HADIN ALLAH 21-25
Cikin mamaki nura da mumy ke kallon driver da yake ta faman shigo da kayan nur a akwati,
" lalaima yarinyar nan watakan bata san gatse ba kenan" nur ya fda a ransa
" Hadi me zan gani haka wadannan kayan fah, kan yay magana Nur ta shigo mumy nawa, Nur wannan kayan ai sunyi yawa
" a'a mumy basuyi yawa ba, toh nur Allah ya tsare " Amin mum"
.
Washe da asuba Nur bata koma bacci ba daman batai wani baccin kirki ba,
Kara shirya kayanta tayi sannan ta fito ta Dora girki
A bangaran Aisha kuwa kaguwa tayi nura ya dawo taji dalilin kwasar kayan, amma tin tana duba agogo har ta daina ganin bashi da niyyar dawowa a haka bacci ya kwasheta
Tin da tai sallar asuba ta shiga kitchen ta hadawa nura abinci kala kala, bayan ta gama girki tayi gyaran daki sannan tai wanka, dakin nura ta wuce kai tsaye, da sallama ta shiga dakin, ya amsa mata ba yabo ba fallasa, swt hrt ina zuwa haka naga kana shiri da wuri, unguwa zani, ya fda a takaice, wayarsa ya dauka da mokulli yabi ta gefenta zai wuce, swt hrt bafa ka ci abinci ba kuma na gama, ya juyo a fusace zaiyi magana, sai kuma ya fasa, muje na ci dan sauri nake, murmushi tayi ta rike hannunsa har dining, bayan sun fara cin abinci, Aisha ta dago ta kalleshi, swt hrt wai ina Nur ne naga bata kwana a gidan kwana biyu kuma sai naga jiya tazo ta dibi kaya,
Wani bakin ciki ne ya tokareshi shiyasa kenan yau har dayi masa girki ta zaci sakin nur din yayi kenan, nura ya fda a zuciyarsa, a fili kuwa yace ban sani ba nima jiyan ai da kin tsayar da ita kinji inda zata, ya fda rai a bace tare da daukan key dinsa yay waje daman ba jin dadin girkin yake ba,
Duk suna zaune a falo suna jiransa dan har kayanta ta fito dasu, da sallama ya shigo mumy ta amsa masa, nur kuwa ko kallansa batayi ba bare yaci arzikin gaisuwa, mumy kan kyalesu tai dan ta san da kansu zasu shirya,
Hadi ne ya zo ya debi kayan yasa su a mota sannan suka fice,
Nur ki gaishe da umma kafin nazo ga kuma wannan kya basu ita da Abban naki,
Mumy ta fda tana mika mata wata katuwar leda, toh mumy an gode ta karba tana sawa a motar, murfin motar baya ta bude zata shiga,
Cikin bacin rai nura ya daka mata tsawa " uban waye drivern ki da zaki shiga baya,
" haba nura baka ga yarinya bace, da auta suna nan ma tare zasu tafi toh sun min yajin aiki nima, saura kana mata tsawa a hanya ma
" ke kuma ki fito ki koma gaba ban san rashin kunya, turo baki tayi sannan ta fito ta koma gaba yaja motar suka dau hanya
Tin da suka tafi ba wanda yay wa wani magana, ganin ta gaji da yin shiru yasa ta dakko wayarta da mumy ta siya mata jiya ta fara kallo da ita, a haka har suka karasa garin panisau mai albarka, gari mai niima garin da kowa yake son sa,
Yi hakuri sister Haima kar kiji ina koda garin mahaifata ce
Ihu nur ta Saki sanda ta ganta a kofa, wannan dalilin ne yasa nura sa burki bbu shiri
" ke meyasa baki da hankali nur sbda munzo zakinayi ma mutane ihu, turo baki tayi bata kulashi ba ganin bata da niyyar yin magana tasa shi jan motarsa sukai ciki,
" suna isa fada kowa ya bi su da kallo kuma ana yaba kyan yarinyar da ke gaban motar, a haka har suka shiga layin su, motar bata gama tsayawa ba nur ta fice da gudu
" ummana ummana ummana,
Kamar daga sama umma tajiyo muryar gudan jininta da sauri ta fito daga dakin dan ta tabbatar da ita dince ko gixon da ta sabayi mata nene
Allah ina rokonka da sunanyenka tsarkakaku guda dari bbu daya Allah ya bawa abul kair lpya Allah ya albarkaci rayuwarsa, Allah yasa ni auntynsa, mamansa da kuma duk wani alummar musulmai suyi alfahari da shi amin summa amin
.
Mutuwar tsaye umma tayi sanda taga yadda gudan jininta ta zama babba,
Rungumar da nur tayi wa umma ne ya katse mata tinaninta,
" ummana nayi misssin dinki alot,
Murmshi umma tayi dan ba sanin mene mssn tayi ba,
" nur kece kika girma haka,
" ummana nice ina Abba, kan umma tai magana nura ya shigo rike da karamar akwatin nura yara biyu kuma matasa na rike da sauran kayan
" yanxu nura da tare kuke kika kyaleshi da dibar kaya, sannu da zuwa nura umma ta fda fuskarta dauke da mirmushi kuma tana shimfida musu ta barma,
Bayan sun gagaisa umma ta gabatar musu da abinci da ruwa suka ci sannan suka dora hira sosai umma taji dadin yadda yarta ta ta koma
.
Bayan sallar laasar nur ta sake yin wanka ta shirya cikin wata dakakiyar doguwar riga ta shadda, tasa takalmi da jaka sai gyale kalar kayan, tsayawa fadar irin kyan da tayi bata lokaci, bayan ta gama shirinta ta fito ta tadda umma na shan inuwa,
Ummana bari na dan zaga zan iya kaiwa dare idan yayana ya dawo kice mashi na fita zaga gari,
" toh nur a dai kula, kai ummana yanzu fa na girma sosai, " ai naga alama kan, dariya nur tayi tana ficewa
Ajiyar zuciya umma tace in banda *Hadin Allah* nur da ban san ya rayuwarta zata kasance ba, Allah ina godema, Allah kara hada kansu,
" nur na fita makotansu ta zazagaya duk inda taje sai tayi bayani ake gane ta
Wani gida ta shiga da ke gab da wakeken dutsen panisau yana kallon ramin da kuma masallaci a kofar gidan da sallama ta shiga,
Wata mata ta amsa mata tare da mata shimfida,
Bayan sun gaisa matar tace baiwar Allah ban gane ki ba fah,
Murmushi nur tayi,
" yanxu baba magajiya baki ganeni ba, daman zuwa nai ki kwatanta min gidan Asabe naje mu gaisa, cikin mamaki matar tace a ina kika santa, " baba nur ce fah dazu nazo,
Sosai baba magajiya tai mamakinta,
Sannan ta kwatanta mata ta tafi,
Gidan dama ba boyayye bane a wajanta irin katan gidan nan ne da kowa da bangaransa,
Da sallama ta shiga ta kwa ci saa duk suna tsakar gida,
Wata kujera da ke gefe ta zauna tare da gaida su,
Sannunki asabe wallahi baki da kirki da auren ki ya tashi ko ki aika mini in ma fishi kike da ni ni yanxu nazo neman yafiya, cikin rashin fahimta matan gidan da kuma asabe ke kallonsu
" nifa baiwar Allah ban sanki ba, asabe ta fda cikin rashin fahimta
" mutum sai bakin jinin jaraba a kasa masa talla amma baa siya wlh in nice mai kasa miki tallan nan na dena kasa miki" amma ai baki manta mai fda miki wannan maganganun ba koh"
Nur ta fda tana kashe mata ido,
" in kinga na manta da mai fdan wadan nan zancen tah tabbas zan mata da zan mutu asabe ta fda tana kallon nur
" aikuwa rukayya (sunan asabe na gaskiya) kin manta kwa da zaki mutum dan kwa nur ce ni, ihu sosai asabe ta saki tana ruko nur yan gidan ma sakin baki sukai suna mamaki, dakin asabe suka nufa, sosai suka sha hira duk da mafi yawan maganar nur turanci ce yafiyar asabe ta nema sannan da zata tafi ta bata kyautar dubu goma, asabe sbda murna har kuka tayi, sukayi akan gobe da safe asabe zata xo gidan umma suje gidan ladidi sa sauran kawayensu,
Tana barin gidan asabe ba inda ta wuce sai gidan kaka,
Lkcin kaka na girkin abincin dare dan an kusa mangariba
" kaka wai umma tace ki bata dadawar hamsin da goran ashirin, nur ta fda tana turo baki a gaban kaka
Dariya kaka tayi " jairar banza iskancin da kika tina kenan, murmushi nur tayi tare da rungumo kaka ta baya, a nan suka zauna suka fara hirar yaushe gamo har akai ishai ta ci abinci taiyiwa kaka sallama
Karon da nur taji tayi da mutum a sorone yasa kwala ihu
.
Tsawar da taji an daka mata shi ya dawo da ita daga hayyacinta, ke! Bakya ganine kina buge mutane?, jin muryar Nura yasa ta danyi ajiyar zuciya, kokarin janye jikinta takeyi ya kankame ta ajikinsa, suna tsaye ahaka cikin soron, takun tafiya suka ji yayi saurin saketa.
Ficewq tayi daga gidan, gidansu ta nufa, umma tana kwashe tuwo Nur ta shiga da sallama, ganin Nur yasa umma yin turus ke!,lfy kika dawo? Ina mijin naki?, turo baki Nur tayi tace yana gidan kaka, kan ta karasa magana tajiyo muryar abbanta, "maza ki kama hanya ki koma gun mijinki wannan ai sakarcin banxa ne, " haba abba nifa hutu nazo, hutun uwarki bace mun dagani cewar abban, da hanzari ta fice, tana tafiya tana hawaye.
Sake karo tayi da mutum cikin hanzari ta dago jin kamshin turaren Nura ya tabbatar mata shine, toh ina zaije ta tambayi kanta, Kanwata ya ina kuma zaki?, " abbane yace sai dai naxo gunka mu kwana tare bayan nikuma hutu naxo, taso bashi dariya amma ya gimtse dariyar yace"kanwata toh meyasa bakice musu ni nace ki kwana can ba, na fada musu abba yace ban isa ba, wani dadi yaji rike hanunta yayi suka juya gidan kaka.
.
Sai karfe goma Nur ta tashi daga inda suke hira ta nufi dakin kaka, ai kuwa kaka tayi maxa tace"maza fitomun zokibi mijinki dakin shi, turo baki tayi ta fara bubbuga kafa tana kunkuni ita ba inda xata, Nura kam ko ci kanki baice musu ba ya mike ma yayiwa kaka sai da safe ya tafi daki, kaka ma ta mike, tayi nata dakin, nur kuwa na tsaye abin duniya ya isheta, ta rssa nayi dankwalinta ta shimfida kan barandar inna ta kwanta, amma sam ta kasa bacci.
Nura yana daki shiru shiru ba Nur ba alamunta, har bacci ya fara daukansa, mikewa yayi ya fito hango Nur yayi kwance akan baranda cikin hanzari ya karasa, Nur ya fada, bata tashi ba bare ta amsa, idonta arufe kamar me bacci, ya sake kiranta Nur, nan ma shiru sai daya sake kiranta akaro na uku sannan ta bude ido, ransa ya gama baci, cikin bacin rai yace" tashi mu tafi daki, ganin yanayinsa yasa ta mike ba musu, dakin ta shiga kan kujera ta xauna, anan ya taradda ita ya haye gado abinsa, bai kara bi ta kanta ba.
Washegari tun kafin Nur ta tashi ya shirya yaje yayiwa su umma sallama ya bar garin, ransa duk a jagule.
Nur lokacin data farka ta ganta kwance kan kujera, ta mike tayi salla sannan ta fita dakin kaka ta wuce taje ta gaidata, bata tambayeta Nura ba, itama kakan bata ce gashi ba haka tayi wanka ta nufi gidansu.
.
Tun ransa nura yabar panisau bai kara waiwayar garin ba kimanin kwana ashirin da shida kenan, Nur kam duk tabi ta damu ta dena walwala kuma sam taki fadawa kowa halin datake ciki, haka abba yasa ta fara shirin komawa, tace ai sai yayanta yazo, nan abba ya rufe ta da fada akan maxa ta hada kayanta jibi xata bar gari.
Hakan kuwa akayi ranar da xata tafi sai kuka takeyi, suna zaune da iyayen suna mata fada, driver yaxo daukarta, nan ta fito suka dau hanya.
Direct gidan mummy aka wuce da ita, tarba kam tasha ta gun sirikanta.
.
Nur tana zaune falon mummy tana kallo Nura ya shigo da sallama, ta amsa mai juyawa yayi gun da take ya watsa mata harar yayi gaba abinsa, murmushi kawai tayi, dakin mummy ya nufa da sallama ya shiga, ina kwana mummy"lfy lau ya Aisha take, lfy lau tana gaisheki, mummykam tajine amma tasan sam Aisha bazata ce agaidata ba, nan suka tattauna abinda ya kawo shi sannan ya fito, daidai coridor suka hadu da Nur sannu kawai tace mai tayi dakin mummy, shiko ya kuma cika fam yayi waje.
Tunda ga ranar Nur bata sake sa Nura a idonta ba, haka ko yaushe xaixo bata sani sai dai taji yaxo, sosai abun ke damunta amma bata da wata mafita data wuce hakuri.
*bayan kwana biyar*
.
Nur tana son tafiya taje ta zaga gari, dakin mummy taje ta zauna, tayi shiru mummy tace"lfy kuwa yar mummy kikayi shiru koda damuwane?, kai Nur ta dagawa Mummy, sannan tace mummy dama ina so nadan fita na zaga garine, murmushi mummy tayi tace yo banda abinki ai mijinki xaki tambaya, inya barki shi kenan, maza kirasa awaya.
MiMikewa Nur tayi ta nufi dakinta, tagumi ta zuba, ta rasa ya zatayi tasan da kyar yayanta zai barta fitan nan, mika hanu tayi ta dauko wayarta akan bedsite, dialing number Nura tayi cikin sa'a kuwa ya shiga sai dai ba'a daga ba, ta kira kysan sau uku ba a dauka ba mayar da wayar tayi, can kusan minti talatin ta ji wayar na ruri, hanu takai ta dauko wayar, karawa tayi akunne tare dayin sallama.
Hello yayana antashi lfy, lfy lau ya kuke yasu mummy"kowa lfy, yayana dan Allah inaso ne in dan fita xaga gari shine mummy tace na fada maka, shiru yayi yana wani nazari, har Nur tace hello yayana ko baka jina ne, gyaran murya yayi yace ina jinki, ba yau ba sai wani lokaci kawai ya katse wayar, bin wayar Nur tayi da kallo tana mamakin Yayan nata, toh meta mishi haka da zafi daxai sa ya tsane ta haka, haka ta wuni adaki jiki duk ba kwari, taki fadawa mummy gaskiya yadda sukayi.
*3 weeks later*
Nur ce durkushe sai sheka amai rake, cikin hanxari mummy ta taimaka mata ta gyarata suka nufi asibiti, a mota ma sai aman takeyi, waya mummy ta dauka ta bugawa Nura, a rude yace gani nan xuwa.
Minti kusan talatin da isar su har anbasu gado Nura ya iso, gani mummy na safa da marwa yasa jikinsa yayi sanyi, ganin Nura yasa tayi gunsa da sauri, lfy mummy? Ya tambaya kwantae da hankalinka Nura xata warware laulayine, suna tsaye sai ga dr ya bukaci ganawa da mijin Nur cikin hanxari Nura ya bishi office.
Gaskiya tana tsananin bukatar kulawa, kuma ya kamata ta rage yawan damuwa don karya haifar mata da ciwon hawan jini domin yanxy ma jininta ya fara hawa kasan mai ciki, dafe kai Nura yayi yana sauraron likitan nan, godiya ya mai sannan ya fita.
Dakin da Nur take ya nufa, tana kwance tana bacci mummy na zaune kusa da gadon da Nur take, sosai tabashi tausayi guri ya nema ya zauna yana ta karanto addou i gareta.

Ku kasance tare damu anjima .
Allah ubangiji ka karawa sis na lfy, shamsiya abokiyar aikina(antyn abul), amin ya Allah.
0 comments:
Post a Comment