JUWAIRIYYA Part 1
.
Zuciyarta cike da fushi tana ta sauri kamar ta tashi sama. Duk wannan saurin tsoronta daya kada Tasi ya shiga gida kafin ta cimmasa. Yau sai ta masa dukan tsiya wallahi don ita bata tsoron ta mutu bare tayi rai. Nafisa ce ta taba ta tace Yaya kinga Tasi chan da abokansa. Kafin ta gama magana yayar tata ta ruga da gudu taci kwalar Tasi cikin fushi tace kai don ubanka me ka fadawa malam dazu a islamiyya. Ya make mata hannu tare da cewa gaskiya na fada masa, ba wani abu yasa kuke makara ba face rike sandar tsohonku da kuke aje bara. Abokansa kuwa sai ihu da dariya suna fadin sai 'ya'yan Idi makaho. . Zuciyar mata fa tazo wuya nan ta rufe ido tana kai musu dukan mahaukata. Da Allah Ya bata sa'a ta kama kwalar Tasi sai kokawa ta kachame. Nafisa da Bidaya suna ganin abin ya baci sai gida da gudu. Mama tana kwasar tuwo ta gansu a gigice ta fara fadan yau ma tseren kuka yi ko kamar maza. Bidaya tace Mama Yaya Ju ce suke fada da Tasin Baba Ya'u. Nan take ta saki marar dake hannunta tana kwalawa Ismail kira. Ya fito yace mama naji abinda suka ce muje ki raka ni Bidaya. Akan Tasi ya hango ta tana tula masa kasa a baki yara sun taro ana ta wakar ku casu bamban ku casu. Ismail yayi sauri ya finciko kanwarsa tare da bata kyawawan mari har biyu sannan yaja hannunta gida. . A tsakar gida suka riski iyayenta wanda tun kafin su iso ake jiwo kukanta daga soro don ta maru. Mama cikin fushi itama ta damko ta ta fara duka tana fada. Yanzu Juwairiyya bakya jin dadi sai kin dauko min magana ko. Ta cigaba da cewa shekarunki goma sha hudu fa amma bazaki dena dambe da maza ba. Na fada miki ke macece ba namiji ba yayyanki maza ma wallahi basuyi abinda kike ba. Duk wannan abin da ake Juwairiyya bata ce komai ba kukan ma ta dena ganin yadda babanta yake lalube da hannunsa yana kokarin hana mama dukanta. Yace Mariya kiyi hakuri don Allah ki bar dukanta. Juwairiyya ta kama hannun babanta ta zaunar dashi akan tabarma. Yana zama ya lalubi kunnenta yace wai meyasa bakya jin magana. Ta share hawayen idonta tace Baba zaginmu suke harda cewa bara muke raka ka. Wallahi idan zasu zageka sau dubu zan rama sau dubu ai ba tsoronsu nake ba. Ismail yayi saurin doke mata baki wato ana miki fada ke ko gezau bakiyi ba har kina dada maida martani. Baba yace bari dukanta haka. Ya sake rike mata hannu yace Juwairiyya kinsan dai dani da baban Tasi wa da kani ne ko. Ta kada baki tace ai ba babarku daya ba. Mama ta jefa mata harara tace wai baza kiyi shiru ba. Baba ya cigaba da cewa ki rinka hakuri akan duk abinda zasu fada miki ko yan uwanki.
.
Kinga Ismail da yayanku Najib basa kula su, kuma ma ai duk garin nan babu wanda zaice ya taba ganina da kwanon bara. Nan duk 'ya'yansa dake wurin suka yi murmushi saboda yanayin da ya fadi maganar banda mama da ta ce Alhaji kaine kake sa yaran nan basa daukar maganarka da girma saboda kana musu wasa. Yace to kowa ya kallo ni nan suna kallon shi kuwa ya sha kunu a dole ya bata rai suka sake yin murmushi Ju kuwa har sautin dariyarta ake ji. Yace don Allah ku dena biye musu ko me zasu fada. Lalurar makanta jarabawa ce daga Allah. Da ina da idona rangadau farare kal kamar na Najib da Ismail. Kuyi hakuri yan mata bansan yaya naku suke ba. Amma dai abinda nake so ku gane shine ni bana bakin ciki da niimar da Allah Yayi min da kuma cikin ikon Sa yanzu ma da lalurar tazo bamu kasance cikin kaskanci ba. Zai cigaba da magana yaji kiran sallah sai yace a tashi ayi alwala Allah Yayi muku albarka. Ju ta debo wa babanta ruwa ta zuba masa yayi alwala ismail yayi masa jagora zuwa masallaci
**********************
Bayan kwana biyu da fadan Ju da Tasi tana dawowa daga makarantar boko taci karo dashi a kwanar gidan liman shima ya taso da yan korarsa a baya Lado da Haladu. Suka fara binta da sauri dama yaci alwashin rama abinda tayi masa a rannan duk da rashin mutumcin da babarsa taje tayiwa maman su Ju har gida da wanda babansa yayiwa babanta a kofar gida. Ju dai ko a jikinta data gansu duk da cewar ita kadai ce yau abokiyar tafiyar tata Madina bata je makaranta ba saboda ranar hutu ce garesu yan aji biyar an gama jarabawar kwalifayin zasu dan kwana biyu a gida kafin sakamako ya fito. Tasi da abokansa suka samu suka tare mata hanya yace ke ubanwa kika zubawa kasa a baki shekaranjiya?Tace uhmm wai dani kake? Yace hade girar sama da kasa ya sake maimata tambayarsa. Tace to ubanka na zubawa mai jajayen hakora. Tasi yace yarinya yau kin gama yawo. Ya cakume ta zasu fara kokawa ta aje jakarta a gefe ta Allah Ya gani bani na takali fadan nan ba.tana fadin haka ta kai masa duka a ciki nan fa maxa uku suka far mata suna dukanta amma bakinta yaki mutuwa sai masifa take tana dukansu itama. Liman ne ya fito yaga abinda ke faruwa yayi musu tsawa suka tsere. Ju kuwa yau an mata taron dangi hijabinta ya yage har kasa ga wuyan riga shima ya yage har kusan cibiyarta. Gashi ita yarinya ce mai garin jiki kirginta ya kusa gama cika. sai da liman yace wuce ki tafi gida ta kula da yadda kayanta suka yi budu budu ga yagewa. Yau tasan ta gama yawo a wurin mama.
**********************
Ju ta bayan gidansu ta zaga ta taka wani kututturen itace ta haura katanga. Tana dira bidaya tana watsa shara nan take ta kwala ihu. Mama ce tazo da gudu tana tambayar lafiya.itama turus tayi yadda ba don jininta bace itama bata gane ju ba. Bidaya kuwa runtse ido tayi tana fadin mama aljani. Mama kam ko baa fada ba tasan yau ma yar tata tayi sanaar da ta saba. Batare da cewa komai ba ta koma da baya taje ta tada Najib wanda bai dade da dawowa daga makatanta ba yana level 3 a jamiar garinsu wato wudil wadda aka fi kira da KUST. Tace fito a hankali kada babanku yaji ina jiranka a wurin shanya. Ai nan ya sameta da wayar redio a hannu ta bashi ta nemi wuri ta zauna a kasa tace zanemin 'yar iskar yarinyar nan wadda bata jin magana. Najib dama haka nan ma cin zali ne dashi bare an bashi license. Nan ya fara dukanta ko tambayar baasi babu. Kamar kullum yauma ba ihu sai hawaye da take zubarwa a zuciyarta kuwa tana kara rayawa wallahi duk wanda zai zagar mata uba Allah ne zai raba ta dashi.
.
Ju kenan ta baba idris. Tun da ta fara wayo ta gane babanta makaho ne take tausayinsa. Wani lokacin sai ta sami loko tayi ta kuka saboda tausayinsa. Akan baba Ju ta fara qiyamul layl tunda wata rana malamin su yace duk mai yinta komai ya roka Allah zai amsa. Mama da kanta ta fuskanci hankalin Ju kamar baya tare da ita tace wa Najib ya kyale ta. Suna juyawa suka ga baba a tsaye rike da hannun bidaya. Yace idan kun gama dukan ku bani 'yata. Ju wadda kanta yake a durkushe tana jin muryar Baba sai kuka mai tsuma zuciya taje ta kankame shi tace wallahi baba na tsane su kuma bazan yafewa duk wanda ya zage ka ba. Wannan abu yasa Mama kuka itama. Suka koma dakin Baba gaba dayansu sai yace a fita a barshi da mama da ju.
.
Kowa na fita yace Juwairiyya kina so inyi fushi dake ne. Tayin saurin cewa a'a. Yace to daga yau idan kika sake fada a waje a kaina bani ba...bata bari ya karasa ba tace WALLAHI WALLAHI WALLAHI bazan kara ba.Sai yace tashi kije Allah Yayi miki albarka. Tana fita yace mariya yarinyar nan ta gado fushinki. Ita kanta mama yadda Baba ke magana ya bata tausayi domin tunda ya kamu da lalurar nan baya ko daga murya yace yana gudun kada ladan hakurinsa ya ragu. Mama tace Alhaji yau fa duk kayan jikinta a yage suke gashi kamar an mata wanka da kasa. Yarinyar nan mace ce amma abinda take ko namiji ne dole ayi masa fada.Baba yace mu cigaba da yi mata adduar shiriya da kuma sassautawar zuciya.
********************
Hajiya Asiya ta dubi yar uwarta tace ni tun ranar da kika min waya akan fadan da Juwairiyya tayi hankali na bai kwanta ba don babansu Amal baya nan ne da washegari zaki ganni a garin nan. Idan kin yarda mariya ki barni na tafi da ita kano tunda ta gama jarabawa kafin result ya fito. Mama tace anya yaya ayi haka da dai kin bari sai nan da sati ukun muzo bikin Amal tare. Yarinyar nan kawa zucin gida gareta gashi duk safiya da dare sai tazo taga babanta. Haj Asiya tace wai kin manta yadda kike likewa baba ne da kamar kaska ta fada taba dariya. Kuma yarinyar nan ina ga kawai tausayin babanta take yi. Ga karayar arziki ga makanta lokaci guda dole a tausaya masa. Ki bari mu tafi muyi shirye shiryen bikin yayarta Amal da ita tunda su nafisa basu yi hutu ba ga Alhaji bazaki iya zuwa da wuri ba. Baba ma ya amince bayan da mama tayi masa bayanin shawarar da yayarta ta kawo. Ju kuwa an gama hada kaya da murnar zuwa wurin yaya amal sai dai kafin ta isha ta lallaba ta fita taje gidan wan mahaifinta wanda shine silar karayar arzikinsa da makantarsa ta sami Baaba mai koko tana tatar gasara ta tsaya ta kama kugu tana murguda baki tace mai koko zan tafi kano gobe nasan duk kowa yana ciki suna sanaar kallo to ki fada musu duk wanda ya zagar min uba ko yan gidanmu Allah Ya isa. Tana fadin haka ta ruga ta koma gida. Mai koko ta bata sami mayar da magana ba ta rike baki tace bari malam ya dawo idan bamuyi da gaske ba yarinyar nan zata tona mana asiri wata rana.
.
Sai mun sake haduwa da jin rayuwar Juwairiyya (Ju) a kano da asirin da su Mai koko suke tsoron ta bayyana.
.
KUNA TARE DA NI MU CI GABA?
0 comments:
Post a Comment