Page dinku ne wannan Fans gaba daya da wanda na sani da wanda ban sani ba.
Daddy ne ya samu Babban Amininsa Ahmad Naira Bola suka yi shawara kawai zai auri Ammah yanda Aayan yace, Sunyi Shiri tsab suka tafi neman yardar Ammah kafin aje danginta,Driver na parking a gidan Ammah lokacin Aayan yaje gidan da yamma shima zai kwashi gaisuwa,Karaf yaga Daddy harda abokinsa,Farin ciki ya kamashi amma Bai tsaya ba yayi sauri ya karasa palon Ammah domin ya fada mata taci kwalliya sai yaga Ammah ta hade cikin wata dakakkiyar shadda Maroon tasha kyau,bai taba Sanin Ammah nada kuruciya haka ba sai yau,abinda Aayan bai sani ba kafin Daddy yaje sai da ya nemi Number din Ammah a hannun Ameer sannan ya sanar mata sabo da haka tare da Inna yar uwarta suka shirya girki tasan Daddy bature ne dama kuma baya cin abincin Hausawa sabo da haka na turawa tayi masa irin su Snacks duk Ameer ne munafikin da ya fada mata ta waya wasu ma bata iya ba amma ya tura mata Masu yi ma Daddy girkin na gida suka koya mata da yawa a ciki,ta kuwa yi kuma yayi harma yafi nasu.
Ammah na ganin Aayan kunya ta kamata sauri take ya tafi amma yaki tafiya har Daddy Me aiki tayi musu Iso suka shigo,Aayan sai washe baki yake harara Daddy ya watsa masa da Ido ya nuna masa ya fita amma yace ni matata nake jira tace na jira ta a nan gidan sai dai na koma Bedroom din can ya furta tare da komawa Bedroom,Ammah ta gabatar musu da kayan abinci ta zauna a kunyace Daddy a ransa yace Allah yayi Halitta a nan,da naso na tafka kuskure Allah yayiwa Aayan albarka,nan abokin Daddy ya Sanarwa Ammah meke tafe dasu,itama dai tace ita kunya takeji gaskiya a kyale maganar,Aayan yana labe yana ji a daki,yana why Ammah wacce kunya kuma kai Hausa People,da kyar Abokin Daddy ya dage tare da Inna da ta zauna a wajen yanzu tace Allah ya halatta baza ki Haramta ba kinfi so ki zauna a haka,nawa kike da kuruciyarki,Ammah dai tace to Allah ya tabbatar da Alkhairi na Amince amma da sharadi bazamu zauna a gidan suruki na Aayan ba,Daddy yace Ni kaina yanzu ba a gidan nake ba dama lalura ce tasa amma tuni na koma gida na,Aayan ma kwanan nan zasu koma Abuja da zama tare da zaga kasashe mu kuwa muna kano sabo da Mahaifiyata,idan ma Abuja kike so sai mu zauna can ki zabi gidan da ya miki,Ammah tace a'a nan ma yayi abincin suka dan ci kadan sannan suka musu Sallama tare da zube Kudi masu yawa suka tafi,sai da Aayan yaga Daddy ya fita sannan ya fita da Sauri yana Ammah na tafi tace na gaidaki dariya ma ya bawa su Ammah dama sa ido ya zauna Ashe.
Yana fita lokacin Daddy zai shiga Mota Aayan ya rungumeshi yana Dariya Daddy Ashe zance kazo da ka fada min nine dan rakiya,Abokin Daddy Alhaji Ahmad Naira Bola dariya yake musu shi dai rayuwar Daddy da dansa tana birgeshi,Duka Daddy ya kaiwa Aayan Yanda Aayan ya dage yana gwada yanda Daddy yayi,Mota suka shiga suka barshi yana dariya sai lokacin Shima ya shiga motarsa Driver ya jashi sai gida,ya shigo da Murna ya tarar na kafa kaina a cikin wani Vaseline ina shakar Kamshin kwanan nan dadin Kamshinsa nake ji ban san me yasa ba.
Kallona ya tsaya yi ko Sallama na kasa amsa masa sai a zuciyata hancina yana cikin robar Vaseline,lfy kuwa? Na fada miki ciki ne da ke kinki yarda,gobe asibiti zamuje ko bakya so,Vaseline din na lakuto tare da laftawa a saman Hancina wai na dinga jin kamshinsa ba ruwana,Ina zuwa nace masa na fice can garden jikin bishiya na samo Kasa a dan karamin Kwano na dawo na tankade abata luwai na dan kwabata da ruwa ina dan ebowa da cokali ina shanyewa,a kitchen ya sameni tunaninsa wani abin nake Sha me dadi,tsoro ne ya kamashi ya kwace kwanon ya zubawa kasar ruwa ya wanke dan Plate din, mene haka dan Allah?karki kara sha ko bana gidan nan kashe min jaririn zakiyi da kasa,idan ta tsotse miki jini fa ko ta miki illa ko akwai kwayoyin cuta ke kika ci fa,Kuka nasa masa nace Ni ba a sona sai jariri tun bai zo duniya ba tunda haka zaka dinga nuna banbanci to indai ciki ne zubarwa zanyi,Wasa nake miki Baby haba ni na isa ai kinfi Jariri shin din Banza,ya isa ina ruwana dashi,sai lokacin to in dai ka kara nuna ya fini wlh sai nayi ta Shan kasa da kanwa ko nasha gayyen darbejiya daci yasa cikin ya zube idan shine kawai wani yazo sama ta kai a nuna ya fini,Aayan yace ni ai ban isa wani fiki ba,waye ma ya isa na daina sonsa tuni yaje yasha zamansa,Hannunsa na rike nace wayyo..yace Mene Allah jiya naji ana min Usha Usha a cikina,ka gani yanzu ma,dariya Aayan yayi yanda nake gwadawa da Hannu kamar Yar China,cikina na rike nace wash..wash..Allah na Yau Kungfu ne ake min idan kuwa jariri ne wannan to dan kasar China ne zan Haifo shi a nan kasar.
Aayan yace shine ma yasa kansa a gefen cikina yace kai jariri ka daina kuka kana wutsil wutsil bazan taba sonka kamar matata ba,nafi sonta itace gaba da kai,Dariyar jin dadi nayi na zauna tare da cewa woo...ba a sonsa,Aayan dariya yake sha abinda nakeyi na kuruciya.
Meenat ce ta bude idonta daga baccin wahala da takeyi While Ameer yake shakar na dadi abinsa,a hankali ta zare jikinta a nasa ta fada Toilet,wanka da duk abinda ya dace tayi ta fito sosai ta gasa jikinta,Sallah ta gabatar tare da azkhar sannan ta shirya sama sama ta canja New night Gown me dan sauki saukin tsaraici ta kwanta a gefensa again kwanciyar da tayi ne ta tashi Ameer,da sauri Meenat ta rufe idonta amma ya rigada ya ganta,yaga alamar tayi kokarin yin wanka ta shirya kanta Jarumace Meenat,shima toilet ya fada ya gama komai ya fito ya gabatar da Sallar asubah tare da azkhar daga shi sai boxers ya koma Bed din tare da shigar da Meenat jikinsa sosai yana kissing dinta a wuya da gashinta zuwa gashin kanta dake kamshi baccinta takeyi kawai abinta.
Bacci suka ci gaba da yi ba su suka tashi ba sai wurin 11am hakan ma shi ya takura sabo da bata ci,Ameer waya ya buga min lokacin zanyi shirin zuwa schl sabo da muna shirye shiryen fara Waec da Neco, Sister Mufee dan Allah do me a Favour Meenat Bata da lfy ne abinci muke so,Ok zan bawa Driver ya kawo muku,kitchen na kara shiga na dan musu masu sauki,Dama nayi farfesu sai kawai na soya Chips da kwai tare da ruwan tea na shirya komai sharp sharp na bawa Driver ya kai musu,Meenat ya matsawa dole sai ta tashi taci abinci, Da kansa ya kaita ta kuskure bakinta sannan ya zuba musu abinci a Bedroom din ya dinga ciyar da ita shima yana ci har suka koshi,duk abinda yakeyi Meenat taki bude idonta bare ta masa magana wai kunya takeji ita har suka gama cin abincin ya bata Mouthfreshner ta kuskure bakinta shima haka,zata koma ta kwanta ya riketa tare da cewa dan zauna kadan ba kyau ana gama cin abinci a kwanta,Kayan da suka bata ya maida kitchen ya gyara Bedroom din sannan ya hau Saman Bed din tare da cewa kwanta Sweetlove ya sata cikin jikinsa suka kwanta ya fara kokarin cire mata yar rigarta,da sauri ta bude idonta cike da muryar kuka tace shike nan tunda kashe ni kake son yi sai ka dauki raina,Murmushi yayi tare da cewa ba abinda zan miki nafi so kawai najiki a jikina ba kaya kiyi hakuri My Meenat,Kai kawai ta daga mishi yana lashe mata hawaye da harshensa,tana shesheka tace ka..ka..kira min Ammah na gaisheta dasu Sisters kwana biyu bamuyi waya ba,Jiya fa ne kawai bakuyi magana ba Babyna amma bari na kira Sis Mufee,Yana Dialing Number din Mufee Aayan ne ya dauka yace tana schl sai anjima zan dakko ta ya akayi? Ameer yace kai ya Aayan wayar ma Tata idan tana schl tana hannunka kamar wani P.A,idan ta dawo kace ta kira Meenat back,ok cewar Aayan ya datse kiran,Ameer kuma ya Kira Ma'eesha wacce yanzu ta dan saba da harkar Yarima da sukeyi tana jin dadi kadan,Suna murza juna Kiran Ameer ya shigo Amma Yarima yace baza a daga yanzu ba sai sun gama tukun zasu kira back,Ammah kadai aka samu a waya sukayi Hira ba tare da ta gane komai ba,suna gamawa Meenat ta makale a jikin Ameer tana masa magana kasa kasa Allah ka bani wahala Honey jiya ko tausayina baka jiba,Am so sorry My love Bazan kara ba kinji yana lallashinta tana shagwaba .
Alhmdllh Daddy ya yaje Dangin Ammah Sati daya aka daura auren Ammah da Daddy ko su Aayan basu sani ba Hajja kawai ya fadawa tana asibiti har yau ba a sallameta ba, ina fitowa daga class an tashi naga Ma'eesha tana daga min hannu ita ta tafi Yarima yazo daukanta,ina daga mata hannu kawai naji an daga ni sama nasan Aayan ne ina jin kamshinsa,ana kallonmu fa zaka Sa ace bani da kunya,thts y nake so ai mu koma Abuja dagani sai ke babu me Sa mana Ido jira nakeyi ku gama zana last Exam ta Neco,Murmushin dake kara min kyai nayi tare da rike Hannunsa nace Muje Mijina,Office dina zamuje ki jirani na gama sai mu wuce gida ko,amma fa kasan bani da wata lfy kasala,ga saurin jin yunwa kuma ina tashin zuciya kaga kuwa akwai Matsala kar nayi maka Amai a Office,ba damuwa muje haka gobe baku da schl asibiti zamu je kar Babyna ya girma ba a fara dura masa kwayoyi ba,biyu da Safe biyu da dare,dariya na farayi shima haka nace kamar kasan yaran yanzu duk yan kwaya ake haifowa,sabo da tun a ciki ake dura musu kwayoyi.
Muna ta hirarmu har ya bude min mota na shiga shima ya shige Driver tare da escort suka ja sai Office katafaren building.
Tun a hanya nace a tsaya a siya min Doya da kwai haka yasa aka siya min,ya kwanto dani jikinsa yana tambayata sai me kike so Babyna?Nace Coconut da Alkubus,Ina zan samo Wani Alkubus ni kiyi hakuri na fadawa Ammah tayi miki idan zamu tafi gida sai mu biya mu karbo,banyi musu ba nace masa to Allah ya kaimu yace Ameen Sweetyna, ina jikinsa muka karasa Office yana signing da Sauran ayyuka ni kuma ina saman Cinyarsa a zaune kamar yarinya karama motsi kadan idan nayi sai yace min ya akayi ina ta ciye ciye na hankali Kwance,Duk abinda nace ina son ci da Sauri yake Bada Umarni lallai a kawo min naci rashin kunyar da yake zubawa kuwa na caring sai dai idan baza ka kallemu ba ka tafi.
Yau kwana Uku da Angwancewar Ameer jinya yakeyi har yau Meenat taki ta daina lango kullum tace bata warke ba ta wani narke zatayi kuka,amma a fagen Romancing itace kan gaba, 9pm Meenat taci uwar kwalliya sanye take cikin English Gown iya rabin cinya light blue and White sai kamshi takeyi gashinta yasha gyaran gaske kamshi ke tashi kawai ta ko ina,palon Angonta Ameer ta nufa tana Tafiya cikin nutsuwa tare da jan Hankali yana Palonsa sai chat yakeyi a waya yana Jin kamshin ta da Sauri ya fita daga WhatsApp din ashe Meenat ta gane me yayi,cikin takunta na kasaita ta karaso inda yake zaune Saman 3seater kafin ta zauna ya jawota jikinsa saman cinyarsa ta zauna yana shafa mata wuyanta da kafadunta ta baya,cikin muryar da ba a san Meenat da ita ba tace Ashe da ka shirya nan ka dawo? Yeah Princess ya furta yana Jan zip din rigarta kasa baya har yayi Zipping dinsa, Bra ya balle mata tare da janye rigar ya jata kasa ta koma kasan cikinta,Dukiyar Fulaninta masu matukar kyau da sheki suka bayyana juyowa tayi gaba daya a jikinsa ta kwanta Saman kirjinsa tare da rungumeshi tana rufe ido wai Kunya,Na shanunta ya shiga wasa dasu tana masa shagwaba,a shagwabe tace Husband ya amsa da Naam cikin dishewar murya,nuna min Chat dinka na WhatsApp na gani,Murmushi yayi tare da cewa gaskiya sai dai kiyi hakuri bazan iya nuna miki ko Contact dina ba, Ni Din?tana kallonsa kamar zatayi kuka,yace to me zaki gani in ba neman rigima ba,ni...Ni...Allah sai ka nuna min,am sorry to say gaskiya bazan iya ba,Fushi tayi a fusace ta kwace jikinta tare da maida Bra da rigarta tana niyyar tashi ga Kwalla na shirin kwararo mata,Ba shiri ya fisgota ta fado jikinsa me laushi da kamshi nan take ya mika mata wayar gashi kalla kuma nima sai naga naki murmushi tayi kyawunta ya kara bayyana ta karba tana me dauke da murmushi a fuskarta ta fara duba Contact,tana tambayarsa kowa taga Number din mace,haka WhatsApp nasa ma sai da ta bincika tas taga babu mace da suke chat,farin ciki ta shiga yi mijinta baya kula wata,Shi kuwa ko duba nata baiyi ba don baya zargin Meenat da komai.da kanta ta ja Hannunsa zuwa Bedroom dinsa sabo da tasan tayi masa laifi wajen danne masa hakki yayi hakuri da ita har ta fara Jin kunyar Ameer din nata,Rigarsa armless ta zare masa a hankali itama sannan ta kashe Light duf duhu ya gauraye dakin sai karar ac da kamshi kawai ke tashi,Bai ma san ta cire kayan ta gaba daya ba sai jinta yayi a jikinsa ta rungumeshi sosai Albarkatun kirjinta suka sashi ya saki ajiyar zuciyar ba tare da ya shirya ba ya dauki Meenat zuwa saman Bed,a nutse cike da wayewa suke gudanar da harkarsu har ya samu abinda yake so ba tare da tasha wahala ba,Gaskiya Ameer karshe ne hakan Meenat ke ayyanawa a ranta tana Jin dadi,bangaren Ameer ma hakan yake ji a ransa tana manne cikin jikinsa suna hira Sama sama har sukayi bacci abinsu.
Kwanci tashi yau Sati Uku kenan da auren Su Ma'eesha Sameera Yar daba taji sauki Sosai ta warke inda ta fitar da Alhajinta me kudi zatayi aure itama ta saduda da al'amarin duniya,an sallami Hajja daga Hospital Ta samu Lfy amma matan su Abbi basu canja ba,su Khaleel ne ma watarana suke dan tarewa Hajja sabo da su Abbi sun koma abin tausayi sun koma rakumi da Akala,Kullum Hajja kuka take sharba musamman idan taga danta Abbi Mustapha yana wanke wanke da shara yayi duhu ya rame,yau kamar kullum matar Abbi Sani ta sashi wankin kayanta sai zufa yake hadawa,Hajja ta fita tana dingisa kafarta da bata gama warkewa ba,tana fada kan ya daina wankin haka ya isa,suna haka sai ga matar ta fito babu bata lokaci ta shiga Zagin Hajja Munafuka,Karuwa sannan ta ture Hajja ta fadi rim again akan kafar data karye nan take kafa ta kara samun matsala dama bata gama warkewa ba aiki ya lalace ya dawo baya,Hajja yau tayi kukan da bata taba yi ba,ba shiri ta fara Allah na tuba ka yafeni,Na jawowa kaina,na cuci kaina da yarana na ruguza farin cikina na tarwatsa kan yarana,Hajja tana ta tuba tana tona asirinta,Khaleel da Mujaheed ne suka hango me ke faruwa da Sauri suka karasa kan Hajja suka sata a mota sai asibiti tare da sanarwa Daddy,Aayan da Ameer abinda ke faruwa,Ameer bakin ciki ya kamashi Key din mota ya dauka kawai Meenat lokacin tana kitchen ya leka da Sauri yace na fita ana kira na Babyna yanzu zan dawo har ya tafi ya dawo da Sauri ya rungume Meenat tare da kissing dinta a lips yace take care of ur self for me Wifedina,same too u Darling banda tukin ganganci kaji mijina,ya fita yana daga mata hannu ta kwalla da karfi am gonna Miss u Sweetheart kar ka bari a kalle min kai,shima da dan karfi yace Already started Missing u SweetMeenat ya fice dauke da murmushi ya manta ma da fushin da yakeyi Meenat ma murmushi take bazawa kawai.
Bai zarce ko ina ba sai gida wajen Su Abbi,yana zuwa a fusace Ameer bai kula kowa ba ya fara shigewa Bedroom din Abbi Mustapha Baban Ameer kenan ya fara watso kayan matar anci sa'a Abbi yana bayi yana wanka,kasan Bed din ya dage katifar sai ga Wata yar tukunya dauke da tarkacen tsafi a ciki tare da ruwan rubutu,Ameer bai jira ba ya fito ya jefota ta saman Bene tukunyar tsafi ta ragargaje,haka ya fita ya shige dakin Matar Abbi tana cikin gyara kaya taga Ameer ya fado da zureriyar Sandarsa tunaninta dukanta zaiyi ko Ya haukace sai ta fita da gudun tsiya,Abbi na ganin haka ya rufa mata baya dama sai abinda tace Kan tace ne kafin tace ya aikata,nan Ameer ya kulle dakin da key ya shiga bincike a dakin ya dinga samo guru,laya,ruwan rubutu,ya duba kasan bed din ba komai cikin pillow ya duba tare da Sa wuka ya tsarge pillow din ta ko ina ya fito da soson da suke ciki sai ga layu iri iri a Cikin pillow an hada dashi an dinke pillow tsab baza ka taba ganewa ba,yanzu mata abinda sukeyi kenan za a kai Amarya kafin a kaita sai an yanka pillow da razor a tura kulunboto sannan a mayar a dinke yanda ba Uban wanda zai gani sai kaga pillow normal ashe da tarkacen tsafi a ciki,miji yana ta kwanciya a kai,wasu har katifa ake yankawa asa sai a Sa zare da allura a dinke ba me ganewa Allah ka shirya mu.
Ameer yana fitowa ya fada dakin Abbin Yara Duk ya fita a hayyacinsa matar ta sashi sai ya goyata ya dinga zaga Bedroom da ita,gata wata me kiba katuwar gaske suna ganin Ameer da shegiyar wuka suka saki ihu ta fisgi Hannun mijinta suka gudu nan ma haka ya dinga kwakwulo kayan tsafi,sabo da Ameer duk irin wannan harkar ta malamai ya santa tunda suna zuwa da Hajja kafin Allah ya shiryeshi sannan Hajja tana sasu suna yin irin wannan abun wajen iyayensu mata,haka ma da Matar Daddy da kuma Matan Aayan duk irin wannan yasan su shi yasa yake da saurin gane irin wannan harkar,a leda ya kwaso komai ya fito dasu yabi ta baya duk ya warware layun sannan ya yayyaga komai da almakashi into pieces ya konesu tas,Sai ga su Abbi nan take sun dawo hayyacinsu,Hajja kawai suke nema da yaransu,Matar Abbi Mustapha kuwa taci duka hannun Abbi kamar jaka wai ta rabashi da Uwarsa,a wajen duk suka rubuta musu saki dai dai na musulunci Ameer da kansa yasa Securities sukayi waje dasu suna kuka tare da nadamar halayensu.
Da su Abbi tare da Sauran Yara suka dunguma zuwa asibiti wurin Hajja da take fadawa su Khaleel ku taimakawa iyayenku da addua su dawo cikin hankalinsu su dawo da iyayenku mata yan albarka masu biyayya,ni na jawo da nace sai sun sake aure,banyi adalci ba ko a baro sai an turani naje har gida na basu hakuri da kaina zanyi bikonsu ko da kafar katako ce,Mufeeda tare da kannenta suma zan nemi gafararsu,Daddy ne ya shigo a birkice nan Hajja ta damki hannunsa tana bashi hakuri tana kuka ka yafe min ni na jawo nice....Hajja na yafe tuntuni ni dama ban rikeki ba kuma aike Mahaifiya ta ce ba komai ya wuce ki bari kiji sauki ko na fitar dake kasar waje?Hajja tana goge Hawaye tana Allah ya maka albarka Ka yafe min dana,na maka abubuwa suna haka sai ga Aayan da Mufee duk ta kara wani fari tayi kiba da kyau Sabo da cikin dake jikinta,Hajja ta shiga bawa Aayan Hakuri da Mufee,Aayan yace shi ya hakura ta ma daina bata bakinta,Su Abbi su Ukun tare da Ameer suka shugo suma nanfa Hajja bata boye ba tace da kanta ta lalata zumuncin yaranta,To Allah yasa su Abbi sunyi Nadama nan suka shiga Yiwa Hajja fada da nasiha sannan sukace duk itace ta cucesu Amma tun da Allah ya ganar dasu sun yafe suma a yafe musu,a asibitin aka shiga yafewa juna anyi wa'azi tare da Nasiha wa juna an tunatar sosai dama wasu Iyayen da kansu suke bata zumuncin yaransu suna raba kan yaransu,a karshe Hajja tace da kanta zata je bikon iyayen su Ameer babu wanda ya kai su Abbi Murna za a dawo musu da matayensu yan kirki
Su Abbi sai gafarar Daddy suke ta faman roka sai lokacin ya fada musu ya auri Ammah kuma a satin nan zata tare a sabon gidansa daya tsantsara na fitar hankali,sun tayashi murna sosai har Abbi Mustapha na tsokanarsa an samu dangin kyau,Hajja kuwa Allura akayi mata anci sa'a ashe bata kara karyewa ba ta dan bugu dai a wajen Amma Dorin bai lalace ba,Aayan sai murna yakeyi shi da Mufee ashe Daddy ya auri Ammah basu sani ba,nan Mufeeda ta fita waje ta kira Meenat da Ma'eesha ta sanar musu Ammah ta auri Daddy ta labarta musu yanda Daddy ya basu labarin har yanda aka daura aure,Sunyi farin ciki Ammah ta samu me kula da ita,Meenat tace Sis kicewa Darling yataho gida haka na gaji da jiransa,Dariya Mufeeda tayi tace idan yazo me zai miki sarkin jaraba Bazan fada masa ba,dan Allah Mufeen Ammah ki fadawa Ameer dina na kira wayarsa a kashe,tana cikin haka sai ga Ameer ya fito, na mika masa waya nace ga Meenat tana magana,da Sauri ya karbi wayar yana murmushi yace Hello...tuba nake ranki ya dade kaina bisa wuya gani nan yanzu ki bani 15mnt Insha'allah ,Meenat sai Kukan shagwaba take masa ita yayi Sauri ya barta ita kadai.
Yarima da Ma'eesha saura 1wk zasu wuce Us sannan suje saudiya za a kwashi Amarci,dama anan ma Yarima baya daga mata kafa ko kadan,itama ta zama irinsa mayyarsa ce bata zuwa ko ina kullum tana gidanta kusa da Mijinta Office ma kusan kullum da ita suke zuwa,yauma 1pm yana Office ya kasa aikata komai kawai matarsa yake so yaji kusa dashi suna ta faman waya Amma bata gamsar dashi gaba daya,sai kawai yasa Driver ya dakko masa abarsa,ta gama shirya abincin da ake kai masa Office kenan tayi wanka tana shiri ya kirata a waya lallai tabi Driver suzo tare,zatayi Musu Yace dama ai ba sona kike ba yana narkewa kamar mace dole ta hakura ta shirya a mutunce tabi Driver tare da basket din Abincinta,tana zuwa yasa key a Office dinsa yace ya tashi daga aiki yau ko uban waye ya dawo gobe ko knocking kar ayi Masa suka shiga Soyewa da abar kaunarsa Ma'eesha itama ta gama gogewa da rashin kunya biye masa takeyi shi yasa yake kara sonta.
Kwanan Hajja Hudu aka sallameta tana dan digishinta haka tasa Driver ya kaita gidajen matayen su Abbi na farko tare da Daddy suka Bada hakuri da kyar suka amince aka sake daura aure tare da tarewa gaba daya,Daddy ya Mayar da Su Abbi kan aikinsu na da,tare da siya musu motoci na alfarma, Su Ameer da Sauran Yara sai murna iyayensu sun dawo Alhmdllh,lokacin kuma bikin Khaleel da Mujaheed,Sajeeda da Haneefa ya matso tunda ansa rana tuni,Saura Meenal,Sabeer da Aliyu nan gaba,gidan yanzu ya Zama gidan masu tarbiya da hankali kowa ya nutsu yasan mene rayuwa ba wulakanta dan Adam ba komai,mutanen unguwar ma yabonsu sukeyi yanzu sosai ana zaman lfy da mutunci da makwafta ba irin da ba,Su Haneefa gayu ya dawo yaci uban na da Amma yanzu na mutunci akeyin shigar mota sai wacce suka ga dama.
Yau Sati guda cif Sunday yaune kuma Ammah ta tattara nata kaf dama an shirya komai kamar wata budurwa,da wasu dattijai yan matasan iyaye kawayenta su Uku tun na tsohuwar unguwarsu tare da yan uwanta guda biyu sune suka kai Ammah dakin mijinta Daddy cikin lafiyayyun motoci guda kusan biyar,Ammah ba a ganeta sam Sabo da Su Mufeeda sun takura an kaita gidan kwalliya anyi mata,ga gyaran jiki ko ina kamshi fata na sheki gashi etc tasha tsumi iri iri abin ba a magana gata dama Ammah matashiyar Uwa me ji da kuruciya dai dai gwargwado tasha kyau an kaita duk an maida kowa gida lfy sai ita kadai a katafaren gidan sai yan aiki masu kaiwa da kawowa ko ina kamshi na tashi.
8pm Daddy ya shigo Bedroom din Ammah tana gefen Bed suna waya da Inna,tana ganinsa tace zan kiraki gobe Insha'allah ta kashe wayar, ta kalli Daddy dauke da lafiyayyen Murmushi yasha farar Shadda sai yau ta hango tsan tsan kuruciyarsa shima hakan dan sai yau ya tabbatar Ammah ta hadu ta ko ina,Gefenta ya zauna da ita suna shakar kamshin juna jikinsa na gugar nata,kunya ta lullube Ammah ta sunkuyar da kai kasa,Daddy irin Aayan ne sai zumudi yakeyi Da kyar ma ya Umarceta sukayi Sallar nafeela suka ci kayan makulashe Ammah da kyar ta karba Daddy yana bata a baki,Suna gamawa suka sake brush tare da wanka kowannensu yayi shirin Bacci suka haura Saman Bed,Ammah kunya take ji ta kasa sakin jiki,yana janta da Hira Amma da kyar take bashi amsa,Daddy cike da kulawa tare da tausasa murya yace Kin san nifa Bature ne kin sani asalin Bature ne mu ba haka muke rayuwarmu ba,ban saba da hakan ba,Mun zama daya ai ke matatace mene ne abin jin kunyata matsalar Hausawa kunya gaban me gida,am serious ni bana son kunyar nan ki tsaya mu nunawa juna so tare da kulawa shi muke bukata. murmushi tayi tare da juyowa suna facing juna tace na gane me kake nufi ta furta tana me rufe fuska da tafin hannunta,wanne suna kike so na fada miki? Ko wanne ma cewar Ammah,tunani ya shiga yace Honey?dariya tayi tace ai zanji kunyar yarana,yace to Maman Aayan? Taji dadi irin karar da Daddy yayi mata baice ta Mufeeda ko Meenat ba sai dansa ya nuna dansa nata ne nan take Ammah tace kai Kuma Daddyn Mufeeda ko? farin ciki ya lullube Daddy nan labari ya canja Salo suka koma soyewa suka lula duniyar ma'aurata abinsu.
5pm Mufeeda tana zaune ta baje kasa saman Center carpet na gaske Madara da sugar ta hada take faman lasa tana jin dadi Aayan yana gefenta sai cike takaddu yakeyi,Ba tare da ya kalleta ba yace Queen yau kinsha maganinki kuwa na rana wanda Doctor ya baki kafin mu koma Next wk?fuska na hade ina shagwaba tare da tirje tirje ina kuka a hankali nace ni na tsani magani ka sani bana sha sai kana takurawa sai na sha lafiyata kalau,Queen ki taimaka min Dan Allah kisha ya kike so nayi da raina idan baki da koshin lfy kuma kin san akwai Baby na a cikinki,ni dai Bazan sha ba na furta tare da fashewa da kuka,Da kansa ya tashi ya dakko maganin a leda da ruwa ya ballo kala wurin Uku yanda akace a sha ya mika min da ruwa dan Allah kisha My Queen kinji ya shiga lallashina Amma naki sha,yace zan siya miki mota fa sabuwa dal me tsadar gaske,sai lokacin na kalleshi da Hawayena nace da gaske?Yace kin san ai idan nace bana canjawa,Kasuwancinmu zamu dawo dashi idan nasha magani zaka siya min wani abu ko ka bani kudin?Aayan ya dinga dariya yace lallai me hali baya fasa Halinsa ashe har yau da ragowa,Ni ka amsa min kawai pls,yace ae to min dawo da kasuwancinmu kisha magani na baki kudi idan kin sha wannan mota ce guda gobe kudi jibi wani abu haka har ki sauka lfy,Murna ta kamani na karbe na shanye magani tas sannan ya ci gaba da aikinsa,yana farawa nace ni tausa nake so dole ya ajiye aikin ya shiga yi min tausa me dadi ina kwance saman Sofa.
Ma'eesha yau jirginsu ya lula zuwa Us a jirgi ma suna manne da juna ana kissing din juna,Ameer yau ya gaji a Office sosai Meenat kuma ta koma schl University dinta tana zuwa tana tashi daga schl ta wuce Office wurin Ameer tunda Driver ya turo mata wai su biyo su daukeshi su koma gida tare ya gaji,amma tunda yaga Meenat bata kansa yake ba ta Meenat yakeyi wai ta gaji sai lallaba abarsa yakeyi,Suna cikin mota ya kwantar da ita a jikinsa bacci ya sace ta har suka Isa gida tana bacci,Sai daukanta yayi kamar Jaririya suka shiga ciki kana ya kwantar da ita Saman Bed shi kuma ya shiga toilet da niyyar yin wanka,
Ya kusa gama wankan yaji Kukan Meenat da karfi karfi ya firgita da Sauri ya ya daura Towel ya fito,baki ya bude tare da rafka Salati.
AsmaBaffa
[3/4, 11:23 PM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
141-150
Official
By
AsmaBaffa
a kasa ya hango Meenat Dafe da Mara jini na bin kafafunta,mamaki yakeyi wata daya da sati Uku da bikinsu Meenat tana da shigar ciki Ashe da Alama bai dade a jikinta ba ya zube,da Sauri ya kamata ya kaita toilet tare da yi mata wanka still jinin na zuba da sauri ya bata pad, Meenat tana kuka tace jini na zai kare zan mutu,duk Ameer ya rude da sauri yasa boxers tare da zura jallabiya a jikinsa ya koma toilet inda Meenat ke zaune Jini na fita a jikinta sai kara karfi ma yakeyi kaya ya sa mata ya dan shirya ta sama sama yanda jinin bazai batata da yawa ba sabo da dankwalinta na atamfa ya linka ya mata kunzugu dashi haka,mota ya sata ya zauna gefenta tana cikin jikinsa sai kuka takeyi tana Salati zata mutu,Ameer yana aikin lallashi Driver na tuki da gaggawa suka isa Katafaren Private Hospital akayi ciki da Meenat wacce ke jin mararta kamar zata balle,Emergency aka shiga da ita,nan likitoci suka rufa a kanta,Ameer yana gefe daga waje an hanashi shiga Kawai zaga wajen yakeyi hawaye ya zubo masa na tsoro karfa Meenat dinsa ko ta mutu,Wurin 3hrs Nurse ta fito tayiwa Ameer magana shiga tana nemanka,Ameer da sauri ya shiga har an canjawa Meenat daki ta warke kamar ba ita ba a zaune ma ya sameta gefen Bed,Ameer yaje da niyyar rungumeta amma taki yarda wai batayi wanka ba,likita ne ya shugo ya musu bayani ciki ne ya shiga baifi 1mnth ba ya zube kuma tunda har wankin ciki anyiwa Meenat,Magunguna ya rubuta musu har na Karin jini da shawarwari ya basu sannan ya rubuta musu Sallama,Ameer daukan Meenat yayi kamar yar Baby ya kaita mota Driver ya jasu suka tafi gida ba tare da kowa yasan me ya faru ba tunda ko a waya Ameer yaki sanarwa kowa.
Suna komawa gida shi ya gyara toilet din da kansa sannan ya hadawa Meenat ruwan Zafi ya gasa ta sosai sannan tayi wanka,tana fitowa ya shirya mata jikinta har Makeup shi yayi mata kana ya bata abinci taci tasha magunguna ta kwanta bacci ya kwashe ta,shi kuma ya kara wanke toilet tare da gyara Bedroom din komai yana kamshi shima yayi wanka ya shirya kayan Meenat daya zuba a washing machine su ya kwaso ya shanya su tas sannan ya wanke nasa Suma a washing Machine ya shanya yana danna system gefen Meenat dake bacci kayan suka bushe ya goge su ya adana su dama Ameer akwai tsafta bai son kazanta.
Ammah ya kira a waya ya sanar mata Meenat tayi bari amma ta warke ba matsala,ya sanarwa Ummansa,ya kira Mufeeda lokacin ina jikin Aayan dina yana shafa dan cikina da yanzu ya turo ana iya jin tudunsa,Ameer yace Anty Mufee Meenat ce tayi Bari yau dazu muka dawo daga asibiti amma ta warke lfy take, cike da tsoro nace yaushe zatayi wani cikin da har zai zube 2mnths fa da bikin,Ameer yace ai Doctor yace watansa daya ya fita bafa wani abu da aka gani kawai Blood ne,Mufee tace to tunda da sauki Alhmdllh zamuzo da dare,Aayan ne yace me ya Samu Meenat din?bari tayi wai na cikin 1mth,Murmushi Aayan yayi yace shege Ameer ai dole ma ya barar da cikin da kansa baya saurarawa yarinyar nan ga ciki dan karami an dameshi da jaraba, na masa hararar wasa tare da cewa kai ai kafi Ameer zaka ce Ameer kai baka ganin me kakeyi,Aayan yace Saura dan duniya Yarima,wasa nakeyi da Kirjinsa ina zaga yatsana a kai,yana shafa min dan cikina.
Maeesha ma an sanar mata da barin Meenat tayi mamaki,da dare duk munje har Ammah Daddy da kansa ya kaita suka duba Meenat,Ammah ta sanarwa Ameer yanda zai kula da Meenat har ta warware sosai,Ni kuwa kawai dariya ma Meenat take bani har yanga takeyi ita ta samu ciki har da bari ga shagwaba da take uban zubawa musamman idan taga Ameer a wajen shike lallaba ta,Muna zaune saiga su Hajja dasu Hanifa kusan gaba daya gidan sunzo Duba Meenat,Daga baya su Abbi suka zo da matayensu harda Umman Ameer sai da ta kawowa Meenat Soyayyun Zabbi cikin wani Bowl.
Bayan mun watse Ameer ya matsa jikin Meenat dinsa yana murmushi tare da zuba mata kallon so kana yace Meenat dina ni kadai sai lokacin ta kalleshi itama dauke da shauki a fuskarta ga wani son Ameer dake Karuwa mata a ranta ko dan yana da kyau ne oho ta kasa ganewa, bakinsa ya shigar cikin nata ya shiga tsotsa,Meenat ta lumshe ido itama tana mayar masa da martani sun dauki tsawon lokaci a haka Meenat ta janye jikinta taga Ameer din nata duk ya hargitse kuma baza ta iya bashi abinda yake so ba bata da lfy,Idonsa jajir ya kalleta da kyar ta iya magana murya a dishe yace pls Baby ba dai hanani zakiyi ba? Hannayensa ta riko da hannayenta a nutse cike da Ladabi tace Honey am so sorry yau kaima kasan baza ka samu ba ko ba komai Yau nayi Bari fa ai yakamata ko ba komai ka bani hutu ko na 1mnth ne tunda shima ai kamar Haihuwa ne yama fi haihuwa wahala ance,Marairaicewa yayi kamar zaiyi kuka yace Dan Allah kin ga fa ba jini kike ba har sallah kinyi dazu,kamar fa haihuwa ce Prince,Ni dai ban yarda ba yana shagwaba kamar jariri,Meenat tace yanzu ni danya ce fa?hakan nafi so ai danyar sharaf,dariya tayi kawai tace kama daina Sa Rai ka bari zan baka labs dina thts all,Ameer yace ni dai ba haka naso ba Amma ya zanyi dake Amma ki min alkawari yaushe zaki bani gobe? 1mnth nace fa,Ameer da kalar tausayi yace dama ance Mata Bedding dinma sai sunga dama zasu baka,kasa kasa Meenat ke dariyar mitar Ameer,mikewa tayi ta barshi ta nufi Sama,Kamar Ummansa haka ya bita a baya kamar jela yana roko Harda komawa bara irin ta almajirai Yara yana Iya... ko dan kanzo...Almajiri bara iya..,Iya ni ban samu ba iya...Meenat tana dariya ta shige Bedroom Amma Ameer bai daina ba Sai ma cewa yayi Iya ni ban samu ba...ko ni Mijinki ki san mini Iya....Meenat tana dariya tace Allah ka daina ce min Iya kamar wata tsohuwa,to kice zaki bani yau ko gobe sai na daina shuru ta masa yace zanci gaba Wahidin Iya....da Sauri Meenat tace gobe ka kawo Kwanonka dan anace,Murmushin dake kara masa kyau ya saki ba tare da ya shirya ba,Dan sajen nan tare da gemu firit suka kara kawata fuskarsa, Dimple dinsa ya loba,Meenat ta saki baki tana kallon haduwa kamar tayi yawa da Aayan kamar Babansu daya,jikinta ne ya mutu Sabo da ta dade tana kallon Ameer musamman da taga ya tube daga shi sai Boxers tana son Surar Ameer matuka,a hankali ta mike ta Isa gabansa sosai suna dan gogar juna kadan a hankali ta zagayo da hannayenta ta cikinsa ta rungumeshi a jikinta sosai,suna kallon juna kowannensu da salon iya kallonsa da suke Aikawa juna,a nutse tace ina Sonka da yawa Mujina,Kara matseta yayi a jikinsa yana rada mata wasu zafafan dalasaman so a kunnenta karshe yace muje muyi wanka muyi bacci ko Sweet Princess? Kai kawai ta iya daga masa ya gama Tafiya da imaninta.
Ma'eesha da Yarima cikin Sweeming Pool na alfarma suna wanka a katafaren gidan su Yarima dake Us,idan kunga Ma'eesha baza ku gane ta ba,kamar baturiya daga ita sai Swimming Dress Kalar Bra da pant,Yarima dan short ne a jikinsa a Cikin Pool din suke shagalinsu kawai,Yana ciki ta shiga saman Bayansa ta makale suna wankansu tare sai dariya sukeyi cike da so,gabansa ya dawo da ita Sabo da Ma'eesha bata iya ruwa ba koya mata yakeyi a tsorace take duk tabi ta makalkaleshi, peace kibi a hankali duk kin wani Tsorata,ni kasan ban iya bafa ta kara manne masa,Kanta ya dago cike da nutsuwa ya tura harshensa cikin bakinta ya shiga tsotsa,Maeesha ta kara matseshi a jikinta tare da maida masa da martani,kasa ta zame a hankali ta nutse a Cikin ruwa ko second bata yi ba ta dago kamar ranta zai fita wai ita ta koyi Swimming,tace Baby kalla na fara iyawa kamar kifi ta kwanta saman ruwa sai ko tayi kasa kamar an jefa dutse ta dago da Sauri tana facal facal da ruwa ita bata yarda ba ta iya ruwa,Yarima dariya yake ya riko ta tare da kunna uban nutso da ita suna kasan ya riketa ya shiga murza Boobs dinta,dago da ita saman ruwa yayi Ma'eesha ta fara tari zatayi kuka za a kasheta a ruwa wai,Sun dade suna murza juna a Cikin ruwan nan sannan suka fita tare da kwanciya saman kujerun hutu suna kora Juice da kayan ciye ciye.
Bayan 3wks Dan cikina ya girma ba laifi har ana iya hangoshi kadan muna mota tare da Aayan Driver na janmu yau gidan Ammah zamuje mu gaishesu,sallama mukayi a palon Ammah na zaune gefen Daddy tana yanke masa farcensa suna hirarsu ta masoya,Har kasa muka gaida su suka amsa da fara'a na koma jikin Ammah na makale Aayan yana hararata,shima ya koma kusa da Daddy suna maganganunsu na aiki,Daddy ne yace Aayan yaushe zaku tafi ne? Sai ta Haihu Bazan yarda ta shiga jirgi da dan cikin nan ba ya zube,Kunya ce ta lullubeni kamar na nutse,shi kuwa ko a jikinsa,Daddy ne ya tabe baki tare da cewa shashasha to ai inda zakuje suke da Doctors manya ka kaita kawai taga dangin kakanka sai ku zauna a can idan Allah ya sauketa lfy sai ku dawo,Ni Daddy ya barmu anan muje kawai mu dawo,Ammah tace to yanda kuka ga dama mu cikin satin gaba zamu tafi Saudiya da Us Insha'allah,farin ciki ya mamayeni Ammah fa an waye an san gari, addua mukayi musu mun dade har dare muna gidan tare muka shiga kitchen da Ammah,Sai bayan Aayan da Daddy sun dawo daga Sallar Isha mun ci abinci muka bar gidan abinmu,Ammah ta bani wasu tarkacen na mata da turaruka na kwanciya.
Kullum muna waya dasu Ma'eesha yayin da Bikin su Hanifa ke matsowa ana ta shirye shirye sosai.
Ammah da Daddy su zasuyo order din kayan lefen mazan da Furniture na mata kaf shi yasa ma zasu bar kasar,Sameera yar Daba anyi bikinta itama da gwaninta suna can suna shan Amarci da katuwar muryarta kamar ta Maza.
Hajja zaune take tayi tagumi tana Jan carbi sai Istingifari takeyi bata gajiya da Nadamar Halinta ga ciwon kafa ya hanata sakat duk kayan dadi an hanata ci a Hospital ba cin jan nama,kaji ma sai dafaffiya ba kullum ba,Yanda take mutunci da Ammah ba a magana kamar zata goyata haka kaf jikokinta ta kara rikesu musamman Aayan sai yanzu take nuna masa so tasan Muhimmancinsa,Matayen su Abbi girmamata dama can basa gajiya bare yanzu,itama ta rikesu da mutunci,Sai yanzu take so ta gyara zumuncin tana kokarin hada kan su Abbi da Daddy Amma sai dai ayi Amma basu shaku ba,ta rigada ta raba,sai dai komai suyi sama sama duk da cewar ba wata matsala Amma abinda take nema bazai samu ba a yanzu.
Sabeer,Aliyu da Meenal ma sun gama University dinsu yanzu saura Yara yan Secondary da Primary kawai.
Ameer ne ya shigo a gajiye yau ya dade a Office yasha wahala,lokacin Meenat tasan lokacinsa yayi na dawowa wanka ta dauka Cikin kana nan kaya Wando Short Jean blue ko Mazaunai da kadan ya rufe mata su da yar riga karama ko cibi bata rufe ba,Ameer tunda yayi tozali da ita hankalinsa ya tashi,kamshi kawai ke tashi ta ko ina a gidan sabo da yasha gyara ga matar gidan ta cakare,cikin salon tafiyarta ta jan hankali ta karasa wajensa a hankali kafin ma tace ko a ya fisgota jikinsa ya kankame abarsa yana sakin ajiyar zuciya,nan take ya birkice mata kissing dinsa ta fara cikin kwarewa Meenat ba sanya fa,Daukanta yayi zuwa Bedroom da kyar Meenat ta kwaci kanta wajen lallabashi ya bari sai yayi wanka yaci abinci sai ma yayi ko me yake so,yaki yarda Meenat tace haba mana dan Allah so kake yunwa ta kama min kai?Ka rufa min asiri kaci first abun nan ba guduwa zaiyi ba yana jiranka ai naka ne,ta dade tana lallashinsa sannan yace sai dai ita ta masa wankan idan yaci abincin,Abincin kuwa ya fara ci, da kanta ta ciyar dashi ya koshi sannan ta kaishi toilet tare da taimaka masa yayi wanka da Brush,mai ta shiga murza masa kafin a gama Ameer ya kasa jurewa ya shiga wani Salon na daban.
Hankali kwance muke shan Amarcinmu,Kwanaki suna shudewa Ma'eesha da Yarima sun dawo daga turai da dan karamin cikinta na wata 3, ciki na ya shiga 7mths muka sha bikin su Khaleel da kyawawan Amarensu Aayan ne ya bawa Khaleel da Mujaheed gidaje dankarere ,Haneefa da Sajeeda suma da angwayensu ya musu kayan daki na fita kunya,saura bikin Sabeer da Aliyu Sabeer Meenal zai aura,auren zumunci za ayi musu suna son junansu,Aliyu kuma yar kanwar mamansu zai aura an Sa bikinsu cikina yana 9mnths dai dai ba wani girman ciki gareni ba,kullum addua mukeyi tare da Aayan Allah ya saukeni lfy, ba sosai yake fita ya barni ba Sabo da cikin ya girma ko Haihuwa zata taso min,Ammah ta turo min Dattijuwa guda bayan yan aikin da suke gidan zata dinga kula dani Sabo da Haihuwa, Baba nake cewa da ita Sabo da bata girmanta,da kyar na lallaba Aayan kan yaje Office tunda Haihuwar taki zuwa,cikin rashin Sa'a ya samu Tafiya ta kamashi zuwa Turkysh wani Meeting kan harkar Business dinsu,a gurguje ya shirya na hada masa kaya yace 1wk zaiyi ya dawo Sabo da cikin da nake dauke dashi.
Na damu matuka ban so tafiyar tasa ba Amma sai ban nuna a fili ba na boye nasan idan yasan ban so zai fasa Tafiya kawai,Nace Zan bika airport yace a'a yamma tayi sosai ga Babyna zai sha wahala ki hakura kinji,Hawaye ne ya shiga sintiri a fuskata gani nakeyi kafin ya dawo ko na mutu ma Maybe,Fuskata ya leka Oh...Common Sweetheart mene abin kuka zaki Sa na fasa tafiyar nan ko me zai faru ya faru,Da Sauri na shanye Kukana tare da share hawayena ina murmushin Dole,Nasha Lallashi kafin ya yarda zaije da kyar muka rabu da juna ya tafi cikin zugar motocinsa,suna zuwa jirgi ya kusa tashi kawai yaje da Sauri ya wuce ciki,ba a dade ba jirginsu ya daga.
Ina nan ina kewar Mijina,ranar kuma na fara ciwon Mara sama sama,yana sauka ya kirani a waya yaje lfy,cikin dare ma mun dade muna waya dashi,tunda Aayan ya tafi kullum sai munyi waya har ya cika 4days a can duk da haka ina dan jin Ciwon marar sama sama,yau tun asuba bayan nayi Sallah kafata ta rike na kasa tashi,Baba na shiga kwalawa kira iya karfina ta fado dakin da gudu tana lfy Hajiya? dake ta manyanta sai ta gano Haihuwa ce nan ta fita ta sanarwa Driver,Ita da Abu me aiki suka kamani zuwa mota Driver ya kaimu Private Hospital din da muke zuwa da Aayan,Sunce na kira Aayan nace a kyaleshi kar hankalinsa ya tashi,ciwo sai gaba yake yi Baba tana a fadawa yan uwanki da mijinki sai nace a'a bana son hankalin Mijina ya tashi,ciwo yana ci gaba duk na fita a hayyacina ban ma san me nakeyi ba nace a kirashi din Hankalinsa yayi ta tashi ina ruwana,ban dade ba Allah ya taimakeni na Haifo dana katon gaske Namiji kyakyawa, bayan an gyarani har wanka Baba me aiki tayi min na shirya,shima Jariri an shiryashi tsab cikin kayan sanyi farare masu tsada da kyau, Ameer na kira nace kar ya fadawa Aayan komai,Ameer na fadawa Yazo asibiti na haihu,15mnt sai gasu Shi da Meenat,addua da komai shi yayiwa jaririn,nima nayi masa Meenat ce ta koma gida ta shiryo min girki iri iri ta kawo lokacin anyi min Allurai ina bacci,Sai yamma lis na tashi naji karfi sosai a jikina ga yunwa na ci na,Abinci naci na koshi kamar ciki na zai fashe,Doctor tazo ta bamu takardar Sallama muka tafi gida gaba daya tare dasu Meenat,gidana muka je na kwaso kayana akwati guda dana jaririn da muka tara har gadonsa muka tafi gidan Ammah baki daya, sai ganinmu tayi da jariri,Murna takeyi kamar me,Daddy yana dakinsa ta kirashi ya dauki Jariri shima sai murna ga yaro kyakyawa kamarsa daya da Aayan,Nan Ammah ta dinga min fada ban fadawa mutane ba,har Aayan ta kirashi da kanta tana sanar masa yace Ammah shi yasa nayi ta kiranta tun jiya bata shiga Ashe bata da lfy bata fada min ba,Murna Aayan yace shi tahowa gida zaiyi ya fasa kaiwa sati guda,da kyar Ammah ta bashi baki ya hakura,su Hajja,Abbi da matayensu duk sai gasu,Maeesha me dan karamin ciki ita da Yarima sun zo suma,Su Hanifa Amare tare dasu Khaleel duk sun cika gidan Ammah ana ta hira ana Jin dadi.
Bamu muka samu Saukin mutane ba sai dare suka tafi sannan Ammah ta hada min ruwa na sakeyin wanka da kanta ta gasa min jikina shima Jariri anyi masa wankan an shiryashi cikin kayan baccinsa yana dan bed dinsa yana bacci,lotion na shafa me kamshi na shirya nima cikin kayan baccina lokacin masu aiki sun kara Gyara ko ina,zan kwanta Ammah tazo da abinci lafiyayyu tasa dole sai da naci da yawa nayi Brush sannan na kwanta,har bacci ya fara daukana Ammah ta shigo tana fada wai Mufeeda baki da hankali ne ko me kin kashe wayarki mijinki yana ta kira bata shiga kuma ke baki kirashi ba ko laifi yayi miki ko wani abu ne ya faru?bafa na son irin wannan ban son neman rigima,yanzu baki tambayeshi ba kin kwaso jiki kin dawo waje na,idan baya so fa? Da bamu dawo daga kasar waje ba wajen wa zaki?ai dole ki zauna a gidanki,bana son ki zubar min da mutunci a gaban suruki ki kiyayeni,kiyi Hakuri Ammah mantawa nayi yanzu zan kirashi,tsaki taja ta fice daga dakin,Da sauri na jawo wayata na kunna kana na shiga kiran Aayan na kira yakai sau biyar sannan ya daga Cike da bacin rai yace ina jinki ya akayi?
Naji haushin maganar amma ai nice da laifi sai nace barka da dare Yanlabai Allah ya taimaki ranka ya Dade Baban Baby,tuba nake nayi laifi Mijina uban dana a yafe min,duk wani fushi da Aayan keyi nan adtake ya yaye baki daya sai ma farin ciki da ya shiga yi na gama kashe masa jiki,yace ba wani kinyi laifi zaki min dadin Baki dama ai haka kike min kullum sai ki dinga cutata dan kin San ina da hakuri,Dariyar jin dadi nayi nace Hakurin da ka saba yi dani shi zakayi Dad din Baby, Hmm to ya jikin?dana ya fito lfy ko?cike da shagwaba nace da sauki bayan ya bani wahala kamar zan mutu ai ni fushi nakeyi dashi,Aayan yace dan Allah? Nace sosai ma dan kawai baka ji bane aka ce sai nayi nishi na daddage nayi daya yaron nan dake bashi da kunya yaki tahowa sai ya makale kafada yace bazai fito ba wai,Aayan ya sheke da dariya yace a ina kika ji sanda ya makale kafadar? Ina dariya nace a cikin cikina naji wani bangare yayi min bake bake wani kababa a nan na gano me yayi ai ko nace zanyi maganinsa na kara yi da karfin tsiya yaji na shakeshi da yawa yace zan dan fito shine ya taho kadan,Ina yin na hudu yaji wuya ba dadi sai ya fito yana tsala uban ihu,Dariya Aayan yayi tare da cewa to Alhmdllh tunda kin sauka lfy ai ba matsala,Duk abinda kuke so Na fadawa Ammah baki da prob nima jibi zan dawo Insha'allah,Ina Baby Boy dina da wa yake kama?nace gashi baccinsa yakeyi ma ko Na mintsineshi kaji Kukansa,da sauri yace a'a ko da wasa Karki fara,Dariya nayi nace kamarku daya baka ganshi ba wlh na iya haihuwa zukekene yan mata zasu dinga rubibinsa idan ya girma,Allah yasa ya samo min suruka ta gari kyakyawa kaga ya gaji Ubansa,dariya Aayan yakeyi sosai yanzu daga haihuwa har kin fara zancen Suruka,nace ae idan Meenat ta haihu nasan kyakyawa zata haifo ko Ma'eesha sai a bashi matarsa,Aayan yace baki isa ba babu me yiwa dana auren dole, sai ya Zaba ya darje, haka muka dinga musu,kaji yana motsi,Ko Nono yake son sha? Ya tambaya, hannu nasa na daukeshi ya fara kuka Aayan yana ji ta waya sai murna yakeyi baki yaki rufuwa nace bari na kara masa waya a kunne kayi masa magana,Jariri na kuka ni kuwa na manna masa waya a kunne Aayan kuma ta waya yana Hello My Son,Dad dinka ne,Abbanka ne Be quite yaro bai San me akeyi ba,na shiga bashi Nono yayi shuru kuwa muna waya da Aayan.
Yace muyi video call haka na kunna light na kirashi ta Skype muka fara Video call yana ganinmu ni da jariri,muna ta hira cikin Jin dadi mun dade sannan muka rabu da juna muka fara baccinmu cikin nishadi,washe gari ma haka gidan ya cika da yan Uwa da abokan arziki,kamar ba ni na haihu ba haka nake shiga cikinsu muna hira ga waya Aayan ya Dameni da ita muntuna kadan zai kira yaji ya muke muna haka har na kwashe Kwana hudu da Haihuwa tunanina ma sai bayan suna Aayan zai dawo tunda naga an kusa, 8pm Ammah tayiwa Jariri wanka tare da shiryashi tsab cikin kayansa masu kauri da kyau nima na bashi Nono ya koshi yana yin Bacci na kwantar dashi saman Bed dinsa nima nayi wanka nayi shirin bacci kamshi ne kawai muke zubawa ni da jaririn,Sallamar Aayan naji ya turo kofar bayansa kuma mata masu aiki ne suka shigo da Akwatuna har uku suka fita,wani sanyin dadi ya kamani naga Rabin raina ya dawo yanzu zan na ganin abina a kusa,Cike da murna ina zaune tsakiyar Saman bed nace Oyoyo ina murmushi ga wani Mashahurin kyau dana kara sabo da samun kulawa,Kallona yakeyi tun daga sama har kasa kamar ba nice na Haihu ba sai ma kyau da na kara,Saman Bed din ya hauro ya bani zaffafar Runguma da Kiss sannan ya Koma gadon Jariri dake bacci ya daukeshi yana zuba masa adduoi,Sai da ya gaji sannan Ya kwantar dashi daga bisani ya shiga wanka,Ammah ce ta kirani a waya wai naje kitchen na dauko masa Abinci,Mamaki nayi wai Ammah Ashe tasan Aayan zai dawo shine ba wanda ya fada min har ta masa Abinci da kanta,Kitchen na shiga abinci na Alfarma na gargajiya dana zamani Ammah ta gama shiryawa na dakko masa komai da kayan sha masu sanyi, bayan yayi shirin bacci ya zauna dirshan yaci yasha,yace shine baza ki bani a baki ba?nace na sani ko zakayi kyankyami na kasan wasu kyankyamin matarsu sukeyi idan ta haihu,Fuska ya bata ke ni zaki bata min rai ke zanyi kyankyami?kin Zama jinina fa bana son irin maganganu nan ko ni Bahaushe ne? Yi hakuri na daina,Brush yayi yasha Ruwa sannan ya kashe Light ya kwanta gefe na,Nace Ammah fa zatayi fada,wa yace ki dawo nan? Kin fada min zaki dawo ko kin nemi Izinina? Kince nan da can dayane to mene ko dan kin haihu sai akace miki kar na kwanta Bed daya da matarsa? a'a amma ai ni dai Allah tsoro nake ji,shuru yayi min da kaina naga kamar baiji dadin maganar ba sai na juya na rungumeshi kamar jira yake ya makalkaleni a jikinsa muka Sha baccinmu.
Kwanci tashi yau ranar suna Ammah ba taron Suna Aayan dan Ahlul sunna ne ba a taron Suna yace a masallaci yaron yaci Sunan Abbanmu Abubakar Saddiq Aayan yayi min kara naji dadi,haka Ammah dasu Meenat har godiya muka yi masa,Fhadeel muke ce masa.
Bayan 1mnth Aayan ya kaini Hospital aka bamu shawara na family planning shi baya son Haihuwa kamar tattabara duk mace ta ragargaje ta fita daga hayyacinta sabo da kwanika a samu ciki kafin a yaye daya ya Kamu da cuta ga na ciki ba a da tabbas zaizo da rai,Da kyar ya barni muka zaga dangi yan Uwa da abokan arziki munje har Maiduguri da Kauyen su Ammah,gidajen frnds duk munyi Zumunci tare dasu Meenat.
Gidanmu gaba daya ya canja komai na gidan da kyar ake ganewa ya kara tsarashi,Direct mukayi Sallama da kowa muka dage zuwa Us daga can zamuje aikin Hajji mu kuma zaga wasu kasashen tare da jaririnmu Fadeel.
Ma'eesha ciki yana ta girma ya shiga wata Bakwai,Yarima da Ummansa suna ji da ita kusan ma a gidan su Yarima ta tare gaba daya tare dashi suna soyewa watarana Umman ta koresu idan suka dameta,Abban Yarima kuwa Bai cika Zama a kasar ba sai lokaci lokaci yake zuwa ko matarsa ta bishi can, yanda Yarima ke Lallaba Ma'eesha har yayi yawa ta gama sangarcewa dake ya nemo mata Wata Private University tana karatu kusan tare suke karatun ma har ta gama level 1 idan sun dawo Hutu zata shiga level 2,Yayin da Meenat ta gama level 2 zata shiga 3,ni kuwa ina Zero level sai mun dawo Aayan zai kaini wacce yaga dama komai a karatu jaraba nice a karshen baya ina takaicin wannan abu amma haka Allah ya tsara ya zanyi.
Meenat ce kwance saman Bed tayi shirin bacci Ameer yana kasa jikin Bed yasha shirin bacci sai rubuce rubuce yakeyi na Office kafin gobe sabo da Aayan ya bar masa aiki,juyi Meenat tayi ta kara juyi ta matsu yazo su kwanta,y ana jinta sauri yake ya gama yasan Halin Meenat yanzu zatayi zuciya da kyar zai lallasheta ta hakura,bai karasa ba ya hakura ya Mike tare da kwanciya a gefenta gani yayi har tayi baccin karya wai dan kar yace ta damu dashi,Shuru kowannensu yayi kawai shima yayi baccin karya kamar da gaske,Meenat taji shuru ko hannunta bai rike ba,fuskarsa ta leka ta shiga mamaki ganin yana bacci a fili tace bacci yayi a wannan situation din da ni Meenat kamata ina kusa dashi bai ji komai na feeling ba ya fara bacci,Kwanciya tayi a fili ta kuma cewa ko Hannu bai iya rike min ba ina kusa dashi wannan me ya faru ko ya daina sona ne?wayyo karfa ko wata ya hango Ameer yana jin Meenat tana surutunta dariya ta cika masa ciki,shuru tayi ta rufe ido ta bude taja dan tsaki sannan ta kara rufe ido itama,cikin nutsuwa da muryarsa me dadi taji yace ya akayi My love? Na isa Hamshakiya tana kusa na kasa tabata a hankali ya sa hannunsa cikin nata ya juyo tare da hayewa samanta a hankali ya shiga matsawa da fuskarsa hancinsa yana Gogan nata ya hade bakinsu waje daya ya fara tsotsa kamar zai cinye bakin ya huta,hannayenta ya rike da hannayensa ya maida su saitin kanta ya bankareta kamar me shirin yi mata fyade Meenat dadi yana ratsata a hankali ta zare masa riga tana shafa shi ta ko ina musamman kirjinsa Nishi kawai sukeyi Sweet words na tashi daga bakunansu,Basu gama gigicewa ba sai da ya shiga Murza Albarkatun kirjinta yana shansu Meenat kamar wata me shirin hawa Bori Gogan kuwa ka rantse Aljanune bakake dashi masu Zafi suka motsa kusan raba dare sukayi suna jiyar da juna dadi kafin su sararawa Kansu basu ma San sanda bacci ya kwashe su ba.
Cikin Ma'eesha ya shiga wata tara Haihuwa ko yau ko gobe,Wata ranar Juma'a ta fara Nakuda aka kaita asibiti kamar zata mutu Yarima ya dinga Kuka ana bashi hakuri yan Uwa da abokan arziki jiki yayi Sanyi asibiti ya cika ana tunanin da kyar Ma'eesha ma zata tashi,muna Can Russia dama Saura 1wk mu dawo Nigeria Meenat ta fada min tana kuka,da sauri Aayan ya hada mana komai muka sauka a Nigeria,Asibiti muka wuce muna zuwa tana Haihuwa ta santalo Danta Namiji katon gaske kowa ya kalli jaririn yasan ansha wahala kafin a haifeshi,sai ga Ma'eesha ta farfado aka gyara ta da jiriri tare da canja musu daki,Yarima ya riga kowa shiga yana kuka idonsa ya koma red sai yaga Ma'eesha tangargar abinta,Munsha murna muka koma gidanmu mukayi baccin gajiya,gaskiya Aayan yana kashe min kudi a duniya ba abinda na nema na rasa,sutura kuwa ko matar shugaban kasa sai ta jinjina min, Fadeel ya girma yayi wayonsa gwanin sha'awa kamar dan Bature jajir dashi.
Yarima bakinsu daya da abokinsa Aayan shima ba a bikin suna dan ma kar a damesu sai ya dauke Ma'eesha da Jaririn suka hau jirgi zuwa Cairo wai sun tafi hutawa suna can akayi yanka aka radawa yaro Suna Ashman,acan Cairo sukayi jegonsu yana kula da abarsa,basu dawo ba sai da suka kwashe 3mnths lokacin Meenat a fara laulayi sosai,cikinta wata hudu,Duk inda Ameer yayi tana tare dashi Har masallacin juma'a tare suke tafiya tayi sallah cikin mata ta jirashi a mota,Ko taki binsa sai ya matsa sun tafi tare wai kar ya barta ita daya a gida tana laulayi,Ammah tayi fadan har ta gaji,ni ko Aayan ya samomin private university a Abuja can zamu koma dashi gaba daya mu da kano sai dai muzo Hutu,Daddy yace bazai yuwu ba sai dai mu dinga zuwa akan lokaci baya so mu tafi mu zauna ba zumunci.
Na fara lecture da wata biyar matan su Khaleel duk suna da ciki haka Su Hanifa ma an kusa Haihuwa, tuni anyi bikin Sabeer da Meenal,Aliyu da yar uwarsa shima, Meenat ta Haifo yarta mace kyakyawar gaske, Su Ameer har Dinner akayi hadaddiya a katafaren waje yan AsmaBaffa Fans club duk sunzo,Kasuwancina true fans duk gasu nan anci an Sha an cashe yarta taci Suna Fadeela.
Bayan Sunan Meenat muka koma Abuja ni da Aayan sai ga Kiran Ma'eesha wai Ammah ta samu ciki,Kunya ta kamani na saki Salati Aayan ya sameni na zuba tagumi.
Meenat kuwa harda rawa Ammah zata haihu,Hajja ma taji labari sai murna takeyi,Ammah kunya takeji wai Yayanta na haihuwa itama haka,Daddy yafi kowa kamar zaiyi hauka Sabo da Murna ya rasa inda zai Sa kansa.
Kwana biyu bana muku posting kuyi hakuri kawai gajiya nayi sam ban son Typing din shi yasa bana yi akan lokaci kun san Jiki da jini dan Adam ajizi ne sai Hakuri.
AsmaBaffa
[3/6, 10:54 AM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
151-160
Official
By
AsmaBaffa
FINAL
Daddy murna tasa ya rasa inda zai sa Ammah yace sai ta zabi abinda takeso a duniya yayi mata taki fada wai ita kunya,Hajja tunda taji cikin nan ta kara son Ammah kusan kullum sai tasa an kawota a mota ta duba lafiyar Ammah,h aka ni dasu Meenat ko yaushe muna hanya nice ma ban cika zuwa ba sabo da nayi nesa dasu ina Abuja,Aayan ya Kira Daddy a waya yace Congrat Dad, Daddy ya shiga dariya yana godewa Aayan da ya matsa lallai akan a auri Ammah gashi ya Zama alkhairi.
Meenat yarta Fadeela tayi dan wayo kadan,Yarta ta shirya ta kawo mata ita gaskiya Fadeela tana da kyau ta hadu karshe,tsakanin ita da Fadeel dina ban san ma wa yafi wani kyau ba,Ameer ne ya fito cikin takunsa yasha wankan wani farin yard ba karamin kyau yayi ba,mikewa tsaye Meenat tayi tare da cewa Ina kuma zaka fita da yamma haka? Sarkin kishi ba inda zanje Aayan ne ya aikeni gidanmu yanzu zan dawo,to muje tare mana ba musu yace shi yasa kika shirya kema kenan dakko mayafin mu tafi,Ba musu ta dakko harda jaka da takalminta me tsini ta bishi suka tafi shi ya dauki Fadeela yana mata wasa,bayan sunje gidan suka ji Matar Mujaheed ta haifi mace,sunje sunyi barka suka wuce gidan Ma'eesha a can har dare suna gidan,sai 9pm suka dawo gidansu Meenat ta shirya Fadeela tare da lallabata wai tayi bacci lokacin Ameer ya fito daure da dan Towel fari a kugunsa yana goge jikinsa da wani karami gefen Bed jikin Meenat dinsa ya zauna wacce ke aikin jijjiga yarta,ki bata tasha Milk dinta mana sai ki ta wani mata wayo a haka yarinyar nan bata wani koshi da Nono kike hanata,ko na baka ita ka bata naka ne maybe zata fi koshi,Murmushi yayi tare da cewa ba sai kin fada min baka ba,kuma kema kin san da ina dashi har amai sai ta dinga yi yanda zan na cika mata ciki,ga Fadeel nan Har ya fita kiba,ai dama to ya girmeta yaro zaka ce wani abu,Nine yaron? Kalli yata katuwa,Fadeela taki bacci kawai ta zuge zip na rigarta ta fara bata Nono tana sha,Ameer har ya tashi ya nufi Wardrop ya dawo ya zauna shi burinsa yaga ana bawa jariri nono yana sha abin birgeshi yakeyi,Sai kallonsu yakeyi kamar maye,A hankali shima ya kwanta saman cinyarta ba shiri ta matsar da jaririyarta shima ya kwanta kadan,tana taje mata gashinta bata san me yake ba babu zato taji shima yana zuke daya Breast din kamar maye,da Sauri ta gama bata ta gyara rigarta tasan Halin Ameer sai ma ya shanye du ya zuke mata nutrients dinta.
Bayan wata Uku cikin Ammah ya girma sosai zama da kyar Sabo da cikin yana bata wahala, ina gidan Ammah Aayan yazo daukana muna cikin mota ya bani shawara Honey tunda naga kinyi dan nisa a karatun kuma gashi an kusa yaye Fadeel me zai hana a daina planning din kafin ki samu wani cikin kinga an yayeshi tuni,sai mu kara Haihuwa Allah shi ke rayawa Amma baza mu zauna ayi ta planning ba tunda bamu ke da kanmu ba ya kamata ace nima na tara Yara ko Uku ne sai ki huta da yawa,ko dan lafiyarki ma idan mace tana Haihuwa tafi lfy ko? Fuska na bata nace banfa gama karatu ba,ni gaskiya ko zan haihu sai na kara 3yrs sai na daina planning kaine fa kaki kaini schl da wuri yanzu kuma ga schl ga ciki ni Bazan iya ba,Baki ya bude Yanda yaga ina masa masifa daga kawo shawara yace Iyyeee lallai kinci abinci Mufeeda ke kike aurena ko ni? Kinga ina biye miki zaki rainani dama ance mata basu san kadan ba idan kana biye musu sai su fara rainaka suna takaka,Shawara fa na bayar baza ki fada min direct ba kema a shawarce zaki fada min sai a gane a dauki wanda ya fi dacewa yanzu ma Umarni kika bani sam ga abinda zakiyi ke kinje University ko?kuma ni zaki ma shouting kamar danki? Ransa ya baci sosai Amma zuciyata bata kawo komai ba sai ma cewa nayi Oho ni dai Bazan yi wani ciki yanzu ba,duk wahalar da na sha,kasan zafin haihuwa kuwa dole kace haka,a hasale yace Ok to zamuga me iko tunda kikace haka na fasa shawarar Haihuwa nake so kuma dole a daina Planning ai ni naga dama.
Ni da jikina sanda zanyi ma ka sani ne,har muka karasa gida cacar baki mukeyi har ya shareni kowa ya fita daga motar a fusace,ko dakinsa banje ba nayi kwanciyata a dakina,shima haka Amma gaba daya tunaninsa nakeyi kuma nasan shine da gaskiya kawai neman fada ne irin nawa,Kowannenmu da kyar ya samu bacci ya daukeshi,ba abinda yafi damuna irin yanda ya daina cin abincina,ya daina kula ko kallo ban isheshi ba har muka kwashe 1wk a haka kullum sai nayi kuka na godewa Allah,yau nayi niyyar bashi hakuri naga ya sakko yana jan Trolley yasha kana nan kaya masu tsada da mugun kyau,ba karamin kyau yayi ba kamar a saceshi,sai dai da gani yana cikin damuwa,bai ko kalleni ba ya nufi wajen Fadeel dake kwance yana wasa yana wutsil wutsil sai dariya yakewa Aayan yaga Babansa,ina kallo ya daukeshi suka danyi wasa sannan ya kwantar dashi ya sa masa farar takarda a hannunsa ya rike kam sannan yaja akwatinsa ya tafi,gabana ya fadi sosai yana fita na karbe takardar da Sauri na bude an rubuta gabana yana faduwa nasan ko bai sakeni ba to sai ya ci min mutunci a ciki ga abinda na gani a rubuce:
Na tafi Saudiya Nextwk zan dawo Insha'allah Bazan dawo nan ba Abuja zan wuce idan kun gama sanda kika ga dama ki koma schl,ke wato baki da kunya tsagera ce ke ko? ki tabbatar kin Daina planning din nan kafin na dawo ciki zan miki Sabo ki Haihu,Yarinya ba a Isa da ke ba sai rigima iri iri.
Love u,am gonna Miss u Darling bae.
Ina gama karantawa ban san sanda Hawayen farin ciki ya zubo min ba,ina dariyar jin dadi Kaji fa manya,masu Ilmi da wayewa,ba a fada ayi ta gaba ana fushi a kullaci mutum a zuciya,komai cikin ilimi akeyinshi ba irin mutanenmu ba,a fuska mutum ya nuna baya jin haushinka ko ka bashi hakuri yace ya hakura sai ya dinga gana ma azaba iri iri sai ya rama abinda ka masa,wasu kuma abu kadan sai a maida shi babba ayi fushi,baza a danne zuciya a hakura ba,ga Aayan duk yanda na bata masa naki bashi hakuri na daina zuwa dakinsa bai Sa yayi fushi dani ba,sai ma ya maida abin wasa,ni da kaina naji kunyar kaina,naji ban kyauta ba,kuma ko yanzu nasan Aayan ya gama wayewa ya nuna shi me Ilmi ne ba irin wasu ba ga Ilmi Amma Jahili ya fisu hali me kyau,gaba daya naji Bakin cikina ya yaye,nan take na jawo wayata da Sauri na danna Number dinsa,lokacin yana Airport ana screening bai samu damar dagawa ba,sai Text na tura masa ga abinda nace:
Allah ya kiyaye Hanya Mijina,Allah ya kaika lfy ya dawo mana da kai lfy,kayi hakuri ka yafe min a bisa bijirewa Umarninka da nayi,na tafka kuskure dan Allah ka yafe min My Man,Fadeel yana gaishe da Abbansa.
Love u much more Dear,already started Missing u My Husband.
Yana ganin sakon ya cika da farin ciki marar misaltuwa gashi har anyi solving case din,dama fushi ko masifa ba lallai su kawo gyara ba.
Tunda ya tafi yaki yarda muyi waya dashi sai text kawai kullum ba adadi,Kwanansa biyar nayi booking flight muka koma Abuja na shiga gyaran jiki ba ji ba gani zan tarbi Ango na.
Sajeeda ta Haihu da sati Biyu matar Khaleel me sabulu ma ta sauka lfy duk Maza suka haifa,yayin da su Sabeer suke kwasar Amarci,Sameera ma ta haifi mace tuni.
Lokacin kuma Daddy da Ammah sun tafi Us wai acan zata Haifa masa dansa ko yarsa.
Meenat uwar yan shiga kitchen yau ma tana kitchen tana girki Fadeela na Rarrafe ta biyota kitchen din Ameer ya shigo cikin 3qtr da yar t-shirt yau a haka ya fita ya dawo Sumar nan ta kara yawa yanzu ma yake ji da daukan wanka,Fadeela tana ganinsa ta dinga washe yan hakoranta wai ya dauketa tana mika masa hannu,Meenat tace wane ke yarinya sai ya fara da Uwarki tukun,dariya Ameer yayi ya fara Huging din Meenat tare da dagata Sama ya direta suna dariya har Fadeela kamar ta san me suke itama ya dauketa yana mata rawa tana dariya gwanin sha'awa,
Ameer Tafiya yayi da yarsa har wanka shi yayi mata ya shiryata cikin kaya kanana masu tsada da kyau har kwalliya yayi mata harda jambaki,shima yayi wanka ya dakkota suka fito Meenat tana ta dariya yanda ya mata kwalliya harda Jambaki kuma tayi kyau,Meenat tace Babyn Fadeel ce ai wannan,Ameer yace na bashi ita ma sukayi dariya,suna cin abinci na kira Meenat a waya nace zan kawo Fadeel yaye wajenku,Meenat tace Sister Kukan dan yaye nake tsoro wannan yaron naku miskili ga masifa yazo yana hanamu bacci wlh wajen Hajja can zamu maida shi,dariya nayi nace koma ina ne ku kaishi kawai,kwana Uku na sanarwa Aayan na masa text baiyi musu ba na shirya Fadeel da kaina nabi Flight na kawoshi gobe Aayan zai dawo,lallai aka tsantsara min gashi naci gyaran jiki ina sheki na koma Abuja da dare,washe gari na shirya abinci iri iri ina jiran isowar Aayan dina,Meenat ta kirani tace abin mamaki Sis ko kuka Fadeel baiyi ba kamar nice Mamansa kuma yana cin komai ko nono sau biyu ya nema na bashi milk shike nan Amma fa Fadeela tana cin duka a hannunsa,Dariya mukayi gaba daya tana bani labarin Fadeel.
Wanka nayi na shirya cikin fitted Gown Black and Golden color Ready made ce tayi kyau,kamar Wata balarabiya haka na fito,Gidana da jikina kamshi kawai yakeyi ina cikin gyara fuskata naji dirin Motoci nasan ma Aayan ne ya dawo,palo na sakko na tsaya jikin kofa ina jin Door Bell na bude da murna,dukul na tsaya ganin Ma'eesha da Yarima tare da Ashman dinsu,Daga ina kuke haka yanzu ko waya babu ku shugo ina murna,suna shigowa sai ga Aayan ashe yana bayan Yarima ban san dashi ba na juya baya naji ya rungumeni kamar zai maidani cikinsa,cike da murna na juya na kara makaleshi ina murna na bashi kiss a lips mun dade a haka yana kare min kallo,ga Lallena ya tafi da Imaninsa,a kunne ya rada min Abban Yarima ne ya turo shi Abuja zai masa Wani aiki na 1wk anjima zasu tafi gidansu ziyara suka kawo mana,a kunne nima na rada masa na gane yanzu muje kayi wanka kaci abinci,Yarima suna Palo basu san ma me mukeyi ba,Maeesha tace yunwa mukeji mu dan Allah kizo ki bamu abinci,Hanyar Sama Aayan yabi ni kuma na shiga kitchen na shirya Dining komai da Komai Yarima yace to mu baza mu jira ku ba ci zamuyi,dariya nayi nabi bayan Aayan lokacin ya shiga wanka.
Da kaina na shirya Mijina na bashi yaci ya koshi nima haka,bayan munyi Sallar Isha Yarima ya dauki matarsa da dansa suka tafi masaukinsu,Suna Tafiya Aayan ya jawoni jikinsa,nace jibi Allurar da akayi min date zai cika kaga ba sai mun kara yi ba tunda Haihuwar kake so,Murmushi yayi sannan yace ai ba yanzu nace ba daga yayewa sai an kara kamar ta 3mnth sai a bari,dadi naji sosai ina masa godiya ina bashi hakuri, bakinmu ya hade waje daya muka shiga sarrafa juna kamar ba gobe,kusan kwana mukayi muna abu daya gaskiya baza mu manta da daren yau ba mun jiyar da juna dadi wanda bazai misaltu ba.
Bayan wata Uku Ammah Haihuwa ko yau ko gobe tana shan wahala a Us Daddy kuwa ji yake da ita kamar itace wacce ya fara aura a duniya,Wata ranar asabar Ammah ta tashi da Nakuda suka tafi asibiti tare da Daddy kamar jira akeyi suna shiga da 5mnt ta Haifi Namiji kato kyakyawa 15mnt tsakani wata sabuwar nakuda ta kama Ammah ta Haifo Mace ta biyu,Yayanta biyu ta Haifa manyan gaske Namiji da Mace abin sha'awa,Tunda labari ya iske mu muke faman Murna,Babu wanda bai taya Ammah Murna ba,sai a Pics da video call muka gansu gwanin birgewa,ranar suna Aka Sa musu Hameed da Hameeda.
Sai da Ammah suka kwashe 2mnths yaran sunyi wayo sannan suka dawo gida,tattarowa mukayi da Aayan muka zo Kano munsha kallon kyawawan yan biyu,Aayan yayi kanne muma munyi kanne abin murna Fadeel dina ya kara girma da wayo yana yawonsa ko ina,Haka Fadeela ta Meenat tana Tafiya Ashman din Yarima sun saba Sosai da Fadeel.
Su Khaleel dasu Haneefa duk da yaransu dagwas dagwas kowa na ji da gayu,Matan su Sabeer ma sun kusa Haihuwa abin ba a cewa komai Zuriyar Hajja tana yaduwa Babban abin farin cikin Family din duk sun gyara halayensu,Hajja tafi kowa Murna da hakan sai dai lfy bata isheta ba jikin tsufa yau fari gobe baki.A mmah ta dakko Inna da wata Kawarta sun dawo Kano gidan da Yarima ya siya mata tace su zauna a ciki suma.
Bayan Shekara Biyu tuni Meenat ta gama Degree dinta ita da Ma'eesha,nima ina daf da gama nawa,lokacin Na kara Haihuwar yata mace sunan Umman Aayan taci Amma muna ce mata Royal Angel,haka Ma'eesha ta Haifi Namiji again Fhudal,Meenat ciki ne da ita kawai bata haihu ba,Su Hanifa ma daga me ciki sai wanda suka kara Haihuwa.
Bayan 1yr na gama Degree dina mun dawo kano yanzu hutawa muke zuwa Abuja kawai lokacin Ammah ta kara Haifo Namiji kato sunansa Muhsin.
Meenat ce kwance ita da Fadeela da Danta Ahmad dan karami sunyi rubdugu a jikin Ameer yana aikinsa a System duk sun Hanashi yi har bacci ya kwashesu duk suna saman cinyarsa,Meenat tayi matashi da kafadarsa Allah yasa sunyi shirin bacci,Saman Sofa ya kwantar da Meenat sannan ya dauki Fadeela ya kaita Bedroom ya kaita tayi fitsari sannan ya sa mata sabuwar Pampers Sabo da tsaro ya kwantar da ita saman dan Bed dinta dake jikin nasu,Jariri dan 4mnths ya dakko shima a shirye yake kawai dan Bed dinsa shima dake jikin nasu ya kwantar da shi,Wasu suna gangancin saurin Barin Yara su kadai a dakinsu wai gayu ko ace haka turawa sukeyi wani abu ya samu Yara kina can kuna bacci,ya kamata ana dan bari Yara suna kara dan girma da wayo, ko kuma a hadasu da Nanny suna kwana tare wannan duk bai dace ba a dinga bari Yara suna wayo kafin.
Ameer wajen da Meenat ke kwance ya je ya koma ya dakkota kamar Jaririya itama ya kaita saman Bed din su kato ya shimfidar da ita zai bar saman Bed din yaji hannayen Meenat ta sakalosu ta wuyansu tare da jawoshi ya fado kanta ciki mayen bacci tace Dan Allah mu kwanta ka hakura da aikin nan tunda kayi shirin bacci,Ok ai dama yanzu time dinki ne sakeni na dawo,Kayan wuta ya kashe ya dawo suma ya kashe musu light suka kwanta bayan yayiwa yaransa adduar bacci,Meenat ta shige jikinsa Ameer ya canja Salo na daban,bata san sanda ta biye masa ba suka Tsunduma a tafikin so addua dauke a bakinsu.
Ammah dai tun daga wannan Haihuwa guda uku Allah ya yaye mata bata kara Haihuwa ba.
Ma'eesha tana kitchen tana shirya girkin dare Ashman shuru ko motsotsinsa ba a ji ashe yana Palo Computer din Ma'eesha yake wasa da ita ya fasata yayi mata kaca kaca,ya dakko Handrier ma nata ya fasa,Body Cream ya kwaso yayi faca faca dashi a jikin kaninsa dake kwance wai shafa masa yayi,Maeesha ta fito kenan tayi arba da abinda yakeyi,takaici ya rufe ta tama rasa me zatayi masa, ai kawai sai ta fashe da kuka taga ta kanta zai gudu yasan yayi laifi ta cafkoshi tare da cire takalminta daya ta masa Flat ta Zane masa Duwawu yana ihun Kuka sai Dad yake kira,Suna haka sai ga Yarima ya shigo da Sauri kamar zai tashi sama yana masifa ya karbe Dansa yana tambaya lfy? Ma'eesha tace kalli kalla pls abinda yayi min gwara ka bani shi na ballashi,Harara Yarima ya zabga mata kuma shine zaki dukar min yaro karki kara taba min dana,ki fadi kudin na biyaki,ban hana ki masa hukunci ba ko ki masa fada Amma ban son duka kina masa kuka so kike ya lalace Uwarsa na zubar da Hawaye a kansa,yaro ai ba a masa fada ta haka,Nasiha zaki masa,ko zaki dakeshi ba irin wannan ba,kaima idan ka kara lalata abu a gidan nan Tiger zan siyo ta cinyeka Oya bata hakuri,da Sauri Ashman ya durkusa kasa yace kiyi Hakuri Mummy na daina,Maeesha bata ce komai ba ta dauki Danta ta sake masa wanka ta shiryashi,me aiki ta gyara wajen da komai,Maeesha yau sai fushi takeyi sai da Yarima yace zai siya mata duk kayan da dansa ya fasa sannan ta dan hakura kadan,Da dare ma fushi takeyi kuma da Yarima take fushin,Suna kwance da yayi niyyar riketa sai ta matsa gefe,da Sauri ya fisgota ya hade bakinsu ya shiga Tsotsa yana lallashinta tare da fada mata Sweet words har ta sakko ta Bada kai Bori ya hau.
Alhmdllh Family da kowa ana zaune lfy cikin so da kaunar juna,ba wani fada etc,ga zumunci anayi ana zaman lfy da kowa,Haka kawaye da abokan arziki lfy ake rayuwa dasu,gaskiya kowa ya gammu sai yayi sha'awa bamu da wata matsala.
Wanka Aayan yasha cikin wata Shadda light blue me matukar kyau da tsadar gaske dinkin zamani fitted na Maza,sai kamshi yake ba karamin kyau yayi ba kamar a saceshi yaro yake kara dawowa,fitowa nayi daga Bedroom dina sanye cikin wasu kana nan kaya ba karamin kyau nayi ba,jean Black da t-shirt white and Blue gashina yasha gyara sai sheki da kamshi ke tashi a jikina,Magan nayi cike da Salo na lankwashe Murya kana nace My Man ba dai fita zaka yi ba? a hankali yace ae gashi ma almost 9pm,Dan Allah ka fasa muyi hira ka dan jira na gama abinda nakeyi na dawo na kula da kai bana son fitar nan taka kaji My Man na karasa cike da shagwaba,tsigar jikinsa ta tashi yaji wani yarrrrrrrr wanda yasashi komawa sama kawai ya fasa fita,Baba Me kula da Yara ta kawo minsu ta gama shiryasu gwanin sha'awa yan gayu a gidan yan gayu,iyayensu ma yan gayu,Fadeel yana bina a baya ina dauke da yata mace muka haura Sama,Fadeel da gudu ya fada jikin Aayan ya wani kwanta mala mala sai tumurmusa Aayan yake yana Ihun wasansa,Bari Fadeel bana son shirmenka sauka ka tafi dakinku wurin Baba sai tsalle kake min a Bed sai ka lalata min Bedsheet,Aayan yace kaji Me Mummy tace,Kafada ya makale shi a nan zai kwana dama da gadonsa kawai na dakko na danna abu sai ga Bed din Fadeel ya bude ya Zama gado na Yara hadadde, jeka kwanta kuma kayi bacci ban son wasa,kwanciya yayi itama Kanwar Fadeel Angel na kwanta na daura ta saman cikina tana bacci,Aayan duk hankalinsa ya tashi shigar dake jikina da kamshina ya gama ruda shi,matsowa yayi jikina a hankali ya rada min a ajiye Baby girl din nan a bani lokacina Honey,Nima a hankali nace kasan dai Fadeel baccinsa baiyi nisa ba,dan Allah tashi ki duba idan yayi bacci ki kaishi dakin Baba,Kwantar da Royal Angel nayi saman Bed dinta,Aayan yace tsaya na kaishi da kaina ya furta yana dauke da Fadeel ya kwankwasawa Baba ta karbeshi tare da kwantar dashi,har dakin ya shiga da kansa yayiwa Fadeel adduar bacci sannan ya fito yana Yiwa Baba sai da Safe.
Kafin ya dawo nayi shirin bacci na Angel tana bacci abinta nayi mata addua shima Aayan yazo yayi mata tasa sannan ya hauro Saman Bed,Direct Samana ya haye ya sani a corner ya shiga Kissing din Goshina,saman hanci na,zuwa lips dina da wuyana,duk ya rude ganin Albarkatun kirjina sai kara kyau sukeyi basu da alamar zubewa kamar ban taba shayarwa ba,muryarsa na rawa yace I love u My life,kullum sabuwa kike dawowa Darling,Kaima haka Darling Bae Bazan daina Sonka ba bana gajiya da kai,ajiyar zuciya muka saki a tare lokacin da yake shigata dauke da addua a bakunan mu,Ba abinda mukeyi sai Nishi da Kukan Dadi Kalamai masu sanyi da gardi suna fita ta ko ina sai da muka tabbatar mun raya wannan dare wajen daffaka Sunna.
Aayan sai addua yake min yana Sa min Albarka nima haka a zuciyata ina alfahari da samun miji irin Aayan samun irinsu sai an tona,ba abinda na nema na rasa shi yasa ko aiki bama yi na Gomnati ko Company komai mazajenmu suna mana kuma muna godewa ba hadama da son zuciya.
Mun kara gogewa mun zama matan attajirai masu ji da kansu kowa ya kallemu sai ya koka musamman ni yanda ba a magana ma,fadar yanda na koma bata baki ne,ko yaushe mune Abuja,Saudiya,Us da Sauran kasashe muna zaga duniya,M otoci sai wanda muka ga damar hawa Ameer mota har biyu ya siyawa Meenat,Maeesha ma haka ni kuwa sai yanda nayi da motocin Ogana,yace zai siya min nace motocin sunyi yawa haka iya na gidan sunfi kala goma na alfarma.
Muna taimakawa na kasa damu da dangi abokan arziki sosai muna taimaka musu har Alummar Musulmi indai munga wani a wani Hali sai mun tallafa musu, gaskiya Allah ya zuba mana baiwar kyau gaba dayanmu dasu Meenat sai ka rasa wacce ce tafi Haduwa ma,muna kashe wanka.
Bayan wuya sai dadi haka Allah yake ikonsa baka zama wani sai ka sha wahala,idan akayi hakuri komai sai ya wuce kamar ba ayi ba,dama rashin hakuri shike jawo barna iri iri,wani kullum cikin rana yana neman na Halak bai samu ba,wani sai kaga Bai shiga ranan ba Allah ya bashi ya kara masa,kyauta ce ta Allah,wani kullum addini yana bin dokokin Allah sai ganshi bashi da cin yau bare na gobe Ammah sai kaga me sabon Allah gashi attajiri na gaske,Sai ayi Hatsari kaga Malami me tsoron Allah yayi kaca kaca ya rasu ka Hango Karuwa a gefe can tana cin chewgum dinta ko rauni bata ji baπ
π
haka Allah yake ikonsa,duk halin da ka tsinci kanka ka gode masa,sannan aci gaba da addua karki ga Mufeeda da Aayan tare dasu Meenat kamar Allah ya basu komai na duniya kice kema sai kin dawo haka,kowa da Kaddarar Sa kowa da jarabawarsa kuma questions na kowa daban ne idan kikace zaki copy jarabawar wasu to zaki fadi Zero Katon kan jaki zaki ci π
Sabo da ba questions dinku daya ba kowa da kalar nasa wani yafi wani,kuma bawai Su Mufeeda za ace shikenan baza a kara jarabtarsu ba no zasu ci gaba da karbar jarabawa daga Allah sai ko in su samu me sauki.
Aayan karki ga me kudine da lafiya ga kyau kice kema dole irinsa zaki samu ko mijinki sai ya dawo Ameer ko Yarima π
duk Halittace ta Allah sai kiga dan Mummanki yafiye miko ko wanne namiji a duniya Halitta ce ta Allah kuma kowa yana da tasa baiwar ta musamman,mata a kara hakuri da juriya sannan mu kara jajircewa wajen kula da mazajenmu tare da tarbiyyantar da yaranmu.
NAN ZAN AJIYE ALKALAMINA NA KYALE SU MUFEEDA HAKA.
ALHMDLLH da Allah ya bani dama da ikon kammala wannan Novel,ina matukar Godiya gareku masu kaunar wannan Novel,ina jinjina ga masoyana kaf duk a inda kuke ina kaunarku da wanda na sani da wanda ban sani ba,Masu kirana ta waya,text etc na gode Allah ya bar zumunci.
Ina neman Afwarku na rashin karasa muku Novel da wuri da banyi ba na samu kaina da rashin son Typing da fatan zakuyi hakuri ni kaina ban so hakan ba.
Naso ace duk masoyana dana sani na baku kyautar page ko na kwala muku kira na gaishe daku a Cikin Novel dinaππ
Amma hakan Bai samu ba,ayi hakuri ina kaunarku fans.
Groups wanda suka fi kowa birgeni wajen yin Sharhi Har na Samu na gama typing ina jinjina da godiya:
ASMABAFFA FANS CLUB
KASUWANCINA TRUE FANS
HOUSE OF HAUSA NOVELS
TASKAR SURAYYARMS
TASKAR FIDDAUSI SODANGI
LATEST NOVELLA
UWARGIDA da Sauran Gp na gode Allah ya bar kauna.
Sai kurakurai dole za a samu da yawan gaske wanda ku masu karatu zaku fi gane hakan,da su Typing error ayi min Afwa wannan Halayyace ta dan Adam wanda ya Zama dole tunda dole za a samu wani abin da bai muku ba,ga kuma halin mantuwa shima sai anyi mana Uzuri.
Kuskurenmu a ciki Allah ya yafe mana,darasin da muka koya Allah ya bamu ikon yin aiki dashi Ameen.
Fans Allah ya biyaku ya saka muku da alkhairi baki daya.❤❤π
Sai mun sake haduwa a sabon Novel dina nan gaba Insha'allah idan Allah ya kaimu da rai da lfy zan sake Sambado muku Sabo idan na huta da dan yawa.πππ❤❤❤❤❤❤ππ Kar naji an tambaye ni sabon Novel da wuriπππsai na huta da yawa.
Zanyi Missing dinku fans musamman masu Sharhi yanda muke rakashewa muna wasa da dariyaπππππππ€£wayyooooo.
AsmaBaffa loves u all.....
AsmaBaffa
COPY BY ZAINAB BUTALAWA
0 comments:
Post a Comment