xaxxabin kwana biyu ko kofar parlor Bai fito ba nooriyah itace Mai jinyar haka duka ya kashe wayoyinsa,
dakinsa ta tare ana jinyar tare .da dare yayi xata hau kan doguwar soofa dinsa dake dakin tayi kwanciyarta ,shi Kuma Yana kan bed arana ta ukku ne ya samu sauqi har ya samu damar fitowa cikin parlor ta kasance Ranar talata Aliyu Bai fita aiki ba,
Nooriyah na kitchen tana shirya masu lunch,sukaji ana buga masu door Bell har ta fito xata nufi kofa ya dakatar daita Yana fadin taje tayi aikinta xaije ya duba,Bata yi musu ba ta koma cikin kitchen din,Yana bude kofar sukayi ido biyu dashi tana cikin shigar riga da wando da bakin glass a idonta,sai Dan karamin veil da tayi Rolling kanta dashi Wanda Rabin gashin dokin da tayi Kari dashi duka a waje tamkar ba musulma ba,tana jayeda Yar karamar trolley ware masa ido tayi ta saki trolley din Hannunta ta wani shige jikinsa ,
Tana fada masa tayi kewarsa sosai.jin shuru yasa Nooriyah fitowa daga kitchen ta nufi kofa turus ta tsaya gabanta na mugun faduwa mugun ganin da tayi ,Juyawa tayi batasan lokacin da hawaye suka fara Rolling Akan kyakkyawar fuskarta ba,badai Aliyu bin Mata ya farayi ba??"ita kuma wannan kyakkyawar baturiyar a Ina ya samota."Juyawa tayi ta koma kitchen Haka hawaye Basu daina xubar Mata ba,haushin kanta take ji meye Kuma na kuka??"wata xuciyar ta fada Mata tana son Aliyu waxeer haka tana kishinsa baxata iya kallonsa da wata macce ba,da sauri Aliyu ya rabata da jikinsa ya shiga dube-dube kar Noory ta gansu girman da take gani nasa yaxube a idanunta,da murnar Areefa Mansoor ta nufi cikin parlorn ta xauna acikin fararen soofa,shi dae Aliyu Yana tsaye ya kasa xama .Areefa ta kallesa da mamaki tana fadin"Banga kana farin ciki da xuwana ba baby??"kayi Rashin lfy ko ka sanarmin ta waya".
a wajen laylah na samu lbr."kasan Saboda Kai kawai naxo kasar Nan ,yanxu haka exam's muke bana fahimtar komai sabida ciwon ka,Amma akwai wacce ke rubutamin exam's din."ta karasa Maganar da murmushi tana kallonsa."You are so careless Areefa kuna exam's shine xaki tsallake karatunki kixo."Ta turo Baki tana fadin ,nidai ya wuce tunda na riga da naxo din yanxu ka fara bani Abinci yunwa nakeji."xuwa Nan nayi wanka mu fita yawo, na riga dana Nasha barci acikin jirgi. Juyawa yayi ya nufi hanyar Kitchen xuciyarsa na bugawa bai san mexai fadawa Noory ba Kai tsaye xae fada mata budurwarsa ta kawo masa xiyara tun daga kasar Egypt.........Yankan Albasa kawai take hankalinta baya kan Abunda take,hoton Aliyu waxeer da kyakkyawar baturiya ke dawo Mata,batayi aune ba taji ta datsawa kanta wuka,Karar axaba ta saki gamida wullah wukar gefe dai-dai lokacin Aliyu ya karaso cikin kitchen din da sauri ya nufeta ,
Yana rike hannunta Yana kallonta cikin taushin Murya yake fadin"bakya bin komai Ahankali meya kaiki yankewa mekike tunanine Haka??''Hawaye taji suna ciki Mata ido hannun ya Tara a famfo Yana wankewa ,runtse ido tayi shiya yimata dressing hannun,ya kalleta yana fadin"muna da bakuwa ki shirya Mana lunch nasan kin gama ,kallonsa tayi tamkar ta tambayesa wacece?''sai Kuma ta share ,Juyawa yayi Yabar kitchen din tabisa da kallo xuciyarta na narkewa Ahankali da wani irin sonsa,Haka ta jera komai a table Areefa sai kallonta take cike da kishi Bata san meyasa ta kishinta ba,ko gasar sauraniyar kyau xasu fito tasan itace kan gaba,tafi Nooriyah kyau wayewa, kudi ,komai da komai ta fita Amma batasan meyasa taji Nooriyah din Bata yimata ba karon farko da ta ganta kenan. Idan farhaan ya Aureta duk dadin da Yake Bata xai maidasa ne Akan Nooriyah??"wani irin kishi taji ya taso Mata ,batasan tana kishin farhaan Shagari har hakaba sai da taga Nooriyah agabanta a matsayin wacce Yake tsananin so da kauna........tasan Bata da matsala akan Aliyu waxeer miskilin gaske ne ba komai ke burgesa ba haka yarda tasan halin Aliyu waxeer tasan tsarinsa,
Xaiyi wuya yaso nooriyahkasancewar ta bakar macce. murmushi tayi na gefen Baki,tare dukan su sukayi lunch Areefa sai baiwa Aliyu labarin karatun ta take ,sauran 6 month ta gama komai da komai na karatunta harta project nata.sai Maganar Auren su."Jin Maganar Aure yasa Nooriyah ta shiga tari da karfi ,da sauri Aliyu waxeer ya cika glass cup da ruwa ya Mika Mata Amsa tayi tana fadin"Ta gode,ta rigasu barin dinning Area din Areefa Mansoor tabita da wani shegen kallo ,da gudu ta nufi dakinta gamida Rufo kofar kukane taji Yana xomata Wanda Bata shirya tarbarsa ba,wannan kenan itace Areefa Mansoor itace budurwar Aliyu waxeer."itace Yake da burin Ya Aura,dole Aliyu waxeer yaki kallan kowace ya'h macce a dunia ,gaya da Areefa Mansoor ko ita dake matsayin macce ta yaba kyawun Areefa Mansoor da jar fatarta,wani irin kishin Areefa Mansoor taji yaxo ya rufe Mata xuciya,xamanta tayi a daki.kusan minti talatin sai gashi ana buga kofar dakinta,shuru tayi tamkar baxata bude ba sai Kuma ta bude kallon cikin idanunta Yake,kafin yace meya samu idon naki.?""Bata kallesa ba take fadin babu komai ta juya ta koma cikin room din tabarsa Nan tsaye ,karasowa yayi cikin dakin Yana kallonta.kiyi hakuri ku xauna daki daya da Areefa kwana biyu kawai xatayi yanxu ma tana so tayi wanka,taxo ga dakin Nan ni xan koma boysquaters."tayi Maganar cike da wani irin kishi.babu bukatar ki koma acan Idan bakison takura sai ta xauna a dakina ni Kuma na dawo naki dakin??"haka yayi maki,daga Kai tayi tana kallonsa shurunta yasa ya juya Yabar Mata room din ,
Sai gata ta biyo bayansa da sauri Areefa na kasan stairs tana kallonsu,kabarshi muyi using nawa."da Haka ta juya ta koma dakinta,sauka kasa yayi Yana fadin muje kiyi wankan a dakin Nooriyah ."lokaci daya Areefa Mansoor tayi mugun hade Rai tana kallonsa da mamaki take fadin"dama idan naxo gidanka Raba daki mukeyi??"ki fahimce ni Areefa bamu kadai bane a gidan Nan .Haka ko muna kwana daki daya ae ba waje daya muke kwana ba"Baki wangalau ta saki tana kallonsa,
Saboda itane xaka canja???"Bana son musu plz Areefa kaina na ciwo,xai dauki bag dinta tayi saurin dakatar dashi da mugun fushi take fadin"plz kabarsa muje ka saukeni gidan laylah baxan iya hada daki da wannan kaxamar ba."wani iri yaji da ta Kira Noory da kaxama,car key ya Mika Mata Yana fadin taje daga baya xai sameta."kallon mamaki kawai take binsa dashi duk yabi ya canja tunda ya Auri wannan yarinyyar......Amma koma minene xata dau mataki,karbar key din tayi ya subbaci goshinta Yana fada mata anjima kadan xai shigo ,har mota ya rakata sai da yaga fitar ta ya sauke wata irin ajiyar xuciya Mai nauyi ya koma cikin gida,shima nashi dakin ya shige Dan yin wanka.......sakin Baki laylah tayi tana kallon Areefa Mansoor,wani irin murmushi Laylah tayi ta Bata hanya ta shiga cikin parlorn tabita tana fadin"Yaushe a gari naxata fa wasa kike ??''barni nayi wanka na kwaso gajia ,da Haka laylah ta daukar Mata bag dinta xuwa dakin dake kasan parlorn sama Wanda ya kasance Nan ne dakin da suke saukar baki.wanka Areefa tayi ta saka riga marar nauyi tana gaban mirror dressing tana shafa turarrukanta masu sanyi kamshi,laylah waxeer ta turo kofar Mai aikinta na binta a baya dauke da katon tray ta aje Mata akan rug laylah waxeer ta xauna gefen bed tana kallon Areefa din ,ya naganki da trolley ba agidan Aliyu xaki sauka bane."sai lokacin Areefa ta kalli Layla ta hade Rai tana fadin"Kibarni da Aliyu da wannan bakar yarinyyar kin San rainin hankalin da sukayi min??" Kan up stairs na hangosu suna magana sunfi minti nawa ,sai gashi ya sauko Yana fadin muje dakinta nayi wanka."Ta karasa Maganar sounding so very Angry,ni xaya kalla yace naje nayi sharing daki da wannan Yar dajin Yaushe ma tayi wayewar da xan hada daki daita."Yarda yakeyi tamkar Yana tsoronta tunda na sauka gidan bai wani sake Dani ba,tamkar wata shegiya a rabon gado."Laylah tayi Rolling eye's dinta tana fadin "mena fada maki akan maxa,you tell me ."ae kin San Aliyu baxai yaudareki ba,maxa munafukai ne."tsinannune basa Jin kunyar soyayyarki xasu maki tijara da Rashin mutunci idan suka tashi laylah waxeer ta bude ido tana fadin"ko ki yarda ko karki yarda Aliyu ya fara son yarinyyar nan."Lokaci daya Areefa Mansoor ta dakatar daita tana girgixa Kai tana fadin"Bata yi isar da Aliyu xai sota ba barantana taja hankalinsa,kidaina fadamin haka laylah xuciyata xata tarwatse,laylah ta taba hannu tana Daria tana fadin"xuciyarki kuwa fitowa xatayi Idan Baki tashi kikayi fighting akan soyayyarki ba,tun farkon kinyi babban kuskuren barin Yarinyyar Nan ta shigo cikin Rayuwarsa ,bakiga yarda family waxeer ke sonta ba suke girmamata tamkar diyar wani Kusan gwamnati."kin yarda maxa suna iya canjawa lokaci daya??kin yarda Aliyu waxeer ya canja."kin yarda shi din munafukine Yana cin amanarki bayan idonki"da sauri Areefa Mansoor ta katseta cikin tsawa take fadin ki daina fadin Haka ni nasan Aliyu waxeer baxai taba iya hada jiki da wata macce ba Bayan ni."kin manta Aliyuna yarda yake da wani irin aji tayaya xai hada jiki da wannan kaxamar,pls Laylah mubar wannan Maganar tana batamin Rai Dan Allah,
Murmushi Laylah tayi tana juya ido take fadin"Idan na kawo maki Evidence xaki yarda Dani??tashi tayi tabar room din Bata fi minti biyu ba ta dawo da Yar karamar camera a hannunta,xaunawa tayi ta fuskanci Areefa mansoor da taga jikinta yyi sanyi lokaci daya , Mika Mata camera din tayi.buda ido tayi sosai tana kallon Aliyu waxeer dake kissing din Nooriyah with so much emotion and Romantic way"........Wanda ko ita da Yake dating dinta Bai taba yimata hakan ba,kashe camera din tayi ta mikawa laylah mikewa tayi tsaye hawaye na cika idonta lokaci daya Kuma jikinta na wani irin kadawa tamkar Mai Jin sanyi,da gudu laylah ta tare kofa tana kallon Areefa wacce ta fice daga hayacinta lokaci daya,
"Kefa dadina dake bakida Hankali Areefa wani lokacin??"ina xakije haka."cikin ihu take fadin xanje na Sami yarinyyar saina kasheta wlhi ita wacece da xata hada bakinta da Aliyu waxeer haka ta hada jiki dashi,toh kina tunanin xai barki ki tabata ne??wani kallo Areefa Mansoor take bin laylah dashi ,ae shima yasan waceceni wlhi tallahi yau koni ko yarinyyar Nan,Sai Aliyu ya Bata takardar sakinta Nan da wani watan xakiji Auren mu na dau Alwashin sai na fitar daita cikin gidan sa,kafin nabar kasar Nan........Laylah ta girgixa Kai tana fadin baxaki iya ba."key ta sakawa kofar gamida cire key din,ta kamo Areefa din wacce hawaye sun gama Bata Mata fuska jikinta sai kadawa Yake,ki dawo natsuwarki plz Areefa laylah ta fada mata tana kwantar da kanta kan shoulder dinta,
"Ki xauna a daki yanxu xan Kira Aliyu a waya .xan fada masa bakida lfy yanxo yanxu,,ke kin San yarda xakiji da sauran xan bar maku gidan dama xan fita,komai rintsi kisan yarda kikayi kika rabasu".haka ban Baki shawarar ki turawa farhaan vedio din Nan ba,kin San mahaukacine shima Alllura ce xata tono garma."kin yarda da bayani na??shuru Areefa Mansoor tayi karshe rufe idonta tayi mugun kishi nacinta,
Kusan minti talatin da yin wayar,sai ga Aliyu a gidan laylah najin horn dinsa da sauri ta Isa down stairs dama tayi Shirin fita kofar dakin ta tura ta hango Areefa Mansoor a tsakiyyar bed tana xukar sigari,hakan yayi mugun daga hankalin laylah .da sauri ta karaso gabanta gamida fisge sauran ta hannunta ta nufi toilet da sauri tayi flushing dinta,ta dawo cike da masifa take fadin u are very stupid Areefa hakan da kike shi xai canja komai ne."Idan yaxo yaji room din wani iri mekike tunani??"kina ganin Aliyu tamkar Wawa baisan komai ba,wlhi Yana sane kawai Yana daga maki kafane."ki daina waya'nann Abubuwan inhar kina so ki shigo cikin familyn waxeer,
Sai ki shirya ga shi can Yana gyara parking da Haka laylah ta juya Rai a bace tabar room din,
Haukan Areefa Mansoor da kishinta na Bata mamaki wani lokaci haka xata tayin Abu batareda tunanin Mai gaba xai haifar ba,
A kofar shigowa yaci karo da laylah ,kallonsa tayi shima kallonta yayi Yana fadin "good evening.......da haka yyi shigewarsa cikin parlor wani banxan kallo tabisa dashi ,har Aranta tana Jin tsanarsa yarda ya xama fav din Khaleel waxeer Ammah dukama familyn waxeer.........a parlor ya sameta kwance kan doguwar soofa xubama fararen kafafunta ido yyi kafin ya maida kansa kan fuskarta Yana gani yasan tayi kuka,Abu ga farin mutum.da sauri ya karasa gabanta ya Dora hannunsa bisa kanta ,kalau yaji da sauri ya kalleta da mmki Yake fadin"akace bakida lfy meke damunki Naga idanunki wani iri.batayi magana ba ta Mika masa wayar hannunta,kallon wayar kurum Yake da mamaki.Yasan ko aikin wanene wannan
da mamaki Yake fadin"meya faru Kuma."cike da mugun Jin haushinsa da kishi take fadin"me kake tunanin kayi Aliyu Yaushe ka xama Maci Amana."maicin Amanar Abokinsa ,
Yaushe ma ka fara kula yarinyyar Nan ban sani ba???"Yaushe ka sake daita har haka Aliyu da xaka hada jiki daita ,ta karasa Maganar a tsawace.
Cikin tsawa shima ya katseta yana fadin ni yaronki ne da xaki tsareni da waya'annan silly Questions din ,
Sai me Dan na hada jiki daita ban Isa bane ko ban Kai ba,keda ma ba muharramata ba na hada jiki dake barantana ita da aka daura Mana Aure."da mugun shock take kallonsa hawaye na cika idonta,plz ka fadamin ba gaskiyya bane wlhi xuciyata xata fashe xan mutu Aliyu Idan ka fara kula yarinyyar Nan,Dan murmushin takaici yayi ki tambayi munafukar da ta shirya maki duk wannan Abubuwan ,ya akayi na hada jiki da Noory kwaya ta samin acikin abun Shana,koni dutsene??"yyi Maganar so pissed up ,da mugun mamaki take kallonsa tasan halin Aliyu kaifi dayane baya karya haka baitaba yimata karya ba,Dan Haka Bata ga dalilin da xaisa ya fara yinta yanxu ba,tasan halin laylah da makircinta xata iya fiye ma da haka.juyawa yayi a mugun fusace ya nufi hanyar barin parlorn.........
Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma'u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN..ta wannan lambar#
09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#
ASMY#❤️
WM#❤️
Team#NooryAli forever🔥
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: *_Waminal Hoob_* 16
PAID BOOK
_Asmy b Aliyu_
Kallon Aliyu tayi tana fadin muje kar dare yyi ,Yyi murmushi Yana fadin"ga saurayinki Nan shi xai saukeki,hade Rai tayi tana fadin"Idan baxa kaje ba kabani car key din peter ya saukeni .
Mika mata car key din yyi tana gabda ficewa daga parlorn farhaan ya wani irin fixgota Yana kallon fuskarta ,
Kokarin fisge kanta take ya riketa sosae Yana girgixata a tsawace yake fadin"Kara ki fito fili ki fadamin kin tsaneni kin daina yina yanxu sai na San matsayina a wajenki da wannan munafurcin da kike min,fisge kanta tayi tana fadin"kaje ka fara tambayarka Farhaan
Kaje ka tambayi kanka meyasa alakarmu ta canja."ka sauya gaba daya tamkar ba farhaan din da Yake sona a baya ba wannan daban ne ,,da wanda na sani,wata irin Daria farhaan din yyi wacce Bata tattare da nishadi acikinta,
Ta gefen sa tabi xata wuce ya Kara fisgota Yana fadin,Ina kike tunanin xakije da wani kato......"!komawa tayi parlorn tana kallon Aliyu waxeer dake kallonsu tun daxu tamkar ya samu Tv.,Yanxu Kai nake Aure ba farhaan Shagari ba,kayi min ixini fita Dan Allah naje gyaran Kai......."Tayi Maganar da rawar Murya,kalllonta kurum Yake Yana karantar yanayinta nishadin da takeyi xuwan farhaan ya kawarda shi kije kawai Allah ya kiyaye."Ya fada Yana kallonta fisgota farhaan yyi ya xabga Mata Mari akan fuskarta Yana huci Yake fadin"ni xaki rainawa hankali ,Aliyu waxeer ya daka masa tsawa Yana fadin"Ka fara shaye-shaye ne??"Kai waye da xaka mareta ??'''ka fitar min a gida tun kafin rayukka su baci,ya kalli Nooriyah da hawaye sun gama wanke Mata fuska tana kallon farhaan din,wuce daki."da gudu ta nufi dakin barcinta tana barin parlorn farhaan ya karaso gabansa Yana kallonsa a xafafe Yake fadin"Ae ni ne dai silar wannan Auren kou."To ka saketa ynxu kabani takardar sakinta ,,ni da Kai ae kasan mun San hakan,kawai ka saketa ni xanji da sauran nagode da dukkan Karamci ,duk da wata xuciyar tana fadin ka fara cin Amanata shiyasa Nooriyah ta tsaneni, murmushi Aliyu waxeer keyi Wanda ya tsaya iyakarsa labbansa,xuciyarsa ta girgixa akan kalaman da suka fito daga bakin farhaan Shagari sai dai Bai nuna hakan a fili ba,Auren shekara daya kabani ba Auren wata daya ba,macce ce xata shiga tsakanin mu Besty Kuma ka yarda da hakan???"Abokantar shekara talatin tana neman ta rugeje sabida macce."Ba Kai bane Besty wannan ya canja,Kai kana tunanin xan iya son Abunda kake so."wani murmushi Mai ciwo yyi Yana fadin" hakan kakeso?? sakin Nooriyah inhar hakan xai sakaka farin ciki kabani wata daya xan fara shawo kan Ammah."kasan ciwon da take dauke dashi ,xan iya rasa komai Banda mahaifiyata ,Idan wani Abu ya sameta baxan taba yafewa ba."farhaan yyi murmushi xuciyarsa na tafasa Yake fadin"meyasa baka fada Mata contract marriage bane,akan me xata damu da Nooriyah har haka."batareda Aliyu ya Kara kula sa ba ya dauki laptop dinsa ya nufi dakin barcinsa da sassarfa ,dauriya kawai yake agaban farhaan da ya ambaci kalmar sakin da ta Kusan tarwatsa xuciyar Aliyu waxeer a wannan lokacin,da ya runtse idonsa maganganun farhaan Shagari ke dawo masa cikin kunnuwan sa,hannu biyu yasa ya dafe kunnuwan sa Yana sauke wani irin numfashi........A bangaren farhaan kuwa dakyar ya Kai masaukin sa,fridge ya bude dake gefen bed dinsa kwalaben beer ne masu tsadar gaske aciki ya fito da kwalba daya,ya cire marfin ya kafa a bakinsa sai da yaji bbu komai ya sauke haka ya tada kwalbar beer guda ukku da alamar ya Saba Sha sosai ,Amma har ynxu fuskar Nooriyah Yake gani agabansa.watsi da komai na Room din ya shigayi kafin ya xube Akan bed ya shiga surattai."wlhi tallahi baki Isa ba bbu Namijin da kika Isa ki so sai farhaan Shagari,ni kadai xaki so da ni kadai xaki rayu,bbu namijin da ya Isa ya soki bayan ni!"".......Sai ga hawaye na xuba akan fuskarsa........saloon din da ba samu xuwa kenan ba har washe gari basu sake haduwa da Junan su ba,kowa da abunda ke cin xuciyarsa .A bangaren Aliyu ya xabi akan ya rage mu'amala da Nooriyah hakan ne kadai xai samu ya rage Jin Abunda Yake ji akanta,duk da xuciyarsa ba karamin axabtuwa take da hakan ba,baisan shi so ba ruwansa da wannan ba ."sabida xuciya an halicce tane da soyayyar Mai kyautata mata ,Yana daukarka minti daya kacal kaji kana ra'ayin mutum,xai iya daukarka kwana daya kaji ka kamu da xaxxafar soyayya Amma Kuma xai daukeka tsayin Rayuwa kafin ka manta wannan soyayyar,cikin sati daya ba karamin axabtuwa Aliyu waxeer yyi ba yarda ya kauracewa nooriya ko abincinta ya daina ci ya daina xama a duk inda take xama,ko gaisuwarta ba ya amsawa cikin kwanakki kalilan nooriyah tayi wani irin Rama ta ban mamaki,
Kasar London gaba daya ta fice Mata arai,
Ko gaisuwarta Aliyu ya daina amsawa,Wanda Linda ta lura da haka, Abubuwan da take ko yamata ta rage fahimtar ta,akwai ranar da ta tsareta da tambayar meke damunta."Hawaye kawai ke xuba a idonta ta kasa baiwa Linda Amsa,ganin haka yasa Linda ta fada Mata bara ta Bata hutu na sati daya kafin ta dawo natsuwarta,godia tayiwa Linda.tana kwance a dakinta kamar yarda ta Saba,
Wayarta ta fara ring kurawa wayar ido tayi
Har tagama ta katse sai ga wani Kiran ya Kara shigowa tasan shi da mugun naci a Kusan karo na biyar ya sake Kiran ta daga Amma batayi magana ba,ina kiranki a waya baxaki daga ba Wai mena maki Noor kinbi kin tsaneni??"Farhaan Shagari yyi Maganar cikin kwantar dakai,
Hawaye na xubar Mata take fadin bakai na tsana ba Farhaan halinka ne na tsana duk kabi ka canja,ka juyamin baya haka ma Aliyu tun ranar da abun Nan ya faru na nemi farin cikin da nakeyi a gidan sa na rasa ,sai da nace kar ayi wannan Auren gashi yanxu tun baaje koina ba Kai da kanka kakeso ka lalata komai.........."ni na fada maka da bakina ina son Aliyu waxeer ne??"da xakayi min irin wannan mummunan fahimtar ,shuru yyi Yana sauke ajiyar xuciya maganganun ta kurum sun kwashe Rabin damuwar da Yake ciki. Haka Kuma yayi nadamar abunda yyiwa bestyn shi.ina sonki baxan iya rasaki ba wlhi."Shuru Nooriyah tayi xuciyarta na bugawa da wani irin yanayi.ka kula da kanka ina son na kwanta kaina na ciwo."Ta fada hawaye na xubar Mata tana mamakin Hawayen da basa gajia da xuba a idanunta tausayin farhaan takeji,Ashe da can baya haukan banxa takeyi akan son da take yiwa farhaan yanxu take ganin banbancin hakan da son da takeyi wa Aliyu waxeer.tana Jin lokacin da Farhaan ya fada Mata Kalmar ina sonki fiye da son da nake yiwa kaina......"Batace komai ba har ya kashe wayar,tana ta kwanciyarta a daki har Kusan karfe 2 na Rana kasancewar week End ne,a hankali ta Mike tsaye tana Jin jirin da takeji tun safe ,tana alakanta hakan da Rashin cin Abinci da baxata iya tuna Yaushene na karshe da taci Abincin ba,lemu da ruwa da bescuit sune Abun shanta Idan suka kare xata koma store ta kwaso wasu,fitowa tayi a falo tayi ido biyu dashi cikin kananun Kaya na Shan iska,
Da mug a hannunsa batasan menene aciki ba.wani irin faduwa gabanta yyi shima dauke kansa yyi xuciyarsa na wani irin Rawa,tana dawo masa da sabon ciwon da ya kwana biyu da mantasa ,duk da xuciyarsa ta kasa cire Nooriyah daga ransa,
Har aransa Yana Jin da gaske ba son Nooriyah yake ba kyawawan halayenta kawai ne yakeso ba ya Mata soyayyar Aure Yana sonta kamar yarda yakeson Batool waxeer.saurin mikewa tsaye yyi gamida daukar car key da alamar fita xaiyi tayi saurin shan gabansa hawaye na xubar Mata da rawar Murya take fadin"me nayi maka kabi ka tsane ni??"Kamo hannunsa tayi tana fadin ka manta Amintakar mu??"meyasa xaka biyewa shirmen farhaan ka yarda da maganganun sa kenan,ganinta kurum Yana ruguxa masa duk wani shiri da yyi axuciyarsa musamman da yaji tattausan hannunta cikin nasa,Xare hannunsa yyi cikin nata idanunsa na juyewa da wani irin yanayi,xamuyi magana wani lokacin inason xama ni kadai."Ya fada da wata irin murya,ki shirya Mana Abincin dare ya fada Yana barinta tsaye a wajen Dan sanyi taji aranta ,ya fara saukowa kenan har xaice ta hada masu Abincin dare.
Ranar farhaan ya kirasa yafi sau goma Amma Bai daga ba,
Suna da exam's baxai iya barin Cyprus ba da yaxo har kasar London ya basa hakuri ,shima abubuwa sunyi masa yawa ,Mami ta kirasa an Kai kudin Aurensa da ya ruguxa sauran hope dinsa,da ba Mami ce maihaifiyarsa ba waya Isa yyi masa wannan Karen tsaye da shisshigi acikin Rayuwarsa , sunyi waya da Aunty Nafisa wato yayarsa ita ta tabbatar masa da hakan,haka tace yakira xahra a waya tana ta korafi baya kiranta haka itama Idan ta Kira Bata samun sa,su basu sani ba ya dde da yin blocking dinta,Koda rantsuwa nawa xaiyiwa Mami akan xahra azeex Ali Yar hannuce baxata taba yarda ba,xata iya cewa sharri yayi Mata dama ya nuna bayason Auren tun farko
Bbu Abunda Bata Sha na kayan maye ,,haka tasan maxa kala-kala a rayuwarta shi baxai iya Aurenta ba wlhi ,yadai gama karatun Ya dawo gida ya fuskanci Mami.Shima exam's kawai Yake Amma hankalinsa gaba daya yayi gida Nigeria........da murnarta ta shiga kitchen Bayan la'asar har sai da peter yyi mmkin hakan,Tuwon shinkafa Mai Rai da lafia tayi masa,Wanda kafin ta gama kamshi ya cika koina ,tana gamawa ta hada masa coconut juice Dan tasan Yana sonsa,Wanda ta lura Aliyu ya fison juice din gargajia fiyeda na kanti,Ana gabda sallar magrib ta jere komai a dinning Area,Koda ta koma dakinta Kusan 5 miss call ta gani duk daga farhaan,wanka ta shige .tana fitowa mayukkan ta kawai ta shafa masu sanyayyen kamshi ta nemi riga marar nauyi ta saka ta tada sallar magrib tana cikin sallar taji rurin motar Aliyu da alamar ya dawo.kusan bakwai da rabi ta fito daga room dinta cikin shigar doguwar rigar Abaya kalar maroon Mai ratsin Baki ajikinta sai veil din da tayi Rolling kanta dashi,Bata samesa a parlor ba tasan Yana bukatar wanka da gabatar da sallah,xamanta tayi a parlor gamida kunna tv.tana kallon program din da suke na tashar larabawa,sosai ta maida hankali suna fada cikin harshen turanci Wanda ta fahimta tana rubutawa a takarda ,Wanda Bata fahimta ba xata nunawa Linda tayi Mata bayani,tana cikin rubutun sai Gaya ya fito,yyi wanka har ya sauya kayan jikinsa.
Wani irin sanyi nooryn taji lokacin da taci karo da kyakkyawar fuskarsa,shima a wurinsa hakan ne sai dai dukan su bbu Wanda ya nuna hakan a fili Kai tsaye dinning Area ya nufa,ita tayi serving dinsa da yarda ta lura ya natsu Yana cin Abinci tasan yamasa ddi,ke baxaki ci Abincin ba."Yyi Maganar da sauti marar Amo.,,sai lokacin yyi Mata magana tun xamansa ,Bata kallesa ba take fadin sai xuwa anjima.sabida saurayinki na fushi dake shine xaki kashe kanki da yunwa."wannan karon da Dan daga Murya yyi Maganar Kuma akwai wani yanayi na kishi acikin muryar tasa Wanda baisan Yana dashi ba,ta girgixa Kai tana fadin ba Saboda shi bane bana son naci Abinci banyi sallar ishaai ba ,farhaan yanata Kiran ka a waya kaki ka dauka ".dan Allah kayi hakuri cikin fushi yyi hakan."kallonta kurum Yake da wani sabon bacin Rai acikin fuskarsa,tambayar kansa Yake Yaushe suka shirya suka Jone kansu wuri daya."kenan shine mahaukaci sun ware kansu gefe suna faranta ran Junan su ,Jin yyi Abincin ya fice masa arai sabida kishi mikewa tsaye yyi
Ta kallesa da mamaki
Tana kallon Abincin da iyaka Rabi yaci ko coconut juice dinsa Bai shaba,bar Mata wurin yyi batareda ya Kara kallon inda take ba ,xuciyarta na bugawa take binsa da kallo.tayi tunani iya tunani Bata hango Kalmar da xa fada Dan ta Bata masa Rai ba,kodan tace sai tayi sallar ishaai xata ci Abinci shine yyi fushi??''har aranta Bata Jin Maganar farhaan xata Bata ransa lokaci daya.....Kusan 9 tayi fito wanka kenan Dan tana so ta kwanta da wuri yau ,taji ana knocking kofarta da sauri ta xura hijab tana basa umurnin ya shigo ,Kai tsaye ya sanyo kansa cikin room din da sallama a bakinsa cikin Italyn suite bakake da sukayi mugun karbarsa.yyi kyau har ya gaji kallonta yyi daga dama har kasa ,
"Ki shirya yanxu xaki rakani wani wajen."da haka ya juya Yabar kofar batareda ya Kara kallonta ba, murmushi ta shigayi ita daya Aliyu waxeer Yana da wani irin good personality da ba duk maxa suke dashi ba,
Tukish gown ce a jikinta kalar mint green Wanda tayi Mata kyau sosai,itama kallon kanta ta shigayi a madubi turarrukan da take amfani dasu ta saka da Wanda Aunty Ramla waxeer ta Bata tace ta rika using dashi duk lokacin da xata kasance tareda Aliyu waxeer,tana fada Mata turaren Kusan 50k ta sayeshi Yana mallake xuciyar maxa,baa fi sati da sukayi waya ba ta Kara tambayarta turaren da tabata tana amfani dashi kuwa Yana da kyau."kunya yasa ta fada Mata Yana da kyau,Alhalin Bata taba amfani dashi ba,tasan ba Auren gaske bane."Amma kasancewar xata fita da Aliyu waxeer yasa taji tana son amfani da turaren ko kadan ne,maybe yace Yana son turaren ko ya yaba kwaliyyarta,Babu wani tunani ta bude Yar karamar kwalbar tana jujjuya sa a hannunta Wai wannan shine dubu hamsin?"kadan ta xuba a hannunta tabi koina ajikinta dashi har akan dogon wuyanta.cover shoe ta xura a kafanta Wanda sukayi shige da gown din jikinta,A hankali ta tako cikin parlorn Yana xaune cikin soofa yyi crossing leg's dinsa Yana danna waya,kamshin turarenta yasa yaji tsikar jikinsa na wani irin tashi catching breath dinsa ya shigayi tamkar Mai Asmaa,wani irin tari ya shigayi da sauri Nooriyah ta nufi kitchen Dan dauko masa Bottle water,Mika masa tayi ya amsa sai da yyi rabi ya Mika Mata sauran dawowa tayi gabansa tana jera masa Sannu ,mikewa yyi ya nufi kofa turarenta na Kara saka sa cikin wani yanayi Bai taba Jin irin wannan kamshin ba rabonsa da Jin haka,tun ranar da aka daura Auren su."meyasa yanxu xata saka,Jin yyi tamkar ya fasa fitar Amma yasan xaisha korafi wajen Khaleel waxeer,yau Yake birthday a gidan sa laylah waxeer ta hada masa Party,Abokan business dinsu duka ta gayyacesu.Haka Ammah ta matsa masa Akan laillai yaje da Nooriyah,A mota ya dubeta da idanunsa da suka fara canja kala,Yake fadin meyasa kika saka wannan turaren bana Jin ddin sa.da sauri ta kallesa gabanta na faduwa,,Amma Kuma Aunty Ramlah ta fada Mata turaren Yana da kyau,meyasa shi baiji ddin sa ba."shuru kurum tayi masa tana ganin yarda Yake tukin motar duk baya cikin yanayi Mai ddi sai Tasha jinin jikinta tana da na sanin sakawa.......
Waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma'u Buhari Aliyu
Katin Wayar MTN.ta wannan lambar #
09060259200
Shidar Biya ta wannan lambar
08086207764#
_Duk barauniyar da ta karanta min book Bata Biya ba ban yafeba."_😡
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: *_Waminal Hoob_* 17
PAID BOOK
_Asmy b Aliyu_
Halin da taga Aliyu waxeer ya shiga duk ya daga Mata hankali."Kasan baka da lafia meyasa ka fito damu cikin wannan daren??"tayi Maganar da karaya a muryarta,shi dai baice komai ba har suka kawo gidan Khalil waxeer ,maigadin gidan Wanda ya kasance bature shi ya bude masu get din gidan,ya samu wuri cikin rumfar adana motoci yyi parking,
Ahankali kidan taushi ke tashi,Kusan tare suka fito daga motar
Booth din motar ya bude ya fiddo da gifts din da xai baiwa Dan uwan sa da shi da Noory tun acan yasa akayi wrapping dinsa,
Da Kuma kyawawan flower's mikawa Noory gift din yyi shi Kuma ya rike flowers ,Idan muka shiga sai ki baiwa Yah Khalil yau Yake birthday daga haka ya lalubi hannunta ya rike Cikin nasa duk da tsikar jikinsa yarda take tashi dauriya kawai Yake haka suka jera suka nufi Entrance din shiga gidan xuciyar kowane na bugawa da wani irin yanayi........Khalil waxeer ne da Layla tsaye a bakin kofar cikin shiga ta alfarma sunyi kyau har sun gaji ,sune ke taron duk bakon da ya shigo wurin haka ga gifts din da suka samu Nan daga gefe cikin wani katon basket da baxan iya kwatanta girman sa ba,,Khalil ya wara idonsa Yana yiwa Noory din Sannu da xuwa hugging din Aliyu yyi ,cike da ladabi Noory ta gaisheda Layla wacce ta saki Baki tana kallon yarda nooryn ta goge lokaci daya tayi wani irin fresh na ban mamaki ,dan kwakwalo murmushi tayi tana yiwa nooryn Sannu da xuwa,da haka suka Mika masu gifts Aliyu ya Rika hannunta suka nufi cikin katon parlorn nasu da akayiwa wani irin decorating ga turawa Nan a wajen da Kuma business partner dinsu hausawa da matansu ,kowane cikin shiga ta alfarma.
Wasu na rike da matansu suna rawa wasu Kuma na xaune suna ciye-ciye sosai wurin ya kayatar da Nooriyah,haka Aliyu yabisu suna gaisawa Anan wajen Yabar Nooriyah gefe ya koma ya xauna cikin soofas Yana dafe kansa dake mugun yimasa ciwo ga Kuma gefen marar sa da Yake Jin tamkar ana soka masa wani Abu a wajen,A hankali Nooriyah ta hngo wani kyakkyawan bature Yana xuwa ta wurinta. ya tsaya gabanta Yana gabatar mata da kansa ,cikin turancinsa da take fahimta kadan ,xai riko hannunta da sauri ta xaro ido gamida jada baya gabanta na faduwa ta shiga jada baya tana tunanin ta inda xata hango Aliyu baturen ya nace Mata sai magiya Yake yimata ,
Can take hango Aliyu dafe da Kai da sauri ta Isa garesa still baturen Bai daina binta ba ,Wanda shekarun sa baxasu wuce Ashirin da biyar ba........Jin an tsaya agabansa yasa ya dago jajjayen idanunsa ganinta yasa gabansa ya Kara faduwa,Kuma ya hango wani a bayanta.
da mamaki Yake tambayarta ya akayi ne."cikin harshen hausa take fada masa ga Wanda ke biyar ta Nan,,wani mugun kallo Aliyu waxeer yake masa tsoro yasa baturen ya juya da sauri ko waiwaye hakan ya Kusan saka nooriyah Daria,Aliyu ya dakune Fuska Yana kallonta yake fadin"Na sakaki ki tsaya cikin maxane?"ta wara ido tana fadin"ni ban shiga cikin maxa ba,ina tsaye ya sameni ae."Aliyu na girgixa Kai Yake fadin"wannan shaidanin turaren da kika saka ba dole duk inda kikayi maxa subi ki ba."Yayi Maganar Yana wani hade Rai,
Turarenta na Kara dagula lissafin sa.bata wani fahimci Maganar sa ba ,xatayi magana sai ga laylah waxeer da Waiter a bayanta dauke da tray ,ta dauki dayan cup glass Mai dauke da juice aciki ta mikawa Aliyu tana murmushi take fadin komai baka Sha ba,haka ta mikawa Nooriyah dayan ,kafa Kai Aliyu yyi batareda tunanin komai ba yasha Kusan Rabi ya aje itakuma Nooriyah Bata Sha ba,Layla ta Dan hade Rai tana fadin''sai kace wata bakuwa ke baxaki Sha ba."Nooriyah na murmushi take fadin"bana Jin ddin cikina Amma xan Sha xuwa anjima."Haushi laylah waxeer yasa tabar wurin..........Dafe kansa yyi dake mugun ciwo tamkar Yabar jikinsa haka Yana jin wani Abu na yawo acikin jikinsa har cikin tafin kafarsa dauriya kawai Yake ,Noor na kula da yanayinsa."A gaggauce ya mike tsaye laylah waxeer na gefe tana sakin wani irin murmushi tana Jin hirar da sukayi da aminiyarta a waya ,na dawo mata
"Baki da hankali Areefa Mansoor kina da tabbacin Bai taba kama Koda hannun yarinyyar Nan ba,kinga yarda ta xama lokaci daya tayi wani irin cikowa."Daria Areefa din tayi nasan waye Aliyu laylah bafa sonta yakeyi ba Auren su na Dan wani lokacine budurwar Farhaan Shagari ce taimakonta kawai yyi sabida gidan su xaa yiwa yarinyyar Auren dole kafin Farhaan ya gama karatu."wani irin murmushi Laylah waxeer ta saki anxo wurin da ya kamata taji gaskiyyar lamarin"shine Ammah ke wani rawar Kai ,Ashe karya Aliyu yayi masu ??"Amma ya xama a tsakanin mu sirrine daga ni sai Aliyu sai farhaan muka San da wannan xancen?""Aran laylah waxeer ke fadin Amma kin cika wawuya shasha da kika Bari akayi wannan Auren??''xan tabbatar maki da namiji ko baya son macce akwai Abunda xai sa ya kama hannunta har yakai ga jikinta,Da wannan dalilin ta sakawa Aliyu kwaya acikin drink daga shi har Nooriyah din Amma ita batasha ba,
duk da haka ta samu Evidence din turawa Areefa Mansoor,ta dau Alwashin Kota balai Kota masifa sai ta kuntata xuciyar Ammah kamar yarda ta saka Mata ido da Aurenta,sai ta tarwatsa dukkan farin cikinta ta hanyar shiga cikin Auren Aliyu waxeer da Nooriiyah,
Ta riga tasan da Ammah ba sonta take ba ,xaman dole kawai ne take daita karama hawan jinin nata ya tashi Idan taji Auren Aliyu waxeer contract ne......."Idan yaso xuciyarta ta buga ta mutu kowa ma ya huta,wani irin fisgo hannun Nooryn yyi Yana wani hadata da jikinsa Yana shinshinar Wuyanta Nan take ya wani irin haukace,A tsorace take kallonsa kallo daya tayi masa xuciyarta ta shiga bugawa Bata taba ganinsa cikin wannan yanayin ba,Laylah waxeer tayi saurin shiga tsakanin su tana masa wani irin kallo take fadin"meye Haka Aliyu??"meke damunka.?""tambayar da ta masa yyi balain Bata masa Rai,komai xakayi matarka ce Amma Bai kamata kayi acikin mutane ba.
Ta kama hannun Nooriyah da jikinta yyi balain sanyi gabanta na mugun faduwa ta nufi stairs daita tana ma Aliyu Alama da ido akan ya biyota ,dama tamkar ana basa umurni haka ya bita jikinsa na mugun rawa duk sanyi
Ac.dake makale da kowane kussuwa na cikin parlorn ya jike shakaf ko gabansa baya gani ,laylah waxeer ta bude dakin barcinta tayi Dan murmushi tana kallon Nooriyah wacce duk ta gama daburcewa daganinn yanayin Aliyu waxeer ,ki xauna Anan yanxu Aliyu xai sameki da haka ta juya tana Rufo Mata kofar Kusan cin karo sukayi da Aliyu Wanda take kallo a daburceta ka shiga tana cikin dakina.........."da haka ta wuce Aliyu tana sakin wani murmushin mugunta ,Yana turo kofar dakin ta Mike a tsorace gabanta na mugun faduwa ,tana ganin yarda jikinsa ke wani irin kadawa.Jawota yayi ta fado kansa Yana wani irin shakar kamshinta Yana sakin ajiyar xuciya ,Yana lalubar Wuyanta Yana saka kansa cikin Wuyanta wani irin Abu takeji tamkar Mai Jin fitsari,kokarin turesa take ya riketa sosae tana kallon cikin kwayar idanunsa wacce ta canja kala har kwalla kake hangowa acikin su,cikin rawar Murya take fadin''meye haka Aliyu me kake yi haka pls ka dawo natsuwarka."Kara manna ta yyi ga jikinsa ,ko Maganar nata wani irin shauki take sakar masa,xata turesa ya wani fisge veil din da tayi Rolling kanta dashi ,sai ga gashinta ya bayyana da ta tufke da ribbon sai walwali Yake Haka wani kamshi na musamman na tashi acikin sa,wani irin shinshinar gashin Yake a haukace ya shiga subbatarta ta koina har xuwa cikin Wuyanta,hawaye taji suna cika mata ido tuno farhaan kurum,
Xip din rigar ya soma kokarin ja kasa lokaci daya ta fashe masa da wani irin kuka tana girgixa masa Kai...Hade fuskarsa yayi da Tata Yana gogar hancinta da wata irin Murya Yake fadin"I try Am very try Noory."U belong to some one else,,ya fada muryarsa na karyewa a hankali kafin ya samu ya hade bakinsa da nata ,wani irin Rawa kafafunta suka farayi tunda take a rayuwarta Bata taba sanin haka kiss yake ba sai yanxu da Aliyu waxeer keyi Mata,sai dai ta karanta a novels
Ko ta gani a Tv......Xuciyarsa taji tana wani irin bugawa tamkar xata fito daga kirjinsa ,Ahankali ya saketa ya shiga Jan wani irin numfashi,wani irin amai yaji Yana taho masa da gudu ya nufi kofar toilet,Amai Yake xubawa tamkar xai fiddo da hanjin cikinsa duka,tana jinsa Yana Aman da ya daga Mata hankali sai dai Bata da natsuwar tunkarar sa barantana takai masa taimako,
Xip din rigarta take laluba Wanda har ya kaisa karshe dakyar tajasa sama,ta Mike ta nufi toilet din da wani irin yanayi haka lokaci daya xuciyarta na wani irin bugawa....Ya dde kwance akan bed kansa tamkar xai fice sabida ciwo, Nooriyah ta koma karshen bed ta xauna tana kallonsa,lokaci daya ya bude idanunsa da suka gama canja kala.tuno moment dinsu na daxu yasa yyi saurin rufe idon bayason tunosa ko kadan,bani wayana."Ya fada da muryarsa da Bata gama dawowa dai-dai ba,kan mirror dressing ta nufa ta dauko wayar ta Mika masa itama kallonsa kurum Yana sakata Jin kunya da wani iri.Bata san waya Kira a wayar ba taji dai Yana fadin yaxo yanxu."Baifi minti biyu da gama wyar ba aka turo kofar.......Khaleel waxeer ne Layla na biye dashi a baya ganin sun hada ido da Aliyu tayi saurin dauke Kai gabanta na mugun faduwa ,shi Kuma ya kasa dauke idonsa akanta kallonta Yake tamkar Mai son ya gano gaskiyyar Abunda ya faru cikin fuskarta,kallonsa ya maida kan Khaleel da ya ishesa da tambayar ko bayada lfy ne."Ya hade Rai sosai tamkar shine babba ba Khaleel waxeer ba,
"Wace irin kwayace xaku sakawa mutane haka acikin drinks Yaya."Idan mutum Bai da Aure Kuna so yayi xina ne??''Yana Maganar ne cikin sanyi Murya Kuma cikin harshen turanci,
da mamaki Khaleel ke fadin acikin Abun shanka ne aka saka kwaya"Kallonsa ya maida kan laylah waxeer wacce ta hade Rai,da sauri ta daga masa hannu cike da balai da masifa take fadin"karka yimin sharri plz Ban San anyi ba Kuma bbu wani Abu da aka saka ,da Haka ta juya cikin fushi tabar room din gamida bugo masu kofar duk sun Bata Mata plan,shima Aliyu mikewa tsaye yayi jikinsa duka bbu kwari Yake fadawa Khaleel xasu wuce,
"Dama bada Shirin kwana kaxo ba.??"Aliyu na girgixa Kai Yake fadin"bana tunanin haka ,har mota Khaleel din ya rakasu sai tambayar Aliyu Yake Yana iya driving kuwa."sai da ya ga fitarsu ya juya cikin gidan,ya samu laylah a dakinsa sai cika take tana batsewa,cikin ihu da fada take fadin"Saboda ya rainaka ya shirya maka karya shine xaka yarda dama ae a dole yaxo baiyi niya ba ,tamkar baka San rainin wayon Aliyu da wulakancin sa ba,dama ai Kaine ke rawar kafa akansa shi ya damu da Kaine,Hannunta ya riko tana fisgewa sai famar hakuri Yake Bata da lallashinta.
Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma'u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#
09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#
Team#NooryAliForever#
_ko kalma daya Kika karanta Baki Biya ba na barki da Allah.!"_
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: _*Waminal Hoob*_ 20
PAID BOOK
_Asmy b Aliyu_
Dakin barcinta ta nufa kai tsaye , daman Ammah ta saka kowane gida an shiga an gyarasa daga gidan Khaleel har na Aliyu,tana shiga ta saka key jikin kofar toilet ta wuce wayarta ta fiddo ta shiga Kira daga dayan bangaren aka daga,kana jina ko Sabi'u ehh ina jinki Hajia plz ka kawomin maganin da kasan Yana saka tashin xuciya Idan aka shasa yanxu -yanxu ina gida??da mamaki Yake fadin Ban fahimta ba??Dafe Kai tayi kafin tace kwaya Mai karfi nakeso wacce xata iya saka mutum Jin jiri har ma da Amae,a dauka mutum Yana da shigar ciki ka fahimta yanxu??tayi Maganar a Dan hasale nagane Hajia Nan da awa daya nake bukata Idan ka kawo kayimin waya,da haka ta datse Kiran tana sakin murmushin mugunta tana wani juya ido ,xatayi wasa da hankalin Ammah xata xuba ido kurum Tasha kallo Yar Daria ta saki tana tafa hannu har ta hango yarda Ammah xatayi ,ta dakune Fuska tana kallon mirror din toilet din tana xaro ido take fadin"Allah yasa Aliyu shine ajalinki !!"Allah yasa ma ki mutu kowa ma ya huta ,wlhi tallahi yarda Baki kaunar ganina cikin farin ciki Nima Haka ,kin hanani Jin ddin Rayuwar Aurena yarda kike min wasa da farin ciki agidan Aurena Haka Nima xan tarwatsa farin cikin ki."Da Khaleel baya tsananin Sona da na shiga ukku na lalace."cire kayan jikinta ta shigayi wanka tayi tana son taga wanna dramar.........Ta lura tunda Ammah tayi Maganar Rashin samun cikinta duk Aliyu ya shiga damuwa,itama a bangarenta Kusan hakane,wani irin soyayyar Ammah da tausayinta taji ya tsaya Mata arai,duk ranar da Ammah ta gano matsayin Auren su Bata San mexai faru ba."Hawaye taji suna cika idonta Wanda Bata San ko na menene ba,a karo na bbu adadi tana da na sanin yin wannan Auren,duk da Auren ya kawo Mata Alkhairi sosai acikin Rayuwarta ,ta tabbata data Rabu da Auren Aliyu waxeer babu ita ba sauran farin ciki Koda ta Auri farhaan Shagari kuwa."Bata yiwa farhaan Shagari soyayyar Aure,da tayi wanka daki tayi ta kwanciya har Kusan 5 har lokacin Bata San halin da Aliyu Yake ciki ba,gajia da kwanciyar tayi ta fito parlor bude Baki tayi tana kallonsa Yana kwance akan soofa Yana barci ,Bata taba ganin Wanda barci Yake yiwa kyau ba kamar Aliyu waxeer..........ta dau tsawon lukkuta tana kallonsa,lokaci daya ya Buda ido Yana kallonta wara ido tayi ta juya masa baya cike da wata irin kunyarsa."xo Nan.!''taji ya fada mata Juyawa tayi a hankali ta fara tafia kanta na a kasa ,
Kallonta Yake tun daga sama har kasa ,wandon Jean's ne ajikinta Wanda ya kamata sosai sai farar shirt tayi parking kanta tsakiyyar kanta ko hula babu akanta ,tayi wani irin kyau.har ta karaso wajensa xuciyarsa Bata daina bugawa ba,xama tayi tana kallonsa." Mekika shirya Akan Rabuwar mu??"da sauri ta dago tana kallonsa xuciyarta na wani irin harbawa,Batayi tsammanin Jin waya'nnan kalaman daga garesa ba."wata biyu ya rage Mana,ban san me xai faru da Ammah ba Idan wannan Auren yaxo karshe,Dan murmushin Nooriyah tayi da dukkan kwarin gwiwarta take fadin"karka damu acikin watanni biyu din Nan xan samo Mana mafita insha Allahu Ammah baxatayi blaming Dinka da komai ba believe me??"tayi Maganar tana kallon cikin kyawawan idanunsa,saurin dauke nasa idon yayi ya mike tsaye Yana fada Mata Bayan sallar magrib xasuje su gaisheda Baffa waxeer ta hada tsarabarsa shida Ummah,da Haka ya nufi dakin barcinsa Dan yin wanka.Bayan sallar magrib kamar yarda ya fada sukayi shiri dukansu cikin shiga ta alfarma sai xuba kamshi suke A mota daya suka hade,cike da fara'a ummah tayi masu tarba ta musamman ,Haka ta masu jagora a parlorn baffa shima yayi murna da ganinsu sai saka masu Albarka Yake,cike da girmamawa Nooriyah ta baiwa Baffa tsarabarsa Wanda turarruka ne masu tsadar gaske na maxa,sauran ledar ta mikawa ummah itama turaren ne da dogayen riguna masu kyan gaske ,lokaci daya Laylah tayi mugun hade Rai shima Khaleel cike da kunya ya saukar da kansa kasa ganin Bai rikowa baffan nasa komai ba,
Idan Yana biyewa laylah yasan babu Abunda xaa taho dashi,tana ma iya yin fada tace Mai suka nema suka rasa ae suna da komai ,kyautar ma idan anyi masu ae bayarwa suke meye Amfanin yinta.basu Jima ba sukayi masu sai da safe har sun nufi gidan Ammah laylah ta kalli Khaleel ta Dan shagawabe fuska take fadin"sweetheart Ice cream din Aliyu ya kaini na karbo,Baki na duk Babu dadi".gyaran Murya Khaleel yayi Yana fadawa Aliyu ya juya motar laylah xata Sha ice cream ,Aliyu yasan da gangan tayi haka baice komai ba ya juya kan motar.......dukansu a mota suka xauna laylah ce kurum tafita karbo ice cream din da kallon takaici yabita ganin wasu shegun Kaya dake jikinta wanda dakyar take Buda Kafa tayi tafia acikin su sabida yarda suka kama jikinta,mayafin shi Kuma a kafada kawai aka dorasa,wani tsakin takaici ya saki .Yana taya yayan sa jimami da Rashin dacen Abokiyar Rayuwa.bata Jima ba sai gashi ta fito gefen da Noory ke xaune ta bude ta ajey Mata nata ledar ,da Dan murmushi Nooriyah ke fadin nagode,tun a mota laylah ta fara Shan nata .itama Nooriyah da ta kwana biyu Bata Sha ice cream ba ta dauko daya ta Buda ta gefen ido take kallon Aliyu,
Ya girgixa Kai Yana fadin kin San sanyi baya Baki lfy why not...."ki Bari sanyin nasa ya rage,yayi Maganar sounding so very cool."..Yama fara yin melting ba duka Yake da kankara ba,
"Idan kika dameni da dare kina min korafin Akan hancinki ya toshe sai na fasa maki baki."Yayi Maganar Yana dakune Fuska kallonsu kurum Khaleel keyi cike da burgewa ,Yana mamakin yarda Wai Aliyu waxeer ne ya iya kula da macce har Haka."ita dai laylah murmushi kurum take,
Dukan su suka samu Ammah a parlor tana using laptop da medical glass a idonta,xubewa sukayi a gabanta suna kwasar gaisuwa ta daga Kai tana kallon Nooriyah tana fadin Kara da Allah yasa kuka taho yanxu mugama cin Abincin dare ki tayani caculating kayan Nan,
Da sauri Nooriyah ta karbi laptop din tace bara na maida a daki idan mun gama xan xo na duba."da Haka ta nufi dakin Ammah na barci laylah tabita da wani mugun kallo haka ta hade wani Abu da taji ya tsaya mata arai.kowa shi yayi serving mijinsa,
Nooriyah tun da ta fara serving Aliyu taji xuciyarta na wani irin tashi haka kamshin Abincin na wani irin hautsina cikinta,dauriya kurum take bayan ta gama xuba masa ta koma ta xauna Ammah ta kalleta da mmki tana fadin"ke baxaki xuba Abincin bane,xatayi magana taji amai yaxo mata da gudu ta rufe bakin ta nufi hanyar kitchen da sauri Ammah ta Mike tsaye tabi bayanta shima Aliyu Bayan su yabi , Khaleel waxeer yayi murmushi Yana fadin"Allah yasa mun samu karuwa."shima yayi Maganar sounding so very happy Wanda Jin kawai yayi Maganar tafito masa ,da sauri laylah ta kallesa da mamaki cikin hade Rai take fadin"mekake nufi da hakan??"Ya Dan fiddo manyyan idonsa ya kalleta yana fadin ,kawai na masu fatan Alkhairine ."tsaki laylah tayi tana fadin ni bana son munafurci Kara ka fito fili ka fada kaima ka shirya son haihuwa ."Tayi Maganar cikin bacin Rai xaiyi magana sai gasu Ammah sun fito Aliyu rike da Nooriyah wacce tabi duk ta galabaita lokaci daya,
"Bari na dauko mayafi muje Asibiti ,da sauri Aliyu ya katseta yana fadin"Ammah wane irin Asibiti Kuma yanxu xata dawo normal maybe akwai Abunda taci Wanda ya lalata Mata ciki."wani irin Kallo Ammah tayi masa da yasa shi saurin saukar da kansa kasa gabansa na mugun bugawa ,har ga Allah baya son aje Asibiti sabida kar agano babu ciki a karya xuciyar Ammah ,tunanin hanyar da xai dakatar da Ammah Yake,da sauri Ya kalli Khaleel waxeer Wanda shima kallonsa Yake,ka fada Mata Yaya plz......."Khaleel ya girgixa Kai Yana fadin"kabari aje a duba Yar mutane Mana,xaiyi magana sai ga Ammah ta fito sanye da hijab waya a hannunta tana neman layin Dr.Billy wacce ke aeki acikin Asibitin waxeer Kusan shekaru biyar itace family doctor dinsu,komai da komai itake dubasu ta fannin Rashin lafia,Jin yayi hankalinsa yayi mugun tashi,rikata muje Ammah ta fada tana nufar kofa da sauri tamkar itace Bata da lfy,Allah kawai ne ya kaisu Asibitin Dan baima San inda Yake jefa motar ba,duk sanyin Ac.dake motar xufa Yake hadawa.sunyi sa'a tana office dinta ,
A kofa Aliyu ya tsaya ya kasa shiga cike da tsoro Ammah ce da Nooriyah suka shiga,
Sun shiga da minti biyu sai ga Dr.billy ta fito dama Aliyu ya tura Mata sako,tana ganinsa tace lfy Aliyu meyasa baka shigo ba??"da sauri ya saukar da Murya Yana fadin ina son muyi magana private Aunty kafin ki duba Nooriyah plz."owk ina xuwa??''ta fada tana komawa office din ta kalli Ammah da murmushi tana fadin"bara naje na dawo Ammah pls minti biyar toh ina Aliyu Kuma??"Ammah ta girgixa Kai tana fadin"Auh komawar sa yayi".Dr.Billy ta nufi kofa tana fadin ina Jin baiyi nisa ba fa"......Dan Allah Aunty ki tabbatarwa da Ammah Nooriyah nada ciki ajikinta plz kiyimin wannan alfarmar,Baki sake Dr.Billy ke fadin"kasan kuwa hukuncin wannan karyar shin meyasa ma xakayi Mata wannan karyar."Aliyu waxeer ya girgixa Kai xuciyarsa na karyewa yake fadin"Sabida farin cikinta xanyi haka kin San ciwon Ammah damuwa kadan ke dagasa duk tabi ta daga hankalinta na rashin samun cikin Nooriyah,
Inhar xaki taimaka Mana da maganin da xata dauki ciki Nan da wata daya pls ki taimaka Mana,na rasa yarda xan nunawa Ammah hakan daga Allah ne,idan Nooriyah ta fara Shan magani Nan da wata daya Idan Allah yayi xata samu cikin kinga karyar mu Bata tafi a banxa ba.?""Toh Anya kuwa Aliyu kana kusantar matarka akai-akai kuwa"Haka Kuma Kai daita duka Kuna lfy,lafiar mu kalau Aunty."ya fada Yana Jin xuciyarsa nayi masa wani irin nauyi da karyar da ya Saba tun da Nooriyah ta shigo cikin Rayuwarsa,yasan muddin Ammah taji Nooriyah Bata da ciki sai ta gano gaskiyyar meya hanata yin cikin,
Yasan halin Ammah da saka Abu agaba ,Haka Kuma da wuya taki yin Nasara,
Duk ta gano basa zaman Aure da Nooriyah komai xai iya faruwa."naji na aminta da bayanin ka ,Amma ka dawo gobe Kai da matarka na binciki lafiar ku kafin na Baku maganin da xakuyi Amfani dashi,godia sosai yayi Mata Yana Jin wata natsuwa na saukar masa,mota ya koma yayinda Dr .Billy S fari ta nufi katafaren ofeshinta ,gwaje-gwaje ta saka akayiwa nooriyah din Wanda ta gano akwai Abunda ya hutsina cikinta magani ta rubuta ta ajey takardar gefe. Wanda Aliyu ne ya kamata tabaiwa takardar,ta kalli Ammah da murmushi a fuskarta tana fadin"Hajia Allah fa ya karba Addu'arki kin kusa xama Kaka."!"wani irin dagowa Ammah tayi da kwallar farin ciki a idonta tana kallon Dr .Billy wacce take daga Mata Kai Alamar tabbatarwa ,wani gefe tausayin Ammah ne ya rufeta.da mugun shock Nooriyah ke kallonsu,Hawayen rudewa taji suna cika idonta lokaci daya,
"Duka kudaden Jakarta ta xube a table din dr.Billy cike da Hawayen farin ciki take fadin"ban san Dame xan biyaki ba doctor ga wannan ,su kawai ne a jakana xuwa gobe xaki ga babban Goran Albishir ,Aliyu ta shiga Kira cike da murna take fadin"yayi sauri yaxo office din Dr. Billy dama yasan hakan xata faru wani irin soyayyar mahaifiyarsa da tausayinta yaji suna cika masa xuciya,Dr .Billy ta Mika masa takarda tana tayasa murna haka ta fada masa yabiya pharmacy ya karbowa Nooriyyah maganunnukan dake jikin takarda,kallonsa kawai Noory keyi da mugun shock shi Kuma yaki yarda ya kalleta,A mota ma duk yarda taso su hada ido yaki bada damar hakan,a hanya ya tsaya babban wani pharmacy ya karbi magani,suka nufi gida tun a hanya Ammah ke sanarwa ya'n uwa da abokan arxiki a waya ,tana jira Ammah tayi gaba ta tsaya tareda Aliyu .Ammah Taki bada damar hakan suna gama parking ta rika hannunta suka nufi Entrance din shiga cikin gidan,laylah da Khaleel ne xaune a parlorn Ammah suna kallo,
Dama laylah Taki tafia ne har su Ammah su dawo daga Asibiti suji meya faru ."da fara'a Ammah ta karaso cikin parlorn ta kallesu tana fadin"dama Baku tafi ba,no Ammah muna jiran dama ku dawone."laylah ta fada tana kwakwalo murmushi ,Ammah ta xauna ita dai Nooriyah tana ta tsayi xuciyarta tana Jin ba dai-dai ba,
Ammah ta kalleta tana fadin"xauna Mana Nooriyah ta kalli Khaleel waxeer da dukkan farin ciki Akan fuskarta Wanda Khaleel Bai taba hangowa ba take fadin"ka kusa xama daddy Khaleel."!shima Khaleel wani irin farin ciki Ya bayyana akan fuskarsa yake kallon Aliyu waxeer Wanda yayi tsaye tamkar an dasa sa a wajen ,wata irin ruguma Khaleel din yayi masa Yana sakin dariar farin ciki.
Har kwallah na cika idanunsa,ita dai laylah kallonsu duka take a rude,Taya hakan ta faru??"Taya Nooriyah xatayi ciki yanxu."wani abun takeji wani iri tamkar a wasan kwaikwayo ,Dan murmushi tayiwa Nooriyah tana fada Mata tana tayata murna,ta kalli Ammah tayi Mata sai da safe ta riga Khaleel barin gidan,tun a hanya take Kiran Sabi'u Yana dagawa take fadin"wane irin magani ka bani wannan daga shansa sai ciki."tayaya?''da mmki Yake fadin"hajia sai idan dai dama akwai cikin,xufa ta fara hadawa ta katse Kiran ta ta gwada Kiran Areefa Mansoor naso ba adadi a kashe wannan daren Bata taba ganin dare Mai tsawo irinsa ba a tsayin Rayuwarta.matsuwa tayi garin Allah ya waye.nooriyah Bata samu damar ganin Aliyu ba Dan agidan Ammah ta kwana,shima dama Yana tsoron haduwar daita Dan Bai shirya karbar tambayoyinta a yanxu ba."sai Kusan 12 ya shiga gidan Ammah,bbu kowa a parlon Kai tsaye bedroom din Ammah ya nufa,dama bedroom din nata biyu ne Wanda Yake tunanin Nooriyah na ciki can ya nufa,Yana tura kofar sukayi ido biyu daita,tana ganin sa da sauri ta Mike ta nufosa idonta na cika da hawaye,xatayi magana yayi saurin Dora yatsan sa a bakinta,lokaci daya ta fashe da kuka ganin haka yasa yayi saurin Jawota ajikinsa gamida rungumeta."
Littafin Waminal Hoob na kudi ne #500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma'u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar
09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#
ASMY#❤️
WM#❤️
Team#NooryAli forever❤️
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: 19
Da mugun shock take
binsa da ido har motarsa tabar gate din gidan,hawaye taji suna Rolling Akan fuskarta wani irin ciwo takeji aranta,Kiran laylah ta shigayi a waya Amma Bata daga ba,sai ana ukkun ta daga cikin shesshekar kuka take fadin"he's gone.......!"Da haka ta katse Kiran batareda ta jira Mai laylah xata fada Mata ba,a wannan lokacin beer kurum ce xatayi maganin damuwarta tana ganin farhaan Yana kiranta a waya ta kashe wayar duka Bata bukatar kowa da komai a yanxu,Shirin fita tayi taje ta nemowa kanta Abunda xai kwantar daita kar xuciyarta ta buga ganin komai take tamkar A mafarki..............Kallonsa kurum take da mamaki har ya gama hada kayansa a trolley ya Mika Mata yace ta xuba kayanta na sati daya aciki ya tabbatar bag din xata ishesu na 1 week yasan ko wane lokaci Areefa Mansoor xata dawo gidansa yasan halinta Kara Yabar Mata gidan baxai saurareta ba wannan lokacin.sai ya koya Mata mugun hankali ita xata kirasa da mugayen sunaye munafuki Maci Amana."dama tun a waya ya masu booking tsadadden hotel,ita dai Nooriyah bin wurin kurum take da kallo yayi matukar tsaruwa,ganin sunan dake jikin wurin ta juya da sauri tana kallonsa.hotel ya kawosu to meye dalilin yin haka"Kuma har kwana bakwai Bata ga fuskar yimasa tambaya ko daya ba,
Damuwarta daya ganin sun kama daki daya komai da komai akwai ciki ,ita damuwarta Taya xasu sharing daki daya.Bayan magrib ya fada Mata Idan tana bukatar wani Abu ko sako ta tura masa a waya xai sa akawo Mata xaije ya dawo ubangidan sa Yake yimasa Kiran gaggawa Addu'a yake Allah yasa ba tafia xasuyi ba. Dan muddin ya daga Yabar kasar Nan Areefa xata iya yin komai,Bayan ya fita ta samu tayi wanka harda su sakawa kofar key.........lokacin da take Buda jakar kayansu har ajiyar xuciya ta sauke ganin kayan barcin da ta dauko duka masu kaurine ,bbu Mai bayyana tsaraici wasu riga da wando ta dauka ta saka farare sol."dama da ta dauro Alwallah tada sallar ishaai tayi har Kusan 9 babu Aliyu bbu Alamarsa sa duk tabi ta damu,bata tura masa sakon tana bukatar wani Abinci ba, Amma yasa an kawo Mata Abinci Mai Rai da lfy,
Tayi xaune ita daya tana kallon Tv.sai wayar da tayi da Yah Kabir Wanda ya shiryu yanxu har Aliyu ya Samar masa gurbin karatu a N.d.A.dake kaduna ,dama Kabir Yana sha'awar xama soja Rashin wadata da kawayen banxa ya tarwatsa Rayuwarsa Kuma tunda Aliyu waxeer ya shigo cikin Rayuwarsa komai ya xama tarihi a kullum yanayiwa Aliyun Addu'a Allah ya cika Rayuwarsa da farin ciki fiyeda Wanda ya Basu ,ko mahaifiyarsa duk tsanar da ta nunawa Nooriyah yanxu ta xubar da makaman yakinta Addu'a take Mata da fatan Alkhairi acikin rayuwarta,aduk lokacin da ta Kira kawu balele Idan har Yana gida xai hadata da Adama ne ,a wannan fannin itama tanayiwa Aliyu waxeer fatan Nasara aduk kan lamarunsa Bata da abunda xata biyasa ,sai dai Addu'a dabin duk wani umurni nasa."idan tana kirgar watannin Auren su har fargaba take,batasan mexata fadawa Y'an gidan su ba,ranar da Aurenta itada Aliyu waxeer yaxo karshe"...........Bata san ya xasu dauki hakan ba,dama kawu can ya tsani farhaan Shagari wacce bata san inda tsanar ta fara ba,kawu yace Dan iskane idonsa a tsaye suke baya basa girma komai a gadare yakeyin sa.murmushi kurum take Idan ta tuno hakan tasan kawun nata Bai fahimci Farhaan bane ,Dan Aliyu yafisa miskilanci da tsare gida,yayin da farhaan din keda fara'a da faram-faram da mutane......shikuma Farhaan acewarsa ya tsani kawu balele sabida xaluncinsa ga wacce yafiso fiye da komai a Rayuwarsa,
Kusan 10 Aliyu ya dawo ,har lokacin batayi barci ba,sannu da xuwa tayi masa kayan jikinsa Yake kokarin cirewa agabanta tayi saurin runtse ido gamida daukar pillow ta dannawa fuskarta ,Dan murmushi ya saki kunyarta na burgesa Amma ba Koda Yaushe ba.sai da taji ya shige toilet tayi saurin cire pillow tana sauke numfashi,Kusan minti Ashirin taji Yana kokarin bude kofa tayi saurin maida pillown Akan fuskarta,ya fito daure da towel babba da Dan karami Yana tsana jikinsa da ruwa,
"Idan numfashin ki ya tsaya bakina xan saka na xukosa Yar baka."Yyi Maganar da wani irin sauti tana jinsa Amma Taki bude fuskarsa,Jin tayi an fisge pillow lokaci daya ta Buda ido ta kallesa gamida xaro ido tayi saurin rufe idon,har yau Bai saka kayan ba daga shi sai towel daure a kugunsa.xama yayi a kusa daita cike da tsokana,Yar Kara ta saki tana matsawa plz saka kayan ka."ta fada still idonta a rufe to ki bude ido idan Baki bude idoba xan subbaceki." yyi Maganar sounding so very serious Jin haka da sauri ta Buda idon da yasa ya saki wani irin murmushin da gefen kumatunsa suka lotsa murmushin da ya Kusan sumar daita ,Bai taba murmushi Wanda yayi masa kyau ba tamkar wannan.mikewa tsaye yayi ya saka kayansa na barci ya hau kan bed Yana fadin.""Ban yarda da kwana kan soofa ba Idan na farka na ganki ,xan maidaki Akan bed da Haka ya kwanta gamida Jan duvet ya rufe har fuskarsa,Kusan awa daya tana ta xama taji dai shuru da alamar yayi barci,kwanciyarta tayi kan doguwar soofa ta kashe wutan dakin..............Koda safe da ta farka taganta kan bed a tsorace ta kalli gefensa barcinsa kurum Yake,wata irin kunya taji ta kamata ,da sauri ta sauka kan bed din xuciyarta na bugawa da gudu ta shige toilet gamida murxa key......kurawa fuskarta ido tayi cike da takaici take Fadi." ,ki dawo hankalinki Areefa hankalinki nake bukata,Taya xan dawo hankalina laylah Bayan ke kika jawo yakai jikinsa wajen wannan kaxamiyar yarinyyar ." Baki sake laylah ke kallonta tayi mugun hade Rai take fadin ya shirya maki karya shine xaki yarda."ta girgixa Kai xuciyarta na mata ciwo take fadin Aliyu baya karya laylah Bai tabamin karya ba Kuma baxai farayimin yanxu ba ,baya gidansa Babu ma kowa a gidan bana samun sa awaya.ya kikeso nayi laylah??''
Me xanyi maki tunda kin yarda dashi fiye Dani kinga karki Kara sakani a sha'anin ku Dan Allah duk Abunda kika yanke dai-dai ne ,da Haka tabar Mata room din Rai a bace.da wani irin kallo Areefa tabita har yau tana Jin kanta ya kasa dawowa dai-dai da ciwon kan da ta kwana dashi duk da a buge ta kwana,kwanan ta biyu bataga Aliyu ba Haka yasa tabi shawarar laylah ta koma Egypt ,ta fada mata yaudarar ta Aliyu kawai Yake Amma tabata lokaci su San yarda xasu bullowa al'amarin........
10 month leap..watannin su goma da Aure xuwa wannan lokacin komai ya dai-daita tsakaninsu da farhaan Haka Areefa Mansoor ta basa hakuri ta fada masa baxata Kara xarginsa ba,cikin wannan lokacin ya shirya masu tafia gida Nigeria ya samu hutun wata biyu acikin Kuma wata biyun ne xaayi Aure a familyn waxeer Yar baffa xatayi Aure . shirye-shirye kurum Yake batareda ya sanarwa Noory ba,wacce yanxu ta xama Yar kasuwa Ammah ta sakata cikin harkar business dinta da take na online kudi Ammah xata turo ta siya English wears na Yara maxa da na Mata har na manyya bags shoe's komai da komai na kyale-kyale ,
A tura gida Nigeria dama Ammah ta riga ta Buda manyyan shaguna a kaduna da Abuja ciniki ake na fitar hankali,sosai Nooriyah ta maida Hankali babu laifi ta xama Abunda Ammah take so ta xama Dan Aliyu har mamakin Wayewar Nooriyah Yake lokaci daya ,Idan bbu Kaya a London har kasar tukish take xuwa Dubai ma Haka ,
Haka sunje umra itada Aliyu wannan shekarar,
Ta xama wata irin big hajia.Alakarta da farhaan Shagari tana Nan bbu Abunda ya canja sae dai Bata jinsa aranta tamkar yarda take Jin Aliyu waxeer,dauriyace kurum take ana sauran kwana biyu tafiar su ya sameta a daki da laptop agabanta da farin glass Mai karama idonta gani wata biyu kenan da idonta suka fara samun matsala sabida yawan using da Hasken waya da Kuma laptop ,sanadin Haka sai da suka ga babban likitan ido ,har takai Idan Abu Yana daga nesa Bata cika ganinsa ba.dr.Ya dorata akan magani na wata daya still bbu Abunda ya canja dole akayi mata medical glass Mai karawa idon gani Wanda daga nesa xaka dauka na passion ne Wanda yayi Mata matukar kyau,ya fito da kyawawan fararen idanunta,wasu Kaya take turawa Ammah da tayo masu order dinsu daga kasar Pakistan dogayen riguna new designers.daga Kai tayi tana kallonsa,
Ya xauna kan soofa din dake cikin dakin Yana kallonta,Yana mamakin kwaxonta da son aekinta ,in har xasu samu Nooriyah acikin companyn waxeer ba karamin cigaba xata kawo masu ba,sai dai yasan mafarki kawai Yake Ammah baxata taba Bari ba,ko matar Khaleel waxeer Dan tafi karfin sune.turarensa duk ya gama cika Mata daki ta dago tana kallonsa,
Yayi murmushi yana fadin"jibi ne xamuje Nigeria Amma ban sani ba ko xaki samu xuwa,wara ido tayi gamida ture laptop din gabanta ,tareda wani irin farin ciki take fadin"meyasa baka sanarmin ba har sauran kwana biyu,Kuma ko daxun Nan munyi waya da Ammah ,Batool dukansu Babu Wanda ya fadamin."dage gira daya yayi Yana fadin"dama surprising dinki xanyi oya ki shirya mufita shopping ,ta langabar da Kai tana kallonsa da kyakkyawan idanunta masu gigita Aliyu waxeer ,take fadin siyayyar me Kuma ina da kayan tsaraba Kusan trolley biyu na dde ina hada su ,kabarshi mutafi dasu."Ya girgixa Kai Yana fadin ni ne bakiso Aljihuna yayi motsi haka bakyaso na Samu lada to naki wayon.!"ki shirya yanxu ya fada Yana bar Mata dakin murmushi tabisa dashi ,Rufe laptop din tayi wanka tayi ta saka wata rigar lace purple wacce ta kasance doguwar rigace sai mayafi wanda yayi shige da kayan,Buda Baki tayi tana kallonsa ganin ya xauna front seat ganin haka tasan meyake nufi.wato tayi driving dinsu ya dde da koya Mata mota,ta xagaya ta bude tana kallonsa tana fadin"Yallabai yau baxan iya tuki ba yau bayana na min ciwo ,Nasan da farhaan ne baxai barni nayi tuki ba."ta fada cike da tsokana tana kallon reaction dinsa.
Lokaci daya ya wani irin fisgota ta fado kansa,Hade Rai yayi cike da kishi Yake fadin"mekika ce??"gabanta na faduwa take kallonsa ,
Hannunsa ya saka ya matse bakin da karfi karar axaba ta saki harda guntuwar kwallarta,Saboda bakida Hankali kina da Aure kike Kiran wani kato."Gobe ma ki Kara ,yayi Maganar da wata irin Murya Mai tattare da kishi.da sauri ta kallesa ganin har yanxu tana kan jikinsa da sauri ta sauka ,ta rufe masa kofar ta xagaya ta xauna maxaunin driver taja motar suka bar gidan har lokacin fuskar Aliyu babu wani walwala.shopping yyi masu tamkar baisan xafin kudi ba,ita dai Nooriyah duk Abunda yace a dauka sai dai ta dauka karku ma ya Kara dalle Mata Baki,ta lura Abun laifi baya wuya a wurinsa musamman Maganar farhaan ta rasa dalili,Koda suka dawo mota bayan a saka acikin Booth ta tarar da Miss calls na farhaan ,gabanta ya Fadi yanxu Idan Kuma ta Kira xatayi laifi a wajen Aliyu silent ta saka wayar Idan sun Isa gida xata kirasa.sai ga Kiran farhaan ya shigo a wayar Aliyu dagawa yyi suna gaisawa,tana Jin yana fada masa baya gida ,ita dai Batace komai ba Bayan sunyi sallama ta juya tana kallonsa koxai ce wani Abu,
Ki kalli hanya karki xubar damu a titi."yayi Maganar cike da bacin Rai ,hankalinta ta mayar kan titi itama ta daure fuska tana mamaki tana karawa duk wannan Fushin na minene.....?"koda suka koma gida kowa ya shige dakin barcinsa har washe gari Basu hadu ba,yinin ranar ma Basu xauna ba shirye-shiryen tafia suke sai ma yanxu takeji a bakinsa tare xasu tafi dasu laylah washe gari jirginsu ya daga nigeria shigowar yamma sukayi a Abuja suka sauka ,duka dama suna da gidaje acikin maitama sai washe gari suka karasa kaduna.Ammah tamkar xata goyasu Saboda farin ciki sai kallon Nooriyah take cike da damuwa ,ta xata ta ganta da ciki sai taga a kasin hakan,sabida da wuya suyi vedio call da Ammah sai dai waya ,sunfi yin vedio call da Batool mafi yawanci Kuma a school suke yin Haka,
Tare sukayi lunch da Ammah,cike da damuwa Ammah ta kalli Aliyu tana fadin"ko dai kaima baka shirya haihuwa yanxu ba tamkar yarda Dan uwanka ya fadamin A baya."Ammah tayi Maganar cike da damuwa lokaci daya Laylah tayi mugun hade Rai, girgixa Kai Aliyu yayi Yana kamo hannun Ammah Yake fadin"Allah Bai kawo ba Ammah kiyi Mana Addu'a,ita dai Noory Batace komai ba saima saukar da kanta tayi a kasa cike da wani irin yanayi xuciyarta na bugawa."kuyi wanka ku huta ku shiga ku gaisheda Baffan ku yayi Rashin lfy,ta kalli laylah da Nooriyah tana fadin kar wacce ta Dora girkin gidanta xan shirya Mana Abincin dare,da Haka ta Mike tana fadin"Allah ya hutar da gajia,wani irin banxan kallo laylah tabita dashi tana sakin wani irin murmushi,haka Aliyu yaji duk Babu ddi ganin halin da Ammah ta shiga,da sauri yabi Bayan Ammah har dakinta na barci ya cimmata ,xaune ya sameta cike da damuwa yaje ya durkusa agabanta ya riko hannayenta Yana fadin"Ammah damuwar Nan ta menene."lokaci ne baiyi ba Idan lokaci yayi Allah xai bamu haihuwa duka -duka Yaushe akayi Auren."girgixa Kai Ammah tayi cike da damuwa take fadin."gobe ka shirya ni da Kai da matarka xamuje Asibiti a Auna ta agani Idan akwai matsala xuciyar Aliyu na bugawa Yake fadin"Ammah Baki yarda Dani bane."kawai kayi yarda nace ,tashi kuje bangarenku ku huta Allah yay maku Albarka ,xuciyarsa na bugawa Yake fadawa Ammah Ameen.jin yayi kafafunsa nayi Masa wani irin nauyi ita dai Ammah binsa kurum take da ido ,tana ji ajikinta daga Aliyu har Nooriyah Bata yarda dasu ba.koma Menene xata bugi cikin Nooriyah taji gaskiyyar lamarin.''
Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma'u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar
09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#
ASMY#❤️
WM#❤️
Team#NooryAli forever#
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: da wani irin shock take kallonsa ,Haka lokaci daya take xare jikinta cikin nasa hawaye na xubar Mata tana girgixa masa Kai.cikin rawar murya take fadin"karya Kuma ,karya kan Karya komai namu karyane meyasa?''ta fada da Dan daga Murya saurin rufe Mata Baki yyi Yana kallon kofa komawa yayi ya sakawa kofar key ya dawo ya riko hannunta ya xaunar daita gefen gado,shima ya xauna cikin sanyi Murya yake fadin"sabida farin cikin Ammah nayi Haka Nan da wata biyu insha Allahu xan samo solution din matsalar mu ki yarda Dani pls....."!yayi maganar cikin raunin murya Yana jin shima kamar Bai kyautawa Noory din ba,inhar hakan xai saka Aliyu farin ciki da Kuma mahaifiyarsa A shirye take da tayi masu ma fiye da hakan,hannu ta saka tana dauke hawayen idonta ta kallesa gamida shagwabe fuska tana kama cikinta take fadin"baby xaici gwaiba,ta fada tana murmushi tana ware masa ido Bai San lokacin da ya saki murmushi ba.dama fuskar sa takeso ya saki, pillow ya dauka ya jefa Mata itama haka,haka suka fara xagaye dakin sai Daria suke cike da nishadi tamkar babu Abunda ke damunsu dukansu,Yana so ya rikota Taki basa damar hakan shammatar ta yayi ya damkota Yar Kara ta saki dukan su suka xube kan bed suna maida numfashi tana Jin yarda xuciyarsa ke bugawa.saurin dagasa tayi tana mirginawa gefe ,daga can gefe sukaji ana buga kofa da sauri Noory ta Mike tsaye tana xaro ido ,Dan murmushi yayi gamida gyara kwanciyarsa xuwa tayi ta bude kofar Ammah ce da Mai aeki a bayanta ,wata irin kunya ta kamata lokacin da Ammah ta shigo dakin tana bin koina da kallo yarda aka hargitsa komai ,da mmki take kallon Aliyu .Mai aikin ta ajey kular tsakiyar rug ta fice ,
Tsaye bakin kofa Nooriyah tayi cike da kunya,gaisheda Ammah yayi Yana kokarin Buda kular Ammah ta dakatar dashi tana fadin"me xakayi??''Ya dakune Fuska yana fadin Ban karya ba Ammah."tace kaje dinning area akwai break fast wannan na Nooriyah ne."suna hada ido tayi masa gwalo,Ammah ta kalli Nooriyah da har yau ke tsaye bakin kofa tace xo ki xauna ga alalen an gama,cikin sanyi jiki Nooriyah ta karaso ta xauna kan rug din tasa hannu ta bude kular alalar ciki sai tiriri takeyi ga manja Nan an xuba samanta,sai kamshin yajin tafarnuwa ke tashi .Aliyu waxeer ya dakune Fuska yana kallon Ammah yana fadin"Ammah kin manta bana cin wannan Abar,ya mike tsaye yana kokarin fiddo wayarsa dake famar Kara ya fiddo ganin Mai Kiran sai da gabansa ya Fadi."saurin maida Wayar yyi cikin Aljihun wandonsa da mmki Ammah ke fadin"Ana Kiran ka a waya baxaka dauka ba,xan dauka Ammah ya fada Yana kallon Noory daita ma take kallonsa,
"xan dawo xuwa anjima."Ya fada Yana kallonta daga masa Kai tayi ya juya yabar room din ,Ammah ta kalleta tana fadin"kici kar yayi sanyi bara naje na karasa aekina."da haka itama tabar room din Yar ajiyar xuciya nooryn ta sauke .batasan Kuma sai xuwa Yaushe wannan karyar xata kare ba,,ta gaji ta gaji da wannan karyar.
(Omar Shagari mention)Shirin fita Yake yi daga gidan ko kadan baya son haduwarsa da Mami satin sa daya kenan da dawowa,sanin Mami sunje graduation dinsa na kammala masters yasa ya yarda yaxo yanxu din Haka Mami ko Yan gidansu Babu Wanda ya fada masa me Mami ke shiryawa ,sai da yaxo yaga lefen da Mami ta dankara Wai duk na xahra Axeez ne Nan da wata biyu aka sanya Auren su."tun daga lokacin ya hau fushi da kowa a gidan ko Abincin gidan bayaci tun Mami na lallashi har itama ta daina lallashi dan acewarta tunda ba ubanta bane ta daina binsa ,Yasan dai hukuncin Wanda yaki bin umurnin uwarsa,knocking yaji anayi bakin kofar shigowa room dinsa yayi mugun hade Rai gamida harara kofar Yake fadin"Uban waye ke bugamin kofa!"yayi Maganar sounding so very Angry,dan duk a zaton sa Jamila Shagari ce wato autar mami wacce itake bin Farhaan, cikin fushi Mami ke fadin Uban Kane ke bugawa,baxaka xo ka budemin kofa ba sai na sassaba maka farhaan."A fusace yaxo ya bude kofar yabata hanya ,ya dawo Cikin dakin ya dauki car key dinsa ya juya xai fita Mami ta bude ido da Baki tana kallon Rashin kunyar Farhaan din."lallai kenan da na Bari ka Auro yarinyyar Nan shikenan na shiga ukku na lalace juyamin baya xakayi farhaan."Mami tayi maganar da tsananin shock a muryarta ,Juyawa yayi Yana fadin"Mami fita xanyi da wani irin fushi Mami ke fadin biyoni a parlor tana fadin Haka tabar masa dakin a fusace tamkar xata tashi sama sabida masifa.........Mami ta xauna ta xuba tagumi cike da Abubuwan da sukayi Mata yawa,duk Saboda farhaan Nafisa ta karaso cikin parlorn da mamaki take fadin Mami Baki same sa bane ."ko ya fita??tambayoyin da Nafisa ta jero Mata kenan,wallahi Nafisa jikina yayi sanyi Anya basai na shiga malammai Akan farhaan ba,yarinyyar Nan ba banxa tabarsa ba,kinga yarda nake fada Yana fada." Nafisa ta girgixa Kai cike da takaici take fadin"bbu komai akan sa Mami iskanci ne kawai ke damunsa,idan an daura masu Auren ya saketa ranar,Mami komai rintsi karki Bari farhaan ya Auro matsiyaciyar yarinyyar Nan,Dan wlhi juya maki baya xaiyi."Nafisa sai kace kin mantani ne aeko Bayan Raina farhaan ya Auri shegiyar yarinyyar Nan ban yafe masa ba dunia da lahira Haka Kuma baya taba ganin dai-dai cikin lamurrransa."sai acikin kunnen farhaan Wanda ya Kara Shan jinin jikinsa kallonsa Mami kurum keyi,ya xauna Yana fadin"Mami ita wannan da xaki Auramin kin manta Yar iskace bin maxa takeyi."!yayi Maganar da karaya a muryarsa,
Baki bude Mami ke kallonsa ta kalli Nafisa tana fadin"kin jisa da sharri kou."Kai da idonka kaga katti na dannarta a dakin hotel,cike da takaici Yake fadin Mami waye baisan Zahra axeez ba har shaye-shaye take ."Mami dai kallonsa ta tsaya yi,kafin ta Mike tsaye tana fadawa Nafisa ta Miko Mata mayafinta a daki Mai shige da kayan jikinta ,sai ga Nafisa ta dawo dauke da mayafi ta mikawa mami.amsa Mami tayi ta saka,hannu ta Mika masa tana fadin ya Bata car key din hannunsa,Yana hade Rai yake fadin"Mami fita xanyi Aliyu na can na jirana akwai inda xamuje."wani kallo da mamin tayi masa yasa ya Mika Mata car key din,wuce muje."Mami ta fada tana nuna masa kofa, Mami ina xamuje na fada maki fita xamuyi......."gidan ubanka xamuje farhaan!"tayi Maganar cikin daga Murya da bacin Rai,har Mami ta fara driving masifa take shi dai baice komai ba yayi shuru yana binta da kallo,
Ganin unguwar da suka shigo yasa ya juya Yana kallon mami,amma mamin Bata ko kallesa ba taci gaba da tukin ta .har suka kawo katon get din gidan su xahra Axeez,horn ta shiga dannawa maigadi ya leko,ganin Mami yasa ya wangale masu get.
Motar ma sai na fito da Kai."Rai Abace ya fito daga cikin motar ya nufi Entrance din shiga gidan ma'aikatan gidan sai gashesu suke da ladabi ,Banda mugun kallo babu Abunda yake binsu dashi,da fara'a hajia Yasira ta tarbi Mami tana masu sannun da xuwa."ta kalli farhaan tana fadin"sai yau kaga damar xuwa ,tun Yaushe kadawo??"shi dai baice komai ba sai Dan murmushin da ya kwakwalo na dole,
Xahra ce ta shigo parlorn tana Amsa waya,wata fitted gown
Ta atamfa ce ajikinta ta kamata sosai ,sai kanta da yasha kananun kalaba,tana da kyau sosai Dan farace sosai Haka tana da tsayi kiba daice Bata daita ko kadan,Amma tana da wani irin shape Mai daukar hankali ganin farhaan Shagari a gidan su tayi saurin katse wayar da gudu ta karaso cikin parlorn
Tana sakin murmushi take fadin"Yaushe kaxo??"kaga damar xuwa kenan..."Mami ta washe Baki ,hannunsa taja tana fadin"muje parlorn Baki,gaisheda Mami tayi cike da ladabi,suna shiga parlorn ya fisge hannunsa Yana binta da wani mugun kallo.
ta juya ido tana fadin wulakancin naka kenan Ya motsa."xata tabasa ya fisge hannunsa Yana fadin"karki tabani da wannan kaxamin hannun."!yayi Maganar da bacin Rai da wata irin tsanarta ,
Ta girgixa Kai tana sakin murmushi gamida dage gira daya take fadin"Ya Rabbi!""so much Anger!"yau kawai farhaan ,Kai kullum fada baka taba yimin magana Mai Dadi ba,
Ya harereta Yana fadin."in har kina son kanki da arxiki ki fasa wannan Auren."mexai faru idan Anki hakan ??"ta fada tana kallon cikin idanunsa,Aurenmu duka taimakon junane ,ni shegiya kai shege."kowa sai yayi Rayuwarsa yarda yakeso ko Bayan Auren mune.'"ko ka xata Ban sanka ba farhaan!''ban San iya matan da kasani a Rayuwar bariki ba.haka Nima baxan iya kirga maka maxan da nasani ba,komai dai ya wuce yanxu tunda ina sonka baxan taba ganin illarka ba."kallonta kurum Yake da idanunsa da suka fara canja kala,
Ta rungumesa sosai take fadin"Auren mu Alkhairi ne dukan mu farhaan Shagari babu takura acikin Auren mu kowa xaiyi Rayuwarsa yarda yakeso."ya tureta daga jikinsa ya juya yabar gidan duka batareda sanin Mami ba xuciyarsa na tafasa..........sigari Yake kokarin kunnawa Aliyu waxeer ya dakatar dashi Yana dakune fuska Yake fadin"plz karka kunna kasan bana son warinta wlhi."badan farhaan din yaso hakan ba ya mayar,ya kallesa da wani sabon bacin Rai Yake fadin"kasan me Mami tayi min kuwa??Aliyu na girgixa Kai Yake fadin"ya xaayi na sani sai ka fada,Nan ya fada masa Abunda Mami ke kokarin yi da Rayuwarsa ,cikin bacin Rai Yake fadin"Mami ta kusa kure hankurina da na Auri wannan yarinyyar karama duk Abunda Mami xatayi tayi bantaba ganin Haka ba Wai yiwa namiji Auren dole."Ta rasa ma wacce xata hadani Aure daita sai karuwa wacce ta gama watsa duwawunta atiti."Daria sosai Aliyu keyi Yana kallon farhaan ,Mami ta rantse ko Bayan ranta ban Isa na Auri Noory ba,plz kabani shawara ya xanyi da Mami."Ya karasa Maganar da karaya a muryarsa,Aliyu ya lumshe ido na dan lokaci ya budesu akan farhaan din Yana fadin duka ka samu a matsala Farhaan Shagari ina da nasanin biye maka tun farko dama da Kai aka daura Wannan Auren kayi tafiar ka da Yarinyyar can kasar da kake karatu idan ka dawo sai ka fuskanci Fushin Mami ."Nima gashi yanxu kasani A matsalar Ammah."Ya fada Yana basa labarin Abunda ya faru daren jia,dafe Kai Farhaan yayi Yana fadin"innalillahi aransa ,Ya kalli Aliyu Yana fadin matsalarka Mai sauki ne fiye da tawa ,wani kallo Aliyu keyi masa Yana fadin"Mai sauki fa kace Kasan babu Abunda Ammah ta tsana fiye da karya,
Kasan ciwonta har kake Kiran hakan da me sauki,ka samo Mana mafita wata biyu sukayi saura,ga Areefa mansoor tana ta kirana a gefe na turo magabata na mu
."kasan me xai faru ??''Aliyu ya kalli farhaan Yana girgixa Kai,sakin Noory Mai sauki ne guduwa xanyi wlhi muje can muyi Auren mu Dana Auri xahra Axeez Kara na mutu."shi dai Aliyu kallonsa kurum Yake da nashi tashin hankalin da Yake hangowa,kayi shuru ko baiyi ba??Aliyu ya girgixa Kai Yana fadin ban san me xance ba ."Kiran Areefa mansoor ne ya shigo a wayar farhaan shagari gabansa na bugawa ya kalli Aliyu da hankalin sa baya kansa Yana kan wayarsa ,saurin saka wayar silent yayi .Aliyu ya kallesa Yana fadin"ana Kiran ka a waya ko Mami ce."Kafin yayi magana Kiran Areefa ya Kara shigo masa da sauri ya mike tsaye ya fice daga parlorn ,Yana dagawa Yake fadin"kina damuna dayawa Areefa kibarni naji da damuwata,muna tareda Aliyu Kuma."Bashi ya dameni ba farhaan ciki ne ajikina."ta fada da muryar shock.!"cike da mugun bacin Rai Yake fadin"dama ni kadai ke ganin duwawun naki.??''kinyi mugun Raina ni Areefa karki fara wasar da baxai yi Mana kyau ba pls."Ya fada Yana kashe wayar duka da wani sabon tashin Hankali."Yana Juyawa yaga Aliyu na nufosa ,
"Meya faru Kuma??Aliyu ya fada Yana karantar tashin hankalin dake kwance Akan fuskar farhaan,
Muyi waya bana Jin Dadi."da mamaki Aliyu ke fadin ka fasa shiga wajen Ammah kenan??"Yana girgixa Kai Yake fadin xuwa gobe dai."Kayi wani Abu cikin satin Nan Besty mu samarwa kanmu solution .Yana fadin Haka ya shige motarsa yyi Reverse ,shi dai Aliyu tsaye yayi Yana kallonsa har ya bar get din gidan hannunsa xube cikin Aljihun wandonsa,Yar ajiyar xuciya ya sauke dama ko kadan bai son Farhaan din ya hadu da Noory ,ya Kuma nemi dalilin hakan Ya rasa.A parlorn ya samu Ammah daga gefe masu decoration ne ke gyara parlorn da wani irin flowers masu kyan gaske ,ya xauna cikin soofas Yana kallon Ammah Yake fadin"duk wannan na menene??"Ammah na murmushi take danna wayar hannunta tana fadin"xan hada waleemar dare ne Yan gidane kurum xaa xo aci Abinci Ayi Addu'a Allah ya kawo Mana baby lfy,dinku nan ka na daki jeka duba Nooriyah din ma tana ciki itada Batool ya bude ido Yana fadin"ita kuma dake Makaranta meya kawota??"Ammah ta hareresa tana fadin"ina ruwanka ,girgixa kansa ya shigayi Al'amarin Ammah Yana karasa jikinsa yin wani sanyi,Yana tura kofar dakin Ammah sukayi ido biyu da Batool waxeer,
Ihun murna ta saki taxo ta wani rungumesa tana fadin"Yaya Mana.!""ina ka shiga inata nemanka,Yaya mun kusa samun baby !"kaji dadin da nake ji Ya jayeta daga jikinsa idonsa na kan Noory wacce take tsaye tana duba kayan da xai saka xuwa anjima.Batool ta kalli nooryn tana fadin kiyi sauri sistr inlaw xan tsaya parlor na jiraki lokaci na tafia da Haka ta fice daga room din,rufe kofar yayi ya jingina bayansa ga kofar ya harde hannayensa Akan kirjinsa Yana kallonta,karaso kaga wane xaka saka aciki yadin xaka saka ko shadda Ammah tace xuwa anjima Mai daukar hoto xaixo."Kunyi magana da farhaan a waya?"Tambayar da yyi Mata kenan."tana girgixa Kai take fadin"Bai kirani ba meya faru Kuma??"Nan ya fada Mata abunda farhaan keso Ayi."ta dago manyyan idonta tana kallonsa,tayi murmushi xuciyarta na bugawa batasan meyasa duk lokacin da aka ambaci saki ba ,sai taji hankalinta Yana son barin jikinta dauriya kurum take ,
"Nifa baxan iya Auren Farhaan Shagari ba batareda ixinin mahaifiyarsa ba,Kuma ni ba jahila bace da xanbi namiji wani wurin A daura Mana Aure."kuskure dukan mu munyi sa Amma wanna shawarar batayi ba gaskiyya."Kai Kuma ka shirya raba Auren mu ina fatan ka shirya kalaman da xaka fadawa Ammah."ta fada tana kallonsa ,karasowa yayi har gabanta Yana kallon cikin idanunta,
Jin tayi tana neman faduwa sabida yarda ya kura Mata ido saurin tarota yayi da wani irin yanayi yayi mata rumfa tana Jin yarda xuciyarsa ke bugawa da wani irin soyayyarta Wanda baisan ta inda ta fara ba,hade fuskarsa yayi da Tata saurin rintse idonta tayi xuciyarta na harbawa da Jin saukar numfashin sa,
Wani irin sonsa na Kara narke Mata xuciya.xatayi magana
Yayi saurin hade bakinsa da nata ido ta bude sosai tana karbar sakonsa,
Wani irin kiss Yake Mata Ahankali yaji xuciyarsa na saukowa daga bugawar da take ,sakinta yayi a hankali ya juya ya nufi kofa batare da ya Kara hada ido daita ba Yake fadamata ta xabar masa dinki da yafi dacewa dashi ta samesa a mota da kayan itada Batool xai sauke su wajen saloon."da Haka ya fice daga dakin duka yabarta da kamshinsa,hawaye taji suna cika idonta meyasa kaddara xatayi Mata Haka,meyasa xata jefota awajen da Bai kamata taxo ba.farhaan Shagari ya cancaci tayiwa soyayyar Aure ba Aliyu waxeer ba...."
Hawaye kawai ke xubar Mata cike da bakin ciki da mugun kishi dake cin xuciyarta, Khaleel waxeer ya riketa sosae Yana fadin"ki dawo hankalinki pls laylah Wai meke damunki ne."Yyi Maganar a Dan tsawace ,cikin ihu take fadin"tun da na aureka Ammah Bata farin ciki da Auren Nan ,Haka Bata Sona Bata kaunata Yaushe ma Aliyu yyi Aure da xata fara son matarsa har haka.komai na business dinta Noory ce kan gaba ,Akan me baxan damu ba.ta fada a haukace tana wani rike Khaleel gamida Fashewa da wani irin kuka,meye abun damuwa aciki duk da Haka bakin fi nooryn samun Albashi sosai ba,Kuma tarairayar da Kika ga Ammah nayi Mata cikine jikinta kin San burin Ammah taga ya'yan mu sai gashi Allah ya kawo,kema hnya abude take Idan kin shirya haihuwar ynxu sai ki daina Shan duk wasu pills na Hana daukar ciki."wani kallo ta rika yimasa,duka -duka shekarar mu nawa da yin Auren kake Maganar ciki da Tara Ya'yah??"toh idan har hakane sai kibari a tarairayi wacce keda ciki,Kuma dole kije gidan Ammah xuwa anjima idan har bakije ba familyn waxeer xasu ga kamar kina bakin cikine ,da Haka Yabar Mata dakin tabisa da wani irin kallo.xama tayi akan gefen bed tana juya maganganun Khaleel waxeer,ya kamata tayi wani Abu xuwa daren nan.tana ta Kiran wayar Areefa Mansoor Bata xuwa ,Kuma tasan tana Abuja baifi sati biyu da gama karatun taba ,ta dawo gida duka......shiya kaisu wajen saloon haka ya jira suka gama ya maidosu gida,Batool kawai ce ya aje agida ,Yana fada Mata ta fadawa Ammah xuwa anjima xasu shigo.gidan su ya kaita wani irin farin ciki ya rufeta ,suna gama parking ta balle marfin motar ta fita da gudu batereda ta jira Aliyu ba,ganin ta kawai sukayi ta fado masu Adama na a tsakar gida tana wanke-wanke Baki Adama ta bude tana kallonta tana fadin"wana ke gani Anan??tamkar Nooriyah,duk da Nooriyah tayi haske tayi kiba Adama ta ganeta sai dai tana tababar itace ko baita bace,mikewa tsaye Adama tayi tana xagaye Nooriyah din da wani irin kamshin Yan gayu da Taji tanayi,Nooriyah ta wara ido gamida Rungumeta duka,Daria Adama tayi tana fadin"da gaske kece Nooriyah kinga yarda kika xama wata hajia ,
Daria Nooriyah tayi da sallama ya shigo cikin gidan Yara biye dashi dauke da Kaya suna saukewa,sannu da xuwa Adama ta shiga yiwa Aliyu tamkar xatayi Masa sujada,
da sauri ta nufi daki ta dauko tabarma ta shimfida masa,kallonsa Noory kawai takeyi da wani irin yanayi a fuskarta Wanda baxai fassaru ba,shima kallonta Yake da idanunsa ya wara ido Yana Mata tambaya da ido Menene???sai ta kwantar da Kai tana girgixa masa Kai,Adama ta dauko hijab tana fadin"Bari na karbo maku Ruwan Sha a bakin titi ,duka yaran basa Nan......."da Haka ta fice daga gidan dukansu suka bita da kallo,Yan mintuna kalilan Adama ta shigo gidan dauke da bakar Leda ta aje agaban su Noory din tana fadin ga ruwa Nan susha,gorar Ruwan swan ne da Kuma lemun fanta.ruwan kawai Aliyu ya Sha ,ya kalli Adama Yana fadin"kawu ya fadamin baya gari Yana Kano."Ehhh hakane ya tafi Kano xuwa jibi xai dawo da yardar Allah,Allah ya kawosa lfy." Aliyu waxeer ya mike tsaye da bottle water A hannunsa,Yana fadawa Adama xasu koma sai an kwana biyu Kuma.Rafar dubu daya ya aje agabanta ta ,ya fice daga gidan Nooriyah ta kalli Adama cike da damuwa take fadin"ummah Safiyya fa tunda mukaxo ban ganta ba,kin San safiya Bata son xama wuri daya tun can dama. Ynxu haka tana gidan kawayenta."mikewa Noory tayi tana fadin"ummah xamu koma insha Allahu xuwa jibi xan dawo idan kawu ya dawo ,da fara'a Adama ke fadin"toh Allah ya kaimu,Allah yay maki Albarka keda mijinki ya Baku xuri'a Mai Albarka a duk inda kuke,ya tsareku da Yan iska da shaidanu,
Har kofar gida Adama ta raka Nooriyah da Addu'a tamkar ta hadeta Dan so."Nooriyah ta kawo sauyi Mai yawa acikin Rayuwarsu,ta kallesa da sauri tana fadin"gidan Ammah fa.ya kalleta yana fadin"gidan Ammah ne gidan Aurenki,
Muje malama ki Samar min lunch yunwa nakeji."ko a kitchen din tsareta yayi duk inda ta wurga idonsa na kanta,a kitchen din yaci Abinci,har Kusan magrib suna tare sai ga Kiran Ammah ya shigo a wayarsa,Yana dauka Ammah ta fara fada,ya kawo Mata Noory Bata jira Mai xai fada ba ta kashe wayar,Koda suka Isa gidan Ammah ana Kiran sallar magrib anyi wani irin kawata parlorn Ammah,koina an axa pics din Aliyu da nooriyah wani pics duk na bikin sune,da sauri Batool waxeer taja hannunta suka wuce sama,shima Aliyu gudun haduwa da Ammah yasa ya juya ya nufi massallaci,Bayan ya fito massallaci sai ga motar farhaan Shagari na shigowa cikin gidan,tsayawa Aliyu yayi har yyi parking.Ya kalli farhaan din Wanda har ynxu kana karantar damuwa a fuskarsa,tare suka jera suka shiga gidan Aliyu,, hop yau xanga noory."xaka ganta bara na shirya muje gidan Ammah ,da Haka ya nufi stairs xuciyarsa yaji tana yimasa nauyi,
Baa jimaba,sai gashi cikin farar shadda da Noory ta xabar masa.har suka karasa gidan Ammah a motar farhaan din bbu Mai magana,kowa da abun dake cin xuciyarsa.kusan tare suka shigo parlorn na Ammah ,kowa idonsa Akan Noory wacce ta hade cikin shigar English gown kalar Army green da mayafinta,tayi wani irin kyau acikin kayan.su Batool waxeer sun sakata tsakiyya sai daukar pics akeyi kida na tashi a hankali acikin parlorn,wasu na xaune wasu na tsaye suna rawa wasu Kuma Abinci suke ci.danna xuciyarsa kurum Yake ganin irin mayen kallon da farhaan kebin nooryn dashi Yana hade wasu irin yawu,Haka noor dinsa ta ciko ta xama macce lokaci daya."Kai talauci balai ne jin ddi da hutu Kuma baiwa ne daga Allah.Farhaan ya russuna Yana gaisheda Ammah,
Batool waxeer taxo taja hannun Aliyu tana fadin Yaya Kai ake ta jira xaayi muna pics,
Haka ta hadasa da nooryn ana daukarsu pics sunyi wani irin kyau Haka sosai suka dace,kishi kamar farhaan xuciyarsa xata fito ganin yarda nooryn ta shige jikin Aliyu ana daukar su pics,duka hankalin su nakan farhaan din musamman nooryn da taga irin kallon da Yake yimata,duk Akan idon laylah waxeer wacce ta koma gefe ta harde kafa tana kallon farhaan din tana sakin murmushi a hankali,Batool ta xuba Abinci a plate ta damka masa a hannunsa tana fadin"Ammah tace kabata Abinci taci karta xauna da yunwa ,tana kula da Baki."Amsar plate din Aliyu yyi tura Abinci Nooriyah kawai take hankalinta na kan farhaan,shima Aliyu ya lura da hakan duk yaji bbu ddi,muje ku gaisa da farhaan.har sun juya xasu nufi farhaan sukaji muryar Ammah na fadin"Ina Kuma xaku xo ku gaisa da ummah da matansu Nasir duka sunxo suna main parlor ba yarda suka iya suka juya suka bi Ammah,Haka ta shiga gaisawa dasu Batool nayi Mata bayanin su daya Bayan daya,kowa da kyautar gift's dinsa,
Ummah ta kalli Aliyu cike da murmushi take fadin"Captain kyautar me xaka baiwa surukuta irin wannan big happiness da tabamu,dan Sosa kansa yyi Yana kwakwalo murmushi,
Aysha waxeer ta karaso gaban Nooriyah ta rufe fuskarta da farin kyalle,ta kalli Aliyu waxeer tana fadin Yaya dauketa muje ka Bata kyautar ."yin yayi tamkar baiji Aysha waxeer ba,sai da Batool waxeer ta fada da karfi tana fadin Yaya masu daukar pics suna jira ,
Daukarta yayi cak!xuwa compound din gidan aka bisu a baya ana sakin shewa Batool sai famar daukar su pics take,har gaban motar Aliyu ya Kai Noory,new model(BMW 7 series)baka wuluk sai sheki take wani irin ihu batool waxeer ke saki tayi hugging din Noory din,idanun farhaan yaji suna yawo akansu sai yaji duka ba ddi,dauriya kurum yake.ummah ce ta rungume Noory tana saka Mata key acikin hannunta,hawaye taji suna cika idanunta.bata san dame xata biya su ba kaunar da suke nuna Mata,ba xato taga Aliyu waxeer ya Jawota ajikinsa Yana subbatar goshinta da bakinta Yana fadin "thank you for d love and everything my wife."pics aka shiga daukarsu,da Haka Aliyu yaja hannunta xuwa motarsa,ya bude Mata front side ta xauna ya rufe, wurin Ammah ya koma Yana fada mata xasu wuce gida kansa na masa ciwo , Ammah tayi murmushi tana fadin ka Sha magani."Kuma ka kula da Nooriyah Naga itama da alamar akwai gajia a tare daita ,ya subbaci hannunta Yana fadin insha Allahu."Nan ya juya Yana yima su ummah sai da safe,ummah ta kalli Ammah tana murmushi take fadin"bbu wani ciwon Kai shi dai Yana bukatar matarsa,itama Ammah murmushi kurum tayi.ganin motar Farhaan yyi acikin parking lot din gidan sa,shima parking yyi .Kusan tare suka fito motar tareda farhaan Wanda fuskarsa ko kadan bbu wani walwala ,gaban Nooriyah din yyi wani irin bugawa ganin farhaan din ,Bata daice komai ba farhaan ya karaso wurinsu Aliyu ya kallesa Yana fadin"mukarasa a parlor da Haka dukansu suka nufi Entrance din shiga gidan,Farhaan ya xauna acikin soofas,yyi crossing leg's dinsa Yana Danna waya batare da yace komai ba,Aliyu da Noory na tsaye a wajen,dakyar Aliyu ya tattaro jarumtar sa Yana fadin xaije yyi wanka da haka ya juya da sassarfa xuciyar sa nayi masa wani irin nauyi ya nufi stairs,Jin tayi kafafun ta nayi Mata nauyi lokaci daya tabi Aliyun da kallo,kallonta farhaan yyi ganin inda take kallo ya mike tsaye ya wani fisgota ta fado kansa duka .matseta yyi cikin jikinsa yasa hannayen sa Yana xagaye kugunta dasu ,Aliyu Yana Juyawa ya hango nooryn cikin jikin Farhaan,wani irin ciwo Yake ji Akan kirjinsa da sauri ya juya ya shige master bedroom dinsa,cikin muryar rada Yake fadin"Ina son wannan kamshin naki my Noor,did you miss me??kamar yarda Nima nayi kewarki ba kadan ba,cikin rawar Murya take fadin"meya haka farhaan Dan Allah ka cikani."ta fada tana kallon cikin idonsa da suka fara canja kala,Kara riketa yyi sosae.wannan karon ba riko Mai sauki yyi Mata ba har da mugunta ya hada Mata."Meyasa xan cika ki,saboda Aliyu Yana kusa??ya fada da muryar kishi."girgixa Kai tayi hawaye na tarar Mata take fadin"ba Saboda shi bane farhaan muna daukar xunubi ne,Akwae igiyoyin Aure akaina."Cikin daga Murya da xafin Rai Yake fadin"sai me nace sai me??"kin manta only contract marriage,meyasa xaki wani damu."Yarda Yake Mata ihu da tsawa jikinta yasa ya fara kadawa,ya Kara damko kugunta Yana fadin."meyasa shi Idan ya tabaki bakya hanasa??"Ya fada Yana kallon cikin idanunta da Yake hango wani Abu acikinsu,ki Amsa min."ta fisge kanta ta shiga Jada baya,shi Kuma Bai fasa binta ba,da mayyun idonsa .kokarin faduwa take yayi saurin tarota Yana fadin"karki Jima kanki ciwo,xuwa Nan da sati daya xan kawo karshen wannan Auren."in har saboda wannan Auren kike Avoiding Dina."da Haka ya saketa ya shafa kuncinta Yake fadin"Ina sonki a Koda Yaushe,da Haka ya fice daga parlorn xuciyarta na bugawa take binsa da kallo,
Da gudu ta nufi dakinta na barci batareda ta kalli dakin Aliyu ba........Ya hargitsa dakin nasa Yana neman takarda da biro kurum lokaci yyi da xai Raba kansa da wannan Auren ko xuciyarsa xata samu sassauci,xama yyi ya Dora pen a takardar,lokaci daya yyi jifa dasu Yana dafe kansa dake neman rabe masa gida biyu ,wani irin Rawa jikinsa keyi jijiyoyin kansa lokaci daya suka mike idonsa ya kada yyi wani irin ja,are you fall in love with her Ali??"wata xuciyarsa ta shiga tambayarsa,da sauri ya dafe kansa cikin ihu Yake fadin"no I'm not fall in love with her."I'm not!"ya shiga maimaita Kalmar hawaye na xubar masa Yana dafe kirjinsa da yakeji tamkar xaya cire,
Jin ihu a dakin Aliyu yasa ta fito nata dakin da gudu ta nufi nasa nakin,Koda ta tura dakin a bude Yake hango Aliyu tayi kan marbles ya dunkule wuri daya tamkar Mai Aljannu da gudu ta nufesa tana dagosa,
Da idonsa da suka fara yimasa nauyi ya dago Yana kallonta,
Lokaci daya hotosu itada Farhaan ya fado Masa,na rungumar da yayi Mata daxu.fisge kansa yyi lokaci daya Yana matsawa gefe Yake fadin"karki tabani karki tabani muguwa kawai !!"meyasa xaki Rungumesa da Ina da Ina ya taba ajikin ki."Ya fada cikin ihun tsawa Yana dafe kirjinsa da Yake Jin tamkar bana sa ba, maganganu Yake xuba Mata cike da kishi ,pls go away !!"bana son ganinki."Jin yyi numfashinsa na neman daukewa dakyar Maganar ke fitar masa,dafe kanta tayi hawaye na xubar Mata ta karaso ta rikesa take fadin"pls kayi shuru Dan Allah."ta fada tana saka sa cikin jikinta duka tana Fashewa da wani irin kuka Mai cin rae,Jin tayi baya numfashi hankalinta yyi mugun tashi dagosa tayi tana Kiran sunan sa,Jin tayi baya numfashi ,da sauri ta ajesa dube-dube ta shigayi a dakin gaba daya ta rude wayarsa ta hango akan mirror dressing da dugu ta nufi wayar,Danna wayar ta shigayi sai dai akwai lambobin security ajikin wayar,aje wayar tayi ta nufi nata dakin da gudu ta dauko wayarta. Sai dai cikin Rashin sa'a Bata da caji Kuma saka wayar caji ma Bata lokaci ne hijab ta saka ta nufi masu tsaron dake gadin gidan ,fada masu ta shigayi hankali a tashe,su suka taimaka aka sakasa motarsa,
da gudu ta shiga motar ta jata da wani irin speed tana barin gidan, mention din Ammah ta nufa ,ko kashe motar batayi ba ta nufi cikin gidan da gudu sauran kadan suyi karo da Khaleel waxeer,yaja baya Yana kallonta xuciyarsa na bugawa.Ammah!""Ammmah."Ta shiga kwalawa Ammah Kira,
Khaleel waxeer ya riketa Yana fadin"meya faru ??''jan numfashi ta shigayi takasa magana.xuciyar Khaleel waxeer na bugawa Yake fadin "kiyi numfashi Noory Ina Aliyu??"kofa ta shiga nuna masa tana fadin"mota!"da gudu Khaleel waxeer ya nufi kofa,Ammah ta riketa cike da sabon tashin Hankali take fadin","meya samu Aliyun.?"hawaye na xubar Mata ta wani rungume Ammah tana fadin"ban sani ba Ammah.baya numfashi.!""likitocine a kansa acikin Asibitin waxeer dakyar suka samu dai-daituwar numfashin sa ,sunyi Mai Allurar barci oxgyen ke rike da numfashin sa,Ammah da Noory suna xaune a wani daki na musamman kowace idonta ya kumbura saboda kuka,har washe gari Aliyu barci yakeyi Ummah ce ta kawo masu break fast karfe takwas na safe ,
Cikin Ammah da nooryn ba wacce ta kalli break fast din,
Dakyar da lallashi Ummah ta samu kowanen su ya Sha tea da ta hada masu,
Dr.Arhaam ne ya turo kofar da sallama A bakin sa da sauri Ammah ta amsa tana kallonsa,ya karaso cikin room din Yana gaisheda Ammah cike da girmamawa,ta Amsa tana kallonsa da alamar so take ya fada mata ya jikin Aliyu,xaiyi magana Khaleel waxeer ya shigo bayansa laylah waxeer ce wacce taci kwaliyya cikin wani uban less Wanda kudinsa xasuyi naira dubi dari da hamsin tana rike da basket,
Wanda kallo daya Ammah tayiwa basket din tasan A restaurant ya fito.. Khaleel waxeer ya karaso cikin room din Yana baiwa Dr.Hannu sukayi musabaha...
0 comments:
Post a Comment