'YA'YA DA KUDI Page 21-25
.
Sai da yayi musu, sayya mai yawa, ya nufi Asibiti. Ko da ya shiga, sai da ya biya office dinsa, ya ajiye wasu files, kafin ya nufi ,d’akin da su, Khadi suke. Da sallama ya shiga, suka amsa masa. Beebah ne “ta gaida shi, cikin girmamawa ya amsa, “ya tambayeta ya mai jiki?. “Ba shi amsa da sauki Alhamdulilah!. Fita tayi ta basu guri, ya kali Khadi da ke kwance, “ta gaida shi, cikin muryan, marasa lafiya, “ya amsa mata, tare da tambayan ya jikinta?. ta bashi amsa da sauki. Ido ya zuba mata, har saida tasoma jin kunya, ajiyar zuciya ya sauke, ya kara lumshe idonsa, a hankali ya bud’esu, cikin wani salo, da karya murya, ya kira sunan Khadeejat!!!. Duk da rashin lafiyan da take fama dashi, sai da taji, jikinta yamata, wani iri,”Na’am ta amsa masa cikin siririyan muryanta. Ya kaleta, yace”Khadeejat!. Na kasa hak’uri akanki, Khadeejat!. Ki taimaki zuciyata, da take fama da azaban sonki, My Khady tun randa, na fara d’aura idona a kanki, nakamu da qaunar ki, ki taimaka in samu gurbi, a cikin zuciyarki. Duk maganan, da yakeyi Khadi, bata ce komai ba. Sai lumshe idonta datayi, kamar mai jin bacci, cikin kasa-kasa da murya, harda d’an sauk’owa daga kujera, Yace”pls Khadeejat ki taimaki rayuwata. Tabbas nasan ina aure ki, a matsayin mata, kuma uwar ‘YA’YA NA, nasan zasuyi alfahari dake, a matsayi uwa ta gari. Khadeejat!. Ki sani duk wani abunda akeso, mace ta gari ta had’a, kin had’a. Khadeey na!! I’m deeply in ur love,pla don’t let me go!! You d joy of my lyf, pls n pls Khadeey!!, ki samamin matsuguni, a zuciyarki, ko k’ad’an ne. Ganin shiru batace komai ba, Yace”Khadeetaul~Kubrah, in kin amince pls ko murmushi, kimin in samu sanyi, a zuciyata. Ganin shiru yasa yanayinsa ya canza, duk da idonta na rufe, tana iya ganinsa, amma shi bai lura, da hakan ba.
.
“Wani lallausan murmushi ta saki, tare da rufe fuskanta. Ganin haka, ya sauke ajiyar zuciya, yayi godiya ma Allah. Juya masa baya tayi, duk yanzu kunyansa, ta soma ji, ya dad’e yana mata hira, ganin tana jin kunyarsa, ya ajiye mata waya tare da mikewa, Yace”yau k’anwata kunya na takeji, amma badamuwa, wataran zanyi maganin kunyan nan. “Ga wannan d’an ajima zamuyi waya, ya fita abunsa, a waje yayi sallama da Beebah. Ko da tashi go d’aki, lokacin Khadi ta mike, sai murmushi take zubawa, Beebah tace”Addah lafiya naganki cikin wannan fara’a?, cikin zumud’i ta labarta ma Beebah, itama tayi murna sosai,nan suka bud’e, kayan da yakawo musu, yasha addu’a kam, suna bud’e na waya, kalo ya koma kansa, sun yaba da kyan, wayan sosai. Sai can dare taji wayar na k’ara, ko da tad’aga wayar kasa d’aukan kiran, duk sun rasa ma ya’akeyi, Beebata tayi nata basiran ama ina! Har wayan ta yanke, sai can dai Khadi tace”tsaya inaga wannan, ruwan ganyen ne amsa kira, do d’azu jan ya katse ne. Tana jan ruwan ganyen, ta tafara jin magana. Assalamu’alaikum! Wa’alaikumusalamu! Ta amsa, sai tayi shiru, ” Khadeejat ya jikin?. “Da sauki Alhamdulilah!. Hira ya rinka janta dashi, har sai da yaji, kamar bacci na son d’aukanta, ya kyaleta. Kwanan Khadi 7 aka sallameta, tayi fress kamar batayi rashin lafiya ba, suna dawo gida, suka samu Gwaggo bata nan, suka shiga, harda Dr Umar ganin irin yanayi, d’akin da Khadi take kwana, ransa ba dad’i ya kira waya, ba’a fi minti talatin ba, sai ga mota da sabuwar Katifa, irin manyan nan, da filo da bargo, aka gyara d’akin fess, ya musu sallama ya tafi, ko da Malam ya dawo yayi godiya, ana haka sai ga Gwaggo.
.
Yau kam ta cika kamar zatayi hakuka, don ba haka taso ba, taso a fitar da kayan amma Malam ya hana. Rayuwa sai tafiya yakeyi, soyayya tsakanin Khadi da Dr Umar sai abunda ya karu, kulum suna gaisawa da Ilham, harta sata a group d’in novel ta yi kawaye yanzu. Duk inda kake da jama’a, baka rasa yan gulma, acikin mukaraban, Dr Umar ansamu wanda ya sanar da Sakeenat, Dr Umar yana neman wata yarinya, yanzu haka ana kan shirin magana Aure, nan take hankalinta ya tashi, bashi ta biyo jirgi yau ta tazo 9ja. Karfe shidan yamma, jirgin su ya sauka, acikun garin Abuja. Bata bata lokaci ba, ta sake shiga jirgin Kano, ko da ta iso, anyi sallah magriba, ana shirin yin isha’i, taso yau taje taga yar gidan uban waye, Dr Umar ke sonta, kuma da me tafita da shi, da har zai aureta, tabbas yarinyan sai ta raina kanta, washe gari da had’a security dinta, wankan kece raini tayi, ta kira kawarta, Zulaihat tace”Zuly ki shirya kizo, zaki rakani, wani karamin unguwa, wai shi Dakata. Cike da tsokana Zuly tace”kawas mai zaki dakata acan, nan Sakeenat, ta sanar mata da komai, Zuly tace”ban minti kad’an ina zuwa ko ku biyo ku d’auken. Haka akayi, suka dauketa, cike da rashin mutunci a fuskokinsu. Khadi ko wanka tayi, sabi da tasan yau weekend, Ya Umar d’inta zaizo, tayi kyau kamar wata amarya. Suna tsakar gida suna tad’i’ ita da Beebah kasancewan, Gwaggo ta tafi gidan kawarta, shiyasa suka sami freedom yau. Tun daga nesa suke jin, wi wi wi wi, kukan jiniya alamar, wani babab yazo unguwan, har sai da aka zo qofar gidansu, tukun kukan ya tsaya, cikin mamaki suna jira suji maisu shigowa, Khadi tace”Beeba kardai police ne suka zo gidannan?. To wayayi laifi?. Tana wannan tunani ko taga masu bakaken kaya, suna shigowa cikin gidan, nan take hanjin cikinta ya kad’a. Sai da suka shigo, sun tsatsaya musu, wasu yan mata ne biyu, su ka danno kai cikin gidan, kalo d’aya zaka musu ka gane, sun san bariki, idonsu abud’e yake, ga fiskansu ta sha man bleaching. Cikin isa da taunar chewing gum, ta iso gaban su, sai da suka musu kalon, sama da kasa, kafi ta juya, ta kare ma gidan kalo. A tare suka kwashe da dariya, Zuly tace”kai yayan talakawa, a cikin ku waye Khadi ko Khadija, shiru ba wanda ya bada amsa.
.
Cikin zafin rai suka sake magana, da kyar, Khadi tace” gani nice Khadi. Sai da suka kaleta sama da kasa, sai da gaban Sakeenat ya bmfad’i don sai yanzu ta lura da Khadi, tabbas yarinyan ta had’u, dole Dr Umar ya makance a sonta. Daurewa tayi, ta fara yi ma Khadi, “concrete warning, duk randa naji ance kin kula Umar sai na muki rashin mutunci, sai nasa an d’aureki, tabbas duk halin naka-naka ne, mai rashin kunya ma wataran yana da rana. Beebah da Khadi kasa magana sukayi, Rabee’at dake bacci a d’aki, hayanayi ya fitar da ita, jin yanda, aketa zaginsu, dana iyayensu ta karaso da gudu, ta kalisu Sakeenat, ta sama da kasa, ta nuna su da yatsa, tace”banza mai fiskan biri, kin wani sha bleaching, waye ke?. Da har zakina zagin iyayena, nan Rabee’at tashiga sauke musu, kwandon rashin kunya.
.
Dr Umar yayi wankan sa ya nufo, gidan su Khadi, tun da ya shigo unguwan ya fara ganin motoci, har ya iso qofar gidansu Khadi, nan yaga security, gidan gwamnati, da sauri ya fito daga mota, ya kira wani body guard, tambayesa mai ya faru, nan yake basa bayani, Sakeenat ne a ciki, da sauri ya shiga gidan, dai-dai likacin da, Sakeena ta harzuk’o zata mari Rabee’at da sauri Khadi, ta shiga tsakanin su, sai jikayi tasss!!, karan saukan mari a fiskan Khadi, kafin ta motsa, sai nasojin wasu karan tass!! Tasss!! Tass!! Gar sau uku, Dr Umar ya mari Sakeenat. Ya juya ya kali security d’in, da sauri suka bar cikin gidan. Cikin fushi ya kali Sakeenat, Yace” kee waya baki izinin zuwa gidan nan?. Duk randa na k’ara, ganin k’afarki sai kinji ajikinki, ki kuma sani Khadeejat ta miki nisa, itace uwar ‘YA’YA Na, ita nakeso, itace rayuwa, farinciki na, in part rayuwata bazatayi dai-dai ba in ita, banza sakarya, ko ana soyayyan dole ne?. Nace bana sonki bana sonki, ba kuma zan soki ba. Cikin b’acin rai yazo, rik’o hannu Khadi yace”My wife kiyi hak’uri dan Allah, hannu yasa, ya share mata hawayenta. Ya rike hannuta, ya Sakeenat da bakin ciki ya isheta, kaman ta shid’e a gurin. Yace”kee Sakeenat! Kinga wannan ta fi minke komai, itace mahad’an rayuwa ta, tafiki kamun kai, da nutsuwa, in kin…
…
Da gudu ta bar cikin gidan tana kuka, wi-wi da hawaye. Tabbas yau taja ma kanta raini agaban, wayanda take takasu son ranta, yau Umar ya mata haka?. Tana fita mota tashiga, Zuly ma ta biyota, rake suka bar unguwan.
0 comments:
Post a Comment