Suna zaune Bobby ya shigo rikeda waya a hannunshi kai tsaye ya karaso ciki tareda mikama Aunty Sumy wayan yace"Its your call"...ba musu tasa hannu ta amsa wayan tareda karawa kunnenta tayi sallama...a daya bangaren Hafsa tace"wa'alaiki salam Maman Miemie..inata kiran wayanki no answer shine nace bari inyi trying na Bobby in gani sai gashi kuma ya shiga..Ilham ce ta dameni wai tanason mgn daku"..Aunty Sumy ta dan saki murmushi tace"oh Hafsa wai kece?..dama kinada Number Bobby knn?.."Hafsa tace"bani dashi wlh Ilham din ce ta bani wai tunda naki baki dauka shi a kirashi..gata kuyi mgn"..daga haka ta mikama ilham dake zaune kusada ita wayan...yarinyan da bazata haura 8 to 9 years ba ta amsa wayan full of happines tace"Auntyyy"..aunty sumy ta saki daria jin yanda taja sunan nata tace"na'am 'yar gidan aunty ya kike?.."tace"am fine aunty just missing you..i want to come back home"..aunty sumy tace"hope dai ba rigima kikema aunty hafsa ba koh?.."tace"bana rigima aunty kullum sai mun fita yawo..yau ma saida aka kaimu shopping dasu fadeel"..aunty sumy tace"inyee 'yan gidan aunty hafsa..ilham banda fitina kinji?..kuma banda kiriniya banda sa aunty hafsa magana"...daria ta saki sosai kaman wata babba tace"aunty i want to speak to everyone please..where is my Uncle Bobby?.."Aunty sumy tayi putting nata on speaker snn tace"your uncle bobby is here"..cikin excitement ilham tace"my uncle bobby"..yace"yes my mummy how are you?.."tace"am fine uncle bobby ya aiki?.."yace"aiki fine ilham gobe zaki dawo ba?.."tace"yes..kasan me na siyo muku daxu da mukaje shopping?.."yace"sai kin fada mummy"..suna jin yanda ta danyi kasa da murya snn tace"na siyo maka cheesy na siyoma uncle sab sweet na siyoma yaya chocolate snn na siyoma Mummy da aunty biscuits"..dan bata rai Bobby yayi yace" seriously ilham?..of all abubuwan dake wajen ki rasa abunda zaki siyomin sai cheesy?.."daria ta saki sosai tace"to ba kace min kana son cheesy ba..shknn zan sake maka wani yanxu ka bama Mummy da uncle sab muyi mgn"..bai sake mgn ba ya mikama Mummy wayan..nan ma hira suka sha sosai sai kace wata babba snn sab ya karba shima aka sha hiran dashi...miemie ce karshe aka kai mata wayan har daki nan ma suka dora daga inda suka tsaya...Bobby na duban Mummy in a serious tone yace"Mummy nidai kada a sake bari wani daga cikin mutanen nan yazo yace zai dauki yaran nan bana so wlh..after duk abubuwan da suka yi mana yanxub zasu ringa wani zagayowa suna daukan yara sbd mu yadda dasu?.."girgiza kai Mummy tace"kaidai ka fiya riko wlh Bobby..baka manta abu komai qanqantarshi...abun daya faru ya riga ya faru saidai a kiyaye gaba"..aunty sumy tace"kuma Mummy duk abubuwan da suka faru babu ruwan hafsa a ciki..lokacin ma tana england komai ya faru so bazan iya hanata ba muddin ta nuna tanason daukansu koba komai qanwar mahaifinsu ce"..wani kallo Bobby yayi mata yace"sbd tana qanwar mahaifinsu bashi zai daman zuwa koda yaushe tace zata daukesu ba..idan abun da gaske ne meyasa shi baban nasu ya kasa nemansu duk tsayin wadan nan shekarun sai ita?.."dafe goshi kawai Mummy tayi dan tasan kome zaa fada bazai yadda ba tunda ya riga ya dauki zafi haka...itama aunty sumy sanin halinshi yasa taja bakinta ta tsuke tunda it's of no use trying to explain things to him bazai taba fahimta ba..ya mike zai koma flat dinshi Mummy ta kira sunanshi...ba musu ya dawo ya zauna yana fuskantarta...itama tana dubanshi tace"wane magana kukayi da Nuru dazu kace bazaka iyaba?.."da sauri ya kalli Nur da yayi wani kasa da kai sai kace mutumin kirki...wato ma karanshi yazo ya kawowa Mummy sbd yasan ita kadai zata iya mishi dole koh...rai a dan bace Mummy tace"bada Bobby nake mgn bane?.."a hankali yace"Mummy lecturing fa yakeso inje inyi..sbd Allah Mummy ta ina zan wani fara shiga class ince zanyi lecture bayan ba tabayi nayi ba..idan tsakani da Allah ne shi meya hana bazai je ya koya musu da kanshi ba"..yana rufe baki Nur yace"amma kasan da field dina ne ba abunda zaisa ma in tambayeka sbd nasan 6atamun lokaci zakayi..kaine gynaecologist dan haka kai ya kamata ka koya musu ba ni ba"...wani irin daci yaji yana taso mishi tun daga throat dinshi zuwa bakinshi..gaba daya sai ya zama speechless a wurin..nan take Mummy tace yaje ya taimaka musu koda na one or two days ne...as usual ya amsa mata da toh snn ya mike zuwa flat dinshi...Nur ya bishi da kallo yana kunshe daria...sallama yayi dasu Mummy snn ya mike zuwa flat din Bobby ya sameshi kwance kan three seater a parlor idanunshi lumshe yayi pillow da hannayenshi...murmushi ya saki tareda sunkuyawa saitin kunnenshi yace"this is your punishment for making Lamido cry"...Bobby da yaji mgnr kaman daga sama baisan lokacinda ya mike zaune da sauri yana kallonshi ba...mamaki ne karara a fuskanshi jin abunda yace...shi kuwa Nur juyawa yayi ya fita daga parlon yana daria kasa kasa yasan yanxu komai taurin kanshi dole yayi abunda yakeso tunda Mummy tasa baki...Bobby kam sbd tsabar takaici baisan time daya dunkule hannunshi tareda naushin kujeran da yake kai ba yana fadin"Fuck you Nur".
Har washegari Saturday ranshi bai dena 6aci kan abunda Nur yayi mishi ba..neman hanyan da zai rama kawai yake amma ya rasa...mikewa yayi daga karshe ya bude wata kofa ta cikin parlonshi sai gashi wajen wani tafkeken swimming pool daga gefenshi kuma gymnasium dinshi ne daya cikashi taf da kayan motsa jiki...kai tsaye gym din ya nufa dan a al'adanshi every Saturday and Sunday sai yayi training kafin yayi komai dan haka yana shiga ya fara training dinshi...ya 6ata lokaci sosai yanayi dan bai baro gym din ba sai da ya hada gumi sharkaf snn ya bude fridge dake ciki ya dauki chilled water ya bude yasha snn ya fito daga gym din yana cigaba da sipping a hankali...direct bedroom dinshi ya wuce bai kobi takan wayanshi da yaga yana haske ba ya fada bathroom...wanka yayi a tsanake snn ya fito yana goge jiki da towel..ya isa gaban mirror yayo shafe shafenshi snn ya shiga closet dinshi ya sako kaya ya fito snn ya isa ga wayanshi da har yanxu bai dene haske ba alamun ana kira knn...missed calls ya gani har 8 biyu na wata Nurse dake Hospital dinshi,biyu na Nuru sai ragowan hudun kuma gaba daya na Rayhan ne...baibi ta kan natan ba ya fara kiran Nurse din..bayan sun gaisa tace"Sir dama da akwai emergency ne kuma Dr Isaac baya nan"..yace"doc Vivian fa?.."tace "itama bata nan Sir".. kmr bazaiyi mgn sai daga baya kuma yace"alright i will be coming".. ta amsa da" ohk sir"..snn ta kashe wayan...suna gamawa ya shiga kiran Nur shima bai dade yana ringing ba yayi picking yana fadin"Bob ina ka shiga naketa kira baka picking?.."ba tareda ya bashi amsan tambayan ba yace"what's the call for?.."da sauri Nur yace"wlh yanxun ake kirana daga Hostel wai wuta tayi spark a wani apartment kuma baa san me yayi causing ba shine naga ya kamata muje mu duba to make sure ba wani babban matsala bane"..shiru Bobby yayi yana sararonshi har ya gama snn yace"yanxun Hospital zanje munada emergency sadai in na gama da can in shigo"..da sauri Nur yace"No problem kana gamawan ka shigo i'll wait for you"..bai sake cewa komai ba ya kashe wayan...karasawa gaban mirror yayi ya sake feshe jikinshi da turaruka snn ya dauki dayan phone dinshi ya fita daga dakin...kai tsaye parlon Mummy ya shiga bai sameta ciki ba dan haka ya wuce bedroom...tana zaune kan sallaya sanye da hijab a jikinta tana azhkar ya shigo...ya nemi wuri ya zauna saida ta gama azhkar din ta juyo tana kallonshi tace"Bobby"..yace"Mummy ina kwana"..tace"lafia lau..in zakaje haka da sassafe?.."yace"Hospital zanje wa there is emergency..daga can kuma zan shiga college amma ba jimawa zanyi ba"..Mummy ta mike daga inda tace"to muje kayi breakfast "..tana rufe baki yace" Mummy am ok plss..bana jin yunwa"..zaunawa tayi kusa dashi tareda kamo hannunshi a hankali tace"wai sbd maganan jiya ne kaketa 6acin rai haka?.."ya dan turo bakinshi yace"Mummy nifa ba ta6a lecturing nayi ba kin sani..kawai sa inje in wani ce su zauna zanyi musu lectures "..murmushi Mummy ta saki tareda gyara zama tace" ko da baka ta6ayi ba am 💯 sure you can do it..besides taimakawa zakayi Bobby dududu baifi kuyi na two or three days ba zaa samu wani..ko kana ganin as the proprietor bazaka iya shiga class ka koyar dasu ba?.."da sauri ya girgiza mata kai yace"that's not what i mean"..tace"to ka kwantar da hankalinka nasan you can do it..and believe me zaka kara qima a idonsu idan sukaga har ka shiga class dinsu da kanka ka koyar dasu so relax"kasa ce mata komai yayi sai dan murmushi daya saki...murmushin itama tayi masa tareda mikewa ta kama hannunshi suka fita zuwa dinning...da kanta tayi serving dinshi baiyi musu ba ya shiga cin abincin...jin shiru da yayi gidan yace"wai duk ba wanda ya tashi?.."Mummy tace"kasan weekend ai dama ba tashi da wuri suke ba..kowa yana ramuwar bacci"...gyada kanshi yayi yace"amma shi Sab ramuwar baccin uban me yake shida ba fita ko ina yake ba?..wai yaushe ne ma zasuyi resuming school?.."tace"nan da two weeks ina tunanin"..yace"Allh ya kaimu..gara ya koma ko don sbd mu huta da rigimarsu da Miemie..kullum cikin cin zalinta yake"harara Mummy ta maka mashi kafin tace"bayanta kake goyo sbd ita 'yarka ce koh?."ya dan saki murmushi yace"aah Mummy gaskia dai nake fada"..tace"to rike gaskiyan naka baa son ji dan bazan bari ka dorama d'ana laifi ba"...murmushi kawai ya sakeyi baice komai ba...saida ya gama cin abincin ya mike Mummy ta rakashi har centarl parlor tana mishi addu'a..yayi mata side hug tareda fadin"Ameen Mummyna..bari inga aunty Sumy kafin na fita"...gyada mishi kai kawai tayi snn ta juya ta koma ciki shi kuma ya nufi flat din yayar tashi...Miemie ce kadai kwance a palor tana kallon wani Series ya shigo..ta mike zaune da sauri tana gaisheshi yace"lafia..bata tashi bane?.."tace"ta tashi tun dazu tana daki"..bai sake mgn ba ya nufi bedroom dinta..zaune ya sameta a kan gado tayi tagumi tareda zubama wayanta dake rike a hannunta ido sai kace zata gano wani abu a jiki...ya karasa ya zauna kusada ita yana kallon wayan nata snn ya kalleta yace"Aunty Sumy lafia kuwa?.."firgigit ta dago tana kallonshi dan batasan ya shigo ba...ta boye wayan hannunta da sauri tana kakalo murmushi tace"yaushe ka shigo?.."maimakon ya amsa sai cewa yayi"lafia wai?..meya faru naga kin zubama waya ido haka?..did somebody called?.." girgiza kai ta shiga yi da sauri tace"b..ba wanda ya kirani"...bai sake cewa komai ba yakai hannu ya amsa wayan daga hannunta..direct call log ya shiga aikuwa yaci karo da wata international number..yayi tsai yana karema number kallo nan take kuma ya gane number England ce...ya dago yana kallonta fuskanshi har ya sauya sbd 6acin rai yace"why did he called?.."murya a sanyaye tace"don't know..maybe sbd kids dinshi"..bata rufe baki ba cikin tsananin 6acin rai yace"but how dare he called you?..a ina ma ya samu numberki koda yake nasan qanwarshi ce zata bashi..wnn shine dalilinda yasa nace maku bana son mu'amala da mutanen nn..idan ba munafurci ba all these years meyasa bai ta6a kira ya tambayi kids din nashi ba sai yanxu?..after all what he's done to us har yanada guts din dazai daga waya ya kiraki?..is he Maddd?.."shiru kawai Aunty Sumy tayi tana kallon yanda ya rufeta da masifa as if shine yayanta..tasan duk wnn abun da yake yanayi ne akan gaskiyarshi and bazata ta6a ganin laifinshi ba..ita kanta kusan mutuwar tsaye tayi da taji voice dinshi ta kuma tabbatar da cewa Ismail nefa da gaske ya kirata after 5 long years...to me zai fada mata?..me xai fada wanda bai fada mata shi a lokacinda zasu rabu ba?...a hankali tace"ka kwantar da hankalinka plss"..bai bari ta karasa ba yace"i will have to deal with him myself"..bata ce komai ba tana gani yayi blocking number snn ya mika mata yace"he might use another number to call..yana kira ki fadamin"..a hankali ta gyada mishi kai shi kuma ya mike ya fita sbd 6acin rai ko mgnr daya kawoshi bai fada mata ba...sauke ajiyar zuicya tayi bayan ya fita ta koma ta kwanta kan gado tana sake sake..ita kanta tasan idan yaji anyi blocking dinshi zaiyi using wani number ya kira..idan ya kira din kuma batasan me zata fada masa ba as gabaki daya kanta a daure yake yanxun..ga kuma Bobby da tasan muddin ya samu labarin ya sake kira din shima ba karamin rikici zaayi dashi ba..she knows how stubborn he can be and ko kadan bata blaming dinshi because duk abunda yakeyi yanayi ne sbd su..tasan yanda yakejin ciwon abubuwan da suka faru a baya shiyasa har yanxun ya kasa mancewa...yanada son 'yan uwanshi sosai shiyasa duk wani abu daya shafesu yake bashi muhimmanci...ta lumshe idonta ta bude data tuna yanda yake dawainiya dasu Miemie tamkar shi ya haifesu..bama su kadai ba hatta ita kanta Bobby shine komai nata a yanxu..tun daga kan Mummy,Sab,Miemie da Ilham zuwa ita kanta shine ya zama tamkar mahaifi a garesu...duk tsawon shekarun nan bai ta6a bari sunyi missing wani abu ba ya zama gatansu sosai...kusan duk neman kudin da yakeyi a kansu yake karewa tunda shine komai nasu...kuma da yake Allah ba azzalumin sarki bane sai yake buda mishi a harkokinshi sosai kuma mishi albarka business dinshi har ya kawo level din da yake a yanxu...tayi nisa cikin tunani har batasan time din da ta fara hawaye ba..tausaya ma kansu takeyi yanda basu da kowa sai junansu a yanxu sai few daga familyn Mummy da suka rage..yanda familyn dad dinsu dana baban yaranta sukayi abandoning dinsu kawai sbd kasancewar Mummy ba bahaushiya ba...yanda sukayita truggling su kadai har Allah yasa suka yanxu...zuwa yanxu kuka takeyi sosai shiyasa bata cika son tana tunawa da past dinsu ba domin yin hakan yana dawo mata da baya gaba ne..gashi duk yanda takai da kokarin dakatar da kanta abun ya gagareta haka taci kukanta sosai ta godema Allah har 6arawon bacci ya lalla6o yayi gaba da ita.
Kai tsaye yana fita parking space ya nufa...driver na ganinshi ya mike da sauri yazo ya gaisheshi tareda tambayanshi motan da zasu fita...Bobby bai iya cewa komai ba sai juyawa da yayi yana kallon motocin..idonshi ya sauka kan wata Benz dinshi daya dade bai hau ba dan haka yace a fito da ita kawai..cikin hanzari Mr.Obi yayi clearing motan dukda dama ba wani datti ke gareta ba cox ana yawan wankesu snn ya fito da ita..ya bude back seat da kanshi ya shiga snn driver yaja motar bayan ya gama warming dinta suka fita daga gidan..kai tsaye yace ya fara kaishi Hospital.
Bai baro asibitin ba sai after 11 kai tsaye kuma suka wuce College...suna hanya ya kira Nur yace gashi nan zuwa shima yace dama already yana cikin college din shi yake jira...da yake akwai dan nisa tsakanin Hospital da College din basu suka isaba sai 12...bai fito daga mota ba ya kira Nur sai gashi ya fito daga office hihi ma ya da cikin motan nasu suka shiga Hostel din...as always sukayi parking daidai second gate snn suka fito zuwa ciki...daya daga cikin Matrons dake kula dasu tayi musu jagora har cikin apartment da abun ya faru..wutar apartment din ya dauke gaba daya..Nuru yace"amma daga wane room abun ya fara?.."ba musu Matron ta kaisu har cikin dakin..babu kowa ciki kasancewar an riga an sanar dasu cewa Provost zai shigo dan basu san har proprietor zaa zo ba...karema dakin kallo suka hau yi idanun Bobby ya sauka kan gadon Lamido da har yanxun ke shimfide da bedsheets na Man Utd..ya kalli gadon da kyau sai kuma ya ta6e baki cikin ranshi yana mamakin wai mace da football...duk iya dubansu basuga wani alama na wani abu ba har sun juya zasu fita ta fito daga kitchen hannunta rike da plate din indomie tana cewa"Billy you need to taste this..."magananta ya makale sakamakon mutanen data gani a dakin...yau ma dai kaman ko yaushe jessy ne a jikinta fara na Manchester sai wandon jessyn daya tsaya mata iya guiwa...gaba daya tsayawa sukai suna kallonta...ita kanta mutuwar tsaye tayo a wurin don kwata kwata batasan suna cikin dakin ba...juyawa tayi da sauri tana zazzare idanu kaman wanda tayi ma sarki karya...idanunshi ya sauka bayan rigan nata da aka rubuta POGBA da capital letters sai a kasa kuma aka zana katoton number 6...wani haushi yaji ya sake turnukeshi...ita kuma kaman wanda aka tsikara ta bude wardrobe da sauri ta rarumo hijab din Billy ta zura a jikinta...sai a yanxu Nur ya samu baki mgn"Lamifo is this your room?.."tana kokarin kakalo smile tace"yes sir..good afternoon "..yace" afternoon amma garin ya wuta yayi spark a nan?.."tayi kasa da kanta ganin irin kallon da Bobby ke mata tace"muma bamu saniba sir..kawai muna zaune sai mukaji wani kara"..bata rufe baki ba Bobby ya juya ga Matron data rakosu yace"waye dayan wanda suke tare a dakin?.."da sauri matar tace"bari a kirata Bilkisu ce"..daga haka ta fita sai gasu sun dawo tareda Billy da tayi kasa da idanu sbd idanun Dr.Bobby da ko kusa bata kaunar ya zuba mata su...sumi sumi ta karaso cikin dakin tareda tsayawa kusada Lamido da itama nata tun dazun yake kasa...shi kuma ya shiga binsu da kallon da suka tsana ya ganeta sarai itace ta rakata Clinic ranan da ya mata allura..baisan meyasa jikinshi ke bashi akwai dalilin yin spark din ba..kuma as far s Lamido is concern yasan abunda yafi haka ma zata iya aikatawa cox a dan ganin da yayi mata yaga alaman ba karamar fitinanniya bace..cikin voice din daya sake tsoratar dasu yace"now tell me..waye ya kusa haddasa min gobara a building?.."sukayi shiru ba mai kwarin guiwar yin mgn cikinsu...ya daka musu wani tsawa yace"are the two of you deaf?.."jiki na rawa Billy tace"Sir itace ta jona iron ta barshi a jiki"..tana rufe baki itama Aysha tace"Sir karya ne itace ta jona iron din ta tafi tayi bacc.."ragowar mgnr nata ya makale sakamakon idanu data hada dashi...wani irin kulululu taji cikinta nayi kaman zataje toilet..Allah ya zubama idanun nan nashi wani kwarjini na musamman dake sa mutum ya shiga taitayinshi da zaran ya hada ido dashi...shi kuwa Bobby da gayya yayi hakan don yasan duk iskancinta ta kalli cikin idonshi saita saduda...lokaci guda wasu hawaye suka ciko idanun nata gashi har yanxu ya kafeta dasu ko blinking bayayi...hatta Bilkisu da nata idanun ke kasa ji take kaman ana wura mata wuta a cikinta tsabar tashin hankali...maimakon ya dauke idanun nashi sai ya shiga takawa a hankali har zuwa inda take...ya tsaya dab da ita hannayenshi zube cikin pockets dinshi cikin wani stern masculine voice dinshi yace"Now speak"..idanunta ta lumshe hawayen dake ciki suka cigaba da gangarowa cikin ranta ko duk addu'an da yazo bakinta yi take dan yanda taji kaman an daureta da sarqoqi ne an kuma jefata a cikin kurkuku tsabar rudanin data shiga...ganin halin data shiga Nur yayi saurin matsowa inda suke saidai kafin yayi magana Bobby ya daga mishi alaman he shouldn't say a thing..ba yanda ya iya haka ya koma baya tareda rungume hannu yana binsu da kallo.
Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank..sai a tura evidence of payment ta 07063800556.
Rano✨
🤍Dr.BOBBY🤍
By Aysha Rano✨
Wattpad@aysharano22
07
Saida ya sake dinke fuskanshi tsaf snn yace"i said speak"..a hankali tayi kasa da kanta tana fidgeting fingers dinta kuma har yanxu gayyar hawaye basu dena sukuwa kan fuskanta ba tace"Sir bacci ne ya daukeni"..ba tareda ya dauke idonshi daga kanta ba yace"da kika jona iron din sai bacci ya daukeki right?.."a hankali ta gyada mishi kai...a fusace yace"how dare you do that?..qona min building kikeso kiyi?.."tayi shiru kanta a kasa..yace"i said qona min building kikesonyi?.."ba tareda ta dago ba ta girgiza kai alaman aah..shi kuma cikin wani additional 6acin rai da yaji yana saukan mishi yace"Billahi if you dare repeat this again you will see the devil side of me..are you mad da zaki jona abu a wuta snn kije kina bacci?.."ya karasa mgn yana wani huci..shi kanshi baisan daga ina wnn 6acin ran ke saukan mishi ba...Nuru ya karaso tareda kama hannunshi yace"zo mu tafi dan Allah what's done is done saidai a kiyaye gaba kuma"..baiyi masa musu ba ya bishi suka fita daga dakin matron ta bi bayansu...suna fita ya daddage ya fizge hannunshi dake cikin na Nuru snn ya karasa inda motarshi yake ya bude ya shiga...shima Nur karasawa yayi ya shiga snn ya dauko wayanshi ya kira mai gyara musu wuta yace azo a gyara a yau din nan...bayan ya kammala ya juya yana kallon Bobby daketa faman cika yana batsewa yace" Bobby are sure you are alright?.. wnn 6acin ran duk na meye?.."ko kallon inda yake baiyi ba balle yasa ran samun amsa...shima baiyi expecting amsan nashi dan haka yaci gaba da mgnrshi"you shouldn't have acted like that sai kace secondary school?..besides kudi fa suka biya"..tun kafin ya rufe baki ya juyo yana kallonshi da wani irin karaji yace"seriously bayansu kake bi?..yanxu da sun konamin building zaka iya biyana ne?..kuma da suka biya kudi ai ba kudin building dina suka biya ba kudin zama cikin Hostel suka biya so dole inyi mgn idan naga zaayi min 6arna"...shiru kawai Nuru yayi yana kallonshi deep down yasan da akwai abunda ke damunshi...ya tabbata wnn fushin ba iya na an kusa kona masa building bane dole da akwai wani abun a kasa...har suka koma cikin makaranta ba wanda ya sake cewa komai a cikinsu...kafin su fita Nuru yace zai sauka dan bai gama aiyukan da yakeyi ba..babu wasting of time driver yayi parking shi kuma ya bude motar ya sauka snn suka cigaba da tafiya...bayan fitarshi Bobby ya sauke wani numfashi da yake rike dashi tun dazu tareda jingina jin seat din da yake hadi da lumshe idanu...baisan wane irin bala'i bane ya hau kanshi yau din nan...shi kanshi haushin kanshi yaji yanaji bai kuma san dalili ba...har ga Allah maganan da Nuru ya fada yasan its not that far from the truth..bai kamata yayi acting kaman yanda yayi ba amma ko Allah ya san shi kanshi baisan abun da ya hau kanshi ba a lokacin..bai kuma san daga ina duk wnn masifan yayita tahowa gareshi ba...kawai shidai ya tsinci kanshi cikin tsananin 6acin rai which he couldn't control..ya lunshe ido yana sake budewa har yanxun idanunshi basu dena hasko mishi ita sanye da kayan 'yan ball ba...ya saki wani tsaki kuma wai sbd tsabar iskanci shine ta juya musu baya wato tunda sun gama ganin gaba su kalli bayan ma knn...yau ya sake tabbatar da cewa ita din sangartacciya ce..idan ba haka ba why yarinya mace kamarta zaa barata tana supporting wani football club kuma har a gidansu a biye mata ana wani siya mata jessy da gajeren wando tana sawa..wai har bedsheet na Manchester sai kace wata namiji...runste idon yayi yana wani girgiza kai duk a kokarinshi na ya dena ganin pictures din nata saidai to no avail...gaba daya yaji yayi dana sanin zuwa Hostel din ma at the first place..daya sani da Nur ya kirashi kawai yace mishi bazai samu daman zuwa ba da shknn babu shi babu ganin wnn masifa...wnn yarinyar ya rasa wace iri ce ita da take kokarin yi masa kutse cikin rayuwarshi...ya tabbata masifan daya rufeta dashi hadda tsanar da yayi ma 'yan garinsu yasa shi haka...kilan da bai san 'yar Gombe bace bai zama lallai ya aikata abunda yayi ba...jingina ya sakeyi yana kara sakin wani tsakin duk ranshi yabi ya jagule...a daya 6angaren kuma ga wancan mara kunyan da yake kokarin sake kustowa cikin rayuwar 'yar uwarshi again..baisan me yake takama dashi ba har da zai dauki waya ya kirata sbd bashida kunya...sai kuma wnn kaddararren lecture da Mummy tace sai yaje yayima yaran can..shi sam wnn abun bi gamsheshi ba...baima san taya zai fara shiga class ya rike marker yace zaiyi musu lectures ba..baisan ta ina zai fara ba...a takaice har suka kai gida bai dena wadan nan tunane tunanen ba..gaba daya kanshi ya dauki wani zafi kaman wanda ke amfani da wutar lantarki.
Tunda suka fita Lamido ta zube nan kasan dakin tana sakin wani marayan kuka...Bilkisu ma batasan lokacinda ta durkusa nan kusa da ita ba suka taru suka hada kai sunata kokawa abunsu...if you see yanda suke kuka zakayi tunanin mutuwa akayi musu...saida sukayi na sama da one hour Billy ta dakatar da nata snn ta shiga rarrashin 'yar uwarta amma a banza...ta kwashi wasu 30 mins tana rarrashi ganin ba denawa zatayi ba ta mike tareda rage kayan jikinta ta fada bathroom...wanka tayo tareda alwala snn ta fito ta gabatar da sallahn azahar da akayi tun dazu basu tashi sunyi ba suna aikin kuka...har ta idar da sallahn Lamido bata dena kuka ba...ta karasa wardrobe dinta ta dauko dan dogon riga mara nauyi tasa snn ta sake komawa gun Aysha data koma kan gadonta ta kwanta tareda lullubewa da blanket...kawai ayyanawa take da ace daddynta irin easy going mutane ne da babu abinda zaisa ta sake kwana a FCNM saidai kawai su ganta a gida...to sanin da tayi kota fada mishi ma ba goyuwa da bayanta zaiyi ba kilan ma saidai ta janyo ma kanta fada yasa ba yanda ta iya haka nan zata hakura tacigaba da zama ko bataso...tun dazun wayanta ke vibration amma ta kasa tashi ta dauka...Billy da ta gaji da jin vibration din ta dauka tareda picking call din ta kara a kunne...a daya 6angaren Hamma Najeeb yace"Maama are you mad anata kiran wayanki bakya dauka?.."cikin voice dinta da bai gama warewa ba Billy tace"Hamma ba ita bace"..da sauri yace"Subhanallah Bilkisu what happened?.. you sound somehow..ina Maaman take? "..a hankali ta juya tana duban Aysha da har yanxun ke kudundune kan gado tace" Hamma gata...kuka takeyi tun daxu"..a dan rikice ya sake fadin"Ya Ilahi meya sameta?..bata wayan muyi mgn"..ba musu ta karasa ta yaye blanket data lullu6e dashi ta saka wayan a speaker snn ta ajiye kusada face dinta tace"Hamma gashi nan na bata"...da sauri yace"Maama can you hear me?..what happened?.. why are you crying?.."da sauri ta mike zaune tareda daukan wayan ta rike a hannunta har yanxun bata dena hawaye ba tace"Hamma bana son makarantan nan please..inaso in dawo gida dan Allah"..hankalinshi duk ya tashi yace"Aysha me yake faruwa ne wai?..me akayi maki?.."tana kuka tayi mish bayanin duk yanda sukai da proprietor daxun...yayi shiru har saida ta gama snn yace"to ki kwantar da hankalinki ina nan zuwa gobe kinji..first thing in the morning zan taho inshaAllah amma ki dena maganan dawowa gida kinsan daddy bazai yadda ba"...ta kai hannu tana goge hawayenta tace"Hamma to nidai kazo dan Allah...i really want to see you"..yace"ba damuwa zanzo inshaAllah..stop crying kinji"...gyada mishi kai tayi kaman yana kallonta...saida ya tabbata ta dena kukan yace"to bari in kaima Ammi zakuyi mgn dama itane tace in kiraki and karki nuna mata wani abu ya faru okay?.."a hankali tace"toh"...bai sake mgn ba ya fita zuwa parlor inda gaba daya suke zaune snn ya mikama Ammi wayan yace"yauwa Ammi gata"..Ammi ta amsa wayan tana fadin"kun gama sirrin naku knn?.."baice komai ba yayi daria ita kuma ta kai wayan kunnenta hade da sallama..a hankali tace"wa'alaiki salaam Ammi ina yini"..tace"lafia lau ya jikin naki?.."tace"naji sauki Ammi..ina Yusra"..Ammi tace"Yusra gata nan..kina jina?.."da sauri tace"inaji Ammi"..."wani mgn kika kira fiddausi kika fada mata?."..lokaci daya Aysha ta wani zaro ido hadda su rufe baki tace"aunty fiddausi wai?..Ammi me zan fada mata ni toh?.."bata rufe baki ba Ammi tace"zakici ubanki wlh..kin kirata kin hadata da 'yar uwarki shine yanxu kike tambayana me kika fada mata?.."ta marairaice tace"wlh Ammi kome Husna ta fada karya take..ya zaayi ma ki yadda na da mgnrta ni da nake babba baki yadda da nawa ba?."dan tabe baki Ammi tayi tace"da kike babba ai ba hankali gareki ba har yanxun..kuma kome kika fada mata maza maza ki kirata yanxu kice mata karya kike dan ba cikakken hankali gareta ba itama fiddausin"..batasan lokacin da murmushi ya dan subuce mata ba tace"kai Ammi maman tawa?.."Ammi tace"Maman taki fa shiyasa duk wani rashin mutuncinta ai kikayi gado..lokacin da muna gida Fiddausi ai ba karamar fitinanniya bace"..batace komai ba sai daria da tayi...Ammi tace"iceko kina kiran daddy ki gaisheshi?.."tace"ina kira Ammi..ko jiya saida na kira ban sameshi ba"..tace"to ki sake gwadawa yau ko gobe..ya danyi tafiya ne amma nasan a yau ko goben zai dawo"..tace"InshaAllah zan kira Ammi..ki bawa habibty mu gaisa plss"..ba musu Ammi ta mikama Yusra wayan snn ta bar parlon...Yusra ta amsa da murnanta saidai kafin tayi mgn Husna ta kwace wayan tareda kaiwa kunnenta tace"to Adda ni da baki nemana sai me?..duk tsiya dai ni kika fara sani kafin Yusran"...wani murmushin Aysha ta saki tanajin yanda lokaci daya duk wnn damuwan data shiga na tafiya tace"kuma dana fara saninki ai ba cewa akayi dole sai nafi sonki ba"...Husna ta wani murguda baki kaman tana ganinta tace"kuma ko Hamma zaizo na fasa biyoshi wlh"..tana gama fadin haka ta ajiye wayan tayi gaba abunta...Yusra ta dauka tana murmushi suka fara mgn...duk abunda suke Hamm na zaune yana kallonsu...lokaci daya Aysha ta mance da wani 6acin ran proprietor sukaita hira da qanwarta...basu suka gama ba saida ya kar6e wayan da kanshi...sai a lokacin ta samu ta shiga toilet tayo wanka snn tazo ta shirya ta sake hayewa kan gadon ta kwanta sbd Billy bata dakin...tana kwanciya sai abubuwa da suka faru suka shiga dawo mata...ta tuna yanda ya daure fuska ya kuma tsareta da wnn shegun idanun nashi mai kama dana aljanu ta bakin na Billy...batasan wane irin magic ke gare idanun nashi ba da yana dora mata su taji kaman an tattaro duk wani rashin nustuwa da tashin hankali na duniyar nan an dora mata su akai...anya kuwa mutumin nan ba wani abu yakema idanunshi ba?..tana cikin tunanin Billy ta shigo dakin ta mika mata wayanta dake hannunta tace"kar6i ki ce masa ya dena kirana dan Allah..haba! tun daxun yaketa faman kira ko yanaso ya shanyemun caji ne?.."ba musu Aysha ta mike zaune tareda amsan wayan daga hannunta taga Lamido's bestie ke kira...dariya ta saki sosai dan har gobe bata dena dariyan wnn sunan da tayi saving number besty dashi..wai Lamido's bestie sai kace wani yace bestienta ne ita...har kiran ya katse wani ya sake shigowa bata dauka ba...Billy data kulu tace"malama idan bazaki dauka ba bani wayata dan Allah"..bata bata wayan ba tayi kokari ta tsayar da dariyan snn tayi picking tareda karawa a kunne...yanajin an dauka yace"Haba my Billy"..Aysha ta wani zaro ido jin abunda ya fada hadda toshe baki tace"besty ba ruwana wlh"..dan dariya shima yayi kafin yace"inata kiran wayanki bakya dauka itama kuma wnn 'yar rainin hankalin sai wani jamin class takeyi taki daukan wayan sai kace saurayinta"..yana rufe baki Billy da taji kaf abinda ya fada ta daga murya tace"Allah ya kiyaye na rasa dawa zanyi soyayya sai kai...kuma a kashe a bani wayana sai ka kira wayarta ku cigaba da shirmenku"..dariya yasa sosai Lamido na tayashi...saida sukayi me isarsu snn yace"besty wai an fasa zuwa saloon din ne?..kin ganni fa tun dazu a bakin gate dinku ina jiranku"..tana dan girgiza kai tace"anya zuwa saloon din nan zai yiwu kuwa besty?..i don't feel like going out"..tana rufe baki yace"kuma shine baki kira kin fadamin ba saida na baro gida nazo?..fadamin me yake damunki da zakice you don't feel like going out?..na sanki da son yawo fa besty"...tayi shiru tanajin yanda 6acin ran dazu ke son dawo mata sabo fil...shi kuma jin tayi shiru sai yace"alright ki fito waje sai muyi mgn..ina bakin gate"..bata ce komai ba ta kashe wayan snn ta mike ta zura hijab tace ma Billy"taso muje"..tayi mata wani kallo tace"je ina?.."tace"wajen besty mana bakiji yace yana bakin gate ba?.."tsaki ta saki tana kokarin hawa kan gadonta tace"sai kin daw.."bata gama mgnr ba ta shiga janta suka fita daga dakin tunda already da akwai hijab a jikinta...har suka fito waje bata dena jan hannunta ba itama kuma bata dena kokarin kwatan hannun nata ba har suka karasa inda yake...ya bude mota ya fito yana kallonsu one by one kafin ya danyi murmushi yace"to a bani labari menene ya faru?.."Bilkisu ta daure fuska tana kawar da kai Lamido kuma tace su fara samun wuri su zauna first... duk basuyi gardama ba suka karasa wani dan wuri da aka zagayeshi da flowers tsakiya kuma cement chairs ne suma aka zagaye wurin dasu suka zauna...suka danyi shiru na wani lokaci kafin Aysha ta bashi labarin duk yanda sukayi da proprietor daxun...shi kanshi baiji dadi ba kuma suma yaga yanda duk Mood dinsu ya sauya dan haka yace ko baza'a je saloon ba shi yanaso ya kaisu wani wuri...Bilkisu ce ta fara cewa bazataje ba kunsan mutumiyar taku😂sai da kyar suka samu suka lalla6ata ta amince ta bisu..daga nan basu koma ciki ba suka shiga motanshi suka wuce..kai tsaye Ten to Ten ya fara kaisu yayi musu ordern abinci mai kyau yace suci dan yasan yau da kyar idan sunyi lunch gaba dayansu...ba suyi musu ba kuwa sukaci dan da gaske ba abinda sukaci tun breakfast... suna barin nan ya kaisu park nan kuwa duk suka ware suna enjoying kansu...bayan sun bar park din suka shiga Ado Bayero Mall sukayi shopping snn sukai branching a gidan grandmother dinshi dake Tarauni...tana zaune parlor tanashan nono da fura suka shigo...ta dago tayi musu kallo daya tareda ta6e baki snn ta cigaba da shan furanta...saida suka karasa ciki suka zauna Sa'eed yace"Hajjaju baki ganni da mutanen naki bane?.."sake ta6e baki tayi ta kur6i furanta kafin tace"ai ni ba ruwana da mutanen nan yanxu...tsakani da Allah suna cikin garin nan yaushe rabon da naga kafafunsu cikin gidana?.."dan murmushi Billy tayi tace"Haba Hajiya kinaso Sa'eed yaji kanmu knn?.."tace"yo jin kai na nawa kuma Bilki?..ai saidai kar a kuma"...Aysha daketa murmushi itama tace"to munji mun dauki laifinmu Hajiya kuma mun bada hakuri inshaAllah baza'a sake ba..daga yanxu duk weekend sai bestie ya kawomu mun gaisheki"...harara mai kyau ta watsa mata tace"sarauniyar 'yan dadin baki..to na hakura dai ba dan halinku ba..ya kuke ya karatun?.."sukace"karatu Alhamdulillah Hajiya..ya gida"..tace"lafia lau..ya wajen iyayen naku?.."Sa'eed dai na zaune yana kallonsu..lokaci guda i hira ya 6arke a tsakaninsu dama hajiya ba daga nan ba akwai labari su din ma kuma ba baya bane...a takaice sai da sukai sallahn magrib suka bar gidan...kai tsaye ya maidasu Hostel kowacce rikeda kayan kwadayin da suka siyo a shoprite..duk wnn kunci da 6acin rai da suka shiga daxun yayi disappearing..besty kam yayi kokari.
Wahsegari sunday karfe 7 daidai Bobby ya dannawa Nuru kira...bai dauka ba sai a karo na biyu ya daga cikin magagin bacci...Bobby ya dan ta6e baki jin bacci ma yake yace"kana jina?..ka fadama students din naka zan shigo 8 muyi lectures din..and tell them duk wanda ta wuce 8 batazo ba batada C.A"...yana gama fadin haka bai tsaya jin me zai fada ba ya kashe wayanshi...da mamaki sosai Nur yabi wayan da kallo kafin ya sake danna masa kira...saida ya kusa katsewa snn ya dauka..da sauri Nur yace"Bobby me kake nufi ne wai?..i don't understand"..babu gardama ya sake repeating abunda ya fada daxun..Nur ya wani marairaice yace"amma Bobby ka duba time kuwa ka gani?..this is past 7 yanxu har yaushe aka kira aka sanar dasu su fito gashi yau weekend"..a takaice Bobby yace"that's non of my business.. ba kai kakeso inyi musu lectures ba?..to gashi nan zanyi and wallahi duk yarinyan da ta sake na rigata shiga class din nan tayi loosing c.a so kindly call and ask them to start coming tun kafin 8 din yayi"...still yana gama mgn ya kashe wayanshi...Nur ya girgiza ya shiga neman number Lamido ya samu ya kirata...yasan duk meyasa Bobby ke wnn abun sbd yayi amfani da Mummy ya tilastashi yin abunda baiso ba shine shima yakeso ya rama ta wnn hanyan...yana zuwa kan numberta yayi dialing amma har ya katse bata dauka ba..shi kuma bai hajura ba ya sake kira..yana dab da katsewa ta dauja cikin muryan bacci tace"good morning sir"...yace"Morning Lamido inaso ki sanar da duk 'yan class dinku su shigo college zuwa 8 an samu wanda zaiyi taking over reproductive health dinku"..da sauri ta kalli wall clock dake manne cikin dakin nasu kafin tace"but sir this is 7:15"..yace"i know just try your best..tell them duk wadda batayi attending ba tayi loosing c.a and i want yiu to be fast about it please"..a hankali tace mishi"ohk"..snn ya kashe wayan...Billy dake bacci ta fara tashi tayi mata bayani snn ta dauki wayanta ta kunna data tayi musu bayani ta voice note ta tura a group snn kuma ta dhiga kiran duk wanda tasan zai iya sanar da wasu tana sake fada musu...Billy kuma fita tayi tayi announcing wa 'yan class dinsu dake cikin hostel din...saida ta tabbata ta fadama kowa snn ta koma daki..itama Aysha daidai lokacin ta gama kiran duk wanda zata sanar ma...tana duba agogo tana 7:35 dan haka ta mike da sauri ta fada bathroom tayi wanka sharp sharp tana fitowa itama Billy ta shiga...karfe takwas saura mintina goma suka gama shiryawa..ita tana sanye cikin abaya sky blue tayi rolling mayafin rigan..Billy kuma dogon riga ta saka na atampa ta daura dankwali sai veil dinta a kafada...koda suka fita compound drivern school bus har ya fito dan haka suna gama fitowa suka shiga motan zuwa cikin makaranta...motan na gama parking duk suka fito suka nufi class dinsu makarantan yayi tsit sai few students dake shigowa karatu...mutum 8 kadai suka samu a class din sunzo idan aka hada dasu da suke cijin hostel su 15 sun zama 23 knn out of 38...hankakinta duk yabi ya tashi ta dauki waya tana kokarin sake kiran wasu kiran provost ya shigo wayan...tayi picking da sauri tace"Sir wlh har yanxu da yawa basu karaso ba..mu 23 ne kadai a class din"..yace"no problem ki fada musu suyi sauri suzo before 9 ni zanyi kokari in rike maku shi har zuwa 9 din"...tace"thank you sir"..snn ta katse wayan...group dinsu ta sake shiga tayi announcing cewa an kara musu 30 minutes dan haka kowa yayi sauri ya karaso.
Cikin ikon Allah kafin 9 din gaba daya sun hallara...shi kuwa Bobby yana office din Nur time to time yana duba agogo...9 din nayi daidai ya mike duka fito daga office din tareda Nurun...suna haurawa sama ta window ya hangosu zazzaune cikin class din kowa da kalar kayansa sai ya dan dakata da tafiyan yana duban Nur yace"and why are they not in uniform?.."Nur yace"dama lectures din weekend bada uniform suke zuwa ba gaskia..kuma kaima bakace ace musu su sa uniform ba ai"..bai sake cewa komai ba suka karasa class din hannayensu zube cikin aljihu.
Masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank..sai a tura evidence of payment ta 07063800556.
Rano✨
🤍Dr.BOBBY🤍
By Aysha Rano✨
Wattpad@aysharano22
08
Suna shiga gaba daya class suka hada baki suna gaishesu..Nur ne kadai ya amsa musu da "morning class ya weekend?.." suka amsa da lafia yace"well as a result of maternity leave da malaman Reproductive Health dinku ta tafi nasan you people do miss alot a karatunku ga kuma exams dake approaching...Class Rep dinku tazo ta sameni da maganan and our Generous Proprietor here says he will assist you guys har kuyi covering syllabus dinku"..ya karasa mgn da wani killer smile a fuskanshi tareda dan juyawa ya kalli Bobby dake tsaye rungume da hannaye yana sauraronshi...lokaci daya Class din ya dauki tafi jin Proprietor da kanshi yace zaiyi assisting nasu nan kuwa basu san saida aka kai ruwa rana before ya amince ba...Lamido da Bilkisu kuwa kallo daya sukayi masa gaba daya sukayi kasa da idanunsu..Billy dai addu'a take kada Allah ya kawo dalilinda zaisa wnn shegun idanuwan nashi su sauka a kanta..ita kuma Aysha hararan gefen ido take binshi dashi cikin ranta tace"inyamurin banza inyamurin wofi"..daidai nan kuma Nuru ya dubi Bobby yace"to Dr.Bobby bismillah"..daga haka ya koma can karshen class din ya samu wani empty seat yayi zamanshi a wurin...shi kuma Bobby ya dan kalli class din har yanxun yana rungume da hannu thinking from where to start...saida yayi shirun amost 3 mins kafin yace"where do you guys stop?.."daya daga cikin 'yan class din ta fada mishi last topic da sukayi...yana dan gyada kai ya tambayi course outline nan ma suka bashi...saida ya gama studying course outline din snn ya ajiyeshi kan table dake gabanshi yace"well according to the course outline kunada remaining 5 topics to cover before the exams..now zamuyi kokari muyi covering 2 topics the ramaining ones kuma zakuyi dividing kanku into 3 groups..each group su dauki one topic suje suyi studying dinshi sosai zuwa ranan Thursday zakuyi presentation..do u get me?.."gaba daya suka amsa da sun gane...shi kuma ya juya ga board dinsu yaga akwai rubutu a jiki sai ya sake juyawa garesu yace"who's ur class rep?.."gaba daya suka nuna Lamido...shi kuma ya wani daure fuska ganin itace dan lokaci daya incident din jiya ya fado masa a rai...itama daure nata fuskan tayi snn ta mike kanta a kasa..dukda ba kallonshi take ba tanajin wnn shegun idanun nashi a kanta..."come and wipe the board"..ya fada still looking at her...batayi musu ba ta fito tayi wiping board din ta juya zata koma ya sake fadin"da fingers dina kikeso inyi maku rubutun?.."bata juyo ba ta karasa seat dinta ta bude locker dinta ta dakko wani pink marker ta kai mishi snn ta sake dawowa ta zauna...duk wnn abun dake faruwa Dr.Nuru na bayan class din yana kallonsu...murmushi kawai yake yana girgiza kai cikin ranshi yace"zamuga yanda za'ayi wnn lecture"...sunan topic din Bobby ya rubuta jikin white board snn ya juyo yana facing dinsu yace yanaso daya daga cikinsu ta danyi briefing dinsu about the topic before he starts...wajen mutum biyar ne suka daga hannu shi kuma ya shiga binsu da kallo daya bayan daya yanaso yayi choosing mutum daya a cikinsu karaf idonshi suka fada kan Lamido...ya dage gira yana kallonta da kyau hadda sakin wani dan iskan smile cikin ranshi yana ayyana ita zaiyi selecting dukda ba daga hannu tayi ba kawai dai yanaso yana brain dinta da kullum Nur ke cewa she's genius she's this she's that..yau yanaso ya kure brain din nata...daga nan inda yake tsaye yayi pointing dinta da finger dinshi yace"You.."da sauri ta dago idanunta saidai suna sauka cikin nashi ta sake mai dasu kasa...still yana duban inda take yace"fito kiyi briefing namu akan topic din ba kece class rep ba?.."ya karasa mgn still da wani killer smile a face dinshi...ita kuwa qala batace ba ta mike daga seat dinta ta fito...ta juya taga sunan topic daya rubuta snn ta sake juyawa tana facing class din making sure bata kalli inda yakeba don kada ma ya zuba mata wadan nan idanun nashi yasa ta kasa ta6uka komai...bayani ta shiga yi musu dalla dalla kaman ba briefing dinsu yace tayi ba...tunda ta fara dama ya jingina da wall ya wani lumshe ido yana sauraronta sam baiyi tunanin zata iya ba...a yanda take explaining ma sai yakega kaman koshi da yake certified gynaecologist bai zama lallai ya iya yanda tayi ba..sam baiji dadin hakan ba kuma dan so yayi ya kunyatata a gaban Nur da kullum yake kiranta genius...yanxu kam ko da bai yadda she's genius ba tabbas yasan she's brilliant tunda har ta iya explaining abunda ba'a koya mata ba haka..daga yanayin yanda take magana kuma ya fahimci kaman she's used to it dan babu wani alaman tsoro ko rashin sabo a tattare da ita...duk sai yaji ranshi ya fara 6aci all of a sudden...hada ido sukayi da Nur aikuwa ya dage gira irin ya kaga?..shi kuma ya dauke kanshi ba tareda ya kalleta ba yace ya isa haka ta koma ta zauna...6oyayyen ajiyan zuciya ta saki cikin ranta tace"Finally"..sa zahiri kuma batace qala ba ta wuce ta koma seat dinta..shi kuma ya dora daga inda ta tsaya...bayani yake musu sosai shima irin bayanin da bai ma ta6a zaton zaiyi musu ba..suma kuma class din suna participating sosai...nan take yaji ashe yin lectures dinma is not as bored as he thinks...a da kawai gani yake irin boring lectures zasuyi sai kuma yaga ba haka ba baisan ko sbd class din suna participating bane...yana karasa topic din data fara ya shiga yi musu dayan shima kuma suna understanding sosai...a takaice saida suka dauki almost 3 hours kafin su gama...bayan ya gama amsa tambayoyinsu ya sake jaddada musu mgnr presentation da zasuyi ran Thursday snn yayi musu sallama ya fita mai girma provost yabi bayanshi...har ya fara sauka stairs Nur ya bishi da sauri suka shiga sauka tare yace"ko baka fada ba nasan u enjoyed it"...harara kawai ya watsa mashi baidai ce komai ba...shi kuma ya saki wani smile tareda dan lowering voice dinshi yace"and ya kaga brain din Lamido?..hope you are now satisfied?.."tsaki kawai Bobby ya saki yaki kuma kulashi...saida suka fito yace mishi"zamuyi dropping dika ne?.."Nur yace"don't bother nazo da mota kawai dai dan Allah kace ina gaida su pretty idan kaje gida"...bai sakeyi mashi mgn ba ya shiga mota bayan driver ya bude mishi..shima drivern ya zaga ya shiga snn ya tayar da motar suka tafi...shi kuma Nur saida ya shiga office ya dauko wasu files snn ya shiga nashi motan shima ya wuce.
Da wuri suka fito daga Class din as a result of message data gani na Hammanta yana ce mata sun karaso...suna fitosa ta hango motanshi ai batasan sanda ta taka a guje zuwa wurin ba...Bilkisu ta shiga girgiza kai tana fadin"Allah nunamin randa zaki girma Lamido"...tun kafin ta karasa duk suka bude mota suka fito...Hamman nata ne da Yusra sai kuma Husna mai cewa ko zaizo bazata zo ba...kai tsaye tana isa ta wani d'ane jikinshi tana dariyan farin ciki...shi kuma ya rabata da jikin nashi yace"ke har yanxun bakisan kin girma ba koh?.."daria ta saki tareda dan kwa6e fuska tace"nidai ban wani girma ba"...murmushi kawai yayi ya girgiza kai yasan Maama will never change...ita kuma sai ta juya ta janyo Husna da Yusra ta rungumesu gaba daya kafin ta dago tana cewa Husna"kikace kuma bazaki zoba?.."murguda baki kawai Husna tayi batace komai ba...a daidai lokacin Billy ta karaso garesu aikam Husna na ganinta ta karasa gareta ta wani rungumeta kafin ta dago tace"nima ga yayata nan"...murmushi kawai Billy tayi tareda kama hannun Husna suka karasa ta fara gaida Hamma...bayan sun gama gaisawa tace ya kamata su karasa daga ciki...kaman jira suke kuwa duk suka shiga mota zuwa cikin Hostel...daidai inda ake parking yayi snn suka bude mota suka fito...yace su shiga ciki dasu Husna shi da akwai inda zaije ya dawo...su Aysha hadda wani marairaicewa akace"amma dai Hamma ba dadewa zakayi ba koh?.."ya saki murmushi ganin wnn shagwa6an nata da bai karewa yace"bazan dade ba Maamata...da wuri zan dawo muyi mgnr daya kawoni garin"..nan dai sukayi sallama dashi ya wuce su kuma suka shiga ciki...direct dakinsu Billy ta bude suka shiga Husna tayi wani irin tsalle ta dire akan gadon Billy tana fadin"nima dai ina candy FCNM din nan taku zance daddy ya kawoni...makarantan ba karamin burgeni take ba"...Aysha data kama Yusra suka zauna kan nata bed din tace"ba wani FCNM da zakiyi yarinya...ni kaina yanxu da za'a cireni so nakeyi dan bakisan yanda take ba shiyasa kike sonta"...tace"koma dai ya take Allah Adda ina sonta"...Billy ta fito daga kitchen dauke da lemuka da ruwa sai Cake dasu meatpie ta kawo musu..ta nemi wuri ta zauna kusada Husna tace"to me kukeso a dafa muku?.."Yusra tace"Hamma yace idan ya dawo zai kaimu eatery ko Adda?.."Aysha tace"yes Billy kawai mu bari ya dawo sai ya kaimu muyi lunch dinmu a waje"..Billy tace"to ku fara cin wnn din"..ba musu su hajia Husna aka sauko aka dauki lemo da cake za'a fara sha sai tace"wai ni ina bestynku ne kam?..tunda mukazo banji wata tayi mgnrshi ba"..dan ta6e baki Billy tayi tace"bestynta dai"...Husna na daria tace"aah Adda Billy hadda ke wlh"...tace"God Forbid"...Lamido dake sauraronsu tana daria itama tace"Husna karki damu anjima kadan zaki ganshi a nan indai besty ne...baima san zakuzo ba nasan da tun daxun yazo"...Husna data fara shan lemo da cake dinta tace"ya kamata yaxo mu gaisa dai gaskia...Yusee bazaki ci cake din ba koh?.."Aysha da kanta ta dauki lemo da cake din ta mika mata itama ta amsa ta fara ci.
Karfe daya da wajen rabi Hamman nasu ya dawo...nan ya kirasu a waya duk suka sake shiryawa snn suka fito ya kwashesu suka tafi...basu tsaya iya eatery kadai dan har shopping saida ya kaisu dukda suna ce mishi basu bukatan komai and sun kusa yin hutu Hamma Najeeb bai sauraresu ba saida ya kwasan musu duk wani abu da yasan students kamarsu suna bukata...su Husna kuwa kayan kwadayi sukaita kwasa itada Yusra kaman ba gobe...kan hanyansu na komawa Hostel Husna taga wani sabon cinema a kan zaria road tace"Hamma dama ka shiga damu cinema muyi kallo wlh..kasan inason kallo a cinemas"...shidai baice komai ba sai kai daya girgiza mata...bayan sun koma hostel suka samu wani wuri kaman garden suka zauna su Yusra nata cin kayan da suka siyo shi kuma ya dubi Aysha sosai yace"i hope kin hakura da batun komawa gida koh?.."ta wani rausayar da kai tace"ai nasan daddy bazai yadda ya cireni ba"..yace"good u understand that..yanxu inaso ki zama more careful kan komai da zakiyi..kinga ko a gida dama kinada wnn careless din sai ki jona abu a wuta kice zaki tafi wani wurin ki barshi ko kuma kice kin manta dashi..yanxun da yazo da tsautsayi wuta ya kama dakin fa kinga da gaba daya konewa zakuyi"...tana wani turo baki tace"na dena Hamma"...yace"Good...kema Bilkisu inaso ki kara kisa min ido a kanta sosai...duk kikaga ta jona abu zaka tafi ta barshi ki kira koni ko Ammi ki fada mana"...da sauri Billy tace"inshaAllah Hamma"...daga haka ya mike zuwa mota sai gashi ya dawo da wani da akayi wrapping kaman gift guda biyu...ya mikama Aysha daya itama Billy ya bata daya...Aysha ce ta fara bude nata taga wani hadadden mug fari mai daukeda logon Man United sai wani sbu kaman doll da akayi mishi siffar Pogba yana sanye da kayan ball sai kuma hannunshi rikeda ball din a can kasan abun aka rubuta Man of the Match sai kuma latest jessy dinsu red and black mai daukeda logon Man U itama bayanta kuma sunan Pogba ne da katon number 6 a jikin wandon ma haka...sbd tsabar farin ciki Aysha batasan sanda ta rungumeshi taba daria ba...wnn karon shima rungumeta back yayi yana ganin how happy she looks...dama yasan yanda take son Manchester da Pogba dole ma zataji dadin gift din shiyasa ya siyo mata...saida suka gama hug dinsu snn ya dagota yana kallonta yace"hope u like it"..da sauri tace"i like it mana sosai ma Hamma...kasan tsakanina da Pogba ai"...yace"na sani shiyasa na siyo miki"...tace"nagode sosai Hammana Allah ya saka maka da alkhairi ya baka mata ta gari"...ya dan ja cheeks dinta yana daria yace"Ameen Mamana"...Husna ta hade rai tace"ai dama Hamma munsan zaman da zamuyi dakai...nasan wlh kafi son Adda akanmu"...murmushi kawai yayi yace"Husna kenan"..ya juya ga Billy dake rikeda nata gift din tana kallonsu tana murmushi...yace"if you are done smiling kema saiki bude mana naki mu gani"...ba musu ta dakatar da murmushin da take ta shiga bude nata...komai na ciki iri dayane the only difference shine ita nata na PSG ne madadin Manchester doll din kuma na Mbappe instead of Pogba...sosai murmushin dake fuskanta ya fadada...sai taji itama kanta da d'an uwanta ne ba abunda zai hanata rungumarshi tsabar farin ciki...full of excitement tace"Nagode Hamma Allah ya saka da alkhairi"..yace"Ameen Hajia Bilkisu..yanxu bari muzo mu dauki hanyan kunsan tafiyanmu da nisa"...nan da nan Aysha ta kwa6e fuska tace"Hamma tun yanxu?.."yace"banaso muyo dare ne Maama kuma anjima kadan zakiga Ammi ta fara kira so gara mu tafi sbd mu sauka da wuri"...bata kuma cewa komai ba sai turo baki da tayi...gaba daya suka mike suka fita daga wajen...suna zuwa jikin motanshi kafin su shiga motan Sa'eed ya karaso wurin...yayi parking da sauri ya fito zuwa inda suke yace"Hamma badai tafiya zakuyi ba?.."yace"wlh tafiya zamuyi Sa'eed banaso muyi dare a hanya"..Sa'eed ya juya yana duban su Husna yace"yammata"..tana wani fari da ido tace"sunana Husna Lamido"...yace"to sannu Husna Lamido ya hanya?.."tace"Alhamdulillah Hamma bestie"...ya dan wara ido kafin yace"har yanxu Hamma bestyn nan dai?.."tace"eh mana ba bestie sunanka ba?.."yace"sunana Sa'eed"..ta wani makale kafada tace"oh oh nidai hamma bestie zance"...bai sake mgn ba sai murmushi da yayi...ya karasa wurin Yusra suka gaisa itama tana cewa hamma besty shi kuma yana bayaso...haka dai suka gama gaggaisawa daga nan suka shiga mota suka tafi...Lamido tabi motan nasu da kallo idonta na cikowa da hawaye...Billy ta kwashi gifts dinsu tayi ciki shi kuma Sa'eed ya jata suka zauna yana fadin"haba mana bestie..bakya gajiya da kuka ne?.."ta wani sake tale baki tace"bestie na gaji da makarantan nan wlh..infact am tired of the whole city i want to go home"...murmushi ya saki ganin yanda take mgn sai kace yarinya cikin ranshi yace"gaskia mijin bestie zaisha fama wlh"..a fili kuma sai ya shiga ban baki da bata hakuri har ya samu da kyar ta tsayar da kukan.
Koda Bobby ya isa gida Mummy kadai ya samu a central parlor...ya karasa kusada ita ya zauna yana duban illham dake bacci kusada ita yace"Mummy ke kadai?.."tace"wlh ni kadai ne Bobby yanxun Miemie da Sabeer suka fita wai zata rakashi anguwa..Sumayya kuma tana daki tun safe ni bansan meke damunta ba"...da sauri yace"ni nasan abunda ke damunta..Isma'il ne"...da mamaki sosai Mummy ke dubanshi tace"Isma'il kuma?..wane Isma'il kenan?.."yace"Isma'il dai da kika sani baban su Miemie"...idan kaga yanda Mummy ta zaro ido zakayi zaton wani gagarumin abu ya fada...tana shirin bude baki tayi mgn Aunty Sumy ta shigo parlorn...saita dakatar da abunda zatace kawai ta juya tana kallonta har ta karaso ciki ta zauna kaman itace Isma'il din...Mummy tace"are you serious Bobby ko dai wasa kakeyi?.."yace"Mummy am jet serious wlh..nayi blocking number nashi dai ban saniba ko ya sake kira".. yans rufe baki Aunty Sumy tace" ya kira"...gaba dayansu suka juya suna kallonta...tace"yanxun nan ya kira shiyasa ma fito dan in fada maku"...wani salati Mummy ta saki tace"to me yake nema kuma a wurinmu?..me yake ce miki idan ya kira?.."tace"ranan dai ban tsaya naji me zaice ba kawai ina jin voice dinshi na kashe...yau kuma tambayana su Miemie yake kuma wai in taimaka in yafe mishi"...shiru kawai Mummy tayi tana kallonta kaman statue...Bobby kuma ranshi yaji ya 6aci da wnn rainin hankali...idan ba rainin hankali ba yaran da yayi abandoning shekara shekaru bai ta6a kira yaji ya suke ba a matsayin babansu shine rana tsaka yanxu zai wani kira ya tambayesu?..shi har yanxun bai dena mamakin irin guts din Isma'il ba...hannu kawai ya mikama Aunty Sumy yace"bani wayan"..ba musu ta mika mashi..yana kar6a ya zare sim card din gaba daya snn ya mika mata wayan yace"saidai ki hakura da amfani da sim din for a while...idan na shiga ciki zan dakko maki new sim card ki fara using zuwa dan wani lokaci"...batayi masa musu ba ta amsa da toh...ita kanta tasan ajiye sim din is the only way da zai rabata dashi don tasan indai yana nan a Isma'il data sani some years back to bazai ta6a dena kiranta ko zatayi blocking dinshi sau 100 kuwa...idan babu sim din kuma dolenshi ya hakura idan ya kira yaji baya shiga...Bobby dai mikewa yayi ya wuce flat dinshi cikin ranshi yana ayyana kalan rashin mutuncin da zaiyima Isma'il din nan...su kuwa zaman shiru sukayi a parlorn sai kace kurame...suna nan zaune Miemie da Sab suka shigo suna fada kaman ba sune suka fita daxu rimi rimi ba kaman basu ba...Aunty Sumy ce tayi karfin halin cewa"meye haka ne wai?..wane irin iskanci ne wnn zaku shigowa mutane kuna fada?..bakuda hankali ne?.."Sab yace"Aunty wai Miemie sbd batada kawai sbd wani friend dina yace yana sonta saita yadda?.."juyawa tayi tana duban Miemie fuska daure kafin tayi mgn Miemien tace"Aunty na ranste da Allah ba haka bane...ina cikin zamana fa kawai yazo ya fara min mgn shine shi kuma yake cewa wai na kulashi"...tun kafin ta rufe baki Sab yace"karya kikeyi i saw the two of you laughing "...itama ta bude baki zatayi mgn Aunty Sumy ta daka musu wani tsawa tace su 6ace mata a wurin...ba shiri suka kada kafafuwansu suka bar parlon.
Masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment ta 07063800556.
Rano✨
🤍Dr.BOBBY🤍
By Aysha Rano✨
Wattpad@aysharano22
09
Ranan Thursday da wuri suka shiga school sbd sunaso su zauna da group dinsu before time na presentation...tun 7 suka hadu gaba daya class suna rehearsing karatunsu...karfe 8 daidai kuma suka fara lectures dinsu...inshort basu fito daga class ba sai around 1..suna fitowa suka nufi cafeteria don cin abinci...a ciki suka hadu da Sa'eed yayi musu reserving table suka karasa suka zauna kowa ya bada ordern abinda yakeso...sunyi shiru kawai abincin sukeci don ko breakfast basuyi ba suka fito...kaman daga sama kawai suka ga mutumi yaja empty kujera dake kusa dasu ya zauna...a tare suka dago kansu duk su ukun suna kallonshi...Tajuddeen ne sanyeda uniform dinshi as always yanata kallon Lamido yana sakin murmushi...Billy taja wani tsaki tacigaba da cin abincinta...shima Sa'eed cigaba da cin nashi yayi ba tareda yace komai ba...a hankali Lamido ta ajiye spoon din hannunta tana dubanshi kaman zata sa kuka tace"what?.."kaman jira yake yace"magana nakeso muyi dake kinata min wulakanci Lamido...dan Allah ki bani dama ko Hostel ne nazo sai mu tattauna a can"...yana rufe baki tace"ba damuwa u can come to the hostel anytime u like...yanxun dai kayi hakuri ka tafi cox muna gama cin abincin nn class zamu koma"...ya danyi shiru yana kallonta kaman bai yadda da abinda ta fada ba yace"U sure?.."cikeda assurance tace"💯Sure...just go we'll talk later"...bai sake cewa komai ba ya tashi daga wurin...sai kuma ya tsaya yana kallonta yace"i love you "...gyada mishi kai kawai tayi ya juya ya bar wurin...yana tafiya Billy kaman jira take ta dago tana hararanta tace" ki tabbata a kunnen Ammi duk wnn maganan da kukayi...shine hadda wani cewa yazo hostel ya sameki sbd tsoronshi kikeji koh?.."girgiza kai kawai tayi ta cigaba da cin abincinta as batada energy din rigima da Billy yanxu sai cikinta ya dauka...bestie dai yana zaune pretending kaman baya sauraronsu har suka kammala ya biya kudin gaba daya snn suka fita...su suka wuce female masjid dan yin sallah shi kuma ya koma class cox ya riga yayi sallah tun daxu...suna idar da sallah kiran provost ya shigo wayanta...ta dauka da sauri tana fadin"Good afternoon Sir"...yace"afternoon Lamido are you guys ready?..proprietor ya shigo tun daxu and in the next few minutes zakuzo Auditorium hope you are all set?.."tace"we are Sir "...yace" alright tell them mu hadu auditorium by 2".. a hankali tace"toh.."suna gama mgn ta ajiye wayan a hankali cikin ranta tana nanata Auditorium kuma?...Common presentation da zasuyi shine sai an kaisu har wani auditorium sbd shegen iyayi...tasan duk wnn ba plan din kowa bane sai na wancan inyamurin mutumin...kawai presentation za'ace su tafi har auditorium sbd neman magana.
Karfe biyun kuwa cikin Auditorium din yayi musu...basu jima da zama ba malamai suka shigo su wajen 4 hadda Sir Abdool dinta inji Billy😆..sai shi proprietor din sai provost...daga dan sama kadan malaman suka zauna inda aka tanadar musu kaman high table haka...bayan gaisuwa da dogon bayani daga malaman akace the 1st group should come forward... a yanda suka tsara abun dama ba gaba daya members na kowane group zasu fito ba..each group dunyi selecting mutum uku da zasuyi representing dinsu cox idan akace gaba daya kowa sai yayi bazasu samu gamawa da wuri ba...kaman yanda yake alphabetically group din farko nasu Lamido ne dan haka ba wasting of time suka fita ita da sauran colleagues dinta...first speaker ce ta fara musu bayani tun daga introduction zuwa definition of terms haka..bayan ta gama second speaker itama tayi nata Lamido kuma itace karshe...saida duk suka kammala ta amsa markern dake hannun colleague dinta tareda karasawa jikin white board dake daga gefensu ta zana diagrams dake cikin topic din nasu tayi labelling snn ta fara explanation...sosai Audit din yayi tsit tun daga dalibai har malaman kowa ya nutsu yana sauraronta...da yawa daga cikin malaman dama sun santa tunda akwai wani end of year presentation da sukeyi duk end of session and ko na last year da akayi itace tayi winning...bayan wnn akwai wani tradition da suke dashi a school din at the end of every session ana fitar da overall student for both Nursing and Midwifery departments snn kuma a fitar da Wanda yafi kowa point a gaba daya college din as the overall student of the year...zaayi printing qaton poster mai daukeda pictures na overallers din kowa da sunanshi dana department dinshi sai kuma point dinshi...haka zaa kafe wnn postern kusada general notice board snn a sake kafe wani ta wajen admin block...so da yawa cikin malaman ko basu santa a zahirinta ba sun santa either a wancan poster tunda last year ita tayi overalling a department dinsu ko kuma a end of year presentation da akayi na last year...shi kanshi Bobby yau sai yaji wani abu daban gameda yarinyar...bama ita kadai ba gaba daya class din sun burgeshi sosai coz sunada kokari..cikin ranshi yake ayyana wai haka duk students din nashi suke da kokari ko kuwa iya class dinsu ne haka?..yana cikin tunaninshi yaji Audit din ya kaure da wani irin loud tafi yana dubawa sai yaga ashe sun gama shine ake musu tafi...babu 6ata lokaci group two suma suka fito sukayi nasu followed by group three wanda sune last group...bayan sun gama gaba daya student affairs dinsu ya tashi yana praising dinsu tareda karfafa musu gwuiwa kan karatunsu...bayan ya gama provost ma yayi nashi sai kuma mai gayya mai aiki Alhaji Dr Bobby jikan Waziri lol😃..shima praising dinsu yayi sosai snn ya fadam each group marks din da sukayi scoring wanda dashi zaayi amfani a matsayin c.a dinsu..bayan ya gama malamai suka fara fita followed by students din...kafin su karasa class kiran Sir Abdool ya shigo wayanta...ta dauka tana gaisheshi yace"Lamido can i please see you now?.."ta danyi shiru tana tunanin ne zatace mishi ya sake cewa"ba dadewa zakiyi ba Please!"...ba yanda ta iya haka nan tace mishi gata nan...ta dubi Billy da suke tafiya tare tace"kinji Sir Abdool wai inje...ni kuma na gaji wlh so nake in koma hostel in kwanta"..kar6an text book dake hannunta Bilky tayi tace"yace fa ba dadewa zakiyi ba..kiyi hakuri kije ni zan jiraki a class"..Aysha tayi murmushi tana jinjina wnn so da Billy ke mishi ta juya ta tafi...tazo daidai kofan office dinshi tana shirin budewa Bobby da Nur suka fito daga office din Nurun...ta dauje kanta da sauri sakamakon idanunshi da suka sauka a kanta...ta budr office din da sauri ta shiga su kuma suka wuce don dama tafiya gida zasuyi...tana shiga ya mike daga zaunen da yake tareda dawowa kan soafer ya zauna ya nuna mata kusa dashi itama batayi mishi musu ba zauna...ya tsura .ata ido yana sakin wani shegen murmushi yanajin ina zai saka yarinyar nan ne tsabar son da yake mata...itadai kanta na kasa as batason wnn kallon kasa kasan da yake mata...shi kuwa rasa kalmomin da zai furta mata yayi sai kawai ya kamo both hannayenta yakai su bakinshi yayi kissing kafin ya ajiye yana fadin"i love you"...daure fuska tayi sosai tana dan turo baki ta kalleshi...yasake sakin wani murmushi yana shafa gashin kanshi yace"Ya Allah"...ganin ta sake tsuke baki ya kama ears dinshi yace"am sorry sonki ne yayi min yawa wlh Lamido..so accept my apology inshaAllah bazan kara ba"..batace mishi komai ba sai mikewa da tayi yace"please forgive me"..ta gyada kanta kawai ta fita daga office din.
Da dare Hostel suna cin abinci itada Billy kiran Daddy ya shigo wayata...tayi saurin hadiye na bakinta ta sake daidaita nutsuwarta snn ta daga tana cewa"Hello daddy barka da dare"..Daddy yace"sallamanki kenan ba?.."da sauri tace"sorry daddy..salamu alaykum barka da dare"..yace"barka dai ya studies?..hope you are doing well?.."tace"inayi daddy ya aiki"..yace"Alhamdulillah na dawo gida..ba wani matsala koh?.."tace"ba komai daddy"yace"MashaAllah bawa Bilkisu waya"..ba musu ta mikama Billy wayan..itama ta kar6a da sallama tana gaisheshi..yace"inda kika fita hankali knn?..ya karatu fatan ba wani matsala?.."tace"babu komai daddy"..yace"to Alhamdulillah aci gaba da dagewa sosai..Allah muku albarka"..Billy ta amsa da"Ameen mungode daddy Allah ya kara girma"..shima yace"Ameen"..daga haka ya kashe kiran...Aysha ta kar6i wayan tana sauke ajiyar xuciya tace"sai yanxu hankai na ya kwanta..da naga kiran nayi zaton ko wani laifin nayi"...Bilkisu ta girgiza kai tana cigaba da cin abincinta tace"bakida gaskia ne ai shiyasa".
Bobby bai samu dawowa gida ba sai yamma likis...su Miemie ya samu a parlor suna kallo..gaba daya suka mishi sannu da zuwa ya amsa idonshi kan Sab da hankalinshi gaba daya ke ga phone dinshi yace"kai yaushe zakuyi resuming school ne?.."Sab yace"next week ne but dan Allah inaso in kara ko one week ne plss"..bai rufe baki ba Bobby yace"C'mon keep quiet..waye zai bari ka kara one week din?..you are deceiving yourself"...daga haka ya kama hanyan parlon Mummy...ga mamakinshi bai sameta a parlon ba sai ya nufi bedroom dinta yana mamakin meye sa bedroom da wuri haka...Allah yasa dai lafiyanta qalau...yana tura kofan ya shiga sai sallaman da yake kokarin yi ya makale a bakinshi sakamakon abunda ya gani...Mummy ce zaune gefen gado tana hawaye Anty Sumy na zaune kusada ita tana hawayen itama...baisan lokacinda ya saki suit dinshi dake a hannunshi ba ya karasa cikin dakin da sauri...gefen Mummy ya zauna ya kamo hannayenta hankali tashe sosai yace"Mummy what is happening here?..why are you two crying?.."damke hannunshi Mummy tayi ta juya tana kallonshi tace"your grandfather Bobby..Waziri..idan bawan Allahn nan ya mutu baisan inda kuke ba bazan ta6a yafema kaina ba Bobby..you need to see his condition..he is seriously.."bai bari ta karasa ba ya rungumeta a jikinshi...itama saitayi lakwas a jikin nashi tana cigaba da hawaye...suka hada ido da Anty Sumy dake kallonsu tana hawaye itama..da ido ya tambayeta me yake faruwa ta buda mishi hannu alaman he has no idea...saida yaji kukan nata ya dan tsagaita snn ya sake dagota still yana rikeda hannayenta yace"Mummy kukan ya isa haka please kar bp dinki yayi rising..besides waya fada maki condition da wazirin ke ciki?..how did you know?.."tace"a news na gani wai ciwon nashi yayi worst har sun daukeshi daga Egypt zasu maidashi india..Bobby he is seriously sick inaso kuje ku dubashi idan ya dawo"..cikin 6acin rai tuno abubuwan da suka faru a baya yace"but Mummy why?..why zamuje dubashi bayan bai damu damu ba..bai damu ko muna raye ko mun mutu ba?.."yana rufe baki tace"because he is your grandfather Bobby..komai girman laifin da yayi he is still the father to your Dad and nobody can change that"..ta kamo hannunshi snn tacigaba"do you think if your Dad was alive zaiji dadin yanda kake treating mahaifinshi?..do you think he would be happy if we choose to hide ourselves from them komai girman abunda suka aikata?.."a hankali ya zame hannunshi daga nata lokaci daya idonshi sukayi jajir sbd 6acin rai yace"but Mummy we didn't hide ourselves from them sune basuga daman su nemi inda muke ba..for five long years Mummy idan suna sonmu meyasa basu nememu ba?.."yana rufe baki tace"because he is sick Bobby..sanin kanka ne tun ranan da mahaifinku ya fadi ya mutu bai sake samun lafia ba"...cikin anger daya fara kasa controlling yace"dukda bashida lafia if he really love us..if he really want to see us he could've at least ask one of his selfish and wicked sons to look for us but he didn't and do you known why?..because he hates us..he despise..."bai kai ga karasawa ba yaji saukan kyakyawan mari a cheeks dinshi...ya dafe cheek din da sauri yana duban Mummy dake kallonshi rai a 6ace itama...Anty Sumy ta taso da sauri ta kama hannun Mummy hawaye na wanke fuskanta tace"Mummy take it easy please..kinsan condition dinki Mummy kar wnn abun yasa bpnki yayi rising please"..ta karasa mgnr tana kuka sosai...Bobby da yayi suman wucin gadi sai yanxu ya dawo hayyacinshi...tun da yake zai iya counting sau nawa Mummy ta dakeshi but now she slapped him sbd azzaluman mutanen can..wasu hawaye yaji suna cikowa idanunshi amma ya dake bai bari sun zubo ba ya dora kanshi a shoulder dinta murya can kasa yace"am sorry for hurting you Mummy amma kinsan gaskia nake fada fa..mutanen nan basu ta6a kaunarmu ba Mummy..kema basa sonki amma meyasa kikeso mu sake kai kanmu inda suke bayan duk laifukan da sukayi?.."dago kanshi tayi tareda cupping fuskanshi tace"because they are your relatives Bobby..they are your Family and Family will always be considerd as Family nor matter what..so try to understand me please"...shiru kawai yayi yana yanajin yanda maganganunta suke neman kashe mishi jiki...Anty Sumayya dai na zaune tana kallonsu..itama Mummy ganin tasirin da maganganunta sukayi ta sake yin kasa da murya tace"try and understand Bobby please..ko bamu nemesu yanxu ba dole watarana dalili zai sa mu nemesu shiyasa nakeso mu daidaita dasu tun kafin zuwan wnn lokacin.."shiru ya sakeyi idanunshi lumshe yana sauraronta...ita kuma Mummy ta dan saki murmushin cin nasara snn tacigaba"kaga watarana Aurenku ne zai taso kuma nasan kasan duk dunia babu inda mutum zaije neman aure a bashi ba tareda dangin mahaifi ba..and gaba daya ku ukun babu wanda keda aure gara Sumayya ta ta6ayi hadda yara amma kai da Sabeer baku ta6ayi ba Bobby..dole kuma watarana lokaci zaizo da zamu bukaci suzo su nema muku aure"...sake daure fuska yayi jin ta fara zancen aure yace"indai wnn mutanen ne zasu nemamin aure Mummy wlh na gwammace har in mutu banyi aure..Anty Sumy da Sab kuma duk wanda bazai kar6i aurensu a wurina ba saidai ya hakura"..ta bude baki zatayi mgn ya dora finger dinshi kan bakinta yace"enough talking about them please..yanxu ki samu ki kwanta kina bukatan hutu sbd bp dinki..maganan zuwa dubiyan Waziri kuma Allah ya dawo dashi lafia sai muje"...lokaci daya murmushi ya mamaye fuskanta tace"da gaske zakuje Bobby?..tasan indai ta samu ta shawo kanshi ragowar basuda matsala dama Bobbyn shine mai taurin kain...yace"anything for you Mummy..yanxu dai ki samu ki huta sosai"..da sauri ta shiga gyada mishi kai tace"Allah ya muku albarka"..yace"Ameen Mummy"..Anty Sumy ce ta taimaka mara ta kwanta shi kuma ya juya a hankali ya fice daga dakin zuwa nashi...a gurguje yayi wanka tareda alwala ya fito ya tayar da sallah tubda an idar a masallaci...ya dade zaune yana addu'a kan Allah ya mantar da Mummy mgnr zuwa dubiyan nan dan fa shi har yanxu baiji zai iya daukan kanshi ya kai Gombe ba..har abada gani yake bazai ta6a iya mace kalan rashin imani da suka gwada musu ba har shi wazirin daya kasance kakansu...da kyar ya samu ya mike daga wurin da yayyi sallahn ya fada kan gado ya kwanta...ya runtse idonshi da karfi yana jin duk wani abu daya faru na daow mishi kaman yanxu yake faruwa...bayason yana wnn tunanin amma ya kasa dakatar da kanshi.
ASALIN LABARI...
Our free pages sun kusa karewa fa..keep on subscribing before kuji diff kaman an dauke wuta😹
Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment ta 07063800556.
Rano✨
🤍Dr.BOBBY🤍
By Aysha Rano✨
Wattpad@aysharano22
10
ASALIN LABARI...
Lokacinda Attahir wato mahaifin Bobby yakai ma mahaifinshi Wazirin Gombe mgnr yanason Auren Nadia daya hadu da ita a kano kai tsaye yace bai amince ba sbd kasancewarta ba bahaushiya ba...hankalinshi ya tashi sosai ganin da gaske waziri naso ya rabashi da matar da yafi kauna a dunia..ya jema mahaifiyarshi da mgnr itama ta nuna batada taimakon da zata iyayi masa har tunda mahaifinshi yace ya hakura da ita kawai ya hakura...bai hakuran ba yacigaba da lalla6a waziri yana nusar dashi illar nunama wanda ba yarenku daya ba banbanci...ya kuma nusar dashi cewa har tunda ta kasance musulma kuma yar Nigeria yana ganin ko addini bai haramta mishi aurenta ba...ran waiziri ya 6aci sosai ya kuma ce matukar shi ya haifeshi bazai ta6a amince mishi ya auri inyamura ba...wnn mgn ba karamin daga hankalin Attahir yayi ba...step brothers dinshi da suke ganin waziri ya fifitashi a kansu nan suka samu damar shiga suna cigaba da ingizashi kan kar ya yadda ya amince ya hada jini da inyamurai wnn zuga kuma yayi tasiri a wurinshi sosai...Attahir da yaga bashida wani mafita kuma bazai iya hakura da Nadia ba kai tsaye yaje ya samu kakarshi mahaifiyar waziri knn yayi mata bayanin duk abunda ke faruwa nan kuma ta goyi bayan lallai sai an aura mishi matar da yakeso...hakan ba karamin 6ata ran waziri yayi ba amma ya hakura ba don yanaso ba ya tura aka nemo masa auren yarinyar har Enugu state bisa umarnin da mahaifiyarshi ta bashi kan lallai lallai ya aurama Attahir matar da yakeso idan baiyi haka ba kuma itama zata tsine masa kmr yanda yayi ikirarin zai tsinewa nashi dan.
Cikin lokaci kankani akayi bikinsu aka gama...sbd sanin da yayi cewa yan uwanshi da mahaifinshi ba son auren suke ba sai ya nema mata gida a kano ta zauna itama tacigaba da karatunta...tsakaninshi da Gombe saidai yaje ya gaisa dasu ya dawo kanon ma kuma bai cika zama ba sbd a lokacin yana aiki a Delta state...tun bayan aurensu kuma ko mutum daya baizo daga cikin 'yan uwanshi da sunan yazo ganin matarshi ba...a haka suka dauki tsawon shekara daya bata ta6a ganin wani nashi a inda take ba..a lokacin ta damu sosai da rashin zuwan nasu shi kuma saidai ya bata hakuri yace mata komai zai wuce...ana haka ya samu kira daga waziri kan lallai ya tattaro ya dawo Gombe da zama a cewarshi wai matarshi ke hanashi zuwa ziyararsu yanda ya kamata...baiyi nasa musu ba ko kadan as baison ya sakeyin laifi a wurinshi haka ya tattarata kaman yanda wazirin yace suka koma gidanshi dake cikin Gombe...da farko Nadia taji dadin komawan nasu sbd tana ganin idan tana kusa da yan uwanshi zasufi saurin kar6anta a matsayin suruka sai kuma daga baya ta gane mutanen nan bazasu ta6a kaunarta ba...kyara da tsangwama ba kalan wanda bata gani ba a wurinsu abun har ya kai ko taro sukeyi bata isa ta shiga cikin matan brothers dinshi ba dan zasu yita jifanta da munanan kalamai suna cewa ita inyamura ce..hatta yaransu sunan da suke kiranta dashi knn inyamura...a lokacin data samu cikin Sumayya tayi farin ciki sosai sbd tana ganin kilan idan ta haihu zata iya samun soyayyar waziri dana sauran 'ya'yanshi ko dan sbd abunda zata haifa...mahaifiyar mijinta dama bata ta6a samun matsala da ita ba hakama Munubiya..kawai dai basa iya sakewa su nuna damuwa da ita sosai sbd gudun 6acin ran waziri...duk wnn abun da ake Attahir bai ta6a daga baki yace zaiyi mgn ba sbd yasan ko yayi ba amfani zaiyi ba tunda goyon baya suka samu wajen waziri...'yan uwanshi da dama tuni yasan basa kaunarshi sbd soyayyan dake tsakaninshi da waziri shiyasa suke amfani da wnn damar suna rura wutar tsanarshi cikin zuciyar babanshi...yana sane sarai suke tunzurashi yake aikata duk abubuwan da yakeyi shiyasa bazai taba bude baki yayi complain ba fatanshi daya Allah ya rabashi da mahaifin nashi lafia.
Lokacin da aka haifi Sumayya Attahir yayi farin ciki sosai hakama qanwarshi mahaifiyarshi sun tayashi murna matuka saidai babu daman nunawa sbd waziri...lokacin da ya dauketa ya kai masa ita ko kallonta baiyi ba yace ya fitar mishi da ita a wurin...wnn abu ba karamin 6ata ranshi yayi ba...yana ganin ko arniya ya aura bai kamata ace his own father yayi treating yarinyarshi irin haka ba..abun ya 6ata ranshi matuka...wnn dalilin yasa baiyi shawara dashi kan sunan da zaa sama yarinyar ba kamar yanda sauran 'yan uwanshi sukeyi duk wanda matarshi ta haihu shi ke za6an sunan da za'a sa...baiyi shawara da kowa ba yasa mata Sumayya sunan qanwar Nadia da bata dade da rasuwa ba a lokacin...aikam taji dadi sosai dan bata ta6a zaton zaisa sunan yar uwarta ba.
Haka rayuwa yacigaba da tafiyan musu yau dadi gobe babu har Sumayya ta fara wayo..a lokacin itama sai aka fara tsokanarta da inyamura ko kuma su kirata da 'yar inyamura..wnn abu ba karamin daga hankalin mamanta yake ba amma ba yanda ta iya haka a koda yaushe take bata hakuri tareda fada mata cewa watarana komai zai wuce wnn dalilin yasa ko ina bata zuwa kullum tana gida nane da mamanta idan mahaifinta na gari kuma tana nane dashi...duk wnn abun dake faruwa Nadia bata nuna mishi damuwarta sbd yanda yake iya bakin kokarinshi yaga basuyi lacking komai ba itada 'yarshi.
Bayan Sumayya saida ta dauki tsowon shekaru hudu kafin ta samu wani cikin...farin cikin da Attahir yayi da jin labarin cikin har mamaki ya bata...da dadewa tasan yanada son yara tunda tana ganin yanda yakeji da Sumayya amma yanda yake farin ciki da cikin ko wanda bai ta6a haihuwa ba sai haka...wnn dalilin yasa yake kulawa da ita yanda ya kamata...duk yake gari da kanshi yake kaita antenatal idan baya nan kuma tayi driving kanta...a kullum cikin godema Allah take sbd yanda mijinta har yanxu kiyayyan mahaifinshi dana brothers dinshi baisa ya canxa mata ba..ga kuma budi da Allah ke kara mishi a kullum.
Lokacinda haihuwa yazo mata sai akayi rashin sa'a baya gari...daga ita sai Sumy a gidan gashi tanata kiran wayanshi bai shiga as dama ya fada mata zasu shiga jeji she might not reach him sbd network issue...ba yanda ta iya haka ta kira number wani brother dinshi tayi mishi bayanin halinda take ciki yace mata baya gari saidai ta kira wani...bata hakura ba ta sake kiran wani shi kuma yace zai turo matarshi amma shiru har kusan bayan awanni bai turo kowa ba..gaba daya ta fita hayyacinta as ciwon kara gaba yakeyi sosai gashi kuma batada number wani cikin brothers din nashi sai su biyu ga kuma sumayya daketa faman kuka tun daxu ganin halinda mamanta ke ciki...tayi kokarin kiran munubiya a waya itama bata sameta ba..a karshe dai dole sai sumayya ta aika tayi mgn da wata neigbour dinta ba bata lokaci matar tazo ta taimaka mata suka tafi asibiti...lokacin wajen karfe 9 na dare...suna zuwa aka kar6eta akayi labour room da ita..midwives kusan uku ne kanta suna kokarin taimaka mata amma har gabannin asuba bata haihu ba ga dan karen wahala da takesha...sun kira doctor da yake on call sun mishi bayani yace zaizo kawai ayi masa Cs kafin doctor din yazo kuma sai ta fara fitting(jijjiga)..hankali tashe one of midwives dake kulada ita ta sake kiran doctor ta fada mishi tana fitting yace gashi nan kan hanya ya kusa zuwa...dama tunda suka fada mishi yanda blood pressure dinta yayi rising yasan da kyar idan baiyi leading to preeclampsia ba.
Doctor na karasowa basuyi wasting time ba suka shiga da ita theatre...neighbor dinta data kawota asibitin na tareda Sumayya da aka samu tayi bacci da kyar sbd jiya bata samu tayi sosai ba...before a shiga da ita theatre din kiran mijinta ya shigo wayanta dake hannun matar data kawota...nan tayi picking ta kumayi masa bayanin halinda ake ciki...hankalinshi ya tashi sosai ya kuma ce gashi nan tahowa Gombe yanxun nan...suna gama mgn ya wuce airport ya taki sa'a kuma ya samu flight din Kano nan ya sayi ticket ya zauna jiran lokacin tashi yayi.
Bai samu isowa Gombe ba sai around 10...daidai lokacin kuma ake fitowa da ita daga theatre..baisan time din da hawaye ya cika idonshi ba ganin yanda aka turota kan trolley bed an rufeta da wani green kyalle kaman babu numfashi a jikinta...shiyasa tun jiya yakejin hankalinshi ba kwance ba ashe halinda suke ciki knn.
Kai tsaye akayi moving nata Amenity dake female surgical ward...wanda suka kawota suka dagata daga kan trolley bed snn suka dorata kan bed din dakin suka fita...Nurse din da tayi resuscitating baby ta mika mishi babayn ya amsa da sauri itama ta juya ta fita..ya rage dagashi sai Sumayya a dakin dan matar data kawota kin shogowa tayi tace mishi zata koma gida...yayi mata godia tareda kyauta mai tsoka snn ta tafi...a hankali ya karasa kan wani kujera ya zauna har yanxun yana rikeda babyn a hannunshi...ya sauke idanunshi kan babyn da a kallon farko yaga tsantsan kamannin da yakeyi dashi...lokaci guda wani murmushi da bai shirya mishi ba yayi escaping lips dinshi...soyayya babyn yaji yanaji sosai har cikin jininshi..haka suka hada kai shi da little sumayya sunata kallon babyn daketa mustu mutsu abunshi.
Lokacinda Anaesthesia ya saketa ta tashi daga bacci sai yaga hawaye a idonta...hankalinshi yakai kololuwar tashi ya kuma ce dole ta sanr dashi damuwarta...itama din ba yanda ta iya duk yanda take kokarin 6oye mishi abubuwan da suka faru kasawa tayi saida ta fada mishi...6acin ran da ta gani a fuskanshi bata ta6a ganin irinshi a tattare dashi ba..yanxu kiyayyan da suke masa har yakai ga suyi abandoning matarshi tana labour wanda ba dob taimakon neighbor dinsu ba da kilan yanxu ya rasa matarshi da kuma babyn data haifa..zai iya yafe komai amma banda wnn cin kashin da sukayi masa..wnn dalilin yasa ya yanke shawaran da zaran ta warke zai daukesu su bar Gombe gaba daya tunda baiga amfanin zaman nasu ba.
Haka yake jinyar matarshi shi kadai sai neighbors dinta dake yawan xuwa kullum wasu har suyi girku su kawo...mahaifiyarshi ma bata taba zuwa ba sbd waziri daya hana amma munubiya zuwanta biyu shima duk wazirin bai sani ba take zuwa...saida ta samu sauki sosai yace ta fadi sunan da takeso a sa ma babyn nan take kuma tace sunanshi takeso yasa sbd tana ganin duk dunia yanxu batada wanda ya kaishi sai 'ya'yanta...baiyi mata musu ba yayi mishi hudu ba da sunan Attahir tace zasu ringa kiranshi Bobby.
Daga asibiti ko gidansu basu koma ba suka wuce kano...bayan kwana biyu suka bi flight zuwa delta state inda a nan suka cigaba da rayuwa tareda yaransu.
Bayan shekara biyu suka koma Lagos sakamakon transfer da akayi mishi ya koma Lagos din da aiki...lokacin Sumy nada 6 years Bobby kuma nada 2...tsahon wadan nan shekarun kuma basu sake zuwa Gombe ba saidai yaje shi kadai ya dawo...ana haka Allah yayiwa mahaifiyarshi rasuwa...wnn karon kam gaba daya suka tafi kuma basu dawo ba sai bayan kwana bakwai...har zuwa lokacin kuma daga waziri har sauran siblings dinshi babu wanda ke kaunar matarshi da yaranshi...haka akwa kwashi tsahon shekaru babu jituwa tsakaninsu wanda hatta yaran dukda ba wasu shekaru sukeda ba sunsan akwai matsala tsakanin iyayensu da familyn babansu especially Bobby da yafi 'yar uwarshi riko da kuma zafin zuciya.
Sbd wnn matsalan yasa ko auren qanwarshi da zaayi bai samu labari ba sai gab da bikin...yaji ciwon hakan sosai sbd ganin cewa yarinyar nan batada kowa yanxun daga wazirin sai shi da suke ciki daya da ita tunda mahaifiyarsu ta rasu...haka sukaje Gombe suka dawo bayan kammala bikin.
Bayan shekara goma Nadia da yaranta ke kira Mummy ta sake haifan namiji wnn karon yaron yaci sunan waziri Adam suke mishi laqabi da Sabeer.
Zaman Lagos na musu dadi sosai don basuda damuwan komai kuma babu wanda ke kyamansu unlike Gombe da ko zuwa basu sonyi sbd yanda 'yan uwan Dad dinsu suke treating dinsu.
Bobby nada 17 years ya gama secndary school Sumayya kuma already ta fara karatu a University of Lagos shi kuma Sab yana primary school...zuwa wnn lokacin mahaifinsu yayi kudi sosai dan yana matakin deputy controller General na Nigerian Custom...kai tsaye ya tura Bobby America dan yacigaba da karatunshi a can.
Sumayya na kammala karatu aka aura mata isma'il da suka fara soyayya tun a university aka mikata gidanta dake Kanon dabo...unluckily itama mother inlow dinta bata sonta...dama Isma'il kadai ne danta namiji sauran duk mata ne suma kuma ba son nata suke ba...bayan shekara daya da biki ta haifi Miemie da aka sama sunan grandma dinta ta wajen uba wato Maryam ake kiranta Miemie...har zuwa wnn lokacin basa jituwa da sisters din mijinta dama mamansu gaba daya..kullum cikin nuna mata kiyayya suke kawai sbd ba ita sukeso ya auraba snn kuma da kasancewar Mum dinta igbo...wai Isma'il ya gur6ata musu family tunda ya hada musu jininsu dana inyamurai...haka aka cigaba da tafiya har ta sake haifan Ilham...ita kuma sunan Mummy aka sa mata Nadia ake ce mata ilham...wnn maida suna ba karamin tada rigima yayi tsakinshi da familynshi ba..wai don me zai sama yarinya sunan inyamurai...Sumayya da bata ta6a tanka duk abunda suke mata ba wnn karon kasa hakura tayi saida ta wanke su tatas ta kuma ce duk wanda ya sake izgili ga sunan mahaifiyarta sai sun kwashi 'yan kallo dashi...labari na zuwa ga Isma'il mahaifiyarshi ta sanyashi gaba da kuka wai matukar yana sonta sai ya saki Sumayya tunda batasan darajanta ba tayi mara rashin kunya...da sukaga bazai saketa ba sai sukasa ya sake auran 'yar sister din mamanshi sbd a kuntatawa Sumayyan...sunyi nasara kuma domin duk son da mijinta ke mata saida ta fara ganin canji tattare dashi...ya fara mata abubuwa wanda da ba haka yakeyi mata ba...gaba daya ma sai rayuwarshi ta koma 6angaren amaryarshi ita kuma ko oho don ko inda take bai cika zuwa ba...wnn abu yayi matukar daga hankalinta sosai tana ganin ko don yaranshi ai bai cancanci yayi abandoning dinta haka ba...daga karshe datayi kokarin nuna masa rashin dacewar abunda yakeyi sai yace taje ya saketa saki daya...bata sake wasting time ba kuwa ta hada kayanta ta wuce Abuja sbd a lokacin Daddynsu na matakin Controller General na Nigerian Custom so sun koma Abuja da zama...lokacin Ilham tana da shekara uku...haka suka cigaba da zama tareda iyayenta da kuma yaranta basu da matsalan komai...after a year Bobby ya kammala karatunshi a America lokacin shekaranshi kusan 9 a can...gaba dayansu suka shirya suka tafi America sukayi witnessing convocation dinsu snn suka dawo tareda shi Bobbyn da yakeda 27 years a lokacin...Sab kuma yanada 17 years kuma shima ya kammala secondary school.
Bayan kaman sati biyu da dawowanshi suka tafi kano wani taro da akayi inviting Daddy sai yace suje gaba daya...suka sauka nan gidanshi dake garin shi kuma ya wuce inda zasuyi taronsu...duk tsahon wnn shekarun daga Bobby har siblings dinshi babu wanda ke marmarin zuwa Gombe sbd cikinsu ba wanda baisan kalan hatred da sukeyi ma Mummynsu da su kansu ba...Bobby kuwa a lokacin ko mgnrsu ma baisonji...wani lokaci sai Daddy ya kira waziri ya waya ya hadasu su gaisa amma kowa zai kar6a shi kuma sai ya kirkiri wani abun ya tashi ya bar inda suke...Mummy duk tana lura dashi ta kuma san baya kaunarsu ne sam amma ko kusa batajin dadin hakan...tanaso ace ya samu kyakykyawan mu'ala da dangin mahaifinshi ko don sbd nan gaba ba wanda yasan me zai faru sai Allah.
A ranan bayan sun tashi daga taron shima ya wuce gida tareda zugan securities dinshi...misalin karfe 4:16 na yamma kiran wani brother dinshi ya shigo wayanshi...bayan ya dauka yake sanar dashi cewa waziri ne ba lafia kuma tun jiya yake cewa a kirashi yazo yanason mgn dashi...hankalinshi tashe sosai yace gashi nan zuwa Gomben yanxun...ba yanda Mummy batayi dashi kan ya bari da safe ba tunda yamma yayi amma yace sam bazai iya kwana while mahaifinshi nacan babu lafia kuma yana son ganinshi ba...babu yanda ta iya haka tabishi da addu'a...before ya fita ya shigo cikin gidan ya samu Miemie da Sab sai Sumayya a parlor nan yace musu zaije Gombe ya dawo suma suka mishi addu'an sauka lafia...yana shirin fita Bobby ya shigo parlorn rungume da Ilham da tayi bacci a hannunshi...shi kanshi yana ganinshi all dressed up yasan da akwai inda zaije...bayan ya fada mishi Gombe zaije ga mamakin dukkaninsu da shi kanshi Bobbyn yace zai rakashi...Daddy yayi mamaki sosai don sarai yasan duk yaran ma babu wanda yafi tsanan Gombe kamanshi amma yau shi da bakinshi yake cewa zai rakashi...bai yadda ya bishi ba yace zai tafi da driver shi kuma yanada bukatan ya zauna ko don ya kula da Mummy da sauran yaran...haka nan ya hakura amma har cikin ranshi baiso haka ba...shi kanshi baisan dalilinda yasa yau yaji yanason bin mahaifin nashi zuwa Gombe ba...duk abunda ke faruwa Mummy na zaune tana kallonsu itama bason tafiyan nashi takeba especially da yace dagashi sai driver zasu tafi bazai tafi da securities dinshi ba...a takaice bai samu ya bar gidan ba sai around 5...kaman yanda ya fada dagashi sai driver din nashi sukashiga mota suka kama hanyan Gombe...suna dab da shiga garin dan sun wuce Azare kawai sai ganin babban mota suka from no where tayo kansu gadan gadan...a kokarin driver na ya kaucewa motan sai kan motan ya kwace daya hannunshi gaba daya...daga nan kuma basu sake sanin inda suke ba sai ganinsu sukayi a Hospital...yana bude idanunshi yaci karo da waziri dake rikeda hannunshi idonshi yayi jajawur sbd tsabar rudun da yake ciki...ga kuma wasu daga brothers dinshi suma zaune a wurin...cikin tsananin ciwon kan dake addabarshi yayi kokari ya rike hannun mahaifinshi dake rikeda nashi...idonshi na zubda hawaye yake neman mahaifin nashi da ya yafe mishi...shima kanshi wazirin kaman zaisa kukan yace ya yafe mishi dunia da lahira..shima kuma yana rokon yafiyanshi kan duk abubuwan da ya aikata wa iyalinshi...shi kanshi yasan bai kyautawa abunda yake amma sam ya kasa denawa...yanxun kuma daya ganshi kwancs cikin jini sai duk wnn tsanar da aka sa yake mishi ya 6ace 6att sai tarin kaunar da yake mishi tun can baya suka shiga dawo mishi...lokacinda su Mummy suka karaso gaba daya ba wanda ke cikin hayyacinshi...kuka kawai suke har suka karaso inda yake...idanunshi ya shiga zagayawa akansu yanajin kaman kallon karshe yake musu...ya kalli Mummy da idanunta sukayi suntum sbd kuka sai Sumayya da har yanxu bata dena kukan ba...can gefe kuma Sab ne da Miemie suma rungume da juna suna nasu kukan sai kuma Bobby dake rikeda hannun ilham idanunshi a kasa sbd bayason suga yanda idanunshi suka sauya sbd kuka...hannu kawai ya mika mashi alaman yazo gareshi...cikin karfin hali ya saki hannun ilham tareda karasawa kusa dashi ya zauna ya kama dayan hannunshi da yake free...murmushi sosai yaga yanayi dan haka shima sai shiga kakalo murmushin yana kallonshi...cikin muryanshi da ko fita baiyi sosai ya nuna su Mummy dake jere suna faman kuka yace"na bar maka su amana...inaso ka kulamin dasu fiyeda yanda nakeyi...inaso ka zama gatansu...ko kusa kar ka bari suyi kukan rashina Bobby...they are now your responsibility"...kukane sosai ya kwace ma Bobby ya kasa cewa komai sai kai kawai da yake girgiza mishi...shi kuma ya sake kallon Mummy cikeda wani irin rauni yace"Your Mom...batada kowa Bobby...banaso tayi kukan rashina make sure ka kulada ita yanda ya kamata"...wnn karon ba Bobby kadai ke kuka ba gaba daya sauran ma kukan suke wiwi...suka hada ido da Sabeer shima ya mika mashi hannu yazo nan suka hada kai da Bobby sunata kuka abunsu...waziri dake zaune yana kallonsu bai ta6a jin ya tsani kanshi ba kaman yanda yaji a yanxu...kallonsu kawai yakeyi tunda suka shigo yanda ba wanda yabi ta kanshi a cikinsu...ya fuskanci akwai soyayya sosai tsakin yaran snn kuma yayi mamakin ganin yanda sukayi girma gaba dayansu...sai yakejin wani ciwo na rashin sakewa jikokin nashi da har Sumayya tayi 'ya'ya biyu bai taba ganinsu ba...ya kasa dauke idonshi daga kan Bobby sbd tsantsan kaman da yakeyi da Attahir dinshi...gaba dayansu ma sai yaji wani soyayyansu na daban na shiganshi...yaji gaba daya suna wani burgeshi gasu gaba dayansu tubarkallah dasu akwai kyau...hakika ya aikata kuskurenda shi kanshi baya tunanin zai iya yafema kanshi...bayan like an hour doctor yazo yace su barshi ya samu hutu...haka suka fita daga dakin sukayi cirko cirko a waje...Waziri dake waiting room yana hangosu sai ya fita daga dakin yace ace musu su shiga daka ciki su zauna...basuyi mishi musu ba suka shiga cikin dakin shi kuma ya kowa wani tareda yaranshi guda biyu da sukayi mishi rakiya...suna nan zaune akazo aka sanar dasu rasuwar drivern da suke tare dashi...hankalin kowa ya sake tashi masu kuka suka cigaba da gashi.
In summary dai shima Daddyn cikin dare Allah yayi mishi cikawa...fadan tashin hankalin da suka shiga 6ata baki ne...Mummy kuwa dama ana fada mata ta fadi wurin a sume...har wahegari bata farfadoba ga kuma bp dinta da yayi rising sosai dole aka bata alluran bacci.
Daga nan direct Gombe suka wuce dashi...lokaci daya mutuwan nashi ya watsu a gari kusan ko ina...karfe goma na safe akayi jana'izarshi aka kaishi gidanshi na gaskia(ubangiji kasa muyi kyakkyawan karshe)...shina waziri tun a wnn lokacin ya fadi dan ko jana'iza ba'ayi dashi ba...mutuwan ya dakesu ne sosai ba kadan ba...su Mummy kuwa gidanshi dake nan Gombe aka bude suka shiga itada yan uwanta da abokan arziki.
Ranan da akayi kwana bakwai rigima ya 6arke tsakaninsu brothers din Daddy suka dage kan lallai bazasu fita daga Gombe ba tareda anyi rabon gado an fiddama mahaifinsu kasonshi ba...a cewarsu tunda mahaifinsu nada gado suma suna dashi wai idan suka yadda suka bari Gombe ba'a raba ba suna iya yin sama da fadi da wasu abubuwan...kasancewar Waziri na kwance tunda akayi rasuwar sai baisan abunda yake faruwa ba...tareda Bobby sukaita yawo duk inda kadarorinshi suke ya kaisu suka gani snn aka shiga kotu akayi rabo aka fitarma waziri da rabonshi kaman yanda yake a addinance...a ranan da aka gama a ranan ya tattara su gaba daya suka bar garin ba tareda ko waziri sunje sun duba ba...duk yanda Mummy tayi dashi kan suje suga jikinshi snn suyi mish sallama kin yadda yayi dan shi gani yakeyi ma kaman da wazirin aka hada baki aka kashe musu mahaifi tunda kira akai aka ce shine bashida lafia amma da sukazo sai sukaga akasin haka.
Abuja suka koma direct sukayi parking abunda zasuyi parking...ya sai musu sabon gida a kano kuma bai yadda wani cikin 'yan uwan Daddy sun saniba snn ya sake daukosu suka dawo...gaba daya saida yabi ya canxa musu sim card dukda dama ba wani communicating sukeyi da yan uwan daddyn ba amma still saida ya canxa musu dan kwata kwata baison sake ganin kowa a cikinsu...su barsu suji da ciwon kashe musu mahaifi ma da sukayi...ko Sab da ba wani contact dinsu yakeda ba saida Bobby ya amsa layinshi ya bashi new one...Mummy dai bada son ranta yake abubuwan nan ba amma ko yaya tayi mgn sai taga ranshi ya 6aci fiyeda tunani...da farko ma cewa yayi sai yayi bincike if ya samu da akwai sa hannun one of them a accident din Daddy then bazai ta6a hakura ba saiya mgnr court...da kyar da sidin goshi Mummy ta samu ta taushe shi ya hakura da zancen...itadai har zuciyarta bata zargin akwai sa hannun wani a cikinsu...kawai tanaga ai duk kiyayyan da suke mishi bazasu iya aikata wnn danyen aiki especially akan dan uwansu...a lokacin abokan mahaifinshi da yawa suna kokarin taimaka mishi ya samu aiki amma yace shi sam bazaiyi aikin force ba infact bazai ma iya aiki under government ba...da taimakon wani uncle din Mummy wanda ya kasance likita ya bude katon Hospital dinshi mai suna Freedom Specialist Hospital...ya dauki ma'aikata sosai kuma most of them yare ne as gaba daya yanxu ya tsani hausa fulani because yana ganin kaman duk halinsu daya da 'yan uwan daddy...snn kuma ya tsani Gombe ya tsani duk wani abu daya fito daga garin...bayan shekara daya Allah yasa mishi albarka sosai dan ya kusan ninka abunda ya kashe a iya wnn shekaran...daga nan sai yayi tunanin ya bude Nursing and Midwifery College snn ya bude primary da secondary school duk a nan cikin kano...da yake kudi ne suke aikin in no time ya samu fili ya siya aka fara mishi aiki...a shekara na biyu ya bude Freedom College of Nursing and Midwifery Kano da kuma Freedom Science Academy Kano...nan ma yayi employing staff sosai suma kuma daga igbo sai yoruba sai kuma sauran tribes amma bai dauki bahaushe ko daya ba...a lokacin ya damqa Freedom Science Academy a hannun Aunty Sumy cox 6angaren data karanta knn shi kuma College din ya damqashi hannun abokinshi Dr.Nur...da shawarwarin Mummy dana sauran mutane abubuwa suke tafiya yanda ya kamata...cikin shekaru kalilan ya samu kudi fiyeda tunanin mai karatu...ya cire Miemie da ilham daga school da suke zuwa ya maidasu freedom shi kuma Sab ya nema mishi admission a Nigerian Police Academy Wudil as yana matukar son ya zama Police sbd it was his Dad's ambition.
In summary cikin shekara biyar Bobby ya zama hamshakin mai kudi a kano state...tuni ya gina musu very big mansion a can airport road inda babu mutane sosai...gaba daya rayuwarshi yanxub bai cika son mu'amala da mutane ba especially hausawa cox yana ga kaman suma zasuyi treating nasu some how sbd kasancewar Mummy inyamura...gidane mai kyau da girman gaske inda babu wanda zai takurama wani a cikinsu...a takaice dai yana kulawa dasu sosai sosai kaman yanda yayima Daddy alkawari...cikin shekarun nan kuma ya sake bude another College of Nursing and midwifery a Lagos sai kuma Freedom College of Health Sciences and Technology shima a Lagos...da yake a can ya girma har yayi primary da secondary school so yanada mutane a can sosai da suke handling mishi Colleges din as bai cika samun time yana zuwa sosai ba saidai yana providing musu duk wani abu da suke bukata...bayan nan kuma ya bude Freedom Medical College Gwagwalada Abuja...itama ba karamin kawo mishi kudi takeyi ba and a wata baifi yaje sau daya ba wani lokaci ma sai yayi two months baije ba sbd aiyuka da suke mishi yawa...haka rayuwansu yacigaba da tafiya har zuwa yanxub da Mummy ke son dawo mishi da duk pain da agony da suka fuskanta a baya.
Inaga gobe zaku jini shiru sbd zan danyi tafia...sai zuwa jibi in Allah ya kaimu💞🌸
Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidencs of payment ta 07063800556.
Rano✨
0 comments:
Post a Comment