HADIN ALLAH Page 1-5
.
Na Shamsiya Salis(Auntyn Abul) .
Bismillahir rahmanirrahim Sanye take da wata kodaddiyar atamfa koriya xanin ta kasa arage yake an dinke da zare da allura,ga tiren tallar gyada akai tana ta faman taunar cingam, a haka har ta karasa dai dai wasu yammata saan nun ta, ajiye tiran gyadar tayi gefe tare da janyo takalminta Dan ta kara daure shi da leda, Dan taga ledar ta fara kwancewa, ba Wanda ta kula a cikin wanda ta tadda a wajan ba ta fi minti biyarba gyadar ta tafara karewa sosai mutane suke san gyadar ta, duk da kasancewar ta bata da tsafta hakan baya hana mutane siyan kayanta, musamman gyada da suka san ba ita take soyawa ba kuma a bawo take sannan a leda A hankali take magana wanda in ba kana kusa da ita ba baza ka taba jin me take cewa, mutum sai bakin jini tinda kika zo naga alama ko Biyar baki ba wlh in nice mai gyadar bazan kara samiki ba, a fusace yarinyar da take kusa da ita wuyan ta ta shakuma suka fara dambe, mutanan wajan ne suka taso da gudu dan su rabasu, " ke asabe me ta miki kawai dan neman masifa ki shakumi wuyan ta, wani dattijo ta ya rike hannun ta ke tambayqr ta, Wlh tsokanata take yi" Babu wani nan tin da *NUR* tazo wajan nan babu wanda ta kula taya zakice ta tsokaneki, wata yarinya dake talla a gefe ta fda, duk yadda asabe taso su fahimta suka ki fahimta amma suka ki fahimta saima rashin gaskiya da suke bata, suna hada ido da Nur tai mata gwalo, sannan ta cigaba da matsar kwallah, Cikin fushi asabe ta dau farantin gyadar ta tai gaba, bayan ta saida gyadar ta dau farantin ta tai hanyar gida Garin panisau gari ne mai rahama, ga kuma gonaki, sosai jamaar garin ke da sannar su Allah kuma ya azurta garin da mahauta, duk inda kika zaga zakiga ana saana, musamman wajan kofa sannan kuma da fada duk wuraran sanaa ne, kuma a wajan yammata garin ke zama dan saida abinci ko kuma wata sanaa tasu ta hannu, Mutanan panisau akwai zuciyar neman na kansu ko yaro karami ne zaka gansa da sanaarsa, sosai garin yake da niima Tana tafe tana waka har ta karasa gdan su, ko sallama Nur ba tayi ba ta shigo gda direct kitchen ta nufa wata roba ta dakko zama tayi a kasa ta fara cin abinci a nutse kadan taci abinci ta maida kwanon kitchen ta goge hannun da taci abinci dashi akanta, sannan ta shiga cikin dakin su Ku kasance da mu dan jin abinda labarin ya kunsa .
.
Umma Umma Umma kina Ina ne, Nur ta fda tana daga labulan dakinsu, " ban sani ba ke wai baza kiyi hankali ba ne , kullum girma fa kike karayi, dan iskanci uban me ya hana ki yi sallama kawai zaki hau kwallan kira kamar baki san inda nake ba, wlh Nur ki fita idona na rufe duk sanda na danke ki baza ki ji da dadi ba, turo baki Nur tayi ta dauke kanta kamar ba ita akewawa maganaba, au dan wulakanci ina miki magana kina turan baki sbda kin raina mutane koh, umma ta fada tana janyo ta " wayyo umma kiyi hakuri bazan kara ba dan Allah kar ki dake ni, tureta umma tayi ta mike dan fita " haka kawai dan an tsani mutum sai ana dukanshi, wlh ba dan nasan umma ce ta haifqn ba Allah sai nace kishiyar uwa ce, dan dai kawai muna kamane, dariya ta kusa subucewa umma amma ta dake ta juyo, Nur me kikace, hanjin cikin nur ne suka mada ummana ba magana fa nayiba haka nace ki soya gyada da yawa gobe dan yau ana ta nema sosai, Kuma ki kace baki magana ba, mantawa nai ummana Dariya kawai umma tai tayi waje tana rokon Allah ya shirya mata yarta Malam habu ne ya turo kekensa har cikin gda da sallama ya shigo gdan, umma sake zaune akan tabarma ta amsa masa sallamarsa, bayan ya jingine keken ya zauna kusa da umma, " sannu da zuwa malam" yauwa dije, ina nur ne, na aiketa gdan atine ta karbo mun kudi tin kan ai kiran mangariba kaga yanxu har kusan 8:30 amma bata dawo ba, umma ta fda tana daga labule dan ganin ko karfe nawa, " Allah dawo da ita lpya" Amin malam, umma ta fda tana mikewa dan dakkowa malam habu abincin sa Idan na zagayo idan na zagayo idan na zagayo ace tafi kanwar maza ni kanwar maza bazan ki maza ba ko yanxu ma daga gun mazan na........ Dukan da umma tai wa nur a bayane yasa kin karasa wakar, nur sau nawa zance ki daina shigo min gda da waka gashinan ko kallon gabanki ba kyayi kin zubar min da miya, Ganin abba a zaune yasa ta karasa da gudu ta fda kansa tana kuka, rarashinta dady ya fara yi hkri nur amma daga yau kar na kara ganin kin shigo gda bbu sallama, toh Abba, Yauwa yar gdan Abba tashi ki wanko hannun ki muci abinci, ba musu ta wanko hannunta suka fara cin abinci, baifi loma hudu nur tayi ba ta dauke hannunta daga abinci, " me zan gani yar gdan abba naga kin dauke hannunki" eh abba na koshi ne" dije ya kamata a nemowa nur maganin cin abinci bnsan meye masalar yarinyar nan ba kwata kwata bata san cin abinci, zan tqmbayi atine ko tasan India zaa samu maganin dan nima rashin cin abincin yarinyar nan na damuna, Honey pls ka hakura da tafiyar nan kaga fa yanxu kusan karfe uku gwanda ka bari sai gobe, sweat heart kiyi hakuri nan da panisau ai ba nisa bane dashi, kawai yau zuwa zanyi na ga kaka, insha Allahu gobe zan dawo da wuri, cikin shagwaba ta kara shigewa jikinsa, toh honey ka kula da kanka bnda kallon mata a hanya, kar ki damu sweat heart ai ke kadaice a raina bbu na biyun ki, dariyar jin dadi tayi ta rakoshi har mota tana daga masa hannu har ya tafi
.
'Cikin mintuna da basufi arba'in ba ya isa garin panisau, daidai bakin tasha yaxo zai wuce kenan wata yarinya ta taho aguje tabi gabansa ba shiri yaja burki ya tsaya, ita kuwa batama san tayi ba, tasha damara da wani dukukkunannan hijab, cikin zafin rai Nura ya fito ya bi yarinyar nan, shakota yayi ya riko gashin kanta, ta waigo ta sauri zata mai rashin kunya, ya dau hanu zai kwada mata mari ina yaji sam bazai iyaba yarinyar tamai kwarjini dayawa. Sakinta yayi tayi gefe tana huci, budar bakinta tace Allah ya isa mugu kawai, cak Nura ya tsaya yakasa aiwatar da komai, haka yayi ta binta da kallo har taje gidin wata bishiya ta dauki tiren gyadarta tayi gaba, sai da ta bace masa sannan ya shiga mota ya karasa gida. Salama alaikun kaka"a'a wanakeji kamar Nura badai kaine tafe da yamman nan ba, "Wlh nine kaka ta shimfida mai tabarma ya zauna, ruwa taje ta kawo mai mai sanyi cikin kwanon sha, ya karba yasha sannan suka gaisa, " ina kuma kishiyar tawa"tana lfy tace agaisheki"ina amsawa Aishatulle, kai kaka kidena batamun sunan mata, "toh mai mata sukayi dariya duka. Suna zaune sunata hira da kakartasa Nur tayi sallama ta shigo tasha damara a kugu, ga wata kwalliya data chaba adole wai tayi wanka kenan, ta gaishe da kaka, ta dinga hararar Nura dake zaune bai ma dago yaga ko wayeba yana ta danna wayarsa, kakata tace Nur me zaa baki?" kaka muka da daddawa da magi, sai lokacin ya dago suna hada ido ta gaa mai harara, kaka ta mike taje dakin ta daukowa Nur aikenta, Nur kuwa kaka na shiga daki tafara zagin Nura shi muma yarasa me yasa yakasa yiwa yarinyar komai kasancewarsa mutum ne wanda bayason raini, tace mugu kawai azzalumi Allah ya isana, dai dai nan kaka ta iso, "ke Nur menaji kina cewa, " a'a kaka waka nakeyi, ta amshi aikanta tayi waje. Sai jinjina sunan yake aransa Nur, tunda yani kaka ta fada shikenan ya ji sunan ya masa dadi kamar yadda yarinyar ta masa kwarnini, da tunani kalakala ya karasa hirarsa da kaka. Da magriba Alh Abubakar kakan Nura ya dawo daga kasuwa, sosai yaji dadiin ganin Nura saboda ya kwana biyu bai zoba, tare sukaci abincin dare sannan sukayi ta hira, karfe tara na dare Nura ya tafi dakinsa dake zaure ya kwanta don hutawa amma me tunanin Nur yaki barin zuciyarsa, dakyar bacci barawo ya sace shi. Misalin karfe sha biyu Nur ta fito sanye da wata bakar doguwar riga duk tasha faci, tana dauke da tiren gyadarta, dai dai kan dakalin gidan Kaka ta hango wannan bakon birnin aikuwa da hanzari ta karasa ta sake yimai tsiwa kamar yadda tamai jiya sannan ta fara tafiya, sai yace Nur taja ta tsaya amma bata juyo ba, cike da mamaki tace to ina yaji sunana"can sai ta tuna niya datane gun kaka, yace bani gyadar ta dari biyu, ta juyo ta aniye tiran tace mai ya diba goma goma ce, ya kwasshi kulli ashirin yabata mudinta ta dau tiranta tayi gaba. Misalin karfe biyar ya shirya sukayi sallama da kaka ya tafi, kafin ya wuce sai dayabi ta tasha ya sayi gyada gun Nur har yace tabar canjin dubu dayace dama, ta dari biyu kuma yasaya. Wlh sai naci ubanki uban waye ya baki kudi, nan ummanta tafara dukanta sai ga abbanta ya shigo, nan Nur ta nufi gunshi tana kuka, lfy dai ko, ina fa lfy malam yarinyar nan ta fara juyen gyada, nan abban ya tambayeta yadda akayi ta fada mai dake ita duk rashin kunyarta da rashin tsabtar ta bata karya.
.
A gajiye ya shiga gida, tun yana parking mota, Aisha ta fito tasha kwalliya sanye da wani less pink da stoch baki, yayi mata kyau sosai, da hanzari ta karasa gunsa"sannu da zuwa honey, ya dago habarta ya sumbaci goshinta sannu swt heart, nasameki lfy, "lfy lau sweet heart, yasu kaka?" Suna lfy sunce ma agaishe ki"ina amsawa, yana rungume da ita suka karasa falo, dakinsa ya nufa direct toilet ya shiga ya sakarwa kansa shower, tana hada mai abinci akan dinning. Daure da towel ya fito, daya kuma yana goge sumarsa ya zauna ya shafe jikinsa da mai, wadrobe ya bude zai dauki kayan sawa Aisha ta rungumesa ta baya, ya juyo da ita, suna kallon juna, sakarwa junansu murmushi sukayi, ya dauko kayan ta taimaka mai yasa kayan suka nufi dinning, ta zuba mai yadda zai ishe sa. Suna zaune a falo suna hira, Nura na zaune akan capet, inda Aisha take kan kujera, ya juyo yace af na manta, ashe nazo da gyada, da hanzari ya mike ya dauko key motarsa ya nufi waje, jim kadan sai gashi yadawo dauke da daurin gyada, da sauri Aisha ta karba, la!, tasoyu ce ashe sweetheart, kai kawai ya daga mata alamar eh, nan suka fara cin gyadar. Honey a ina kasamo gyada haka mai dadi?, "hmm kodai kaka ce ta baka, " a'a saya nayi gun wata yarinya NUR, Aisha najin sunan taji gabanta ya fadi, amma ta rasa dalili duk da tasan Nura bazai taba son yar kauye ba bare yar talla. Yanaji kinyi shiru?"a'a babu gyadar ce akwai dadi, nan yaji dadi anyaba gyadar Nur, anan ta tashi ta yi daki don tafara hamma.ai kuwa tana tafiya Nura ya fara tuna haduwarsu da Nur, kusan sai karfe sha biyu ya shiga daki, lokacin har tayi bacccinta. Nur kizo maza kije ki kaiwa kaka aikan nan sannan ki siyo mun kubewa, kai dan Allah badama mutun ya huta, dawa kikeyi Nur inace nikike zagi?, nifa badake nake ba tana tura baki ta amshi aikan. Nura ne ya fito sanye cikin kananan kaya, Aisha na zaune afalo misalin karfe tara na safe, da hanxari ta mike don taga alamar fita zaiyi, "Honey sai ina kuma?, ta tambaya atakaice, ba kalli inda take ba yace" panisau zani amma da yamma xan dawo, cikin rashin kuzari tace to baka karya ba, "hanu ya daga mata alamar baya bukata, shan gabansa tayi lfy kuwa honey?ba yadda nasa ba ganinka bane kodai na maka laifine, yayi murmushi ya rungumeta jikinsa, no sweet heart ba abinda kika mun yau koko da kosai nake shaawar sha shiyasa sainaje panisau xan karya, ta gamsu da jawabinsa tare sukaje parking space har ya tada mota tana daga mai hanu. Isar sa keda wuya ya samu kaka ta sauke kokon kuwa, dama yasan daidai lokacin da take karyawa, bayan sun gaigaisa da kakannin nasa ne, ya dubi kaka, " nikam akwai wata yarinya dana sayi gyada gunta ranar ko kin santa, gyadar me dadi, "kodai gyadar Nur ce domin duk garin nan gyadarsu tafi ta kowa dadi, inaga itace domin gyadar tana da dadi, kana sone?, " eh asayaomun ta dubu daya saboda Aisha ma tanaso.
.
Cikin mota nura ya Shiga ya dakko mata chocolate kwali uku, da murmushi ya karaso inda take " kanwata ga tsarabarko, zaro ido nur tayi kai yaya nura so kake ummana ta Zane ni tace waya bani, murmushi yayi kanwata Umman mu baza ta dake ki ba kinji, naki wayyan, sanda zaa dakeni ai baka sani ba, nur ta fda tana turo baki, sosai nur ta burge nura, zuwa yanxu dai ya tabbatarwa da zuciyarsa yana san nur san da bai taba yiwa wata mace ba " yaya kana ji ina ma magana kai shiru, jin shirun yayi yawa nur ta tabashi yaya magana nake, Sai da nur ta tabashi ya dawo daga duniyar tina nin da ya tafi, yi hakuri kanwata wani tina nin na tafi da ban, " ni dai na tafi kar ummana taga na dade, toh kanwata ki dauki chocolate din ko daya ce, ba musu ta dauka tai gaba ba tare da tajira taji me zai ce ba , tana tafiya ya Shiva gidan kaka " kaka akwai maganar da zamuyi da ke dan Allah" toh miji na ina jinka cikin nutsuwa nura ya fara magana , " kaka wata yarinya nake so a garin kuma wallahi da gaske auranta zanyi, kuma bansan abin ya dau lokaci sbda makaranta zan sata, Toh wace yarinya ce mai saa a garin nan da har ta rikita tina nin mijina, ta sashi zuwa garin nan duk sati" murmushi nura yayi ya fara magana " Nur nake so tin lokacin dana sata a idona naji ta shiga raina da farko na zaci tausayi take bani sai naga kuma ashe harda kaunarta, Sosai kaka taji dadin zancen nura, farin ciki ta nuna sosai, domin tana san nur sosai kuma zata so su hada zuria da gidan su malam habu sbda mutuncin su Nura da namiji tilo wajan mahaifansa Alhaji Abdullahi, da kuma mahaifiyarsa hajiya memunatu, yana da yaya mace guda daya Ummul kairi sai kuma kannansa biyu mata Fiddausi sai kanwarsu karama fatima itace wadda shekarunta basu wuce goma ba, asalin Alhaji Abdullahi haifafan panisau ne su Biyar ne wajan babarsu da babansu, Alhaji Abdullahi Dan kasuwa ne ya fara daga dako a kurmi had Allah ya daukakashi, har uban gidanshi ya bashi auran yarsa memuna sbda yadda yake da amana, ba yadda Alhaji Abdullahi baiyi da mahaifansa su dawo hotoro inda yake amma suka ki Malam habu asalin Dan garin panisau ne yana da mata data khadija amma dije ake ce mata, tin da sukai aure basu haihuba, har sun shire rai da haihuwa, Allah ya basu ya mace suka sa mata suna Nur sosai suke santa amma kuma hakan bai hana sun bata tarbiyya ba sai dai bata makarantar boko tana zuwa islamiyya har yanxu da take da shekara tara da haihuwa
.
*cigaban labari*
Nura bai ba ranar sai da ta tabbatar masa da cewa insha Allahu Zara shawo kan iyqyan Nur su yadda, sosai nura yaji dadi, Karfe tara na dare nura ya dawo gidansa da sallama ya shiga falon, Aisha sake zaune a kujera tana kallo ta amsa masa sallamarsa ciki ciki, kusa da ita ya zauna tare da janyota jikinsa, ture hannayansa tai ta canxa kujera, kusa da ita ya kara zama, zata tashi ya janyota ya matseta a jikinsa tare da tura bakinsa cikin NATA, saida sukai kusan minti goma a haka sannan ya dagota, sweat heart kiyi hakuri wallahi aiki ne yake min yawa yanxu vai kamata kina fushi Dani ba sbda kefa nake aikin nan, nura bai kyale Aisha va sai da ya tsarata sosai, ranar baccin farin ciki sukai sosai
.
Jikin Nur yayi zafi sosai, kaka ta jika maganin data karbo tabawa nur maganin sai shegen daci, dakyar ta iya hadiyewa. Nura yana fitowa yaga wani dan matashin yaro, "zo dan Allah in tambayeka, cikin ladabi yaron ya karaso kusa da Nura ya gaidasa, Nura ya amsa ya kuma ji dadin hakan, dan Allah ina ne gidansu Nur?ya tambaya yana kallon yaron, yaron yace bayan layine muje in kaika, godiya Nura ya dinga yiwa yaron, tare suka nufi bayan layi, adaidai kofar gidansu Nur yaron yace " ga gidan nan, Hanu Nura yasa a aljihu ya cire kudi ya mikawa yaron yace gashi ko nagode, yaron ya girgiza kai alamar bazai karba ba, dakyar Nura yasa yaron nan ya karbi kudin nan, yace dan Allah ka shiga kacewa kaka Nura ne yazo. Da sallama yaron ya shiga gidansu Nur bayan sun gaisa da ummanta, yace an aiko sane gun kaka, kaka dake daki tace zo gani nan, yace wai Nura yaxo, tace to kace ina zuwa yaron ya fita.
.
Nura yana tsaye sai ga mahaifin Nur ya dawo, ganin bakuwar fuska yasa shi yayi turus, cikin ladabi Nura ya gaida abban Nur sannan, yace lfy dai malam dai dai lokacin kaka ta fito, a'a sannu da dawowa malam, a'a kece agidan namu h nazo duba jikin Nur ne, toh, wannan Nura sunansa jikana ne, abban Nur ya fadada murmushinsa yace a"a bismilla shigo. Tare suka shiga gidan, tabarma umman Nur t shimfida mai, ya xauna ya gaida iyayen Nur cikin girmamawa sannan kaka ta shiga ta taso Nur wacce jikin yanxu da dan dama dama, tana ganin Yayan nata ta sake mai murmushi, wanda hakan shi kadai yasan abinda yaji. Kusa dashi ta zauna, tace ina wuni yayana, lfy lau kanwata ya jikin ki?, jiki da sauki yayana ina Aunty Aisha, tana lfy tace na gaida kanwata, ina amsawa, yaya ina alawa ta, yace tana nan dayawa ma nakawo miki, yanxu nazo ne in kaiki asibiti, iyayen Nur kuwa ttsayawa sukayi suna kallon ikon Allah, kaka kuwa hakan ya mata dadi, Abbab Nur yace dama Nur kin san shi ne?, kai ta daga alamar eh, shine yaban kudi ranar har umma ta dakeni, kuma shiyake sayan gyada sannan yake kawomun alewar birni, sosai ta burge Nura ya sunkuyar dakai, abba ya shiga godiya, kaka tace ba komai malam ai wannan ba komai bane. Da kaka da Nurane suka kai Nur asibiti, nan aka mata allurai aka bata magunguna, ya shiga da ita shoprite ya mata sayayya sosai harda kayan sawa sannan sukaje parks tadanyi wasa kadan kasancewar jikin da dan sauki. Sai magriba suka koma panisau, sosai iyayen Nur sun yaba da hankalin Nura kuma sun samai albark, Nura bai bar gidansu Nur ba sai kusan karfe goma na dare, haka dayazo da safe sai azahar ya tafi, yanxu kusan kullum gidan yake wuni, har sun saba da umma.
.
Fuskar nan ta ta a daure ta fito kamar wadda bata taba dariya ba, kusa da umma ta zauna, " umma gani ta fda tana turo baki, ni nace ina kiranki, kuma bakiga yayanki ba ne baki gaidashi ba, " ina wuni" nur ta fda tana murguda baki, " lpya lau" nura ya fda fuskarshi dauke da murmushi, Umma ta mike ta shiga daki, kusa da ita nura ya dawo, nur me ya faru kike fushi dani, idan laifi nayi kiyi hakuri, " au bakasan ma kayi laifin ba bayan ka gani a fada har Zan taho shine ka juya ka canxa hanya, sai a lokacin nura ya gane nur ta ganshi, rausayar da kansa yayi, kiyi hakuri kanwata, kinga da auntyn ki muke tare kuma tana da fda sosai in taga ina miki magana zata fara miki masifa, ni kuma ban san bacin ranki, turo baki nur tayi ba tare da tace komai ba, Baki hakura ba, ba dole na hakura ba, da kyar nur ta sakko suka fara hira sosai, ya dade a gidan sannan sukai sallama ya tafi, Kullum sai nura ya zo gaidasu su danyi hira ba sosai ba sannan ya taxi sbda gudun kar Aisha ta masa korafi Yau ta kama lahadi kuma yaune zasu koma gida Aisha ta azzazaleshi su tafi ita ta gaji ba yadda ya iya dole ya tafi ba dan ransa ya so ba ko sallama baima nur ba ya tafi, tinda nur ya tafi bai kara waiwaiyar panisau ba sbda ba yaso Aisha ta zargeshi ya fiso sai an tambayar masa auran ta sannan kowa ya sani, Yau satin nura biyu baizo panisau ba tin nur na damuwa har ta shire shi aranta, "Nur wai bazaki zo ki dau tallarba sai ranki ya baci koh, " umma yanxu zanxo so nake na dauraye jikina, au baki wanka ba, " umma ana wannan sanyi na yamma zanyi wanka, sbda kwaliyar jumaar ma da zanyi ne kawai yasa zan wanke jiki na, cikin bacin rai umma ta fito daman ta dora tukunyar sanwa, kwashe ruwan tayi sanan ta sirka, nur na kuka umma ta janyo ta yi mata wanka, sosai nur ta shiga rera kuka kamar wadda ake mata azaba, sanda aka gama mata wanka ta shige daki rai a bace, Jin kukan nur ya sashi saurin karasowa cikin gidan, cikin girmamawa ya gaidata ta amsa, " umma me ya sami nur nake jiyo kukan tin a waje" bari kawai nura yarinya sai shegiyar kazanta kullum a na nuna mata bata ganewa, Allah sa umma baki dakar min kanwa ba, a'a ban dake taba wanka kawai na mata shine take ta rero kukan nan, Bari na shiryata kar tamin ba dai dai ba toh umma bari naje na dawo, Ya fda yana mikewa, sosai umma ta gyara yarta ta tamata kwaliya, sannan ta dora mata talla tai waje Bayan sallar isha'i nura da kaka suka zo gidan su nur sun kwa ci saa Abba na nan tabarma umma ta shimfida musu suka zauna Daman malam habu jika nane yaga nur yace yana so shine yake so a tambayar masa izini idan ba wanda ya rigashi, yana santa kuma baya so abu yay tsayi sbda yana san sata makatanta, da kyar Abba da umma suka yarda sai da nura yay musu kuka sosai ba karamin tausayi ya basu ba hakan yasa suka yarda akan ya turo mahaifinsa ai zancen auran, washe gari tin safe ya tafi gida wannan karan ko haduwa basuyi ba " mlm kaga *hadin Allah* koh jibi yadda yaron nan yake san nur fatan mu dai Allah yasa tayi alfahari da auran da za a mata
.
da daddare nura yaje ya sami mahaifinsa a daki, cikin girmama ya gaidashi, bayan ya gaida shi, sai yace ahm baba daman sai yafara Sosa k'eya, daman me mahaifin yace, "um daman baba wata yarinya ce nagani danaje gidan kaka shine... Sai mahaifin nasa yayi murmushi yace, nura daman na dade ina jiran wannan ranar sai gashi allah yakawo ta, Allah yasa yar gidan mutunci ka samo, akwai wani abokina ma da naso ka auri yarsa amma tinda ka samo da kanka ba matsala fatana dai Allah yasa ka iya adalci tsakanin matan naka, Cikin jin dadi yace insha Allahu dady zan iya Allah yasa dady ya fda yana fadada dariyarsa " yanxu ya kukayi da iyayen yarinyar, dady ya fda yana kallon Dan nasa, dady munje ni da kaka neman ixini mahaifin nata yace na turo manya na, kuma dady ban san abin da tsayi sbda yarinya ce ina so ta fara makaranta sbda bata yi, " kar ka damu nura insha Allahu zuwa ranar lahadi tinda bani da aiki sai naje, idan naje zan nemi amini na a garin muje ya rakani neman auran nata, " toh dady na gode Allah ya kara girma, nura ya fda yana ficewa daga dakin " nura meke damunka ne naganka fuskarka cikin farin ciki kamar anma bushara da aljannah, wata mata datijuwa ta fda wadda ga dukkan alamu mahaifiyarsa ce " mumy bbu komai kawai dai aure nakesan karawa ne, " kai Alhamdulilah amma nura kayi tinani mai kyau, ai gwanda ka kara auran yau shekarar ku kusan biyar da Aisha ko watan bata bata tabayi ba bare musa ran jika, " mumy ni ba sbda haka zan kara aure ba kawai dan dai ina san yarinyar ne, kuma na fdawa dady yace lahadi zaije neman auren ta " kai amma naji dady, ai bnyi tinani dady zai yarda ba haka, a ina ka samo mana yarinyar yar gidan wace, mumy ta fda cikin jin dadi " mumy ba yar kowa bace hasalima yar kauye ce kuma karamace sanda naje panisau na ganta da fari na zaci tausayi take bani sai daga baya na gane ashe santa nake kuma....
.
Maganar da mahaifiyarsa ta fara ne yasa shi saurin dago kansa, Wallahi Allah nura baka isa ba dan wulakanci duk matan garin nan karasa wadda zaka so sai wata yar kauye jahila kaskantacjya, wadda da ita da kare basu da maraba a wajena, " haba mumy dan Allah mutum ce fah bai kamata kina mata haka ba, kar ki manta itama mutumce kamar kowa haba mumy, nura ya fda cikin Bacon rai, " inalilahi wainailaihir rajiuna na shiga uku ni Hindatu, nura tin kafin kayi auran har ka fara min rashin kunya mumy ta karashe maganar cikin kuka, Gaba daya jikin nura yay sanyi, ruko hanunta yay ya zaunar da ita a kujera, " haba mumy dan Allah ya kike so nayi so kike azabar Allah ta hauni, yaza ki dinga zubda hawaye sbda ni, Dan Allah ki duba girman Allah ki daina kuka" " nura tashi ka tafi gida dare yayi" dady ya fda ransa a bace, " dady mumy fa fushi takeyi dani, nura ya fda kamar zai yi kuka, " nace ka tashi ka tafi kafin ranka ya baci koh' Ba yadda nura ya iya dole ya tashi ya tafi " wallahi wallahi wallahi kinji na rantse sau uku ko hindatu mudum kika ziga yaron nan ya fasa auranta wallahi kema sai na sakeki, kuma ko nura baiyi tina nin auro yar asalinsa ba, ni zan aura masa" dady ya fda ransa a bace, mumy zatai magana ya daga mata hannu, bnsan jayayya, ya fda yana shigewa ciki, ba yadda ta iya dole ta hakura amma a ranta ita kadai tasan muguntar da ta shiryawa yarinyar Kamar yadda dady yayi alkawari haka kuwa ya cika, tin safe nura da dady suka kama hanyar panisau karfe tara suka isa garin panisau, Da sallama suka shiga gidan kaka, suka kwa ci saa kaka na tsakar gida, cikin girmama suka gaidata bayan tayi musu shimfida " baba gidan malam habu zani ko yana nan sai ya rakani nemowa nura auran yarinyar da ya gani, cikin mamaki kaka ta kallesa wane malam habu din bayan wajansa zaka neman auran , zaro ido dady yayi,baba kina nufin aminina malam habu yarsa nura yake so, eh, "Alhamdulilah amma naji dadi sosai nura dama ita ce yarinyar da nake fda ma zan aura maka, sosai yaji dadin lalai wannan shi ake kira *hadin Allah* Kuyi hakuri naso page din yafi haka amma kasancewar ina busy shiyasa banyi da yawa ba amma insha Allahu za muyi muku wanda yafi wannan insha Allah
.
KUNA TARE DA NI MU CI GABA?
0 comments:
Post a Comment