A nata 6angaren itama tayi kuka tayi kuka har wani bacci ya lalla6o ya dauketa a nan inda take zaune ba tareda ta shirya ba..ba ita ta tashi a baccin ba sai after nine ta shiga bathroom tayo alwala snn tazo ta gabatar da sallah tareda da addu'an Allah ya daidaita tsakaninta da mijinta don bazata iya jure wnn fushin nashi ba..tana idar da sallah ko hijab din jikinta bata cire ba ta sake komawa flat dinshi wai ko Allah zaisa ya bude mata kofa amma iya tsaiwanda tayi a wurin ko motsinshi bata ji ba balle tasa ran ya bude mata kofar..tana kuka sosai ta sake komawa bedroom dinta ta wurga kanta kan sofa tareda kudundunewa cikin hijab dinta nan take kuma zazza6i mai zafin gaske ya rufe mata jikinta..dama tun safe takejin alamun zazza6in amma bai sauka ba sai yanxun tasan kuma bazai rasa nasaba da zullumi da kuma uban kukan da taci bane..ko baccin ma kasayi tayi don basu taba kwana separate room ba tunda sukayi aure sai yau..kuma ita tsoro takeji don ko a gida bata saba kwana ita kadai ba suna tareda Husna a school kuma tareda Billy so zata iya rantsewa ma ita bata taba kwana ita kadai a daki ba ko gidan aunty Fiddausi taje tareda Mufida suke kwana..tun kukan nata na fita tareda sound har ya koma zallar hawaye takeyi babu saurin komai sbd disashewa da muryanta yayi...har dare yayi nisa sosai bata samu bacci ba sbd zazzabin dake jikinta sai gabannin asuba ta samu baccin yayi gaba da ita shima kuma cikeda mafarkai marasu dadi.
Shima Bobby sbd rashin samun enough bacci har ya makara sallahn asubah dan lokacin da ya tashi an idar da sallah a masallaci..alwala ya shiga yayi snn ya gabatar da sallah yacigaba da zama nan yayi su azkhar da addu'o'i har saida gari yayi haske snn ya mike daga wurin ya fita direct to her bedroom dan tashinta tayi sallah..a nan kan sofa ya sameta kwance ta kudundune da hijab dinta..ya karasa a hankali ya zauna kusa da ita yana kallon yanda face dinta yayi jaa sbd kukan da kwana tanayi..lumshe ido yayi ya bude tareda kai hannu da nufin ya zare hijabin dake jikin nata sai yaji jikin ya dauki wani irin zafi kaman ana hura mata wuta..da sauri ya daga hijab din nata yana sake dora hannu jikinta yaji still temperature yayi rising baisan lokacinda ya dagata gaba daya ya cire mata hijabin ba..a firgice ta tashi taga baccin tana hada ido dashi ta mike zaune da sauri tana kwabe fuska tace"par..tner"..daure fuska yayi yana kallonta yace"what's wrong with u?.."kuka ta farayi tana cewa"partner dan Allah let me explain"..bai bari ta karasa ba ya dora finger dinshi akan bakin nata still fuskanshi daure yace"i said me yake damunki?.."kasa tayi da idanunta hawaye na sake cikowa cikinsu tace"fever.."yace"only fever?.."kai girgiza tana share hawayen tace"da ciwon kai"..dauke idonshi yayi daga kallonta dan yanda yaji kukan nata na neman karya mishi da zucia yace"kinyi sallah?.."Kai ta girgiza mashi alamar no yace"then shiga bathroom kiyo alwala"..kallonshi ta tsaya yi zatayi mgn ya dan daga murya yace"just go don't waste my time"..mikewa tayi da sauri ta shige bathroom tana shiga ta durkushe nan kasa ta fashe da matsanancin kuka..gaba daya gani tayi ya dawo mata asalin Dr Bobby data sani..gabanta har wani faduwa yakeyi duk ta kalleshi taga fuskan nan nashi a cunkushe..da kyar ta iya mikewa tayi easing kanta tayi brush snn ta daura alwalan ta fito tana takawa a hankali sbd zazza6i dake sake rufe mata jikinta..tana karasowa ya nuna mata inda ya shimfida mata praying carpet ya mika mata hijab dinta without looking at her yace"kiyi sallah"..ba musu ta amsa hijab din ta saka snn ta tsaya kan carpet ta tayar da sallah shi kuma ya mike zuwa kitchen don nema mata abunda zataci kafin ya bata drugs..hankalinshi ya tashi sosai da jin yanda temperature dinta yayi high hakan Sam bazai hanashi nuna mata girman laifinda ta aikata ba..takeaway din daya ajiye mata jiya a dinning yaga yana nan untouched meaning bataci abinci ba ta kwanta knn..duk sai ya sake jin jikinshi yayi sanyi kawai ya shiga kitchen yana tunanin abunda ya kamata yayi mata yanxu taci kafin ya bar gidan.. custard dinta ya gani inda ta ajiyeshi jiya dan haka ya dora ruwa a gas da sauri ya dama mata custard din ya zuba Madara da sugar snn ya koma dakin nata..a kwance ya sameta inda ta idar da sallah ta sake lullu6e kanta da hijab ya karasa ya ajiye custard din akan table snn ya mikar da ita tsaye bayan ya cire mata hijabin ya nuna mata custard din da hannunshi fuskan nan ba sarari yace"dauka Kisha"..kallon custard din tayi kafin ta dawo da kallon gareshi kmr zatasa wani kukan tace"na..koshi"..saida gabanta ya fadi da ganin yanda ya sake hade rai yana kallonta..murya a cunkushe yace mata"ina wasa dake ne?.."da sauri ta hau girgiza kai tana goge hawayen dake zubowa face dinta tace"ah..ah"..yace"then ki dauki custard din nan kisha idan baso kike kiga other side of me ba"..wani yawu ta hadiye mai daci snn takai hannu ta dauka custard din ta fara sha a hankali tana yatsine fuska kmr mai Shan magani..baifi spoon biyar tasha ba zata ajiye cup din yace"don't u dare..shanye shi zakiyi gaba daya"..haka tacigaba da danna custard din cikinta tana hawaye tana komai har Allah ya nufa ta gama shanyewa..dauka cup din yayi ya fita daga dakin can sai gashi ya dawo da drugs da goran ruwa a hannunshi..daga nan inda take ya tsaya ya 6alli drugs din ya mika mata tareda ruwan dake hannunshi yace"amsa Kisha"..nan ma ba musu ta amsa drugs din daga hannunshi ta fara zuba ruwan a bakinta snn ta watsa drugs din ta hadiyesu aikam tana hadiyewan taji wani irin amai ya taso mata tayi saurin mikewa tana toshe da bakin zata wuce bathroom saidai kafin ta karasa bathroom din ta durkushe nan kasa ta shiga kwarara aman a nan..Bobby na tsaye rungume da hannu yana kallonta..tausayinta yakeji sosai amma taurin kai da kuma zafin abunda tayi bazai bari ya nuna hakan ba..karasawa yayi shima ya durkusa nan inda take ya dagota jikinshi bayan ya fuskanci ta gama aman ya dauketa cak ya shiga bathroom da ita..ruwan zafi ya hada ya mata wanka da kanshi yanata wani daure dauren fuska shi a dole baiji wani abu ba har ya gama ya daura mata towel ya fito da ita..da kanshi ya shiryata yasa mata simple doguwan riga mara nauyi snn ya kwantar da ita kan gado ya fita daga dakin..tea ya sake hada mata da Milo kadai sai sugar snn ya hada da injection ya dawo dakin nata..wnn karon da kanshi ya bata tea din tasha snn ya shiga withdrawing alluran da zaiyi mata..tana ganin allura duk ta rikice tana kuka tana rokon yayi hakuri shidai baice mata komai ba har ya gama hada alluran sai kawai ya tsaya yana kallonta..duk wnn abun da yake Allah ya sani karfin hali ne kawai amma shi kadai yasan yanda yakeji a cikin ranshi..yasan halinta ne indai ba wuta wuta yayi mata ba bazata shiga hankalinta ba shiyasa zaiyi iya bakin kokarinshi yaga bai bar tausayinta da yakeji yayi tasiri a yanxun ba har saita fahimci kuskuren data aikata..zaunawa yayi kan gadon ya dagota yayi mata alluran tanata faman ihu amma bai saurara ba saida ya gama snn ya rungumeta a jikinshi yana patting bayanta a hankali..wnn zafin na jikinta har tsoro yake bata wlh..ji yake kaman yayi transferring ciwon daga jikinta zuwa nashi da kilan bazai dingajin yanda yakeji yanxu da ciwon yake a jikinta ba..karfin hali kawai yakeyi amma yana cikin damuwa sosai..bai ajiyeta ba saida bacci ya dauketa snnya kwantar da ita ya rufeta da duvet ya fita daga dakin..wanka yayi shima ya shirya snn ya sake komawa dakin nata ganin baccinta yayi nisa sosai yayi deciding ya dan leka hospital kona few hours ne ya dawo tunda yanada aiyuka a can..ko abincin shi baici ba ya karasa shiryawa ya bar gidan tareda driver dinshi..yau ko main house bai shiga ya gaida Mummy ba sbd baison ta tambayi abunda ke damunshi.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
65
Har wajen 1 yana Hospital yanata duba patients ga kuma hankalinshi gaba daya yana kanta..so yake yaji halinda take ciki kuma yanata Kiran wayanta bata dauka dan haka yayi deciding ya kira Mummy tasa aje a duba mashi ita..bayan ya sallami patient din gabanshi bai sake Kiran wata ba yayi relaxing kan seat dinshi yana dialing number Mummy..tana dauka ko gaisawa bai bari sunyi ba yace"Mummy aje a dubamun Aysher plss..batada lafia and inata kiran wayanta bata picking"..da dan damuwa Mummy tace"subhanallah what's wrong with her?.."murya can kasa yace"fever da headache"..Mummy tace"amma kasan batada lafia shine baka zauna tareda ita ba Bobby?..yanxun idan wani abun ya sameta fa?.."a hankali yace"Mummy nothing will happen to her inshaAllah..ya kama dole ne fitan nima da bazan fito ba..yanxun dai ko Miemie ki tura taje ta ganomun halinda take ciki plss..i still have lots of patients ne da zuwa zanyi da kaina in ganta"..ajiyar zucia Mummy ta sauke kafin tace"don't worry yanxu zataje ta ganota..i will get back to u"..yace"alright Mummy.. nagode"..Mummy bata sake cewa komai ba tayi hanging Kiran..fitowa tayi da kanta tacema Miemie dake karatu sbd sun kusa fara waec taje ta duba mata Aysha wai bata da lafia..da sauri ta warware veil dinta data daura a kai ta yafashi snn ta fita daga gidan..ta main gate ta fita sbd taga kofan cikin kaman a kulle ne..tana zuwa ta kwankwasa mai gadi ya bude mata ta shiga cikin gidan kai tsaye..a bedroom dinta ta sameta tashinta daga bacci knn sai kuka take har lokacin kuma akwai fever sosai jikinta..hankali tashe ta kira Mummy ta fada mata halinda ta sameta a ciki don haka Mummy ta turo driver dinta tace ya daukesu kawai su wuce asibiti tunda Bobby yana can sai ya dubata..Miemie ta dauki hijab dinta tasa mata snn ta kamata suka fita compound inda driver je jiransu..suna shiga motar ya tadata suka fita daga gidan.
Suna shigowa hospital din Miemie ta fita da sauri zuwa office dinshi ta banka ta shiga ko sallama batayi ba ta fada mashi halinda ake ciki..yanda ya fito a rude har mutane saida sukayi mamaki dan lokaci daya yaji komai nashi yayi tsaye cak..da sauri ya karasa inda motar yake ya bude back seat nan ya ganta jingine jikin seat din idonta na fitar da hawaye..hannu yakai ya ta6a forehead dinta yaji still da zafi a jikin kawai sai ya dauketa a hannunshi ya fito da ita daga motar zuwa cikin asibitin..sauri kawai yakeyi ya karasa office dinshi bai ko damu da kallon da jama'a ke binshi dashi ba..yana shiga ya kwantar da ita kan gado snn ya cire mata hijabin jikinta kawai sai ya tsaya yana kallonta without saying anything..Miemie data shigo office din da sauri yace ta shiga bayi ta kawo mashi warm water da towel..ba musu tayi yanda yace ta kawo mashi yace taje driver ya maidata gida..shi kuma ya fara jika towel din yana shafa mata ruwan a jiki sbd temperature nata ya sauka..bayan ya gama ya fita zuwa pharmacy da kanshi ya kar6o drip da allurai snn ya koma office din nashi..tana ganin drip da allurai hannunshi ta fara kuka shidai bai iya ce mata komai ba ya samu ya lalla6a yasa mata drip din don yasan ba wani abinci zata iyaci ba..yana gamawa ya mata alluran da zaiyi saurin saukar mata da fever din snn yaja seat dinshi ya zauna nan kusada ita yana kallonta..Aysha na kuka sosai tace"partner am so sorry plss"..hannunta ya kama ya rike cikin nashi baidai ce mata komai ba..mikewa ta shiga kokarin yi shi kuma yayi saurin maidata yana nuna mata cannular dake hannunta yace"careful mana"..komawa tayi ta kwanta tanacigaba da kallonshi tana hawaye..shima kallonta yakeyi yanajin wnn abun da yazo ya tsaya mashi a throat dinshi tun jiya yasan indai ba mgn ya samu yayi da itaba wnn abun bazai fada ba dan haka ya dan runste eyes dinshi kafin a budesu a kanta voice dinshi kasa kasa yace"so da gangan kikayi hakan koh?.."da sauri ta hau girgiza kai tace"wlh coincidence ne..i never knew such thing will happen am sorry"..yace"but u even hugged him..why did u do that?.."tace"i thought it was u sbd eyes dina a kulle suke saida naji perfume dinshi ba irin naka ba nasan u are not the one..kayi hakuri ka yafemun dan Allah"..ta karasa mgnr tana kuka sosai..shiru kawai yayi yana kallonta yasan shima yayi over reacting jiyan nn amma it wasn’t his fault..sake matsawa yayi yuana rikeda hands dinta yace"nima am sorry for reacting the way i did..i shouldn’t have done that so kiyi hakuri"..kai kawai take gyada mishi..ganin yanda har jikinta na rawa sbd kukan da takeyi yace she should stop talking zasuyi mgn anjima..sosai ya sake bata hakuri yana cewa yasan bai kyauta ba..itama tace mishi ko dan gaba if wani abu irin wnn ya faru saurin fushi bayada amfani gwara su zauna suyi communicating that communication is a solution to any problem..shiru kawai Bobby yayi yana kallonta dan kunya yaji sosai wai itace take fada mashi what is right..sauka ajiyar zucia yayi yana ayyana idan fa bai dena wnn saurin fushi da zafin ran ba watarana zaiyi dana sani duk sai yaji jikinshi yayi sanyi yace inshaAllah zaiyi kokarin gyarawa kuwa..ita kuma tayi shirun bata sake mgn ba har drip din ya kare zuwa lokacin kuma fevern dake jikinta ya dan sauka shima sai a lokacin ya dan samu peace of mind..a hankali ya mike zuwa inda wayanshi keta ringing ya dauka snn ya samu wuri ya zauna bayan yayi picking call din..a daya bangaren Nur yace"hey are u at the office?.."kmr bazaice wani abu ba sai can yace"what?.."Nur yace"just answer me dan rainin wayo"..lumshe ido yayi yana kallon inda take kwance kafin a hankali yace"ina nan".. Nur yace"ohk gani nan zuwa"..daga haka ya ajiye wayar tareda mikewa zuwa inda take ya maida mata hijab dinta yana cewa"do u need anything?.."a hankali ta girgiza mashi kai alamar no..yace"bazaki ci komai ba?.."nan ma kan ta sake girgiza mashi yace"bari Nur yazo idan ya tafi sai in maidaki gida tunda zazza6in ya sauka"..kai kawai ta iya gyada mashi shi kuma ya fita daga office din..can parking space yaje ya tsaya tana jiran isowar Nur bai dade da tsaiwa ba kuma sai ga Nur din ya karaso..bai bari ya karaso nan inda yake ba ya nufi wurin motar shi..yana zuwa ya bude ya shiga tareda relaxing yana kallon Nur din a hankali yace"daga ina kake haka?.."maimakon ya bashi amsa sai cewa yayi"wai what's wrong with ne?..u look disturbed..ina Lamido?.."a hankali Bobby yace"she's inside"..Nur ya dan wara idanu yace"inside kuma?..yanxu wurin aikin ma saika taho da ita Bobby sbd gajen hakuri"..harara ya watsa mashi mai kyau tareda sakin wani tsaki yace"u are annoying wlh..to batada lafia kuma ni bana gidan shine aka kawota na dubata"..wani murmushi Nur ya saki yana shafa gemu yace"so meke damunta?.."Bobby yace"fever..amma nasa mata drip yanxu fevern ma ya sauka"..Nur na gyada kai yace"Allah bata lafia..amma why ba'a yi mata test ba?.."juyawa yayi ya kalleshi rai a dan 6ace ganin kmr neman zance kawai yakeyi yace"ban saniba".. Nur ya kwashe da daria yana kallon abokin nashi yace"kaga malam ka maida wukar ka ni bani na kar zomon ba..am only trying to be of help"..a dan fusace Bobby yace"to hell with u and ur help"..kallonshi kawai Nur yake har yanxu bai bar murmushi ba yace"ohk let me keep quiet tunda bakaso..dama cewa zanyi kasa ayi mata pt kilan she's pregnant"..da sauri Bobby ya juya yana kallonshi idanu a waje yace"what do u mean?.."Nur yace"Ina nufin kilan ciki ne da ita mana..kai ina ka taba ganin anyi haka kawai matarka ba lafia kazo ka wani farayi mata blind treatment baka tunanin ko karuwa ka samu"..wani irin diff Bobby yayi yana bin Nur da kallo kmr bai gane abunda yace ba..tunani ya tafi yi tabbas tunda akayi bikinsu bata ta6a period ba and idan ba wai manta lissafin yayi ba bikinsu saura 2 weeks tayi period and idan akayi adding two weeks to that shine ovulation period dinta kuma a daidai wnn time din akayi bikinsu so there is 90% possibility na zata iya samun cikin within wnn kwanakin sbd time din ovulation dinta ne..nan take fuskanshi ya washe da wani irin murmushi yana sake wara idanu akan Nur hannunshi dafe da bakinshi cikin tsananin farin ciki da kuma mamaki yace"oh my Goddess..why didn't i think of this?.."harara Nur ya watsa mashi yace"oho banza"..sake juyawa yayi yana kallon Nur da kyau yace"Nur ina kyauta zaton wnn mgnr naka gaskia ne..she might be pregnant oh Allah"..ya karasa mgnr full of excitement kaman an tabbatar mishi tana dauke da cikin already..shi gaba daya tunaninshi baizo nan wurin ba all he was thinking was incident daya faru jiya har ya kulle mashi kai ya kasa zargin cewa cikin ne da ita.."ikon Allah"..ya sake fada out of excitement Nur dai na zaune yana kallon ikon Allah at the same time yana mishi daria..shi kanshi zai so ace yau Lamido tanada ciki ko dan yayi kallon uban rawan kan da Bobby zaiyi akan cikin...bude motar yayi ya fita shima Bobby ya fito da sauri ya kama hanyan cikin asibitin yana fadin"we need to conduct this test now..i pray it turn out to be truth"..Nur dake bin bayanshi ya amsa da"Ameen"..har suka shiga cikin building din..direct office dinshi suka shiga lokacin tana kokarin mikewa tsaye Bobby yayi saurin karasawa inda take yana kallonta full of love and excitement yace"baby where are u going?.."a hankali tace"ruwa zansha"..ruwan ya dauko da sauri ya kawo mata yana cewa"here u go"..ta saki dan murmushi snn ta amsa ruwan tasha cikeda mamakin sudden change din nan nashi?.. it's like ya gama saukowa completely..saida ta gama Shan ruwan snn ta lura da Nur dake zaune kan sofa yana kallonsu..ta danyi kasa da kanta tace"sir Ina yini"..yace"lafia ya jikinki?.."tace"naji sauki"..yace"to Alhamdulillah".. Bobby dai drawer ya bude ya dauko duk wani abu da zaiyi amfani dashi snn ya koma wurinta ya shiga lallabata wai zai dauki blood sample..itadai batace komai ba ya dauki sample din snn yaba messenger bayan ya rubuta test din da za'ayi a paper yace ya kai lab yace yana jiran result yanxun nan.
Ana kawo result din Bobby yayi saurin karba daga hannun messenger daya kawo har ya fara budewa sai kuma yayi saurin maidata yanda take tareda juyawa yana kallon Aysha da har yanxu ke zaune tana kallonsu..juyawa yayi suka hada ido da Nur sai kuma ya sake juyowa gareta ya sakar mata murmushi.. Lamido data kasa gane what they are up to kawai sai ta sauka daga gadon a hankali tana kallonshi ta nuna bathroom dinshi tace"zanyi alwala"..da sauri kmr jira yake yace"ok babe"..ta saki murmushi snn ta juya ta shiga bathroom din...tana shiga Bobby yayi saurin bude papern ya wara ido sosai yana karanta content din dake ciki idanunshi na sauka inda yaga an rubuta positive yayi saurin yar da papern tareda juyawa ya kankame Nur sosai kmr zai maidashi ciki..cikin so much excitement ya juya language zuwa Igbo yanda bazata fahimta ba yake cewa"Nur it's positive.. it's positive wlh.. Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah"..ya karasa mgn still yana rungume dashi kaman shine mai cikin..shima Nur farin ciki sosai ya taya abokin nashi dan haka yayi hugging nashi back tareda daka tsalle yana wani iri ihu shima da Igbo yace"ekele bro..ekele"(congratulations bro.. congratulations)..shima Bobby tsallen yayi exactly irin yanda Nur din yayi kawai sai Hamdala yake yama rasa inda zaisa kanshi sbd excitement..haka suka rungume juna suna ta faman tsalle a dakin kmr kananun yara..Aysha dake la6e bakin kofa tana kallonsu batasan lokacinda ta fashe da daria ba..yanda suka rungumi juna suna tsalle tsalle sai suka koma mata kaman small kids..wato dai su biyun nan are so something else..dama tunda taga yanda suke kallon kallon tasan kilan space sukeso ta basu and gashi nan ta gani saidai Allah kadai yasan dalilinda yasa suka wnn farin cikin because ba gane language da suke speaking take ba..daria takeyi sosai wanda rabonta da irinshi tun kafin faruwar incident din jiya...Saida suka gama tsalle tsallensu Nur yayi saurin daukan paper da Bobby ya yarda a kasa shima ya karanta..nan take ya wara ido yana sake duban abokin nashi da wani killer smile ya danyi kasa da voice dinshi yanda bazata jiyoshi ba yace"oh my Goodness yanxun five weeks knn da aurenku and the pregnancy is four weeks..what a sharp shooter"..ya karasa mgn yana kashe mashi ido shidai Bobby bai iya cewa komai ba tsabar farin ciki kawai sai ya durkusa ya fara sujood shukur shi kuma Nur ya kama kugu da hannunshi daya..dayan hannun kuma ya dafe forehead dinshi dashi snn ya danyi bending kaman zaiyi ruku'u ya shiga juya waits dinshi yana taka rawa a hankali yana cewa"aga m abu nna..aga m abu nna"..(am going to be a father..am going to be a father)..cikin excitement sosai yake rawa yana waka Kai kace shine za'ayi ma haihuwan..Bobby daya gama sujood dinshi tun daxu dagowa yayi kawai yana kallonshi with a very wide smile..yanda yake rawan ba karamin daria ya bashi ba..da dadewa dama yasan Nur yafi karfin aboki a wurinshi saidai ya kirashi da brother so ko kusa baiyi mamakin wnn farin cikin da yake tayashi ba..shi din mai sonshi ne kuma tsakani da Allah..ya tabbata wnn excitement da yake ciki da za'a bincika zuciarshi za'a ga har cikin ranshi yake tayashi farin cikin..he is one in billion..samun aboki irinshi yana da wahala sosai and shiyasa yake godia wa Allah for having him..soyayyan da suke ma juna genuine ne ba fake ba...Lamido dake bathroom tana kallonsu tayi daria kaman cikinta zai kulle..dukda batasan me sukema wnn farin cikin ba ta tabbata it's something huge don tunda take bata taba ganinsu cikin such excitement ba..Saida ta gama kallon snn tayi alwalan ta fito daga bathroom din kanta a kasa tana kokarin boye darian dake son sake kufce mata.. Nur daya dage yana dirkar rawa yana ganinta yayi saurin mazewa yana wani shafa kai shi a dole ba kamashi tayi ba...Bobby dake kokarin danne dariar dake cinshi juyawa yayi ya isa gareta kafin ta zauna kan bed ya janyota jikinshi kawai sai ya rungumeta so tight yana sauke numfashi..ta kwalo ido waje tana kokarin kwace kanta sbd presence na Nur amma sam yaki sassauta rikon da yayi mata balle ta samu daman kwacewa din..wani irin farin ciki ya tsinci kanshi a ciki.. right now gani yake dunia babu Wanda ya kaishi farin ciki kaman dai ba shine yake ganin babu wanda ya kaishi shiga kunchi da damuwa a while a go ba..wato Allah ba yanda bayayi da bayinshi a duk lokacin da yaso..idan yaso ya saukar Maka da farin ciki haka idan yaso ya saukar maka baqin ciki.. that's how life is shiyasa masu iya mgn sukace ba kullum ake kwana a gado ba and it's true..ba koda yaushe mutum ke dawwama cikin farin ciki ko akasin haka ba..dole watarana za'a jarrabaka da either happiness or sadness saidai Allah ya bamu ikon yadda da qaddara mai kyau da mara kyau...yayinda yake rungume da ita Nur sai ya zaro phone dinshi daga aljihu ya shiga camera ya fara musu video yanajin yanda shi kanshi suka burgeshi sai yaji inama shi da pretty ne haka..at this point sai yaji wani shaukin sonta ya kamashi..yaji inama a bashi ita ya aura koda bata gama secondary din ba amma yasan that can never be possible..Saida Bobby ya dauki lokaci mai tsaho yana rungume da ita yana kuma sake ma Allah godia cikin zuciarshi snn ya raba jikinshi da nata tareda hade goshinshi da nata ya lumshe ido yana sakejin wani extraordinary feeling yana sake bijiro mishi..he missed her like crazy sai kuma abun ya hadu da farin cikin samu karuwa tsakaninsu..he just can't thank Allah enough for such a blessing..hannu ya sake mikawa ya zagayo waist dinta dashi pulling her more closer to himself snn ya lumshe ido ya manna mata peck a goshinta followed by cheeks da tip of her nose..yana bude ido yaci karo da Nur da har zagayowa yayi ta saitin da faces dinsu zaifi fitowa sosai yana cigaba da recording video din yana sakin murmushi hadda su gyada kai..suna hada Ido yayi saurin saving video din ya wani kashe mashi ido daya yana cewa"ahuru m ihunanya"..(I see love)..murmushi Bobby ya saki tareda gyara mata hijab dinta snn yayi mata side hug yana kallon beautiful face dinta yace"i think we should go home now"..batayi musu ba ta gyada mishi kai alamar ok shi kuma ya sake pecking forehead dinta snn ya kama hannunta suka bar office din Nur na binsu a baya..sallamar driver dinshi yayi yace ya wuce da motar gida su kuma suka shiga motar Nur suka nufi gidan a cikinta..duk yanda Aysha taso ya zauna front seat kin yadda yayi wai saidai ya zauna kusada ita gashi kuma ya kasa dauke ido a kanta daidai da one second..gani yake kaman idan ya rufe idanun za'a tasheshi daga bacci ace dreaming yake..ita dai mamakin wnn sudden change din nashi take don batasan meya sauko dashi daga dokin zuciar da ya hau all of a sudden ba..amma koma menene she's happy tunda ta dalilinshi ya dena fushi da ita..sai satar kallonshi take tanajin yanda tayi missing dinshi itama..ba dan presence na Nur ba da babu abunda zai hanata mannewa a jikinshi kafin su karasa gida amma bazata iya ba sbd tanajin nauyinshi sosai..gashi kuma suna hada ido dashi sai yayi pecking forehead dinta dan haka tilas ta dena kallon nashi sbd batason wnn abubuwa da yake mata gaban provost wlh..idan shi yana ganin friend dinshi ita fa har yanxun tana mishi kallon gentle provost dinsu mai bala'in kirki da mutunta students dinshi.
Suna isa gida dama direct main house Nur ya shiga yayi parking snn ya bude kofa ya fita..shima Bobby fitowa yayi snn ya zagaya ya fito da ita sai wani hadata da jikinshi yake ita kuma tana kaucewa amma still bai bari bar har suka shiga gidan..Nur dai a baya yake binsu yana murmushi har yanxu kasa dena smiling sbd excitement..he is so happy for the both of them..suna zuwa daidai entrance Lamido ta dakata tareda zare hands din Bobby daga jikinta tana kallonshi da dan marairaicewa tace"partner just stop it mana..Mummy fa tana ciki"..murmushi ya saki tareda bending ya danyi pecking lips dinta snn ya kama hannunta ya rike yana kallon eyeballs dinta yace"is this ohk?.."girgiza mishi kai tayi da sauri tana kwabe fuska tace"Noo"..sai kuma ta shiga bubbuga kafa zata fara mishi kukan karya yayi saurin sakin hannun nata yana cewa"No no don't do that plss..gashi na saki hannun naki is that ok?.."kai ta gyada mashi tana sakin murmushi sai kuma ta shige cikin parlon..da kallo ya bita har ta 6ace ma ganinshi snn ya sauke wani ajiyar zucia mai karfi daidai lokacinda Nur ya karaso inda yake dan haka suka shiga ciki a tare..Lamido na shiga Miemie dake zaune dinning tana karatu tayi saurin mikewa tazo gareta tana wara idanu cikeda mamaki tace"Goodness!..aunty Aysha me yayi maki haka naga kin samu sauki?.."Bobby da yaji duk abunda ta fada ya dan watsa mata harara yana cewa"gidanku nayi mata"..da sauri ta kama bakinta tana yin kasa da kanta tace"ohh yi hakuri Uncle Bobby"..bai sake ce mata komai ba ya wuce flat din Mummy shi kuma Nur ya karaso nan cikin parlon ya zauna yana kallon Miemie da yakejin kmr ya maidata ciki yace mata"hey pretty"..kama hannun Aysha tayi suma suka karasa ciki suka zauna snn ta dawo da kallonta gareshi tana murmushi tace"Uncle Nur ina yini"..yace"fine pretty..ya exams?.."tace"Monday zamu fara"..yace"MaashaAllah..Allah bada sa'a..yasu aunty da Ilham?.."..tace"Ameen Ameen Uncle Nur nagode..su Aunty suna gidansu muma gobe zamuje ko aunty Aysha?.."ta karasa mgn referring to Lamido dake zaune tana sauraran conversation dinsu tana daria kasa kasa..da sauri tace"yeah indai naji sauki sosai gobe zamuje inshaAllah"..sai kuma ta mike tunawa da batayi sallah ba tace ma Miemie"rakani daki inyi sallah plss"..ba musu Miemie ta mike suka nufi dakinta dake nan cikin parlon don ta baro flat din aunty sumy tun baya barinta gidan..suna shiga Aysha tace mata ta koma kar su bar Nur shi kadai a parlor dan haka Miemie ta koma parlor yayinda ita kuma ta tayar da sallahrta..har yanxu kuma ba wani karfi takeji a jikin nata sosai ba.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
66
Bobby na shiga ya iske Mummy a parlor suna waya da aunty sumy..bai damu ko ta gama wayan ko bata gama ba kawai yana zuwa ya zauna kusada ita tareda mata side hug ya kwantar da kanshi a shoulder dinta cikin so much farin ciki yace"nwunye m di ime Mummy"..(my wife is pregnant Mummy)..da sauri Mummy ta dago kanshi tana kallonshi cikin tsananin farin ciki tace"are u for real?.."da sauri yace"yes i am Mummy..she is four weeks pregnant"..wani irin zare idanu Mummy tayi cikin so much excitement kafin tace wani abu aunty sumy data gama sauraran duk abunda ya fada sbd call dinsu is still connected ta saki wani irin guda tana cewa"My Bobby is becoming a Father.. Alhamdulillah"..da sauri Bobby ya dauki wayan daga jikin Mummy ya manna ta kunnenshi yace"yes aunty am becoming a father..am becoming a father"..wani murmushi ta karasa saki before tace"congratulations qanina..Allah kawo mana babyn nan lafia and extend my regards to Aysha kace mata nace she should take care of our baby sosai"..ajiyar zucia ya sauke yana cewa"aunty ai har yanxu bata sani ba..i didn't tell her"..da sauri aunty sumy tace"why?.."yace"rigima zataimun ne..i have to wait for the right time..yanxun allow me to talk to my Mummy plss..my regards to Ilham..kice mata her Uncle Bobby yayi missing dinta da yawa"..yana gama fadin haka bai jira jin me zata ce ba yayi disconnecting call din don yasan aunty sumy da zance sake dauko wani dogon surutun zatayi..yana ajiye wayar Mummy dake kallonshi full of surprise tace"meyasa baka fada mata ba Bobby?.. what's the meaning of this?.."kama hannunta yayi yana dan marairaicewa yace"Mummy nasan halinta rigima zataimun wlh..kullum cewa take ita batason ta samu ciki da wuri and tunda Allah baisa ta gane ba we shouldn't tell her plss"..a hankali Mummy tace"amma kasan zata iya ganewa ko ba'a fada ba Bobby..she is a health worker too..zata iya noticing some changes a jikinta da zaisa ta fahimci ciki ne da ita"..yace"na sani Mummy amma we shouldn't tell her now..gwara mu bari har zuwa lokacinda zata fahimci tana dashi din da kanta maybe by then bazata dagamun hankali ba"..ajiyar zucia Mummy ta sauke sai Kuma ta rungumeshi cikin so much happiness tace"am so happy for u son..Allah ya basu lafia ita da abunda ke cikinta snn Allah ya sauketa lafia"..rungumeta back shima yayi yana wani lumshe ido sbd dadi yace"Ameen Ameen Mummyna..i can't love u less".
Da dare bayan sun dawo gida ya tilasta mata taci abinci snn ya bata paracetamol sbd fevern da yaji kaman zai dawo mata..suna zaune parlor suna kallo tanata faman cin apple daya yanyanka mata a plate daga ita sai dan sweet pants dinta blue da crop top baby pink..kanta da akayima kitso a bude sai daukan ido yake sbd kyan da yayi..yayinda ta maida hankali wajen cin apple dinta Bobby kuma yana zaune yana kallonta kmr yau ya fara ganinta..she looks do adorable right now..so looks cute that har baison ya dauke idanunshi daga kanta..kallonta kawai yake yana imagining yanxun da akwai da ko 'yarshi inside her tummy..banda smile ba abunda yake saki yana shafa saje zuwa gemunshi cikin so much happiness..kawai he's eager to see tummy dinta ya zama qato..he can't wait for the baby to come..he wants to hold the baby's hands snn yayi kissing forehead dinshi yace he loves him or her..he just can't wait for the baby's arrival..he's so desperate..yayi nisa sosai cikin tunaninshi sai sakin smile yake kuma har yanxun yana shafa beard dinshi kmr wani sabon kamu..kamar daga sama yaga ta mike da sauri ta kama hanyar bedroom dinta har tana hadawa da gudu sbd ringing din wayanta data jiyo..nan da nan ya dawo hayyacinshi tareda mikewa shima yabita da sauri yanajin wnn gudun da take har cikin zuciarshi wlh..yayi zaton wani gagarumin abun zatayi a dakin but to his biggest surprise yana shiga yaga ta dauki wayanta da bai dena ringing ba tayi saurin picking call din ganin Hammanta ke kira ta zauna gefen gado tareda Kara wayan a kunnenta tana wani cunno baki tace"ba ruwan ni dakai"..daga daya bangaren Hamman nata ya saki daria yana cewa"C'mon mana Maama..ba'a jin tsakanina dake fa?.."sake turo bakin tayi tace"ba wani Maama ni ka dena kirana Maama tunda baka damu dani ba"..jingina Bobby yayi jikin kofar dakin tareda rungume hannu yana kallon ikon Allah..yanxun Najeeb din takema wnn shagwaban sai kace muharraminta?..Najeeb dake dariar wnn rikicin nata yace"ohk wait kiji abunda zan fada maki..gobe zamuzo Kano"..batasan lokacin da ta saki wani irin ihu ba sbd farin ciki tace"dan Allah da gaske Hamma?.."yace"of course mana..tareda su Husna da Bilkisu"..nan take ta Kara sakin wani ihun tana cewa"Hamma amma dai kwana zakuyi koh?.."da sauri yace"Ammi tace banda kwana so a goben zamu dawo"..dan marairaicewa tayi kmr yana ganinta tace"haba mana plss..ya kamata ku kwana ai"..yace"idan kinaso su kwana saidai ki kira Ammi da kanki"..yana gama fadin haka tace"alright let me call her yanxu"..daga haka ta kashe kiran sai kuma ta shiga neman number Ammi zatayi dialing..a hankali Bobby ya karasa inda take ya wani daure fuska ya fizge wayar daga hannunta yace"are u mad?..bakida hankali zakizo kina gudu haka?..and waya fada maki ana yima cousin irin wnn shagwaban?.."murmushi ta saki tana kallon yanda ya hade girar sama dana kasa..batace dashi komai ba sai mikewa da tayi tareda matsawa inda yake ta shige jikinshi..a tare suka saki ajiyar zucia Bobby ya zagayeta da hands dinshi murya can kasa yace"how many times do i have to tell u this?..na fada maki cewa duk wani cousin dinki ba muharraminki bane amma bakiji..ko so kike na fara kishi dashi?.."a hankali ta girgiza mashi kai alamar no..yace"then meyasa kike mashi abubuwan da ni kadai ya kamata kiyima a matsayina na mijinki?..kina tunanin bana jin haushi ne?.."a hankali ta dago kanta tana kallonshi shi kuma yayi cupping fuskanta yana cigaba da kallonta yace"if u think bana jin haushi u are very mistaken baby..kishi nakeji sosai duk naga kina mishi wnn shagwaban..banaso"..hannunta ta mika itama tayi cupping nashi fuskan tareda dan dage ta manna mishi peck a forehead snn tace"to na dena partner..am sorry".. pecking nata back shima yayi yana cewa"na hakura love..yanxun yaushe ne zasuzo?.."da sauri ya dago taga jikinshi tana cewa"gobe..inaso in kira Ammi ince ta barsu su kwana yace saidai inyi mgn da ita"..ba musu ya kama hannunta suka zauna snn ya mika mata wayarta dake hannunshi yace"ohk call her"..da sauri ta karba tayi dialing number din Ammi..tana dagawa Aysha ta wani marairaice tana langabar da wuya kmr Ammin na ganinta tace"Ammi banida lafia"..daga daya bangaren Ammi tace"Amin wa'alaiki salaam"..da sauri ta gyara mgnrta da cewa"sorry salamu alaykum Ammi"..Ammi tace"wa alaiki salaam..ya gidan"..tace"lafia lau amma banida lafia"..ta karasa mgn kmr zatasa mata kuka ta wayar..Ammi tace"rashin lafiar kikema wnn abun sbd har yanxu bakida hankali"..turo baki tayi tace"Ammi zazza6i nakeyi sosai fa..kuma hadda amai"..Ammi tace"to Allah ya sawake..laifin Bobbyn ne da bai danqara maki allura ba"..daria sosai mgnr Ammi ya bata aikam ta shiga yinta kmr ba gobe..Saida tayi me isarta snn tace"Ammi wai su Husna zasuzo gobe?.."Ammi tace"eh zasuzo inshaAllah..tareda Bilkisu da Najeeb"..Aysha tace"Ammi dan Allah dan annabi su kwana"..Ammi tace"aah Aysha su da zasuzo da yawa banason suzo su takurama mijinki ne gwara suzo a goben su dawo ai yafi babu"..da sauri tace"Ammi dan girman Allah su kwana shida bama a dakina yake kwana b.."bata karasa ba Ammi tace"zakici ubanki wlh..wa kikaji ya tambayi inda yake kwana..wato har yanxu wnn shashancin yana nan kanki koh?.."shiru tayi tana danne dariarta tace"to Ammi kiyi hakuri..amma dan Allah su kwana ai munada dakuna da yawa"..Ammi tace"shknn sai suyi kwana biyu..dama shi Najeeb yace akwai aikin da zaiyi a garin na kwana biyu so idan ya gama sai su dawo tare"..cikeda farin ciki tace"yauwa Ammi nagode sosai Allah ya kara girma..Ammi kema dai ya kamata kizo wlh"..Ammi tace"zanzo amma ba yanxu ba..saiki daure ki dinga shan magani ba sai ama tilastaki ba..Allah ya baki lafia ya maku albarka gaba daya"..cikin tsananin jin dadin addu'an na Ammi tace"Ameen Ameen Ammina..nagode"..Ammi tace"shknn sai anjima..ki gaida Bobbyn dasu mamanshi"..da sauri tace"zasuji inshaAllah..sai da safe"..daga haka sukayi sallama..Bobby kmr jira yakeyi ta ajiye wayar ya shiga kyalkyala mata daira sosai..dama da dadewa ya fuskanci there is a little drama between the mother and the daughter..hakan kuma its the sign of love they have for each other..yanda ta dauko zancen ba'a dakinta yake kwana ba ita kuma Ammin ta katseta was so very funny to him..kallonshi tayi yanda yake mata daria tana dukan chest dinshi tace"what?.."ya kama hannunta ya rike yana kokarin dakatar da darian nashi yace"nothing baby..kawai dai am happy gobe su Husna zasuzo"..lokaci daya ta washe bakinta itama tace"nima am happy sosai sbd nayi missing dinsu..i can't wait to see them"..tana rufe baki ya dauketa suka fita daga dakin yana cewa"yanxun muje ki karasa cinye apple dinki sai muje mu kwanta sbd mu tashi da wuri koh?.."kai ta gyada tana sake lafewa a jikinshi..daga haka suka fita daga dakin..parlor ya koma ya dauki sauran apples dinta snn ya wuce flat dinshi..zaunar da ita yayi kan sofa tareda dora mata plate din apples din akan laps dinta yace he's coming..parlor ya koma ya kashe su tv da bulbs snn ya rufe gidan da key ya koma flat din nashi..kwanciya yaga tayi bayan ta ture apple din nata gefe..ya karasa da sauri ya dagota yana cewa"baby what?..why baki cigaba da cin apple dinki ba?.."hannunshi ta kama ta dora a forehead dinta idonta har ya ciko da hawaye tace"kaji fevern nefa zai dawo"..da sauri ya zauna tareda dorata a jikinshi yana girgiza mata kanshi yace"no don't cry plss..bazai dawo ba inshaAllah"..kuka ta fara mishi sosai tace"Allah zai dawo..yanxu haka su Husna zasuzo gobe ni banida lafia"..rungumeta yayi sosai yana shafa bayanta cikin sanyin murya yace"baby dan Allah stop crying..idan kina kuka zakiyi ciwon kai fa"..shiru tayi mishi tana cigaba da hawayenta as Allah kadai abunda takeji..nan take hankalinshi ya tashi ya shiga aikin rarrashi..gani yake kmr wnn kukan zaiyi affecting babyn cikinta..yasan yanda baason pregnant woman da damuwa shiyasa yake tsoron wnn halin nata.. yanxu idan wani abu ya samu babynshi ya zaiyi?..lalla6ata ya dingayi sosai har tayi bacci a jikinshi ya samu ya kwantar da ita..har zuwa lokacin kuma jikinta akwai zafi sosai dan zafin ma yafi wanda yaji a jikin nata daxun..lumshe ido kawai yayi yana tunanin taimakon daya kamata ya bata..yasan babu treatment din da zai dauke mata wnn zazza6in indai ba lokacin daukewan shi ne yayi ba..gashi kuma yanxu tunda yasan tanada ciki dole bazai dinga bata drugs anyhow tana sha ba tunda yafi kowa sanin illar hakan..addu'a kawai yake kada Allah ya dora mata laulayi mai wahala dan baisan yanda zaiyi da ranshi ba..shi kanshi yasan daga mashi hankali zata dingayi da wnn koke koken nata shiyasa yake fatan Allah ya bata mai sauki yanda bazasu sha wahala sosai ba..ya dade nan zaune yana kallonta saida dare yayi nisa snn ya samu ya gabatar da sallah shima ya kwanta nan kusada ita tareda sanyata a jikinshi.
Washegari har wajen goma bata tashi ba sbd baccin da bata samu tayi sosai ba jiya..Bobby na nan zaune yana kallonta ko nan da can ya kasa matsawa sbd gudun kada ta tashi baya kusa..saida yaga rana ta farayi gashi kuma yau Friday snn ya samu yayi wanka ya shirya kanshi cikin farin shadda da akama dinkin kaftan..yasa hula white sai takalmin kafarshi shima white..bayan ya gama feshe jikinshi da turaruka ya dauki wayarshi ya fita sbd kiran da Nur keta mishi tun daxun..yana fita parlor yayi picking call din yana cewa"yane"..a daya bangaren Nur yace"normal..ya jikinta?.."a hankali yace"gata nan dai wlh..har yanxu tana kwance".. Nur yace"subhanallah zazza6in dai?.."zaunawa Bobby yayi kan one of kujerun parlon before yace"shine fa..amma dai yanxu naji da sauki sosai..bata samu bacci bane jiya shine yanxun take ramawa"..Nur yace"ohk Allah ya kara sauki..gashi kuma kace yau zatayi baqi koh?.."Bobby na shafa kanshi yace"sun kusa zuwa ma yanxu haka..kana ina yanxu?.."Nur yace"ina shiryawa kafin sallahr jumu'a".. Bobby yace"alright mu hadu a masallacin nima yanxu zan fito"..yace"alright sai ajima"..shima yace"sai anjima"..daga haka suka aiye waya..Bobby ya sake komawa dakin har lokacin bacci takeyi..ya taba forehead dinta yaji babu zafi sosai sai ya gyara mata kwanciya tareda pecking forehead dinta snn ya dau keys dinshi ya fita zuwa main house..bayan sun gaisa da Mummy yace mata zaije masallaci daga nan zai biya eatery ya siyo ma su Husna abinci tace he shouldn't buy anything tasa ayi musu girki sbd tasan dama Ayshan ba lafia..godia yayi mata sosai snn ya mata sallama ya fita bayan yace Miemie ta dinga shiga tana duba mashi ita time to time idan ta tashi ta kira ta sanar dashi.
Around 2:17 su Billy suka shigo Kanon Dabo.. Husna ce ta kira Bobby ta sanar dashi karasowarsu yace su karasa gida shima yanxun zasu wuce..kusan a tare motocinsu suka yi parking a compound din gidan..nashi da na Nur sai kuma na Hamma Najeeb da sukazo a ciki..shi ya fara fita ya nufi inda suke sukayi musabiha da Najeeb snn yace su shigo su fara gaisawa da Mummy sai suje inda Aysha..Mummy ta tarbesu da farin ciki sosai suka gaisa tana tambayarsu ya Ammi da daddy suka amsa da suna lafia..bayan Miemie ta gama setting dinning tace suje su fara cin abinci kafin Aysha ta tashi daga bacci sai suje itama su gaisa.
Bayan sun kammala suka nufi gidan nasu gaba daya tareda Najeeb dake sauri ya wuce aikinda ya kawoshi...suna shiga compound Yusra tayi saurin kwace hannunta cikin na Billy ta shiga cikin gidan da gudu tana kiran"Addah..Addah"..da sauri Bobby yabi bayanta gudun kar ta tasheta a bacci..suna shiga parlor yace they should make themselves comfortable shi zaije ta fito musu da ita..Husna ta bishi da kallo tana kunshe daria tace"Allah sarki Uncle Bobby..da gani Adda ba karamin wahalar dashi takeyi ba"..Miemie dake kusa da ita ta dan matsar da kunnenta kusa da nata tace"ke batada lafia"..da sauri Husna ta juya tana kallonta tace"da gaske?..ko ciki ne da ita?.."gyada kai Miemie tayi tana sake yin kasa da murya tace"but don't tell anybody oo.. Uncle Bobby might slaughter me"..hada ido sukayi suka tafa Billy dai kallonsu kawai take tana mamakin yaushe suka zama kawaye...Bobby na shiga dakin yaga kan gadon wayam dan haka ya bude bathroom da sauri ya shiga sai ya ganta tsaye jikin sink ta zubama mirror idanu tana hawaye..da sauri ya karasa tareda janyota jikinshi hankalinshi har ya fara tashi tace"what?.."goge tears dinta tayi tana girgiza masa kai..rikota yayi ya fito da ita snn ya zaunar da ita gefen bed shima ya zauna yana rikeda hannunta yace"baby menene plss?..akwai inda ke maki ciwo ne?.."girgiza kai ta sakeyi tana cewa"No"..hannu yakai ya karasa goge mata tears din snn yace"kinga su Husna sunzo dan Allah ki bar kukan nan indai baso kike suyi tunanin wani abu ke damunki ba"..kai ta sake gyada mishi without saying anything..shi kuma yayi pecking cheeks dinta snn ya mike yana cewa"let me get u something to wear sai muje parlor ku gaisa dasu"..kallonshi kawai tayi batace komai ba shi kuma ya fita da sauri zuwa bedroom dinta don dauko mata kayan da zatasa..tagumi tayi da both hands dinta tana tunanin abunda ya dameta..lissafi tayi yau kusan 2 weeks knn ya kamata period dinta yazo amma baizo ba sai kuma ga fever ta farayi da amai..dukda ba test tayi ba tanada tabbacin morning sickness take..tasan ciki ne da ita wlh.. musamman data tuna yanda suka rungumi juna suna farin ciki jiya a hospital sai ta sake tabbatar da zarginta..kawai gani takeyi baici ace ta samu ciki yanxu ba..Ina ma laifin tayi ko 6 months ne idan batayi 1 year ba amma wai ciki tun yanxu knn dai haihuwan 9 months din da bataso shi zatayi and Allah kadai yasan what will people say about her..kilan haka za'a zauna ayita gulmarta kaman yanda take zama tayi na mutane itama..ita bawai haihuwan ne bataso ba kawai bataso mutane suce daga yin bikinta ta samu ciki sai kace dama jira take..tayi nisa cikin tunani har batasan time din da ta fara hawaye ba..she knows for sure yasan da mgnr cikin yana sane ya boye mata..bayan few minutes ya dawo da kayan nata a hannunshi..ya taimaka mata tasa snn ya dan gyara mata fuska yanda bazasu gane tayi kuka ba ya kama hannunta suka fita zuwa parlon.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
67
Hannunta na cikin nashi har suka shigo cikin parlon..tana hada ido dasu Husna batasan sanda ta kwace hannunta daga nashi tayi saurin karasawa inda suke kawai sai ta shiga kokarin daukan Yusra da itama tana ganin nata ta taso cikin farin ciki sosai take cewa"Habibty"..itama Yusra rungumeta tayi tana daria tana kuma jin yanda har yanxu take kokarin dagata amma ta kasa..ta dago tana kallonta tana daria tace"Addah bazaki iya daukana ba yanxu"..da sauri Bobby daya karaso ya zauna kusada Nur yace"tell her"..Aysha tayi pecking forehead dinta snn taja hannunta suka zauna tana cewa"I missed u guys sosai wlh"..itama Yusra zaunawa tayi kusada ita tace"muma munyi missing dinki Addah"..daga haka ta juya tana kallon Billy data wani kura mata ido tana kallonta tace"what?."Billy tace"aah me kikaji nace?.."dan murmushi ta saki tareda matsawa tayi hugging dinta itama tana cewa"nayi missing dinki"..Husna da tun daxun bakinta ke kaikayi ganin hug din nasu bana kare bane tace"Adda kinga yanda kikayi kyau kuwa..kinyi wani fresh kin canxa"..juyawa Aysha tayi tana kallonta sai kuma ta dungure mata kai tana murmushi tace"idan bakiyi haka ba ai ba sunanki Asma'u Lamido ba"..Husna da har yanxu ke murmushi itama tayi hugging dinta tana cewa tayi missing dinta..Hamma dai na zaune yana kallon wariyar launin fata..saida ta gama da kowa snn ta dawo da kallonta gareshi tana wani murguda baki tace"ba ruwana ni dakai"..daria ya saki tareda juyawa yana kallon Bobby yace"inaga saika lamarin nan Dr..wnn matar taka rikicinta yawa ne dashi wlh"..dan murmushi Bobby ya saki yana kallonta yace"baby C'mon mana..ko me yayi ai yakamata ya wuce tunda har ya taso yazo inda kike"..da sauri Najeeb yace"exactly..kuma bayan zuwa ma har matata na kawo mata da qannena amma still take cewa ba ruwanta dani"..ya karasa mgn yana kashe ma Billy dake kallonshi idanu..tayi saurin kawar da kan nata tana daria..ita bazata iya wnn abun nashi ba..Lamido kuwa tasowa tayi daga inda take ta dawo nan kusa dashi ta zauna tana kallonshi da smile din nan nata dake sa both dimples dinta fitowa tace"to Hamma sannu da zuwa..Ina yini"..juyawa yayi yana kallonta da kyau shima yace"lafia lau my Maama..hope kina lafia"..tace"am fine..ya aiki".. yace"Alhamdulillah"..juyawa tayi ta kalli Billy da wani dan iskan murmushi snn ta sake dawo kallonta gareshi tace"Ya Billy?.."kallon Billy shima yayi kafin ya dawo da dubanshi gareta yace"aminiyarki ce ai..so Kunfi kusa"..da sauri tace"aah wlh ni Kunfi kusa yanxu"..daria ya saki yana girgiza kanshi yace"yanxun dai tunda na kawo maki su i have to take my leave"..da sauri ta mike tana marairaicewa tace"ko ruwa fa baku sha ba..kuma ni banyi girki ba"..Najeeb yayi relaxing yana cigaba da kallonta yace"kuma gaskia yunwa mukeji"..sake marairaicewa tayi tana kallonshi sai kuma ta juya gasu Billy suma duk tana sunyi wani kalar tausayi Husna hadda cewa"yanxu Adda mu taso gari ya garara tun daga Gombe muzo gidanki amma ko abinci bakiy mana ba..gaskai saina fadawa Ammi"..hankalinta ya sake tashi jin tace zata hadata da Ammi tayi rau rau da ido kmr zatasa kuka tace"ai dai banida lafia"..daga haka ta juya zata nufi kitchen Bobby yayi saurin mikewa ya kamota yana fadin"baby wasa fa suke maki sunci abinci"..dagowa tayi tana kallonshi a hankali tace"da gaske?.."hannu yakai yana goge mata dan guntun hawayen daya gani a Idonta tace"da gaske nake mana..Mummy tasa anyi musu abinci"..rungumeshi tayi da karfi tana sakin murmushi tace"Allah ya sakama Mummy da aljannah"..ya dagota yana jan dogon hancinta yace"Ameen Ameen love"..daga haka ya dawo da ita parlon sai taga duk suna mata daria..samun wuri tayi ta zauna tanata daure dauren fuska shidai Najeeb ya mike yace zai wuce don ana can ana jiranshi..sukayi sallama da Bobby da Nur snn ya fita su kuma suka bishi a baya..har mota suka rakashi suka sakeyi sallama snn suka dawo ciki shi Kuma yaja motar yayi gaba...suna dawowa Nur da gaba daya hankalinshi ke gare Miemie yace"pretty yau ba zuwa gidan aunty knn?.."da sauri Miemie ta dubi Aysha tace"zamuje mana..ko aunty Aysha?.."Lamido da taga yanda Bobby ya wani tsareta da ido yanason yaji amsar da zata bada ta hade ranta itama tareda fadin"eh mana"..tana gama fadan haka ta jasu suka wuce bedroom dinta Bobby yabisu da Ido..suna shiga ciki Nur ya kwashe da wani daria yana cewa"tofa kai saidai kayi hakuri na yan kwanakin nan dan naga alama Lamido tunda ta samu mutanen nan mantawa zatayi dakai"..harara mai kyau Bobby ya watsa mashi yana cewa"do u know ur problem?.."Nur yace"nope"..Bobby yace"dan iska ne kai wlh..kuma a haka kake tunanin zan dauki 'yata in baka..u better wake up dan idan ba canxa hali kayi ba tsakaninka da Miemie saidai kallo daga nesa"..ya karasa mgn yana wani daure fuska kai kace da gaske yake..shi kuma Nur nan take ya shiga hankalinshi sai ya hau bashi hakuri yana cewa"kaifa matsala na dakai bakasan wasa ba"..kallonshi Bobby yayi yana kokarin sakin dariar dake cinshi yace"inyamurin banza"..yana rufe baki shima Nur yace"Kai kuma bafulatanin banza ba"..gaba daya suka hada baki suka sheke da daria kaman wasu kananun yara..bayan sun gama Nur yayi saurin cewa"yauwa ya mgnr cikin?..did she knows?.."a hankali Bobby yace"anya kuwa?..i don't think so..kawai nidai addu'a nake koda ta gane kar ta daga hankalinta da yawa"..dafashi Nur yayi ganin kmr abun na damunshi yace"don't worry bazata damuba inshaAllah..mutum nawa ne ke neman haihuwan basu samu ba so ita da Allah ya bata am sure bazata kasa nuna farin ciki ba"..gyada kai kawai Bobby ya iyayi yana cewa"i hope so".
Suna shiga daki Aysha da Billy suka baje kan gado suna hirar yaushe gamo yayinda su Miemie,Husna da Yusra suka bar musu dakin suka shiga dayan bedroom dinta suma suka dasa nasu labarin..yanda Husna da Miemie suka sake da juna zakayi tunanin tun tasowarsu dama suie qawance while ba haka bane..kawai hali ne yazo daya shiyasa qawancen nasu yayi daidai..har yamma yayi suna nan suna abu daya dan sallah kadai ya tada su shima suna idarwa suka sake dorawa daga inda suka tsaya..magrib na kawo kai jikinta ya fara rufewa da zazza6i wanda a daidai lokacin shima Bobby da suka fita da Nur tun daxun duk hankalinshi ya dawo gareta dan yasan daidai wnn lokacin zazza6in yake rufeta..sallama sukayi da Nur ya dawo gidan da sauri don yanaso yaga halinda take ciki..gashi yinin yau dama duk bataci wani abincin kirki ba..yana shiga ya iske Miemie da Husna sun wani baje a parlor suna labari suna kallo..suna ganinshi kowa ta shiga taitayinta har hada baki sukayi wajen fadin"Uncle Bobby sannu da zuwa"..yana dan murmushi yace"yauwa..Ina Bilkisu da Aysha?.."Husna tace"suna daki.. should i call them?.."yace"eh kice musu suzo"..da sauri ta mike zuwa bedroom din da suke ba'a dauk lokaci ba sai gashi sun dawo tareda su..tun daga nesa yake kallonta yana ganin yanda fuskan nan nata ke a daure yasan abunda ake gudu ya afku..suna karasowa ciki Billy na dan murmushi tace"Sir sannu da zuwa"..yace"yauwa Bilkisu..dama ce muku zanyi u should go get ready we are going out for dinner"..da sauri Miemie tace"Uncle Bobby Mummy tace an gama abinci fa"..kallonta yayi kmr bai gane me tace ba ita kuma ta sake cewa"tun daxu ta kirani tace zata aiko suwaiba ta kawo abincin nan..that ba sai Aunty Aysha tayi girki ba"..ajiyar zucia ya sauke yana gyada kai kafin yayi mgn Billy tace"Sir basai an kawo ba zamuje can muci"..tana rufe baki Husna ma tace"eh zamuje can Uncle Bobby"..kai kawai ya gyada tareda cewa"ohk"..yana kallon Lamido da har yanxu batasa baki cikin mgnr nasu ba..karasawa yayi inda take tsaye ya kama hannunta suka nufi flat dinshi..Husna tabisu da kallo tana murmushi Saida suka shige snn ta dawo da kallonta ga Miemie tana cewa"gaskia kuna ganin love a gidan nan..anya kuwa nima ba inyamurin zan samu in aura ba..naga kaman sunfi hausawa iya soyayya"..tana rufe baki Miemie ta sheke da daria tace"kamar a kunnen Uncle Bobby kika Fadi mgnr nan"..Husna ta wara ido da sauri tana cewa"ki rufamun asiri dan Allah in mutu maza su kaini ba yammata ba"..Billy dai daria ta saki tareda juyawa ta koma bedroom.
Suna shiga ya zauna nan parlor tareda zaunar da ita kusa dashi yana kallonta kmr zaisa mata kuka yace"zazza6in ne koh?.."Kai ta dora a shoulder dinshi tareda gyada mishi kai..a hankali yakai hannu yana shafa kanta yace"kiyi hakuri kinji..zai dena inshaAllah"..lumshe ido kawai tayi hawaye na cikowa cikinsu ta kira sunanshi"partner"..yace"na'am baby"..runtse idon ta sakeyi nan hawayen dake ciki suka silalo ka fuskanta tace"ciki ne dani koh?.."yayi shiru yana kallon spot daya kmr bazai ce komai ba sai can yace"who told u that?.."da sauri tace"i don't have to wait sai wani ya fadamun..i noticed some changes a tareda ni and koda banyi test ba na tabbata am pregnant..morning sickness nakeyi"..ta karasa mgn tana rushewa da kuka..da sauri ya juya tareda rungume gaba daya a jikinshi yana patting bayanta yace"stop crying plss"..batace mishi komai ba saida ta gama kuka iya son ranta snn ta sake dagowa tana goge tears dinta tace"kasan ciki ne dani koh?.."yayi mata shiru kawai dan baisan me zaice ba..ta shiga gyada kai tana cewa"ko baka fada ba nasan u knew it all along..ai jiya Ina kallon yanda kuke murna kai da Provost bayan an kawo result"..kallonta yakeyi har yanxu ya kasa cewa komai..saida ya bari ta gama mitarta tsaf snn ya mikar da ita tsaye yana cewa"now u need to stop talking..muje kici abinci sai kisha magani before fevern naki yayi yawa"..batace mishi komai ba itama tabishi suka fita daga dakin..gaba daya suka fita tareda su Billy zuwa main house tunda sunce a can zasuyi dinner...Mummy na ganinsu ta tarbesu da fara'a snn tace su karasa dinning ga abincin can..duk suka isa suka zazzauna Miemie na kokarin serving Husna tace a barta tayi..ba musu kuwa suka barta duk tayi serving din nasu suka fara ci shidai Bobby na tsaye kusada Aysha yana kallon yanda take ta faman jujjuya abincin ta kasa kaiwa bakinta..kujera dake kusada ita ya janyo ya zauna yana kallonta kmr zaisa kuka yace"eat mana baby"..kallonshi tayi a hankali sai kuma ta girgiza kai tace"bashi nakeso ba"..matsawa yayi kusada ita sosai tareda kama hannunta yace"then me kikeso?.."ta juya ta kalli su Billy taga duk hankalinsu naga abincin da sukeci snn ta dawo da idanunta gareshi tana wani hade rai tace"Custard zansha"..ya dan marairaice mata yace"amma baby custard kadai bazai rikeki ba tunda duk yau bakici abinci sosai ba"..kallonshi ta danyi yanda taga duk ya tashi hankalinshi sai ya bata tausayi dan haka ta sake janyo plate din abincin tana jujjuyawa tace"to zan faracin wnn idan mun koma sai insha custard din".. kanshi ya shiga gyada mata yana murmushi sosai yace mata"yauwa partner"..ta saki dan smile snn ta shiga cin abincin a hankali shi kuma yana aikin kallonta..ganin shi baida niyyar cin abincin ta juya tana dubanshi tace"kai bazaka ci ba?.."hannunta ya kama ya rike idanunshi a kanta yace"ni ke nakeso kici..banso kina zama da yunwa"..murmushi ta Kara saki snn ta maida plate din nan tsakiyarsu tasa mashi spoon tana cewa"to muci wnn din tare"..murmushin shima ya saki bayan yayi pecking hannunta snn ya dauki spoon ya shiga cin abincin shima..daurewa kawai take tana turawa amma ko kadan batajin dadinshi a bakinta..bayan sun kammala suka dawo parlor inda Mummy ke zaune tana jiransu suka dan taba hira bayan sunyi sallahn isha yace su mike su koma gida..Husna dai tace"Uncle Bobby nidai zan kwana a nan tareda Miemie"..Bobby na murmushi yace"to Mummy kinada baqi knn"..Mummy tace"aikam kin kyauta Asma'u dan da baki Fadi haka ba nasan ita kanta Miemien cewa zatayi a can zata kwana"..Aysha dai kunyarta takeji yasa ta kasa cewa komai..bayan sun mata sallama suka koma gidan tareda Billy da Yusra..duk yanda taso ya bari taje inda su Billy hanata yayi sbd fever dake sake sauko mata..dole tayi sallama dasu ta dawo dakinshi inda yake nan zaune yana jiranta...custard din da tace tanaso yaje ya dama ya kawo mata tasha sosai snn ya rage mata kayan jikinta suka kwanta..can dare ta tashi tana ta kwarara amai don kaf abincin da taci saida ta amayar dashi..duk hankalinshi ya tashi haka ya gyara wurin tsaf snn yayi mata wanka ya dawo da ita ya kwantar a kan gadon tanata faman kuka kmr karamar yarinya..hankalinshi yakai kololuwar tashi gaba daya ya rasa inda zaisa kanshi yaji dadi..da dadewa dama yasan zaisha fama da ita musamman daya fuskanci dan banzan raki ne da ita..dan ciwo karami da bai taka Kara ya karya bama langwai take mashi balle laulayi da kowa yasan yanda yake da cin rai musamman daya kasance shi ba wani specific magani yake dashi ba dole saidai mutum yayi hakuri har lokacin tafiarshi yayi..duk yanda yaso ko black tea ne tasha kasa Sha tayi wai idan tasha zatayi amai haka nan ya hakura ya kyaleta bayan ta gama kukan bacci yayi gaba da ita.
Wahsegari ta tashi normal babu fever as usual dama kullum kalau take tashi da safe sai dare yake sake dawowa..da kanshi ya mata wanka ya bata one of three quarters dinshi ta saka da wata shirt dinta dake dakin nashi snn ta fito zuwa wurin su Billy..da mamakinta sai taga suma sun tashi itada Yusra har ma sunyi wanka sun shirya..zama tayi suka fara labari kafin Kuma daga baya tace su shiga kitchen su fara girki don yau dai ba bazata bar Mummy da sawa ayi musu girki ba tunda ta samu sauki.. tare suka shiga kitchen din da Billy Yusra kuma suka barta a nan parlor tana kallon cartoon..Billy ce ta shiga peeling Irish yayinda ita kuma Aysha ta dauko chicken a freezer ta shiga gyarawa zatayi musu pepper soup..karnin Kazan na bugun hancinta taji wani irin amai ya taso mata aikuwa ta matsa jikin sink da sauri ta shiga kwarara aman..Billy ta bar peeling Irish da takeyi ta karasa nan kusada ita tana mata sannu..bayan ta gama ta bata ruwa da kuskure bakinta snn taja stool ta zauna tana maida numfashi..Billy dake murmushi tun daxun ta karasa ta dauki Kazan ta shiga wankewa tunda ta gama gyaran tace"ohh Allah da iko yake"..a kule Lamido ta juya tana kallonta tana daure fuska tace"ban gane ba"..Billy ta gama wanke kazar tasa ruwa snn ta dora a kan gas ta zuba duk abunda ake buqata snn ta rufe tukunyar ta koma kan Irish tacigaba da ferewa ta kuma kasa dena murmushi..ganin yanda taki kulata tace"Billy wai meye haka?.."Billy tace"kici gaba da 6oyemun kinada ciki nima ramawa zanyi wlh"..shiru tayi kmr bazata ce komai ba sai kuma can tace"shi ya fada maki koh?.."Billy tace"wlh ba wanda ya fadamun..bayan duk wnn fever da amai da kikeyi still sai inyi zaune sai wani ya fadamun kinada ciki kmr dai ba health personell ba..have u forgotten am a registered midwife?.."Aysha ta dan saki murmushi tana cewa"to registered midwife munafuka"..Billy ta shiga wanke Irish data gama peeling tace"ba wani munafurci fa.. addu'a na ya karbu knn"..tana rufe baki Aysha tace"wlh ke kimamun baki muguwa.. inshaAllah kema yanda bakinki ya kamani sai nawa ya kamaki..ke preterm ma zaki haifa inshallah 7 months da biki kawai saidai Muji ance kin haihu"..Billy ta kwashe daria tana cewa"aikam bakinki saidai ya tsaya kanki inshaAllah"..Lamido tace"idan na fara labour zan roka maki tunda kinsan ance adduar mace mai labour karbabbiya ce"..Billy tasa daria..haka dau suka cigaba da aikinsu suna hira kmr wanda sukayi jiya bai ishesu ba..Bobby dai ko da ya fito yana jiyo sautin dariarta a kitchen tayi Hamdala dan yasan tunda yaji haka sauki ya samu knn.
Karfe 11 suka gama shiryawa bayan sunyi sallama da Mummy suka shiga mota zuwa gidan aunty sumy kmr yanda Aysha ta dage ma Bobby kan sai ya kaisu sun gaisheta..ita da Billy da Yusra suna motarshi yayinda Husna da Miemie suke motar Nur da sai wani giggiwa yake yau gashi ga pretty a mota daya..sai kuma abun ya hadu da Husna mai shegen rawar kai itama aikam baka sukaita zuba masa iyayi yana kallonsu da murmushi yana kuma mamakin wnn iyayin da suke dashi a shekarun nan nasu...aunty sumy ta karbesu hannu bibbiyu ta dinga nan nan dasu kmr ta maidasu ciki don so..sosai suma suka ware suka saki jiki da ita suka kwashi labari don itama ba daga baya ba wajen surutu..Nur ne kadai ya kasa sakewa duk yajishi a takure sbd nauyinta da yakeji yayinda ita kuma ko a jikinta don batasan ma yanayi ba..Bobby banda tsokanarshi ba abunda yake yana masa daria amma bai kulashi ba sbd baida lokaci tanka mashi tunda a gidan surkai yake..sun jima sosai a gidan don a nan sukayi lunch daga nan kuma suka mata sallama suka wuce bayan ta cika su Billy da gifts iri iri..basu zame ko inaba daga gidan nata sai wani park mai kyau..sunyi enjoying wajen sosai don sai after four suka bar wajen..daga nan kuma ya kaisu shopping yace kowa ta dauki abunda takeso..su Husna an samu abunda akeso nan aka shigo kwasan kaya kmr wanda zatayi changing wardrobe..Billy dai kasa daukan komai tayi sai Lamido ce ta daukan mata snn ta dauka ma Yusra..har su Ammi saida yace ayi musu tsaraba dan haka sukayi spending lokaci mai tsayi a nan cikin mall din basu gama ba..bayan sun bar wurin yanaso ya biya eatery suyi takeaway na abinci Mummy ta kira tace he shouldn't buy food that already an gama preparing musu dinner..haka suka koma gida sukayi dinner din a nan zuwa lokacin Aysha dauriya kawai take don abokin daren nata ya fara dawowa wato fever amma bata bari sun gane ba har suka gama hiransu snn suka wuce tareda Yusra da Billy kmr dai jiya Husna da Miemie Kuma suna gidan Mummy.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank State...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
68
Washegari around 2 Hamma Najeeb yazo ya daukesu suka wuce bayan sunyi sallama da Mummy da kuma Aysha da taci kuka ta koshi kmr idan sun tafi bazata sake haduwa dasu ba..sosai takejin zatayi kewarsu..Mummy da Bobby sun cikasu da tsaraba sosai na abun arziki haka suka tafi suma sunajij kewarta kaman yanda itama takejin nasu..Yusra har kuka saida tayi wai zata zauna tareda Adda amma haka nan ba yanda suka iya suka rabu suna kewar juna.
Laulayi sosai Aysha ke fama dashi dan tun zazzabin yana tashi da dare har saida abun ya dawo kusan ko yaushe akwai fever jikinta ga kuma ba dama taci abinci sai ya dawo kmr zata fitar da kayan cikinta..sosai take shan wahala cikin lokaci karami ta rame tayi wani irin haske fau wanda kana gani dama zakasan ciki ne daita..Bobby kullum yana tareda ita dan zuwa yanxu ko hospital bai fiye zuwa ya dade ba sbd yanda hankalinshi bai kwanciya idan baya tareda da ita..ko abinci bata iyaci saidai taita kame Kamen kwadayi amma abincin kirki dai bazata tsaya taci ba sai idan jan ido yayi mata..sosai shima take bashi wahala dan gani yake ko ita da cikin ke jikinta bazata kaishi shan wahala ba..kullum fatanshi shida Allah ya rabata da cikin lafia don sosai ya matsu yaga ya rike da ko 'yarshi..wani lokaci sai ya zauna yayita surutu shi kadai wai babynshi yake mgn..ko Kuma yakai kunnenshi cikin nata wai yanaso ya jiyo heartbeat din babyn..sosai yake kulawa da ita da kuma cikin dake jikinta don duk wani abu da mai ciki ke buqata yana mata likewise wanda ba'a buqata ya nesanta ta dashi..lokacin da cikin ya isa antenatal da kanshi yake zuwa hospital da ita yayi mata duk wani necessary abu snn suje ayi mata duk tests daya kamata..scanning ma da kanshi yake mata don haka nan ma wani lokaci zaice suje yayi mata scanning yanason yaga ya kwanciyar babynshi yake..haushi yake bata sosai idan taga yana wnn abubuwan don gani take duk ranan da ta haihu kilan dena ma kulata zaiyi ya koma kan babynshi..tana ganin abubuwa iri iri dai akan wnn cikin ba daga Bobby ba ba kuma daga Mummy dasu Hajia Aunty Sumy ba..har kunya suke bata idan sukayi wani abu akan cikin amma su ta fuskanci ko a jikinsu..koda yake zuwa yanxu ta riga ta gama gane cewa jinin igbo dake running a jikinsu shike haifar musu da wnn rashin kunyan dan abubuwa da yawa idan sukayi saidai ta tsaya tana kallonsu tunda hausawa dai da Fulani tasan bazasu iya rabin rabin abunda sukeyi ba..tun cikin nada 3 months suka fara siyan kayan baby suna ajiyewa daga shi Bobbyn har zuwa kan su Mummy ta kasa gane Wanda zafi zakuwa da haihuwarta..yanda suke tulan kayan suna ajiyewa kai kace a kanta za'a fara haihuwa duk dunia..kulum cikin browsing unisex kayan yara suke designers masu kyau wai they don't want the baby to lack wani abu a dunia..kulawa sosai take samu ta kowane bangare amma hakan bai hanata wani lokaci ta sanyashi gaba tana kuka wai itadai ya cuceta musamman yanxu da cikin ya fara girma sai yasa mata wani irin qiba kusan duk kayanta sunyi mata kadan saidai taita fama da dagayen riguna...gashi mugun kunyar cikin takeji shiyasa ko Ammi ta kasa fadawa saida wasu sisters din daddy sukazo suka ganta da cikin shine da suka koma suka cema Ammi sai ta fara shirin tarban jika..sosai Ammi tayi mamakin wai Aysha nada ciki amma ta kasa fada mata dan dai ta Santa da rashin kunya kilan dai hankali ta farayi shiyasa ta kasa fada ma kowa kuma wai har uwar tata Fiddausi bata fadama ba lallai Aysha ta fara hankali kam..cikinta nada wata shidda aka sanya bikin Hamma da Billy four months masu zuwa aikam tasha takaici sosai wai ba'a tashi sa ranar ba saida aka daidaici lokacin haihuwarta sbd baaso taje biki..Billy taita mata daria tana tsokanarta wai Kilan lokacinda za'a fara bikin ita tana cikin labour room tana fama da kanta hakan kuma ba karamin bata ranta yakeyi ba dan har kuka saida tayi da akace four months aka saka.
Wnn knn...
Zaune take cikin parlonshi ta tasa katon warmer dake cike taf da awara a gabanta tanaci tana hadawa da uban yaji data ajiye kusada warmer din..daga ita sai wani qaton rigarshi blue daya tsaya mata iya guiwa..cikinta yana nan yayi zaune kmr yanda itama take zaune..a gefe guda kuma tv na aiki tana kallon wani series..yanda ta dukufa tanacin awaran dama kana gani zakasan ba lafia take ba dan mai lafia dai bazaiyi wnn abun ba saidai irinsu masu juna biyu..after like 7 mins Bobby ya shigo parlon hannunshi rikeda katon jug da aka zuba tamarind juice a ciki..yana zuwa ya ajiye matashi gabanta yana kallon uban yajin data ajiye gabanta yace"yanxu sake dauko yajin nan kikayi baby?.."dan marairaicewa tayi tana kallonshi tace"nifa bazan iyaci a haka ba partner"..tun kafin ta rufe baki ya dauke yajin daga gabanta yana hararanta yace"to bazaki karaci ba wlh"..kallonshi tayi da sauri tana kwabe fuska tace"dan Allah partner ka bani dan kadan zan zuba wlh"..girgiza mata kai yayi yace"No kici haka..ga tamarind din nan Mummy tayi maki"..turo baki tayi ta wani daddage ta ture warmern daga gabanta snn ta mike da tulelen cikinta a gaba ta wuce bedroom dinshi..da kallo kawai ya bita yana jinjina kokarin da maza suke da matansu masu ciki..gaba daya yanxu ta zama masifaffiya dan dan abu karami zaiyi ta haushi da fada Kai kace itace Hajia Nadia data durkusa ta haifeshi..hakan kuma bai taba damunshi ba dan yasan ba yin kanta bane condition din da take ciki ne ya haifar mata da haka..mikewa yayi shima ya dauki tamarind da sauran awaran nata ya bita dakin dashi..saida ya ajiyesu bisa table snn ya karasa kan gadon tareda dagosu gaba daya itada cikin nata ya dorasu kan laps dinshi..hawaye sosai ya gani a fuskanta nan take kuma hankalinshi ya tashi dan dunia idan akwai abunda ya tsana yanxu bai wuce wnn kukan nata ba..sam bayason gani sai yaga kmr yana affecting da ko yarshi dake cikinta..rungumeta yayi batareda damuwa da cikinta dake zungurinshi ba yace"yanxu baby sbd yajin kikemun kuka haka?..bakiso hankalina ya kwanta koh?.."hannu takai tana share hawayen tace"to ai bazan iyaci a haka ba kuma ni ban koshi ba"..nashi hannun ya mika ya karasa goge mata tears din yana cewa"banason yajin yayi affecting babyna ne ke kuma naga baki iyacin kadan ba"..kallonshi tayi hawaye na sake ciko idonta tace"ai dama baka damu daniba ni..wlh tunda na samu ciki ka dena sona"..cupping fuskanta yayi tareda manna mata peck a forehead dinta yana kallonta da murmushi yace"i love u both baby..ku biyun are my family so i love u equally"..tun bai rufe baki ba ta kwace fuskanta daga hannunshi tana sake rushewa da kuka tace"wato u love us equal..tun babyn baizo dunia ba kana cewa u love us equal then idan yazo kilan watarana cewa ma zakayi baka san wace ni ba".. Bobby couldn't help it but laugh da jin wnn mgnr nata..rungumeta yayi yana daria sosai yace"don't tell me kishi kikeyi da abunda ko dunia baizo ba"..sake daure fuska tayi tana turo baki tace"kaima ba gashi kana nuna bambanci ba"..dagota yayi ya sake cupping fuskanta yace"u don't have to be jealous baby..i love u more..my every little happiness depends on u love so i love u more..i promise i love u more"..sake turo baki tayi tareda raba jikinta da nashi tace"indai da gaske u love me more ka bani yajina in karasa cin awarata"..ba musu ya dauko yajin ya zuba mata dan kadan snn ya daukota ya ajiye kan sofa ya fara massaging legs dinta yace"to gashi nan yi sauri ki karasa ci sai ayi wanka"..bata sake cewa komai ba tacigaba da cin awaranta shi kuma yana massaging legs dinta da suke dan kumbura time to time..dan kadan ta rage cikin tulin awaran dake gabanta snn ta kora da tamarind da Mummy keyi mata kullum sbd shi kadai take iya sha..shi kuma ya dauketa suka shige bathroom.
Washegari kafin ta tashi ya fita sbd kiran da Nur keta Maka mashi wai there's emergency a college clinic kuma shi bai cikin makarantan..kafin ya fita saida ya tabbata ya ajiye mata duk wani abu da take buqata tareda dan short note snn yayi pecking forehead dinta da katon cikinta ya fita..lokacinda ta tashi was around 11 ta shiga bathroom dinshi tayi wanka snn ta fito ta shafa cream da turare ta zura jallabiyarshi ta fita..these days gaba daya kayanshi take sawa dan nata kusan duk sunyi mata kadan..riguna ya ware mata manya da jallabiyas marasu tsayi sosai ya bata yace ta dinga sawa tunda duk maternity gowns da yasa aka dinka mata bata sawa wai nauyi suke mata..tana fita parlonshi taga ya ajiye mata goruba da tsamiyar biri da shansu zame mata kullum kmr ka'ida..ta saki murmushi tareda karasawa zata dauka sai taga ya ajiye mata note a kusa dasu dan haka ta zauna snn ta dauki note din ta fara karantawa kmr haka"hey love..sorry zaki tashi baki ganni ba naje clinic ne wai there's emergency but bazan dade ba zan dawo..take care of urself and my baby for me..love u"..da murmushi sosai ta karasa karantawa snn ta dauki gorubarta ta fita main parlor tanaci..bangaren mai aikinta ta nufa tayo mata mgn snn ta dawo cikin parlon ta zauna..mai aiki na zuwa bayan ta gaisheta tace"dan Allah saude kin iya wainar flour?.."da sauri mai aikin tace"na iya Hajia"..tace"yauwa to shi nakeso kimin yanxu..akwai flour a store kar kisa kwai amma kisa attaruhu sosai yanda yajin zai fito and kisa maggi ma da yawa"..yarinyar ta amsa mata da"toh"snn ta juya zuwa kitchen ita kuma ta shiga cin goruba tana kokarin kunna tv..Kiran daddy ne ya shigo wayarta ta dauka da sauri tana cewa"daddy ina kwana"..yace"lafia lau Aysha ya jikinki?.."tace"Alhamdulillah"..yace"to Allah kara lafia ga mamanki zakuyi mgn"..daga haka daddy ya bawa Ammi wayar itama Aysha ta gaisheta ta amsa da tambayarta ya jiki..duk kunya suke bata idan suna tambayar ta ya jikin nn wlh..kawai saita dinga imagining shknn sun san yanda akayi ta samu cikin..Ammi tace"maganin nan da aka kawo kinasha yanda akace maki dai koh?.."tace"Ina sha"..Ammi tace"to kicigaba da Sha dan Allah yanda aka fada maki..amfani ne dashi sosai karkiyi wasa dashi"..kanta a kasa tace"toh Ammi..yanxu Ammi dan Allah bazaki sa baki ya barni inzo in ganku ba?.."Ammi tace"keda kike da tsohon ciki Aysha Ina ke ina zuwa Gombe a yanxu?..ki bari idan kika haihu lafia sai kizo amma dai yanxu bazai yiwu kizo har Gombe da tsohon ciki ba"..kmr zatasa kuka tace"Ammi ba tsoho bane it's just 6 months ai zan iya zuwa"..dan murmushi Ammi ta saki tana girgiza kai tace"6 months din ne bai tsufa ba?..kinfiso kizo kiyita yawo da ciki knn kowa yana kallonki".. tayi shiru batace komai ba Ammi ta sake cewa"idan ma kinzo yanxu nasan bazai fi kiyi one week ba amma idan kika bari kika haihu saiki dawo gida gaba daya idan kinyi 40 sai ki koma"..nan da nan ta washe baki jin abunda Ammi ta fada tace"to Ammi na bari"..Ammi da yanxu sosai suke shiri da yar tata dan a ganinta tayi hankali tace"yauwa ko kefa..Allah dai ya saukeki lafia"..tayi murmushi cikin ranta tace"Ameen"..daga haka sukayi sallama da Ammi ta ajiye wayar.
Ana kawo mata wainar flour ta tasa a gaba ta faraci tana hadawa da yaji kaman yanda ta saba..ga kuma sauran tamarind dinta na jiya da tasa a fridge shima tana korawa dashi..ita yanxu har ta mance yaushe rabonta da shan tea dan koda safe ko rana ko dare batada abunsha daya wuce tamarind..ko ruwa bata cika sha ba yanxu sbd batajin dadinshi a baki amma tamarind Kam yana mata dadi sbd wnn tsamin da yakeyi..saida taci tayi nak snn ta ture plate din tacigaba da kallonta time to time tana duba agogo ganin har rana ya farayi bai dawo ba..har ta gaji da kallon dayi bacci a nan cikin parlon kawai taji ana shafa cikinta ta bude ido da sauri tana ture hannunshi tace"meye haka?.."zaunawa yayi nan kusada ita yana kallonta da murmushi yace"ina mgn da babyna ne fa"..murguda baki tayi tana hararanshi shi kuma yayi pecking goshinta yana cewa"to am sorry"..banza tayi mishi batace komai ba shima bai sake mgn ba sbd kiran Nur daya shigo wayarshi..dauka yayi suka gama mgn snn ya janyota jikinshi yana gyara gashinta da bata gyarashi ba yace"what is it baby?..waya ta6amun ke?.."tale baki tayi kmr zatasa kuka tace"shine ka dade baka dawo ba"..yace"sorry naje hospital ne sai kuma Nur ya kirani wai da akwai emergency a college clinic so shine naje na dubata"..da sauri ta dago tana kallonshi jin ya ambaci college clinic tace"u mean college clinic kaje?.."gyada kai yayi yace"yes"..tace"kuma mara lafiyan da ka duba mace ce?.."yace"mace ce mana baby akwai wani problem ne?.."tun bai rufe baki ta hau girgiza kai tana hawaye tace"amma ka cuceni"..mikewa take kokarinyi yayi saurin dawo da ita jikinshi yana patting bayanta yace"subhanallah me nayi?.."tace"amma tun yaushe nake fada Maka banson kana zuwa clinic din nan..ni college din ma da inada dama wlh bazaka sake zuwa ba dan bakasan yanda mata suke kallonka bane"..wara ido yayi yana kallonta da murmushi yace"so kema kina kallona knn lokacin da kike makarantan?.."harara ta watsa mashi jin zai canxa mgn tace"don't change the topic"..kissing gashinta yayi yace"am not changing the topic baby i just want to know..kinsan dai dunia ya nade bazan so wata mace apart from u ba so ki kwantar da hankalinki"..sake turo baki tayi tace"how will ever kwantar da hankali bayan nasan yanda halin maza yake especially now that my body is Chang..."bai bari ta karasa ba yace"kome zaki zama ni ina sonki haka and ba abunda zai canxa hakan..i love u for who you are bawai dan kyawunki kadai nake sonki ba so stop saying your body is changing indai baso kike muyi fada ba..i love u and only you".. kallonshi tayi yanajin wani irin sanyi na mamaye zuciarta..wato she is so lucky to have found this guy..he is so amazing and she loves him so much..rungumeshi ta sakeyi tana sakin murmushi tace"to na dena..amma da gaske tsoron yammata nakeji"..hannu yakai yana shafa kanta yace"u don't have to baby..duk macen da zata kalleni saidai kallon kawai amma bazata iya dauke heart dina wajenki ba for i love u unconditionally"..smile ta Kara saki tana shakan kamshin perfume dinshi tace"nima i love u more partner..u are my world"..dago face dinta yayi yayi pecking forehead dinta yana cewa"now tell me are u among wayanda suke kallona lokacinda kina school?.."murmushi ta saki tana gyada kai tace"sosai ma amma kasan irin kallon da nake maka?.."girgiza kai yayi yana smiling yace"no"..tace"irin masifaffun inyamuran nan masu shegen taurin kai..har cewafa nake da kyar in baka cikin masu assasa yaki Biafra"..wara idanu Bobby yayi yana kallonta yana daria yace"so yanxu baby kallon mai son a raba Nigeria kikemun?.."kama hannunshi tayi tayi pecking tana cewa"it was then ai..amma yanxu i know better..nasan duk dunia za'a dade ba'a samu namiji kaman kai ba shiyasa nakesonka sosai"..murmushi shima ya saki yana rike da hannun nata yace"amma gaskia baby baki kyautamun ba..koda yake ba laifinki bane laifina ne dana sa maki ido ma takura maki"..murmushi take tana kallonshi as abubuwan da suka faru rush back to her tace"ai gaskia partner ba karamin wahala ka bani ba..ka takuramun a lokacin nan kullum saika mun masifa"..murmushin shima yakeyi yace"and believe baki kaini shan wahala ba..duk wnn abun da nake maki qi fadi ne kawai amma Allah kadai yasan halinda nake ciki a lokacin"..daria ta saki sosai ta rungumeshi yace"shiyasa idan kika haifamun babygirl kaman ki bazan yadda in kaita irin colleges din nan karatu ba sbd kar taje tarwatsa rayuwar proprietor kmr yanda kika tarwatsa nawa"..dukan chest dinshi tayi cikin shagwaba tace"tarwatsa rayuwarka ma nayi koh?.."ya sake rungumeta da hannunshi daya dayan hannun kuma ya dauko wani abu cikin pocket dinshi snn ya dagota yana cewa"now close ur eyes in nuna maki wani abu"..ba musu ta rufe eyes dinta shi kuma ya bude hannun nashi snn yace ta bude idon..tana budewa taci karo da zabunanta na gold guda biyu daya ta6a kwace mata a college aikam ta wara idanu sosai tana kallon rings din tace"oh my Godd..kasan gaba daya na mance dasu wlh"..kama hannunta yayi ya shiga kokarin zura mata su a fingers dinta yace"ai ni ban manta dasu ba"..tana daria tace"ai ranan haushinka naji bafa daka kwacemun su"..shima yana dariar yace"ni kaina a lokacin saida naji haushin kaina ta yanda har idanuna suka gano abunda ko Nur da yake mgn dake bai gani ba..a duk lokacin da muka hadu kokari nakeyi sosai na ganin ban kalleki ba amma bansan ya akeyi ba kawai saidai in tsinci kaina Ina kallonki kuma ba tareda na gaji ba especially idan kikasa wnn glasses din naki".. kallonshi kawai takeyi tana murmushi har ya gama saka mata rings din snn yakai hannun bakinshi yayi kissing yana cigaba da murmushi yace"ya kamata dai acigaba da samun glasses din nan a gida ina gani dan da gaske ji nake kaman in daukeki duk lokacinda na ganki dasu"..har yanxu murmushi take tace"da wnn tulelen cikin ne zan wani dinga da glasses?.."kissing cikin yayi yana cewa"itama zan siyo mata irin naki yanda idan kin haihu sai ku dinga sakamun Ina gani"..daria kawai ta saki tana girgiza kai shi Kuma ya sake janyota jikinshi ya dan rage muryanshi yace"kinsan fa ni mace nakeso ki haifa"..gyada kai tayi tace"i know..ni kuma nafison namiji"..kallonta kawai yake yana murmushi lokaci daya kuma ta fara ganin wasu abubuwa cikin idanunshi..a hankali yakai hannu yayi cupping fuskanta fasu snn ya dora forehead dinshi akan nata..kallon eyeballs dinshi takeyi kmr yanda shima yake kallon nata dan zuwa yanxu tana iya daukan lokaci tana kallon idonshi amma dukda ba kmr yanda shi yakeso ba..a hankali ya lumshe ido tareda dora lips dinshi akan nata murya can kasa yace"baby please..i missed us"..hannunta ta zagaya wuyanshi dashi snn tayi grabbing bakinshi shima nan da nan ya kama kaman magnet..daga haka kuma na baro musu parlon and ban sake dawowa ba sai bayan wata uku...lol😂
Bayan wata uku...
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
69
Bayan wata uku...
Cikin Aysha ya shiga wata na tara knn cif and edd dinta baifi saura 3 days..gaba daya ta canxa daga Lamido da kuka sani a baya ta dawo wata irin salaha kmr dai ba itane ke ba iyayenta ciwon kai ba..sosai ta zama kalar tausayi dama ga cikin nata da girma sosai musamman yanxu da haihuwan ta kusa sai girman ya sake fitowa..ga kuma nauyinshi da takeji wani lokaci har cewa take kilan twins zata haifa maybe scanning machine dinsu ne baida kyau shiyasa bai nuna haka ba..duk ta Fadi haka saidai Bobby yayi daria dan yasan baby daya ne cikinta saidai girman kawai..ga masifa data koya da rashin hakuri Dan abu karami zata hau fada tana cewa ai dama dole ya dena sonta sbd yanxu tayi Muni shidai banda daria ba abunda yake mata..wani lokaci har video yake mata bata sani ba idan tana wnn sababin yasan idan ya nuna mata nan gaba daria zatayi..sai kuma fever da take yawan kwana dashi da ciwon baya wanda har yasa take cewa kilan mutuwa zatayi..sosai take daga hankalinshi duk tayi wnn mgnr amma bai taba nuna mata ba.. addu'a kawai yake mata tareda fatan Allah ya sauketa lafia..a bangaren mummy ma tana kulawa da ita sosai dan da dadewa itace ta dauki nauyin dafa mata duk abunda takeso tunda ba komai take ciba..yanda take lalla6ata ita har kunya ma takeji amma sai taga su ko ajikinsu..siyayya kuwa zuwa yanxu ba abunda basu gama siya ba tun daga kan kayan baby har zuwa ita kanta nata kayan..bedroom guda ya ware cikin nata yasa akayi renovating dinshi zuwa baby room mai kyau aka kuma cikashi da kayan yara iri iri tun daga kan furnitures har zuwa su toys da sauran kayan wasa na yara..tsakaninta da Amminta ma yanxu mutunci sukeyi sosai dan yanxu tayi hankali ta dena rashin kunya a cewar Ammi shiyasa suke dasawa abunsu..kusan kullum sai sunyi waya da ita dan ko ita Ayshan bata kira ba Ammi zata kirata taji ya jikinta..tana kuma turo mata addu'o'i tace taitayinsu daga nan har lokacin da Allah zai kawo haihuwar wai sai yazo mata da sauki..sosai itama take tausayawa 'yar tata sbd halin da take ciki shiyasa Husna na gama ssce daddy yace tazo ta zauna tareda ita ko ba sbd aiki ba at least zata dan dauke mata kewar gida da take fama dashi..zuwan Husnan kuma ya yayi mata dadi sosai dan kusan kullum suna tareda ita da Miemie a gidan su suke mata komai saidai mai aiki ta tayasu kawai..shima Bobby yana bakin kokarinshi kwarai wajen ganin batayi lacking wani abu daga gareshi ba including time dinshi da kuma caring..sosai yake tsayawa ya kulada ita don ko wurin aiki ma sai ya tabbatar ya gama mata komai snn yake wucewa hakan da yakeyi kuma ba karamin faranta mata rai yake ba..tana jin dadi sosai idan taga yanda daga shi har Mummy da siblings dinshi ke nuna tsantsar so da kula wa cikin nata har watarana takejin ta matsu ta haihu sbd taga irin kaunar da zasu nunama babyn..gani take kmr Mummy da Bobby sunfi ita kanta da babyn ke jikinta kaunarshi amma batasan ko dan riga yazo dunia bane..a halin yanxu dai duk wani fatanta bai wuce Allah ya sauketa lafia ba.
Yau Friday suna zaune parlor ita da Miemie da Husna suna kallon wani film Sab ya shigo gidan da sallama yana hararar Miemie da gaba daya hankalinta ke ga film da suke kallo..bayan ya karaso ciki ya zauna sai ya dan saki fuska yana duban Aysha da murmushi yace"sannu Aunty Aysha"..murmushi itama ta saki tana girgiza kai tace"bazaka dena cemun sannun nan ba koh?.."yana cigaba da daria yace"ai dole ace maki sannu matar Uncle Bobby..wnn babyn namu nasan da kyar idan baya baki wahala don da gani nasan fitina zaiyi wlh"..daria gaba daya suka saki har su Husna da hankalinsu ya dawo kan hiran nasu..Husna tace"wlh uncle Sab kmr kasan nima tunanin da nakeyi knn..na tabbata indai ya dauko halin Adda to wlh ba karamin fitinanne za'ayi ba"..ta karasa mgn tana daria Aysha Kuma tace mata"zanyi maganinki wlh..ki bari insamu time dinki"..Sab yace"ai idan ya dauko halin babanshi bayan fitina ma sai ya hada da masifa da rashin mutunchi..ta6 Uncle Bobby ai ba baya bane wajen wadan nn dabi'un"..da sauri Miemie tace"wlh kuwa uncle Sab..ni kaina gani nak..."bata karasa ba ya katseta ta cewa"C'mon keep quiet wayasa dake a wurin nan?.."turo baki tayi tana rungume hannunta tace"ai nima ba da kai nakeba"..kwafa yayi yace"kicigaba da murguda min bakin nn watarana saina karyashi wlh..badai ni kikaje kikama munafurci a wurin Mummy ba..zan kamaki ne"..sake daure fuska tayi tace"nidai gaskia na fada mata ai..kuma ba ruwanka dani Uncle Bobby yace ka dena shiga harkata"..ya bude baki zaiyi mgn Lamido tace"ya isa haka dan Allah..na rasa meyasa ku kullum cikin fada kuke kmr tom and Jerry".. Sab yace"yarinyar nan batada kunya bakisan halinta bane..wai har ni zataje tayima gulma a wajen Mummy"..Husna tace"ASP Uncle Sab da gaske ba gulma tayi Maka ba..a gabana Mummy ta tambayeta"..wani irin daria Sab yayi yana cewa"bazaki dena Asp Uncle Sab din nan ba koh?.."dariar itama takeyi tace"to ai Asp ne naga"..murmushi kawai yayi ya gyada kai kafin wani cikinsu ya sake mgn Bobby da Nur sun shigayi parlon a tare..da sauri Sab ya mike yana kallonsu da murmushi yace"sannunku da zuwa"..Bobby yace"kai baka zuwa sallahn jumu'a knn?.."Sab yace"yanxun na dawo ai..ask Aunty Zata fada maka ban jima da shigowa ba"..Bobby bai sake cewa komai ba suka karasa parlon suma suka zauna..Miemie da Husna suna gaishesu suka bar parlon shima Sab yana gama gaisawa dasu ya fita dan dama akwai inda zaije...kallon Aysha da har yanxu take zaune yayi kafin a hankali ya mike ya koma kusada ita ya zauna yayi mata side hug yana fadin"how is my baby doing?.."a dan kufule tace"ban sani ba"..yayi murmushi yana nuna cikin nata yace"bafa wnn babyn nake nufi ba wnn"..hannunshi ta ture daga jikinta tana duban inda Nur yake zaune tace"Sir Ina yini"..murmushi ya saki yana kallonta shima yace"lafia lau Lamido..ya jikinki?.."kanta a kasa tace"Alhamdulillah"..Bobby yace"baby bana hanaki kiranshi da Sir din nan ba..call him Nur mana ai sunanshi ne"..girgiza kai tayi tana dan murmushi tace"bazan iyaba"..tana rufe baki Nur yace"kinji mutumiyar kwarai..duk iskancinka dai haka zaka hakura ka barta tace bazata iyaba"..Bobby yayi daria kawai tareda dan rage murya yana kallonta yace"kinsan mene?.."kai ta girgiza mashi alamar bata sani ba..yace"zuwa mukayi dai yau mu fadawa Miemie cewa muna sonta"..dan wara ido tayi tana kallonshi tace"da gaske?.."yace"eh mana..nine ma zanyi masa zancen sbd a abokin Nur nazo yau ba Uncle Bobby ba"..murmushi kawai Aysha tayi tana girgiza kai tasan wnn mgnr wasa yake mata..mikewa zatayi yayi saurin kamata ya mikar da ita snn yace ta turo musu Miemie idan ta shiga..tana murmushi itadai ta wuce zuwa bedroom dinta ta tura musu Miemie kmr yanda suka bukata...tana zuwa ta nemi wuri ta zauna kasa Bobby yace ta koma kan kujera ta zauna..ba musu tayi hakan sai kuma duk sukayi dif aka rasa wanda zai fara mgn cikinsu..can Bobby ya nisa tareda Kiran sunanta..ta amsa kanta kasa dan har wani faduwar gaba taji tanayi ba gaira ba dalili..a nutse sosai ya fara mata bayani ta sigar da yasan zata fahimce shi sosai.. already dama Saida ya fara mgn da Mummy da parents din Miemie snn yazo gareta so ba tareda wani shakku yake mata bayani ba..itadai tsit tayi tana sauraran yanda yake koda mata abokinshi sai daga karshe kuma yace zai barta dashi ya karasa Mata sauran bayanin..bayan ya bar parlon Nur ya dora daga inda ya tsaya itadai kusan mutuwar zaune ma tayi jin wai da gaske Uncle Nur ne ke sonta..sosai ya kakkashe mata jiki da salon soyayyarshi wanda ita halin yanxu dai bazata iya gane shin tana sonshi ne ko kuma bata sonshi ba..shima baiyi gaggawa ba yace she should go and think about it idan ma tanada Wanda zatayi shawara dashi tayi idan ta gama yana jiran feedback dinshi..haka ta mike ta bar parlon jiki a sanyaye kmr kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Wnn knn...
Washegari bayan ta idar da sallahr asuba ta dade sosai zaune inda tayi sallahr tana ta addu'o'i bayan ta kammala azkhar dinta..Bobby kuma na masjid bai dawo ba..sosai take addu'a tana rokon Allah ya sauketa lafia ya kuma raya mata abunda zata haifa cikin tafarki madaidaici..saida gari ya fara haske snn ta shafa addu'an snn ta shiga kokarin mikewa amma sai me?..kugunta taji ya rike gam ta kasa ko kwakwkwaran motsi a wurin..ta kai hannayenta biyu ta dafe waist din dasu snn ta sake yunkurawa zata tashi sai kuma taji bayanta shima ya rike da sauri ta sake komawa ta zauna ta rintse ido tana maimaita innalillahi a cikin ranta..Saida taji ciwon ya dan lafa snn ta sake kokarin mikewa a karo na uku still taji bazata iyaba dan haka ta koma tacigaba da zama tana salatin annabi..Bobby daya dawo daga masjid direct kitchen ya shiga ya hado mata tea da shanshi ya zama mata constant duk ya dawo daga sallahn asubah dama saiya fara hada mata yake shiga daki..yana shiga ya ganta zaune nan inda tayi sallah ya ajiye mug din hannunshi kan table da sauri ya nufi inda take yana dagota yace"baby are u alright?.."a hankali ta dago ido tana kallonshi yaga eyes din are so red nan take hankalinshi ya tashi baisan sanda ya durkusa nan kusada ita ya kamo hannnuwanta yana tambayanta what's wrong ba..dan murmushi ta saki ganin har hankalinshi ya tashi tace"ba komai fa partner..kawai tashi zanyi naji bayana ya rike amma believe me yanxu banajin komai"..kamata yayi ya mikar da ita tsaye snn ya shiga kare mata kallo wai ko zaiga wani canji tattare da ita still yaga ba komai dan haka ya rike hannunta ya zaunar da ita kan sofa bayan ya zare hijabin dake jikinta..tea dinta ya dauka ya mika mata yace"to ga tea dinki Kisha"..murmushi tayi ta karba shi Kuma ya dauke carpet da tayi sallah dashi ya ajiyeshi inda ya dace snn ya sake dawowa ya zauna nan kusada ita yana kallonta tana shan tea din...bayan ta gama ya sake kamata suka kwanta kan gado ya rufesu da duvet cikin lokaci kankani kuma bacci yayi gaba da ita shi kuma ya kasa baccin sbd har yanxu bai gama yadda she's alright ba..gani yake kmr idan ya rufe ido ya fara baccin wani abu na iya faruwa da ita har saida ya ga baccinta yayi nisa snn shima ya lumshe ido baccin yayi awon gaba dashi...can cikin bacci Lamido taji kaman ana yi mata suka a maranta nan take ta bude ido baccin ma gaba daya yayi kaura daga idonta..dan motsawa tayi da nufin ta gyara kwanciya sai kawai taji wani irin ciwon mara ya sake kamata har batasan lokacinda ta wani irin salati cikin tsananin tashin hankali ba..da sauri Bobby ya bude ido jin kmr kuka take aikam yana ganinta ya mike zaune da sauri yana janyota jikinshi yace"baby what's wrong"..hannayenta na rike da mararta tace"ba..ya..na..mara..ta..way..yo"..sauka yayi daga gadon da sauri ya dora t shirt akan singlet da three dake jikinshi snn ya dauketa cak ya fita daga dakin da ita..sbd tsabar bala'i ko kuka ta kasayi sai faman salati take dan da gaske tayi zaton karshenta ne yazo..Bobby ma duk a gigice ya fita daga gidan kai tsaye mota ya bude ya sakata ciki snn ya shiga ya tayar da ita suka fita daga gidan..direct hanyar clinic dinshi ya nufa ita kuma tana baya sai faman murkususu take tana maimaita innalillahi..har wani zufa ke keto mata despite air condition dake aiki cikin motar..Bobby gaba daya gigicewa yayi ko driving din yaji kaman bazai iya ba amma dole yacigaba dayi dan kafin ma yace ya kira driver dinshi yazo wani bata lokaci ne haihuwa Kuma ba zaman jiransu zaiyi ba ya sani.. addu'arshi dai bai wuce Allah ya sauketa lafia ba..yana shiga hospital ko parking space bai karasa ba yayi parking daga nan bakin gate tareda bude motar ya fita itama ya fito da ita da sauri yayi cikin asibitin..da yake safiya ne babu mutane sosai asibitin sai few daga cikin staff da masu jinya da suka kwana a nan..labour room ya nufa da ita kai tsaye yaci sa'a kuma ya tarar da matron salamatu on duty dan haka yayi saurin shigar da ita ciki yace tazo ta duba mishi ita..babu wasting of time matron tayi mata ve nan kuma taga cervix dinta is 4 cm dilated koda ta sanar dashi hankalinshi sake tashi yayi don yasan zaiyi taking nata so many hours before ya gama fully dilation tunda primi ce..ga kuma ciwo da take fama dashi tun yanxun dan yanda takejin maranta kamar zai rabe gida biyu ne dan azaba..waya ya zaro daga aljihunshi ya kira aunty sumy yace ta samesu asibiti that bazai iya fadama Mummy ba don tashin hankalinta zatayi sosai so gwara ya bari idan ta haihu sai a fada mata..suna gama waya da ita ya kira Nur shima ya sanar dashi suna asibiti daga nan kuma ya ajiye wayar tashi ya shiga taimaka mata da kanshi..hannunshi ta rike gam cikin azabar da takejin kmr shi zaiyi ajalinta tace"par..tner..zan..mutu..mutuwa..zanyi".. girgiza mata kanshi yakeyi duk a rikice yace"bazaki mutu ba inshaAllah baby..lafia zaki haihu"..girgiza kai kawai Lamido take tana karanta innalillahi wainna ilaihi rajiun..har yanxun bata dena zufa ba ga kuma ciwon yakici yaki cinyewa..tun tana ganin abun kmr wasa har tazo ta fara gaskata tunaninta da gaske mutuwarta ne yazo..sosai take shan wahala amma wai ace har yanxu 4 cm take?..anya kuwa zata iya haifan babyn nan da kanta?..Bobby dai na tareda ita duk ya rikice dan kmr ma bazai iya cigaba da aikin ba amma da taimakon matron ya samu yayi gripping kanshi snn yacigaba da bata duk wani taimako da yasan tana bukata at this stage of labour..bayan lokaci kada n aunty sumy ta karaso asibitin nan Kuma yace taje gida ta taho musu da kayan haihuwa Dan shi bai samu ya dauko komai ba sbd rudu daya shiga..ba musu kuwa ta koma gidan ta dauko kayan da taimakon su Husna da suke gidan ta kuma ce kar su bari Mummy taji labari har sai idan ta haihu..lokacinda ta dawo asibtin suka hadu da Nur a kofar shiga labour room din yanata kiran Bobby amma baya dauka..a karo na farko da taji wani irin nauyin Nur ya kamata kasancewar yanxu tasan shine yake son Miemie..gaba daya sai tajita wani uncomfortable dashi unlike before da har wasa da daria sukeyi a tsakaninsu..shima kanshi Nur din rasa abunda zai ce mata yayi sai yayi kasa da kanshi kawai yana gaisheta cikeda respect kmr yanda ya saba..aunty sumy ta amsa snn tayi excusing kanta ta shiga ciki ward din ta bada kayan aka Mika masu..waiting room aka bude mata ta shiga yayinda shi kuma yaketa sintiri yana kai kawo a wurin yanda kasan matarshi ce nan ciki zata haihu.
After a long suffering Allah ya taimaketa da kuma taimakon perfect hubby dinta ta haifi santalelen yaronta namiji..yana zuwa dunia dama daya tsala wani irin kuka hatta Nur dake waje saida ya jiyo sautin kukan..sosai Bobby ke farin ciki da kanshi yayi mata komai ya gyarata matron kuma ta gyara baby snn sukayi moving nata to postnatal matron na rikeda jaririn dake lullube da shawl..har lokacin Bobby bai amsa yaron ba duk kuwa da yanda yakejin kmr ya ajiye duk wani abu da yakeyi yaje ya karbeshi amma baiyi hakan ba saida suka kaita postnatal snn matron ta mika mashi babyn ya karba da Bismillah yana kallon cute face din babyn da at once yaji wani iri so da kaunarshi na sake mamaye ko wane lungu da saqo na heart dinshi..lumshe Ido yayi tareda matsar da bakinshi ya Karanta addu'a sosai ya shafama babyn sai kuma yayi kissing forehead dinshi tareda mannashi da chest dinshi a fili ya shiga furta"Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah..Allah ya rayaka cikin tafarkin islam"..ya jima sosai rungume da yaron kafin ya kwantar dashi a cradle tareda karasawa kusada ita ya zauna ya kama hannunta ya rike bayan yayi pecking forehead dinta cikin tsananin happiness yace"Rabbi ya saka maki da aljannah..i love u so much"..itadai bata ma San yanayi as tunda ta samu ta haihu wani baccin wahala yayi gaba da ita..sai a lokacin ya tunada su aunty sumy dake waje nan yace matron ta turosu ciki shi kuma yayi saurin daukan wayanshi ya dannawa Mummy kira...tana dagawa cikin excitement yace"Mummy guess what?.."Mummy tace"just go straight to the point which one is guess what?.."murmushi ya karasa saki yana sake godema ubangiji cikin zuciarshi yace"Mummy Aysher ta haihu..u need to see my son Mummy he is so so very cute..he is more than handsome Mummy ina sonshi sosai wlh"..shiru Mummy tayi kmr bata fahimci me yace ba har saida ya sake kiran sunanta snn tace"u mean Aysha ta haihu?.."yace"yes Mummy tun asuba muke asibti and bata dade da haihuwa ba"..wani Hamdala yaji Mummy ta saki kawai sai yaji tayi disconnecting call din ya maida wayarshi aljihu dan yasan yanxun nan za'a ganta ta iso asibtin..aunty sumy na shigowa ta rungumeshi cikij farin ciki take cewa"Oh Allah mungode Maka..Alhamdulillah"..shima rungumeta back yayi har yanxu ya kasa dena murmushi yace"am now a father aunty Sumayya..i can't believe this"..rabashi da jikinta tayi cikin tsananin murna ta karasa inda babyn ke kwance ta daukoshi tana kallonshi with so much love tace"Allah ya Maka albarka"..daga haka ta ajiyeshi tareda komawa inda Aysha ke bacci itama ta rike hannunta tana kallonta with smile tace"sannu da kokari Aysha..Allah maki albarka kema ya baki lafiar breastfeeding"..Bobby dake tsaye yana kallonsu yace"Ameen Ameen"..daidai lokacin Nur ya shigo Bobby na ganinshi yayi saurin isa inda yake yayi hugging dinshi so tight yana ce mishi"u have become a father man.. congratulations to u"..rungumeshi back Nur yayi cikin so much excitement yace"Congratulations to u too bro..am so happy for u..Allah ya raya mana boy"..da sauri Bobby yace"Ameen..Ameen Ameen"..har yanxun sai suna rungume da juna sun kasa rabuwa musamman Nur da yakejin kaman ya taka rawa dan farin ciki amma ba halin yin haka sbd aunty sumy dake cikin dakin..duk sai yaji kaman baby expressing farin cikinshi yanda ya kamata ba..a hankali ya zame jikinshi shima ya nufi cradle din yaron..ya dagoshi yana washe baki kmr gonar auduga yace"Allahumma barikh ya Habibi..barakhallahu lakha"..ya karasa tareda yima yaron addu'a ya shafa mashi shima snn yayi saurin ajiyeshi ya fita daga dakin yana cewa"i will be back soon"..daga haka ya fita waje shi Kuma Bobby ya karasa inda babyn yake yanata kallonshi yanajin kmr zai maidashi ciki sbd son da yake mashi..ko 30 mins baiyi da zuwa dunia ba amma jin sonshi yake ta ko ina a cikin zuciyarshi wnn baisan ya zaiji ba idan yaron yafi haka girma Kuma.
Finally dai yau an haifi dan soyayya😂 welcome to parenthood Uncle Bobby and Aunty Lamido❤️🥰
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
70
Nur ne ya dawo dakin dauke da zamzam da dabino kai tsaye inda babyn ke kwance ya nufa ya daukoshi snn ya mikama Bobby ruwan zamzam din yace"come and give it to him"..ba musu Bobby daya kasa dena smiling ya matso yana bude zamzam din shi kuma Nur yana rikeda babyn haka sukayi bashi zamzam din yasha tareda dabinon da Bobby ya danyi chewing snn ya matsa mashi ruwan a bakinshi..aunty sumy dai na zaune tana kallonsu tana smiling..wnn friendship nasu ba karamin burgeta yakeyi ba tuntuni..they treat each other like brothers..Saida ta bari sun gama bashi snn tana dan murmushi tace"so doctors basa ma kids dinsu exclusive breastfeeding knn?.."kallonta sukayi gaba dayansu ba dai Wanda yace mata wani abun ita kuma ta sake cewa"naga dai kune kullum kuke counselling mutane kan su dinga ma yaransu ebf amma ku gaku nan Medical doctors daku kunzo Kuna bama yaronku ruwa ko one hour baiyi a dunia ba"..Nur dai kanshi na kasa ya kasa cewa uffan sai Bobby ne yace"aunty wnn ai ba normal water bane..zamzam ne fa"..daria kawai tayi bata sake cewa komai ba.
Mummy na shigowa dakin direct dama inda ta hango cradle ta nufa Bobby yayi saurin mikewa zakiyi hugging dinta tayi saurin kaucewa tana cewa"abeg let me pass..ana ta sabon jini wa yake ta kai"..daga haka ta karasa inda cradle din yake ta dauko babyn ta shiga kare mashi kallo..Bobby ya wani kwabe fuska yace"Mummy amma nine danki fa bashi ba"..harara ta sakar mashi tace"to daga yanxun shine yarona not u"..sake kwabe fuska yayi yana kallonta sai ta bude mashi hannu tana daria sosai tace"come here my son..the latest dad"..da sauri ya karasa ya shige jikinta Mummy ta hadasu shi da yaron mashi tayi hugging nasu so tight tana yima Allah godia cikin ranta..saida suka gama expressing farin cikinsu snn ya janye jikinshi Mummy kuma ta maida babyn cradle snn ta nufi inda Aysha..kallonta tayi yanda take bacci peacefully ta sauke ajiyar zucia tareda furta"Alhamdulillah Alhamdulillah..Allah shine abun godia".
Karfe 12 saura driver ya kawo Husna da Miemie tareda abinci da Mummy tace suzo dashi..zuwa lokacin Aysha ta tashi daga baccin har ma ta dan ware tana responding to mgnr da Aunty sumy ke mata har yanxun ko babyn bata dauka ba wai kunyar mummy takeji..ganin da gaske ba daukan nashi zatayi ba gashi ya fara rigima dole ta tashi suka bar dakin itada aunty sumy da Miemie ya rage daga ita sai Husna..cikeda farin ciki Husna ta karasa ta dauko mata babyn ta kawo mata shi tana cewa"take a look at him Addah..he is more than cute..har na kira Ammi na fada mata"..kallon nashi Lamido tayi tanajin wani irin sanyi na ratsa zuciarta..soyayya mai girma taji tanayima yaron just by looking at him..nan take taji she's so attached to him kaman dai ba yau yazo dunia ba..tana dan murmushi ta dagoshi ta mannashi da chest dinta snn ta sauke wani ajiyar cuzia tana godema Allah cikin zuciarta Husna Kuma na zauna tana kallonsu with adoration..shigowar Bobby yasa ta mikewa ta fita daga dakin bayan ta gaisheshi..a nutse ya karaso cikin dakin ya zauna nan kusada ita tareda yi mata side hug yana lumshe eyes dinshi yace"na gode sosai partner..May Allah reward u abundantly"..dan murmushi ta saki tana Kara rike babyn a jikinta shi kuma ya dagota daga jikinshi tareda durkusawa nan kasa ya kama hannunta yana kallon eyeballs dinta yace"i don't have enough words to thank u baby..i just want u to know that ina sonki and zan cigaba da sonki till my very last breathe..thank u for making a father today..Allah ya raya mana shi yayi mashi albarka"..kai kawai Lamido take gyada mishi tama kasa cewa komai.. shi kuma sosai ya rikice mata yanata faman godia hade da expressing mata how much he loves her..banda blushing ba abunda takeyi sbd dadi..itama tana sonsu fiyeda komai nata.
A ranar akayi discharging dinta suka koma gida bayan an tabbatar da itada babyn suna cikin koshin lafia..suna komawa gida ta samu kira daga daddy da Ammi duk sai murna suke sun samu grandson ita har ta kasa tantance wanda yafi wani murna da haihuwar nata..a ranar wata Goggonta tazo daga Gombe sbd ta zauna da ita ta kuma kula da ita da babyn gaba daya..Billy ma dake can tana ta faman shirin biki without her best friend tana samun labarin haihuwar ta kirata vid call tanata ihun murna wai a nuna mata danta ta gani..sosai suka bata lokaci suna video call Billy sai santin babyn take wai kmr tayi tsuntsu tazo Kano.
Bayan kwana hudu...
Cikin kwanakin nan Lamido taga asalin so da kauna daga wajen family da friends..ba family dinta ba ba kuma familyn Bobby ba..sosai suke samun kula itada baby abun har mamaki yake bata..mutanen Gombe zai zuwa suke ganin baby wasu kuma suna nan bazasu tafi ba sai bayan suna ciki hadda aunty Fiddausi..Besty ma yana samun labarin haihuwar a bakin Husna ya kirata ya mata barka tareda alqawarin zaizo ganin baby..haka zalika yan school dinsu ma da yawa sunzo abun dai ba'a cewa komai..Bobby kuwa bai cika zama ba yanxun as yanata shirye shiryen raka Waziri India ganin doctor dan Waziri da kanshi yace lallai saidai suje tare dashi..shima da kanshi yazo ganin baby har Kano tareda uncles din Bobby da kuma some of their family members..family din Mummy ma sunzo sosai kasancewar ita din mace ce mai zumunchi so kusan kowa yana kokarin yazo duk wani sha'ani daya shafeta...ahalin Lamido ma sunzo sosai tun daga kan uncles dinta da aunties dinta dama sauran family da friends..wasu sun wuce a ranar wasu kuma sunan nan sai anyi suna.
Yau ma kmr kullum tun safe suke fama da baki yan barka gashi babyn sai kuka yake an rasa abunda ke damunshi..har kuka itama saida tayi wai batasan me yakeso tayi mashi ba kuma..da kyar ta samu yayi bacci da taimakon Goggonta dake tareda ita..tana zaune gefen gado tana kallon yanda yake bacci peacefully sai taga ya koma mata kmr babanshi..he looks exactly like Bobby dan ko abu guda nata bai dakko ba..haskenshi eyes dinshi nose dinshi bakinshi and even fingers dinshi irin na Bobby ne sak..komai da komai irin nashi ga kuma dan banzan rigima da yake dashi shima ta tabbata na baban nashi ya dauko..hannu takai tana shafa soft hair dinshi tana cigaba da kallonshi tana murmushi Goggonta ta shigo dakin da ruwan zafi a flask tace"au yanxu Aisha har yanxu kina nan zaune kina kallon danki sbd rashin kunya so kike ruwan wankan ya gama wucewa ne kome?.."dan daure fuska tayi tana duban Goggon nata tace"yanxu dan Allah Goggo baza'a hakura da wankan yamman nan ba..shima fa da kanshi yace a denamun wanka sau biyu nidai dan Allah kiyi hakuri tunda anyi da safe sai a bari gobe Kuma"..wani tsaki Goggo ta saki tareda shiga bathroom ta juye ruwan flask din cikin wanda ta sirka tun daxun snn ta dawo dakin ta kama hannunta suka shiga bathroom din tare..duk yanda batason wankan dai saida Goggonta tayi mata wai shine zaiyi saurin dafa mata jikinta tunda yanxun ya dawo danye sbd haihuwan da tayi..suna gamawa ta dawo dakin tanata wani bace bacen rai itada Goggo bata kulata ba tayi wucewarta as tun daxun ta riga tayima babyn wanka..shiryawa tayi cikin dogon riga bayan ta gama shafa cream da perfume dinta snn ta koma kan gadon ta zauna tana cigaba kallon yaronta..a haka Bobby ya shigo dakin ya sameta..har ya karasa ya zauna kusada ita bataki shigowarshi ba Saida yayi mata side hug snn ta dawo hayyacinta sai kuma itama ta zagaya hands dinta around waist dinshi tana pecking shoulder dinshi tace"so u are back?."yace"yes baby how is my baby and u"..tace"as u can see we are all fine..just missing u"..juyoda ita yayi hugging dinta sosai snn yayi breaking hug din yana rikeda hands dinta yace"believe me i missed u more"..murmushi kawai ta saki tana cigaba da kallonshi..a hankali ya saki hands dinta tareda dauko baby dake bacci abunshi shima yayi pecking goshinshi yana kallon yanda he looks just like him ya dan bata face dinshi"i told him to look like u but he didn't"..daria Aysha ta saki tana kallon babyn itama tace"and i told him to look like u so mgn na yaji ba naka ba".. murmushi shima yakeyi yace"don't worry nasan next ones bazasuyi kama dani ba..inshaAllah next baby girl dake zatayi kama ba dani ba..now do u have any name in mind da kikeson asa mashi?.."girgiza kai tayi tana dora kanta a shoulder dinshi tace"No..duk sunan daka sa mashi is ok by me".. pecking forehead dinta yayi yana cewa"that's why i love my baby so much..u are one in zillion"..daria kawai ta saki jin wai ya ambaci zillion.. hankalinshi ya maida kan babyn yana tuna conversation dinsu da Mummy a while ago..he asked if da akwai name da takeso a saka mashi and her reply was duk sunan daka saka mashi daidai ne Bobby.. already dama yanada sunan da yakeson sa mashi amma sbd ya basu right dinsu yasa ya tambaya and he's glad sun bar mashi zabi..a hankali ya daga babyn yayi mashi huduba cikin ears dinshi snn ya maidashi kan shoulder dinshi yana patting bayanshi murya can kasa yace"he's named Noor.. Nuruddeen"..wara ido Aysha tayi out so much excitement tace"sunan provost right?.."a hankali Bobby ya daga mata kanshi yana cigaba da patting bayan babyn yace"yes..he's more than a friend to me u know..we became brothers"..tayi hugging dinshi tana cigaba da smiling tace"i knew that already..Allah ya raya little Noor Allah kuma yasa ya dauko halin mai sunanshi"..dan tabe baki Bobby yayi yace"ba kowanne ba gaskia..bakisan yanda Nur yakeda sa ido bane and i don't want my baby to be like him"..daria ta saki shima yana dariar ya hadasu yayi hugging da ita da babyn yana sake jin kaunarsu har can cikin zuciarshi.
Lokacinda labarin sunan ya iske Nur Saida yayi kaman zai zauce sbd excitement..he can't believe wai sunanshi Bobby yasama boy din..Allah ya sani dama tuntuni yakeda burin ya haifi danshi yasa mashi Bobby amma he never thought Bobby zai iya sama babynshi sunanshi..yaji dadi sosai and duk Wanda ke tareda shi Saida ya fahimci hakan..uban kayan daya siyo ma babyn ko shine babanshi sai haka..gaba daya ya rasa inda zaisa kanshi sbd farin ciki..har su raguna ya kawo manya guda biyu wai a yankama namesake dinshi..Bobby dai saidai ya bishi da kallo kawai dan baima san me ya kamata yace ba...ana gobe suna Bobby suka wuce India shi da Waziri da wani small uncle dinshi.
Ranar suna mutanen Gombe da yawa sunzo tun daga familyn Ammi zuwa na daddy da kuma familyn babansu Bobby..sosai gidan nasu ya cika da yan uwa da abokan arziki..da yake ha gida sukayi sunan ba wani hall sukayi booking sukaje sukasha shagalinsu a can..Billy da baifi saura 9 days aurenta ba Saida tazo itama Dan cewa tayi baza'a barta a baya ba..sosai yan class dinsu ma sukazo haka sukayi taro lafia suka tashi lafia mai jego da babyn sunsha gifts sosai kmr dai a kansu aka fara haihuwa a dunia.
Bayan suna da two days suka wuce Bauchi ita da Billy da Husna da kuma su Aunty Fiddausi da basu koma ba sbd bikin Billy daya gabato..Lamido a nan Bauchi ta sauka gidansu Billy dan ko Gombe tace bazata je ba sai bayan biki duk kuwa da kasancewar angon Hammanta ne to amma tunda a Bauchi duk zatayi events din tasan ko taje Gomben ma kullum suna hanyan zuwa Bauchi ne so gwara tayi zamanta inda aminiyarta itama ta taimaka mata da shirye shiryen kaman yanda tayi mata.
Ranar Thursday suka yi kamu a wani hall dake nan cikin Bauchi Friday akayi daurin aure da yamma kuma akayi dinner ranan Saturday kuma suka dunguma kai amarya gidanta dake Lamido's Palace..sosai Lamido tayita tsokanar Billy ranar har faduwar mata da gaba saida tayi dan yanda take zuzuta mata first night abun har saida ya kusa sanya Billy kuka..bayan ango yazo kafin ta tafi saida ta sake matsawa dab da kunnen Billy tana wani shegen daria tace mata"hope baki manta addu'an da nayi maki ba.. inshaAllah nan da 7 months zaki haifo mana preterm baby cox i just can't wait in ganki da baby wlh.. besides baby Noor ma yace i should tell u that sister yakeso ki haifo mashi ba brother ba..so take note plss..da safe zan dawo inyi maki sit bath don nasan dai bazaki taba moruwa ba"..tana gama fadin haka ta fita tana mata daria Billy dai da ido kawai ta bita as batada abun fada..duk ta gama tsoratar da ita wlh..gabanta banda lugude ba abunda yakeyi.
An gama biki da sati daya Bobby ya dawo Nigeria and ko gida bai fara zuwa ba suka taho nan Gombe tareda Waziri sbd yasan suna nan and duk dunia yanxu ba abunda yayi missing sama da boy dinshi da matarshi..tunda ta samu labarin zaizo dama ta sanar ma Ammi tasa aka shiga kitchen akaita faman girke girke da za'a tarbeshi dashi..itama taje tayi wanka ta shirya kanta cikin wani purple lace riga da skirt daya fito ainihin shape dinta ta kafa daurin dankwalin nan as always snn tabi duk jikinta da perfume da tasan yanaso..shima little Noor Ammi da kanta ta shiryashi sosai yayi kyau abunshi dama gashi da saurin girma dan yanda yayi 6ulele mutane da yawa thinks he's 3 months or above..sosai Ammi ke kulawa da dan jikan nata dan komai nashi ita keyi abun har mamaki yake ba Aysha..infact duk gidan ma kowa sonshi yakeyi dan daddy shima idan ya daukeshi watarana har bacci yakeyi a wurinshi sai idan yana kuka ne za'a kawoshi tayi feeding dinshi..soyayya da kulawan da take samu a gidan yasa sukayi adding weight daga ita har babyn sukayi wani kyau dasu kusan duk wanda ya kallesu sai yaji kaman ya suresu ya gudu dasu sbd tsabar kyau da sukai.
Bayan ya iso Ammi tasa aka bude mashi parlon daddy ya shiga ciki snn su Husna suka cika gabanshi da kayan ci iri iri shi kuma duk ba wnn ne gabanshi yanxun burinshi kawai yayi tozali da matarshi da yaronshi dan yayi missing dinsu like hell..tana shigowa parlon daukeda babyn nata a kafada Bobby ko jira ta karaso baiyi ba kawai ya mike ya isa gareta yayi wrapping dinsu gaba daya da hannayenshi yana sauke wani wawan ajiyar zucia..Noor ne ya fara mutsu mutsu alamar zaiyi kuka Bobby yayi saurin amsarshi daga hannunta yana dan dungure kanshi yace"abeg allow me to hug my wife mana..don't u know that i missed her"..yaron kmr yaji abunda yake fada sai ya shiga babbaka mashi daria and Bobby couldn't take his eyes off the boy..he looks so cute and adorable right now and he can't thank Allah enough for blessing him with such a lovely boy..a hankali yayi kissing forehead din babyn snn ya mannashi da chest dinshi yana saki murmushi sosai yace"i missed u too aboki..i missed u like crazy"..Karan camera da yaji yasashi dagowa yana kallonta sai yaga pictures takeyi musu a haka..suna hada ido dashi tace"you two looks so so cute..i can't love u less"..dayan hannunshi yayi using itama tayi hugging dinta yana kissing head dinta yace"nima i can't love u less baby..i love u two so so much..you are my whole world"..janyewa tayi daga jikinshi tareda kama hannunshi suka koma cikin parlon suka zauna..tayi serving dinshi abinci snn ta amsa Noor daga hannunshi tana cewa"now kaci abinci dan nasan idan ba daukeshi nayi be he won't let u eat sbd mutsu mutsunshi..duk zanci abinci saidai Ammi ta goyashi dan bai iya zama wuri daya ba nan da kake ganinshi"..murmushi sosai Bobby ya saki yace"bazanyi mamaki ba ai tunda namesake din Nur ne".. daga haka ya shiga cin abincinshi ita kuma tana kallonshi bayan ya gama ya sauke daukan danshi yana mishi wasa Lamido nata musu hotuna da videos dan da gaske kyau sukayi mata fiyeda tunanin mai karatu..ranar kusan gaba daya time din akan babynshi ya karar dashi saida yazo tafia ne yayi hugging nata so tight giving her the hottest kiss of her life snn ya tafi cikin so much so da kuma missing dinsu..the next day ma before ya wuce Kano saida ya sake zuwa and this time around tareda Nur da yazo all the way from Kano don yayi picking dinshi..if u see yanda Nur ya zage yana wasa da namesake dinshi abun zai baka daria sosai dan he behaves kaman yana wasa da babban mutum shi kuma yaron yanata mishi daria..Bobby da Aysha dai sai kallonsu sukeyi with so much love..ganin yanda yake cillashi sama yaron yanata daria Bobby ya girgiza kai yana murmushi yace"duk ka 6ata yaron nan da habits dinka wlh..look at how he's laughing kaman ba new born ba..u two are annoying"..harara Nur ya watsa mashi yana cigaba da wasa da little Noor yace"Kuma a haka baza'a iya rayuwa batareda mu ba..we are some kind of light da bazaka ta6a iya rayuwa without us ba shiyasa sunanmu ya kasance Noor..koba haka ba Namesake?.."ya karasa mgn referring to small Nur da har yanxu bai dena daria ba..Aysha da Bobby a tare suka fashe da daria ganin da gaske fa Nur neman zaucewa yake sbd wasa da karamin Noor.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
71
Bayan sunyi 40 Ammi ta gama gyarata tsaf sai kuma ta shiga zaga dangi duk gidan bata samu zuwa ba taje kafin ta koma Kano..suna nan sun Kara kyau da kiba abunsu itada little Nur..Saida suka gama ziyara kaf snn yazo da kanshi ya daukesu bayan sunsha kukansu itada Billy kmr bazasu Kara ganin juna ba dan kusan koda yaushe tana gidanta tunda anan cikin estate din nasu take..su Ammi sunsha godia sosai wajen Bobby ita har kunya ma ya fara bata kaman wanda sukayi ma wani gagarumin abun..bayan komawarsu gida kuma suka shiga bajema juna kolin love kowa yana nuna ma dan uwanshi yanda yayi missing dayan abun dai ba'a cewa komai..zuwa yanxu soyayya mai karfi ya shiga tsakanin Nur da Miemie dan har an fara mgnr aure sbd Nur da gaske he's desperate shima yayi auren nan ya shige daga ciki ko don as ya huta da walakancin da Bobby keyi mashi..bayan anyi mgn da familyn baban Miemie aka tsayar da biki next five months aikuwa farin ciki da rawar kai a wurin Nur abun sai wanda ya gani kawai.
Biki ya rage saura 2 months Bobby da Aysha suka tafi aikin Hajj hade da honeymoon dinsu wanda Mummy tace itakam bazata je ba sbd shirye shiryen bikin Miemie..wnn dalilin yasa suka tafi su biyu tareda little Nur da yayi girma ya Kara wayo sosai kuma kamanninshi da babanshi na sake fitowa...Malaysia suka fara zuwa for their honeymoon aikam anyi kara'in honeymoon sosa dan ba wanda zai gansu yace ba latest couple bane saidai idan little Noor aka gani..sosai suke enjoying honeymoon dinsu Aysha mai cewa zata koma karatu duk ta mance da wnn tana enjoying life dinta to the fullest..satinsu hudu suka wuce Saudi inda daga nan kuma zasu dawo gida dan immediately bayan sallah za'a fara bikin Miemie..sun gabatar ibadar su yanda ya kamata sun kumayi addu'a sosai na neman zaman lafia mai dorewa da zuri'a masu albarka da kuma fatan gamawa da dunia lafia..nan ma 4 weeks sukayi kafin su dawo daidai lokacin kuma an fara shagalin bikin Miemie so basu samu zama ba dan suna dawowa suka shiga harkan biki kuma.
Kusan sati guda akayi ana shagulgulan biki dan events sukayi sosai kmr dai bazasu kare ba inji Bobby yace shi har ya gaji da attending events din ma..yan uwan Aysha da yawa sunzo bikin daga Gombe ciki harda Ammi da bata zuwa gidanta ba sai Yusra da Husna da kuma Aunty Fiddausi da Billy dake dauke da katon cikinta itama da alama dai bakin Aysha ne ya kamata don da kyar idan ba haihuwar 9 months din zatayi ba..a lokacin ne Aysha ta samu labarin wai ashe soyayya ne tsakanin Husna da Bestynta abun kuma ba karamin dadi yayi mata ba dan tafi kowa sanin waye Sa'eed haka zalika tasan Husna ba karamin dacewa tayi da damunshi a matsayin miji ba..ranar da aka kai amarya gidanta su Aysha sune gaba gaba itada Billy da sauran familyn Mummy sai kuma yan uwan babanta..su Hajia Husna kuma sune qawayen amarya..sosai su Aysha sukayi mata nasiha sosai kafin su bar gidan ita kuma banda kuka ba abunda take wai tama fasa auren su maida wajen Mummy haka dai suka samu suka lalla6ata suka bar gidan.
Bobby da kanshi ya rako Nur har compound din gidanshi amma kememe yace shi bazai shiga ciki ba tunda amaryar tashi matsayin 'ya take a wurinshi that shi bazai iya wnn rashin kunyan ba..haka Nur yanaji yana gani Bobby yaki rakashi ga kuma wani iskanci da yake ta mashi tunda aka fara bikin wai yabi mashi yarinyarshi a hankali if not da kanshi zaizo ya dauketa if yaga yana neman hallakata..Nur bai samu bakin cewa komai as haushinshi yakeji for not rakashi cikin gidan amma ba yanda zaiyi dashi haka yana gani ya tada motarshi ya bar gidan ya gama masa iskanci iri iri daga karshe dai shi kadai ya shiga wajen amaryarshi as dama idan aka cire Bobbyn ba wasu abokai yake dashi ba.
Allah sarki Miemie Saida ta bani tausayi dan da gaske Nur bai saurara mata sbd tsabar azaba gari na wayewa ta dokowa Aysha kira wai dan Allah dan annabi tace ma uncle Bobby azo a dauketa daga gidan that bazata iya zama ba wai kasheta zakiyi..hakuri sosai Aysha ta bata tareda tura mata Billy gidan taje tayi mata duk abunda ya kamata don hanashi zuwa inda yake tayi balle ya taimaka mata..Bobby Kam yana samun labarin ya dinga 6a66aka daria kmr mahaukaci sabon kamu dan takanas yaje har inda Nur din yake yayita mashi daria yana tsokanarshi wai tsabar shi novice ne shine yaje yayima yarinya fata fata har take cewa bazata iya zama dashi ba..Nur dai baice dashi komai as yasan duk wnn abun ramuwa ne yakeyi tunda shima ba kalan tsokanar da bai masa ba lokacin nashi bikin.
Haka rayuwa yacigaba da tafia musu cikin zaman lafia da kwanciyar hankali..ga kuma uwa uba tsantsar soyayya da kulawa da juna..lokacinda ta mashi zancen komawa asibti yace ta bari idan Nur ya bude asibtinshi sai ta fara aiki a can that idan asibti daya suke bazasu maida hankali suyi aiki ba..hakan kuwa akayi don ana fara aiki asibitin na Nur mai suna Annur specialist hospital ta fara aiki a can as a staff midwife..little Noor da yayi wayo ya zama Kato dashi take barinshi wajen Mummy da ko kusa yanxu bata kaunar rabuwa dashi dan ganinshi takeyi kmr Bobbynta...yanada wata 10 a dunia Aysha ta sake samun wani cikin aikuwa zo Kuga tashin hankali a wajenta kmr wanda tayi cikin shege..wai a matsayina na midwife bai kamata ace tayi haihuwa irin wnn ba ya kamata ace saita yaye Little Noor kafin ta samu wani cikin..Bobby dai baida bakin cewa komai sai na bata hakuri gashi laulayi takeyi sosai kusan fiye ma da wanda tayi a cikin small Noor hakan yasa har aikin ma ajiyeshi tayi tacigaba da rainon cikin a gida..shi kuma small Noor kusan koda yaushe yana wajen Mummy gashi ya hanata yayeshi wai sai yakai 17 months...haka dai ta hakura take fama da ciki da kuma shayar dashi don dai ba yanda zatayi ne amma da tuni ta yayeshi ta huta.
Cikinta nada 5 months Billy ta haifi yarta mace aikam sunje Gombe sunsha suna yarinya taci sunan Maman Hamma Aysha suke kiranta da Maama..Saida sukayi sati biyu itada small Noor daya kara girma da wayo kuma yana yawonshi ko ina snn suka dawo Kano..nan kuma tacigaba da zaman jiran nata haihuwan itama.
Kamar yanda yace yana shiga 17 months ta yayeshi ya koma wajen Mummy gaba daya..cikinta na shiga wata tara ta haifi twins dinta mata masu kama da ita sak kmr an tsaga Kara an karya gasu kuma kamarsu daya da juna dan ko Bobby Saida yayi da gaske snn ya iya ganesu...farin ciki a wajen wnn ahalin ba'a mgn dan duk wani Maison Aysha da Bobby Saida yayi musu farin cikin samun wnn karuwar..Yara masu mugun kyau da shiga rai kuma identical twins..ranar suna Yara sukaci sunan Mummy da Ammi wato Maimunatu da Nadia anci ansha anyi shagali sosai wajen sunan kmr sunan fari.
Bayan wata daya Miemie itama ta haifi baby boy dinta mai sunan Bobby..fadan farin cikin da sukayi is a watse of time amma sunyi murna sosai musamman daya kasance anyima Bobby takwara dan hatta nickname din iri daya ne..Attahir ne sunanshi na gaskia amma za'a dinga kiranshi da Bobby...rana suna shima Bobby ya taka rawa gani sosai fiyeda tunanin mai tunani..haka Mummy da aunty sumy sunyi farin ciki sosai da wnn takwara na Bobby kuma takwara daddy tunda sunan daddy shima yaci.
Twins din Aysha nada one and half year akayi bikin Husna da Sa'eed..su amara Lamido sati biyu taje tayi a Gombe dan har aka gama biki aka Mika Husna gidanta dake Kaduna bata dawo ba saida ta sake komawa Gombe..kowa ya kalleta ita da yaranta sai sun burgeshi dan yanda suke kyawawa dasu kuma masu wayo da shiga ran mutane..kwana hudu suka karayi suka dawo gida Kanon Dabo inda Kuma suka dora daga inda suka tsaya..tuni dama tacigaba da zuwa aikinta so no more zaman banza a gida..daga little Noor har twins din wajen Mummy take barinsu da nanny dinsu taje aikinta ta dawo.
Yau ma kmr kullum tana zaune dakin yaran nata da sukayi bacci ta sanyasu a tsakiya sai addu'a take musu tana bin dukkaninsu tana shafa musu a jikinsu..Bobby dake tsaye bakin kofa yana kallonta a hankali ya karaso ciki yana kallonta da murmushi hannayenshi rungume a chest dinshi yace"this is not fair baby"..kallonshi tayi itama tana murmushin tace"me Kuma nayi again partner?.."yace"kaga daya hankalinki yanxu ya koma kan twins dinki mana..tunda kika samesu ni da aboki kika dena kulawa damu Kuma"..murmushin dai take cigaba dayi snn ta mike daga inda take ta tsaya nan kusa dashi tareda mishi side hug ta dora kan akan shoulder dinshi tana kallon yaran nata dake baccinsu peacefully tace"ni ban wani dena kulawa daku ba partner..kishi kawai kukeyi dasu"..hannu yakai shima ya zagaye waist dinta dashi yana kallon kids din nashi yace"no kinfi damuwa dasu a kaina"..daria ta saki before tace"oh yanxu ka dawo kai kadai banda little Noor knn?.."yace"yes mana duk kinfi basu time dinki akaina..kuma dai kinsan ni nafisu bukatarki a kusa dani"..har yanxu bata dena murmushi ta danyi dagen kafa ta manna mashi kiss a right cheek dinshi snn tace"yi hakuri ai from now zuwa safiya duk time dinka ne and babu yaron da zai cinye Maka shi believe me"..murmushi ya saki yana kallon kids din kafin ya dawo da kallon nashi gareta yana cewa"bazan taba gajiya da godia wa Allah daya mallaki mun such a lovely family kaman ku ba..u guys are my everything and i love u so much"..sake rungumeshi tayi itama tana kallonshi eyeballs dinshi tace"we also love u so much papa..u mean the entire world to us..we are so proud of u"..rungume juna sukayi suna kallon yaransu cikeda so da kauna.. little Noor na kan gadonshi yana bacci likewise twins suma suna kan nasu bed din suna bacci rungume da juna..matsawa yai yayi kissing yaran duk snn ya rufesu da duvet snn ya jata suka fita dakin bayan sun kashe masu haske yana rungume da ita yake cewa"ina sonki kwatankwacin son da Umar Faruk ke yiwa Amal(INA ZAN GANTA)..snn ina kishinki kaman yanda Dr.Taheer ke kishin Layla(Dr.TAHEER)"..murmushi sosai takeyi ta kasa dena blushing sbd words din nan nashi means the entire world to her..Saida suka shiga bedroom dinshi ta hade goshinshi da nata snn tace"nima inasonka sosai partner..u are my hubby,my love,my soul partner,my darling..my very own husband and the father to my beautiful kids..i love u unconditionally"..lumshe Ido Bobby yayi ya hade bakinshi da nata itama tayi grabbing nashi da sauri nan kuma wasan ya sauya tsakaninsu.
Alhamdulillah!
Alhamdulillah!
Alhamdulillah!
Anan na kawo karshen novel dina 🤍Dr.BOBBY🤍..kurakuran da mukayi ciki Allah ya yafe mana.
Dubun godia ga each and everyone of u out there that patronize..May Allah reward u abundantly..Allah ya biyama kowa bukatunshi na alkhairi🙏🏻
Thank u!
Thank u!and
Thank u!
Masu buqatan document should contact me through 07063800556.
Thank you once again and love u all❤️
Am going to miss you guys😭💔
Rano✨
0 comments:
Post a Comment