Yau ko su 3 Kai sukazo Ita,Deejah sai Farty abin yabata mamaki bayan sunfitoh ne Zeemarh tace zataje taduba Salma nan Deeja tace zata farty kuma tace zatakai baby iman hospital batajin dad'i amma su gaisheta sukace zataji Allah ba babymush lafya" Farty ta ansa da anin
Motan Zeemarh suka shiga kasancewan Deeja batazo da natabah,tana zaune a gefe sai babyAff a ba tana surutanta gidan Salma sukayi direct a u/dosa, suna isa mai gadi yabude masu gate suka shiga bayan sunyi parking ne duk sukafitoh
A palo suka taddata dagani Tasha kuka kamar ba Salma yar gayu bah, tana gansu taje tayi hugging dinsu bayan takawo masu juice da cake ne Zeemarh" tace duk kingama wata kalla" Sakma tace ba dole bah Alhaji yahya dai Ashe matan shi biyu nice ta uku gashi yahanani xuwa sch ku duk yanda kukasan shidai bah haka yakema bah zan iya cewa hutun wata shida kawai nayi a gidanan nafara fuskantar bakaken halinshi, ga ruwa ga bakar mako da mugun hali, yaki daukarmin mai aiki ga cikinan nabani wahala" Zeemarh tayi shuru tace mukuma tamu kaddan kenan" Deeja tace wlhy koni hakane rowa yakemin ba nawasa ba da nayi magana yace ai da naci, dai dai da man mota ninakesiya dana yau ba sarki sai Allah nace nahakura" Zeemarh tace naku da sauki nifa Almansur masayi ne sai tafashe da kuka nan duk dukai ta bata hakuri bayan nan Zeenarh tace kilallabashi yabarki kicigaba da zuwa sch kibah komai zaki temaki kanki dakuma ummie"Zeemarh tace kifadama Ummie sai tarokeshi" Salmatace nanawa kuma ya raina Nata ai sai yagadama"Deejah tace insha Allah zai yadda"
"Salmatace Allah sa motanama ko mai babu kuma nasan babani zaiyi bah" Zeemarh ta zuge jaka tabasu 5k dukkansu tace"gashi kowa tayi manage nima cikin kud'inane da su baba suka bani nakayan d'aki sai Wanda Almansur yabani da,nasan yanzo abubuwa xasu chanza Dan yau ko ku'din manmota yak'ibani"Deeja tace ai mungode wlh, wai ace mutane duk sunchaza kuma bawai Dan basudashi ba"Salma tace rabon mumukacinye tin a waje"Zeemarh tace mudage da addu'a insha Allah,Allah xai yayemana"duk suka ansa da Allah sa" nan suka ma Salma sallama suka tafi,
Suna tafiya Salma tak'ira Ummie tana bata labarin kyautan da Zeemarh tamata sai godiya takeyi, nan tafadamata shawaranda suka bata Ummie" tace zatak'irashi taji,inyace ma bazai biyabah ai sai akarasa biya daku'din hayan gidanmu" Salma tace Allah sa mudace nansukai sallahma
*****************
Al'amari na Almansur gaba yakeyi ba bayaba kulin Zeemrh cikin kuka takeyi gashi sisin nairansh yadena bata ga sha'anan bikin Fiddause.
Tafadama Didi damuwanta Didi tayi mamaki matuka da wanan hali na Almansur dakucema Zeemarh ta Dage da Addu'a Allah yamata zabin alkhari *ni biebie* nace AMEEN FA
shirye_shiryen bikin fidaudee aketayi da Mahmud ko naira 'daya Almansur bai ba Zeemarh bah yaushema yake kwana a gidan bare har ta tanbyeshi saide cikin ku'din ta dauko 50k sai wani lace da tasiyarmawa k'awar 100k Almansur ne yakawo Mata lokacin suna zaman da'di shine tahada 150k tabada
Ahmad yayi rawar gani sosai a bikinan komai shiyayi Dan yanzo Ahmad Alhmduulillah yayi ku'di komai mai kyau da tsada yasiya ma fiddause(mahakurci mawadaci)haka muhmud yayi kokari sosai komai dai Masha Allah
Anyi biki da komai lfya kuma yayi kyau babu wani k'arya sai abun ya birge Zeemarh, duk ta gaiyace k'awayenta kuma duk sunzo amma banda Hannah da Nussy Hannah mijinta bai barinta fitah Nussy kuma ba tajin dadi
Ankai Amarya fidause gidan ta a marafa 3bedrooms gida yayi kyau haka kayan ciki ma..
~biebie deee~πΈ
πππ'YANMATAN ZAMANIπππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*STORY&WRITTEN BY*
~biebie deee bukhari~
9⃣7⃣
"""""Yau inbata manta bah 3moths kenan da yin bikin Fiddause,amma Allah haryabata ciki, haka duk friends dinta gashi har sunkusa hyhuwa, ita KO tanan babu ko alama wanan Abu yana damunta duk DA tasan komai na Allah ne.tashi tayi ta haura sama,sch zatashiga sabida project dinta.
Zeemarh gaba 'daya ta chaza,tadawo very silent and simple.da tagama da sch, gidansu ta nufa bayan side mama Murja tafara shiga ta Dade sosai sanan tashiga wajen didi suka gaisa nan didi kefada Mata Anty Haleemah batada lfya ta k'ira ta gaisheta, sanan tawuce side din mama nan duk tayi xamanta har aiki tayima mama,sai Albarka mama kesamata Zeemarh taji da'di sosai, sai bayan sallan magrib da tagaisa da su baba sanan tamusu sallama tayi gida.
Tadawo gida da tunani fal a ranta bayan tayi sallan isha taci abinci bata tsaya jin surutun Salma 'yar aiki ba ta haye sama abinta,kwanciya tayi abinda yafaru tin kafin auranta tashiga tunowa da kallan tsiyar da tayi duk dan kar ta aura Ahmad, gashi Wanda ta aura yanzo auranta dashi bai tsinana Mata komai bah sai nadama da kuma danasani datakeyi ba tinyazu bah ita kanta tasan tana San yaya Ahmad amma San abin duniyanta dakuma reasons dinta na manza yasa ta makanta ba'kin ciki auran mai ku'din mai yimata komai,
Ina ma takeganinshi,
Tamanta 1lst da ku'dinshi yashiga hannunta ita kema manta komai, ah hakama wai gara ita da Salma ita Salma gatadai a gida mai kyau amma komai Ummie keyimata duk Kansu auran masu ku'din bai musu komai bah, share hawayen ta tayi Wanda yagangaro mata, phone dinta ta dauka tashiga Neman layin Yaa Ahmad ringing 3 ya dauka
Zeemarh tafara sallma cikin dauriya tace"Assalamu'alaykum"
Ahmad"wa'alaykissalm,Azeemarh kina lfy?yakuma gida"
"Lfyalau,ya jikin Anty Leemarh"
Ahmad yace toh Alhamdulillahi"
"Toh Allah k'ara bata lfya,ya babyna"?
Ahmad yace Ameen amen,Afra nan lfya"
"Zeemarh tace toh ashafamin kanta, kuma agaida antyleenarh"
Bata tsaya jiran mai zaice bah ta kashe wayan.
Shiko Ahmad wayan yabida kallo yanakuma tuno yadda takemai magana kaman wani Abu nadamunta,tanbayan kanshii yayi toh mekeda munta?mai ku'di takeso kuma ta aura yanasane da duk wani k'aryan Aljanu dataketayi lokacin yanasane Aljanun k'arya ne danshi ba jahili bane yagane dalilin tanayin hakan shiyasa yasamata ido yakuma hakura da ita amma bawai dan baisanta ba, duk dadai abinda tamai yamai ciwo sosai amma yama kanshi al'kawarin k'iranta time 2 time dahakane zai gane damuwarta.
Zaman Zeemarh a gidan Almansur zamana na kunci da ba'kin ciki dan lamari na Almansur kulin gaba yakeyi saidai kawai mommy shi da su Anty lubabatu suta bata hakuri dan sunsan tana fama
Kwana 2 nanma batacika xAma a gida bah sabida savice din datakeyi A wani government sch KO antashi kuma gida takewucewa
Ita kanta mama tagane 'yarta tanacin damuwa
dan taga gaba 'daya ta chanza Randa mama tanbayeta kasabama mama ansa tayi sai kuka kawai datakeyi,shuru mama tayi chankuma "tace didi tasani kuwa"?Zeemarh tace ehh" mama tace shikenan kiyi shuru Zan tanbayeta naji" addu'a mama tabata takumace tacigaba daneman zabin Allah" Zeemarh taji dad'i sosai har sanyi sai datajin a ranta takumayi nadamar abinda ta aikata a baya.
Koda didi tafadama mama halinda Zeemarh keciki ta tausayamata sosai takumayi alkawarin yimata addua.
Hakarayuwa taita tafiya abubuwa da yawa sunfaru game da rayuwan gidan Zeemarh dan yanzo su baba duk sunsani haka Ahmad ma da sauran yayenta ,Ahmad duk yafi nuna damuwanshi a kan lamarin.
Hakadai Zeemarh taketahakuri sometimes kuma tasha kukanta Salma yar aiki bata jin dadin gidan Sam dan tasan antynta ba dadi takeji ba, tadai yi alkawarin tayata da addua dan shine kawai mafitah.
Allah ya sauka Salma lfya tasamu baby girl, tashi wahala sosai alhaji Yahya yarage mugun halinshi dan wanan Karon yadanyi abin kirki,ranan suna anyi dan abubuwa babu laifi yariya taci sunan sister alhaji Yahya wato rabi'a su Deeja,Hannah,Nussy,Hauwee duk da cikin su Zeemarh ne dai shuru, sunji dadin haduwa da junansu sunk'ara bama junansu shawara dakuma hakuri Farty matazo itadai batada matsala(kusan dama k'arfi ba daya ba) Amira kaita kuwa yanzo tana Dubai tana masters dinta
Zancigaba anjima wlhy naganiπ€£π€£π€£π€£
KO zaku k'arasa da kanku????
Inajiran ansankuu
πππ'YANMATAN ZAMANIπππ
*PURE MOMRNT OF LIFE WRITER'S{P.M.L}*
*STORY & WRITTEN BY*
~biebie deee bukhari~
_this page is dedicate ga duc wani makarancin 'YANMATAN ZAMANI, ILYSM all_❣❤❣❤❣
9⃣8⃣
""""""Haka dai akaiyi taron suna a katashi lfya,sai da su Zeemarh suka gyara maa Salma gida tsaf sanan dukkansu sukai nasu gidan.
Abubuwa da yawa yafaru ciki hadda gama sevice dinsu,fiddause ma takusa haihuwa,su Hannah ko duk sun haihu, yau a gida ta yini.
Zeemarh tadawo gida agajiye lis, dan 2days din nan batajin da'din jikinta
Bayan tayi salla da wanka palon k'asa ta dawo ta zauna nan fa Salma yar aiki tashiga zubo Mata surutu kamar radio mai jiini..lol
Zeemarh sai jinta takeyi tana daria sai k'arfe 10:30 Sallma tama Zeemarh sai da safe tawuce dan kwanciya tea taha'da dan baza ta iya cin rice bah.
Tanan zaune har 11:00mp jitayi Ana tura 'kofan da k'afi zuwa tayi ta bude,hanya tabashi dan yawuce amma sai ya tsaya komawa tayi 2siter ta zauna aranta tace yau bai sha ba kenan, zama yayi a gefenta yace" bani ruwa" tashi kawai tayi bata ansa shi bah,tana kawo mai ruwan tayi hanyan sama hannunta ya ri'ke yace" what d u mean hum"kallanshi tayi cikin rashin fahimta gira ya 'daga Mata ko'karin kissing dinta yakeyi tayi fuskan ta gefe, jawota yayi da k'arfin kaske yace"hala kinmanta matsayi nane a wajenki,mijinki neni ko yaya nake dole kiyi abinda nakeso bai tsaya bi takanta ba yashiga yimata abubuwa da k'arfin gske kuka kawai Zeemarh keyi wani tsanar Almansur ne na musanman yak'ara shiga zuciyanta shigo baimasan mai takeyi bah abinda yagadama kawai yakeyi Chan ma daukanta yayi yai bedroom da ita.
Bayan komai yalafa Zeemarh Tasha kuka tayi nadama babu adadi, dalilin kukantane ya saukarmata da ciwankai magani Tasha bacci ya dan dauketa.
Ko da asbah data tashi sallah, da ciwan kai ta kuma tashi hakadai ta rarrafa tayi sallah tak'ara kwanciya,sai k'afe 9 tafarka shima k'arar wayanta ne yatasheta Yaa Ahmad ne kek'ira nan da dan ta dauka sallama tayi mai gami da gaisheshi, ansawa yayi sanan yace"meke damunki naji voice naki somehow diriricewa Zeemarh tayi chan tace banajin dad'i ne dogon nunfashi yajaa sanan yace" kishirya kije wajen doctor'n haleemah doctor buhari a prime hospital, zank'irashi nafada bashi zuwanki"Zeemarh tace toh nagode Allah bar zumici Allah shirya maka zuri'a" Ahmad ya ansa da amin
Yaji dadin addu'an sosai murmushi yayi ya aje phone kan bedside Haleemarh ne ta shigo cikin d'akin zamatayi a side dinshi gami "dacewa abbanAff breakfast yayi ready fa" kallanta yayi yace sweetheart wats wrong wit u" leemarh tace nothing"gami da tashi hannunta yarike k'ara zaunar da ita yayi yamaida duk hankalinshi kanta sanan yace"tell me" hawayene yazubo Mata durkusawa yayi a gabanta yana share Mata hawayen chan tace"am pregnant sweetheart, amma kasan problem din,wlhy inaso na haihu da kai sosai kodan kyawun hakinka amma kana naka Allah na nashi"kuka takuma sawa hugging dinta yayi gami da shafa bayanta a hankali yashiga yimata magana a kunne" stop crying babe, insha Allah nothing will happen 2 dis time, inma cikin bai zaunabah munada enough time ai babyafff baby ce still,just 2n half yrs so please kibar kuka banaso yanada kyau k'arban kaddara mai kyau da Mara kyau" 'dago da kanta tayi tace"hakane insha na bari, amma inaso yaxauna cikinan" hancin ta jaa yanacewa"in mungama brkfst sai muje muga doctor" ta ansada yes sir" dariya yayi yaja hannuta sukatafi yin brkfst.
Itako Zeemarh bin wayan tayi da kallo tana mamakin kula irin nashi,tashi tayi tanufa toilet wanka tayi sharp sharp tafitoh tashirya tayi hospital.
Doc.Buhari yadubata yakuma cemata tarage damuwa magunguna yabata nan Zeemarh ta mai complain din rashin samun cikinta bayan anmata duk gwajin da yakamata doctor yace tadawo gobe nan tamai sallama tayi gida
Su Ahmad sunje asbiti doctor yace babu wani problem zata haihu da yaddan Allah,da'din wajen Haleema ba'a magana haka Ahmad ma _saimuce Allah_ _raba lafiya_
Dawuri tashirya tayi hospital bayan sun gaisa kallanta doctor yayi yace"bincike yanuna mijinki na anfani da wani magani Wanda ciki bazai taba shiga bah,so yanzo dai tinda kekinshirya haihuwa saikije kisamu mijinki kimai magana" tinda yafara magana inalillahi kawai takeyi wasu hawayene yazubo Mata babu shiri ta gogesu gami da mikewa sallama tama doctor tayi gaba tana fita doctor yak'ira Ahmad ya fadamai komai ba k'aramin girgiza yayi ba tausayinta ne yakamashi a ranshi yace dole nashiga kd dis week ina San ganin wanan hatsa bibin Almansur din.
Itako Zeemarh gidansu tayi direct,palon mama Amina ta zube kuka takeyi gami dacewa"natuba kuyafemin hakkinku kadai bazai barni nazauna lfyaba,kutemakeni kuce kunyafemin ko zansamu salama arayuwata" mama Murja ce tazo ta rungumeta, mama ta tausayamata matuka bayan mama Murja ta zaunar da ita, Zeemarh tacigaba da cewa"tin da nafara girma bantaba ganin abinda kukemin ba,kulin burina bai wuce naga inasa komai mai tsada ba,bai wuce naga ina rike ku'dade bah,bai wuce naga nafi kowa bah, bai wuce naga nakai kaina inda Allah bai kayni ba, ashe komai da komai na Allah ne, mama Tasha bani misali da fiddause bana gani, gashi ita tanacikin kwanciyar hankaki nifaa? kulin damuwa abubuwanda nake tunani duk ba haka bane Ashe" kukane yaci k'arfinta tayi shuru duk kansu shuru sukayi kallamun na Zeemarh ya ta'basu cen tacigaba da cewa"ina ro'konku da Girman Allah kuyafemin bazan iya fadan laifin danayi bah, amma ina baku hakuri wlhy natubah"
Baba ne yayi gyran murya yace "Alhamdulillahi hakamukeso kuma ni Abubakar mahaifinki nayafe maki duniya da kuma lahira" hawayen farin ciki ne yazo ma Zeemarh tace" nagode sosai babana hakika kai mahaifine nagari Allah yaja kwana yak'aro lfya mai anfani"duk suka ansa da amin
Mama ta daura dacewa nima Amina mahaifiyarki nayafemaki duniya da lahira"dama abinda naketaso kigane kenan komai lokaci ne a rayuwa,kuma indai kasa San a abin duniya a rai karinka ganin ba dai dai bah kenan" Haka kowa yace yayafe didi ko shuru tayi dan Al'amarin na Zeemarh addu'a yafi bukata.
BYan angama yafiya nan Zeemarh taciro takadda tamik'a ma baba tashi tayi ta tafi side din didi,tashiga d'akin kwanciya tayi dan ta huta jintake kaman ansaukemata babban dutse a kaa.
Bayan su baba sun duba takadda nan sukeganin ashema hadda hawan jini da yad'an kamata sanadiyar tunani ai nafadama didi tasa kuka gami da cewa"wlhh bazai kassaramin jika bah, yakasheta a banxa damai zataji?shangiya ko chacha da meman matan banza?dole yayi anfani da magani mana dan kar yatara shegu, wlhy bazai yuwu bah dole tabarmai gidanshi,ishara iya ishara naganshi tinda a wani bangaren nice *SANADI*dan Hakka dole asan abinyi dan komaii tayi tanada hakki akanmu"kallen mama Murja tayi tace kinada nabar lubabatu ko Binta antishi ai"?mama tace eh" Didi tace samin anan na 'daya daka cikinsu"ansan wayan mama Marja tayi tasa Mata nan didi tashiga k'ira ringing 3 ta dauka bayan sungaisa didi tace"kakar Azeemarh k'ara gaisawa sukayi sanan didi tafada Mata komai,hakuri kawai Anty Binta taita bayarwa didi tace"yaxama dole kuzo aiyi magana dan yarinya bazai taitazama da aure ba"Anty Binta tace zasuzo gobe insha Allahu"
Tana gama waya da Anty Binta Ahmad tak'ira ta fadamashi yanda sukayi da antyn Almansur din yace zaizo gobe shima nan duk sukatashi
Didi tadawo d'aki Zeemarh na bacc kallanta tayi taga duc ta rame tashinta tayi dan taci abinci takumayi salahn la'asar.
Bayan taci abinci tayi salla ne didi tafada Mata yadda duk sukayi Zeemarh tace Allah kaimu lfya"
*********************
Koda Anty Binta ta k'ira hajiya Mariya ta fada Mata yanda sukayi da family Zeemarh kasa cewa komai tayi dan batasan inda zata ga Almansur ba bare har tamai magana daurewa kawai tayi ta ansa da toh Allah kaimu.
Number mai gidan ta Alhaji sulaimai tak'ira bayan yadaukane take fadamai abinda kefaruwa" cematayayi tabari yadawo suyi magana".
Sai bayan sallan magrib ya iso gida, bayan yayi sallah yakuma ci abinci yashiga Neman layin Almansur cikin sa'a yasamu Alh.yace"kazo inasan kaginka"
"Almansur yace saide zuwa wajen 10 inzani gidan dan yanzo am busy"
Alh.yace Allah kaimu"
Haka sukai ta zaman jiranshi sai 10:40 yashigo babu ko sallama alh.yarufeshi da fada yace" wai kai yaushe zakayi hankaline?,kashigo waje babu ko sallama bare gaishuwa" Almansur yace nifa sauri nakeyi" yana maganane yana 'kokarin tashi,koma kazauna mahaifin nashi yace"
Kallan shiyayi nan yashiga karantumai abinda ke faruwa fuska ya 'bata yace"toh wai daddy mai zNyi ne" hajiya Mariyace tace" my boy inbakasanta kasaketa kawai kowa yahuta kafin suzo suce kayi abinda yafi wanan ma" bace komai bah d'akinshi na gidan ya nufa babu 'bata lokaci yarubutama Zeemarh saki batare da tunan komai bah,yanagama rubutawa yayi Palo wajen iyayen nashi a center table ya ajiya gami da cewa gashinan a kaimata bai jira mai zasuce ba tayi gaba abinsa.
Dafe kai alhaji yayi itako hajiya Mariya motsin kirki takasa Alh.yakaleta yace Allah ya sa adalilin sakinnan yaronan ya shiryu,gobe indan Allah yakaimu sai k'ira Binta kifadamata abinda yafaru ta ansa da Allah kaimu cikin sanyin murya
Koda safe Da Haj.Mariya tafamasu abinda yarafu Anty luba "tace sai dai muje tare hadda ke abasu hakuri dan sanin kankine abinda yayi bai kyauta ba"haj.Mariya tace bakomai ai sai muje.
K'arfe 2 daidai su Anty Binta suka Isa gdan su Zeemarh, sunshiga da sallama gabada side didi duk aka hadu Ahmad tin 12 narana ya iso bayan anyi gaishe gaishe ankuma basu abin motsa baki su Anti Binta rasa abincwa sukayi didi ce taganosu tace"ai karkudamu inma dakardane Allah sa hakane Alheri nan su Anty Binta suka mik'ata kadda dami da k'ara bada hakuri su mama sukace ba komai haka Allah yayi Allah sa hakane alkhari duk suka ansa da amin nan sukai masu salmasu tafi.
Aranan Ahmad yasa aka kwasuma Zeemarh duk wani kayanta nasawa dakuma takardun makarantanta kayan gida dama banata bane,sanda akadawo dakayan tayi kuka tayi nadamar abinda tayi abaya nan dai ta lallashi kanta yayi shuru.
Rayuwa yayi gaba Allah ya sauki fiddause lafiya tasamu ibahim khalil,su Salma sanda sugaji ansaki Zeemarh na tsuwace ta k'ara shigansu suma babu laifi yanzo abubuwa na tafiya Alhamdulilahi,sunsamu aiki suna taimakon kansu damuma iyayensu subarma Allah komai abinda yabasu dashi suke tak'ama sunrage bink'awaye babu ruwansu.
Zeemarh ko yanzo watanta 2 da mutuwaan auranta babu inda takezuwa dan ita bata nemi aikiba tukunan,babu abinda takeburi yanzo da yawuce Yaa Ahmad yadawo gareta,da tadauki abun Abu mai sauki Ashe ba hakabane dan yanxo Ahmad bayawani sakarmata fuska daka gaisuwa sai kaisuwa abin namatukar damuta sosai, ganan zatasama kanta tunanine tayanke shawaran shiga islamiyya
Haka ko akayi Zeemarh takoma islamiya tana karatu sosai dan damuwanta yaragu sosai.
Cikin Haleemarh yanata girma saidai yau lafiyane gobe babu haka dai taita rainuncikin har ya Isa haihuwa.
Yau kwananta 2 kenan tana labor har anashirin yimata c.s ne haihuwar yazo Tasha wahala sosai kafin ta haihu akasamu babyboy.
Bayan angyrata ita da baby ta nan Ahmad yama yaro huduba da sunan mahaifin halemah wato isma'i taji dadi sosai nan da nan yashiga k'iran yan U'wa.
Ta haihu da kwana 2 suka dawo Kaduna su didi da Zeemarh kaman jira suke nan fa suka bazama ganin baby Zeemarh jitake kaman itace ta Haifa d'an, dan dad'i haka didi ma nan fa Zeemarh tashiga hidima da maijego da yaranta kulin tana hanyan zuwa gidan kafin suna sunyi wani irin sabo da haleema,fidausee ma tanazuwa kulin Khalil yayi wayo sosai.
Ranan suna anyi shagali Ahmad ya kashe ku'di sosai Zeemarh duk tayi inviting su Salma kuma duk sunzo haka duk friends din Anty Leemarh duk zeemarh ce takula dasu maijegoma Tasha kyau haka taro yatashi kowa yana San barka.
Anyi suna da kwana 'daya ciwan ciki yakama Halermarh nan da nan Akai asbiti da ita nan likitoci sukafara aikinsu.Zeemarh ta tsorata sosai da Ciwan haleemarh ga isma'l(boy sunanda Zeemarh tasamai)sai kuka yakeyi abanyanta dole madara tabashi sanan yakoma bacci
Sai k'arfe 9 nadare Haleemarh ta farka Ahmad ne a daya Daka cikin kujerun d'akin sai kuma didi a gefe d'aya salati tafarayi sanan tace ruwa zanansha nan da nan didi tazuba tabata
Bayan ta shane didi ta taimakamata ta zauna kallan didi tayi tace"dan Allah didi in bantashi ba Ahmad ya aura Azeemarh itace kawai zata kulamin da yarana kuma shima yanasanta nasani ai" Ahmad ne yatashi yace wai maihaka ne anata lfya kina ta wani aure kuma?,insha zakitashi"murmushi tayi tace nidai nafada ma kai koma ina Raye sai ka aureta,didi kina sheda ai" murmushi kawai didi tayi Ahmad yace"naji toh kwanta musmushi takuma mai tace nagode" komawatayi ta kwanta.
Damisalin k'arfe 10 nasafe Allah yayi ma Haleemarh rasuwa...Allah akbar....
~biebie deee~πΈ
_inaganan sakon wayanda kesan kanin picture na follow me on Instagram_
@biebee__ or add me on Snapchat @ biebah3
*much love*❤❤❤❤❤❤❤
_masuyimin messages kuk'ara hakuri nakusa insha Allah_π€Έπ»♀π€Έπ»♀π€Έπ»♀π€Έπ»♀π€Έπ»♀
,
πππ'YANMATAN ZAMANIπππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*{P.M.L}*
*STORY & WRITTEN BY*
~biebie deee bukhari~
_this page is dedicated to All members of Biebie Dee novel thank you for d support, love and care ILYSM_❤❤❤❤❤❤
9⃣9⃣
""""""Allahu Akbar hakika rasuwan Haleemarh ya girgiza kowa dan yarinya ce mai ladabi dakuma biyayya, bata 'dauki duniya da zafi ba Sam.
Bazan iya fadamaku halinda Ahmed yashiga ba a wanan lokacin mutuwar ta bigeshi matuka haka didi da duk y'an gidan
Zeemarh Tasha kuka, sabida Ana gobe Haleemarh zata rasu wasiyya taitamata da tarikemata yaranta amana tabar Mata su har Abada k'arungume boy tayi tana zub da hawaye takuma kudira aranta zata rike su har *karshen rayuwarta*
Mommy ko mahaifiyar Haleemarh ba k'aramin tawakkali tayi ba duk da tasan tayi rashi 'ya tagari amma babu yanda zatayi Wanda yafi Santa ya daukayan sa,haka k'anen haleemarh sunji mutuwar 'yar uwarsu dan tana kyautata masu ba kadan bah.
Sai da duk wani d'an U'wa na jiki yazo yayima Haleemarh addu'a, mummy kasa fita tayi sai a cikin d'aki tamata addu'a takuma Samata Albarka Mara adadi.
Damisalin k'arfe 11:30 ne aka kai haleemarh gidanta na gaskia, sai a wanan lokacin Ahmad yafara hawaye shikanshi yasan yayi rashi babba
_sai muchai Allah jikan haleemarh da Rahma AMEEN_
Gidan su Ahmad ake 'karban gaisuwa dan haka 'yan uwa da abokanan arxiki sai zuwa ta'aziya sukeyi, ba'abar yan *Biebie Dee novel group* abaya ba mota guda duka zo gaisuwa dan suma Haleemarh ta mush alkhari.
Anayin sadakar uku kowa Yakama gabanshi, akabar Zeemarh da yaranta Afra da boy(isma'l)
Tinda Halemarh ta rasu Ahmad yazama shuru_shuru gashi Afra naganinshi zatafara cewa daddy"ina mommy" saidai yace mommy tayi tafiya"
Yau watan Haleema biyar da rasuwa Boy yayi girma sosai haka Afra ma suna samun kula sosai a wajen Zeemarh dan yanda take kuladasu ko kanta albarka.
Tsakaninta da Ahmad gaisuwa ce har yanzo inyayi magana mai tsaye" shine babu wani matsala ko"
Ita tariga ma ta cire rai da wani Ahmad tabarma Allah komai.
Yau Friday Zeemarh batada islamiyya, shiri suketayi zasuje wajen mummy mahaifiyar marigayiya, Afra sai da'di takeji za'aje yawo
Tagama shiyasu tsaf itama ta shirya kanta sunyi kyau matuka,sallama sukama mutan gidan suka tafi.
Mummy taji da'din ganinsu sosai haka sisters haleemarh ma fauzeeya da fa'izah sai daukan boy sukeyi, sai k'arfe 4:30 sukama mommy salama suka fitoh.
Bayan sunrabu da Fauzeeya takoma gida,wata motace tayi parking a gabanta,Kama hannun Afra tayi suka matsa gaba,
Jitayi nanacewa "dama kinhaifamin baby shine ko a sanar da mu"
Juwowa tayi danganin ko wanene AL_mansur tagani,matsawa tak'arayi sanan tace" Ashe shaye_shayen naka ya haukatar da kai haka"matsowa ya k'arayi yace"dan Allah Zeemarh kiyi hakuri nasan ban kyauta ba, amma please give me another chance" harara mai lafiya tabashi sanan tace" Wlhy ka haukace, ai ko zakabani duniya da kayan cikinta bani bakai" 'kokarin durkusawa yakeyi tai maxa tashige napep sukai gaba.
*toh pha*ππππ AL_mansur manya mota yashige yabi bayan napep din da gudun gske.
Zeemarh nashiga gidan d'aki tashige da gudu didi ne tabiyota "tana cewa keko lfyanki"
"Zeemarh tace wlh Al_mamsur nagani hadda cewa wai ashe na haifamai yaro"
Dariya didi tayi sanan tace" lalle baida hankali, yamanta maganin da yake anfani dashi kenan"
Wayanta ta dauka tashiga k'iran Ahmad, fita tayi a d'akin dabataso Zeemarh taji mai zatace,ringing 2 yadauka didi tace" toh dama akan magananku da Zeemarh ne, inbakasan ta nabata daman kula masu Santa" gabanshi ne yafadi cewa yayi" nifa banasan haka, zan shigo kadunan gobe sai muk'arasa magana"
Didi tace" dayafima"
AL_mansur ne ya iso gidan yaro ya aiko "wai Ana sallama da Baba" didi najin haka tasa hijab tafita,daka gefe taganshi gaisheta yafarayi ai ko ansawa batayi ta fara zazzaga mai masifa, kasa magana yayi hakuri kawai yakebata ai kamar k'ara zugata yakeyi saidatayi mai isarta sanan tace kadawo gobe, godiya yayi Mata yatafi.
Ai didi nakomawa gida Ahmad tak'ira ta fadamai "wai AL_mansur yadawo kuma da alama ya chanza hali dan haka tace ma yadawo gobe"
Sandarewa Ahmad yayi wani haushin didi yakamashii number Zeemarh yashiga Kira abinda yadade baiyi ba,sai da yamata 3 missed call
Jefar da phone yayi gami da "cewa Didi hooo"π‘
K'afe 9 a Kaduna yamai bayan ya gaisa da iyayenshi side Didi yayi bedroom yayi direct Zeemarh ya hango sai rawa takema boy Afra ma namai, yadade sosai a wajen yana kallansu sanan yashiga jikawai tayi ance " ina kika yadda wayanki" diriricewa tayi Chan tace nifa bansani bah" na'kiraki ai baki daukaba" kallanshi tayi gira ya d'aga mataπ
Smiling kawai tayi Chan yakuma cewa" banbaki daman kula kowa ba" shirutayi bata ce komai bah daukan isma'l yayi Afra a bayanshi suka fita.
Tsallen murna Zeemarh tasaka didi ce tashigo tanacewa" wai mai hakane kodan Jan ajii babu" Xeemarh tace kaku bazakigane bah"
Sai k'arfe 10 AL_mansur ya iso yaro ya aika, Baba yace yashigo bayan ya gaidasu cikin ladabi da biyya ne yace" yanaso yamai da Zeemarh yayi nadama Yakuma chanza hali,insha Allah babu abinda zai k'aa faruwa, yadora dacewa Ashe ta haihu bamusani bah"?
Dariyansu na manya Baba yayi sanan "yace ai ba yaron ka bane, ko kamanta musababin mutuwar auran ne"?AL_mansur jiyayi kaman k'asa yabude yashiga dan kunya,bakai da magana ba Ahmad yafado d'akin sai da ya k'ara gaida baba sanan yace" ai da ka barshi yatafi baba dan munriga mum sasanta kanmu da Zeemarh" kallan shi Baba yayi batare da yace komai bah, Didi ce tashigo tace" hakane kuwa dama so nakezuwa anjima nayi muku bayani" nan dai Baba yaba AL_mansur hakuri,Ahmad ko lallanshi baiyi bah
Haka AL_mansur yatafi jiki a sanyaye .
Iyayan nasu ba k'aramin dadi sukaji da wanan labari ba, haka mama Amina taita sama Ahmad Albarka nan dai aka tsaida ranan daurin aure Friday mai zuwa tinda abin duk na gida ne.
Duk wanan Abu da aketayi Zeemarh bata sani bah tachan da yaranta,sai da dare suna zaune da Didi nan didi ke fada Mata yanda akayi rungumeta Zeemarh tayi tacewa" ina sanki yar tsohuwa ta"
Cikin Daren Zeemarh duk tafadama su Salma,Hauwee,Hannah, Nussy da deeja sun Mata murna sosai ba k'adan ba haka fiddausee ma taji dadi sosai.
********************
Gyra sosai takesha ciki da waje dan mama da hanta ke Mata haka mama Murja ma didi kuwa ba'a magana.
Shakuwa mai k'arfin gskene yakara shiga tsakan Zeemarh da Ahmad soyyan da sukeyi a cikin 1week dinan ko rabinshi basuyi da ba.
Shiye shirye akeyi bana wasa bah, murna wajen wanan family ba'a cewa komai,duk wani shiri nabiki da Ummie Salma akeyinshi babu ruwanta yanzo tsakanta da 'YAN MATA sai Allah kawo miji nagari.
*Rana bata k'arya*sai dai uwar d'iya taji kunya, yau Friday kuma a yaune aka daura auran *Ahmad Aminu Mani da mamaryasa *Azeemarh Abubakar Mani*
Sai anjimankuu
_gaisuwa mai tarin yawa garwki masoyita Salma 'yarmutan gombe, ina Alfahari da samunki a matsayin k'awa Allah barmu tare_
πππ'YANMATAN ZAMANIπππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*LAST PAGE*
1⃣0⃣0⃣
_I dedicated this page 2 all members of PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S,Allah ya barmu tare yakuma k'ara hada kanmu AMEEN_
*Aysha Ali Garkuwa*
*Aysha Gana*
*samrah*
*Biebee*
*Ummie Garkuwa*
*Zee yabour*
*Sadnaf (lalata)*
*Jannart*
*Hussnah Bauchi*
*zahrah. Surbajo*
*Nana fu'ad*
*Xarah*
*Deeja waziri*
*Ummeen Yusrah*
*MSB*
*Maryerm Abdool*
*Mommyn sultan*
*Anty khady*
*Rafee"at D/dikko*
*Mrs hamisu taura*
*salmah*
*Sumybash*
_kai wlhy kunada yawa,gashinan page d'inan nakune duka_
"""""And'aura aure lfya mutane da dama sun halarta d'aurin auran,Ahmad baki yak'i rufuwa dan murna,haka Zeemarh ma,Didi ko hadda taka rawa dan murna.
Zeemarh tayi kyau bana wasa bah,kana ganta zakasan tana cikin farin ciki Mara musaltuwa,k'awayen ta na asali duk sunzo Salma,Deeja,Hannah, hauwwe,nussy,Farty
Fiddausi gayya tayi ba kadan bah dan ita sai yanzo tasan sis dinta tayi aure .
Didi bata yadda bah sai da tasa aka d'auko DJ tayi rawa ba k'adan bah,ba'a bar yan *Biebie Dee novel group*,a baya ba suma sunzo sunkuma sha rawa.
Mommy da su fauzeeya ma duk sunzo Afra ma Tasha Kyau duk inda Zeemarh tayi tana bayanta.
Washegarin daurin Aure ne aka shirya gagarumin walima a k'auna garden inda mama ta gayyato Aunty Aina'u(Ummu abdulnair) tayi wa'azi a kan halin *'yanmatan*mu nayanzo
"Tayi k'ira da surika godema Allah a duk halinda suka samu Kansu,banda kai kansu inda Allah baikaisu ba,banda bin k'awaye bargate dan anan ne ake haduwa da b'ata gari,banta rokon saurayi ku'di dan yana zubda mutinci,sukasan ce masu kallon na k'asa dasu ba na sama dasu ba,kiyi kwaliya yanda za'asan ke mace ba ballagaza ba,ta kuma daura da cewa duk abinda zakiyi kina buduruwa ba madauwami bane, lokaci ne kawai gidan miji shine zama na har abada sanan ta k'ara Kira sosai a kan YANMATA dasurike mutinsu su akarshe tayi k'ira da iyyaye da sukara sa ido sosai a kan amanar da Allah yabasu _Allah sa mudace ya karemu yakuma tsaremu Ameen_
Zeemarh jikinta yayi sanyi matuka sai taji kaman Ummu Abdul nasir da su takeyi haka su Salma godiya suka k'ara ma Allah da ya yayemasu damuwan su sunkuma dauki Alkawarin bama yaran su tarbiyya mai kyau.
Haka akaci akakuma sha sanan akai addu'a sanan Akatashi walima.
Sai da Akayi d'aurin aure da sati d'aya sanan Zeemarh ta tare gidan ta dake u/Rimi dan tace baxata zauna a Abuja bah su boy ko mommy ne tayi gaba dasu gidanta sai Zeemarh dan kwana 2 za'amaido su.
Har cikin daki Didi takawo Zeemarh sannan duk sukayi gida dama bawasu mutane da yawa bane.
Sai k'arfe 9 dai Ahmad ya shigo gidan sai da yayi Addu'a ya kulle gidan sanan yanufi d'akin Zeemarh
Wanka zata shiga sai gashi hugging dinta yayi sosai magana yakeyi Mata a kunne Wanda bansan meyakecewa ba naga dai Zeemarh sai murmushi takeyin
Bayan duk sunyi wanka sallah yajasu na nafila raka'a 2 bayan sun idar kanta yadafa yaita zuba Addu'a daka k'arshe yashafe.
Shida kanshi yabata nama da frsh milk dayashugo dashi.
Sai da ya k'ara masu Add'a sanan suka kwanta, Ahmad da Zeemarh sun raya wanan dare cikin kwanciyar hankali dakuma soyya na gskia
*asuba nagari*
Soyyah sukeyi bana wasa bah kowan ne su bai San bacin ran d'an uwan shi.
Yau sati uku kenan da tarewar Zeemarh rigima takemai wai ita a dawomata da yaranta kallan ta Ahmad yayi yace" zamu dau'kosu anjima dan week dinan gaba d'ayanmu Abuja zamu koma bazan iya zama ni kadai ba matata na wani U'wa duniya"
Dariya Zeemarh tayi tace" kai sweetheart Kaduna ne U'wa duniya"?
Gira ya daga mata gami da cewa" baxakigane bah yarinya" haka dai sukai tahiyan su har sai da aka Kira salan magrib sanan Ahmad yatafi masallaci
Yana tafiya itama Salln tayi yana dawowa suka nufa gidan mommy a nan suka tadda Daddy yazo wajen fauzeeya dama (tin bikin Ahmad da Zeemarh suka hada Kansu)
Mommy nasiha ta k'arayi yi masu godiya sukayi Mata suka dauki su Afra suka nufa gidansu.
Sai da sukaje side iyayensu suka gaishesu Daka k'arshe suka yada zango a side Didi nan Ahmad ke fada Mata xasu koma Abuja gaba d'ayansu Albarka tasaka masu sanan tace" dole asamo mai Aiki dan rainan su boy, sai 10 na dare sukama yan gida sallama sukai nasu gidan.
Watan su hudu da Aure Xeemarh ta Fara laulayi Ahmad duk ya rude, sai da cikin ya girma sanan ta dawo normal, hakadai sukai ta rainan ciki har ya Isa haihuwa bata sha wahala sosai wajen haihuwa ba nan dai Zeemarh ta haufo baby gal San kowa kin Wanda baisamu ba..lol
Murna wajen Ahmad a cewa komai haka Afra da boy dan yanzo bai yayi wayo sosai shekaranshi d'aya da wata 4
Ta haihu da kwana 1 suka dawo kaduna nan yan U'wa da abokan Arziiki sukai ta zuwa barka.
Ranan Suna yarinya taci suna Haleemarh murna wajen wanan family ba'acewa komai su fauzeeya ne abarorin (dan har anyi bikinsu da daddy)
Haka friends din Zeemarh dasu akai komai suna yayi kyau anci ansha dan Ahmad ya kashe kudi haka dai taro yatashi kowa yana San varka.
*******************
AL_mansur gyra halinshi halin yanzo ma sunyi aure da teemarh kuma suna zaune lafiya.
K'awayen na Zeenarh ko kanne tana zaune lfya a gidan ta da yaranta, basu da wani matsala sai wnda ba'a rasa bah.
*Bayan shekara 8*
Watou in kuka ga Zeemarh bazakugane taba tayi wani fresh ta k'ara kyau da kaganta kaga batar manya ga kyau ga kuma naira.
Iyayansu ko duk sunkaisu makka,umara duk shekara
Tsakaninsu da yaran Add'ace kaawai dan suna kyautata masu ba'kadan ba.
Zaune suke dukansu A babban Palo boy da Leemarh suna game,
Afrah Da twice Bilal da Hilal tana koya masu Home work
Zeemarh ne tashigo palo sanye take da Riga da wando irin na sport
"Oya sport guys daddy na jiranmu"
Afra ce tace" yeee wlhy ina gidan daddy"
Boy yace mami am wit you" shafa kanshi tayi .
Tace "yes my son"
Da gudu Zeemarh ta bar Palo duk suka bita A baya.
Inda zakuga yanda Ahmad da Zeemarh da yaron su keyin basketball dinan zakuyi mamaki barin ma Zeemarh ko jikinta bataji
Bayan sun gama wanka duk sukayi suka nufi family house dan gaida iyayen nasu Dama duk weekend suke zuwa
Anan suka tadda faddause da yaranta nan fa Yaran suka bude sabon shafin wasa ina cikin haka sai ga dddy da Anty fauzeeya sunzo.
Yusuf ma da matanshu nabila sai Hassan da Husain da aketa shirye shiyen bikin su yanzo
Nan duk aka baje a Palo Ana hira, Didi sai zuba take kanan ruwan fanfo,haka yara sukai ta rashin ji ga filinan enough dan tini yaran suka siyama iyayen nasu babban gida,haka dai akai ta hira sai dare kowa yayi gidanshi.
Soyyyan Ahmad da Xeemarh bazai fadu bah yanajij da ita haka itama yaransu kuwa Kansu ahade Zeemarh na kula da su Afra sosai dan basu taba maraici bah.
Yaran Zeemarh uku Haleema ce babba sai twice Bilal da Hilal sai kuma k'aramin ciki Wanda bamusan mace bane ko namiji _sai muce Allah raba lafya_
*ALHAMDULILAHI*
Anan nakawo k'arshen litafina wato *yanmatan zamani*Abubuwan da nafada ba daidai ba Allah ka yafemin.
Allah kuma yasa za'ayi anfani da darasin dakecikin wanan littafi Ameen.
_gaisuwa tamusanma ga_
_BIEBIE DEE&SAMRAH NOVEL GROUP_
_HOME OF NOVELS_
_RAZ NOVELLA~2_
_SADNAF NOVELS_
_ZEEE&HUSSY NOVEL GROUP_
_MIEMIEBEE NOVELS GROUP_
_FADELA LAMIDO NOVEL GROUP_
_RUKKY&ASBAH NOVEL GROUP_
_EXCUSIVE NOVELS GROUP_
_STYLISH HAUSA NOVEL_
_HUSSANAH ONLINE NOVEL_
_DAMA WAYANDA BAN ANBATA BA DUK INA GAISHEKU FATAN ALKHARI KO DA YAUSHE_
_Bazan matanta da kubah_
_Salma_
_Anty rabiela maman arfa_
_Anty Aina'u Ummu abdulnasir_
_Zee zee_
_Nagode sosai Allah barmu tare meen_
*FOR COMMENT*
07039732859
~Biebie deee~πΈ
0 comments:
Post a Comment