MATAR ALI Page 41-50 (The end)
.
.
Shiru-shiru yaga Saude ta kawu ruwa bai ga ku 'kiyarta ba,ga kishin ruwa yana ji,ana cikin wannan hali ne sai ga Yayan *_DEJI_* ya shigo gidan,sa'bi da fatanya a kad'ar shi, yayi sallama daga can d'akin Malam Audu ya amsa yayi kiran shi.
Yace"bani ruwa mai sanyi a tulu insha"
"Inna bata nan ne?"
Yake tambaya yayi hanyar d'akin Saude ya d'auku kofi ya kaima Malam Audu ruwa,turus yayi da ya iske Saude zaune saman tabarma tana daman fura.
Yace "nama d'auka bakya nan ne Baffa yace in kawo mashi ruwa"
.
Banza tayi dashi ta cigaba da dama furarta,amman cikin zuciyarta tana jin ba dadi yanda take ma Malam Audu haka,duk da a ciwarta shiya d'aukar ma kanshi, kuma ta kudurta cewa bata ga ranar barin wannan rigima ba har sai sanda ya maidu mata d'iyarta gida.
.
Banza tayi dashi ta cigaba da dama furarta,amman cikin zuciyarta tana jin ba dadi yanda take ma Malam Audu haka,duk da a ciwarta shiya d'aukar ma kanshi, kuma ta kudurta cewa bata ga ranar barin wannan rigima ba har sai sanda ya maidu mata d'iyarta gida.
Tsawa ta daka mashi tace"zaka tashi ka kaima Malam ruwa ku kuwa,ka nime waji ka zauna"
Tashi yayi yana kara mamakin canjin da yake gani a gidan tun bayan auran 'Kanwarshi *_DEJI_* abubuwa da yawa sun sauya ciki hadda kuda yaushi Innarshi tana cikin bacin rai da kuka, kuma ta daina fira da Baffan shi hatta abinci sai dai ya d'auka ku kuma ta aika shi ya kai mashi.
.
Mud'a ya d'auka ta silba inda ya ga tana dibar mashi ruwa ya cika ya saka marfi ya d'auka ya kai mashi turakar shi,amsa yayi yasha yace"da fatan yau ka gama idashin nomar nan?"
.
Mud'a ya d'auka ta silba inda ya ga tana dibar mashi ruwa ya cika ya saka marfi ya d'auka ya kai mashi turakar shi,amsa yayi yasha yace"da fatan yau ka gama idashin nomar nan?"
"Eh na gama Baffa,yaushi za'a zuba takin?"
"Muna iya bari kamar nan da kwana ukku haka ku hud'u ko?"
"Eh to Allah ya kaimu"
"Ameen,idan ka gama hutawa zan aiki ka gidan Alhaji Iro(mahaifin Saude kinan)"
.
"To Baffa,ya zanci mashi saboda daga masallaci in nayi sallah sai in wuce"
.
"To Baffa,ya zanci mashi saboda daga masallaci in nayi sallah sai in wuce"
"Kaci zanzo in same shi bayan sallar isha'e"
"To Baffa,bari in kawo maka furar"
"Babu damuwa,ngd Allah yayi maku albarka,yasa alkairi a rayuwarku"
Har cikin ranshi yaki jindad'i addu'ar mahaifinshi gari su shida 'yar uwarshi,ya Inna take tunanin Baffa zai iya saida *_DEJI_* zai samu lokaci su zauna yayi mata bayanin yanda abin yaki, kuma mutumin da Baffa ya ba d'an shi Auran *_DEJI_* mutumin kirki ne yana da alheri sosai da karrama mutane.
Tashi yayi ya kuma dakin Saude ya tsaya yace"ina furar Baffan in kai mashi"
Kwarya ta mika mashi sannan ta tashi ta haye gado tana jin ranta babu dadi.
Bayan ya kaima Malam Audu furan ya kuma d'akin saude ya zuba tashi yasha ya kushi sannan ya shiga dakin shi ya cire kayan da yaje gona dasu ya watsa ruwa, sannan yasan ya masu haske sosai, yana da tasafta matuka,kuda yau shi zaka ganshi cikin tsafta gwanin ban sha'awa,alwala yayi sannan ya ji bakin 'kufar Malam Audu yace"Baffa sai ka tahu nayi gaba"
.
"Nima ganinan bayanka ruwa kawai zan watsa in tahu,insha Allahu"
.
"Nima ganinan bayanka ruwa kawai zan watsa in tahu,insha Allahu"
Masallaci Jauro ya nufa shikuma Malam Audu ya dibe ruwa yayi hanyar bayan daki da zummar yayi wanka,shima yayi shirin masallaci.
Ita ma dai Saude buta ta d'auka ta zagaya bayan wani d'aki tayi tsarki ta dawo tayi alwala ta shige daki domin gabatar da sallah.
.
**************
.
**************
*_DEJI_* ta kasa zauni ta kasa tsayi tun sanda ta ankara da katubarar da *_MUNNERA_* ta ingiza ta tayi ba tari da tunanin mai zaiji ya dawo ba,kuma a bayyane yake cewa ranshi ya baci matu'ka,lallai bazata zauna gidan nan yazo ya samita ba, kuka ta saka da ta tuna irin mugun bugun da taga ya gama yima *_MUNAYYA_*, hadda fitar mata da jini duk ilahirin jikinta rawa yake,da sauri ta isa bakin _save_ dinta ta fiddo iya adadin kayan da zasu ishita, ta kuma bakin gado ta dauki filo ta fidda shi cikin gidan shi ta d'auku ta dinga cusa kayan ta ciki har sai da ya cika ta kulle bakin shi, gyalanta ta d'aura saman kugu sannan ta 'kara 'karima dakin kallo tana kuka kamar wadda aka kura,cikin sand'a take tafiya saboda batasan kuwa yasan tana niyyar barin gidan,Allah ya taimakita bata hadu da kuwa ba a cikin falon,kufa ta bud'e a hankali ta tassama main gate din gidan, tun kafin ta idasa karasawa taji ana _horn_ bata kawo kumai ba ta cigaba da dusar bakin gate din da sauri Lawai buzu ya bude gate din gaba d'aya mota ta shigo, *_DEJI_* tsayi tayi tana kallan motar tama manta da abinda ta kudurta a zuciyarta na barin gidan,bata ankara ba sai ganin *_ALI_* tayi da *_OMMAR_* sun fito cikin motar da sauri tayi baya ta buya bayan wani gini,ta makara dan *_OMMAR_* ya riga ya ganta,da sauri ya mika ma *_ALI_* keys din yace _"get in,am on may way"_
Baki *_ALI_* ya ta'ba ya nufi kofar da zata sada shi da cikin gidan, *_OMMAR_* kuma ya iske *_DEJI_* ta dura hannu aka tana kuka mara sauti.
Cikin mamaki *_OMMAR_* yake kallanta yace"lafiya ,ina zaki da kullin kaya haka?"
.
Ajiyar zuciya tayi da ta ga *_OMMAR_* ne tace"dan girman Allah ka rufa mani asiri ka maidani garinmu kada nima yayi mani irin bugun da yayi mata,a gidan mu Baffana bai ta'ba buguna ba,haka ma Innata nasan mutuwa zanyi kada aima Innata asara ta"
.
Ajiyar zuciya tayi da ta ga *_OMMAR_* ne tace"dan girman Allah ka rufa mani asiri ka maidani garinmu kada nima yayi mani irin bugun da yayi mata,a gidan mu Baffana bai ta'ba buguna ba,haka ma Innata nasan mutuwa zanyi kada aima Innata asara ta"
Hannuwan *_OMMAR_* ta kama tace"mu tafi kafin ya fito ya kama ne"
Janshi ta farayi yace"ki tsaya mana babu fa abinda zai maki dan kinga ya buge *_MUNAYYA_* laifi ta mashi ki kuma baki mashi laifi ba"
"Na mashi mana tunda na kai zanin gado ya wanki dan Allah mu tafi ka maidani"
"Kwantar da hankalinki bafa zai daki ki ba,da zai bugeki tun sanda kika kai zai daki ki ai"
Dariya ta saki tace"eh kuma fa haka ne"
"Yauwa to kin gani,To mu shiga babu abinda zai maki"
Hanya ta kama ta shiga gidan da kullin kayanta a bisa kai,shi kuma yana bayanta tana shiga sukayi ido hud'u da *_ALI_* da yake kwanci bisa duguwar kujira,ido ya zuba mata yana kare mata kallo ji yayi zuciyar shi na tashi dakyar ya iya cewa.
"ke daga gidan uban wa kike,kuma da izinin wa kika fita?"
*******
"Ja'iri kawai,na kusa nima nayi maka aure, ai tunda baka sanshi, yaro kamar dan nasara."
"Haba Alhaji, nifa kila sai nayi karatun boko sannan zanyi aure."
.
Shigowar Karime mahaifiyar Saude d'akin ta katse mashi magana, ta hanyar cewa "Allah ya kyauta, muga wani cikin ahalinmu yana karatun yahudawa."
.
Shigowar Karime mahaifiyar Saude d'akin ta katse mashi magana, ta hanyar cewa "Allah ya kyauta, muga wani cikin ahalinmu yana karatun yahudawa."
Dariya jauro ya k'yalk'yale da ita yace "hooo Inna, ai ba yahudawa ke wannan karatun ba, shifa karatun yana kara wayarma damu makiyaya kai, da sauran masu zama a cikin kauye. Sannan kuma a kauda jahilci."
"Kai ar, yiman shiru ma da wannan maganar."
"To nayi shiru Inna, amman nima ku daina maganar auran nan kawai, dan har yanzo akwai yarinta a tare dani, dukka fa shikarata 20."
Alhaji yace "Ai kuwa, ni har na zab'o maka mata ma."
"Ehhm na zauna kuna ta tsokanata, ban fad'i sak'on da aka aiko ni ba."
"To, wani sako aka aiko ka, ka zauna kana mana surutu kai da duk sanda kazo baka rasa abin tsokana."
Ya fada yana rankwashin kanshi.
Ya fada yana rankwashin kanshi.
" uch Alhaji zaka fasa mani kai in rasa mai aurena, da fasashshen kai."
"Karime tace "Ai gwamma ka fasa kan Alhaji, tunda bai son aure boko yake so." ta fad'a tana dariya.
"Yi maza fadi aiken da aka yi maka mana."
"Baffa ne yace, idan anyi sallar isha'i yana nan zuwa wajanka kayi jirànshi."
"Lafiya dai ko?"
"Wannan sai ka bari sai yazo kun tattauna tukunna."
"To ja'iri maza tashi ka kama gabanka."
Tashi yayi yana dariya yace "na tafi tsohu mai ran k'arfi."
.
Daga karime har Alhaji suka dinga dariya, a duk cikin jikokinsu jauro yafi soyuwa a cikin zuciyarsu, saboda ya iya girmama na gaba gashi, farat-farat da kowa ga kamun kai da tsantsan da rayuwa, yaro mai halin manya, da yawa daga cikin dattawan 'kauyan ke fad'a mashi,babban abinda ke burge mutane da yawa dashi, shine yana da tausayi da hakuri, da wuya kaji an rabashi fada da wani, tun yana yaro ballantana yanzu da ya kara zama mutum sosai.
Yan matan kauyan basu da abin so sama da jauro, amman shi ina babu wannan maganar a rayuwarshi.
.
Daga karime har Alhaji suka dinga dariya, a duk cikin jikokinsu jauro yafi soyuwa a cikin zuciyarsu, saboda ya iya girmama na gaba gashi, farat-farat da kowa ga kamun kai da tsantsan da rayuwa, yaro mai halin manya, da yawa daga cikin dattawan 'kauyan ke fad'a mashi,babban abinda ke burge mutane da yawa dashi, shine yana da tausayi da hakuri, da wuya kaji an rabashi fada da wani, tun yana yaro ballantana yanzu da ya kara zama mutum sosai.
Yan matan kauyan basu da abin so sama da jauro, amman shi ina babu wannan maganar a rayuwarshi.
Bayan ya koma gida ya shaida ma Baffanshi ya aiwatar da aikin da yayi mashi, sannan ya dauko jikkar makarantar arabinshi ya fita kofar gida domin telawa, da dan buzunshi rik'e ga hannu.
Daga masallaci Malam Audu ya zarce gidan surukinshi, domin tattaunawa game da lamarin Saude, tun yana hakuri har dai yaga dacewar ya zauna da manyanta.
Keken shi ya jingeni jikin bangon gidan, sannan ya kira wani yaro, bayan yazo ya durkusa har kasa yace "ina wuni Baban Jauro?"
"Lafiya lau" ya fada yana shafa kan yaran, yace"yi man sallama da Alhaji dan Allah."
"To, yana ciki kuwa yanzu ya fito daga masallaci."
"To maza kace ana sallama."
Da gudu yaran ya shiga gidan Alhaji, minti biyu tsakani, sai gashi ya dawo yace "yace yana zuwa."
"To babu damuwa nagode."
Minti ukku tsakani sai ga Alhaji Iro ya fito, tun kafin ya idasa k'arasowa, Malam Audu ya cimma shi har kasa ya duka yana gaida shi, cikin farin ciki da annashuwa ya amsa,bayan nan yace "bismilla mu shiga daga ciki."
A kunyace yace "To Alhaji."
Bayan sun shiga turakar Alhaji Iro, kira ya kwalama yarinya daya daga cikin gidan, bayan tazo yace tayi mashi magana da Karime (mahaifiyar Saude), bayan tazo suka gaisa da surukinta, sannan ta koma. Tayo aike da ruwa masu sanyi cikin kofin silba.
Bayan sun 'kara gaisawa, da fira wadda ta shafe yau da kullum da kuma noma da kiwo ,sai Alhaji Iro yace ina fatan dai lafiya ko?mai ke tafe da kai?"
"Alhaji game da maganar Saude ne, nayi iya bakin k'ok'arina mu zauna lafiya amman abin yaci tura."
Cikin mamaki yake tambaya "Lafiya? mai ke faruwa tsakaninku da har ka kasa maganin abin?"
"Game da maganar auran DEJI ne"
"Me auran yayi?"
"Tun sanda akai auran Saude take tsoru da halayan da ba nata ba, to sai nai mata uzuri da abubuwa da dama a tunanina zata sauko, bayan ta daina fushi, to abu ya gagara sai ma cigaba da take."
"Ban fahimci inda maganar ka ta dusa ba ,ka fahimtar dani yanda zan gane mana."
"Ai kasan wannan Alhajin wanda yake da babbar gonar nan, ta kusa da yankinka."
"To to to na gane, Alhaji Ahmadu ko"
"Eh,to makwafcina ne, a gonata ta kusa da rafi, muna abun arziki dashi, sosai yana da mutunci da dattako, to DEJI takan kawo mana abinci lokaci-lokaci, to ranar nan sai yace mani yana san inba danshi auran DEJI, duba da nagartatun halayanshe sai na amince mashi, akan cewa duk sanda bukatar hakan ta tasu, zai man magana kamar dai yanda nazo na fada maka, watanni goma da suka wuce, to shine bayan wata bakwai yake fada mani cewa wannan magana da mukayi kwanakin baya to yana da bukatar DEJI yanzu, babu gaddama na amince mashi duba da daman anyi maganar, shine aka fara shirin biki kamar yanda kasan komai."
"Muje, ina sauraranka."
,
"To shine tace an saida mata da d'iya, har ya kaiga ta hana kanta sukune kullum kuka,duk wanda ta gani ko yazo za tace na saida mata da d'iya domin inyi kudi,duk wannan baya damuna irin hatta abinci sai dai inji in d'auka da kaina, ku in Jauro na nan ya kawo mani,kufa magana batayi mani"
"To shine tace an saida mata da d'iya, har ya kaiga ta hana kanta sukune kullum kuka,duk wanda ta gani ko yazo za tace na saida mata da d'iya domin inyi kudi,duk wannan baya damuna irin hatta abinci sai dai inji in d'auka da kaina, ku in Jauro na nan ya kawo mani,kufa magana batayi mani"
"Gaba take da mijin auranta kinan?ya fad'a ranshi na matukar bace da abinda ake fada mashi d'iyar shi wadda ya haifa da ciki shi tayi.
" nayi kukarin inga mun dai-dai ta sannan kuma in fahimtar da ita halaccin da nayi mashi amman taki yadda bata ma ku saurare na,shine nace bari inzo infad'a adan tsawatar mata"
"Lallai kayi namiji kukari tsawan wata biyu kana fama da tabarar Saude Malam Audu,lallai ina alfahari da kai a natsayin surukina,nagode sosai"
Cikin girmama wa yace"Nagode Alhaji"
"Kada ka damu,zan dauke mataki sosai, Kuma kayi hakuri"
Godiya yayi mai yawa sannan suka tashi ya rako shi kofar gida,bayan yayi sallama da mutanan gidan.
Gida ya kuma ya iske har ta rufe kofarta,sabanin da da duk inda yaji zai iske tana jiranshi,idan ma har baccin ya kamata zai iske ta a dakin shi tana bacci, girgiza kai yayi shima yayi alwala ya shiga dakin shi domin gabatar da nafila wadda daman saban shi ce hakan.
Bayan gari ya waye wajajan karfi 8:00am akayi sallama aka shigo a kace ana sallama da Saude,daga daki ta fito tace"ni kuma?"
Yaran yace"eh Alhaji Iro ne baban Atine"
.
Anan ta gane mahaifinta ne"to,kaci,ganinan zuwa" da sauri ta kuma gaban ta na fad'uwa tana cikin matsanancin tsoro.
.
Anan ta gane mahaifinta ne"to,kaci,ganinan zuwa" da sauri ta kuma gaban ta na fad'uwa tana cikin matsanancin tsoro.
Tabarma ta dauko da sauri ta nufi kufar soro warwarita tayi tana niyyar shimfid'awa da sauri Alhaji Iro(mahaifinta)yace"kul dinki da shimfid'a mani tabarma da zummar in zauna"
Gabanta ya bada mummunan fad'uwa da kyar ta iya durkusawa kasa"tace
Ina wune Baffa?"
Ina wune Baffa?"
"Baffan uwaki,kuma ki rike gaisuwar ki bana so,sakarar banza sakarar wufi,daman tarbiyar da mukai maki kinan na ki dinga azaftar da mijinki,kina gaba dashi duk wani hakki da ya rataya a wuyanki baki yi mashi saboda ki ga fitsarariya ko,to bud'e kunnuwan ki kiji ne wallahi billahi zan sa'ba maki 'kwarai da gaski,in banda rashin hankali d'iyarki ce ku diyar shi ce,da zaki dinga buri akan ya aurar da d'iyar shi gawan da ya ga dama"
.
Da d'an yatsa ya nunata ranshi a matukar bace yace"kuda yake nasan baki da wannan mugun halin,amman ban sani ba ku saki a kai,tunda tsawan wata biyu kina wahalar da mijinki,bayan kinsan cewa aljannar ki tana gaf dashi amman kike wasa da damar ki ko?"
.
Da d'an yatsa ya nunata ranshi a matukar bace yace"kuda yake nasan baki da wannan mugun halin,amman ban sani ba ku saki a kai,tunda tsawan wata biyu kina wahalar da mijinki,bayan kinsan cewa aljannar ki tana gaf dashi amman kike wasa da damar ki ko?"
Kuka take bana wasa ba gaba d'aya taji wata nadama tazo mata na abinda ta aikata,cikin kuka tace"Baffa dan girman Allah kayi hakuri"
Dakuwa yayi mata yace"anki ayi hakurin tunda ai ki ba yarinya bace,da wayanki,kuma da kike fad'a ma mutane cewa wai ya sai da d'iyarshi ga masu kud'i dan yayi kudi,anya kina da tunani kuwa Saude?yarinya kamar ba d'iyar musulmai ba, to wallahi ki kiyaye ni, zan matukar sa'ba maki"
"Baffa kayi hakuri sharrin shai'dan ne"
"Idan kinga nayi hakuri sai na tabbatar cewa kin gyara gidan auran ki,kuma kin daina wannan shirmen da kikeyi na rashin kyauta ta ma maigidan ki,haka ki kaga iyayan ki nayi,ni dana tashi aurar daki da sauran 'yan uwaki akwai wadda nayi shawara da ita,cikin iyayanku?amman kuma basu tada hankali ba amman wai har kice kike laka ma mijinki sharri wajan mutane,na d'auka zaki tayashi inganta rayuwar yaran ku ne, ba wai ki dinga kirkirar matsala ba"
"Baffa kayi hakuri na tuba bazan 'kara ba"
"To shikinan Allah yayi maki albarka,kuma idan ya dawo yaga canji kada ki sake ki bijiru da wani mugun halin,dan nasan ku mata ba'a iya maku"
"Baffa zan gyara' bazan 'karaba,kayi hakuri dan Allah"
"Shikinan na hakura,idan ya dawo ya tabbatar da cewa an isa daki anyi maki fad'a,kada kuma ki 'kara wannan kuskuran,kima godema Allah kina da miji mai hankali,bai dauki mataki a kan ki ba,har tsawan wata ukku yana d'aukar shirmen,ki ba tari da ya biye maki ba,to wannan ya zama na karshi"
"Insha Allahu Baffa"
"Zan tafi Allah yayi maki albarka,ya kuma bada hakurin zama"
"Ameen Baffa nagode"
Aljihu ya ta'ba ya lalubu Naira d'ari biyar ya mika mata. yace"ungo kin d'an 'batar"
*SADAUKARWA GA....*
*_Lubee mai'tafsir_*
*_Hauwa M Jabo_*
*_Aisha Mazoji_*
[10/07 9:25 pm] +234 703 641 9426: *_MATAN ALI_*
_(The most lovely story of nice famly)_
*_Hauwa M Jabo_*
*_Aisha Mazoji_*
[10/07 9:25 pm] +234 703 641 9426: *_MATAN ALI_*
_(The most lovely story of nice famly)_
®
_Nagarta writter's Association._
_Nagarta writter's Association._
_Mentor's_
_Danladi Haruna_
_Ibrahim Barister_
_Auwal Danbarno Ag_
_Aisha Mazoji_
_Danladi Haruna_
_Ibrahim Barister_
_Auwal Danbarno Ag_
_Aisha Mazoji_
©
*BILKISU BILYAMIN*
*BILKISU BILYAMIN*
0 comments:
Post a Comment