BINTU Part 001
BINTU Part 001 . (Ayimin afuwan rashin zuwan Yar Fillo, Allah bai nufa ba adalilin binciken da ba'a kammala yi ba akan abinda ya shafi sak'on da akeson isarwa. A cigaba da tayamu addu'a...Allah Yayi mu fidda litattafanmu.. Ameen..) 'Yar budurwa ce mai shekaru goma sha bakwai a duniya, kana ganinta ka san rainon k'auye ce. Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa holan. D'inki na zamani ya zauna d'abas a jikinta, maimakon ta d'ora d'ankwalin sosai, sai ta rufe gashinta gami da sak'alo jelolin d'ankwalin ta wuyanta ta k'ullesu. Fuskarta fayau babu ko d'igon kwalli, wannan ya janyo bayyanar 6acin rai k'arara a saman fuskarta. Ita kam an takura rayuwarta a birni, Mami ta hanata shafa ko hoda, a ganinta ta kai minzalin da ya dace ace tana kwalliya, tana tsayawa da samari kamar sauran k'awayenta da ta barosu a k'auye, duk domin a matsawa rayuwarta da karatun bokon da ta tsana, na islamiyyar ma da ya Innarta ta ke turata ballantana wani bokon nasara. Ta ja tsaki a daidai lokacin da ta k'araso babban falon Mami na saukar bak'i don kiran Anti Asma'u, kamar yanda Mamin ta umarceta. Saidai me? Ta yi turus ganin Anti Asma'u zaune tare da Yaya Ma'aruf a gefenta suna hira cikin murya k'asa k'asa. Ta gwalalo ido ganin Yaya Ma'aruf ya saki fuskarsa sosai sai faman doka murmushi yakeyi har hak'oransa sun gaza 6uya. Ta dubi tazarar dake tsakanin masoyan biyu, ba wata tazarar azo a gani ba, kai zaman ma da sukayi ya 6aci. "Tab! Ana iskanci a birni." Ta fad'a cikin k'ank'an da murya. Ta bud'e baki zatayi magana sai kuma ta fasa ganin Yaya Ma'aruf ya rik'o hannun Anti Asma'u, da saurinta ta sanya hannu ta rufe bakinta gami da k'ara la6ewa jikin kakkauran labulen dake a falon wanda ya hanesu ganinta, hakanan ko kad'an basu ji motsinta ba. Abin mamaki, Anti Asma'u ko a jikinta, sai ma dariya da takeyi har tana k'ok'arin fad'awa jikinsa. . Aikuwa tayi wuf ta fito daga ma6oyarta. "Innalillahi!" Ta fad'a da k'arfi tana mai d'ora hannuwanta a ka, a firgice suka dubeta, sam basuji motsinta. Ma'aruf ya ja mugun tsaki. Sam! Ya k'i jinin yarinyar, bata da kan gado. Ita kuwa tuni ta soma ja baya zata fice, ai kuwa kamar yasan niyyarta ya yi azamar mik'ewa ya cafkota. Ta runtse ido. "Wayyo na shiga uku! Don Allah Yaya Ma'aruf kayi ha.." "Shii!!" Ya dakatar da ita ta hanyar sanya yatsu biyu a saman la66ensa. Ya zaro idanuwa yana dubanta fuskarsa a murtuk'e, ita kuwa Anti Asma'u tuni ta mik'e tsaye ta zari mayafinta gami da gyara zamansa sosai a jikinta. Babu inda baya rawa a jikinta, tana bala'in tsoron Yaya Ma'aruf, domin ko kusa baya shiga sha'aninta. Tafison Yaya Rufa'i sau dubu akansa. Haka kuma sunfi shak'uwa. Durk'usawar da yayi a gabanta ne ya sanyata k'ara rud'ewa, kallo d'aya tayiwa fuskarsa tayi saurin mayar da dubanta ga Anti Asma'u wacce ke k'ok'arin ficewa, daga falon da saurinta, da alamun kunyar ganin da Bintu tayi musu a tattare da ita. Jin ya kama kunnenta da k'arfi ne yasa ta sakin k'aramin k'ara, k'afafunta suka d'auki rawa tana mai runtse ido don azaba. "Wayyo, don Allah kayi hakuri Yaya, wallahi bazan k'ara ba." "Tun yaushe kike mana la6e?" Tuni ta soma hawaye, sai k'aramin tsalle takeyi amma bai saketa ba. Dakyar ta girgiza kai cikin muryar kuka ta amsa. "Ni ba la6e nakeyi muku ba, Mami ce ta turoni kiran Anti Asma'u, kwarankwa..." Ai bata k'arasa ba ya make bakin, bayan ya saki kunnen. "Ban hanaki wannan rantsuwar ba? Idan na k'ara jin kin min rantsuwa da kwarankwatsa sai na 6allaki. Sannan ki bud'e kunne ki saurari kashedin da zanyi miki." Ta bud'e idanu tana dubansa, sai kuma tayi saurin sadda kanta tana mai cigaba da kuka ciki-ciki. "To." Ta fad'a, ya jinjina kai. "Good." Ya mik'e ya koma saman kujera ya zauna kafin ya dubeta. "K'araso nan ki durk'usa." Ba musu ta k'arasa ta durk'usa fuskarnan kamar kace "Arr!" ta arce. . Ya kwashi mintuna k'alilan yana mai danna wayarsa, ita kam ta k'agara ya barta ta tafi. Can kuma ta tsinci muryarsa. "Ko da wasa, ko da wasa naji kina bawa wani labarin abinda idanunki suka gane miki yanzu, sai na yanke kunnuwanki. Kinji abinda nace ko?" Da sauri ta gyad'a kanta, gaba d'aya jikinta rawa yakeyi. "Tashi ki wuce." Abinda takeson ji kenan, da gudu ta mik'e zata fita. "Ke!!!" Ta juyo a firgice. Ya rik'e kunnensa kad'an. "Ko Mami kada na sake naji kin sanarmata." Ta gyad'a kanta ta fice. A falo ta sami Mami zaune tare da Anti Asma'u sai Yaya Rufa'i da 'yar uwarta Aisha da suke sa'annin juna. Ta k'arasa shigowa tana kumbure-kumbure, ga hawaye sha6e-sha6e a saman fuskarta, wannan ne ya katse hirar da sukeyi. Ita kuwa Anti Asma'u gaba d'aya ta rud'e, tsoronta bai wuce abinda zai fito daga bakin Bintu ba. Yarinya akwai fitina, kada ta tonamata asiri. "To sarkin kuka, ke da wa kuma?" Cewar Mami tana kallonta. Bintu ta k'arasa gefen Yayanta Rufa'i ta zauna. Bata kai ga magana ba sai ga Ma'aruf ya shigo fuskarnan a murtuke. Ya nemi waje ya zauna a d'aya gefen hannun Rufa'i. Mami ta dubeshi kafin ta k'ara duban Bintu. "Bintu keda wa? Me ka yi mata yau kuma?" Ta maida zancen kan Ma'aruf, sun san kukan Bintu, bai wuce adalilinsa. Shine kawai tasu bata zo d'aya ba a gidan, baya ragamata ko kad'an. Ya d'aga kafad'a "Rashin kunya tayimin, na kama kunnenta nayi mata kyakkyawan gargad'i." Bintu ta dubeshi ya harareta da sauri ta k'ara 6uya ajikin Rufa'i. "Haba Yaya, me Bintu zatayi maka mai zafi kayimata hukunci haka? Mami kinga yanda kunnenta ya fashe, da farce ya kama mata." Fad'in Rufa'i kenan bayan ya duba kunnen. Ransa duk babu dad'i da abinda yayansa ke yiwa Bintu, kamar ba jininsu ba. "Zo mugani." Ta k'arasa ga Mami. Bayan Mami ta ga wajen, ta dubeshi cikin 6acin rai, "Kai dai baka kyautawa abinda kakeyi, to wallahi ka kiyayeni. Koda wasa kada ka k'ara yi mata hukunci irin wannan. Ni ban yarda ma da abinda ka fad'a ba, nasan halin yarinyar nan, bata da tsiwa..." Sai kuma tayi shiru, ta girgiza kai ta kalleshi "Koda tana da tsiwar ai ba yi maka takeyi ba inace dai?" Yayi shiru baice uffan ba, ganin da gaske Mami ba shirun zatayi ba yasa ya mik'e ya dubeta. "Kiyi hakuri Mami." Ta kauda kanta kawai ta maida ga Asma'u. "Tafi da ita d'akina, akwai mentholata ki shafa mata." A kunyace Asma'u ta mik'e, Bintu na kallonta. A ranta tana fad'in. "Oh, dan Allah ji yanda take sunne kai yanzu, hum." Bayan shigarsu d'akin, ta janye hannunta daga na Asma'u. Anti Asma'u ta dubeta da murmushi sannan ta nufi gaban madubin Mami. Bintu ta hakimce saman stool tana kallonta. Asma'u ta dubeta ta madubi tayi d'an murmushi sannan ta juyo ta dawo gabanta ta durkusa. Ganin haka Bintu ta turo baki gami da dauke kanta, ita haushi take bata ma. "Bintu, bakisan Yaya Ma'aruf mijina bane?" Jin furucinta ya sanya Bintu dubanta baki sagale. Amma a 'yan iskan ma Anti Ma'u ta daban ce. Daman haka miji da mata sukeyi? To duk ba haka ba, ita bata da labarin anyi bikinsu ma, ballantana ta ga Innarta ta halarta. Wannan kawai k'arya ce, abinda Mami ta gayamata ko hannu namiji ya rik'e maka zakayi ciki ka haihu? Lallai ma. "Latsi." Cewar Bintu a fili tana mai jinjina kai gami da jan majina don har lokacin ta kasa sakin ranta. Abin ya kusan bawa Anti Asma'u dariya, ta gimtse. Shakka babu, an d'aura mata aure da Ma'aruf wajen watanni uku ma, akwai dalilan da yasa ba'ayi tariya dai. Ta mik'e sanin da tayi ba ganewa zatayi ba. Ta lakuto man ta nufi kunnen tana fad'in "Yayanki mijina ne, ya ci ace a shekarunki na sha bakwai kinsan menene..." Sai kuma tayi shiru, Bintu babu kan gado, ba k'aramin aikinta bane ta nufi Mami da tambayoyi. Ita kam, ta fasa yini yanzu zata zo ta wuce tun kafin tayi mata wata ta6argazar. Kamar kuwa ta sani, Bintu gaba d'aya ta jefa kanta kogin tunani. Ta hau cin farcenta, wai aure, ta k'ara tunano abinda ta gani, ta girgiza kai kamar wacce ta watstsake daga bacci ta dubi Anti Asma'u. Ai da sauri itama ta dakatar da ita. "A'a, karki k'ara wata magana zan had'aki da Mami. Idan kiga bari ta ji wannan maganar dukanki zatayi, Mami ta tsani la6e." Ta numfasa kawai ta kyaleta. * * * Zirga-zirga kawai Bintu keyi a d'aki, a fili take magana. "Na tambayi Yaya Rufa'i?" Ta girgiza kai. "Kai a'a, kada shima ya zaneni." Ta zauna gefen gado tana cin farce, cikin ikon Allah sai ga Aisha ta shigo tana kiranta. Ganinta yasa tace "Au, kizo wai zamuje siyo takalmin sallah inji Yaya Rufa'i." Ai da sauri ta mik'e, ta janyo hannunta. "A'i, au yi hakuri namanta, Aisha, gayamin wani abu." Aisha ta nutsu ganin yanda fuskar Bintu ta nuna dagaske tambayar zatayi babu alamun shashancin nan tattare da ita. "Mene?" . "Anti Ma'u da Yaya Ma'aruf wai an d'aura musu aure?" "Lallai, baki da labari? Ai tun kafin ya tafi bautar k'asa akayi aurensu. Nan gaba zaayi biki. Ai Inna ta sani." Bintu dai bata gamsu da wannan kad'ai ba, saidai ta chanja akalar tambayar daga wacce tayi niyyar yi a farko. "To gayamin, ai Mami dagaske takeyi idan namiji ya kama hannuna zanyi ciki ko?" Aisha ta tuntsire da dariya, bata mantawa, itama Mami ta gayamata haka a baya, don kuwa ta zama budurwa tun tana da shekaru sha uku a duniya, watakila kuma hakan yana da nasaba da cimarsu da yanayin hutun da jikinsu ke samu, idan an ajiye wannan ma, Aisha Allah Yayi mata baiwar hankali, hakanan tana da ilimin addini daidai gwargwado, ana koyardasu duk wadannan hukunce-hukunce da sauran abinda ya dace su sani a addinance. "Ke Bintu, ana fad'a ne fa kawai don a tsoratar. Ni ki kyaleni da wadannan tambayoyin, Yaya na jiranmu kada yayi fad'a." Ta wuce da sauri don d'aukar mayafi. "Toh amma.." Ta katse maganar da tayi niyya sakamakon tunawa da gargad'in Yaya Ma'aruf gareta. "Ki dauko mayafi, zamu biya mu sauke Anti Ma'u a gida sai mu wuce." Dole ta nufi kayanta itama, bayan sun shirya suka fito, a tsaye suka sami Yaya Rufa'i da Mami, tana ba shi sak'o. Aisha ta ja hannunta, "Zo muje wajen Anti Ma'u mu jira tana waje." Suka fito, saidai a 'yar baranda suka iskesu da Yaya Ma'aruf, da sauri Bintu ta tsayar da Aisha suka la6e kad'an. A ranta tana fad'in asirinsu dai zai tonu yau idan itama Aisha ta ga sunyi wani abin. Yaya Ma'aruf sukaji yana fad'in. "Banyarda da wannan satar kallon ba na gulma, ke har yau kin kasa sakin jiki ki dunga kallon kwayar idanuna sosai..." Basu kai ga jin k'arashen ba, Aisha ta figi hannun Bintu suka koma baya. "Wallahi babu kyau la6e ba ruwana, kenan d'azu ma la6e kikayi ya kamaki ko?" Ta harareta "Banza, so nakeyi kiga wani abu amma basuyi ba kika wani janyoni, zo mu koma kigani." Ta rik'o hannun Aisha, Aisha ta fisge ta k'ara janta baya. "Wallahi baruwana, bazamu koma ba." "Ke bakiji wani iskanci ba ma, wai ta kalli kwayar idanunsa. Nasan harararnan zaiyi mata." Aisha tayi dariya. "Ashe na fiki sanin abubuwa Bintu, lallai ke da sauranki. Ai kallon soyayya yake nufi. A shirin RAI DANGIN GORO naji Ahmad Isa yana fad'a, wai da saurayin ya kalleta saida ta ji yarr, wai ta sauke idanunta saboda ba zata jure kallon kwayar idanunsa ba." Bintu ta tuntsire da dariya. Yi takeyi tana k'arawa. "Rainin hankali. Kalleni to mugani." Ta gwalo mata idanuwanta, Aisha ta ja tsaki tana dariya. "Ke dallah, sai da namiji wanda kakeso." Bintu banda dariya ba abinda takeyi don abin dariya yake bata, suna tsaye sai ga Yaya Rufa'i. "Au, maimakon ku shiga mota kuka tsaya anan?" "Yauwa Yaya Rufa'i. Muga ida..." Da sauri Aisha ta toshe mata bakin tana dariya. "Ke wallahi ba'a sirri dake. Sirrine fa." Yaya Rufa'i yayi dariya. "Menene abin? Yau kuma ni kuke yiwa 6oye-6oye?" "Yaya ba haka bane, sirri na bata ai babu kyau fad'awa wani kuma." "Shikenan ai, ku muje, inaso naje amso d'inkuna na ne." Suka kama hanya, har lokacin Yaya Ma'aruf na tsaye da Anti Asma'u. Yaya Rufa'i ya tambayeshi "To, ko mu tafi zaka kaita?" Yaya Ma'aruf ya gyad'a kai, "Yeah kuje kawai." Bintu ta kalleshi, ya bita da harara ta dauke ido. Wai wannan idan Anti Ma'u ta k'ura mishi ido, ai sai ya sanya ta firgice. Koda sukaje nan ma Bintu saida ta tsaya ruwan ido, a k'arshe ta za6o mai shegen tsini, duk yanda Yaya Rufa'i da Aisha suka so hanata d'aukarsa ita kuwa ta dage lallai shi takeso. Dole suka kyaleta, ganin haka ya k'aro mata da wani flat mai kyau da rangwamen kud'i. Murna ya cika Bintu har gwalo take yiwa Aisha. "Wani abin ma sai gobe." Aisha tayi dariyar mugunta "Zakiyi bayani ne." * * * RANAR SALLAH...! . Tun bayan sallar asuba, Bintu bata koma bacci ba. Zama tayi tare da su Mami dake aikin girke-girken sallah tana tayasu da hira. Ko a k'auyensu babu abinda take tsinanawa innarta duk kuwa da faman da Innar zatayi, saidai tayi ta gaji. To zuwanta ne ma wajen Mami abin ya d'anyi sauk'i. "Mami, wai bazamu idin ba?" Mami wacce ta riga ta gama gundura da wannan maimaicin tambayar da Bintu ke yi mata, ta bata amsa a fusace. "Bansani ba, ke wai bakisan abinda ya kamata ba? Tashi ki bar nan tun kafin na 6ata ranki." Ta mik'e tana zum6ure baki, Atine da Magajiya masu taya Mami hidima suna dariya. Tana shiga d'aki ta nufi wajen kayanta dake a goge a ninke. Bayan ta gama shafasu ta janyo takalminta ta gwadashi a karo na shida tun bayan da aka siyo. Kwas kwas d'in da takalmin keyi ne ya tayar da Aisha daga bacci. Ta dubeta tana mutsistsika idanu kafin ta ja tsaki tayi mik'e. "Kedai wallahi kamar na kwasheki da mari nakeji, duk kin wani ishi mutane tun siyo takalmin nan." "Sai ki mareni idan kin isan." Cewar Bintu tana k'ok'arin dafe bango ganin tana neman kaiwa k'asa. "Ki tashi ki shirya, Mami tace Abba ya shirya." Ai da jin haka Aisha ta mik'e zaune. "Dagaske? Ke meya hanaki wankan?" "Kaya kawai zan saka." Hakan da ta fad'a yasa Aisha mik'ewa ta fad'a band'aki. Bayan fitowarta, itama ta soma k'ok'arin shiga. Daman batayi, wankan dai tafiso Aisha ta soma." . K'arfe bakwai, sun gama shiri tsaf. Bintu dole ta bari Aisha tayi mata kwalliya da d'aurin d'ankwali, saidai duk da haka, saida tayi d'igo a goshinta hakan bai hanata fitowa tsaf tayi kyau ba. Shadda ce a jikinsu fara tas, ta sha aiki mai duwatsu. Aisha sai kallon Bintu take. "Ke sai naga kamar fa kin fini yin kyau." "To uwar ba'a, yanzun ma shi kikeyimin? Ke da kike fara tas, menene abin gani a yaba wajen bak'ak'e. Ai dole ma nan gaba na soma kwailin." "A wane gidan?" Suka tsinci muryar Mami wacce sam basu kula da shigowarta d'akin ba kasancewar k'ofar tasu a bud'e take. Ta k'araso ciki, itama shaddar ce a jikinta saidai kala da ta bambanta don ita ruwan k'asa ta sanya, iri d'aya da mijinta, bawani ado sosai ta yiwa fuskarta ba. Sunyi zaton fad'a zatayi, sai kuma ta saki fuska tana dubansu. "Inye, kaga 'yanmatan Abba, to ko ku fa? Bintu har kinso ki fini kyau ni d'inma. Kalarki mai kyau ce kada na k'ara jin kinyi zancen wani shafe-shafe." Bintu ta amsa da toh tana mai washe baki na jin dad'in yabon da Mami tayi gareta. "Toh sai ku fito ga 'yan uwanku da Abbanku duk sun kammala shiri." Kowaccensu ta dauki mayafinta wadatacce ta yafa. Aisha ta dubi Bintu baki bud'e ganin tana k'ok'arin zura takalmi. "Wai dagaske takalmkn nan zaki sanya?" "Me zai hana kuwa? Lallai ke d'innan kina wasa da Bintu." Tuni ta zura tana k'ok'arin daidaita tsayuwarta. Aisha ta girgiza kai. "Wallahi ki chanja ki sanya d'ayan nan, ina jiye miki ki fad'i." "Jikinki ko jikina? Kudai 'yan birni kun maida mutanen k'auye wasu da basu da wayewa. Tunda ke bazaki iya tafiya da shi ba sai ki bar wad'anda zasu iya suyi ai." Daga haka ta nufi k'ofa tana taku gaba d'aya a takure. "Ke muje." Suka fito. A nan farfajiyar gidan suka tarar da su Mami na k'ok'arin shiga mota. Abba yayi murmushi ganinsu. Suka gaisheshi. "Lallai, yaran Abba sun fito. Kamar ba ku ba." Sukayi dariya kawai. Ita dai Bintu da sauri ta fad'a mota sakamakon takalmin dake neman kayar da ita. Mami ta girgiza kai. "Bakya ji Bintu, kinason wahalar da kanki." Yaya Rufa'i yana dariya yace "Barta Mami, jiki magayi." Bintu ta d'ago ido da zummar kallon Yaya Rufa'i, saidai cikin rashin sa'a suka had'a da Yaya Ma'aruf, abin mamaki yau kam babu hararar, kallon sak, kallo d'aya ya maida kansa ga tuk'i. Motar tayi shiru sai kabbara da kowanne keyi a hankali, wato(Allahu Akbar Allahu Akbar, La'ilaha Illallahu Allahu Akbar, Allahu Akbar walillahil hamd) kamar yanda sunnah ta koyar. Bintu wacce bata iya sosai ba, sai mus-mus da baki. A karshe sai ma ta matsa daidai kunnen Aisha. "Ke, wallahi Yaya Ma'aruf yayi min kallon arziki yau. Yayi kyau sosai." Aisha ta harareta kawai, hakan yasa ta dauke kai tana kalle-kallen gari. Takalmi kuwa tuni ta tu6eshi tana hutawa. . Kuka har da sheshshek'a takeyi sakamakon marin da ta sha a hannun Yaya Ma'aruf a dalilin take mishi yatsu da tayi da takalminta, Mami bata ce komai ba ta bi mijinta wanda ya rigasu shigewa gidan, ba'a gabanshi akayi marin ba. Ita kanta yau Bintu ta 6ata mata rai, har kusan fad'awa tayi kan wata tsohuwa wajen idi, tsohuwa ba hakuri tayita 6a6atu, saida Mami ta sanya baki tayi shiru. Mami ta dakawa Bintu tsawa akan maza-maza ta cire takalmin ta rik'eshi a hannu saidai tayi tafiyar haka. Bintu ta k'ara rushewa da kuka, tana murnar Mami bata doketa ba, yanzu gashinan ta takewa Yaya Ma'aruf yatsun k'afa ya mareta. Haka tayi cikin gidan, Rufa'i na kwala mata kira don ya rarrasheta amma ko juyowa batayi ba. Tana zaune tana kuka da jaye-jayen Allah Ya isa, Aisha kuwa banda dariya babu abinda takeyumi mata. Tun Bintu na jin haushinta har itama ta hau dariya tunanowa da yanda ta dage akan takalmin. Tayi kwafa. "Allah kuwa sai ma na tonamai asiri." "Asirin me?" Cewar Aisha. Bintu ta k'ara yin kwafa. "Kedai ki zuba ido." Kiran da Mami ta kwala musu ne ya katse hirar. Bintu tace ita babu inda zata je. Haka Aisha ta fice ta barta. Bata fita ba saida Mami ta shigo da kanta ta d'an yi mata fad'a kafin kuma ta sauko tana rarrashinta, haka ta fito tana zum6ure-zum6uren baki. Anan saman kafet ta tarar da kowa har Abba anyi zaman cin cin abinci. Ta dubi Yaya Ma'aruf ta dauke kai, a ranta tana fad'in. "Ai sai na tonamaka asiri kwanan nan, d'an iska kawai." Abba na murmushi yace "Haba Bintu, wanene ya ta6aki? Zo ki gayamin." Ta k'arasa ta zauna, saidai bata iya cewa komai ba ganin Ma'aruf. Suka soma cin abin, Abba na janta da hira har ta sake. Bayan sun kammala, ita da Aisha suka kwashe kwanukan suka nad'e ledar cin abincin sukayi kicin. Ranar sun sha yawo tare da Rufa'i. . * * * Washegari sai wajejan k'arfe goma Bintu ta farka. Ta kasa kunne sosai jin hayaniyar mutane daga falon Mami. Hakan yasa ta fito daga ita sai riga da wando na bacci. Ta d'an la6e, tana kyallara ido ta gane duk 'yan uwan Abba ne, babu wacce ta soma ganewa sai Anti Ma'u. Kwafa tayi, har cikin ranta ta ji dad'in ganinta, a fili tace "Yau asirinku zai tonu." Ta koma ciki ta fad'a wanka itama. Bayan ta fito tayi kwalliyarta harda jagira irin k'atuwar nan saidai nata yayi girma da yawa. Ta dubi matar jikin kwalin eye shadow, ta dubi kanta kafin ta ja tsaki, ba iri d'aya bane kwalliyarsu. Cikin ikon Allah, sai ga Aisha ta shigo. Tana kallon fuskar Bintu ta soma kyakyata dariya. Bintu ta hau tayata. "Don Allah zo ki yimin kwalliya wacce ta ci uban ta jiya. Yau zan nunawa wata bata da wayo." Aisha ta saki baki ta kama"Toh, wacece kuma?" "Baruwanki Malama, yimin don Allah." "Goge, ke wanke fuskara gaba d'aya." Da gudu-gudu ta fad'a band'akin ta wanko ta dawo ta zauna. Cikin kwarewa irin na Aisha, da baiwarta da Allah Yayi mata na iya tsantsara kwalliya tayi mata kwalliya gami da sanyamata eye-shadow wanda a baya sam Bintu bata amincewa ta sanya. Ai kuwa tayi kyau fiye da zato. Banda "Masha Allah, Subhanallah." Babu abinda Aisha ke ambata, ta k'arashe da "Wallahi kin fi koyaushe kyau tun zuwanki baki ta6a kwalliya irin na yau ba." Bintu tayi farr da ido, kai kace wata budurwar azo a gani ce. "Nasani." Aisha ta kai hannu zata goge mata ta kauce tana dariya. "Au godiya zanyi fa." Aisha zata fita ta tsaidata. "Aramin wayarki." Ta mik'a mata ta fita. Ta hau dannawa, gaba d'aya ta mance yanda Aisha ta koyamata daukar hoto. Ta dire wayar da zummar da zarar ta kammala zataje d'an dolo mai wankinsu ya koyamata don batason Aisha tasan abinda zata aikata. Ta had'e tsaf cikin atamfa ja da fara, d'inkin ya zauna d'abas a jikinta, tayi d'aurin d'ankwalinta na sabo, ta sak'alo jelun wuyanta ta k'ulle. Cikin sa'a sai ga Aisha ta dawo d'akin, tana ganin haka ta gyara mata. Bayan fitarta, Bintu ta fesa turare ta janyo flat shoe din da Rufa'i ya za6omata ta sanya. Aganinta bayar da kai ne ta fad'i a gaban Anti Ma'u, ita daman sam jininta bai had'u da ita ba, sai kuma yanzu ta k'ara gano silar rashin had'uwar jininsu, 'yar iska ce. Ta d'auki wayar Aisha ta fito da niyyar zuwa wurin d'an dolo. . "A'ah Bintuuu!!" Fad'in 'yan matan kenan sa'anninta. Kasancewar gaba d'aya sun santa. Tayi musu murmushi kafin ta k'araso kamar wata mutuniyar kirki ta zauna. Nan suka gaisa, ko kallon Anti Ma'u batayi ba. Har saida Anti Ma'un tayi magana. "A'a, Bintu yau abin ba magana?" Sai lokacin ta d'an yamutse fuska tace "Ina wuni." "Bazan amsa ba tunda saida na rok'a." Fad'in Ma'u cikin fushi, bata ga abinda ta tarewa yarinyar nan ba da ta tsaneta. Ta kusa daina shiga harkarta. Bintu ta mik'e tana dariya. "Ina zuwa." Bata saurari kowa ba ta fice daga falon tana wani jijjiga jiki a dole tafiyar Ma'u take kwaikwaya. Aisha dariya ta su6uce mata sakamakon ta fahimci ko da wa Bintun take. Ma'u ta gane saidai ta basar. Tana fita harabar gidan fa nutsu ta soma tafiyarta sak. Ta dubi hagu da dama, bata hango d'an dolo ba, dole tayi gaba wajen maigadinsu. Yana ganinta ya washe baki. "A'a, d'iyata, wannan cakarewa haka?" Bintu ta rik'e k'ugu tana murmushi. "Nagode Baba, kasan inda d'an dolo ya shiga?" "Ganinan!" Cewar d'an dolo da babbar murya a sa'ilin da yake bud'e kyaure ya sanyo kai, hannunsa rik'e da mp3 yana jin wak'a. "Yauwa, zo muyi sirri." Tayi gaba ya bi bayanta har zuwa wajen shukoki. Ta dubi kusa da su babu kowa, ta mik'a mishi wayar Aisha. "Gwadamin yanda zan d'auki hoto." D'an dolo yayi dariya. "Kai, sau biyar kenan ina gwadamiki. Wane irin kwanya gareki?" Ta harareshi. "Malam idan bazaka koyamin ba, bani waya." "A'a yi hakuri." Ya soma nunamata yanda zatayi, kafin tace bari ta gwada. Ta nunoshi da wayar. "Gyara nayi maka hoto mugani." Yayi tsayuwar DAB😜, ta kyalkyale da dariya kafin ta daukeshi. "Lah kaga ya yi." Suna cikin haka, Yaya Ma'aruf yazo wucewa. Ai da sauri D'an dolo yabar wurin. Ma'aruf ya bishi da kallo kafin ya maido dubansa ga Bintu cikin d'aurewar fuska. "Ke, banyi miki gargad'i ba akan wasa da yaron nan ba ne?" . Ta turo baki, bata da niyyar magana don har lokacin bata bar jin haushinsa ba. Ya matso, ta matsa a tsorace. Ganin yana shirin cafkar kunnenta ya sanyata yin magana babu shiri. "Wayyo, kwa.. Au, wallahi abu ya nunamin. Kayi hakuri bazan sake ba." Ta k'arashe tana dafe da kuncinta. Ya zubamata ido cikin kallon raini. Ganin kamar bai wuce ba tayi magana. "Anti Ma'u ma ta zo." Jin abinda tace ya bashi dariya, hakan ya sanyashi murmushi mai ban sha'awa. Bintu bata ji. Tayi sak'ale tana kallon abin kamar a mafarki har ta saki kuncinta. Ai kuwa ya mintsili kumatun ya ja. "Sa'anki ne ni?" Daga haka ya saketa ta juya sai gida. A ranta tana fad'in. "Yau zan sanyaka kuka ai." Ta k'arashe da dariyar mugunta. Nan ta zauna ta saki jiki anata hira, sai gashi ya shigo. Kowannensu ya gaisheshi. Bintu ta zubamusu ido kamar talabijin, sai wani murmushi suke sakarwa juna. K'arshe yayi mata wata magana k'asa-k'asa sannan ya mik'e ya fita. Fitarsa da mintuna biyu, ta mik'e ta bi bayansa. Gaba d'aya manya da k'ananan 'yan matan irinsu Bintu suka saki shewa. Mami ta fito daidai lokacin tana tambayar abinda yayi musu dadi. "Bakomai." Suka amsa. Bintu ta faki idonsu ta fice ta hanyar kicin. Yau kam komai zai shiga wayarnan. Kai tsaye ta nufi sashen Ma'aruf. Sad'af sad'af take takawa a barandar har ta kai jikin k'ofar. Ai kuwa ta ci karo da takalmin Ma'u. Ta numfasa ta waiwaya bayanta. Babu wanda ke tahowa. Taji k'arar kid'a, wannan ya bata tabbacin koda ta murd'a babu wanda zai ji cikinsu. Ta murd'a k'ofar ta tura a hankali. Ashe dagaske 'yan iskan abinda zasu kuma yi kenan. A tsaye ta hangesu ya yiwa Ma'u kyakkyawar runguma. Hannunta na rawa ta ciro wayar Aisha daga rigarta ta saita ta d'aukesu hoto. Har kala uku, ta ci sa'a akwai wanda fuskokinsu gaba d'aya suka fito sosai. A sannu ta mayar da k'ofar ta rufeta kamar yanda take. Babu wanda ya ji cikinsu sakamakon kid'an dake tashi. Saida tayi nesa kad'an da wajen ta hau kyakyata dariya har tana rik'e ciki. "Zakuyi bayani ne." . * * * Misalin takwas na dare babu kowa a falon Mami bak'o, dukkansu sune. Har Abba yana zaune tare da su ana hira. Can sai ga Bintu ta shigo, bayan tayi zaman dirshan akan gado tayita bincike har ta gane yanda ake bud'o hotuna. Ta dubi kowa tana murmushi. Babu wanda ta ji dad'in gani kamar Ma'aruf. Ya dubeta ta sakarmai murmushi, shima fuska a sake yake kallonta. A yau yana cike da farinciki baison abinda zai dagula lissafinsa. Ta k'arasa ta gaida Abba. Ya amsa fuska a sake. Can ana hira Bintu ta katse ta hanyar kiran sunan Abba. Kowa yayi shiru yana dubanta. "Na'am 'yar Abba, ya akayi?" Cewar Abban. Ta dubi Ma'aruf sannan ta dubi Mami sai kuma tayi shiru. "Bintu ya akayi? Yi magana mana." Mami ta fad'a. "Daman wani iskanci akeyi a gidannan nakeso yau kowa ya ganewa idanunsa." A tsorace Aisha ta dubeta, haka su Abba, abin ya basu mamaki. "Innalillahi, a gidana? Me kika gani?" Ta fiddo wayar Aisha ta bud'o hoton ta mik'awa Abba. "Kagani." Abba ya kar6i wayar yana dubawa. Nan da nan ya daure fuska gami da mik'awa Mami, mik'ewa kawai yayi ya nufi falonsa. . Mami ranta ya 6aci, ga tsananin kunya da ta kamata. Ta rasa wa zata watsawa harara tsakanin Ma'aruf da Bintu wacce sam bata da wayo. Kunya ta sanyata mik'ewa bayan ta bar wayar anan ta bi bayan mijinta. Ma'aruf ya sanya hannu ya d'auki wayar, tuni Bintu ta ja baya a tsorace. Gaba d'aya fuskarsa ta sauya kwarai, farar fatarsa ta koma ja. Ya dubesu. Da sauri Aisha tayi magana. "Na rantse da Allah bansan abinda tayi ba, tace dai na ara mata waya." Gadan-gadan ya nufi Bintu, ya damk'eta kafin ya kwasheta da lafiyayyen mari. Ai tuni ta fasa k'ara. "Wayyo na shiga uku Innata!" "Ma'aruf!" Ya ji muryar Abba cikin tsawa. "Saketa!!" Dolensa ya saketa. "Zo inason magana dakai." Daga haka Abba ya koma ciki, Ma'aruf a kunyace ya bi bayansa. Rufa'i wanda wayar ta koma hannunsa ya goge hotunan gaba d'aya, shi kansa a yau Bintu ta k'ona ransa. Ya ja tsaki ya girgiza kai. "Bintu baki da wayo sam, bakisan ya kamata ba." Ya mik'e tsaye gami da duban Aisha. "Daga yau sai naga wanda zai k'ara baku waya tunda amfaninta kenan a hannunku. Banda abin Abba ma, ina ke ina rik'e waya a shekarunki. Mts." Ya fice bayan ya jefa wayar aljihun wandonsa. A can kuwa Ma'aruf ya sha fad'a kwarai. Abba yace dole Ma'u ta tare a d'akinta babu wani sai ta kammala SS3 kuma. Ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, a k'arshe ya gargad'eshi kada ya kusa yace zai k'ara ta6a lafiyar Bintu, yarinya ce. . Wajejan tara na dare, Aisha d Bintu suna d'aki babu mai kula juna cikinsu. Aisha tana fushi da ita akan ta sanya Rufa'i kwace wayarta, daman sam baya so aka bata wayar, ayau gashinan Bintu ta janyomata. Itama Bintu gaba d'aya haushinsu take ji ganin babu wanda ya goyi bayanta. Ga fad'an da ta ci sosai a wajen Mami akan d'abi'ar da takeso ta mayar da ita jiki, wato la6e. Kuma ta k'ara jaddada mata Ma'u matar Ma'aruf ce. Daga haka ta fice, ko uffan basu cewa juna ba da Aisha har bacci yayi awon gaba da su. Sai zuwa safiya Aisha ta sauko, daman bata kasance mai rik'o ba. Itama labari ta samo wajen Mami cewa za'ayi bikin Ma'aruf bayan sati biyu. Har sunyi magana da Hajiyar Ma'un, itama ta nuna jin dad'inta. Bintu ta mik'e zaune. "Wai da gaske ba'ayi musu fad'a ba?" Aisha ta ja tsaki. "Banza, ai bazaki ta6a ganewa ba. Bud'e kunne ki ji menene aure." Nan ta dunga yi mata karatu dallah-dallah. Bintu tayi shiru tana sauraro. K'arshe ta saki baki da mamakin inda Aisha tasan duk wannan. "A'i wai ina kikejin duk wadannan?" Aisha ta d'aure fuska. "Na gayamiki banason wata A'i." "Yi hakuri, gayamin." "Kinga ga Rai Dangin Goro. Kuma ga whatsapp na matan aure ina ciki. Maman Faruk sunana ma. Amma ko Mami batasani ba." "Kin shiga uku wallahi." Aisha tayi dariya. "Kuma k'awata Safiya Bingel ta koyamin ba." Sukayi dariya kafin alamun tsoro ya bayyana saman fuskar Aisha. "Allah dai ya rufamin asiri na jima da ficewa ciki, da bansan me Yaya Rufa'i zaiyi min ba." Tun bayan faruwar lamarin, ko kallon inda Bintu take Ma'aruf baya yi. Hakanan baya amsa gaisuwarta, a k'arshe ma ya gargad'eta akan kada ta k'ara gaisheshi baya buk'ata. Sannan koda wasa ya k'ara ganinta a sashensu sai ya kakkaryata. Itama tun lokacin ta shareshi. Bayan sati biyu akayi 'yar liyafa sai yini na gida, Ma'u ta tare a gidan mijinta wanda babu nisa sosai da gidansu Ma'aruf. Hatta Innar Bintu wacce kanwa ce ga Mami, ta halarci bikin. Ta ji dadin ganin da ta yiwa 'yarta gaba d'aya ta chanja ta k'ara girma. Matsalar da Bintu ta gayamata guda d'aya, wato karatu. Ita ta gaji da zuwa makaranta gashinan kwata kwata bata da wani basira, bata mayarda hankali. Inna tayita yi mata fad'a, a k'arshe ta rarrasheta da nunamata wataran zata ji dad'in karatun. Jinta kawai tayi, amma sam bata so haka ba, a sonta Inna ta cewa Mami a kyaleta kawai. Babanta ma yazo, shima sai washe baki yakeyi ganin yanda Bintunsu ta koma. Yayita shi wa Mami da Abba albarka yana binsu da addu'o'i na alheri. . * * * Kuka sosai takeyi, ta fito daga cikin motar a guje ta rungume Mami. "Dan Allah Mami kiyi hakuri wallahi zanyi karatu, kada a kaini bodin bana so." Mami ta soma karaya, saidai tana so taga Bintu tayi karatun addini da boko. Shiyasa koda Ma'aruf ya kawo shawarar kaita Bodin batayi musu ba. "Kiyi hakuri Bintu, zaki dunga ganinmu lokaci zuwa lokaci, ga 'yar uwarki nan kuna tare. Kada ki damu kinji ko?" Aisha ta lek'o ta windo tana dariya. "Mami ki kyaleta, seniors zasu jibgeta a banza dole ta nutsu." Mami ta harareta. Dakyar ta rarrashi Bintu, ta shiga mota. Rufa'i ya ja suka tafi. Jss1 aka ajiye Bintu, zatayi repeating. Ita kuwa Aisha ta wuce Jss3. * * * . BAYAN SHEKARU BIYAR...! "Mamina!!" Budurwa mai shekaru sha tara cif a duniya ta fad'a cikin d'aga murya alokacin da ta shigo falon a guje. Mami itama da sauri ta fito daga kicin tana mai cike da murnar ganinta. Ai da sauri ta k'arasa gami da fad'awa jikinta tana dariya, Mami tayi mata kyakkyawar runguma tana murmushi mai bayyana hak'ora kafin ta d'agota. . "Bansan yaushe zaki ajiye shiriritar nan ba." Budurwar ta turo baki. "Kingani ko? Daman nasan yanzu za'a soma takuramin a gidannan. To dai babu inda zan k'ara tafiya, atoh." "Inji wa? Sai mu turaki can k'auyen Rano kije can ki cigaba da haukanki." Cewar Rufa'i wanda ya shigo mata da akwati, Aisha na biye da shi. Sukayi dariya har Mami. Bintu ta dubeshi da fararen idanunta masu kyau manya da su. Ya harareta a wasance, ta dauke kai tana fad'in. "Tab, ai dai dad'in abin bana gudun Innata. Kuma matarka ai itama a k'auyenmu ka kwasota." "A'a malama, Hajara ta fiki kyau da wayewa. Kin manta da yanda kikayi karatun?" Duk wannan maganar suna yinta ne a tsaye. Sai lokacin kuma suka zauna ana dariya. Idan da sabo, ya saba da tsokanar da Bintu ke yiwa Hajara matarsa. Kasancewar kusan sa'anni suke, kuma itama 'yar gida ce. A yanzu ta kusa haihuwa, har lokacin kuwa Ma'u ko 6ari bata yi ba. Allah bai kawo haihuwar ba. Bayan shigarsu d'aki, Bintu ta dira saman gado ta saki k'aramin ihu. "Home sweet home, shikenan babu k'ara kwana a makaranta, ba wani takura kai da karatu." Aisha ta d'aka mata duka. "Karatu yanzu kika soma, wa zai je miki jami'ar?" Bintu tayi murmushi mai k'ara fiddo tsantsar kyawun fuskarta. "Ai gwara jami'a tunda jeka ka dawo zanyi, ke nifa banason kwanan makaranta, wai da yaya na kammala? Ni abu d'aya ma nakejin haushi yanzu." Ta yamutse fuska tana mai zame d'ankwalinta, hakan ya tona asirin gashinta wanda ko kusa bata shafawa relaxer, yana d'aure da ribon, ya cika taf saidai babu tsawo. "Wannan yayan naki mai kama kwara." Aisha ta zaro ido, "Au, iskancin naki har ya kai ki kirashi da kwara? Lallai ma, baruwana." "Abinda yafi haka ma ai zan kirashi. Mutum babu walwala, sai wanda kakeso kad'ai ke ganin hak'oranka. Ji dan Allah idan yana gaban wannan siririyar matar tasa kamar a hure. Ke nan da kike ganina har na mutu bazan ta6a taka gidansa ba. Banje ba ina k'arama ba ballantana kuma yanzu da na k'ara sanin ciwon kaina? Hum um!" Aisha tayi dariya. "Kuma wallahi Anti Ma'u tana damuwa sosai akan rashin zuwanki. Amma tana tsoron rashin kunyarki ne shiyasa itama bata shiga harkarki." Bintu ta yiwa Aisha wani kallo. "Ita Ma'un ta gayamiki haka?" "Kai Bintu, Ma'u babu Anti ma?" Harararta tayi kamar idanun zasu fad'o. "Na fad'a d'in, munafus jeki ki gayamata. Toh wallahi ko mijinta ke kanki kin sani rabona da ganinsa tun ina Ss2 ballantana kuma ita. Kin tuna ko ancemin gashinan a falo bana fitowa indai ina gidannan nazo hutu ballantana wata matarsa. Amma gobe zakimin rakiya gidan Yaya Rufa'i, kinsan shine nawa." Aisha dake kallonta ta ta6e baki kawai. "Kanki akeji." Dariya kawai tayi ta mik'e a saman gadon ta hau rage kayan jikinta tana wak'arsu ta 'yan bodin na rabuwa da sukayi. Nan kuma hirar ta koma ta rayuwar makaranta, suna yi suna darawa abinsu. * * * Bak'a ce, saidai bak'inta mai shek'i da kyawu ne, kana ganinta kasan tana hutawa. Doguwa ce ba can sosai ba, tana da 'yar k'iba hakanan tana da diri mai kyau da burgewa. Hancinta bai cika sirantaka ba, ba kuma zaka sanyata a layin marasa hancin ba(Lol). Tana da magana(Idanuwa) masu k'arawa fuskarta kyau. A yanzun tana da shekaru goma sha tara cif a duniya. Tana sanye da leshi ruwan madara, anyi mata d'inkin riga da siket da ya kama jikinta ya zauna d'abas. Taci kwalliyarta. Fuskarta a tur6une, tana tsaye daga bayan kujera. "Kinji abinda nace ko?" Ta kauda fuskarta daga kallon Mami. "Naji." Aisha wacce dariya ta so su6uce mata, dole ta maida shi sakamakon kallon da Mamin ta jefomata. "Shikenan, kuje, a kula da abin hawa." "To Mami, sai mundawo " Cewar Aisha, Bintu dai tayi gaba. Haka kawai Mami ta sanyata zuwa gidan Ma'aruf dole, ita kam batasan meyasa Mami ke son 6ata ranta akan wanda bai damu da harkarta ba itama bata damu da shi ba. A cikin adaidaita sahu, dole ta saki fuskarta tana hira sakamakon Aisha da ta tunano mata wautar da tayi a baya kafin tariyar Ma'u a gidan Ma'aruf. Itama dole ta biyemata suna dariya wanda suka saba duk sadda suka tuna wani abu cikin wautar da Bintu tayi. "Ke, ni sai yanzun ma nakejin kunya fa, hm, Allah Ya kyauta shirmena dai." "Amin, ai gwara ki dunga yiwa kanki addu'a." Ta ta6e baki. "Mu soma zuwa gidan nasa banaso mu dade, kinga sai mu fito mu nufi gidan Yaya Rufa'i." Aisha murmushi kawai tayi. Dayake ba nisa, nan da nan suka isa. Bayan sun sallami mai napep suka rankaya ciki. Maigadinsu ya bud'e suka shiga. Ta dubi harabar gidan, bashi da wani girma, amma yayi kyau don an k'awata shi da shuke-shuke. Suka k'arasa ciki. Falon ya had'u, abinka da 'yan boko (Lol), babu wani tarkace sosai amma fa an zuba kujeru masu tsada, hakanan kafet da labulaye. Babu kowa a falon sai Sa'ade yarinya mai shekaru goma sha uku dake taimakawa Ma'u da aiki. Bintu ta zauna gami da d'ora k'afa d'aya kan d'aya sannan ta dubi Sa'ade. "Ke, masu gidan basanan ne?" "Suna nan." . Aisha ta dubeta. "Mu jira, nasan sun ji shigowarmu." Ta ta6e baki gami da yin k'as da cingam dake bakinta. "Minti biyar, idan basu fito ba sai mu k'ara gaba zuwa gidan karamci." Harararta kawai Aisha tayi batace uffan ba. Bintu ta d'aga kafad'a alamun batasan tana yi ba ko a jikinta. Suna zaune har suka ci mintuna uku, a fusace Bintu ta mik'e. Ta rattaba sallama cikin d'aga murya. Har sau uku. Zatayi na hud'u ta ji an murd'a k'ofar dake a bayanta. Wannan yasa ta fasawa. Ta juyo duk a zatonta matar gidan ce.
0 comments:
Post a Comment