NI A.Y.S NAKESO Page 21-25
.
WRITEN BY Princess Eshat Aysm
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
A.Y.S
.
.
.
.
.
Sabon dogon riga Lidia ta ?auko mata daga cikin kayan da suka sayo mata, ta mik'a mata tana murmushi ta ce "idan kinshiga wanka ki canza na jikinki yau kam".
?an murmushi tayi ta kar?a.
Shiru sukayi na?an lokaci, can Lidia ta ce "yau bakiyi karatu ba".
bata gane me take nufi ba don haka ta sunkuyar dakai, Lidia tayi murmushi ta matsa kusa da ita ta ce "kada ki damu, ina miki fatan samun lafiya, tashi kiyi wankan".
koda ta fito dogon rigar tasaka ta shafa mai.
Zata kwanta Dr Abdul ya shigo ?auke da takaddu a hanunshi, fasa kwanciyar tayi tabishi da kallo, abunda bayaso kenan wannan kallon nata, tana sakashi a ru?ani, ita kuma so takeyi ta gano wani irin rayuwa sukayi dashi?.
harya k'araso gabanta bata daina kallonshi ba, lumshe ido yayi ya bu?e ya ce "yakamata kidaina bina da kallo haka".
murmushi tayi ta kauda kai daga gareshi, takaddun ya mik'a wa Lidia ya ce "kije kimun typn wannan takaddun yanzu ina jiranki".
Amsa tayi harda tsugunawa sannan ta fice, tana fita yaciro alluran dake ledan hanunshi, harha?awa yayi sannan ya matsa daf da ita, kamar me ra?a ya ce "kada kimun kuka".
rigar ya ?aga yayi mata alluran, wani k'ara ta saki da k'arfi saboda zafin alluran ba irin na kullum bane, runtse ido yayi yana girgiza mata kai, hanunshi ta rik'e gam har yagama yi mata, ajiyan zuciya yayi ganin lokaci guda jikinta ya saki, kallonta ya shigayi cike da tausayawa, minti biyu da yi mata k'wak'walwarta ya fara juyawa, wani k'aran ta saki ta kama kanta zata fara bugawa yayi hanzarin rik'e hannayen, girgiza kai tashiga yi cikin wani irin yanayi, a hankali ya fara k'iran sunan ta, abubuwane suka fara mata yawo a kai, sosai ta fara tuna Momi, da k'arfi kuwa ta fara k'iran sunan, rungumeta yayi sosai ajikinshi ganin tanaso tayi wa kanta illah, anan yagane jininta bashida k'arfi sosai allurar ya mata k'arfi, bai damuba don ya lura tafara tuna abunda ta manta, lokaci guda kuwa ta fara ganin fuskar Faruq, a take ta tuna dawowarsa da irin dukan dayakai mata, kalamansa suka fara yi mata yawo a kunne, lokacin da ya furta mata kalmar saki, hawayene ya fara malala a fuskar ta, ta ?aga kai ta dubi wanda take rungume a jikinsa, a razane ta fara k'ok'arin k'wace kanta, ko shakka babu wannan mutumin datake ganinshi cikin Computer ne, shi take mafarki tun ranarda tafara ganinshi, shikam rik'eta gam yasakeyi, ya zuba mata ido yanaso ya gano wani hali take ciki, jin yak'i saketa sai tayi luf a jikinsa idanuwanta yana cikin nasa, a haka jiri ya fara kwasarta nanda nan bacci ya ?auketa.
Murmushi yayi ganin alamar nasara, gashin kanta daya barbaje ya gyara mata sannan ya kwantar da ita a wajen, tsintar kanshi yayi da sumbatar goshinta, Farinciki fal a ranshi, futa yazoyi Lidia ta shigo ?auke da takaddun ta mik'a masa harta gama, "da fara'a a fuskarshi yace nagode" itakam sai mamaki take taganshi a sake yau, abunda bai ta?ayi ba, "tana farkawa kiyi hanzarin k'irana".
haka kawai ya fa?a ya fice, da sauri ta isa jikin gadon da Aisha take ganin sai zufa takeyi, ga ?ankwalinta a yashe a wajen, bin ko ina najikinta ta farayi da kallo, kama baki tayi tana tunanin me yayi mata, shi ya tsani mata balle nace wani abun yayi mata, to kodai tafara haukane, a hankali ta fara shafa fuskan Aisha idonta cike da hawaye, itadai tana k'aunar Aisha har cikin ranta.
Bata tashi ba sai dare, lokacin kuwa Lidia harta yi bacci, kallon ?ayi tashiga yi, lokaci guda ta tuna komai, gani takeyi kamar mafarki tayi a baya, wani kuka ne ya kufce mata, ta shiga rerawa mara sauti, saida tayi me isan ta tashiga bayi, dirje jikinta ta rink'a yi tana jin kamar ta shekara batayi wanka ba, saida ta juma kafin tayi alwala ta fito, Sallah tayi sannan ta kifa kanta ta fara kuka, "duk abubuwannan ba mafarki nakeyi ba, hauka nayi kenan".
Kukan tafarayi da k'arfi har Lidia taji ta farka, kallon kallo suka farayi wa juna, da sauri ta ?auko wayarta ta k'ira Dr Abdul ta shaida masa ta farka.
yana kwance ne amma duk hankalin sa yana kan Aisha, tanaso ta zauna a cikin tunanin shi amma ya alak'anta haka da cewa tausayin ta yake ji, alha?in bai ta?a saka tunani da tausayin wata a ranshi haka ba, sai Aishar sa daya rasata har abada.
da hanzari ya tashi yanufi asibitin, a zaune ya sameta tanata kuka, kusa da ita yaje ya tsuguna, cikin sanyin murya ya ce "share hawayenki".
?ago idanuwanta tayi, lokaci guda ta waresu, cikin sark'ewa ta ce Dr Abdul! ashe ban farka ba, meyasa kake zuwamun a mafarki alhalin kasan...
shiru tayi ta kasa k'arasawa, lumsassun idanuwansa suna kanta yayi murmushi ya ce "rayuwar da kikayi anan kina ganina ai ba mafarki bane, Allah yasa kin warke kamar yadda nake sa rai, kuma nake fata".
fuskarta fal hawaye ta ce "hauka nayi ko".
"ba hauka kikayi ba ESHA.." mummunar fa?uwar gaba taji, itakam sunan a bakinshi kamar muryar AYS ?inta, binshi tashiga yi da kallo bako k'yaftawa, kashe mata ido yayi ya ce "ko baki warkeba ne, ko kuma haka kike kallon mutane"?
kunya taji ta sunkuyar dakai tana dariyar daya zo mata bata shirya ba, kamar wacce aka zabureta ta ce "ina Ammina? Ina Abbah na, ina k'anne na, ko duk sun gujeni"?
murmushi yayi ya ce "nan asibitine, su suna gida gobe zasu zo".
shagwa?e fuska tayi tana kallonshi, Lidia ya kalla ta sake baki tana kallonsu fuskarta fal murna, sai yanzu tagane abunda yayi mata, "kibata abinci taci sosai, kada tasha madara, 'ya'yan itace zaki bata, sannan ki ha?a mata zuma da tasha".
wayarshi yasa a kunne dayake ta faman ringn yasa kai yafuta.
.
Matsawa kusa da ita Lidia ta kamo ta tana dariya, "ina farinciki da samun lafiyarki".
murmushi Aisha tayi.
Duk abunda yace ta ha?a mata saida ta ha?a mata, zama tayi tabata labarin ?an zamansu da sukayi, musamman karatun da takeyi na AlQur'ani me girma yafi komai burgeta, duk abubuwan Aisha takanga tasansu saidai kamar a mafarki, kallon rigar jikin ta tayi ta yamutsa fuska ta ce "wannan rigarfa, nakine"?
Dariya Lidia tayi don ta gano k'yank'yami takeyi, ta ce "sayo miki akayi, ga sauran can awancan jakar".
Ta murmusa ta ce "?auko mun nagani".
basufi kala 5 ba, duka dogayen riguna ne, ta ?an ha?a rai ta ce "Abbah na yana zuwa"?
Shiru Lidia tayi tana kallon ta, "ya kikayi shiru, da yana zuwa nasan da ya kawomun kayana".
sai kuma ta fashe da kuka, ru?ewa Lidia tayi, ciwon nata zai iya dawowa ko wani lokaci, baki ta shiga bata tare da tabbatar mata iyayenta suna zuwa kamar yadda taji Dr Abdul ya fa?a mata.
ya kwanta ne kawai amma yanaso yaje ya sake sanin wani hali take ciki, lumshe ido yayi tuno hawayen dayata sauk'a akan fuskarta, yayi murmushi aranshi ya ce "wannan yarinyar daban take".
Tsam ya mik'e yasaka jallabiyar sa me ruwan madara ya zari key ya fita.
suna cikin wannan darun ya shiga, lokacin k'arfe 12:14
Lidia ta russana ta shaida masa, ha?a rai yayi ya ce "da darennan zakiga iyayen naki".
Harara ta watsa mai tana zun?uro baki, waro ido yayi ya ce "ohh ashe kin warke ko, ni kike harara"??
da?a zun?uro baki tayi ta ce "bakai kayimun tsawa ba".
D'an murmushi ?auke a fuskarsa ya ce "ki kwanta ki huta, da safe sai nakaiki gida tunda kin warke".
Ya k'arasa maganar yana kashe mata ido ?aya.
.
Neman waje yayi ya zauna ya fara danna wayarshi, binshi tayi da kallo tana mamaki, mutumin da take ganinshi a photo inbanda ikon Allah me yakawo ta wajenshi, lokaci guda taji tsanar Faruq ya mamaye ranta, tuno abunda yamata tayi, ta runtse ido da k'arfi, duk hankalinshi yana kanta, da sauri ya taso ya rik'eta ya fara girgiza mata kai, alamar tadaina tunanin da takeyi.
kuka ta farayi k'asa2 tana cewa "Faruq me yasa kamun haka, me nayi maka".
?Lidia ya kalla da niyyar yace mata tarik'e masa ita ya?auko allura sai yaga tuni tayi bacci harda wangale baki, yayi tsak'i ya dubi Aisha, jikinshi duk yayi sanyi, tsura mata ido yayi na tsawon lokaci, tsananin tausayin ta yaji ya kamashi, ya ?aura kanta a faffa?an kafa?anshi, "kiyi hak'uri *ESHA*, koda bansan Waye Faruq ?in a wajenki ba, bansan me yamikiba, inaso kisa a ranki komai a rubuce yake, haka Allah ya k'addara miki, kada kibari damuwar wani ta illata rayuwarki, bakiyi girman da zaki ?au tension da yawa ba, kinga yanzu kina cikin yanayin da komai zai iya faruwa dake, ko hauka ko ta?in hankali, kinga kinbar iyayenki da wahala, ki nutsu kada kisake tuna abunda wani yamiki na ?atanci".
sosai maganar ta ratsata, ta sauke ajiyan zuciya me k'arfi, a hankali ta ce mishi "nagode".
murmushin k'arfafa gwiwa yayi mata ya ce "kinyi alk'awari zaki manta komai"?.
ta ?aga kai, ya harare ta da wasa ya ce "da baki zaki fa?amun".
murmushi tayi da fararen hak'oranta suka fito ta ce "nayi alk'awari".
shima murmushin yayi ya cikata ya mik'e ya na cewa "ki tabbata kinyi bacci, idan bakiyi ba zanji ajikina zamuyi fa?a dake".
zuba mishi ido tayi, itadai yana masifar yi mata kyau da k'warjina, yana burgeta matuk'a, hure idon yayi ya fita yana dariya, bin bayanshi tayi da kallo har ya ?ace, murmushi tayi, alwala taje tayi ta da?e tana addua kafin ta kwanta, AYS ta fa?a ahankali, da sauri ta mik'e, lalla?awa tayi ta ?auko wayar Lidia dayake jikin soket, bata ?ata lokaciba tayi login Fcbk ?inta, sunannashi yana nan ra?au akan mssg ?inta, take matsanan cin kewarshi ya kamata, ta lumshe ido tana tunano kalamanshi, lokaci guda wani sanyi ya ratsa cikin zuciyarta, har zata sauk'a sai kuma tayi mishi sallama sannan ta sauk'a, addua ta sakeyi sannan ta kwanta, nanda nan kuwa bacci ya ?auketa.
Duk yadda yaso yayi bacci gagara yayi, idonshi biyu har gari ya waye, ruwan tea kawai yasha bayan yayi wanka, ya?au duk abunda zai buk'ata ya nufi mota, akwai aikin dazaiyi ma wani shiyasa yaketa sauri,.
Agogon hanunshi ya duba yaga da sauran lokaci, don haka bai nufi National hospital ?inba sai ya nufi MANAYS.
A durk'ushe ya sameta tasawa Lidia rigima lallai ita bazata saka dogon rigaba, hannuwanshi ya har?a yana kallonsu, dariya ta bashi sosai, baisan rigimarta yakai hakaba, a hankali ya k'arasa ciki, da sauri Lidia ta durk'usa ta gaisheshi, rana ta farko kenan da ya fara amsa gaisuwan ta, mamaki ya cikata
.
Hijabin dake ninke akan drowar ya jawo ya mik'a mata, tanata zun?ura baki ta kar?a.
a hankali yace "taso muje".
Da sauri ta mik'e, zuciyarta fal farinciki tana tunanin zataje gida yau.
Da murmushi Lidia tabisu har suka bar ?akin.
Motarshi ya nufa ya bu?e mata gefen da zata shiga sannan ya shiga shima ya tada motar, yaso yakaita ta za?i kayanda takeso ne, ya tuna aiki zaiyi ma wani yasa ya nufi asibiti, bin ko ina takeyi da kallo tana nazari kamar ba garinsu ba, a hankali yake tuk'i yana satar kallonta, can hak'urinta ya k'are ta ce "Dr wai ko na mutune"?
Waro ido yayi ya ce "mutuwa? Haka ake mutuwa"?
Fuskantarshi tayi sosai ta tsareshi da ido ta ce "naga banta?a ganin irin nanba, shiyasa na ?auka ko ba'a duniya muke ba".
Dariyane ya su?uce masa ya ce "a duniya muke".
"gidanmu zaka kaini ko".
Ta jefa masa tambayar, ya murmusa ya ce "a'a, rakani zakiyi".
Tsuke baki tayi, tayi shiru bata sake magana ba har suka isa.
.
Office ?inshi dake cikin Asibitin ya kaita, nuna mata wajen zama yayi ya ce "ki jirani anan".
Kafin yagama fa?i ta ?arke masa da kuka, da mamaki yabita da kallo ya ce "kina cikin hankalinki kuwa".
Kukan taci gaba dayi, ya matsa daf da ita yace "meyasa kika cika futuna ne"?
Zun?uro baki tayi tana kunkuni, binta yayi da kallo da lumsassun idanuwansa, yayi tsaki yaja hanunta suka fice.
Tafiya kawai sukeyi yana rik'e da ita har suka k'arasa cikin asibitin, tunda suka shiga ake binsu da kallo, mamaki yakama mutanen, sun sanshi da miskilanci ko kallon su bayayi balle ya amsa musu gaisuwa ko sake fuska, ware ido Aisha tayi tanata kallon mutane, yana rik'e da hanunta yayi ta duba wanda zai duba, damuwarsa kada ya saketa tayi wani waje, don bai yarda ta gama warkewa ba, ?akin dazaiyi aikin suka shiga, waje ya nema ya zaunar da ita yace "kada ki tashi anan, kijirani".
Kai kawai ta ?aga masa sannan ya shige ciki, tananan zaune can tafara jin wani irin gurnani ha?e da kuka, da gudu ta mik'e taje tafara lek'ensu, jikinta yayi sanyi ganin inda mutumin yakeyi, ga wani na'ura duk an zagaye kanshi da ita, hawayene yafara sauk'a mata, tana mak'ale a wajen har tsawon minti 40 taga ancire masa, allura taga ya ha?a yayi masa, duk idonta nakai.
A wajen yazo ya sameta, har lokacin tana hawaye, jan hancinta yayi ya ce "wayace kitaso".
Manyan idanuwannan nata ta zuba mishi, wani irin kasalane ya sauk'ar mishi, ya janye idonshi akanta da sauri yana murmushi.
Kaya yakaita taza?i wanda takeso tanata murna, sannan ya sai mata abunda zataci, abunka da wanda bai saba yawo ba, ji take kamar suyita zagayawa tana ware ido da hanci tana kallon gari, daidai zasu shiga wayarshi tafara ruri, ta gefen ido ya kalleta ha?i da jan tsak'i yace "?auka kice bana kusa".
da hanzari takai hanu ta ?auki wayar ta kara a kunne.
"Assalamu Alaikum".
shiru tayi ta kasa magana, kallon sunan dake kai tayi ansa UMMANA, ta kalleshi ta ce "Ummace fa".
Bai kalleta ba ya ce "kiyi magana".
sake mayarda wayar kunnenta tayi ha?i da amsa sallamar, "ina Abdul ?in"?
shafa fuskarta tayi ta ce "ya?anyi nisa ne".
"wacece ke". umma ta tambaya, ta juya da sauri tana kallonshi, kamar yasan abunda akace ya ce "kidaina kallo na, kice matar da zan aura ne".
ta zaro ido ta girgiza masa kai, ta ce "idan yadawo zai k'iraki".
Katse kiran tayi ta na kallonshi, ya ha?a rai ya ce "nace kidaina kallo na ko, idan ina tuk'i bana amsa k'ira, nasan maganar aure zatamun shiyasa nace ki fa?i haka".
Dariya ta tuntsire dashi ta ce "babba dakai bakada mata".
murmushi yayi ya ce "to wazan aura, bana iya magana da matane".
"meyasa". "bansanni ba, haka naga inayi".
dai2 lokacin suka iso, yana faka motar tafito da sauri ta nufi ?akin, duk dogon rigar yagama isarta, tana alla2 taje ta cire, Lidia tana ganinta ta washe baki ta ce "kun dawo"?
murmushi tayi mata ta ce "eh".
.
Dariya yayi ya ka?a kai ya ?i?i kayanda suka siyo yanufi ?akin dashi, lokacin har ta shige wanka, ijiyewa yayi ya fita abunshi.
.
.
.
Momi ce zaune a gaban Ammi suna lissafin yaushe Aisha zata cika Watanni uku suje, ganin ko wata batayi bane yasa duk suka k'agu tayi.
Ammi ta nisa ta ce "ranar munyi maganar Faruq bakice komai ba, kinsan duniya kana naka wani yana binka da sharri, ni a yanda na fahimta ba banza zai aikata haka ba".
Momi tayi ajiyan zuciya ta ce "wlh nima ina wannan tunanin, narasa abunyi ne kawai".
Ammi ta ce "idan Abbahn nasu yadawo zan mishi magana, sai a ?auko malami a masa karatu, ko akwai aljanu a ciki ko sihiri, yanda naganshi a hargitsennan gaskiya akwai wani abu".
Haka kuwa akayi, malam Hassan dake bayan layinsu suka ?auko, shima Abbahn baiyi musuba, karatu yayi masa sannan ya bashi adduo'i, hatta ruwan shansa ya zama addua ne, yayi masa fa?a sosai akan ya kula da ibadansa, zasuyi ta karatu har natsawon kwana 7.
Tunda aka fara suka fara ganin canji, gaba ?aya nutsuwarsa ta fara dawowa, wani iri yakeji, yana jin zafin rabuwarsa da Aisha, har kuka yake zama yayi wa Momi akan a taimaka adawo masa da ita, Momi mamaki ya cika ta, watau dagaske sihiri ne, to waye da wannan aikin, tadai bar mutum da Allah kawai, ta duk'ufa wajen rarrashin ?anta.
"Faruq, ka nutsu kaji me zan fa?a maka, saki uku kayiwa Aisha, me zata dawo tayi maka".
"Mom ai nasani, lokacin nakasa kai zuciyata nesane, amma yanzu zan iya jure komai Momi, kome tamun zan zauna da ita a haka".
momi ta kama baki ta ce "kanka ?aya kuwa Faruq, ana gyara saki uku ne ko me"?
ganin bashida niyyar daina sumbatun tace "kaje gidansu saika fa?a musu".
A k'ofar gida yasamu Abbah da jarida a hanunshi, ya tsuguna har k'asa ya gaishe shi, da fara'a Abbah ya amsa ya ce "yaya Momin taka".
Sunkuyar dakai yayi yana susa kai ya ce "dama ita ta turoni, wai.. Wai dama Aisha...".
nanda nan Abbah ya ?agoshi, ya ce "kada kafara wannan maganar, saki uku kayi mata, a yanzu batada maraba da mahaukaciya, me kake ayi maka".
Kuka ya fara k'asa2 kamar yaro, yana tsananin tausayin Aisha, har cikin ranshi yaji maganar, gashi babu aure a tsakaninsu, Allah ya isa yayi ta ja a zuciyarshi, Abbah sarkin tausayi, ji yayi ya bashi tausayi, musamman daya tuna cewa ba laifinshi ba ne, ya dubeshi da kyau ya ce "
.
Babu aure a tsakaninku, kafin ta warke nasan lokacin ta gama iddarta, kai kuma zanyi maka fatan samun wata kamarta".
Yana fa?in haka ya shige gida abunshi, AMMI dake tsaye a bakin k'ofa tana baiwa Sadiya aika Abba ya shigo, bayani yashiga yi mata, tayi salati ta ce "ni dama nasan ba laifin yaronnan bane".
Faruq ?inne ya shigo duk suka zuba mishi ido, Abbah ya ce "wani abune".
Tsugunawa yayi a wajen yana hawaye ya ce "bazan iya tafiya ban baku hak'uri ba, tabbas kun mun karamci sosai, wlh ni kaina sai yanzu nake dana sanin abunda na aikata, amma nayi alk'awari zan ?au nauyin jinyar tata har ta warke, kuma ko a haka tasamu miji zata iya aurenta, saboda babu iddah akanta"....
Wangale baki Ammi tayi, "tsawon shekaru uku Faruq kace babu iddah? Me kukayi to"?
Susa kai yayi kunya takamashi kamar ya nitse, Abbah yayi murmushi ya ce "kajiki da wani magana, wannan bata taso ba, bincike ya nuna anshiga tsak'aninku ne, banga laifinka ko ?aya ba, zan sake maka alfarma a karo na biyu, ka nemi auren k'anwarta SADIYA idan ta amince ni kuma zanbaka".
Da sauri Sadiya ta sake baki tana kallon Abbah, shima Faruq ?in shi yake kallo, wannan mutumin ya shammaceshi da yawo, bai isa yace masa a'a ba, shidai yasan Aisha kawai yakeso ba wata ba, murmushi ya k'irkira da iya kacinsa fatan baki ya ce "Nagode Abbah".
.
Jiki a sanyaye yabar gidan, ita kuwa Sadiya tsananin tausayin Aisha ne yasake kamata, share hawaye ta farayi Abbah yace "kukan menene kuma, idan bakiso bazan miki dole ba, yabani tausayi ne, mutane basuda imani ko ka?an, amma nafi tunanin aljanin yaronnan ne zaiyi haka".
Ammi ta ce "wani yaro kuma".
ya ka?a kai na takaici ya ce "yaronda ta ha?u dashi wai AYS ne ko waye, ranarda yazo daga ganin k'wayar idonshi zai aikata haka".
Ajiyar zuciya ta sauk'e ta ce "Allah yasa hakan yazamo mana alkairi".
Duk sukace "Ameen".
Abbah yace "kina sonshi ko kuwa"?
Zun?ura baki tayi ta ce "ni bana sonshi".
Ammi tayi dariya ta ce "tafi abunki ki barshi, haka ake tambayar".
murmushi Abbah yayi kawai.
.
Tunda daga ranar ta fara mak'alewa Dr.Abdul idan zai tafi tare suke tafiya, idan baizo ya ?auketa ba tayi ta kuka kenan, su kuma abunda basu so kenan kada ciwon yadawo, da safe idan yabata magani tasha tare zasuyi ta zagaya wajen, babu wanda zai ganta yace jinya aka kawo ta, ahaka har tafara gane kan aikin nasu, ta fara gane matsalar kazane ake bada magani kaza, ko National zai tafi tare suke tafiya, tayi ta raba ido, wani lokacin tasa masa rigima ita dole akaita wajen Abbanta da Ammin ta, dak'yar suke shawo kanta.
Watanta biyu sukayi wani irin shak'uwa da ita, Dr Mansur tunda yatafi Sudan bai dawo ba, saidai suna waya kullum da Dr Abdul.
Lidia kuwa tajata a jiki sosai, A hankali musulunci yafara shiga jikinta, saboda Aisha bata wasa da ibadanta ko ka?an, duk abunda takeyi bata manta Allah, dare kuwa rabashi takeyi ta kwana tana Ibadarta.
Abu ?aya yake damun Abdul yanda tunanin ta yake nema yafi k'arfinshi, dazaran sun rabu zai fara tunanin ta, duk wani nutsuwar shi ya koma kanta, a baya babu abunda yake hanashi tunanin Ayshar sa datayi aure, sai ha?uwarsa da wannan Aishar a fa?ansa.
Ganin bacci yak'i zuwa masa ya ?au wayarshi ya hau Fcbk, yakan juma bai hauba, saboda aikinsa yayi yawa yanzu, ?an murmushi ya sake tuno abubuwa da yawa da yayi, mssg ?in dayak'i bu?ewa kusan wata guda yace bari ya duba yagani, ganin sunan Aisha ne saida gabanshi ya fa?i, sallamace kawai amma saida yaji hawaye yafara sauk'o masa, a fili ya ce "nayi rashin abunda nafiso fiyeda komai nawa, Allah ya baki zaman lafiya ESHA ta".
Kamar zai sauk'a sai kuma ya tura " _ESHA kinada aure, don Allah kada kisake mun magana_".
Runtse ido yayi yana tunanin tsawon shekaru uku yakasa cireta arai, ?an tsuka yayi ya ce "Allah yagani nayi k'ok'arin cireta nakasa".
Dak'yar bacci ya ?aukeshi donma ?arawone.
.
Ta idar da Sallar asuba kenan tana shirin shiga wanka taji an bau?e k'ofar, da sauri ta juya don ganin waye, Dr Abdul ne, shi kanshi baisan yaya akayi ya taho ba, suna idar da Sallah ya figi motarsa ya taho, bak'ar jallabiyace ajikinsa me ha?e da hula, binshi tayi da kallo har yanemi waje ya zauna bata daina kallonshi ba, ha?e rai yayi irin borin kunyarnan, tayi murmushi ta ce "yau da wuri zamu tafi kenan, amma naga baka shirya ba".
Da?a ?ata rai yayi ya ce "kiyi abunda zakiyi, nazo duba wanine".
shiru tayi tasan duk saurin dayakeyi sai yasaka Unifoam yake fitowa, ganin tana tsaye yasa ya mik'e, a hankali ya taka har inda take, bakinta ya kama ya?an mur?e, ai kuwa taji zafi sosai ta k'wala k'ara saida Lidia ta farka tana zare ido, ya ce "idan kika sake ganina baki gaisheni ba saina cire bakin".
kuka ta fashe dashi sosai, wani tsawan yadaka mata "kewai kullum sai kinyi kuka ne"?
kukan taci gaba dayi abunta, ya runtse ido ya toshe kunnuwansa yana mata dariya, Lidia har tasaba da fa?ansu, dariya tayi tashiga bayi ta barsu a wajen.
dai dai kunnenta ya ra?a mata "idan bakiyi shiru ba bazanje ko ina dake ba".
harara ta watsa masa ta zun?ura baki ta ce "don Allah ka kaini gida tunda na warke, ko Abbah na ka 'kiramun naji muryarsu".
shiru yayi yana nazari, can ya ce "banida numban".
da sauri ta ce "inadashi".
mik'a mata wayar yayi ya ce "ki k'ira kafin nadawo kin shirya, yana fa?in haka ya fice.
tsalle tayi tana murna, abun haushi tayita k'ira a kashe, kuma numban kawai ta haddace, jiki a sanyaye ta ajiye wayar, lokacin Lidia har tayi wanka ta fito, itama wankar tashiga, tana fitowa ta samu har tajera mata abun karyawa, cikin k'ank'anin lokaci ta shirya, cikin riga da siket, siket ?in har k'asa, rigar ta ?an kamata ka?an, Lidia ta bita da kallo ta ce "kinada kyau".
murmushi tayi mata ta ce "nagode".
jakar kwalliyarta ta jefa mata ta ce "kiyi kwalliya zakiyi kyau".
bataso ba don dai batason musu da mutane shiyasa tayi yak'e tafarayi, hijab tasaka me?an girma, wayar ta?auka tasake k'ira amma akashe, me makon ta ajiye sai tafara masa bincike, duk pix ?insa ne a wayar, yana masifar yimata kyau, ita ka?ai taketa murmushi, anan taga Umman tasa, suna kama sosai, gajiya tayi da kallon photonan tasauk'a ta kunna data, kamar mayya ta haura fcbk nasa, zatayi log out ta haura nata taga sunanda ya girgiza ta.
.
Ware ido tayi sosai taga dagaske ABDULLAHI YAHYA SA'AD tagani, da sauri ta fara bincikawa, babu tamtama shine, hawayene tare da dariya suka gauraye fuskarta, ta manna wayar a k'irjinta tana kuka sosai, lallai yau ta yadda *SO AJINI YAKE.*
Tunda taganshi taji yafi kowa burgeta, ashe Ays ?inta ne, dariya kuma sai ya su?uce mata tashigayi babu k'akk'autawa, Lidia ta tsura mata ido tana tausayin ta, tana tunanin ashe har yanzu bata warke ba.
Tana cikin wannan yanayin ya shigo, da sauri ta ?aga ido tana kallonshi hawaye nabin kumatun ta, jiki a sanyaye ya matsa kusa da ita ya ce "banson kukan nan Esha".
Kallon shi tashiga yi sama da k'asa kamar taga sabon abu, hanu yasa ya zare wayar a hanunta yana cewa "kullum sai kinyi kuka bansan matsalarki ba".
Tsurawa wayar ido yayi, lokaci guda ya ha?e rai ya ce "meyasa kika shiga nan"?
Wani irin sonshi ne taji yana ratsa ta, fuskarta ?auke da murmushi ta ce "bani nashiga ba, gani kawai nayi".
Yanayin kallon datake mishine ya burgeshi, murmushi yayi ya ce "mutafi".
Juyawa yayi da niyyar fita, sai ji yayi ta ?ale bayanshi tana dariya, a ki?ime ya fara k'ok'arin cireta amma ta k'ank'ameshi, bata daina dariyar ba sai lafewa datayi a bayan.
ya kama kanshi yanajin wani abu yana mishi yawo, Lidia ta ce "nifa inaga wani matsalar ta samu".
A hankali ya ce "sauk'o kiji".
.
Sauk'owa tayi ta ce "kayi hak'uri, bansan lokacin da nayi hakaba".
Hancin ta yaja ya ce "kincika rigima".
Murmushi kawai tayi yayi gaba tabishi a baya, kamar kullum saida yagama duba kowa suka wuce ?ayan asibitin, tunda suka ?au hanya ta zuba mishi ido, har yafara tsarguwa ya ce "kidaina kallo na".
A hankali ta ce "bazan iya dainawa ba".
Da sauri ya kalle ta, ganin idonta yaciko da hawaye ya ce "haba mana, menene na kuka kuma, kiyi ta kallona to".
Yana magana tanabin bakinshi da kallo, batasan tanason AYS ba sai yanzu, runtse ido tayi tana tunanin iko na Allah da ya kawota wajenshi cikin sauk'i, a hankali ta ce "nagode Faruq".
mamaki ya kama shi, lokaci na farko dayaji yanaso yasan wanene Faruq ?innan.
har suka isa baice mata komaiba,Da yake babu aiki sosai ranar lahadi Office ?inshi suka wuce yafara bincike akan Computer, tana zaune daga can gefe tayi tagumi tana kallonshi, bai ?ago ya kalleta ba yace "Aisha, meyasa kike kallona dayawa".
Ajiyan zuciya tayi ta ce "inaso in maka tambaya ne, ranar naji kace bakada mata".
barin abunda yakeyi yayi yana kallonta, ya ce "eh inajinki".
"gani nayi yadace ace kanada ita, don Allah kabani labarin ka".
Tunda suka fito yana mata kallon me ta?in hankaline, amma yanzu yanda take maganar a nutse ya tabbatar lafiyanta k'alau.
Kallon ta yayi na?an lokaci ya ce "a wani dalili".
Shiru tayi kafin ta ce "akwai dalili da yawa, nayi maka alk'awarin zaka sani bayan naji abunda na tambaya, abu ?aya nakeso shine ka yadda dani".
Nutsuwarta yayi matuk'ar bashi mamaki, har wani kunyarta ya fara ji, ya lumshe idanuwansa kafin ya waresu a kanta.
"a tak'aice ni mutumin Zaria ne, acan nayi karatuna, iyayena ba wasu masu k'arfi bane, don haka makarantar danakeyi bawani me tsada bane, amma inada k'wak'walwa sosai...
Kusan zan samu addmsion na ha?u da wata, bansan kamannin ta ba amma syyr ta me tsananin zafine ya kamani, in tak'ai ta miki ranarda naje garinsu a ranar aka ?aura auren ta, dani aka ?aura bansani ba, koda nadawo saida nashafe wata bani ci banasha, suma kuwa nayi yafi misali, ina cikin wannan halin na tafi karatu a ABU ZARIA, anan na ha?u da Mansur, yanada mutunci sosai, munshak'u dashi sosai saboda yanda yake kula da damuwata sai ya zamto bana iya ?oye masa komai, saboda tunanin yarinyar sai ya zamto bana gane komai a makarantar, duk wani k'ok'arin iyayena hakan baisa namaida hankali ba, soyayya ce bana wasa ba ya kamani, Mansur kuwa dama bashida wani basira sosai balle ya ganar dani, mahaifinshi yanada ku?i sosai, dama babu inda baiyi ba akan ya turashi waje yayi karatu yace yafiso a garinsu, k'arshe dole ya tilastashi ya tafi can yayi karatu, nan mansur yace bazai iya rabuwa dani ba, babu yanda ba'ayi ba dole mahaifinshi ya ha?a dani muka tafi, tafiyata can yarage mun tunanin abubuwa da dama, kuma wanda ya?au nauyin nawa bazaiji da?i ba idan na koma ban tsinana komai ba, cikin shekara ?aya nazama wani a makarantar saboda tsananin k'okarina, Mansur ma ba laifi ina tursasa masa yayi karatu, shekaru hu?u akeyi amma shekaru biyu nazarce 'yan gaba dani, wannan dalilin yasa mahaifin Mansur ya gina mana Asibiti, shine wanda aka kawo ki, *MANAYS*
Sunan mansur da nawa aka ha?a, har yanzu ban manta ta ba, kuma inbanda mahaifinta bansan kamannin ta ba, wannan shine ni a tak'aice".
tana share hawaye da tsananin mamaki ta ce "Kana wajen aka ?aura aurenta, kuma da gaske kaga mahaifinta"?
?aga mata kai yayi alamar jaddada wa, zatayi magana ya ?aga mata hanu "tambayar ta isa".
murmushi tayi ta ce "menene dalilin ka nak'in neman wata".
hararta yayi ya ce "tashi nakaiki".
???

0 comments:
Post a Comment