'YA'YA DA KUDI Page 11-15
.
Gwaggo cikin hayaniya da masifa, Tace”mai yasa baka tura, Beebah ko Rabee’atu, sai Khadi, to sai dai na k’ona kayan. Malam kasa magana yayi, tsaban takaicin dake damunsa, wannan wace irin fitinaniyar macece?. Gwaggo ta d’ibi kayan, tayi hanyan kitchen dasu, Malam na ganin haka ya bita, kafin ya isa, har ta fara sawa a wuta, kwacewa yayi tare da zaro na wutan, wani gyalens mai kyau, da sauri ya taka, da takalmin sa, wutar ta mutu. Wani gumun kalo ya mata, duk iskancinta sai da ta shiga taitayinta, ta fito a kitchen, koda tazo dai-dai gun Khadi shureta tayi da kafa, sai da Khadi ta fad’i, ta Beeba ne ta d’aga ta, rana mata sannu, Malam yace”Hauwa mai yasa baki da tausayi ne?. Kina tuna kema zaki mutu kuwa?. Ki sani fa duk inda, iyayen Khadeeja sukaje, kema zakije, kuma Allah baya kyaleki bane, kuma nima ba wai fa tsoronki nake ji ba, ina d’aga miki k’afa ne. Hauwa kisani ‘YA’YA DA DABBA, DA DUKIYA, BA’A K’ETAR SU, bakisan wacce irin baiwa Allah yayi ma Khadija ba, bakisana wani irin taimako, zata miki a rayuwan ki nan gaba. Gwaggo ta kali Malam cikin kalon da ban d’au maganar ka da muhimmanci ba, tace” ehehehe Khadi ne zata taimaken, ahir ahir, Allah ya tsare gatari da saran k’ota, ni da Khadi badai muzauna inwa d’aya ba. Malam ya kaleta yace”Hauwa da badun Allah bayason saki ba, to da yau tabbas sai kin bar gidana, kuma kinci albarkacin Khadi da ‘YA’AYAN da kika haifa. Koda Malam ya ambaci saki, sai da k’irjin Gwaggo bada sautin damm! damm!..
.
Amma cikin k’arfin hali, dake shaid’an ya mata kururuwa, tace”sai me in ka sakeni?.daman wani abu nake samu a gidanka, in banda gayyan tsiya. Malam ya d’aga hannu yace”Ya Allah kana jina, kana ganin abunda ke faruwa, Ya Allah ka azurta Khadi da abunda zata taimaki Hauwa’u. Yana dasa aya, Gwaggo tace” ba amin ba har abada, sai dai ku da wannan mayyan, talashe zuciyarku. Fuuuu Gwaggo takama hannu Rabee, tajuya ta kali Beebah, kee da ta lashe maki zuciya, saikiyi ta makale mata, suka shiga d’aki. Malam ya kama hannu Khadi, da Beeba ya kaisu d’akunsa, albarka ya samusu, ya musu nasiha, tare da k’ara bama Khadi hak’uri. Tace” Baba ba komai, ae Gwaggo uwatace, ita na bud’i ido na gani, ita na santa, kuma ina mata fatan Allah yasa ta gane Ameen ya amsa. Dr Umar kuwa, yana komawa gida, ya tarar da Mum d’insa, suna hira da Ilham, shima zama yayi, tare dacewa washh, Mum tace” daga ina haka Son?. Gyara zama yayi, ya kali Mum yace”daga gidansu Khadeejat nake. Kafin Mum tayi magana Ilham tace”bros nikam ina son gani Aunty Khadejat d’inana. Kulum sai labarinta mukeji, fuskansa cike da murmushi, yace”zaki ganta har sai kin gaji da ganinta ma. Mum tace” Alhamdulilah! Allah ya nunan ranan da Babana ya samu wacce yake so, sai fatan Allah ya kaumu lokacin biki, cike da zumu d’i ya amsa da Ameen. Dr Umar yace” Mum baki ga yarinyan bane, gata da hankali, kuma inkinji rayuwanta abun tausayi, nan ya basu labarin had’uwansu, da irin wahalan, su Mum da ilham sun tausaya mata. Ilham tayi karaf tace” bros to ina wacce katab’a ban lbr ta, itama wacce Khaji a agun Dr Abdul?. Ummm itakam har yanzu ba labarinta. Mikewa zai haura sama, yakali Mum yace”yau she Dad zai dawo daga Dubai d’in?. Umma tace” umm sai next week. Ok! Allah ya kaimu. Sai da ta dad’e kafin, ta d’an tashi, sannu suke mata, bata iya amsawa ba, sai da ta huta sosai, Dr Umar ya kaleta, cike da tausaya, Yace”yan’mata mai yake damunki haka?.
.
Da har kike irin wannan tunanin?. Kasacewa komai tayi, sai da yamata fad’a sosai, Yace” ki tashi mukauki gida, sai a lokacin ta zaro ido, kai ta girgiza musu alamar a’a, bayanda basuyi ba, amma fir taki, daga k’arshe Dr Umar ya tsara mata Napep, nan ta bada kwatance gidansu, sai da tashiga Napep sun d’au hanyan, Dr Umar ma motarsa yashiga, har yayi hanyan gida, komai tuna ya juya kan motarsa zuwa Dakata, gudu yakeyi sosai, cikin sa’a ya hango Napep d’insu, a baya ya rinka binsu har suka kai k’ofar gida. Mai Napep ya tafi, ta tsaya a k’ofar gida, tana tunani shiga, gashi yamma tayi sosai, ga yunwan da takeji, da kyar ta iya shiga gidan. Ganin ta nufi cikin gidan ya fito daga motarsa yazo dai-dai zauren. Assalamu’alaikum ta fad’a cike da tsoro, kara shiga ciki tayi ganin Gwaggo bata kusa, da sauri Gwaggo ta fito,”kee karuwa yar’iska ina kika fito?. Cikin fargaba da zaro ido, Khadi tace” wallahi Gwaggo gun d’inki naje. “Karya kike dan ubakiki, dukanta Gwaggo tayitayi kamar ta samu jaka. Dr Umar tun daga, nesa ke jin murtan ta tana ihu, sai leke yaykeyi, zuciyarsa na tafarfasa, ganin Gwaggo ta d’auko muciya, Beeba da ke gefe sai kuka takeyi, tana bama Gwaggo hak’uri, Dr Umar dake cikin zaure, ganin Gwaggo, ta d’aga muciya zata kwada mata, bai san lokacin da ya shiga gidan ba, rike muciyar. Gwaggo cikin fushi, d’ago tana masa kalon raini, daga kai waye ne?. K’ok’arin fincike muciyar takeyi, Malam da ya dawo daga tafiya, yaji da sauri ya k’araso cikin gidan, ganin abunda ke faruwa yace”Hauwa mai kikeyi haka?.
.
Nan fa tafara ba Malam labarin karya da gaskiya, ta d’aura dacewa”Khadi karuwa ce yar’iska, da sauri Malam ya dafe kansa, don harcikin zuciyan sa, yaji kalman ta dake shi. Cikin kunan rai, Dr Umar yace”wannan sharri ne wlh, nan ya kwashe abunda ya faru ya fad’a musu. Gwaggo nan ta tire, “sam ni banyarda ba, shine ya d’auketa suke iskanci tare, Malam ya mata kwalon uku saura kwata, hak’uri ya fara ba Dr Umar, tare da masa godia. Dr Umar yayi musu salma ya nufi gida, cike da jimamin rayuwan Khadi. Tun daga wannan ranan, Dr Umar yasamu gurin zuwa, gidan gun Malam susha hira sosai, wani lokaci Malam ya turo Khadi su gaisa, sam bainuna musu ko shi waye ba, kuma bai taba sayan wani abu ya basu ba. A hankali shak’uwa ta shiga tsakaninta da Dr Umar. Kamar kulum Dr Umar, yayi wanka cikin manyan kaya, yayi kyau sosai, sai da ya biya ta, Sahad store yayi sayya, kaya ya had’a ma Khadi, less da atamfa da shadda d’inkaku, da su takalma da jaka.
,
A hankali yake tafiya, har ya shigo unguwan, cikin sa’a ya samu Malam na gida, sai da suka gaisa, ya bud’e boot din motarsa, buhun shinkafa biyu, na tuwo dana dafawa, sai taliya carton biyar da makaroni, harda su maggi star. Malam dake gefe, ya tsaya yana kalon ikon Allah. Sai da aka gama shigarwa, Yace”Umar mai yasa kayi irin wannan d’awainiyar, kai ya sunkuyar, Malam ae ba komai, kai mahaifi ne ae. Godiya yayi masa sosai, dai-dai lokacin, Khadi tafito Gwaggo ta aike ta, tazo wuce musu, ta gaida Dr Umar ya amsa cikin kulawa zata wuce, Yace”tsaya ki amshi sak’onki, don ina sauri yau, wasu manyan ledoji ya miko mata, Malam Yace” Umar d’awainiyan yayi yawa, bakomai Baba sauri nake, sai na dawo, godiya yayi masa Dr Umar yaja motarsa ya bar gidan, Khadi ne tafara shiga cikin gidan da laida, Malam na biye da ita. Gwaggo tana ganin laida a hannu Khadi, da sauri taso zata amsa, ganin Malam tace”yau samuwa mukayi haka?. Malam yace”eh! Wallahi wanda ya taimaka ma Khadi ne yayi mana alkairi, Gwaggo ta dafe k’irji lokacin ta zazzage kayan ciki, nan fa ta tsorata, “ae wallahi abunda bazai yuwuba kenan, wannan k’arya ne. Malam daman funa furci ka kula shine ka tsiri kai Khadi koyar d’inki, don kana son ta had’u, da wanda ya kawo kayan, mai yasa baka tura Beebah ko Raee’atu ba?. Sai Khadi, nan tafara tonan silili ma Khadi, cikin takaici Malam ke kalonta. Da sauri ya tareta, ta fad’a hannusa, sunanta yakira, Khadijat! Khadijat Khadijat…
.
Pls ki tashi, kar ki tafi ki barni lokacin dana ke bukatarki, kene farin cikina. Pls Khadijat, yana jijigata, amma sam ko motsi batayi, Dr Umar ya fita a hayyacinsa, sai sam batu yakeyi, Gwaggo ko wani ruwan sanyi, tasake d’ebowa bata tsaya, wata-wata ba, ta k’wara ma Dr Umar. Duk da na da lafiya sai da ya razana, ajiyar zuciya ya sauke, nan take ya dawo cikin hayyacinsa, hannu sa ya kala, da sauri ya d’auketa, cikin mota ya sanya ta. Da gudu yabar unguwan. Asibitin Murtala ya wuce, yana zuwa ya d’auketa a hannu, Emergency yayi da ita. Kasancewar shi duty safe ke dashi, Dr Abdul ke duty kwana. Da sauri ya d’aga waya ya kirashi, “Dr Abdul dan Allah kazo Emergency, Khadija tace bata da lafiya, kazo ka taimka min, muryansa kaman zaiyi kuka, duk ya rud’a Dr Abdul, don bai kuma taba jin, Dr Umar cikin wannan, yanayin ba. Dr Abdul yace”Friend wacece Khadija?.cikin fushi yace”Malam in zakazo to in bazaka zo nakira, DR James, kashe wayan yayi, yafara kiran Dr Jame kenan, Dr Abdul ya turo qofar ya shigo. Da sauri yayi kanta, yana ganin Khadi ce, mamaki ya cikasa, tambayoyi yafara yi makansa,” daman Umar yasan Khadi ne?. “To mai yasa yarinka min tambayoyi akanta?. “Ta ya’akayi tazama Khadijansa?.
.
Maganan Dr Umar ne ya dawo da shi, daga dogon tunanin daya shiga. Dr Umar Yace”kai Malam, lafiya kake mata, irin wan kalon?. Da sauri yazo ya kareta, cikin kishi da jin haushi, yake maganan. Dr Abdul bai cemasa uffan ba, cikin hanzari yasoma dubata, daman yariga yasan matsalanta, cikin ikon Allah, ansamu numfashin ta, ya dawo dai-dai. Sai dai bata farka ba, sun mata aluran baci, don ta samu hutu. Special room aka kaita, don hutawa ita kad’aine a d’akin. Dr Umar ya zauna, a bakin gadon ya zuba mata ido, ko kyaftawa ba yayi. Ji yake kaman ya k’arba mata ciwon, Dr Abdul ne ya shigo, yace”Ya mai jiki?. Da sauki ya bashi amsa. “Allah ya k’ara sauki. “In ka gama kasameni a office d’ina. Ok! Dr Abdul ya fita, office d’insa ya koma, ya zauna cike da tambayoyi, a fuskansa. Dr Umar sai daya kai, kusan kamar 1hrs, kafin ya kira nurse, yace”ta kulamasa, da patient d’insa. Da sallama ya shiga office d’in Dr Abdul, bayan ya zauna ne, Dr Abdul Yace”friend ina kasamu Khadi?. Ko dama ka santa tun-tuni, Dr Umar yace” kai ka santa ne?.
.
Dr Abdul ya d’aga masa kai alamar eh!. Ajiyan zuciya Dr Umar yayi, nan ya kwashe labari, tunga randa ya fara ganinta, har yanzu, dayake fama da azaban sonta. Sai da Dr Abdul ya jijina kai, yace”Allah mai iko, to ae itace Khadijan, da ranan kaji ana case akanta. Cikin mamaki Dr Umar yace” mai kace ne ban fahimta ba. Nan Dr Abdul yabashi labarinta, iya yanda ya sani. Umar ya tausaya mata ba kad’an ba, wani Sonta da Qaunarta, suka k’ara shigansa. Cikin tsokana Dr Abdul yace” friend amma gaskiya, ka cika kishi, kawai don ina mata kalon sani, amma kawani tare, dariya Dr Umar yamasa, tare da kai masa dukan wasa. Malam dawowansa, daga kasuwa kenan, aka basa labarin, abunda ya faru bai iya shiga gidan ba, ya juya zai tafi kenan, yaga Beeba ta fito, duk ta rud’e hijab ma bai-bai tasa. Da sauri ta bisa, Napep ya tsara musu, suka nufi Asibitin Murtala. Zuciyan Malam sai tafasa yakeyi, yana tunanin wani kalan hukunci, zai yanke ma Gwaggo. Don abuntan yayi yawa,”to wai mai Khadi ta tsare mata a rayuwanta ne?. Da takeson ganin bayanta, tabbas zai Aura da Khadi, don ta huta da bala’in Gwaggo.
0 comments:
Post a Comment