AGOLA Page 16-20
.
Tundaga ranar Jidda takoma ruwa, fiye da baya, sosai Al,amin yake kashe mata kudi, dan shide Allah yajarabeshi da son Jidda, itama haka tana masifar sonshi, dan danan Zarah takara jawo Jidda jikinta ganin yanzu tana samun kudi fiye da da. Haka tafara zirya zuwa Zariya, itama kanta Asabe tayi murnar dawowarta, dan tasan zata cigaba da cin dadi, dan ita tasan abinda Jidda take aikatawa, kuma bata damuwa, dan itama tsohuwar yar duniya ce. Jidda har kasar waje tafara fita ita da Al,amin sbd yanzu arzikinshi yakara habaka, har waje yake zuwa saro kaya, kuma duk sanda zeje tare suke zuwa da Jidda, dan Jidda akwai gayu da gyara, bata wasa da kayan mata.
Zarah ce zaune adakin Asabe, tagama fadamata abinda takeso bokayayi mata. Asabe tace ai dama kyaleki nayi mutuwar tadanyi nisa, sannan inzo maki da irin maganar nan, segashi kinrigani, bara inkira Dije muje, amma ai baje yuwa ba ace AGOLA tafi masu gida. Kuma wlh wannan yaron damuke rainawa, idan har bakiyi da gaske be, wata rana zesaki kuka daga shi har AGOLAR.
.
Bayan Dije tazo ne suka fada mata abinda suka shirya, murmushi Dije tayi tace meyasa kukeson yin abu bakwa tunawa da mutanen gari, kunsan fa yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba, akwai matsala 2 dazaku fuskanta idan har kuka aikata abinda kukace. Tafarko de idan kuka sa aka kori Falak da Ameer daga gidanki, mutane babu wanda zasu zarga seke, har Mijinki keze zarga.
Matsala ta 2 kuma idan har kuka kashe Falak da Ameer, wlh ina me tabbatar maki da kotu seta daureki, dan nasan mijinki baze taba yarda dakeba, dole yasa yan sanda su bincikeki,
Asabe tace wlh shiyasa nakesonki kawata, yanzu me kike ganin za,ayi? Gyara zama Dije tayi tace zanbada shawara 1 amma fa idan tayi maku, Zarah tace wlh kifada zatayi,
Nafarko de za,a kashe Ameer, amma ta hanya mafi sauki wanda babu wanda zeyi zargin kasheshi akayi.
Na biyu kuma, dole zaki mallake Alh, za,a kawar da kanshi daga Falak, tayanda zemanta da ita acikin gidan kome zakiyi mata baze ce komai ba, sauran yan gida kuma ke keda iko akansu, bakamar wannan tsohuwar munafukar, wadda kika yarda da ita sosai.
Se kuma Jalila, ita kuwa diyarki ce kinsan yanda zaki tafiyar da ita. Falak kuwa kada kiyi mata komai, hakan zesa kifita daga zargin mutane, Ameer dama kowa yasan beda lafiya. Amma Falak kimaida ta ita da almajira basuda bam banci, duk wannan dadi datakeji kihanata, Mairo takoma girki kawai, sauran aikin gidan sukoma kanta. Wannan kyawun nata kimaidashi muni, kuma kirabata kwana daki daya da Jalila,
Kimaida ta store tarika kwana ita da kwari sucinye wannan shegen jikin nata, duk wani kayan more rayuwa ki anshe su, kayanta ma zanbaki wasu tsofaffin kayana ki kaimata, tarika sawa, ko aike kasuwa yatashi daga kan driver yakoma kanta.
Kuma kicema Mairo tamaida rikon Ameer hannun Falak bazaki iya cin abincinta ba, tana renon yaro me zubda miyau. Daga karshe kuma kisamu dan kwaya ki aura mata shi, idan bahaka ba kina gani masu kudi zasu aureta, dan kinsan tafi yayanki kyau.
Shiru Zarah tayi, Asabe tace yanaji kinyi shiru, tobari infada maki, wlh ba,a samun duniya da tausayi, idan baki sani ba, nidin nan seda nakashe mutane 2 saboda kudi, kuma duk mazaje nane, nakuma gudu da dukiyarsu, Babanki ma........ Saurin hadiye maganar tayi tuna dawa take magana tayi. Babanki ma saboda irin Son danake mashi ne, yasani zuwa naroki ya aureni, kinsan tunda nake bantaba son wata halitta kamar Babanki ba. Shiyasa gashi nan muna zaune lafiya abummu. Murmushi Dije tayi jin irin saurin kwaskwarimar da Asabe tayi.
Dije tace idan har kika iya aikata abunda nace maki, kawai kihangoki cikin jerin manyan mata masu fada aji akaduna, yanzu ina kawarki Karima, bakince tunda mijinta yamutu ba, tabar garin tana can Abuja gidan kudi, batada aiki sefita kasashe, ina da bakinki kikecewa yanzu ko wayarki bata dauka saboda tayi kudi, wani lokacinma sese me aiki tadauka tace tana bacci.
Haba Hajiya kalleki fa, yanda kike da kyan nan rashin samun kudi masu yawa ne da hutu yarage maki kyawunki, yanzo dan kasuwancin dakikeyi ma kudin duk sushige gurin boka, yanzu haka kila bakida wanda zamuje gurinshi yanzu, dan kinsan aikinshi kamar yankan wuka ne shiyasa yakeda amsar kudi masu tsoka.
Zarah tace wlh, ashirye nake da inyi abinda yafi hakama matukar zansamu kudi, kuma arayuwata babu wadda na tsana kamar Falak, zanyi duk yanda zanyi in kunta tama rayuwarta, bazata taba fin yayana ba, ita Kuma Jalila nasan yanda zanyi da ita, kunsan babu abinda ta tsana kamar fushi na, ko kuma ince zan tsine mata, bakaramun shiga tashin hankali take ba, idan taji furucina ba.
Saboda tana zuwa islamiyya, kuma suna aiki da abinda ake koyamasu sosai, Mairo kuwa kubarni da ita, akarkashin ikona take, kome zanyi bazata iya fadama kowa ba, Alh, ne kawai zata iya fadamawa kuma shima zan mallakeshi. Dariya sukayi gaba daya. Suka tashi zuwa gurin boka.
Wata irin dariya boka yayi yace lallai Hajiya kinzo da babban aiki, kuma aikinki zeci kudi sosai, dan wannan karon zakisani karya maganata dan banayin aiki 2 alokaci 1, amma idan har zaki saki kudi bakida matsala.
Zarah tace boka kamar nawa ne kudinka? Aikin Alh, mesauki ne, zaki bada 150, shikuma Ameer nashi 200 ne, sekizabi 1 idan bakida kudi.
Zarah tace atemaka mun boka yanzu babu kudi sosai, amma ga na Alh, afara yimani aikinshi, se abani na Ameer dana koma bayan kwan 2 nayi maka alkawarin zanturoma Inna Asabe, kudin aikin Ameer takawo maka.
Dije tace boka atemaka mata, kasan yanzu munzama daya. Magani 2 yadauko yabata 1 yace wannan zaki saka ma Alh, acikin abinci, dazaran yaci kingama dashi, wannan kuma wuta zaki samu ko garwashi kifita waje kizuba kamar yanda hayakin nan zetashi sama baze kara dawowa ba, haka tunanin Falak zefita daga zuciyar mijinki, ko yaganta baze tuna amfaninta agurinshi ba.
.
Wani dan butum butumi yadauko yakama wuyanshi yasa zare yashake wuyan, yace wannan kuma Ameer, tundaga yau babu abinda zekara shiga cikinshi, kome yaci iyakarshi makoshi zedawo, nabaki nan da wani lokaci zemutu. Kuma daya mutu Alh, zemanta dashi, zakici duniyarki da tsinke, sauran kuma sekinje gurin me hukunci. Dariya yasa yace kutashi kutafi, Dije kije sebayan anbaku kudin kwa dawo, Zarah de bata fahimci abinda yake nufi ba.
Baba Mairo itadasu Falak suna zaune adakinta suna fira, ita kuma tana bama Ameer abinci abaki, Jalila tace wai gashi har yamma tayi amma Ummi bata dawoba, bansan meyasa yazu Ummi yawan zuwa Zariya ba, wanda ada batason zuwa.
Baba mairo tace keko tunda tana da mahaifi araye ai dole tarika zuwa. Aranta kuwa tana fadin Allah yasa bawani mugun abun bane yakaita...... bata karasa ba, Ameer yashiga amayar da abunda yakeci, cikin sauri ta dagashi tana sannu ka kware ko,
Ruwa Falak tamika mata tana fadin aishine yacika cin tsiya, ke kuma Baba mairo kita bashi abinci, karbar ruwan tayi tana fadin tunda beda baki aidole inrika bashi abinci akai akai, kodan ke abincin beda meki ba ne, Jalila tace kyaleta Baba mairo sotake shima yazama kamarta yar siririya,,,,,,,, ruwan Baba mairo tabashi, yana amsa yasake amayoshi.
Tadashi zaune tayi takara bashi, abun tunbe basu tsoro har yafara basu, jikinshi Bab mairo ta taba taji babu zafi, tace tomeke damunka Ameer haka? Jalila tace Baba kawai akira driver yakaimu asibiti tunda dady nenan nasan gobe zedawo.
Shiryawa sukayi suka kulle gidan suka ba megadi key din suka tafi, kafin su kai duk yajike Baba mairo da miyau, dan har miyan baya iya hadiyewa. Sunazuwa suka wuce gurin Dr, bayani Jalila tayi mashi, ruwa yadauko yabashi amma yamaidoshi.
Abu kamar wasa jikin yaro yafara rikicewa, tun likita yana daukar abun wasa, shima yafara shiga damuwa, daki yabasu aka kwantar dashi aka samashi karin ruwa da allurai, sannan yayi bacci.
Baba mairo babu wadda take zargi se Zarah, dan tariga data lura duk lokacin da taje Zariya sewani abu marar kyau yafaru akansu Hajjo, yanzu gashinan ta kauda Hajjo takoma kan danta, duk da tasan cewar itace tayi sanadiyyar maidashi dolo, yanzumma bata debe tammanin tanada sa hannu acikin wannan ciwon nashi ba.
Jalila takira dadynsu awaya tafada mashi, yace gashi nan yanzu zetaho, haka sukacigaba dazama, Falak se kuka takeyi, Jalila tana lallashinta, duk itama hawayen takeyi.
.
Koda Zarah tadawo, megadi yabata key, yace mata sunje asibiti kai Ameer, murmushi tayi aranta tace boka aikin ka nakyau, saurin shiga cikin gida tayi, kayanta kawai ta aje tadauko gawayi tadorashi akan electric burner seda yayi ja, sannan takashe, dauka tayi tanufi gurin part din Hajjo daga baya ta ajeshi, maganin tadauko tazuba aciki, nan take hayaki ua turnuke, sama yayi tayi har yacinye, kakkabe hannunta tayi tana fadin su AGOLA anzama baiwa. Saura kai Alh, Allah yamaidoka gobe.
Ciki tashiga tayi wanka tana saka kaya taji horn din. Alh, murmushi tayi tace wato kai game da anayi maka waya harkataho, nasan Jalilan banzan nan ce zata fada maka, kema zaki dawo kisameni ne,
Da sallama yashigo yace ah, Hajiya bada ke aka tafi asibitin ba? Yatsina fuska tayi tace nim yanzu nadawo daga Zariya, megadi yake fadamun, wanka nayi nake shirin tafiya, ok fito mutafi gaba daya. Falak ce takiraka ko? Shiru yayi yana kallonta, jin ankira sunan Falak seda kanshi yasara.
Murmushi tayi tace yanaji kayi shiru, Fala...... tsawar daya daka mata ce tasa ta yin shiru, meye haka wacece kuma wata Falak, kada inkara jin wannan sunan agidan nan, kema kika santa, Jalila takirani amma kirika fadamun wani suna, banaso, kiwuce mutafi.
Suna zuwa office din likita yawuce, bayan sungaisa Dr, yace agaskiya Alh, nakasa gano wace irin cutace ajikin Ameer, duk wani gwaji munyi mashi amma bamu sami wata cuta dazata nuna mana asalin ciwon shiba.
.
Abinda nake ganin zefi kumaidashi gida acigaba dayi mashi na hausa, dan gaskiya ina ganin ciwonshi kamar akwai aljanu aciki. Alh, yace hakane, nikaina nafara tunanin haka, tun sadda yafara zubar da miyan bakinshi, da kuma kanshi da baya zama, haryanzu fa Ameer baya iya zama. Bakomai nagode bara naje mutafi, dr, yace nacire mashi karin ruwan ma dan naga jikinshi baya bukatar ruwa, sede matsalar rashin cin abincin shi, idan har kuka koma gida yacigaba da mayar da duk abinda yaci, zan iya zuwa gidan, ko insa azo arika samashi karin ruwa. Godiya sosai, yayi mashi yatashi suka fita.
Tunda yashiga dakin Jalila da Falak sukayi mashi sannu dazuwa, ya amsa yace Jalila yagidan, tace lfiya lau dady, ko kallon inda Falak take beyiba. Baba mairo tagaisheshi ya amsa yana tambayarta Ameer da jiki.
Zarah farin ciki ne aranta, fal, ganin yanda yayi ma Falak, sukuwa basu kawo komai aransu ba, ganin halin da ake ciki, Alh, yace sutashi sutafi gida, ansallamesu, anan yayi masu bayanin da Dr, yayi mashi. Baba mairo tace idan ko haka ne, Alh, se akaishi gurin Malami. Zarah tace koma de menene kuwuce muje, gida. Kallon mamaki Baba mairo tabita dashi, haka suka wuce da driver ita kuma tabi Alh, aranta tana fadin dole yau kaci maganin nan ko aikina zefara dawuri.
.
Suna zuwa gida Baba mairo ta kwantar da Ameer, su Falak kuma suka wuce daki domin yinsallar magrib. Wucewa kitchen Baba mairo tayi domin dumama masu abinci tayi, shikuma Alh, tadora mashi abinci mesauki, daki takoma tayi sallah.
Bayan tafito ta koma kitchen tana hadama Zarah abincin Alh, Zarah ce tashigo kitchen, din, tace yau mairo jeki dakina kidauko mun wayata bisa gado, tana fita tayi saurin bude cooler din Alh, taciro magani tazuba, kokarin maidawa tayi azaninta, juyawar dazatayi taci karo da mairo tana kallonta mamaki dauke afuskarta.
.
Cike da duniyanci Zarah tace shigo mana Mairo naga kintsaya kina kallona, Mairo tace dan Allah Hajiya wane irin magani ne kika sama Alh, kinga duk abinda yasame shi ni za,a zarga tunda ni nayi girkin.
Murmushi Zarah tayi, tace bazan fada maki ko maganin menene ba, idan yaci kome yasameshi aka kamaki, zakiyi bayani, ido waje Mairo tace kirufa mun asiri dan Allah hajiya.
Zarah tace naji. Amma da sharadi, banaso kowa yaji wannan maganar, kuma daga yau duk abinda zance maki banason gardama kinsan de ni nakawoki gidan nan ko? Saboda haka kina karkashin ikona, banason shishshigi, ki tsaya amatsayinki na me aiki, daga yau banaso ki kara fitowa daga dakinki matukar Alh, na gidan nan.
Kuma daga yau, zaki maida Ameer hannun Falak, dan baze yuwa kina girki kuma kina renon kazamin yaro ba, aiki yanzu ze koma girki kawai, naruwanki da wanke wanke nasamu wadda zata rikayi mani harma da wankin kayana.
Inafatan kingane menake nufi, idan kinbi umarnina kicigaba dazama agidan nan, idan kuma kinki, zaki tafi kuma kibar amanar da Hajjo tabaki, dan nasan kafin tamutu tamika amanar yaranta agurinki.
.
Zabi yarage naki, kuma wlh idan kika kuskura kika rika shiga harkar Falak sekin barmun gidana. Zaki iya tafiya. Fita Baba mairo tayi tana kwalla, wannan wane irin sabon yanayine yashigo gidan nan, anya Hajiya bata fara shaye shaye ba? Ya Allah katsare bayinka kuma marayunka, tabbas Falak nasan rayuwarku zata shiga, kunci, sede bazan bari inyi abinda za,a koreni daga gidan nan ba, nasan idan natafi zakifi shiga damuwa sosai, kuma nasan wasiyar ummanki bazata bari kibar gidan nan ba, dasemu tafi tare.
Abincin tadauka takaima Alh, yana shirin zuwa yaga Ameer tashiga, tace ina kuma zakaje Alh,? Yace Ameer. Zan dubo, tace daga can nake yasamu bacci, kuma yaci abinci, kabarshi yayi bacci tunda yasamu yayi. To Alhamdulillah, Allah yakara bashi lfiya, wlh har hankalina ya kwanta, banason ciwon yaron nan.
Abinci tazuba mashi tana ta janshi ta wasa, sewani shige mashi takeyi, shi kuma duk ya rude, abaki tadebo zata bashi, ganin yana niyar yin bismilla, yasata fadawa jikinshi, dariya yasaka yana shirin yin magana tayi saurin saka mashi abincin abaki.
Taunawa yakeyi yana fadin Hajiya yaude naga alamar amarci kikeso musha, ko? Kara debowa tayi tasaka mashi yakarba, tana ta yimashi kwarkwasa, shikuma duk ya rude. Ahaka haryagama ci beyi bisimilla ba.
.
Yana gama ci yasha ruwa, ana take yai kanshi yayi mashi nauyi, rike kanshi yayi, kamoshi tayi ta dorashi bisa cinyarta tana shafa bayanshi, da haka haryaji kan ya lafa. Shiru yayi nawani dan lokaci, sannan yatashi yace zanyi wanka idan nafito se inje inga jikin Ameer. Bata fuska tayi tace nace bazaka jeba, kabari se gobe. Nan take yace to hajiya, inje inyi wankan ko?
Wani murmushi Zarah tayi, aranta tana fadin wlh dagaske maganina yaci, kai amma dole incika ma boka alkawarinshi. Kara daure fuska tayi tace zauna inason magana da kai, zama yayi yace inajinki. Kudi nakeso zansaro kaya. To to kamar nawa kike bukata? Dubu dari 5 nakeso.
Yace toshikenan yanzu na hannuna basu kaiba, tace ina check dinka? Yace yana nan, to kadauko karubutamun gobe se inje incira. Tashi yayi jiki na rawa yadauko ya rubuta mata, yamika mata, tace haba Alh, atsaye zaka bani kamar wata yarka, yace yi hakuri Hajiya, dukawa yayi yabata. Tace tashi kaje kayi wanka idan kafito kuma bance kafita ko ina ba, sallar isha,in ma kayita agida, idan kagama katsaya afalonka kayi kallo, idan kanajin bacci kayi kwanciyarka. Yace to Hajiya sekin shigo.
Fita tayi tana me cike da fari ciki tana shiga dakinta tace wlh, Alh, sekayi dana sanin yimani kishiya, sena maidaka abun tausayi arayuwa, daga yau bakai ba Ameer da shegiyar AGOLAR KA.
Juyawar dazatayi taci karo da Jalila tana gyara mata gadonta. Cike da firgici, tace Uban waya kawoki dakina? Jalila da tunda taji kalaman Umminta jikinta yafara rawa, kafin tayi magana hawaye sun wanke mata fuskarta.
.
Jawota tayi ta kwada mata mari tace ina magana shine zakimun shiru, wato labe kikemun ko, Jalila tace dan Allah Ummi kiyi hakuri, nibanji abinda kika ceba, kawai nashigo inamaki gyaran dakine.
Zarah tace idan ma kinji, bakiji karya ba, kuma zauna kibude kunnuwanki da kyau kije abinda zan fada maki, nasan sarai kinji maganar danayi, to haka yake bakiji karya ba, tunda Babanku ya auro uwar su Falak naji natsanesu, gashi nj bantaba haihuwar naminj ba, amma tana zuwa tahaifa.
Saboda haka idan harkina kishina, kuma kindaukeni amatsayin uwa, wadda ta tayi renonki tunkina jini harkika koma tsoka, akasa maki kashi, kika girma acikina, ki hanani bacci, kocin abinci, kika hanani sukuni, sannan nasha wahalar haihuwarki, seda nadauki tsawon awa 1 ina nakudarki kafin kika buda jikina kika fito.
Nashayar dake daga jinin jikin, suk dare duk rana kina tare dani, bana bacci sekinyi, kimun fitsari da kashi in wanke, har kika girma ina dawainiya dake harzuwa yanzu.
Shin akwai wani umarni dazan baki ki kasa binsa? Kai tashiga girgizawa tana kuka, jin yanda Umminta tasha wahala akanta. Murmushi Zarah tayi ganin yanda jikin Jalila yayi sanyi.
.
Tace Jalila amatsayina na mahaifiyarki, inaso duk abinda zakiga ya canza agidan nan kada kiyi magana ko kuma kiyi tambaya akanshi.
Daga yanzu tarayyarki da Falak tazo karshe abanason ina ganinku tare, bazata kara zuwa isilamiyya ba, kuma ayau zata bar dakinki, zata koma store itada kaninta dan renonshi yakoma hannunta, kuma daga yau itace sabuwar me yimun wanke wanke da wanki, harma dazuwa kasuwa.
Idan harkika kara yima Dadynku maganar Ameer ko Falak, sena tsine maki, dasauri Jalila tadago kanta tana kuka, tace Ummi dan Allah kada kitsine mun, wlh wuta zanshiga, nayarda zanbi duk abinda kikace, amma kijanye maganar tsinuwa.
.
Murmushi Zarah tayi, tace bazan janyeba harsenaga kinbi umarnina, ko Alh, yamaki maganar makaranta, nasan naze saka da Falak ba, danshima yamanta da ita, bance kimashi maganarta ba. Kinji abida nafada maki ko? Tace E Ummi, kiyi hakuri dan Allah, tace shikenan nayi tashi ki kiramun Falak.
Fita tayi tana wani irin kuka, tana zuwa takalli Falak gaba daya tausayinta yakamata. Falak tace Jalila lafiyarki kike kuka? Tace bakomai kije Ummi nakira, fita tayi tana murmushi tace yanzu haka laifi kikayi mata ko, bara inje inji mekikai mata, idan har bata mata rai kikayi kisani nima baruwana dake. Wani sabon kuka ne yazoma Jalila, tanajin tausayin Falak sosai.
Tana zuwa tayi sallama tace Ummi hala Jalilace tayi...... Saukar marin datajine yahanata karasa maganar datakeyi, zaki tsugunna ko kuwa sena takaki agurin nan, munafuka me kama da Uwarta. Mamaki ne yakama Falak jin yanda Ummi take zagin Ummanta, zama tayi akasa, taan fitar da kwalla.
.
Zarah, tace kibude kunnuwanki da kyau kiji abinda zan fada maki, daga yau rayuwar gidan nan, tacanza. Babu ke babu sauran jin dadi, dake da shegen kaninki, inaso kije kicire kayan jikinki daga yau kin koma yar aiki agidan ana, zaki rika wanke wanke, da wankina.
Kuma daga yau zaki koma store da kwana, koda wasa naga kafarki ta taka falon Alh, ranki seya. Baci, ga kaya nan kidauma ki kai store domin shine dakinki, tashi kibani guri.
Fitowa tayi tana kuka, tanufi dakinsun haka tazauna taci kukanta dan Jalila tana dakin Baba mairo, haka falak ta cire kayan jikinta tana tunanin wasiyar da ummanta tayi . Mata, akan kada tabar gidan harse aurenta. Wani irin kuka tashigayi.
.
Kayan jikinta tacire tadauki wanda Zarah tabata tasaka, kayan sunyi mata yawa, gashi duk sun kode, kuka kawa Falak takeyi, haka Tanufi store ta gyara shi sannan ta aje kayanta. Agurin domin yayi mata kadan.
Jidda ce kwance abisa kirjin. Al,amin yana wasa da gashinta. Al,amin yace baby na akwai wani friend dina bature ne ahi dazu muna chrt, yaga pic dinki akan fp na, yace mun gaskiya yana sonki, kuma zeso kije mashi hutu, a london yake dazama, me kudine na karshe, idan kikayi harka dashi zakizamo Babbr Hajiya.
Ammafa kisani bawai dan banasonki nace zakije ba, kawai abokina ne sosai, kuma yamun mutunci lokacin muna school, koyanzu ma yana temaka mun sosai, idan banida kudi, shine yake bani, nayi mashi alkawrin wata rana zan kawoki wajenshi kiyi mashi koda wata 1 ne.
Ammafa bayanzu ba, bamma saka rana ba, amma kowane lokaci zaki iya tafiya, yakika ce. Murmushi tayi tace da gske zan samo kudi? Yace sosai ma, kinga dakin dawo semuyi aurenmu ko? Tace hakane, insha Allah zamuyi aure dana dawo. Dariya yayi yajawota yarungume.
.
Tun daga wannan rana Falak takoma me aikin Zarah, Alh yamanta da Falak, ko Ameer yadena tambayarshi, tunda Zarah tace mashi ya warke, kuma tana kula dashi, gashi yanzu baya zama sosai,
Kudi sosai Zarah take samu agurinshi, yazama matar dazama mijin, Baba mairo da Jalila kuwa sunzama yan kallo, sosai suke tausayin Falak, aboye Baba mairo take temaka mata,ga aiki ga renon Ameer, kusan kullum seyayi suma tafi 3 saboda baya iya cin komai.
Damma Falak tana yimashi addu,a shiyasa yake dan samun sauki, Baba mairo tace mata idan zata bashi abinci tarika yin addu,a, dahaka yake samu yana cin loma 3 ko 4.
Falak duk ta rame tayi duhu, gashi bata samun bacci sosai, dan store din wasu kwari ne, suke cizonsu, kullum cikin dare Ameer kuka yakeyi, se idan ta goyashi ne kadai yake bacci, ita tahakura da bacci, wani lokacin a kitchen take samu tayi bacci, idan Zarah bata leko ba.
Jalila kanta tayi rama, saboda bakaramar damuwa tashiga ba, datayi nufin temakon Falak seta tuna kalaman Umminta, gashi tana tsoron fushin Umminta, saboda a islamiyya anfada masu muhimmancin Uwa.
.
Akwai ranar da Alh, yadawo cikin dare yarika jin kuka kamar na yaro, tashi yayi yace Zarah kamar kukan Ameer nakeji, tashi tayi tace wane Ameer kuma, bacin ya dade dayin bacci, kila de makwafta ne,
Alh, yace yaushe harzamu iyajin hayaniyar makwafta agidan nan, muda mukeda da nisa dasu, Zarah tace to karya nakeyi, kasan ai nasaba yinta. Alh, yace Allah yabaki hakuri bahaka nake nufi ba, tace zauna bara inje inlekosu.
Fita tayi tana surutai, store tanufa, Falak tagani se kuka takeyi Ameer kuma yana hannun Baba mairo yanata suma, Zarah tace wai meye haka, dan iskanci zaku fito ku hanamu bacci, Baba mairo tace Haba Hajiya kalla fa kiga yanda yaron nan yake suma, ki kira Alh, mukaishi asibiti, tundazufa beci koma ba.
Zarah tace wlh babu inda za,a kaishi, daukarshi kushiga dakinki kiyi mashi wanka ze farfado, kuma ki kulle dakin banason karajin kukanshi, wlh idan kuka bari Alh, yafito sekinbar gidan nan gobe, wucewa tayi tana zage zage.
.
Dakin Baba mairo suka wuce, ruwan sanyi Falak tadauko suka samashi da kyar yafarfado, kuka yasaka, haka sukayita lallashinshi Falak tana mashi addu,a se can suka samu yayi bacci. Kwantar dashi Baba mairo tayi,
Kuka Falak tasa tace shikenan Baba mairo shima kila tafiya zeyi yabarni, nashiga 3 ni kuma rayuwata haka zata kare, wlh gara mutuwa ta da rayuwata, rufe mata baki Baba mairo tayi itama tana kuka.
Tace Falak kiyi hakuri, duk tsanani yana tare dasauki, kuma duk wanda yayi hakuri yana tare da nasara, ninasan wata rana komai zewuce, Falak tace Baba mairo kina ganin yanzu ko Dady baya nemammu.
Ina alkwarin daya dauka akan rikemu da amana, gaskiya Dady yazama butulu. Baba mairo tace Falak, akwai abinda nasani wanda baki sani ba, banyi niyar fada maki ba, amma dole infada maki kodan ingoge bakin panting da Zarah tayima Alh, agurinki.
Anan Baba mairo takwashe komai tafada ma Falak, kuka sosai, Falak takeyi, Baba mairo tace ko tan tama banayi wannan maganin da Zarah tasama Alh, maganin mallaka ne, domin rannan inajinsu tana yimashi tsawa, shi kuma duk yarude, yana bata hakuri, bakiga yanzu kamar itace mijin shine matar ba?
.
Kiyimashi uzuri, wata rana asiri zetonu, Jalila ma tana cikin damuwar halin dakike ciki, babu yanda zatayine, dan Zarah tace idan har tarika shiga harkarki zata tsine maki, shiyasa tace makarantar kwana zata tafi bazata iya cigaba dazma tana ganinki cikin damuwa ba.
Falak tace yanzu Baba mairo haka zamu zauna da Ameer babu magani, tace kiyi hakuri gobe idan zakije kasuwa zanbaki kudi kitsiyo mashi magani, haka Baba mairo tayita lallashin Falak, harta hakura, kuma tayi alkwarin saka Alh, cikin addu,a. Dahaka suka kwanta, rabon datayi bacci medadi kamar na yau harta manta.
Washe gari bayan tagama aikinta, taci abinci tayi wanka, tasaka kodaddar atamfarta, ta amshi kudi agurin Baba mairo dan zataje kasuwa, dakin Zarah tashiga da sallama tace mata tashirya, kallonta tayi tace dauka ga kudin nan, kidauka, saura kije kidade,
.
Fita tayi taje yima Baba mairo sallama, tace Baba mairo natafi, kudi Baba mairo takara bata tace amsa, Falak tace nameye Baba? Tace idan kinje kisiyo turare naga naki yakare, kwallan idonta tagoge, tace nagode Baba mairo, tace haba Falak ai bakomai, yisauri kije kidawo ki amshi Ameer inshiga kitchen kafin Zarah tafito. Kallon Ameer tayi yana bacci, duk yarame,fita tayi tana goge idonta.
Abakin gate taci karo da Alh, yana kokarin shiga mota, binta da kallo yayi, Zarah wadda take gefenshi tace lafiya de naga kana kallonta? Yace naga bansanta agidan nan ba ne shiyasa, murmushi tayi tace oh, sabuwar me aikina ce, mota yashiga yace yatafi.
Bayan Falak tagama siyen abinda zata siya, taje chemist tasiyoma Ameer maganinshi, sannan taje gurin siyen turarenta. Bayan tasiya, tajuya kenan taji kamar ana kiranta. Haka tawuce batare data juya ba.
Malama Falak, yau kuma babu magana inata magana, juyawa tayi domin taji muryar malam. Sameer, ido suka hada dashi, yana cikin wani yadi mekyau yakara haske, duk se kunya takamata ganin kayan dake jikinta,gashi duk tayi baki.
.
Bayan sungaisa yace Falak yagida, nima jiya nadawo, shine yau nafito shago, ashe dama kina shigowa kasuwa, ke kadai, yau ina Jalila ne? Shiru tayi kanta yana kasa tana wasa da ledar hannunta, idonta har yafara kawo kwalla.
Yace Falak lafiyarki kuwanaga kamar kina cikin damuwa, gashi naga duk kin rame, inafatan de lafiya? Hadiye kwallanta tayi, tace malam, rana tanayi kada ajirani agida, zanwuce. Murmushi yayi yace shikenan, tunda bazaki fadamun ba, kodan nan kasuwa ce, amma anjima zamu hadu a islamiyya ko? Shiru tayi, yace Falak bani no wayarki mana, tace aikam banda waya, yace tobani ta Jalila, tace barade Inbaka ta Baba mairo, kallonta kawai yakeyi hartagama saka mashi, tamika mashi, amsa yayi yace sena kiraki ko.
Godiya yayi mata ta tafi, kallonta yacigaba dayi, jikinshi yana bashi kamar tana cikin damuwa, ammade bari anjima zan tsareta seta fadamun koma meke damunta, ko intambayi Jalila, haka yajuya yana me farin cikin ganin abin sonshi, dan tunda suka gama makaranta yake dokin dawowa yaganta, kuma wannan karin yayi alkwarin fada mata abinda ke cikin ranshi.
Tun daga nesa tafara ganin mutane akofar gidansu, haka takarasa, gabanta yana faduwa, da kyar tasamu tashige cikin gidan, Jalila tagani tana kuka, saurin matsawa tayi tana tambayarta meyafaru, hannunta Jalila taja suka shiga cikin gida, dakin Baba mairo suka shiga.
Yarda ledar datake hannunta tayi, tasaka wani irin kuka ganin Ameer shimfide akasa bisa tabarma, duk ya mimmike, kuma anrufeshi da zani. Baba mairo shikenan shima ya mutu ko? Kamata Jalila tayi suka zauna, tana bata hakuri.
.
Baba maito tace kidena magana Falak kada kiyi sabo, kinsan Allah yafimu sonshi tunda har ya amshi abunshi, addu,a yakamata kiyi mashi, kuka kawai Falak keyi, dahaka wadda zatayi mashi wanka yashigo, komawa gefe Falak tayi tana kallon yanda akeyima Ameer wanka ko motsi. Bayayi.
Bayan angama Alh, yashigo shima yana kuka, hankalinshi duk yatashi da kyar yadauki Ameer yafita dashi akayi mashi sallah sannan suka kaishi makwancinshi. Zarah kuwa tana falonta, tarufe fuskarta. Da hijabi duk wanda yashigo gaisuwa seya dauka kuka takeyi, haka yan unguwa suka rika shigowa yin ta,aziya.
Washe gari Falak ta tashi da zazzabi me zafi, bata iyama tashi ga ciwon kai, Baba mairo duk tashiga damuwa, Jalila cetasamo mata magani adakin Zarah, haka akayita karbar gaisuwa har kwana 3, su Asabe da kawarta Dije ma sunzo.
Jidda kuwa batama san abinda akeba dan suna Lagos ita da Al,amin. Bayan sadakar 7 su Asabe suka koma suna cike da farin cikin abinda Zarah tayi masu dan tabasu kaya da kudi masu yawa saboda tana cikin murnar aikin boka yayi.
,
Malam. Sameer zaune a dakinshi yana tunanin kome yahana Falak da Jalila zuwa makaranta, gashi no da Falak tasa mashi yakira harya gaji tun aranar amma bata shiga, jawo wayarshi yayi, yaduba agogo yaga karfe 9 n dare.
No yakara kira, cikin sa,a kuma tashiga, zaune au Baba mairo da falak suke adakinta, dan tunda Ameer yarasu adakin Baba mairo take kwana, wayar Baba mairo ce tayi kara, dauka tayi da sallama, bayan sun gaisa yace Baba mairo dan Allah ko Falak tana nan? Cike da mamaki tace e tana nan, wayene, yace Malaminsu ne na islamiya Sameer.
Washe baki Baba mairo tayi, dan tanajin labarinshi agurin Falak da jalila,hartake tonan Falak tana cewa kode siriki tasamo mata. Baba mairo tace e gata nan bari abata, mika mata wayar tayi, bayan sungaisa, yace haba Falak tunda kika bani no kuma bansake ganinki a makaranta ba, gashi idan nakira ma bata shiga.
.
Na tambayi yan ajinku sunce wai kindena zuwa Jalila ce kadai take zuwa itama ba sosai ba. Meyafaru dan Allah, kinsan tun rannan naga kamar akwai abunda kedamunki.
Shiru tayi saboda wani kuka daya taho mata, Baba mairo kallonta kawai takeyi, tama karajin tausayinta. Hello Falak kinajina kuwa, sautin kukanta kawai yaji daga nan takashe wayar, tafada bisa katifa tana kuka
Kara kiran wayar akayi, ganin harta kusa katsewa yasa Baba mairo ta dauka. Sameer yace hello Falak kinajina, dan Allah kiyi shiru, bana son jin kukanki wlh, yana tadamun hankali, tunranar damuka hadu akasuwa naga kamar kina cikin dakuwa nima nashiga damuwa. Kiyi hakuri idan akwai abinda yake damunki. Wlh ashirye nake da intemaka maki.
Hawayen idonta Baba mairo ta goge aranta tana mejin dadin yau Falak tasamu wanda yake damuwa, da lamuranta. Hello Falak kiyimun magana. Baba mairo tace yaro kanajina, yace e,e Baba inajinki ina Falak din?
.
Tace Falak bazata iya maka magana yanzu ba, dan kamata fami akan abinda kedamunta, sede bansani ba, kawai naji ka kwanta mun arai, dama kuma inajin labarinka agurin su Jalila, tun lokacin daka bama Falak addu,a tayima Ummanta sanda batada lafiya.
Agaskiya Sameer bazan iya boye maka abunda yake damun Falak ba, saboda inaji ajikina, kaine zaka temaketa, idan harkaji labarinta, idan harzaka iya sauraron labarin Falak, kabari se gobe idan kasa kudi awaya kamar irin wannan lokacin seka kira inabaka labarinta.
Sameer yace a,a Baba mairo wlh inada kudi awayata zasu isa inji labarin Falak, bazan iya hakuri xuwa gobe kamar yanzu ba. Gyara kwanciya Baba mairo tayi, tace zanbaka labarinta, amma inaso kazam merikon gaskiya da amana idan kaji labarinta............. Anan Baba mairo tafara bashi tarihin Falak.
.
Kuka kawai Sameer yakeyi, yana sauraron Baba mairo, hartagama bashi labarin Falak, be iya magana ba, yace nahode Baba, Sautin kukanshi kawai takeji,da haka yakashe wayar.
Tunda yake arayuwarshi betaba jina labari me firgitarwa kamar na Falak, jiyake kamar a film akayi abun, da ace ba Baba mairo bace tafada mashi, labarinta ba, naze yarda ba.
.
Wata irin soyayyar Falak ce take shigarshi, gatausayinta daya ke shigarshi jiyake kamar yaje yadaukota tadawo kusa dashi, kuka kawai yakeyi, yana jin zuciyarshi kamar zata fito, aranar kasa bacci yayi, sede yayi alwala yafara nafila, har asuba tayi, seda yayi sallar asuba sannan ya kwanta, saboda ciwon dayaji kanshi yana yimashi.
Falak ma haka ta tashi da ciwon kai me tsanani, da zazzabi, da kyar tayi sallah ta kwanta, Baba mairo tana gama sallah taji Zarah tashigo ta watso kayan wanki tace idan wannan AGOLAR tagama sallah kice mata tayi mani wanki, saura kuma tabari gari yawaye infito bata gama ba.
Fita tayi takoma dakinta ta kwanta, Kallon Falak Baba mairo tayi wadda batama san me akeyi ba, saboda bacci me nauyi yadauketa, saurin tashi Baba mairo tayi tadauki kayan tashige bandakin dake cikin dakin tafara wankesu. Dayake bawani yawa garesu ba, kuma basuda datti, cikin minti 20 tagama, cikin sando tafita taje ta shanya, tadawo.
Kitchen tawuce tayi wanke wanke sannan takoma daki ta kwanta ganin haryanzu gari be ida haske ba, kuma dama bata fara girkin safe se karfe 7. Kwanciya tayi tana tunanin hanyar dazata bi Falak tabar gidan, sede tana tunanin Falak bazata yarda tabar gidan ba, inde ba aure tayi ba, saboda tana riko da wasiyar da Ummanta tabar mata. Addu,a tashiga yi Allah yasa Sameer yace ze auri Falak, da cikin lokaci kadan zatace yafito, sede bata sani ba ko Zarah zata yarda Falak tayi aure yanzu.
.
Har karfe 10 Sameer be fito daga daki ba, ummanshi Halima data gama saida kosanta harta gama aikinta, tajishiru, kuma besaba yin haka ba, dakinshi tashiga da sallama. Tsaye tayi ganinshi zaune yabuga tagumi yana tunanin, ga kuma hawaye suna fita daga idonshi.
Kusa dashi tazauna jikinta duk yayi sanyi ganin danta yana kuka, dan tasan kila mahaifinshi yatuno. Sameer lafiyarka kuwa, kake kuka? Goge idonshi yayi yace Umma ina kwana, kiyi hakuri yau natashi banajin dadi shiyasa banfito dawuri ba.
Lafiya lau, Sameer amma bawannan na tambayeka ba, rashin lafiyar ce tasa kuka kome? Tashi yayi yace Umma bara inyi wanka zan fada maki damuwata, waje yanufa domin yin wanka.
Seda Falak tayi wanka sannan Baba mairo takawo mata abinci, fa kyartaci tasha magani, dan tadanji sauki datayi bacci sosai, kallon Baba mairo tayi tace Baba mairo yaushe aka wanke ma Ummi kayanta harnaga kina linkewa? Anan Baba mairo tafadima Falak abunda yafaru da tana bacci, kwalla ce tacika idonta, tace bansan da abinda zan saka maki ba, Baba mairo, Allah yabani tsawon rai nima inyi maki wani abu wanda zakiji dadi arayuwarki.
Murmushi Baba mairo tayi tace ai keda Ummanki kungama mun komai tunda har kuka daukeni amatsayin uwa, kinga ko babu abinda yafi wannan dadi, nide fatana Allah yabani tsawon rai in kaiki dakin mijinki. Murmushi Falak tayi tace Uhm Baba mairo kenan, aini bana sa rai zanyi aure, dan nasan Ummi bazata barni inyi aure ba, tunda batason cigaba na.
.
Baba mairo tace insha Allahu sekinyi aure Falak, kuma ni harna zaba maki miji ma, Allah yasa zakiyi na,am da zabina. Dariya Falak tayi tace lallai Baba mairo kinkosa kirabu dani, to afadamun wanda aka zaba mun, ina fatande ba tsoho bane?
Dariya Baba mairo tayi tace a,a wanda kike sone kika boyema ranki na zaba maki, fiddo ido Falak tayi tace kai Baba mairo, yaushe mukayi haka dake, ni babu wanda nakeso. Har Malam. SAMEER din? Rufe fuska Falak tayi tana murmushi, tace yaushe nacemaki inason malam. Sameer kuma? To inma baki sonshi ni shina zaba maki. Kai Baba mairo shifa bece yana sona ba,
Yace mana, jiya ai naji abinda yace, da kika aje waya nadauka, haka yayita surutai, yadauka kece awayar. Dariya Falak tayi tace nide banyarda ba, Baba mairo tace Allah Falak a aje batun wasa agefe, dama inaso muyi magana dake akan Sameer, nide tabbas nayarda dashi, shiyasama jiya nakasa boye mashi labarinki.
Inaso Falak ki nutsu kigane mesonki, kada kiyi la,akari da Sameer malamin makaranta ne, kice bakisonshi, nide nayarda dashi , kuma nasan zerikeki da amana, inaso insamu lokaci inganshi koda awani gurine, ko kuma yazo yakaini gidansu muyi magana dashi. Allah yasani inaso inga kinbar gidan nan. Falak tace to Baba mairo Allah yazaba mana abinda yafi zama alkairi. Amma kisani duk ranar dazan bar gidan nan kafata kafarki, idan bahaka ba, sede na hakura da auren dan kowa zan aura, seya yarda zaki bini. Dariya Baba mairo tayi tace ti naji insha Allahu ma bakida mijin daya wuce Sameer. Murmushi Falak tayi tadauki kayan Zarah tafara gogewa.
.
Zaune suke afalo Alh, yakalli Jalila, yace Alhamdulillahi gashide na amso maki, admission dinki, kuma nabama wani abokina yayi maki registration ana A,B,U tunda de kince bazakiyi karatu anan kadunaba, wato kinfison makarantar kwana ko? Dariya Jalila tayi tace ai Dady anfi yin karatu acan, amma nan kila inacikin yin karatun wani abun yadaukemun hankali.
Zarah tayi murmushi tace can dinma ai gidane, damma tace bazata zauna agida gurin Inna asabe be, tafison hostel, me suka bata ne? Biological science ne suka bata, to Allah ya bada sa,a seki dage.
Alh, yace Hajiya watodesu Inna su kwace mana Jidda ko? Yanzu ko lekomu batayi, naso ace tadawo insa ayi mata exam ta kudi itama tafara karatun tunda taki fidda miji, dazama haka nan, amma gaskiya banajin dadin rashin zamanta agida kusa damu. Zarah takalleshi fuska ahade tace to mekake nufi? Tunda yarinya tace batason karatu abarta mana aiba dole bane, ni karatun nayi dakake zaune dani. Kuma menene bana yi maka, wama ze kalleni yace secondary kawai nayi, itama ta gwamnati, ina laifi ma ita tayi makarantar kudi tasan yes tasan no.
Nifa banason takura wlh, kuma dakake maganar tadawo gida tazauna, kana nufin gidanmu ba gida bane kome? Inma kyamarsu kake nima acan nataso harka ganni kace kanaso, idan tadawo nan, mezatayi maka, kaima da bazama kakeba, kuma acan tana taya Inna zama tunda ita kadai ce.
Allah yabaki hakuri Hajiya wlh ba haka nake nufiba, kawaide nafada ne, amma kiyi hakuri ba za,a sakeba. Kallon mamaki Jalila take bin Umminsu dashi, ganin yanda takema Dadynsu fada, wanda ada ko gardama batayi mashi, amma wai yau shine yake bata hakuri, har muryarta tana fin tashi yin sama. Tunowa tayi da wa,azin da malam Sameer yayi masu akan hukuncin matar datake daga ma mijinta murya. Wasu zafafan hawayene suka rika fiyo mata, saurin gogesu tayi.
Alh, yace Jalila zaki iya tafiy, amma kizama cikin shiri nan da sati mezuwa zaki tafi, anjima kizo ki amshi kudi seki siyo abunda kike bukata. Tashi tayi jikinta duk amace, tafita.
Halima tace Sameer lallai akwai abinda yake damunka, kuma ba karamin abu bane, kallifa dan abincin daka ci. Sameer yace wlh Umma banajin dadin abincin ne. Rufe kwanon tayi tace inajinka fadamun damuwarka.
.
Gyara zama yayi, ya kwashe duk abinda Baba mairo tafada mashi yafada ma Ummanshi. Kasan cewar Halima mace me tausayi, bata san lokacin da hawaye suka wanke mata fuska ba.
Tana goge idonta tace wai Sameer wannan labarin ba ta tsunniya bace kake bani kuwa. Wlh Umma ni kaina faba Babbar mace bace tabani labarin Falak ba, dabazan yarda ba, kuma nima naga wasu alamomi agurinta lokacin damuka hadu kasuwa, bakiga kayan jikinta ba, bazakice daga gidan masu kudi tafito ba.
Umma tace tabbas nima bantaba jin abinda yabani tausayi da tsoro irin labarin Falak ba, agaskiya Sameer ina yimaka sha,awar aurenta, koda bakace kana sonta ba, nizanyi maka umarni da aurenta kodan kafidda ta daga rayuwar datake ciki, dan wannan mata batada imani zata iya kasheta wlh.
Kuma naji dadi, dakace kana sonta, tunkafin kaji labarinta, hakan zesa nayarda bawai tausayinta ne yasa zaka aureta ba, dama nafison ace akwai soyayya atsakaninku kafin kuyi aure, hakan zesa auren yafi dadewa.
Tunda baze yuwu kaje gidansu ba, meze hana kadauko Baba mairo kuzo nan muyi magana ba. Yace shikenan Umma zanyi yanda kikace. Yauwa Sameer amma dan Allah kacire damuwa aranka, insha Allahu bakada mata se Falak, zantayaka da addu,a har Allah yadoramu akan wannan muguwar mata. Sameer yayi murmushi yace ai damuwa takare, dama ina tsoron kiji labarinta kice bazan aureta ba. Dariya tayi tace haba Sameer ai yakamata kamun sheda mekyau, Allah kada yakawo ranar dazan tauyemaka hakkinka, kamar yanda kakemun biyayya dolene nima inso abunda kakeso, matukar baze cutar da kaiba.
.
Sameer yace amma Umma anan gidan zamu zauna ko? Kinsan banason nisa dake, tace a,a kada ma kafara, bazan zauna da surika agida daya ba, gara de muna nesa, idan kata fima akwai A.isha diyar yaya Zainabu tagama makaranta kuma dama tace mun zata bani ita, tunda tana da yan mata, seta dawo nan mucigaba da zamammu.
Sameer yace to umma ina zan zauna? Tace bade ka gama karatunka ba, haya zaka kama kafin Allah yabude se kafara gina wancan filin naka. Amma Allah bazamu zauna tare ba. Dariya yayi yace toshikenan Umma ai base kinrantse ba, yanzu de bani abincina incinye. Dariya tayi tace oh baka koshiba kenan.
Sati yana zagayowa Jalila tagama hada komai, nata, dakin Baba mairo tashiga, zaune ta iskesu suna fira, mikama Falak takaddu tayi, idonta yana kallon kasa, saboda gab take da fashewa da kuka, ita kadai tasan abinda takeji. Falak tace nameyene Jalila? Budawa tayi tafara dubawa, cike da farin ciki ta rungume Jalila, ganin result dinta ne ta amso mata kuma gaba daya tacinye both waec dan Neco.
Kuka sosai Jalila tasak tana kara kankame Falak, cikin muryar kuka tace Falak kiyi hakuri nasan Ummice tasakaki cikin halin da kike ciki, gashi yanzu zantafi makaranta batare dakeba, wlh saboda ke nazabi intafi boarding saboda bazan iya kallonki cikin damuwa ba, ki kara hakuri akan wanda kikeyi.
Kuma dan Allah ki amince da malam. Sameer yafito kuyi aurenku kema kibar gidan nan, dan wlh koni bansan lokacin dawowata ba, banason gidan nan, gara inzauna amakaranta yafi mani zaman gidan nan. Nizan tafi, inada no Baba mairo zamu rika waya, Kudi masu yawa tasaka ma Falak ahannu sannan ta bata wata leda wadda kayan shafa ne, aciki masu yawa. Tasiyo mata.
Kuka sukeyi sosai, harseda Baba mairo itama ta tayasu, seda suka gaji sannan sukayi shiru, kufi Jalila tamika ma Baba mairo,godiya sukayi mata. Har bakin kofar dakin Baba mairo suka rakata da kyar Baba mairo taja Falak suka koma ciki ita kuma Jalila tafita tana kuka tasamu su Alh, da zarah suna jiranta awaje, dan sune zasu kaita.
0 comments:
Post a Comment