'YA'YA DA KUDI Page-1~5
.
Tarin wanki ne a gabanta, sai faman wanke su takeyi, kalo d’aya zaka mata ga gane ta gala baita sosai, har k’arfin har bata jin karfin jikinta. Gwaggo ne ta taho da wasu kayan wankin ta kara mata, tace “Khadi maza- maza kiyi sauri ki wanke ma Beeba kaya, zata gidan Innarku. A wahale na d’ago nace “Inna ga wasu sabbin kayanta can na wanke su, sun bushe tasa su, kuma suna da ky’au, gash’i nayi wankin da yawa na gaji. Gwaggo wani uwar ashar ta narko, wanda ni Rash bansan lokacin da nayi baya da sauri ba. Shako ta Inna tayi tace”dan jakar ubanki ni zaki fad’a ma kin wanke wasu, kuma har kina iya cewa kin gaji. Eh! Lallekam yau zaki gwadan ke yar Zamani ce, ban isa dake ba ko?.
.
Khadi cikin muryan kuka tasoma cewa”dan Allah! Gwaggo kiyi hak’uri wlh ba da wara manufa na fad’i hakan ba. Gwaggo kara shaketa tayi tace”ko uwar ki ma bazata mayar min da martani ba. Kafin Khadi tayi magana ji kake tass tass tass ta wanke ta da mari har sau uku, dukanta tafarayi ta kota ina. Wayyo ni kaina Rash na tausaya ma Khadi, don ga alama fuskan gwaggo nan bata da tausayi ko kad’an Taku a kullum mai k’aunar ku Gwaggo sai da tayi likis ma Khadi kafin ta ky’aleta, tace”wlh sai kin gama wankin nan yau ko na miki dan banza duka, sha-sha kawai, mts tayi tsaki ta nufi cikin d’akinta. Khadi kam kuka tasha ga wani yunwan da ke murd’amata ciki. Kama cikin tayi ta tamke da d’an kwali abunka da Khadija maganin Maza cikin dakiyar zuciya ta fara wankin , da ikon Allah kafin akira Sallah la’asar ta gama. Gwaggo ta fito da abinci a d’an k’aramin kwano wanda ko d’an yaro bazai ish’esh’i ba. Ta turo mata kwanon ta juya tayi d’akinta ko tausayin Yarinyan nan bata ji ba. Ga uban aikin da ta mata a cikin gidan kamar jaka. Malam Ahmadu ne ya sh’igo da Sallamansa, in donsa ne ya sauk’a kan Khadi dake kwance tamkar wanda aka d’aura ma dutsin dala da gauron dutsi aka. Da sauri ya k’arasa gurinta cike da tausaya wa, ya tallabo ta yace “Mama na ya dai? Mai ya same ki na ganki haka? . Gwaggo ta fito cike da masifa tace”komai ne ya same ta ko zaka karb’a mata ne, sai in sani. Cike da b’acin rai Malam Ahmad ya nufo ta, yace”kee Hauwa wlh ki kiyaye ni zan sas-saba miki akan Khadija sam ba kya tausayin yarinyan nan. Gwaggo tace “ina ko zan tausaya mata ba sanin zafinta nayi ba bare na san miye tausayi. Malam yace”duk aikin da take yi a gidan baky’a gani ko?. Kuma ba ky’a sanya yar cikinki. Wannan yarinya Yata ke a gun mu, duk irin rikon da muka mata Allah zai tambaye mu, Hauwa kiji tsoron Allah. Gwaggo tace”ehehe wa’azi zakamin ai tsoron Allah kulum cikinta muke, yar wani ba yata bace nawa kawai na san, fuuu tayi d’aki in ka gama sai ka sanar min.
.
Taku a kulum mai k’aunar ku Cikin ta kaici yazo ya tallabi Khadi ya d’agata sai a lokacin ya kalli d’an abinci da gwaggo ta bata. Taburma ya d’auko a d’akinsa ya sh’in fid’a mata, ya zaunar da ita. Kular abincinsa ya kawo mata tare da juye ruwa mai zafi ya had’a mata Lipton ya bata da kyar ta iya sha. Abicinsa ya kara mata, sai da ya tabbatar ta kosh’i kafin ya ci sh’ima. Khadi ta mik’e jiki ba kwari ta nufi rijiya ta d’ebo ruwa ta nufi bayi, wanka tayi ta fito, ta sha fa mai kayanta masu d’an kyau ta saka ta dawo waje gun Malam don gudun bala’in Gwaggo. Malam yace”Mama nah bazan fasa miki nasiha ba, inaso ko kasance mai yawan hak’uri kinga halin Gwaggon ku kullum Addu’a nake mata Allah yasa ta gane gsky. Khadiya duk halin da kika samu kanki, ki kasance mai hak’uri zakici riban rayuwanki. Kai ta d’aga masa alamae Eh!. Heeba ce ta sh’igo da Sallaman ta, cikin fara’a ta k’araso gun su, sannu da gida ta musu kafin tace”Addah ina ta sauri inzo in tayaki aiki, da aka tash’i a makaranta, ban samu abun hawa ba, Gash’i har kin gama. Khadi tayi murmushi tace”ba komai k’anwata, ya makaranta?. Alhamdulilah! Ki d’auko abinciki kici to Adda. Malam yana jin dad’in yanda yaransa suka had’a kai, baran Beeba da sam bata gado halin uwarta ba, heeba ya rinya ce mai hankali kamar Khadi. Sabanin Rabi da ke ji da taken rash’in kunya, halinta sak na uwarta hatta kama da Gwaggo take kama. Gwaggo tafito tsawa ta daka ma Beeba kee mai kikeyi a gunsu, kin dawo ko sanar ni bazakiyi ba, ni bana son kina taraya da mai fiska kaman na muciya. Oh! Ni Rash nace”wannan Gwaggon wata irin macece ta fiye son kanta, anya ma idonta na gani kuwa?. Duk irin kyan Khadi tana zaginta. Ko beeba ma bazata gwada mata kyau ba don ta d’aran mata nesa ba kusa ba. Taku a kullum mai k’aumarku . Jiki ba kwari Beeba ta nufi d’akin, don sam ita bata son irin yadda mahaifiyarta ke nuna tsana ma Khadi.
.
Gash’i ko kad’an Khadi bata nuna damuwarta kuma hakan ba sh’i zai hanata biyayya ba.Allah yasa Gwaggo ta gane. Ya sh’irya mana ita Ameen. ‘Dakin su tash’iga Gwaggo ta balbaleta da masifa, Gwaggo tace”Beeba bana son ganin ki da wancan mai fuskan mujiyan, kema kuma sai niman kai kike da su. Ni har Malam da ke biye mata ba kyalesh’i zanyi ba, ko kad’an bana k’aunar in bud’e ido imganta a gidan nan. Beeba tace”haba Gwaggo ba kyau fad’an haka fa, kuma ae Addah tana iya k’ok’arinta gurin kyautata miki. Ita ne kulum cikin aiki bata hutawa ko ni bana miki aikin da take, nikam ina son Addah na tana da halaye mai… Bakinta Gwaggo ta make tare da wata harara tace”kee a kul d’inki kar na kara jin cewa kina had’a kanki da wannan yarinya, Ko kema ta shanye miki Zuciyan ne?, kama yanda ta shanye na Malam baya ganin laifita baya son amata fad’a. Beeba tace”ko d’aya Gwaggo gsky kenan Khadi tana da halaye mai kyau. Mts Gwaggo ta ja tsaki ga abinki can maza ki ci don zaki gidan Innan ku, zaki anso min aika a gunta. Beeba ta d’auko abinci zatafita gunsu Malam Gwaggo ta dakatar da ita, ba yanda ta iya dole yasa taci a d’aki badan taso ba, don ta fi jin dad’in kasancewa da yar’uwanta.
.
Gwaggo tace”Beeba yi sauri ki sh’irya kije min gidan Inna ku. To ta amsa ta kammala cin abinci tayi wanka ta d’auko kayanta masu kyau ta sanya su, ra fes da ita. Gwaggo “nagama sh’irin ke nake jira kizo fad’an sakon, don inje kar dare ta min a hanya. Sai da Gwaggo ta d’auko sakon da zata kai ma Inna kafin ta bata kud’in mash’in tace”kice ta had’a miki duka aikan harda kayan da na saya d’in, to ta amsa ta fito sai da tayi sallama wasu Malam kafin ta tafi. Taku a kullum mai k’aunarku
.
KUNA TARE DANI MU CI GABA?
0 comments:
Post a Comment