Free page.
_Asmy b Aliyu_
A fusace ta nufi stairs da axamarsa ya cimmata gamida fisgota ta fada kan jikinsa,farar fuskarta ya kurawa ido.Wanda yana daya daga cikin Abunda yakeso ajikinta,haka Allah yayisa A rayuwarsa yana son farar Macce.lokaci daya ta fara Tara kwallah a idanunta,kara narke mata yayi .cikin fushi take kokarin fisge hannunta,daukarta yayi gaba dayanta ya nufi part dinsa daita,kafa yasa ya tura kofar dama a bude take bai direta koina ba sai akan farar soofa ,kokarin mikewa take .ya xuba mata blue Eye's dinsa,Wanda yasan sune weakness dinta.Hannu ta saka ta koina tana kai masa duka take fadin"I hate you ."I hate you Aliyu waxeer!!""ta fada da dukkan karfinta hawaye na Rolling akan face dinta,Dora kanta tayi akan kafadarsa tana kara volume kukanta,Sam shi baya jure kukan macce ko kadan,ya tsani kuka.....
Ya rike kyawawan hannayenta yana murxawa a hankali ,cikin sanyi muryarsa yake fadin. "I miss you my girl,
" you did not tell me xaki xo ae."ya fada yana Dan daga kafada gamida Dan buda kyawawan idanunsa,wata irin harara take yimasa da fararen idanunta Wanda suka fara canja kala.sau nawa Haidar?""Har sai yaushe xaka daina wahalar da xuciyana."muna gari daya,na dawo Hutu ka kasa xuwa ka dubani.sai nice xan rika biyoka naku gidan,nice xan rika daga waya na kiraka nice mai xuwa hira gidan Ku.wannan wace irin soyayyace marar tsari.?"ta fada cikin sanyi murya,Dan karamin bakinta ya kaiwa kiss ya saki murmurshi gefen kumatunsa duka suka lotsa..fuskarta ya kara kaiwa kiss yana fadin"Am sorry my girl friend my one and only."ke kinsan baxan shareki ba haka kurum ina busy ne kuma Bestyna ya shigo gari ,harara ta shiga watsa masa cikin shagwaba take fadin"Dama nasani ka fison Farhaan Shagari akaina,da karfi ya shiga fadin "Nooo kowa matsayinsa daban,duka ina sonku wlhi,ya fada yana Jan kumatun ta tamkar wata Bby haka ta rika turo masa kyakkyawan bakita.ya mikar daita tsaye yana fadin mu fita yawo yau tym dinki ne....
★ ★★
Baki sake Mami ke binsa da kallon takaici,kallonsa ya mayar kan daddy Wanda yaki yace komai.sai ma jarida da ya dauka gamida saka farin gilashinsa mai karawa idanunsa gani,salati Mami ta shiga xubawa tana fadin anya kuwa kanka daya Farhaan?"tayi maganar a mugun fusace,shuru yayi batare da ya kalli Mami ba.......Ya rabbi Allah yasa mafarki nake,Allah yasa ba gaskiyya bane Mami ta fada tana rufe idanunta Dan tabbatarwa,tana buda idanunta taga farhaan xaune agabanta." Farhaan gobe ka shirya kayanka kabar kasar nan,
Wlhi baxaka kunyatani ba,shekarar ka talatin da biyu fah."yayunka duka mata ne,kaine kawai nake dashi da xan jingina a kafadarsa nayi alfahari dashi a matsayin Namijin da ya fito daga cikin tsatsona,Farhaan ba yanxu nakeso kayi aure ba,,ka fahimta ina son ka xama wani Abu a rayuwarka,ina son ka kasance cikin manyyan attajiran da xaa rika gogawa dasu a kasar nan,me malami ya fada maka."kasan dai halin dangin ubanka kou."bawani kaunata sukeyi ba,kuma duka Rabin su a karkashin companyn mahaifinka suke aiki,,Allah kadai yasan cutar da ake yi masa."idan ma Hajia Yasira taji baxata ji ddi ba,ji yarda take son kaxama surukinta ,nan ba da jimawa ba Idan Alh.Azzex Ali ya hau kujerar governor shi xaa tsayar da ixinin Allah.,Allah kadai yasan irin alkhairin da xamu samu."ka mayi shuru da wannan maganar kar aji a waje ayi mana daria Dan Allah."ya dago da idonsa da suka kada sukayi ja yana kallon maminsa yana mamakin ta yana karawa,
Akan wani ra'ayinta marar tushe.....kiyi min rai Mami,ya fada da wani yanayi a muryar sa gidan su noor sunce ta fiddo da miji Idan ba haka ba xasu aura mata duk Wanda sukaga dama."su Aura mata mana me ake da gayyar talakkawa ,dama baka rabu da wannan matsiyaciyar yarinyar ba,,idan mafarki kake ka farka.tana nuna sa da yatsa cikin natsanin fushin da bai taba gani a idanunta ba take fadin"idan kana son kanka da lafia Farhaan shagari ,inhar ni na haifeka na dau cikin ka watanni Tara nayi nakudarsa,karka kara kawomin xancen yarinyyar nan,batayi Isar da xan hada jini daita ba."Farhaan shagari tun daga kansa har yatsan kafarsa yake hada gumi duk da sanyin split dake ratsa falon,haka Mami ta tsallake sa cikin fushi tabar masa falon...Ya juya kan Alh.Omar shagari Wanda har lokacin yaki yace komai akan xancen......dajan duwawu ya karasa gaban mahaifinsa ya rike kafafun sa gagam,hawaye na xubar masa yake fadin"Daddy kayi min rai idan ban samu Noor ba mutuwa xanyi wlhi."ka fahimtar da Mami hakan Dan Allah,shafa kansa daddy yayi yana fadin"kayi abunda mahaifiyarka keso Muhammad, nan shima daddy yabar masa falon,dafe Kansa yayi Wanda ke baraxanar yimasa ciwo,ya rasa waya'nne irin iyaye Allah yabasa masu akidar nasara......
★★★
Wani mugun kallo Aliyu kebin Farhaan dashi,Ahankali ya shiga girgixa kai yana sakin murmushin da shi kadai yasan ma'anar sa.da alamar bakada hankali Farhaan ka samu tabin kwakwalwa,
"Ni kake tunanin naje na auri yarinyyar da kake so har na tsawon shekara daya."Aure ta kurane Farhaan Shagari ko kusa ban kawowa kaina Aure nan kusa ba,,kaima kaji xaka iyane yarinyya duk tabi ta wani shanyeka sai kace manyya." Kama daina wannan maganar ko nayi fushin da ban taba yimaka irinsa ba,ya fada so pissed up yana hade rai,Farhaan ya lankwasa kai yana kallon Abokin nasa da idonsa da suka fada lokaci daya,
"Nasan nooryna bata cikin kalar matan da kakeso ,nasan ba ajinka bace,nasan baka sha'awar (BAKAR MACCE)."
Nasan ka nasan natsarinka Mr.Aliyu waxeer galadima.Abokin ka xakayiwa wannan alfarmar,da xarar na kammala masters dina xan dawo gareta muyi Aure."Nasan karatuna shine burin Mami ni kuma burina na mallaki Noor,xan mallakawa Mami duk abunda takeso."nima xata barni na Rayu da wacce nakeso,xan saka Noor makaranta bayan Auren Ku ina son Noor ta samu ilimi sosai,nasan baxaka ci amanata ba xaka kular min da Noor fiye da yarda xaka kula dani idan ina kusa."girgixa kai Aliyu ya shigayi yana fadin ka haukace Farhaan wallahi ka haukace...!"
PAID BOOK
ASMY#❤️
Haske Writer's Association #
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: *_Waminal Hoob_* 2
PAID BOOK
Free page.
_Asmy b Aliyu_
Areefa!!"Ya fada yana sauke numfashi ,kara damke hannunsa Farhaan yayi ,Aliyu na girgixa kai yake fadin "nasan Yarda Rayuwa take xo muna ne Farhaan,A tare take tabamu a tare muke Raba duk wata kaddara da xata samu dayan mu"........Banda wannan besty ban dashi karka bari na dauki abunda baxan iya karasawa ba Dan Allah."Aliyu ya karasa maganar cikin karaya,Hawaye suka cika idon Farhaan lokaci daya.idan ban samu Noor ba zan iya mutuwa besty."ya fada yana sauke numfashi ,nasan Areefa mansoor xata iya kisan kai akan ka ,zamu taru duka mu fada mata gaskiyya,bana son wani Abu ya samu Noor dita."
Kansa ya Dora kan sitarin motar yana sauke numfashi gaba daya Farhaan din ya gama dauresa,ya tsani ganinsa cikin damuwa.tun suna yara haka suke tare suke Raba damuwarsu,yana dago kansa yaga Farhaan ya xuba masa ido,shaye da toka Aliyu ke fadin kan wannan Noor din xaka bi ka wani daga hankalin ka."bana son wannan Noor din taka,gata yar baka."Aliyu waxeer ya fada yana sakin daria,
Wanda yayi ne Dan Farhaan din ya sake......duka Farhaan ya shiga kai masa yana fadin bana son wulakanci dama nasan Nooryna batayi maka ba ae."ko bayan Aurenku ban yarda ka wulakan tamin baby ba.tada motar yayi sukabar wurin......
★★★
Cikin sanyi ta take nufar motar Farhaan, kureta da ido Aliyu yayi. ya tsani koda cin karo da bakar fuskarta ne , da ya yarda ya kalleta gabansa ke faduwa,saboda bakin ta.irin yaran nane da baxasu wuce cwt 16 ba,kuka kikayi ko Noor?""Farhaan ya fada yana kafeta da idonsa,lokaci daya kuma yake karantar yanayin ta.
Ahankali ta shiga girgixa masa kai haka tana wasa da dogayen yatsun hannayenta,
Gefe Aliyu ya koma ya xuba masu ido,kare mata kallo yake daga sama har kasa,ko kadan bbu wata wayewa a tattare daita sai tarin kauyanci da gidadanci ,gaskiyyar Mami ne,Asiri!""ya fada yana hade rai,
Yes Asiri akayiwa Farhaan dinsa,idan ba Asiri ba taya xai so wannan bakar kuma yar tallakawa likis.!".........Jin yayi Ahankali Ransa na baci ,xuciyarsa na narkewa.sai da Farhaan ya Dan tabosa ,meyasa kake haka Besty ina jin Noor na gaisheka kaki ka amsa ko fuska kaki ka sakar mata,haka xakuyi xaman Auren."kana iya hango wani yanayi acikin kwayar idon Aliyu,da alamar shi kuma Farhaan kallon da Aliyun keyiwa Noor yana tabasa....kallon kyama da tsana,
"Besty xo muje nayiwa Noor bayani agabanka ya fada yana Jan hannun Aliyun batareda ya yarda sun hada ido ba,
Hawaye na xubar mata take girgixawa Farhaan kai,cikin sanyin murya da gigita take fadin baxan iyaba Farhaan."baxan iya wannan Auren ba,wannan wane irin Aure ne?ta fada tana jin wani irin ciwo aranta,
Ni baxan aure sa ba kawai mu hakura Farhaan,wannan itace kaddarar mu baxan iya auren Aliyu waxeer ba."Yafi karfina ta kowane fanni na Rayuwa,
A fusace taji an fisgota tamkar Ya riko takarda haka yake jinta a hannusa,hannu yasa xai xabga mata mari yaji an rike hannun,
Afusace ya turata yana huci tamkar zuciyarsa xata fito sabida bakin ciki,
Farhaan ne yayi saurin tarota da tasha kasa.
A fusace ya juya ya nufi Mota ,ya mata key anan yabar wurin da wani irin speed yana badesu da kurar wajen,Ahankali Noor ta kwace kanta daga rikon da Farhaan din yay mata nan ta xube a kasa tana sakin marayan kuka,hannu ya saka yana squeezing sumar kansa,cike da bacin rai yake fadin"laifinki ne Noor meyasa xakiyi Rejecting dinsa haka,
Kin San ma waye Aliyu??
Baki San taya ma na lallabasa ya yarda xai aureki ba ."saboda ya tsaneni haka bana da gata kou."Ta fada still hawaye na xubar mata,
Auren Ku na Dan wani lokaci ne sabida kawu nayi haka,sabida kar ya Aura maki kabeer nayi haka,kinfi son ki auri kabeer ki xauna da shi fiye da bestyna?"Ya fada a tsawace,bata taba ganin Farhaan haka ba.tsawon haduwarsu na shekara daya,
Motar kawunta taga tana tahowa ,ta masu jigilar xuwa garuruwa......da gudu ta nufi hanyar gida ,A fusace Farhaan ke kallon motar ,kallo-kallo suka tsaya yi shida kawu balele dake maxurai.
Koda minti daya bai kara wajen ba ya taka xuwa bakin titi da kafa........tunanin sa daya ta yarda xai kara shawo kan Aliyu xaiyi wuya ya kara sauraren sa,
★★
Yarda ya wani shigo falon a hargitse ,yasa Ammah da batool da suke xaune a falon suka bisa da kallo lokaci daya.kai tsaye kitchen ya nufa sai gashi dauke da bottle water a hannunsa,cikin kyawawan kujorun da suka kawata falon kalar maroon yayiwa kansa masauki ,kafa kai yayi sai da yaji babu komai ya dire kwalbar,har yau mahaifiyarsa kallonsa take tana mamakin yanayinsa........hannu yasa cikin sumar kansa mai kama da ta labarabawa yana hargitsata ,kasa daurewa Amma tayi tana fadin"kai lafian ka??
Kurawa mahaifiyarsa ido yayi na Dan wani lokaci ,
Aliyu bana son iskanci!!"
Ya mutse fuska yayi yana fadin babu komai Ammah na gajine,
Dan ka gaji shine xaka shigomin falo a haka."
Tashi kabarmin falo,ammah ta fada tana Dan daka masa tsawa,.
Babu musu ya mike yabar falon Dan yasan sarai Ammah bata daukar raini ,akwai yar tafia daga part dinsa xuwa na Amma.hango motar Areefa mansoor yayi tana parking yayi mamakin ganinta yanxu,
Kananan kayane ajikinta Wanda sun Dan kamata,sai Dan karamin veil da tayi Rolling kanta dashi,tun kafin ta karaso yakejin mayen kamshinta,
Tana karasowa ya shiga dube-dube kar batool ta gansu,yana daure face yake fadin meyasa bakyaji Areefa??Dan bude ido tayi tana fadin "me kuma nayi ,kin San Ammah bata son wannan shigar meyasa kikayi?"ya fada da xafin rai,dage kafada tayi tana fadin kai nakeso kuma irin shigar da kakeso kenan,ae Ammah bata da Matsala tana son Abunda kake so."ni kuma manyyan kaya suna takurani ae kasan da haka." Ta fada cike da Rashin damuwa a fuskarta,
Shigewar sa falo yayi ya barta nan tsaye yana gafda shiga master bedroom dinsa ta cimmasa,rike kofa yayi yana kallonta.
"Kije gida gobe xan shigo........kullum haka kake fada,ni baxan iya bari har gobe ba." Ta fada da damuwa a fuskarta,
OK ranar da kika shirya ki kikirani naxo banda yau bana son hayani ya fada yana buga kofar a fuskarta....
PAID BOOK
ASMY#❤️
Haske Writer's Association.. #
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: _*Waminal Hoob*_ 3
PAID BOOk
Free page.
_Asmy b Aliyu_
Tun daga karkashin xuciyarta takejin wani bacin rai na saukar mata,da gaske Aliyu waxeer ya daina yayinta kwana biyu duk yabi ya canja mata, ido biyu sukayi da batool waxeer wacce ta crossing hand's dinta akan kirjinta tana bin Areefa mansoor da wani irin kallon da ta kasa fassara sa.lokaci daya ta wara hannayenta gamida buda ido tana sakin daria,Dan Allah bakiji kunya ba."kinxo wajensa hira ya koraki kina matsayin macce,duk wannan ajin da kike tunanin kina dashi ina yake?"sai na hadaki da Ammah billah."batool ta fada tana wani bude mata ido,bata karabi takan Areefa ba ta juya da sauri tabar part din Dan taga yarda Areefa mansoor ta fusata .
Yana kwance cikin doguwar soofa daga shi sai farar vest da trouser ba barci yake ba,sai dai idonsa a rufe suke ya kure A/c da volume din T.v tamkar zai tada gidan so yake koda so dayane ya manta fuskar bakar Yarinyyar nan,amma ya kasa da ya rufe idonsa ita yake gani,yana cikin wannan yanayin yaji ana buga kofar tamkar xaa ballata ,
Ya Riga da yasan bbu mai wannan Aikin sai batool waxeer.yana buda kofar ya wani fisgota tamkar xai rabata gida biyu,
Wayyoni Yah Aliyu ko ba Ammah bace tace na kira ka."ta fada tana wani turo baki gamida shigewa jikinsa,cike da balai da masifa yake fadin sau nawa xan fada maki ki daina bugamin kofa??jikinta ne ya kama kyarma ko ba Ammah bace tace na kiraka."turata yayi da karfi ta dafa bango tana kallonsa a tsorace,ya daka mata tsawa yana fadin ba magana nake maki ba."hannu ta fara yarfi dashi tana fadin sau dayawa mana........ta fada tana jada baya gamida yarfi da hannunta,Am sorry karka dakan Dan Allah."da haka ta ceci kanta ta fita da gudu,kwala mata kira ya shigayi tayi masa banxa.
Yarda ta shigowa Ammah a falo yasa Ammah kallonta tana girgixa kai take fadin kin jawo rigima kou."ko takan Ammah bata bi ta nufi nata dakin......da sallama Ya shigo falon ya nemi wuri ya xauna wani irin kallo Ammah ke binsa dashi ganin yarda ya shigo mata falo,jeka ka sawo jallabiyya Aliyu nan ba cikin barak bane."
Ammah mana."Ya fada yana wani hade rai,
Wani irin kallo Ammah ke masa ya Riga da yasan ma'anar kallon bbu musu yabar falon bai dde ba sai gashi sanye da brown jallabiyya Wanda yayi mugun karbarsa ,mai guntun hannu .sai da ya xauna ta kallesa tana fadin wacece taxo part dinka??"shaye da toka yake fadin Ammah wake kawo maki irin waya'nnan maganganun??"ya xaayi macce taje part dina."Ya fada yana wani hade rai,
Karya nake kenan??"Ammah plz............"yyi maganar cikin daga murya da alamar ya manta agaban wa yake,yana mmkin yarda baya iya controlling din fushinsa,
Ni kake dagawa murya don ubanka."Ammah ta fada cikin bacin rai,Am sorry ya fada cikin sanyin murya yana kamo hannunta,fisge hannunta tayi tana yimasa wani irin kallo take fadin Aliyu na baka nan da sati daya ka tsaida maganarka akan Yarinyyar nan,xanyi magana da baffanka ajey aga magabatan ta ya ,na gaji da wannan rashin kunyar xanyi abunda kake so...."kasan bana cikin iyayen dake tauyewa yayansu hakkinsu ae kai xaka xauna daita Right."duk rashin kunyarta idonka a rufe yake baka gani gaka ga wayewa ,nidai na gama magana baxa awuce sati daya ba nagama magana."Ahankali ya shiga hargitsa sumar kansa da wani irin yanayi yake kallon mahaifiyarsa,
Kusan sau ukku yana sauke ajiyar xuciya da wani irin yanayi a muryarsa yake fadin"kiyi hakuri Ammah Dan Allah kar ranki ya baci,xanyi aure kwanan nan tunda kin matsa, Amma ba Areefa ba wata daban."da mmki Ammah ke kallonsa karka fara irin wannan wasar Aliyu bana son xalunci."!lumshe idonsa yayi ya rasa ta yarda xaiyiwa Ammah bayani yasan muddin ya fada mata irin auren da xaayi shida farhaan baxata barsa ba,
Ammah karki damu watace daban kin san Areefa bata kammala karatun ta ba,,murmushi kurum Ammah ta saki ta San akwai wata a kasa.
Sai dai bataso ta kuresa ,
"Allah ya kaimu ya kuma nuna mana lokaci ."da sauri ya mike tsaye yana fadin" Ammah bara naje masallaci....da ido kurum tabisa.
****
Bokitin dake tsakiyyyar gidan Wanda yasha gyara ya koma kalar ruwan toka sabida dauda ,shi kawu balele ya kaiwa hauri........Adama!!"Adama wai kina ina ne?"Adama dake cikin kitchen tana kasa shinkafa da wake na siyarwa ,tana xubawa kowa kwano-kwano .ga yara nan sunyi layi harda samari,
Afusace ta fito tana gyara daurin xaninta wanda yasha gyara tana fadin"wai lafia malan kake xabgamin kiran Ya'n wuta."tayi maganar so pissed up..da alamar ta gama raina sa,ina bakar yarinyyar nan ta shige ne."wato da ixininki take xuwa xance kofar gida,kuma kin San matar kabir CE da xai aura??"shaye da toka take fadin can Ku karata kaida yaron naka,ni kabarni naje ga sana'ata ta fada tana barinsa a wajen.wani Dan karamin daki ya nufa yana fadin"ina kike bakar munafuka mai bakin hali,Nooriyyah najin muryar kawu balele ta kara lankwashewa kan tsohuwar tabarmar da ta gama yagewa sabida tsufa .idan akwai abunda ke hargitsata yake firgita ta to masifar kawunta ne,,ta sansa tun tana karama Allah yayi masa masifa da fadan tsiya."sanin halinsa yasa ta fito a tsorace har tana batun cire babban yatsan kafarta,kafin tayi magana taji saukar mari sai da taga wuta daga hannu yyi xai kara sauke mata wani Marin yaji an hankadasa gefe Allah yaso sa ya dafa bango ya xube a kasa yana sakin salati..........da balai da masifa ya dago yana kallon wane arnen ne yay masa wannan danyen aikin sukayi ido biyu da kabeer Wanda ya xaro ya'r karamar wuka a kugunsa,yayo kan kawu balele yana shako masa wuya,.tarin axaba ya soma saki dakyar ya banbari hannun kabir a wayunsa.
"Don ubanka ni kake kamawa wuya kabeer??"ni mahaifinka.?''kawu balele ya fada yana tsare kabir din da ido ,kara shakosa kabir yayi yana hadasa da bango wukar hannunsa ya dorawa kawu balele .nan take wandon kawu balele ya cika da iska.........Baba !" Baba!""baban."ehhhh na'am ya fada a mugun tsorace .sau nawa na kira sunan ka."shaye da toka kawu balele ke fadin sau ukku mana."sau nawa xanyiwa kowa kashedi akan yarinyyar nan?"Ya fada cikin maye da alamar baya cikin hayacinsa,tari kawu balale yaso mayi A tsorace nooriyah ta rike hannun kabeer pls yah kabeer ta fada hawaye na Rolling akan face dinta sakin kawu yayi yana riko hannunta,kwace hannun tayi tana goge hawayen idonta.Ya tsani ganin wannnan fuskar da kuka ,juyawa yayi yabar mata dakin batareda ya kara magana ba.
***
Sautin talkamin ta masu kama da tangaran su ya sanar dasu xuwanta,kowace sautin tafiar Areefa mansoor na buga xuciyar Aliyu waxeer .bai San ya xai fuskanci Areefa mansoor ba farhaan yana kallon yarda Aliyu ke hada xufa .kamshin turaren da yaji ya sanar dashi xuwanta da sauri ya daga kansa yana kallonta ,Dinkin Riga da skirt ne ajikinta na atamfa Wanda ya kama jikinta sosai.............tayi kyau tamkar wacce xata shiga sarauniyyar gasar kyau ta dunia,kallonsa Farhaan yyi sai yaga hankalinsa yana kan Areefa mansoor ,mikewa tsaye farhaan yyi agaban Areefa mansoor ya kame gamida bata salute ."sannu da xuwa Mrs.Areefa Aliyu waxeer,Ya fada batareda ya dauke hannunsa ba.ta wara ido tana sakin murmushi jin an kirata da sunan da tafi kauna a dunia,ta rausayar da kai tana juya yan kananun idanunta.farhaan ya saki daria ,ta xauna kusa ga Aliyu ta langabe kai tana masa kallon so.murmushi ya saki gamida riko hannunta yana murxawa cikin sanyin murya yake fadin kinyi kyau fiye da koda yaushe."...........Fisge hannun ta tayi tana harararsa take fadin bbu wani can tunda ka manta dani farhaan ya fini."ta karasa maganar shaye da toka,
Farhaan ya karbe xancen yana fadin wani nan ae ban isa ba,tana hararar farhaan take fadin bbu wani ae ina ganin Ku Ku biyu nasan akwai magana."ta fada tana kallonsu,
Yarda farhaan keyi mata bayani ko fahimta batayi so kawai take yakai karshe,tuni hawaye suka fara Rolling akan farar fuskarta wacce taji make up .Yarda Aliyu yaga ta rude yarike hannayenta yana fadin Relax Areefa mansoor.........."Ya fada da wani irin tone a muryarsa ,ta fisge hannunta tana matsawa kusa garesa cikin shesshekar kuka take fadin taya ya??wannan wane irin Aure ne."Yarda jikinta ke mugun rawa yasa Aliyu sakata duka acikin jikinsa .Ahankali ta kwantar da kanta cikin jikinsa.tana shesshekar kuka take fadin Aliyu please karka yimin haka ,kace wasa farhaan yake ahankali ya xagaye hannayensa da kugunta da sexy voice dinsa yake fadin open ur eye's Areefa mansoor??Ya fada da wani irin tone ta bude ido tana kallonsa ya rike hannayenta ya saki murmushin karfin hali,anan ya warware mata matsalar farhaan,wani irin kallo take masa gamida mikewa tsaye Ahankali taji jiri na kwasarta har ta daina ganin komai da kowa.nan take ta xube a hannun Aliyu waxeer sumammiya ,cikin tashin hankali yake kwala mata kira gaba daya ya gigice .kusan minti goma sha biyar sun samu Areefar ta farfado tareda taimakon Yayarta Aunty Siddiqa ,farhaan mota ya koma yabar Aliyu da Areefa ,cikin taushin murya Aliyu ya riko hannunta."kin San kece maccen da nake so a dunia Areefa taimakon besty xamuyi bakiga yarda yake sonta bane,,
I'm Gone Haidar!!"
Tayi maganar cikin sanyi murya ,
'gone where??".......Ya fada yana tsareta da ido .
Egypt....ya wara ido yana fadin har hutun ya kare,bata kallesa ba ta mike ta fara tafia yasha gabanta yana fadin."Areefa wannan wane irin wulakanci ne bamu gama magana ba,wani irin kallo take masa ta daga waya ta kira sufyan mansoor a waya yyi mata booking first flight xuwa Egypt.duk da she's not sure xata samu ,,nan ta wuce Aliyu bude da baki.
PAID BOOK#
ASMY#❤️
Haske Writer's Association #
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: *_Waminal Hoob_* 4
_Asmy b Aliyu_
Kawu balele na parking motarsa ,motar Aliyu waxeer na tsayawa.saurin fitowa Aliyu yyi ya mikawa kawu balele Hannu sukayi musaba ha.Baba idan bbu damuwa Dan Allah inada magana."sai da kawu balele ya karewa motar kallo yaga motar ta manya ce sa'annan ya saki fuska ,da kansa ya budewa kawu balele front side ya xauna .wani irin kamshi da sanyi A/c ya xiyarci hancin kawu balele ,masu kudi najin ddinsu Allah ka kaimu ga wannan ddin kafin rai yyi halinsa ,Allah karka kasheni yanxu sai naxama daya daga cikin masu kudin garin nan."Ya fada yana wani murxa kunnensa,
"Baba Auren Yarka nakeso kabani nooriyah !!"" Jin maganar kawu balele yyi daga sama,kan wannan maganar xaka sakani a motarka,to bude min na fita nayi mata miji."kawu balele ya fada shaye da toka.
Yana kokarin fita daga motar ,
Da wani irin yanayi Aliyu waxeer ya juyo ya xubawa kawu balele fararen idanunsa.xan siya maka gida xan baka irin wannan motar guda biyar inhar xaka auramin nooriyah."nan take kawu balele Ya rude ya cakumo hannun Aliyu waxeer yake fadin Yaro da gaske kake Dan Allah."Aliyu ya daga kafada yake fadin Aliyu waxeer baya magana biyu......
"Ko yau kake son Aurenta xan baka ,dama yar kanwata ce tun tana karama take hannuna marainiya ce Babanta mutunen Sudan ne, har ya komawa Allah bamu san dangin sa ba.Kasuwanci ya kawosa anan ya hadu da kanwata." Amma sai dai wani hanxari ba gudu ba,inada wani yaro Wanda ke sonta nayi masa alkwarin xan aura masa ita."nasan idan yaji lahira xai kaini bayada imani."nan kawu balele ya shaidawa Aliyu halin Kabir ,Aliyu yayi murmushi yake fadin xan saka sojoji suka maminshi makarantar gyara hali xan kaisa ,xakayi Alfahari da Rayuwar kabir nan gaba."
Rafar dubu Dari Aliyu waxeer ya damkawa kawu balele yana fadin gobe xaa xo nema min Auren nooriyah ,bana son Auren ya dauki lokaci sai ranar da aka dauramin aure da nooriyah xan cika maka alkawarin da na dauka ,jiki na rawa kawu balele ya fito daga mota yama kasa baiwa Aliyu amsa sai famar daga masa hannu yake yana bude baki.Dan ganin yake Aliyu na iya kwace kudin,
Motarsa ya koma ya xauna.ya shiga buda kudin yana sakin ihu Ahankali yana fadin"kudi !kudi!kudi!"duk yabi ya rude sai xufa yake hadawa.......Acikin motar yyi masu boye na musamman sa'anan ya fito ya nufi cikin gidan sa yana wani sakin blushing sai fadin "Yake na kusa xama Alhaji balele har naga yarda kofar gidan nan xai cika da yan maula."A tsakar gida ya tsaya yana kwalawa Adama Kira ,yau kuma dakin bakonka ne da baxaka iya shigowa ba." banda lokacin fitowa ina lissafin cinakin da nayi.
"Aike kinji tsiyarki duk lokacin da mutum keso ya fada maki abun Alkhairin da ya samesa ,ke kuma lokacin kike jin naki Rashin mutunci ya fada yana shigowa daga cikin dakin,bbu komai a dakin sai katuwar katifa da sauran tarkace na mata.
A bisa katifar yyiwa kansa masauqi ya dauki kafa daya ya Dora kan daya,yana yiwa adama din wani irin kallo..............Tsoki ta kara bugawa kafadi abunda ke tafe dakai Dan Allah ka tashi kabani wuri."Dan wlhi yau ddin bakin ka baxaiyi tasiri araina ba,ko kwandala baxakaci acikin kudin nan ba." Ta fada tana kara boye sauran kudadenta acikin xani ,wani kallon raini yake mata cikin daga harshe yake fadin"ni xakiyiwa biyayya ko kya tsira na siya maki buhun shinkafa,,baki wangalau adama ta saki tana kallonsa,ganin tana masa kallon shasha yasa ya Ciro kudi a Aljihun sa yan dubu-dubu guda goma sabi dal"Ya watsa kan jikinta ,ki kara da wannan ki sayi koda itace ne."wawurar kudin tayi tamkar mahaukaciyya ta soma hadasu jiki na Rawa tana yiwa kawu balele wani irin kallo,bata samu magana ba sai da ta hadasu waje daya ta shiga juya kudin a hannunta,idan ma da wasa kake wlhi naci waya'nnan kudin baxan dawo dasu ba".Dama ina binka bashi har na dubu biyu da dari biyar, ta fada tana tura kudin duka cikin rigarta,daria Kawu balele ya saki yana buga kafa,dadina dake Adama a wajen kudi bakida imani kafura kike xama inhar xaki samu kudi."ba wannan ba bude kunnenki na baki labari ,amma kafin nan Dan xubomin Abinci ya fada yana wani kara gyara xama,shaye da toka take fadin da xaka fita uban me kabar min nida Yara'",ko kabir din dake ajewa Dan bakar yarinyyar can mai siffar mayu uban komai yau bai bada ba,bana dashi nima kadan na aje nasa a bakina"........Ta fada tana jawo kwanon wake da shinkafa xuwa gabanta ,xama yayi kawu balele a kusa daita ya xura hannunsa,tsaki ta shiga buga masa tana hararar sa.Bbu dai kowa a gidan nan kou." Dan bana son baki labari kabir na gidan nan,,tun safe da ya fita bai dawo ba ,ita kuma wannan mai kama da Aljannun na aiketa kasuwa ta auno min shinkafa su tariq kuma sun fita makota."ajiar xuciya ya shiga saukewa nan ya soma bata labarin yarda sukayi da Aliyu waxeer,maimakon yaga Adama tayi farin ciki sai yaga ta shiga yimasa wani irin kallo cike da bakin ciki take fadin"wannan bakar yarinyyar xaka aurawa mai kudi har haka,,ita kuma safiyar ubanwa kakeso ya Aureta.???''ta fada cike da jin xafin sa,
Cike da mmki kawu balale ke fadin duka-duka safiyar nawa take shekara goma sha daya kike tunanin nayi mata Aure."Uban mene bata dashi na halitta ajikinta,
Bakaga harta fi wannan bakar yarinyyar jiki ba,
Ita kuma gatanan kullum kamar takarda.'karma ka fara wannan ganganci bbu ruwana wlhi Idan kabir Yaji kasheka xaiyi wlhi."ta fada tana bar masa dakin duka,
Xufa kawu balele kawai yake hadawa yasan halin Adama xata iya fadawa kabir shaidaniyace,
Mafita kawai xai nema lalubo yar karamar wayarsa yyi daga aljihunsa wacce tagama mannewa da bakin salatif ,neman wayar Aliyu waxeer ya shigayi kara ya shaida masa matarsa xata kawo matsala ,gara su gama da matsalar kabir ,tashi yyi ya kakkabe Rigarsa yabar gidan Adama tabisa da kallon takaici tana fadin"wawa kawai in banda wawanci ga yar cikin ka agabanka ,amma kana kokarin nemowa yar da bata kaba Hutu da jin ddi inhar ina Raye ni Adama matar balele nooriyah bata isa tayi Aure a gidan Hutu ba wlhi ,kenan bakin nata ma xaa daina ganin muninta gogewa xatayi fatarta tayi kyau."to ba a gidan nan ba wlhi,muna nan daita anan xata mutu,ko kabir da xai aureta bai isa ya kaita wani waje daban ba ga gidan ubansa."........haka ta rika mita ita kadai a tsakar gida.
***
Ahmad waxeer shine Asalin mahaifinsa Dan kasuwane ,haka babban Dan siyasa ne.Ya Gina asibitoci daban-daban A gida nigeria harma a wajen Nigeria haka ya mallaki manyyan manyyan company's da gidajen man fetur masu suna( waxeer) ,yabar masu dukia mai tarin yawa kafin yabar dunia matar Auren sa daya ,da yayan su ukku hajia Maryam itace mahaifiyarsu Asalin bafulatana CE Ibrahim waxeer shine babban yaron su .Wanda suke kira da Khalil sai Aliyu waxeer mai bimasa,sai kuma Auta Fatima batool ,basu San wani Abu waishi rashi ba a dunia dukan su koda mahaifinsu yabar dunia cikin gata suke ,har yanxu cikinsa suke sabida mahaifiyarsu ta tsaya masu ,haka suna tsaye akan dukiyar mahaifinsu bbu Abunda ya canja saima daukaka ta karayi ,tun tasowarsa yake matukar sha'awar tukin jirgi a rayuwarsa ,tare da taimakon Mahaifiyarsa da yayansa ya cika burinsa na xama pilot .lokaci daya ya xama millionaire ,haka duk magazine din da xaa buga ana maganar Dukiar Aliyu waxeer ne da aikinsa,bbu inda sunan sa baiyi fice a kasar nan ba tamkar mahaifinsa har ma yafi mahaifinsa suna.yana daya daga cikin Abunda yasa baya shiga cikin taron mutane ,
Ganin yarda Ammah ta xuba masa ido yyi saurin sauke kansa kasa,wani irin murmushi Ammah ke saki tana fadin"finally yarona xaiyi hankali kwanan nan."da sauri Aliyu ya dago yana kallon Ammah yana hade rai yake fadin"Ammah Dama can bani da hankali ne."bai cika ba sai ynxu xai cika,
"Munyi magana da Baffanku Khalil waxeer sai jibi xai iso kara su tafi agama magana ,bikin abarsa nan da 1 month haka akwai shirye-shiryen da xanyi."da Sauri ya katse Ammah yana fadin"No Ammah bafa wani biki xaayi ba kawai Aure xaa daura ta tare shike nan,bana son mutane su San nayi Aure kin San social media."da mmki Ammah ke kallonsa ,ganin taki cewa komai yasan bata karbi xancen ba .Ya rasa ta yarda xaiyiwa Ammah bayani yasan yarda aka kashe kudi ga Auren Khalil waxeer haka bikin ya kama yawo a dunia ,shikuma baxai iya fitowa da wannan yarinyyar a dunia ba a matsayin matarsa ae sai a raina matsayinsa."jiki sabule yabar parlon yana fita kiran kawu balele na shigowa a wayarsa ,tsoki yaja farhaan ya hadasa da ciwon kai,harta tsinke bai daga ba.kiran captain bilal ya shigo a karo na biyu dagawa yyi captain bilal na fada masa sunyi nasarar kama kabir ,godia ya masu yace xuwa anjima kadan xai samesa barak su tatauna matsalar kabir din.da haka ya nufi part dinsa,yana Neman layin farhaan....
PAID BOOK
ASMY#❤️
Haske Writer's Association #
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: _*Waminal Hoob*_ 5.....
_Asmy b Aliyu_
"Taya kakeso na fahimtar da Ammah duk bakai ka jawo mana wannan Rigimar ba ." yarinyya tamkar manyya kabi ka makale mata nima kana so ka sakani a rikicinku,nidai baxan iya hada fuskata da wannan bakar yarinyyar ba koda pics ayi mana ." kasan yarda xaka fahimtar da Ammah nagama magana." Aliyu waxeer ya fada yana barin farhaan shagari a wajen tsaye,shidai Inhar Aliyu waxeer ya amince xai auri noory dinsa baida matsala.Ya tabbata koda shekara Goma nooriyah xatayi da Auren Aliyu ,Aliyu waxeer baxai taba cin Amanarsa ba Dan yasan kaunarsu mai girma ce,
Washe gari Aliyu da kawu balele suka gama tsara komai har daukarsa Aliyu yyi ya kaisa inda Kabir yake yaga yarda ake kula dashi,har haske yyi na kwana daya.matsalarsa Adama har yau taki amincewa akan maganar Auren Aliyu da nooriyah shima kawu balelen da yake Dan masifa ne, sai ya baiwa banxa ajiyarta ya cigaba da hidimomin gabansa.itama Adama anata bangare tana ta kiran layin Kabir amma a kashe gashi bai kwana a gida ba,shi ya kara daga hankalinta da safe har Marin nooriyah tayi .Haka ta shige daki taci kukanta ,ga kawu ya fada mata masu Neman Aurenta xasu xo ,
Ta dauka ko maganar Aurenta xaayi da Kabir duk tabi ta daga hankali ta ,tana ta kiran wayar Farhaan tun safe a kashe............haka tayi taxama a daki,
Sai bayan La'asar kawu balele yasa yara suka rinka shigowa da buhuhuwan shinkafa da kayan Abinci da lemukka da suka cika Dan karamin tsakar gidan su ,Nooriyah ya shiga kwalawa kira da sauri ta fito tana durkusawa a gabansa ,dagota yayi yana fadin"tashi tsaye yar Albarka Leda baka ya bude ya fiddo rafar kudi yan dubu-dubu kwara biyu yace ga sadakin ki nooriyah Allah yay maki Albarka. nan da kwanakki kalilan xakiyi bankwana da Rayuwar talauci."Gasu naira dubu Dari biyu ne, nayi alkawari xan baki kudinki ranar da xan kaiki gidan Aurenki."da mugun sauri ta dago tana kallonsa gabanta na faduwa idonta na cika da hawaye lokaci daya ,cikin rawar murya take fadin Aure kuma kawu dawa??"daria kawu yayi yana fadin"ke kwantar da hankalinki ba siyar dake xaayi ba,wani yarone mai kirki xaaya aureki ae yace kin San sa,sunan sa Aliyu."Kawu balele ya fada cike da jin ddi ,maimaita sunan ta shigayi juyawa tayi ta koma daki jikinta na rawa hawaye na xubar mata take kara gwada kiran farhaan ."karkayi min haka Dan Allah farhaan karka hadani da wannan mutunen kar mu fara wannan wasar da baxamu iya karasata ba.cikin sa'a wayar farhaan din ta shiga dama tana da naira talatin da biyar a waya tasan xasu isheta...........noory !''taji ya fada cikin sanyi murya ,tana jin yarda muryarsa ke narka mata xucia .cikin kuka take fadin"plz farhaan karkayi haka Dan Allah ,kaxo yanxu gida akwai matsala ."ta fada tana fashe masa da wani irin kuka mai cin rai,xubewa tayi a kasa tasa hannu tana toshe bakinta kar kukan Ya fita,
****
Tunani na a kullum ya xaayi watarana na wayi gari bbu kai atare dani ,shiyasa nake addu'a A kullum allah yasa na rigaka mutuwa Farhaan, ina sonka ina tsananin sonka son da ban taba yiwa wani a dunia ba,Kaine mutun na farko da ka nunamin gata da soyayya a dunia ,Dan Allah karkayi haka karka bari Aliyu waxeer ya aureni nayi alkawarin xan jiraka koda shekara nawane farhaan."Ta fada hawaye na xubar mata ,harde hannu yayi a kirjinsa yana kallonta .nooriyah idan soyayya birni CE to ki tabbata ke kike mulki a wannan birnin,tana girgixa kai take fadin acikin soyayya son kan da kanuna shine bajintarka ,cikakken masoyi shi xai kauda kansa daga hawayen da kowa xaiyi Dan ya xauna da masoyinsa,pls nooriyah kidaina yimin gori wannan itace kawai mafitar mu."Ae dole nayi maka gori karasa Wanda xaka hadani Aure dashi Sai Aliyu waxeer ,kasan xaman mu baxai yuyuba.idan ya nemi ya wulakanta ni baxan barsa ba wlhi."daria Farhaan yayi ae baxai ma fara ba ,kema Dan Baku fahimci juna bane Aliyu yana da saukin kai ,saima kin xauna dashi keda kanki xaki bani labari shaye da toka da turo baki take fadin "Ae dama nasan kafi son wannan Jan kosan akaina,wara ido farhaan yyi yana daria sosai yake fadin" bbu ruwana idan yaji kina kiransa da wannan sunan,yaji mana nima bakaji yafi karfin ya kirani da sunana ba ,saboda girman kai"Bakar fata kuma ina Alfahari da sifar da Allah yayi ni"...........sun dde suna magana daga nan sukayi sallama tamkar karsu rabu koba komai cikin damuwarta kashi goma farhaan ya tafi da kashi shidda.shirye-shiryen Auren Aliyu waxeer Ammah ta shigayi dama a kwanakkin baya,ta fara hada lefensa ta dakatar sabida taga Aliyun kamar bai shirya Aure lokacin ba,,sai yawo yake yimata da hankali shiyasa ta dauki itama Al'amarin ta watsar,kayan da ta ajey xasu dauki saiti daya .Dan Haka ta kira kanwarta dake xaune a maley Dan Neman shawarata ,in saiti daya din yyi idan kuma karawa xaayi sai a kara."Ammah a kara mana Aliyu waxeer ne fah."ko Auren Khalil waxeer saiti biyu akayi ,mexai hana ynxu shi ayi masa saiti hudu,xaki kasheni da raina kenan Hannatu."toh ki kira ango ya bada kudin hada saiti hudu ae yana da kudi,daria hannatu tayi haba Ammah kamar Aliyu ya xaayi ace saiti biyu ,xan mashi magana ae."kamar Areefa mansoor wacce yake ji daita ae sai saiti hudu ,ammah ta sauke ajiyar xuciya tana fadin"Bafa Areefa bace ya canja,da mugun shock Hajia hannatu ke fadin"meyasa Ammah??fasawa yayi fada sukayi ne."Lokaci daya hannatun ta jerowa Ammah tambayoyin ,
Nima ban sanni ba Hannatu haka na tsinci xancen har araina bana son wannan Yarinyyar Areefa ,sabida idonta ya gama budewa dayawa .burina A kullum Aliyu ya samu matar Aure marar son abun dunia haka Marar kyale-kyale Wanda wayewarta ya xama na addinin islama ne,,wannan lokacin ina ji ajikina Allah ya karbamin Addu'ata duk da banga matar Aliyun ba xuciyana ya natsu da Auren."ajiyar xuciya hannatu ta sauke , kina ganin Aliyun xai iya Auren macce wacce bata wayeba marar kyale-kyale duba da yarda Aliyun yake.sun dde suna tattauna matsalar Aliyu ,sa'anan sukayi sallama.........Bangaren Aliyu kuma komai bai fara shiryawa ba tamkar ba Auren sa xaayi ba ,farhaan ne gaba wajen komai ko dinkunan biki duka farhaan ne yyi da Aljihunsa ,Wanda sai da ya girgixa .Aliyu gefe ya koma yana kallon yarda farhaan ke rawar jiki da Auren.....
***
Ta cakumi kwalar rigarsa tana masa tsinannen kallo take fadin"Na rantse da Allah yau sai ka fadamin wurin da ka kaimin Yaro."Adama ta fada cike da masifa,kawu balele ya hankadata yana fadin"Ashe bakida kirki har haka Adama ki kalli tsabar idona ki rika fadamin na fito maki da Yaro ni Aljani ne da xan boye maki Yaro."waya sani ko kafi fiye da haka yau kwana biyar Kabir bai tako kafarsa a gidan nan ba."Bai tabayin haka ba,duk lalacewarsa kuwa.........Yarda naga baka wani maida hankali a batan nasa ba nasan da saka hannunka,toh wlhi baxan yarda ba polisawa xan dauko maka su tafi dakai,salati kawu balele ya shiga xabgawa yana fadin"Yanxu ni balele ni xaki daukowa polisawa akan batan Kabir wai adama na tambayeki ,ni Kabir ba Dana bane halama."Yyi maganar so pissed up itama sounding so very harsh take fadin"Dan kane amma xaka iya kaisa wajen masu shan jini ,Dan kasamu kudi yarda na sanka tamkar yunwar cikina xaka iyayin komai akan kudi........."ni ban ma yarda da Wanda yaxo Neman yarka Aure ba wlhi wayasani koda shi ka hada baki kabasa Kabir Dan ya baka kudaden da ka fadamin haka ka dauki waccan bakar yarinyyar kabasa Auren ta ,baa dde ba sai ga motar polisawa har kofar gida dama Adama ta kira abokanin Kabir ta shaida masu,shahoo ne yyi sallama.da sauri adama ta sakesa tayi wurinsa tana fadin"shahoo kun taho da polisawa ,gasu a kofar gida Ummah."kai Baba wuce muje.".......gidan ubanwa xaku kaini ",idan mukaje xaka gani idan baka fitomana da oganmu ba wlhi tallahi sai Mun illataka mu illata banxa.!" Haka shahoo yaja rigar kawu balele har kofar gida,akwai wani kurtu tsaye awaje shi ya sankame hannayensa da sarqa akasa sa a mota.
"Shahoo da Adama suka bi motar polisawa a baya cikin adaidaita sawu.cike da tashin hankali nooriyah ta shiga Neman layin Farhaan,dama sunyi magana da kawu Kabir an kaisa makarantar gyara hali.hankalita ya kwanta sosai da hakan dama a kullum tana addu'a Allah ya kawo lokacin da Rayuwar Kabir xata canja duka.,,cikin rawar murya Nooriyah ta shigayi masa bayani yan sanda sun tafi da kawu balele.;bari na nemo Aliyu ya fada yana datse kiranta,
" Amma kasan yanxu shigana police station wata matasalar CE babba yan jarida xasu iya samuna a wajen,bara na kira commissioner a waya kafin nan ka kira kawu kaji a wane station ne,da sauri farhaan ya kira wayar kawu kusan kira ukku baa daga ba sai a na hudun wani officer ya daga,nan sukayi magana da farhaan cikin natsuwa ya fada masu a station din da case din yake,Farhaan yace yana xuwa nan da minti Talatin ,da yake wajen akwai nisa daga wajen da yake.
Cikin kankanin lokaci farhaan ya iso dama su Adama suna a reception kawune kawai aka tura cikin cell ,kai tsaye office din d.p.o.ya nufa ,kusan minti goma ya shafe ciki,
Sai ga wani officer ya leko ya kirasu Adama .Nan d.p.o.ya fada masu ba sace Kabir akayi ba,taimakonsa akayi."wane arnen ne ya shimfida maka wannan karyar,yau ni Adama naga abunda ya isheni."taimakon ubanwa kayi masa an fada maka yarona musakine da xaka taimakesa,ko kuma Jan duwawu yake."Adama ta karasa xancen cike da masifa da balai,
Dakyar d.p.o.ya lankwasata ,Ya fada mata xasu dauketa su kaita inda yaronta yake ,
Amma da sharadi idan tayiwa mutane hayaniya na lahira sai ya fita jin ddi hannun sojoji yake ba yan sanda ba."tun awurin shahoo ya sare, yana hada xufa yake fadin"Ummah ni na wuce dama innata na kwance gadon Asibiti yanxu hakama can na nufa,
Baki bude ta saki tana kallon shahoo ganin irin karyar da ya sharara...........Itada kawu Farhaan ya daukesu a motarsa ,haka cikin su bbu Wanda ya shaida fuskar farhaan din sabida toshewar basira ,
Yarda taga ana kula da Kabir sai taji jikinta yyi wani irin sanyi,amma duk da haka xuciyarta ko gixau baiyi ba.baxata bar kawu da nooriyyah ba har sai sun amsa mummunan hukunci a hannunta ,Kabir ya kamo hannun Adama yana fadin"Ya kk Ummah nayi kewarki ya nooriyah hop bakya dukanta bakya sakata debo Ruwa a bakin titi cikin maxa,kina Bata Abinci kuwa"kinga yarda Rayuwa ta juyani ko Ummah,Ashe ba karamin so Allah yake yimin da Rahamar sa ba.nagodewa duk Wanda ya canja min rayuwata har haka,ki kularmin da kanki da nooriyyah nasan idan na fito taga yarda na xama xatayi farin ciki da hakan......."Adama xatayi magana akaja Kabir akace lokaci yyi sai wani lokacin kuma.duka jiki sanyaye adama ta dawo gida ta kasa koda kallon Kawu balele...
****
Janta ta shigayi Haka tana kai mata mari ta koina ,har tayi narasar fasa mata baki.kawu balele yana mata magana ko takansa bata biba. haka ta shiga janta tana fadin"wlhi tallahi !"xama na da yarinyyar nan cikin gidan nan ya kare tunda Kabir yabar gidan nan dolene itama tabar gidan nan,
"Idan tabar gidan nan ina kikeso ta tafi??Anya Adama kina da imani kuwa,wani banxa kallo
ta shiga watsa masa fadin take kai baka isa ka fadamin yarda xan tafiar da gidana ba,bbu ko kwandalar ka acikin siyen gidan nan kaima Xaman bulus kake acikinsa,Dan Haka ka rufemin baki ."xubewa nooriyah tayi akasa ta game hannayenta hawayen na xubar mata ta shiga Rokon Adama akan tayi hakuri ,wani hauri takai mata cike da jin haushin ta take fadin yau duk sanyi kalamanki baxasu narkar da wannan xuciyar tawa ba xo kifice min agida don ubanki tun kafin na hada maki jini da majina............" Haka Adama ta shiga Jan nooriyya cike da toxarci kawu na bata hakuri ko kallo bai isheta ba ,tura nooriyah tayi da karfi taje xata fadi tajita a hannun mutum.kyawawan idonta ne suka sauka cikin nashi idon,sanye yake cikin farin yadi Fari kal"mai shara-shara har ana hango farar shimin dake jikinsa ,ta lura yana son manyan kaya kuma farare sabanin farhaan dinta da baya shiri da manyan kayan.da sauri ya saketa ,
Salati Ammah ta shigayi tana fadin"baiwar Allah lfy kuwa??wani kallon banxa Adama keyiwa Ammah taja tsaki gamida shigewarta gida ta kalli nooriyah tana rike da kofa take fadin"idan kika kara tako kafarki cikin gidan nan wlhi tallahi sai na maki illah sai na karawa shegiyar fuskar nan taki baki."Adama ta fada tana buga kofar tabar Ammah tsaye da mugun mmkinta ,dama ita tace Aliyu ya kawota gidan su Nooriyah ta sanar da iyayen nooriyah yarda suke gudanar da bikinsu inhar Xaa auri yarinyya acikin xuri'ar waxeer ,uwar miji xata dauki amaryar na tsawon sati daya a bata kebantaccen daki na musamman ayi mata gyaran jiki haka idan anfara hidimar biki.Ranar salalle da amarya da ango lokaci daya xaa saka su lalle a gidan su Ango.wannan Al'adar xuri'ar waxeer CE.........da sauri kawu balele ya nufi Aliyu waxeer sai hada xufa yake yana fadawa Aliyu abunda yasa Adama tayi haka,wani irin tausayi da son nooriyah suka shiga xuciyar Ammah lokaci daya,Bata taba ganin matar da tadace Da Aliyu waxeer a dunia ba irin Nooriyah.
Mami ta kama hannun Nooriyah ta dago fuskarta duka tana kare mata kallo,Nooriyah tana da wani irin sanyayyen kyau Wanda a boye yake.tana da cikakkar fuska mai dauke da cikar xati da kamala haka hancinta dogone sosai tana da matsakaitan labba,tana da manyyan idanu farere kyal."sai dai nooriyyar bakace sosai ,Wanda harda wahala ya kara sakata baki.nan gaba idan ta goge bakinta mai kyau ne. "Wani irin murmushi Ammah ke saki,batareda Ammah tace komai ba ta juya ta nufi mota da nooriyah da kanta ta bude mata gaban motar tace ta xauna tana xuwa,a tsorace nooriyah take.nan Ammah ta dawo tana gabatar da kanta a wajen kawu balele,
Haka kawu balele ya shiga fara'a tamkar yayi mata sujada .wani irin haushinsa Aliyu waxeer keji." Ina ganin na dauke nooriyah daga yanxu har xuwa lokacin da xaa daura Aure."Ranar daurin Aure kaxo da waliyan nooriyya ,karka damu daga yanxu nan xan cigaba da kula da Rayuwar nooriyah har karshen Numfashi na bbu abunda xai kara samunta."Ammah ta karasa maganar ta juya tana barin wurin ,cike da tausayin nooriyah din..
"Me Ammah keyi hakane??Aliyu waxeer ya fada yana hargitsa sumar kansa,xamuyi waya kawai ya iya fadawa kawu ya juya ya nufi motarsa cikin takunsa mai daukar hankali ,kallo kawu balele yabisu dashi sai yaji wani iri karo na farko acikin rayuwarsu da xaiyi nisa da nooriyah samun kansa yyi da daga mata hannu kwallah na cika idonsa,itama nooriyah daga masa hannu ta shigayi hawaye na xubar mata.tausayin yarinyyar ya kara dagula xuciyar Ammah.dukansu xaman shuru suka xauna a mota ,ganin Ammah har lokacin taki magana yasa Aliyu yaji duka bbu ddi,yasan xai sha tambayoyi awajenta duk farhaan shagari shiya saka sa a wannan halin yana xaman xaman sa.
daga kanta tayi tana kallon cikin unguwar ,Tamkar a kasar turai Dan kyau wasu irin tangama tangamen get ne awajen Wanda bata taba ganin kalar su ba,
Kusan gidaje hudu ne Jere a wajen masu kalar get iri daya,na karshen taga motar Aliyu ta nufa. Horn ya shiga dannawa da sauri aka wangale katoton get din ajikin get din anyi wani Rubutu akai( AHMAD WAXEER MANSION)wara ido nooriyah tayi tana kallon Aljannar dunia tsoki Aliyu waxeer ya buga karo na farko,yana wani bin nooriyah da harara Dan ya manta suna tare da Ammah,sauti kasa -kasa yake fadin ki kama kanki yar kauye kawai."da sauri ya dauke kansa tamkar bashi yyi magana ba,maimakon Taji haushi sai ta saki murmushi gamida dauke kai,yana gama parking yyi saurin fitowa ya budewa Ammah motar ita kuma ta nufi side din nooriyah da Sauri ta bude mata.cike da jin kunya nooriyah ta sunkuyar da kanta haka kurum ta samu kanta da jin kunyar Ammah.tsaye Aliyu yayi yana kallonsu,hanyar Entrance din shiga gidan suka nufa,da sauri yabi bayansu yana son yin magana da nooriyah sai dai da alamar Ammah ta rufe kowace kofa.Dan gyaran murya yyi Ammah kawai CE ta ta juyo tana kallonsa ,shafa sumar kansa yyi yana fadin"ina son magana daita Ammah."yyi maganar yana wani dauke kai,
Ammah ta girgixa kai tana fadin ba yanxu ba Aliyu waxeer xuwa da Yammah kadawo."tana fadin Haka ta juya rike da hannu nooriyah samun kansa yyi dajin haushin Ammah kan wannan Ya'r bakar xatace ya tafi sai xuwa anjima tamkar wata sarauniya juyawa yyi ya nufi part dinsa.
Baki nooriyah ta saki tana kallon katon falon Ammah sai ta xama tamkar wata sakaryya sabida kallo,xama sukayi acikin Maroon din soofas din da sukayiwa falon kyau,ga fotunan su Aliyu nan jere a falon shidasu Ammah wani shi kadai,
"Jikin ki yana bukatar wanka Nooriyah ya kamata kiyi wanka kici abinci ki huta,anjima Aliyu xai iso kuyi magana." Saukar da kanta kurum kasa tayi tana wasa da dogayen yatsun hannunta.waya Ammah ta dauka ta kira yar aikinta murja wacce xata kai kimanin shekaru talatin da biyar wandda duka yan aikin gidan suna xaune a boys Quartet's sai idan suna aiki suke shigowa part din Ammah.murja itace Babbar yar aikin Ammah duka sauran a karkashinta suke ,Dan ita kadai ke shiga part din Ammah ta gyara mata.
Baa fi minti biyar ba sai ga murja da sauri ta xube agaban Asma'u waxeer ,
"Murja xaki tafi da bakuwar nan dakin baki a hada mata ruwan wanka .ki taimaka har kanta ta wanke ki bata abinci ki xauna tare daita anjima xan kiraki." An gama Hajia xan sa batool tazo maki da kayan da xata saka."da sauri murja ta mike tsaye Nooriyah na biye daita da kallo Ammah tabisu har suka bacewa ganinta.wani irin murmushi Ammah ke saki tana mamaki tana karawa ina kuma Aliyu ya samo wannan yarinyyar ,
Aliyunta ne xai Auri bakar macce kuma Yar tallakawa ??"yaushe tunanin Aliyun ya canja haka,tasan Aliyu tun yana Dan karami yake fadin"shi baya sha'awar bakar macce a tsarin Rayuwarsa fara yakeso kamar shi sabida kaf familyn waxeer farare ne koda yayi Rayuwa cikin yan uwansa babu bakar fata......har yau mmki yaki barin Ammah sai kai da kawo takeyi a tsakiyyar falonta ,Aliyu waxeer ne kawai xai amsa mata dukkanin tambayoyinta.......
****
Aliyu ya akayi haka??badai wannan itace matar da xaka Aura ba."Ammah tayi maganar sounding so very confused.........itace Ammah meya faru batayi bane."Aliyu waxeer ya fada cike da dakewa ,Aliyu inhar tausayin wannan yarinyyar kakeyi karka cuceta Dan Allah ."Akwai hanyar taimako dayawa ,gaba daya ban yarda da wannan Auren ba."Ammah ta fada cike da karaya.
Xufa yaji ya fara hadawa ganin Ammah na Neman ganosa,da sauri yace Ammah inason nooriyah ni ba tausayinta nake ba."Yayi maganar cike da kwarin gwiwa.tsaresa da ido Ammah tayi tana juya ko wace magana tasa,Yaushe ka fara son bakar macce haka gidan tallakawa wacce bata waye ba.??'wannan karon sai da ya girgixa jin tambayar da Ammah tayi masa,xuciyarsa yaji tana tsalle lokaci daya,"I'm going to kill you Farhaan Shagari idan mun hadu ka sakani a matsala." Yyi maganar duka acikin ransa ,wayarsa CE tayi kara da sauri ya Ciro wayar ganin farhaan ne ke kiransa ya mike tsaye yana fadin"Ammah zamu fita da farhaan yana jirana,har ya juya yaji Ammah na fadin"baka Amsa min tambayana ba Aliyu."Jin yyi xuciyarsa na tsananin bugawa da sauri da sauri,
dauriyarsa ya tattaro yana fadin"Haka Allah ya nufa Ammah ,Nooriyah itace Allah yayi xan Aura ta xama uwar Ya'yana.da haka yabar falon har yana hadawa da gudu ,wata irin dariar farin ciki Ammah ke saki fadin Take ."Alhmdullhi na godewa Allah da ya cikamin burina Aliyu xai Auri irin matar da nakeso ,duk da bata xauna da Nooriyyah ba taji aranta tana da hali mai kyau haka xasu xauna da Aliyu lafia....
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: *_Waminal Hoob_* 7...
PAID BOOK
Free page.
_Asmy b Aliyu_
Baki jin hausa ne??"Ya fada sounding so very harsh,malam meye matsalarka da hijab Dina."itama tayi Maganar cike da gajia da al'amarin Aliyun,
Fisgota yyi yana huci yake fadin ni kike fadawa magana.."Kallonsa take a tsorace ganin yarda ya rikota ,kokarin kwatar kanta take Amma ta kasa shaye da toka yake fadin"kin san cikin Rules dinmu bbu gardama karki yimin Rashin kunya ya fada yana saka hannunsa yana cire hijab din jikinta duka,wannan karon riga da skirt ne na material ajikinta kalar pink ,kallo daya yayiwa kayan yasan na batool waxeer ne .Dan ita kadai ke saka ire-iren waya'nnan dinkunan,tsaki yaja sosai kayan gaba daya basuyi masa ba duka sun fito mata da halittar jikinta,ki canja kaya gani a bakin kofa ina jira......."Ya fada yana barin dakin,da kallo tabisa cike da mugun Jin haushinsa,wasu kayan ta shiga dubawa black Abaya ta fidda ta saka gamida Rolling din mayafin akanta samun kanta tayi da fesa turare tana fita sukayi ido biyu dashi,
daure fuska tayi shima Fuska bbu walwala yayi gaba tana binsa a baya.gaba dayan su kallo ya dawo kansu,
Wara ido batool waxeer tayi tana kallon yayan nata ,ina ya samo wannan black beauty din."laylah sai bin Nooriyah take da kallo,har suka karaso cikin dinning Area din.da sauri batool ta karaso gabansu ta kama hannu Nooriyah ,tana murmushi take fadin Yaya ina kasamo wannan kyakkyawar."Yaya itace wacce xaka aura??"Gaskiyya tana da kyau ,batool waxeer ta fada tana wani rungume Nooriyah ,toh saketa haka mana jamata kujuera ta xauna."Ammah ta fada tana kallon Batool din,
Murmushi batool tayi tana jawa Nooriyah seat ta kusa ga Aliyu waxeer,ta russuna cikin girmamawa tana fadin barkar ki da xuwa cikin familyn waxeer."Batool waxeer ta fada sounding so very happy,wani irin Abu ya tsayawa Layla a wuya.sai murmushi take kwakwalowa ,bata san meyasa tun farkon ganinta da Nooriyah taji Bata sonta,har ga Allah tasan tafi Nooriyah komai sai kamar tana ganin kamar ba haka bane,tana son wani ya fada mata Nooriyah tafita komai .kayi serving din matarka ka tambayeta mexa taci."da ido yake bin Ammah da kallo tamkar da wani yare ta fada masa hakan,
dan russunawa yayi murya can kasa yake fadin"tell me mexaki ci??"Kur idon laylah akan su ,sai taga sunyi mata wani irin kyau.har sai taga Aliyun yafi Khalil waxeer iya kula da macce."Abunda xaka ci shi xanci ta fada tana kallonsa,daure fuska yyi ganin ta gama Raina sa.ganin ido akansu yasa baice komai ba ya shiga serving dinsu plate daya yayi masu,sakin baki da ido batool waxeer tayi tana sakin wani irin blushing.bata taba ganin yayanta yana tarairayar macce ba irin yau,ko Areefa Mansoor da yake fadar yana so bai Bata irin wannan kulawar,
Da ido kurum Nooriyah ke binsa me Aliyu waxeer ke nufi??"Yana nufin agaban Ammah xataci Abinci tare dashi,muryar Ammah taji akanta tana fadin"kici Abinci Mana Nooriyah ,ta Yaya xataci Abinci plate daya da Aliyu waxeer".suna hada ido ya wani ware mata ido gamida bude mata hannuwa,duk Abunda suke a idon laylah sai taji gaba daya ta tsani Abincin,wani irin kishin Nooriyah yaxo ya tsaya mata a xuciya ,idan batayi da gaske ba Nooriyyah xata xama best daughter in-law a wajen Ammah ,taga yarda Ammah ke wani rawar kafa akanta....A hankali ta Mike tsaye ,ta subbaci Khalil waxeer gefen kuncinsa tana fada masa ta wuce sashensu kanta nayi mata ciwo,nan ta juya tana yiwa Ammah sai da safe.ita dai Ammah binta kurum take da ido ganin yarda yanayinta ya canja lokaci daya,gefen Nooriyah mamaki take taya Layla xata subbaci Khalil waxeer agaban surukarta?"
Nan laylah ta juya tabar parlon da sassarfa ,shi dae Aliyu cin abincinsa kurum Yake,hakama Khalil waxeer sunaci suna hirar business dinsu,
Ammah itama ta Mike ta koma parlor har lokacin Nooriyyah takicin komai, Khalil ya kalleta yana fadin kici Abinci plz kibar biyewa Aliyu shegen cin tsiyane dashi ,xakiyi aiki sosai a wannan bangaren."da sauri Aliyu ya kalli Khalil waxeer yana dakune fuska.dage gira Khalil yayi yana fadin"na fadi karya ne."Kusan lokaci daya Aliyu da Khalil suka Mike suka bar dinning area din,ya rage daga ita sai batool dama batool ta matsu subar dinning din,ta dawo kusa ga Nooriyah tana murmushi take fadin"Aunty noory taya kika sace xuciyar Yah Aliyu haka?"murmushi kurum Nooriyah tayi taki cewa komai,Haka batool ta shiga janta da labari sama-sama take Bata Amsa,bbu laifi ta Dan sake da batool,sai kusan 10 sukayi sallama da batool kowa ya nufi makwancin sa,washe gari Mai gyaran jiki taxo ta fara yiwa Nooriyah gyara ,kusan kwana 4 Aliyu baisa ta a ido ba gata bangaren farhaan ya damesa ya hadasa vedio call da Nooriyah.Ammah taki basa damar hakan,
Tace baxasu hadu ba sai ranar da xasu hadu wajen sakasa lalle.haka Aliyu yyi xuciya ko parlon Ammah ya daina shigowa,bangaren kayan da Nooriyah xatayi amfani dasu na hidimar biki tayi magana da laylah ta damka komai a hannunta,cike da kosawa da xance laylah ke fadin"Ammah ki samu wani ki basa banda lokaci Kuma duka masu yimin dinkuna basa da Alkawari kar axo asamu matsala."tayi Maganar in I don't care manner.murmushi kurum Ammah tayi tana fadin bbu komai xata samu wani,karshe batool ta damkawa komai ita duka ta xabarwa Nooriyah din kalar dress din da xatayi Amfani dasu,da aka kawo kayan Ammah ta yaba sosai da hakan,acan bangaren laylah kuwa bincike takeyi sosai taya Aliyu waxeer ya yarda xai auri wannan Yar kauye marar wayewa wacce,da alamar batada ilimin boko ko kadan."tasan wannan bashi ne mafarkin Auren Aliyu waxeer ba,tayi ta Kiran lambar Areefa Mansoor a kashe ko xata samu karin bayani akan hakan ,Areefa Mansoor kawarta ce ta sanadiyarta suka hadu da Aliyu waxeer.Yarda tasan Areefa Mansoor haka kawai baxata barwa wata Aliyu waxeer ba.yarda take mafarkin samun sa,tasan akwai dalilin wannan Auren dalilin takeso taji ko Ammah xata daina wannan Rawar kafar Akan Nooriyah.....
ASMY#❤️
Haske Writer's Association#
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: *_Waminal Hoob_* 6.....
PAID BOOK
Free page.
_Asmy b Aliyu_
Murja ta hada mata ruwan wanka ta fito ta samu Nooriyah duk ta takure kanta waje daya,murmushi murja tayi tana fadin ki saki jikin ki Dan Allah."daga kai kurum Nooriyah tayi ,na tayaki wanke kanki ko xaki iya??murja ta fada tana kallon Nooriyah, kitayani bana iya wanke kaina ni daya yana dayawa......tare suka nufi toilet dakyar Nooriyah ta rage kayan jikinta murja ta fiddo mata da sabon towel ta daura ,ganin yawan kan Nooriyah sai da yaso ya firgita murja tana mmki tana karawa duk wannan tulin gashin na mutum dayane,ba laifi bayada wani datti sosai sabida duk Karshen wata farhaan na bata kudin saloon tana shiga wajen wata makociyarsu inya mura tana wanke mata.rabi kawai suka kai murja taji ta gaji ,dakyar suka samu aka gama.murja na xufa tana fadin"kibarsa haka xanyiwa Hajia magana kawai akaiki kiyi saloon.
Wanka murja tabarta tanayi,tana fita batool ta shigo dauke da kaya cikin leda."Aunty murja Ammah bakuwa tayine??''mekika gani Autar Ammah."nagan Ku Anan dakin inhar Ammah ta sa aka kawo bako anan wajen to nasan special ne,ina bakuwar batool ta fada tana bin dakin da kallo.Amsar kayan Murja tayi tana fadin"tana wanka ko xaki jirata.noo xamu fita tareda Aysha waxeer idan na dawo anjima ma gaisa da haka batool tabar dakin da sauri,Alwallah Nooriyah ta dauro Dan ta lura ana gabda sallar xuhur,da taimakon Murja Nooriyah ta busar da kanta da drayer......ga kayanan ki saka inji Hajia bara naje na hado maki Abinci,da haka murja ta nufi kofa.Dan ajiyar xuciya Nooriyah ta sauke farhaan ya sasu a matsala,dakin ta shiga karewa kallo komai na cikin dakin blue black ne har pentin dakin.bbu komai acikin room din sai ltalyn bed da mirror dressing dinsa,sai kuma wardrob dinsa mai gida biyu,da kuma doguwar soofa itama kalar blue black.....dakin yyi matukar yin kyau,ledar da Murja ta ajey mata ta jawo xuwa gabanta tun Kafin ta buda ledar taji tana wani kamshi na musamman,buda ledar tayi ta fidda Turkish Abaya kalar brown,masu wasu irin duwatsu gaban rigar sai Dan karamin mayafin abayar.sai bran da pant suma sabbi dal da kuma ,agurguje ta shiga saka kayan.tana cikin saka kayan aka wani bugu kofar ,ido biyu tayi dashi wani irin ihu ta saki gamida xubewa akasa tana wani kare kirjinta ,shima da sauri ya juya har yana buga kansa ga kofa.wani irin bacin rai ya saukarwa Nooriyah shi wannan mutunen bayada hankali xaya shigowa mutane a haka."kuma ai lokacin haduwarsu baiyi ba,da sauri ta rarumi hijab dinta ta saka.juyawa yyi yana wani hade rai,gamida shigowa cikin dakin duka.karki bada hanyar da Ammah xata gano bbu auren soyayya acikin auren mu,haka karki fadawa kowa yarda Auren nan yake."kibarsa mu ukku kurum yarda muka tsarasa ,juyawa yyi ya nufi kofa batareda ya kara kallon inda taketa ba.......da kallo tabisa ,
Tsaki tayi ta cire hijab din gamida saka doguwar rigar tamkar Dan jikinta akayi rigar tayi kyau sosai acikin kayan.da sallama murja ta shigo dakin dauke da katon tray,mai dauke da cima kala-kala da sauri Nooriyyah ta karbi tray din tana yimata sannu.kallon ta Murja tayi tana fadin"kinga shigowar babana kuwa?da ido Nooriyah tabita Dan bata fahimci xancenta ba,Dan murmushi murja tayi tana fadin Aliyu nake nufi ya shigo ."Ya fadamin Bayaso Hajia tasan ya shigo,,ya shigo har ya tafi.Nooriyah ta fada tana komawa gefen gado ta xauna,ya kuma kin xauna sauko kici abinci.bara na baki waje ,xan dawo anjima murja ta fada tana barin dakin.samun kanta tayi da fadin"nagode Aunty..........murmushi kurum murja tayi gamida ficewa daga dakin duka,
Farar shinkafa ce da stew ,sai dayar cooler mai daukeda farfeson naman Rago,sai katon kwalin five alive.kadan taci abincin kasancewar ba mutum CE mai cin abinci sosai ba,tana idar da sallar axxahar barci ya dauketa akan carpet ba ita ta tashi farkawa ba sai kusan 5....Ahankali ta fara mika ta soma bude idonta tana karanto Addu'ar barci,ido biyu tayi dashi wani irin faduwar gaba ta tsinci kanta dashi,shima kusan hakane awajensa.baisan meyasa duk lokacin da suka hadu daita ba,xuciyarsa xata fara bugawa .baxata daina ba har sai lokacin da yabar wurinta,wani irin irritating look yake watsa mata fuska a daure yake fadin kin watse baki kina barci ,kinji sanyi A/c an samu banxa na baki minti biyar ki shirya farhaan na nemanki ."Ya fada yana bar mata dakin cikin takunsa na kasaita haushi da takaici suka cika xuciyarta lokaci daya,tambayar kanta take tsawon Mintuna nawa yayi yana kallonta ,tsaki tayi ta tsani ganin wannan fuskar tashi mai kama da kosai,haka kurum taji jikinta duka na kamshin turarensa,da dakin ma gaba daya.toilet ta shige ta dauro alwallar la'asar ,
Sai da tayi sallarta cikin natsuwa,tana linka sallayar murja ta turo kofar da sallama.Babana yana ta jirafa ."hijab dinta take kokarin sakawa kalar Ash colour Wanda ya Dan fara tsufa ,da sauri Murja ta karaso gabanta tana fadin"ki Dora mayafin Asama mana,ina ganin xaifi kyau...........wani iri Nooriyah taji aranta karo na farko da xata tsaya a haka gaban mutane ,ko acikin gidan kawu kullum tana sanye da hijab ko barci xatayi.
Da sauri tabi bayan murja,ta godewa Allah da ya kawota da batasan hanyar da xatabi ta koma wurin Ammah ba.
A falon Ammah suka samu Aliyu tsaye yana kaida kawo ,Ammah na xaune cikin soofas.da sauri Aliyu ya karaso gabanta yana fadin"kin kyauta shine kika shanya Aliyu waxeer har haka???"Ya fada sounding so cwt yana yimata wani irin kallo,dauke kai tayi ta isa gaban Ammah ta durkusa tana gaisheda Ammah.da murmushi Ammah ke fadin kin tashi barci jewel?"sannu da tashi ,cike da jin kunya Nooriyah ta daga kai.
Aliyu yana son magana dake kina da lokaci ko sai gobe."cike da takaici Aliyu waxeer ke kallon Ammah.jira yake yaji me Nooriyah din xata fada sai yaji tayi shuru tana wasa da yatsun hannunta,Aliyu kuje karka wahalar daita da yawa.Rabin awa na baka ka dawomin da ya'ta ."Ammah ta fada tana barin su A falo.wani bacin rai ya sauka a xuciyar Aliyu waxeer me Ammah ke nufi??"me ma xai kaisa yawo da wannan bakar Yarinyyar.........tare suka jera suka fice daga cikin parlon suna fita ya nufi part dinsa ita kawai binsa take xuciyarta na bugawa ,batasan meyasa duk lokacin da ta hadu da Aliyu waxeer ba ,xuciyanta tana hanata hutawa daga bugawa.aduk lokacin da suka hadu itada Aliyu waxeer ,batasan meyasa ba.ko farhaan da suke soyayyah batajin bugawar xuciyarta idan suka hadu,sauran kadan tasha kasa wajen kallon haduwar parlon Aliyu waxeer ,idan baxatayi karyaba wannan parlon har yafi na mahaifiyarsa kyau da tsaruwa sai kace akasar turai Dan kyau ,komai na cikin parlon Fari ne Sol"har ta da fentin parlon Fari ne wato Fari shi daine Fav din Aliyu waxeer. Farhaan ne yayi saurin tarota a hannunsa,wara ido tayi tana kallon farhaan shagari cikin kananun kayan da sukayi matuqar karbarsa,
Da sauri Aliyu ya juya xuciyarsa na tsananin bugawa bai kara koda second 1 a wurin ba ya nufi hanyar stair's da ido farhaan yabisa yana sakin murmushi......Da sauri Nooriyah ta kwace kanta a hannun farhaan ,harde hannunsa yyi akan kirji yana binta da wani sanyayen kallo.
Shigen ba karamin kyau yyi mata ba,lumshe ido yyi ya kara budewa akanta.ta Dan turo baki tana fadin baka fadamin xaka xoba.ko awaya."nima Ramawa nayi na shanyaka ,meyasa xaka aikosa kasan bayada kirki."ta karasa maganar tana wani hade rai ,hade hannu yyi alamar yana Neman Afuwa xama sukayi acikin fararen soofas din da suka kayata parlon na Aliyu,ya dafe kansa dake yimasa ciwo tun Daren jia sabida maminsa tayi Rantsuwa ayau xaibar kasar nan ."Ba haka yaso ba sai yaga Auren Noory dinsa da Aliyu ya tabbata ,jirgin karfe 6 xanbi xuwa cyprus....... Wani mummunan faduwa gabanta yyi har hawaye sun cika idonta cikin rawar murya take fadin"Baxa ka bari sai an daura auren ba??"ta fada hawaye na sauka a fuskarta ,kuka kuma noory??''bafa mutuwa zanyi ba,xan dawo nan da watanni shidda Kafin mu idar da gamawa gabaki daya,ina jin tsoron duniar nan Farhaan .shigowarka cikin Rayuwata Alkhairi ne Farhaan ina addu'a Allah yasa wannan Auren kar yaxamo silar tarwatsa farin cikin mu,ina sonka farhaan!!"Dan Allah karka manta dani ko na sakan dayane cikin rayuwarka,
"Waye kika taba ganin ya manta da xuciyarsa kin manta ke xuciya ta CE gabaki dayanta ,ki kwantar da hankalin ki bbu abunda xai faru ,kuma ae xamu rika waya wannan karon harda vedio Call .xaki rika ganina nima na ganki......."haka Farhaan yyi xaune sunata hira,
Ga Aliyu yaki fitowa shi xai saukesa a airport ,
Acan kuma bangaren Aliyu waxeer wanka ya shige yana sakarwa kansa shower,wani irin numfashi yake saukewa xuciyarsa na bugawa da karfi tamkar xatabar kirjinsa ,da ya runtse idonsa Nooriyah yake hangowa tana sakarwa farhaan sanyayyen murmushi baisan meyasa hakan ke hurting dinsa ba,meke damunka ne da lamarin Yarinyyar nan Aliyu waxeer??? Xuciyarsa ta fada masa tsaki yaja a karo na farko yana basar da tunanin Nooriyah aransa,koda ya gama wanka ransa a bace yake,agurguje ya shirya cikin blue din jeans,da farar shirt mai dogon hannu sosai yyi kyau acikin shigen ,turarukkansa ya saka masu tsadar gaske,
Agaban mirror dressing ya tsaya yana gyara sumar kansa tamkar ta macce wadda ta taru sosai akansa,wani irin faduwa gabanta ya shigayi da sauri da sauri kamshin turarensa ya sanar mata da xuwansa,Kafin takunsa ya fara ansa amo acikin kunnuwanta,Runtse ido tayi gagam tamkar mai Asmaa ta rika Jan numfashi tana dafe da xuciyarta dake tsananin bugawa ,da sauri farhaan ke tambayarta lfy???dai-dai isowar Aliyu waxeer cikin parlon bude ido tayi suka sauka cikin nasa,
Da sauri ya jaye nasa idon ya wani hade rai.
Ya maida idonsa cikin na farhaan yake fadin"baka duba tym ne besty.?mikewa yyi hannunsa xube cikin aljihun wandonsa ,yana bin Nooriyah da wani irin kallo itama kallonsa take idonta na cika da hawaye.mika mata hannun sa na dama yyi Ahankali ta samu kanta da Dora hannunta cikin nasa,lokaci daya Aliyu yabi hannayen da kallo xuciyarsa na bugawa.,,mikar daita yyi tsaye gamida jawota jikinsa duka abunda baitaba yiba,tun haduwarsu.suna hada ido da Aliyu gabanta yyi wani irin faduwa ganin yarda idonsa ya koma mata kalar red,dauke kanta tayi ta mayar kan farhaan .Hannayensa yasa ya rike kugunta ,cikin tsawa Aliyu waxeer ke fadin"meye Haka farhaan???''shi kansa baisan meyake fada ba ,baisan lokacin da maganar ya fito ba.da sauri farhaan ya saki Nooriyah yana shafa kansa yake kallon Aliyu da wani irin yanayi.............Idan Ammah ko wani ya gani fa??shirin mu xai wargaje duka.Ka sallameta pls mutafi,Aliyu ya fada yana barin wajen.dafe da kirjinsa dake Neman tarwatsewa ,Ahankali farhaan ya rika daga mata hannu .hawaye taji suna cika idonta, xubewa tayi daya daga cikin soofas din parlon Aliyu.sosai hawaye ke gudu akan fuskarta,A mota ma Aliyu kin kula farhaan yyi baisan meyasa yake jin haushinsa ba.murmushi Farhaan yyi yana riko hannunsa yake fadin fushi kayi ne besty?"
Nan ma Aliyu yaki kulasa har lokacin yaki saukowa,koda suka isa a air port akwai sauran mintuna xaman su sukayi a mota farhaan na Dan Jan Aliyu da hira kafin a fara kiran sunaye,,
Da an daura aure wani satin xan koma London ,,da sauri farhaan Ya kallesa yana fadin da wuri har haka???toh ya xakayi da nooriyah wani kallo Aliyu yayiwa farhaan yana fadin"tare aka haifemu da xata riqa bina duk inda na shiga bakin aikina xan koma ,ga kuma wasu kudi da suka bata a companyn waxeer dake kasar London ga kuma aikina."Yana aiki da airport din (LHR)London Heathrow airport, duk da yanzu wani Dan siyasa dake kasar ta London ,ya dauki Aliyu waxeer aiki a karka shin sa.abunda yasa ya Dan kwana biyu a Nigeria shima baya kasar Yana kasar Indian,
Ajiyar zuciya farhaan ya sauke ,xaiyi magana Aliyu ya daga masa hannu yana fadin"xamuyi magana besty,kusan tare suka fito daga motar side hug farhaan yabasa,
Daga kai Aliyu yyi yana fadin"ka kula da kanka........sai da yaga shigar Farhaan acikin jirgi shima ya juya ya nufi motarsa.cikin gari ya shiga bai dawo gida ba sai bayan magrib ,da mmki yake kallon compaund dinsu ganin motar mum dinsu farhaan,mmki yake Mai ya kawota gidan su a irin wannan tym din."Jin yyi xuciyarsa na tsalle bai gama dawowa normal ba ,sai ga Kiran Ammah ya shigo a wayarsa.dagawa yyi batareda yayi magana ba ,kana ina??"Yaji Ammah ta fada tamkar yace mata baya gida sai yaji baxai iyaba.ka shigo ga hajia Maryam ta shigo da haka Ammah ta kashe wayar ,cikin takunsa na kasaita ya shiga parlorn Ammah dauke da sallama a bakinsa,da fara'a Mami ta amsa tana fadin"Aliyu yaushe ka xama surikina ban sani ba."Dan sosa Kai yyi ya xube agaban Mami yana gaisheta da ladabi Mami ta amsa tana fadin"nayi fushi Aliyu wannan satin ake daura maka Aure ko ka sanar Dani,ko a bakin farhaan banji xancen Auren kaba.......
Mami ta karasa xancen tana kallonsa,Dan shafa kansa yyi gabansa na faduwa yake fadin"Am sowiee mami Auren ne yaxo a haka,da mamaki Mami ke fadin"Amma wacece wannan Mai sa'ar haka ??Ammah ta fadamin bada Areefa Mansoor ba.dan shafa sumar kansa yyi yana murmushi batareda yace komai ba,wayarsa ce ta fara ring wani irin ajiyar xuciya ya sauke ko wanene ya cecesa daga tambayoyin Mami,da sauri ya Mike ya nufi hanyar barin parlorn nan Mami ta juya suna magana da Ammah akan yarda xaa gudanar da bikin Aliyu,kasancewar Mami da Ammah kawayene tun su Aliyu na kanana ,Wanda sanadiyar yaransu Allah ya hada jinin su.
Shifa yace baxaayi wani taro ba kawai a daura aure akawo masa Amaryarsa."da mamaki Mami ke. fadin shine Kuma xaki biyewa shirmen Aliyu."shi yaji xai iya Ammah ta fada tana basar da hirar gamida dauko wata hirar,
Washe gari Khaleel waxeer ya iso shida Mai dakinsa laylah waxeer part din Ammah aka tarbesu ,cike da damuwa Ammah ke bin laylah din da ido ,ganin shekara kusan 3 har yanxu Layla din Koda batan wata Bata tabayi ba,sosai Ammah ta damu akan hakan,Haka Yan uwanta suna Maganar rashin haihuwar matar Khalil din,Bayan sun kammala cin Abincin.Ammah ta Kira murja tana fadin taje ta sauko da Nooriyah xata gaisa dasu Khalil da mamaki Laylah ke fadin har iyayen nata sun kawota kenan Ammah."da murmushi Ammah take fadin Nina bukaci hakan me yayi saura jibi xaa su shiga lalle,kusan minti goma sai ga Nooriyyah tana saukowa akan stairs itada murja wacce ke take mata baya,tana cikin shigar doguwar rigar atamfa kalar red and yellow wacce tayi matukar dacewa da kalar fatan jikinta,sai wani irin sheki take acikin kayan sai babban mayafi Wanda ta axa akan kafadarta,
Babu kwaliyya a fuskarta ,duka xuba mata ido sukayi daga Khalil waxeer har matarsa Laylah baki bude duka suke kallonta,ganinta bakar fata dukansu tunani daya suke yaushe Aliyu waxeer ya sauya tunaninsa akan bakar fata.?""xubewa tayi akan carpet tana gaishesu cikin sanyi muryarta, Layla ce ta amsa cike da tambayoyi a bakinta ,
Da murmushi Ammah ke fadin tashi ki xauna cikin su Nooriyah Yan uwanki ne........da murmushi Laylah ke fadin Amaryar mu gaskiyya kina da sa'a da kika samu Aliyu waxeer a matsayin mijin Aure ina maki fatan Alkhairi acikin Rayuwar Aurenku."murmushi kurum Nooriyah tayi batareda tace komai ba, Khalil ne ya Mike yana fadawa Ammah xasu wuce part dinsu suyi wanka.a fito lafia
Abinci dare na jiranku karfe takwas na dare".mun gode Ammah Allah ya kara nisan kwana ya fada yana kallon laylah ,kusan tare suka fice daga part din na Ammah,tamkar jira laylah keyi su fito ta kalli Khalil da sauri tana fadin"Wai da gaske leel Aliyu ne xai auri wannan Yar kauyen??"ko kadan Bata dace da taxama matar Aliyu waxeer ba wlhi."Laylah ta fada tana dakune fuska,Wai taya ma xaayi Aliyu yaso bakar macce??"Khalil ya dage kafada yana ware mata ido yake fadin"Waike me ya dameki kiyi Abunda ya dameki plz ya fada cikin Dan daga murya,shuru Layla tayi tana bin Khalil din da ido.....kamar yarda Ammah ta fada bayan ishai sai ga Khalil waxeer shida Aliyu sai Kuma Layla dake bayan su taci ado cikin wani tsadadden less Wanda yayi mugun karbarta ,dama laylah badai gayu ba.tayi simple make up Wanda ya Kara fitowa da Asalin farinta dama farace sosai,da fara'a Ammah ta tarbesu,.wannan karon Ammah Bata tura murja xuwa ta taho mata da Nooriyah ba Aliyu ta kalla ta fada masa yaje yaxo da Nooriyah xasuci Abincin dare tare ,shaye da toka Aliyu ke fadin Ammah plz...wani kallo da Ammah tayi masa yasa ya Mike da sauri ya nufi part din da Nooriyah din take,da ido laylah tabisa.tsaye yyi ajikin kofar yana sauke ajiyar xuciya baisan meyasa duk lokacin da xai kusanceta ba yake jin bugun xuciyarsa na karuwa,yafi minti biyu tsaye a kofar dakin kafin yayi knocking ,gamida tura kofar .gefen bed ya sameta ta buga uban ta gumi sanye take da hijab,tsaki yaja aransa .tana cikin daki Kuma sai ta saka hijab sabida kauyanci,gyaran murya yyi ta dago dara-daran idanunta ta xuba cikin nasa,yana wani daure fuska yake fadin,kixo Ammah na nemanki."Ya fada yana nufar kofa har yakai kofa ya juyo da sauri yana fadin Kuma ki cire wannan hijab din,Yar kauye kawai....."Ya karasa maganar fuska bbu walwala da mamaki take kallonsa,saka hijab din shine kauyanci,ki fito yanxu malama kina Bata mana lokaci ya fada da Dan daga murya.mikewa tayi tsaye ta nufi kofa sanye da hijab dinta baki ya bude yana kallonta.....
0 comments:
Post a Comment