.
Fatima nadawowa daga rakiyar Hydar,Khairat tajata zuwa d'akinsu,ko zama bata bari sunyiba tace, "Sis wai nufinki ke Hydar yakeso?,kuma shine wanda ya amshi numbern ki?,pls ineed more explanation." "Why are you asking me all those questions?,ina tunanin bakya buk'atar k'arin bayani sabida tambayoyinki tafe suke da amsoshinsu,tunda idonki yagane miki,I hope you understand what I mean?". Ajiyar zuciya tayi ta nemi guri ta zauna tayi tagumi,Fatima ce ta dafata tace, "Sis are you ok?". Asanyaye tace,"yes am ok, but Sis let me ask you something". Fatima tace ,"uhum inajinki".
.
"Dama ba wani abu bane tambayarki zanyi kuma kema kina sonshi?,sannan zaki iya auranshi?"Khairat tafad'i kamar me shirin yin kuka. shewa Fatima tayi tafad'a jikin Khairat d'in tace, "Wlh Sis har kinbani wata bazawarar dariya,to ke ko idona kika kallah ay kinsan na mato akanshi,wacce macece aduniyarnan zata samu kamar Hydar tace bata so ay wlh sede in bata samuba,ni wlh yanzu banida wani buri daya wuce naga na aureshi badan kudinshiba sedan nagartattun halayansa wanda najima ina burin miji me irinsu, ay Sis ki tayani addu'a kawai Allah yabarni tare dashi kusha biki,"tak'ara rungume Khairat cikin farin ciki mara misaltuwa. Khairat jitayi kamar ta watsamata wuta ajikinta,a sanyaye tace,"Allah yanuna mana lokacin natayaki murna y'ar uwa". Ranar Khairat batayi bacciba sabida tunanin yazatayi, tanason y'ar uwarta matuk'a amman batajin son datakema Fatiman yakai wanda takema zuciyarta,tanaji zeyi wuya tabar Fatima ta haramta mata abinda ta dad'e tana nema wato Hydar. Koda safiya tayi zasu tafi makaranta,khairat sam babu walwala atattare da ita gaba d'aya ta sauya,cike da kulawa Fatima tace. "Sister alamu sun gwada baki da lafiya don Allah ki sanar dani meke damunki,kinsan banison damuwarki hankalina tashi yake don Allah ki sanar dani ko hankalina ze kwanta". Azuciyarta tace,"kece damuwata Fatima,kuma kece ciwon dake damuna,neman hanyar dazan magance hakanne yasa kika ganni haka",amman afili setace mata,"Wlh da ciwon kai na kwana Sis shiyasa kika ganni haka amman ba abinda yake damuna".
.
Haka suka tafi makarantar Fatima se tausayawa Khairat takeyi,bata zargi komaiba game da sauyawar Khairat d'in daga jiya zuwa yau. Son da Fatima takewa Khairat rai ne kawai bazata iya bata ba jinta take har ranta burinta ta faranta mata akullum dan farin cikin Khairat shike sata farin ciki. Ana tasosu daga makaranta gida suka dawo ga mamakin Fatima Hydar tasamu a k'ofar gidan yana jiranta,tun kamin Ta k'araso ya iso inda take jakar makarantarta ya amsa yace. "Barka da dawowa me d'akina ya karatu,?ina fatan baki wahala ba?". kunyace duk ta rufeta ganin irin kallon dayake mata murmushi kawai takeyi ta rufe fuskarta a hijab,takasa bashi amsa. Khairat jitayi kamar ta kurma ihu dan bak'in ciki ga wani azababben kishi daya tasomata,maganama takasa. Hydar ne ya waigo ya kalleta yace, "k'anwarmu ungu jakar Auntyn ki kishigar mata da ita yanzu Zata shigo itama".yamik'a mata jakar,yata iya dole ta amsa tashige gidan,shikuma da Fatima suka shiga daga cikin gidan amman ba sit room ba. Agurguje suka gaisa yace ze wuce Abuja ne yanzu shine yace bari yazo yaganta dan inyatafi zekai two months acan sabida zeyi wata tafiyane daga cand'in,Fatima ranta besoba hakade yay ta kwantar mata da hankali da alk'awarurruka masu yawa har tak'aitaccen tarihin rayuwarsa seda yabata,itama akunyace tabashi nata. "Princess zamu fahimci juna kamin nadawo sabida ina dawowa zan turo zancan auranmu bawani lokaci nakeso ad'aukaba nak'osa naganki gidana wlh kuma zuwa lokacin kungama Waec d'inku dan haka don Allah ki amince muyi aure Kya ci gaba da karatun agidana". murmushi tayi tace, "bakomai Allah ya zab'a mana abinda yafi zama alkha'iri Allah kuma yakaika Lfy yadawomin dakai lafiya",tana gama fad'a tak'ara rufe idonta tana dariya mara sauti,shima dariyar yayi yace, "Ameen my Princess".
.
Kayan dayayomata shopping su yadunga fito dasu almajirai suka shigar mata dasu cikin gida haka sukai sallama kowa na bak'in cikin rabuwa da d'an uwansa. Khairat ganin kayan da Hydar yakawowa Fatima shi yasa tak'ara kwad'aituwa da son mallakarsa,numfashinta har rik'ewa yakeyi inta tuno da irin kallon dasukewa juna d'azu tsakanin Fatima da Hydar. *Waye Hydar* Hydar Jeebrin Lameed'o shine cikakken sunansa,d'ane guda ga Alhaji Jeebrin Lamid'o. Shikad'ai Iyayensa suka haifa shiyasa yataso cikin so da kulawa,hydar miskili ne na ajin farko baruwanshi dashiga sabgar dabata shafeshi ba shi mutumne meson girma,kuma yanada tsaron Allah duk abinda addininsa yahana yana k'ok'arin kiyayewa yana takatsantsan da imaninsa kud'i da mulki basu sa ya kauce hanya ba.
.
Mahaifinsa babban ma'aikacin gomnati ne ajihar kaduna amman asalinsa d'an jahar Adamawa ne acikin garin michika zamane yakawosa kaduna kuma anan ya had'u da Hajiya Hadiza wato mahaifiyar Hydar kenan. Suna zaune acikin wata anguwa me sunshine kinkinau dake garin kaduna. Hydar cikakken d'an siyasane wanda kowa kesonshi,yayi degree har zuwa Masters duka akan fannin siyasa shiyasa yake yinta bisa tsari, yarik'e muk'amai kala-kala a ma'aikatun gwamnati har zuwa yanzu dayake wakilcin Kaduna South a Abuja. Hydar yayi aure da matarshi me suna Maryam Sun haifi yaro d'aya mesuna Haisam inda tasake samun wani cikin gurin haihuwa tarasu bayan ta haifi y'amace inda yariyar taci sunan mahaifiyarta wato Maryam suna kiranta da Iman. Tunda Maryam ta rasu Hydar yarasa natsuwarsa sabida Maryam tana da kirki ga hak'uri duk abinda yakeso shi take mishi shiyasa yakasa mantawa da ita,seda iyayensa sukai ta nemar mishi taimako daga malamai sannan zuciyarshi ta natsu,amman duk sanda yakalli yaransa se yayi kuka na rashin mahaifiyarsu, yaran na hannun mamanshi ita take kulawa dasu. Sam Hydar yacire batun aure aranshi kwatsam se yahad'u da Fatima kuma Allah yajarabceshi da sonta wanda har yasanar da iyayensa yasamu mata in yadawo daga tafiyar nan dazeyi ze turasu aje anemar masa auranta.
.
Tundaga wannan lokacin Khairat tafara sauya yanayin alak'arsu da Fatima Sam bata zama inda Fatima take hassada muraran takemata,intaji suna wayako jitake kamar tafasa wayar dayake kullum suna mak'ale a waya. Fatima tasha yimata kuka akan tasanar da ita metayimata amman sede taimata banza ko tabar gurin. A haka har suka gama Waec d'insu cike da nasara kowa se murna yake musu. Hydar yau yadawo daga tafiyar dayayi,hutawa kawai yayi yataho gurin sanyin idaniyarsa wato Fatima kuma surprise visit yakeso yabata shiyasa be sanar da ita yadawo ba sede taganshi kawai. Sanda ya iso lokacin sunfito daga gida zasuje kiran da Abban Khairat yake musu. Dukansu tsayawa sukayi suna kallonshi cike da mamaki,Fatima farincikine yakamata game da ganinnashi k'arasawa tayi inda yake ta gaisheshi cike daso da k'auna Khairat ma k'arasowa tayi gurin tagaisheshi sewani gwalli take harda su fari da ido.ganinsu cikin alamar wani gurin zasu ne yasa yacema Fatima bari yatafi anjima ze dawo,yajuya yatafi sukuma suka wuce kiran da ake musu.
.
A falonshi suka sami Abban shida umman Khairat gaishesu sukayi cikin ladabi, yamusu umarnin su zauna,bayan Sun zauna ne yafara magana. "Bakomai yasa nace kuzo ina nemankuba sedan lokaci yayi da kowaccenku zata gabatar mana da mijin dazata Aura karatu kwaci gaba dayi ad'akunan mazajenku danhaka ina sauraranku kunsami wanda kukesone?". Shuru sukayi dukansu zuwa can Khairat taimaza tace. "Abba dama ni inada wanda nakeso mun dedeta kanmuma yace ze turo Fatima ce de har yanzu Allah be kawo mataba tukuna",tafad'i tana dokawa Fatima harara ta yadda babu wanda yagani. "To shikenan kituro manashi cikin satinnan dan bawani lokaci zamu jiraba, Jemima Fatima ki yi hak'uri aure lokacine in lokacin yazo kamar Hab'o ne sekiga anyi,"inji Abban yafad'i cikin sigar tausayawa ga Fatiman. "To amma naga kwanaki wani yana zuwa gurin Fatima har suna hira a sit room shiyana ina dabazaki turoshiba,"inji Momyn Khairat ta fad'i tana kallon Fatima wacce tsananin mamaki yasa takasa ko motsi. "Lah mommy plan ne muka had'a gurina yake zuwa dan karku ganene yasa Fatima take zuwa ansar key ko sister?".Khairat ba tsaron Allah ta ke kallon Fatima.da kyar Fatima tace. "Eh hakane mommy gurinta yake zuwa". "To kutashi kuje y'an nema kawai shiyasa kuke fad'a da Hajiya kuncika wasane".inji Abba. Mik'ewa sukayi suka fita gidansu Fatima suka shiga, d'akinsu Fatima tanufa ta kwanta akan gado sabida jirin dataji yana d'aukarta kuka takeson yi Amman hawayen sunk'i fitowa,k'anwarta *YASMEEN* nazaune a d'akin lokacin.
.
Yarinyace y'ar kimanin shekara takwas se d'an banzan wayo shiyasa duka family kowa ke sonta gata akwai tsokanar fad'a komai girmanka seta zageka tas inde kashiga gonarta baruwanta,miskilace tak'arshe inzaka kashe mutum agabanta inde baka takata ba ko kallo baka ishetaba,gata tanada ruk'o musammam inka b'ata mata rai tana jimawa bata yafe makaba,tun tana k'arama bata wasa da Ibaba,ga kyau kamar ita tayi kanta dan duk kyan Khairat Yasmeen tafita,uwarsu d'aya ubansu d'aya da Fatima,rashin kunyarta yasa basa shiri da Fatiman,Khairat tafi kowa sonta a family Khairat nason Yasmeen kamar ranta shiyasa bata son b'acin ranta.sunsha yin fad'a da Fatima in ta Dakar mata ita. Wannan kenan. Koda Fatima tashigo d'akin ko kallonta Yasmeen batayiba,zuwa can sega Khairat tashigo ganin yasmeen ad'akin bedametaba dan tasan tanada sirri kulle k'ofar d'akin tayi sannan tak'araso bakin gadon da Fatima ke kwance tace. "Sis inaso kid'auki abinda nayi miki amatsayin k'addara kuma ki d'auka damacan dani Hydar yadace bakeba,wlh zan iya komai wajan ganin nasameshi,umarni zanbaki yanzu kuma wlh inkika k'i bi zakisha mamakina,yazama dole kicema Hydar yaturo neman aurena gidannan bakeba, kuma dole kisa yasoni cikin gidansa inba hakaba narantse da girman Allah zanje nayo cikin shege awaje nace shine yamin nab'ata sunanshi a duniya sannan kema kin rasa dan su Abba bazasu aura miki mazinaci ba,in haka bata faruba wlh kashe kaina zanyi don nafiki son Hydar." Agigice Fatima tamik'e takamo Khairat tana kuka tace. "Inda bacci nakeyi danace bantab'a mafarki irin wannanba,khairat bantab'a tsammanin haka daga gurinkiba son abinda kikasan inaso kuma ni yakeso,ashe kinfi son kanki dani kenan?,ni bazan bari ki b'ata sunan masoyinaba dan nasan ke ba son tsakani da Allah kike masaba,kuma bazan bari namiji ya shiga tsakanina dakeba, bazan bari nayi asarar rayuwarkiba Khairat ina sonki fiye da kaina inde auran Hydar shine farin cikinki kije nabar miki shi,"numfashintane yasark'e tafara tari harda aman jini yanke jiki tayi tafad'i. Agigice Khairat tabud'e k'ofar d'akin taje takira Maman Fatima koda aka tambayi meya sameta cewa tayi itama bata saniba,Yasmeen ko kamar bata gurin ko kallo basu ishetaba,kwasar Fatima akayi arud'e zuwa asibiti.
.
Suna isa asibitin emergency room aka kaita, gwajin farko aka basu sakakamakon Fatima ta kamu da ciwon zuciya me tsanani wanda single mistake za ayi tarasa rayuwarta. Khairat tafi kowa kuka a gurin kamar gaske sauran dangi har tausayamata suke sabida ansan sun shak'u da Fatima. Fatima ko batasan waye akantaba ko numfashi da taimakon oxygen take yinsa lokaci guda tafita hayyacinta ,kowa yaganta seya tausaya mata.
.
Khairat ta k'osa fatiman ta farka dan tasa Hydar ya aureta wanda tayi imani inde ba Fatima ce tasashi ba wlh baze aureta ba,bata tsaron tonuwar asirinta gurin iyayansu dan tayi imani son da Fatima kemata baze bari ta tona mata asiriba shiyasa hankalinta yake kwance bata damuwa. Hydar da yamma yadawo gidansu Fatima anan yasamu labarin abinda yasameta sawa yayi arakashi asibitin lokacin daya ga halinda Fatima take ciki kusan fad'uwa yayi dan jirine yake d'aukarsa da kyar ya samu guri ya zauna yagaishe da iyayensu dake gurin Khairat se wani kwarkwasa take yi ta yadda iyayen dole zasu d'auka itace budurwar tashi. Fatima seda tayi sati biyu tukuna ta farfad'o da sunan Khairat a bakinta.tsawon wannan lokacin kullum Hydar a asibitin yake wuni se dare yake komawa gida har mahaifansa seda yakawo suka duba Fatima a asibitin.abinda ya d'aurewa iyayen su Khairat d'in kai kenan,irin d'awainiyar dayake da Fatiman dan tunda yazo asibitin kullum shike siyan duk abinda ake buk'ata. Khairat da sauri ta matsa kusa da Fatima tarik'e mata hannu tace. "Sis ganinan Sannu kinji Allah yabaki Lafiya kuma mungodewa Allah dakika farko lfy". Tsananin mamakin makircin Khairat ne a fuskar Fatima,tunaninta yaushe Khairat tazama mara imani irin haka.kauda tunanin tayi da cewa, "naji sauk'i"cikin muryarta wacce da kyar take fitowa. Dangi kowa murna yake da farfad'owarta se tattalinta sukeyi Khairat ce gabagaba gurin nuna tausayawa ga fatiman.
.
Hydar dayazo yaga fatiman shi ta farfad'o murnarshi kasa b'oyuwa tayi rasa ina zesata yayi,itako Fatima ganinshi datayi ta tuno yanzu ya haramta a gurinta wani dunk'ulallen bak'in ciki ne ya tokare mata wuya,runtse ido tayi tana hawaye. Duk abinda ke faruwa hankalin umman Khairat nakansu kuma dama tun ranar da Khairat tace musu Hydar ita yakeso ba Fatima ba itade bata yarda ba dan ita ta haifi Khairat ita zata fad'awa kowa halinta,tasan Khairat ta wuce duk inda ake tunani,sannan kuma taga fitarsu daga gurinsu ko minti talatin ba ayiba Fatima ta kamu da wannan ciwon shiyasa take zargin akwai wani abu ak'asa wanda dole seta bincikoshi ci gaba tayi da sa musu ido. ko abinci daza'a ba Fatima shi ya amsa yadunga bata abaki tanaci tana hawayen tausayin makomar soyayyarsu. Seda kowa yatafi yin Sallah yarage daga ita se Khairat da Hydar ad'akin,dayake shi tun k'arfe d'aya yaje yay tashi sallar. Fatima tace Khairat ta rufe k'ofar da yake abud'e suka barta,ba musu ba kunya taje tarufe tadawo tazauna. Ruk'o hannun Hydar Fatima tayi tana kuka tace, "Hydar duk abinda na rok'eka zaka yimin amatsayin sadaukarwarka gareni?". Cike da kwarin gwuiwa shima yakama nata hannun yace. "My happiness ki tambayeni duk abinda kikeso matuk'ar inada halin yimiki kuma akwaishi a duniyarnan wlh ko inane ko menene shi zan mallaka miki shi matuk'ar shine farin cikin ki". murmushin k'arfin hali tayi sannan tace. "Hydar aduniya babu abinda nakeso inka cire iyayena sama da Khairat,banida wani farin ciki da yawuce nata buri na shine nasanyata farinciki shin ko kaima kanason farin cikina?". Jiki asanyaye ya d'aga mata kai dan yafara tsorata da yanayin maganganun nata. "To idan har da gaske kai me k'aunar farinciki nane yazama wajibi agareka ka auri Khairat domin tafini sonka". Are you crazy!!!!!! Hydar yafad'i hankali atashe jijiyoyin jikinshi har sun tashi idonshi yay ja jikinshi na rawa yafara magana.
.
"How dare you Fatima? I said how dare you? Kinsan abinda kike fad'a kuwa?kina cikin hankalinki kuwa?kinsan bakya sona tun farko meyasa kika Bari nayi nisa asonki,meyasa kika yaudareni?ni ke nakeso ba Khairat ba,khairat bata cikin jerin kalar matan da nakeso,meyasa Fatima kika zab'i farincikin Khairat akan namu farin cikin,meyasa?"!!!!! Cikin sark'ewar murya take magana numfashinta na rik'ewa tace da kyar. "Hydar inason Khairat fiye da kai da kuma kaina y'ar uwatace ta jini kuma ganinta cikin farin ciki shi kad'ai ke sanyaya zuciyata wallahi idan kabari rayuwarta tasamu Matsala bazan yafe makaba, auran Khairat da zakayi shi zesa zuciyata tayi sanyi inba hakaba kamanta daka tab'a sanina arayuwarka".tana fad'in haka tari yataso mata tafara ama'i harda jini agigice sukayi kanta zasu rik'eta. "kar wanda ya tab'ata a cikinku". suka jiyo ance musu daga bayansu, mommyn Khairat ce atsaye idonta kamar garwashi,wanda ko ba'a fad'a musuba sun fahimci taji duk abinda suke cewa. Khairat har kusan fad'uwa tayi sabida tsabagen razanar da tayi da ganin yanayin fuskar mahaifiyar tata. Mommy k'arasawa tayi tarungumo Fatima jikinta hakan yay dede da shigowar likita,fad'a yashigayi akan meyasa zasu b'ata mata rai kode rayuwarta bata da amfani a gurinsune,hak'uri mommy ta dunga bashi.
0 comments:
Post a Comment