AGOLA Page 41-50 (the end)
.
Suna zuwa aka nufi labour room da ita, shi kuma Saleem yashiga da Jalila su Bilkisu suna binshi abaya, itama daki aka nufa da ita domin adubata. Sameer gurin su Baba Mairo yanufa, koda yaje ya iske har ansaka gawar Jidda ambulance, za,a kaita gida, Baba Mairo tace lafiya Sameer naganka arude? Alh wanda fuskar shi take jike da hawaye, ya goge idon shi yace lafiya de Sameer? Yace bakomai dama Falak ce zata haihu tana dakin haihuwa.
Alh, yace to ina Jalilan kotana gidanta? Kai yasosa yace a,a nabarta ita da Saleem inaji befada mata ba, yauwa kada kufada mata kawai yadauketa yakaita gida. Baba Mairo kikoma gurin Falak din mucemu wuce da gawar, tunda Halima tana gurin Zarah.
.
Goge kwallan idon ta tayi tace a,a Alh muje inaso inyima Jidda wanka da kaina, kai Sameer kasamu Halima tunda dazu akayi ma Zarah allurar bacci kace taje gurin Falak din, nizanje can gidan. Yace to nima yanzu zanzo kafin agama shiryata tunda ance yau za,a kaita tunda dare beyi ba.
Haka suka nufi gida da ita kowa yana cikin damuwa. Babu bata lokaci Falak ta haifi kyawawan yaranta guda biyu, Mace da namiji, cikin koshin lafiya, bayan angama shiryasu aka fada masu Sameer, Bakaramin murna Sameer yayi ba, dan betaba tunanin samun yan biyu ba. Wayarshi ce tayi kara, yana dubawa yaga Saleem.
Dauka yayi yace Saleem ya Jalilan ta farfado? Yace E amma haryanzu kamar bata gama dawowa hayyacinta ba, amma likitan yace zeyi mata allurar baccin dazata kaita har gobe dan tasamu ta huta. Sameer yace toshikenan yanzu itama Falak ta haihu, ansami twins, fito muhadu semuwuce can gidan.
Saleem yayi farin cikin ganin jariran masu kyau dasu, bayan ankai Falak dakin hutu, itama haryanzu kuka takeyi, suka dubata da jiki, suka ce zasuje sukai Jidda, Falak tace Allah sarki Yaya Jidda Allah yajikanta, naso ace nakara ganinta. Sameer yace se hkr addu,a zamu cigaba dayi mata, bara muje semun dawo, nasan se gobe za,a sallameki gara kizauna ana ku huta, tace tosekun dawo ina Jalilafa? Anan suka fada mata abinda yafaru, tace to Allah yabata lafiya, haka suka fita suka bar Umman Sameer agurinta.
.
Gida mata se kuka sukeyi, Baba Mairo da Matar Kawan Alh, su sukayima Jidda wanka, suka shiryata, babu bata lokaci aka fiddota, akayi mata sallah,aka nufi gidanta na gaskiya da ita.
Koda sukaje Alh, kasa sakata kabari yayi, sbd kukan dayakeyi, sede su Kawu ne da Baba na Zariya da Kawun Sameer suka sakata, Alh, yabama kowa tausayi agurin, haka aka gama sakata akabarinta aka rufeta, suka dawo.
Aranar haka kowa yazauna masu bacci kadan ne, dan Alh, tunda yashiga daki, yayi wanka yayi alwala yayita nafila da karatun Qur'ani har seda aka kira sallah sannan yanufi masallaci. Bayan sunadawo ne, yake tambayar Sameer yabega Jalila ba, anan yake fada mashi halin datake ciki, da kuma abinda Falak tasamu, yayi murna sosai, yace tobai bazama zamuyi ba, muwuce muga jikin nasu.
Lokacin dasukaje asibitin har Falak tayi wanka Anyima jariran wanka suma, sunyi gwanin kyau, sede daka kalli Falak kasan tana cikin damuwa. Baba Miaro tana kusa da ita dan agurinta ta kwana, ita kuma Umman Sameer ta kwana agurin Jalila ita dasu Bilkisu.
Jalila kuwa tafarka, tunda tayi sallah itama take kuka, se lallashinta sukeyi, haka Alh, yasameta, yana ganinta shima yaji wani sabon kukan yazo mashi, da kyar yasamu yadedeta kanshi yashiga, shima lallashinta yashiga yi, sannan suka nufi gurin Falak, acan ma du lallashin ne, daga can yawuce gurin Zarah.
Zaune suka sameta duk ta kwance bandage din da aka rufe mata ciwon tana ta wasa dashi, cikin sauri Saleem yaje yajira nurse, ana suka riketa aka sake mata wani sabon dressing din. Tagumi Alh, yayi, yana kallonta, yarasa neke mashi dadi aranshi, addu,a kawai yakeyi itace take kara sanyaya mashi ranshi. Fita yayi yace bara yatafi tunda gari yayi haske sbd masu zuwa gaisuwa.
Karfe 10 aka sallami Falak da Jalila, Baba Mairo tace awuce da Falak gidansu Jalila, idan kunje se a bude part dinsu nada tazauna aciki, sbd asamu saukin zirga zirgar. Sameer yace hakan ma yayi, tace nima anjima zanzo sbd nasan babu wanda ze zauna agurinta, idan yaso se Halima tazauna agurin Zarah, anjima se indawo.
.
Sunzo tafiya, su Bilkisu sukace bara suwuce gida anjima zasu dawo, godiya sukayi masu, Saleem yabasu kudi suka tafi, sun fito kenan suka hadu da Al,amin, Jalila yagane, hakan yasa ya tsaya suka gaisa, kallonta yayi tana kuka yace ina fatan kunshedani? Al,amin ne, yame jikin? Falak tashare idont tace Allah yayi mata rasuwa jiya da dare. Kiyayi kamar ansara mashi icce akanshi, wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo mashi. Yace shikenan Jidda ciwo ya warke, darabon mugana ashe, sallama yayi masu yace zeje yadauko Ameerah suzo tare.
An gyara part din su Falak na da dama kuma babu abinda aka cire aciki, tunda Hajjo tarasu da aka kulle shi ba,a kara amfani dashi ba, share shi akayi aka goge, sannan Falak da Jalila suka shiga ciki, amma Falak cewa tayi adakinta na da zata zauna bazata shiga dakin Ummanta ba, Sameer yaje yadauko mata duk kayan dazasuyi amfani dasu yakawo, Baba mairo ta dora ruwa takara yima yaran wanka, tasa Falak itama takara yi.
Saleem ne zaune afalo shida Jalila, haka yayita lallashinta da kyar yasamu taci abinci shima kadan taci, yace Jalila inaso ki kwantar da hankalinki yanzu babu abinda Yaya Jidda take bukata daga gurinmu se addu,a. Kirika yawan ambaton Allah da addu,oi zaki samu sauki aranki, nasan dole kiyi kuka amma hakuri zakiyi. Allah yaji kanta, yabama Ummi lafiya, tashi yayi yace zeje waje. Itama shiga gurin Falak tayi, dan batason zuwa bangarensu.
.
Haka aka cigaba dazaman gaisuwa, Al,amin da Ameerah sunzo gaisuwa, itama tasha kuka, Al,amin yakira Jalila yace yadauki nauyin ginama Jidda rijiya amakarantar almajirai kamar yanda taroka, kuma zeginata ne da sunan ta, amatsayin sadakar daze bata. Sosai Jalila tayi mashi godiya, seda suka jera kwana 7 suna zuwa gaisuwa, ranar da akayi sadakar 7 aranar akayi sunan Falak, bawani taro akayi ba, bayan sadakar 7 akayi radin suna.
Namijin aka samashi sunan Alh, wato Abba, ana kiranshi da Ameer, dan Falak tace tana son sunan, Macen kuma Aka samata sunan Hajjo, Zainab, ana kiranta da Ameerah. Falak tayi mamaki sosai da Sameer besa sunan babanshi ba, har seda tayi mashi magana, murmushi yayi yace haba Dear, Alh, shine mutumin da yayi sanadiyar haduwata dake, kuma ya cancanci abinda yafi haka agurina dake baki daya. Umma kuma dana sa sunanta, kinga tarasu kuma saka sunanta zesa murika tunawa da ita, jawota yayi yace kada kidamu nasan nan da shekara 2 zaki kara sama mana wasu babies din. Murmushi tayi tace nagode.
Ayau ne, Jalila zata koma gidanta, dan Alh, yace sutafi gida zatafi samun sakewa idan tana kusa da mijinta, sauran mutane ma, duk sun watse se yan uwa kawai suka rage, yan Zariya ma yau zasu tafi, Alh, yasa aka kira kowa yace yana son magana dasu, anan falonshi suka taru, hada Kawunshi, da Kawun Sameer, da Mal. Garba dasauran mutanen.
.
Bayan anbude taro da addu,a, aka kara yima Jidda addu,a sannn Alh, yafara magana, hakuri yakara bama kowa, sannan yace Jalila,Falak, ayau nakeson kowa takoma gidanta, wanda yarasu yariga da yarasu, dan haka addu,a kawai zamu cigaba dayi mata, banaso insamu labarin acan kun kasa sakin jikinku, kowa hkr yakeyi arayuwa, kuma dama dan Adam baya zama haka, har se Allah ya Jarabceshi, dan haka murika daukar kowace kaddara tazo mana da hannu 2, Allah yayi maku Albarka.
Kuma itama Zarah munyi magana da Malam, yace gobe Malaminshi zezo yafara yimata rukiya, dan haka nayima Dr, magana zamu maidota gida yau, idan yaso se arika zuwa gida ana mata dressing, tunda yanzu yakoma bayan kwana 2. Kallon Kawaunshi yayi yace Kawu ko akwai abinda zakace?.
Gyara zama yayi yace hakane, duk abinda kafada yayi dede, sede abu 1 nakeso inkara, Baba Mairo mungode kwarai da irin abunda ku kai mana, daga ke har Halima, tabbas kunzama yan uwa, sede ina rokonki wata alfarma, daga ke har Halima, duk da bata nan, amma ga malam nan, muna neman alfarmar daka barsu sudawo gidan nan dazama, kaga akwai marar lfy, kuma yanzu Zarah ba matsayi matar Abba take ba, asali ma, babu sauran igiyar aure atsakaninsu, idan har kayarda mun rokon alfarmar dasu dawo nan dazama, hakan zeyima Abba sauki dan baze yuwu ace mubama shi mal. Garba ita yatafi da ita ba, duk da tayi mana laifi amma ba,a kallon abinda yawuce, idan ka kalli alherin da mutum yayi maka zaka iya temaka mashi dashi.
Kaima Abba dole kayi hkr da duk abinda Zarah tayi maka, tabbas tacutar da kai da kowa naka amma, ka kalli darajar yaranku kayi hkr, inaso tacigaba dazama agidan nan har Allah yabata lafiya, daga nan kuma seta zaba ma kanta abinda taga zefi mata.
Amma inaso inji daga bakinka ka amince zata cigaba dazama agidanka harta samu lafiya?.
Se kunjini a next page dina wadda insha Allah shine last page. Nagode da kaunarku gareni.
.
Shiru Alh, yayi nawani lokaci, sannan yace shikenan Kawu duk abinda kace yayi dede, Allah yabata lfy. Kuma nagode da abinda kuka yi mani, Allah yasaka da alkhairi. Kawu yace Alhmdll, anjima malamin ze iso, dan haka se kuje kudauko ta. Haka suka tashi kowa yafara shirin tafiya.
Bayan andauko Zarah daga asibiti duk wanda yaganta seya tausaya mata, takoma kamar skeleton ne aka sama fata, tayi baki, ga kafarta da aka yanke tundaga cinyarta har kasan kafar sun shanye tazama siririya, ta yanda bazata kara amfanuwa ba, sede ciwon dake jiki yayi sauki, sbd Kawu yabada ruwan addu,a ana shafa mata akan ciwon, hakan yasa yadena fitar da ruwan dayakeyi, kuma dama aljanun jikinta ne suke sakashi zuba.
Jalila da tunda ta kalli Zarah take kuka, a part dinsu Falak Alh, yace akaita, awani daki dayake farkon shiga daga gefen falon, anan aka saka mata katifa, dayake akwai bandaki aciki, sede dakin bawani girma gareshi ba, bayan su Baba Mairo sunyi mata wanka, suka gyarata aka daureta tana kwanciya tayi bacci.
Saleem ne yazo daukar Jalila, tana kuka haka suka tafi su Baba Mairo se hkr suke bata, Falak ma seda tayi mata kuka, Sameer yace kema shiryawa zakiyi anjima zamu tafi, Baba Mairo tace gsky bazaku tafi ba, dama inaso inga Alh, muyi magana, dama ace yaro daya gareta se kutafi, amma yara har biyu, sannan kai kuma aikinku idan kafita wani lokacin har dare kake kawai, yazatayi da yaran? Kuma kaga muduka muna nan bare ma ace ni inje inzauna mata. Sameer yayi murmushi yace haba Baba yanzu dan Allah so kuke inzama gauron karfi da yaji? Inde haka ne, nima sede indawo nan. Baba Mairo tace nidama ai bance zan hanaka ganin matarka ba, sekaje ka kullo gidan kaima kadawo nan idan sukayi ko wata daya ne, sunyi kwari se ku koma gidanku. Yace shikenan nagode, tace yauwa zanje insamu Alh.
Da misalin karfe , Kawun Sameer suka iso da Malamin dazeyima Zarah karatu, Alokacin shima Sameer ya iso gidan da akwatinshi, dan Alh, yace shima yadawo, a dakin Falak yasauka, su kuma su Baba Mairo suna dakin Hajjo, Alh, shi kadai a part dinsu.
Afalo akayimata shinfida bayan sunyi mata alwala, malamin yazo yafara yi mata karatu, yadade yana karatu amma sunkiyin magana, sbd manyan aljanune, kuma bakake, yasha wahala sosai, kafin suka fara magana.
Wayyo Malam, ya isa zamuyi magana wlh, zufar goshin shi yagoge yace inajinku..... nide sunana Zurkum, kuma nine shugaban bakaken aljanu, wannan matar bata da kirki, sunyi da megidanmu akan duk lokacin da mijinta yagane halin datake ciki, akwai abinda ze sameta, amma haka ta amince, mu kuma dama mune yasa muke mata aiki, kuma dama duk wanda ya kasance yana maka aiki duk ranar daka dena biya mashi bukata, to kanka ze dawo, hakan yasa tundaga ranar da asirinta yatonu muka shiga jikinta.
.
Mune nan muka fado mata da durowa akafarta, kuma muka shanye jinin jikin kafar da bargon kafar, hakan yasa bazata kara amfani da kafar taba, tabbas wannan mata tayi sa,a tasamu masu yimata addu,a amma munso semun bi duk wani jini dayake jikinta munshanyeshi duka sannan daga karshe mukasheta, amma karfin addu,ar da akeyi mata yasa muka kasa aikata abinda mukayi niya. Amma kusani wannan mata bazata kara ganin haske arywarta ba, sbd tasamu mun cuci mutane, aciki harda karamin yaro wanda besan komai ba.
Dan haka kada ka konamu zamu tafi amma duk lokacin data kara shiga gonarmu tabbas takira ajalinta. Malam yace kuyi mani alkawarin bazaku kara shiga jikinta ba, idan kun fita. E munyi alkawari, amma itama ta gyara rayuwarta, takuma koma ga Allah wanda take bautamawa, hakanne ze kareta daga shrrinmu. To nagode.
Wata irin kara Zarah tasaki tare da atishawa, har so 3 sannan takoma ta kwanta, bacci yadauketa. Malam yace Alhmdllh, insha Allahu data farka zata dawo hankalinta, sede ina tunanin zata iya kaiwa gobe, dan haka zantafi gobe da safe zandawo. Ga wannan asamu wani ya zauna kusa da ita, aduk lokacin data farka abata wannan ruwan addu,ar tasha. Allah yakara sauki, kome kenan sauran bayanin idan nazo gobe zakuji.
Godiya sosai, sukayi mashi, yatashi yatafi. Falak, tana gefe se kuka takeyi, Baba Mairo tace banga amfanin asarar hawayen da kikeyi ba Falak, ace kuka yaki karewa, haba dan Allah, so kike kijama kanki wata cutar. Umman Sameer tace gsky Falak ya isa haka, kin sande kuka baya maganin komai, nasan akwai abubuwa da yawa dakike tunawa, amma kiyi hkr kisama kanki dangana, kinga kinrasa mutane dayawa arayuwarki, kuma duk da haka numfashinki bedena tafiya ba, dan haka kimanta da duk abinda yafaru dake arayuwa, Allah yana tare dake.
.
Idan kika kalli baiwar da Allah yayi maki ta yara 2 ya isa ki godema Allah, ada kinkasance ke daya, yabaki miji nagari, sannan yazo ya azurtaki da yara, Allah kadai yasan iyakar abinda zaki haifa, kinga wannan ma wata rahama ce daga Allah. Falak tagoge idonta tace nagode, da irin kulawarku gareni, kuma insha Allah, nadena saka damuwa araina. Baba Mairo tace yauwa kokefa, tashi ki kaima mijinki abinci kije daki kidauko yan biyu ki maidasu dakinku.
Bangaren Amarya da Ango kuwa, da kyar Saleem ya lallashi Jalila, taci abinci tayi wanka, yasa sukayi sallah, yajata zuwa gado yacigaba da lallashinta yana kara kwantar mata da hankli, taji dadin irin kalaman dayake fada mata sosai, cikin lokaci kankani taji zuciyarta tayi haske, duk wata damuwa ta gushe, daga lallashi shima ango ya canza tasha, naja masu kofa nace seda safenku.
Washe gari da safe har 8 tayi amma Zarah bata farka ba, mutanen gidan harsun gama karyawa, sunyi wanka, suna jiran tashinta, Baba na Zariya kuwa har yagama shiryawa dan yace shima yau zetafi, jiran tashinta kawai yakeyi da kuma jawabin da malam yace zeyi, se wajen 8:30 sannan ta farka cike da firgici, Baba Mairo tayi saurin riketa tana tofa mata addu,a Umman Sameer tamiko maganin da malam yabasu aka bata, kallonsu kawai takeyi Babanta yace kintsaya kina kalon mutane bazaki bude baki kisha maganin ba? Baki ta daga tasha maganin, sannan tamaida kallonta zuwa cikin Falon, akan Alh, tasauke idonta, suna hada ido yayi saurin dauke kanshi tare da kara daure fuska. Juyawa tayi tana kallon Baba Mairo da Falak, wacce take rike da Ameerah, dan Ameer yana bacci.
Sauke kanta kasa tayi dasauri takara kallon Alh, idanunta suka ciko da hawaye ganin kafarta datayi anyanke, kuma ta koma siririya. Haka falon yayi shiru kowa yana kallonta. Sallamar su Kawu da Malam sukaji, anan Alh, yafita domin ya shigo dasu. Bayan sun shigo aka gaggaisa, suka samu guri kowa yazauna, Sallamar Saleem da Jalila sukaji, dan Alh, yayi ma Saleem waya akan suzo. Falak da tunda taga yanda Jalila ke tafiya tafara dariya ciki ciki, suna hada ido da ita Jalila ta maka mata harara. Sameer ya zunguri Falak ahankali yace kede kincika sa ido. Zama sukayi suka gaida kowa, Jalila se kallon Zarah takeyi wadda kanta yake akasa tana kuka.
.
Bayan kowa yayi shiru Kawun Alh, wanda shima yana cikin falon, yayi gyaran murya yafara magana...... to Alhmdllh Allah mungode maka da ka kawo mana karshen wannan iftila'i da muke cike, wanda bakowa bane yayi sanadiyar shigarmu cikinshi seke, Zarah, tabbas kincutar da mutane dayawa arayuwarki, ki godema Allah daya barki harzuwa yanzu da ranki, wanda yabaki damar neman gafarar wadanda kika cuta, sauran kuma da kika kashe, sede ince tsakaninki da Allanki ne, kuma ki kara godema tsohon mijinki,,,, saurin dago kai tayi jin abinda Kawu yafada, wai tsohon mijinta.
E tsohon mijinki, dan yanzu haka babu igiyoyin aurenshi akanki, duka ya sauke maki su, kuma duk da irin abinda kika yimashi besa yayi watsi dake ba, ya tsaya akanki ganin baki wulakanta ba, duk da ke burinki kenan inda Allah yabaki dama, kiga kin wulakanta shi, sede ahi azuciyarshi ba haka bane, asali ma, yahanaki fita kije ki gogu da sauran yan'uwanki mahaukata, kuyi yawo aduniya kuna bin bola, yara suna jifarku, wasu marasa imani kuma suna binku suna maku fyade, kuna haihuwa akan titi, duk wadan nan abubuwan babu wanda Abba yabari kikayi, asalima acikin unguwar nan, bakowa yasan halin dakike ciki ba. Sannan wadan da kike da burin ganin bayansu, sune suka zama gatanki, alokacin da kika rasa wadanda zasu zauna dake, Falak, yarinyar da kika tsana, kinso ki lalata mata rayuwa, Allah yatsare abinshi, kin kashe mata Uwa, kaninta ma baki barshi ba, amma duk da haka ta tsaya domin ganin kinsamu lafiya,
.
Baba Mairo dattijuwa me kirki, wadda ahaife ta haifeki, bake bama, Abba kanshi ta haifeshi amma bata isa ki daraja taba, sbd kawai tana aiki a karkashinki, segashi yau tayi maki abinda Mahaifiyarkice kadai zata iya yi maka shi, tazauna dake acikin halin hauka, na tsawon kwanaki, tayi jinyar diyar cikinki, wadda ayanzu bata duniyar. Harma wata daban wadda baki sani ba, kawai ta dalilin yarinyar da kika tsana itama ta amfaneki, kinga kenan kinci darajar Falak, sirikarta gatanan azaune, sbd ke take zaune gidan nan, kuma ita tayi jinyar Jidda.
Saboda haka yanzu shawara tarage naki, dama ni naroki Abba akan yabarki kizauna agidanshi harki samu sauki sannan sekizabama kanki rayuwar data yimaki, mahaifinki ma nine na tsaidashi, sbd baki daukeshi da muhimmanci ba, bare kuma yan 'uwanki, wadan da tunda sukazo bikin Jalila sukace bazasu dubaki ba, sbd kema kin manta dasu, dan haka yarage naki ki gyara rayuwarki, duk wanda ya yarda zumunci to wata rana seyayi dana sani.
Shiru falon yayi inbanda kukan Zarah bakajin komai, sauran masu tausayi sede hawaye, Jalila, kam idanunta harsun kumbura, azuciyarta tana tirrr da irin halin Umminta, yanzu agaban kowa harda mijinta kalli yanda ake fada mata bakaken maganganu, jitake kamar tabar falon.
Malam yayi gyaran murya yace to Zarah, kinji de da kunnenki irin abubuwan da kika aikata, ace wai musulmi ne, da kanshi ya aikata wannan abun, sbd son zuciya da kuma kwadayin abun duniya, gashi nan ta sanadiyar abinda kikayi kalli irin abinda kika jama kanki, yanzu bakida saura daraja agurin kowa, sede idan har kin tuba kuma kin gyara halinki, abinda nakeso dake, idan har kinyarda zaki canza halinki, to dole sekin koma baya kin gyara rayuwarki daga farko, dan kinada karancin addini, kuma dole sekin gyara ibadarki, sannan zaki samu damar neman gafara agurin ubangijinki, sauran mutanen da kika cutar kuma gaki gasu, zaki iya neman gafararsu, saura kuma sede ince Allah ya gafarta maki,amma tabbas kina da kalubale agabanki, kuma duk wanda yayi niyar tuba, to dole seya bar duk wani abu najin dadin duniya sannan ze iya samun lokacin ibada. Daga karshe kuma ina maki ta,aziyar mutuwar diyarki, tare da fatan alkhairi na auren diyarki Jalila.
.
Kuka sosai Zarah takeyi, jitake dama Allah yadauki ranta, da irin wannan rana daya gwada mata, jan jiki tayi ta matsa kusa da Babanta, wanda shima kanshi yake kasa yana kuka, kafarshi takama tana kuka tana fadin Baba kaine mutum na farko daya kamata infara neman gafararka, tabbas na cuceka, na wulakantaka, ban baka darajarka ta Uba agareni ba, kai cona, daban zama 'ya tagari ba,nahada kai da makiyiyarka munzalunceka. Dan girman Allah Baba kayi hrk kayafemun, nasan idan baka yafemun ba, raywata bata da amfani, wlh ko haka Allah yabarni naga rayuwa kayafemun ko naga haske arayuwata. Kamota yayi yana kuka yace, ya isa haka Zarah, nayafe maki, duniya da Lahira, idan kina da laifi nima inadashi danayi sakaci da addu,a har wata tasamu galaba akaina, tazo taruguje tarbiyar dana baki afarko, tabbas, yanzu kam naga falalar addu,ar iyaye akan 'ya'yansu. Allah yagafarta mana gaba daya. Kije kinemi gafarar mijinki, shine yafi can canta daya yafe maki.
Matsawa tayi kusa da Alh, wanda shima yake kuka kamar karamin yaro, zata kama kafarshi yayi saurin janyewa, tace nasan banida bakin dazan nemi gafararka, na cutar da kai, na wulakanta ka, naci amanarka, na ha'inceka, nakasa bama yaranmu tarbiya mekyau, amma dan Allah kada kadubi laifukan dana yi maka, ka kalli girman Allah da darajar yaranmu ka yafemun, kaima Allah ze saka maka da mafificin alkhairinsa, kayi hkr da duk abinda nayi maka.
Shiru Alh, yayi yana kuka, Jalila ta matsa kusa dashi tarike kafarshi tana kuka tace, Dady dan Allah kayi hkr ka yafema Umminmu, nasan ta cutar da kai amma idan baka yafe mata ba, zata shiga wata irin rayuwa, dan Allah Dady. Goge idonshi yayi yace shikenan Jalila nayafe mata, ko alahira wani yanacin arzikin wani, haihuwa me rana, kigodema yarki kinci darajarta, nayafe maki.
.
Komawa gurin Falak tayi tana kuka tama kasa magana, dan muryarta harta dashe, Falak ta tashi ta aje Ameerah, tadawo takama Zarah tana goge mata kwallan idonta, itama tana kuka tace haba Ummi, kintaba ganin inda uwa tadurkusama yarta? Kamar yanda bazaki durkusama Jalila ba, haka nima agurina na daukeki Uwa, kada ki wahalar da bakinki gurin neman gafarata, ni 'yarkice, na dade dayafe maki, kuma har cikin zuciyata nayafe maki, Allah ya yafe mana gaba daya, Zarah jitayi gaba daya kunyar Falak da sauran mutanen falon takama ta, kallon Baba Mairo tayi tace Baba Mairo dan Allah kiyafemun abinda nayi maki, tabbas ke Uwa tagari ce dayakamata ace narikeki amatsayin Uwa, amma sena wulakantaki narike wadda tayi silar shigata wannan rayuwar amatsayin Uwa, gashi ta dalilinki nasamu alkhairi inbadan keba, dayanzu nakarama kaina zunubi me yawa,amma se bakibi son zuciyarki ba, kika kareni daga fadawa halaka. Nagode da irin zaman da kikayi dani da yarana. Baba Mairo tace ai bakomai Hjya. Zarah tace zanso kidena kirana da wannan sunan, dan yanzu nazama diyarki, narasa gatana Uwa, inaso kimayemun wannan gurbin dan Allah.
Kwalla Baba Mairo tagoge tace bakomai Zarah dama can ni amatsayi diya na daukeki, Allah yayi maki albarka,kuma Allah yajikan jidda, kallon Umman Sameer tayi tace Umma duk da bansanki ba, amma kinmun alkhairi, nagode maki sosai, Allah yasaka maki da gidan Aljannah. Tace Kawu kaima nagode kayi sanadiyar samun lafiyata.
Sameer kaima bansan dawane baki zan nemi yafiyarka ba, amma dan Allah kayi hkr da duk abinda namaka, kuma kayafemun, nagode sosai da dawainiyar da kukayi mana kaida Saleem, Allah yabiya ku. Suka ce amin. Zarah tace Allah sarki Jidda Allah yaji kanki, banida rabon neman gafararki, nasan banzamo Uwa tagari agareku ba, amma ina rokon Allah ya yafe maki laifukanki, kema Jalila kiyafemun. Kuka tasaka, kowa seda yatausaya mata.
.
Malam yace to Alhmdllh naji dadi sosai da kuka zamo mutane masu yafiya ga junanku, kuma dama haka Allah yakeson bayinsa masu saurin yafiya akan laifin da,akayi masu, dan duk mutumin da,aka cuta, yana da ikon daukar mataki amma yayi hkr ya yafe tabbas wannan mutumi Allah zesaka mashi da mafificin alkhairinsa. Allah yakara yafemana laifukanmu, yashiryar damu da iyalanmu, Allah yasa mufi karfin zuciyarmu. Daga karshe Alh, inason inroki wata alfarma agareka, inaso kamar yanda su Baba Mairo zasu zauna agidanka, inaso itama Zarah kayi hkr kabarta tazauna agurinsu, tunda zatafi samun matemaka, akan idan takoma gidansu, tunda shima babanta ba aure gareshi ba, kaga idan Allah yakawo mata miji setayi aure hakan zetemaka mata tasamu saukin damuwar datake ranta.
Kawun Alh, yace tabbas Malam karigani, nima abinda ke raina kenan, kaima Alh, bazeyuwu kazauna haka ba, amma kome kenan, nan da kwana 2 zanzo akwai maganar dazamuyi. Zarah jitayi kamar ta kurma ihu, wai agabanta ake maganar mijinta zeyi aure, ita kuma gata ta nakasa, kilama bazata kara aure ba. Goge idonta tayi aranta tace kaicona. Jalila ma hakanan bataji dadin abinda Kawu yafada ba, taso ace ba saki 3 Dadynta yayi ma Umminta ba, da tasashi ya maidata.
.
Malam yace to ai semu rufe taro da addu,a ko? Anan yayi masu addu,a yayi masu sallam Alh yabashi kudi masu yawa, yace baze karba ba, Kawu yace a,a ai ba biyanka mukayi ba, kyauta ce yayi maka, anan ya amsa yayi masu godiya yatafi tare da Kawun Sameer. Alh, da Kawu da Mal. Garba suka fito suka nufi part din Alh, Kawu yace kaima Mal. Garba yakama kasamu kayi aure zama babu mata bakaramin matsala bane, sbd akwai lalurar ciwo kuma ga al,amuran rayuwa.
Murmushi yayi yace wlh Alh, ni tsoron ma matan nakeyi, dariya Kawu yayi yace kada kasamu damuwa, idan har kabani dama nizan zaba maka. Yace haba ai yanzu munzama daya, duk wacce kazaba mun nikuma na amince. Yace dama akwai wata diyar kanina da mijnta yarasu yabarta da yara 2 mace da namiji, yanzu haka tana gidana anan take zaune, idan har ka amince zaka aureta, amma kuma da yaranta zata zauna, to? Malam. Garba yace ai babu damuwa, yaro ai nakowa ne, wlh na amince, sede bansani ba ko ita. Kawu yace kamar yanda mukayi maganan nan da kai itama haka tacemun inzaba mata, nikuma gsky nayaba da kai, shiyasa kuma idan bazaka damuba, zanso kabani dama inmaka gyaran gidanka.
.
Alh, yace a,a kawu kabarni nizanyi wannan aiki, Kawu yace ai ni narigaka, dan haka kaima seka samu wani abun kayi mashi. Har kuka seda mal. Garba yayi, yace babu abinda zance maku se godiya. Alh, yace shikenan nikuma zanbude mashi babban shago wanda zerika kula dashi. Kawu yace yauwa, dan haka bawani daukar lokaci abun zeyi ba. Yace nagode sosai. Kawu yace kaima kashirya kilama tare za,ayi bikinka dashi. Alh, yayi dariya yace haba Kawu niyanzu ai nagama kallon wata mace ince inasonta, inama zan tsaya kallonsu. Kawu yace ato aini harna kallo maka. Dariya suka sa gaba daya.
Baba mairo se lallashin Zarah sukeyi, tace tashi muje kiyi wanka kici abinci, inaso kisaki ranki kada wata cuta tadameki, kidauka kamar ba,ayi komai ba, Jidda kuma addu,a yakamata kirika yimata. Haka suka kamata suka kaita bandaki dan tayi wanka.
.
Falak taja Jalila daki tana tayi mata tsiya, Jalila tace wlh ke muguwa ce, koma kimun sannu shine daga shigowata ina kallonki kinamun dariya, wai dan Allah ya akayi kika gane? Falak tace yo daga tafiyarki mana. Jalila tace nashiga 3 yanzo kowa yasan abinda yafaru dani, har Dady ko? Falak tana dariya tace ke kwantar da hankalinki ai babu wanda ya kula dake, kinsan hankalin kowa yana gurin Ummi. Jalila tace wash, harnaji dadi, Falak tace to Allah yasa nan da wata 9 musami yan biyu. Jalila ta kaimata duka tace wlh yan biyu su tsaya akanki, Falak tace toshikenan zamu gani ai. Baba Mairo tashigo tace to meza,a dafa ne agidan yau? Jalila tace a,a Baba kibari tunda ina gida indora, tace a,a Jalila daga ganinki bakijin dadi, kawai kibarshi kizauna kihuta. Dariya Falak tayi tace Baba kawai kidafa komai medadi, Jalila tajuya tana gungunai, Baba Mairo tace waini menace ne? Falak tace rabu da ita Baba, Jalila tadauko pillow tana dukanta dashi, baba mairo tayi waje tana dariya.
Bayan kwana 2 komai yafara dedeta, sede haryanzu Zarah takasa sakin jikinta agidan, duk da Baba Mairo tana kokarin ganin tana janta ajiki, gaba daya sunkwaso kayansu sun maido gidan, zamansu gwanin ban sha,awa Umman Sameer da Baba Mairo sune suke girkin gidan, Zarah kuwa ansama mata sanda hartafara amfani da ita, kuma kafarta tana kara samun sauki, sede aje ayi mata dressing, kuma jikinta yafara haske. Kullum tana cikin jan carbi tana istigifari, sallah akai akai takeyinta. Sameer yace ze kawo mata malamin daze rika kara mata karatu.
Bayan kwana 2, Kawun Alh, yazo, kai tsaye gurin Baba Mairo yawuce, waje suka fito, wata magana suka gamayi, sannan nga sunnufi bangaren Alh, Bayan sungama gaisawa Kawu yace dama nace maka zanzo bayan kwana 2 togashi nan nazo, kuma tare muke da Baba mairo dan ina ganin maganar zefi ayita tana nan.
Bawani abu bane akan maganar auren danayi maka ne, akwai wadda nagani kuma na yaba da hankalinta, bakowa bace se sirukarka, Zaro ido Alh, yayi yace bangane ba. Yace E sirukarka nace, wato mahaifiyar Sameer mijin Falak, tabbas tana da halin kirki inaso kayi hkr ka karbi zabin damuka yimaka nasan bazakayi dana sanin abun ba.
Shiru yayi Baba Mairo tace gsky Alh, nima ina maka sha,awar auren Halima, nina zauna da ita kuma kasan bazan zaba maka abinda ze cutar da kai ba. Amma me kace? Alh, ya sosa keya yana murmushi. Kawu yace shikenan nagane, kuma naji dadi daka amince, insha Allahu kasamu wadda zata share maka hawayenka, Allah yabada zaman lafiya, kuma insha Allahu nan da asabar mezuwa za,a hada dana mal. Garba, kaga tsohon sirukinka da kai zaku Angwance arana daya. Dariya Alh, yayi yace kai kawu. Godiya yayi masu.
.
Haka Baba mairo tasamu Umman Sameer da maganar, amma da kyar ta amince, dan cewa tayi tana jin kunyar Zarah, Baba Mairo tace bakomai zanyi mata bayani kuma nasan zata amince. Zarah wadda take jin duk abinda suke fada dan tazo zata shiga falonsu taji suna magana. Kuka kawai takeyi tana kara tsanar Asabe da kuma irin halinta, share idonta tayi, tayi sallama tashiga, bayan tazauna tace Baba Mairo kuyi hkr naji duk abinda kukace, nazo shigowa naji kuna magana amma wlh ba labe nayi maku ba. Umma kada kidamu babu komai, koma menene nina jama kaina, kuma zanfi son ace kece kika auri Alh, akan yaje waje yasamo wata, Allah yabaku zaman lafiya. Fita tayi tana kuka. Baba mairo tace tokinji abinda tace, Halima tace shikenan, Allah yazaba mana abinda yafi zama alkhairi.
Baba Mairo tace amin, dan haka kinga saura kwana 5 daurin auren kuma da an daura zaki tare, dan haka dole ingyaraki dan bawai tsufa kikayi ba, kawai rashin gyarane, murmushi tayi ta tashi tafita. Kowa yaji dadin wannan hadi da akayi, duk da Jalila bataji dadi ba, amma kuma taji dadin da akace Umma Alh, ze aura dan tasan halinta.
Haka akayita shirye shirye Umman Sameer cikin kwana 5 tayi kyau sosai tafito mace me kyau, dan komai yana son gyara. Sameer se tsokanarta yakeyi yana cewa dama Ummanshi tana da kyau amma batason yin kwalliya, itade sede tayi ta murmushi. Sameer yazo gurin baba Mairo shida saleem yace gsky Baba ana daura auren su Umma nima zandau matata mukoma gida, dan gsky abun da kunya. Saleem yace hakane Baba dan Allah kibarsu su koma. Tace to ai shikenan, dama ita nake tausaya mawa, tunda kace ku koma se kutafi amma wlh karika dawowa dawuri, yace angama Baba Mairota. Dariya tayi, sukayi mata godiya.
.
Ayau asabar aka daura auren Alh, Abba Bala da Halima kan sadaki dubu 30, se Mal. Garba da Samiyya suma sadaki dubu 30, kuma aranar aka kai kowa gidanta, Kawu yayi kokari na gyran gidan Mal. Garba, gashi Alh, yabude mashi babban provision store, haka aka kai amarya Samiyya sede ance yaranta sedaga baya za,a kawosu.
Halima ma Alh, yasa mata kaya adakin Zarah, ita kuma aka maida mata kayanta can part dinsu, akace idan su Falak suntafi seta koma dakin falak, aranar zarah ko abinci bata ciba, tana dakinta takasa fitowa, kuka kawai takeyi, seda tabama kowa tausayi, amma kuma ita tajama kanta.
Bayan kwana 2 da biki Sameer yadauki matarshi suka koma gidansu, wanda yakara shan gyara kamar wata sabuwar amarya, tayi mamaki sosai ganin irin gyran da yayima gidan, haka suka bude sabuwar rayuwa.
.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya cike da jindadi Alh, yanajin dadin zama da Halima, shikanshi yasan yanzu yana cikin kwanciyar hankali, har mantawa yakeyi dawata Zarah, dan koyaje gaida baba Mairo bata barin su hadu, shima baya nemanta, yana bama Baba Mairo girma sosai kamar ita ta haifeshi, kuma yahanata yimasu girki, yacika masu store da komai na abinci yace suyi iyakar nasu, bayaso ta wahala. Jikin Zarah kam ya warke, har ancire daurin kafar tazama dungulmi, sede haryanzu bata maida jikinta ba, dan kullum cikin kuka take, da tunani, sede kawai bakin datayi ne yaragu amma duk wanda yasanta ada yanzu baze iya gane taba. Malamin da Sameer yasama mata yana zuwa yana mata kari kullum, tamaida hankali sosai gurin koyon karatu.
Bayan shekara daya Jalila tahaifi yaronta me kyau aka samashi sunan Mahaifin Saleem, suna kiranshi da WALEED.Taro yayi kyau, yaran Falak sunyi wayau sosai, kamar sunfi shekara daya, kuma alokacin ne tafara laulayi, bayan suna sukaje asibiti, likita yace bakomai zata iya cigaba dabasu nono, amma tafara basu abinci, idan cikin yayi girma seta ciresu.
Halima ma tasamu ciki wanda haryayi girma, Alh, bakaramin farin ciki yayi ba, ganin zekara samun haihuwa. Zarah ma jiki yayi kyau, tafara dangana, har tafara kiba, kullum Baba mairo cikin kulawa da ita takeyi.
.
Ayau Halima ta tashi da nakuda sede har Alh, yafita bata fada mashi ba, sede takira Baba mairo, tana zuwa ta temaka mata, cikin lokaci kankani tahaifi danta namiji, Baba mairo tayi mashi wanka ta gyara gurin itama tayi wanka sannan aka kira Alh, akace yazo an haihu, lokacin dayazo yaga abinda aka haifar mashi seda yayi sujada yagodema Allah, har kwallan farin ciki seda yayi. Zarah ma tayi farin ciki, kuma tazo tayi mata barka, dan bata shigowa gidan idan Alh, yana nan.
Bayan kwana 2 da haihuwarta Samiyya matar Mal. Garba ma ta haifi mace, zarah bakaramin jin dadi tayi ba, haka tashirya ita dasu Jalila da Falak sukaje barka, Aranar sunan halima bakaramin kashe kudi Alh, yayi ba, seda ya yanka manyan raguna Biyar, taro yayi taro, yaro yaci sunan Alh, Abba, dan yace sunanshi zesama yaron za,a kirashi da KARAMEE. Bayan kwana 2 akayi sunan Samiyya, itama tasamu alkhairi sosai.
.
Cikin Falak yana wata 6 ta yaye yan biyu, aka kaisu gurin Baba mairo, haka suka cigaba darenon cikin Falak, harya kai lokacin haihuwarshi, da dare suka nufi asibiti, suna zuwa ta haifi yaronta me cike da lafiya, nan Sameer yarika kiran waya yana fadama mutane, bayan ta huta aka sallameta, suka dawo gida.
Ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Sameer Abdullahi ana kiranshi da SUDAIS, Falak ansha kyau sosai, dan takara zama babbar mace, haka taro yatashi cike da farin ciki.
Bayan shekara 2 an maido su Ameer da Ameerah gida, har ansasu makaranta, kowa yagansu yana sha,awarsu, domin suna matukar kama, gasu kyawawa, Jalila takara haihuwa tasamu mace, aka samata Zarah, suna kiranta da AMAL, shima Waleed an saka shi makaranta, hada Karami ma Alhn yasashi makaranta, dan itama Halima wani cikin gareta.
.
Haka rayuwar Zarah tacigaba da tafiya agidan Alh, kullum jinta takeyi kamar tana kurkutu, idan tayi tunanin komawa gidan ubanta setaga gara tayi zamanta, dan batada daki agidan, gashi de tana cin abinci mekyau, amma kullum kamar ana dibarta, Baba Mairo harta gaji da lalllashi tasa mata ido, shiyasa yanzu idan zatayi kuka seta shige daki sannan, amma duk da haka da baba Mairo ta ganta seta gane tayi kuka sede kawai ta kyaleta. Ga Son Alh, dayake hanata bacci, batason tana sonshi dayawa hakaba seda tarasashi, kuma taga yayi aure, wani lokacin har labewa takeyi idan yashigo tayi ta kallonshi. Zama tayi bisa gado tace Oni zarah, yanzu wai nice haka, lallai rayuwa ta koyamun hankali, Danasani nayi hkr da Hajjo munyi zaman mu Da yanzu nasan nazama wata babbar Hajiya.
Danasani banyima Alh, asiri ba, dayanzu ina nan da kafata lafiya lau, Danasani ban dauki shawarar Asabe ba, dayanzu bnshiga wannan kangin ba. Ya Allah kaji tausayina ka kawomun karshen wannan zaman danakeyi.
Allah kashirya duk masu irin halina ya Allah. Kwanciya tayi tana kuka me tsuma rai.
Nikam dariya nayi nace Zarah ada kenan, dama ai Danasani keya ce.
Wata bakar jaka Falak tadauko taciro wani abun hannu, tadawo
kusa da sameer tazauna, yana kallonta, tace Ameerah zonan, hannunta takama tasaka mata abun hannun, Ameerah tace lah, Momy ke kika siyomun? Kwallan idonta tagoge tace a,a Grandmother dinki ce tace inbaki, Ameerah tace toyaushe zan ganta? Sameer yajawota yace kin kusa ganinta kinji. Ameer yace Dady nito ina nawa? Tashi yayi yadauko wani karamin agogo yace kaima ga naka, yace toni wayace abani? Murmushi yayi yace kaima GrandFather dinka yace abaka, tashi sukayi suna tsalle, sukace Thank you Momy and Dady, waje suka nufa suna murna.
.
Jawo Falak yayi yace haba my dear kin manta kince bazaki kara kuka ba, tace dole inyi kuka my Luv.
Kawai natuna wani abune, wai yau nida ake kira AGOLAH, nice nake zaune da yarana har 3, suke kirana momy, agaskiya ina tausaya ma duk wata AGOLAH datake AGOLANCI awani gida, Allah yajikanku Umma da Abba, badan narasa kuba da babu wanda ze kirani da AGOLAH, har yau idan natuna sunan nan yanamun ciwo.
Sameer yace banaso kina rike abu aranki, kinmanta kince kinyafe masu? To kibar tuna abun, komade menene yanzu gashi kin daukaka, ayanzu kina sama da ita kuma ita tana kasa dake, kuma kinmata nisa, sosai. Yanzu albishirinki. Tace goro, yace hajjin bana tare za,ayi damu. Tsalle tayi ta rungumeshi tana murna tace wow amma gsky kayimun babban albishir, bansan ma dame zan gode maka ba. Dariya yayi yace ni ai nasan da abinda zaki godemun, kuma Falaka, kinfi haka agurina, kece farin cikina, kin bani kyautar yara har 3 kina kula dani yanda yakamata, nine zance bansan dame zan gode maki ba. Amma yanzu tashi mushiga ciki kibani goron albishir. Tashi tayi tana dariya tashige daki.
ALHAMDULILLAH
.
Ina mika godiyata ga Allah daya bani ikon kammala wannan littafi nawa mesuna AGOLAH.
Kuma ina mika sakon gaisuwa meyawa ga dukkanin masoyana nagode da irin kulawarku gareni. Allah yabar zumunci, abinda nafada da kuskure sekuyi hkr dan dan Adam ajizine.
Nasadaukar da wannan littafi ga mahaifina, ALLAH YAJI KANSHI DA RAHAMA AMIN, ALLAH YAJIKAN DUKKANIN MUSULMAI BAKI DAYA, MUKUMA IDAN TAMU TAZO ALLAH YABAMU GUZURIN TADDASU.
ALLAH YAKAREMU DAKA SHARRIN ZUCIYA YASA MUFI KARFINTA AMIN.
..
CALL or SMS
07066508080
.
Whatsapp
07066656752
0 comments:
Post a Comment