Ma'eesha tasha baccinta ta tashi ba hankali ta fara bude abincin iri iri sai ta rufe ta dawo gefe na tare da nuna min da yatsanta tana Sis ni wancan nake so cike da shagwaba tace ni me tiririn can nake so,saida ta bawa mutane dariya,da rana kuwa tana cin tuwon shinkafa tace Sis wai kamar ana biki? Muci tuwon mu musha Kokonmu Ammah ta tafi Rimin Gado kafin ta dawo. haka muke ta amsar gaisuwa,har akayi sadakar uku dangin nesa duk wasu sun tafi sai iya na Ammah mata da wasu mazan su uku wanda suke uba daya da Ammah,makwafta suna kawo mana abinci iri iri kullum,da kudin sadakina nake yin komai na kashe kudi sosai domin mutuwa yanzu kamar biki haka take,Meenat sunji ana ta ce min Amarya Allah sarki jiya aka daura mata aure sabo da har yan unguwar mu sun San anyi auren domin munzo da Aayan tare dasu Abbi sunga gidanmu na asali da muke rayuwa,haka kuma na hada su da wasu manyan dake makwaftan mu tunda mu bamu da yan Uwa a cikin kano sai abokan arziki,gashi Ammah na asibiti kuma Bai dace ace anyi aure ba wasu shedu ba babu Sanin mutane ai babu dadi a ganina bai dace ba,shi yasa nace dole Muzo sharp sharp su gani su San inda muke da zama duk da cewa dangin Aayan sun min kallon wulakanci ganin inda muke da zama har dariya suka yi masa dama sun San ai sai talaka ce zata iya aurensa.
Ni dai ko a jikina tunda kudi zan samu gani nake kudi sune maganin komai,sai gashi tun ba aje ko ina ba an saukar min da Aya,Meenat ce ta jani gefe tace Sis ya naji ana ce miki Amarya?ki Bari baki su tafi zan sanar daku komai,da gaske kinyi aure? No ki Bari idan mun nutsu zaki ji.Bayan anyi sadakar Bakwai muna zaune Dangin Ammah suka samu a tsakiya cewar zasu dauki Meenat da Ma'eesha su tafi dasu kauye ni kuma tunda nayi aure na zauna dakin mijina duk da cewa abin ya daure musu kai rashin ganin angon nawa a wajen janaizar Ammah,amma sai nace dasu baya kasar yayi tafiya kasar waje,cikin ladabi nace Ni bance karku tafi dasu ba dama Ku ya dace Ku rike mu,amma sabo da karatunsu kuma kauye ba schl baya ga haka basu saba da rayuwa acan ba,kuma nima zan shiga damuwa na rashinsu ga rashin Ammah me zai hana a bar min su mijina zai rike su ba matsala zai musu komai sai mu zauna tare,Dangin Ammah dama kadan suke jira nan suka fara masifa to ai gaki gasu in dai rikon dadi gareshi,sannu yan Birni Ku yan boko ko to dama dan mu fita hakkinku mukace zamu tafi daku amma tunda haka kuka Zaba shike nan, a cikin matan ma daya tace a'a haba a bisu a hankali ai yara ne ga rashin Uwa sunyi amma har ita Mufeeda kanta nawa take kuruciya ce kawai,nayi mamaki a birni guda amma kamar Mufeeda wai Fatima ta yarda tayi aure tana yar Sha bakwai a shekaru,duba fa yan Birni da sai su kai shekara talatin yarinya na yawo a titi wai karatu take.
Daya cikin maza kanin Ammah yace to Alhmdllh ai mijinta me kudi ne da alama zai iya rikesu da Amana na tabbata amma ya dace ace munje munga gidan mijin naki,gumi ne ya keto min nan take na rude.
Karya na kakalo nace ai ba yanzu zan tare ba,dazu munyi waya dashi jibi zai dawo daga turai sannan zasu sa ranar da zan tare sai na fada muku a waya ko nazo har gida na kawo kati sai kuzo ayi komai da Ku,ganin mijin nawa me kudi ne tunda sun ganshi tare da danginsa ba karya gashi sunsha kyautar kudi kawai sai suka washe baki tare da cewa to Allah ya kaimu ki tabbatar kin yo mana waya,da sauri nace Insha'allah,to yanzu abinci fa da sauransu wa zai baku kuma Bai dace Ku zauna Ku kadai ba a wannan gidan ba,nace ai masu gadi zai kawo mana yace suna kan hanya ma sojoji ne,da mamaki sukace lallai kunyi dacen me kudi ke ko yar nan kin huta a duniya dan Allah a dinga tunawa damu dangi kar a samu a manta damu,nace haba dai ai daku za a ci komai,nan dai suka yi ta kauyancinsu na Fulani daga nan suka tattara gaba daya suka mana Sallama zasu tafi,har kudin mota na basu muka rakasu har tasha sabo da bamu saba dasu ba ko kuka bamuyi ba sabo da sun ishemu dama sai bata mana gida sukeyi suna samu aiki.
Suna tafiya mu Ukun muka tsaya a wani gidan yan haya,gidan haya ne Babba,daki daki ake bada hayar kowa da dakinsa sunfi mutum ashirin a gidan kuma toilet daya garesu,Meenat tace me zamu yi a nan? Ko magana banyi ba nace suzo muje,muna shiga muka gaisa dasu suna ta mana ta'aziyya,dakin wata Dattijuwa Uwaliya na shiga tana zaune gefe tana Shan kunu,Uwaliya bata taba haihuwa a duniya ba,danginta duk suna kauye sana'ar aikatau wanke wanke da shara ce ta kawota birni,bata yi dacen gidan da take aiki ba kuma bata son zaman kauye sabo da babu sana'ar kirki a can,sai ta kama hayar daki a birni tana zuwa gidan aikin haka da safe ta dawo da yamma kullum,da fara'a ta tarbeni muna gaisawa nace Uwaliya idan baza ki damu ba ki dawo gidanmu da zama mana kyauta na baki daki daya mu kuma sai mu dauki daki biyun,dama gidanmu daki Uku ne sai dan kitchen da toilet ammafa bashi da wani kyau gidan gidane na talaka amma nasan yafi wanda Uwaliya ke haya a ciki,da murna Uwaliya ta dinga godiya,haka mutane suka tayata murnar daina biyan kudin haya zata zauna kyauta a gidanmu,wasu suka dinga mamaki wai duniya ta juya min baya duk son kudin Mufeeda yarinyar da komai nata na kudi ne yau gashi taji uwar bari kar a hauro ayi musu fyade har roko take a zauna musu kyauta a gida lallai duniya tun ba a je ko ina ba kenan.
Uwaliya ta kwaso kayanta kaf tare da sanarwa me gidanta ta dawo gidanmu sabo da gida ba Babban gida bane gashi mijin kasuwancin nawa ya kashe min Uwa ya gudu ban kara ganin sa ba,ya barni da igiyar aure mara amfani a kaina,idan bai nemeni ba ya zanyi wayyo neman kudi ya jawo min.
Dare yayi Uwaliya tana dakinta ta gama cin abincin da na siyo mana har ita na bawa tana ta godiya sabo da Uwaliya mutuniyar kirki ce ba ruwanta da kowa ba gulma ba sa ido.
Na tasa kannena a gaba Meenat da Ma'eesha nace dole suci abinci naga duk sun rame,duk da cewa na fisu ramewa sosai,Bani da karfin gwiwar da zan mana girki duk cikin kudin Sadakina nake cinyewa,Meenat tace sis kici mana idan baza kici ba mu taya zamu iya ci,duk kin rame dan Allah ki kara hakuri kullum fa sai kinyi kuka cikin dare muna jinki,Maeesha tace kuma ance ba kyau ana yiwa wanda ya mutu kuka yanzu Ammah kina kara mata azaba fa,wani hawayen tausayin kanmu ne ya zubo min na share ina kakalo Murmushin dole tare da sa hannuna a abincin muka fara ci badan muna so ba,kawai tunanin Ammah nake da kanmu tare da igiyar dake kaina,miji bai San me nake ciki ba,kaico na nikam na tafka kuskure dana sani nakeyi da nadama,ganin basa ci da yawa na shiga basu da kaina ina ciyar dasu suma suna bani abin haushin na fisu saurin kuka kawai hawaye nake ina ci har sai da na karya musu zuciya suma suka fara,Maeesha tace Wai Ammah baza ta dawo bane? Wai Sis ba a dawowa? Nace baza ta dawo ba ina shesheka na kara fashewa da kuka babu me lallashi,muna ta tuno Rayuwar da mukayi da Ammah me dadi tun tasowar mu,dan ma Allah yasa gaba daya kayan Ammah na sawa na kwashe na bawa Danginta dan kar ma na gansu bakin ciki na damuna da yawan kuka,sai pics Namu da nata amma komai nata na kwashe na bayar,masu amfani kawai na ajiye tunanina ko da kuwa Allah zai bayyana mana Abbanmu watarana.
Uwaliyace ta shigo ta zauna kusa damu ta fara yi mana nasiha tana lallashi tare da kwantar mana da hankali har mukayi shuru,sai ta fara yi mana labaran tatsuniya na abin dariya muka dinga ta faman dariya kamar ba mune dazu muke kuka ba,mun dade sosai sannan nace muyi bacci ta tafi dakinta,nima na kulle mana daki,muna kwance mun cure waje daya,cike da nutsuwa nace Meenat Ku tashi muyi magana,da sauri suka Mike zaune a saman katifar domin ko arzikin gado bamu dashi.
Rungumesu nayi a jikina sannan na kwantar da Ma'eesha saman cinyata ina shafa kanta,Meenat ma tana jikina ta jingina,nace Meenat nasan kinfi Ma'eesha hankali zan baku labari akan zancen da kuke ji nayi aure,ba wai bane tabbas da gaske Meenat nayi aure nan na kwashe labarin duk yanda akayi tun daga fitar da nake nemo kudin maganin Ammah har haduwata da Aayan,Yarima tare da Aurena kaf na basu Labari Ma'eesha nasan duk da ta fahimci komai amma baza ta kai Meenat fuskanta ba,gani nayi Meenat tana ta murna tana dariya,nace mene haka ke kuma? Sis wlh kin cikawa Ammah burinta shi yasa,kuma Alhmdllh kin samu me kudi Allah yasa na gari ne sis ya tallafa mana,kawai ni shawara mu dage da addua kamar yanda muka saba sai kiga Allah ya canja masa zuciya from bad to good,kuma am serious bashi ya kashe Ammah ba domin kina fita aka fito da Ammah lfy an mata aiki tuni kinga lokacin ma baki je wajensa ba bare yace miki baza a hada ta ba sai kin aureshi kawai wayo sukayi miki, naji dadin zancen Meenat sosai da ta ganar dani amma da haushin Aayan nakeji cewar shi ya kashe Ammah amma duk da hakan ban wani yarda ba kawai shi ya kashe min Uwa.
Meenat tace lokacin da Ammah ta farfado Sis tana ta nemanki bakya nan,sai tace mana naji a jikina wani abin Alkhairi zai samu yata Abin alfaharina Mufeedata yau Alkhairi zata hadu dashi,naso ace zanga wannan lokaci da Idona amma kash,sai muka ga tayi shuru,ta kara rike hannuna tace Meenat kuyiwa yar uwarku biyayya idan kuka saba mata bazan yafe muku ba,ku hada kanku karku taba rabuwa sai aure,Mufeeda zata rike min Ku da Amana kamar ina raye,ta Zama madadina,sai tayi tari taci gaba kuce ina son Mufeedata Allah ya bata miji na gari me kaunarta wanda zata huta taji dadi a hannunsa,sannan Ku fada mata nace duk Wanda ta aura ko waye tayi masa biyayya,ta kara hakuri sannan ta kula dashi da rayuwarsa tare da komai nasa da ya shafeshi,karta bari a take mata yanci duk Rintsi ta kwace yancinta,Mufeedata nasan ba me tsoro bace dan haka kar taji tsoron fadan gaskiya a duk inda take,taji tsoron Allah a duk inda take,tabi Allah,ta kula da ibada,ta tsare mutuncinta na ya mace,sannan tabi mijinta ta kula da iyayensa,ku rike addua, kuyi Zumunci dangina dana babanku baku da kamarsu, ba da iya Mufeeda nake ba,gaba dayanku yarana wannan shine abinda zan bar muku,shine a matsayin gadonku tunda ban bar muku komai ba,karshe Ku fadawa Mufeeda idan Allah ya bayyana babanku kuce masa duk abinda ya min na yafe masa baki daya,ni nasan ban zalinceshi ba amma shima ya yafe min,naso ace na aaaabaku labari akan zamana da babanku har zuwa sabanin da muka samu,da dalilin sabaninmu amma idan ya bayyana nasan zai sanar da......Nan mukaga Ammah tayi shuru Sis sai ga Doctor ya shigo yayi aune aune sai muka ga ya lullubeta suna magana da turanci da wasu nurses nan take mukaji ashe mutuwa Ammah tayi,gaba dayanmu kafin Meenat ta gama bamu labari mun jige rigarmu da hawaye..Nan Ma'eesha tace Sis Meenat kin manta tace mu fadawa Mufeeda wai tayi aure shine burinta sannan idan tayi aure ta fadawa mijinta Ammah na gaisheshi kuma ga Amana nan ta yarta Mufeeda abin sonta me share mata hawaye,ya daya tamkar da Dubu,mace me kamar maza ya riketa Amana ya bawa mufeedanta farin ciki shine bukatar Amman Mufeeda,nan take da jin zancen Ma'eesha sai muka koma muna dariya muna hawaye kamar Ammah ce ke maganar,dama Ma'eesha akwai iya bada labari gashi bata mantawa yanda ka fadi abu haka zata bada labari. Haka mukayi ta hirar Ammah har dai na sa Ma'eesha a tsakiyarmu muka kwanta abinmu har bacci me nauyi ya kwashe mu.
Sati biyu da rasuwar Ammah cikin kudin Sadakina na kara jarin sana'oina,cikin Sadakin na canjawa su Meenat makarantar Kudi aka yi musu transfer a secondary schl me Saukin kudi sunfi na Gomnati karatu ni kuma bani da burin da ya wuce suyi karatu,Komai har su Uniform nayi musu har kala Hudu hudu su schl bags littatafai etc,haka nayi mana sababbin dunkuna masu dan kyau,na kara siya mana abincin gida domin tuni na cire rai da auren da nayi na gama tabbatarwa cutata Aayan yayi sabo da haka kawai nayi watsi da wani aure,na manta ma ina da igiyar aurensa sam duk da cewa abin na raina amma na hakura na rungumi rayuwarmu ace anfi sati biyu da daura aure amma kamar wanda ya auri karya ai idan da gaskiya sai yazo ya biya ni kudin kasuwancina dana yarda na aureshi bisa sharadi.
Haka na kwashe wata guda da aure amma babu labarin Aayan abin takaicin kuma duk na karar da kudin sadakina,gashi kuma sana'ar tawa yanzu Sam bata tafiya ba kudi a hannun mutane,sai a yini guda ba a zo ance za a siyi ko Wake ba,duk na shiga damuwa ina tunani idan komai ya kare mana ya zamuyi ina zan sa kaina,abinda ya Dameni shine nayi Nadamar Halayena na Algus a sana'a ta tuni yanzu tsakani da Allah nake yinta bana kara komai marar kyau,kuma Istigifari nakeyi Allah ya yafe min,Amma Kuma dana gyara halina sai ma na daina ciniki,komai ya tabarbare,ba riba,lokacin kuma da bana yin ingantacciya komai tafiya yake min dai dai ina samun ciniki da riba,ikon Allah kenan yanzu Kusan duk sun karye ma,idan ya kare sai dai na iba a cikin Sadakina na kara dama duk kudin ma sun kare sabo da nayi mana abubuwa ciki da dama.
Sai da nayi dana Sanin canjawa su Meenat makarantar Kudi yanzu da uban me zan biya musu idan shekara ta kare,nidai haka nake ta yawon saro kaya da siyarwa ina sana'ata tunda ba labarin angon,ni kuma bazan je gidansu ba,ga rasuwar Ammah kullum sabuwa ce a wajenmu ko yaushe muna kuka muna tunaninta.
Yau juma'a na kai wata daya da sati daya da Aure kuma haka da rasuwar Ammah,tun safe na sallami su Meenat suka tafi schl,Uwaliya ma ta tafi gidan da take aiki,ni kadai ce a gidan sai da na gyara ko ina dake gidan fes fes tare da kunna turaren wuta,na kunna turaren wuta har Toilet sannan na dawo tsakar gida jikin Rijiyar gidanmu ina wanke mana kayan sawarmu ina shanyawa ga girki ina yi jullof din shinkafa taji kayan hadi harda kifi sabo da bamu da yawa shi yasa girkinmu ke dadi,sai dana cika igiya da kayanmu kana na shanya tare da kara wanke wajen,kwashe abincin nayi a wani foodflask me dan kyau sabo dana siya mana shi set biyu.
Lokaci na kalla naga bani da abinda zanyi kawai na kwashe yan kudin da suka rage min na zuba cikin Aljihun tight wando na na ciki,sabo da ni duk tight din dana ke sawa cikin kaya to sai na kaiwa wata tela ta dinka min aljihu da zip a jikinsa sabo da ko ina zanje a duniya da kudi a jikina kaf nake tafiya tun Ammah Nada rai,bare yanzu da nake tsoro kar na barsu a gida wani cikin yan iskan gari su shiga su yashemu tas mu rasa inda za muyi shi yasa kamar me aikin Hajji kudina na jikina wanda zanyi amfani dasu kawai nake rikewa a hannuna,kulle gidan nayi tare da tafiya gidan kawata Nawwara sabo da tana ta zuwa ni bana zuwa,da Sallama na shiga muka gaisa da Ummanta tare da Yayanta Hammad,tunda na shiga Hammad yake ta kallo na har kunya naji,Umma tace shiga ciki mana Mufeeda mutuniyar taki yanzu zata dawo ai,ina Zaune sai ga Nawwara ta dawo dama Salat aka aiketa ta siyo,Da gudu ta fado palon tare da miko min hannu muka tafa,tace shegiyar gari sai yau zaki zo, nace ke dai bari ba lokaci wlh yanzu ma dan kar na karya alkawari nazo miki sauri nake na koma kafin su Meenat su dawo kin San yau Friday,Nawwara tace hakane uwar mata,Wlh ina tausaya muku musamman ke da kike komai it's not easy ace kamarki ke kula da gida just 17yrs,ni abinda ma ya Dameni Mufeeda auren nan naki kinji yanda ake gulmar a unguwa dan abin ya shafeku ne ba za ayi a gabanku ba,wasu sunce karya ne dama,wasu kuma sunce ai auren kudi kika yi sabo da son abin duniya gashi wai ya gudu yaki zuwa ko kallonki baya yi,wasu ma sunce bature kika aura,wasu kuwa wai ciki yayi miki shine aka zubar dan kar a gane shine akace ya aureki,wasu kuma sukace ai ana daurawa ya samu ya kwanta dake shine ya fece,ke kowa da abinda zaice,murmushin takaici nayi nasan ni na jawowa kaina sai nace can da matsalarsu zasu gani ai watarana gaskiya zatayi halinta,yanzu gulma ba kauye ba birni kowa yinta yake.
Ita kanta Nawwara karya take tace tasan sirrina ni dama can ban damu da kawaye ba bare duk sirrina na kwaso na fada musu a dinga gulmata sabo da mutum mugun ice wani jira yake yaji sirrinka yaje yayi ta yadawa a duniya shi yasa ni bana so wata ta fada min sirrin rayuwarta kuma nima bazan fada miki nawa ba kawai ayi hirar duniya,duk inda mutum ya kai da gulmarsa bazaice ya San sirrin gidanmu ba,shi yasa ko ita Nawwara tayi tayi taji gaskiyar Aurena da halin da nake ciki amma naki yarda ma Sam ta sani daga ni sai yan uwana suma kuma haka Ammah ta tarbiyar damu,sirrinmu iya mu kawai family,share zancen Nawwara nayi na saki wata hirar can ta duniya daban,daga nan na Mike nace yan makaranta sun kusa dawowa ni zan wuce,Hammad yana Jin haka ya mike tare da fitowa waje,saida ta rako ni har waje muka yi Sallama,ina cikin tafiya Sai ga Hammad yana cewa Mufeeda na amsa a mutunce,Yace wai da gaske kina da aure dan Allah? Nace ae,da gaske ko wasa ni fa ban yarda ba na dawo daga service naji labari,murmushi nayi nace wlh yaya Hammad da gaske ne, bata rai naga yayi tare da cewa to gaskiya wannan ba mijin kirki bane kisa ya sake ki kawai ai gwara ki zauna ba aure,nace to idan ya sakeni wa zan aura?Ni ina son mijina bazan iya rabuwa dashi ba,komai shi yake daukan nauyinmu,Hammad yayi wani dariya kamar Boss yace sannu yar karya da ba a San Asalin balbela ba da sai ace daga masar take,ance me kudi ne ya akayi kike sana'a?kina ci da kanki,wa ya taba ganinsa yazo wajenki?makaryaciya rufa miki asiri zanyi kisa ya sakeki na lallaba Na aureki Ku ba gata ba,ba yayan uban kowa ba sai shegen iyayi wai ku kyan da kuke dashi ne yake rudarku ko?
Nima fa bani da hakuri watarana nace ina ganin mutuncinka Hammad karka bari na yaga ma mutunci a unguwar nan,ka gyara kalamanka,ni yanzu me daraja ce da tsada domin ina da aure kuma da ace kasan wa nake aure da sai ka raina kanka tare da yin nadamar kalamanka,ni nafi karfinka wlh ko ace bani da aure hankalinka da nutsuwarka sun min kadan a matsayin mijina,ina fadar haka na juya cike da Raunin zuciya ina son fara Kuka... dum gabana yayi mugun faduwa ganin motocin Aayan sun kai su Bakwai a jere kofar gidanmu,juyowa nayi na kalli Hammad kana nace ga dan Halak can, zo ga mijin nawa sai ka mutu na juya ina tafiya,na barshi nan tsaye,kusa da inda suka yi parking akwai me salat ba ruwana na tsaya na siya mana salat da tumatir sannan na rike ledar zan shiga gida,muryar su Meenat naji da fara'a suna sis mun dawo ina kika je?da sauri suka karaso tare da rungumeni ina musu Kiss a goshi domin mun saba da hakan ma,Ma'eesha ce ta karbi ledar salat dake hannuna ni kuma na karbi jakankunan makarantarsu muka nufi shiga gidanmu,ko kallon motocinsa banyi ba,yana ciki duk abinda mukeyi yana kallonmu,yasha mamakin ganin ko kallon motocin banyi ba kuma yasan na gane shine saima gida yaga mun shige,ni kuma cike da bakin ciki na banko kofarmu da karfi da niyyar na rufe dan Ubansa tunda baida mutunci nima zan nuna masa abin haushi da kunya kawai sai kofar ta balle baras ta fadi kasa rigijif ai ko har securities dinsa sai da suka barke da dariya yanda na shiga gidan cikin fushi da hasala tare da mako kofar kuma sai ta balle.
Aayan ma sai da ya dara duk kuwa da kuncinsa,muna shiga na taimaka musu suka cire kayansu,nace suje suyi wanka muyi sallah sai muci abinci, shi kuwa Aayan ganin masallaci za a fara sallar Juma'a sai yace suje suyi sallah sai su dawo,a nan masallacin unguwarmu sukayi Sallar, kafin su fito na gyara salat na yanka mana,Bayan munyi sallah na zuba mana a tire kato kun San dai akwai ci ni kam,a tsakar gida saman tabarma na wani baje cinyoyina,sanye nake da Vest red,sai skert din atamfata yayi mugun Dameni gani da hips tare da da tudun Mazaune kamar babbar mace,haka nayi wani cas dani ga skin dina jajir da ita fara,ko dankwali ban daura ba sabo da ni dama a gida bai Dameni ba,jelar gashina har yaso wuce tsakiyar baya na,sajena da gashin gaban goshina sun kwanta luf,ina ta bawa su Meenat abinci a baki kamar wasu yara nima ina ci suma suna bani muna hira.
Wani yaro ne ya shigo da Sallama wai Mufeeda tazo sauri yake zai tafi,nasan bazai wuce Aayan ba cike da masifa nace kace bata da lokacinsa,yaro ya je ya fada sai ga yaron ya dawo yace wai idan ya iskeki sai kin gwammace kida da karatu,Mufeeda tace kace nace yazo din koma mene yayi idan zai iya,yaro yace ni dai tsoro nake ji bazan iya fada masa ba,Mufeeda tace to dan uwarka nice sa'arka zaka zo ka fada min fice min a gida,yaro ya fice da sauri yana kuka Mufeeda ta zageshi,can sai ga Oga Aayan da kansa ya shigo gidan cike da bacin rai yana huci,kamar ance wani ya mutu yanda yake kunci,yanda ya hadu yau ba a cewa komai,yayi masifar kyan da ban taba gani ba,cikin kana nan kaya yake hadaddu duk gidanmu ya gauraye da kamshinsa.
Wani Kwarjini ya min tsoronsa ya kamani na fara da na Sanin maganar dana fada masa,Ma'eesha sarkin Surutu tace sis gashi nan ya shugo ko shine mijin naki? Meenat ta kalleshi ta kalleni haka take yi sannan sukace ina yini? Da kyar ya iya bude baki yace am fine tare da kare min kallo ta kasan ido,
ni dai naci gaba da basu abinci a baki ina cewa kuci abinci akwai Islamiyya kun sani, ganin su Meenat a ransa yace har kanne gareta Ashe,muryarsa naji yace ina Mum naki,cike da zafin rai nace taje inda ka aiketa, ba wannan ne ya kawo ni ba ina da aikin yi,kizo muyi magana dake,Meenat tace Sis kije mana,sai da na ebi abinci a hannuna sannan na Mike da abina ina ci kamar mayya,ya kalleni yana mamakin jarabar ci na ko micijin ciki ne da ita oho,hannuna da shinkafa a ciki na dunkuleshi nace shigo wannan dakin,ya wani yatsina fuska yana tabe baki haka dai ya shiga yana wani makale jikinsa irin zai kwashi dirty,
Ji nayi yace ba a gidanmu zaki zauna ba yanzu,wani gidan za a kaiki daban,kiyi fixing Date da kike so su Abbi sunce ba yanzu zaki shiga family house ba sai nan gaba,so gidan dana kaiki rannan kike gyarawa nan zaki shiga,ki sanarwa Mum naki,wani farin ciki ya kamani kamar na taka rawa wannan hadadden gida ga kayan dadi zanci na koshi, ban san sanda na fashe da murmushi ba tare da cewa wannan gidan me kayan dadi? sai kuma wani bakin ciki ya tsaya min wato bai ma San Ammah ta rasu ba,kuma ko irin yace min ya me jiki ko ta warke Sam,nace aiko ya me jiki kace min ko? Au bata warke ba?kamar na mareshi haka naji,nace ta rasu,Allah yaji kanta ya furta irin ko a jikinsa,nace daga ni sai kannena mu uku,yace then? kuma ni yanzu na fasa auren ka sakeni kawai yafi min bashi da amfani sam,murmushi yayi yana daga tsaye yace kin makaro kinci Sadaki,kuma na biya kudin Magani na cika alkawari dole ki cika min nawa,don haka sai ki biyani ko ki karbi aure zabi daya,Hawaye ya zubo min da muryar kuka nace mugu ka kashe mana Ammah zaka ce na biyaka kudi,ai kaine ya dace ka biyani kudin diyyar Ammah kai ka jawo ta rasu,da tuni muna nan da uwarmu,Kuma haka ake Business din idan banda sadaki me ka bani,bayan kai kace zamu ji dadin duniya da kudin,zaka yiwa kannena komai na rayuwa zanyi abinda nake so da kudi yanzu me kayi daga ciki,haka ake Deal din,ai sai na fara gani a kasa tukun,Oya na mika masa hannu nace miko kudin fara harkoki da jin dadi first mu fara murmurewa muma muji dadin duniya sai na yarda nima a kaini gidanka,kuma dole ka sai min injin Markade na dinga yiwa mutane ina samun kudi domin makociyar mu da kudin Markade taje Makkah, tare da keken saka kayan sanyi, bai sanda yayi dariya ba matar dake neman jin dadin duniya kuma wai itace da Markade a inji, ita nufinta duk cikin Jin dadi ne bata saba da dadin ba to,nace kuma sai ka sai min irin abin rannan me dadi,ka bani kudin kashewa,yace nawa zan baki?Na gama tunanina na shirya masa mugunta zanci kudinsa da yawa nan take na sosa kaina nace Dubu bakwai duk wata daya,kacal?yace, Na hangame baki nufinsa basu da yawa nace Dubu goma Sha daya to,ya juya tare da cewa get ready Next wk Driver zaizo ya daukeku.
nace to haka za a kai maka Amaryar taka kai ba dangi?ba kwalliya?ba gyaran jiki?ko haka kaga anayi ko kuma son kudi da tsumulmula ce tayi ma yawa,mene Tsumulmula? Nace gashi nan haka wai ake kasuwancin zaka tafi ko sisi baza ka bani ba cikin kudina na business,abinci ya kare hakkinka ne,bani da Vaseline,ina so zan yi kitso ai sai ka kawo kudin ko? Ni tunanina ai nayi ne dan na tatseshi kudi na hada masa mugunta zan cinye masa kudi su kare,ya kalleni tare da daure fuska yana dariya a ransa yace nawa ne kudin?Na shirya karya na ninka kudin nace Dubu biyu,wata dariya ta kamashi amma ya maze ya zaro Dubu biyu sababbi kar yace gashi,na karba nace tsaya na irga domin kudi suna da doka tare da ka'ida,na dankwali yawu kamar me irga wasu milliyoyi na irga nace sun cika,yayi hanyar fita daga gidan, wai duk cikin Jin haushinsa dan na kona masa rai nace amma wlh girma ya fadi,an fadi kasa ba nauyi,ka bani kunya kuma ka bada guys ashe ma duk bogi ne da ake kurin ana da kudi sai dai a kwashi motoci ana yawo a gari,a tambayi Dubu biyu ba kari ba komai ina laifin ka bani Dubu uku ko ka kankaro girma da mutuncinka,amma yanda na fada haka ka bani a haka kamar gaske,ana tafiya kamar dan sarki aji tsoron Allah wlh azara'ilu ko yaushe zai iya zuwa, ficewa yayi da sauri sabo da dariya taci karfinsa bai so kuma taga hakorinsa yana dariya, haka ya shiga mota yana dariya,su Kansu escort din nasa mamaki sukeyi Aayan kamarsa duk jarabarsa wata na sashi dariya.
AsmaBaffa
[1/5, 5:03 PM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
26-30
Official
By
AsmaBaffa
MAMAN MEENAT ina godiya da Sharhi,taku ta manya ce kunfi karfin kowa sai dai mu kwashi gaisuwa. page na yara neπHAFCYCY this page is for u Sweety.
QUEENMERMU tamu dubun gaisuwaπππ❤❤❤❤
MAMAN WALEEDA kin boye Allah yasa lfy.
Masu Sharhi yan albarka
ASMABAFFA FANS CLUB
TASKAR SURAYYARMS
TASKAR FIDDAUSI SODANGI
HAUSE OF HAUSA NOVEL tare da sauran Gps ina matukar jinjina muku da godewa.masu min magana ta Pc tare da masu kira ina rangado muku gaisuwa me yawa Allah ya kara kauna.
Koda ya fita basu zarce ko ina ba sai gidan Yarima Bobo abokinsa wanda suke shirya komai tare,ni kuwa mamaki nakeyi kamarsa duk kudinsa wai yanda na tambayi kudin ba kara ba komai iya 2k din ya bani,nan nace bari ya dawo sai na gwadashi nace ya bani Naira Dari kacal na gani iya 100 zai bani,Meenat ce tace Sis mijinki me kyau dan gayu wlh kinyi sa'a wannan irin kyau amma dai dan kasar waje ne ko? Kyan banza ne dashi Meenat sai fadan masifa,Hmm to Allah yasa ya canja ya koma Sonki Sis ai idan munje gidansa kwalliya zaki dinga yi ta jan hankali ki sace masa zuciya da wuri,idan mun ganshi a gidan ko?ai ba gida daya zamu zauna dashi ba main gidansu daban inda za a kaini daban kuma ni ai ba sonsa nake ba ina ruwana da har zanyi kwalliya sabo dashi,sis ke har yau da sauranki Allah ana gabas kina yamma irin wannan ai abin a so ne,baki na tabe tare da cewa ke karki Dameni me zanyi dashi auren Kasuwanci nayi ba abinda ya Dameni ya dauki nauyin mu komai da komai muji dadi shike nan buri na,kallo na Meenat tayi tare da cewa Sis ke bakya sha'awar maza ne kamar wacce wanzami ya cirewa Budurci?ko dai ba a sani ba Ammah tasa wanzami ya yanke miki Belin ki? Dariya nayi domin Mufeeda ta fini Sanin duniya tana zuwa schl,nace baki da kunya Meenat ai ni bana son wani Namiji me zanci dashi tir Allah kiyaye,Meenat ta dinga dariya tare da cewa Sis yanzu ko yar Runguma kuyi bacci ba kya so ga dan Kiss ma? Baki na rike ina kallonta nace ke wanne kiss wanda nake gani a film? Wlh bai isa ba idan yace ma zai min za a kwashi Bala'i da yan kallo ke nifa duk irin harkar nan bata damuna gwara kudi kawai,Meenat tace ni kuwa da nice na Samu me kyau haka ga kamshi,kudi komai ya hada ai da anga kwasar duniya,ke Meenat yarinya dake kike irin wannan zance,da nawa kika girmeni wai ma ki zauna kamar ba yar cikin birni ba gaki a cikin Birni amma kamar kina kauye, ae naji tunda Ku zaku Zama yan birnin ba komai zan muku ko mene abinda nake so kawai na koma makaranta idan ya Amince amma ni me ya Dameni da wani love.
Muna rayuwarmu bayan kwana uku su Meenat suna zaune suna ta faman game a wayata Nokia a tsakar gida,ni kuma sanye nake cikin wando tight 3qrt blue sai rigata iya rabin cinya me gajeren hannu pink kaina ba dankwali jelar na lilo ina kusa da Rijiya na ebo wanki ina ta wanke mana kayan sawa kusan ko yaushe sai nayi wanki haka nake bana son kazanta.
Sallamar mutum muka ji kawai a cikin gidanmu kamshinsa ya gauraye ko ina nan take muka gane Aayan ne yazo yaji lokacin da na Zaba a kaini gidansa matsayin matar Aure,mamakina shine rannan a waje ya ganni ina yawo amma Bai ko tambaya me yasa na fita bada saninsa ba,kaina na bawa amsa ai ba Sonki yake ba ina ruwansa ko ma ina zaki je.
Ganin su Meenat suna wajen yasa na amsa Sallamarsa tare da mikewa ina goge hannu na,gabansa na karasa tare da cewa sannu da zuwa wani Kwarjini da tsoronsa yasa na dan duka nace Ina yini,ko amsawa baiyi ba,na Mike na kawo masa wata kujerar roba fara tare da kara goge masa kujerar da wata duster,sai lokacin ya zauna kamar wani sarki yasha kana nan kaya yau ma wandon kansa abin a kalla ne ya hadu pencil dashi,Meenat ga Uncle yazo nace sabo da shishigina shi kanshi sai da ya tabe baki wai Uncle,da sauri suka zo suma tare da durkusawa a gabansa suna gaisheshi to su dai sun fini samun matsayi sabo da ya amsa musu sau daya da lfy bai kara ko ce musu komai ba suka koma inda suke suna ta game dinsu,Yau wacce rana ya ganni bana cin komai, bai gama tunaninsa ba yana zaune yaga na shige dan kitchen dinmu na fito da pure water a plate guda biyu na ajiye masa,ko kallon plate din baiyi ba sai faman chat yake a waya yana wani murmushi,kara komawa kitchen nayi na dauko Ayaba guda wajen biyar na mikawa Meenat da Ma'eesha guda biyu,tuna ninsa shi zan bawa ragowar sai yaga na koma inda nake wankina na bare guda daya gutsira biyu na cinye gudan Ayaba,na dan ci gaba da wankina na kara bare guda itama gutsira biyu na cinye duk yana kallona ba tare da na gane hakan ba,guda daya na rage na koma wajensa tare da dora masa saman ruwan dana kawo nace gashi nan Kaci sabo da Ido guba ne shi yasa,komawa kitchen nayi tare da zubowa su Meenat tuwon shinkafa miyar ganye tun daga Ido zaka San akwai dadi,Nace kuzo Ku kara abincin yamma kar yunwa ta kama min Ku,dama indai ba schl to dole muna kara cin abinci da yamma,ni kuwa a rana sau hudu sau biyar nake cin abinci,shi yasa kannena ma haka nake dura musu ko basa so sai nace sai sunci kadan.
Ma'eesha tace nidai sis na koshi har sau nawa za muci tuwon nan gashi da dare ma kice sai munci,Na bata rai tare da cewa kin san tunda na zuba sai an cinyeshi ko Amai zakuyi sai kunci,Meenat cike da shagwaba tace pls Sis mun koshi Allah,nace to Ku kuzo muci tare nima zanci na zauna wajensu na fara ci ina dura musu ta dole suna yatsina fuska sun koshi,sai da muka cinye dole sannan na wanke plate din na maida kitchen,nace Ku ajiye wayar nan kuzo Ku karasa wankin nan da sauri suka taho tare da karba sunayi,ni kuma na koma kusa da Angona Aayan na zauna saman tabarma na kalleshi tare da cewa Angon Business,ba tare da ya kalleni ba yace wacce rana kike so? Nace to wai dangina baza suzo a dauki Amarya ba? Ni bana son mutane a harkar nan Business ne mene amfanin sanin mutane,ba auren so ba mene sai an sani wani auren kirki ne wannan da har zan nemi mutane,Allah baka hakuri zabi date da kanka idan ma yau kake so muje,amma kuma da mun tafi tare da Uwaliya da take gidan nan ko? Wani kallo me cike da masifa ya wurgo min tare da cewa wannan gidanku ne ko na haya? Namu ne na kanmu cewa ta,yace to bana son kwashe kwashe ku din ma dole ce zata sa Ku shigar min gida bare wata Uwaliya ko me,ku Uku nan zan iya rikewa wannan gidan kusa yan haya ko Ku bar matar a ciki ko Ku siyar da gidan ni ba matsala ta bace.
Burina kawai muje hadadden gidan nan ace yau gamu a ciki zamu zauna wayyooo dadi gashi nasan ma zai dinga siyo mana kayan dadi ai nan take nace azo gobe a dauke mu,mikewa yayi zai fita,wata dabara ta fado min na Mike da sauri tare da dauko Hijab na saka nabi bayansa da sauri sabo da so nake wasu yan unguwa masu sa ido su ganni tare dashi su tabbatar da gaske ne aure na a daina zagina a gari,sai da nayi sauri na jera dashi har waje,ya kalleni tare da cewa ina zaki je,nace uhmmm makwafta zanje tunanina zaice kar naje ai ina da aure sai naga ko a jikinsa,muka fita har waje tare ina ta faman Mannewa kusa dashi sabo da yan unguwa suga fa ae ga zahiri ga sheda,na rasa me zance nace wai ka tsaya mana banfa gama magana ba,ina jinki ai,sabo da na jashi da zance har mutane su ganmu da yawa nace haka ake Business din kuma ni me zansa idan anzo daukan Amarya? Banza ya min,nace sannan ina son Naira Dari zan sa kati a wayata na kira Family,da mamakina sai naga ya tsaya a jikin motarsa ya zaro Dubu guda sabuwa ya kira Almajiri ya mika masa tare da cewa dan Allah samo min canji ka ce a hada ma da yan 100.
Muna tsaye mutanen Layinmu yan sa ido yau sunga zahiri da idonsu motoci sunfi 8 a kofar gidanmu,sunga da gaske ne me kudinma na gaske ga kyau,muna tsaye dan mutane suce auren soyayya ne sai wani murmushi nakeyi ina washe baki,shi kuwa tunani yake anya lafiya ta kalau kuwa ko dai ina da tabin kwakwalwa mutum shi kadai ya dinga dariya yana murmushi haka,wasu maza ne matasa duk na sansu mugayen yan sa ido ne a unguwarmu hango su nayi sun taho wajen mu da alama ball zasu je duk sunyi shigar Jersey ina ganin haka na kara matsawa jikinsa kamar zan shiga cikinsa,kamshinsa yana ratsani ba zato yaji na saka hannuna a cikin nasa na rike kam kam kamar za a kwace shi,dama tuni na gano ba ta rike hannu ake yin ciki ba Meenat ta fayyace min komai,hannunsa yaja yayi yayi ya fisge amma sai dai ya girgiza da jikina gaba daya na rike hannun kam,idonsa yayi ja sabo da bacin rai da ace ba mutane yau da naci ubana a hannunsa dan Zane ni zaiyi kawai,Sake min hannu mana are u mad? Cewarsa ina murmushi tare da tamke lips dina ina mamularsa nace uhm uhm ni bazan saki ba kawai ka tafi baka bani kudin ba,su kuma mutane na layin yan sa ido ana wlh da gaske ne yana sonta sosai kalli soyayya,matasa suna cewa tayi dace Allah ya bata,wasu matan da suka sanni cewa suke ina ma sune wayyo dadi suna sha'awata,haka Nawwara ma ta fito ta hango mu nan ta tabbatar da wannan soyayya ce me karfi rike juna har a bainan nasi,Haka almajirin ya kawo canji still ina rike dashi ya hakura ya kyaleni ya karba abin al'ajabi sai ya cire Naira Darin dana tambaya ya mika min yace jeka da sauran Dari taran na bar maka kyauta,yaro ya tafi yana ta tsalle da murna,ni kuma ya bani Naira Darin,Nace ka rike albarka bana so tunda Ka iya bawa Almajiri Dari tara ni ko Dari,hannunsa ya fisge tare da maida Naira Darin aljihunsa ya shiga mota escort suka ja motoci suka kara gaba,ni ma nace Alhmdllh an samu shedu a unguwa na koma cikin gida abina.
Uwaliya tana dawowa na sanar mata cewar gobe Mijina zai turo a dauke mu zamu koma can da zama ita kuma ta nemi wata suci gaba da Zama a gidanmu suna gyara mana shi,ta dinga godiya sosai,nace danma mijina bai yarda bane da tare zamu tafi dake,Uwaliya tace hakan ma na gode ai kun gama min komai akwai wata kawata Kaltume zan nemota mu zauna tare,nace to ba matsala ga kayan kitchen da komai kuyi amfani dashi mu iya kayan sawarmu kawai zamu Eba. A daren muka hada kayanmu tas marasa kyau muka zubar domin babu wanda zamu bawa sun lalace da yawa.
Gidan mu kuma so nake na samu kudi na gyara shi na zuba yan haya a ciki shi yasa nace su Uwaliya su zauna kafin na samu kudi.
Washe gari 5pm Driver da katuwar mota ya Parker yace mu fito inji Oga,muka zuba kayanmu a boot Uwaliya munyi Sallama tuni ta tafi wajen aiki,munsha kyau domin duk jaraba sai da na dinka mana Atamfa me kyau ko wacce kalar tata daban,tasha dinki me masifar kyau riga da skert,da mayafi me kyau tare da takalmi me dan tudu me kyau,muka je saloon,sannan akayi mana lalle me arnen kyau har su Ma'eesha akayi komai.
Bayan munyi wanka Meenat ta tsantsara kwalliya tare da dauri me kyau dama ta iya watarana Amare marasa kudi suna kiranta tayi musu kwalliya da daurin gogoro sabo da tana da basira a nan sai ka rantse make up kaje aka yi ma,Haka tayiwa Ma'eesha ma kamar ka sacesu haka suka koma.
Amarya kizo na miki kwalliya kar mijinki ya raina ki yana kallonki a bagidajiya,da kyar na yarda Meenat ta zauna ta fara sheka min kwalliya tare da dauri me masifar kyau,ni kaina ji nayi kamar na lashe kaina sabo da tsananin kyan da nayi,kowa ya kalleni sai ya kara,sai kuwa ga Driver yace mu fito,Maeesha ce ta dinga kai kayanmu Driver ya zuba a boot dama ba wasu masu yawa bane,muka yafa gyalenmu kamar yan mata zamu party,Hips dina kamar zai fado tsabar tudu da fadinsa a skert, muna fitowa Driver sai wani girmamani yake,muka shiga mota nace Baba zaka kaimu makwafta muyi musu sallama,samun waje ga baki ga hanci amma haka nace Driver ya dinga kaimu gida gidan da muke mutunci sosai harda Nawwara mukayi musu Sallama cewar zamu dawo sai mu basu address na gidan mijina.sai kallo da gulma anga uwar motar da muke ciki makwafta ma sai an kaimu a mota,wasu suka ce Allah ne yasan manufar Jaki shi yasa bai Yoshi da kaho ba.
Bayan mun gama nace wa Driver muje ya kaimu gidan mun gama,ya fige mu muna dan kamshinmu har gidan Aayan dama na rigada na San gidan,Driver na parking muka ga wasu sunzo sun dauki kayanmu tare da shigar mana dashi ciki suka fito tare da cewa Oga yana ciki Ku shiga yace.
A raina nace ai ko bai ce ba zamu shiga kunji fa,muna zuwa kofa na danna Door bell ya bude muka shiga sanyi da kamshi ya ratsamu,yana jikin kofar ya bimu da kallon mamaki yanda yaga munsha kyau kamar yayan Larabawa zasu je Party musamman ni ba a magana,a ransa yace ashe dai suna da kyau,sai kuma a fili ya tabe baki yace kuje ciki mana kun zura min Ido,a hankali muka shiga tare da Zama a saman kujera,yana zuwa yace ba a Zama min a kujera,ya kalli Ma'eesha yace wannan ce kadai zata dinga Zama a kujera amma Ku banda Ku,shuru mukayi muka ji ya kuma cewa Bedroom guda daya gashi nan shi zaku dinga Zama bana so ana fitowa Palo ana takura min,bana son Surutu a gidana,akwai komai a kitchen na girki,dan ma bana so a bata min gida da hayaki ne amma da itace zan siyo muku yanda kuka saba kuyi girki dashi a Compound amma kunci Sa'a zaku iya amfani da Gas,wani dadi da murna ya kamani zan dinga dafa mana kayan dadi dama nasan gidan nan akwai harkar dadi.
Je ki duba kitchen abinda babu ki dawo ki fada min,da sauri na Mike ko kunya irin zan ga harkar dadi,ina shiga na tsaya turus ganin buhun dawa,gero,masara,wake,shinkafa yar hausa harda ta tuwo fara, sai maggi kala biyu Rak fari ajino motor da star,harda kanwa,Flower,kukar miya etc duk dai wani abu na cimar talaka futuk shine cikin kitchen,haka kayan cin abinci ma komai ya siyo na roba kar mu taba masa nasa na glass,komai irin cimar mu ta talaka ya kawo,haka fridge ba komai a ciki ko ruwan roba wai musha na pampo alhalin ko a gida pure water muke Sha duk talaucinmi.
Jiki a sanyaye na fito cike da jin haushinsa,nace Meenat kuje Bedroom,ba tare da nace komai ba na zauna a kasa tunda yace kar wacce ta hau masa Kujera,ko kallo na baiyi ba yana ta kallon News abinsa,nima ina kallo ne kawai don bana jin me suke cewa sai dai dai nake tsinta,sai satar kallonsa nake yana ta Shan juice lafiyayye da gani zaiyi dadi,yasha rabin kwalin sai naga ya ajiye glass cup din ya Mike tare da haurawa samansa,sai da na tabbatar ya shiga sannan na daga kwalin na kafa a baki na tare da shanyewa du na lashe bakina sai na fada kitchen na ebo ruwa a tap nazo na dura a cikin kwalin dai dai yanda ya bar lemonsa na maida cup din tare da dawowa kamar da na zauna na wani langabe kai irin Allah sarki din nan.
Kamar jira yake sai gashi ya fito sanye da shadda yar gaske yana sheka kamshi da alama fita zaiyi,yana zuwa sai aka yi sa'a ya bude kwalin lemon da niyyar ya tsiyaya yasha Sam bai zata nice zan yi haka ba,yaga maimakon yaga lemo sai yaga ruwa na tsiyayowa da sauri ya jefar da kwalin tare da yin gefe ya firgita ko Aljanune,tunani ya shiga sai ko ya kalli bakin kwalin ya hango jambaki na a jikin abun,nan take ya gano nice na shanye na zuba masa ruwa,ni kuwa tuni na Mike tsaye cikina ya Duri ruwa jikina ya fara bari,yasan guduwa zanyi don yaga har na tattare skert sai naga kawai yayi hanyar fita waje,nan na sauke ajiyar zuciya,ashe Duk bedrooms da kitchen tare da sauran kofofi ya kulle ta yanda bazan iya guduwa ba, tuni Idona ya kawo Ruwa nasan yau sai dai gawata,saman 3 seater ya koma ya zauna tare da nutsewa a ciki yayi dai dai cike da isa yace zo,nace ni?yace no ni,da sauri na karasa tare da durkusawa a gabansa yace bude bakinki na gani,ba shiri na bude ya kuwa ganshi wani fes dashi,ruwan dana dura a kwalin ya dauko ya fara dure min shi a baki ina kwat kwat har ya kare ,jefar da kwalin yayi tare da barin gidan gaba daya.
Yana fita nace su Meenat su fito mu shiga kitchen,kayan abincinmu na talakawa muka shirya a store sannan na ebo dawa muka gyara ta na wanke na shanya ta a kwandon ta bushe,haka masara ma,na ebi gero cup 4 na jika shi zan kai markade sabo da kokon safe,waken da zan soya mana kosai ma haka na ebo komai dai muka gyara komai abinmu,Na fito wajen masu gadi nace dan Allah a ina za a kai min nika da Markade? Wani cikinsu yace Hajiya unguwar masu kudi irin wannan sai ansha tafiya me nisa,nace ni dai a gwada min,ai ko ya gwada min,nasa Meenat ta dauki Dawa a cikin Leda Viva,nima na dauki masara duk sun kai kwano uku uku,sai geron dana jika na Koko a cikin dan botiki dan kadan Ma'eesha ta dauka,muka fito tare da tafiya me uban nisa muna tambaya har sai da muka bar layin sannan muka samu gidan wata mata me Markade wani namiji kuma da injinan nika,na bada kudi nan take akayi mana komai da komai muka dawo gidan tare da tankade garin muka adana abinmu,Nasa hijab na kara fita yan su Curry da sauran abubuwan girki na bada kudi na siyo mana harda su kayan kamshi,kayan hada lemo,da zobo da sauransu,ina dawowa a gate na bawa gate man kudin pure water nace ya siyo mana manyan Leda biyar mu dinga Shan abinmu, na dawo su Kubewa bushashiya na bawa su Meenat dama akwai turmi dan karami a kitchen din suka daka mana muka tankade da yawa duk sai da muka shirya kayan abincinmu komai na marasa karfi na shirya kitchen tsaf muka gyara shi tas,pure water kuma na shirya wasu a fridge wasu kuma a can gefe na ajiye idan mun shanye sai mu dinga zubawa ciki,a hakan ma sai murna mukeyi abinci available zamu ci mu koshi a kan lokaci ba sauran wahala da babu kaza babu kaza,shi abinci ko garau garau ne kake ci in dai ba yankewa kuma akan lokaci to Shar za a ganka.
Bare har da su shinkafa ga ta tuwo ma,mangyada manja ai shike nan mu,shi yasa dana fita ma sabo da yau jira nake Allah ya kawo Aayan da dare na nuna masa cewar ina da zuciya.
Shi ko Aayan jira yake yazo gidanmu da wuri yaga wanne girki zamu kwaba tunda yasan ko kayan miya bai ce asiyo mana ba,ba nama bare kifi bai San na siyo mana kayan miya harda naman rago na Dari uku tare da danyar Kubewa zamu zabga girki.
Meenat tace sis mu wlh ai indai zamu dinga samun wannan ai Alhmdllh a gida ina muke samun haka kullum sai dai fa muyi girki tazarce,Nace Ku canja kaya kuzo muyi sauri mu kara gyara gidan nan sabo da idan yaga dirty daya to jaraba zai mana,nan take muka kara gyara gidan ya dau kamshi,ni kuwa ina kitchen sai girki nakeyi kamshi na tashi,Magrib nayi mukayi Sallah lokacin na gama miya tuwon danyar shinkafar nake karasawa,ina gamawa mukayi wanka da Sallar Isha tare da canja kaya marasa nauyi, Ma'eesha tasha 3qtr dinta dan me kyau da nake siya musu tare da yar vest na sa mata, Meenat kuma riga da skert tasa suma English wears na gwanjo amma masu kyau kalar yan gayu, ni kuwa doguwar rigar material nasa fitted nayi kyau amma ba kwalliya a fuskata.
A katon wani tire na roba na zubo mana miyar Kubewa danya da naman mu kowa yanka uku,Sai tuwon a leda har guda hudu manya,ga pure water shima na zubo a wata roba kalar ta Almajirai duk cikin kayan da Aayan yace a ciki zamu dinga cin abinci ne.
Na dakko mana komai muka zauna tsakiyar center Carpet na tattare rigata zuwa wajen hips gaba daya cinyata a waje take fara sal da Ita mul mul da su,Meenat ta fara dariya wai Sis ke baza ki taba cin abinci a hankali ba kuma sai rufe dankwali kin wani kwaye cinya jiba ana hango short wandonki,to mu da waye a cikin gidan daga ni sai ku,zamu fara ci kenan muka ji karar bude kofa kamshinsa ne yasa muka san shine ya shigo,Sallama yayi muka amsa na fara basu abinci a baki,tsabar sa ido shine yazo ya wani baje saman 3seater yana kallonmu a nutse,yanda yaga na kwaye cinya dankwali yayi kasa duk sabo da abinci,Maeesha tace Sis ki san masa abincin mana nayi banza da ita muna cin abinmu,ni na manta ma yana wajen Sam ina ci har cinyata nake dana da duka sabo da dadin girkin,idan na ci Loma daya sai na sosa kunne sai soshe soshe nakeyi kamar me kwarkwata ko cutar karzuwa sabo da ni idan da abinci a gabana mantawa nake da uban kowa,Meenat su Kansu dariya sukeyi tace sis ya dai wai abincin nan ko yafi Nama dadi ne,Ina lashe hannu tare da tsotse yatsu na ina tande baki nace ke Wannan gonar da aka shuka kubewar nan daban ce maybe kasar kalarta daban kinji har zaki zaki haka,wajen mutumin nan zan dinga siyowa,suka sheke da dariya shi dai Na'im yana kallo ina ta side plate din,Maeesha tace Sis ki kyale kwanon haka mana nace baki San ba kyau cin abinci ba tare da an side kwano ba ai sai Abar albarkar abincin a kwanon.
Aayan yana kwance yana ta faman kallon ikon Allah cike da alajabin abin nawa,muna gama nace muje a wanke hannu Muzo asha karatu,yana zaune yaga na Mike ina uban nishi tare da jansu muka je muka wanke hannu da baki sai ko muka kwaso jakan makarantarsu muka dawo palon kusa da shi yana kwance kai ka rantse nice shugaban masu ilmin boko na duniya yanda na faffake ina bude littatafai,Aayan yana jira yaji yanda zan fara koyawa kannena karatu.
Ga mamakinsa sai yaji Meenat ta bude wani English book tace fada min words din jiya naji,Bai san sanda ya bude baki ba wanda bamu San ma yana yi ba,Na fara cewa Singular and plural,Abu me guda daya da abu me biyu,Examples like Mango-Mangoes,Orange-Oranges,Bag-Bags,Lady-Ladies ina fada ina rubutawa a littafi har na gama,Maimakon nasa Ladies sai nasa Ladys nan take Ma'eesha yar karama taci gyarana tare da kwace biro tace sau nawa za ace miki haka ake rubutawa ladies wai yau kusan wata daya kenan kullum sai kin manta,Meenat tace to Saura mu fara present tense and past tense amma yanzu a koma baya muji,mene Noun? Nace Noun? Noun... to ....Noun.. dai shi sai na fada tunani tare da kallon sama kamar a nan zan samo amsa,nace to shi dai Noun... shine dai,nan take Aayan bai San sanda ya kwashe da dariya ba sai da muka kalle shi yanda dariya ke masa mugun kyau,Meenat tace Sis what is a Noun? Shine dai me? Na kara kallon sama tare da zura biro a bakina nace shi dai Noun is a name of....of.....yawwa shi dai Noun is a Name of Yawwa uhmmm....yes Animal dabbobi irin su Damusa, Kunkuru,zaki,kuma dai shi dai Noun is a Name of place like harda yanga irin na gano gaskiya harda daga yatsa kamar malama na kwalla da karfi nace like capital city of Nageria Abuja,na kara karfin muryata nace also kasar Masar,na daga kai sama nace yes Habasha,idan muka dawo gida Nigeria zan iya ce muku Rimin Gado,Kura,Kasuwar Rimi,yan Kura and also kofar wambai market,Aayan Dariya ta mugun kamashi duk uban labarin nan wai a Noun akeyinsa.
Meenat tace yes muna jinki sis,Nace kuma dai shi Noun is a Name of person na saki murmushi irin shegiyar nan nace like ni Mufeeda,Ammah Allah yaji kanta duk da ta riga mu gidan gaskiya amma zan sa da sunanta Fatima,Abba wanda ya arce,Maeesha kema kina cikin Noun,Meenat ma ta shiga ciki,Aayan ma gashi nan a kwance,Maeesha suka sheke da dariya, nace ah to dana fadi wasu banza na waje ai gwara na gida.
Na kara daga murya kamar me koyar wa a class nace Kai Noun shege ne wato shi ya hada komai harda Things kinga Bag,pencil,biro,spoon duk suna karkashin Noun.Meenat suka dinga dariya sosai suka ce kinyi dai dai amma labarin ai yayi yawa,nace wai me yasa Noun bai hado da abinci masu dadi a ciki ba aikin banza,ai kamata yayi ace akwai su Hen,su Ram,kabewar miya,Danwake,Taliya,Apple.
Aayan yana ta boye dariyarsa,Ma'eesha tace Saura Verb, nace Verb gaskiya ita bata dadi is an action word or a doing work, ni Verb bata birgeni sam,kamar yanzu munyi aiki yawwa Cooking,jumping,running,washing,kuji wani iskanci wai harda kallo watching ace yana cikin aiki,eating ma ai ba aiki bane amma a ce harda shi ciki,haka dai suka dinga tambayata ina bada amsa amma sai nayi dogon bayani da Hausa na cinye lokaci.
Ma'eesha tace daga yau an daina hausa sis duk bayanin da zakiyi sai dai kiyi mana da turanci kaf,na zaro Ido tare da cewa dan Allah kuyi hakuri ni dai me zance,Meenat tace wlh ba hausa gobe ki shirya naga Alama indai ba haka ba baza ki iya ba.
Sabon karatu sukayi min present tense an past tense,sannan sukayi nasu na manyan kwari tare da assignment ina kallonsu,sai kuma muka koma Islamiyya,anan kuwa nasan komai Qur'ani suke kara min da wasu littafan amma duk na iya tunda na iya karanta larabci da rubutu kuma ni nafi kokari a fannin Arabic sosai ko Aayan ya sheda daga jin yanda nake karatu ina cin gyaran su Meenat.har muka gama abinmu sannan Ma'eesha ta mayar da komai Bedroom ta dawo still Aayan yana kwance abinsa yana danna waya, nace su tashi muje su kwanta bai kula mu ba muma haka,amma yayi mamakin ganin yanda muka yi girki lafiyayye haka gamu yara kuma yasan fita nayi na siyo wasu abun amma abincin ya birgeshi sabo da shi yafi son abincin zallan hausawa fiye dana turawa.
Sai da ya dade sannan muka ji karar mota tare da bude gate wato mu kadai zamu dinga kwana a gidan,munyi addua na kara yi na tofa mana baki daya muka haye saman lafiyayyen bed din da bamu taba ganin irinsa ba muka fara bacci sosai,can cikin dare wurin 12:30 naji motoci sun shigowa gidan na farka tare da mikewa na daga labile na leka ta window Aayan na hango da ledojin take away dinsa a hannu ya dawo.A zuciyata nace dama yana kwana a nan? Na tabe baki tare da komawa na kwanta,shi kuwa yana shigowa sama ya haura yaci kayan dadinsa ya fesa wanka tare da shirin bacci yayi addua ya kwanta sai bacci.
Washe gari na tashe su mukayi sallar asubah tare da azkhar sannan nayi wanka suma suka yi tare da shirin makaranta ni kuma nasa kaya Atamfa riga da skert me kyau harda shafa powder tare da lipgloss,wake na gyara da sauri na fice tun gari baiyi wani haske ba na taka har inda ake markade sabo da Blender bata yin laushi yanda ake so,dan markade kadan nayi na dawo da sauri na daura ruwan dama Koko,sai na fara soya kosai yasha kayan miya kamshi ka rantse wani nama ake soyawa,Aayan yana jin motsinmu tare da kamshi yana tunanin wai ina muke samun abun girki me kamshin dadi haka, ruwa na tafasa na dama Koko me dadi da lfy,na ebi nawa a cup ina cin kosai ina kora Koko Malam,Meenat ma suka shigo sanye da uniform dinsu na zuba musu suka ebi kosai a plate da sugar suka fito Palo suna Shan abinsu,sai ga Aayan ya fito sanye da Jallabiya fara,suka ce ina kwana ya amsa ba yabo ba fallasa da lfy Alhmdllh,Ya kalli abinda suke ta ci bilhakki da gaskiya ganin yana kallonsu Ma'eesha tace Yaya gashi in zaka ci,baki ya tabe tare da cewa ban iya ci ba,d a dadi fa,yace am Ok,Meenat a tsorace tace ka dandana,a ransa yace wannan jagwalgwalon zanci ganin bana wajen ya mikawa Ma'eeshah hannu wai ta bashi ya gwada,da Sauri ta mika masa kosai daya yaci yaji shegen dadi,dama kosai yana dadi haka? Abinda ya ayyana a ransa kenan,Meenat tace a karo? Ba tare da yace komai ba ya mika hannu a karo masa,ta dauki plate din suka koma gabansa gaba daya Yana sama suna kasa zaune,Yana Sa hannu ya dauka yaci suma suna ci suna shan kokonsu,Maeesha tace Yaya a kawo ma kokon da dadi fa,karon farko kenan da ya kalli Ma'eeshah ya gansu kyawawa gwanin sha'awa ga tsafta,yace sai dai ki bani naki nasha,ta mika masa ba kunya ya karba yana sha da kosan,dan rashin Imani bai ce tazo a kara mata wani ba dan shi sam bai iya kula da mutum ba,ba ruwansa da wani caring ko kina cikin yanayi na Kaza yace je kiyi Kaza sam bai san wannan ba,yaci ya sha abinsa ya mike bai ce ko a dawo lfy ba yana uban takama da gadara ya koma sama abinsa,a haka na fito suka bani lbr nayi mamaki da ya iya ci,na Sa Hijab na rakasu a kafa har Babban titi tare da sasu cikin Napep suka tafi schl nace idan an tashi kar su taho su jirani zanzo na daukesu a schl tunda baza su gane gidan ba.komawa nayi gida lokacin yayi shiri zai fita an kawo motoci wasu kalar,ni na manta ma ina da aure Sabo da ba abinda na fasa yi ko ina fita nake yi,shima bai ce min ina naje ba ko mene ma nayi ina ruwansa ko kallo ban isheshi ba haka ya shiga mota aka jashi nima nayi ciki tare da fara gyara gidan ko ina.
AsmaBaffa
[1/6, 11:20 PM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
31-35
Official
By
AsmaBaffa
SAMEERAN GAYA yar ALBARKA ga page naki.
HAFSAT KHAIRAN Tare da MAMAN SAMHA ina gaisuwa.
JANNAT jinjina gareki me tarin yawa.
Dan Allah masu Sharhi kuci gaba da yi ina gani,kwana biyu Net yana bani prob zaku ga reply baya zuwa da wuri ina matukar damuwa wlh,fans kun san dai AsmaBaffa ba haka take ba,ina kokarin Yiwa kowa reply sai daΓ idan ban gani ba,dan Allah ayi min uzuri ko da wata tayi magana taji ban mata reply ba to wlh ban gani ba ko matsalar networkc.sai masu yi min magana ta pc kuma indai anga ba reply da wuri to net ne kwana nan matsala yake yi,kuma ko wacce nayi reply back sai yaki Tafiya sai da kyar,dan Allah ina kara baku hakuri za a gyara kuma ayi min sharhi na ina gani Sabo da nayi typing me kyau.
Sai kuma typing error ayi hakuri dashi,sai kuma kuskure na Dan Adam dole zaku ga abinda bai muku a ciki ba,har kullum ina so kusan cewa Sako ake isarwa,idan mutum shine star bazai yuwu ace baya kuskure a rayuwa ba,dole sai yayi abubuwa shima na kuskure tunda ana so a koyi darasi da shi ne,baza ace star shi ya Zama halaye 100% ba,so ayi hakuri aci gaba da karatu da Sharhi Insha'allah Novel zai tafi dai dai.
I really love my fans wlh sosai Sabo da so nake na dage ko wacce Insha'allah masu Sharhi sai na baku page Insha'allah sai daΓ mantuwa,wadda bajintarta tayi yawa har 2 ko 3 page ma zan bata suna nan kuma ina ta ganinsu AUTA, FlOWER ma suna ciki etc Bazan fadi sauran ba yan kuri ne zasu cika min Gpπ€£.
Ko da na shiga gidan kawai aikina nayi ta faman yi sai da na gyara ko ina har Bedroom din Aayan ko ina sannan nayi mana miyar jajjage na siyo kifi na Sa mata,tayi dadi sosai,na dafa farar taliya na gama ,a gurguje nayi wanka na shirya tsaf sannan na maka Katon Hijab na tafi dakko su Ma'eeshah,ina zuwa suna fitowa da Sauri suka karaso inda nake tare da frnds dinsu wai zasu gaishe da Sis din frnd,harda gaisheni da turanci kawai na amsa tunda nima na dan iya a raina nace da kunyi hausarku Yara nafi karfi a nan wai su a dole yan private,shi kanshi me Napep yayi mamakin shegen gidan daya sauke mu,yace kamar wannan gidan ace za hau Napep ga yan mata zuka zuka haka,Me Napep tunaninsa ko yan aiki ne tunda yaga bamuyi kalar masu kudin ba,kawai sai ya fito daga Napep zai gwada sa'arsa a wajena ko zai dace da ya more ko yar masu kudi ce ai zaiyi auren jari.
Yashe baki yayi tare da cewa yan mata ku bar kudinku ai kyauta na kawoku ni,kamarki Hajiya ai kin wuce a karbi kudinki,na daure fuska tare da cewa kaga Malam karbi kudin ka ban son kinibibi ina da aure ni koma meke Ranka ka Adana kalamanka,yace yar yarinya dake yana dariya yace sake magana yan mata ido ba mudu ba ai yasan kima,tsaki Naja nace karbi da Allah kar mijina ya ganni a nan,yaki karba yana kallo na,muna haka sai ga motar su Abbi ta shugo tare da mata ciki manya biyu da yan matan nan dai abokan fada na su Uku, tare da dattijai su Abbi su biyu suma.
Cikina ne ya wani kulu kulu Sabo da tsoro nan take gumi ya keto min,na cillawa me Napep kudi Naja hannun su Meenat muka bi su ciki domin tuni sun shige da motocin su ciki,gashi basu san Code din kofar ba,nima ban sani ba Ma'eeshah ya rubutawa a paper jiya yace ta bani,dole suna jikin kofa suna jirana,a hankali na taho,suna bina da wani banzan kallo wanda saura kadan na fara Kuka,wata a Cikin manyan matan ta ja tsaki tare da cewa an kawo mana irin jaraba kuma dangin matsiyata sai abinda muka gani,Abbi yace taki yin Sauri ma kamar gidan ubanta,Yan mata a ciki daya tace zaku gaji da kallo indai wannan Villager din ce bata da kunya wlh zaku ce ni na fada muku,Dayan Babban yace wa zata Yiwa ai ko masa a saketa dan ubanta,cikin manyan matan wacce batayi magana ba tace dallah ki Sauri ki bude mana ko gidan uwarki ne wannan dole a maida ita Family house ko dan ta koyi Ladabi,nan take Abbi yace a'a ba yanzu ba tukun na gama planning idan lokaci yayi zakuji.
Ni kuma jin matar nan tace ba gidan Uwata bane jin za a zagi Ammah ta yasa zuciya tazo min wuya,haushi ya kamani gani dama da saurin fushi ni ban fiye jure a fada min magana a gabana kuma ace na danne ba zai wahala,ana fada min nake tunzura nima sai idona ya rufe ko za a kasheni sai na rama.
Ina zuwa gabansu na bata rai nasa hannu zan bude matar nan ta dungure min kai dan ubanki baza kiyi Sauri ba,a fusace na juyo tare da maka mata uwar harara ba ruwana ko uwar Aayance ni ban sani ba kawai kasa dannewa nayi,aiko yan matan nan da kadan suke jira suka fara salati suna zuga tare da cewa kun gani ko ai mun fada muku to wlh nan gaba ko marinta kukayi sai ta rama,Abbi yace Dan ban tan ubanki baza ki bude ba,aiko na kara harzuka kawai na fasa budewa Naja hannun su Meenat na juya inda na fito ina Tafiya a hankali cike da gadara ta nima,maganar duniya sukayi ko ehem basu ji muryata ba,ina ji suna lalalala lallai dole a dauki mataki ba karamar yar iska bace wannan magana ma tafi karfin tayi,shima dayan yace wannan tantagararriyar yar iskar tsagera ce,bata da kunya bata da mutunci kamar mu ta iya yi mana haka,ka duba Nafisa da Bilkisu babu abinda ba a musu ba Amma yaran nan basa iya daga mana ko yatsa,ka duba Shema'u zagi duka duk taci a gidan nan Amma ko daga ido bata taba yi mana ba sai wannan yar matsiyata,talakawa ma sauran kuwa daya aura daya ke yayan masu kudi ne dama su basu gaji tsiya ba,Abbi yace bar shegiya zata shigo gidan ne sai tafi kowa wahala da kanta zata bar gidan,nan take suka kira Aayan yayi Sauri yazo,minti 10 sai gashi a mota daya shike Driving,yana shigowa ya hango mu can gefe a zaune,gashi dama kuma Business din namu yace a gaban danginsa a nuna soyayya,ni kuwa na manta ma tunda ban gani a kasa ba,ba a biyani kudin ba,banci na ta da kai ba,nan take ya canja fuska ya koma nishadi da farin ciki ko kulasu baiyi ba sai wajena da ya taho yana wani murmushi muna hada ido sai ya maka min harara,yana zuwa kusa dani ji nayi kawai ya riko hannuna,na fisge hannuna yace film za ayi gasu nan zasu gane, nace can da matsalarku abinda ba sanin darajar business kayi ba ina ruwana ni, zan mareki kin san Halina wlh idan kika bari suka gane sai na yagalgalaki na koreki kuma,ni kuwa nasan zai iya mun samu rufin asiri ai ba shiri na mike,ina murmushin yake ya dauki Ma'eeshah a kafadarsa kamar yarsa yana mata wasa wai dan ace ana soyewa da mata kannenta ma ai kamar kannensa,Meenat tace a ranta kaga makirin Namiji a fili kuwa ya jawota kusa dashi itama ni kuma hannuna na cikin nasa,Maeesha an samu sake har wasa take da gashinsa a ransa yana ta jin haushinta tana lalata masa gashinsa me kyau yasha gyara.
Muna zuwa yace ur welcome, Abbi karami barka da yini,Aunty ya kuka tsaya a nan,My life bude musu mana,Abbi ya fara masifa wannan har kake kira da ur life yarinyar da ta zage mu taci mana mutunci yar Iska,Aayan ya bata rai a ransa fa Amma don yasan Halina ba tin yau ba bana iya hakura idan anmin abu,yasan tabbas zan rama indai sun min tunda yasan halin danginsa,a fili yace ko baki ganesu bane Dear,nayi shuru ya mintsini hannuna na saki murmushi tare da cewa ban ganesu ba naga suna fada ne tunanina kar suzo har gidan mijina suyi min sata,aiko nan take suka yo kaina ubanki zamu sata,yan matan nan sunfi kowa,Abbi yace Kafura da fuska kamar ta mage,na faki ido na Galla masa harara,yace wlh wlh sai nayi maganinki,na kara fakar ido na Galla masa harara tare da juya idona sannan na murguda baki,karaf a idon Aayan,a gabansu bai nuna ya gani ba,sai da muka shiga ciki na zame hannuna Meenat ta rada min ki kirashi da Babyna,nan nace Babyna kawo min Ma'eeshah taje ta huta nasan kasha nauyi,ya miko min ita tare da zama kusa da su Abbi,ni kuwa ko ta kansu banbi ba nayi Bedroom abina har suka gama fada da jaraba wa Aayan ina jinsu wai ya auro gadon rashin mutunci bani da tarbiya,shi kuma yana basu hakuri suka dai gama mitarsu suka bar gidan cikin bacin rai dama wai a haka ganin Amarya suka zo za ayi gulma.
Suna Tafiya ya haura Samansa yayi wanka da komai tare da cin take Away dinsa har Bedroom dinmu ya leko yace zo ke,lokacin wayata kawai nake dannawa ina game,su Meenat sun Tafi Islamiyya.
Na mike na bi bayansa har palo,yana zaune na durkusa a gabansa ya dauki dogon lokaci sannan yace ke baki da kunya ko? Ana tausayinki ba kya jin tausayin kanki,baki na turo gaba,yace ko nima zagina zakiyi,baki da hankali ai ko ba komai sun girmeki,kuma kina Matata ko darajata ai baza ki raina min dangi ba,nan gaba ke zaki sha wahala awajensu ni ba ruwana iya kaci idan sunce na rabu dake nayi musu abinda suka ce,kamar Abbi zaki kalla ki harara Kanin mahaifina ne fa kamar mahaifina ne.
Bazan hanaki yi ba tunda ke zasuyi ma ba ni ba,kinga ba ruwana,baki na kara turowa Hawaye yana zuraro min sannan nace haka kawai shike nan ni bani da yanci,ni mene baka Yiwa Kannena ba ashe da dadi kenan yanzu nayiwa naka kaji Haushi,sannan su zagar min iyaye sai nayi shuru Sabo da bani da zuciya ina...... wlh zuciyata bata mutu ba,babu wanda zai zagar min Uwa na kyaleshi ko shi waye,kai ko ni wlh Bazan dauki zagi da Duka ba sam bazai yuwu ba,bari kaji ko kai da bana so aka zaga Bazan kyale ba tunda yanzu kaine kake ciyar damu ko dan darajar wannan idan naga me cima mutunci sai inda karfina ya kare,sannan da kake cewa ana tausaya mana ai dai banzo gidanku nace ka taimakamin da sisinka ba bare kace taimako nazo nema,hasalima ni kake zalinta,tunda duk Aure ai aure ne ba banbanci,da kudinka Allah ya hore ma ka hana iyalinka sai daΓ ka bawa na waje ina zaka ci gaba ai baza suyi albarka ba kuma baza kaga dai dai a komai naka ba,tunda kana da Halin siya min Nama ka makale kudinka,ko kwai dan kwai ma babu,bare su madara me kwakwa ba daya bare kanwar biyu,sabo da son kudinka ko tsire baka siyo ba dan ka kyautatawa iyalinka,sai kudina na ma da suke hannunka tunda har yau Banga an fara bani kudin auren Business ba,ai in kana so nayiwa danginka biyayya to ka tabbatar sai ka karbi aurenka kace ba na kasuwanci bane tunda kai kace ba aure bane to mene hadina da wasu danginka da zan girmamasu,dadinka nake ji da zan mutunta su? kuma ko ba komai suma ai basu mutuntamu ba ko mu ba mutane bane bamu da daraja sai ku Sabo da kuna da kudi,Deal ne tsakaninmu zancen mutunci bai taso ba,a fara biyana kudi ayi a gama auren,idan kuma ka soke kasuwanci ka zabi daya ciki sai ka min komai da Allah yace miji ya sauke a kan matarsa nima zan sauke nawa,amma sai kazo kwata kwata ana abu ba akan dokar Allah ba mun tsara tamu dokar kace zaka zo da wani zance wlh kama zo da da bidi'a ....kau.....nake jin maruka ta ko ina a fuskata inba a lokacin sai da na dena gani kaf bana jin magana, yayi niyyar ya dinga ball dani kawai ya kyaleni da iya marukan da ban san adadinsu ba,na mike kuwa ko Hawaye babu na karkade jikina irin na gama kangarewa din nan nace Bazan fasa fada ba idan kana so na bisu wlh sai daΓ ka soke kasuwanci muddin kasuwanci za ayi wlh basu Isa ba ko su waye a danginka in dai sun min sai na take su nima,ni so nake ma ka kaini can Sabo da mufi goge raini,,na tattare skert zan Arce ya biyoni na kwalla kara nayi saman Bene da gudu,ya biyo ni a ransa yace yau sai ya hallaka yarin nan yana magana tana yi,ya auri mata manya manya ma magana basa iya yi masa sai wannan yarinyar, Ina gudu ina hakki nace dan Allah kayi hakuri karya nakeyi Bazan iya ba zan bisu sau da kafa,wayar chager naga ya fisgo ai na koma kasa da gudu garin gudu na fadi yazo kuwa cike da bala'i ya juya daukan wayarsa data fadi na mike idan guduwa zanyi kamani zaiyi,kawai ya sunkuya zai dauki waya na Arce ,nasan ina tsayawa zai ci Ubana, ina shiga su Meenat suka firgita suma sun dauka wani abu ne, jikin kofar yazo yace zaki fito ne,nace ni dai na fada ko gobe suka zo sai nayi musu,kwanan nan zan fara taka kowa, zaki fito ne sai na yankaki,nace ae idan anyi zuciya a biyani kudina,yace ko ina bayarwa ma Bazan taba baki ba,da na baki gwara na zubar kuma ko ina Tafiya ina taka kudi Bazan baki ba,shuru nayi masa Sabo da ina tsoro kar ko yar dubu daya ya hanani da me zanyi Cefane ko kudin Napep na schl din su Meenat.
Meenat ta kalli fuskata tare da cewa Sis dama ke ai akwai jure duka, shawara kawai mu daina fita ko palo sai in baya nan,Nace baki da hankali ai gwara ana damawa damu idan ya gano tsoronsa muke ji raina mana hankali zaiyi,ni yanzu da kike gani na Salo Salo zan dinga rikida ina canjawa tunda naga ba kudin nan za a samu ba bare idan na samu nace ya sakeni kinga gwara kawai mu samu na lallabashi mu samu kudin siyen kayan daukan wanka muci mu sha mu baza gayu,idan ya maidamu Family house a haka mun gama yawo kalli bamu da kayan sawa na kirki,
Meenat tace ni tsoro nake ji Sis bazan iya ko daga musu yatsa ba wannan uban kudi da suke dashi haka, tsoro ma nake ji kar a sakeki,nace ke ki daina min fatan saki yanzu gidan nan shine rufin asirinmu,ni ina son aurena wlh rike abina zanyi da daraja,gwara kawai nayi dan samun lada tunda kudin nan naga Alama ba sune komai ba, Meenat ta dinga dariya tace kowa ya tuba dan wuya ba lada Sis.
Ke na hakura da kudin na koma kama mutuncina ni kam harkar auren nan zan dawo na gaskiya,Idan ma ya sakeni Allah yagani,Meenat tace Good yanzu za a fara zaman aure kenan? Nace ae,tace to ai kin batawa mijinki rai sai ki fara zuwa ki bashi hakuri,haka ne miko min Katon hijab din can na Ammah nafi daraja a idonsa,hhhh Meenat tace yo wacce daraja zakiyi kinje wajen miji da Hijab ai kamata yayi ki dau wankan sugar,baki da hankali Meenat cewa zaiyi sonsa nake,ni kuwa ba sonsa nake ba bautar aure zanyi,so kike ya rainani ba class yana kallon tsaraici na,kin manta jiya da kika bude cinya kina lashe lashe a gabansa fa,to ai ni mantawa nayi dashi kuma in Allah ya yarda daga yau na koma yar gayu nima,ko kayan dadi ne sai nayi yanga zanci,kuma bazai kara ganin jiki na ba,Meenat ma ba hankali tace kin san kuwa Maza ba kunya garesu ba zaneki zaiyi kuma ta kalle miki jiki,nima nace ai yanzu zan fara bawa jikina tsaro.
Sadaf sadaf na fito da shirgegen Hijab dina,ba kowa a palo na tafi ina taku na nutsuwa irin nayi hankali fa,baya palo nayi ta Maza na haura samansa,har hadadden Bedroom dinsa na kwankwasa tare da Sallama na leka kaina ciki,na hango abinci lafiyayye da abubuwan dadi iri iri a gefensa yana ci yana aiki a system,Na murda handle na shiga,da mamaki ya kalleni yanda yasan tsorona na iya fitowa yanzu duk rashin kunyar da na masa,Har gabansa naje na durkusa tare da cewa sannu Aayan dan ni ba ruwana da wani yaya ko waye waye kawai Aayan tunda ba Masoya bane akan me zan boye suna.nace dan Allah kayi hakuri kaji wlh wasa nakeyi zanyi musu biyayya Bazan kara ba ni dai mu zauna lfy,da mamaki naji yace kin kyautawa kanki idan ma baki ba ke zaki sha wahala,ki nutsu ki san me kike abinda Family dinmu sukeyi bana wasa bane,har yau baki san dalilin auren Ki da na yi ba,kiyi abinda nace zan biyaki kudinki ko wani kike so ki fada min muna gamawa sai na warware aurenmu na aura miki wancan a ranar tare da kudade,nace to Alhmdllh ai ta kwana gidan sauki,amma da ni nufina zanyi bautar aurena tsakani da Allah,no..no..no Need kawai kowa yayi rayuwarsa cewar Aayan,nifa ba wai nufina aure kayi min wani abu na mata da miji ba ai na rigada nasan baza ka iya Yin komai ba,baka da lfy, a firgice naga ya dago tare da cewa a ina kika sani?nace ranar dana fara ganinka tare da Abbi time din da ka fadi nazo taimako ka min duka duk naji me kuke cewa,oh shine kika zo ki fada min kenan? karki jawo na goge miki hadda yanzu ki gani zan iya ko Bazan iya ba,nace ni ba haka nake nufi ba ina magana hankalina baya jikina sam yana ledar dana ga kayan tande tande a ciki har dogon wuya nakeyi haka nake ni Allah ya zuba min kwadayi a rayuwata tun ina karama Ammah bata yawo dani Sabo da babu dama naga me talla sai na mika hannu a bani,ko kuma nayi ta kuka sai an siya min,ko gidan biki idan akaje dani to fa kowa sai yasan kwadayi na,Ammah watarana sai dai ta goyani a baya tasa Zani ta daure ni har hannaye tam,sai dai nayi ta kuka a baya ina kallon masu tallan kayan ciye ciye.
Yana satar kallona yanda nake kallon abin ledar sai yace bari ya gwadani,Muryarsa naji yace ko zaki ci ne? Da Sauri nace a'a na gode ni bama na ci,murmushi yayi kana yace to shike nan dama na koshi zubarwa zanyi dasu,da Sauri nace kawo na zubar ma,a'a kyale idan zan fita zan zubar da kaina,Nace da dai ka kawo na hutar da kai kamarka dan gayu ka tsaya zubar da shara ai bai dace ba wannan sai irinmu,gaskiya ne dauki to kije dustbin kasa ki zubar,da Sauri na dauka tare da cewa sai da safe,yana ta jinjina kwadayi na don yasan ba zubarwa zanyi ba,kuma dama shi din yaga damar bani ne ganin yanda nake shi yasa yace na kallon abun shine tace a zubar,ni kuma tunanina wayo nayi masa na fita ina dariyar mugunta irin na cuceshi.
Ina shiga Bedroom na bawa su Meenat labari suka ce lallai Sister kin iya wayo,muka sha ice cream,Nama,lemo da wani chips yasha hadi.
Tun daga wannan Rana bamu kara ganin Aayan ba ko kamshinsa har muka kwashe sati biyu mu kadai muke rayuwa a gidan kuma sisi bai bar mana ba haka ya tafi,a bakin masu gadi naji wai yana Abuja,nima ban damu ba sam tunda Allah yasa ina dan boye kudi a hannuna kuma na saba da irin wannan ni dama tun ina yarinya a wahala na taso da tunanin ya zamu kare.
Sati daya shuru,biyu shuru,kudina duk sun kare gobe ma su Meenat basu da na zuwa schl nayi Cefane dana hannuna,muna zaune a palo na gama gyarawa Ma'eeshah kai na fara Yiwa Meenat kitso itama, door Bell muka ji, nace Ma'eesha je ki bude ta mike da gudu tare da bude kofar gani mukayi an mako kofar tare da ture Ma'eesha ta fadi gefe bakinta ya fashe,ba kowa bane face yan matan nan na gidan su Aayan su Uku har yau ban san sunansu ba, da sauri na mike tare da daukan Ma'eeshah ina mata sannu tare da goge mata baki da tissue,saman kujera na kwantar da ita ko kallonsu banyi ba naci gaba da Yiwa Meenat kitso,muna kallonsu suna ta jan tsaki ana yanga tare da taku dai dai muna kallo suka haura saman Aayan,da Sauri na mike tare da bin bayansu suna yanga na sha gabansu kafin su karasa bedroom din na riga su shiga ciki tare da zaro key din dake jikin kofar na rufe kofar da key na zare key din zan bar wajen suka tareni a palo dole sai na basu key dakin dan uwansu ne dole suyi abinda suka ga dama.
Kallonsu nayi sama da kasa sannan nace Bazan baku ba,a saman nan 2 palo ne ga Bedrooms har Uku kasa ma haka ku shiga duk inda kuka ga dama Amma banda dakin mijina.
Bazai yuwu ku dauki abu ya dawo yaga babu ba ni zai tambaya,hakki nane kula da kayan me gida tare da dukiyarsa,sannan dakin nan sirrinmu ne na ma'aurata bazai yuwu dan kuna danginsa ku shigar mana dakin bacci ba salon a ga gadon kwananmu, kaina sukayo gaba daya zasu dakeni na zame tare da guduwa muka shige Bedroom muka danna key suna nan tsaye cike da mamakin kalamai na tare da rashin kunya ta Amma ba komai zasu gyara ni Allah kawo ni Family house.
Nan take suka kira Aayan wai sunzo na zagi iyayensu,Yace su jirashi gashi nan ya dawo daga Abuja yanzu flight nasa ya sauka yama kusa da gida, 15 mnt muka ji motoci lokacin na fito daga wanka daure da towel na Sa Katon Hijab dina har kasa na fito don tunanina matan nan sun tafi sai na gansu a palo suna ta faman kallon kida a TV, dariya suka kwashe min da ita tare da cewa kaga yar kauye wai miji ya dawo Amma jibeta yanda ta Fito suna ta faman yi,ni dai ban kulasu ba na bude kofar da naji kara,wow yanda ya wani mugun kyau ba a cewa komai kamshinsa na tashi,Kallonsa na tsaya yi sai da yace Madam ya akayi ne yana murmushi ganin idon danginsa a wajen Amma nasan da basa nan ko kallona bazai yi ba,sai kallonmu sukeyi ganin idonsu yace ko Hug babu ya miko hannu zai rungumeni da Sauri Naja baya tare da cewa nayi fushi ai ka bata min,nan kuwa kawai ban so ya taba min jiki a wani auren business,Baki ya tabe sannan yace ni ko?yanda ya dage girar ya masa kyau,muryarsu muka ji sunce ur wlcm ya Aayan, tnx kawai yace musu yayi sama abinsa na dauki jakar nabi bayansa sama,su kuma suna ta tabe baki,ni na mika masa key ya bude dakin,Yana shiga Bedroom na ajiye masa jakar zan juyo naji yace me ya hada ku? Bakya jin magana wato ke ko? Duk abinda zakuyi karki sake kuyi min kokawa a gida tunda nasan kun saba,nace ni hauka nake na hada jiki dasu ai yanzu na girma Antynsu ce ni ai yanzu,zuwa sukayi tare da make min Ma'eesha harda fasa mata baki daga ta bude musu kofa,suka shigo har sama zasu shigar ma daki ni kuma naga bai dace ba ai nice matar gidan in banda an raina ni taya za a wuce dakin mijin mace kawai wai zasu dauki abu shine na kulle kofar na fada musu bai dace ba,ko ba komai idan wani abu ya bata ai ni za ace,Murmushi ya saki tare da cewa ashe kina da hankali,ina dashi mana ai kaine dan baka sanni ba kake tuna nin yarinya ce ni,ko magana bai kara yi ba ya wani shige toilet abinsa nima nayi waje,suna jiransa ya fito ya dauki mataki a kaina,amma shuru yama manta dasu gaba daya yana bacci abinsa.
Suna komawa gida suka fadi karya da gaskiya wurin kakarsu Hajja nan take tayi masa waya lallai ya dawo damu Family House a yau ba sai gobe ba.
Kawai ji mukayi yace mu hado kayanmu Driver zai maida mu can gidansu zamu koma da zama, haka muka shirya har kuka nayi a boye dan nasan shike nan mu kuma,Har part din Aayan na gidan Driver ya kaimu,dama na taba zuwa sau daya lokacin dana kai masa takarda ya nemo min Yarima abokinsa akan Aikin Ammah,part din ya tsaru harda na masifa,sama da kasa kasa 2bedroom da palo sama ma haka sai kitchen da store ya hadu iya karshe don yafi gidan da muka bari kyau da komai a kasa still muka zabi daki daya abinmu mu Uku,na duba kitchen da store wayam ba komai sai Indomie,kayan tea dana Coffee sai kayan sha dana gwangwani shirye cikin Fridge.
Yanzu za a fara rayuwar fa.
AsmaBaffa
[1/8, 1:24 PM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
36-40
Official
By AsmaBaffa
ZAINAB ATIKU SALAMA and MRS Hamza wannan page din sadaukarwa ce gareku.
Jinjina gareku
HEENDU
RAMCY MAKE UP
MOMMYN ZAHRA
HAJIYA ABOU
AUNTY SUMEE
HUMAIRA
ZULAIHAT
SAFEEYA AHMAD
Ina muku fatan Alkhairi tare da godiya da Sharhi.
Masu Sharhi na ko wanne Gp da wanda kuka min magana ta pc ina gani kuma zaku ganni Online wlh Simcard dina ne yake da matsala sai kun min Uzuri kafin na gyara,sako yana shigowa ina gani Amma ni Idan nayi reply baza su zo da wuri ba,kuyi min Sharhi ina gani kuma zan bawa ko wacce amsa Fatana kuyi min Afwa da Uzuri.
Kamar an sanar a gidan Radio haka muka dinga ganin yan gidan suna shigowa mata da Maza wasu na taba ganin su wasu kuma ban sansu ba,Kowa da kallon wulakancin da suke mana,ni kuwa ko magana banyi ba ko ina wuni bance da kowa ba nima kuma na cewa su Meenat karsu kula kowa,kaf yan gidan nan sai da suka sheda bani da mutunci bare kunya Sabo da zaman kawai da nayi a kujera ya isheka amsa, manyan ne kawai suke min kallon Banza ina kyalesu Amma indai mutum matashi ne ko budurwa yaro ko yarinya indai suka min sai na mayar musu da matartani ina daga zaune abina nima kuma basu Isa na gaishesu ba bare su Sa rai da mutunci na shigo.
Wasu manyan samari ne su Uku za suyi basu kai Aayan shekaru ba sunji labari ance musu Amaryar Aayan kyakyawace ta karshen gaske sai dai bata da kunya ko kadan,gata kuma kalar kauye ce duk iyayin Aayan ya kare a yarinya karama kamata kuma ba yar gayu ba,da sallama suka shigo bayan Sallar Isha Sabo da su Maza ne kuma suna da dan hankali,kallo daya na musu na dauke kai tare da amsawa a hankali,Ganin basuyi min kallon Banza ba yasa na saki fuska tare da cewa ina wuninku,suka ce lfy sannu Amarya ya gajiya nace Alhmdllh babu wanda ya kara magana,Sai kare min kallo sukeyi musamman wani a cikinsu kallo kamar maye hakan ma da Hijab dina,Sai ko naji yace Amarya ya kamata a mana girki muci mu ji,nace sai dai ku shiga kitchen da kanku ni yanzu sai na huta nasha gajiyar hanya daga wancan gidan zuwa wannan na jigata a Cikin mota Driver ya jijjigani da yawa a hanya na fada ina yatsina,mamaki ya kashe su abinda sun san gidan ba wani nisa da wannan unguwar Amma wannan yar rainin hankali ce wai mu shiga kitchen ma,
tasan ko mu su waye,kaji yar talakawa cewar daya a cikinsu ya fada a hankali bai san naji ba,daya kuma yace min kannen Aayan ne mu ni sunana Khaleel,ga Ameer sai wannan Mujaheed, nace good bari na shiga daga ciki,wanda ke yawan kallo na wato Ameer kenan yace a haba ko hira ba ayi ba,zama nayi kawai nayi shuru suma suna zaune sun dade sosai har wurin 8:30pm
Sai ga Aayan ya shigo rai a bace kamar zai daki mutane kadan yake jira,suna ganinsa suka min sallama suka fita,ni kuma na kalleshi yanda ya wuce da Sauri yana bin steps,Saman bed ya fada tare da kwantawa ruf da ciki ko me yake tunani oho ko wani abu akayi masa ban sani ba ni dai,nasan dai bazai wuce matsalar yan gidansu bace ni kuma ban san mene dalili ba bare nayi wani abu a kai,shi baya kulani bare nasan matsalarsu,ban ma san ko tarihin gidansu ba sai wanda na tsinta ranar ganina dasu na farko sai kuma abinda na fara gani yanzu a gidan kamar dai shi Aayan kadai shi suke warewa basa so Amma dai ban san komai ba,duk da haka sai naji tausayinsa,naji ba dadi me ciyar da kai ace yana cikin wani Hali dole ai kaji ba dadi sai kawai na wuce kitchen,Sharp sharp na dafa Indomie da kwai kar ma yazo yasa a kwashe su ya kawo mana su garin danwake shi yasa nace bari muci rabonmu,na bawa su Meenat na zuba wata a plate na nufi dakinsa can sama a nan na sha kallon haduwa.
Saman Bed na hangoshi a kwance ban san me yake yi ba bacci ko tunani,Aayan...Aayan na fada a hankali,a hankali ya bude idonsa tare da cewa Lfy? Abinci idan zakaci Indomie naga ka dawo daga Abuja baka ci komai ba,ko kaci? Kansa ya dago a hankali tare da kallo na ya dauke kai yace ni bana cin Indomie yanda ya fada kamar dan yaron goye a shagwabe,nace to me kake ci? Ai nasan baza ki dafa min ba bakya jin magana,fada zan dafa ma ai nayi hankali na daina, yaushe kikayi hankalin? Na daga kai ina tunani sannan nace an dade fa tun shekaran jiya, murmushin da bai shirya ba yayi kana yace Kosai nake so da kunun gyada sai danwake,nace to ai nan babu kayan yi a wancan gidan ne akwai,Waya naga ya dauka nan take naji yace a kwaso kayan dake kitchen da store na abinci a kawo masa part dinsa,wani bakin ciki ya dirar min shike nan mu baza muci abincin zamani ba,kamar yasan me nace sai naji yace shi kuka saba ci ai a gidanku idan na baku na yan gayu baza ku iya ci ba,nace mu dai zamu iya dan Allah,yace to ba yanzu ba sai watarana idan naga dama, cike da takaici nace shike nan ai,su Meenat basu da kudin Napep na zuwa schl,sannan nima dan Allah ka sani a schl,budar bakinsa sai yace ni bani da time idan kina da wani zan baki kudi ki zabi schl me araha private ya kaiki zan biya ni Bazan iya biya miki private me tsada ba,sabo da na raina basirarki, nace wai mene amfanin kudinka? Kallona yayi tare da Sa Headphone a kunnensa irin na takura masa haka na fita na kyaleshi cike da tunanin to wai me yasa ya aureni yana kallo ko kayan sawar kirki bamu da Amma ko Ya siya mana wasu to bai bamu abincin kirki ba ma sai wasu kayan sawa kawai dai raini ne ya jawo mana a danginsa.
Ina zaune a palo sai gashi an kawo komai na girkinmu irin na can gidan su dawa gero masara etc,Kitchen na shiga na fara shirin hada gyada da danyar shinkafa tare da lemon tsami na kunun gyada,ina cikin aikina sai ga samarin nan Ameer me kallon tsiya,khaleel da Mujaheed har kitchen suka ce Amarya girki ake shirya mana nasan ganin kwakwaf suka zo kuma sun gani su masara dasu geron,dan masifa suka ki fita daga kitchen din sai suka ce wai sai sun taya ni,nace a'a bana so kannena zasu tayani,sai ga Meenat ta shigo kitchen cikin English wears riga da skert tayi kyau Sabo da wanka tayi tare da fesa kwalliyarta da ta saba,aiko suka bi ta da kallo sunga me kyau da diri,ni kuwa a hijab nake baza su gane komai ba sai fuskata da take da tsananin kyau,Meenat tace Sis kawo na hada waken muna ta aikinmu tare suna kallo don zama sukayi a kitchen din wai sai an fara girkin sunci sunji,Ina tsoron tambayarsu gidan da ake markade na hakura mukayi a blender sai suka ga kosai mukeyi da kunun gyada,basa cin kosai su Amma suna shan kunun gyada,Aayan ne ya fito daga dakinsa Ya taho kitchen da niyyar daukan ruwa abin ya daure masa kai ganinmu gaba daya da rida ridan kannensa a kitchen muna yar hira jefi jefi sai tambaye tambaye suke mana akan girkin nan,ina tunanin zanga ya bata rai ko yaji haushinsu ko Ya musu magana su fita Maza bai dace su dinga shigewa mace me aure ba Amma sai naga ko a jikinsa ruwansa ya dauka tare da ficewa.
Muna gamawa naga sun zaro cups zasu fara eba,nace ku tsaya mijina fa? nasa ne dole sai na fara ebar masa,Ameer yayi murmushi tare da cewa Amarya ai ko nasan ne muna da yancin shigowa mu eba ko shi bai Isa yace kar mu eba ba,Kallonsa nayi nace to ni na Isa dan shi yasa ni nayi masa sai na ebar masa,Na gano ba so suke su sha ba takura min suka zo yi don kamar ma turo su akayi su Sa min ido.
Sai da na dauki wani jug me kamar flask na zuba ma Aayan, meenat bata ce mana komai Sabo da na hanasu magana akan dangin Aayan kosanta take soyawa,naje na ebarwa Aayan na ebar mana namu tare da kai mana Bedroom,na dawo lokacin Meenat ta gama soya kosai muka gyara kitchen sannan nace to zaku iya eba dan bakar jaraba suna palo sai da suka shigo kowa ya eba a cup suna sha duk wanda nayi suka shanye ba ruwansu da tambaya,Khaleel ma da yafi su rashin kunya Na Aayan yazo wai zai kara a ciki ya masa dadi, nan take na dauke komai tare da jerawa a wani tire me kyau sannan nace bazai yuwu ba kunsha rabonku nayi gaba na Barsu a palon,sama Na haura tare da knocking sannan na shiga yana zaune saman Sallaya yana addua na ajiye masa zan fita naji yace wait,ina tsaye ina jiransa ya gama tare da shafawa sannan naji muryarsa yace Zauna,can gefe na durkusa yace me suka ce miki su Ameer? Na bashi labari har abinda nace musu,yace to daga yau ko me suka ce ki musu kiyi musu ko nawa ne ki basu,nace ni Allah Bazan basu ba,nasha wahala kace na basu,to ba nawa bane nace ki basu,to me ya hanasu suyi auren su ko su tafi wajen iyayensu ni na haifesu da zan dinga wahala suna raina min Hankali,ina matarka tunda kannenka ne ai kamata yayi su dinga girmamani kuma sai suzo kitchen su tsaya min a kai ai duk kai kake basu kofa,kamar wanda ke jin tsoronsu ni ban gane maka ba,kace rannan na dinga ramawa yanzu kace na daina na bari kenan su takani ko? Shuru yayi bai ce komai ba,sai can yace nima kinga ban san me ke damuna ba ths month ina jin bani da lfy ni ban san ma meke damuna ba gaba daya,ina ke maka ciwo? Yace babu a jikina nake jin kawai da matsala bani da lfy ban san ya zan iya fada miki ba,tunanina mutuwa zaiyi sai na fara hawaye nace ni dai karka mutu dan Allah irin Ammah yanzu wa zai bamu abinci gashi muna ci muna koshi,kallona yayi da mamaki shi da yake bamu abincin talakawa Amma har dadi nake ji a haka ina fata kar ya mutu Sabo da wannan.
Miko min abincin,mika masa nayi sannan na zuba masa da Sauri wai dan kar ciwo ya kamashi ya mutu,ya karba a hankali yana cije lips ni tunanina ko jikin ne yake jin bazai iya karba ba,sai nace tsaya tsaya na karbi cup din nasa spoon a ciki ina juya sugar din sannan na rike masa a hannuna nace to bari na rike ma a haka kai kuma sai ka dinga sha ko na baka yanda nake wa su Meenat tunda baka da lfy? Banza ya min tare da bata rai yana ta fushi kuma yanzu kamar yaron da aka Zane,Sai ji nayi yace rike abinki ki sha,na fasa, yi hakuri gashi rike abinka Allah Sarki sha abinka kaji,ni kar na baka? Yace ae bana son naki, nace to gashi nan ni na tafi ma,na mike tare da bar masa dakinsa,na rigada na saba da Yiwa su Ma'eesha irin abun Yara idan zan basu abinci ko ina basu sai na dinga ta lallabasu shi yasa,ko ina basu ta dole.
10pm muna daki muna karatunmu ya shigo Bedroom dinmu tare da cewa zo,Maeesha tace Hi Uncle,murmushi ya mata tare da daga mata hannu,Meenat ma ta gaisheshi ya amsa da sakin fuska kadan,Hijab dina na Sa tare da binsa a baya har Bedroom dinsa yana Saman Bed ina kasa a tsugune yana ta faman cika yana batsewa ga jarabar takama,yace gobe ki shirya 8am kuje ku gaisar da Hajja kakarmu ko me zata ce karki mayar mata da martani kiyi biyayya,nace to Insha'allah,yace muje yanzu wajen Abbana,nace au kana da Baba mahaifi? Yace of Course ai ni dan gata ne Umarninsa nake bi,murmushi nayi nace kuna kama? Yace mene kika tambaya? Idan kuna kama to nasan Babanka ma me kyau ne ko Ummanka ka biyo?ke dadina dake shirme,Ummanka ta rasu ita? Ya daga kai tare da cewa kuma nafi son Abbana ba tun farko,Nace tab ni kuwa nafi son Ammah,Abbanka yana Sonka kenan da yawa gani nayi yana ta farin ciki kawai akan nayi zancen Abbansa lallai yana sonshi,fuskarsa na leka nace Dan Abba zan dinga ce ma yanzu,muje na ganshi ma zan dinga kai masa abinci,yace ai ba komai yake iya ci ba,bashi da lfy ya fada kwalla kamar zata zubo masa,nace eyya ai Insha'allah zai warke ne,lets go kawai yace min,nabi bayansa falau falau da hijab muna ta sheka uban tafiya yana gaba ina bayansa har muka je wani building a Cikin gidan katafaren me kyau,ciki muka shiga kafin ma mu Isa inda zamu hau steps duniya ce guda ko ina kuma Securities ne masu tsaron Daddyn Aayan, sannan muka haura sama can wani Bedroom shima nan duk sune suke tsaro har cikin dakin,saman Bed na hango shi dattijo kyakyawa irin Aayan suna kama sosai sai daΓ Aayan ya fishi farar fata,sallama mukayi masa da mamakina naji ya amsa yana murmushi tare da cewa My Son kazo ke nan,Aayan ya karasa jikin Bed din tare da rike hannunsa yace Daddy ya jikin? Alhmdllh Son yanda kasan jikin kullum haka yake ina so na taka kamar kowa Amma bazai yuwu ba,kana gani komai sai dai ayi min haka nake ba inda ke motsi a jikina sai baki na,addua kawai itace Mafita tunda ba inda ba aje ba ciwo yaki ci yaki cinyewa,to hakanma mun godewa Allah.
Ina mamaki yanda yake fes haka cikin koshin lfy ace wai baida lfy komai nasa baya motsi gashi shar dashi muryarsa ras haka,a hankali naga Aayan ya rada masa magana a kunne nan take ya fara murmushi tare da cewa Yata matso kusa ya kika tsaya nesa,Da Sauri na karasa gaban gadon tare da durkusawa har kasa nace Ina yini ya jikin?Yace Alhmdllh,nace Allah kara lfy,Ameen yata Gashi nan sai kinyi hakuri kin ganshi baya jin magana na dade da cewa ya kawo min ke sai ya dinga min hanya hanya,Murmushi nayi ina jin kunya nace ai yanzu ya kawoni kuma kullum zanzo ba sai ya kawo ni ba yanzu tunda na gane hanya,Murmushi yayi tare da cewa na gode Allah ya muku Albarka,ya albarkanci aurenku ya baku zuria ta gari,Ya sunan yar tawa nace Mufeeda,Alhmdllh naji ance da kannenki ko?nace ae yace to Allah rayasu ya musu Albarka nace Ameen,Allah yaji kan mahaifiyarku nace Ameen Daddy, ki kara hakuri kinji,zaman gidan nan sai hakuri,wannan dan nawa baya ji kin ganshi ina fama dashi sai kinyi da gaske saurin fushi gareshi ga zurfin ciki,ki rike min shi da Amana yata kinji,nace Daddy ai shine sai ya dinga fada yana fushi, Dariya yayi sannan yace to zan masa fada,nace to Daddy,Harara Aayan ya zabga min nayi shuru dani,Mun dan dade a dakin Aayan suna ta hira sannan yayiwa Daddy sallama muka dawo part dinmu,na wuce dakinmu shima yayi samansa.
Cikin dare 2am na farka da ciwon Mara sosai naji kamar abu ya zubo min a pant,mikewa nayi da Sauri na shiga toilet,sai naga period nima na fara dan ban taba yi ba sai yanzu,Meenat kanwata kuwa ita tun tana Jss 2 ta fara dama ta fini kiba, fitowa nayi tare da tashin Meenat nace Meenat tashi ki bani pad nima na fara period,cikin magagin bacci tace Sis ta kare tun last month wacce kika siyo min na karar da ita,To fa yanzu ya zanyi kenan,ki Sa tsumma kafin gobe,ke da rushing na fara fa wlh tsumma bazai daukeni ba kinji yanda yake tsiyayowa kuwa,to yanzu ya za ayi kenan,nace bani dankwalin tsohuwar a tamfar nan taki na Sa naje Wajen Aayan ya san ya zaiyi dani,Meenat tace baki jin kunya? Kuma kin san bazai je ba sai dai yasa me gadi,a'a zai iya karbo min ko wajen yan matan gidan nan ne kema kin san Bazan iya kwanciya haka ba gashi dare yayi dole tunda lalura ce kuma yasan mata sunayi ai dole gunsa zan je.
Haka ne kam jeki to muji,nan na karbi karamin dankwalin na koma toilet tare da gyara jikina don nasan kafin naje sama Na dawo na bata kayana ko ma ya dinga saukowa saman tiles.
Cike da tsoro na masa knocking shuru har sai da nayi yafi sau goma sha sannan naji yace Am coming yana jan tsaki ya bude min kofar daga shi sai wani dan tight short karami ko riga babu a jikinsa,daki ya koma nabi bayansa Sabo da ya kunna light din haske ya gauraye dakin,lfy ciki dare? Na fara ina ina uhm...uhmm..na juya baya tare da tamke idona kawai na maze kamar bani na fada ba nace ehmmm wai..Wai,yace to fitar min tunda baki da abin fada,da Sauri nace period na fara kuma bamu da pad gashi dare yayi ko zaka karbo min wajen kannenka na karasa tare da matse idona kam na juya masa baya.
Tsaki yaja tare da cewa sai ki bari sai gobe kya siya ni me ya shafeni a nan fitar min a daki na zata wani abu ne,Marairaicewa nayi ina rokonsa dan Allah Dan Abbansa ka amso min pls haba Na Daddy,kallona ya tsaya yi yanda nake shagwaba kamar yarinyar yaye, hannu ya daga min hey..hey Hold it thr ban son shirme see u ko kunya baki ji kina min shagwaba ya fice fuuu ya barni,murmushi nayi tare da cewa oho dai ni dai ka karbo min shike nan.
Yana fita na fada saman Bed dinsa nace sai na more naji dadinsa yau dai na dinga birgima a kai ina tunanin zaman da zamuyi wanne Hali zan aro na daurawa kaina dan naga karshen yan iskan gidan nan,tsawa naji keee...Ban san sanda na fado kasa ba dan na manta a Bed dinsa nake,yace Iskancin naki har ya kai Bed dina nan take ya bude wardrop tare da dauko sabon bedsheet ya jefo min tare da cewa cire min wannan kazantar zaki shafa min a Bed shimfida min new, ban bata ma bafa kalla ba komai a kai fa,i wl slap u,ba shiri na cire wancan na shimfida masa wanda ya bani tare da dame masa yayi kyau,wani turare ya miko min ungo fesa a saman Bed din,haka na fesa,yace to jeki da wannan ki wanke min gobe ki dawo min da Abuna Kazama,nace haba Ranka ya dade ka rage irin wannan ni fa matarka ce Amma kwata kwata baka kyautata min,ko Auren business ai ka bari dai mu rabu lfy Amma ba komai bani abun na tafi,naje sunyi bacci ban samo ba,To su manyan matan su Abbi fa? Ko lokacinsu ya cika basa yi su? Baki ya tabe tare da cewa bama shiri taya zanje nace su bani sun san ke zan bawa baza su bani ba,kuma dare yayi bare a siyo,sun tsofe ma wanne period zasuyi ai sai yayansu, nace to ni yanzu ya zanyi na fada kamar zanyi kuka ina doka kafafu,tafi ki san me zaki Sa sai gobe,ni Bazan tafi ba ya kake so nayi dan Allah,tunda farko ne ai bazai miki da yawa ba kije kawai,nace to ni nawa ba haka yake ba kana ta sani ina fadar badala da rashin kunya a baki na,baka san yanda nake ji ba idan ina ambata irin wannan lafazi na Badala a gabanka, murmushin da bai shirya ba ya saki,oh nan kunyata kike ji kenan,wlh da kyar nake iya magana lalura ce ta kawo ni dan Allah a san yanda za ayi dani Na Daddy Allah dai yaji kan Mommynka ya dauraka akan makiyanka,jin nayiwa iyayensa Addua sai naga ya saki ransa kamar wanda aka Yiwa Bushara da Aljanna yace to yanzu ya za ayi kenan? A raina nace na gano lagonka,nace babu 24hrs ne a Kano?Yace da dai Abuja ne sai a samu kuma kinga 2am ba kyau fita ko fitsari tsakar dare nace haka ne,amma muje mana wajen yan matan ka rakani ni zan san yanda dole ma su bani.yace to muje a Cikin wardrop ta jikin Bed suke ajiyewa,nace an gama muje.
Tiryan tiryan muka je har kofar dakin daya,yace wannan dakin Hanifa ne,ai ko na dinga knocking kamar dakina ta bude sai ta ganni tare da Aayan da har zata min masifa ganinsa yasa tayi mukus don tsoronsa suke ji,ni kuma da tsokana kawai nayi ciki da ita tare da tureta na banka cikin dakin,direct na bude wardrop Aiko na gansu a jere na dauko sinki daya na bude na kwashi guda uku sannan na watsar da ragowar a kasa nazo zan wuce na bata rai,tace wlh baki Isa ba ni zakiyiwa wulakanci har Bedroom,na kalleta sama da kasa nayi irin gwanar nan nace How Dear u zaki na min magana any how duk wanda yaji zaice na gama kwarewa da Turanci,taki Sakina kuwa,na kira Aayan Babyna da Sauri ta sakeni tana hararata na fito nace masa muje to,muna Tafiya a hanya nace nayi fashi da makami kaga abinda baza ka iya ba,kai kullum sai ka dinga zura musu ido kamar wanda suka Yiwa asiri danma suna jin tsoronka ai da tuni ina ga kowa ma taka ka zaiyi.
Ki shirya gobe zasu zo daukan fansa wlh harda iyayensu,nace dan Allah ina son muyi magana da kai Na Daddy Allah ya karawa Daddy lfy da nisan kwana, ina binsa a baya da Katon Hijab dina har Bedroom dinsa,ya fada saman Bed dama yasa jallabiyarsa,a hankali na zauna a gefen Bed din ina jin tsoro,ina jiran naji tsawa sai naji shuru,ina zama ina cewa Fatana Allah ya bawa Daddy lfy wlh a gidan nan,da anga yanda zaifi kowa Sonka ai da kafi karfin kula mu ma Sabo da ka zama Gold,yanda naga Daddy na Sonka abin sai wanda ya gani inama Abban mu haka yake irin naka na furta tare da kwanciya na mike sambal a gefensa,tunanina wayo zan masa shi kuwa tuni ya san me nake nufi Amma sai ya shareni ya gama ganin iya wayon nawa me nake nufi.
Dan Daddy wai ya maganar schl din tawa,yace anzo wajen,nace dan Allah Oga kwata kwata ka kaini schl,yace hmm yana dariya a ransa wai shi yar wannan Jaririyar zata Yiwa wayo,yace dama Arabic da boko kika shiga a hade tunda naga kinfi kokari a Arabic sai ki hada biyu abinki,nace ah gaskiya a'a nima nafi son na zama yar boko sosai,to ki zabi wacce kike so sai na biya miki,Nace to, Amma ai sai dai wani ya kaiki,bani da time ki samu wani a yan uwanki ko frnds su kaiki zan baki kudin,nace to zanje Amma dan Allah kasa a kaini a mota kaga raina ni za ayi a gidan nan,yace an gama,duk tunanina da gaske yakeyi sai murna nake yi nayi masa wayo,nace saura kayan sawa zamuje shopping Sabo da goge raini,yace nawa ne zai Isa a goge rainin?nace ko dubu goma sun isa,ya kyalkyale da dariya ku Uku dubu goma to kaya kala nawa zaku dinka kenan nace kala Uku Uku ko hudu,yace lallai dasu zaku goge rainin kenan? Nace to ni ban san kaya ba tunda ai kasan ba siya muke sosai ba.kawai biye min yake yaga iya wayon nawa.
Dan ya nuna min na masa wayon sai yace bude can,naje na bude wata Wardrop,nan take na kusa sumewa kudi ne a jere a jere bundles da yawa na Dubu dubu da dollers,yace ebi yanda zai isheku,nan take gumi ya keto min na rude na rasa yanda zanyi jikina yana rawa na ja baya tare da cewa ni dai sai dai ka bani da kanka, ba yanda baiyi dani ba kan na dauka Amma na kasa sai ma shagwabewa danayi zanyi Kuka kudin sun tsoratani,mikewa yayi tare da kwaso Bundles goma yan dubu dubu ya zube min a gabana yace jeki dasu ai sai na fashe da kuka nace bana so ni,kamar naga wani Dodo na dinga ja da baya,yana dariya a ransa a fili yace kefa kike son kudi,nace ni ba irin wannan nake so ba,tunda kace sai na Eba da yawa to bani dubu ashirin sun ishemu komai da Komai,yace naga ai an baki kudin Sadaki har dubu dari Uku ya kikayi dasu?lokacin ai bana cikin hankalina Sabo da rashin lfyar Ammah da rasuwarta duk a nan suka kare.
Bundle guda ya bani na yan dubu da kyar na karba na tsaya ina tunani,kafaduna biyu ya rike tare da bude kofa ya jefa ni waje tare da rufe kofarsa,Bedroom dinmu naje da murna na nunawa Meenat tace gaskiya Sis tsakani da Allah kin damemu a wannan tsakiyar dare 3am ta wuce kinki bacci sai labarin mijinki kike mana ki kwanta mana ki huta,ni dama idan labari na Cina to komai dare sai na tashi mutum na fada masa,bayan na shirya kaina duk sun koma bacci har na kwanta nima na tuna ban fadawa Meenat labarin Daddy Baban Aayan ba.
Tashinta na fara yi Meenat Meenat ku tashi kuji banza suka min nace wai ina magana kun rainani ko,muna ji ki fada mu wlh bacci muke ji ke bakiyi ba kin hana kowa yi,ina basu labari suna uhm..eh...to...har bacci ya kwashe mu,kafin asuba wayata tayi kara ta tasheni ban dauka ba Amma sai na tashi Meenat,kawai sai ta fashe da kuka wai na hanata bacci,nace to yi shuru kwanta jaraba bakwa jin maganar Ammah tace kuyi min biyayya Amma bakwa yi,Maeesha ta farka itama tayo fitsari muka koma bacci,ni dai banyi wani baccin kirki ba sai na dinga tunanin Mijin Kasuwanci na.
Washe gari da Safe lafiyayye tea na hada mana Sai kwai na hadashi murtuk dashi naga banza ta fadi irin muci rabonmu kafin yasa a kwashe mu koma Koko,sun sha Uniform dinsu ni kuma doguwar riga da dan hijab karami,tun Safe yan gidan suke ta buga mana kofa ina ji naki budewa,bugun duniya naki budewa sai ma kara Sa lock da nayi,Ina jin Abbi yana zunduma mana ashar akan naki budewa yaransa kofa,wai nice ma zan musu breakfast kuma abinda suke so haka kowa zai fada na dafa musu,ai kuwa bugun duniya muka ki bude kofa gashi suna jin motsinmu,Abbi na gani ta jikin window ya leko yace sai kun bar gidan nan wlh tunda ba yar arziki bace ke,yar Iska,guntuwar shegiya haka ya dinga zagina ta window,na kalleshi ido da ido tare da Galla masa harara na murguda masa baki,yace zaki ci ubanki wlh sai naga waye ubanki a kasar nan,tafi nayi da hannuna na kara Harararsa ina gatsina masa goshi da gira,ni dai bance komai ba,yana ta zagina,ke yarinya ki shiga hankalinki,a nan nayi magana nace Yarinya tana bayan Uwarta ni dama haka nake idan naji haushi bani da mutunci ba kowa nake iya dagawa kafa ba ko za a kasheni,Meenat tana ta dariya Abbi ya kara kulewa,ya bar wajen a fusace yana baza babbar riga.
Aayan ne yake saukowa yasha wankan gaske cikin kana nan kaya,kamshi na tashi,Meenat tace ina kwana suka gaisa,Maeesha ya rikewa hannu tare da cewa ba gaisuwa yau?tace ina kwana tana dariya,tace kayi kyau Yaya,tnx yace sannan ya kalleni tare da cewa Abincina fa? Ai ban san zaka ci ba bari na hada ma tea,yace a'a Kunun gyada nake so ko Koko ni,idan babu kuma sai ki bani Tea,ai dole nayi maka,yo Allah na tuba ko ba gasara ai dole a nemota kamar Dan Daddy guda yana so akanta ba sai ayi yaki ba a gidan nan,Dariya na bashi sosai yanda nake maganar cike da girmamawa kamar Ina gaban Sarki,kun san wasu mazan akwai son a yabesu ko a girmamasu,wasu kuma suna so a daraja musu iyaye ya dace mata su dinga fahimtar mazajensu.
Shi Aayan a ransa yace zan gama kure wayonki yarinya har yaushe aka haifeki,Kitchen na shiga dama jiya na tace mana markaden koko,sharp sharp nayi masa tare da soya masa Chips tunda ba time din yi masa kosai,a Dining na ajiye masa sannan na dawo palo wajensa nace Ranka ya dade an gama,a ransa yace zanyi maganinki soon wai ke me wayo.
Ni na zuba masa da kaina,yana shan abinsa yayi nisa nace da sha nace Dan Allah ina neman wata Alfarma idan da hali ba damuwa kuma ban takura maka ba,yace ina jinki,nace so nake ka bani Driver daya da mota za a kaini unguwa zanje shopping sannan zamu je schl din da zan shiga,waya naga ya dauka tare da danna kira Malam Garba shugo ina son ganinka,minti kadan sai ga Malam Garba Driver yazo,Key din mota ya miko min na karba,yace gasu nan daga yau in zasu je unguwa zasu dinga kiranka kana kaisu inda suke so,ga key din mota nan a hannunta idan zaku fita ka karba idan kun dawo ka bata key din a hannunta,har schl zaka na kaisu,Malam Garba yace an gama Alhaji,nace ga key din ka kaimin su Meenat schl da yamma kuma zamu fita na fada ina wani mazewa irin matar Alhaji,Aayan yana kallona duk abinda nakeyi.
Yana gamawa ya mike tare da kara ajiye min Bundle guda na yan dubu yace gashi ki biya kudin schl din ragowar ku kara a shopping karki dawo da kwandala gidan nan duk ki tabbatar kin karar dasu a shopping,nace da gaske mu kashe duka zaka kara mana na cefane?Yace yes.
Yana fita na dinga tsalle da ihu tare da su Meenat,nace ai na fada muku ni ba a ja dani duk jarabarka sai na ma wayo,gashi dai kwana biyu har na samu abinda nake so,Meenat tace to bari mu dawo muje shopping wlh za a buga damu har mota ya bayar ana kaimu unguwa fa,Meenat tace Sis yau sai munje tsohuwar Unguwarmu a motar munyi musu birga,nace ke banza ce ba yanzu ba sai mun siyi kaya masu tsada mun koma yan gayu sai muje a gaisa ayi zumunci
Muje na rakaku mota daga nan mu ganta,gaba daya muka fita har inda Aayan ke ajiye Cars nasa,Malam Garba muka hango a wata shegiyar Benz yar gaske sabuwa dal wai itace zamu dinga hawa,su Meenat suka gaisheshi ya amsa yana me fara'a don gidan kaf babu wanda ke Saurarar dan aiki bare a gaisar dashi komai girmanka.
Meenat suka kame a gidan Baya,sai ga yan matan nan sun fito zasu tafi schl suma ina ganinsu nace pls Baba Driver ka kular min da motata ,ido suka zaro yaushe na samu matsayi har Aayan ya bani mota.da Sauri naga Hanifa ta koma ciki tana zuwa ta zayyanewa kakarsu dasu Abbi.
Ina ciki ina aiki naji bugun kofa na leka ta yar kafa na hango su Aiko naki budewa bugun duniya naki aikina kawai nakeyi.
Aayan na gani ya dawo yace na bude ina budewa Hajja kakarsu ta wankeni da Mari,ga hannunta kamar jikin bishiya Sabo da fatar duk ta tsofe ta bushe.
Zata kara min na goce,nayi niyyar magana haka nayi shuru ganin Aayan na kusa.
Abbi da Maza da mata sun kai su goma kowa da kalar zagin da yake min,Aayan na gefe ya kalleni na kalleshi,matar Abbi tace ke har kin Isa matsiyaciya daga kawoki cin arziki,na kalleta idona a bushe nace yo ai bake kika auroni ba,kema ai ba gidanku bane aure ne ya kawoki,kuma wlh Bazan ragawa kowa ba tunda ba aurenku nakeyi ba,Hajja tace iyye au Iskancin naki ya girma haka ina magana kina magana kin san dawa kike magana,nima ai baku san wace ba,Aayan ta kalla tace kai saketa yanzu na bada Umarni,maza rubuta mata saki,nace ku kuke tsoron saki idan an sakeni sai me rayuwa zan fasa ko me,Kaka tsohuwa Hajja ta rike baki dan tunda take babu wanda ya taba mata ko musu Amma gashi ni tana fada ina fada,tace saketa nace,Aayan yace baku kuka Sa na aureta ba ni ne naga dama kuma da dalilina Bazan saketa ba ya juya yayi ficewarsa tare da cewa idan kin gama ki kira Malam Garba a waya na ajiye miki Number dinsa a Dining,nace to Ranka ya dade a dawo lfy Allah ya tsare min kai,yace Ameen,nace Million dayar daka bani sunyi kadan Yanlabai,yace kin san inda suke kije ki kara yanda zasuyi,na Gode Allah ya kara budi,yayi gaba na kalli Matar Abbi Hajiya Karima nace kiji dan Allah Baby bashi da dama wlh common shopping a baka yafi million ga kyautar gida ga mota yau da Safe,tsaki naji sunja Hajja tace a sannu zan shayar dake mamaki wlh sai na canja miki kamanni ba a takani da yarana a zauna lfy.
Na kalleta nace aiki ya ganki ga tsufa ga shiga rayuwar wani Allah ya taimaka,wlh dan ina ganin girmanki ne ko ba komai zaki ci darajar tsufa da kuma matsayinki na Mahaifiyar surikina kakar Mijina idan da mutunci ke kakata ce Amma baku san haka ba,ku tambayi wace Mufeeda a Unguwarmu kowa yasan yarinyar kirki ce kuma ta wanni fannin bani da mutunci wlh da ace haka kawai ne da kun san wace ni Amma kunci darajar Mijina,ba tabani a zauna lfy dan ma ba akan kudi bane,bana yarda a taba lafiyar hanyar cin Abincina akan wannan bana dagawa kowa kafa.
Matar Abbi ce ta fisgoni suka hadu da Sauran matan suka fara dukana,sai da suka fasa min gefen bakina kadan hakan ma dan na gudu ne da Allah yasan irin Illar da zasuyi min.
Daki na fada na kulle nayi Kukana boye a fili nace wlh kun jawowa kanku dan ni indai ba lallabani akayi ba to kara lalacewa nakeyi, musamman akan kasuwancina dan yanzu auren nan ta hanyarsa muke ci muna sha shine kasuwancina kuma kowa yasanni akan Business ba mutunci zan iya ja da kowa.
AsmaBaffa
[1/9, 4:55 PM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
41-45
Official
By
AsmaBaffa
MMN BASMA,SALMAT BASHEER,SUBYUSMAN ga page na baku Sabo da kauna ina Godiya.
Gaisuwa cikin Trailer zuwa ga
HAFSAT KHAIRAN
OUM FAROUG
MUM SUHAIL
MAMAN HAIDAR
HAJIYA JAMILA
MAIMOUNA MATER ta NIGER.
Kuna Raina
MEENAL SIDI
YA SALAM
DJU LUV
NANA KHADIJAH
OUM SALM@
Ina jinjina muku da Sharhi na gode.
Bayan na gama gyara gidan kaf ko ina yana sheki da kamshi,tuwon danyar shinkafa nayi tare da miyar egusi harda naman Kaza Sabo da a kwai a fridge,a dining na shirya mana komai cikin Food flask masu shegen kyau,wanka nayi na shirya cikin material cotton riga da skert nayi kyau sai ka rantse me tsada ne,dan Mayafi kawai na Sa a saman kaina wanda yasha gyara,1:30pm Sabo da a motar gida ne ba bata lokaci sai ga su Meenat sun dawo suna kwala min kira,Ku karaso mana ina ciki kuma sai kirana kukeyi,Sis yanzu muka ga Yaya Aayan a Compound su Abbi sun sashi a tsakiya tare da tsohuwar nan kakarsu sai masifa suke masa,ko saurararsu baiyi ba kawai jinsu yakeyi,Baki na tabe nace saji dashi can kuje kuyi shirin Islamiyya ga abinci nan a Dining,Bari na kira Malam Garba ya karbi abinci yaci sai muje unguwa, a waya na kirashi ya shugo na bashi abinci a flask dama na ware masa nasa daban Aiko yaji dadi sai murna da godiya yakeyi don ba a basu abincin gidan yan aiki suke burkuta musu ko wanne kwamacala ko dadi babu,fita yayi yaci ya koshi sannan ya kawo min flask din,nace in ba damuwa mu fita ka kaini unguwa,yace ai ba matsala,kudi na zuba a jakata na yafa gyale na me dan girma kalar kayana,can na hango dandazon Family ana meeting akaina irin yanda za a dauki mataki a kaina,Aayan yana zaune gefe yana latsa waya,kamar ance ya dago muka hada ido dashi, hannu kawai na daga masa irin na fita,baki ya tabe irin ina ruwansa,bayan tsadajjiyar motarmu na shiga na wani lafe a kujera ina game da yar Nokia ta wacce dan gidan Comissionar ya bani ,wata Aisha College nace ya kaini kana na Yiwa Malam Garba bayanin ya Zama wakilina a matsayin Babana ya kawo ni schl nan na tsara masa komai,yace ba damuwa yata.
Schl din 2 to 5 pm ce yare biyu akeyi Arabic da boko,Kafin ka gamata ka kware wajen Turanci da larabci tare da Sauran karatun addini dana boko,tana da kyau sosai,bayan munje wajen Pc mun masa bayani yace kinci Sa'a saura kwana Uku mu rufe daukan student na wannan shekarar,da kansa Yamin tambayoyi a lokacin na nutsu na Bada amsar wasu wasu na fadi,yace Ss1 zai sani nace to na gode,haka na biya 15k kudin schl fees,na Bada kudin Uniform har kala Hudu,sai kudin littatafai,nace Ina da aure ayi min Hijab me dan girma,haka aka gwada Size dina da komai na mikawa Malam Garba kudin ya biya a matsayin shine Ubana,aka Sa min sunana Mufeeda Adam Fatima yanda muke amfani dashi.
Bamu zarce ko ina ba sai inda ake siyar da schl bags da su Sandals na siya kala Hudu hudu suma tare da Sauran kayan karatu da komai,komai me kyau me tsada na siya,muna Tafiya a mota naga masu saida Glass na fuska,nace ya tsaya na siya,haka na zabi maka makan glass na yan gayu na gwada sunmin masifar kyau,da baki,da Brown sai farare biyu wanda ake yayi na zamani latest,yanda suka min kyau ba a magana,tun a motar na kara gyara fuskata na sa bakin nan faskeke kowa ya kalleni sai ya kara ya min kyau gashi kuma No respect.
Yanda na fita na barsu haka na dawo na samesu ana ta maganganu an hana kowa tafiya tsohuwar banza tana ta isa da Mulki ita ke magana har da wata jaka ta yan mata a gabanta wai itama fa bata tsufa ba,ganin suna wajen koda mukayi parking ban fito da wuri ba sai da na dauki lokaci yanda naga Aayan yana yi,sannan na zuro kafa daya da sabon cokeken takalmina me tsada dana siyo a wajen masu takalma na ganshi ya birgeni Dubu Bakwai na siya da jakarsa me kyau,irin zanen dake jikin material din Golden,ba wani iya tafiya nayi da me tsini ba amma karfin Hali yasa nace ai dole a je damu muma,ina fitowa sai da kowa ya Bini da kallon kurilla,yanda naci uban acuci da gashina kuma ba dankwali na daura ba kawai gyalen me dan girma da dan kaurinsa na mutunci na yafa a kaina sannan ga glass dina,Malam Garba ne ya kwaso min kayan a ledojin store din dana je,karba nayi nace na gode kaje kawai Baba sai zuwa bayan Magrib zamu fita again sabo da zamuje shopping da kannena na,yace ba matsala Allah ya kaimu,nace Ameen sannan na bashi Dubu Dubu biyu nace a saiwa iyali Alawa,ya dinga godiya nace No Need Baba Ai ba komai.
Su kuma dangin Aayan tunaninsu wasu kudi Aayan ya fara sakar min yanzu,nan take bakin ciki ya rufe su,musamman yan matan nan yau daya sunga na fara komawa wata Baturiya, Aayan yana ganin irin tafiyar da nakeyi ni ga yan mata,kwas kwas na cuno lips gaba irin yar gayun nan,nazo ta gabansu na makale Murya tare da Sallama ba wanda ya amsa nima ban damu ba dama na sani,na matsa kusa da Aayan yana zaune na sunkuya tare da rada masa taso Kaci abinci tuwo ne nasan kana ci ko? Yace zanzo kije yanzu magana akeyi min na Family,nace wanne family? anan tashi mu tafi ni dan Allah wannan har wasu dangin kirki ne,Yana so ya Harareni ko ya min rashin mutunci amma ba Hali sabo da Idan ya min haka zasu gano gaskiya sannan zasu kara wulakanta mu.ganin yaki tashi still ina tsugunne a gabansa nace ko tsoro kakeji? Naga Alama wlh tsoronsu kakeji muje ni zan tare ma fadan ko me za suyi ma zan amshe ma,tsaki yaja kadan tare da mikewa yace muje naga kin fara rainani dan kinga ina sakar miki fuska,ko kallonsu baiyi ba suka ga na janyeshi munyi tafiyarmu,Hajja makirar Tsohuwa tace kar kowa ya masa magana Ku kyaleshi ai Ubansa ya isa dashi zan yi maganinsu,kowa yaje yasha sha'aninsa zan nemeku,
Haneefa tace wannan kwai tsinanniyar Yarinya wlh,Allah ya dau ran shegiya a huta da yar Iska,Dayar a ciki tace shike nan na kasa cika burina sai da nace wa Abbi yasa Aayan ya Aureni yace baya so naje na fada sonsa na kasa cika masa burinsa,Sauran yan matan suka ce ke dai bari ai Allah ya yarda sai an saki yarinyar nan shegiya ko Nono bata dashi bata fi 16yrs ba fa,Ameer yace 17yrs take amma wlh ta iya girki dan baku jiba ne gata me kyau da tsafta inama ni na aureta,ai ni wannan ko Haihuwa nawa tayi burina Aayan ya saketa ko ta halin yaya sai na aureta,Dariya sukayi dukkansu suka tafa da yan matan,Khaleel yace mayen mata yaga kayan Dadi kana jin Aayan zai kyale yarinyar nan ko Sufi ne shi? Ameer yace ina ai wlh ko abarshi bata motsi indai bata motsa akan yarinyar nan ba to ina tabbatar ma har abada babu kuma macen da zata gani ta motsa a kanta,Dariya suka kara shekewa da ita su Haneefa harda shewa,Mujaheed yace ka manta Aayan din yanzu ne fa dan bashi da lfy ya rage amma sha'awarsa ta kai karshe,jarababbe ne na karshe kullum cikin chargi yake baya Free dan bura uba ai yanzu ya gama da wannan yarinyar fitsararriya sai shegen baki kamar gidan tsutsa,Ameer yace ai zaiyi dadi ne lips din,Haneefa tace Ameer da Alama ka kyasa fa,yace tuni ni wlh sabo da ita nake shiga part dinsa so nake ko hannunta ne watarana dole na shafa dole sai mun raba jikin nan nata da Aayan,Mujaheed ya jinjina kai to ka dai bi a hankali kasan halinsa wlh kana ganin kamar baya damuwa ana abu kasan ba a taba masa mata ko zai shekara dubu bai taba abarsa ba indai wani ya taba masa mata wlh yaki kawai za ayi gidan nan,dan kasan shegen akwai kare mutuncin iyali,za kaga kamar bai damu ba yana sani kai kasan yanda Khaleel sukayi akan matarsa Bilkisu wacce Daddynsa ya fara aura masa Sabo da karfin sha'awarsa aka masa aure da wuri tun bai gama Degree ba,kuma duk da haka bai ko taba jikin Amaryar ba ya gano cewar da yarinyarka ce tun tana waje kuma kun sheke da ita,ya akayi farko sanda kake zuwa har Bedroom dinta kuna shoshalewa ya sani Amma ya muku banza kalli dai irin yanda ya gasa mata aya a hannu ga na Family sannan kuma ya mata saki mafi muni,sai a lokacin muka san ko yatsanta bai taba rikewa ba,hmm kai dai bari ashe matsiyacin ya sani tuni,Ameer yace ai ni so nake ma na kulla mata sharrin da zai saketa ni kuma na koma wajenta,ina nan ina hada mission dina.
Ni kuwa tare muka jera muka shiga ciki ba wanda yayiwa wani magana ya wuce Bedroom a matukar gajiye,nima na samu su Meenat basu dawo daga Islamiyya ba,a gurguje na cire mayafin da glass dina tare da takalmin,na dauki kayan gaba daya nayi saman Aayan dasu,sai da na shiga naji karar ruwa yana wanka,ajiye ledojin nayi na koma tare da kawo masa abincin na ajiye,ina Zaune ya fito daure da dan Towel yana goge jikinsa da wani karami a hannunsa,kaina na dukar kasa ina wasa da yatsuna ban dago ba,shi kuwa ko a jikinsa har ya gama shirinsa sai kamshi naji yana tashi,ina dagowa naganshi Sanye da 3qrt da t-shirt yasha kyau yana jikin Mirror yana gyara gashinsa,na kalli Namiji yanda yake ta shafa man gashi masu tsada kala kala yana tajewa, sabo da bana gani na kyale nace to ai ya isa haka wannan ai sai ka karar dashi da wuri kunfi so kuyi ta asarar kudi amma wannan shanana mayuka da kake haka ko Mace albarka,naga ya bude wani kala yana fesawa shuuuu,na Mike nace dan Allah ka barshi haka yanzu idan kasa kadan ka adana abinka gobe ma ai sai ka dauka ka sa amma rana daya ka kusa karar dasu a dinga tausayawa kudin mana.
Kawo na karasa ma,ya fisge abinsa,nace nafa iya naka ma da yake na maza da wuri zan gyara ma shi kuma wlh ko fita kayi sai an San kana da mata,kasan shi gwauro idan ya fita tun daga shigarsa ake ganewa sabo da babu me nuna masa inda aka samu matsala,wani sai kaga gashi a wuyan rigarsa ya zuba,murmushi yayi Bai ce komai sai yace ai bakinki ne Gwauron gashi nan yi min naga iyawar taki kuma karki min da zafi,Ina murna nace ai nasan har kyauta yau sai kayi min,sunkuyawa yayi tare da miko min kan,nace zan gaji da wuri a haka,na zauna Saman Bed shi kuma na shimfida masa Sallaya nace zauna ka gani ni da nake me kitso,Kamar bazai Zauna ba sai kuma ya zauna,na ware cinyoyi kamar zanwa wata kitso dai yace ke hade wannan cinyar taki kina period,nace sai na fasa ma dan zan maka shine zaka fada min magana.
A hankali na dinga taje masa ina fesa masa abun gashin,sai wani lumshe ido yakeyi zaiyi bacci,nace kudi biyu zaka biya ga na gyaran gashi ga kuma na hannun mace yana taba ma kai kasan hannun mace daban ne sai an biya,wannan hannun naki kamar Dutse gwara na maza dashi,ni kaina ba wani yi nake ba kawai tajewa nakeyi ina wasa da gashin dama karya nake ban iya ba,bacci ne ya fara kwashe shi har na gama,nace na gama tashi ga abincin can,yana son yayi bacci na mika masa,yace Hannuna da Mai ban son tashi kisa spoon ki bani naci,ba da wani abu ya fada ba nima haka nasa spoon ina bashi har yaci ya koshi nace lemo zaka Sha?yace Ruwa ni ban fiye Shan lemo na kwali ba nafison fruits ko ruwa,ruwa na mika masa yasha,na kwashe komai na maida,su Meenat suna dawowa nace su shirya muje shopping,wanka muka Sha nasa doguwar rigar da Aayan ya bani nasa lokacin da ya kawoni wajen Family dinsa shiri mukayi sosai Meenat ce tayi mana kwalliya mun Sha kyau,mun fito nace suje jikin motar Driver yana can bari na fadawa Aayan.
Knocking nayi masa sannan nayi Sallama na shiga yana zaune yau magazine yake karantawa,nace zamu fita Shopping,hannu kawai ya daga min irin muje kawai,katon store muka je munsha siyayya sosai da sosai,Cosmetics,shoes,bags,mayafai,jelweries,Night wears,sai atamfofi kala biyar biyar,shadda kala Uku uku,sai materials tare da laces suma,Ready made dogayen riguna da riga da skert,mayafai dasu Inner wears duka masu kyau yan tsakiya dan yan tsakiya za ace baza ace masu tsada na karshe ba kudin baza su kai ba,wajen telanmu muka wuce duk Wanda za a dinka muka bayar,lokacin har dare yayi kusan ma 8:30pm,nace yau ba girkin dare nace Baba Driver dan kaimu Yahooza suya sai murna su Meenat sukeyi,mukaje na fita na siya mana muka zauna inda aka tanada don Zama ga masu son ci a wajen,muka ci abinmu muka koshi tare da ice cream,na siyowa Aayan ma nasa harda kilishin da suke siyarwa, Malam Garba ma na bashi nasa harda shi na siyawa,ya dinga godiya da addua,
Wasu sai kaga suna cin abu ma a gaban yan aikinsu wai baza a iya bashi yaci ba,bare aje dashi waje shima a dan siya masa ko kadan ne babu me kulasu Sabo da son kai su tunda talakawa ne suci irin nasu,
sai 9pm muka dawo gidan,a gurguje nayi wanka nasa rigar baccina kamar T-shirt take amma yar doguwa iya rabin cinya tsayinta,powder na murza nasa lipgloss sai dan turare na Amtek na shafa na dauki Take away na Aayan na wuce Samansa.
Da Sallama na shiga Yau ma yana saman Sallaya Sanye da Jallabiya yana karatun Qurani,ina zaune gefen Bed dinsa ya gama adduoin nasa sai lokacin ya juyo ya kalleni tare da cewa ya akayi? Ko ka tambaya mun dawo lfy? Gashi to na mika masa take Away,ledar ya bi da kallo sannan ya kalleni da baki ya nuna ledar tare da cewa bude na gani,da sauri na sakko kasa yace to Ustaziyya gyara Hijab din kina samun a fuska,Dariya nayi kawai na tsuguna tare da bude masa ledar duk kamshinsa ya cika min hanci me dadi ji nake kamar na fada jikinsa na shako kamshin da yawa,na bude yaga package na kilishi,daya ledar kuma Kazace da yawa tasha hadi,sai Fura da ruwa harda yoghurt,son jin dadi na da kwadayi na ya jinjina a ransa duk wata hanyar cin dadi na Santa har na iya na siyo masa wannan.
Muryarsa naji yace ina naku?nace ai mu a wajen muka zauna muka ci Namu kawai sabo da nafi so muna dawowa yaran nan suyi bacci su kyaleni na huta,Murmushin da bai shirya ba ya saki gaba daya ya tafi da Imanina don idan yayi murmushi wani masifar kyau yake karawa na musamman,ke ba yaranki ba amma feeling kikeyi kamar yaranki ne kika haifa sai son girma,
Fari nayi da Ido wanda ban san nayi ba nace ai ko Ammah na da rai nice kamar uwarsu,rufe wannan ledar bari na gyara farce na,nace au baka zuwa a yanke ma farce?yace a'a basa min yanda nake so ne a Abuja nakeyi ko kuma lokacin dana zauna a London,amma nan garin Sam nasu bai min ba tsoro ma nakeji kar su samin cuta,na kalleshi nace iyye kaji Manya Ashe har a London ka zauna uhm lallai dole kayi yanga,kallo na kawai yayi ya mike tare da dakko abun da yake yanke farcensa kalarsu ma daban ne, kawo na yanke ma kaji na iya sosai,Ba musu ya mika min na gyara Zama a gabansa, nace to fa sai ka koya min yanda ake amfani da kalar Nail cutter en nan ban gane ta ba,
gwada min yayi tare da cewa indai kika lalata min Nails sai kin biyani farce na in dai bai min kyau ba,ae naji kawo kafar to, kafarsa na jawo wani mugun laushi ba duk mace ba, na daura saman cinyata da na rufe da hijab, na mika masa take Away din tare da cewa to ci mana, naman ya fara ci ni kuma na dukufa ina yanke masa Farce,yana ci yana latsa waya yana murmushi ko chat yakeyi oho, ji nayi yana dariya nace mu gani me kake gani na dariya haka,ba komai kawai yace, da na dan shigar da zafi zai ce karfa ki yanke min precious skin dina, wannan kayan da kika cike min Bedroom dasu fa,nace au na manta ne na schl ne na kawo ma ka gani na bashi Labarin komai gobe ma zan fara zuwa,ba sai na gani ba kawai ki kwashe abinki,nace to ba damuwa.
Ina gama yanke masa na kafa ya gama cin abincin nasa,hannu ya goge da tissu ya miko min yatsun hannu masu shegen kyau dasu,na fara gyara masa farce ina cewa Dazu mun siyo kayan mun kai wasu dinki,du na karar da kudin Dubu uku ce kawai ta rage.
Ok yace ke kika bawa Malam Garba Abinci? Nace ae har ba dare ma,ya min waya yana ta godiya Ashe kina da hankali dai? Murmushi nayi nace Kai wai nufinka bani da hankali?to ba karamin Hankali da wayo ne dani ba,yace sai dai kiyi wa wani wayon na ki,harda kai ma zan mawa,Sau nawa nayi ma wayo kaine dai baza ka gane ba,a ransa yace lallai yarinya zan nuna miki baki da wayo soon,ina gama masa ya kalli yatsun tare da cewa uhm ba laifi,toilet ya fada yayi Brush dama yayi wanka kaya ya canja zuwa na bacci,yana fitowa yaga na kwashe kayan dana kawo du na tafi dasu,light ya kashe ya kwanta abinsa tare da Addua.
Washe gari ina gama aikace aikace na shiri nayi cikin riga da skert English wear nayi kyau na yafa mayafi na fita na tafi har part din Daddyn Aayan,securities basu barni na shiga ba sai da suka sanar masa matar Aayan ce yace daga yau indai itace a barta ta shigo kawai.
a saman Bed dinsa na ganshi an canja masa kaya yana kwance abinsa,cike da ladabi na durkusa har kasa na gaida shi ya amsa da fara'a,daga nan yace zauna ya ta,a gefen gadon na zauna,nace Daddy da har zan kawo ma abinci na tuna Ya Aayan yace ba komai kake ci ba,murmushi yayi tare da cewa ae ni abu me ruwa nake ci sai kuma vegetables sai ko snacks amma duk sauran abinci basu Dameni ba,tun farko haka nake ni dama abincinmu na Hausawa basu Dameni ba sai Fura da Kunu kawai amma na turawa nake ci,me girki na ma daban take yata,nace Daddy shi kuma Aayan ko yana yaro amma na Hausawa gargajiya yafi so,yace ai wannan kyaleshi kawai Uwarsa ya gado ta nan.
Kuna zaune lfy dai ko?ae Daddy lfy Alhmdllh,to idan ya miki wani abu kizo ki fada min kinji,nace to,idan kin samu lokaci kizo watarana zan baki labarin tarihin gidan nan namu kaf sabo da ki koyi Zama dasu,ranar da bani da schl zanzo,Allah ya kaimu,na mike nace na tafi zanje makaranta,yace na gode Mufeeda Allah ya taimaka,na fito a hanyar dawowa part dinmu na hadu da Ameer a hanya yana kallona zan wuce amma yaki matsawa sai ma hanyata da ya kara tarewa,na kasa gane masa kawai na matsa can na wuce abina tare da ja masa tsaki,a ransa yace zanyi maganinki.
1:30pm ina bedroom na fara shirin zuwa schl ina cikin sa sabon Uniform dina sai naji knocking ba zato,da sauri na zura hijab dina na fito da tunanin ko Aayan ne ya dawo to in ba shi ba waye zai min knocking a Bedroom,ina fitowa naga Dan iskan nan Ameer, ina ina ya fara ahm...ahm...abinci zaki bani,harara na maka masa nace banyi da kai ba don ba auro ni akayi dan na dafa ma abinci ba,na koma Bedroom tare da sa key,abin nasa ya fara tsoratani tun daga irin kallon da yake Bina dashi.
Cikin Uniform na fito ba karamin kyau nayi ba black and white komai nawa har jaka da takalmi kowa ya kalleni a uniform din sai ya kara nayi matukar kyau,Sallamar su Meenat naji Ma'eesha tana Faman Kuka,lfy Ma'eesha ina Meenat din na ganki ke daya,Sis wannan matan ne suka Mareni kuma ga Meenat can a Compound wai shoe maker ya tareta wai sonta yakeyi,wanne kuma me wankin talkami, wannan su Haneefa yake wankewa takalmin schl baki ganshi ba cikinsa kato hannunsa da jikinsa siriri kamar tsinke cikinsa kuwa katon gaske kamar zai fashe,sunce wai Meenat sai ta kulashi dole.
To shine kike mana kuka haka,to ai marina wannan Haneefa din tayi akan nace Meenat tazo mu tafi,ok wuce kiyi wanka ga abinci nan a Dining na tafi schl ni daga can zanga Meenat,maza Ku fara shirin Islamiyya,Bye Sis nace Bye, na fita rataye da jakata,saida nayi tafiya kadan sannan na Iske Meenat Tsaye tare da wannan mutumin me gyaran takalmi,ni tunda na ganshi ma dariya ta kamani don cikinsa girmansa ya isa ga jikinsa siriri kamar a bushe shi ya fadi,su Haneefa suna zaune suna faman latsa waya.
A fusace na karasa wajensu nace Malam mene haka lfy kazo ka tare min yarinya anan ko kunya baka ji idan kudin magani kake nema ai sai kayi magana a baka kaje Hospital,Meenat tace ba ke bace Sis nace ki bamu dama amma kince kar mu kula su ko me zasuyi mana dole kece zakiyi kawai,Yan matan nan ne suka taso kanmu,ke wace da zamuce ayi abu kice zaki hana wannan ya gani yana so kuma dole ta kulashi in dai tana gidan nan,sabo da shine dai dai ita,Haneefa tace au Ku nan har kunfi karfin wannan kuna yayan talakawa,dama kadan nake jira Mari lafiyayye na zabgawa Haneefa dama kin Marar min kanwa wlh ba wanda ya isa ya taba mana lfy ya kwana lfy,nasan in suka hadu zaneni zasuyi Marin ma da kyar nayi ta maza na shammaceta na fesa mata shi, Cikinsu Sukace KWAJA jeka ka dawo gobe dole sai ka auri wannan suka nuna Meenat,Meenat tayi dariya tare da cewa au dama sunanka KWAJA? Lallai Kaci sunanka ta kara sakin dariya,nace wuce to ciki yar iska idan kika kara tsayawa dashi wlh zan miki rashin mutunci,to ba ke kikace kar na dau mataki Kansu ba,motocin Aayan ne suka shigo ya hango Su Haneefa sun rike min Hijab gashi nayi kyau, har gabanmu yazo yace sake min mata yana gyara wayar Usb da ya Ciro a motarsa,Haneefa ya damko ya dinga tsula mata wayar tana kuka da ihu,su kuwa sauran tuni sun Arce,wlh duk ranar da kuka kara taba jikin matana sai na kusa kasheku a gidan nan kuma kinsan ba abinda zai faru,nasan kin san da haka,kallona yayi tare da takowa wajena zai damko ni nima na kwashe da gudu,ya biyo ni taku biyu ya damko ni Ransa a bace ya kalleni ido da ido sai yayi murmushi matsoraciya yi mata dariya zance shine kika gudu,aiko Nace Haneefa tana Kallona na kyalkyale da dariya nace wooo ayi mata gwalo,Aayan yace fara frog jump dan ubanki kafin nazo nan na halaka ki,da Sauri ta fara yi,yace yi mata dariya ke kuma Aiko na dinga yi ina wooo harda tsalle,muna Haka sai ga Hajja kakarsu ta fito kamar zata make mutane,Aayan yace jeki schl tana cewa tsaya dan ubanki Karuwa Amma ko kallonta banyi ba na shige mota abina Malam Garba yaja,ta glass tana Kallona ina kallonta na mata gwalo,Aayan ya daga min hannu bye,tana zuwa ta daga hannu da niyyar sharawa Aayan Mari ya rike hannun caraf tare da matsar da ita gefe ya wuce ya bata waje bai ce kala ba,Kuka da kara tare da ihu ta fara yi a gaban yan aiki,Sai ga Abbi yana huci an taba Uwarsa.
Tunda na fara zuwa schl yau Sati guda kenan lfy nake zuwa ina dawowa abina cikin jin dadi,haka su Meenat ma,Aayan kuwa tun daga ranar da ya Zane Haneefa ban kara ganin Sa a gidan ba,ashe wai ya tafi Umrah Saudiya bamu sani ba sam,koda kudina suka kare Bedroom dinsa na shiga na duba inda yake ajiye kudi na ebi dubu biyar idan ya dawo sai na fada masa.
A schl dinmu har kawa nayi yar gayu wayayya MARYAM ga hankali ga sanin ya kamata,kullim tunda taji ina da aure take fada min yanda ake Tafiya da Imanin me gida,nace ai ni kullum da Hijab nake zama a gida idan zanje unguwa ne nake Sa mayafi watarana,aiko ta dinga dariya tana wayar dani ni kuwa dan kar ma Aayan yace Dan shi nakeyi nace ko Ya dawo bazanyi ba.
Yau da yamma su Meenat sun dawo kenan daga Islamiyya KWAJA me gyaran takalmi ya biyota tun daga wajen gate,dama su Haneefa sun fadawa Securities in dai Kwaja ne a barshi ya dinga shigowa yana da budurwa a gidan bayan haka ma yana goge musu takalmin schl.
Direct Kwaja ya shigo yana wargaje baki da wata falkekiyar T-shirt,hannun rigar Sabo da ramarsa kamar skert hannu tsilili a ciki, kansa har wasu jijiyoyine ke tashi kamar me kwoshokwo, wuyansa kamar mirkin laima,dan kirjinsa kuwa kamar Allo,hakoransa guda biyu manya a waje na gaba,bakinsa yake dargajewa shi tunaninsa ai dole ma ya auri Meenat tunda yayyenta sunce sun bashi ita.
ta window din sama Na hangosu yana tsaida Meenat yana Meenatu Meenatu yan mata dan Allah ki tsaya,haba Meenatu so kike sonki ya kashe ni? Meenat ta ja tsaki tare da hararsa Malam Kaja mituncinka mun san darajar Dan Adam shi yasa nake daga ma kafa Amma tunda kaki ji zaka ga abinda zanma.
Kwaja yace ko me zaki min ni Bazan ji haushiba tunda ina sonki,da wlh ba da gaske nake ba Amma na yaba da hankalinki da nutsuwarki,gaki kyakyawa ni yanzu ba zancen yayyanki nake bi ba wannan da gaske ne daga makwallaton zuciyata a daina maganar wasa, to bana sonka kaja Life dinka ka kara gaba Malam cewar Meenat,Murmushi yayi yace yan mata bani da Lifan ni bana karya dan a soni,karki kiyi tunanin Ina da Lifan kice Naja Lifan dina na tafi wlh Allah ko Keke bani dashi idan zaki soni ki soni dan Allah nasan ku manya ne kun wuce ayi muku karya,Takaici ya kama Meenat tace ina ruwana da karyarka ka ja rayuwarka kayi Out a gidan nan,Haushi KWAJA yaji yace na fuskanci Ku kunfi son dan karya azo ana muku birga da mota kullum idan nazo zance na baki Dubu daya ko Dubu daya da Dari biyar koma fiye da haka,to ni ba haka nake ba gaskiya da gaskiya nakeyi wlh da zaki aureni kullum sai na dinga siyo miki kifin gona kina soya mana,watarana ma Miyar zabo zaki dinga yi mana,Taliyarmu guda da macaroni da wake gongoni guda ya ishemu na na kwana hudu zuwa biyar, tsaki Meenat taja tayi gaba ta barshi nan,ina jikin Window ta sama ina ta dariya gaskiya Su Haneefa yan Iska ne,Meenat ta shigo na dinga mata dariya,nace Allah sarki kanwata duk iya kwalliyar nan kuma taki sai ki kare a KWAJA tumburarre,Dariya tayi itama tare da cewa ai Allah ya tsinewa su Haneefa yanzu idan nayi wani Saurayin yazo ya ganni da wannan ai wlh rainani kawai zaiyi ya daina zuwa,ina ta dariya harda kwalla Meenat tace dan Allah ki daina,har dare muka kwanta ko farkawa nayi sai nace ta KWAJA tashi na baku lbr,banza tayi min tace wlh sai na fadawa mijinki idan ya dawo tunda haka kike min.
Yau nayi shiri tsab ba schl zanje wurin Daddyn Aayan ya bani labarin gidan nan da yace zai bani,koda naje Sallah ya idar daga kwancen,yana murmushi muka gaisa,nace Daddy yau na shirya a bani Tarihin naku. Yace to yata bude kunnuwanki kiji.
Next page is very Important readers ku tsaya ku karanta da kyau shine zamu san waye Aayan.
Raffa
Asma Baffa
[1/10, 10:37 PM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
0 comments:
Post a Comment