.
Tafe suke bame cewa kowa komai,se y'ar satar kallo sukeyiwa juna. Carab Hydar ya kamata tana kallonshi duk kunya tabi ta kamata,muryarshice ta dawo da ita seti. "Allah de yasa baki da maita bayan kwacen masoyi",ya fad'i batare da ya kallo inda take ba. Ranta ya b'aci dajin zancannashi amman tasan dole dama zata fuskanci irin hakan daga gurinshi,dan haka dole seta zama me hak'uri kamin taci riba murmushi tayi tace. "Ay sede kar a kuma amman inde maita ce tonice shugaba a wannan fannin kuma duk Wanda na kama sena tabbatar dana lasheshi nake k'yaleshi",ta fad'i cikin muryarta me d'aukar hankali duk wani me sauraronta. Waigowa Hydar yayi yana kallonta ayko ta haskeshi da fararan idanuwanta datayi fari dasu,kan motar ne yakusa kwacewa a hannunshi da sauri yamaida kallonsa kan titi sannan yace. "Ashe ko kin had'a kanki da wahala dan inde Hydar ne ba maita ba kukar bulukiya ma taci ubanta, sede ki ganni ki k'yale wlh,ni nafi k'arfin wannan maitar taki". "Honey kenan ay ba'asan maci tuwo ba se miya ta k'are,kuma bakasan inda rana zata fad'i ba". "Karki sake kirana honey d'inki sunana Hydar in baki iya fad'a ba ma kice Aliyu,Rana kuma ta gabas take fitowa ta fad'i ta yamma,kuma banajin akwai wata rana da Kare yake da ita data wuce ta haushi kamar yadda kikeyi yanzu".
.
maganganun sun doketa shiyasa bata sake cewa komai ba har suka k'araso gidan. kyau da tsarin gidan shi ya k'ara rikita Khairat aranta tace, "wai wai wai dank'ari wai gidan iyayensa kenanma inaga gidanshi kuma". k'arasawa falon gidan sukayi,Hajiyar na zaune ita dasu Haisam suna kallo,da gudu yaran suka nufi daddyn su suna kiranshi rungumesu yayi ita kuma Hajiya tasowa tayi ta rungumi Khairat tana fad'in, "sannu da zuwa y'a ta". Khairat ko se rurrufe fuska takeyi alamar jin kunya,tsugunawa tayi ta gaida Hajiyar,yaran Hydar d'in suma suka gaisheta,nan Hajiya tasa aka cika mata gabanta da kayan lashe-lashe,kasa cin komai tayi se nonnok'ewa takeyi wai kunya. Hydar ji yayi kamar ya doketa dan takaici,yanzufa suka taho tana mishi rashin kunya amman shine dan munafunci wai yanzu kunya takeji,k'wafa yayi yawatsa mata harara a fakaice gudun kar Hajiya ta gani amman ita wacce akayi dominta ta gani. Y'an uwansu ne suka shigo falon da yake suma nan y'an bikin sun taru,nanfa suka shiga tsokanarta da yake yawancinsu abokan wasan Hydar d'inne,Khairat rasa inda zatasa kanta tayi, Hajiya kwab'arsu take amman ina kamar ta zugasu kowa se son cusa kansa yakeyi a gurinta. Hydar Hajiya tacewa. "Wlh Hydara ka d'auke matarka a gurinnan kamin su kurmanta maka ita, irin wannan hayaniya haka ay se kunne yasamu matsala". Da k'yar ya samu ya isa inda take d'agota yayi,ayko nanfa suka fara yimusu gud'a,khairat ko k'ank'ame Hydar d'in tayi gudun karsu ruk'ota a haka har ya fice da ita b'angaren Hajiyar,part d'inshi na gidan ya kaita suna shiga ya k'wace jikinshi anata,itako se ware ido takeyi sabida tunda take bata tab'a jin hayaniya irin ta yau ba kamar zasu cinyeta,ita abun har haushi yabata duk sun gama dak'una mata jiki. "Jita don Allah kamar tsohuwar munafuka se wani zare ido kikeyi to wlh karki sake inji wani acikinsu yayi ciwon kai, dan yadda kike zare idanuwannan alamu ne na maitar ki tafara motsawa to wlh kul". Hawaye ne suka zubo mata na takaici da k'yar tace. "Don Allah kamai dani gida ay mungaisa da Hajiyar pls" "Ba yanzu zan maidakeba sekun gaisa da Alhaji dan ya kusa dawowa,keda kika fito yawon maita menene naki nason komawa gida da wuri?".
.
Bata bashi amsaba illah samun guri da tayi ta zauna.shima ficewa yayi daga d'akin,part d'in Hajiya yanufa yasamu wata acikin y'an uwan nashi yace ta kwashi kayan abincin da aka kawowa Khairat takai mata part d'inshi, ayko nanda nan takwasa takaimata. Hajiya ko bin Hydar tayi da kallo fuskarta d'auke da murmushi tace, "wlh Hydara na ka iya zab'en mata Allah yasa yadda take Da kyau na zahiri yasa har bad'ini haka take, Allah yabaku zaman Lafiya da hak'uri da juna". murmushi kawai yayi bece mata komai ba, sema kawar da zancan da yayi da cewa,"zuwa anjima zan maida ita gida sabida muna jiran Alhaji ne yadawo su gaisa". "Gaskiya ka kyauta, yanzu kaje kasa ta taci abincin inta gama seka dawo da ita nan tunda nasamu na kad'asu cikin gida masu hayaniyar". "To Hajiya bari naje",ya mik'e yafice daga falon,part d'inshi yanufa inda yasamu Khairat se share k'walla takeyi. K'arasawa yayi inda take yaga bata ci komai ba acikin abincin,be cemata komai ba yad'ebo abincin yanufo bakinta dashi,da sauri ta d'ago ido tana kallonshi gyad'a mata kai yayi ba musu ta amshi abincin,haka yadunga bata har taji ta k'oshi sannan ta kawar da kai. Bakomai yasa Hydar yayi mata haka ba, illah shi mutum ne da baya son ganin mace na kuka yanzu hankalinshi ze tashi musammam ma ace shi yasata kukan, shiyasa yanzu ya rarrashi Khairat ta wannan sigar,duk da ranshi besoba amman de ya daure. iyayensa sun had'a mata shatara ta arzik'i sannan ya d'auko ta ya dawo da ita gida. suna zuwa tun kamin ya gama parking tasoma k'ok'arin bud'e k'ofar motar amman se taji a kulle take,har seda yayi parking Ya kashe motar ya waigo yana kallonta itama shi take kallo,yace. "Na b'ata miki rai ko? am sorry bada son raina nai miki hakan ba, dan ba halina bane sa mutum b'acin rai laifinki ne da kika tursasa y'ar uwarki wajen ganin ta bar miki ni wanda kinsani ita nakeso itama kuma ni takeso, amman sabida biyan buk'atarki ke kad'ai kinsa mun haramta ga juna, duk abinda namiki ki kuka da kanki ba Hydar ba". zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu sannan yace. "get out from my car I need to go". Jiki a sanyaye ta fito daga motar bayan ya mik'a mata tsarabar da aka bata a gidansu,yaja motar yabar gurin. Da murna Fatima ta tarbeta itama Khairat d'in haka dan b'oye abinda ya mata tayi nan suka d'unguma d'akin Maman Fatima anan aka bud'e tsarabar. *RANAR BIKIN* Ko ta ina in ka duba jama'a ne birjik wa'inda suka halaccin d'aurin auran. Y'an majalisu, sanatoci, ministoci, da tawagar shugaban k'asa kowa yazo d'aurin auran. Inda aka d'aura aure lafiya jama'a se fatan alkaha'iri akewa angwaye da amare. Taro yayi taro inda k'arfe hud'u aka wuce dinner amare sunyi kyau har sun gaji haka suma angwayen anci ansha anyi godiyar Allah inda k'arfe takwas na dare taro ya watse. Tara daidai aka Kawo motocin d'aukar amarya Fatima sabida ita kad'ai za'a kai ranar,ita Khairat da yake Abuja ne se gobe da safe za'a tafi da ita. kuka Fatima da Khairat sukeyi kamar anmusu mutuwa, kowa a y'an biki seda ya tausaya musu sanda aka kai Fatima gurin umman Khairat taimata fad'a bayan tagama yimata fad'anne Fatima ta rik'e k'afarta tana kuka take nemarwa Khairat yafiya, sosai take kuka da yake su biyu aka bari a d'akin sauran mutanen suna waje seda Fatima tajima tana rok'on Umman, tausayin Fatiman ne yasa Umman tace ta yafewa Khairat d'in,Allah ya musu albarka duka.
.
Da kyar aka b'anb'are Khairat a jikin Fatima,se yanzu Khairat take danasani na gasken gaske,se yanzune soyayyar Fatima ta gasken gaske ta kamata,kuka take kamar ranta ze fita tana sake neman gafarar Fatima a haka har aka wuce da Fatima gidanta dake unguwar dosa GRA dake kaduna tana kukan rabuwa da gida. Ankai amarya gidanta lafiya kuma y'an kai amaryar basu jimaba suka juyo,suka barta ita kad'ai se kuka takeyi abin tausayi fuska da idanunta duk sun kumbura sabida kuka. Tawagar ango ne da abokanshi suka shigo gidan se barkwanci sukeyi. A falo suka zauna sannan Kamal yanufi d'akinta domin kiranta su gaisa da abokansa. A kwance ya sameta ta k'udundune jikinta acikin lafayar da aka nad'eta aciki,se sautin kukanta yake ji kad'an kad'an. Da saurinsa yak'arasa kan gadon ya d'agota a hankali ya rungume be cemata komai ba itama batayi k'ok'arin kwace jikinta ba,shafa bayanta yashigayi alamar rarrashi yana hura mata iska a kunne. Tun tana kukan har wani baccine yaso kwasheta dan tuni ta manta kuka take, a hankali ya rad'a mata akunne. "Wake up baby is too early, kizo muje kugaisa da friends d'ina kinji,inmuka dawo sekiyi baccin pls". Da kyar ta yarda ta sakko akan gado shida kanshi ya k'ara gyara mata lafayar sannan yaja hannunta suka nufi falon. Kamar de yadda kuka sani,shegan taka da akeyi gurin siyan baki itace ta faru suma anasu daga bisani sukayi musu addu'ar samun dawwamamman zaman lafiya tare da zuri'a d'ayyiba.Rakiya ya musu daganan ya rufe gidan sannan ya dawo,k'ofar falonma rufewa yayi dayake gidan two bedrooms plat ne. A d'aki ya sameta duk tayi wani tsuru tsuru abin yakusa bashi dariya amman ya maze,sata yayi tayo alwala shima yayo yajasu Jam'i, raka'a biyu domin nuna godiyarsu ga Allah daya nuna musu wannan rana. Bayan sun idar ledar kajin dasuka shigo da ita yajawo musu gamida fresh milk me sanyi da ruwan faro,kitchen taje ta d'auko musu plate da kofuna sannan ta dawo shi ya juye kajin a plate d'in sannan ya tsiyaya musu fresh milk d'in. Sam ta kasa sakin jikinta taci dan haka jawota yayi jikinshi yashiga bata da kanshi yana mata kalamai masu dad'i a haka har ta k'oshi sannan shima ya maida hankali yaci, d'aukar sauran yayi yakai kitchen da kanshi sannan yadawo yajata zuwa toilet sukayi brush. Bayan sun fito kyaleta yayi ya nufi d'akinshi domin yayi wanka ya sauya kaya. Itama yana fita gudu gudu sauri sauri ta cire kayan jikinta ta fad'a toilet domin tayi wanka,dan tana ganin har ta fitoma be dawoba dan ta d'auka irin masu shekara a toilet d'in nanne,yariga ta fitowa dayake zafi akeyi be shafa mai ajikinshi ba kayan bacci kawai ya zura ya feshe jikinshi da turare sannan yanufo d'akinta.
.
Koda ya shigo be gantaba yasan tana toilet dan haka kwanciyarshi yayi akan gado yana jiran fitowarta. Da saurinta ta fito d'aure da tawul wanda ko cinyoyinta be gama rufewa ba, burinta tai sauri ta shirya kamin ya dawo k'ofar d'akin taje ta kulle,sam hankalinta bekai kan godon ba dan dama ance hankali ke gani ba idoba. gaban wardrobe taje ta bud'e ta d'auko rigar bacci da fant dan ita bata iya bacci da bra,bayan ta d'aukosu gaban mirror Ta nufa tafara shafa turaren humra ajikinta har ta kwance tawul d'in ta dawo dashi daidai k'ugunta taci gaba da shafa humrar har ak'asan dukiyar fulaninta sosai take shafesu da turaran zata kwance tawul d'in gaba d'aya kenan idonta ya sauka acikin nashi ta mudubi. A gigice ta waigo tana kallonshi ganin ba fuskarta yake kallo bane yasa itama tabi inda yake kallon da ido ihu ta saki ganin Ashe kirjinta yake kallo da gudu ta haye kan gado ta lullub'e jikinta cikin bargo se kyarma takeyi kamar me zazzab'i. Murmushi kamal yayi ya kashe hasken d'akin shima ya haye kan gadon,bargon ya bud'e da kyar sabida tarik'e iya k'arfinta tana kuka shima yashige cikin bargon tun kan yace mata komai tafara had'ashi da girman Allah akan yayi hak'uri. Rungumota yayi jikinshi had'uwar kirjinsu guri d'aya seda ya haifar musu da shocking dukansu a jikinsu,da kyar ya saisaita tunaninshi murya can k'asan mak'oshi yace mata. "relax Baby am not going to hurt you meyasa kika gigice haka tsaron mekike ji haka uhum?". "Bbbbbbb ba tsoro nake jiba yaya kamal ba kaya ne ajikina ka ganni shiyasa don Allah kafita insa kaya".Ta fad'i bakinta na rawa kamar an jona mata shocking. "Kin manta ni mijin kine yanzu ko tsirara kike Allah ya yarjemin inganki a haka kuma kema kinsani,kuma banason kisa kayan kibari da safe kyasa banason musu kuma". Shuru tayi dan tasan yafita gaskiya amman a tsorace take dashi ay bata gama guntun tunanin nataba taji bakinshi acikin nata kissing d'inta yakeyi very romantic tuni ta fara enjoying abin da yake mata ta gefe guda kuma hannunshi ne ke yawo a kowanne sassa na jikinta.
.
Sanda ya kwance tawul d'in dake jikinta ne hankalinta ya dawo jikinta rik'e hannunshi tayi tana magiyar don Allah ya kyaleta amman ina akan kari ake sallah in yawuce ramakone. Kamal beji be gani bema san me yake yiba shide yajishi a duniyar da koda wasa be d'auka akwaita ba ashede geographers da gaske suke dasuka ce duniya Kala tara ce shi ma yashaida dan gashi ya shiga wata wacce bemasan sunan taba. Da kyar ya saurara mata, in banda kuka ba abinda takeyi tayi lamo ajikinshi se albarka yake sa mata,daganan d'aukarta yayi yakaita toilet ya tara ruwan zafi yasata aciki se kukan shagwab'a take masa shiko se rarrashinta yakeyi daganan wankan tsarki sukayi ya D'aukota suka dawo d'aki, zanin gadon ya sauya sannan suka kwanta se shagwab'a take zuba masa son ranta shiko se rarrashinta yakeyi kamar zeyi kuka. *K'alubale gareku y'anmata* (wallahi ku gujewa zubar da mutuncinku a waje babu wata soyayya da saurayi ze nuna miki ki yarda dashi da zaran yatab'a saninki awaje wlh koshine mutum na farko daya tab'a saninki bazaki tab'a daraja a idonshi ba kuma babu wata kulawa daze baki ga d'umbin zunubin dakika aykata muji tsaron Allah). A haka har bacci yayi gaba dasu,basu farkaba se k'arfe bakwai na safe, da sauri sukayi alwala sukayi sallah Fatima se kunyar had'a ido dashi take shiko se tsokanarta yakeyi irin magiyar da ta dunga yimasa ya dunga tuno mata seda yaga zatayi kuka ya kyaleta ya koma aykin rarrashi. wanka suka shiga tare Fatima kamar zata yimishi kuka akan yabarta tayi ita kad'ai amman ina be kula ta ba a haka sukayi wankan yana ta sata jin kunya. koda suka fito da kanshi ya shiryata sannan shima yakintsa,suka fito falo sak'on Umman Khairat ne ya iso abinci lafiyayye ta dafo musu ta ayko yara suka kawo musu. Khairat Amarya. K'arfe goma na safe motocin d'aukar Amarya suka iso,cikin Khairat ne ya kad'a sanda labarin isowar motocin ya risketa tun kan ace ta fito ta fara kuka, haka aka d'auketa aka kaita gurin iyaye kowa ya mata fad'a,Umman ta ma se yanzu tausayin y'ar tata yakamata rungume juna sukayi Umman namata nasiha a haka aka jata zuwa mota tana rusa kuka. Gidan iyayen Hydar aka fara kaita tukuna sannan aka kama hanyar Abuja da ita. Da azahar suka isa Abuja,kai tsaye gidan Amarya aka saukesu. Gidan fad'in had'uwarsa ze zama k'auyanci domin karshene gurin had'uwa.
.
Da yake ba kwana zasuyiba nan da nan suka gyara gidan ko ina k'amshi ke tashi kamar yadda itama Amarya ta gaji da had'uwa se wani k'amshi ke tashi a jikinta. Suna yin sallar la'asar suka baro Abuja Khairat taci kuka har ta godewa Allah,dole ta hak'ura ta rarrashi kanta. Tun tana sa ran ganin angonnata har ta cire ga yunwa da takeji,mik'ewa tayi tafara neman kitchen,Allah ya taimaketa ta ganshi acikin kitchen d'in store yake koda ta lek'a shak'e yake da kayan abinci, fridge kuma ga nama nan kala-kala da kayan miya. Bata bata lokaciba ta d'ora fried rice and chicken domin daga ita har Fatima gwanayene gurin girki kan kice me gida ya bad'e da k'amshin girkin,nan da nan ta gama. Juyewa tayi a cooler sannan ta d'ebi nata ta d'auki juice na chivita ta d'auko abincin ta kawo dinning ta zauna ta fara ci hannu baka hannu kwarya dan yunwa ta kamata sosai. Tana gamawa kwashe kayan tayi takai kitchen bata fitoba seda ta tsabtace komai ta maidashi mazauninsa. Har zuwa dare ba Hydar ba alamarsa tsoro duk yabi ya kamata inta Kira number d'inshi sede ace akashe ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba,tayi kuka har ta gaji. Ta idar da sallar isha kenan taji ana nuking k'ofar falo da sauri tazo ta bud'e,wani ta gani a tsaye tun kan Tai magana ya duk'a ya gaisheta sannan yamik'a mata wata y'ar k'aramar jaka yace inji Hydar. Amsa tayi jiki a sanyaye ta maida k'ofar Ta rufe ta dawo falo ta zauna sannan ta bud'e jakar kud'ine a ciki kimanin dubu d'ari uku se wata takarda mak'ale a jikin kud'in. Takardar ta d'auka da sauri ta fara karantawa kamar haka. _"hmmm Amarya kinsha k'amshi ina miki barka da zuwa gidana,naturo miki wannan sak'onne sabida hasashena ya nunamin kinfi buk'atarsu akan kulawata ni nayi tafiya bana k'asar, may be nanda wata biyu nadawo inzaki iya jira to inkuma bazaki iyaba hanya a bud'e take inkin tafi kiba megadi key ze ajiyemin,in kuma kin zab'i zama dan gama ba zuciya ce dakeba to na yarje miki ki d'auko wani acikin k'annanki yatayaki zama kan nadawo duk abinda kike buk'ata kiyimin text banason jin muryarki"._
.
Rushewa tayi da kuka gwanin ban tausayi fad'i take. "Haba Hydar meyasa zakamin haka,akawoni gidanka a matsayin amarya amman ka iya barin k'asar batare da kazo kaga lafiyata ba",cigaba tayi da kukan kamar ranta ze fita. A gurin bacci ya d'auketa bata farkaba seda tafara jin kiran sallah,da kyar ta mik'e ta haura sama inda d'akinta yake,wanka tayi ta d'auro alwala tazo Ta tada sallah,tana idarwa ko mai bata shafaba ta jawo wayarta ta kira Fatima bugu biyu zuwa uku ta d'auka cike da murna tace. "Sister ina kika baro angon naki?kike kirana da asubar fari idar da sallah ta kenan". Rushe mata tayi da kuka,hankalin Fatima mugun tashi yayi ta shiga tambayarta abinda ya faru,da kyar Khairat ta bata labarin komai. Sosai Fatima ta tausaya mata hak'uri ta dunga bata da kwantar da hankali harde ta hak'ura sukayi sallama. Shiko Hydar ba komai yasa shi barin k'asar ba sedan tabbacin rasa Fatima da yayi,a daren da aka kaita gidan miji kwana yayi yana kuka sabida kishi koya ya rufe idonsa ganinsu kawai yake suna rayuwar aure, a daren kawai har rama yayi shiyasa ya k'auracewa k'asar gaba d'aya Uwa uba da haushin Khairat da yakeyi sabida itace sila. Khairat Umman Fatima Ta kira ta shaida mata Hydar yayi tafiya amman ta b'oye mata be kwana ma agidanba,sede tace mata yace ta d'auko wani acikin k'annanta daze tayata zama shine takeso abata yasmin kamin ya dawo. fad'a Umman Ta rufeta dashi akan tayi zamanta ita kad'ai base an kawo mata kowaba Tunda akwai masu gadi. kuka Khairat ta samata wanda ya tirsasa umman amincewa da cewa gobe za'a kawota amman yana dawowa zata dawo itama. Godiya Khairat tadunga yiwa Umman daga karshe suka tsaida magana akan drivern Khairat d'inne zeje ya taho da Yasmeen d'in. Koda Umman ta shawarci Abban su Yasmeen d'in be hanaba se fatan alkha'iri da yayi,gurin Umman Khairat d'in taje ta sanar mata itama bata hanaba.
.
Yasmeen duk miskilancinta seda ta nuna taji dad'in zuwa Abujan da zatayi,nan da nan ta shirya kayanta. Khairat ko k'osawa tayi gari ya waye akawo mata Yasmeen dan kad'aici ya isheta,uwa uba kuma dama tayi missing d'in Yasmeen d'in. Da sassafe driver ya tafi d'auko yasmeen k'arfe biyar na yamma har yadawo tare da Yasmeen d'in. Khairat da gudu taje ta rungumeta tana murna da zuwanta itama rungume Khairat d'in tayi tana murna. D'aki Khairat takai Yasmeen,wanka taimata sannan ta kimtsa ta suka dawo falo suka ci abinci. Sosai Khairat take kulawa da Yasmeen,don ba k'aramin so take mata ba,cikin sati guda har Yasmeen tak'ara haske jikinta yayi kyau. Zuwan Yasmeen yasa Khairat damuwarta ta ragu sede kullum kwanan duniya seta tura masa sa'kon gaisuwa be tab'a dawo mata da amsaba ita kuma bata fasa ba. Yasmeen bata da ayki daya wuce ta zauna ta Kalli cartoon domin yana d'aya daga cikin abun da yake sata nishad'i, in ko ba kallo takeyiba zaka sameta a garden d'in gidan tana wasa,ta sake da gidan sosai. Sakin jikin Yasmeen a gidan har mamaki yake ba Khairat sabida tasan halin Yasmeen na rashin sabo da wuri,kome zaka bata dan ku saba inde ba itace taso ba to kayi kad'an ko kallon arzik'i taimaka. Yasmeen tun yanzu da take y'ar shekara takwas,in mutum ya kalleta yasan in ta girma ba k'aramar mace bace,domin Allah ya kyautata surarta farace amman ta sirka da ja hakan yabata damar yin shige da indiyawa,tana da yalwar gashi akanta bak'i me santsi sam tun tana k'arama batason Kitso,irin yaran nanne masu y'ar k'iba irin ta yarinta shiyasa ko kaya aka samata zakaga sun amshi jikin nata, tana da manyan idanuwa sede yawan lumshesun da takeyi kamar me jin baccine yasa basa fitowa sosai su ake kira da sexy eyes,koya ta motsa bakinta dimples d'inta se sun fito,inko tayi murmushi kyakkyawar hushiryar tace take bayyana,Yasmeen kenan yarinya me tsada. Kud'in da Hydar yaba Khairat su ta d'auki dubu d'ari aciki taba d'aya daga masu gadin gidan yaje boutique me kyau ya siyowa Yasmeen kaya masu kyau,tare da ita ya tafi. Basu jimaba suka dawo da kaya nik'i-nik'i masu kyau da tsada,Khairat siyayyar ta burgeta sosai sab'anin Yasmeen d'in da bakomai ne in aka mata take nuna taji dad'i ba koda kuwa taji dad'in sabida tsabar miskilanci. Tundaga ranar kullum Khairat cikin yiwa Yasmeen kwalliya take don so take kar Hydar ya dawo ya raina mata k'anwa,sabida tana kallon hakan amatsayin gazawa shiyasa kud'in da yabata akan Yasmeen suka K'are. Hydar yana can Hajiyarsa ta dame shi da waya akan ya dawo gida haka kar kuma abin ya koma d'aukar alhakin y'ar mutane,sosai tayi masa fad'a akan ya dawo gida.
.
Lokacin watanshi d'aya da sati biyu beso hakanba amman bashida zab'in da ya wuce yabi umarnin nata. kasuwa yashiga domin yayiwa yaransa tsaraba da iyayensa,amman shigarsa inda zeyi siyayyar ganin kayan mata masu kyau kawai se ya tsinci kansa da son Siyawa Khairat don yanzu ya fara Hak'ura da Fatima ya amshi Khairat a matsayin k'addararsa,siyayya sosai ya mata da yaransa. Washe gari jirgi ya d'aukoshi daga k'asar Singapore zuwa gida Nigeria batare da ya sanarwa kowa zuwanshiba. Lokacin daya iso gida masu gadin gidan kansu sunyi mamaki da ganinsa. Kai tsaye bakin k'ofar falon gidan ya nufa koda ya murd'a a kulle yake,dan haka yashiga nurking lokacin Khairat ta shiga wanka Yasmeen ce tazo bud'e k'ofar. Sanye take cikin riga da siket pink color gamida ratsin fari,rigar me hannun vest ce siket d'in kuma ko cinyoyinta be rufeba k'afarta sanye cikin takalmin nan da ake yayi me kamar cambas shima pink and white ne se kanta daya sha ado da ribbon masu kyau suma pink and white farkon inda aka kama gashin pink akasa sedaga k'arshen gashin akasa white wanda aka zagayo da gashin ya sauka akan k'irjinta. Hydar kusan suma yayi a tsaye gurin kallon wannan cute little girl dake tsaye a gabansa. "from where are you? and then what do want?"muryar Yasmeen ta katse shi,don ita bata sanshi ba duk zuwanshi gidan su basu tab'a had'uwa ba. Da sauri ya kalleta itako se farfar take da ido gamida murgud'a d'an k'aramin bakinta alamar rashin kunya,harda rik'e k'ugu. Dariya ce ta k'wacewa Hydar dan in yace Babyn bata burgeshiba yayi k'arya,da kyar yace mata. "Am Hydar me gidan nan ko zaki min izinin shigowa?". kallon up and down taimasa sannan ta kad'a gashinta tabashi guri ya wuce ta Maida k'ofar ta rufe ta bishi a baya.
0 comments:
Post a Comment