Suna isa asibitin emergency ward aka shiga dashi
Wani kujera suka zauna akai Hakeem yana shafa bayan Mami a hanakali yana bata hakuri shimade hawaye yakeyi a hankali
Can setace mai ya kira Daddy ya fadan mai beyi musu ba yadan fito waje ya shiga kiran numbershi
Bugu daya ya daga ku gaisawa basuyi yace "Daddy, Abbah ba lafiya yanzin muka kawoshi asibiti"
"Subhanallah amma da sauki koh"
"A toh har yanxin de za'a fito daga dakin bah"
"Waiyazubillaha toh gani nan zuwa" seya katse wayan
Number Ameenah ya shiga kira na farko bata dauka ba sena biyu tana dagawa se tace Ya Hakeem
"Uhmm Ameenah Abbah fa bayada lafiya"
Mikewa tayi da sauri tace meyafaru dashi
"Sumewa yayi muna gida yanzin de yana asibiti but ya sama sauki" fada yayi kawai dan karta bamu sosai
Kuka ta farayi sosai shi kuma seya kasa magana
Katse wayan tayi kawai tana kuka ta shiga kiran number Adeel be wani dadi yana ringing ba ya daga
Kukan da yaji tanayi ne ya mugun firgitashi mikewa yayi zaune yana tambayan lafiya meyafaru
"Abbah!!"
"Abbah ya maimaita meya faru dashi Ameenah
"Wai yana asibiti an kwantar dashi bayada lafiya"
"Subhanallah"
"Ni inason naje na ganshi"
Da Mamaki yace "Ameenah are you kidding me ke kadai zaki kaduna"
"Dan Allah i really want to see him please"
"Kin manta abunda ya faru damune a hanyan Abujan"
Tace i really don't care i just want to see him seta sake fashewa da kuka
"Toh ya isa barinsa a turo maki wani daga office dinmu yazo ya kai ki dan is not save kije ke kadai"
"Noh please befa da lafiya i want to be with him now dan Allah this the one thing am asking from you ina zuwa naga ya sama sauki zan dawo"
"Ameenah bafa zuwanki bane banso ki kama hanyan tun daga kaduna zuwa Abujah ke daya shine banso"
"Why do you care i just want to see my father" seta sake fashewa da kauka
"Because i care about you Ameenah i don't want anything to happen tou you"
Se yayi shiru
"Ya Adeel this once please" kuka me tsuma rai ta saki da sauri yace "toh ya isa haka dena kuka kinji"
Daga mai kai tayi kaman yana gabanta
"Ameenah be kamata ace yanxin ke kadai ki kama hanyan Kaduna ba be kamata wlh kuma kince bakison na turo da yanxin ya iso har kun kama hanya"
"Ya Adeel wlh bazanyi gudu bah i promise" batasan sanda kuka ya sake kwace mata bah
Ya isa toh ki dena kuka mana ya isa haka tashi ki tafi besan sanda ya fadi haka bah ko dan besan jin kukan nata ne
Wani tsalle tayi "Thank you so much i love you, U're the best" seta kashe call din ta ajiye wayan akan kujera mikewa tayi dakinta ta shiga dayake duguwan riga ne a jikinta armless gyale ta yafa irin babban nan amma babu kauri dakin Adeel ta shiga key din tsohowan motanshi ta dauka fitowa tayi da sauri
Code din security ta danna nan da 1minute ze shiga security dan haka duk wanda ze shigo gidan seya danna
Motan ta shiga taga full tank fita da motan kawai tayi babu abunda ta dauka ko wayanta ma bata dauka bah kota manta ne oho
Addu'a tayi seta fita ta kama hanya ba wani gudu takeyi bah amma tama driving tana hawaye
Shi kam haryanxin wayan na manne a kunnanshi cus he is shock by what she just said
Itaa bata ma san ta fada bah dan dadi ne kawai
Ya dade a haka har wani team mate dinshi ya shigo dakinshi bema san ya shigo ba seda ta tabashi ya furgita seya cire wayan
Tambayanshi yayi meya faru dashi
"Nothin" kawai yace seya mike jakanshi na sport ya dauko suka fito
PARIS
Afra ne da Afreen keta shirya kayansu dan gobe zasuzo one week zasuyi su kuma se faman dauki akeyi
Wayan Afra ne yayi ringing tana dagawa taga saurayinta ne salman ke kira
Soyayya suke sosai tana sonshi shima yana sonta dande ba wani babba bane shiyasa basuyi aure bah
Afra da Afreen mate din Ameenah ne da safieyarh
Sunada hadin kai yaran sosai dan ku a school ne ba'a tabasu ka zauna lafiya duk inda sukaje ana sansu
Afreen batada saurayi ita cus tace she's not ready to date farkon haduwan Afra da salma lokacin bata sonshi kullum seya zo gidan idan batajin fita seta tura Afreen ta fita dan ba'a taba ganesu se wanda ya dade dasu ke ganesu
Mama ce ta shigo ta kalla Afra wani kallo da seda kayan cikinta ya kada tace ba nace maki jiya karki fita bah na gayan maki salman dinnan is a bad influence on you amma baki yarda bah koh
Afra zatayi magana Mami ta mika mata hannu tace bani phone dinki you are grounded for two days
Babu fita koh tv bazaki kalla ba
Ba yadda ta iya haka tayi ending call din ta mika mata
Afreen zatayi magana Mama ta dakatar da ita tace don't even start dan duk abunda zakiyi bazaki zauna da ita a daki bah and maganan zuwa Nigeria se nan da two days na fasa goben
Saboda sun saba duk sanda za'ayi punishing daya toh dole se an hada da dayan zata tayin rashin ji harse itama an hada daita
Zuwa tayi ta dauka laptop din Afra ta fita dashi
A cikinsu Afra ce mara jin magana Afreen kuma duk abunda ka sata babu musu zatayi shi and idan kace ta zauna anan for two hours zata zauna toh banbancinsu kenan da yar uwanta
Duk basuji dadin daga tafiyan da Mama tayi masu bah kuka Afreen ta farayi tana cewa its all your fault seda nace karki fita amma kika fita
Hakura Afra ta ringa bata har seda tayi shiru
NIGERIA
Abbah har yanxin be tashi bah su Daddy sun iso hadda Mommy da Safieyarh
Mami gabadayanta a rude take se kwantar mata da hankali akeyi
Adeel kowa tunda suka fara match dinsu hankalinshi be kanshi kwata-kwata se tunanin Ameenah yakeyi besan dalili ba amma se ji yake daman be yarda ta tafi bah yayi zurfi cikin tunani se kawai yaji an bugu mai kwallo a kanshi
Seya dawo hayyacinshi kallon wanda ya bugu mai kwallon yayi yaga yana mai dariya dan dayan team dinne
Wani murmushin mugunta yayi ya cigaba da kwalla
Kallonshi ya sakeyi kawai ya bugu mai kwallo a abunshi (dick) rike wajan yayi kawai seya kwanta a tsakiyan feild din dan azaba
Wani wawan dariya Adeel ya saki
Bashi red card akayi kawai ya dauka jakanshi ya bar wurin dan daman baya cikin kanshi
Gida ya wuce abinshi
Ameenah tafiya take a cikin low speed guntun tsaki ta saki seta fuzga motan da karfi gudu ta ringayi
_40 minutes later_
Abbah ya farfado har an barsu duk sun shiga dakin
Dr yace daman gajiya ne kawai yanxin za'a barshi a asibitin na kwana biyu yadan hutu dan be kamata a age dinshi ya ringa aiki sosai bah
Hira sukeyi dukkansu hadda Abbah kaman bashi bane ya sume dazin daga kan da Hakeem zeyi ya kalla tv kawai seya mike a furgice yace "Wannan ba motan Adeel bane"
Gabadayansu suka maida hankalinsu kan tv
Abbah yace daga ganin mota anyi accident a tv se kace na Adeel ne shine kadai me irin motan
Cameran dake daukan accident din seya tsaya akan number motan yace yanxin nan akayi accident dinnan dan koh 10mins ba'ayi bah kuma mace guda dayace a cikin motan
Ga number motan nan duk wanda ya santa azo a dauki gawanta a bakin tall gate dake kaduna kafin a tafi da ita
Jiri ne ya fara kwasan Hakeem Daddy dake kusa dashi ya tareshi yace lafiyanka
"Wlh motan Adeel ne ga number nan"
Mami ce ta karaso gunshi tace meya faru ne
"Mami wlh Ameenah ce nina gayan mata Abbah bayada lafiya kuma wlh number motan Adeel ne wannan" seya fashe da wani kuka
Mami kasa yarda a abunda take ji a kunnanta take seta fara baya-baya a hanakali tana girgiza kanata "No! No!! No!!!" Kawai take maimaitawa
Abbah na ganin haka seya mike kafin ya karasa gunta harta fadi sumammiya
Salati duk suka farayi safieyarh ce ta fita a guje ta kira doctor ba'a bata lokaci ba akazo aka dauketa wani daki aka shiga da ita Abbah ya bisu
Daddy ne ya dawo gun da Hakeem ke tsaye ya kasa ko motsi ne se cewa yake "nine wlh its all my fault"
Daddy yace Hakeem ka fahimtar damu abunda ke faruwa mana
Dakyar ya rike kukan da yakeyi yace "Daddy dazin sanda Abbah ya suma na kira Ameenah na gayan mata bata bari na gama magana ba ta kashe tana kuka and wlh wannan number motan Adeel ne dan tare mukaje muka sayo"
Ya karasa magana yana wani irin kukan da be tabayi bah
"Innalillahi wa'innailaihir raji'un" shine kawai abunda suke maimaitawa safieyarh kowa kuka takeyi kawai ta durkusa a kasa
Hawaye Mommy ta farayi itama
Daddy kowa ya kasa magana se salati yakeyi
πππ
[14:10, 3/22/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: Daga baya Daddy ne kawai yayi karfin hali yakama hannun Hakeem suka fita motanshi suka shiga
Tall gate suka tafi Hakeem ba abunda yakeyi se kuka ji yake kaman a mafarki "this not happening ya Allah kasa ba ita bace Allah ina rukanka kasa ba Ameenah bace" kuka ya sake saki wane danshi aka aikoshi duniya
Abbah ne ke tsaye a bakin dakin da aka shiga da Mami yana leka ta window se kawai doctor ya fito yace
Alhaji be kamata ka fito ba munason ka hutane
"Dr meyasa zakace haka matata ce fah wannan and you are expecting me na zauna kawai"
"Noh ba haka nake nufi bah and anyways she's going to be okey shock ne kawai ya sameta, wai meyasa ta samu shock dinne??"
A lokacin ne ya tuna abunda Hakeem ke fadan masu dan haka da sauri ya wuce dakin yabar doctor a tsaye a wurin
Yana shiga dakin Safieyarh ya sama tana durkuse se kuka takeyi haka ma Mommy ta dafe bango tana kuka kasa magana yayi seya taba aljihunshi yaji wayanshi dan haka seya fito dashi number Ameenah ya shiga kira dan kwata-kwata be yarda da abunda Hakeem ke cewa bah
Ya kira yafi so 10 amma ba'a daga bah still be hakura bah ya cigana da kira zuciyanshi na mashi wani radadi dan he can't bare it to lose his daugher that he care so much of
Cigaba da kiran number yayi yana zazzaga cikin asibitin
Basu wani dade suka isa tall gate saboda gudun da Daddy keta famanyi a titi
Suna isa lokacin wanjan a ciki yake kowa yana ganin mumunan hatsarin da ya faru wasu hadda kuka
Ambulance ya iso gun dan haka harsun dauka gawan ansa a mota police kuma sun fara binkice akan hatsarin dansu ganu idan ganganci ne ku kuma kasheta akayi
Suna zuwa dakyar Daddy ya cusa kanshi cikin mutane gun motan yaje yaganshi a mole kaman irin an maidata ball ji yayi kaman ya fashe da kuka
Tambaya ya farayi ina yarinyan cikin motan yake wani police ya gayan mashi tana cikin Ambulance dan haka wajan ya nufa
Driver yayi ma magana yace mashi shine baban yarinyan fitowa sukayi gefe suka raba yake cemai yanason ya tafi da ita gidane ayi mata sutura
"Ka tabbata yarka ce"
"Mallam wannan wanna irin tambayane zanzo nayi maka karyane barin kira maka yayanta" be jira amsanshi bah ya juya cikin motan ya kuma ya kira Hakeem fitowa sukayi dakyar Hakeem ke tafiya idon nan nashi jajir kaman gaiwashi suna zuwa gun mutumin yace ga yayanta nan kuma mijinta baya kasan ance mata babanta ba lafiya ne daga Abuja take shiyasa ta kamo hanya
Girgiza kai yayi alaman yaji tausayinsu zuwa yayi ya bude masu ita ba'a ganeta dan ta kune ta kuma baka sosai baxa'a taba cewa ita bace dalili dayane za'a tabbatar itace shine kibanta da tsayinta
Hakeem yana gani fashewa ya sakeyi da wani kuka
Mutumin da sauri ya kulleta
Daddy koma da aka budeta kauda fuska yayi sauri yayi kawai se hawaye ya fara zubu mai rike Hakeem yayi ya maidashi cikin motan kaman karamin yaro
Sake dawowa yayi aka bashi wasu yakardu yayi signing sannan ya kuma cikin motan
Hakeem ne ya kalleshi yace ina take dakyar yake magana dan muryanshi har ya fara dashewa
"Zasu biyomu da Ambulance din" kawai ya iya cewa yana tada motan
Fita daga motan Hakeem yayi ko magana beyi ma Daddy bah gun Ambulance din ya nufa kawai budewa yayi ya shiga ze zauna kenan wani mutum ya tambaueshi "lafiya ?"
Beyi mashi magana bah se driver yace yayanta ne ka barshi
Zama yayi kusa da ita dafata yayi se kuka yake kaman ranshi ze fita
Daddy harya biyoshi amma dayaga ya shiga motan seya kuma nashi motan gaba ya shiga yana tafiya while Ambulance din yana binshi a baya
*************
Abbah kowa harya gaji da kiranta waje ya samu ya dafe kanshi kawai yana hawaye danya fara yarda da abunda Hakeem yace
Adeel kowa yana isa gida jikinshi yaji ya fara rawa wanda ya kasa gane dalili wayanshi ya dauka ya shiga kiran number Ameenah amma bata daga bah se jikinshi ya fara sanyi koma....
IG.Tyetyelorh
[18:28, 3/23/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: πππUMARNIN IYAYEπππ
WRITTEN BY:
TYETYELORH
EDITED BY:
AMEENATOU
πππ
*123*
Su Daddy gida suka wuce (gidansu Ameenah) da Ambulance din har a lokacin Hakeem yana dafe da yar uwarshi yana kuka yan cikin motan harsun gaji da bashi hakuri duk sunyi shiru
Gawan aka fito da ita me gadi yana ganin an shigo da gawa ga kuma Hakeem na faman kuka ga Daddy shima yana hawaye seya fashe da kuka yana " Innalillahi wainna'ilaihirraji'un Alhaji lokaci daya zaka tafi ka barmu"
Babu wanda yabi ta kanshi shiga da ita cikin dakin Abbah akayi a lullubeta
Fitowa sukayi Hakeem ya sama waje ya zauna kusa da yar'uwar shi kuka yakeyi sosai har a yanxin yana dafe da ita yana kuka while a zuciyanshi yana hada mata da addu'a kuma yana blaming kanshi wai duk lefinshi ne
Police din shiga Amblance sukayi suka kama gabansu
***********
Abbah beyi kwari a gwiwa bah ya cigaba da kiran number nata idan nashi ya shiga sena Adeel shima ya shiga haka suka ringayi can se doctor ya leko ya kirashi akan matanshi ta tashi mikewa yayi da sauri ya shiga dakin
A kwance ya sameta tanata faman ajiyan zuciya fuskanta ya jike sharkaf da hawaye karasawa yayi kusa da ita da sauri ya dafa ta
Kafin yayi magana se tace "Alhaji an dauko gawanta"
Dumm!! Yaji kirjinshi ya buga "Gawanta kuma" ya maimaita
Cire hannunta yayi daga jikinshi seya fara baya a hankali "Kema kim yarda ta mutu No!! Ameenah tana nan Ameenh bata mutu bah she's too young to die this not right No!!! Please Ameenah bata mutu bah"
Se yayi waje a guje mikewa tayi itama ta bishi da sauri
Suna shiga har a lokacin Mommy da safieyarh suna kuka kaman ransu ze fita tsayawa yayi yana kallonsu hawaye ne ya fara zubu mai kama hanya yayi ze fita Mami ta rikoshi itama tana hawaye "Alhaji ina zaka"
"Dauko maku Ameenah zanje nayi ku ganta dan bata mutu bah"
Mommy ce ta mike dakyar fitowa tayi kuma se duk suka biyota da doctor suka ci karo a bakin kofa
"Lafiya ina zaku haka dukkanku"
Bude gefan jakanta Mommy tayi credit card dinta ta ciro mika mashi kawai tayi danta san kudinsu yakeso
Beyi magana bah ya amsa saboda ba a wannan asibitin suka buse file ba a Giwa suka bude toh abunda ya kawosu nan shine dan yagi sauri yakeyi lokacin Hakeem a rude yake
Bata jira yayi wani magana bah ta wuce Mami na rikeda hannun Abbah suka bita while safieyarh na biye dasu itama a baya
Gun packing mota suka tsaya Abbah na kokarin ciro key ya shiga Mommy tace ya bata key din danta san baze iya tukawa bah
Mika mata yayi kaman robort
Goge hawayenta tayi seta amsa shiga tayi safieyarh ta shiga gaba Mami da Abbah kuma suna baya kwantar da kanshi yayi akan kafadanta kaman karamin yaro yana hawaye itama tanayi
Tada motan tayi suka fara tafiya
Kuka safieyarh keyi mara sauti sosai wayanta ta ciro messege ta farayi cewa Ameenah ta rasu a yau dinnan marking number Ameerah,fatye da Ummitarh tayi ta masu sending
Motan shiru se shan majina da kowa ke faman yi a cikin motan
Suna isa gidan har mutane sun cika dan dayawan mutanen unguwa sunji karan Ambluance dan haka aka leko se kuma sukaga an shigar da gawa
Wani wawan kuka Safieyarh ta sake saki
Gabadaya suka fito
Daddy ya rike hannun Mami se kace karamin baby
Cikin gidan suka wuce se kallon Abbah akeyi dan acikin 100% na mutanen gidan toh 80% duk sun dauka Abbah ne ya rasu basu kula kowa bah suka hau sama a zaune suka tarar da Daddy yana dafe da kanshi
Dagowa yayi da yaji motsin mutane fuskanshi sharakaf da hawaye
Kasa magana Abbah da Mami sukayi suna kallonshi kawai
Karfin hali yayi seya nuna masu kofan dakin kawai
Shiga sukayi dukkansu hadda shi a hankali Abbah ke tura kofan Hakeem ya fara hangowa ya rungumeta yana kuka amma ba'ajin komai dan muryanshi ta gama dashewa
Mami ce ta karasa gunta seta yaye abunda aka lullubeta dashi tana ganin fuskan a kune yake
Fashewa tayi da kuka se tayi waje a guje
Safieyarh kowa tana makale a jikin bangon dakin tana rera nata kukan Abbah kowa ya kasa komai yana tsaye kawai
Can ya kalla Daddy daketa kallon Hakeem yana share hawaye yace "Alhaji Adeel kowa ya sani?"
Girgiza mashi kai yayai alaman be sani bah dan haka se yace "Toh a kirashi ace ya dawo gida yanxin dan yayi ma matanshi addu'a kafin akaita final destination dinta"
Kallon Hakeem yayi yace "jeka kira liman"
Be tsaya yaji amsanshi bah ya fita daga dakin
Daddy yace ma Hakeem dake niyan tashi yana share hawaye " bari zan kirashi" seya fita
Wayanshi ya ciro kan Number Adeel har ze kira se kuma ya tsaya yana kallon number kawai ya kusan 10mins yana kallon number kawai se finally ya kira
Lokacin Adeel harya gaji da kiran number Ameenah ya kira na Hakeem shima yafi sau 10 be daga bah na safieyarh shima ya ringa kira bata dauka bah saboda wayan a silent yake toh se jikinshi ya fara bashi babu lafiya ya kira Number Mommy itama thesame answer dan haka kawai seya kulle gidanshi ya fito dagashi se wayanshi da passport dinshi se credit card
Airport ya nufa dan zuciyanshi na ayyana mashi kawai Abbah ya rasu yana isa Airport din jet ya sama wanda ze kawoshi kaduna direct (shata kenan inji mama π)
Harya shiga sunyi nisa se wayanshi ya fara kara da sauri ya duba yaga manager shi dan yau da yamma yanada wani match din guntun tsaki yayi amma be daga bah
Yana gama ringing harzesa a Airplane mode seya kara ringing amma wannan karan Daddy ne
Da sauri ya dauka a kunne ya kara yace "Daddy"
"Uhmmm ka taho gida yanxin"
Gabanshi ne ya fadi dumm!!! "Lafiya Daddy? Meyafaru?"
Ka taho de kawai kuma meye zaka gani kuma kazo kaduna ne gidan Abbah ku.
Dumm!! Ya sake fadi
Daddy be tsaya yaji meze ce bah kawai yayi hanging up
"Innalillahi wa'inna"ilaihirraji'un " abunda ya fadi kenan a fili "Allah sarki Ameenah only god knows halin da take ciki yanxin i really want to be by her side right now" tunanin da yakeyi kenan yana ji kaman ya bace ya ganshi tare da ita
Kwantar da kanshi yayi a jikin sit din idonshi a kulle kawai se wayan ya sake ringing dagowa yayi ya duba kan screen din still it was his manager
Dugan tsaki yaja seya kashe wayan gabadaya ya saka a aljihu ya kumar da kanshi inda yake da yana tunanin yanzin dukka family kowa na nan shine kadai agogon hannunshi ya dago ya kalla seya leka window "God" ya fadi a fili gabadaya ya kago yaga sun isa ji yayi dama tun farko beyi wannan tafiyan bah "Mteww" ya sake jan wani
*********
Abbah daya fita daga dakinshi dakin Ameenah ya wuce yayi sa'a a bude yake dan da safe Mami ta bude ta dauka abu
Yana shiga ya maida kofan ya rufe hadda saka key
Kawai sake wani kuka yayi seya durkusa a kasa "How he wish all this was a dream ji yake dama shine ya mutu ba Ameenah ba cus she has a life ahead of her"
Kuka yake rerawa kaman yaron shekara 10 wanda mamanshi passed away recently
_Some hours later_
Lokacin har anyi mata wanka an sakata a likafani Hakeem na ganin haka kaman a mafarki kuka ya sake fashewa dashi yace "Be kamata a sata cikin wannan abun bah wlh bata mutu bah Ameenah is still alife bacci takeyi wlh bacci takeyi karku dauka hakkinta ku kasheta Ameenah please ki tsaki ki gayan masu ba mutuwa kikayi bah zasu kasheki da ranki fah"
Sanbatu yakeyi wasu ma gani suke kaman ya fara taubuwa Daddy ne ya kama hannunshi dakin Mami suka shiga ya zaunar dashi bakin gado kwantar mashi da hankalinshi ya farayi but it does'nt work shi kawai so yake yaga sistershi ta mike
Adeel ne ya sauka a Airport din kaduna taxi ya samo ba tareda bata lokaci bah ya shige koh ciniki basuyi bah
Saka shi yayi ya zinga gudu a titin nan kaman wanda saku haura sama.
πππ
[21:36, 3/23/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: Suna isowa bakin layin motoci ne a cike a layin
Har kofan gida taxi driver ya ajiyeshi ya fito da sauri harze shiga cikin gidan driver yace mashi kudinshin fah
Dawowa yayi kawai ya cire designer watch dinshi ya mika mai dan koh biyar bedashi a hannunshi credit card dinshi ne kawai
Be tsaya jin me zece bah ya shige gidan
Motane ne cike a gidan tun daga bakin gate din aka fara mai gaisuwa
"Allah jikanta Allah sa ta huta"
Kallonsu kawai yakeyi amma beyi magana bah dan kanshi ya daure
Cikin mutane ya ringa shiga se "Allah jikanta" ake cemai amma se yayi ignoring dinsu
Sama yahau kawai se yaga Abbah ya fito daga dakin Ameenah
Wani wawan firgita yayi tsayawa yayi chak a wajan ya kasa motsawa
Abbah na ganinshi da sauri ya karaso yayi huging dinshi yana hawaye
Har a lokacin yana tsaye kaman kendil and ya kasa huging nashi back
Dagowa yayi ya kalleshi irin kallon da yake mai ya tabbata shima ya aza shine ya rasu girgiza kai yayi yana shafe hawaye seya wuce inda gawan yake dan yayi mata addu'a
Binshi da kallo yayi kawai ji yayi an fada jikinshi ana kuka juyawan da zeyi yaga Safieyarh tana kuka tana cewa "Ya Adeel, Why would this happen to her she don't deserve it"
Dagota yayi yace waye wai? Meke faruwa? Wait ina Ameenah take batazo bane
Kuka ta sake fashewa dashi ta kasa magana kawai sega Ameerah ta shigo tana hawaye gunta taje tayi huging dinta sunata kuka abun tausayi
Kallonsu yakeyi gabadaya kanshi ya dagule ya rasa tunanin me zeyi wai ina ma Ameenah take
Dakin da yaga Abbah ya shiga nan ya nufa jiki a sanyaye yanxin kuma seya fara tunanin koh Mami ce ta rasu
Tura kofan yayi se yaga Daddy ,Mommy, Mami da Hakeem a ciki da kuma Abbah daya juya ma kofan baya yana durkushe kaman mutum a gabanshi
A tare gabadaya suka juyo suka kalleshi banda Abbah
Dukkansu kuka sukeyi kallonsu shima yakeyi
Mami ce ta mike da sauri ta rungumeshi tana wani kuka ita kwata-kwata batayi wani kuka sosai ba seda taga Adeel kawai se taji tausayinshi
Chak ya tsaya can yace Mami ina Ameenah take ko bata iso bane har yanxin
Kuka duk suka sake sekewa a lokaci daya
Kwace kanshi daga runguman da Mami tayi mashi yayi yace "Can someone just tell me what the fuck is going on here why do you people keep crying and where the hell is my wife"
magana yake a tsawa ce abunda be tabayi ma babba ba kenan gashi kuma harya kaiga yima iyayenshi
Hakeem ne yace gatanan ya nuna mai gawanta
Kai kallonshi yayi zuwa inda ya nuna mai seyaga Abbah gaba ya karayi for better view mutum ya gani a lullube cikin likafani
"No!! No!!" Ya fada da karfi karasawa gun yayi da sauri se kuma ya tsaya can ya cigaba da tafiya daya isa gun durkusawa yayi a hankali yakai hannunshi ya yaye fuskanta
Kauda fuska yayi da sauri "No!! This not Ameenah wlh ba ita bace Ameenah fa yanxin zata iso ba ita bace wannan ba ita bace ita fah bata iso bah wlh bata iso bah No!!! You can't do this to me " seya saki wani kuka me tsuma rai kaman ba namiji bah
Mommy ce ta taso ta rungumeshi itama tana kuka
"Mommy kema kin yarda itace wlh ba ita bace ku dena mata kuka Ameenah bata rasu bah nasan bazata tafi ta barni bah you can't just live ki tashi ki gayan masu baki mutu bah i have so much to tell you bazan iya rayuwa ba tareda ke bah " kuka ne yaci karfinshi
Abbah ne ya taso ya rikeshi yana cewa "Adeel addu'a ya kamata kayi mata ba kuka ba saboda haka ya isa haka kuzo muje muyi mata sallah" karfin hali kawai yakeyi shima din
*******
An riga anyi mata sallah an ajiye ta akace family ta suzo suyi mata addu'a kafin akaita makwancinta haka akayi daga kan Abbah aka fara
Ya dade yana mata addu'a yanayi yana kuka Mamai itama tayi mata tasha kuka majina baja-baja a fuskanta
Se Daddy shima ya dade yana mata Mommy itama tazo tayi nata
Se Hakeem durkusawa yayi ya dade yana kuka kafin yayi mata addu'a sosai se safieyarh ita kasa addu'an tayi kuka kawai takeyi kaman za'a cire mata rai Mommy ce tazo ta dagata
Adeel shine karshe yana durkuse kusa da Mami yama kasa kuka binsu yake da ido kawai Daddy yace yaje yayi ma matanshi addu'a kafin akata makwancinta na hakika
Dakyar ya mike yana zuwa gabanta ji yayi wani kuka ya kwace mashi se kawai ya rungumeta kaman ze sata a ciki kuka yakeyi kaman ba namiji bah riketa yayi gagam
Dakyar ya saketa still yana kuka addu'a yashiga yi mata kusan 30mins yana mata addu'a sosai yake kuka
Matan wajan suma kuka suka shigayi saboda tausayi
Anzo daukanta dayake daman an sakata a makara
Riketa yayi yace kar wanda ya taba mashi matanshi ze cigaba da zama da ita karwanda ya tabata
Kuka yake abun tausayi shima haka su Hakeem da safieyarh
Abbah ne ya rikeshi yana bashi hakuri kan cewa ya bari a tafi da ita kwace jikinshi yayi da karfi
Yayi kan gawanta "Ameenah dan Allah ki mike ki tashi karsu tafi dake i love you so much wlh idan kika tafi kika barni zan kashe kaina na gwammace na biki mu tafi tare Ameenah ki tashi karkiyi min haka please"
Kukarin daukan gawan suka farayi Abbah yana hawaye yana kukarin rikeshi " Abbah dan Allah am begging you guyx ku barmin matana wlh zan iya zama da ita a haka ku barmin ita karku rabamu"
Su Mami kuka sukeyi sosai dan ya mugun basu tausayi kallon Daddy yayi seya je gunshi da sauri ya rikeshi "Daddy kayi masu magana su barmin matana zan iya zama da ita a haka wlh Daddy zan iya mutuwa idan suka tafi da ita"
Abbah ne ya bada izinin a tafi da ita Hakeem yana kuka yazo ya rike Adeel
"Hakeem kaima hadda kai kaima zaka bari a tafi da ita am really disappointed in you" juyawan da zeyi kawai yaga sun wuce da ita hadda Abbah da Daddy kama hanyan binsu yayi su Mami suka rikeshi suna bashi hakuri kallon gawan ya sakeyi kawai seya zube a kasa .....
IG.Tyetyelorh
[21:34, 3/26/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: πππUMARNIN IYAYEπππ
WRITTEN BY:
TYETYELORH
EDITED BY:
AMEENATOU
πππ
*126*
Hakeem ne da Afra suna zauna a dakinshi ita tana kan gadonshi da wayanta a hannunta dan tun zuwansu Mama ta bata kayanta
While shi kuma yana kasa a kwance da wani novel a hannunshi _What to expect when you are expecting_
na Ameenah ne tun zuwansu ya sace mata tayi-tayi ya bata kayanta amma yaki shine ya fito dashi yana karantawa dakin shiru
Afreen ce ta shigo ta fuzga wayan Afra "Mama na kiranki kuma wlh naga fuskanta a daure"
"Nashiga uku Allah sa bata gane na saya sabon sim card bane"
"Hehe yau wata yarinya zataci gidansu " Hakeem ya fada yana dariyan mugunta shida Afreen
Punching kafadanshi tayi irin na wasa ta mike ta fita jikinta har rawa yakeyi dan duk rashin jinta Mama na gyara mata zama
Tana shiga dakin Mami ta ganta a zaune akan kujera
Murmushi Mama ta sake mata kafin ta karaso dakin
Wani wawan ajiyam zuciya tayi tunda taga fuska karasawa tayi gunta tace gani Mama
Nuna mata gefanta tayi zauna anan baby girl
Zama tayi
"Yawwa kinsan muna sonku keda sister ki bazamu so abunda ze cutar daku bah koh"
Daga mata kai tayi alaman ehh
"Toh barin tafi kan zancen munga kin girma dan haka muka zaban maki mijin aure a garin nan"
Da sauri ta dago kanta tareda dafa hannunta kan kirjinta "Aure!!!" Ta maimaita
Daga mata kai tayi alaman taji daidai "muna son kibi Umarnin mu dan har Baba ma ya yarda da zancen nan da two week za'ayi bikin
Kuka ta fashe dashi "Mama dan Allah kuyi hakuri ku rufa min asiri idan de salman ne wlh i promise you na rabu dashi daga yau bazan sake kulashi bah am still young dan Allah kuyi hakuri wlh frnds dina zasu ce-"
"Me frnds din naki zasuce since when do you care about what people say about you Afra? yanxin de maganan aure babu ja dole se kin zauna ko kinaso ko baki so"
"Mama Hakeem ne??"
Kallonta tayi da mamaki yadda ta dauke kukan lokaci daya tana tambayan idan Hakeem ne"
"Toh bashi bane Adeel ne"
"Innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un" na shiga uku yau Mama Ya Adeel zaki aura min mijin Ameenah wayyo yau an kasheni ta daura hannu akai tana ihu
Daka mata wani tsawa tayi "bakida hankali koh meye haka toh"
"Mama yanxin fisabilillah Mijin Ameenah zaki aura min" seta fashe da kuka dan Allah ku taimaka min ni wlh na yarda da auren amma dan Allah da Ya Hakeem nakeso
Mikewa tayi ta zare mata ido "Baza'a aura maki Hakeem dinba Adeel zaki aura babu gudu bajada baya dole ki zauna dashi" har zata fita se kuma ta tsaya
"Sauran kuma ki kira Baban ku wlh nida kene"
Seta fita daga dakin
Fashewa tayi da kuka wai ita wlh batason ta aura mijin Ameenah ya zataji idan ta gane ta auran mata mijinta dama dane kafin ya aureta toh da zata iya aurenshi dan yana mata kyau kuka take sosai
Ashe duk wannan zancen a kunnan Afreen da Hakeem dan tana fita suma suka biyota suka labe da Mama zata fito kuma sukuyi sauri suka sauko
Daman shi Hakeem ya gane tun zuwansu tana sonshi so be wani damu da abunda tace bah
Afreen ce ta dawo ta rungume Yar'Uwarta sunata kuka tare
Shima Hakeem beji dadi ba
********
Zance de ya garara gari da dangi cewa za'a hada auren Adeel da yar'uwan marigayiya matanshi wasu na zagi cewa koh wata biyu ba'ayi bah wasu kuma Allah bada zaman lafiya kawai suke cewa
Adeel de har yanxin kaman ana miya dashi se wani kara ramewa yakeyi yasa a ranshi kawai mutuwa zeyi shima dan haka maganan aiki gabadaya ma ya dena tunanin shi
Amma su office din sun gane halinda yake ciki saboda haka basu mai maganan komawa bah sun bashi time dan ya kuma abun tausayi
Rayuwa ta cigaba da tafiya anata shirya-shiryen bikin kullum Afra cikin kuka take ita batason tayi aure yanxin
Har Babanta ya turo makudan kudi wai a sayan mata kayan daki dasu dan Mama tace mashi a kaduna zasu zauna shi yafison ayi auren sesu kuma paris din da zama
Ana sauran One week a lokacin Alhaji ya bada kyautan gida wanda zasu zauna a ciki dakyar Daddy ya yadda ya amsa dan seda yaga Alhajin ya bata rai
Alhaji yace "Ni kamar yaran cikina na daukesu dan haka karku damu"
Godiya yayi mai a gaban Adeel ya bada gidan amma seya dauke kai yayi kaman besan abunda sukeyi bah ji yake kaman ya shake wuyanshi ya mutu ko ze huta
Daddy ya basu Mami key din gida su uku sukaje ganin gidan Mami,Mama da Mommy sunyi santin gidan sosai dan ya hadu ga gun parking babba hadda garden a cikin gidan
Afra dukta rame tana kwance da waya a kunnanta tana waya da Salman "Babe har yanxin fa suna kana bakansu basu chanja ba ni wlh bazan iya aurenshi bah"
"Ya isa dena kuka kinsan wani abu ranan daurin auren idan basu chanja ba kawai ki kamu hanya passport dinki na gunki koh"
"Aa yana gun Mama"
"Toh ae kinsan yadda zakiyi ki dauko zan turo maki kudi kawai seki kamu hanya ni senazo na daukeki a Airport"
"Haba yanxin so kake na gudu daga gun iyayena ni gaskiya bazan iya bah"
"Bazaki iyaba wanda suka nuna basu sanki shine kike cewa bazaki gudu ba toh shi kenan kita zama nasan daman baki sona ae"
Da sauri ta tsayar dashi" Am so soryy zanzo nasan Mama batasona ae Baba ne kawai ke suna shima hadda shi aka hada abun nan gara na gudu kawai "
Haka suka gama plan dinsu akan ranan dauren aure zata taho
Bayan two days hartaji alert ya turo mata kudin
Su Mama anyi ordering kayan dakin Afra online har an kawo masu dan haka aka je mata jere hadda Safieyarh dasu Ameerah suna cikin yi Ameerah ta fashe da kuka tace ita bazata iya ba jakanta ta dauka ta fice sunata bata hakuri ta dawo amma taki gida ta wuce abinta tanata kuka
Gidan Afra yayi kyau sosai ba'a magana komai nata me tsadan gaske an gama shirya komai
Ku ina acan-acan gwanin sha'awa
Kuma an kawo mata wata mata yar muduguri tazo tana mata gyaran jiki itama Afreen tace dole se an hada da ita ba yadda ta iya se ta mata itama
Su Daddy koma sun hada akwatuna duk abunda akeyi dukkansu basusan ya ake ciki bah kowa na daki gara ma Afra dan Afreen takanzo ta gayan mata abubuwa kaman gidanta ya hadu an kawo akwati
Adeel kowa duk wanda ze shigo mashi daki seya hanashi shigowa wani katon drawer ya saka ya tare kofan daki
Daddy yazo yata knocking amma baze bude mai bah haka ze hakura danshi duk haushinsu yakeji ji yake kaman basu damu da happiness dinshi bah shiyasa suka sake hada aurenshi da wata
Ana gobe daurin aure Afra ta lallaba dakin Mamansu taje ta dauko passport dinta ta boye cikin jakanta tareda credit card dinta ta ajiye dan batason ta tafi da komai saboda idan tazo fita daga gida aka ganta da kaya za'a gane
Auntie kowa Mami ta kirata akan tazo harta gaji danta ki zuwa dan tun zanda aka gayan mata za'ayi hadin batayi magana ba de amma bata sake lekowa gidan ba dan taga be kamata ba kaman basu tausaya ma Adeel a yanxin tace bazata sake saka kafanta a gidan bah tunda su basuda tausayi
Abbah ne a kofan dakin Adeel yanata knocking da wani bugeggen shadda a cikin leda irin farar ledan nan
Ya dade yana knocking amma ba'a bude bah idan ya tura seyaji abu ya tare kiran sunanshi ya shiga kira amma be amsa ba dukda yana jinshi sarai
"Adeel taso ka bude min kofan nan tun kafin na bata maka rai"
Shiru ba'a bude bah
"Adeel you know we all love this the best we can do for you please open up"
Lallaman shi ya dade yana yi a bakin kofan kawai se Adeel ya mike ya bude mai seya kuma ya zauna bakin gadonshi
Binshi yayi a baya ya zauna kusa dashi
"Adeel i know exactly how you feel-"
"No you don't" ya kaste shi da sauri
"Noh you have no idea how i feel have you ever lost some one you ever loved have you???
Have you ever lost a girl you loved and never told her you love her??
You don't have any idea how it feels you don't" ya kare maganan yana niyan tashi
Rike mai hannun yayi ya maidashi ya zauna "You are right i don't am so sorry but this the best we can do for you right now ga kayan nan gobene daurin auran wannan kayan shi zaka saka nasan duk wannan abunda kake yi saboda ka faranta mana ne kuma insha Allahu, Allah ze saka maka Allah yayi maka albarka yasa ka gama da dunyi lafiya yajikan matanka"
Da sauri ya amsa da "Ameen "
Murmushi yayi se yace dan Allah ka aske wannan gemu kaji dana
Daga mai kai kawai yayi yana fita yamaida drawer ya kuma ya kwanta
A daren ranan Babansu Afra ya iso fadawa tayi jikinshi tanata faman kuka wai ita yace a fasa auren
Hakuri ya shiga bata dan haka seta mike ta barshi a wurin
πππ
[22:29, 3/26/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: _Washe gari_
Ranan ya kama ranan juma'a tou an yanke se an sauko daga sallah juma'a se a daura auren se ayi walima akai amarya anata shirye-shirye
Daddy yasa Adeel a gaba sedaya aske gemun nan gabadaya sannan ya shiga wanka yayi ya fito ya saka bugaggiyan farar shadda yayi kyau sosai duk a ganban Daddy yake shirin saboda yasan idan ya fita baze shiraya bah
Yana gama shiryawa seya fita Mommy ta shigo tana fesa mashi turare seya tuna haka ranan dauren aurensu da Ameenah ta ringa mashi wanka da turare dukda yana hanata
Rungumeta kawai yayi murmushi tayi se tayi huging nashi back tana tapping bayanshi a hankali
Sun dade a haka daga baya ya saketa
Mama ce da atamfa a hannunta super ta bada a dinka ma Afra saboda ta saka
Dakin ta shiga babu kowa seta ajiye kayan kan gado tayi knocking kofan birthroom amma shiru dan haka seta murda ta bude babu kowa a ciki
Tazo fita ne se taga paper akan mirror kai hannu tayi ta dauka ta bude
Karantawa ta farayi seta saki salati
"Afra abunda kika zaban ma kanki kenan toh kije duniya ce"
Fitowa tayi parlo taga Mami da Afreen a zaune duk Afreen ta haye jikinta kaman maje
Hawaye cike a idonta tayi gunsu mikama Mami paper tayi
"Lafiya takaddan meye wannan" tana tambaya tana kukarin buedeqa
"Afra mana"
Afree ita ta leka ta karanta salati itama saki tana tafa hannu
"Yanxin abunda Afra zatayi kenan ta gwammace tabi saurayi akan tayi aure"
"Hmm ki barta kawai duniya ce da kaman ita kadai na haifa se nayi hadiyan zuciya Allah nagode maka"
Tana gama magana se tayi parlon Abbah
Dukka ta tarar dasu acan Abbah da Baba se Hakeem take gayan masu abinda ake ciki
Waya Baba ya dauka ze kirata
"Don't bother tace tabar wayan a gida dan haka ka barta da kafanta zata dawo" inji Mama
Abbah yace "ae sujuji za'a kira a dubata tin kafin tayi nisa
Hanawa Mama tayi tace wlh abarta duk dadan dadewa da kafanta zata dawo
Badan sunsu ba suka hakuri
Baba yace toh ayi auren da Afreen dan yasan ta fita biyayya ita zata yarda
Mama tace toh shikenan seta fita
Acan parlo kowa Mami ta dauka wayanta ta kira Number Mommy tana bata labarin abunda ya faru
Itama salati tayi Adeel dake kusa da ita wanda yaji abunda suke fara seya saki murmushi wanda rabanshi dayin murmushi tun wayansu na karshe da Ameenah randa zata rasu
Abbah shima ya kira Daddy yake gayan mashi amma yace ya kwantar da hankalinshi da Afreen za'a daura
"Amma dukda hakan Alhaji kamata yayi ya bincikata koh"
"A hakane ni na rigada nasa a dubata amma karku damu yadda aka saka lokaci a lokacin za'a daura"
"Toh shikenan Allah sa shiyafi alkairi"
Ameen ya amsa dashi seya kashe call din
Mama ta fito parlo taga Afreen dan haka seta ja hannunta sukayi daki a bakin gado suka zauna
"Afreen kinga abunda yar'uwarki tayi koh nasan ke bazaki yi haka ba dan kinada biyyaya
Afreen am begging you-"
"Mama ki dena rukana nasan abunda zakice min karki damu na amince your wish is my command"
Wani wawan hug Mama takaima Afreen hadda hawayenta
"Afreen kin gama min komai Allah maki albarka saka wannan aure alkairi na"
"Ameen Mama"
Saketa tayi jekiyi wanka kizo na shirayaki dakaina
Murmushi tayi ta mike ta shiga toilet
An gama magana an sanar da kowa cewa da Afreen za'ayi yanxin a take a wajan ta sama motoci guda biyu daya daga gun Daddy while dayan taga gun Abbah dan ba karamin dadi sukaji bah kuma duk masu tsada
Ta gama shirinta ba karamin kyau tayi ba tasha zinare gashi daurin dankwanin nan yayi kyau ba karamin kyau tayi bah
Mami ce ta dauka waya tana kiran Auntie dakyar ta samu ta dauka kafin tayi magana tace
"Aysha wlh idan bakizo a yanzin ba babu ni bake" se tayi hanging up
Badan taso ba ta kama shiryawa dukda yau mijinta ze dawo suka kamo hanya itada Meemah
Adeel ya gama shirinshi suka shigo mota yana baya shida Safieyarh se Mommy da Daddy suna gaba dan gidansu Hakeem zasuje yanxin daga nan se'a tafi masallacin ayi sallah juma'a se'a daura aure
A tare suka iso da Auntie dan tana shigo da mota suma suka shigo da nasu
Tana fitowa suka gaisa dasu Daddy seta kalla Adeel wani mugun tausayinshi taje kawai seta shige gidan dasauri
Babu kowa a parlo dan haka seta leka na Abbah acan ta gansu dukka amma banda Afreen dake daki ita daya
Gaida kowa tayi amma Mami take amsa nata
Matsawa tayi kusa da ita ta ringa lallamata abunka da jini nan da nan ta hakura
Meemah kowa tana makale a jikin Hakeem
Su Adeel suka shigo suka sama waje suka zauna suma
Adeel a kasa ya zauna aka gaigaisa
Shima ya shiga gaida kowa tunda ya shigo gabashi ke fadi sosai
Zama akayi anata hira amma shi tunda ya dukar da kanshi be daga bah
Can Hakeem,Safieyarh da Meemah suka fito tsakar gida suna hira a bakin mota yasha shadda shima ya daura Meemah a saman motan se faman hira sukeyi suna dariya
Se sukaji an shigo a tare suka daga kansu suna ganin wanda ya shigo gabadaya suka saki wani dan banzan ihu a tare kuma suka kasa motsawa
Can Hakeem yayi karfin amma be bar ihun ba yayi parlo a guje itama Safieyarh ta bishi anan suka bar Meemah tana kan mota se ihu takeyi tana kuka
Suna shiga parlon a guje a tare kowa ya tashi a tsorace yana tambayan lafiya sun kasa magana se nuna kofa sukeyi
Auntiee kowa tamabayan yarta takeyi
A tare Auntie da Adeel sukayi waje se kuma suka tsaya a tare sanadin abunda suka gani sun kasa motsi kwata-kwata
Yan parlon gadaya suma suka fito Hakeem da Safieyarh ne a baya dan su kadai suka san abunda sika gani
Suma tsayawa sukayi they were all shocked ko motsi ba meye a gun se Meemah daketa ihu tana kan mota bazata iya saukowa bah
Sun kusan 10mins a tsaye babu wanda yayi kwakwaran motsi se Adeel daya bude bakinshi dakyar yace "Am......."......
IG.Tyetyelorh
[14:40, 3/26/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: πππUMARNIN IYAYEπππ
WRITTEN BY:
TYETYELORH
EDITED BY:
AMEENATOU
πππ
_#I give zero fucks and i got zero chill in me_❣
*125*
_Some minutes later_
A lokacin su Afra sun iso layin dayake taxi suka sama Mama ce ta zauna a gaba tana hango mutane a kofan gidan kuka ta saki kawai
Afra ce ta fara tambayanta meyafaru shiru tayi still batayi mata magana bah
Parking taxi driver yayi yace gaskiya mota bazata iya wucewa ba daga nan dan haka bari ya taya su shigar da kayansu
Fitowa sukayi ya bude trunk din ya fara fito da kayan suna gaba yana binsu a baya
Jikin Afra da Afreen de ya fara sanyi da suka shiga gidan dan se kuke-kuke ake famanyi
Mama tana hango Mami aguje taje ta rungumeta suna kuka
Kallon juna twins suka se kuma suka maida kallonsu gunsu Mami
Can da suka saki juna se Afreen taje gun Mami ta rike mata hannu tace "Mami meyafaru wai meyasa kuke kuka meyasa kowa ke kuka?"
Itama ta rike mata hannu tace "Afreen ,Ameenah ce.Ameenah ta tafi ta barmu"
Da sauri Afra ta motsu kusa dasu "Mami what do you mean by that?"
"I mean Ameenah left us she left all of a sudden she's too young to die" ta gama tana kuka
Mama ce ta riketa tace Mami ke dena irin wannan maganan "kullu nafsin za'ikatul maut" so duk kankantan yaro dole ya mutu
"No!! Noh!!! Munyi da ita fah zamuzo why?? Meyasa zata tafi" seta fashe da kuka Afra ce me wannan maganan durkusawa tayi a kasa suka hada kansu itada Afreen suna kuka sosai
Durkusawa Mami tayi ta rungumesu tana tapping bayansu
While Mam tana tsaye ta saka hannunta akan baki tana hawaye
Shide driver ya gama ajiye masu kaya dayaga alaman rasuwa akayi seyayi masu gaisuwa ya tafi
Acan hospital din kowa Adeel rai a hannun Allah dan sun isa akayi emergency ward dashi abunda Alhaji yayi using ya daure mashi hannun dashi har ya kuma jajir dan farar shadda ce
Kuka Mommy keyi sosai Alhaji yana bata baki sesu Abbah suma suka iso
*******
Doctor ne ya fito da sauri sukayi kanshi suna tambayan jikinshi murmushi yayi "Allah de ya taimaka cut din da yayi be taba vein din nashi bah dan haka fatan hannunshi ne kawai ya yanke so yanxin de munyi mashi alluran bacci kuma an dinje wajan saboda yana cikin tashin hankali se maganganu yake akan...... Ameenah ryt ita"
Girgiza kai sukayi Alhaji ya mika mai hannu sukayi musabaha "toh mun gode sosai doctor yanxin mahaifiyarshi zata iya shiga ganinshi"
"A zata iya amma please kar ayi surutu sosai yadda ze huta sosai"
Mommy da sauri ta shige dakin
Su kuma suka dan zauna suna jiran ta fito dan kar suyi yawa a ciki
Tana karasawa bakin gadon kallonshi tayi har ya rame kaman wanda yayi kwana biyu yana jinya
Gashinshi ta shafa tana hawaye she really can't afford losing him
Ta dade a haka seta share hawayenta ta leko dan haka suma suka shiga sun tausaya mai sosai kuma haka ya tabbatar masu cewa yana son matanshi
_Two weeks later_
Kwanansu Adeel biyu aka sallamesu maimakon suyi gida se suka kuma gidansu Hakeem acan suke kwana dukkansu hadda Daddy
Su Afra ma anan suke kwana a cikin dakonan dake kasa
Yanzin Adeel ko magana bayayi be fitowa daga daki se daki anan yake sallah abinci ma ya yaye shi se idan Mommy ta sashi a gaba tana kuka yake ci duk ya gama lalacewa ya kare a lokaci daya kwata-kwata be bacci yana kwantawa tou dole yayi mafarkin Ameenah koma ya ringa kiran sunanta kenan
Idan Hakeem ya shigo dakin binshi yake da kallo yake kawai idan ya mashi magana kuma kaman da gwinki yake magana shi jiran mutuwanshi kawai yakeyi dan his life is totally over and is useless without Ameenah
Manager shi ya ringa kiran numbershi na can amma baya shiga ya fara trying na Nigeria shima thesame answer danshi yanxin ko wuka za'a saka mai a wuya ace ya gaya inda wayanshi yake bazeniya gaya bah
Da ya gaji seya kira na Daddyshi anan ne yake gayan mai ae Matanshi ta rasu ne
Yayi amshi ta'aziya bayan kwana biyu ya debo team mates dinshi dukka hadda ugansu da kadan daga cikin yan dayan team suka zo mai ta'aziya dukda kusan dukkansu arnayene dan a cikin 10% toh 8% duk kafirai ne 2% ne kawai musulmai
Duk sun tausaya mai yadda ya koma kwanansu daya suka koma
Office dinsu ma sunzo gasu Zaid da Fa'iz duk sun mai kara
Kuma duk wanda yazo sede kawai ya bisu da kallo be magana kaman kurma toh haka ya kuma duk wanda yasanshi a da toh idan ya kalleshi yanxin seya tausaya mai sosai
Dangi da sukazo daga gari daban-daban duk sun koma amma su Afra suna nan Baban su ma yazo lokacin anyi bakwai a washe gari ya kuma
Daddy ya yanke hukunci su kuma gida haka akayi duk suka shirya suka koma tun randa suka koma da Adeel ya shiga dakinshi yayi lockin be sake fitowa ba kwananshi biyu Allah kadai yasan me yakeci randa ya fito ma dakyar ya fito seda Mommy da safieyarh suka zauna a bakin kofan dakin suka ringa kuka sannan yazo ya bude ya kuma ya kwanta yana sana'arshi wato tunanin Ameenahshi
Cire keys din Mommy tayi ta tafi dashi
Da abun ya ishe Daddy masallatai ya saka aka ringa mashi addu'a sannan ruwan shan Adeel ya kuma ruwan rubutu da zam-zam amma dukda hakan ba nasara se kara tsotsewa yakeyi
Wata rana duk suna zaune a parlo Daddy suna shawaran akan abun Adeel se kawai suka ganshi ya shigo parlo kallanshi sukeyi da mamaki harya zauna
"Daddy daman inason kumawa Abuja ne dan nafison zaman can"
"Habah Adeel ae be kamata ka koma can ba kai kadai mukasan abunda zaka ma kanka a gaban mu ji abunda kayi balle ace kasan babu kowa sede gawanka ae" Daddy ne ke wannan magana
Dukar da kanshi yayi kawai beyi magana bah
Wa'azi suka shiga mai akan ya dugara ga Allah dan wannan JARABAWA CE wata kila Allah yana shirya mai wani abu ne anan gaba
Bece kala bah har suka gama ya mike ya kuma dakinshi Qur'ani ya dauko ya ringa karantawa da kira'arshi me dadi ya kusan Two hours yana karantawa daga baya ya kulle addu'a ya ringa ma matanshi dan ya saba tun randa ta rasu haka yake mata
_One month later_
Yau watan Ameenah daya da sati biyu da rasuwa
Har a lokacin Maman Afra sunki komawa Abbah yayi fadan harya gaji kusan kullum se Alhaji yazo shida wani danshi me suna _Marwan_ sun gaisa da Abbah sannan yaje ya gaida Adeel dan yana tausaya mai sosai
_Marwan_
Yarone dan shekara 22 kyakkawa ne sosai gashi kuma fari kaman balarabe dansun hada jini da larabawa saboda mahaifiyarshi balarabiya ce dan Alhaji Lawal bame zama waje daya bane yana tafiye-tafiye sosai saboda haka a dubai suka hadu da ita har sukayi aure dan haka ya saya gida a can yana xama da ita idan akayi hutu kuma sesu dawo gida har wata rana ta sama juna biyu
Ciki yayi girma ya isa haihuwa
A randa ta haiwa ta haifa danta namiji lafiyaye kafin ta daukeshi ta rasu Alhaji yayi suka kaman yayi hauka dan haka ya dauka Alkawari ze zame ma Marwan Uwa da kuma Uba baze taba neman abu a gunshi ya rasa ba kuma baze taba rashin uwa ba
Dan haka Marwan ya taso cikin so da kauna ga ilimin boko dana arabiya duk ya sani be taba kukan rashin Uwa bah amma yana mata addu'a sosai
*******
Ranan da Daddy yaje yaga yadda Adeel ya kuma har hawaye ya zubar mashi saboda haka ya zauna yayi tunani toh meze hana ya sake aure koh abun ze ragu
Da wannan tunanin ya sama Daddy shima yaji dadin shawaran nan haka duk aka zauna meeting hadda Safieyarh da Hakeem se Mamansu Afra
Amma banda twins
Kowa ya yarda da shawaran
Abbah yace shi harya saman mai mata a take kowa ya tambaya wacece ita
Yace "Afra"
A take gaban Mama ya fadi dan tasan kowa ze yarda amma ita Afra bazata taba yarda ba saboda tana bala'in son salman
Kallonta kowa keyi amma ita hankalinta baya wajansu
Mami dake kusa da ita tace lafiya kikayi shiru
"Aa babu komai zan kira Babansu anjima sena gayan maku yadda yace"
"Toh shikenan Alhamdullilah" Daddy yace yana jin dadi
πππ
[15:58, 3/26/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: ***
Wuraren karfe takwas na dare Maman Afra ce ke kwance da waya a kunnenta tana waya da Babansu bayan yan gaise-gaise take gayan mashi halin da ake ciki
dan dumm yayi se kuma yace toh shikenan ae shima Babanta ne yanxin kin tambaya ta bakinta ne??
"Aa daman nafison idan ka yarda sena tambayeta nasan zatayi musu da UMARININ IYAYEnta bah"
"Toh shikenan ki bita da lallama ne dazin ma Abbah ya kirani yake gayan min toh amma nace mashi zanyi shawara. yanxi barin kirashi na sa'anar dashi daman na aza beyi maki magana bane"
Toh shikenan seda safe haka sukayi sallama ya kira number Abbah ya gayan mashi babu komai duk rannan da aka saka se a kirashi a gayan mashi da haka sukayi sallama
Abbah ba karamin dadi yaji bah
Hakeem kowa soyayya sukeyi sosai da Safieyarh yanxin kuma suna zama ayita wasa da dariya dasu Afra amma shi gabadaya abunda aka yanke na hadin auren nan shi beso bah besan dalili ba amma abunda ya sani kawai beson ayi wannan auren (ze taya yar'uwanshi kishiπ)
An sake taruwa amma wannan karan iyaye ne kawai aka yanke nan da two weeks (ya zama 2 months kenan da rasuwan Ameenah)
Aka kira Babansu Afra aka fadan mashi yace toh Allah sanya Alkairi ana gobe daurin aure zezo dan yanada aiyuka dayawa a gabanshi
*******
Daddy ne da Mommy a parlo suka aika Safieyarh akan ta kira Adeel
Tana shiga dakinshi a gaban dadduma ta sameshi ya gama sallah isha'i yanata addu'a hadda hawaye a idonshi zama tayi a kusa dashi harya zama addu'an ya shafa itama ta shafa
"Ya Adeel Daddy yace kazo zasuyi magana dakai"
Daga mata kai yayi kawai ta mike har zata fita seta dawo "Ya Adeel nasan kanason Ameenah but she's in a better place Allah ya fimo sonta shiyasa ya dauka abunshi but abunda take bukata a wurin mu yanxin shine addu'a shi kawai take bukata and ka sani we are all here for you we love you so much"
Daga mata kai ya sakeyi dan yasan yana magana kuka ze iya saki koma beson yayi kuka agaban kanwanshi (daga baya kenan)
Tashi tayi tayi huging dinshi seta fita
Hawaye ne kawai ya fara zubu mai kaman ruwan fanfo dakyar ya samo ya tsaya seya mike ya fito a hankali yake tafiya abun tausayi fuskan nan kowa har gemo ya taro sosai daman gashi da dan banxan gashi kaman mace
Yana isa besan dalili bah kawai se gabanshi ya fadi saboda kallon da suke mai samin waje yayi jiki a sanyaye ya zauna "Daddy gani"
"Yawwa daman kiranka mukayi dan na sanar dakai wani abunda muka yanke kuma nasan zaka bi Umarnin mu kaman yadda kabi a baya"
Kirjinshi ne ke bugu da saurin gaske amma be dago ba balle yayi magana
Daddy ya cigaba "Adeel mun gaji da ganinka haka kalla yadda ka kuma kaman ba kai bah munsan kana son marigayiya amma Allah ya fimu dukka sonta dan haka mun yanke hukuncin hadaka da Afra
Dagowa yayi da sauri ya kalla fuskanshi seya kalla fuskan Mommy sena Safieyarh duk shi suke kalla Safieyarh kowa har hawaye ya cika a idonta
"Haba Abbah so kuke ku kasheni bakujin tausayina yau kwata kwata ko wata biyu Ameenah bata shiga da rasuwa ba but you want me to get MARRIED AGAIN dan Allah ku taimaka min ask for something but not this anything zanyi maku but please banda wannan"
Shiru sukayi gabadaya suna kallonshi
Matsuwa yayi kusa da kafan Daddy ya rike gam yace "Daddy, Mommy dan Allah karkuyi min haka ku taimaka min ku barni a haka har nima na kuma ga ubangiji na idan bakusan zamana ne a gidan zan kuma can Abuja nayi zamana ni kadai harse Ameenah ta dawo Amma dan Allah i beg of you ku taimaka ku barni a haka wlh idan akayi auren nan dukkan mu wiya zamusha dan ni wlh bazan taba son wata mace bayan Ameenah bah and i believe wata rana zata dawo min wlh akan ku aura min wata gara ku kasheni"
Tashi Safieyarh tayi a guje tabar parlon tana kuka sosai saboda itama bata son auren kwata kwata
Mommy itama a lokacin kuka takeyi she can't bare to see her son suffering this way
Saukowa tayi ta rikeshi
"Adeel kayi hakuri ka yarda da wannan abun is for your own good bazamu taba zaban maka abunda se hallakar dakai bah da-"
Be bari ta karasa bah yace "toh shikenan Mommy idan wannan shine abunda kukeso zanyi yadda kukeso amma dan Allah karku taba komai nata ku barshi yadda yake"
"Karka damu munyi magana da Abbah yace a bar komai har se randa ka shirya" Daddy ne yayi wannan maganan
Agiyan zuciya Adeel yayi can yace "duk abunda kuke bukata zanyi but you should just know this duk abunda ya faru i mean ko meye is all you fault karkuyi kuka da kowa da kanku zakuyi "
Seya mike yana tafiya a hankali kamar yadda yazo yana share hawaye dakinshi ya shiga ya kulle kofan
Kuka Mommy ta shigayi Daddy na bata hakuri
πππ
_I don't care anymore mind yor business and take you ass off mine why do you care so much about me?? Please i beg of you stay out of my life and stop reading my Novel if that happen i will be so happy i care about you nomore why won't you do thesame you freaking loser_
_i know am not that popular but i don't care all i care is my dream to come true nothing more and nothing less i have a number of people that like me thats encough for me so please am begging you one last time leave me out of this please._
IG.Tyetyelorh
[11:39, 3/28/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: πππUMARNIN IYAYEπππ
WRITTEN BY:
TYETYELORH
EDITED BY:
AMEENATOU
πππ
*127*
Bakinshi rawa yakeyi hadda harcenshi ma ya kasa prouncing sunan gabadaya "A..aaaa......mm"
Kawai yake iya fada gara shima su Mami dukkansu babu me iyayin komai se tsayuwan da sukayi kaman statue
Kuka Meemah keyi sosai babu wanda yabi ta kanta
Seta dosa gunta zata dauketa Auntie a guje tazo ta rigata daukanta se tayi gefe da sauri
Murmushi tayi "Tsoro na kukeji yanxin"
"It's really you Ameenah" se hawaye ya fara zubu mai kaman ruwa
Dosan gunshi tayi shima ya fara tafiya yana yo gunta da sauri Abbah ya rikeshi yace "Ko waye ko munfi karfinku da hannun mu muka burne yarinyata"
Adeel ya kwace jikinki "Ameenah.Ameenah kece"
Daga kanta tayi tana hawaye" Ya Adeel its really me"
Suna zuwa kusa da juna se suka tsaya kallonta yakeyi seya daga hannunshi a hankali yakai gun fuskanta a hankali yakai seya shafa fuskan
Kulle idonta tayi a hankali tana murmushi ga hawaye dake zubu mata
Rungumanta yayi da sauri yace wlh Ameenah ce itace yana magana yana hawaye
Huging nashi back tayi "Someone really missed me" magana takeyi tana murmushi amma hawaye se kwaranyo mata yakeyi itama
Su Abbah kowa kallon ikon Allah sukeyi kawai dan duk basu yarda ita bace
Afreen kowa tana daki taji ihun dasu Hakeem sukayi se kuma taji shiru dan haka ta mike ta fito a hankali tana fitowa taga kowa na kallon bakin gate se itama ta kalla
Ameenah data ganta da sauri take Afreen
Tana jin sunata kowa ihu ta saki se tayi gun Mamanta taje tsaye taredasu Abbah
Hawaye ne ya fara digan mata yadda taga kowa ya gudunta
Hakeem ne ya tako a hankali ya iso gunsu "Ameenah " ya kira sunanta a hankali
Bude ido tayi seta saki Adeel shima ya saketa amma hannunshi yana rike da bayanta dan kwata-kwata he don't want to let go of her cus he believes yana saketa she will be gone again
"Ya Hakeem" itama ta kira sunanshi in a soft voice
"Ameenah kece dagaske" murmushi tayi kawai tana share hawayen dake zubu mata sosai amma bata amsa ba
"Idan kece ki ansa min wannan Wanna novel na dauka naki"
_What to expect when you are---_ bata karasa ba ya kai mata wani wawan runguma "Ina kikaje for all this time wait amma hadda ni fa muka burneki " ya fada tareda sakinta
Juyawa tayi ta kalla matan da suka shigo da ita ta daga mata kai
Se matan tace "Wannan de itace Ameenah da kuka sani wanda kuka zauna da ita for 18yrs amma mu shiga daga ciki muyi magana"
Daga masu kai Adeel yayi har a lokacin hannunshi na dafe da bayan Ameenah
Hakeem ne ya fara gaba ya shiga parlon matan ta bi bayanshi suma suka bisu
Suna zuwa gunsu Daddy matsa masu sukayi sosai suka shiga parlon Ameenah kallonsu takeyi kawai
Ta rame dan kiban da tayi ya sabe dukka amma de ta kara haske sosai dan tamafi da haske dugan hijab ne me hannu a jikinta
Zama sukayi a two sitter itada Adeel suna zama seya rike mata hannu kallonshi tayi seya sakan mata murmushi itama ta maida mai seta kalla su Daddy dake bakin kofa haryanxin sun juyo suna kallonsu hadda Safieyarh da Auntie
"Abbah ku shigo mana kuji abunda ya faru" kallan juna sukayi se kuma suka shigo dukkansu kujeran da ke facing dinta suka zauna Safieyarh da Auntie suna bakin kofa sun kasa shigowa
While matan da sukazo dare da Ameenah me kamada bafulatana itama tana zaune a kasa tana facing su Mami
Girgiza kai Ameenah tayi dan bataji dadi abundasu Mami suke mata ba kaman ba yarsu bah
Magana ta farayi
_"Abunda ya faru shine a lokacin da Ya Adeel ya yarda nazo Kaduna na fito inata gudu dan Hakeem yace min Abbah ba lafiya toh inata gudu a titi na fito daga Abuja kenan sega wata yarinya mate dina ta fito daga daji a guje ta shiga titi se nayi sauri na tsayar da motan dan haka se tayo gun motan a guje tana kuka da alaman ana binta ne tace min dan Allah na taimaka mata ga wasu maza suna binta zasu kamata ban tsaya second thought ba na bude mata ta shiga ta saka sit belt na tayarda mota da sauri muka ringa gudu a titin bayan munyi nisa sosai sena naga kuma babu me binmu sena rage gudun na kalleta se faman kuka takeyi se nace mata tayi hakuri ta gayan min abunda yasa suke binta. Dakyar na samu tayi shiru se ta fara ban labari "Auren dole za'a mata a gida ita kuma batasonshi saboda yana shaye-shaye kuma yana bin mata toh ya gama saye iyayenta saboda hake suka yarda da auren a lokacin da yace masu yana sunta dukda sunsan beda hali me kyau tayi-tayi dasu akan karsu yarda basu damu ba suka yarda harya kawo baikontaa dan haka tege gun me unguwa ta gayan masa halinda ake ciki dakaishi yazo gidan be aika an kirasu ba dakainshi yayi masu nasiha akan a ganye maganan dan shima yayi shidar yaran beda hali me kyau rashin mutunci suka mai suka zazzageshi sannan suka koreshi ba yadda ya iya haka ya cire hannunshi daga zancen haka suka ringa shirya-shiryan bikin har ranan daurin aure aka daura aure toh kafin akaita seta yarke shawaran gara ta shiga duniya akan ta zauna dashi dan tasan wata rana idan ya bugu ze iya kasheta" Shawara na fara bata akan da ta yarda tabi UMARNIN IYAYENTA ta zauna dashi duk tsanani se shiryu su zauna lafiya muna cikin maganan ne kawai mukaji anyi jifa a motan ya fasa glass din motan Ya Adeel danni motana babu bakin mai koma bansan yadda ake sawa bah ina juyawa sit din baya naga wata kwalbace da wuta a ciki ta se kwallabn ya fashe sanadiyan wurguta da akayi ana da nan sit din ya kama da wuta salati muka farayi kuma na kasa tsayarda motan dan haka muka fara kokarin fita dayake ni babu sit belt a jikinta sena fara kokarin taya yarinyan cirewa amma mun kasa motan se ci yake harya fara kama kujeran da muke kai sena kai hannuna na bude kofa na dan muna cire belt din semu fita mukayi-mukayi mu cire amma muka kasa se yarinyan tace min na fita kawai na barta tana magana tana kuka se nace mata aa tare zamu fita muka ringa kokarin cirewa yaki cirowa wuta harya fara kama min kayana kafin na ankara kawai ji nayi ta turoni waje na gangara cikin daji tou daga nan ban san abunda ya faru bah sanadiyan black-out dinda na samu_"
Ta kare maganan tana kuka sosai
Adeel ne ya kwantar da ita a kafadanshi yana shafa mata bayanta
Se matan ta cigaba
_"Mu kuma a lokacin ne muka ganta malam yaje nemo mana ice saboda a dagin muke zama tareda shanun mu toh daya ganta ne se kuma yaga mutane a titi dayawa an zagaye wata muta data kune kurumus dan haka seya dauketa akan shanunshi ya kawota gida muka zauna da ita dan Allah daman be bamu haihuwa ba toh daga ni seshi muke zama kwanata biyu muna mata magana saboda ta buge kanta sosai toh ta zubarda jini munata mata magani data tsahi se bata tuna abunda ya faru ba kwata-kwata ta manta da kowa da kuma komai naso a bada cikiyarta se malam ya hana yace ze iya yuwuwa idan aka fada ana cikiyar mutum wasu zasuzo suce sune iyayenta tunda ita ba gane iyayen nata zatayi ba haka muka cigaba da zama da ita tareda mu harta saba ta daukemu kaman mune iyayenta kullum cikin shan rubutu take kuma mallam ya fito cikin gari ya bada sadaka dan a sata a addo'a bayan wata daya da sati uku da faruwan abun wata rana kawai ta dawo mana lebu ice dan tun samun lafiyanta tace ita zata ringa lebowa dan haka itada malam suke zuwa suna dawowa zata shigo gida kawai setayi karo da bango toh daga lokacin ne ta tuna komai da komai akan rayuwanta cikin ikon Allah. Ta tambayemu kwananta nawa da zuwa muka gayan mata seta tayarda hankalinta akan cewa zata dawo gida dan mahaifinta beda lafiya tanason taje ta ganshi dan saboda shi ta fito tun farko shine muka fara shirya-shiryan dawowa se shi kuma ciwon kafan malam ya tashi dan haka nace ya zauna ni kuma na rakota gida amma a gaskiya yaso zuwa shima Amma kunsan abun mamaki tun zuwan Ameenah gidan mu komai namu ya chanja wata rana malam daga zuwa masallacin juma'a aka bashi zakka makudan kudi ne sosai munyi murna sosai seya tafi kasuwa ya sayo ma Ameenah kaya kala-kala bafa shi kenan ba daga a bashi kwautan abinci sena kudi kuma munsan sanadiyan Ameenah ne haka ya faru danni sheda ce Ameenah tanada baiwa wanda ba kowa keda irinta bah baiwan da ba ko wannan dan Adam keda irinta ba"_
Juyowa Ameenah tayi da sauri ta kalleta "Baiwar da ba ko wanan dan Adam keda irinta ba " abunda ta maimaita kenan danta tuna abunda tsohuwar nan ta taba gayan mata kenan
Bata karasa tunanin nan ba taji an rungumeta
Maido da kanta tayi gun wanda ya rungumeta tayi Mami ce ta rungumeta tana kuka itama huging nata back tayi ta fashe da kuka dan tayi missing arms dinta sosai
"We all thought you left us we are so sorry we tired to make your husband marry again"
Dagowa tayi da mamaki "Aure, waza'a aura mai ??" Ta tamabaya a rude
Mami ta kalleta se kuma ta juya ta kalla su Abbah ta kasa magana
Afreen ce ta taso ta rike mata hannu se kawai ta rugumeta ta fashe da kuka " thank god you are back i wanted to betray you i was the one who almost marride your husband after Afra left am so sorry"
"Its okeyy nasan *Umarnin iyaye* zakibi bason ranki bah ina Afra take" ta tambayeta tana dagota tareda share mata hawaye
Kuka ta kara saki "ta gudu wai bazata iya auran mijin da kika aura bah i really want my sister back"
Kwantar da ita tayi akan kafadanta ya isa "she will definately come back kuma Allah xe kareta insha Allah ki dena kuka kinji" ta kare maganan itama tana share hawaye
Daga mata kai tayi
Mikewa Ameenah tayi taje gun Abbah wanda tun shigowanta beyi magana ba kallonta kawai yakeyi
Durkusawa tayi ta rike mai hannu "Abbah you still don't believe its me ryt"
πππ
[11:50, 3/28/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: Seda ya dade yana kallonta se kuma ya sauko shima ya rike mata hannu
"Its not that my daughter am just surprise and a little shocked" seyayi huging nata sosai
Murmushi tayi seta rikeshi itama sun dade a haka
Adeel kallonsu yakeyi yana hawaye da style yake sharewa cus he can't ask for more Allah ya amsa Addu'an na ya dawo min da matata Allah nagode maka thank you so much ka gama biyamin bukatuna dukka
Mommy ce itama tayi huging dinta tanata kuka Se Daddy ya dade yana rike da ita ya dagota
"Duk a cikinmu Adeel ne kawai be yarda da mutuwanki ba. Ameenah ki godiwa Allah ya baki miji nagari me sonki dan so nawa yana kukarin kashe kanshi wai ze biki he really loves you ban taba ganin irin wannan son ba yana sonki sosai"
Murmushi tayi ta juya ta kalla Adeel ya wani dake kaman bashi ba ya juyarda kanshi a hankali ta furta "I love you so much" inda ko Daddy dake kusa da ita baze jiba
Tun sanda ta dawo da memory ta tasan taan son Adeel dukda bata taba soyayya ba but she believes tana sonshi sosai dan gabadaya kullum se tayi tunaninshi kullum seta fada she loves him kullum se tayi kuka cus she missed him alot
Dawo da kallonta tayi gun Mamansu Afra data tsureta da kallo
"Mama" ta kira sunanta
Hawaye seya fara zubu ma Mama
Da sauri Ameenah taje ta rungumeta tana shafa bayanta kuka kawai takeyi kaman karamin baby
Ita kukan da takeyi dadi takeji da ba'a rigada an daura auren ba sake riketa tayi sosai sun dade a haka sannan tayi breaking hug din
A guje Safieyarh itama tazo ta rungumeta ta fashe da kuka
Yaude Ameenah tasha hugs daga gun kowa
Auntie ce da take kallon ikon Allah tazo tace "thank god kin dawo dan kwata-kwata banson auren nan aradu seta" rungumeta
Dariya Ameenah tayi tace kece me tayani kishin kenan
"A mana nida Hakeem ba shiryawa mukeyi yadda za'a fasa auren nan segashi Allah ya kawo gidan sauri" kowa ya fashe da dariya dan sunsan tabbas zasu rina idan de Auntie ce itada Hakeem
_20 minutes later_
After all the hugs and crys aka zauna ana dan hira duk an dame Abbah da Daddy da kira wai ga yan dauren Aure sun iso fah tuntuni
Adeel kowa yana rike da hannun Ameenah kaman za'a kwace mashi ita
Kallonshi tayi tace "is it true you tired to kill yourself for me "
"Ban sani bah" ya fada seya mike ya fita daga parlon gabadaya ya kuma hanyan hawa sama
Itama fitowa tayi ta bishi
Su Mami murmushi kawai sukeyi dan basusan me zasuce ba Allah ya gama masu komai
Kafin ta fito harya kai karshen step din binshi tayi da sauri
Gun fridge din parlon ya nufa ya bude ruwan sanyi ya dauka ya bude kwan-kwada ya farayi
Tun randa akace Ameenah ta rasu babu abunda ke mai dadi a baki koh ruwa ya sha wani daci yake mai
Amma yau har alaman saukan ruwan yakeji
Karasowa tayi ta tsaya tana kallonshi
"She loves him so much and she admit it he has everthing she wants her husband to be like"
Be gama sha ba ya saukar dan yadda yaga tana kallonshi
"What!!" Ya tambayeta
"Can't i look at my prince charming a person that can die for me"
Yaji dadin abunda take sosai se yace" bafa dagaske bane Daddy ne kawai ya fadi haka"
"Hmmm kaga ango' tana magana tana kallon babban rigan dake jikinshi
Shima rigan ya kalla se yayi guntun tsaki ya cireta a hannun kujera ya kifar da ita se ya maida kallonshi zuwa gun Ameenah hannunshi ya daura akan kafadanta
"Tunda na shigo gidan nan gabana keta faman fadi ashe saboda kene"
Murmushi ta sakar mai seta kalla kofan dakinta
"Allah sarki dakina zo kaga dakina"
Taja hannunshi suka shiga
Suna shiga ya tura kofan
"God i missed you so much" ta fada tana refering ma dakin
Closet dinta ta shiga se tsalla-tsalle takeyi ba karamin dadi takeji bah ta dade tana haukanta shi kuma kallonta kawai yakeyi "He loves each and everthing about her"
Dawowa tayi inda yake tsaye se idonta yakai inda ya yanka a hannunshi da sauri ta riko gun
"Meyafaru da nan" tayi pointing gun
Saka dayan hannun yayi a kan yankan dan ya warke sede spot dinne kawai agun
"Nothing" ya fada
"Me karya" tace tana cire dayan hannun
"Da gaske ne koh kaso kayi commiting suicide kasan me nakeso kayi min yanxin"
Girgiza kanshi kawai yayi
"Just say you love me so daya na jika kawai"
Kallonta yayi se yayi guntun murmushi babu secoud thought ya fadi
"Ameenah ni Adeel love you with all my heart and zan iya fadi a gaban kowa"
Murmushi tayi kawai se tayi huging nashi "i missed you alot"
Dagota yayi yana kallon fuskanta "i missed you more" kafin ta ankara yakai lips dinshi kan nata
Da ta fara pulling back setaga rashin amfanin haka hannunta ta daura akan wuyanshi ta zagaya dashi itama seta fara kissing nashi back
Shi kuma hannunshi ya zagaye a kukunta yana kissing dinta sosai
There first french kiss and the sexiest among them..
IG.Tyetyelorh
[10:40, 3/30/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: πππUMARNIN IYAYEπππ
WRITTEN BY:
TYETYELORH
πππ
_I dedicate dis page to Lawizas guyx i love you so very much and i will always do_❣
_Yanxin kam na huta aradu Ameenah is back_π
_#12 April is the date am so damn excited can't wait_
*128*
Sun dade a haka dan sun kai 20mins se daga baya Ameenah ta janye jikinta but idonta were still closed
"Meyasa se yanxin kikayi pulling back??"
Ya tambayeta dan yayi tsammanin tuntuni zata kwace
Juyawa mai baya tayi tasa hannu a fuskanta not ready to answer him
Rungumota yayi ta baya hannunshi yana gun cikinta while kanshi yana gun wuyanta ya kulle ido"i still can't believe you are back how i wish this dream never ends
Rike hannun nashi tayi seta budesu but tana rike da hannun seta juyo sannan ta kulle hannun as in ta zagayashi a waist dinta tana ciki kenan "idan mafarki kake za'a maka haka"
Seta mashi light kiss akan lips nashi
"Yah why not. so nawa ina irin wannan mafarkin"
Zata sake magana kenan sukaji muryan Hakeem yana kiran sunanta
Wani burkicewa tayi ta juya zata gudu toilet se yayi sauri ya riko hannunta "Meyasa ina zaki"ya tambayeta
"Ya Hakeem nefa daga dawowa na a ganni dakai" ta gaya tana kukarin kwacewa again
"Toh whats wrong with it niba mijinki bane and since when kika fara tsoran Hakeem"
"Ae ba tsoranshi nake bah be kamata bane sakeni dan Allah na boye idan ya shigo kace kaima nemana kakeyi"
"Bazanfa sakeki ba afterall we are not doing anything wrong" yana magana yana sake jawota jikinshi
Sunajin ya duso bakin kofan ae hadda shi aka boye closet suka shige itace a gaba
Bude kofan yayi yana sake kiranta dayaji shiru harze juya se yaga hijab dinta murmushi yayi "Toh Abbah yace kozo yana nemanku seya kulle kofan"
Har zasu fito se kuma ya dawo "Nima i want to see my sister cus i misses her too" seya sake kullewa
Dariya Adeel keyi a hankali juyowa tayi ta kalleshi ta hada fuska seta buga mai cikinshi "awwchh menayi"
"Ban sani bah" seta wuce mekewa yayi yabita
Harta wuce hijab din zata bude kofa seya mika mata fuzga tayi hannunta ya janyo
"Its only Hakeem fah"
"Toh kasan ko ze gayan masu muna tare" ta gaya tana kukarin amshe hannunta
"Toh tsaya barin fara fita kaman 20mins kema seki fita kinji bazasu ce muna tare bab"
Daga mai kai kawai tayi
Hijab din ta amsa seya fita a parlo ya tsaya ya dauka babban riganshi ya saka seya fito parlon Abbah ya shiga da sallama aka amsa mai inda yake zaune ya kuma ya zauna
Murmushi Mommy keyi yadda taga ya chanja hadda murmushi kwance a fuskanshi its all what she's asking for taga danta yana jin dadi once again
Dayake Abbah ya kira Alhaji ya gayan masu cewa Ameenah ta dawo ya labarta mashi komai a waya da murna seyace toh gashi nan zuwa dan shi harya isa masallacin kuma har an gama sallan juma'a magabatan Afreen kawai ake jira
Tare suka taho da marwan gudu kawi seyi a titi danshi yana son yarinyan sosai
An kira Baba shima an gayan mai da murna yace gashi nan a hanya shima ya shigo motanshi dan daman ya fita ne
Daddy ne ya kalla Adeel "yanxin hankali ya kwanta zamu huta muma kai Allah mun gode maka Allah ka kara soyayya tsakaninsu ya baku zaman lafiya da yara na gari ya sake hada kawonanku"
"Ameen" kowa ya amsa dashi hadda Adeel din
"Toh ina Ameenah take" Daddy ya tambayeshi
Sosa keya yayi can se yace "Nima bansan inda take bah"
"Ina tare kuka fita da ita"
Mommy ce ta dan bugeshi tana murmushi "kabarsu mana he missed his wife" ta gayan ma Daddy a hankali
Shima murmushi yayi se yayi alaman yayi ziping bakinshi
Matar da Ameenah ta zauna gunta wanda ake kira da inna tace "Atoh ku barsu wata biyu wasane suma suna bakatan junasu ae sunyi kukari" tana magana itama tana murmushi
"Nifa bamu tare da ita ruwa naje nashi" Adeel ya gaya
Hakeem yace toh waya ce kuna tare nide ban gayan masu shima yana magana da alaman zulaya a fuskanshi
"Ya Hakeem ka cika gulma ina ruwanka dasu ka barsu " Safieyarh ce tayi magana
Hakeem yace "Toh nayi shiru ranki ya dade
Abbah da Mami kowa murmushi sukeyi kawai dan rabanda a zauna a ringa irin wannan abun tun barin Ameenah gida gashi daga dawowanta an cigaba
"Kai Ameenah baiwa ce a tare damu Allah mun gode maka Allah kaine abun godiya daka azurtamu da yara nagari masu bin Umarnin mu badan sunaso ba kawai dansu faranta mana rai Allah kabarsu tare"
Mami ce ke addu'an nan ita daya a zuciyanta
Can sega Ameenah ta shigo kana ganinta kasan batada gaskiya dan gabadaya a rude take ga kuma alaman kunya a tare da ita tana shigowa kowa ita yake kalla seta dukar da kanta kasa gun Mami ta nufa ta zauna gunta
Hakeem yace "Lafiyanki kike wani dukar dakai kaman bakida gaskiya"
"Ina da gaskiyana ina ruwanka dani ma ne banson gulma fa"
Matsawa yayi kusa da ita haba Baby sis you know i missed you alot
Murmushi ta sakar mai and i missed you more se tayi huging dinshi
Adeel kowa kallonta kawai yakeyi daga nesa ji yake har yanxin kaman mafarki kwata-kwata be yarda ta dawo ba kuma he feels close to her so easily da kullum suke cikin fada he can't wait su kuma gida ji yake kaman ya suntumeta kawai su tafi.
Dafata Mami tayi "daga ina kike wai"
"Uhmm toilet din dakinki na shiga" kana kallonta kasan karya takeyi cus shes not good at lying tana karya ake ganota
"Aa bade dakina ba yanxin fa daga can nake"
"Na dakina fa nace"
"Atoh gara ki gyara"
Shiru tayi kawai sega Alhaji ya shigo da sallama ku gaisawa dasu Abbah beyiba yayo kan Ameenah itama ta mike ta rungumeshi shi kawai yanason yarinyan ne ji yake kaman yarshi ta cikinshi
"Am so glad you are okey" yayi magana yana dagota
Smiling kawai tayi mai sannan ta gaidashi ya amsa da fara'a sosai a fuskanshi
Seta kalla Marwan "Kai bakayi missing dina bane" ta gaya kaman da shagwaba
"I just can't believe its really you" ya gaya yana dosan gunta se tayi huging nashi
Dan suna shiri sosai sede shima be cika zama bane se yayi shekara biyu bezo 9ja bah
Hakeem yace "Amma yarinyan nan tasha runguma da addu'oi barin ma Adeel dayafi kowa dade wa agun"
Kwashe wa akayi da dariya Mami tadan buge Hakeem kadan
"Ae she deserves it cus she sacrifies her life for me and ni danasan daga inda take da naje na tayata neman gafara gun iyayenta"
Tayi magana hadda kwalla a idonta
Shafa mata baya Marwan yayi a hankali kallonshi tayi tadan mai murmushi
Auntie tace "Insha Allah ma sun yafe mata kuma sun gane kuskuransu"
Alhaji gun inna yaje ya durkusa har kasa suka gaisa yake mata godiya sosai akan abunda suka ma Ameenah
"Babu komai Alhaji ni jinta nake kaman yar cikina kuma kuda mun rabu haka zan ringa daukanta"
"Bazama mu rabu ba inna na muna tare" Ameenah ta fada tareda kwantar da kanta akan kafadanta
Murmushi tayi tana shafa kanta
"Toh yanxin yadda za'ayi driver za'a turo se a tahoda Mallam din kawai daga nan se'a tafi dashi ayi mai passport a wuce india ayi mai aikin kafan koh" Abbah ne yayi maganan
"Har india Alhaji ni ko anan ma idan aka mai kun gama min komai"
"Aa ko saudiya ne zan iya kaishi dan abundan kuka mana kun chanchanta abunda yafi wannan"
Kuka ta saki mungode Alhaji Allah jikan mahaifa ya kara zumunci
"Ameen ya Allah" kowa ya amsa
Meemah Ameenah ta dauka dan tun dazin se binta take da kallo
"Meemah yada kallon "
"Auntie ina kikaje anata kuka"
Dariya kowa yayi agun amma bata amsata bah
_10 mins later_
Baban Afreen ya shigo ae aguje ta rungumeshi dan suna dasawa saboda yana aeko mata latest lipsticks na kylie toh dan haka suna shiri sosai dan ita kana hadata da wani abu na kylie toh ka gama da ita
*****
Zama akayi ana shawara yadda za'ayi da mutanan dake masallaci Se Alhaji yaga Afreen tana kukarin cire daurin dankwalinta dannita gabadaya daman bason auren takeyi ba dan kawai tasan mahimmancin bin UMARNIN IYAYE ne shiyasa batayi musu dasu bah amma ita asali Marwan take crushing mawa tunda ta taba ganin hotanshi a snapchat din Ameenah lokacin birthday shi yake burgeta
"Aa karki cire" Alhaji ya fadi da sauri kowa ya kalleshi maida kallonshi yayi gun Baban Afreen
"Alhaji ina roko idan ka bamu Afreen toh se'a hada aurenta da Marwan danya matsa min tun randa ya ganta toh seda naga kun yanke hukuncin auren da ita se nayi shiru"
Kallon Afreen Baba yayi ita kuma da taji abunda yace dukar da kanta tayi dadi kasheta
Seya kalla Mama murmushi takeyi tana daga mai kai alaman ya yarda dan batason yarta tayi feeling bad kuma ta taba nuna mata hotanshi wai yana burgeta
Murmushi shima ya sakar mata se yayi mata alama ta tambayeta aji ta bakinta
Kusa da ita ta kuma "Afreen kinji abunda akace kinasonshi"
Hannu ta saka a fuska seta mike a guje tabar parlon
Dariya kowa ya saki se Abbah yace toh ta yarda dan haka mu tashi muje a daura kawai
Hamdala Mama tayi danta ji dadi sosai
Ameenah dariya tayi ta matso kusa da kunnan Mami tace "daman can tanasonshi"
Murmushi tayi kinga dai-dai kenan Allah bada zaman lafiya
"Ameen"
Marwan ji yake kaman yaje ya rungumota yata tsalle da ita dan dadi mikewa yayi ya fita waje fuskanshi wani annuri yakeyi waya ya shiga kira yana fadan ma abokanshi na kusa akan suzo _Sultan bello_ yau aurenshi
Wasu sun yarda while wasu sun karyata dan haka yace suzo se su ganma idonsu
********
Fitowa mazan sukayi dukka kowa ya shiga mota aka kama hanyan masallacin
Adeel ne karshen fitowa toh dayake duk matan sun shiga ciki hadda su Auntie daga Ameenah se Adeel ya rage
Kallonshi tayi "kai bazaka masallacin bah?"
"Zani but banson zuwa"
"Kayi zamanka kawai toh"
"Dagaske?" Ya tambaya da zumudi
Murmushi tayi babu ruwana
"Wait wai ina wayana i missed it"
"Kezan tambaya ae baki fito dashi bane?"
"Yh a kan kujera na barshi"
"Shiyasa na ringa kira ranan ban samu bah ae har yau banje gidan bah"
"Meyasa?" Ta tamabaya da mamaki
"Because idan na shiga zan iya haukace wa and su Daddy ma sunki barina wai zan iya kashe kaina a gidan"
"Awwn you really love me don't you?"
"I seriously do and i can do anything for you" ya fada yana riko waist dinta
Murmushi tayi tana futa daga rikon "sunyi nisa fah bazaka bisu bah"
"Wlh banson zuwa kuma idan banje bah drama ne"
"Ango dakanshi bazaki bikinshi bah"
Hada fuska yayi seya fara kokarin cire babban rigan dake jikinshi
"Meyasa kuma?"
"Dan banso" cirewa yayi seta amsa wuyan rigan ta gaira mai
Smilling yayi yana kallon fuskanta harta gama gyarawa pecking dinta yayi seya fita motanshi ya shiga ya kama hanyan masallacin
Wani ajiyan zuciya tayi tana shakar kamshin riganshi "She loves him so much Allah nagode maka"
Abunda ta fada kenan ta kama hanyan hawa sama tana shakar rigan
πππ
[11:00, 3/30/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: "Se yanxin Adeel ya tafi?"
Kawai taji ance mata
Rigan tayi sauri ta boye a bayanta seta kalla ta inda taji muryan Mami ce a tsaye tana murmushi danta ga abunda takeyi
Girgiza mata kai tayi se kuma tace "yes" danta rude
Dariya ta saki seta wuce
Da sauri ta bi bayanta Mami ban gane wannan dariyan ba
"Me nace daga dariya nide bance komai bah"
Seta wuce dakinta dan acan suke dukka hadda inna amma banda Mama da Afreen
Seda taga ta shiga dakinta se itama ta wuce nata dakin still babban riganshi was with her
Kan gado ta kwanta tayi hugging rigan kawai ji take kaman ta dade da sabawa dashi kaman sunyi shakuwa sosai dashi
Safieyarh ce ta fado dakin kawai se tace "ewww"
Dagowa tayi da sauri ta kalleta se kuma ta tura rigan a bayanta "mena shigo min daki babu ko sallama
Zama tazo tayi bakin gadon "Me kikeyi da rigan Ya Adeel haka?"
"Ina ruwank nida rigan miji na banson gulma" se kuma ta fito dashi ta cigaba da shaka
Yamutsa fuska tayi "dan Allah ki dena sena fita ki cigaba its annoying"
"Toh naji me kike so"
Yawwa seta riko hannunta dukka biyun
_"Ameenah niba yarinya bace nasan bakison Ya Adeel dan ko zuwana gidanki na gane haka so please am begging you ko yayane ki fara sonshi he truely loves you wlh Ameenah so nawa yana kukarin kashe kanshi saboda ke gabadaya yabar kula kowa yabarcin komai kullum yana dakinshi wai yana jira shima lokacinshi yayi shima ya mutu Ameenah you have no idea how it feels saboda ke ya kuma rago kullum cikin kuka yake yayana ya kuma kaman bashi ba ko zama bamuyi muyi hira gabadaya ya dena murmushi se yau yayi tun barinki riga Ya Adeel wanda yasan kaddara amma shi yake cewa ze kashe kanshi saboda ke wlh ranan nan haka ya yanka hannunshi wajan vein nashi ikon Allah ne kawai ya saka yake raye wlh kin yi sa'a da kika sama miji wanda zeyi komai saboda ke ze iya kashe kanshi saboda baki tare dashi, Ya Adeel has never falling in love this his first time Ameenah am begging you as your sister please give him a chance how i wish nice na sama miji me suna haka wlh na gama samin komai a rayuwata"_
Ta kare maganan tana hawaye
Itama Ameenah hawaye takeyi sosai
_"Safieyarh you have no idea just how much i love your brother da bansan da haka ba seda bana tare dashi nasan ina sonshi i love him so much with all my heart and am ready to be the perfect wife he ever wished for i can do anything he ask for from me so please ki dena damun kanki kinji"_
Rungume juna sukayi very tight can se Ameenah tace "su Ameerah sunzo ne suma"
Dagowa tayi"Hmmmm duk sunzo barin baki labari wai lokacin da mukaje ma Afreen jere Ameerah kawai seta fashe da kuka wai ita bazata iya ba she feels kaman tana cheating nakine"
"Allah sarki babe kira min su plzz"
"Chab ae tun dazin na kirasu duk suna hanya"
Sun dan jima suna hira Safieyarh na bata labarin haukan da akayi lokacin da akace ta rasu har hawaye takeyi cus she had no idea her family loved her that much"
Daga baya safieyarh ta mike ta fita ita kuma seda ta sake shakar rigan seta mike ta shiga toilet wanka tayi ta wanke gashinta sosai dukda bayi datti ba saboda Inna na iya kokarinta kullum sai mata combing nashi tana mugun ji da ita
Ta fito ta busar da gashin tayi oiling nashi zama tayi a bakin gadonta tana shafa mai daga ita se towel.
Tunanin yadda zata farantama mijinta rai kawai takeyi
*********
Adeel yana isa masallacin ana daura auren toh dan hotuna akayi da gaida jama'a a lokacin har zance ya garara gari da dangi cewa ba Ameenah bace ta rasu wasu harsun fara shirya-shiryan zuwa
Marwan se hotuna akeyi an zama ango se wani murmushi yakeyi gashi daman shima gabane gun kyau abokanshi sunzo sun tabbatar dan haka a cikin suka fara shirya mai dinner
Adeel ne karshen zuwa gun dauren auren kuma shine farkon dawowa se zabga gudu yakeyi dan yafison ganinshi kusa da Ameenahn shi dan he don't want to let go of her anymore
Afreen ce da Mama a daki tanata bata shawara tareda nasiha akan rike miji
"Afreen nasan saboda UMARNIN IYAYEN da kika bine bakiyi musu ba Allah ya hadaki da Marwan Allah maki albarka yasa shine alkairi a tareda ke ya baku yara na gari Allah baku zaman lafiya da hakurin juna"
Jan hancinta tayi saboda kukan da takeyi "Ameen Mama"
Seta rungumeta riketa tayi itama tana hawaye dan a yanxin tafison Afreen akan Afrah tunda ita ta fifita saurayi akan iyayenta Allah ya shiryeta Ameen
Mami, Mommy,Inna se Auntie da Meemah suke dakin Mami suna hira Inna ke basu basu labarin zaman da sukayi da Ameenah hadda hawaye dan batason a rabata da yarinyan
Abbah ne a waya ya matsa gefe guda dan hayaniyan mutane yayi yawa da PA dinshi yake magana akan yayi mai passport guda biyu ze tura mai information nasu idan ya kuma gida
IG.Tyetyelorh
[14:01, 4/1/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: πππUMARNIN IYAYEπππ
WRITTEN BY:
TYETYELORH
πππ
_#12 Aprl_❣
*129*
Yana isowa parking yayi ya fito parlon Abbah ya fara shiga amma babu kowa dan haka seya wuce sama shima babu kowa a hankali yayi hanyan dakin Ameenah yana zuwa kawai ya murda handle din ya shiga dagowa tayi ta kalleshi har a lokacin tana shafa mai murmushi ya sakar mata itama ta maida mai kawai seta tuna babu kaya a jikinta zare ido tayi setayi sauri ta dauka pillo ta kare jikinta dashi "Ya Adeel" ta fada irin a tsorace
Dosowa yayi gunta "Ya Adeel me kakeyi anan"
"Bazanzo inga matana bah"
"Har an dauran, bafa kaya a jikina"
"So" yana kokarin zama kusa da ita matsawa ta farayi murmushi yayi "idan kin gama goduwa ki gayan min
"Dan Allah Ya Adeel ka bari in gama saka kaya" kaman zatayi kuka
"Toh baga closet dinki ba nifa ina dakin nan babu inda zani"
Sake maraice fuska tayi tana kallonshi
Hijab dinta ya hango mikewa yayi ya dauko ya mike mata da sauri ta amsa ta saka seta mike ta nufa closet din da sauri
Hannunshi ya saka a aljihunshi ya zaro wayanshi missed call din wasu daga frnds dinshi ya gani hadda na Muhseen mijin Fauziyya dan duk Abbah ya gayan masu daurin auren duk kaman sun hada baki kowa yace be garin dukka Zaid yana nan shi kawai baze iya zuwa bane dan yana matukar tausayin Adeel
Text ya shiga rubutawa dan yaga missed calls dinsu
Akan Ameenah ta dawo ya hada BC na kaman su biyar ya fadan masu ae kafin ya maida wayan Muhseen ya kirashi daga wayan yayi
"Ban gane Ameenah ta dawo bah "
Labarta mashi abunda ya faru ya shigayi kaman mace se ihu yakeyi shida Fauziyya dan har kuka yayi sanda akace ta rasu
"Toh gamunan a hanya yanxin nan"
"Yamma bazata maku ba kafin ku kuma"
"Ae ko dare ne semun zo" se yayi hanging up murmushi ya saki
"God am the happiest living thing in the world today Allah nagode maka Allah na gode maka"
Seya shafa
Ameenah kowa tana can a kayanta daman akwai atanfofin da bata taba sakawa ba da suke dakin su ta shiga sakawa duk wanda ta saka daga wuyan ya zamule se skirt ya fada se tsaki take zubawa daga karshe de ta sama wata duguwan riga daman sanda aka dinka mata yayi mata kadan shi ta saka ta fito tana ware dankwalin
Dago kai yayi yana kallonta gaban mirror ta zauna powder kawai ta shafa se eye liner da chapert seta shiga daurin dankwalin ya dauro sosai
Mikewa yayi yazo bayanta ya tsaya yana kallon fuskanta ta mirro din
Tana kukarin daukan dankunne seta kalleshi ta mirror din itama
Murmushi ya sakar mata
"Meyafaru kake min kallon nan"
"Hmm i just can't believe you are really back i missed you so much i missed each and every event about you"
"Awwwn mee too"
"You too what?" Ya tambayeta yana kukarin amsan sarkan dake hannunta yana kokarin saka mata
"I missed you too" ta fadi da alaman kunya murmushi kawai yayi yana gama saka mata bakin gadon ya kuma ya zauna
Ita kuma se fesa turare take famanyi tana gamawa tazo kusa dashi "inga wayanka i missed selfie i swear"
Beyi musu ba ya zaro ya mika mata
Hotuna ta ringa dauka shi har a lokacin kallonta kawai yakeyi can seya kwanta still his eyes were looking at her yana wani lallausar murmushi
Tana gamawa ta mika mai kayanshi se yace
"Come over" yana mata nuni da inda yake kwance
"Meyasa" tayi kaman da shagwaba
"Please" ya fadi tareda yin wani face
"You know i can't refuse this face" ta gaya tana hawowa kan gadon
Kwantawa yace tayi kusa dashi
"Dan-kwalina ze baci fah"
"Se na gyara maki please ki kwanta"
Bata sake magana ba ta cire daurin gabaki daya ta kwanta a jikin hannunshi seya matso da ita kan kirginshi yana shakar gashinta
A tare suka saki ajiyan zuciya se kuma sukayi shiru
Can yace "yaushe zamu kuma gida?"
"Se su Daddy sun kuremu"
"Wai anan zamu kwana yau"
"A mana za'ayi waliman Afreen fah kuma idan muka ce masu zamu kuma ae rashin kunya ne, so kake mu kuma tare?" Ta tambayeshi tana kallon fuskanshi
"Why not i want to show you how much i love you and miss you"
"You are so cute"
"Cute!" Ya maimaita "kaman baby"
"Toh what are you idan ba baby bah"
"Who's baby"
"My baby" ta fadi a hankali wanda dakyar ze jita
"Uhm banji ba" dukda yaji but yanason ya tabbatar da abunda kunnanshi suka jimai
"You heard me"
"Seriously noh just repeat it once"
"I said my baby" ta gaya tana kukarin kulle fuska
Wani dadi yaji se ya manna mata peck akanta se shiru ya ziyarci dakin
He can't believe Ameenahn shice ke wanan magana duk ya gama kusawa su kuma gida cus he wanna shower he his love he want to make her feel very special dukda he knows she's special but he want her to know she has a paticular place in his heart
He want to make her feel like a princess
Shi bawai jikinta yakeso ba ko wani abu Noh ita kanta yakeso shi ze iya zama da ita a haka ba tareda wani abu ya hadasu ba dukda yasan its impossible amma baze taba yi mata abunda bataso bah
Sun dade a haka anyi shiru se sake-saken da kowa keyi a zuciya daga baya Ameenah ta dauke da bacci
Baccin da ta dade batayi irinshi ba
Da yaji shirun yayi yawa seya kira sunanta a hankali amma shiru seya tabbatar tayi bacci shime be dade ba bacci yayi awon gaba dashi
Mami ce ta shiga dakin da Maman da Afreen suke ciki da wani cup a hannunta ta mika ma Afreen "drink up kiban cup din"
Amsa tayi seta kalla Mama ta kalla Mami se kuma ta kalla cup din seda ta yamutse fuska setakai baki ta kwan-kwade tass ta mika mata cup din
"Yawwa yar gari Allah maki Albarka ya bada zaman lafiya"
Ameen suka fadi dukka seta kalla Mama
"Za'a iya bani gu da diyata" tayi magana da alaman zolaya
"Abun hadda yar gori toh shikenan nima ae inada yar" ta mike
"A naji a tafu de"
Dariya sukayi gabadaya se Mama ta fita Mami kuma ta zauna kusa da Afreen ta rike mata hannu
"Afreen Allah maki albarka Allah sa Marwan shine alkairi a tareda ke ya baku yara nagari"
Addu'a take mata sosai tareda shawarwari kala-kala gameda yadda zata rike mijinta
Da ta fara kunya se kuma ta saki jikinta
Tanata fadin mata yadda zata ringa gyara jikinta
*******
Can masallaci kowa an gama gaishe-gaishe aka kamo hanyan gida hadda Hakeem da Ahmed dan tunda Hakeem ya bashi labarin dawowan Ameenah ya fito daga gida zeje ganinta
Mommy ta fito neman Ameenah seta leka dakinta kawai ta gansu suna bacci hankali kwance basuda damuwa ita ta aza ma yana can masallacin ne
Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyanta danta ji dadin ganinsu haka
Finally her son is back ta fadi a zuciyanta seta janyo masu kofa
Tana wani sanyayan murmushi dan a rayuwarta idan yaranta suna cikin damuwa har zuciyanta takeji
Dukka iyaye ma
Suna isowa da mamaki sukaga motan Adeel shiga ciki akayi hadda Alhaji amma Ango bezo ba
Motan Abbah a waje ya barsu dan yanason yanxin su tafi dauko Mallam
Kiran Mami yayi ta kira mashi Inna su tafi
"Dear bazaka ci abunci ba first"
"Aa sena dawo kinga yanxin shi kadai tace yake zaune muje mu taho dashi tukunna kafin a hada masu Passport din"
"Shikenan" seta haye sama ta kirawota nan da nan yace ta fito su tafi
Su biyu suka tafi
Inna tana cikin 30s dinta bata wani tsofa ba kawai wahalan duniya ne ya tsofar da ita while Mallam kuma yana cikin 50s dinshi su duk ba wasu tsofaffi bane amma sun cire hope din haihuwa a rayuwansu.
Su Ameerah ne suka iso su uku Ameerah,Fatye da Ummitarh
Safieyarh na ganinsu ihu suka saki tare
Gaida iyayensu sukayi se suka nufi dakin Ameenah they were all eager to see her
Suna zuwa bakin kofan Safieyarh ta tura suka cusa kai dan duk basuyi expecting ganin Adeel a dakin bah.
"Awwwn" duk suka fadi a tare hadda saka hannu akan kirji kallonsu kawai suke suna murmushi dan sun burgesu
Su kam baccinsu suke tsakani da Allah dan dukkansu sun dade basu sama irin wannan baccin bah hankalinsu kwance Ameenah ta wani lume a jikinshi ta daura kafanta daya akan kafanshi guda daya shi kuma hannunshi daya ya rungumota dayan kuma ya sake rungumota dashi kaman za'a kwace mashi ita
Ameerah ce ta ja hannunsu dukka suka fice ta tura masu kofa
Dariya suka saki a tare suka sauka kasa dakin Hakeem suka shiga suna hira Safieyarh tana basu labarin halinda Adeel ya shiga sanda Ameenah bata nan
_One hour later_
Brand Walima akeyi a gidan an cika rabin mutanen da sukazo dan ganin Ameenah ne
Su Zaid suma sunzo se zuba soyayya akeyi shida Ameerah
Fatye kuma da Ahmed se Ummitarh da Fa'iz kowa yana soyayyanshi gwanin sha'awa
Suma Hakeem suna nan suna nasu
Har a lokacin Ameenah suna baccinsu Mommy ta hana a tashesu dan gadinsu takeyi tana zaune a parlo duk wanda ya nufa dakin take dakatar dashi hadda Mami
Afreen tana can a daki itada Safieyarh da Hakeem suna hira ta sake jikinta abunta
Marwan kuma suna tareda frnds dinshi a babban parlon kasa anata zulayanshi shi kuma bakinshi har kunne sakashi a gaba sukayi wai seya kira amaryanshi
Ya dauka wayanshi daman tun-tuni yanada number ta ya shiga kiranta amma ya matsa gefe
Yanata ringing harya katse bata dauka ba dukda tana gani ita bata dauka number ne
Ya sake kira Hakeem ne yace ta dauka mana taki kawai se ya daga call din ya sa mata a kunne dan dole ta amsa
"Assalamu alaikum" taji muryan Marwan me dadi masifa dan seda tayi ajiyan zuciya
"Waalaikumus salam" ta amsa a hankali
Lumshe ido yayi "Amarya kinsha amshi"
Murmushi kawai tayi batayi magana ba dan tanada masifan kamun kai
"Angonki ne " taji wani ya fadi daga gefe
"Banson iskanci fa Mu'azzam" ya fadi yana mikewa parlon ya bari gabadaya
Ita batayi magana ba tana jinshi kawai
"Afreen" ya kira sunanta wani murmushi ta saki dan bata taba jin wanda ta iya kiran sunanta ba kaman haka
"Na'am" she answerd with her sweet voice
Hira suka danyi kaman wanda suka saba ita kawai
"Uhmm ko Aa" take fadi
Har daga baya sukayi sallalama
Tana kashewa kwanciya tayi kan gado tana wani murmushi
Dariya su Hakeem suke mata dansun gane dawa take waya.
πππ
[14:01, 4/1/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: Walima sosai akeyi se ciye-ciye akeyi kuma kowa se tambayan Ameenah ake
Yan uwansu dake kusa harsunzo anata murnan dawowanta wasu kuma jahilan cewa sukeyi
"Waya sani ma ko aljani ne yayu suffanta yace itace"
Hakade kananan maganganu
Su Ameerah harsun gaji da jiran tashinsu Zaid kowa cewa yayi shi tashi zeyi ya tafi Ameerah ta hanashi
Hakeem ne a kofan dakin yana son ya tasheshe amma ya rasa ya zeyi dan ya gaji kowa idan yazo shi ake tambaya Ameenah
Kujeran dakin Mami na mirror ya jawo yazo daidai kofan dakin kawai seya daga ya buga a kasa da sauri ya dauka ya maida seya sauka kasa yasan dole su tashi
A tare suka furgita suka bude ido
Ameenah taga inda ta shege jikinshi kaman mage se abun ya bata kunya cire kafanta tayi tana mika tareda salati shima haka
Agogan hannunshi ya kalla yaga 4:32pm zare ido yayi yana kallonta
Hannunshi taja gun agogan itama ta kalla ae seta diro daga kan gadon ta shiga toilet dan tayi alwala tasan an nemeta
Tana fitowa shima ya shiga yayi zama tayi tana jiranshi dan yaja masu
Fitowa yayi yana gyara hannun rigan seya kalleta mikewa tayi ta dawo kan dadduman kaman yasan abunda take nufi seya shiga gaba ya tada suka fara sallahn
Suna gamawa tayi addu'anta seta mike ta cire hijab din gaban mirro taje ta gyara fuskanta ta dauka dan-kwalinta ta shiga daurawa ya gama shima amma yana zaune yana kallonta shi be gajiya da kallonta kwata-kwata.
Tana gamawa ta juyo" How many hours muna bacci ze kai 3 fah"
Murmushi yayi mata kawai seya mike "Can we go no"
"Tare" ta fada tana zare ido
"Yah Why not se kace ba matana bah"
Taso tayi magana se kuma ta mike bude mata kofan yayi ta fara fita shima ya fito ya janyo kofan dafa hannunshi a bayanta yayi suka jero
Ba suyi nisa ba sega wata mata irin family frnd dinsu ce kawai seta rungume Ameenah
Itama tayi huging nata back tana murmushi
"Wlh se yanxin na yarda kin dawo am so glad"
Can bayan yan surutai suka sauko tare har a lokacin yana dafe da ita
Duk inda ta wuce daga me rungumeta seme rike mata hannu hadda masu kuka
Dakin Hakeem suka shiga suka tararda kowa a ciki (frnds) hadda Afreen se hira akeyi su Ameerah suna ganin shigowanta a tare suka saki ihu sukayo kanta se kuma aka fashe da kuka rungume juna akayi sosai dukka su hudun sun dade a haka aka sake juna
Su Zaid sannu da zuwa suka mata ita kuma ta gaidasu da fara'arta
"Matarshi ta dawo yaki barin kowa ya ganta"
Abunda Zaid ya fadi kenan yana ma Adeel wani kallo
"Daman yaza'ayi na barta yanxin ma sa'a kukaci ta fito kana bata min rai sena maidata dakin"dariya kowa ya saki
"Ayi mana hakuri" Ameerah ta fadi
Ita kowa Ameenah murmusawa kawai takeyi
waje suka sama aka zauna anata hira Ameerah tana rike da hannunta har a lokacin hawaye takeyi
She can't believe her best frnd is really alife
Ahmed ne ya shigo yana ganinta kanta yayo da sauri ze rungumeta dan zumudi seyaja burki ya kalla Adeel daya zare ido yana kallonshi
"Ya Adeel zan dan iya rike kanwata kadai kawai" da zulaya yake magana
"Uhmmmm Noh!!!" Shima ya fadi
"Toh shikenan tunda an min ruwanki" yana magana yana kallon Ameenah
Mikewa tayi tayo gunshi tana dariya kawai seta rungumeshi "Am so glad you are here"
"And am so glad you are alife"
"1....2... idan na kai 3 baka sake ba i will punch you" Adeel ya fadi yana dosan gun
Ahmed kokarin ganyewa yakeyi amma Ameenah dan mugunta seta ki sakeshi
"Ameenah ki rufamin asiri ki sakeni" dariya takeyi sosai
Adeel yana zuwa gun seta sakeshi ajiyan zuciya ya saki "Amma wlh ke muguwa ce har yanxin baki bar mugutanki bah"
Fashewa akayi da dariya kowa Adeel kuwa murmushi yayi ya riko matanshi
Hakeem yace "Nifa tun zuwanki Adeel ya hanani rikeki" yana magana kaman karamin yaro yanson yin kuka
"And meyasa zan barka"
"Because nima i missed my sister"
"Awwn really you do?" Ta fadi tana zuwa gunshi ta rungumeshi
"And i missed you too big bro"
Kallon dakin tayi taga babu mirror shi dukka biyu
"Ina mirror ka suke wai dakin yayi wani iri haka"
"Hmm ba mijinki bane ya fasa min dukka ae ina jiran randa zaku kuma ne na biko na dakinki zan ciro"
Kallon Adeel din tayi "How comes?" Tana dusan inda yake
Shiru yayi ya wani hada hannunshi gu daya yana kallon gefe kaman badashi take magaba bah
Safieyarh tace ni zan gayan maki abunda ya faru
"Wlh idan kikayi magana Motan da nayi maki alkawari on your 18th birthday zan baki is done"
Ae komawa tayi ta zauna bata sake magana ba
"Ni barin baki labari" Hakeem ya fadi wani kallo Adeel yayi ma
"Ae sefa na fada sede idan zamu sa labule zanyi shiru"
"Zamu saka"ya fadi da sauri
"Haba mana dan Allah ku gayan min"
Auntiee ce ta shigo ni zan gayan maki
Ita tun dazin ta kuma gida tana ma Daddyn Meemah girki dan yau ze dawo se yanxin ta dawo tareda shi
"Haba Auntie karki fadan mata mana" Adeel ya fadi
"Why?? You don't want her to know you love her, tou sena gaya"
Ta kwashe dukka event daya faru ta gayan mata hadda maganganun da yakeyi dukda itama Mami ce ta fadan mata
Ameenah ji tayi ita ta gama sa'a a rayuwa she have nothing else to ask for sede godiya dan ta gama samun komai ga iyaye masu sonta kuma nagari ga kuma mijinta
"Allah nagode maka" ta fadi a zuciyanta
Tana wannan tunanin amma idonta na kan mijinta shi kuma wani basarwa yakeyi
Su Muhseen suma sunxo amma basu wani dade ba suka kuma sunyi murnar ganinta sosai
*****
Abbah sun isa an dauko Mallam amma dakyar ya yarda har seda matanshi abun kaunanshi tayi hawaye seya yarda a taho dashi kulle gidan sukayi aka kamo hanya a lokacin an gama masu komai isowarsu kawai ake jira daga nan ma baze tafi gida ba Airport din Kaduna ze kaisu sesu tafi su uku da PA dinshi ne
Suna isa Airport din Abbah ya bama PA din makudan kudi wanda zasuyi amfani dashi kaman gun sayan kaya dan basu dauka komai ba da kuma gun zama amma komai da komai an gama biya jiranshi kawai akeyi
Godiya suka ringa ma da Addu'oi kala-kala suna kuka dakyar ya lallasesu akan abunda suka mai yafi abunda ze masu
Suna gamawa ya taho gida abunshi sati biyu zasu acan su dawo.
Misalin karfe 7pm
Ameenah da Afreen se Safieyarh suka zaune a dakin Ameenah suna hira abunsu dansu Ameerah duk sun tafi gida dan su shirya saboda kai Amarya da za'ayi se'a tafi Dinner daga nan dan a gidan Amaryan zasu kwana dukka
Dan ita Afreen batada kawaye kwata-kwata anan so sune zasu mata kara
Kaya Mami ta kawo ma Afreen dakin kala biyu
Da wani less da zata saka yanxin idan za'a kaita da kuma na Dinner
Ameenah ce ta amsa wai ita Afreen kunya takeji
Bayan Mami ta fita suka sakata tayi wanka dan sune manyan yayyu saboda Auntiee ta tafi ita tana fitowa aka shiga shiryata cikin less din yayi mata kyau sosai daukwalin ya zauna kwalliya aka shiga mata suna gamawa gyale aka yafa mata Mommy tazo ta fita da ita dan kaita gun iyayenta suyi mata fadi
Su kuma a lokacin suka shiga nasu shirin
Safieyarh daman ta dinka sabon kaya saboda bikin Adeel da Afra ita kuma Ameenah daman tanada kayan da bata taba sakasu ba daman
Cikin atanfa suka shirya sunyi masifan kyau
Jaka Ameenah ta samo ta dauka kayan da zata saka da Dinner da kuma kayan baccinta se duguwan riga kuma
Itama haka Safieyarh ta saka nata a jaka
Number su Fatye aka shiga kira sukace gasunan a hanya sunma iso
Fada ake ma Afreen sosai se kuka takeyi duk ta bata kwalliyan Mama ma ita kukan takeyi kaman ba gobe suna gama mata seta rungume Mama wai ita batasan a rabata da Mamanta dakyar aka rabasu aka fito da ita
A lokacin an kawo motocin daukan Amarya se aka fito da ita waje se kuka takeyi a motan dake tsakiya aka ajiyeta Safieyarh taje ta zauna kusa da ita Ameenah na shirin shiga taji an jawota kawai taga Adeel
"Wlh ka ban tsoro"
"Ina zaki da kayan nan"
"Kai Amarya ofcourse"
"Ki fasa zuwa mana kawai"
Murmushi ta saki "ae kasan baze yuwuba dagani ni se Safieyarh manya kaga dole muje"
"Tou Auntie fah ita bazata bane"
"Zatazo Dinner amma baza'a kai Amarya da itaba dan mijinta ya dawo"
Da kyar ya samu ta yarda akan ta jirashi ya shirya seya kaita daga nan sesu tafi Dinner tare
Cema Safieyarh tayi su tafi ita zata zo anjima
Kumawa ciki sukayi dakin Hakeem suka shiga wanka ya wuce kawai ya wanke gashin kanshi ya fito dagashi se towel ita kuma tana zaune bakin gado da wayanshi a hannunta tana kallon hotona
Hotonanta ne baja-baja a ciki hadda wanda batasan ya dauka bah
Daga kan da zatayi se ganshi da towel kawai idonta akan 6 packs nashi suka sauka tayi 3mins tana kalla shi bema san tanayi ba dan ya rufe fuskanshi da wani towel yana guge gashinshi
Dauke kanta tayi da sauri gabanta na dukan uku-uku kawai se taga ya duso gunta ae wayan dake hannunta hannunta kallonshi kawai takeyi amma hankalinta be gun jikinta har wani rawa yakeyi
Gabanta ya tsaya dai-dai ita seta dago yana kallonta hannunta tayi sauri ta kare idonta "Ya Adeel meye haka babu kayafa a jikinka"
"Wannan towel din meye toh"
Kawai se taga dukuwa gunta baya-baya takeyi amma a zaunan shi kuma se binta yakeyi fadawa tayi kan gadon ta kwanta har a lokacin idonta na rufe
Cigaba da binta yayi
"Ya Adeel please stop it"
Hannunshi yakai seya dauka kayanshi a bayanta seya sakar da murmushi danya ga ta tsorata juyawa yayi ya nufa closet din Hakeem
Da taji shiru seta bude ido taga babu kowa a gun ajiyan zuciya ta saki dan ta aza tabata zeyi se kuma ta saki murmushi
Can seya fito a shirye gaban mirror ya shafa ya gyara gashinshi ya feshe jikinshi da turare
Da sauri ta mike "Nima bani na fesa"
Be bata ba seya shiga fesa mata seda tayi atishawa ya barta
Buttile din riganshi ta gyara mai seya riko waist dinta tana gamawa zata juya se taji be sake ba kallonshi tayi seya ce
"Just a kiss"
"Ammm Nop Akwai lipstick a bakina"
"So zema fi dadi please just one"
"Kasan fa ana jirana kilan ma yanxin sun isa dan Allah kazo mu tafi"
"Seriously bazan sake-"
Ba karasa ba takai mai hannunta na kan packs dinshi shi kuma a waist dinta seda taga yayi nisa se tayi pulling back ta kwace gabadaya tana murmushi
Kallonta yayi "Anya dagaske Ameenah ce wannan" yana magana yana kokarin sake kamota
Tuni ta kama hanyan fita tana dariya biyota yayi suka fito yana rikeda jakanta
Kawai se sukaci karo da Mamai "Daman baku tafi bah "
Kunya ne ya lullubeta seta kasa magana dan taga Adeel ya fito
Shima susa keya yakeyi can yace wayan Afreen muka dawo dauka ta manta dashi ne
"Ohh tou sekun dawo" seta wuce
Can kowa an kai Amarya yar'uwan Mami ce ta sakata tayi addu'a kafin ta shiga haka tayi dukda tana kuka da kafar dama ta shiga ciki basu tsaya ko ina ba se dakinta fuskanta a lullube se kuka takeyi Safieyarh ce keta faman bata hakuri
Suna zuwa gun motan seda ya bude mata ta shiga ya ajiye jakan seya zagaya ta gefanshi shima ya zauna tada motan yayi suka kama hanyan gidan
Suna isa ba tareda bata lokaci ba suka fito ya rakota har bakin kofan dan akwai mutane ne amma yayi niyan shiga har ciki
Mika mata jakan yayi "karfe tara fa zanzo mu tafi tare" daga mai kai tayi seta shiga ciki seda ya ganta ta shige har ciki seya juya ya shiga motanshi
Tana shiga dakyar ta iya shiga cikin dakin dan mutane sunyi yawa a cikin parlon a bakin gado ta samesu Safieyarh nata bata baki amma kaman tana kara zugata ne
Zama tayi itama ta shiga lallashinta dakyar tayi shiru su Ameerah suka iso suma duk suka shigo dakin
Ba'a wani dade ba yan kawo amaraya suka tafi daga Amarya sesu Ameenah a cikin gidan hira duke danyi dan Afreen ta saki jikinta
9:30pm
Suka shiga shirya ta cikin wata blue gown yayi mata kyau sosai Ummitarh ta daura mata head golden da golden takalmi tayi mata kwalliya tayi masifan kyau kaman ba Afreen da aka sani bah se suma suka fara kokawan shiri
Wayan Safieyarh ne ya fara ringing tana dubawa taga Hakeem a kunne ta kara
"Babe kuna inane wai tun dazin muke jiranku a waje da Marwan kuma se kirana akeyi wai an cika Amarya kawai ake jira"
"Gamu nan fitowa yanxin muka gama shiri"
"Tou shikenan" seta kashe
Gayan masu tayi ana jiransu a gurguje suka karasa shiryawa aka fito
Ameenah na rikeda hannun Afreen fuskanta a lullube
Itama Ameenah tayi kyau dan red gown suka ska dukkansu da kuma black head
Daman safieyarh ce ta fara siya tou Ameenah nadashi se suka fadan ma su Ummitarh suma su saka shiyasa sukayi anko
Bude motan tayi Marwan ne a ciki yasha shadda ba karamin kyau yayi ba da wani murmushi kwance a fuskanshi
Tana shiga ciki se Ameenah ta kalleshi "Ka rike mata hannu duk abunda ya sameta nida kaine wlh"
"Tou Auntie babba" seya kai hannunshi ya rike nata a tare jikinsu yayi wani yarrrrr!!!!
Murmushi tayi ta kulle kofan Afreen kowa kanta a kasa yake
Kowa ya shiga motan saurayinshi aka hada convoy suka tafi se Ameenah kawai tana juyawa taga Adeel daman shi take nema kallonta yake dan ta tafi dashi
"I thought bazakazo bane"
Riketa yayi you look amazing
"Thank you"
"Amma zaki saka gyale koh"
"Iyye kishi kakeyi ba gyalen da zan ska"
"Haka zaki jikinki a bude tou ae gara a fasa zuwa gabadaya"
"Tou tsaya naje na dauko" da sauri ta kuma ta dauko ta dawo suka kama hanya hotona taketayi a motan wayan Adeel de ya bani
Cewa tayi ya juyo ta daukesu tare dakyar ya juyo se dauka takeyi rabi fuskanshi jefe ake gani saboda driving da yakeyi.
0 comments:
Post a Comment