Da misalin karfe goma bayan kowa ya karya suka sirya aka shiga gari
Da mools da kasuwan ni babu inda basu shiga bah dayake a babbar garin suka sauka mumbai
Bayan an dawi gida aka shiga bude kaya kowa ya saya kayan sawa banda Adeel yashi wani abu ya saya kaman earpice ne irin wanda ake sawa a jefan hannu idan za'a fita gym toh irinshi ya saya
Ameenah ta kalleshi irin kallon mamaki
Ya daga kai ya kalleta ya daga giranshi irin alaman me kike kallona ta girgiza kai ta juya
Tace ma Mami
Mami ke baki bude jayan ki bah tace ae baxan bude bane
Hakeem yace meyasa tace wai ina ruwanku
Hakeem yace ae kuwa Mami se munga me kike buye mana ya taso ya kama kokarin bude jakan shida safieyarh
Mami ta mike tana kokarin dauke jakan itama Ameenah ta mike duk suka tarun mata
Adeel ne ya taso yace tubda tace babu wanda zega jakan toh babu me gani ya shigan ma Mami ae ko ya fuzgo jakan a hannunsu
Mami tayi dariya tayi masu gwalo
Ameenah ta kalla hakeem tace wai kaman bamuda namiji a cikin mu
Hakeem yace aekam fuzga daya ya amsa yana magana yana kallon safieyarh kaman itace namjin
Se kuma yace waittt nine namijin
Mami da Adeel suka kyalkyale da dariya
Safieyarh tace ae ba lefinshi bane kinga fa inda yake kaman nace
Hakeem yace ohhh yanxin kuna cewa banda karfi kenan
Ameenah ta nannade hannunta tace yap
Kowa yace a mana
Yace ni kuma zan nuna maki ni namiji ne muyi compotition nida Adeel tunda shi kuke cewa namiji koh
Adeel yayi murmushi yace wannan irin competition chose anything
Hakeem ya tsaya yana kallon dakin seya hango wani side drawer agefe
Yace wancan kowa ya dagashi sau uku banda ajiye wai
Adeel ya kalla yace good by me amma wait idan aka ci me gift din mutum
Mami tayi sauri ta amsa tace gift guda biyu ne zan bude mashi bag din ya gani sannan zan bashi wani ticket na wani show da za'ayi gobe
Hakeem yayi sauri yace idan naci nida safieyarh zamuje
Safieyarh ta washe hakuri tace yawwa yaya hakeem jai zaka ci
Mami tace kaifa Adeel idan kaci dawa zaka
Ya tsaya ya kalla Mami sannan ya kalla Ameenah yace ni kuma da Ameenah zani
A zuciyanta tacr kaji munafuki
Amma a zahiri ta daure fuska shi kuma seda ya tabbatar Mami na kallonsu yayi mata murmushi
Mamu kuwa se murmushi takeyi tana jin dadi Adeel ya fara son Ameenah alahalin shi ganin idonta yakeyi dan Allah kadai yasan abunda yake shirya ma Ameenah idan ta shigo gidanshi
Safieyarh se zuga Hakeem take shi se wani bubbuga hannu yakeyi waishi me karfi
Ameenah tana dariya tana hawaye tace karfa ka balla hannunka kana jinka kaman pencil
Ya juyo ya galla mata harara
Mami da Adeel suka ringa mai dariya
Adeel yace toh waje fara
Hakeem da karfinshi yace kai
Yace okeyy oo
Ya mike ya fara daga drawer kaman yana daga loka daya na shinkafa haka takeji ya daga so uku cigan iyawa
Yana gamawa Mami ta fara mai tafi da durgura Ameenah itama tayi mai tafi
Hakeem ya taso kaman wani lagwani yace matsa ma master
Adeel yayi murmushi ya matsa mai
Shi hakeem inda yaga Adeel ya daga toh seya aza beda wani nauyi dan haka da karfinshi yaje wajan
Yana fara daga na farko se bayanshi yayi wani kara ji kake kasss
Da sauri ya ajiye yace i give up
Dukkan su suka ringa mai dariya hadda hawaye shi kuma kaman yayi kuka yace safieyarh hadda ke i thought kina cikin team dina
Ta daure fuska tace a mana ina cikin team dinka
Yana juyawa se dariyan ya tsinke ta kasa contrlloing dinshi
Mami ta bude jakanta tace toh ga gift dinka
Ya amsa seya mikama hakeem da murmushin shi ze amsa Mami ta buge hannun tace baka isa ka bashi bah ba kace tare zaku da Ameenah bah
Adeel yace a amma su suje nan mu kuma zamu wani wuri goben
Ameenah tayi sauri tace gobe am not free suka juya suka kalleta Mami tace uban me zakiyi goben
Tace Mami bacci mana yau bazanyi bacci bah se 4am
Tace ni bansan da wannan bah gobe zaku fita tare da Adeel
Adeel yace Mami ki barta tayi bacci
Tace noh bata isabah
Hakeem yayi sauri yace Mami baki bude bag dinba
Tace ina ruwanka
Yace wlh Mami kin iya gwale mutum
Mami tace Adeel zo ka bude ka gani yace nohhh ba sena gani bah ni seda safenku yayi masu sallama ya fita
Daya fita Mami tace ni dannan yana burgeni yana jin maganan manya sosai daman hakeem ka kuma irinshi
Hakeem yace nah am happy been who i am shima ya fita safieyarh tace se yaya hakeem dina kana burgeni
Yayi murmushi yace kinsama kyautan headphone daya
Ameenah najin haka itama ta mike ta bisu ta ringa wasa shi yace kije gun Adeel mana ya baki
Safieyarh tayi mata gwalo
Mami kowa se dariya take masu dan suna burgeti inda suke shiri
πππ
[11:21, 1/5/2017] Tyetyelorh-❣: Shi Adeel irin mutum nr ba murdadde sosai bah yanada jijiyoyi dayawa a jikinshi amma shi ba irin katon nan bane inda de jikin *yash* yake na married again haka yake ta wani fannin ma suna dan kama kadan dan ranan da suka fara shiga cikin garin mumbai mutane se tsaidashi sukeyi ana selfie dashi
Kuma dayake dan kwallo ne so wasu sun shanshi a cikin su
WASHE GARI
MISALIN KARFE 2pm duk suka shirya mommy tasasu dole se sun fita tare
Su kam su hakeem tuni aka shirya aka fita
Ameenah ta shirya tayi kyau sosai black doguwan riga tasa normal dressing dinta kenan sannan ta daura wani red raw silk akai
Tayi masifan kayau damn ita baki na amsanta tunda ita fara ce sannan ga red
Babu wani kwalliya a fuskanta eye pencil tasa kawai tayi lining sannan tasa powder se maroon lipstick ta feshe jikinta da turaruka
Ta fito dakin Mami ta shiga Mami tace kinga kyan da kikayi kuwa ta ringa daukanta picture daman ita bata gajeya da daukan hoto
Sega Adeel shima ya shigo shima ya hadu ba'a magana
Black kaftan ne a jikinshi shima wannan shine dressing dinda ya saba yi
Black kaftan da bakin wando gashin nan nashi a kwance yana shigo se kallon Ameenah yakeyi itama shi take kallo dan ya mta kyau
Daga baya koma se tayi sauri ta juya ta amsa phone dinta a hannun Mami tana ganin pictures din
Mami ta kalla Adeel tace kunga kyan da kukayi kuwa kaman yan gari
Adeel yayi murmushi ita kuwa Ameenah ko daguwa batayi bah
Mami tace ku tsaya na daukeku hoto
Ameenah tace Mami dan Allah ki barshi
Ta galla mata waji harara bada son ranta bah haka ta tsaya ta ringa daukansu pictures
Daga baya de tace su tafi kar yamma yayi
Sukayi mata sallama suka tafi suna fita cap suka tara dan basu amso mota bah
Ita ta fara shiga sannan shim ya shiga suka tafi a wani resturant suka tsaya ta bude ya fito itama ta bishi binshi kawai takeyi kaman jela
Suna shiga daman ansan zasuzo toh an rigada an shiya masu wurin zama
Suna zuwa shi ya fara zama ko kallonta beyi bah itama ta zauna
Ya dauka menu card din ya mika mata
Tace nop ita baza taci komai bah
Ya daura fuska yace amsa
Ta kalleshi tace wlh bazan amsa ba tunda banyi niya bah ta dauka phone dinta tana dannawa
Abun ya kullar dashi ya fuzga wayan ta dago ta kalleshi tace give it back
Yace ae kina da karfi koh zaki iya kwata
Abun ya bata haushi ta mike ta kai hannunta tana son ta kwata ya kauce haka ya ringa mata kaman tayi kuka
Tana juyawa se taga wasu couples suna kallonsu macen tan filming dinsu
Tace mata uban me kike video taping
Adeel yace yar 9ja toh batajin hausa
Tace mai na tambayeka ta kuma ta zauna
Matan tazo gunsu tace am vry sorry is jst dat you guyx are the bst couple i have ever meet
Ameenah ko kallonta batayi bah
Adeel yace thank you but we are not really a couple
Matan ta kalla Addel seta bude baki ta kuma wurin mijinta suka zo tare mijin yace plzz are you Adeel the great footballer
Yayi murmushi yace yess matan tayi wani ihu tace ohh myy god tace plxx can i have your authorgraph
Yace why not ya amsa yayi mata suka ringa daukan pictures
Abun ya kullarda Ameenah ta mike ya rikota yace ina zaki
Tace restroom ko zaki bini ne
Yace yes yayi kaman ze mike
Tayi sauri ta fuzga hannunta ta wuce yayi murmushi
Tana shiga ta kalla fuskanta a jikin mirror tayi murmushi tace not that bad ta gama shirmenta a toilet din daga baya ta fito
Tazo wucewa kenan se taji a bigan mata ass dinta ta juya da sauri abun ya bata mamaki
Tana juyawa setaga wani katon gardi yana zaune yana mata murmushi
Da ta juya ne da niyan mashifa amma tana ganinshi seta wuce wurin Adeel ta tsaya tace mai kaga yanzin wani ya dakan min duwawu ina cikin tafiya
Adeel ya mike ya ce what yana ina
Ta nuna mai shi ya tafi wurin tana binshi a baya
Yana zuwa kan mutumin seda ya tabashi ya juyo sannan yayi mashi wani wawan punch
Tyetyelorh❣
[13:39, 1/11/2017] Tyetyelorh-❣: πππUMARNIN IYAYEπππ
WRITTEN BY:
TYETYELORH
EDITED BY:
AMEENATOU
IN DEDICATION TO LAWIZAS
6⃣0⃣ ↗ 6⃣5⃣
Ya sake buga mai wani nan da nan jini ya fara kwaranyuwa
Mutane aka fara rikeshi ana bashi hakuri
mutumin ya mike yace wat d fck is wrong with you
Ameenah tazo tace this for touching my butt tayi kicking d***k dinshi yayi ihu ya rike
Adeel shima yace this for touching my wife ya ya sake kaimai wani punch din a jefan fuska
Ameenah ta kalla Adeel da mamaki
Wani mutum yace is it not Adeel one of d bst footballers Adeel ya kalleshi amma beyi magana bah
Mutane suka ringa daukan selfies dashi ya ja hannun Ameenah suka fita daga gun
Mutanen wajan aka taro akan mutumin daya taba Ameenah se fada ake mai shi kuma kallonsu kawai yakeyi
Suna zuwa gun dazasu hau mota suna jiran cap yazi su tara har yanxin hannunshu yana rike dana Ameenah
Ta kalleshi ta kalla hannun tace can you......
Ya juyo ya kalleta se yaga tana kallon hannun se yayi sauri ya sake dan ya manta yana rike da hannunta
Tace yah tnxx cuz you are hurting me
Yayi kama be jita bah can se tace why do yiu did that dan yanxin Mami bata nan bare kace saboda ita kayi
Yayi shiru dan besan me xe ce mata bata can seya ce because you are my sister bazan bari wani yayi humiliating dinki a cikin mutane bah
Zatayi magana kenan sega wani cap
Ya tara suka shiga tare
Da suka shiga babu wanda yayi ma wani magana a cikin su shi Adeel phone dinshi ma ya dauka yanata dan na danne
Ita kuma kallan nails dinta take tayi Allah kadai yasan tunanin me takeyi
Suna isa bakin hotel dinda suka sauka Ameenah tayi sauri ta fita daga motan ta shiga shi kuma ya tsaya yana biyan me taxi din kudin shi
Yana biyan shi ya shiga shima shi duk ya kusa su koma gida dan idan yana nan yana yawan ganinta toh he think he may have feelings for her shi kuma abunda be so kenan
Ameenah tana shiga dakin Mami ta wuce
Data shiga bata ga kowa bah a ciki dan haka se kawai ta juya ta tafi dakinta dan tayi wanka
Shi ma dakin Mami ya wuce
Tana fitowa daga dakin setaji tayi karo da mutum dana dagowa ta ganshi
Se yace God why do i keep touching dis thing
Ta bude baki irin excuse ne
Se kuma ta juya tayi tsaki sannan ta wuce
ae kuwa yayi sauri ya kamota yace wa kika na tsaki ya kamo bakinta da hannunshi
Nn da nan se yaga idonta sun fara kawo kwalla ta saketa
Tace mugu kawai tayi daki a guje
Shi kuma ya girgiza kai ya wuce nashi
Tana shiga daki wanka ta shiga sannan tayi alwala ta fito ta gabatar da sallolinta sannan ta haye gado ko kayan arjiki babu a jikinta daga ita se bom shorts se weist dayake da katon hijab din Mami tayi sallan
Shima ta gefanshi hakane wanka yayi sannan yayi sallah sannan ya haye lallausar gadonshi se bacci
Duk basu tashi ba se misalin karfe takwas kaman hadin baki a tare suka tashi
Ita Ameenah tana tashi sallah magrib tayi da isha sannan ta dauka wani jallabiya ta saka ta tafi dakin Hakeem
Tana shiga ta tarar dashi yana zaune kawai yana kallon kofa
Ita dariya ma ya bata
Ta tabashi tace yaya Hakeem lafiyanka ya daga kanshi ya kalleta kawai se yace babu komai
Ameenah taji wani iri dan tunda take bata taba ganinshi in a serious tone ba danshi kullum yana cikin wasa ne
Ta rikeshi tace yay Hakeem pls tell your baby sis meke faruwa da kai
Yayi shiru can kuma seya ce its safieyarh i think i have falling for her
Ta fashe da dariya kawai
Ta kalleta se ya mike ya ja hannunta yace fitan min daga daki tunda you can't help me feel better dariya kawai zakiyi min
Dakyar ta hadeye dariya sannan ta bashi hakuri ta ringa bashi baki har ya fara dariya sannan suka fito daga dakin suka tafi dakin Mami acan suka sama safieyarh yana ganinta seya juya ze fita tayi sauri ta kamo hannunshi sannan suka kuma cikin dakin
Ana zaune anata hira hadda Adeel itade Ameenah mamakin Adeek takeyi dan ta san shi kwata kwata be cika magana bah
Hakeem kuwa shiru yayi kawai yana satan kallon safieyarh
Mami ta lura da shirun da Hakeem yayi amma batayi magana bah
Can Mami tace gobe fah zamu kuma ae da sauri Adeel da Hakeem suka mike
A tare Mami da Ameenah sukace lafiya a tare suka ce kayan mu zamu shirya suka kalla juna sannan suka fita
Ameenah tace lallai kuwa ya gaji kenan
πππ
[07:43, 1/13/2017] Tyetyelorh-❣: WASHE GARI
Tun asuba da suka tashi ba wanda ya kuma se hada kaya akeyi
Ameenah da akwati daya taje amma ta taho da akwati biyu da kuma wata karama
Itama safieyarh tayi siyayya sosai
Adeel kuwa ba abunda ya saya se abu daya
Hakeem kowa kuwa na faman shirya kaya shi kuma yana zaune da waya a hannunshi yanata murmushi safieyarh ce ta shigi dakin yana daha kai yaga itace yayi saurin boye phone dinda yake kalla
Ta karaso tana murmushi tace yaya Hakeem me kake boyewa
Ya fara inina Ammm.......mm.....babu komai se ya mike ya kama hada kayanshi yace kije ki hada kayanki mana tace ae na gama tun dazin
Se ya sake cewa toh kije ki taya Adeel
Ta kalleshi tace yaya Hakeem are you avoiding me
Ya juyo seya sosa keya ya kasa magana
Ta tsaya tana kallonshi tace do you know what you have been weird lately duk sanda na zauna kusa da kai seka fara wani kame kame you are making me feel like ina shishige maka luke you want to get rid of me toh daga yau na fita daga harkanka
Tayi wulli da headphine dinda Hakeem ya bata daman yana hannunta ta fita daga dakin
Shide yana tsaye kawai beyi magana bah tana fita yaje ya dauka headphone din se yayi pecking nashi yasa a akwati
Shi kuma Adeel yazo wucewa ya ganta ta fito da fushi ya tiketa yace mata meyafaru dake seta fashe mai da kuka tace yaya Hakeem ne yanxin ya dena kulani
Yayi murmushi rungumeta yana bata hakuri harta kwantar da hankalinta sannan suka je dakinta suka lebo akwatinta suka fito
Kowa ya fito daman an kawo masu motan da zasu tafi airport dashi toh shiga motan kawai sukayi irin babbn motane driver ya ringa jida kayan nan a cikin trunck din motan
Yana gamawa suka kama hanyan airport
Da suka isa ba'a wani dade ba aka kirasu suka shiga
Wannan karan de Ameenah tayi sauri ta shiga plane din seta zauna kusada safieyarh shi kuma Hakeem tare suka zauna da Adeel
Suna zaune Adeel ya kalla Hakeem dan yau abun ya bashi mamaki wai tareda Hakeem suka zauna amma yayi shiru kaman bashi bah
Yace mai wai lafiyanka kwanan nan baka cika magana bah
Murmushi kawai yayi beyi magana ba
Adeel yace kaga abunda nake gaya the Hakeem i know baza ka taba zama dashi ma kaji yayi shiru
Yace i promise you babu komai kawai de na gaji da kasan ne
Toh shikenan
Ameenah suna zaune tace safieyarh wai meke damunki yau baki zauna da Hakeem bah
Shiru tayi bata.mata magana bah
Ta buje ta tace am talking to you
Se a lokacin ta dan furgita tace me kikace
Ta kalleta baki ma san ina magana bah
Wlh tunanin wani abu nakeyi me kika ce
Tace cewa nayi meyasa baki zauna da yaya Hakeem bah yau
Ta daure fuska tace we had a fight
A fight meya hadaku
Seta fara hawaye tace yanxin idan naje gunda yake seya changa gabadaya seya kusa na tashi ni kuma i dn't want to feel like besan ina zama kusa dashi shiyasa
Ta share mata hawaye tace ya isa gajiya da yayi da garin ne yasashi haka amma
Gajiya da garin. kwata kwata kwanan mu nawa ne da har za'ace ya gaji
Tayi shiru batayi magana bah
Mama tana kallonsu duk ta gane abunda ke faruwa sannan ta gane itama safieyarh tanada feelings akanshi
πππ
Ana isa Abujah suka fito daga plane din suna fito daman driver yaxo daukansu dan haka suka shiga aka cigaba da tafiya motan shi dan kuwa ya gaji.......
πΈInstagram-_tyetyelorh_
Wattpad-tyeetyeeloh
[19:37, 1/16/2017] Tyetyelorh-❣: πππ _UMARNIN IYAYE_πππ
_WRITTEN BY:_
_TYETYELORH_
_EDITED BY:_
_AMEENATOU_
_IN DEDICATION TO LAWIZAS LUV YUH GUYX_❣
6⃣5⃣ ↗ 7⃣0⃣
Suna isa Kaduna aka bude masu gate suka shiga gidan
Da driver yayi packing kowa ya fito da kayanshi amma safieyarh da Adeel nasu na ciki motan dan bazasu dade ba suma zasu tafi gida
Suna shiga dayake Mami tabar wata yar uwarta _kande_ ake kiranta
Suna shiga suka tarar kan dining a cike da abinci kala kala ae kuwa nan kowa ya nufa sega kande ta fito ta masu sannanu da zuwa ta kalla Ameenah tace uwata lallai garin nan ya amshe ki kinga inda kika kara haske kowa
Ta washe baki ta fara juye juye tace danma na debi rana ne barinyi wanka
Tace iyye se yan india
Ta kyalkyale da dariya
Bayan da suka gama cin abincin akayi sallah su Adeel suka tafi gida bayan Mami ta bashi tsaraban Mommyshi yakai mata
Ita kuwa safieyarh ko kallan Hakeem batayi bah ta fita Ameenah ta rakata
_ANA SAURAN KWANA GOMA A FARA BIKI_ Mami ta samo ma Ameenah me gyran jiki(dilka) daga maiduguri aka je musamman aka daukota aka fara mata gyara ita kuwa idan za'a mata kaman tayi hauka takeji dan se ta tube ga kuma wani hayaki da ake kunnawa sau biyu akeyi a rana duk sanda aka fara harse an gama tanata mita wai ta ringa tubewa tsindir gaban matan da bata santa bah
Ana cikin kwana na uku da aka fara mata dilka gidan su Adeel suka kawo akwatinta
Akwati yayi ba'a magana dan guda shida ne se kit guda daya
Ita Ameenah tana zaune a dakinta da phone dinta a hannu akace mata an kawo akwatu seta sa kuka
Ita kanta batasan dalili bah bayan yan kawo akwatin sun tafi Mami ta shigo dakinta tace mata tazo taga akwatin sunyi kyau seta sake sa mata kuka
Ta tsaya ta kalleta tace toh me amfanin kukan
Tazo ta zauna kusa da ita tace mata ta gaya mata dalilin kukan da takeyi
Tayi shiru bata amsa mata bah
Ko baki son auren ne Ameenah da sauri ta daga kanta
Tace aeko aure kaman anyi an gama da izinin ubangiji ta tashi ta fita ta barta se kuka takeyi kukan da takeyi yana cin mami amma batasan abunda zata mata bah
A ranan Ameenah tayi kuka harta gode ma Allah idonta sunyi lubu lubu dan kuka
Da daddare bayan an gama yi mata dilka ta shiga wanka bayan ta fito aka fara mata gyaran gashi
Daman duk sanda akayi dilka se anyi gyaran gashi wani abu ake shafa mata shi zata kwana dashi sannan washe gari da safe ta wanke haka ma kafanta foot smoting ake sa mata shima
Ita yan gidan ma dukkansu haushi suke bata dan tabar zama tayi hira dasu kullum tana dakinta tana video chat dasu fatye
Wani sa'in idan yan tsokanan suna mintsinin hakeem ze shigo dakinta yata neman tsokanan ta amma bata cika kulashi bah haka ze kari abunshi ya mike ya fita
Akwai wata rana yazo yata tsokanan ta bata kulashi ba tana kallonshi kawai seya dauka wayanta ya mike
Kawai seta fashe mai da kuka
Ya juyo ya kalleta se yaji ta bashi tausayi shi se a lokacin nema ya lura da raman da tayi
Ta rame sosai amma ta wani fanin raman ya kara mata kyau da shape dan hips dinta suka kara fitowa ga boobs dinta suma sannan idonta sun sake manya da kuma wani karin hanci da ta sakeyi
Yazo ya zauna kusa da ita ya rungumota ta gefe yanaya bata hakuri da kyar ya samu tayi shiru seya mike ya shiga closet dinta ya dauko mata wani maroon jallabiya da black veil ya mika mata
Dayake daga ita se dugan wando da top a jikinta
Ta kalleshi tace me zanyi dashi
Kisa zanu fita ne
Babu musu ta amsa daman gata uwarson yawo
Tasa suka fito daga dakin suka sauka kasa gun motoci suka je
Hakeem ya fito da key din BMW dinshi daga aljihu ya danna motan ya bude seya mika mata keys din
Ta kalleshi tayi wani murmushi ta amsa tashiga shima ya shiga gateman ya bude masu gate suka fita
_πππ_
[20:05, 1/16/2017] Tyetyelorh-❣: Suna fita ta kalleshi tace ina zamu
Yace anywhere you wish
Ta fuzga motan da karfi cikin zumudi bata tsaya ba se a wani babban titi wanda zakaga mota jefi jefi suna tafiya dan haka ta tafi can karshe seta tsaya tasa sit belt
Ta kalla Hakeem tace shima ya sa nashi sit belt din yasa
Data fuzg motan nan da karfi Hakeem iyayan tsoro ihu yasa a cikin motan itama ihu takeyi tana dariya
Tana zuwa karshen tayi wani U Turn
Ta sake wani ihu ta kuma hakeem yace dan Allah ya isa haka
Tace mai kasani maybe wannan shine opputunityna na karshe ka barni nayi enjoying
Ta sake fuzgan motan da karfi bata lura da wani me rake da yazo wucewa bah da dan barunshi yana tafi
Yana daga kai yaga tayo kanshi aeko a guje ya sake baron ya juya a guje
Ta tsayar da motan se dariya suke mai
Dayaji ta tsaya ya juyo ya kallesu suka fito daga motan suna dariya
Ya dawo yaja baronshi ya cigaba da tafiya
Hakeem yace mata suje pack
ae ko haka akayi pack suka tafi suka sha ice cream sukayi selfies sannan suka zazzagaya wurin se kallonsu akeyi seka rantse saurayi da budurwa ne idan ka kallesu
Irin tasa hannunta ne a cikin nashi
A ranan sunyi yawo tun karfe biyu suka fita se shida suka dawo duk suka kashe wayansu seda idan zasuyi selfie suke kunnawa
Ita Ameenah taji dadi sosai dan rabonda tayi dariya tun ranan da suka dawo daga india se yau
Da suka dawo suka shigo da mota cikin gida ta fito tazo tayi huging Hakeem tace _Thank you so mch you are the bst brother ever_
Yayi murmushi yace Awwwwwwwn u re wlcm and you are the bst sister ever and am gonna miss you so mch
Mami tana daga dakinta ta hangosu taji dadi sosai dan haka seta fasa masu masifan datayi niya
_WASHE GARI_
Sister Mami tazo Auntie Aysha Ameenah tace ita wlh seta bita gidanta inya so se a cigaba dayi mata dilken acan dan ita kanta tana jin dadin jikinta babu karya
Haka ta tattara kayanta ta tafi da ita can gidanta saboda yan uwa sun fara zuwa
Kati ya fito Mami ta kira _bridesmate_ dinta wato _Ameerah,fatye,safieyarh da dayan Ameerah sister Ahmed_
Ta kirasu ta basu katin biki da kuma na dinner tace masu su raba ma frnds dinsu dan tasan idan taba ma Amaryan toh ajiyewa zatayi harse bayan biki ta fito dasu
Hakade akayita shirya shiryan biki ta gefan Adeel kuwa shi mantawa yakeyi kwanaki ya rage a daura masu aure amma ya gama gina gidanshi dake Abuja acan zasu zauna amma ance kar a gayan ma Ameenah dan za'a sha wiya da ita.
πππ
πΈ
_ tyetyelorh_
[21:33, 1/19/2017] Tyetyelorh-❣: πππ _UMARNIN IYAYE_πππ
_WRITTEN BY:_
_TYETYELORH_
_EDITED BY:_
_AMEENATOU_
_IN DEDICATION TO A VRY SPECIAL PERSON *AMEERAH BAWA* ALLAH YABAR MIN KE HAR ABADA YOU ARE THE BST AMONG THE BST FRNDS U WILL OLWAYS LUV YOU_
7⃣0⃣ ↗ 7⃣5⃣
Bridesmate din Ameenah ne ke video chat suna son su hada mata bridal shower but suprise dan basu san ta sani idan ta sani zata bata masu ne kawai
Safieyarh tace ita ta dauka nauyin snacks da ice cream da za'a ci a wurin
Ita kuma Ameerah sister Ahmed tace ayi a gidansu dan sunada babban parlo kuma ba'a cika yin bridal shower a hall ba dan haka duk suka yarda kuma tace ita zatayi decorating wurin
Ameerah ta fatye kuma sukace su zasuyi gift dinda za'a ba kowa dan frndz dinta za'ayi inviting kawai
Duk abunda mutum yace shi zeyi safieyarh ke rubutawa sannan suka fitar da dress code
Ameerah tace ita zata ma Ameenah dress dinda takeso dan tasan perfect dress dinda take dreaming idan zata aura prince charming dinta ranan da za'ayi bridal shower toh an bari ita zata mata dress din
Dress code dinsu ix red gown
Hakade suka gama shirya komai kuma akace kar wanda yayi magannan a gabanta
Ita kuwa Ameenah tana kwance a daki gidan Auntie Aysha ta kwanta akan gado tana kalan sama kawai abun duniya ya isheta
Se kawai birthday dinta ya fado mata ta mike zaune tana lissafi yau sauran kwana biyar ta shiga 18
Se kawai ta fara hawaye tace inda take tunanin 18 birthday dinta ze kasance amma yanxin its impossible
Ta dauka ipad dinta dake kusa da ita ta hadashi da bango ta sake fashewa da kuka
Meemah ce ta leku dakin seta ganta tana kuka seta kuma gun mamanta
Auntie Aysha tana kitchen tana girki se meemah ta shigo tana jan mata skirt tace mommy Auntie Ameenah is crying in her bedroom
Tayi sauri ta wanke hannunta ta fito ta shiga dakin seta sameta a kan gado tanata kuka
Ta jirjiza kai taje ta sameta tace meyafaru kike kuka
Se Ameenah ta fada jikinta ta sake sa wani kukan
Ta dade tana kukan can tace Auntie seriously i hate this marrige infact i hate d guy
Ta dagota tace dn't say dat Adeel is lyk a brother to you and i promise you zakuji dadin auren nan tunda *_UMARNIN IYAYE_* zakubi wlh wata rana dakanki idan an tambaye ki a raba auren nan zakice no dan nasan Adeel yanada hankali wata rana fa yana zuwa gaidani kuma meemah na sonshi tana ta mata wa'azi
Ameenah tayi shiru kaman tana jin abunda take gayan mata alhalin ita ipad dinta take kalla tana bala'in sonshi toh meyasa tayi jifa dashi
Ta kalla Auntie Aysha tace Auntie ipad dina fa tana magana irin na shagwaba
Tayi murmushi tace karki damu
Birthday dinki sauran 5 days koh
Ta daga mata kai
Seta mike ta fita can se gata ta shigo da wasu pappers a hannunta ta ajiye akan gadon tace kalla katin bikin
Ameenah ta hada fuska koh kallon su batayi bah
Auntie Aysha ta dauka ta kalla ranan daurin auren on 5th rana daya da birhday ta
Ta kalleta tace on 5th daurin auren ki fa
ae batasan sanda ta fuzga katin ba ta kalla
Wai abunda za'a mata kenan on 18th birthday dinta memakun abarta tayi shagalinta tunda zata zama adult
Tayi shiru kawai tanata tunani
Auntie ta amsa katin tace nasan me kike tunani karki damu ko an daura aurenki ne se munyi chason mu
Ae Ameenah batasan sanda ta rungumeta ba tana murmushi tace thank you so mch
Washe gari da safe misalin karfe 12 ta gama wankanta ta shirya cikin normal dressing dinta wato duguwan riga sannan ta daura dankali ta dauka handbag dinta ta bude ta ciro wallet dinta ta tabbatar credit card dinta na ciki sannan ta sake fesa turare ta dauka phone dinta ta fito ta tafi dakin Auntie
Ta sameta tana zaune akan dadduma ta gama sallalan arzahar
Meemah tanata tsalle akan gadonta
Tana shiga Meemah taje tayi huging dinta kaman wanda ta fita
Tace Auntie zan rakaki please
Tayi murmushi tace toh dauko takalminki ae aguje ta shiga dakinta ta dauka
*_MEEMAH_*
Meemah ita kadaice yarinyan Auntie Aysha shekaranta 3 yarinyace fara gata da pink lips ga gashi
Kuma gata shiririya sosai dan yarinyan is a vigan kwata kwata bata cin nama ko kifi tana ci zatayi amanshi da kuma indomie tana cinsu zatayi amai
Idan kana son ka burgeta kace mata Meemah zo ki amsa corn flask ku kuma ice cream kai hadda ma garin rogo duk a cikin su yafi burgeta
Yarinyace me farin jini sosai
Akwai wata rana suna zaune ita da mamanta a parlo da daddare se akayi sallalma maman ta tashi ta bude se taga wata makuciyarta yar meduguri ce tayi tafiya seta aiko mata da fara
To se maman meemah ta bude faran ta fara ci ta sa faran ne ta bayanta saboda kar meemah ta gani se meemah tace ita setaci faran se Nepa suka dauke wuta
Se maman meemah tace mata toh ta bude baki tasa mata faran a ciki
Suka runga cin faran acikin duhu ita meemah batasan meye bah
Can setace mommy ki samin babba mana
Zata kai mata baki kenan se aka maido wuta Meemah ta kalla paran tace mommy meye wannan
Tace mata fara tace ewwwww ta ringa kwaran amai to tun lokacin idan zata sa mata abu a baki seta amsa tasa da kanta
πππ
[22:02, 1/19/2017] Tyetyelorh-❣: Meemah ta dawo a guje da takalman a hannunta ta mika mata
Tayi murmushi ta durkusa ta sa mata
Auntie Aysha bayan ta idar da sallah ta kallaeta tace se ina
Tace zanje na sayo wasu kaya ne wlh
Tace amma kinsan amare basa fita koh
Ta dan yi fuskan shagwaba tave haba Auntie plxxxx yaune karshen fita
Tace to shikenan seta kalla Meemah da duk ta gama kusawa su tafi dan se janta taketayi
Tace ke kuma dawo nan ba inda zaki ae aguje ta boye bayan Ameenah tace ni tare zanu tafi bazan sake dawowa ba se daddy ya dawo
Tace haka kikace koh toh shikenan nima yau zanje na sayo ice cream nasha ni kadai
T
A guje tazo ta rungumeta tace Am srry mommy na dawo tare zamu koh
Ameenah tace ni kuma yanxin zanje nasayo nawa ta juya tayi kaman zata tafi
Ae Meemah se tayi waje ta rigata fita
Suka kwashe da dariya
Auntie tace da wannan mota zaki
Tace ni ko wannne ne
Ta mika mata key din RANGE ROVER da zumudi ta amsa ta fita tana jin dadi
Tana fita ta same Meemah tana jinjine da motan tana jiranta motan is white and black tana budewa tasa Meemah a dayan sit din sannan tasa mata sit belt seta bude jakanta ta dauka glasess dinta ta bude sit din baya tasa bag din a ciki sannan ta shiga suka fito
Meemah duk dadi ya isheta
Wani shoping mool suka tsaya ta fito da ita sannan ta ciro handbag dinta suka shiga wurin tana rike da hannun ta
Wajan dresses suka tsaya ta diba kaman guda biyar seta shiga wajan changer kaya tana sawa duk wanda tasa idan ta fito se Meemah ta yamutse fuska ita kuma seta changa haka suka ringa yi harde ta sama wata black gown irin me armless ce ta bude sosai har kasa tana fitowa meemah ta ringa tafawa tayi murmushi taje ta changa suka dauketa sannan suka tafi gun na yara ta debo ma meemah gowns kala kala daga pink se purple dan idan zata gwada mata wani clour seta ki yarda ta sa mata ta deban mata kusan goma sanan suka je gun biya ta mika mata credit card dinta ta cire kudin sannan tasa mata kayan a leda suka fito
Suna fitowa taci karo da wani haddde se kayan ya zube daga hannunta tana daga kai ta kalleshi kawai seta Adeel wani haushi ya turniketa ya durkusa ya debu mata kayan shi bema ganta bah yana mika mata kayan a lokacin ya lura da ita
Shima ya hada fuska
Meemah tayi ihu tayi huging dinshi tace Uncle Adeel damab biyo mu kakeyi
Yayi murmushi yace a mana dole na biyo ku karku bata
Tace zamuje mu sayo ice cream yace a mana
Ameenah ta kalleta tace ba kince tare zamuba
Tace nop n fasa zuwa dake
Ta kalleta ta kalla Adeel ya mata gwalo taji haushi ta dauka kayanta tace kuma na fasa baki kayan tace Uncle Adeel ze sayan kin ae
Yace wanda yafi wannan kyau ma
Ya juya ta wuce gun motan .........
πΈ
_ tyetyelorh_
[21:23, 1/21/2017] Tyetyelorh-❣: πππ _UMARNIN IYAYE_πππ
_WRITTEN BY:_
_TYETYELORH_
_EDITED BY:_
_AMEENATOU_
πππ
7⃣5⃣ ↗ 8⃣0⃣
Tana shiga motan ta fuzga ta kama hanyan store din cakes taje tayi ordering cake din birthdayta ta gayan masu ranan da zatazo amsa
Red and black takeso
Akace mata 15k dan ta masu bayanin yadda takeso ta mika masu credit card dinta suka cire kudin sannan ta amsa ta wuce tana shiga mota phone dinta yayi ringing
Tana dubawa taga Abbah ta dauka
Yace princess ya kike
Tace lafiya lau Abbah suka gama gaisawa can yace kina enjoying yau koh
Tayi murmushi tace naje sayan outfit dina ne na birthday na
Yace no wonder su biyu ana min sndin message cewa an cire kudi a account dinki
Abbarh seda nace maka ka saka number na amma kasa naka
Yace nop nafison nasa number na dan naga yadda zaki ringa spending kudi
Haka suka ringa hira har daga karshe sukayi sallama sannan ta tada motanta ta kama hanya gida
Seta tuna da Meemah tace lallai yarinya yau zakisan ni kika ma wulakanci ta tsaya a ostrich backery ta saya snacks da ice cream sannan ta wuce gida
Tana shiga gida aka bude mata gate ta shiga tayi packing malam musa yazo ya mata sannu da zuwa ta amsa tareda gaidashi sannan ya bude baya a ciro kayanta suka shiga ciki
Suna shiga parlo suka tarar da Auntie tana kallo ita kadai
Ta baje kan kujera tare da cewa wash
Ita kam Auntie sake baki tayi sanda taga mallam musa yayi sallam ya shigo da kaya ya ajiye sannan ya fita
Ameenah ta mai godiya sannan ta sauko daga kan kujeran tana bude kayan
Auntie ta mike ta leka waje bataga alaman Meemah ba ta dawo tace ina take wai
Ameenah tace aww na manta ban gayan maki bah muna fitowa daga mool barawun yara ya saceta
Hadda min gwalo wai zasuje su sayo kaya
Auntie ta zare ido can tace hmm wasa kikeyi
Tace toh shikenan tunda baki yarda bah
Ta ciro kayan data sayan ma Meemah tana nuna ma Auntie ita kuwa se murna takeyi dan ita idan mutum ze burgeta toh kaji da yarinyarta
Auntie ta cire kaman set shida ta ajiye a gefe tace wannan se ranan bikinki zata sasu ta ciro wata pink dayake duk gowns ne
Pink din har jan kasa yakeyi tace ita zata sa ranan dinner dan itace a gaba idan zaki shiga
Ameenah ta daure fuska tace bani kayana tunda ni na saya
Ta kwashe tace wlh baki isa bah sema nasa mata me pink and Ash dinnan ranan kamu ta kwasa tayi daki
Itama Ameenah ta mike ta bita tace ta fasa kyautan daman Meemah tace itama bata so haka suka ringa guje guje a gidan kaman yara harseda Auntie tana haki tace ta yarda bazata sa mata rannan biki bah
Ta ciro wata tace kinga wannan rannan daurin aure daddy ta ze dawo daga tafiya shi zan sa mata
Sannan nema Ameenah tadan hakura ta kuma parlo ta ciro gown dinta ta nuna mata
Auntie ta kalla ta yamutse fuska tace wannan rigan fa kaman na vampires
Tace A ahaka nakeso
Amma ita Auntie tasan rigan yayi kyau
Ta mike tasa ledan ice cream a cikin frigde tace se Meemah ta dawo zan ciro na mata gayu dashi
Tace barita je tayi wanka
Ta mike ta dauka handbag dinta kawai ta shiga dakin
Tana tafiya Auntie ta zauna kusada snacks din ta ringa ci kaman me ciki
Ita kuwa tana shiga daki phone dinta yayi ringing tana dubawa taga Hakeem tayi murmushi sannan ta haye gado ta daga call din
Tana dagawa yace mata lallai tun kafin ayi biki harta manta dashi
Tace wlh bata manta dashi bah
Muryanshi a hankali yace kinsan wani abu
Tace aa
Ya cigaba gidan babu dadi idan baki nan se hayaniyan mutane kawai da kukan yara i really missed you
Ita da hawaye beda tsada agunta nanda nan ta fara hawaye muryanta na rawa tace i really missed you too
Suka sha hiransu amma rabin hiran ita hawaye takeyi
Yake bata labarin tunda ita bata gida yanzin ya rasa wanda ze tsokana ya leka dakin Mami ya tarar da ita akan gado ta juyama kofa baya tana waya seya kuma cikin dakinshi ya ciro wani mask fuskan me kama dana boss din cikin wannan horror film dinnan _*saw*_ yasa ya tafi dakinta
Ita Mami ta tsana film din duk sonda takema horror film dan yadda ake kisa a film din yayi yawa
Ya shiga a hankali dayake gadonta kasanshi irin me space din nan ne sosai toh nan ya shiga ya zagaya ta gabanta amma be fito ba yana jira ta gama waya
Ae kuwa tana gamawa ya fito
Ita tana ajiye waya tanada niyan tashi kawai sega shi ya fito ta gabanta ae datayi wani ihu tareda salati kafin ya cire mask din kawai ya hangota a bakin kofa
Ya cire ya ringa mata dariya tana ganin shine ta ciro takalminta tayo kanshi abinka da dan siririn mutum ae a guje yayi super ya bar dakin yana mata dariya
Ameenah ta ringa dariya shima haka
Tace this how it feels idan bani akayi pranking bah
Tace wlh wata rana seka sata hawayn jini
Yayi dariya a tare sukace am gonna miss you sukayi murmushi sannan sukace mee too sannan suka ma juna sallama
Dukda ta kashe wayan se dariya taketayi ta mike taje tayi wanka sannan ta biya sallolinta ta zunbula wata riga ta fito parlo ta sama Auntie kusa da snacks dinta tanata ci ta rike baki tace wlh zance kar a kawo min cake dina nan se ranan birthday dan kafin na tashi daga bacci kin cinye dukka
Ta kalleta tace dan miko min ruwa na kura sannan naci gidan ku
Tayi murmushi ta dauko mata ta bata sannan tace dan gidanku wai ina yarinya na
Ta bude burger daya sannan tace na gayan maki ae baki yarda bah
Zata kai baki kenan sukaji sallama
Tana daga kai setaga Adeel ne Meemah ta shigo aguje da ice cream a hannunta taje gun Ameenah ta zauna akan laps dinta
Ameenah tace saukan min daga jikina mutum kanan mage ba kince kin fasa zuwa dani bah toh na sayo gari hadda gyada maga wanda ze baki
Meemah tayi fuskan tausayi dan an tabu weak point dinta tace Auntie am sryyyy
Auntie ta jayo gyale ta yafa ta amsa mai sallama ya shigo ya durkusa ya gaidata sannan ya zauna ita kuwa Ameenah ku kallonshi batayi bah tanata fada da Meemah ji tayi an buda mata dundu tace auchhh
Auntie tace dan gidanku kikace min an sace ta
Tayi murmushi ta mike zata gudu ae ji tayi ta kamota tace zauna dan gidanku kafin a zaune ki
Ta kuma ta zauna dan tasan zata iya kuma idan ta zauneta toh se makabarta
Auntie suka danyi hira da Adeel Meemah kuwa tana nan tanata ba Ameenah hakuri akan garin kwaki
Adeel ya mika mata kayan daya sayo ma Meemah tamai godiya sosai sannan ya mike Meemah ta rungumeshi tace Uncle Adeel thank you
Yayi murmushi ya mata peck yace you are highly wlcm sannan yayi masu sallama ya fita
Ameenah ta galla mai harara ta gefan ido
Auntie ta mintsineta tace tashi ki rakashi tayi ihu ta kalla wajan tace ba inda zani
Tace wlh idan baki tashi bah sena zuga Mami da Abbah su hanaki celebrating birthday ki
Seta mike dan tasan kadan daga cikin aikinta ne saboda zataje ta hada abubuwa ne harse sun yarda kuma zasu iya hanata and idan aka hanata zata iya karamin hauka dan tana planing abubuwa kala kala
Ta rike hannun Meemah tace zuki rakani
Auntie tace ba inda zata haka ta hakura ta bishi tana fita kaman daman jiranta yakeyi dan be shiga motan bah
Ta tsaya bakin kofan bata karasa ba ta hada giran sama dana kasa tana kallon nails dinta
Shi kuma yana juyawa yasan sarai se Auntie tace tazo ta rakashi shiyasa yaki sauri dan yanason yamata rashin mutunci
Yazo gunta yace wani shishigin yasa ki biyoni abun ya kullar da ita ta juya zata koma dan haka yayi saurin rikota
Ta juyo tayi saurin fuzgan hannunta
Yace God i can't wait na ganki a gidana cux am gonna kill you
Tayi wani murmushi sannan tace Hell no we are gonna kill each other and karkaga ina ma shiru iyayena kawai nake bi dana yarda zancen nan kuma bari kaji wani abu wlh i won't take anything non-sence
Ya kalleta ya girgiza kai yace you are still young
Ita kuma a rayuwanta abunda ta tsana kenan ace mata karaman yarinya
Yace your face looks cute idan kinhada rai
Ta juya kawai batayi magana ba
Shima ya ja motanshi ya tafi yana jin haushin kanshi da ze aure wannan karaman yarinyan shi da yake sha'awan auren wanda ta gama school ma'ana babban mace
πππ
[22:09, 1/21/2017] Tyetyelorh-❣:
_*WASHE GARI*_
Misalin karfe 3 ta fito daga dakinta ta tarar da Meemah tana kallon carton a parlo seta wuce kitchen ta debu garin kwaki ita ba wani sha takeyi bah amma danta ja mata rai ne kawai
Taje ta wanke sannan tasa madaran ruwa da peanut a ciki da sugar ta ta fito ta zauna kusa da ita
Ta daga kai ta kalleta taga tana shan abu a cup dan haka ta leka ta ga gari ta matso kusa da ita tace Auntie Ameenah wai Uncle Adeel yace kinada kirki bakida rowa
Tayi murmushi kawai tana juya garin da spoon tace zakisha ne
Da sauri tace yes please
Zan baki amma se kinyi promising abu daya
Tace whatever it ix i promise
Ta mika mata sannan ta tashi daman me kurkur tazo dan haka taje sukayi
Ita kuma daman Auntie ta tafi kasuwa sayo yadin kayan da Amarya zata sa na Kamu, Mothers day da kuma na Dinner
Hadda Indian night za'ayi amma Mami ta sayo masu kayan da zasu sa ranan hadda Adeel
Yau ta kama ranan Monday ana sauran kwana biyu a fara biki dan Ranann
Wedesday za'ayi lalle da daddare kuma ayi Indian Night
Thursday za'ayi Kamu da yamma
Firday Mothers day da misalin karfe 2:pm
Da yamma kuma bridesmate dinta zasuyi bridal-shower
Saturday daurin aure da safe se yini sannan da daddare ayi dinner sannan akai amarya
Sunday kuma ayi budan kai
Amma duk wannan shirya shiryan duk Ameenah bata sani ba ita tana can tana tunanin yadda takeson brithday ta ya kasance batasan ranan birthday ne za'ayi yini da Dinner babu time
A yaune zata kuma gida dan akwai wani kawan Mami a layinsu take tace taba ma Amarya da kawayanta part daya a gidanta toh can zasu kuma harse an gama biki..........
πππ
πΈ
_ tyetyelorh_
[18:53, 1/24/2017] Tyetyelorh-❣: πππ _UMARNIN IYAYE_πππ
_WRITTEN BY:_
_TYETYELORH_
_EDITED BY:_
_AMEENATOU_
πππ
8⃣0⃣ ↗ 8⃣5⃣
Da aka gama mata kurkur sannan Auntie ta dawo dan data sayo kayan ta tsaya ta hadu da telon da gidansu Adeel suka turo ta mashi snding styles dinda zeyi sannan ta tsaya a wani shagon takalmi da poss da sayo kala uku ku wanne da dan uwanshi sannan ta taho gida duk a gajiye
Seda ta huta tayi wanka taci abinci ta biya sallah sannan tasa Ameenah ta hada kayanta suka kama hanyan gidansu ita ke driving Ameenah na zaune dayan sit din ita kuma Meemah tana baya an hada ta da video game tanata faman yi
Suna isa ta fito daga motan tayi cikin gida a guje tana kiran Mami. Hakeem amma bata gansu ba se uban mutane yan kauye yan uwansu ne duk sun ciki gidan
A ranta tace ina biki sude kawai azu a cika cika tayi tsaki tana shiga parlo sega wata yar tsohowa abukiyar fadan ta ce
Tace Amarya bakya lefi kuda kin kashe baban angon ta kalleta batayi magana ba
Ta cigaba kinga inda kikayi kyau kuwa
Tace toh ina ruwanki da kyan da nayi wlh inna lami tsofanki yana kara saki gulma
Inna lami ta mike wai zata kamota da dan sandanta
Ameenah ta tsaya tana mata dariya tace ae base nayi godu bah dan ba iya kamani zakiyi ba mutum ma da kyar yake tafiya amma se gulman masifa
Da taga ba iya kamota zatayi bah seta daga sandanta zata buga mata ae se Ameenah tasa kafa tana mata dariya ta godu.
Tace ae da kin tsaya da yau se anyi amarya me kafa daya
Ta kofan baya ta shiga dakin Mmi dan taga mutane sunyi yawa a gun da zata wuce kuma duk masu surutu ne
Tana shiga dakin Mami ta tarar da ita a tsaye tana neman abu cikin handbag dinta ae aguje taje ta rungumeta tana ihu
Mami ta juyo itama ta riketa dan tayi kewanta babu karya
Tace Mami me kike nema haka
Ta saketa tace wlh keys din dakinki na nema na rasa dan zanba Abbah ajiya danni bakin sunyi yawa a dakina
Kuma idan kin haihu kika zo gida wanka seki sauka anan tana magana tana dariya
Ta hada fuska kaman baza tayi magana bah tace toh kaya nafa da handbags dina ga shoes dina rabinsu fa ban taba sawa bah
Kuma akwai wasu kayan da na sayo masu fatye a india suna ciki
Mami tace toh bari na nemu sena baki ki debu su
Sega Auntie ta shigo ta wulla ma Ameenah handbag dinta tace kin barma baiwarki da dauko maki koh
Ta amsa tana mata dariya tace ina Meemah
Wlh tana gun Hakeem suna kasa tare da Ahmed na gansu
Ta cigaba Mami nida wa zamu geran ne dan yanxin aka kirani wai sun iso da kayan dakin Ameenah
Mami tace keda Ameerah zaki dan kinsan yakamata ace akwai frnd dinta daya tunda ita zatasan yadda takeson dakin ya zama kuma tun dazin ma suka iso itada fatye suna gidan da zasu zauna
ae a guje Ameenah tayi waje dan ta je gun frnds dinta
Auntie ta girgiza kai tace toh barin je mu wuce dan kinga Yamma yayi daga nan kawai zamu tafi da ita na tabbata ta fadan ma iyayenta ae amma se wesnesday da safe zamu dawo
Tace toh Allah ya kiyaye hanya amma Meemah fah
Tace tare zamu da ita
Toh shikenan se kun dawo Allah bada sa'a
Ta amsa da Ameen sannan ta fita dayake ta hadu kayansu daman harse bayan biki zata kuma gidanta ranan daurin auren kennan kuma ranna daddy Meemah ze dawo
Ameenah tana fita ta dan rage gudu amma tana dan sauri kadan seta hango Hakeem ae batasan sanda ta fara gudu ba tayi huging dinshi shima ya riketa yace ae na aza bazama ki kulani bah dan naga shigowanki
Murmushi kawai tayi
Meemah ta kallesu ya yamutsa fuska tace act mature plxx
Duk suka bude baki suna kallonta ita babu ruwanta ta cigaba da playing video game dinta
Ameenah ta dungura kanta
Tace auchhh
Ahmed yace dn't hurt my wife
Hakeem yace aa matana de
Meemah ta daga kai ta kalle Hakeem tace you are not my type but Uncle Ahmed is my type
Yace dats what am talking about suka tafa
Hakeem ya kalla Ameenah yace na tabbata ke kike koya mata wannan abun
Tayi dariya tace ae yarinyan nan tafi karfina
Ahmed wlh munada case dakai
Yace me nayi yanxin
Ta lausa hannunshi tace bansani bah ta wuce
Tana shiga gidan part dinda aka bar masu ta wuce ae kuwa ta tarar dasu dukka tayi ihu ta ringa huging dinsu tace i miss you guyx like crazy
Suka zauna akata hira ita kuma Ameerah ta dauka karamin travelling bag tana sa kayanta a ciki dan Mami ta gayan mata tare zasu da Auntie
Ameerah tayi mata wani irin kallo Ameenah ta bugeta tace me haka
Tace wlh kinyi kyau kalla inda hips dinki ya kara fito wa ji boobs dinki
Ta kulla kirjinta tace bansan iskanci wlh kina sani kunya
Duk sukayi dariya
Ameerah tace amma kunsan wani abu a cikin mu fa ban taba tunanin ke zaki fara aure bah dan ke kwata kwata baki san maganan aure
Tace ae da yadda nasone da sena gama karatuna gabadaya sannan na aura prince charming dina
Amma an kama an hadani da wani waishi footballer dukdade inason footballer amma-
Bata kau aya ba fatye ta katseta tace yanada packs
Ameenah tace a mana randa naga packs dinshi ae seda na kware
Safieyarh ce tayi gyaran murya
Se a lokacin suka tuna ita sistern shice
Fatye ta rike baki Ameerah sister Ahmed wanda ake kira da ummitarh ta kawo wani zancen
Haka suka taro akanta sunata mata tsiya
Har Auntie ta shigo suka gaidata sannan Ameerah ta mike suka kama hanyan Abuja
πππ
[10:24, 1/25/2017] Tyetyelorh-❣: Ranan wednesday da misalin karfe 7am duk sunata bacci a dakinsu Amarya da kawayenta Mami dakanta taxo ta tashesu dan me lalle tazo
Ameenah data tashi Mami tace tashi ga me lalle tazo
Se kawai ta fashe mata da kuka tace dan Allah Mami kiyi hakuri ku bar lallen nan gasu safieyarh nan ayi masu wlh ni na hakura
Safieyarh tace idan ba haukanki ba taya za'ama kawayen Amarya lalle amma ba'ama gaiyan biki bah
Ameenah ta kalleta ta mata dakuwaππΌ
tace jiya fa se gun 3am muka kwanta wlh bacci be isen bah dan Allah ku a fara maku
Mami ta wulla mata wani bakin riga tace gashi kisa wannan idan aka fara dake zefi sauri danke hadda jan lalle za'a sa maki
Da kyar aka samu ta yarda amma da zumbure zumburen baki aka fara lallen se galla ma me lallen harara takeyi tun bakwai da fabi aka fara ba'a gama ba se 11 duk ta gaji da zama amma lallen yayi masifan kyau dan atafin hannunta akayi mata design din lalle me kyau sannan aka sa A amma ita Ameenah bata sani ba dan Mami ce tasa me lallen dole tasa
Bayan an gama su safieyarh aka ringa daukan shi photo dan design ya masifan haduwa
Kuma da aka gama ba daman tashi dole seya bushe ga jan lalle a tagin kafa kawai kallanshi takeyi itama tasan ya mata kyau amma ji take kaman ta kwabe shi dukka amma tasan idan ta kwabe Mami zatace se an sake wani
Da safieyarh aka fara bridesmate dinta za'a masu hannu biyu kafa biyu while raguwan yan bikin hannu ne kawai
Ana gama ma safieyarh sega su Ameerah sun dawo daga geren suka ringa ihu Ameenah ba halin tashi dan haka ihu ta ringa yi
Ameerah ta zauna tace kunga gidan waiyazubillah tunda Ameenah ta sama mu semu ruke Allah namu yafi nata
Wlh gidan kaman palace idan zaka shiga gate din cewa zakayi kawai _*open sesame*_
Amma se anyi registering voice dinka sannan dakin Ameenah inda wannan dakin nata yake amma kayan ciki God yafi wannan sosai dan closet dinta ba'a magana kai Abbah yayi kukari wlh dan kunsan wani abu akwatinta ba'a taba bah fa munde jerasu a closet dinta amma ku budewa bamuyi bah dakinta is purple and light pink dakin Adeel ma ya hadu shi gadonshi is blue kai dakinshi shima ya hadu dan ma yafi na Ameenah haduwa
Ameenah ta galla mata harara batayi magana ba duk suka kwashe da dariya
Duk aka gama masu lallensu sannan na Ameenah ya bushe dukka hadda jan da aka mata dan haka safieyarh ce ta taimaka mata ta tayata wankewa tunda nata ya bushe
Suna zaune musalin karfe daya da mintuna Mami ta kira number fatye tace mata suzo itada safieyarh dan haka suka tashi suka tafi gidan
Suna shiga cikin gidan da Hakeem suka ci karo safieyarh ta galla mai harara ta wuce seya jawo hannun fatye yace zo dan Allah akwai maganan da zamuyi
Tace toh ina zuwa barinje na dawo Mami na kiran mu
Yace dan Allah idan kika dawo ki kirani a phone dina
Tace toh ta wuce ta kira safieyarh tace ta jirata
Tana isowa gunta tace wani wulakanci ne kuma wannan kindena ma Hakeem ne magana
Ta kalleta tace ya dena min magana de ta kwashe yadda sukayi sanda sukaje india ta fadan mata
Ta girgiza kai tace amma wlh ke banza ce yanxin baki gane sonki yake ba
Seda gabanta yayi wani mummunan fadi taja burki ta tsaya tace wannan irin sona yake
Tace mude je Mami na jiran mu zamuyi magan wani lokaci
Tace toh shikenan amma jikinta har wani rawa yakeyi
Suna shiga dakin Mami akwai mutane dayawa a ciki dan haka taja su suka shiga dakin Ameenah ta dauko kaya ta mika masu kayan da Ameenah zatasa dan yaune indian Night da daddare
Da suka bude kayan ya hadu irin duguwan rigan nanne zuwa kneels irin budeden nan se wando da veil dinshi kalanshi is golden suka ringa santin kayan
Sannan ta ciro masu nasu dan tasan suma basusan za'ayi indian Night bah
Nasu su hadu is red and blue kalan bridemates kenan
Suka amsa suka ringa godiya
Tace babu komai suma yaranta ne zata iya masu komai
Suka fito gidan suka tafi fatye tama manta da magan da sukayi da Hakeem
Suna shiga suka fito da kayan kowa yazo ya zaba ae ko kaman tasan size dinsu kuwa cicip
Ameenah ta kalla nata tace ba inda zata
Duk suka taro suna bata hakura akan ta yarda taje dukka event din bikin saboda farantama iyayenta rai kodan ta rabu dasu lafiya
Ummitarh sister Ahmed tace wlh Ameenah Abbah da Mami sun kashe kudi a bikin nan kudansu kiyi hakuri mana idan ba haka ba wlh Allah seya tambayeki
Suka ringa mata wa'azi harta yarda
Safieyarh ta bata yan kunne da sarkanshi da abun hannu sannan da abun nan na india suke sawa a goshi wanda zata sa da event din inji Mami
Mami kuwa aeka Auntie Aysha tayi gidansu Adeel takai mai kayan data sayo mai na indian Night din
Shi yana kwance a dakinshi yana kallon football gabadaya ya manta wai yau za'a fara bikinshi se idan ya sauka kasa ne idan yaji hayaniya yake tunawa dan gidansu a cike yake da danji
Mommy ta shigo ta kawo mashi kayan ya kalla yace dan Allah Mommy kiyi hakura amma bazan sama zuwa bah
Ta kalleshi kawai seta mike zata fita
Yayi sauri ya ya kamo hannunta tayi murmushi seta daure fuska sannan ta juyo yace am srry kawo zani
Tayi murmushi tayi pecking kumata tace Allah ma albarka sannan ta fita
πΈ
_ TYETYELORH_
[23:07, 1/29/2017] Tyetyelorh-❣: πππ _UMARNIN IYAYE_πππ
_WRITTEN BY:_
_TYETYELORH_
_EDITED BY:_
_AMEENATOU_
πππ
8⃣5⃣ ↗ 9⃣0⃣
Da misalin karfe takwas bayan sun gama isha aka shiga wanka kuwa ya kara wanka lokacin me kwalliya tazo
Dan haka tana fitowa daga wanka ta shafa mai tasa inner wears sannan ta zauna aka fara mata kwalliyan ita bata san too mch make-up dan haka lips dinta kawai aka gyara mata akayi lining dinshi sosai sannan aka mata gyaran gira amma beyi dark sosai bah se powder shi kenan ko su foundation ba'a sa mata ba ande mata using dinsu a gyaran lips da gira
Sannan aka mata wannan _*cheek-bone*_ dinda ake yayi a make-up tayi mashifan kyau dukda ba wani kwalliyan hauka aka mata bah
Ana gamawa tace ayima frndx dinta duk sukace basaso suma sun iya haka kowa yayi kwalliyanshi
Bayan Ameenah ta gama shiryawa tasa duguwan riga da wandon se aka mata donut da gashinta yayi kyau setasa gyalen inda india suke sawa a kafadansu
Duk suka kalleta sukace bade haka zaki bah tace haka zani mana
Kai Ameenah akwai fa manya agun wlh ban taba ganin Amarya kamanki ba baki damu da auren ba sannan bakida kunya
Ameerah ke wannan magana
Tace toh ya kukeson nayi
Ameerah ta dauko wani katon veil irin na india ne amma is blue tunda blue takalmi zatasa tace idan zaki shiga hall din se ki yafa wannan kina zuwa inda zaki zauna baseki cire bah
Tace tohm naji
Duk suka gama shirinsu se kamshin turare kakeji kawai
Ameenah tasha yan kunnen da Mami ta bada akawo mata gabadaya set din tasa abun goshin nan
Idan ka kalleta sekace indian ce dan kawai haskenta ba irin nasu bane amma tayi kyau ba'a magana
Suna zaune lokacin 8 da mintuna aka aiko cewa ga motan daukansu yazo dan haka duk suka fita ummitarh ta yafa mata veil din suka fita
Adeel kuwa da mommy ta bashi kayan ajiye wa yayi seya cigaba da kallonshi ita se jiranshi takeyi amma be fito ba gashi tym se wucewa yakeyi ka gashi su duk sun shirya wasu ma sun tafi hall din
dan haka ta mike ta shiga dakinshi ae kuwa ta tarar dashi yana kwance harya fara gengedi salati ta fara tana tafa hannunta ae a furgice ya tashi dan yasan bashida gaskiya
Yana mikewa beyi magana ba ya tashi da sauri ya shiga toilet yayi wanka ita kuma ta zauna a bakin gadonshi tana jiranshi ya fito dan tasan idan bata tsaya ba yana fitowa zama ze karayi
Yana gama wanka ya fito ya tarar da ita ta dauka kayan ta mika mai ba muso ya amsa ya shiga closet dinshi anan ya shafa mai ya shafa mai a gashinshi dukda ba me yawa bane gashin sannan ya shafa turaren jikin yasa kayan
Ya kalla kanshi a mirror yayi murmushi kawai ya fito tareda hulan kayan a hannunshi Mommy tayi murmushi tace kaman _yash_ murmushi kawai yayi mata ta amsa hulan tasa mai sannan ta debu turaruka kala biyu ta runga fesa mai seda yayi atashawa sannan ta kyaleshi
Phone dinta ya fara ringing ta dauka Zaid ne tace mai yawwa gashi nan shigo ku fita tare
Abokin Adeel ne shi bema san da bikin ba seda Mommy ta kirshi ta gayan mai
Shigowa yayi da sallama Adeel ya kalleshi da mamaki ya durkusa ya gaida Mommy ta amsa sannan ta fita
Adeel yazo ya rungumeshi yace yaushe a garin
Yace dallah ni sakeni wai ace zakayi biki Mommy ce zata kirani ta gayan min sannan na kira number switched off
Adeel ya ringa bashi hakuri dakyar ya sauka sannan suka fito yan gidan se tsokanshi akeyi ana ango ango shi murmushi kawai yayi masu ya wuce
Suna isa gun motan Zaid
Adeel ya kama kofan gaba yana son ya shiga yace toh wlh baka isa ba a baya zaka zauna
Ya kalleshi meyasa zan zauna a baya
Yaufa kai angone kuma yanxin gidan su amaryan zamu mu daukota tare zaku wajan
Adeel ya juya wai ze koma cikin gida
Yayi sauri ya rikoshi yace meye haka ana jiranmu fah
Yace kaje kawai ka dauko amaryan ku tafi tare ni na fasa zuwa
Zaid yace toh shikenan amma bari kaji wallahi idan ka kuma cikin gidan nan toh karka sake tuna kasan wani wai _zaid_
Ya juya ya kalleshi
Ya daga mai kai yace yes am deadly serious i mean every word i said ya bude motan ya shiga yasa key ze tada kennan kawai yaji an bude kofan baya yayi murmushi amma be juya bah ya tada motan suka kama hanyan zuwa dauko amarya
Suna isa suka faka sega wani yaro yazo wucewa zaid ya aikashi ya kira su dan beda number amaryan
Haka suka fito tun daga ciki suka yafa mata veil din dayake hakeem ma ya dauko motanshi shima Ahmed ya dauko nashi
Toh suna fitowa zaid ne ya karaso gunsu suka gaisa da frndx dinta sannan yace ran amarya ya dade ita bata san muryan ba dan haka ta gaidashi kawai yace shi ze tafi da amarya dan angon yana cikin motan Ameerah tace toh shikenan ta rike hannun Ameenah dan su karasa gun motan ta nuke wai ita bazata shiga mota daya dashi bah
Ameerah tace toh ta ciro phone dinta tace barin kira Abbah na gayan mashi inji ku ranshi ze baci da sauri ta fuzga wayan daga hannunta tace muje
Zaid yayi murmushi yace nice job
Ameerah itama murmushi tamai ta rike hannunta suka tafi gun motan zaid ne ya bude mata kofan da zata shiga ta shiga ta zauna ita kuma Ameerah ta gaida Adeel ya amsa da fara'a sosai a fuskanshi yace ya gajiyan biki tace ae yanxin muka fara
Ameenah tayi mamaki da taji yayi magana ita kuwa rufe kofan tayi ta wuce
Zaid ya tsaya yana kallonta ita bata ma sani bah tanata tafiyanta
Adeel ne yace toh mallam nifa na gaji da zama da wannan abun gu daya kazo mu tafi
A lokacin ne ya shiga motan yana murmushi
Ita kuwa Ameenah abunda ya gaya ya kullar da ita amma tayi shiru kanta a cikin veil
Zaid yana tada motan yace wlh yarinyar ta burgeni ya tada suka fara tafiya
Adeel yace ae daga ganinta tanada hankali da nutsuwa ba kaman- seya juna Ameenah da babban yatsanshi
Ita kuma tana gani ta cikin gyalenta
Bata san sanda ta fito daga cikin veil dinba ta cije danyatsan
Ae da sauri ya janye yace awchh yana rije da hannun
Tace stay out of my business
Ya juyo yace what d heck anan ne yaga kwalliyanta ya tsaya yana kallonta
Ba lefi ta danyi kyau a zuciyanshi yayi maganan
Taja veil din ta rufe fuskanta
Shi kuwa zaid se dariya yake mashi dan yaga alaman yaji zafi
Adeel yace kutt ni kika ciza koh za ki gani yau babu Mami sannan babu Mommy agun nan
Ya fara matsowa kusa da ita a hankali se matsowa yakeyi
Ita kuma dataga haka se gabanta ya fara dukan uku uku
Ya daga hannunshi yasa a west dinta yana cewa ni kika ciza koh
Da taji hannunshi a west dinta ta kwalla wani uban kara da bata taba yinshi ba a rayuwanta dan tasan shine kawai ze taimake ta
Rike kunnanshi yayi yace damn!!!
Zaid kuwa bema san sanda ya sake motan bah ya rike kunnanshi dashi
Dan isaka kawai toh ni ba yar isaka bace mugu kawai seta fara hawaye
Zaid yace dan Allah Adeel kabar yarinyan mutane
Ya sake matsawa kusa da ita yace me kikace dan isaka koh toh barin nuna maki aikin dan iska ya kara matsawa kusa da ita da yaga alaman tana son ta sake wani ihun yayi sauri ya kamo bakinta da hannushi yace plxx karki kara na barki ya saketa ya kuma gun zamanshi
Taji alaman lipstick dinta ya baci ta taba taji yayi baja baja
Seta fara kuka a hankali tace mugu kawai me kamada mugaye ka kama ka batamin lipstick dina
Yayi sauri ya kalla hannunshi gashi nan a jiki yace ewww yayi sauri ya ciro abu ya fara gujewa yace shiyasa kikayi kyau ashe kwalliyan ne
Shi bema san sanda maganan ya fito daga bakinshi bah
Ta dago tace Awwwwwn really?? Nayi maka kyau
Yace who me.Allah kiyaye
Tayi murmushi tace too late
Zaid shi se dariga yakeyi yace you guyx are d cutest couple ever
A tare sukace we are not a couple
Ita Ameenah mamakin Adeel takeyi kaman bashi bane wanda be magana kwata kwata be dariya se idan suna hira da safieyarh amma gashi yau yace mata tayi kyau
Can kuma se tace ewww
A zuciyanta taketa maganan nan
πππ
[13:09, 1/30/2017] Tyetyelorh-❣: Su Ameerah kuwa motan Hakeem ta shiga itada Ummitarh
Ahmed kuwa fitowa yayi daga nashi motan yace lallai se fatye ta shiga motanshi haka kuwa akayi
Safieyarh ma ta biyosu dan tunda fatye ta gayan mata cewa Hakeem sonta yakeyi se gabadaya batasan ma su hadu dashi.
A motan hakeem ummitarh ce a gaba Ameerah na baya se hira sukeyi a ciki
Motan Ahmed ma Safieyarh ce a gaba fatye na baya suka kama hanyan hall din
Dayake a silver-sand za'ayi event din nan suka tafi suna isa an cika dan motoci ne kala kala a gun su Adeel tun dazin suka iso su kawai suke jira su shiga hall din
Suna isowa fatye da safieyarh ne suka je gun motan su Adeel suka bude gun Ameenah
Ta dago da jan idonta tace fatye ko gyara min lipstick dina suka kalla lipstick din gaja gaja a tare suka kalla Adeel
Kaman ance ya juya shima ya kallesu
Safieyarh tace yaya Adeel seya kalla Ameenah
Yace wait nthing happened see your dirty mind
Tayi murmushi tace ae bance komai bah
Ummitarh ta dauko make-up poss dinta ta gyara mata sannan aka aika akace ga amarya da ango sun iso dan haka aka saka masu waka daban na shigowa
Meemah ce a gaba da dan duguwan riganta na india gashin nan an gyara matashi sannan ga lallenta tayi kyau sosai se Amarya da Ango se Zaid da Ameerah sannan Hakeem da safieya se kallonta yakeyi amma ita ta dauke kai se Ahmed da fatye da kuma ummitarh da fa'iz shima frnd din Adeel ne agun suka sameshi ya rigasu zuwa
Sunyi matukar kyau danse daukansu hoto Auntie Aysha ce tazo ta hada hannunsu gu daya
Sukaje suka zauna agun zamasu Ameenah tayi saurin ta kwace hannunta daga nashi
Ameerah tazo ta cire mata veil din
Haka de akayi indian Night anyi barin kudi kowa yaci yasha akace su fito suyi rawa dakyar suka fito anyi masu liki sosai kai anyi barin kudi ba'a magana
Ba'a bar wurin nan ba se 11 da rabi da mutane suka fara tafiya se Ameeenah ta zage tayi rawanta
Yanda sukazo haka suka koma se fada sukeyi a cikin motan a tare suka iso da frndx dinta Zaid ya sauketa yace toh seda safe koh
Tace toh Allah ya kaimu ta gallama Adeel harara tayi shigewanta
Suna shiga kowa changa kaya yayi ya haye gado tunda kafin su tafi sukayi sallah su
Washe gari ya kama ran thursday akayi kamu shima duk sunyi kyau Amarya kuwa ango se satan kallonta yakeyi
Ran firday kuma akayi Mothers day seda yamma ne za'ayi bridal-shower se shirya shirya sukeyi dan tunda aka dawo daga Mothers day suka tafi gidansu ummitarh wato(Ameerah sister Ahmed) sunata shirya gun suka bar Ameenah ita da Hakeem se hira sukeyi kaman basu bane da kullum cikin fada
0 comments:
Post a Comment