SURBAJO Part 01
.
Sauri yake ya isa gida sabida yaga bakwai na safiya tayi. Tunda yaje sallar asuba bedawoba yana masallaci seyanzu
Addua yake Yi azuciyarshi Allah de yasa Aisha taga dama ta tashi daga baccinnata na qaddara
Tundaga shigarshi falo yafahimci adduarshi bata amsuba duba da ganin falon dayayi ahargitse kamar filin dambe duk da de dama sabon falonne zama acikin wannan yanayin
Jikinshi asanyaye yahaura sama inda dakinta yake
Ilai kuwa Tana kwance akan gado tana sharar bacci
Binta yayi da kallo zuciyarshi nakuna sabida tun jiya yashaida mata zekoma bakin ayki yau jirgin karfe takwas zehau zuwa phortercot amma shine ko tashi a bacci batayi ba
Inda sabo yasaba da halinta
Juyawa yayi yakoma dakinshi domin yayi wanka sabida yasan ko toilet dinta yace zeshiga yayi wanka seyakusa amai sabida karni da zarnin da toilet din yakeyi
.
Cikin Rabin awa har yagama shiryawa cikin kakinshi na soja
yayi kyau sosai sabida dama kyakkyawanne
Jakarshi yadauko sannan yadauko key din motarshi dakinta yanufa
haryanzu Tana bacci
Tashinta yayi
Koda tabude ido taganshi tsaki tayi sannan tace Amman wallahi al-ameen kaidan rainin wayone yanzu fisabilillahi ina bacci zakazo katasheni
Beyi mamakiba Dan yasaba dajin abinda yafi haka daga gareta
Nizan wuce yabata amsa
Kudi yaajiyemata kimanin dubu Dari uku a kan bedside drower kallon kudin tayi awulakance sannan tace namenene wannan
Nacefanene kiyi amfani dashi kafin nadawo sabida inna tafi wata uku zanyi kafin nadawo
kan ubance inji Aisha tafadi tana sakkowa daga kan gadon sannan tace wallahi kayi kadan zakayi wata ukunne zaka mikomin 300k wallahi baze yiwuba tafada yayinda ta zubar da miyaun daya taru abakinta ajikin bangon dakin
Al-ameen bameson hayaniya bane Dan haka yace se nawa kike so
500k tabashi amsa bemusaba yadauko yakara mata sannan yace senadawo pls kiyimin addua
Agayas tabashi amsa gamida komawa takwanta
Fita yayi wani kurtun sojane yazo dasauri yaamshi kayansa yasa aboot sannan yabudemasa bayan motor yashiga sannan Shima yazaga mazaunin direba yatada motor sukafita yayinda motoci biyu na sojoji sukasa motor atsakiya suka nufi Airport
suna zuwa kai tsaye jirgi yashiga Dantuni aka gama shirya komai
jirginsu yadaga zuwa rivers state
Safe trip alameen
.
Tunda alameen yafita taci gaba da baccinta bata tashiba se Tara sannan tamike tashiga bayi tayo alwala tayi sallar asuba
Tana idarwa kitchen tanufa madara ta kwaba akofi da Milo tazuba ruwan sanyi tajuya yayi kauri kamar chocolate
Tadauko gorar faro tadawo falo tafarasha
Aduniya babu abinda Aisha ta tsana irin girki Sam batason yinshi shiyasama bata iyaba
.
Zamanta keda wuya taji ana ringing bell dasauri taje bakin kofar taleka Dan ganin waye
Ihu tasa tun kafin ta bude kofar
Tana budewa suka rungume juna ita da bakinnata kawayentane su biyu
Kai tsaye dakin Al ameen tamusu masauki dan batason su rainata insukaje nata dakin
Afalonshi suka zauna hira suka shigayi dawadda tadace dawadda bata daceba suyi gulmar wannan suyi ta waccan
Can kuma tafara basu labarin yadda suke kwanciyar aure da mijinta kamar yadda suka saba (waiyyazu billah)
Shewa suke kawai suna kara zugata suna fadin eshat baby baki da wasa
Dariya tayi tabasu labarin yadda suka rabu yau da alameen
Daya daga cikin kawayennatane mesuna Ruky tace wo mutuniyar kina wuta muna binki da petur ina namu salary din tunda kin tatsa muma seki sammana koya kikace zuly baby
A wannan gaskiyane wacce aka Kira da zuly tabada amsa
eshat ce tafara mgn haba sisters harse kun roka ay kunwuce hakan agurina danhaka ku kwantar da hankalinku nifa wlh kunfiyeminshi so dubu agurina Danni Al ameen dashi da banza duka daya Suke. Kuma sabida nasan zanbaku naku kasonne yasa nace seyakaramin kudin Dankaka zanbaku 200k kuraba
Ihu sukayi suka rungumeta suka hada baki gurin fadin heyyy se madam Allah de yabiya Hajiya.
*ASALIN LABARIN*
.
al-ameen jibrin sulaiman shine cikakken sunanshi matashine Dan shekaru 35 da haihuwa. dane ga rt major general jibril sulaiman
Mahaifinshi Dan asalin garin kanone awata anguwa daake Kira lungun gabari canne asalin tushensu amma sanadin aykin soja yasa yadawo kaduna da zama a malali yake da zama alayin sultan road
Hamshakin mekudine ajihar kaduna domin ajerin masu kudi nagarin in akace daya to tabbas shine nabiyu
Matarshi daya mesuna Hajiya binta suna kiranta da umma yaransu hudu. Kabeer shine nafari sannan alameen se munawwara da autarsu amal
.
gidan alhaji jibrin gidane gidan tarbiyya Dan yaransu gaba daya babu mehalin banza
Mahaifiyarsu nabasu tarbiyya Dede gwargwado kudi besa tayi watsi da tarbiyyar yarantaba
tunbayan da mahaifinsu yayi rt yakoma fannin business nakasa da kasa yanada kamfanoni a fadin jahohin nigeria mutumne shi metsoron Allah bashida buri dawuce a yaransa yasamu megadonsa a gidan soja kullum adduarshi kenan inda Allah yataimakeshi ya bashi alameen
tunda alameen yafara mallakar hankalin kanshi yaji yana shaawar zuwa aykin soja
Koda yatuntubi mahaifinsa da batun bakaramin farinciki yayiba
baayi satiba yasamomishi aykin dayake akwai hanya
shiko kabeer accounting yakaranta yanzu haka yana ayki a cbn yanada mata daya Da yaronshi guda daya mesuna Waleed kasancewar sunan abbansu yaci
munauwara kuwa yanzu Tana js3 yayinda auta amal ke primary 4
tunda alameen yafara aykin soja gabadaya hankalinshi yamaidashi abangaren aykinshi kullum burinshi yataimaki kasarsa
lokacin a kaduna yafara aykin kamin ayi posting dinshi zuwa Abuja
.
kamar kullum yauma yataso daga ayki da misalin karfe shadaya nadare a nda yake aykin dan haka ta Badarawa yabiyo dan zefi mishi saukin isa gida
yawuto bustop kadan Dede galadima road jikin katangar gidan Baba boss yaganta tsugune Tana kuka ga gurin yayi shuru babu mutane har yawuce seyaji yanason sanin meyasa ta kuka kuma take zaune abakin titi
ribas yayi yadawo gurinta layin galadima road din yashiiga Dede gidan kallon kwallo yayi parking sannan yafito yatako da kafarsa zuwa inda take
sallama yamata agigice tadago kanta tana kallonshi kara matsawa kusada ita yayi yace yanmata meyafaru ne kika zauna anan kina kuka
ganin uniform din soja ajikinshi ne yasa tace aranta bari infada masa maybe yataimakamin
cikin kuka tace wlh mamanace tawuni yau Tana wankau har zuwa dare sannan tasamu kudin dazamuci abinci dashi tunsafen bamuci abinciba shine yanzu ta aykoni insiyo garin rogon dazamu sha bansan yaakayiba kudin suka fadi shine nake kuka dannasan yau seta kasheni tafadi Tana sake rushewa da kuka
yaisa haka alameen yafadi yana kallonta balaifi tanada kyau dede gwargwado kuma yarinyace dabazata wuce 18years ba
yasunanki yatambayeta
sunana AISHA tabashi amsa
inane gidannaku nunamasa gidan tayi da hannunta danba nisa
taso muje yace da ita
zaromishi ido tayi tace wlh najemata ba sakonnan yankani zatayi Dan Allah kawuce ka kyaleni anan
bazata yankakiba nizan biyata kudin
Amman Anshi Wannan Kijewancan shagon kisiyomuku kayan tea 2k yabata godiya tashiga yimasa kamar zatayi sujada
dagudu ta tsallaka titin tasiyo kayan tean dawowa tayi tace nasiyo
gaba tayi yana binta abaya harsuka isa kofar gidan yace shiga kiyimin Sallama da mamannaki wucewa tayi tana murmushi Dan ita yau jitake kamar sallah saboda zasu sha tea Wanda rabonta datashashi tun kafin babanta yarasu yanzu ko kimanin shekararsa hudu da rasuwa
mamanta Data fito taga sojane ke sallama da ita cikintane ya murda dakyar suka gaisa sannan yamata bayanin abinda Aisha tafadamasa
yakara dabata hakuri sannan yadauko kudi a aljihunsa kimanin50k yabata yace tayi hkr duk sanda yasamu lokaci zedunga lekosu godiya Mama takeyi harda hawaye
sallama yamata yakarasa gurin motarshi yashiga yanufi gida
*wacece Aisha*
.
Aisha Bello Musa shine asalin sunanta haifaffiyar garin kadunace acikin anguwar Badarawa
Sunan mahaifinta malam Bello mahaifiyarta kuma sunanta maimuna suna kiranta da inna
Su ukune agurin iyayensu Aisha itace tafarko se kannanta guda biyu zaituna da Umar
Shekarar Aisha 18 mahaifinsu yarasu tun Tana js1
Mahaifiyar itace taci gaba da kulawa dasu har zuwa yanzu da Aisha ke ss2 awata makarantar gwamnati dake anguwarsu
Kannanta ma duk government schools sukeyi
Rayuwace suke mecike da kunci Dan abunda zasuci yafi karfinsu se inna tayi wankau suke samu suci abinci so daya arana
Aisha yarinyace me dogon buri arayuwarta kuma bata da godiyar Allah ko kadan
Tahadu dasu Ruky da zuly ne amakarantarsu inda halinsu yazo daya suka kulla kawance
Basuda ayki dayawuce suyi gulmar kawayensu har gida ansha biyo Aisha akan tayi gulmar wata akureta
Mahaifiyarta macece me sakaci da tarbiyar yaranta tun bayan mutuwar mijinta Wanda hakan yasamu asaline asanadin zafin talaucin dasuke fama dashi
kwasam segashi Allah yaturomusu alameen
Tunda alameen yatafi besake zuwa gidanba hasalima baya biyowa ta unguwarsu
Aisha tafi inna Damuwa darashin zuwannashi sabida tunda tadora ido akanshi taji takamu dasonshi
Har bakin titin anguwarsu take zuwa tatsaya kozata ganshi babban abinda yasa takesonshi mijine na nunawa kawa itako bata da buri dayawuce ace taburge kawayenta
.
Yau jummaa dawuri alameen yataso daga ayki ta Badarawa yabiyo har yawuce layin Su Aisha se yatuno da ita danshi harga Allah yamanta dasu tun bayan barinshi gidansu kwana yayi yashiga layin Dede kofar gidan yatsaya
Aisha ce atsaye azauren gidan Kai ba dankwali takira me agwaliba Tana siya tun agurin tafarasha fadi take Kai malam wannan da tsami
Mamakine yacika alameen ganinta dayayi ahaka gashi tasa wata Data bayyana halittar kirjinta Dan har ta saman rigar ana ganinsu
Hon yamata dasauri takai dubanta inda taji hon din dagudu takarasa fitowa tanufeshi dasauri alameen yadauke idonshi daga kallonta sabida yadda take gudun yasa halittar kirjinta yin wani juyi na musamnam sabida Allah yawadata ta dasu
Karasowa tayi jikin motor Tana dariya
Sannu dazuwa soja sunan data kirashi dashi kenan
daurewa yayi yayi murmushi yace yauwa kanwata
Kashigo mana daga ciki tabashi amsa
Fitowa yayi suka shiga zauren gidan gaisheshi tayi
Yaamsa sannan yace
lalle bakyason shiri Dani tunda bakya muamala da dankwali kunyace takamata dagudu tajuya Tashiga gida tasako hijab sannan tafadawa inna sojan rannan yazo murnace takama inna dasauri tace uwaki Aisha shine kika barshi awaje yisauri kije ki kirashi yashigo dasauri tadawo gurinshi tamishi iso zuwa cikin gidan
Kan tabarmar da inna tashimfidamasa yazauna gaisheta yayi cike da girmamawa sannan yasanar dasu sunanshi dana mahaifinshi
Inna da Aisha ne suka hada baki gurin cewa Alhaji jibrin sulaiman de Wanda mukasani
mamaki tambayar tabashi sabida arude suka masa ita
eh shi yabasu amsa
Ajiyar zuciya sukayi dukansu daganan inna tabashi tarihinsu
yatausayamusu sosai inda daga karshe yayi musu alkawarin kulawa dasu
tundaga wannan lokaci alameen yamaida gidan inna kamar gidansu inyazo sallama kawai yake yashiga sosai yake musu hidima dantuni yasauyawa su Aisha makaranta ita da kannenta
Yayinda ita kuma Aisha kullum sonshi Karuwa yake azuciyarta
zuwa yanzu har waya yasemata iPhone6+ burin aisha yafara cika dantuni tasauya tayi kyau namusammam ga sutura Tana shiga ta alfarma bata da wata damuwa data wuce ta auri alameen
insuna waya so tari tasha yunkurin sanardashi halin datake ciki seta kasa
yau alameen ne yakawomusu ziyara bayan sungaisa da Inna ta tashi tafice dama zata barkane Aisha dawowa tayi kusa dashi tazauna tace Yaya alameen kamar yadda take kiranshi juyowa yayi Yana kallonta ganin yadda tanatsune yasa yagane mgnr dazatayi me muhimmaci ce sabida kwatakwata Aisha bata da natsuwa
yaakayine kanwata yatambaya
kunyace tarufeta amna bata dazabi dayawuce tasanar dashi
yaya Don Allah zaka iya aurena? Jin tambayar yayi kamar saukar aradu danshi Sam bayason Aisha amatsayin wacce ze Aura danyafison mace me natsuwa
AA yabata amsa
kuka tasamishi tana Don Allah kataimaka kaaureni wlh tunda nafara ganinka naji inasonka katausayamin sonka zeiya kasheni wlh tafadi Tana ruko kafarshi
dasauri yamike yace amma Aisha bakida hankaliko taya zan iya auranki Bari kiji infadamiki bakya cikin jerin macen danakeson in Aura Danhaka bazan boyemikiba wlh banasonki kiyi hkr kinemi wani yana gama fadin hakan yajuya yafice daga gidan ranshi abace
innace tashigo taga Aisha kwance akasa dasauri takarasa kusa da ita ga mamakinta farin kumfa tagani yana fitowa daga bakinta agigice tadagota ina babu numfashi ajiyeta tayi tafita tsakar layin Tana neman taimako napep akasamo akasa Aishan aciki inna Tashiga suka nufi asibiti
.
Koda isarsu asibitin likitocine suka rufu akanta seda suka share awanni biyu sanna suka fito
Inna dasauri ta sha gaban daya fara cikinsu
Likita ya jikinnata
Dasauki yabata amsa
Sannan yace kibiyoni office yajuya yanufi office dinshi inna nabinshi abaya
Bayan sunzaunane likitan yace mama meyasami yarinyarki hartake yunkurin kashe kanta tahanyar shan fiyafiya
Hankalin inna ne yatashi dajin abinda likita yace
Dakyar tabashi amsa da wlh bansaniba nide nasan bata dawata damuwa danko yauma lfy nafita nabarta dawowa nayi naganta a yadda nakawomuku ita
Murmushi doctor din yayi sannan yace kituntubeta tabbas akwai abinda yake damunta zaki iya zuwa kiganta dan tajima dafarkOwa godiya Inna tayiwa doctor din sannan tanufi dakin da Aishan take
Tana shiga suka hada ido daita dasauri takarasa bakin gadon tarukota
Kuka Aisha keyi tanacewa Inna nashiga uku alameen yace baya sona wlh inna įnasonshi zan iya rasa raina akansa kitaimakeni Inna
Dankari itace kalmar data fito abakin Inna ajiyar zuciya tayi sannan tace Aisha inbanda rigima irin taki inake ina Aminu yafi karfinki nesa bakusaba shine Dan shirme harda yunkurin kashe kanki sabida shi to wlh inbacci kike kifarka Aminu baze sokiba sabida ke ba tsarar auransabace
Kuka tasawa Inna kamar zata mutu hankalin Inna tash yayi rarrashinta tashigayi dakyar tayi shuru bacci yayi awon gaba da ita
.
Yau Monday Alameen ne yataso daga ayki gidansu Aisha yanufa sabida tunda yajita shuru kwana biyu bata dameshi dawayaba yasan tahakura dason datake mishi
Shiga gidan yayi kamar kullum kannen Aishan ne kawai agidan suma daalamun fita zasuyi ganinshi yasa suka nufeshi gaisheshi sukayi sannan yatambayesu inasu innanfa
Suna asibiti suka bashi amsa
meyafaru sukaje asibiti waye ba Lafiya
Aunty Aishane tasha fiyafiya tun shekaranjiya shine aka kwantardasu
innalillahi wainna ilahirrajiun itace kalmar da alameen yake nanatawa aranshi ko shakka babu yasan shine silar shan fiyafiyanta
Arude yatambayesu wanne asibitine
amsa suka bashi dacewa suma can zasu Kai abinci juyawa yayi yace to kutaho mutafi
Sun isa asibitin lokacin Aishan na bacci
Inna seda tayi mamakin ganinshi
Gaisheta yayi gami da tambayar me jiki
amsawa tayi cikin sakin fuska inda takara dabashi hkr abisa katobarar da Aishan tayimasa
Kunyace takamashi matuka inda yagaza cewa komai
Muryar Aishan ce takatsesu dacewa yaya kazo dubanine
dasauri yanufi gurinta yayinda Inna taja kannen aishan suka fice daga dakin
Gefen Gadon yazauna yakamo hannunta yarike yana kallonta tausayintane yakamashi ganin wai duk akanshi takeson barin duniya
Why Aisha? Itace yafurta
Kuka tasamishi tana Dan Allah Yaya ka aureni ko bakasona wlh ni inasonka inka gujeni bansan yadda zanyiba tafadi cikin kuka wanda yakarya zuciyarsa Dan alameen mutumne metausayi
rarrashinta yashigayi da kalamai masu sanyi
Yace kiyi shuru kinji naamice zan aureki amma sekin yimin alkawarin zaki cigaba dasona kobayan muñyi aure Kai tadaga sannan tace har inmutu inasonka yaya nagode Da alfarmar dakamin
hira suka sha tasoyayya wacce azahirin gaskiya alameen tausayinta kawai yakeyi basoba kamar yadda tadauka se shabiyun dare yamusu sallama yawuce da kannanta yaajiyesu gida shima yawuce nasu Gidan da burin gobe zema mahaifinsa mgn akan zeyi aure danso yake cikin wata guda ayi auran dangani yake kamar Zatasake shan fiyafiyar.
.
Koda alameen yama mahaifinsa mgn akan yanason ya auri Aisha be hanashiba sabida dama kullum adduarshi Allah yaba aminun matar daze Aura tagari
Mahaifiyarshima fatan alkahairi tamishi jin cewa Aishan bayar kowabace bedamesuba sude burinsu Allah yabasu zaman lfy
Tuni aka sallamo Aishan daga asibiti aka shiga hidimar biki sosai mahaifin alameen yasaki kudi ahidimar bikin
Kowa yaga hotonsu da alameen acikin kawayenta mamakin inda tasamoshi sukeyi itako Aisha abunnema yasamu se jijji dakai take ita adole tawucema saa
Inna tagyara Aisha sosai inda aka kawo lefenta akwati goma shabiyu cike da kaya na alfarma harda key din mota
Wayyo jamaa kuzo kuga murna gurin Aisha
Andaura aure akan sadakin naira dubu dari inda akabada dukiyar aure naira miliyan biyu
Jamaa Sun sami damar Halattar daurin aure aciki harda megirma gwamnan jahar kaduna inda shine yazama wakilin ango yaamsama alameen auren Aisha ahannun waliyyinta malam Adamu kani ga mahaifinta
bayan daurin aurene akayi walima da da misalin karfe biyar kuma sukaje dinner agaskiya shaanin bikin yakayatar anci ansha Masha Allah
.
Se misalin karfe takwas motocin daukar Amarya sukazo
Jamaa sukai tashiga da yan biki da yan gayyar sodi Dan aje aga mazaunin Amarya
Aisha dakyar aka rabata da inna bayan tamata fada sosai Tana kuka aka shige da ita mota
Ankai Aishan gidan iyayensa tukun
Sosai suka tarbesu hannu biyu cikin mutunci dazaa tafi da ita dubu dari Momy taba Amarya
Sannan akawuce da ita gidanta dake rabah road babu nisa sosai dagindan iyayennasa
gidan yatsaru matuka sabida mahaifin alameen ne yayi komai yace Aishan base tazo dakomaiba
Yan rakiyar Amarya sunwatse inda yaraage daga Amarya se aminanta Ruky da zuly
Abokan angone suka rakoshi su biyar bayan raha dasukayi sukayimusu adduar zaman Lfy da, zuria dayyiba
sannan suka sallami su ruky da 50k sukadaukesu suka maidasu gida
umartar Aisha yayi dataje tayi alwala tazo suyi salla bamusu taje Tayo shidama tuni yayi
jansu sallah yayi rakaa biyu tanuna godiyarsu ga Allah
bayan sun idarne yake mata tambayoyi game da addininta
Yayi matukar mamaki daya tambayeta farillan alwala guda nawane tace guda uku inda farillan sallah suka zama asirin da bakwai
Hankalinshine yatashi yashiga tambayar kanshi wacce irin Uwa nazabawa yaranane
Duk da yana cikin damuwa bebari taganeba inda yabarwa ranshi nanda wata biyu ze sata a islamiyya tamatan aure Dan baze zauna da jahilaba
.
Kajin daya shigo dasu yajawo gabansu inda yatashi dakanshi yadauko musu plate da kofuna
Aisha bazancan kunya zagewa tayi taci kajin sosai Wanda shi alameen abin kunya yabashi daga karshe yaso sashi dariya dangama Amarya Aisha hardasu tauna kashi hakade suka
Gama ci sukaje sukayo brush
Suna fitowa Aisha gado tanufa alameen ne yakwashe kwanukan yakai kitchen
Dakinshi yaje yasauya kaya zuwa na bacci sannan yakoma dakinta tananan kamar yadda yabarta
Cewa yayi bazaki sauna kayan jikin kibane kika kwanta dasu
wata Mika tayi gami da wata gyatsa mekarfi sannan tasakko akan gadon tanufi Wadrop Tana fadin wash wlh nagaji
Doguwar rigar bacci tadauko tasa duk yana kallonta sannan tazo tasake hayewa gado kayan data cire tabarsu akasa shi yakwashe mata yaadana shima hawa gadon Yayi bayan yakashe wuta yajamusu bargo. Kwanciyarshi keda wuya yaji Aisha tamirgino jikinshi inda tashiga bankaro kirjinta suna gogarshi
hankalinshine yafara tashi sabida betaba jinn hakanba
nande cikin dabara har tagama daga mishi hankali
wayyo abunka da sabon shiga yasha wuya kamin yasan hanyar daakebi shima seda taimakon Aisha
se alokacin tayi danasanin daukar shawarar su zuly dansune sukace tayimishi abinda tayi da farko
kuka tasamishi Tana rokonshi Allah annabi akan yayi hkr yakyaleta
ina alameen yayi nisa bayajin Kira duka dayakushi cizo babu wanda batamishiba amma abanza araina nace dama taya zeji bareshi dayake soja
besauraramataba se gefin asuba
kukako tayishi har muryarta ta dashe idanuwa sunkumbura baabinda yafi damunta irin breast dinta dasuke Mata zafi sabida sunji maza uwa uba kuma kasanta
shiyafara yin wankan sannan yahadamata nata ruwan dawowa yayi yabude bargon dasauri Aisha tarufe idonta Dan ba kaya ajikinta murmushi yayi yadaukota Kamar jaririya yakaita toilet jinta aruwan zafine yasata kwalla masa kara dan wani radadine taji yanashigarta
lallabata yashigayi har yasamu tabari yamata wankan yanadota atawul yadawo da ita dakin
itako har yanzu idonta arufe yake azuciyarta ko se tsinema su Ruky takeyi
agurin bacci yadauketa
shikuma kayansa yasauya yadauro alwala yatada sallah yana godewa Allah dayasa rawar kai darashin natsuwar Aisha besa ta zubar da mutuncinta
inda akarshe yaroki Allah dayasa sonta azuciyarshi dansuji dadin zama tare
be tashi agunba sedaeyayi sallar asuba sannan itama yatsheta tayi kuka tasamishi akan ita bazata iya tafiyaba daukarta yayi yakaita toilet din tayi alwala yadaukota yadawo da ita doguwar riga yadaukomata da hijab tayi sallar azaune
bayan ta idar daukarta yayi yanufi Gado da ita kuka tasamishi tana bashi hkr dan tazaci zesake nemantane lakashemata hanci yayi yana murmushi yace matsoraciya babu abinda zanmiki bacci zamuyi
kwanciya sukayi yanata samata albarka abisa Kawobudurcinta datayi gidan mijinta ahaka har bacci yadaukesu yana rungume da ita
.
Basu tashiba se karfe sha biyu narana
Wanka suka shiga Wanda Aisha se rufe idonta takeyi shiko dariya yakemata
Shiryawa sukayi cikin shiga ta alfarma
Falo suka sakko ga mamakinsu kuloli abincine Jere akan dinning
Karasawa gurin alameen yayi wata takarda yagani ajiye agurin anyi shot note ajiki
Morning bross munawwara bye
Shine abinda aka rubuta ajiki murmushi yayi yace munawwara kenan
Kamo hannun Aisha yayi suka zauna suka ci abincin
.
*bayan sati uku*
Rayuwa suke mecike dajin dadi aiya wannan lokacin
Sede alameen yalura Sam Aisha bata iya girkiba Wanda sotari tagwammace suci complaks
Biye mata kawai yakeyi dan beson bacin ranta
Uwa uba ga kazanta setayi sati bakinta bega brush ba
Wanke wanke ko seta tara nasati guda kana shiga kitchen din inbanda wari baabinda yakeyi gata akwai wasa da sallah
Abin yana damun alameen bashida yadda zeyi ne
Koda yayimata mgn akan tadan dunga gyarawa fada tahaushi dashi wai ita dawanne zatajine cikin dare yahanata bacci sabida jarabarshi safiya tayi kuma zatayi baccin yace tayi ayki to itafa gaskiya tagaji sede yazaba ko aykin ko kuma biyamasa bukata Dan ita gaskiya bazata iya Yi dukaba taja tsaki tabar gurin
Ranar kusan kuka alameen yayi sabida Allah yasani shi mutumne mabukaci baze iya jure kin kwanciya da itaba sannan kuma shi mutum ne metsabta baze jure zama da dattiba
Bashida zabi dayawuce yabarta tayi kazantarta son ranta danshi batun Hakura da nemanta baze iyaba
Haka alameen yaci gaba da hkr da halayen Aisha zuwa yanzu seta fice anguwa batare da izininshiba sede yadawo yatarar batanan Uwa uba kawayenta datake fifitawa fiye dashi yasha zuwa yatarar dasu Tana basu labarin yadda suke muamalar aure,abincin gidanshi takwashe takai gidansu taba kawayenta
dazaran yace zemata mgn seta rufeshi da masifa
makaranta dayace ze sata rufe ido tayi taci mushi mutunci akan wai yamaida ita jahila Dan haka ba inda zata
Anyimishi transfer daga Kd zuwa Abuja da murnarsa yazo yana fada mata akan zasu koma can dazama
Tsaki tayi sannan tace Allah yasauwake nakoma Abuja dazama nufinka nabar kaduna shikenan narabu dasu zuly kenan tab to wlh dasake ba inda zani kama rainamin wayo wlh
Haka alameen yanaji yanagani yashirya yatafi batare data bishiba koda yaje yiwa mahaifansa sallama
Seda suka tambayeshi daita zetafiko
Aa yabasu amsa fada daddy yashiga yimasa inda yashaidamusu itace tace batason zuwa
Fatan alkhairi suka masa yatafi
Tunda yaje Abuja kullum cikin azumi yake seda yashare wata shida sannan yasamu pass nazuwa gida tun yanacan yashaidamata jibi zedawo
.
ranar daya dawo bata gidan ta tafi anguwa restaurant yakoma yasiyo abinci amota yaci abincin Dan gidan kamar bola ga wari dayakeyi azatonshi yanaganin rabon gidan da Shara tun kafin yatafi Abuja se dare tadawo
afalo ta tarar dashi koda taganshi sannu kawai tace mishi tahaura dakinta
suman zaune alameen yayi
Ganun tunda tadawo bata Kara bi takanshibane yasa yamike yaje dakinta
tana zaune Tana waya da Ruky
koda yashiga seda tashare fin awa Tana magana da rukyn sannan tagama.
Kallonshi tayi awulakance tace yan Abuja kenan
mikewa yayi yakoma kan gadon daurewa kawai yakeyi sabida warin dakin dakuma warin bakinta
ruko hannunta yayi yace haba Aisha taya zaki fita bayan nacemiki yau zan dawo
tsaki tayi sannan tace shikenan sabida zaka dawo sena Kasa raka Ruky bikin kawarta ko nifa kadawo kenan zaka fara shegen fadanka to wlh easy Dan yanzu badabane
dariyar takaicice takamashi
sannan yace ni duk bawannanba Aisha amatse nakefa pls kitaimaka yafadi yayinda yarungumota jikinshi
nashigesu ni Aisha ace ayi mutum kamar bunsuru bashida hakuri to wlh dasake
alameen dayake yaruga da yakamu hakuri yadunga bata dakyar ta yarda shima seda suka tsadance akan ze sake mata mota
ayko seda yadirji kudin motarshi danse asuba yakyaleta duk da tsamin datake na rashin wanka
.
haka rayuwa taita tafiya kullum Aisha cikin yiwa alameen rashin mutunci take tayi tayi yadaukomata house girl amma yaki Dan yasan tonon asirine agareshi
haka tadunga balai inyakoma Abuja kullum cikin azumi haka inyadawo kaduna ma sabida inde yaje gareta seta bukaci kudi shiyasa wani lokacin yake hakura amma inde zebiya ko so dari zeyi bamatsala sabida pay before service ce ita
motar daya canja mata ita tasake bata damar yawo agari
har alameen yagama zama a Abuja Aishan bata taba takawa ba har zuwa yanxu daaka turashi rivers state
shima dayanuna yanason tafiya da ita balai akayi badan kadanba gashi yanzu yasamu Karin girma sosai a gurin aykin inda yanzu yakai matakin major duk yadda yaso suzauna Lfy da Aishan Abu yaki yiwuwa yayi danasanin aurenta yafi akirga kuma shi abinda yasa bayason sakinta tausayinta yakeji danshi har yanzu baya sonta amma ita gani take sonda yakematane yasa yake hkr
haka yakoma fatakot shikade
wannan Karon iyayensa basu tambayeshi ba.
0 comments:
Post a Comment