fili na furta Alhamdulillah yace da ta farka kar su bata komai su sanar da shi.
Shamaki yace zamu tafi sai kuma gobe zamu sake zuwa. Nace ya barni in kwana,wata tsawa da Abba ya buga min bansan lokacin da a nayi waje da sauri ba.
Muna zuwa gurin mota Sahamaki ya ba Malam Bala kuɗi yace ya hau mashin ya wuce gida bari shi ya ja motar zamu biya unguwa ne.
Na koma gaba ya ja muka tafi. Kawai gari muka yi ta zaga wa muna hira yana ɗan Min wasanni, mushiga wannan Supar market yace in ɗauki abinda nake so har goman dare sannan muka nufi gida lokacin zuciyata ta yi sanyi ta cika da nishaɗi.
Muna shigowa Azima tana shafawa Hajiya maganin ƙafa duk suka bimu da kallo, na ajewa Hajiya ledar hannu na domin naga tana kallon ledar. Tace Menene? Shamaki ya ce turarene mun biya na sayi nawa ne shine na sai muku,ta sa albarka ta tambayi yana yi jiki muka ce da sauƙi. Nan da na barsu na tafi ɗakina. Na yi salloli sannan na shiga wanka na shirya na nufi ɗakin mijina.
Washe gari da safe da ya shigo daga gurin Hajiya zai yi shirin kasuwa nace zaka sa a kai ni asibiti ne ko in zaka kasuwa ne zaku sauke ni?
Yace jirana ake yi bazanbi ta can ba,amma game da naki zuwa ki tambayi Hajiya inta ce ki je zata sa a kai ki. Na yi sororo ina kallon sa kamar in ce Hajiya nake aure?Sai kuma na fasa na fita zuwa gurin Hajiyar irin tambaya tun yana gidan.
Na rusuna na sake yi mata sannu da hutawa, sannan nace Shamaki ne ya ce in tambaya ko zani asibiti? Jin shiru ya sa na ɗago na dube ta itama ni take kallo a zuciyata ta nace kema dai Uwa ce kinsan zafinta. Ga mamaki na sai baki tace ki je ki buga musu yawa kiji lafiyar ta, babu buƙatar zuwanki. Na rusunar da ƙwayar idanuna sannan na miƙe tare da furta to. Ɗakina na koma na zauna a kan gado na ɗora sabon kuka. Ina jin shigowar shi ban ko ɗago na kalleshi ba , ya zauna kusa da ni yana tambayar abinda ke faruwa. Nace ba komai. Yace "Hajiya ce ?" Nace 'A 'a . Ya miƙe tare da faɗin shike nan ni zan tafi kasuwa, na miƙe ina share hawaye na amshi jakar kamar kullum domin yi masa rakiya.
......
Na raka shi har falon ƙarshe ya amshi jakar ya ɗago fuskanta ki daina kuka ya kawo bakin shi kunne na ya raɗa min cewa zanbi ta asibitin zan kira ki in faɗa miki yadda jikin yake kinji?" Nace To kace cewa Umma don Allah ina son zuwa ban samu dama bane ina son in ganta kuma ina yi mata addu'a .
Wasu hawayen suka biyo kumatuna, ya sa hannu ya share yace "zan haɗaku da ita a waya. Nace to. Yace "Share hawayen ki" Nasa hannu na share sannan ya fita ni kuma na dawo, zan wuce nace cewa Hajiya sannu da hutawa. Ta amsa da "Yawwa."
Haka na koma ciki naci gaba da 'yan ayyuka na. Na gama na koma na kwanta . Gurin ƙarfe goma sai ga kiran shi na ɗaga. Yace gani a Asibiti jikin Umma ya yi kyau sosai ki je video call zan kira ku gaisa. Da rawar jiki na shiga video saiga Umma zaune tana min magana cikin murna na gaishe ta, nace ya jiki? Tace "Jikin da sauƙi Alhamdulillahi ya naki jiki?" Nace na samu sauƙi. Tace "Ki daina kuka akan sai kinzo tunda ba daɗin jikinki ki ke ji ba, sannan ki yi godiya gurin Hajiya surukarki muna ganin aiken abincin safe da yamma Allah ya ƙara ɗaukaka." Nace to zan faɗa mata, yanzu dai babu inda ya ke miki ciwo? Ta ce. " Babu inda ke min ciwo Baby ki kwantar da hankali ki, ki ƙaraiwa mijinki godiya ya taimaki rayuwata sosai." Nace To Umma. Muka yi sallama.
Naji daɗin ganin Umma ta sami sauƙi kuma ko da Hajiya ta hanani zuwa ashe tana aika musu da abinci, sannan bata hana mijina zuwa ba ya duba Umma ba.
Kwanan Umma uku a asibiti aka sallameta amma Hajiya bata barni na je ba, koda yake ban tambaya bane ina jin tsoro, da nace zanje sai ya ce in tambayi Hajiya. Ni kuma sai in yi shiru bana sake maganar , kuma ko a fuska bana nuna wata damuwa. Amma kira inna kira su sai munyi waya da kowa a gidan har su Jafar. Na dangana na zubawa sarautar Allah ido. Ranar da zata cika sati ɗaya da 'yar tana raye sai a ce ranar suna, 'yan Kurna za su zo da ƙawayen ta za'ayi ɗan taro. Jamila ce ta tsegunta min gaskiya ina son zuwa dan haka tun yau na rubuta mashi saƙo cewa ina son gobe zanje gida in duba Umma saboda za 'a yi ɗan taro.
Shina amsa ya aiko min da ita kamar kaka..." Ki je ki sanar da Hajiya." Na yi shiru cikin tagumi Hajiya ke aure na da komai zai ce in tambayi Hajiya. To shi mai zai hana ya tambayar min. Na danna kiranshi. Ya yanke ya kira ni. Na ɗaga. Nace ya kasuwa? Yace "Alhamdulillah" Nace dama zance ne ko zaka tambaya min Hajiya ɗin wallahi ni sai inke jin tsoro kar ta ga kamar na matsa mata.
Yace "Baby haka dokar gidan ta ke, ke zaki tambaya da kanki in taga ya dace shikenan zata barki, har yau baki fahimci Hajiya bane shiyasa ki ke jin tsoronta. Ki tashi yanzu kije ki same ta ki faɗa mata uzrin ki, in ta yarda shike nan." Nace To bari in gwada, mu kayi sallama.
Lokacin ƙarfe uku zata yi domin an yi azahar. Na sameta tana karatun wani ƙaramin littafin. Na durƙusa na gaisheta sannan na ce Hajiya dama ina son in tambaya ne ina son inje gida in duna Umma da jikin ta, goben ta ke kwana bakwai.
Ta ɗago kai ta ce za tayi taro kenan? Nace 'yan uwanta ne zasu taru. Ta yi shiru na ɗan lokaci sannan tace "Mijin ki zaki tambaya Ni menene nawa?" Nace ai na tambaye shi yace min duk abinda ki ka ce shi za'ayi. Ta sauke ajiyar zuciya "Kira min Juma." Da sauri na miƙe domin kiran Juma. Tare muka shigo, tace "Juma dubi yarinyar nan sosai ki gani ta canza daga yadda ta zo gidan nan Ni kullum juya iyau na ke ganinta?" Juma tace ta canza gaskiya ta murje ta yi haske Hajiya ai dole a canza kinsan hutu daban ya ke. Hajiya ta dube ni. "Jeki Allah ya kaimu goben zan duba in gani inzaki samu zuwa.
Na ce to, ko fuska ban canza ba har naje ɗaki. To ranar ma dai Shamaki bai dawo ba, daga can wai ya tafi Lagos sai text ɗinsa na gani, wai tafiyar gaggawa ce .Lamarin ya fara sani tunanin ko dai ba wani so da mutumin nan yake yi min. Bana samu wata kulawa da na ke buƙata in nayi la'akari da yadda na ke karantawa a littafai, ko 'yan unguwar mu da na kan ga sun fita da mazajen su irin da da dare haka suna ɗan zaga gari suna shan iska. Ni gani a kulle ba aikin fari ko na baƙi, bani da ko sisi sai dai inyi kallo in ci insha, ko hira mu yi da mijina ta gagara har yau bansan abinda ya fi so ba, shima bai san abin da na fi so ba ko wanda bana so ba .
Da safe bayan na gama komai naje na sake rusunawa gaban Hajiya nace dama na zo ne inji ko in shirya? Ta dube ni, "Kin faɗawa mijinki? ". Nace tun jiya yace in kin amince sai inje. Ta ce to yau kun gaisa da shi?" Nace 'A 'a, da sauri tace "To saboda me mijinki baya gari amma baki kira shi ba?" Na daburce nace na kira bai ɗaga bane shine na aika mishi saƙo. Tace "Karantamin saƙon inji." A zuciya ta nace iko sai Allah. Na ɗauki wayar na fara karantawa.
Fatan ka tashi lafiya,na kira ka baka ɗaga ba,nasan kana cikin uzri dama dai zan gaishe ka ne, fatan zaka dawo lafiya Allah ya bada abinda aka je nema.
Ta dube ni tace "Ameen" Kin kyauta sosai ki yi ta yi wa mijinki addu'a, sai dai ba irin ɗan sunan nan na ku na zamani yadda zai ɗanji sanyi da irin "yan kalamai haka masu daɗi? Na sunkuyar da kai. Hajiya dai son kanta ya kai inda ya kai.Na faɗa a zuciya, a fili kuma nace, zan gyara insha Allahu. Tace "Yawwa ai gara a gyara ɗin. Kije ki shirya sai direba ya kai ki, ƙarfe nawa zaki dawo?" Cike da murna nace duk lokacin da kika ce . Tace ki zama cikin shiri daga ƙarfe biyu zai koma ya ɗakko ki.
Ina fita falon na sheƙa da gudu ɗakina harda rawa ina ɗiban shoki tsabar murna. Na shirya tsaf cikin shigar Atamfa. Gaskiya na ɗan ciko komai nawa ya ɗan ƙaru.
Na fito falon Hajiya na zauna a gefe. Ta dube ni. "Antyn zumuɗi har a shirya kenan, to inga jakar me zaki kaiwa Ummar ta ƙi?" Nace miƙa mata tare da faɗin ba komai zandai je in ganta. Ga mamakina sai naga ta caje kakar sai 'yar hoda ta ce sai tissue. Ta miƙo min jakata. Sannan ta ce Haka" zaki gidan hannu rabbana?" Nace to ai Hajiya Ni bani da abinda zan ba su. Tace Ai abin kunya ne kina auren mai kuɗi kamar Shamaki amma kije gida hannu na dukan cinya haka, ba daɗi ai kyanshi ace kinje jakar nan cike da kuɗi duk wanda ya halarci taron sai ki bashi wani abu."
Take zuciyata ta faɗa min cewa Hajiya tana da wata manufa a maganar ta. Nace to ni kuwa Hajiya ina zan samu kuɗi har in yi hakan? Tace "Ga Mijin ki da kin kira shi sai ya tura miki ta account ku biya da direba ki cire."
Na sunkuyar da kai ina ta nazarin maganar Hajiya duk da cewa sak ta yi maganar kamar daga ranta, amma sai najii a jikina cewa Hajiya tana sane ba domin Allah ta yi wannan maganar ba.
Ta katse min tunani da cewa "Ki kira shi mana." Nace Hajiya ni ko account ɗin ma bani da shi,,kuma banda haka ma yaya za 'ayi yana irin wannan wahalar ko isasshen lokacin kansa baya da shi amma sai inkirashi ya bani kuɗi ba tausayi kenan, inda ace haka ake yi Hajiya da ba'a kawo haka ba. Mu gode da irin ɗawainiya ta kai abinci Allah ya saka a mizani, suma suna ta godiya su Umma da Abban. Ta zura min ido,can tace shike nan ki shiga ɗaki na zakiga wata leda a saman gado na ki ɗakko min." Nace to, na miƙe ita kuma ta ɗauki waya tana kiran layin direba.
Yau ne ranar farko da na fara shiga ɗakin baccin Hajiya, wani mugun ƙamshi ya bugi hancina. Sai dai ban tsaya kallo komai ba, domin ina tsoron ko akwai kyamara.. Amma fa ɗaki ne na alfarma. Na durƙusa na miƙa mata nace gashi.
Tace "To tunda kinƙi tambayar shi ni ga tawa gudummawar nan ki bata Allah bata lafiya. Na faɗa miki tun daga ƙarfe biyu sai ki shirya ki jira zuwan direba kar yazo a barshi yana ta jira." Nace sanyi duk yadda ki ka ce Allah ya saka da alkhari.
Na fito tasa Juma ta ɗauki ledar ta kai mota sannan na fita,sai da na tabbatar gani zaune a mota sannan na kira Jamila ta wayar Umma nace gani a hanya. Sai naji ta kwashi ihu da murna na kashe wayar na jefa a jaka,,sannan na buɗe ledar inga abinda ke ciki. Turmin atamfa guda biyu, sai wata farar Envelope na buɗe kuɗi ne 'yan ɗari biyu rafa ɗaya. Tabbas zargina ya tabbata Hajiya latsa ni ta yi .
Tabbas sai na zama mai kula domin na fuskanci Hajiya ta iya latsin basira.
A bakin lungun gidanmu ya tsaya, ya fito ya bude min ƙofa, sannan na fito ya amshi ledar ya biyo ni.
Kamar na taka da gudu in isa gida haka babu,amma sai na tafi sannu saboda direba da ke biye da ni cikin girmamawa.
Na amshi ledar na yi masa godiya sannan na shiga da sallama, kamar taron suna gida ya cika, ban ko tsaya amsa gaishe gaishe ba na nufi ɗakin Umma da gudu tana zaune a kan gado sanye da atamfar ankon bikina. Na zauna bakin gado na kama hannun ta ina sannu Umma. Sai fara'a ta ke yi tana kallo na. Na gaishe ta na tambayi jiki sannan na gaida sauran mutane. Sai faɗi ake yi amarya tubarkaalla. Umman Amina tace ya surukar ki kuwa? Ai mun taho muna hirar ta wannan mata tana da kirki kuwa? Na yi murmushi nace tana da kirki sosai kuwa. Na ɗakko laidar nace gashi ma tace a kawo wa Umma. Nanfa kuma aka shiga yaba mata.
Jamila ta kama hannu na muka shiga ɗakinmu na da muka zauna,tace "Yaya Baby wai don Allah kina da ciki ne?" Nace ke Jamila yaushe ki ka zama haka? Tace "Ba wai yaushe na zama haka bane, kinsan dai nice abokiyar shawara,nace bani da komai me ki ka gani? Tace "Kinyi kyau." Nace danma baya samun zama Jamila kinsan ko hira bamu taɓa yi ba,amma karki faɗawa Umma. Tace "Kamar yaya ko hira ba ya kwana a gidan kenan?" Na bata labari dai dai da fahimtar ta. Tace "To kinsan me za kiyi?" Nace 'a'a tace da rana kisha bacci da dare ki tashi ki dire ki ce bakya jin bacci shima ki tsare shi da hira."
Nace Gaskiya Jamila kina da kwanya, amma kuma zan tausaya mishi ai in har zaije da rana ya sha wahalar kasuwa dare kuma in hana shi ya huta. Tace Hajiyar ta rage mishi lokacin lissafin da ranar ko da daren mana.
.....
Nace Jamila kenan, zan gwada Allah ya sa dai kada hakan ya zama wata matsalar a gidan kinsan komai a gidan ɗan ƙa'ida ne.
Jamila tace "Ameen insha Allahu ba wata matsala, yanzu dai nasan za'a canza miki waya, ina riƙon taki, ko kiba ni 'yar dubu biyar in sai mai botura." Nace ina naga kuɗin da zan baki, kinsan Allah banda kuɗin nan da Baba ya aiko ki kika ki ka karɓa da sai in ce miki ni ban taɓa ganin takardar kuɗi a gidan nan ba. Shi kanshi ban taɓa ganin kuɗi wai yau gashi a hannun shi ba.
Jamila ta saki baki tana kallo na. "Dama duk kirarin kuɗin basu a zahiri kenan suna ɓoye a banki?" Nace to ƙila hakanne. Tace "Rannan wata 'yar Ajinmu tana labarin Gidan Hajiya Zeena da irin dukiyar da ke danƙare a gidan wai 'yan uwansu ne. Na ce mata ni yayata a gidan ta ke aure. Da farko ta ƙaryata wai Ɗan Alhaji Baita ba zai auri 'yar gidan mu ba. Shiru na yi mata sai da wasu 'yan ajinmu suka tabbatar mata shine ta yarda,tace gaskiya ta dangwalo, ance gidan suna da ɗakin kuɗi ko ƙananan yaran gidan sai dai su shiga su ɗiba, sannan Makka duk wata." Na kwashe da dariya nace kai mutane Allah ya kyauta. Jamila ta ce "Dama ni na musa wannan labarin amma ina kokwanto nace bari dai zan tambaye ki inji tunda na san dai ke yanzu kinsan komai." Na kauda zancan da faɗin, tashi ki rakani gidan su Zuhra mu gaisa da su.
Umman su Zuhra tace "A 'a ,ga fa amare muka gaisa ta tambayi Hajiya nace tana lafiya duk tace a gaida ku. Tace ai wannan mata daga gani zaki sha ɗani a gurin ta, sam mace ba rahma magana ma da kyar a ke yinta ita dole ga mai kuɗi." Nace la kuma Umma sauƙin kai ne da ita dan baki zauna da ita bane. Hajiya ba ruwanta wallahi. Ta taɓa baki, "To kenan mu ta wulaƙanta? Nace ta yi muku wani abu ba daidai ba ne? Tace "Koda yake ke kina rufe radda muka kai ki. Kallo ma bamu ishe ta ba, bare washe gari da muka koma." Nace ikon Allah ƙila dai ko mutane ne suka mata yawa kin san shi'anin taro. Haka dai na yi ta kare Hajiya domin ko iyayena bazan bari su ji sirrin zama na da Hajiya ba, kar in ɗaga musu hankali,ko kuma su zo suna jin haushin ta. Jamila ma sai da nayi mata kashedi domin kar ta faɗa.Na san kuma bazata faɗa ba.
Muka dawo ana ta raha duk wata budurwa ta lungun mu da taji labarin na zo sai ki ganta wai tazo mu gaisa. Kamar yadda Hajiya tace daga ƙarfe biyu in shirya haka na yi, ina yin azahar na shirya ina jira direba. Jamila tana ta mita wai maimakon in kai dare. Nace ana wanke tukunya dan tuwon gobe ne, bazai yiwu in wuce lokacin da aka bani ba. Da naga uku ta kusa na kira Hajiya na gaisheta cikin girmamawa na haɗa ta da Umma ta yi godiyar saƙo, sannan na tambaya ko direban ya iso. Tace "Aka ta aike shi ne in ya dawo zai zo.
Sai biyar da wani abu ya iso,muka kama hanya zuwa gida.
Umma dai citta da daddawa ta bani wai in kaiwa Hajiya. Na kai mata nace inji Ummanmu tace "To an gode jeki kaiwa Juma.
Na kai mata kicin ta ce amarsu ansha gida kin dawo da wuri ko Hajiyarmu ce ta baki lokaci? Na yi ɗan murmushi nace sai anjima. Tace kinga a nan babu wannan na'urar hakan yana ɗaya daga cikin abinda zai sa Hajiya ƙi ta barki ki zo nan ɗin. Nace kalle ta ban yi magana ba. Taci gaba da faɗin "Ko da yake jimawarki a nan shima abin tuhuma ne a gurin Hajiya. Na yi 'yar dariya nace Baba Juma kina da abin dariya wallahi. Tace 'yar nan da baƙin wayo ki ke, kin ƙi ki ɓara dan kar ince kin yi munafircin Hajiya ko? To sha mutumin ki, Hajiya bata amsar magana sai da hujja ba bugar cikin ki zanyi ba. Nace ni Bab Juma bana gane irin waɗannan zantukan. Tace "Ba wani bakya gane wa, daga ganin waɗannan wayayun idanuwan naki kar ki ke kallon kowa.
Ni dai na fice, zan nufi gefena. Hajiya tace "Basa cikine naga kin jima? Nace suna ciki munyi magana ne. Tace to madallah.
Ƙarfe sha biyun dare ina kwance a tafkeken gadon Shamaki ina ta ninƙaya, ina son in gwada hikimar Jamila ne in tsare shi da hira. Na ɗauki wayata ina shirin tura masa saƙo cewa yau dai ina jiransa hira na ke son mu yi.Sai kawai naga saƙonsa kamar haka.
"Baby ban samu dawowa ba ƙila ma ba gobe ba, amma zan sanar da ke in zan dawo. In kin kira ni baza ki same ni ba,amma ni zan kira ki a duk lokacin da na samu dama."
Na karanta na sake karantawa. A fili nace tofa! Ni wai dama wannan ne auren da mata ke cewa Allah ya kai su gidan hutu su yi aure su huta? Hummm gaskiya kam ina hutawa in dai bacci da cin abinci da nama shine hutu.
Na sauka a gadon na nufi ɗaki na na kwanta.
Ban sake ji daga mijina ba sai bayan kwana biyu ina zaune shiru zama ya ishe ni, na tashi na nufi sasan su Mubina, sai ina jiyo hayaniyar su a wani guri. Nabi hanyar sai na riski wani ɗan gurin shan iska da 'yar rumfar gargajiya, ga lilon yara sannan gurin akwai ni'imar bishiyu. Suna ta wasa can kan wata kujera Azima ce tana karanta wani littafi na Hausa. Nace Azima kuna nan kuna shan iska kenan? Ta ɗago ta lalle ni haka sama-sama tace "Umm." Ta maida kanta ga karatun. Na isa gurin su Meema nace ku daina wasa kuzo in koya muku karatu kuna s? Duk duka ce e, suka biyo ni nace muje ɗakin karatun ku inda Antynku ta lesson ta ke koya muku, ni na islamiyya zan muku.
Muna tsaka da karatu daga izifi biyu muka fara zuwa ƙasa. Sai waya ta tayi ƙara,na ɗaga da sauri ganin Shamaki ne. Na yi sallama na ce sannu. Ya amsa. Tare da faɗin Baby gaskiya ki samin suna kafin na dawo in kin ɗaga waya sai dai ki dinga wani kame kame abinda zaki kirani da shi. Nace to zan nemo amma ka taya ni mu zaɓa. Muka gaisa,yace "Abubuwa na sai kinyi haƙuri kinji?" Ina son ki fa Baby karki zata bana sonki." Nace nasani ,yace yanzu kina ina? Nace ina nan tare da yarana. Yace to haɗa ni da su." Na dubi Meema na ce ga Dady. Ta amshi wayar tana murna ta ce Dadynmu yaushe zaka dawo?" Yace "Duk lokacin da na gama abinda ke gabana zan dawo." Tace a kawo mana tsaraba.
Yace to ba mubina ita ma mu gaisa. Ta amsa tace Dady ga mu a gurin Momy muna yin karatun ƙur'ani Momy ta iya karatu mai daɗi. Yace to ku dage ku yi sosai zan kawo muku tsaraba." to zaka kawo wa Momy yace "E ita momy ai babbar tsaraba zan kawo mata sabuwar Baby kuna so?." Tace Muna so Dadi Ya ce "To ana Anisa ita ma." sun gaisa kafin daga bisani na amsa. Yace sannu Malama Baby Allah ya bada sa'a." Nace wai yaushe zaka dawo ne? Ni fa na.. sai na yi shiru,yace "Faɗa min kinyi me?" Kin ƙosa in dawo?" Na ce E "Kina kewata kenan?" Na ƙara ƙasa da murya nace E. Yace "To zaki daina jin kunya ki yi min duk abinda nace kimin ina so?" Nace amma banda ɗayan, cikin shagwaɓa na yi maganar. Yace "Wanne a ciki ne baki so?" Nace ba nace maka ina jin kyama ba?" Yace shikenan ni kuma shi nafi son shi.. zan koya miki amma ki daina jin kyama banda abinki Baby akwai wani abu da zai baki ƙyama a tare da ni? Nace ka ga akwai yara dama zaka kira anjima.
Yace "Yanzu na ɗan samu dama Baby. Nace to zanyi. Yace "Kin ɗauki alkawari? " Nace zan dai yi ƙoƙari in ga ko zan iya. Yace "To ki shirya na faɗa wa yara zan zo da tsarabar Babynmu sabuwar jaririya kin shirya?
Na ce Duk yadda Allah ya yi fatanmu dai mu samu masu albarka. Yace "Amin, to bari in barki ku yi karatun ku ko? Nace To Na gode.
Cikin dare ina bacci kiranshi ya tashe ni, a tsorace na ɗaga wayar" yace "Nasan kin yi bacci kuma na yi laifi na tashe ki, gobe zan dawo Baby a matse nike gida zan wuto don Allah ki shirya. Nace to ba damuwa. Da safe da naje gaida Hajiya nace mata gashin kaina ya yi datti ina son inje gurin wanke wa. Ta saki ɗan murmushi, "Mijinki zai dawo ko? To haka yana da kyau ina ki ke wanke wa?" Nace sai dai ko in yiwa Maman Iman magana wadda ke min a gida ne can Unguwar mu. Tace ba damuwa zan faɗa mata sai direba ya kai ki. Nace To. Na koma ɗaki ina mamaki.
Tun takwas aka ce in fito. Aka kai ni wanki kai aka min baƙin lalle zuwa sha ɗaya da rabi na zama tsaf,sai da na dawo na karya. Hajiya ta dama wani abu a cikin madarar shanu ta aiko min.
Cikin ikon Allah na shiga ban ɗaki zan yi alwala azahar sai ga baƙon mata ya riga shi zuwa. Na zaro ido.
kai tsaye gida ya nufo lokacin ƙarfe ɗaya dan haka ya aiko da kaya ya shiga Masallaci.
🖊️🖊️🖊️
Tamkar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki haka na koma. Falon Hajiya na nufa lokacin da Juma ta zo ta ce Hajiya tace a sanar da ni mijina ya dawo. Har zan ce ki ce ina yi masa sannu da zuwa sai na ji Juma ta yi wata magana, tace kema dai makar sauran ce a faɗa masa kina yi masa sannu da zuwa. Masa sannu da zuwa?" Nace 'a'a ina zuwa dai zaki ce Baba Juma, Yaya mijina zai dawo tafiya ta kwanaki a kira ni kuma in aika da saƙon sannu? Tace "Ashe dai kinsan kan ki. Ta fice wannan ɗin duk cikin jarabawa ce, ki na gani kamar ba gaske bane ko?" Bance komai ba ta fice. Na tashi Na je gaban madubi na dubi leshin jikina ya yi kyau, na shafa janbaki na ɗaura ɗan kwali na baza gashin zuwa kafaɗa ta tunda na san yana son gashin. Na fesa turaruka sannan na nufi falon Hajiya cikin taku irin na matar so. Ya na zube gaban Hajiya kamar zai mata sujjada nan kuma ga Juma nata fito da kaloln abinci, wani daɗi naji ya rufe ni da na ganshi, na nufeshi ina fara'a ina faɗin sannu da zuwa ka sha hanya. Ya zuba min idanu har na zo kusa da shi na tsugunna. Yace bazan amsa ba sai na ji sunan, na kalli Hajiya sannan na fara gaishe shi, ya amsa tare da kai hannu ya shafi gashina, na sake kallon Hajiya da sauri sai naga ita murmushi ma ta ke yi. Na zauna sannan nace ko in sa maka abincin ne? Yace "Da kin kyauta amma fara bani ruwa." Na buɗe murfin robar ruwan na cika tambulan na niƙa mishi, sannan na ce wane abinci zaka ci a ciki?" Ya dire kofin yace duk abinda ki ka ga ya dace Baby ni zanci." Na kuma kallo Hajiya yanzu kam idanuwan ta suna kan talabijin amma na tabbatar kunnan ta yana tare da mu.
Nace zan fi so ka zaɓa amma tunda ka bani zaɓi zance ka ci tuwo ƙila shine tunda kaje can baka ciba. Yace "Gaskiya banci tuwo ba, kuma yana cikin abincin da nake so. Na zuba masa komai da farfesun kaza sai zoɓo. Yana ci ina ɗan danna waya ta shi kuma yana satar kallo na da mun haɗa ido ya ɗaga min gira. Yace amma ke kinci abincin ko?" Nace sai anjima yana ɗaki. Ya yanko lomar tuwo da cokali ya nufo baki na, ki ci anan daga nan ɗakina zamuje ki ɗan matsa min jikina na gaji da yawa. Na kalli Hajiya har yanzu bata tare da mu a ido amma a kunne nasan tana ji. Na buɗe baki na amsa, sannan nace to ya isa haka ban jima da karyawa ba, kai dai ka ci sosai yanzu ka dawo daga tafiya.
Yace na ci da yawa, to ke ma ki ɗan ƙara ko so ɗaya ne, ya kuma miƙo min, na amsa nace. To na gode. Yace "Rama min za kiyi ki daina faɗin wani kin gode." Nace wannan mai sauƙi ne yana cikin aiki na da zaka bani dama in kullum ka ke son in baka abinci zan fi ka murna domin dai nice da ƙaruwar. Muryar Hajiya ta katse ni da faɗin "ƙaruwar me?" Na sunkuyar da kai nace Lada na ke nufi Hajiya. Ta kuma ɗauke kai. Na fara ba shi a baki ina satar kallon Hajiya, tamkar bata san muna gurin ba. Zan bashi Lemon zoɓo ya min cakulkuli na gantsare saura kaɗan in saki kofin cikin dariya nace zaka sani in saki kofin in yi ɓarna. Na je kusa da kunnan sa, nace ka bari Hajiya tana kallo fa. Yace "Hajiya wai kina kallo? Kin gani Mamanmu ce bazata hana mu yi wasa ba ko Hajiya?"
Ta dube shi. "Me ka ke cewa? Yace "Wai kunyarki ta ke ji." Ɗan tsaki ta yi sannan tace ku daina sani a shirmen ku ina kallon wani shiri ne a gidan Talabijin. Haka dai yana ta tsokana ta har muka gama, yace mu tafi ciki.
Har mun wuce Hajiya ta kirani, ta miƙamin wata ƙaramar ƙwalbar zuma mai kyau, tace "ki yi amfani da wannan. Kinsan ya ake yin amfani da shi? Na girgiza kai alamar 'a 'a. Tace "Ki sa auduga ki ɗiba sai ki yi matsai kamar minti biyu sai ki cire." Na.sunkuyar da kai dan kunya nace to.
A ɗaki ina shiga ya hau rawar jiki, nace akwai damuwa fa. Ya tsaya yana kallona nace bana salla. Ya ƙara jana jikinsa ya ce "Karki yi min haka bazan jure irin wannan wasan ba." Nace ba wasa bane bari in nuna maka. Yana gani na ga duk yanayin sa ya canza ransa a ɓace. Nace in akwai wani abu da zai sa ka samu nutsuwa zanyi maka. Yace ke da ki ke kyamata." Nace ai na bari. To haka dai ya sa nayi ta yi masa wasu abubuwa har sai da ya samu nutsuwa.
Duk abin da na ke faɗin ina ƙyamar dole na yi masa saboda ya bani tausayi.
Bacci ya kwashe mu sai kiran magriba ya tashe mu. Yace "Subhanallah! ba mu yi la'asar ba. Tare muka yi wanka muka yi la'asar sannan ya fita Masallaci.
Haka dai zaman ya ci gaba da tafiya duk wanda ya ganni abin sha'awa amma bani da ko ƙarfanfana jiki na ya yi lukui ƙamshi ya kama jikina saboda irin turarukan da Hajiya ta ke bani farko na zargi Hajiya ko kishi take yi da matan ɗanta har ta ke korar su, amma abin ɗaure kai shine, Hajiya bata da wani buri sai in yi abinda zai sa ɗanta ya ji daɗi. Da kanta take bani maganin mata, kitso da ƙunshi kuwa da ya fita zata sa a kuma yi min wani. Sannan kullum in na zo gaishe ta nasiharta shine in farantawa mijina rai kuma in masa biyayya, in jure duk yadda ya zo min domin in kare shi daga matan waje.
Abubuwan da take bani ina sha sun kai matsayin ni da kaina na ke ƙosawa mu yi auratayya da shi.
Haka nan zuwa yanzu duk wani abu da ya ke so na gama gogewa da iya su, har ma nakan tambaye shi ya 'akayi ya iya duk waɗannan abubuwan. Sai yace min koya ya yi shima a karance karance.
Kwatsam wata safiyar Lahadi baya fita kasuwa da wuri, yana falon Hajiya ni kuma ina gyaran sasan shi.
Sai naji ƙarar shigar saƙo a wayarshi na kalli wayar,, gargaɗin da aka min ya faɗo min, amma sai na watsar na ɗauka na janyo saman inna zan iya ganin saƙon sai naga ta Whatsapp ne, an turo Video ne kuma sunan sai naga an saka NFS.
Bansan dalili ba sai naji gabana ya faɗi, an yi min nasiha sosai akan waya kowa faɗa ya ke yi min in kiyayi wayar mijina. Dan haka sai na aje.
Amma tun daga ranar na tattara hankalina sai da na gano cord ɗin wayar. Bayan kwana biyu sai na sake samun dama yana wanka na buɗe kai tsaye na shiga Whatsapp ɗin sa. Na yi searching wannan sunan sai ya fito min da chat ɗin su, duk da cewa da turanci suke magana kuma gaskiya ni bana fahimtar turanci sosai amma na gane hirar ta batsa ce ya goge Videos amma naga inda ya yi taggin yana faɗa mata cewa hoto ya yi kyau.
Motsin sa ya sa na aje wayar na ci gaba da abinda na ke yi. Na yi ta kallon shi ina mamaki matukar mamaki. Ga wata tafasa da zuciya ta ke yi. Ya kalle ni, "Babyna ya aka yi ne?" Na ƙaƙaro murmushi kyau na ga ka ƙara wallahi ina kishinka kamar wasu matan suna sonka a waje. Ya yi 'yar dariya "Baby ke dai Allah ya kyauta amma mata yanzu ai ba'a raba su da son maza, suma mazan haka."
Nace Yawwa dan Allah to ina son ka buɗe min Whatsapp ka ga duk 'yan makarantar mu suna yi, ina son muna zumunci. Ya ɗan haɗe fuska, yace "Ki bari sai na canza miki waya tukuna." Nace to Allah ya baka iko. Yace Ameen Baby na,ya saki fuska. Na raka shi yadda na saba na dawo na shiga ɗakina na soma sabon kuka, ina cewa wai me ya kai ni ne, me yasa na dubo wa kai na damuwa. Amma naji mamaki wai Aliyu Shamaki shine ke neman mata!
Duk da haka ban daddara ba yana bacci na saci wayar na shige ban ɗaki na gama duba duk wasu mata da yake soyayya da su. Mata ne masu aji kyawawa sun fini komai, wani abin takaici harda wasu mata 'yan Film.
Tambaya ta ita ce da wane lokaci ya ke samun haɗuwa da su?
🖊️🖊️
Bani da wanda zan tunkara in sanar da shi halin da nake ciki. Amma abinda ke bani takaici na kasa faɗa masa cewa nasan abinda ya ke aikatawa. Haka son sa a zuciya ta yana nan daram na kasa jin haushin sa, sai ma neman yi masa uzri na ke yi. Ƙila ya fara ne lokacin da yake bashi da mata, yanzu aiki na ne in rabashi sa su. Ko ƙila su ke binshi kuma iyakacin su a waya sai turo hoton kawai. Dan haka na ƙara dagewa na daina bacci sai na jira shi ya dawo kuma duk yadda ya ke so haka nake masa, sannan da safe kafin ya fita wajibi ne sai na sauke wani haƙkin amma da an kwana biyu in na duba wayarsa sai inga anyi masa sabon turi na tsiraici. Gashi na kasa daina dubawa, sai na yanke shawarar komawa ga Allah ya bani mafita. Sai mun kwanta yana bacci zan tashi ina faɗawa Allah halin da nake ciki ya taimake ni ya shirya mijina ya rabashi da wannan muguwar ɗabi'ar.
Yau ma ina tsaka da addu'a sai kuka ya ƙwace min ina kuka ina faɗawa Allah cewa. Ya Ubangiji! Kasan halin da na ke ciki Allah kai ka kawo min wannan bawan naka har ƙofar gidan mu Allah ka sani ban taɓa aikata zina ba, Allah na san cewa akwai wani abu da ka ke nufi da wannan haɗin da ka yi. Bani da wata mafita ko wata dabara Allah ka taikeni ka fidda shi a cikin wannan halin. Kuka ya tiƙe ni. Na shafa addu'o'in na ta shi naje gefen shi na kwanta na matsa na shige jikinshi kamar yadda muka saba kwanciya. Sai naji ya matseni tsam ya ce wai "Baby wace damuwa ce da ke wadda duk dare sai kin tashi kin yi wa Allah kuka. Nasani shine wanda ya fi dacewa da ki kai masa kukanki, amma tunda ya baki ni Baby ki faɗa min mana ko zan iya yin wani abu akai in bazan iya yin komai ba sai in taya ki roƙon sa?"
Na sake matse shi nace nace wai dama ba bacci ka ke yi ba? Ba wata damuwa ce da ni ba, ina yi wa Allah godiya ne da ya bani kai a matsayin miji wanda wayo na da dabara ta ba su isa su bani ba.
Ya sake matseni ya ce "Baby ni ne ya kamata inyi wa Allah godiya samu mace irin ki sai mai babban rabo.Dan haka karki damu ki kwantar da hankalin ki ni baku ne har aljanna."
Cikin kwanaki yanayi na ya fara canzawa na rame kuma na rage walwala. Shima ya lura da haka ya matsa min da tambaya na ce ba komai, ya siya min waya Iphone 13 yace in bawa Jamila waccan buɗe min Whatsapp duk wai dan in saki raina, ya min gargaɗi wai kar in shiga wasu groups irin na Whatsapp ɗinnan wanda ake zuga mata, wai Maman Mubina ta taɓa shiga wani group wanda suka yi ta samun matsala da shi. " Nace masa zan kiyaye nace wa Hajita ta taya ni yi masa godiya dama a gaban ta ya bani. Yana ta ƙoƙarin in saki jiki in koma walwala ta amma na kasa. Ina kuma ci gaba da bibiyar shi ta wayarshi ina ganin yadda yake ci gaba da hulɗa da mata, abinda na gama lura shine ya kan haɗu da wasu, wasu kuma baya haɗuwa da su,amma yana ba su kuɗi.
Cikin haka azumi ya gabato. Da dare yana falon Hajiya da yake tun daga wannan ranar nike zuwa ina zuba masa abincin dare da na safe, wanda da ashe Azima ke zuba masa na daren na safe kuma da kansa. Daga shi har Hajiya ni ce ke zuba musu.
Hajiya tace Baby kin kuwa san Azima bata da lafiya kin duba ta? Nace bansani ba,tace to ya kamata ki yi mata sannu jiya da yau bata je makaranta ba. Nace Subhanallah! Na tashi na nufi duba ta tunda na zuba musu abincin. Tana lullɓe na mata sannu ta amsa,har zan fita sai tace "Ki faɗawa Yaya ina jiran shi." Na yi shiru,sai na juyo nace kamar yaya kina kina jiranshi? Tace " Shi ya sani." Sai na ji gaban ya yi wata muguwar faɗuwa tsoro da fargaba sun kamani kar dai har wannan yarinyar...Ta katseni, "Ko kina nufin baki san ni wacece a gurinsa ba?" Bance ƙala ba na fice domin yin sa'insa da yarinyar zai zama zubda ƙimata.
Na koma Falo na samu su Hajiya suna zancan Umara, nace da Hajiya zan jira in shafa maki maganin ƙafa tunda Azima ba lafiya. Tace "To Allah ya yi miki albarka jiya ma ba'a shafa ba. Na koma gefe ina kallo a talabijin.
Yace "Hajiya kujeru goma ne a wannan karon an ƙara biyu, yanzu sai ki bada sunayen mutane bakwai ni da ke da kuma Baby mune cikon na goma." Kamar a mafarki na ji maganar, zani Umara, amma sai dai ba dani suke magana ba dan haka sai na share na yi kamar banji ba.
Hajiya ta ce ka cire Baby a maganar ta fiya Ummara da aikin Hajji sai wata shekarar. Ban waigo ba kuma ban nuna ina jinsu ba. Ba tare da ya tambayi ba'asi ba ya ce "To an cire ta." Suka ci gaba da lissafin su. Sai kusan goma da rabi tace zo ki shafa min maganin nan. Na zo na fara shafa mata gami da matsa ƙafafun, tace "Kai amma na ji daɗin yadda ki ka matsa min ƙafafun nan, ina ganin ma dai ke zaki koma shafa. min maganin nan domin Azima sai ta koya. Nace to insha Allahu zan ke shafa miki. Shamaki yace, "wai kuwa likita ya duba jikin Azimar ? Hajiya tace ya duba ta,kasan bata rabo da zazzaɓin cizon sauro, can take zuwa ɗan lambu can har magariba. Na dube shi, baka je ka duba ta bane? Yace "Sai na shiga zan kwanta sai in duba ta.'
Daya ke ina son in wanke zargi sai na raya cewa zan bi bayanshi. Haka kuwa nayi mun tafi tare mun sallami Hajiya na ce masa bari inje ɗakina in ɗakƙo kayan bacci.
Yana shiga falon shi na dawo na shiga falon dai-dai lokacin yana fita ƙofar da zata kai shi gurin su. Na bishi sai da
na ga ya tura ɗakin Azimar ya shiga sannan na bishi ciki faduwa gaba tare da fatan kar zargi na ya zama gaskiya. Dai-dai Window bana jin komai na yanke shawarar in afka ɗakin kawai tare da sallama ko zan tsinci kalma guda ɗaya da zan gamsu. Dan haka sai na afka kawai tare da sallama. Yana tsaye bakin gadon ya maida hannuwan shi duka baya, tana kwance riginnine tana kallon shi yana magana. Kalma ɗaya na tsinta a maganar itace.. " Baruwana..." Na kalleshi sai na ga ya yi alamar rashin gaskiya amma sai ya da ke. Na dube ta sannu da jiki Azima fuskarta ba walwala tace Yawwa. Na dube shi, Nace ta ƙi tasha magani ne baji kana cewa baruwanka? Da sauri ya ce ba maganar ki ɓace, muje ya dube ta yace "Allah ya ƙara sauƙi." Na sake kallon ta ƙwalla ce a idanunta,gaba na ya faɗi ko dai ya haiƙewa yarinyar nan ne to Allah ya sa ba ciki ne da ita ba. Sai naji na kasa jan ƙafafuna na tsaya ina kallon ta. Muryar shi ce ta katse ni. "Muje mana Baby" Na ja ƙafa na bishi dai dai window yara ya tsaya yana kallon su. Ni kuma shi nake kallo ina me takaici abinda ya ke aikatawa amma kamannin shi na salihan mutane ba zai taɓa bari a zarge shi ba. Ya yafito ni da hannu na isa gurinsa ya kama kafaɗa ta yace Kalli yaranki suna ta bacci 'yan rigim. Na lalle su abin sha'awa kowacce laf a gadon ta. Nace Ina son yaran nan sosai musamman Anisa ƙila domin ta kasance ita ce ƙara. Yace "Ba domin tana ƙarama bane, tun ranar da mahaifiyar ta ta haifeta kowa ya ganta sai ta shigar masa rai." Nace Allah sarki, wai kuwa iyayen su suna zuwa su gan su? Yace "Gaskiya dai ba sa zuwa,kuma Hajiya ce ta tsara haka,amma duk hutu ana kai su suyi sati ɗaya sai a ɗakko su." Na ɗaga kai sannan nace Allah sarki amma kana yi wa yara nan addu'a ko Allah ya tsare su daga sharrin zamani. Yace "Baby daga dukkan sharri na ke musu addu'ar tsari." Ya kama hannu na muje muje ɗaki ki faɗa min yaushe zaki bani ta wajen ki Baby Zeena ɗin? " Na bishi ina faɗin ni bana son ma in haihu. Bansan a fili na furta kalmar ba sai da naga ya tsaya can. Na kalli fuskar shi launin fuskar shi ta canza gaba ɗaya, wannan ce rana ta farko tunda na zo gidan da naga ɓacin ransa a kaina, ya tsira min ido take fargaba da tsoro suka tsirga min. Ya fincike ni zuwa ɗakin baccin sa ya tura ni kan gado ya jawo kujera ya zauna a gabana ya ce "Maimaita abinda ki ka faɗa." Na girgiza kai cikin tsoro tare da ɗora tafin hannuna a bakina. Yace "Ki maimaita!" Yadda ya yi maganar da ƙarfi sai na tsorata hawaye suka soma zubo wa,nace nifa na yi tsammanin a zuciya na yi maganar. Yace "To me yasa zaki fadi hakan ko a zuciyar ki? Kice ke bakya son ki haihu to faɗa min da lilinki kuma kar ki sake ki min ƙarya." A zuciyata dalilina saboda neman matan da ya ke yi ne, kuma naji ance duk abinda ka yi wa ɗan wani sai anyi wa naka. Amma bani da damar faɗar hakan dan haka sai nace Ni dama na faɗi haka ne saboda ina jin tsoro kada in haihu ni ma ka sake ni kamar yadda ka saki su Maman Anisa kuma ka karɓi 'yar ka kabar ni ina tunanin ku. Na kai ƙarshen maganar da sakin wani kukan. Ya tashi ya dawo bakin gado ya janyo ni jikinsa ya rungume ni tsam. Yace" Baby ni da ke babu abinda zai rabamu sai mutuwa, akan ki na fara soyayya duk auren baya ashe ba soyayya na yi ba sha'awa ce kawai." Na ɗago na dube shi nace dama ana aure saboda sha'awa? Yace "Ni kaina ban gane hakan ba sai bayan auren sai inji duk sun fita a raina." Nace sai kawai ka sake su? Yace 'A'a Baby babu wadda na saka saboda hakan sai bisa wani dalili na Hajiya wanda har yanzu ban san shi ba." Nace Ni ma na fara fita a kan ka ko? Cikin far gaba na yi tambayar. Yace "Baby kullum ƙara son ki nake yi, da kika ce baki son ki haihu kalmar ta min zafi, ya kai hannu ya shafa cikina, na ƙosa inga wannan shafafen cikin ya tasa ya ɗanyi tudu, ina son inga naki salon laulayin dame zai zo." Na zuba mishi idanu a zuciya ta kuwa tunowa ta ke da kalaman da ya ke rubutawa na batsa da hannun sa yana turawa matan banza,ga waccan yarinyar da nake zargin su da ita.
Ya hura min ƙwayar idanu tare da faɗin "Kamar kina min kallon tuhuma Baby." Nace Me zaka yi wanda zai sa in tuhume ka? Kai mijina ne mai gaskiya da riƙon amana,ga ibada kyauta da sadaka gidan ku ya yi fice, gashi ka tsare kanka daga sharholiyar zamani ta bin matan banza da yawancin mazaje ke yi,ko tunanin bayansu basa yi,. Ina matuƙar tausayin ahalin mazinata, domin sai uba ya ja a yi wa 'yarsa a banza ba tare da hakkinta ba .Ko miji ya ja wa matar sa ɗa ya jawa uwarsa...Hannu ya sa ya rufe min baki tare da faɗin "Ki taya su addu'a Allah ya shirye su. Ni yaushe ma na samu lokacin matata har bare in tsaya neman wasu matan. Ina da kamar ki wace damuwa gare ni. Baby komai na ke so kina min yadda ki ke sakin jiki da ni a gurin kwanciya ban taɓa samun haka ba. Kina kore duk wata sha'awa tawa. A zuciya ta nace kaji ƙarya. Ko a wannan daren na yi bincike a wayarsa, kuma sunyi alƙawari da wata za su haɗu ranar Lahadi da ƙarfe sha biyu.
....
A Cikin kwanaki kullum ina yin tunani aka yadda ya kamata in daƙile wannan haduwar ta sa da karuwar nan, kwata kwata bana son yasan nasan abinda ya ke aikatawa domin ɓoye min ɗin ma alfarma ce, in har namiji ya na aikata wani laifi ya ɓoye miki alfarma ce kar ki sake ki binciko, sannan in har kin gano to karki nuna masa domin zai yi borin kunya ne ya nuna miki bai damu ba, sannan zaman lafiya ya ƙare. Zuciya ta ce ta yi min wannan karatun don haka sai na ƙara yin ƙoƙarin daurewa. Kuma na fahimci cewa kowane iyali suna da tasu matsalar wasu rigingimu da munafirci, kamar ahalin su Abbanmu kenan. Wasu 'yan shaye shaye suke da su a cikin nasu ahalin.Wasu kuma ɓarayi. To sukuma nan manemin mata Allah ya basu gane nima ya zama cikin ƙaddara ta. In na tada bala'i na tafi bansan dawa zan haɗu ba a gaba.
Ranar asabar na sake bincika wayar sunyi magana cewa zai aiko a ɗauke ta tsakanin shabiyu zuwa ƙarfe ɗaya.
Na tashi zaune na ƙare mishi kallo cikin dare yana bacci nace zan gwada wata dabara Allah ka tsaya min.
Na riƙe cikina ina ta juyi ina ɗan kuka ina faɗin wayyo cikina. Ya farka a gigice ya kamani yana tambaya ta, da kyar nace cikina ne ke ciwo. Ya tashi ganin yadda ciwon ke ƙara tsananta ya kira wayar Hajiya ya faɗa mata. Tace "Subhanallah! Ka zo ka amshi ko plagin ka bata kafin asbashi a kira likita." To haka dai aka kwana a kaina ina birgima,yau da ga salla wannan zaman na safe na gurin Hajiya ranar bai samu ba, da zai tafi salla sai na yi laf kamar bacci ya sace ni. Yana fita na tashi na yi salla na dawo na ɗora ina juya juya har na faɗo daga kan gadon. Shi kuma bayan sun gaisa da Hajiya ta tambayi jikina yace sai gefin asbahi sannan bacci ya ɗan sace ni, yace shi kanshi bacci ya ke ji yanzu idanunshi sai raɗaɗi suke yi. Hajiya tace "Ka kira likitan ko?" Yace munyi waya yana hanyar zuwa nan ɗin,. Hajiya tace "Allah ya sawaƙa kuma ba ciki gareta ba ko?" Shamaki yace gaskiya dai bansani ba, amma a wannan sati tayi al'adar ta. Hajiya tace To" bari likitan ya ƙaraso muji."
Kiran likitan ya shigo,Shamaki ya ce gashi nan ma bari in shigo da shi. Har Hajiya suka nufin ɗakin Shamaki ni kuwa lokacin ina tsaka da kukan baƙin ciki jin motsin su ya sa na dafe ciki na shiga juyi. Shamaki ne ya rugo da gudu yana faɗin "Subhanallah faɗowa ki kayi haƙa Baby! Ya ɗauke ni ya mayar kan gadon yana min sannu, sai naji muryar Hajiya itama tana min sannu cikin magana da ƙyar nace a kai ni gurin Ummanmu zan mutu ne. Hajiya tace "Inda mutuwar ce 'yannan wane ke ki furta ta,zafin ciwon ne Allah ya baƙi lafiya likita ka duba ta sosai ni bari in koma Allah ya sawaƙa."
Duk inda likita ya latsa da hannu a cikina sai in saki ƙara, yace a sani a mota kawai muje Asibiti a yi hoto domin a gano ina matsalar ta ke, ya kira Hajiya ya faɗa mata, sannan ya canza kaya ni kuma ya zira min hijabi akan kayan bacci ya ɗakko ni kamar ya ɗau jinjiri muka fita mota.
Iya gwaje gwajen likita bai iya go komai a cikina ba, don haka sai ya gayyaci wani likita wanda ya yi shura a fanni cikin kafin yazo aka min allurai dan rage raɗaɗi sannan aka samin ruwa da allurar saka bacci. Bacci ya yi gaba da ni wanda har likitan ya zo suka yi hoto an gane wane ina da sanyin mara da kuma tsakuwa wanda ake ganin tsakuwar ce ma ta soma taruwa, za a bani maganin ta taru guri guda in ya so sai a yimin aiki. In kuma anga yiwuwar ba sai anyi aiki ba sai a bani magani ta narke.
Ni dai ban farka ba tunda a kwai bashin bacci sai kusan ƙarfe biyu, ina ganin Asibiti na tuno komai da komai zan motsa sai ƙaran wayar shi ce ta tashe ni, bai san na farka ba yana magana can ƙasa ƙasa daga can kusa da bakin ƙofa da yake kunne na kamar na maciji ya ke ba dai jiyo magana ba, naji yana faɗin. "Na faɗa miki cewa na miki magana ta Whatsapp ki duba mana mata ta bata da lafiya yanzu haka muna Asibiti in na samu lokaci za mu sake saka rana don haka karki sake kiran wayata.
Alhamdulillah na furta a hankali, na wahala kuma na yi ƙarya,amma na yi nasarar hana aikata babban laifi wato zina. Ya dawo ina miƙa tare da salati, yace "Baby kin farka sannu ya jikin.?" Ya kama hannu na yana murzawa. Na zuba mishi idanu, kishi da son shi suka sake tirniƙe ni. Nima na matsa hannun shi a hankali nace dan Allah kana so na sosai? Ya tsuguno ya ɗora karan hanci shi a kan nawa, yace "Baby me yasa ki ke ta kokwanto?" Ka sake tabbatar min, na faɗa hawaye suna zubowa daga cikin idanuna. Yace "Baby ina matuƙar son ki." Na sa tafin hannuwa na guda biyu na ɗora akan kumatunsa, nace Ni kuma nayi maka alƙawarin zan yi maka duk wata biyayya zan rufa maka duk wani asiri zan baka duk wata kariya wadda nake da iko.
Ya ɗanyi shiru, can ya yi murmushi "Baby za dai ki min biyayya amma rufin asiri ko kariya ai nine zan miki wannan amma ki taya ni da addu'ao nan da ki ka saba." Nace to ba damuwa muje gida tunda na samu sauƙi, gashi baka je kasuwa ba kai sam yau. Yace "Ya zanje kasuwa mata ta tana cikin mawuyacin hali." Nace na gode da kulawa. Yace bari inje in yiwa likitan magana.
An sallame ni da tarin magunguna,muna isa gida Hajiya ta min sannu su Juma kuwa har ɗaki. Ranar dai Shamaki bai fita kasuwa ba,kuma banga Hajiya ta damu da rashin fitarsa ba, yana gurinta kaɗan kaɗan ya zo ya duba ni.
Kwana uku bayan wannan diramar ina zaune gaban Hajiya ina yi mata tausa a ƙafa, tace "Me yasa baki sanar da iyayenki rashin lafiyar ki ba? Irin wannan ciwo da ki ka yi mai azaba zai iya kai mutum lahira." nace na ga ana kula dani sosai kuma kar in tada musu hankali shiyasa. Tace "Kinyi tunani mai kyau, Allah ya ƙara lafiya, ta ci gaba Shamaki ya na sonki, ki yi amfani da hakan ki taimaki rayuwarsa." Kalaman suka ɗaure min kai, me hakan ke nufi? Na tambayi zuciya ta. Hajiya ce kawai zata iya wayar min da kai, don haka sai na ce. Tayaya zan iya amfani da haka in taimake shi? Kuma wane irin taimako? Tace "Babu buƙatar dogon bayani ni dai zan ci gaba da kula da yiwuwar hakan." Nace to Allah ya bani iko, ni zanyi koma menene matsawar hakan zai taimake shi. Hajiya tace kin kyauta
Juma ta shigo ta zauna tace ina son magana da ke ne Hajiya.
A duk lokacin da Juma ta yi irin wannan furucin Hajiya ta san tana buƙatar su keɓe ne. Dan haka sai ta ce, " Rabi'atu ba mu guri mu yi magana. Na tashi na nufi gurin yara. Azima tana zaune kamar kullum da littafin a hannun ta. Ban damu da ƙin amsa sallama ta ba,domin nasani ta saba. Yaran suka nufo ni su duka suna tambaya ko zanyi musu tatsuniya. Nace su bari sai gobe Alhamis tunda babu islamiyya in mun gama karatu sai in yi musu. Juma tayi sallama muka amsa tace "Azima Hajiya tana kira." Sai da ta ja dogon tsaki sannan tace faɗa mata ina zuwa. Juma ta jima da tafiya kafin Azima ta sake yin tsaki ta yashi tana ƙunƙunai. Nabi bayanta da kallo ina mamakin wani faɗi da naga ta yi. Ji nayi duk na tsargu, na tashi na nufi ɗakina,
Gaban hoton mu na tsaya wanda yake bani kyauta ina kallo shi. wayata ta yi ringin na ɗauka na kalli fuskar wayar na sa a kunne tare da faɗin babban baƙo ka dawo ne? Yace "Duk jan lokacin da aka yi ana nema min suna ƙarshe in ƙare da wani babban baƙo babu ko daɗin ji." Na yi dariya nace in har kaine Babban baƙon mu na ranar saukar karatunmu to kuwa sunan da zaka ci gaba da amsawa ke nan. Yace "A hakan ma ni ne da godiya, domin a keɓaɓɓen lokaci akan kira ni da Baby sweet heart da sauran sunaye cikin shagwaɓa. To kina ina ne yanzu?" Nace ina zani ina gida akwai wani abu ne?" Yace "a'a' Na kira Hajiya ne bata ɗaga ba, nace ina ɗakina ne amma bari in duba maka, kariƙe wayar har inja falon, yace "to kije ina jinki.
Na isa falon Azima ce zaune su da Hajiya kan Azima a ƙasa kamar dai tana kuka, Hajiya kuma cikin wani yanayi da bazan iya fassarawa ba. Na ƙarasa nace Hajiya Shamaki ne ya ke son ku yi magana. Hannu kawai ta ɗaga min, wanda bana bukatar sai an faɗamin cewa bata son jin maganar kowa.
🖊️🖊️🖊️
*HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 34*
Ta katse ni, "Bakya buƙatar dogon tunani Rabi'atu, akwai wani sirri ne da ki ke ɓoye wa na sa?" Na girgiza kai babu Hajiya. Tace "Gaskiya ban yarda ba, kina dai rufawa mijin ki asiri ne, ina son ki sani kalmar ki da kika furta ita take nuna cewa mijinki ya na leƙe leƙe." Na ce Subhanallah Hajiya bana zargin sa kuma bashi da kama da haka, in kin duba sam bashi da lokacin kansa bare na yawon banza,kawai dai na furta ne saboda akwai masu yi, ni kuma godiya ce ga Allah da bai bani irin wancan ba,ya bani wanda zai aje mu mu huɗu.
Hajiya tace "To iya magana Sarkin zance Allah ya shiryar da duk ɗan musulmi. Nace Ameen,tace tashi ki kai masa kankanar, saura kije ki faɗa masa abinda na ce game da ƙara aurensa. Na ce bazan ce komai ba.
Na tafi da kankana na tura falon a hankali na shiga baya fakon na aje masa a gurin da yake ajewa na nufi ɗakin zan shiga da yake tun da na saka shi a tarkon zargina bana yin wani kwakwaran motsi in zan shiga gurinsa. Cikin Sa'a naji yana waya, yana faɗin "Sweetheart gaskiya ban taɓa samu mace mai suna mace kamar ki ba, a tafiyar nan ta sati ɗaya kin ji dadi banso muka rabu ba. Ta faɗa masa wani abu sai naji ya ce "Da gaske Babyna to ai kin haɗu ne, bana son a yi min kishiya don Allah a dai riƙe min amana. Kuma a turo min hotuna in kalli abubuwan... Hannu na saka na toshe kunnuwa na,sannan na juya da sauri, cikin rashi sa'a na bigi wata tukunyar fulawa da ke aje a gefe sai ta faɗi. Da sauri ya katse wayar ya fito,daidai lokacin na murɗa ƙofar zan fita, yace Baby! Yadda ya kira ni kasan cikin fargaba ya ke.
Bazan iya juyowa in Kalle shi ba,kalaman sa suna min yawo a cikin kai dan haka sai kawai na fice,da gudu na ƙarasa ɗakina kan gado na faɗa ina maida numfashi na soma karanta duk wata addu'a da ta zo baki na. Ina jin ƙarar buɗe ƙofa nasan shine, don haka sai na soma ƙokarin daidaita yanayi na. Ya shigo ya tsaya yana kallo na. Na ɗago da kyar na zuba mishi ido. Hawaye suka soma kwaranya a idanuna. Ya zauna jiki a sanyaye, ya ce. "Menene ki ka fita da sauri ina kiran ki?" Cikin rawar murya da zubar hawaye nace babu komai. Ya kama hannuwa na, a yau sai naji tafin hannun sa mai taushi kamar ƙaya . Yace Baby dole akwai wani abu ki faɗa min. Na girgiza kai ba komai. Na saɓule hannu na daga nasa,kaje ka ci kankanar ka na ajiye. Ya ƙara kama hannu na "To tashi muje mu sha sai mu kwanta. " Na sunkuyar da kai, ka yi haƙuri yau zan kwana a nan. Ya yi shiru, yana ƙoƙarin tabbatar da zargin sa,tabbas yarinyar nan ta ji wayar sa. Ya sunkuyar da kai yana tunanin abinda ya kamata ya yi. Na zame a hankali na kwanta ina nanata ambaton sunaye Allah a zuciyata ba shakka duk matar da mijinta ke neman matan waje alal haƙiƙa tana cikin masifa.Na lumshe ido hawaye suna kwaranya ta gefe. Ina jinsa ya miƙe jiki ba ƙarfi ya kama hanya,na bishi da kallo har ya fice ya rufo min ƙofa,na tashi na zauna zaman dirshan na saka kuka. Nayi mai isata, sannan na miƙe na shiga ban ɗaki na ɗauro Alwala na zo na shiga jero salla, ba zan iya ƙirga yawan sallamar da na yi ba har sai da naji ina jin kiri sannan na zube a sujjada ina raira kuka a gaban Ubangiji na kasa furta komai sai faɗi nake Ya Allah! kai ne mahalicci na, Allah ka gani,Ya Allah! Ka gani. Bacci ya ɗauke ni a nan, a durƙushe.
Kiran sallar farko ya farkar da ni, na tashi duk jikina ya yi tsami saboda irin kwanciyar da nayi dakyar na yo alwala nazo na ɗora sallah. Aka tayar da sallah inajin yana ƙwanƙwasa ƙofa ta,ban tashi ba na ci gaba da sallah. Bayan na idar na zauna ina tunanin kishin me zan tsaya yi da duk wadda zai auro, domin da ya kawo su ya aje zai komawa matan waje, kuma duk yadda aka yi Hajiya tasan yana bin mata, tana zaton ko na gano ne. Yanzu wane mataki ya kamata in ɗauka shine damuwa ta. Na farko bazan nemi ya sake ni ba, domin yin hakan babban laifi ne,banda haka sonshi ko kyas bai ragu a zuciyata ba amma na san tabbas ina jin haushin sa a yanzu,yana faɗawa wata ƙaruwa wai shi bai taɓa jin mace irinta ba,ni kuma fa?
Wata zuciyar tace ki dafa shi da ruwan sanyi dan kina sonshi kar ki yarda ki zama kamar wata shashasha. A fili nace Allah ka bani basirar yadda zan tafiyar da wannan bawan naka.Allah ka shiryar da shi.
Wayata ta soma ringin a firgice na ɗakko ta kardai wani abu ne ya faru a gidan mu. Ashe shine, yace ki zo ki same ni a gurin Hajiya. Nace to.
Ashe shima haka ya kwana cikin tashin hankali ya tabbatar taji maganar dan haka sai da ya gama tunanin abinda ya kamata ya yi ƙarshe ya yanke shawarar kawai ya faɗawa Hajiya ko ma dai menene ta shawo kanta domin shi duk nauyin ta ya kamashi balle da ya zauna yana tuna kalaman batsa da suka dinga musaya da yarinyar bai san tun yaushe ta shigo ba. Inhar ta ji komai gaskiya ya yi abin kunya babba.
Na durƙusa na gaida Hajiya kamar yadda na saba. Na dube shi shima na gaishe shi kamar ba komai.
Ya kalli Hajiya ya sunkuyar da kai, sannan yace Hajiya na kawo kaina ne bisa ga wani laifi da nayi Wa Baby,ina son a taya ni bata haƙuri kuma insha Allahu zan kiyaye. Ciki mamaki Hajiya ta ke kallon baƙon lamari Shamaki yana neman afwar Babu har da haɗawa da ita,to wane irin laifi ne haka? Na katse mata tunani da cewa Ya Salam! ni ce kaimin laifi? Yace ki bar wani alaye Baby na yi kawai tun jiya kin dage ba komai,amma kina ta kuka shi kuka dama ana yin shi haka kawai ne, kuma na ga tsanata a ƙwayar idanunki kin ƙauracewa shimfiɗa ta ko bacci banyi ba. Bazan jure kiyi fushi da ni ba. Na kalli Hajiya wadda ta tsura min ido, na sunkuyar da kai. Hajiya tace ka tashi ka shiga ciki ka bamu guri.
Na gyara zama,ta ce Rabi'atu jiya ya muka yi dake anan gurin? Na ɗago na dubeta ina ƙoƙarin tunawa, nace munyi magana da yawa musamman ta aurensa da Azima. Tace "Yawwa amma ya muka rabu?" Nace kince kar in nuna masa munyi maganar. Tace Yawwa to kuma ya akayi kika yanke masa irin wannan hukuncin na azabtarwa?" Nace Hajiya wallahi yadda muka yi maganar nan a nan gurin wallahi a nan nabarta. Bance banji zafin kishi ba,amma wannan ba laifi bane dan zai ƙara aure zan bashi duk wani goyon baya Hajiya wallahi bazan ɗaga masa hankali ba.
Tace to faɗa min menene ya yi miki?"
Na sunkuyar da kai nace Hajiya kiyi hakuri nasan Shamaki ɗanki ne,kuma kina sonshi fiye da kowa, amma ni kuma mijina ne akwai wani sirri tsakaninmu wanda ya kamata in suturta shi daga ni sai shi sai Allah. Ina neman alfarma ki bar wannan maganar ta wuce a gurina ki ƙara yi masa addu'a kawai. Yau ce rana ta farko da naga jikin Hajiya ya yi sanyi harma ta rasa abin faɗi na kusan sakwan talatin. Sannan ta ja wani dogon numfashi tace, "Ki sani riƙe abu a zuciya yana haifar da ciwo,tattauna Matsala da wani yana rage damuwar kuma ni ce mafi dacewa ki tattauna wannan damuwar da ni." Nace Hajiya dole ne mu koyi yadda zamu kashe mu rufe domin samun kwanciyar hankalin ki, duk da ban kasance likita ba, a shekarun ki yanzu bakya buƙatar duk wani abu da zai tada miki hankali. Tace "Babban abinda ya fi komai ɗaga min hankali shine inga Shamaki a damuwa, ina yin kowane irin abu dan in samar masa da kwanciyar hankali aurenki misali ne." Na yi shiru, ina tunani Hajiya tana yi wa ɗanta makauniyar soyayya wadda ta sa sam bata iya hango matsala. Na dube ta, zan yi iya yi na inga bai shiga cikin wata damuwa ba daga yau. Naɗaga yatsa kamar mai ɗaukar alƙawari. Bata ce ƙala ba ta ɗaga waya ta kirashi,ya zo ya zauna yana satar kallo na. Tace "Shamaki matar ka ta dage akan babu komai da ka yi mata, sai dai ina mai baka shawara ka yi ƙoƙari ka gyara abinda ka ɓata a idanunta. Ya kalle ni, na yi ɗan murmushi ka yi hakuri da yanayin da na saka ka a ciki. Shi dai idanu ya zuba min yana kallona. Anisa ta shigo ta nufi gurin Hajiya da littafi a hannu ta gaisheta sannan ta gaida Dadynsu,sai ta dube ni Momy ina kwana, ta zauna kan cinya ta,tace Momy Anty Azima bata yi min Homework ba. Na amshi littafin ina dubawa, nace to zo muje gefe mu yi. Na koya mata Rahin ta zo ta tafi da ita domin yi mata shirin makaranta. Na dubi Hajiya suna magana ƙasa ƙasa da Shamaki nace zan dawo kafin su Juma su haɗa abin karyawa.
Lokacin da ya shigo domin shirin tafiya kasuwa ina gyaran gadon shi, ya tsaya ya harɗe hannayen shi yana kallo na, na ce akwai wani abu ne? Ya girgiza kai sannan ya shige banɗaki.
Na fito masa da kaya kamar yadda na saba ya shirya tsaf na ɗauki jakarsa na rataya a kafaɗa. Ya janyo ni zuwa jikinsa ya rungume ya sa hannuwan shi guda biyu ya ɗago fuskata ido cikin ido muke kallon juna, yace "Baby yanzu bazaki faɗa min.. Nasa tafin hannu na narufe mishi baki tare da faɗin shissss ya wuce babban baƙo. Muje ka tafi Allah ya tsare gabanka da bayan ka. Yace kimin alƙawarin cewa bazaki yi kuka ba." Nace bazan yi ba. Ya sunbaci goshina sannan muka tafi tare.
Cikin satin na zama cikin taka tsantsan kuma na duba wayar shi naga 'yan mata sun masa magana amma duk bai bada amsa ba. Babu daɗin ganin haka tabbas an ɗan samu ci gaba domin hakan da ma ya taimaka inda na tada bala'i da sai ya tada borin kunya ya yi bala'i kuma ya murje harma ya ke min gadara a gabana sai ya yi wayar shi tunda ya lura bazan iya komai ba.
Matar Abokin shi Alhaji Shamsu ta haihu , yace in shirya da dare zamuje barka. A gaban Hajiya ya yi maganar na ji daɗi domin ina son muna ɗan fita da shi. Hajiya tace ka je kai kaɗai ita kuma anjima ta shirya direba ya kaita ka bata abin barka. In kuma taron suna zata je shikenan sai ta bari sai ranar. Ya kalle ni kamar yana son yaga yadda zanyi tunda yasan ina son mu fita da shi na sha faɗa masa cewa ina son mu ɗan fita ko a ƙafa ne, sai ya ce inyi hakuri in ya samu lokaci ƙasar waje ma zamu fita.
Washe gari ya bani zannuwa biyu da dubu goma ya ce inje barka shi baya son zuwa suna ɗin nan. Nace to. Na sanar da Hajiya tace to in shirya baya azahar.
Mace mai fara'a maman Haidar wai takwara aka yi wa Shamaki, nace a lallai ki ce ni aka yi wa haihuwar amma bai faɗa min ba. Tace ai bai faɗa masa ba sai ranar zaiji. Nace to ki ce in zuge baki na. Tace gaskiya kam. Da tare zamu zo sai kuma yana da uzri. Tace "Ko kuma Hajiya ta hana ba." Nace Ya zata hana mu fita tare, cikin mamakin yadda aka yi ta san maganar na yi tambayar. Tace "Ba gulma ba amma ko zuwanki na sha mamaki, duk matan Shamaki sai dai su saci hanya su ziyarci mutane, bata son su yi hulɗa da kowa, shiyasa ki ka ga ko gurinki ban zo ba." Na gyara zama domin jin kanun labarai. Nace to ko domin ni ban jima bane shiyasa bata fara min ba? Tace "Ƙila dai ɗan ke yarinya ce ƙarama shiyasa bakya ganewa. Shekara ɗaya na cika ta ke sa shi ya saki mace tace wai bata ci jarabawa ba,ko uban me ta ke jarabtawa oho mata." Nace ce duk bansan wannan ba,ke ya 'aka yi kika sani? Tace "Tsoro na ke kar magana ta fito." Nace sai dai in ke ki ka faɗa amma ni bana haka kamar kin haƙa rami kin saka.
Tace "Ai Kinsan Maman Anisa ƙawata ce munyi makaranta a gurin bikina suka haɗu da Shamaki suka yi aure, kar ki ga irin son da suke yi wa juna amma shekara na cika ta sa ya sake ta. Har yanzu suna son juna kuma tace min kuma zasu iya maida auren su." Gabana ya faɗi amma sai na saki murmushi nace ya faɗa min ai baya ɓoye min komai, ta ce "Haba dai." Nace ƙwarai kuwa. Tace Kenan har irin zaman su da maman Mubina da Meema?" Nace kina shakka ne? Tace "A 'a Naga ita Maman Anisa bai taɓa faɗa mata komai game da su ba." Nace Kinsan so kala kala ne ni komai na shi na sani. Tace ni Uwar gidana sun saba da Maman Meema sun zama ƙawaye tunda matan abokai ne,to ita ke ba uwargidana labarin zaman su shine ta ke bani." Nace dama ku biyu ne? Tace e uwargidana anjima nan zaki ganta tunda muna zama lafiya. " Nace yafi muku sauƙi yaushe zaka tsaya fitina akan namiji? Tace ashe kin gane ga mazan nan namu masu neman matan tsiya kuna nan kuna faɗa wasu na can na faranta musu. Na ce ai kuwa Allah dai ya shirye su. Ta sake kallo na da taji bance komai ba. "Ashe kinsan suna neman mata?" Nayi "yar dariya akwai wani da zaka sheda ne yanzu a maza? Ta taɓa baki tace babu. Amma ya faɗa miki har yanzu suna fita da maman Anisa?" Na yi shiru da alamu matar nan so take ta hasala ni kuma kamar aike. Nace duk na sani, nifa da kika ganni duk wadda ta zubda kanta ta bashi ya bi ya tsallake ruwanta. Ta buɗe baki cikin mamaki, tace "Kin ɗaure mishi gindi kenan? Nace To Maman Haidar ina son mijina ya yi abinda ya ke so. Tace "Yanzu na gane abinda ya sa Hajiya bata nuna muku mugun halinta ba. Ita ke ɗaure mishi gindi yake bin mata." Nace To shi Mijinki wa ya ɗaure mishi nashi gindin? Ta saki dariya gaskiya kullum muna ƙorafi muna masa addu'a. Nace to ya bari? Tace ya dai rage da har a gabanmu yake waya da 'yan matan shi, sai da muka tada balli. Shine yake yi a ɗakin shi .
Sallamar wasu mata muka ji ta amsa ta leƙo sai naji tana faɗin a kamar haɗin baki ga Maman Anisa da Maman Meema. Gabana ya yanke ya yi wata muguwar faɗuwa.
🖊️🖊️🖊
️Na dake domin na gane duk yadda aka yi kiran su ta yi a waya,ko ta tura musu message tun da na lura wayar ta tana hannun ta tunda na zo, amma dai banga ta yi waya ba. Muka bi juna da kallo ni da su, lokacin da suka zauna, na gane Naman Anisa domin suna da kamanni, na kalli. Wadda nake zaton ita ce uwargidan maijego ta ce "Amarsu ce aka zo mana Barka?" Na bi ta da kallo ban amsa ba. Wadda na ke zaton Maman Meema ce tace "Amaryar ma?" Wai a zuwan bata sani ba. Mai jego ta amshe da sauri ta ce "Amaryar Shamaki mana." Maman Anisa ta zaro ido, Tare Da faɗin Shamak dai "Dama ke ce Amaryar Allah sarki, har kin bani tausayi ta yatsina baki, gata yarinya wannan tafi sha biyar ma, kai Allah sarki ya zaman ɗaki? Har yanzu kwanciya bata gundire ki ba.? Kin lura dai gidan Zeena akwai na'ura ki bi a hankali. Ta ci gaba.
"Yawwa ki lura da su Juma 'yan leƙen asirin Hajiya ne. Kin gane ai?" Murmushi na yi,
Kasu dai kamar wayayyu kuma dai kyawawa ne dan na yarda sun fini a kyau,amma abin takaici babu iji ba iya magana bare tauna kalma.
Na maida kallo na ga Maman Meema wadda take faɗin "Ko bata iya magana ne?" Na yi ɗan murmushi sannan nace ina yininku?" "Ai ashe bamu gaisa ba." Inji Naman Anisa. Sai kuma suka amsa lafiya lau." Maman Anisa sai yatsina take yi tana hare harare ta miƙe tana danna waya,can ta kara a kunne sai tana faɗin Dadyn Anisa wannan karon kuma a haka aka ƙare? Duk mu ukun da ka rabu damu muna da kyau da diri bana kuma muciya da zani aka ɗakko." Mai jego ta tashi da sauri hankaɗa ta ciki tana faɗin shiga kiyi a ciki uwar neman jaraba. Na yi ɗan murmushi, ko kusa ban ji wani haushi ba,domin dai ko ma me zata faɗa yanzu dai ni ke da miji to wane kula su zanyi? Maman Meema tace "Nima dai sai kallon ta nake ina mamaki wai ace kamar Shamaki ya auri wannan yarinyar, koda yake tausayi ma ni take bani wallahi, watan ta nawa yanzu?" Kishiyar maijego tace ƙila zata yi wata biyu ko uku.
Ta kalle ni " Ki fara ƙirga lokacin barinki gidan. Allah ya sa dai kema kina da ciki, duk rintsi randa gado ya taso dole sai kin shigo ciki." Hajiya dai baƙin ciki take yi kar a zauna da ɗanta a samu gado, da ace zai yiwu ta bawa ɗanta abinda matan shi zasu bashi wallahi bazata taɓa barin shi ya yi aure ba.
Na lalle ta nace, da farko banyi niyyar cewa komai ba, domin bani da magana da ku duk kun girme ni, kuma banga laifin ku a cin zarafin da kuka yi min ba, laifi nane da nazo barka har maijego ta kira ku domin ku taru ku ci zarafi na, da sirika ta da kuma mijina.
Na miƙe tsaye na turawa mai jegon ledar gashi nan Allah ya raya. Na ciro waya ta na soma kiran layin Hajiya. Ta ɗaga nace Hajiya barka da yamma tace "Yawwa Rabi'atu." Nace direban ya taho ne? Tace yanzu ya kawo min saƙo da nace ya bari sai ya yi la'asar sai ya zo ya ɗakko ki. " Nace in babu damuwa ya zo kawai yanzu. tace to bari insa a sanar da shi.
Ina kashe wayar mai jego tana riƙe hannu na haba amarya wallahi ban yi dan in wulaƙanta ki ba, kuma ba wadda na kira kawai dai arashi aka samu. Dan Allah ki zauna mana kafin direban ya zo."
Na kwace hannu na nace zan jira shi a waje. Tace "Ki rufa min asiri. Kishiyar ta kuwa sai dariya ta ke yi.
Sai kira ya shigo, na duba naga Shamaki ne a zuciya ta nace sun gama waya da Naman Anisa ta gama ci min zarafi na shine ni kuma zai kira ni me zai faɗa min.
Amma sai na ɗaga inji me zai ce,. Sai naji yace "Shugabar ɗalibai kina gidan jegon ko kin koma gida?" Wani lokacin yakan faɗa min haka tun da na sa mishi babban baƙo. Take na gane cewa wayar ƙarya ta yi. Nace babban baƙo gani yanzu zan wuce, danma tsofaffin matanka sun zo ana ta labari. Yace "Su waye suka zo!? Nace kaji ni fa. Cikin shagwaɓa na yi maganar. Sai naji ya kashe wayar. Maman Meema tace "Lallai yarinya mune tsaffin?" Kishiyar maijego tace ita ma kwana nawa ne wai maye ya yi amarya. Maman Anisa ta fito ta na fadin wai me take cewa! Ƙaran wayar maijego ya tsai da ita, mijin maijego ne ya kira ta. Ban san me yake faɗa ba, naji dai tana faɗin nifa ba wanda na kira, to ance maka za 'ayi faɗa ne." Sai ga Shamaki ya sake kirana,"Ina fata dai ba wadda ta zage ki?" Nace , To ko an zage ni babban baƙo ai na kai ne. Zan jira direba a waje ko ka yarda in hau adaidaita sahu? Yace "Na yarda ki ɗauki drop ki bar gidan." Nace yanzu insha Allahu. Ina kashe wayar naga duk suna kallo na. Mama Meema tace Abin tausayi kya gama kicifin ki fice ki bar gidan ba dai Hajiya Zeena da Shamaki ba." Na yi mata kallo sama da ƙasa sannan nace, in banci Jarabawa ba ke nan, kinsan wani abu? Ko a makaranta ban taɓa faɗuwa Jarabawa ba,bare ta gidan Hajiya Zeena mai sauƙi, ku rungumi ƙaddara a kwai zafi ka kasa cin Jarabawa musamman ta shiga ajin gaba.
Na Kalli Maman Anisa nace daƙiƙi shine ya ke maimaita aji, Allah ya sa dai kin fahimta. Na dubi maijego nace Dole Hajiya ta hana zuwa gidan ire Iran naki domin hakan yafi alkhairi. Allah ya raya miki ɗanki. Na rataya jakata na fice, ina ji suna banza a banza kawai.
Ina fita direba yana isowa na shiga muka wuce.
Hajiya ta tambayi maijego da jariri na ce duk suna lafiya. Tace "Amma lafiya lokacin da kika kira ɗazu nake jin 'yan surutai?" Nace hira ce 'yan barka ke yi ni surutun nema ya ishe ni shiyasa nace zan tafi. Ta yi murmushi "Mata ai in sun taru basu da labari sai gulma ko hirar mazajen su, mai tunani kuwa bata da wannan lokacin."
Nace Allah ya kyauta na shige ɗakina.
Da dare Shamaki suna cin abinci, ina dama masa wata fura da ya zo da ita, yace "Wai kuwa Hajiya yarinyar nan ta faɗa miki matan nan sunje gidan Shamsu?" Tace waɗanne matan ne? Yace "Su Naman Anisa da Maman Meema ne nasan tabbas su ne domin Maman Mubina na san bata ƙasar nan, ko tana nan ma bazata zo ba."
Hajiya ta Kalle ni, haka ne? Nace e sune, suma sunzo barka ne. Tace sunzo gulma dai,Allah ya sa dai ba su yi miki wata maganar banzar ba." Nace 'a'a hirar su suke yi. Yace "Ba wata hirar su, yarinyar nan bazata faɗa bane Allah ka ɗai ya san abinda su ka yi mata." Na kalli Hajiya wadda ta zuba min ido. Nace To yanzu kam koma menene ai ya wuce, ni nayi musu uzri domin babu daɗi kana son abu ka rasa shi, sannan ka ganshi a hannu wani kuma wanda ka ke ganin bai kai ya samu ba,kuma ace ya zama nasa,kai kuma shari'a ta shata maka layi da shi. Ni na yafe musu, kuma don Allah ku yafe musu ko domin albarkacin 'yan yaransu.
Suka kalli juna yace "Kinji ko Hajiya, yarinyar nan a kwai ta da ƙume abu a zuciya, to kafin mu yafe sai ki faɗa mana abinda suka ce."
Hajiya ta ɗaga masa hannu, sannan ta ce an yafe musu, Allah ya yi miki albarka.
Na soma tunani cewa ƙarya ne baya nema da Naman Anisa, domin na bincike wayar shi babu alamun sunan ta duk da cewa akwai lambobin da ya ajiye su da haruffa.
Kwanaki uku bayan wannan badaƙalar sai Hajiya ta aiko Juma musamman ta kira ni, na zo,tace min "Abinda ya sa ta kirani,tana son ne ta min wani taimako ta min gata, amma tasan cewa bazan faɗawa Shamaki ba." nace To, tace "Nasan kina samun komai a gidan nan tafannin ci da sha haka ne?" Nace haka ne. Tace "Amma baki da kuɗi ko taro mijinki baya baki ko sisi ko yana baki?" Nace baya bani. Tace "To zan saka dire ba zai kai ki gidan wani malami zan biya shi zai miji aiki yadda zaki samu damar karbar wani abu a gurin shi." Na ɗago kai cikin mamaki na kalli Hajiya. Tace kina mamaki ne ko?" Babu abin mamaki ina son ya zama sai yadda ki ka ce masa zai yi, kuma zaki nesan ta shi da waɗan can mata.Ina jin takaici iyayenki ya kasa yi musu wata kyauta a matsayin shi na ɗan Alhaji Baita." Ina son ya sai miki mota ki ke hawa da kanki." Yanzu dai je ki shirya." Na tsurawa yatsun kafa ta ido ina kallo,nazarin maganar Hajiya nake yi, kamar ba ita ba mai mugun son ɗanta da ɓoye laifin shi ita ce zata ce wai in mallake shi kuma ita zata biya.
Bana zaton za a samu wata uwa ko da mahaukaciya ce da za ta aikata hakan. Wata zuciyar ta ce ko kuma duk cikin gwajin ne. Hajiya ta katse ni. Ki tashi ba'a.bori da sanyin jiki.
Na sunkuyar da kai nace Hajiya ki yi haƙuri, ba sai mun yi masa haka ba, bani da bukatar kuɗi a hannu na, domin yana yin komai yadda ya kamata,rannan cewa ki kayi ya bani abin barka na gidan abokinsa kuma ya bani na kai. Iyaye na kuwa aure suka turo ni suka faɗa min cewa ibada ce zan yi har ma suka tabbatar min anan zan samu aljanna baza su yafe min ba in har suka ji layin da na koma.
Kuma Hajiya yana yi miki biyayya ni kuma yana sona, don Allah kar mu yi masa komai ba zan iya cutar da shiba. Harara ta jeho min, sannan tace Kin Fini sanin abinda ya dace ne?" Nace a a,tace to duk ranar da na saka lokaci dole kije ayi masa wannan aikin." Na ɓata rai ban kuma magana ba. Tace ni kike ɓatawa rai dan zan taimake ki da dangin ki." Tashi ki bani guri. Na miƙe na tafi ina mamaki.
Wai Hajiyar da na sani ce kuwa,kai abinnan fa da ban tsoro. Sam ban faɗawa shamaki ba,sai dai Hajiya na ɗan ja jiki da zuwa gurinta isai in yana gurin, duk da cewa bata sake yi min maganar ba. Umman mu ta sanar da ni tana son ta zo ranar lahadi domin ta ga ɗakina tunda bata taɓa zuwa ba, nace Allah ya kai mu. Da dare ina yi wa Hajiya tausa suna hira da Shamaki nace Yawwa Hajiya Ummana tace zata zo ranar lahadi ta ziyar ce mu. Ta ɗago ta dube ni "Wace ce Ummarki?" Yau ne naji na fara jin haushin Hajiya domin zan jure ni amin komai amma bazan jure a ci zarafin iyayena ba. Shamaki yace mahaifiyar su mana. Ta kalle shi "Ta sanar da kai kenan?" Yace nasan dai ita ce Umman su.. Na kasa ɗago kai dan haushi. Yace Allah ya kaimu amma dai harda su Jamila zata zo ko?" Ya tambaye ni,kamar yana son ya gane ko raina ya ɓaci ne ko kuma ya san cewa ba ayi min adalci ba. Hajiya tace "Yaushe ki ka ce ma?" Na dube ta cikin murmushi takaici nace Hajiya ka wai zance ta barshi ba sai ta zo ba in zuwan nata akwai wata damuwa ne, ni sai in saka lokaci inje ta ganni. Hajiya tace "Tace yi 'yar dariya tare da faɗin yau dai na ga hassala a fuskar ki Rabi'atu ba yadda za a yi mahaifiyar ki baza ta zo gidan ki ba, domin gidanki ai nata ne. Sai ki faɗi abinda ya kamata a bata in zata tafi." Nace ba sai an bata komai ba Hajiya, ita kawai zata ziyarce mu ne.
A ɗaki Shamaki yace ki yi hakuri banji daɗin yadda Hajiya ta yi ba." Nace haba ya wuce ka wai. "Yace ki tuna min ana gobe zata zo,nace nan da kwana uku ne zan tuna maka.
Yace "Ina ta son mu yi wata magana kuma ina ta tunanin ta ina zan ɓullo wa lamarin ne.." Nace ka faɗa min mana. Yace kin san maganar Azima?" Nace wace maganar a ciki ta auren ku, ko ta ɓarin da ta yi? Ya zaro idanun cikin rawar baki ya ke tambayar "Waya faɗa miki?" Na kama tafin hannun shi na sarƙafe cikin nawa nace nifa 'yar gidan nan ce karka manta, dole zan sani, amma ka sani wajibi ne in rufe duk wani sirri na gidan aurena, wannan amana ce. Yace "Amma me kika sani game da ɓarin da ta yi?" Nace bansan komai ba banda ɓarin. Yace "An saka auren mu wata huɗu ina fatan baza ki shiga damuwa ba." Yawun baki na ya tsaya cak. Gaban sai wani irin duka ya ke yi. Na saɓule hannu na daga na shi, nace a haba ba wata damuwa Allah ya baku zama lafiya, amma dai ita ma a gidan nan zata zauna? Yace "To shine dai har yanzu ba mu gama tattaunawa da Hajiya ba." Hawayen da nake ta riƙewa ya kwaranyo min kafin in goge har ya gansu, ya tashi ya je ya kulle ƙofar ɗakin shi ya zare makulin ya saka a aljihu. Ya zo ya zauna kusa da ni ya saka hannu ya ɗago fuskata ya saka yatsa yana share min hawayen yace "Nasan zaki fice ki tafi dakin ki ne kije kiyi ta kuka, bayan kin yi min alƙawarin baza ki ɗaga hankali ba." Na kirƙiri murmushin yaƙe, hawayen suna sake kwaranya,nace kayi hakuri ina ta ƙoƙarin inga cewa na tsaida hawayena amma na kasa. Yace, "Karki damu fa, ko mata nawa zan kawo Baby kinsha gaban kowace a zuciyata, kuma Baby ke ce mace ta farko da nake shakkar in ganta a damuwa bayan Hajiya. Ki tattala hakan Baby ina da tabbacin za muyi rayuwa mai tsawo da tsawon rai." Ya ɗago fuska ta muka haɗa ido "Kinsan me yafi damuna?" Na girgiza kai, ya kai hannu ya ja doguwar rigata ya zura hannu ya shinfiɗa shi a tafin cikina, na ƙosa inga kin samu ciki,na fara tsoron ko akwai wata matsala." Nace duka wata uku da kwanaki ai ba 'a jima ba." Yace "An jima mana, mace bata wata a gidan nan sai ta ɗauki ciki fa." Nace to muyi addu'a jinkirin ya zama alkhairi kuma duk ga yara a gidan. Yace "Wallahi ban taɓa samun kai na da son ganin mace da ciki kamar ke ba." Nace Allah ya bamu masu albarka.
Koda ya ci gaba da sarrafa ni domin biyan buƙatar sa yanayin kishi bai barni na taimaka masa ba kamar yadda muka saba, hasali ma hawaye na na ci gaba da zubdawa har ya samu kansa. Ya dube ni yace "Yau dai ni nayi kiɗa na da rawata ko Baby?" Nace kamin afwa da uzri. Yace shike nan muje muyi wanka.
Gaskiya ina da kishi mai yawa ƙiriƙiri na kasa bacci kuma duk da na tashi na yi sallar dare na faɗawa Allah damuwa ta hakan bai hana zuciyata saƙamin cewa in nemi saki daga gare shi ba. To amma ya zanyi da wutar sonshi da ke ruruwa a zuciyata.
Ranar Lahadi tamkar ranar salla ce a gurina tun safe kowa na gidan ya fahimci hakan Shamaki ya ce to in har Umma zata zo da wuri zata iya samu na, nace bari in kira inji. Jamila na kira na tambaya ta ko da wuri Umma zata zo, sai tace sha biyu zata zo ta dawo ƙarfe biyu.
Ɗaya saura wayar ɗakina ta yi ƙara,na ɗaga Hajiya tace "Ki zo ga Ummanki da murna nace To.
Na fito da sauri ina shiga sam na manta da kowa ita kawai idanun na ke gani a falon naje na rungume ta ina faɗin Oyoyo Umma. Tace "Kai jama'a to ɗagani mana. Na tashi na zauna muka gaisa, na kalli Hajiya wadda ta zuba mana ido tana murmushi. Tace "To kije ki ce Juma ta kawo mata abin sha da abinci." Nace Umma ina su Jafar ke kaɗanki wai ki ka zo? Tace "Abbanku ya hana." Nace Allah sarki ina son in gansu. Na tafi gurin Juma nace a kawo wa Ummanmu abinci. Tace "Au dama Ummanki ce baƙuwar da Hajiya ta sa ayi wa girki na musamman? Lallai ke da alamu kina samun shiga a gurin Hajiya,ko kuma ku ƙarawa malamin ku sadaka domin ina ganin canje canje a gurin Hajiya." Nace ki kawo mata abincin yanzu. Tace "To za 'a kawo yanzu, ɗakin ki za"a kai ko kuwa gurin Hajiya? Ina ki ke ganin zai fi dacewa? Na tambaye ta. Tace "Tunda ki nemi shawara za a baki tsaya kinibibin cewa a kawo musu ɗakin ki ba, a kai mata gurin Hajiya su yi hirar su ta manya. Sannan kar ki tsoma musu baki wai domin kinga Ummanki, abu na gaba ki jira har sai Hajiya da kanta tace Ummanki taje ta ga ɗakinki. Nace Na gode Baba Juma. Na dawo na zauna a gefe shi Shamaki ma ya shiga ciki. Nace Hajiya suna shiryo abincin. Hajiya ta zura min ido tana tambaya ta. Ɗakin ki za'a kai mata ne?" Nace A"a nan dai gurin ku ko Hajiya..Juma ta zo tana jerewa. Umma tace kayya sai da na gama abinci na taho a ƙoshe nake. Nace haba Umma ai dai ko yaya kyaci abincin gidanmu. Hajiya tace "Ai wajibi ne ma ki ɗauki plate ki zuba mata, sai kije mijinki ya shiga ciki zai shirya ya tafi kasuwa." Umma ta yi karaf ta ce kije ki sallame shi zanci kafin in tafi yanzu dai bana jin yunwa. Nace to. Na tafi da sauri, na same shi yana waya da wasu kwastomomin shi ya ce zai fito nan da awa ɗaya.
Na buɗe durowa na fara zaɓo mishi kaya, ya kamo ni "Zo nan mana kinsan yadda ki ka fito da murna da tsalle ki ka faɗa jikin Umma ina kallon ki sai naji kawai ina bukatar ki, dama yanzu zanje in kira ki. " Cikin mamaki nace haba dai aiko ka ɗaga min ƙafa yau ɗaya Ummana ta zo tana gidan fa kuma ba jimawa zata yi ba, yace ai nima ba jimawa zamu yi ba...
0 comments:
Post a Comment