Basuyi minti goma gidan makoki ba suka fito,sabida ko sun tsaya babu wanda ya sansu,sun dauki hanyar wajen gari Areefa wacce itake driving ta kalli Aunty Siddiqa tana fadin"shi malamin naki ya rasa inda xaiyi gida sai a karshen gari,gaskiyya wannan da sake,barazana ne ga rayuwar mu to idan aka sankame mu a hanya fa."wai Aunty Siddiqa haka kike dauriya kina xuwa har Nan tun daga unguwarku??gaskiyya na jinjina maki,kinyi kokari haka hakurinki yayi maki Rana,tunda shegen mijinki yanxu ya daina bin matan waje,an riga an kame maki Abar sai yarda kika yi daita.Areefa ta fada tana sakin dariar shakiyan ci."wanda dole sai da Siddiqa ta saki mumurshi,sunyi sa'a sun samesa sai dai akwai layi........Baki Areefa mansoor ta bude tana kallon manyyan motocin da sukayi parking a kofar gidan da bai wuce daki biyu ba aciki,manyyan hajiyoyi taga suna shiga suna fita.da sauri ta kalli Siddiqa aunty Siddiqa duk wannan manyyan hajiyoyin da nake gani wurinsa suka zo?tayi maganar sounding so very confused."kadan ma kika gani in dai akan aekin malam mai bushasha ne,baya ma harka da kananan mutane,yafi son manyyan hajiyoyi masu kaisa aekin Hajji da umra,auhhh dama zai iya zuwa aekin Hajji kuma yana xuba wannan shirkar,shegen kudi ne dashi har manyyan motoci yana da,to meye Amfanin haka yana zaune cikin irin wannan matsiyaci gidan."Siddiqa ta tabe Baki tana fadin"Ni dai mu shiga kar ayi mana cin layi.da haka suka kutsa kansu cikin gidan,kallonsa kurum Areefa keyi tsoho ne Sosae sai shegen gemun da ya kusa sauka har a kirjinsa fari sol."wata big hajia taga ta aje masa jikar kudi,ya girgixa kudin yana fadin miliyan biyu ne aciki hajia,idan aeki yayi zaki dawo ki cika sauran ladarsa,hajiar ta russuna a gabansa tana famar xuba masa godia,jiki sanyaye Areefa mansoor taja Siddiqa gefen tana fadin"naji yana fadin manyyan kudi aunty Siddiqa nida iyakar kudina baifi dubu dari ukku ba,ki kwantar da hankalin ki,da haka tajasa gaban malam mai bushasha,ya kalli Siddiqa yana fadin."wannan itace kanwar taki??cikin girmamawa take fada masa itace,ya kalli Areefa yana fadin"ta basa hannunta na dama,da sauri ta mika masa hannun ya dade yana kallon hannun,
Kafin ya Runtse ido ya shiga jan tasbahar hannunsa,yafi minti biyar a haka kafin ya bude,yana fadin mekike bukata?"da sauri Areefa ke fadin"dama ina son na shiga familyn waxeer ne,kuma inada ciki so nake duka familyn su yarda da Aliyu yayi cikin,haka ina so na xauna cikin su har lokacin da xan haihu ,ina son na juya yaron da uwarsa,haka ina son a dauki son dunia a ɗorawa cikin jikina musamman uwarsa,ina so Aliyu ya rinka bin duk wani umurnina......."kallonta malam mai bushasha ya tsaya yanayi kafin ya Runtse idonsa ya shiga jan doguwar casbahar sa wacce batayi kama da ta sallah ba ko kadan,dan tashi tana dauke da karafuna a cikinta ,ya shiga ambaton wasu kalaman tsafi ya bude idonsa yana kallon Areefa mansoor yace ladan aekin miliyan daya da dubu dari biyar,ta xare ido tana kallon Siddiqa mansoor xatayi magana Siddiqa ta rigata tana fadin toh Malam xamuje mu hada kudin nan da kwana biyu xamu dawo,daga kai yayi alamar ya gamsu.suna fitowa ta kalli Siddiqa mansoor hankali tashe take fadin"kin haukace ne Aunty Siddiqa Ina xan samu wannan kudaden yanxu??"Ni dai na fasa gaskiyya ,
Baxan iya wannan hasarar ba,xanje kawai na fadawa Ammah.nasan baxata goyi bayan zalunci ba."Siddiqa ta fashe da daria tana fadin"Ashe kuwa xaki rasa sa,wannan karon Siddiqa mansoor ce mai tukin,tana fadin"ban san baki da hankali ba sae yau Areefa kina tunanin kinga sirrinsa kuma kice kin fasa aeki dashi baxai ma yuyu ba,kibari xanyi magana da Ahmad ko aron1 miliyan zamu samu a wajen sa ,bakin ce kina da dubu dari ukku a hannunki ba,ba'a rasa dari biyu a hannun na ba sai a hada ba.ta gama da matsalar Aliyu sauran Sufyan mansoor da Abbanta,tasan taurin ran Sufyan mansoor xai iya kashe Aliyu waxeer idan yaji akwai cikin Aliyu waxeer a tare daita,hanyar tsayar dashi kawai xata nema.har suka kai gida ta rasa madafa,har Farhaan ya cika kwanakki ukku da rasuwa kullum su Ammah na zuwa gidan gaisuwa basa dawowa Sai da magrib haka sun samu zuwa ganin mami A asibiti itama Alhmdullh tana karbar sauqi a wajen Allah .sai dai har yanxu bata magana sai dai ta rika bin kowa da kallo ,sai kuma hawayen da basa gajia da sauka a kan fuskarta,ranar da Nooriyah taga mami a matsayin mahaifiyar Farhaan Shagari wandda Farhaan din gaba dayan sa mami ne,mutuwar Farhaan ya dawo mata sabo ,mota ta koma da gudu.ta shiga rera sabon kuka.cikin kwana biyu suka gama hada kudin suka damkawa malam mai bushasha yana kara tabbatarwa da Areefa mansoor bbu ita babu da nasanin aeki tare dashi,wani bakin kwaliyya ya bata yace kartayi wasa dashi duk ranar da ta shirya shiga familyn waxeer kai tsaye xata shiga ta tabbata ta shafa kwallin nan acikin idanunta,Haka duk bayan kwana bakwai zata rika shafasa, karta yi kuskuren ketare ranar shafasa,
Damke kwallin tayi a hannunta tana yimasa godia,tun kafin su shiga mota ta wani rungume Siddiqa mansoor tana fadin"ina farin ciki ina farin ciki."Aunty Siddiqa ,ta fada sounding so very happy,Siddiqa mansoor taja cheek's dinta tana ware mata ido,itama murmushi dauke a fuskarta,shirin tafia Abuja sukayi dan tun karar Abba da kuma Sufyan mansoor.
Zuciyar Areefa ta riga da ta bushe ko Sufyan mansoor bai isa ya dakatar daita ba,da murna Aunty ta tarbesu wacce ke auren mahaifinsu tun bayan rasuwar mahaifiyarsu,Aunty ta kalli Areefa tana kama baki take fadin"kin ga yarda Kaduna ta karɓe ki naga kinyi wani uban kiba da kumatu,
Me Siddiqa mansoor ke baki, murmushi kurum Areefa tayi tana fadin"Aunty Yah Safwan fa,tun safe bamu hadu ba.daga waya tayi ta kirasa bai daga ba ta kara kira nan ma bai daga ba,duk tabi ta shiga damuwa,tana kallon kofa sukayi ido biyu da Sufyan mansoor ,wanda da ka gansa kaga fuskar Areefa mansoor shima fari ne sol"tamkar balara be,
Ya bude hannuwa gamida ware mata ,ido murmushi tayi gamida make kafada ya karaso cikin parlorn yana fadin."ku wannan irin tafiya haka,kuma kina ta kirana a waya ,muna tare da Adee shiyasa ban daga ba.......toh fadamin yar gidana meya faru ina son Jin good news,shi wannan mutumen da kika bi kika nacewa ya shirya yanxu ko har yanzu."hawaye yaga suna cika idon Areefa mansoor tasan sune weakness din Sufyan mansoor,ke lafia meya faru??"duk yabi ya rude,siddiqa Mansoor ta kallesa ido cikin ido tana fadin"Yaya cikine jikin Areefa kuma cikin Aliyu waxeer."girman kalma Sufyan mansoor yakeji tana masa nauyi cikin kirji,cikin shege ajikin kanwarsa."ya mike a fusace ya xsbgawa Areefa shegen mari ya shakota lokaci daya,tana jin shaƙar da yayi mata tana tabata Amma ko kadan baxata karaya ba,mekake yi haka yaya akwai ciki ajikinta kayi hakuri ka saketa kar kayi mata illah,jikin Safwan mansoor babu inda baya rawa,haka tana hango soyayyarta da kuma tashin hankali lokaci daya acikin idanunsa,sakinta yayi ya juya Yabar dakin ba tareda ya kara kallon su ba,na gama da matsalar Sufyan mansoor bana tunanin Abban,sabida nasan xai fadawa Abban.....har ishai basu kara saka sufyan mansoor a idonsu ba,
Har washe gari,hakurin Areefa har ya kare da safe ta gaisheda Abba sai dai bai nuna mata komai ba,,hakan na nufin Sufyan mansoor baiyi magana da Abba ba,
Wlhi na gaji ki tashi kawai mu kama hanya na karasa saurin aeki na,,meyasa bakya bin komai a hankali."komai kiyi tayi masa gaggawa."Siddiqa ta fadawa Areefa tana kallonta ta dakune fuska tana fadin"na gaji da wannan jiran Aunty Siddiqa kawai mu koma Kaduna idan ya gama fushinsa sai ya samemu acan,abu daya ne baxan iya dauka ba,yace xai taba Aliyu..........."baxan iya daukar hakan ba ina son kayana a haka,kuma bana son yace xaiyi Shari'a da Aliyu Dan wallahi duka arzikin gidan nan xai kare Ni kawai ki fada masa kamar yarda muka tsara ba shikenan ba."wayar Siddiqa mansoor ce ta fara ring ganin me kiran ta kalli Areefa da sauri tana fadin"Yaya ne.....da sauri Areefa tace ki daga kiji me xai ce,ku same mu a parlorn Abba da haka ya datse kiran,
Toh tashi muje maybe ya fadawa Abba komai,sun samu Aunty a parlorn tana haɗawa Abba tea,ko kadan Areefa bata so hakan ba,duk harkar ta bata son yinta da Aunty,kafafunta taji suna rawa ganin irin kallon da taga Abba nayi mata,haka ta kasa karasawa cikin parlorn,Sufyan mansoor ya daka mata tsawa yana fadin"akwai sa'anki anan da baxaki karaso ba,da rarrafe Areefa ta karaso ta xauna akan carpet,cikin rawar murya Abba ke fadin"da gaske ne da gaske ne Areefa akwai cikin shege jikin ki??"dagawa Abba kai tayi,ya kalli Siddiqa mansoor yana fadin"baxata zauna min a gida ba da dan shege ya kalli Aunty fuska bbu walwala,
Yake fadin a hada komai nata yau baxata kwanar min a gida ba,
Ku kaimin shegiya kauye kai Safwan ka fara shiri yanxu,ihu Areefa ta fasa tamkar mai jinnu take fadin"baxan je kauye ba Abba !!"kauye kauye fah."ta fada tana fashewa da kuka,
Cikin sanyi murya Aunty Siddiqa ke fadin"Abba ae idan aka kaita can asirin mu xai tonu kasan mutanen kauye da saka ido,Ni xan bada shawara,mexai hana akaita gidan su wanda yayi mata cikin,suyi renon tsiyarsu acan idan ta haihu dole ya yarda ya Aureta."haka ya kamata ayi Abba dan baxai ci bulus ba wallahi ."Sufyan mansoor ya fada yana kallon Abba,daga kai Abba yayi yana fadin"ku fara shiri har saratu tabiku ku damka masu ita,kar ta dawo min a gida har sai ranar da naganta da auren yaron nan akanta.Alh.mansoor ya fada da bakin ciki a muryarsa,har suka isa Kaduna acikin motar sufyan mansoor kallonsu kurum Aunty keyi,haka kawai take ji ajikinta ba gaskiyya Areefa da Siddiqa suka fada ba,yarda tasan Aliyu waxeer da mutunci sa da martabarsa,xaiyi wuya ace dan cikin jikin Areefa nasa ne,sai dai yawon da takeyi da maxan banxan da ta saba hurda dasu,suka yi mata ciki ita kuma ganin manyyan kudin dake ga Ali da familyn su xatace cikin jikinta nasa ne ,a gidan Siddiqa Safwan ya saukesu yana fadin"sai da dare suje familyn waxeer,da dare shine dai-dai haka kuma yafi sirri,
Saiti daya tayi na kayan da xata tafi dasu gidan waxeer ,sauran tarkace tasan daga baya xata mallaki fiye ma da irin su a familyn waxeer,ko abincin ta kasa ci duk da cikin bai bata wani wahala sai dai yana yawan sakata cin abinci da kuma kwalama.tun bayan Rasuwar Farhaan take zaune a gidan Ammah,suna ta xuba ido suga me Ammah xata yanke akan auren su,har yanzu taki magana haka ta hana nooryn ta koma dakinta,Matakin farko da Ammah ta dauka shine hukuncin rabasu da junan su,daga ranar da akayi sadakar ukkun Farhaan,ta hana Aliyu kwanar mata a gida,
Shi kuma yaki bude baki ya fadawa Ammah matarsa yake so,xuba ido kurum Khaleel waxeer yayi yana ganin sabon salon da Ammah ta dauko,da taga Aliyu ya shigo mata parlor inhar noory na xaune a wajen xata mata umurnin ta tashi ta wuce daki.ba karamin hurting dinsa hakan keyi ba,ko dan kisising din da yake samu yana rage zafi Ammah ta rufe ko wace kofa,
Itama a bangaren nooryn hakane,sosai take kewar mijinta,duk da mutuwar Farhaan yasa ta dan rage kula Aliyun,Haka karya take tace batayi missing kowane happy moments dinsu da sukayi enjoying tareda Aliyu ba."ko yanxu tana kitchen Bayan magrib suna shirya abinci dare itada Ammah,mai aekin ta
Nana ta shigo wacce ke yiwa Ammah wanke-wanke kwata-kwata yarinyyar baxata wuce shekaru goma sha ukku a dunia ba,da ladabi take fadawa Ammah tana da baki.Ammah ta kalli noory tana fadin."bari taje ta duba da haka ta fice daga kitchen din,Jin tayi anyi hugging dinta ta baya,wani irin ihu ta saka da sauri ya rufe bakinta cikin sanyi murya yake fadin"ke nine fah."Jin kamshin turarensa yasa ta sauke ajiyar xuciya ,ya dawo gabanta yana kallonta da idonsa da suka fada lokaci daya,
Da sauri ta kalli kofa tana tunanin ta ina ya shigo,dan Allah ka tafi kar Ammah taxo pls,ta fada tana kallon kofa,make kafada yayi yana hadata da jikinsa,yake fadin"Yaushe kika xama muguwa haka."ta bude ido tana kallonsa,ba sai ki fadawa Ammah gidan mijinki xaki koma ba,
Kinji yarda nayi missing manyyan kayana,ya fada yana tsare kirjinta da ido,
Gabanta na mugun faduwa take fadin"dan Allah ka rufamin Asiri Aliyu kar Ammah taxo ta ganmu,zo muje gida."ya fada yana jan hannunta ,fisge kanta tayi cike da tashin hankali take fadin ka rufamin Asiri Aliyu."wai meyasa kake haka?"ya girgixa kai yana fadin"so kike na mutu kenan?ya isa ga gas ya kashe gas din ya dawo gabanta ya shiga kokarin cire botin farar shirt din jikinsa yake fadin"babu damuwa ko acikin kitchen xan iya shan kayana kin ga idan Ammah taxo ta ganmu a haka ,sai tayi tunanin bani matata .da gudu taxo xata bar kitchen din ya wani fisgota ya hade ta da bango,yana kaima wuyanta wani irin deep kisses,lalubar xip din rigarta ya shigayi ya xugesa iya karfinsa,xatayi masa musu ya hade bakinsa da nata,Haka hannunsa ya sa cikin rigarta ya shiga murxa abunda yafi kauna da so a dunia,wani irin rikesa tayi tana jin leg's dinta na kasa daukarta.sunfi minti goma a haka babu abunda ke tashi acikin kitchen din sai saukar breath dinsu,a haka Ammah tayi mugun gani.da sauri taja da baya tana buga kofar,
Fisge kanta tayi da sauri tana fashe masa da kuka,tana girgixa kai take fadin"shikenan Ammah ta ganmu,Ya shafa sumar kansa yake fadin"duk ddin da kika gama sha yanxu sai ki bude baki kina kuka,ya dage kafada yana fadin"Allah yasa Ammah ta ganmu na fison haka,ya fita daga kitchen din Yana fadin"ta hado masa black tea Yan......kasa karasawa yayi ganin irin kallon da Ammah keyi masa,juya kaxo da matarka muna da baki da haka Ammah ta juya tabar wurin.....
Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
Idan baki biya ba kika karanta ban yafe ba."
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma'u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar#08086207764
*The game has just started now,who is ready for d actual Journey???"*
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: 29
Sosae Ammah tayi farin ciki da zuwan su,ta kalli Aliyu tana fadin"yanxu nake xancen Nooriyah a raina,na xata ma jikin har yanxu."Basu dade da xama ba sai gasu Khaleel waxeer shida Laylah,itama kwana biyu bata shigo wajen Ammah ba ulcer ta sakota gaba.gaisheda Ammah sukayi dukan su,Ammah ta kalli laylah tana fadin"Ya jikin nata hop ta samu sauqi."ciki-ciki laylah ke fadin taji sauki,
Sai da sukayi ishaai Ammah tace su tsaya suci abincin dare tare daita,ta kalli noory tana fadin"zata iya cin tuwon semo ko a girka mata wani??"girgixawa Ammah kai tayi dama can tuwon semo ba cimarta bace,Ammah ba sai anyi ba inada pizza gida idan naje ita xan ci da yougout ,,Kin tabbata zai kosar dake??"daga kai tayi cike da jin kunyar Ammah,typing Khaleel waxeer ya shigayi a wayarsa ya turawa Aliyu..."mekake jira buddy ka kashe boss Dan Allah ,wai meke damunka idan Ammah ta gano akwai matsala kasheka xata yi babu ruwana."jin sako ya shigo a wayar Aliyu yayi saurin duba wayar,da sauri ya kalli Khaleel waxeer ya ware masa ido gamida bude hannuwa,kallonsu kawai laylah keyi.Nooryn ce ke serving kowa,da gangan laylah ta kwantar da bottle water a dai-dai wajen da nooryn take,noory ta daga kafa dan isa ga Aliyu waxeer taji ruwa ya jata,da wani irin sauri Aliyu ya tarota ta fado kansa gaba daya.Ammah na dafe kirji take fadin"meye haka meyasa bakya bin A hankali Nooriyah,Aliyu yabi ruwan dake kwance kan marbles da mamaki lokaci daya ya kalli laylah ta sha toka gamida dauke kai,da sauri Ammah ta kama hannun nooryn ta zaunar daita,ta kalli laylah tana fadin."ta tashi tayi serving Aliyu Nooriyah ta xauna ta huta,bakin ciki tamkar xai kashe laylah waxeer a wajen.........Haka suka karasa cin abinci tana kunci,sai kusan goma kowa yayi shirin tafia,suka yiwa Ammah sai da safe,A mota dukkan su shiru suka xauna,sai ga kiran Farhaan Shagari ya shigo a wayarsa ,kin dagawa yayi dan har yanxu bai sauko daga fushin da yayi da Farhaan Shagari ba,wani irin barci takeji yau duk taji bata jin ddin jikinta haka gabanta taji yana yawan faduwa,wanka kurum tayi tabi lafiar gado,shima a bangaren Aliyu wanka yayi ya duba sako a email dinsa,sai kusan 12 ya kwanta.shima bai dade ba yayi barci,harbin bindiga kawai sukeji kusan lokaci daya mami da daddy suka bude ido,cike da tashin hankali mami ke fadin"daddy bakaji karar bindiga ba,da sauri Alh.omar Shagari ya sauka kan bed yaje ya leka ta window,da sauri yaja da baya yana xare ido,mami ta dafe kirji tana fadin yan fashi kou daddy??"da sauri ta nufi kofa tana fashewa da kuka tashin hankali take fadin"Daddy Farhaan da Jamila, daddy ya jawota Yana fadin".ki natsu Maryam,hawaye na xubar mata cikin tashin hankali take fadin"Jamila daddy."da sauri daddy ya dauko wayarsa ,ya shiga kiran commissioner da yake abokin sane,
Kira wajen 3 yana yi masa bai daga ba,cikin tashin hankali mami ke fadin"bai dauka ba daddy."ta fada tana rufe bakinta,
Da sauri mami ta saka Hijab ta bude kofar batareda ta jira mai daddy xai fada ba,shima akwai jallabiya a jikinsa ,yabi bayan mami da sauri dakin Jamila suka shiga bugawa a hankali,dama kuma Jamila bata dde da kwanciya ba.so barcin nata baiyi nauyi ba,ta bude kofa tana kallon mami da daddy gabanta na faduwa take fadin"mami meya faru??"Barayi jeki ki canja kayan jikin ki da sauri Jamila ta koma daki cikin minti biyu ta xura Hijab ajikinta babu inda baya rawa cikin jikinta,daddy ya kalleta yana fadin"maryam ki tsaya tareda Jamila bara naje na duba Farhaan,
Cikin tashin hankali mami ke girgixa kai take fadin"baxan iya ba daddy pls muje tare....Yarda mami yaga ta daga hankalinta ,
Yasa duka suka nufi bangaren Farhaan zuciyarsu na bugawa,
Su bahago na hango tahowar su dashi da sauran yaransa suka fito daga mabuyar da sukayi a bayan flower's ,suka zagayesu da manyyan bindigogin su a hannu,
Kowane ya rufe rabin fuskarsa da bakin kyalle,cikin karfin hali mami ke fadin"dan Allah kuyi hakuri ko me kuke so zamu baku,Ina yaron gidan nan wajensa muka xo."cikin rawar murya mami ke fadin"Bayana yayi tafia,lokaci daya bahago ya fisgo Jamila wacce ke bayan daddy,yasata cikin jikinsa yana fadin."xaki fadi inda yake ko sai na yaga mutunci yarki a gabanta,lokaci daya hawaye suka wanke fuskar mami,cikin rawar murya take fadin."dan Allah kuyi hakuri kar kuyi mata komai,haka suka saka su gaba har part din Farhaan,tsaye suka samu Farhaan acikin parlor Shima karar bindigar da yaji ya hanasa kwanciya,koda akayi harbin yana parlor ,baiyi zaton harbin ta cikin gidan su bane."A fusace ya karaso gabansu ganin sun rike Jamila,daga hannu yayi xai kaiwa bahago duka ,bahago ya rike hannun nasa,Fashewa da kuka mami tayi ta xube a gabansu tana rokonsu da Allah kar su taba mata ya'yah,bahago ya mikawa Farhaan Shagari hannu yana fadin ya basu wayar hannunsa,wani kallo ya shigayi masu .mami ta daka masa tsawa tana fadin"kaba su mana,
Mika masu wayar yayi dama tana hannunsa,
Laptop Dinka??har dakin barcinsa suka tasa shi gaba ya dauko laptop acikin dakin barcin nasa ,suka rufe mami,daddy da Jamila.suka tasa Farhaan gaba har tsakiyyar parlorn suka ɗora masa bindiga da mugun shock Farhaan ke kallonsu,xai yi magana yaji bullet gefen kirjinsa,jin tashin bindiga yasa mami ta fashe da mugun kuka,tana dukan kofar da duka karfinta, sun kashesa daddy sun kashesa ."!"Addu'a kawai daddy yake a ransa gashi garin sauri ya baro wayar daki,suna ganin Farhaan din ya fadi sukayi takansu ,na daina jin motsin su
Farhaan mami ta shiga kwalawa kira da dukkan karfinta tana fadin yaxo ya bude kofar,sulalewa mami tayi a wajen a sume........cike da wani irin tashin hankali Jamila tayi kanta,wani key ya shiga nema a dakin na Farhaan dakyar daddy ya samo sa, addu'a yake Allah yasa basu bar key jikin kofar ba,
Shi kansa daddy jikinsa bbu inda baya rawa,yana jin key din ya shiga ya sauke ajiyar xuciya,da gudu ya nufi parlor sai dai turus ya tsaya a wajen ganin Farhaan din kwance cikin jini. zuciyarsa yaji tana bugawa , jin yyi wani abu na tsaya masa a wuya.........kusan karfe shidda na safe mutuwar Farhaan babu inda bata xaga ba,tun karfe hudu na Asuba commissioner yake gidan daddy shida yaransa,sosai ya ta baiwa daddy hakuri na rashin daukar wayarsa ,ya sata a caji barci ya daukesa,shima baya gari a ranar ya dawo.duk wani bincike sunyi basu samu komai akan mutuwar Farhaan Shagari ba,sai dai commissioner din ya tabbatar da turosu a kayi,ta yaya zasu karbi wayar hannun Farhaan da kuma laptop kadai,tambayoyi ake yiwa daddy sosai wasu ya bada amsa wasu yayi shiru,shi kansa daddy dauriya kawai yake ga mami kwance gadon Asibiti ,wacce har yau bata san inda kanta yake ba,Yarda Ammah taga ya shigo mata a gida da safe yayi mugun daga hankalinta,Ammah ta kalli Agogo kusan karfe 7,ya xube a gaban Ammah duk dauriyarsa ya kasa rike hawayensa,ammah ta shiga girgiza sa tana fadin"meya faru ina Nooriyah meya sameta ,yana girgiza kai yake fadin Ammah."Besty Farhaan, cikin tashin hankali Ammah ke fadin meya samu Farhaan din'' .Ammah ki cemin barci nake ki tashi ne dan Allah baxan iya daukar rashin sa ba,ki fada masa yanxu yaxo xan sakar masa noory ki bani biro da takarda Ammah.,,salati kawai Ammah keyi maganganun Aliyu din na taba ta,open ur eye's Aliyu..''Ammah ta fada tana daka masa tsawa,ya kalli Ammah yana girgiza kai yake fadin.''xan hakura daita saboda farin cikin sa Ammah .rungume Ammah yayi yana fashewa da wani irin kuka mai fitowa tun daga karkashin xuciyarta,sai jikin Ammah yayi sanyi bata taɓa ganin Aliyunta haka ba bata taɓa ganin sa haka ba,
Shima Khaleel waxeer agigice ya shigowa Ammah ta kallesa tana fadin.''kayi min bayani Khaleel kar yasa zuciyata ta buga .
Ammah dama barayine suka kashe Farhaan Shagari."kabbara Ammah tayi Aliyu ya nufi Khaleel ya rikesa yana fadin Yah leel pls ka fada mata bani ne sanadin mutuwarsa ba,ka fada masa dan Allah ya dawo xan saki noory ya Aureta baxan iya jure rashin sa ba,wai Aliyu ka haukace ne da kake maganar sakin matarka sabida abokinka."Khaleel waxeer na girgiza kai yake fadin"kara ya fadawa Ammah gaskiyya kowa ma ya huta ,cikin minti goma Khaleel ya mata bayanin komai,kallon su kawai take, Khaleel ya rike hannayen Ammah yana fadin"dan Allah Ammah ki dauki abun nan da sauqi Ammah na girgiza kai tana masa wani irin kallo take fadin"wannan abun kake fadin na dauka da sauki ,mikewa tsaye Ammah tayi jin tayi dakin na juya mata saurin riketa Khaleel yayi ya zaunar daita gefen bed,jeka zo min da Nooriyah yarda Ammah yaga tayi yasa ya juya baiyi gardama ba Yabar Room din,tana moping parlor taji ana Danna door bell,Sama ta koma ta sako Hijab taxo ta bude kofar ganin Khaleel waxeer yasa xuciyarta tayi wani irin bugawa.ta gaishesa da ladabi,bai kalleta ba yake fadin"taxo Ammah na neman ta,
Talkami kawai ta xura a kafarta tabi bayan Khaleel wanda har ya nufi motarsa,tun a falon Ammah taji xuciyarta na tsinkewa, kasa ta xube tana gaisheda Ammah,Ammah ta amsa tana kallonta.
Karfin hali Ammah tayi na fadin"Abokin Aliyu ne ya rasu nasan bakiji labari ba,ga mijinki nan duk yabi ya daga mana hankali,
Dafe kirjinta tayi tana xare ido hawaye na taruwa a idonta take fadin."Farhaan !"Farhaan ,sai kuma ta fara ihu,ganin su ukkun sun tsaya kallonta ta ɗora hannu akae tana fadin"dan Allah ku fadamin ta yarda xan gane kuce wasa kuke,
Wlhi Ammah xan fada Maki gaskiyya,komai da komai na Aurenta da Aliyu ta fadawa Ammah,har cikin da ake karya tana dashi duk bata da,baki bude Ammah ke kallonta ........kenan da gaske ne??"ta nufi Aliyu da wani kalar tashin hankali tana fadin"kace wasa ne dan Allah ,na san yayi komai cikin fushine Amma ba halinsa bane,kai ka sani ba halin sa bane."Ammah ta sauke ajiyar xuciya cike da jimami,ta kalli Khaleel waxeer tana fadin yaje da Aliyu su shirya dan samun jana'iza ,suma zasu shirya suxo gidan gaisuwar,ta kalli Aliyu cikin kakkausar murya tana fada masa ya dawo hankalinsa yanxu,kar kuma ace shine ya tura aka kashe Farhaan din tunda har sun samu sabani,kana jina Khaleel karka barsa ya daga daga inda kake,ka tabbata kana tare dashi.noory ta bisu da ido hawaye na xubar mata,wani irin zafi xuciyarta keyi mata da gaske Farhaan Ya rasu."??wani xaxxabi taji yana cin karfinta,kusan karfe takwas da rabi tana kwance kan gadon Ammah,ta dunkule cikin duvet Ammah ta shigo dakin,da mug a hannunta,ta kalli Nooriyah wacce idanunta har sun canja sabida kuka.
Ammah ta xauna gefen bed tana fadin"ta tashi ta daure tasha tea,da sauri noory ta shiga girgiza kai hawaye na kara tarar mata ,take fadin"na koshi Ammah ,to mekika sha zaki ce wani kin koshi."bana son musu tashi ki shanye kibani cup,Bata son yiwa Ammah musu ,ta karbi cup din ta kafa kai bata sauke ba sai da ta shanye duka tea dake cikinsa,da sauri ta koma xata kwanta Ammah ta dakatar daita,tana fadin ta bari ta huta sa'annan ta kwanta.har kusan 12 tana kwance a gadon Ammah,sai da akayi sallar axxahar suka shirya duka familyn waxeer suka nufi gidan gaisuwa,laylah sai kallon noory take dake famar sharar kwallah ta tabe Baki,
Tayi bakin cikin rasuwar Farhaan Shagari, kenan yanxu noory ta samu auren Aliyu waxeer a bagas,
Ammah na rike da hannun nooryn cikin mota take fadin"so kike mutane su fahimci wani abu a fara zargin ki kuma?''da sauri ta shiga goge hawayen idonta,ki natsu dan Allah Nooriyah kar mutane su fara zargin wani abu ki samu a matsala,da haka suka fita daga motar suka nufi cikin gidan,kai tsaye part din Mami suka nufa,yan uwanta kawai ne da yan uwan mijin sai Salma Shagari,mami har yanxu tana kwance a gadon asibiti,Ammah har magrib suna a gidan sai da akayi sallah suka tafi,kowa cike da al'ajabin rasuwar Farhaan din,
Dakin Ammah ta wuce kai tsaye,batareda ta tsaya parlor ba kukan da taji yana shirin taho mata yasa ta rufe bakin da gudu ta nufi toilet.....Ammah ce ta tsare Aliyu da plate a hannunta na white rice da stew ,da sauri ya shiga girgiza wa Ammah kai yana jin zuciyarsa nayi masa wani iri ,Ammah bana jin yunwa idan naci xanyi amai."Ya fada babu wani walwala a fuskarsa,Ammah ta daure fuska tana fadin"ina wasa da kaine??"girgiza kai yayi buda baki yyi Ammah ta shiga basa,kusan rabi yaci ya fadawa Ammah idan ya cigaba daci xaiyi amae,kusan karfe goma ya shigo gidan Ammah ,kallonsa Ammah tayi tana fadin"baka kwanta ba.
Ya girgixa kai yana fadin"baxan iya kwana acan ba Ammah ,toh ka shiga ciki matar ka na nan ,itama xaxxabi take tun safe ,amma ta sha magani.gabansa ya fadi shi sai yanxu yama tuna da Nooriyah yana ta zama a parlor tareda Ammah har Kusan goma da rabi Ammah tace yaje ya duba matarsa,tura kofar dakin yayi can tsakiyyar bed ya sameta ta dunkule waje daya,rufe kofar yayi ya nufi kan bed .duvert din ya shiga ja,sukayi ido biyu dashi da sauri ta Runtse idonta xuciyarta na harbawa,
Murya can kasa yake fadin"Ya jikin ki??"kin ci abinci murya can ciki take fadin"ta samu sauqi kuma taci abinci da haka ta Runtse idonta ta matsu Yabar gaban ta
Shima kamar yasan abunda ke ranta bai takura taba yayi kwanciyar sa akan duguwar soofa din dake dakin,ya rage hasken fitila.dukan su cikin wannan daren babu wanda yayi barcin kirki,washe gari koda ta tashi bata gansa a dakin ba......har kusan 10 bata ga alamar shigowarsa ba,itama kanta dake ciwo tana ta kwanciya a daki.
Areefa tana ta kallon Siddiqa mansoor cike da takaici,wai na tambayeki mana Aunty Siddiqa Wai Farhaan kun hada jini dashi ne,xaki dauki mutuwarsa duk kisa Aranki,Ni dai wlhi bana jin dadin haka,bana son matsala ko kadan dan na girmi kowace irin matsala a rayuwar nan,idan kin shirya ki fito muje gidan gaisuwa ,sai mu wuce wajen malamin."tayi maganar in I don't care manner's!"ita dai Siddiqa batace komai ba ta koma daki ta dauko Hijab dinta,ta dawo parlor tana kallon Areefa din daga sama har kasa take fadin"ba dai haka xaki gidan gaisuwa ba ,na rokeki ba danni ba ki saka Hijab,Areefa tayi wani irin juya ido nacin Aunty Siddiqa na damunta take fadin"mayafin da na saka fa."gidan gaisuwa fa gidan gaisuwa Areefa."tayi maganar da karaya a muryarta ,bakya tunanin a gidan mutuwa kema Allah ya dauki ranki.."tsaya anan dan Allah karki karasa ki daina yimin fatan mutuwa sabida saka Hijab,ki bani naki na saka dan kin san ko acikin kayana babu Hijab,sallah ma da dogayen riguna nake yinta.har suka isa gidan Gaisuwa Areefa na mitaa....
Take Note.!"
Team# bati Reader's ban San ku ba ban san a wace dunia kuke ba,kuna karanta hakkin da ba naku ba batareda ko sisin ku ba,ba sai ku Rufe bakin ku ba sai kuka kasa yin haka sai xagi da cin mutunci,nida hakkina ku hanani magana,baku san ya nake squzzing duk wani free tym da nake dashi dan nayiwa wanda suka biyani dan faranta masu ba.sun san wahalar da ake sha shiyasa suka biyani hakkina tun kafin su karanta,idan na xalinci duk wacce take karanta min book batareda ta biya ba,tana kuma xagina a banxa Allah ya isar mata idan kuma kuka xalince Ni ya Rabbi ka saka min tun a duniya,
Haka wallahi tallahi duk wacce ta karanta koda kalma daya na book din nan,banda wanda na bayar a matsayin kyauta Allah ya isa ban yafe ba..
Littafin waminal Hoob na kudi ne #500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma'u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan layin..09060259200
Shaidar biya ta wannan layin#08086207764..
TEAM#WM
TEAM#NOORYALI FOREVER❤️
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: 31
Kallon Areefa mansoor Yake with so much shock,tashin hankalin da yake ciki baya faduwa,ba zato suka ga Aliyu waxeer ya fisgota ya bata mari Hagu da dama kafin ya shakota,kara ya kasheta da ta cinnawa familyn waxeer wuta,da sauri Sufyan mansoor yayi kansa sai dai shaƙar da yayi mata bana wasa bane,tamkar ba namiji ba haka ya zama ya kasa kwatar kanwarsa a hannun Aliyu waxeer,ya isa ga Ammah yana fadin"ki yiwa mahaukacin yaronki magana rai biyu zai kashe idan wani abu ya sami kanwata shima sai na kashesa baxan jira hukuma ba,
Lokaci daya Ammah ta share hawayen idonta ta nufi Aliyu ta fisgosa lokaci daya ta wanke fuskarsa da mari,xaiyi magana ta Kara xabga masa wani marin.wani irin ciwo kirjinta keyi mata dauriya kawai take a gabansu, fadamin gaskiyya da gaske cikin dake jikin Yarinyyar nan naka ne ko bana naka bane.??"Juya girman ƙaddarar da ta canja masa rayuwa yanxu -yanxu yake har Abada baxai yafewa Areefa mansoor girman laifin da tayi masa ba,Kallon noory kawai yake wanda ko zai samu hop a wurinta tana zaune akan rug,da alama tafi kowa shiga tashin Hankali,baxa kayi magana ba??"Ammah ta fada tana daka masa tsawa,sau kusan ukku yake so ya buda baki yayi magana ya kasa ,
Ga maganar yana jinta aransa fitar ta ya kasa.
Hawaye yaji suna cika idonsa lokaci daya,meke damun sane??""Kar ya dauki girman laifin xina ya ɗorawa kansa,kallon Ammah ya shigayi yana girgiza kai, kallon sa kawai Noory keyi addu'a kawai take aranta ya ƙaryata ba cikin sa bane,shurun sa ya tabbatar mata da Areefa mansoor gaskiyya take fada,wani irin ciwo taji kirjinta nayi ciwon da duk wata macce wacce ke son mijinta da kishinsa xatayi duk lokacin da taji Aliyu waxeer ya ambaci sunan Areefa mansoor a gabanta take jin wannan ciwon,haka ta sha jin yarda Aliyu waxeer ke fadin"Yana son Areefa a gabanta ko a bayan idonta,baya shakkar fadin haka .hawayen Ammah sun kasa tsayawa tana gogesu wasu na xuwa,shurun Aliyu ya tabbatar mata da gaskiyya Areefa ta fada,Ammah ta kalli Aunty wacce ta dan ji tausayin Ammah,wanda uwa kawai ce xata ji irin wannan ciwo."ku taso muje gidan baffan sa,
Ammah ta kallesa ido cikin ido take fadin"ka wuce muje kayi masu jagora su maimaita a gaban uban naka.Wani irin kuka yaxowa noory lokaci daya Rufe bakinta tayi da hannayenta tana girgixa kai kishi na cin xuciyarta, Addu'a take Allah ya cire mata son Aliyu waxeer daga yanxun nan ta huta,daki ta shige ta shiga rera kuka mai ban tausayi,Bayan sun gaisa da baffa dakyar Ammah tayi karfin halin fadin"wurinka suka zo danka ya jawo magana."Ammah ta kalli Areefa mansoor wacce gaba daya hankalinta na akan Aliyu ,take fadin"fada ma mahaifinsa gashi zaune a wajen ,nan ta fada masa akwai cikin Aliyu waxeer a jikinta.
Kallonta kawai baffa yake tamkar wanda keson ya gano wani abu cikin fuskarsa kafin ya maida kallonsa ga Aliyu,da gaske cikin dake jikin Yarinyyar nan naka ne??"Baffa yayi maganar cikin karyewar murya shiru yayi masu tamkar yarda yayi a parlorn Ammah,hawaye yaji suna cika idonsa lokaci daya,ka buda baki kayi magana dan Allah Aliyu karka karyamin zuciya.......Baffa ya fada cike da karaya a muryarsa ,Ammah ta kalli Baffa tana fadin"baxai yi magana ba fa,tunda yasan ya aekata."wannan Yarinyyar xata xauna tare dani harta haihu,
Daga ranar da ta haihu tayi Arba'in Aliyu xai Aureta,haka kuma dayan matarsa ya shirya bata takardarta,
Baxata kara zaman Aure da maxinaci ba."
Baffa ya katseta yana fadin"kiyi hakuri kar abubuwa suyi masa yawa,idan yana son matarsa fa??"Ammah ta mike tsaye ta kalli su Aunty tana fadin"suje,a parlorn Baffa suka bar Aliyu tamkar an dasa sa a wajen,hawaye kawai ke xuba a idonsa,
Meyasa ya kasa ƙaryata Areefa mansoor agaban baffansa,meyasa ya karbi cikin da shi yasan baida alaka dashi,me Areefa take nema da zata yimasa irin wannan sakayyar??".,tashi kaje Aliyu Allah ya sauwakke,wata irin kunyar Baffa taxo ta rufesa wacce bai san yana yimasa ita ba sai yau.bai san yana kewar Khaleel waxeer ba sai yau da baya tare dashi,da yake Khaleel waxeer baya gari yaje Sokoto kan wani business dinsu,haka itama laylah tana Abuja ana bikin kanwarta,a wannan daren noory kawai yake son kasancewa tare daita,
Shi kawai xai sata jikinsa ya rarrasheta ya fada mata ba laifin sa bane,baya da alaka da cikin Areefa mansoor,yasan a duk inda noory take yanxu tana can cikin tashin hankali ,yasan kalar kishinta da yana da dama da ya dauketa daga gidan Ammah,
Sai dai yasan hakan ba mai yuyuwa bane.....acikin daren Ammah tasa aka gyara dakin da Areefa xata xauna harta haihu,su Aunty godia sukayiwa Ammah,har suka bar gidan suna jinjina karamci irin na Ammah,ko kadan basuyi tunanin haka abubuwa zasu xo da sauqi har haka ba,Sufyan mansoor na driving Yana fadin"dama kun daina mamakin saurin karbar ku da sukayi.ko kadan basa so a taba mutuncin gidan su.idan ma sunki karbarta baga yan jarida da media ba.....a wannan daren mutum ukku sunfi kowa shiga tashin hankali da jimami,Ammah Aliyu,da kuma noory idan sunce sunyi barci acikin daren nan,sunyi karya,tunda tayi sallar Asubah take zaune akan carpet idonta sun kumbura sabida kuka,duk lokacin da ta tuna akwai dan Aliyu waxeer kwance acikin wata sai taji duniar na birkice mata,idan tace bata kishin Aliyu waxeer xatayi karya,idan ta Runtse idonta hango Aliyu waxeer take tareda Areefa mansoor cikin wani irin moment da kwalkwalwar kanta baxata iya dauka ba,baxata iya sharing dinsa da wata macce a duniya ba,tunaninta ma yanxu yafi karkata da koda ma can Aliyu na neman wasu matan ,tasan Areefa budurwarsa ce wani irin rashin hankali xai saka Aliyu su aekata irin wannan babban xunubin,turo kofar dakin da take akayi.Ammah ce itama tareda Hijab din sallah ajikinta kallo daya xaka yiwa Ammah zaka san bata cikin natsuwarta,sallamar Ammah ta amsa tana tare hawayen idonta da suka kasa tsayawa,
Ta gaisheda Ammah cikin rawar murya,Ammah ta amsa cike da jin nauyin Nooriyah,da wani irin tausayin ta .
"Ban san kalaman da xanyi amfani dasu wajen baki hakuri ba Nooriyah ,ba kowace macce ce xataji abinda kika ji ba a jia kika kwana dashi acikin ranki,sai maccen da ƙaddarar ta fada kanta,baxan iya cewa komai akan wannan lamarin ba,shurun Aliyu ya tabbatar min da Yarinyyar nan gaskiyya take fada,haka baxan yarda ki cutu da Aurensa akan ki ba,dama Auren contract ne wanda akayi Auren dominsa ya riga yabar mana duniar meyayi saura,kara ya dauke maki wannan Auren kowa ma ya huta xan tsaya maki,Koda yaushe ina bayanki......."kiyi hakuri Nooriyah dan Allah kiyi hakuri,hawayen idon noory suka kasa tsayawa itama Ammah hawaye ne a idonta,cikin rawar murya take fadawa Ammah meyasa take bata hakuri da laifin da ba ita ta aekata sa ba.hukuncin Ammah na karshe ne yafi taba mata xuciya ,baxata iya Rayuwar Aure da wani inba Aliyu waxeer ba,shine komai nata haka baxata iya kallon idon Ammah ta fada mata ta yarda ta raba Aurenta da Aliyu ba,A ganinta Ammah duk ta girmi waya'nnan Abubuwan a wajenta,
Amsar ki nake jira Nooriyah amsar ki kawai ce xata natsar da xuciyata ,dan Allah karki ce kin amince zaki cigaba da zama da Aliyu a matsayin miji,dan Allah karki bani kunya Nooriyah ,
Yanxu ne xaki nunawa Aliyu asalin ko ke wacece??''Haka nayi farin cikin da baki baiwa Aliyu budurcinki ba,sai nayi mugun koya masa hankali,
Ki kwanta ki huta ban Amince kafarki ta taka kofar kitchen ba tunda dukan mu muna azumi Areefa kawai ce xa'a haɗawa break fast,dagawa Ammah Kai kurum tayi.bayan fitar Ammah ta kwanta nan a kasan carpert tana tunanin maganganun da sukayi da Ammah."
Kusan karfe tara na safe har daki Ammah taje ta duba Areefa wacce har tayi wanka taci uban kwaliyya sai kaice mai shirin zuwa party,ta ɗora kafa daya kan daya tana danna waya,ga kayan marmari nan ajeye an yanka su cikin madaidaicin tray ,Kallonta Ammah kawai keyi ta tashi xaune tana kallon Ammah tana fadin"Ammah ina kwana,Ammah ta amsa da lafia tana fadin"a kawo mata break fast ko zata je a dinning area tayi ,dan murmushi Areefa tayi tana fadin"muje nayi acan Ammah dama duk zaman ya isheni,Ammah tasa mai aeki tayi serving din Areefa.
Areefa ta kalli Ammah tana fadin"Ammah ke baxaki xauna muyi ba,
Ammah ta girgiza kai take fadin"ina azumi ne kin san yau Litinin,
Shiru Areefa tayi tana kallon Ammah wacce ta koma cikin parlor ta xauna tana ta kiran wayar Aliyu a kashe,
Har Areefa ta gama break fast ta dawo cikin parlor tana jan Ammah da hira,dai-dai lokacin Nooriyah ta shigo cikin parlorn suna hada ido da Areefa ta wani dauke kai,taxo ta xauna kusa ga Ammah,Ammah ta kalleta cike da kulawa take fadin"har kin tashi barci,ta daga kai tana fadawa Ammah ta tashi ta gaji da kwanciya a daki.da yake itama ta dauki azumin tamkar yarda ta ga Ammah nayi litinin da Alhamis.....Ammah ta kalli Areefa tana fadin ga matar Aliyu ku gaisa Areefa,wani kallo Areefa ta yiwa noory ,kafin tace ya kk
ganin yarda Ammah ke kallonsu yasa Noory tayi karfin halin fadin"ina lfy ya jikin ki."babu abunda tace ta shiga danna wayar hannunta,Aliyu ne ya shigo parlorn dauke da sallama a bakin sa,
Tunda ya shigo parlorn idonsa ke kan noory,wacce kallo daya tayi masa ta dauke kai xuciyarta na bugawa da sabuwar soyayyar sa,Areefa na ganin sa ta shiga sakin murmushi,ya gaisheda Ammah ta amsa can ciki fuska babu walwala ,Ammah ta kalli Areefa tana fadin."kin taba zuwa Asibiti??Areefa ta girgiza kai tana fadin".sau daya tun lokacin da mukaje tare da Aunty Siddiqa,Ammah ta kallesa tana fadin
Ya kamata kuje Waxeer hospital a Buda Mata file,a dubata a san watannin cikin."Ammah muje yanxu ma dan ina jin yana yimin wani iri."Areefa tayi maganar tana kallon Aliyu wanda ya hade rai lokaci daya,jin haka yasa Nooriyah tabar masu parlorn Ammah ta dan yi murmushi tana fadin"toh kije ki shirya ki fito,shi dai Aliyu yyi tsaye a parlorn yana so yabi noory A daki sai dai ganin Ammah ya kasa,Ammah ta hade wani abu da ya tsaya mata arae kafin tayi breaking silent dinsu da fadin."ina jiran takardar Nooriyah nan da kwana ukku,Ni har nayi mata miji."a wani irin haukace ya juya yana kallon Ammah,
Xaiyi magana sai ga Areefa ta fito da dan mayafinta wanda ta axa a kafadanta sai kuma bag dinta,ta mikawa Aliyu bag din fuska bbu walwala take fadin"rika min Captain wani irin kallo yake yimata itama ta tsaresa da idanunta ,wani abu yaga yana fitowa cikin nata idanun,tamkar walkiya haka gabansa yayi mugun faduwa,karbar jakan nata yayi da sauri hannunsa ta kamo ta saka cikin nata,ta kalli Ammah da jikinta yayi sanyi lokaci daya tana fadin"Ammah sai mun dawo pls Ammah ki saka noory tayi min sakwara da stew na egusi,nasan ta iya girki sosai kisa tayi min dan Allah xanfi jin dadin nata fiye da na yan aeki."Ammah ta sauke ajiyar xuciya tana fadin insha Allahu ,da haka suka fice daga parlorn tana sakin wani murmushi,Ammah xuciyarta na harbawa tabisu da kallo.Haka ya rika driving tana masa hira wani ya amsata wani yayi shiru,ta kallesa shaye da toka tana fadin"Yaushe xaka saki wannan Yarinyyar ba naji Ammah na fadin ka saketa ba ."me kake jira kuma.xan saketa Areefa ta bude masa ido tana fadin da yafi dai ,dan Ni bana sonta ko kadan,
Nasan kaima haka ??"ko ba haka ba ta fada tana tsaresa da idonta dake saka sa shiga cikin wani irin yanayi,muga wayar ka, mika mata wayar yayi tana fadin."
Yanxu nake so kayi sakin nan a waya."
Bari kawai na saketa tunda kai baxa ka iya ba,Ammah tana ta fadin ka saketa ka wani nace mata ko ka fara sonta ne??"tayi maganar cikin daga murya tana kara tsaresa da idanunta,cikin rawar murya yake fadin"ban fara sonta ba, typing ta shigayi a wayarsa
Tana fadin"idan Ammah ta tambayeka kai ka saki Yarinyyar nan,ka fada mata Ehhh kana jina??"da sauri ya daga kai,
Zuciyarsa na bugawa.
Taya xai saki noory ya Rabbi kana gani,
Typing ta shigayi cikin minti biyar ta tura ta basa wayar tana fadin"mu tsaya ka siyamin mitpie,bana awa biyu ban ci wani abu ba, ta fada tana rike da hannunsa tana murxawa,tun fitarsu Aliyu da ta shige daki take famar rera kuka,
Wanda ta rasa ko na menene.xuciyarta take jin tamkar xata fita sabida kishi,tana kokarin cire Aliyu daga ranta,sae kara sonsa takeji a xuciyarta ,
Xata fadawa Ammah ta amince Aliyu ya sauwake mata wannan Auren ,idan ta fita daga Rayuwarsa A hankali xataji soyayyarsa xata fice daga ranta batareda ta sani ba....Wayarta ta dauko taga sako ya shigo a wayarta,kuma da sunan Aliyu .da sauri ta buda sakon,
Abun da ta gani a wayar ya saka ta fasa wani irin ihun,da Ammah na zaune a parlor sai da taji ihun,girgixa kai ta shigayi tana fadin"pls karkayi haka Aliyu Dan Allah karkayi haka,banyi fushi ba hakama ina sonka a yarda kake ina sonka."
Na amince ko mata ukku xaka aura a lokaci daya xan xauna da kai a haka,Ammah ta riketa tana girgixa ta take fadin"meye haka noory meya faru??"so kike kiyiwa Kanki illah sabida soyayyar da namiji,
Hannunta na rawa ta mikawa Ammah wayar hannunta,tana murmushi take fadin"kice idona ne Ammah ba gaskiyya bane,,kice soyayyar Aliyu da kishinsa suka mai dani a haka...
Littafin waminal Hoob na kudi ne# idan kika karanta min book baki biya ke ba yar halak bace,Allah ya isa!""Allah ya isa!!!
Account Details.
0004157137
Jaiz Bank
Asma'u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah❤️: 32
wayar kawai Ammah ke kallo itama da nata kalan tashin hankali ,dukkan dauriya Ammah tayi bata nunawa nooryn komai a fuska ba,Take fadin"meke damunki ne Nooriyah??"sabida ya sakeki xaki bare baki kina kuka?.kiyiwa Kanki fada dan Allah,tunda kika ga ya Turo maki sakon saki a waya baya bukatar ki cikin rayuwarsa,ki bude idonki ki fuskanci Rayuwa,ba komai mutum keso a duniar nan Allah xaiyi saurin basa ba,sai an sha wahala ake samu,kina da tabbacin Aliyu yana sonki ne tamkar yarda kike sonsa,ki xama mai tawakkali a duk yadda Rayuwa taxo maki ki karbi duk abubda yaxo maki da hannu bibbiyu ,haka ki godewa Allah da Aliyu baiyi saurin karbar budurcinki ba waya
fada maki irinku na rasa maxaje na gari??"waya fada maki baxaki ssmu mijin da yafi Aliyu Qualities da komai ba,na maki Alkawarin xan Aura maki miji mai nagarta fiye da Aliyu waxeer,
Kuma nasan xaki sosa,xaki sosa noory bada dadewa ba,fatana kawai kiyi kokari ki cire Aliyu daga ranki daga yanxu nan,ki fara fighting da xuciyarki akan wannan soyayyar da kike masa wacce bata da Amfani ko kadan,
Kiyi min Alkawari baxaki bani kunya ba Nooriyah kiyi min Alkawari baxaki kara kula Aliyu waxeer ba,baxaki ko kalli inda yake ba, Nooriyah ,Ammah ta fada tana mika mata hannunta na dama,kama hannunta tayi hawaye na xubar mata batareda tace komai ba,Ammah ta jawo ta ajikinta tana lallashinta,tana fadin"komai Rintsi ina tare dake noory ina bayanki,ta dagota cikin jikinta Ammah na bata umurnin tayi blocking duka lambobin wayarsa yanxu agabanta,hawaye na xubar mata tana blocking kowace lamba tasa tamkar yarda Ammah ta fada mata....sai kusan la'asar suka dawo yau Aliyu waxeer ba karamin wahala yasha a hannun Areefa mansoor ba,daga Asibiti shopping mall suka wuce ta shiga xaben duk abunda takeso na kayan kwalama sun bata fiye da awa biyu acikin kanti,Aliyu yana kallon Areefa mansoor yana mamakin yarda ta ruguza masa Rayuwa lokaci daya,kallon wayarsa kawai yake cike da tashin hankali na sakin da ta turawa noory,mexai fadawa Ammah da noory akan bashi yayi wannan sakin ba,Aliyu na tuki Areefa ta kallesa shaye da toka take fadin"wai meke damunka duk kazama wani kala lokaci daya,
Nifa bana son haka ,bana so gaskiyya .aeni ma sai kasa Kani na shiga wata damuwa har babyn dake jikina ya samu matsala."ka saki ranka dan Allah ,Aliyu ya kamo hannunta yana kwakwalo murmushin dole,A haka yasa aka rika fitar da kayan,ya kira security xasu shiga dasu cikin gidan Ammah,ta dakatar dashi da sauri tana fadin"no bana so su tabamin Abun da xanci.haka kurum xasu taba nasan inda hannunsu yaje ya taba baka ganin kalar sune,kar cikana yazo ya samu matsala pls kai ka shigar min dasu Mana."ta fada tana hade rai,kallon uban kayan dake cikin booth din motarsa ya shigayi,Taya xai kwashi wannan tarkacen yaushe xai gama kwasar su??''ka tsaya ko baxaka dauka ba,ta fada cikin daga murya.Aliyu karka bari raina ya ɓaci,bakaji mai likita ya fada bane.....?"da sauri yake fadin",Am sorry xan shiga dasu ,da haka ta shiga loda masa ledojin a hannu sai da taga hannunsa bbu wani spaces sa'anan ta kallesa tana fadin"muje haka ta sakasa gaba har cikin parlorn Ammah,daga kai Ammah tayi ta kalli Aliyu sai kuma ta dauke kai xuciyarta na bugawa,haka Aliyu ya wuce da kaya a hannunsa,xuwa dakin da Areefa ta sauka .da murmushi Areefa ta xauna cikin soofas tana fadin"Ammah sannu da gida mun dawo,kallo daya Ammah ta mata ta dauke kai tana fadin."Yawwa sannu ki da dawowa,da haka Ammah ta maida hankalinta kan Tv.Haka Aliyu ya rika shigo da kayan har ya gama,ya kalli Ammah yana fadin"mun dawo Ammah,ko kallonsa batayi ba.dan murmushi Areefa tayi tana fadin"Ammah noory fa Allah yasa tayi min sakwara Allah -Allah nake na dawo naci."Bata jin ddi bata yi ba sai a tari gaba,ran Areefa mansoor yayi mugun ɓaci ta kalli Ammah take fadin"ae ko ba danni ba ya kamata tayi sabida dan cikin Aliyu."Areefa ta kalli Aliyu rai bace take faɗin"babyn ka sakwara yake so ko kana so raina ya ɓaci,
Da sauri Aliyu ya girgixa kai ya kalli Ammah da sauri yana fadin"Ammah dan Allah ki saka tayi mata,likita yace a guji duk wani abun da zai bata ranta xai iya shafar cikin jikinta .Ita dai Ammah bude baki tayi tana kallon Aliyu,
Tamkar ba Aliyun ta ba ji yarda macce ke wani juyasa a gabanta,ko kadan bataji haushin Aliyu ba,kara ae ta hukuntashi yarda xaiyi hankali.Ammah ta bude masa ido tana faɗin."daga yau daga yanxun nan karku kara saka Nooriyah cikin lamarin ku,haka ba baiwarta bace da zata rika yimata hidima,yan aeki kuma gasunan ta ko'ina acikin gidan nan,sai ka saka su daka mata sakwarar da takeso,xaiyi magana Ammah tayi masa wani irin kallo da yasa yasha jinin jikinsa,A fusace Ammah ta nufi stairs wani irin kallo take bin Ammah dashi,ta juya kan Aliyu xatayi masa magana,shima ya nufi hanyar barin parlorn tamkar zai tashi sama,
Jin yake tamkar ba dai-dai yake yin komai ba,Areefa na kwala masa kira ko takanta bai biba tayi kwafa tana fadin"zaka dawo ka sameni wlhi.....Ta fada tana barin parlorn a fusace,bayan ansha ruwa bayan ishaai Ammah ta fadawa noory su shirya xasuje gidan Baffa,haka nooryn ta shirya cikin Black tukish Abaya ,tayi kyau sosai
Amma kallo daya xakayi mata kasan tana cikin matsanaciyar damuwa,kai tsaye bangaren ummah suka nufa,da fara'a ummah ta tarbesu tana fadin"yanxu nake so na daga waya na kiraki ga Ankon Rumaisa ,ga nasu laylah da Nooriyah Ammah na fara'a take fadin"dole dai sai a Dubai aka siyo kayan nan,sabida wahalar da kai."ummah ta tabe Baki tana fadin"sunji xasu iya biki fa sauran sati biyu,suna da telan da xaiyi masu na sauri,Batool da Aysha nasu daban suka ce xasuyi da yar wajen Ramlah Inteesar ,ban san sukuma a wace duniar sukayi oder ba."Ammah ta kalli kayan lacess da materials sai kuma atamfa anko yazama kala ukku,dinner sai yinin biki da kuma budar kai,Ammah tace basu fadi Price din Ankon ba."Ummah tace Aliyu ya tura kudin su tun suna can,
Allah yasa Baffa na gida,Ammah ta fada tana kallon ummah.
Yana masallaci Ammah nasan yana hanya yanxu,ummah ta kalli Nooriyah tana fadin"sai kuma naji wani labari marar dadi nooriyah."shiru noory tayi tana jin xuciyarta babu ddi,Allah ya tsare gaba."ko kadan bana son Yarinyyar nan,nifa har ga Allah Ammah ban yarda da Aliyu yayi cikin nan ba,har yau jikina ya kasa bani haka,Ammah ta girgiza kai tana fadawa ummah abunda ya faru da safe tana fada mata saboda shi ma taxo wajen Baffa yanxu."ummah na girgiza kai da shock a muryarta take fadin"da gaske Aliyu ya saki Nooriyah sabida Areefa,anya kun bincika zancen nan gaskiyya ne kuwa."cike da takaici Ammah ke fadin"shi karamin yarone halama?''sako ya Turo a wayarta,ko bashi yayi ba ko shi yayi Nooriyah ta gama Auren Aliyu har Abada."shuru ummah tayi tana jinjina al'amarin,Ammah ta kalli ummah tana fadin"munyi waya da Abdul-Hakeem waxeer,ya fada min wani satin xai shigo dan samun daurin Auren Rumaisa yace xai dawo gaba daya gida Nigeria yayi aeki da Asibitin waxeer,na fada masa da yafi masa .haka kurum yaje yana yiwa wata ƙasa aeki da basirar sa alhalin kasar sa ya kamata yayiwa wannan aekin."ummah tayi murmushi tana fadin.nasan saboda ke zai dawo ae dan gidan kine kunfi kusa,
Abdul-Hakeem waxeer shine da na hudu a wajen ummah da Baffa waxeer,kusan tare suka tashi da Aliyu waxeer Aliyu ya basa watanni shidda da haihuwa,gaba daya Rayuwarsa komai nasa a kasar India ya yisa haka babban likitane,koda ya gama karatu acan ya samu aeki da Asibitin su,
A duk shekara yakan zo hutu gida iyayensa suna so ya baro kasar India ya dawo mahaifarsa yayi aeki da Asibitin waxeer ,ya kafe yace yafison can sunfi mu samun cigaba,Haka dan gidan Ammah ne sosai komai matsalar Rayuwarsa yafi tattauna ta da Ammah fiye da mahaifiyar da ta kawosa a duniya , Abdul-Hakeem ya nisanci gida ne sabida mutuwar budurwarsa
Yumnah Galadima,
Macce kwara daya tilo wacce zuciyarsa ta fara budewa da soyayyarta watan su biyar tare ta kwanta ciwo tana dauke da cutar ciwon daji"wanda a turance ake kira da (blood Cancer)mutuwar da ta girgiza Rayuwar Hakeem waxeer ta dimauta sa da taimakon Allah da Addu'ar iyaye Abdul-Hakeem ya dawo hayacinsa sai dai tun daga lokacin bai kara kasadar fadawa cikin soyayya ba,ya haramtawa kansa ita gaba daya ,
Aekin sa da neman halal dinsa da kula da iyayensa shiya saka a gaba,Ammah ta sha kawo masa yammata ya'yan kawayenta yana kaucewa haka,haka Yarinyyar wajen Ramlah waxeer mai suna Inteesar tana son Abdul-Hakeem da dukkan zuciya da ruhi,
Ammah ko kadan Yarinyyar bata gabansa tayi naci tayi naci ta xubawa sarautar Allah ido,,kusan dukan su tsaran juna ne daita dasu Batool waxeer,itace Ya'h a wajen Ramlah waxeer ta farko,itama tana karatun pharmacy acikin jami'ar Usman dan fodiyo dake garin Sokoto.....buda baki Baffa yayi cike da wani irin al'ajabi yake duba sakin da Aliyu yayi ta cikin wayar Nooriyah ,wannan karon sosai shima ransa ya ɓaci da lamarin Aliyu,Ya kalli Ammah yana fadin"ko ke xaki riketa a hannunki ya kamata a fadawa iyayenta halin da ake ciki,sun fimu hakki da ita,Ammah ta daga kai cike da gamsuwa take fadin"nima ina tunanin hakan Baffa insha Allahu,gobe xasuje itada Nooriyah dan su sanar da kawu balele,
Hakuri Baffa ya hau baiwa Nooriyah yana fadin"tayi hakuri ta yafewa Aliyu kaddara ce ta kaisa ga aekata hakan,nan kuma Baffa ya kalli Ammah.yana fadin."naga gudummuwar da kika Turo ta cikin asusun banki na na Auren Rumaisa Allah ya saka da Alkahiri yabar zumunci, Ammah ta amsa da Amin,sai kusan 10 suka bar gidan Baffa,da mamaki Ammah ke kallon motar Aliyu wato yana cikin gidan kenan??"A parlor suka tarar dasu,shida Areefa dafaffiyar gyada ce yake cirewa Areefa bawonta yana sakawa cikin bowl tana dauka tana ci tana danna waya,zuciyar noory na bugawa take kallonsu saurin dauke kai tayi taji hawayen na cika idonta,itama Ammah kallo daya tayi masu ta dauke kai,ganin nooryn yasa ya mike da sauri ya isa gabanta,xaiyi magana da sauri ta nufi stairs Ammah tayi masa wani mugun kallo,tana fadin."daga yau daga yanxun nan,ko kallon Nooriyah ka sakeyi sai na baka mugun mamaki Aliyu ,babu kai babu ita."xaiyi magana Ammah ta nufi stairs a fusace,
Areefa taja tsaki tana fadin"wlhi ka fiye naci da daukar wulakanci ,
Ana tayi maka wulakanci sai nacewa kake wai yaushe ka xama wawa haka??"ka xauna sae ball suke da rayuwarka,,kar ka batamin rai cikin daren nan dan Allah kaxo mu xauna muci gaba da hirar mu,A hankali yaxo ya xauna batareda Ya cewa Areefa komai ba,ta hade rai sosai ta kallesa tana fadin"daukarni ka maidani daki kayi tafianka gida ka kwanta ta fada fuska babu wani walwala,kallonta ya tsaya yanayi ,tamkar baiji me ta fada ba ta bude masa ido tana fadin Aliyu magana fa nake."zuciyarsa na wani irin rawa ya dauketa cak!"ya nufi daki daita,ya kwantar daita kan bed,ta mike tsaye tana fadin ragemin kayan jikina.
Babu musu yaja xip din doguwar rigar atamfar dake jikinta.
Ya rage daga ita sai underwears,hannunsa ta ɗora kan maballin bra dinta,da sauri ya jaye hannunsa zuciyarsa na wani irin bugawa,ta kafesa da ido tana fadin nonuwa na nayi min kaikayi ko baxaka sosa min ba,
Gabansa na wani irin bugawa yake kallonta,
Zuwa tayi ta sakawa kofar key ,ta dawo ta balle bra din da sauri ya dauke kansa,kana ban mamaki acan baya kasha tabawa babu mai hanaka sai yanxu kake wani shakkar yin haka. tabamin suna damuna da kaikayi,baka san wata mai ciki nonuwanta kaikayi sukeyi ba,
Ko sai nace ka shamin."da sauri ya girgiza kai yana dora tattausan hannunsa akan nonuwanta da sukayi wani irin cika sabida ciki,Auchhh ta fada da karfi ta dafe hannunsa a wajen,kallon cikin idanunsa take kafin ta hade bakinsa da nata ta shiga yawo da harshenta cikin bakinsa,wani irin dadi takeji yarda yake murxa mata nono,
Ji take tamkar Aliyu ya sadu daita dan wata irin muguwar sha'awarsa taji tana ji,
Banana dinsa dake cikin wando takai hannunta saman wandon tana murxawa a hankali,
Jin yayi numfashin sa na wani irin sarqewa da sauri ya hankada ta gefe ya cire key din jikin kofar ya fice daga Room din jin yayi komai na duniar nayi masa xafi.kallon fuskar sa yake cikin mirror ,meke damun Rayuwarsa??''wani irin ciwon kai yaji kansa yana yi,cire kayan jikinsa yayi ya sakarwa kansa Ruwa,
Waxai fadawa damuwarsa yasan cikin jikin Areefa mansoor baya da alaka dashi, haka sakin noory bada hannunsa ya rubuta sa ba,xai iya daukar komai Banda ganganci cire Nooriyah daga cikin rayuwarsa,duk lokacin da ya daga waya da nufin ya fadawa Khaleel waxeer hakan,sai ya kasa harshensa yake jin yayi masa wani irin nauyi.ko addu'a yake so yayi sai yaji an datse bakin,Ammah kiyi min addu'a dan Allah ban san meke damuna na...."Ya fada hawaye masu zafin gaske na mirginowa kan fuskarsa,washe gari tamkar yarda Ammah da noory suka saba tare suka shirya abincin karin kumallo sunayi suna taba hira,haka Ammah na sakowa Nooryn hirar Abdul-Hakeem waxeer cikin hikima,tana bata labarin kurciyarsa da darunsa,Aliyu ne abokin fadan sa,suna dambe da Aliyu ,da yake Aliyu yafi karfinsa,yana dukan Aliyu yana kuka,sosai noory ke enjoying hirar da Ammah keyi mata.A haka suka jera komai kan dinning area,Ammah ta kalli Nana wacce ke gyaran kitchen tana fadin"Nana jeki ce Areefa ta fito muyi break fast,da ladabi Nana ta cewa Ammah toh ta nufi dakin Areefa mansoor,bin dakin kawai Nana keyi da kallo wanda ya hargitse lokaci daya,
Wani kallo Areefa takeyiwa Nana tana fadin."ke xonan."jiki na rawa Nana ta karasa ga Areefa daga hannu Areefa tayi ta wanka mata mari tana fadin"mena fada maki kafin nayi wanka?''bacewa nayi ki gyaramin dakin nan ba,ki maida komai wurin xamansa,hawaye na xubarwa Nana take fadin"kiyi hakuri Ammah na tsaya gyarawa kitchen,Baki bude Areefa ke kallonta cike da takaici take fadin"dani da Ammah waye ya kamata aji tausayi,
Tashi ki gyaramin daki ko na buga Kanki ga kofa,jiki na rawa Nana ta mike tsaye ta shiga hada kayan da Areefa ta bari watse a tsakiyyar Room din,Jin nana Shuru Bata fito daga dakin Areefa ba ,
Yasa Ammah ta mike tsaye tabi bayanta,tsaye tayi bakin kofa tana kallon Nana dake kokarin gyara bed,Ta kalli Areefa dake zaune cikin soofa tana danna waya ta wani hade rai,Ammah tayi kokarin hade fushinta take fadin"Nana bata fada maki sakona bane??"Tana Danna wayarta batareda ta kalli Ammah ba take fadin"ta fadamin yau bana sha'awar break fast a gidan nan,gidan Aunty Siddiqa xanje na karya tareda Aliyu.
Juyawa Ammah tayi a fusace tabar room din ,ganin yarda Ammah ta fito cikin dakin Areefa yasa Noory ta kara shan jinin jikinta ,sai dai har suka gama break fast ran Ammah a mugun bace yake haka batace komai ba,ta dai fada mata ta dauko hijab dinta su wuce gidan Kawu,noory ta wuce dakinta ta dauko Hijab xasu fita sai ga motar Aliyu ta shigo compound din gidan,
Noory ce ta amshi car key a hannun Ammah tana fada mata bari ta jasu,tsayawa Aliyu yayi yana kallonsu ."ina kuma zasu tun da safe,Har suka fice daga get din gidan babu wanda ya kalli motar Aliyu,shima juyawa yayi ya fice daga gidan,dama xaije ya gaisheda Ammah ne,
Kashe wayarsa yayi karma Areefa ta Kara Kiran sa,rasa inda xaije yayi,kawai ya dauke hanyar kawai Kabir xiyara......har kofar gidan Kawu balele Nooriyah tayi parking Kusan lokaci daya ta fito itada Ammah.kalle-kalle Ammah ta soma hango yara samari masu jini ajiki cikin wata rumfa wanda shekarun su xasuyi goma sha bakwai booth ta bude sai ga kayan abinci,wanda ko Nooriyah bata san Ammah ta saka su ba,kallon Ammah Nooriyah ta tsaya yi,
Ammah ta riga ta maye mata gurbin uwa ,wacce bata bude ido taga uwarta tare daita ba.tayi rayuwane acikin innuwar maraici da wani irin kadaici ,shigowar Ammah cikin Rayuwarta Alkahiri ne ,haka Ammah ta zamo wani babban bango abun jinginawa a wajenta,tunanin me kika tsaya kina yi har sun gama kwashe kaya,mu tafi mana.tun dake bakya jin magana shasha kawai."murmushi Noory tayi ta dan turo baki tana fadin"bafa tunaninsa nake yi ba,Ammah tayi gaba cike da jin haushita tana fadin"ke dai kika sani
Sallama Ammah tayi a tsakar gidan Adama ta fito kitchen da fara'a tana fadin",sannu da zuwa Ammah yau kece a gidan,da murmushi Ammah ke kallon Adama tayi masu jagora har cikin dakinta ta shimfida masu carpert kan ledar tsakar daki,ta bude dan karamin fridge dinta Wanda noory ta siya mata dan yin sana'a ta dauko masu ruwan sha,suka kara gaisawa."ummah Kawu fah??noory ta fada tana kallonta,
Yanxun nan ya fita yanata zaman jiran ku,
Yace jia kin kirasa kuna tafe yau,dan haka ma duk yau bai fita shago ba."yanxu xaki gansa sunje ganin malam isuhu a asibiti ,baya da lafiya ne ummah."Adama na girgiza kai tana fadin"dan mashin ya turesa,Ammah ta nisa tana fadin"Allah ya tsare gaba ,basa bi a hankali...Hira suka cigaba dayi kafin ,sai ga kawu yayi sallama...
_wlhi tallahi idan kika karanta min book baki biya ba ,na barki da Allah hakkina na dari biyar baxai barki ba._
0 comments:
Post a Comment