Umma kam neman yanda zata fito da Asim kawai takeyi, sai dai duk inda taje ta nemi taimako akaji wannan uban kudin sai kaga kowa yana dauke kai.
Yau da kanta ta shirya tazo gun Ashraf, bayan sun gaisa ta kalleshi tace " Ashraf in har nai abinda kace zakasa a saki d'ana?"
Ashraf yace " zan biya kudin da ake binsa zai kuma yi bailing sa "
Tace " naji yaushe kakeso in fada?"
Murmushi ya mata yace " zan sanae dake lokacin."
Cikin damuwa tace " Yaushe to zaka sa a fito da Asim din?"
Yace " karki damu saboda ankusa a cikin satin nan ne insha Allah."
Nan ta fito tai gida.
Dady shima yazo, kuka sosai yai agaban Ashraf magana d'aya yake cewa "Ashraf ka yafemin, kalmar da kawai yake fada kenan."
Ashraf ya kalleshi yace " karka damu Dady ko ma menene na yafema."
Yau 'yan sanda suka isa company din da Kawu yake, shi kam a wannan lokacin nema yake ya tattara komai na company din ya gudu, bai taba tunanin za'a zagayo kansa da wuri haka ba.
Yana zaune a office suka iso, ID dinsu ogan ya fito dashi yace " u are under arrest."
Kawu ya daure yace " akan me kenan?"
Officer din yace " mun kama daya daga cikin yaran da ka sa su sa wuta a ginin sannan ya bamu tabbacin kaine ka sasu."
Kawu ya rikice yace " a ina? Karya yakemin, Ashraf ne ya zugashi."
Baiyi auni ba yaji ansa mai ankwa, nan fa hankalinsa ya tashi ya shiga sambatu yana cewa a kira masa Ruma, shifa bai san me ke faruwa ba.
Sudai sukai waje dashi.
A cell aka garkama shi, sannan aka umarci Ashraf dayazo.
Bayan ya zo ne nan ya basu wayarsa sukaji duk abinda ya faru a lokacin.
Hankalin kawu ya tashi, ya dinga musu hauka.
Nan aka shigar da kara kotu.
Kawu kam anga rayuwa, bai taba tunanin zama a cikin dan dakin nan ba duk tsawan rayuwarsa.
Duk yayi baki ya jemi, Ruma kawai yake kira, ya ma rasa inda zaisa kansa, yayi tunanin basu kudi su fitar dashi, sai dai inaa duk inda ya bula abin yaki yiwuwa.
Har ranar zama a kotu.
***********
Nafi sun fito daga masallaci a garin makka, suna tafe ita da Mumy, Mumy ta kalleta tace " gashi har mun kusa komawa banga ko waya kunyi da Ashraf ba."
Nafi tai kasa dakai tace " Nasan zai nemimu in har ya nutsu."
Mumy tai murmushi tace " Nafisa kina birgeni sosai, kinama mijinki uzuri ba kamar wasu matan na zamani ba."
Nafi ta kalli takaru yanda taga anbiyosu sun smkwashi kayan da suka baza akan titi da gudu kamar me suna zabga gudu, ta kalli Mumy tace " nikam Mumy wai haka duka takaru suke zama agarin nan sam ba daraja?"
Mumy tai murmushi tace " ba duka bane suke rayuwa haka, sai dai akasarinsu abinda suke kenan, sai dai addu'a."
Nafi sunzo tsallakawa wata ta taho da kayan saidawarta da gudu ta bangaje ta da karfi wanda sai da ta fadi.
Matar ta tsaya tana ba Nafi hakuri, Mumy ta kalleta tace " haba baiwar Allah kudinga abu da hankali mana."
Nafi ta dago dan yima matar magana, mai idanunta zai gani?"
Mahaifiyarta ce sanye da wata kodadiyar doguwar riga da hijab tana rike da kayan saidaiwa a hannunta tanayi tana waigawa, ganin an biyosu yasa ta juya zata tafi.
Cikin zafin nama Nafi ta kama hijabin ta.
Matarta kalleta tace " Malama kiyi hakuri nace."
Nafi ta kara kura mata ido, tace " Inna?"
Kallan mamaki matar ta mata tace " ban gane ba."
Hawaye ne ya fara zubo ma Nafi tace " Inna nice fa Nafi."
Idanu matar ta zaro cikin tsananin kidima tace " Nafi?"
Mumy kam ta fahimci me ke faruwa ganin an biyosu yasa tace " mu wuce d'aki kwayi magana."
Nan suka karasa hotel dinsu.
Nafi hannunta na cikin na mahaifiyarta kuka kawai takeyi, ita kanta matar kuka take.
Nafi ta daure tace " rayuwar da kikeso kenan ki ka barni a kauye ni kadai?"
Inna ta share tata kwallar tace " Nafi ki yafemin wlh nayi dana sani sosai na barinki."
Nafi cikin kuka tace " menene abin birgewa anan?sannan ina kanina Mudan?"
Uwar ta share kwallarta tace " Mudan tun daya girma ya bi abokai suka shiga hidimar duniya, har abu yake sha, nayi fadan har na gaji, nayi dana sani har ba iyaka, rannan Aka zo min da labarin hadarin mota da sukai."
Hankalin Nafi ya tashi kwarai tace " meyasa baki koma ba bayan rasuwarsa?"
Tace " da wani idan zan koma? Bayan kayan Datti dana sata na bar iyayena sannan na barki, na kuma yi sanadiyar mutuwar dana, nikuwa mai zan koma inyi?"
Kuka sosai takeyi wanda hankalin Nafi ya kara tashi, nan suka shiga yin kuka sosai.
Mumy ta tausaya musu, nan taba mahaifiyar Nafi shawara akan ta dawo nan da zama tunda sun kusa tafiya kuma International ne zata biya kudi au wuce da ita.
Godiya sosai Inna ta dinga yi haka ma Nafi.
*************
Anyi zama a kotu inda Lawyer din Ashraf ya dinga fito da shaidu na garari ciki kuwa harda Auwal Max, Umma, Dady, Alhaji Uba sannan ga wasikar mahaifinsa ga kuma yaran da aka kama yasa wuta.
Ga maganar Kawu wanda Ashraf ya dauka, hankalin Lawyer din Kawu ya tashi ganin ba wata mafita, nan fa kowa ya san abinda kawu yai ma Abbas da d'ansa.
Kotu ta umarci dole ne ayima Dady da Mumy hukunci sannan Umma ma.
Kawu an yanke mai hukuncin daurin rai da rai, saboda ya kashe Abbas sannan ya nemi kashe Ashraf banda dukiyar maraya dayake amfani da ita.
Dady kuma an yanke mai hukuncin shekara 10 saboda shima dashi aka hada baki gunyin kisa, sannan shima yaci kudin maraya.
Mumy kuna an yanke mata hukunci kala biyu, ko ta je gidan yari ta zauna na shekara 2 saboda karyar da tai akan gadon maraya duk da kuwa danta ne, ko kuma ta biya kudi million 30.
Umma kuma an yanke mata hukuncin biyan kudi dubu 200 saboda kin fadar gaskiya datai.
Auwal Max ma an mai hukuncin zaman gidan yari na shekara 8 saboda yayi laifin taimako gunyin kisa.
An sanar da Mumy bata kasar sai dai ana sa ran nan da kwana 3 zata dawo.
Alkali yace tana dawowa a killaceta.
Da wannan zaman kotu ya tashi.
Littke tayi kuka kamar ranta zai fita jin wannan sabon al'amari, hankalinta ya tashi, labari kuwa ya bazu a gari ko ina ka zaka abinda ake fada kenan.
Su Ferry ma Nabil yazo ya basu labari, hankalin kowa ya tashi na mamakin wannan al'amarin, anyi bikin jibiya waccan satin.
Shikam kawu maganarsa daya shifa Ashraf ya cuceshi akuma kiramai Rumarsa.
Hmmmm nace su kawu sai ai zaman yari lafiya.....lol๐
*#ASHRAFEENAH TEAM*
๐
_Barkanmu da shan ruwa, Allah ya bamu ladan ibadar amin_
*ZUCIYA*
_ฤธowa da ฮนrฮนn ัaัa_
© *na Ayฯ
ัะฝer Mฯ
ะฝd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*๐ก
*87*
Little tayi kuka kamar ranta zai fita, Anisa ma haka, haka suka rungume juna itada Little a kotu suna kuka, Ashraf daga gefe yana zaune yana kallansu, shikansa abinda yake tausayi da tsoro kenan bayasan Little tasan abinda ke faruwa sai dai ba yanda zaiyi.
Habib wanda ke zaune kusa dashi idanunsa sun kada sunyi jaa kamar goro, yasa hannu ya buga kafadar Ashraf baice komai ba ya mike zai fita, hannu Ashraf yasa yamaidashi ya zauna sannan a hankali yace " ina zaka?"
Duk yanda Habib yaso ya b'oye hawayensa kasawa yai tun balle daya kalli Little yaga yanda take wani irin kuka, a hankali hawayensa suka ziraro ya kalli Ashraf kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa.
Ashraf ya mai murmushi yace "karkace komai Buddy nasan abinda ke ranka, so stop feeling guilty, ba laifinka bane haka fatanmu dai Allah ya yafe mana kurakuranmu."
Rungumeshi Habib yai alokacin hawaye ya fara zubomai sosai, cikin takaici da tsantsan tausayi yace "Ashraf na na......."
Kasa karasawa yai dan kukan yamai karfi, Ashraf ya bubuga bayansa a hankalu yace " karka damu abokina in har zuciyarka ta karye haka, Little fa?"
A hankali Habib ya d'ago ya kalleta sannan ya kalli Ashraf.
Murmushi Ashraf ya sakar mai sannan yace " kalli Dady ka gani shikanshi murmushi yakema."
Nan Habib ya kalli mahaifinsa wanda za'ai waje dasu, da sauri ya dauke kansa yace " ni ai bansanshi ba."
Ashraf ya hade fuska yace " ka tashi kaje kamai sallama, ko kamanta mahaifinka ne?"
Habib ya kalli Ashraf yace " Haba Ashraf kisa fa?"
Sosai Ashraf ya tamke fuska yace " ka tashi ko kuwa?"
Jiki a sanyaye Habib ya mike ya karasa gun mahaifinsa.
Yana matsowa Dady ya kama hannunsa yace " Habib kayi hakuri."
Habib ya kalleshi cikin takaici yace " Dady ban taba tunanin haka halayenka b'oyayyu suke ba."
Dady ya daure yace " Ni kaina bansan me ya sameni ba, sa dai fatana kada kasa wannan abun a ranka harya xamemaka wani abun, sannan duk da abinda ke tsakanina da mahaifin Little bazai hanani yimaka sha'awar auranta ba."
Habib ya dago cikin mamaki yace " Kanaso kace in auri Little bayan abinda kukama mahaifin Ashraf?ai ba Little ba banaji ma zan iya auran wata a duniya."
Yana kainan yai waje da sauri, Dady ya bishi da kallo hawaye suka zubomai.
Nan akai gaba dashi, kawu kam ba wanda yaje gunsa haka aka fita dasu aka sasu a mota Sai gidan yari.
Anisa kam tana isa gida ta rufe kanta a d'aki banda kuka ba abinda takeyi, tayaya mahaifinta zai kashe mahaifin Ashraf? Itakam ba wani uzuri da zatama mahaifinta ace d'an uwanka?duk da ba uwarsu d'aya ba ai jini jini ne, itakam bataji zata iya ko da cutar da Little ne bari har akai ga kisa.
Duk yanda Umma ke buga mata d'aki taki bud'ewa, a yanzu kam ta tabbatar da aurenta da Ashraf ya kare haka kuma tasan rayuwarta tazo karshe ba tantama.
Ganin taki bud'ewa yasa Umma ta koma falo ta baza tagumi tana kallan tsakar falon, lalai ba shakka duniya abin tsoro ce, itakam komai da yake faruwa jinsa take kamar a wani mumunan mafarki ne da takeyi.
Little kam zazzabi ne mai zafi ya rufeta wanda sai dayakaita ga kwana a asibiti.
************
Mumy da kanta ta nemi mahaifiyar Nafi akan ta zauna da su sannan su tafi tare, Inna kam ta amince da hakan dan batada wani uzuri sai mamakin yanda 'yarta ta zama takeyi balle yanda taga Mumy na ji da ita.
Nafi ta ba Inna labarin duk abinda ya faru wanda yasata kuka kamar ranta zai fita dan kuwa tasan laifinta ne duk abinda ya faru ba shakka itace sila sai dai tayi farinciki na ganin yarta cikin wadata haka da farinciki.
Sun shirya tsaf Mumy ta biya kudin komawa da Inna.
Nan suka shirya suka baro kasa mai tsarki suka dawo gida Nigeria.
A ranar da zasu dawo Ashraf sam ya kasa zaune ya kasa tsaye dama tun washegari kafin su dawo ya dau Dan Litti suka shiga manya manyan company's na yin furnitures yasa kaf kayan bangarensa aka canza ma Nafi, sannan ya sai akwatuna saiti ya zubamata kaya kala kala, dinkakune, wadanda ba'a dinka ba, dogayen riguna da English wears.
Ya dauko masu gyara aka gyara bangaren sosai kana gani kasan amarya za'a kawo.
Kayan Anisa na sawa kuwa aika mata b'angaren mahaifiyarta yai, wanda hakan ba karamin tada musu hankalu yai ba, Anisa kam ko abinci bata iya ci kullum kuka kawai takeyi.
Yau tun safe ya shirya dan sunyi waya da wani abokinsa da suka tafi tare ya sanar dashi yanzu zasu taho.
Bayan ya kintsa tsaf Dan Litti sai tsokanarsa yakeyi wai wannan zumudi haka? Shi bai taba ganin Ashaf a cikin wannan yanayin ba.
Ashraf dariya kawai yakeyi, ganin akwai sauran lokaci sosai yasa kawai ya wuce police station nan yai bailing Asim bai tsaya ya ganshi ba yai gaba.
Asim yayi baki sosai kamar ba shi ba ya rame sosai, ya fito ya tari adaidaita yai gida kamar wani almajiri.
Airport ya wuce suka hau jirgi shida Dan Litti sukai Abuja.
Sun saita abin suna isa ba dadewa Jirginsu Nafi ya iso.
Tunda Jirgin ya fara alamun sauka Ashraf ya kafe jirgin da ido, har ya sauka sannan a hankali alhazai suka fara fitowa kallan mutane kawai yakeyi yanasan ganin matarsa.
Bayan sun sauko ne suka taho ahankali aka musu checking nan ya hango Nafi.
Wani irin sanyin dadi ne ya dinga ratsashi ba shakka bai taba tunanin akwai 'ya macen da zatasa yaji irin wannan yanayin ba amma yanzu ya bada kai bori ya hau.
Su Nafi suna fitowa daga gun daga nesa ta fara kalla kalle, nan idanunta suka hango mata abin begenta.
Tsaya wa tai cak tana kallansa idanunta suka ciciko da kwalla, shikansa kallanta kawai yakeyi, Mumy ganin haka yasa taja hannun Inna sukai gaba.
A hankali suka fara takowa idanunsu nakan juna, Ashraf sam bai kula da wani agabansa ba sai jiyai ya bige wani, ya d'ago ya kalleta dariya ta sakar mai shima yai dariya sannan ya cigaba da takowa, sai da suka zo daf da juna ya kai hannu da niyyar rungumota, ta matsa da sauri tare da cemai "yaya mutane."
Kallan mutanen gun yai sannan yadan sauke fuska alamar takaici, tai murmushin farinciki ya matso kusa da ita yace " ni fa gaskiya so nake na jiki a kusa dani."
Kallan mamaki tamai tace " yaushe yayana ya zama haka?ba kunya?"
Mutanen gun ya kara kalla cikin takaici yace " muje masaukin da nasa a kama mana sai yamma jirginmu zai tashi."
Nafi ta daga kai nan suka fara tafiya a jere, ganin tana jan yar karamar trolly dinta yasa yakai hannu ya amsa.
Mamaki abin ya bata sai dai bata musa ba ta sakar mai tana murmushi.
Can inda yabar Dan Litti ya karasa nan yaga Mumy, da sauri ya mikama Nafi jakarta shifa sam idanunsa sun rufe bai kula da ita ba.
Nafi tai saurin matsawa daga gun jakar tai kamar bata ganshi ba.
Mumy tai dariya tace " Ashraf jakar zata fadi."
Kallan Jakar yai ya harari Nafi wacce ta matsa dan yasan da saninta, da sauri ya waske yace " Mumy lallabani tai akan in rike mata wai ta gaji."
Nafi ta zaro ido tace " a ina kenan akai hakan?"
Harara ya buga mata nan aka kwashe da dariya dukansu harda Inna dan ta gane lalai wannan shine sirikin nata.
Ashraf ne ya kalleta ba shakka ba sai an tambaya ba akwai kama sosai tsakaninta na Nafisa.
Nan ya gaida Mumy ya gaidata sannan suka shiga taxi suka nufi hotel din da suka kama.
D'aki uku yasa aka kama d'aya shida matarsa, daya Dan Litti dayan kuwa Mumy.
Sanda zasu kama D'an Litti har tsokanarsa yai yace "amma dai Mumy da Nafi ka kamama d'aya ko."
Harara ya bugamai yace " to wa ya sani?"
Ana zuwa Mumy ta kama hannun Inna sukai d'akinsu dan tasan da alama Ashraf ba kara a harkarsa ta yau.
Shikam ko a jikinsa ya kalli Nafi yace muje.
Tsayawa tai tace " ina zamu? Yaya tarefa muke da mumy?"
Ya hade rai yace " to ko gabanta zamu in jawoki jikina?"
Idanu ta zaro tace " ba kace yau zamu koma ba?"
Yace " dan yau zamu koma sai aka ce a hanani jin dimin matata?"
Zatai magana taji ya ja hannunta ya turata d'akin ya rufe.
Ita dariya ma abin ya bata tace " yaya wai yaushe ka zama haka?sam ka manta da wata kalma a hausa wai kunya."
Rungumeta yai ya saki numfashi yace " Ahh lalai nayi missing matarnan tawa."
Jikimta tadan janye kadan tace " nifa yaya a gajiye nake sannan wanka nakesan yi."
Zama yai akan kujera tare da juya kai gefe.
Nafi ta dauke kai itama ta dau towel ta cire kayanta ta d'aura sannan ta matso kusa dashi ta manna mai light kiss a lab'ansa tace " is that okay?"
Juyawa tai zatai gaba da sauri yasa hannu ya kamota ta fada kan cinyarsa ya kalleta ido cikin ido yace " Are u kidding me?"
Zatai magana taji bakinta a cikin nasa, wani salo yake mata wanda yasa itama dole ta fara bashi murtani, nan fa ya rabata da towel dinta ya shiga sarrafata ta nayanda yakeso, sai numfashi yake fitarwa itakanta tasan yayi missing dinta........
Sai da suka gama tukunna ya jawota jikinsa ya rungume yace " I really Miss u Feenah."
Yanda taji ya fadi sunan sai da tsikar jikinta ta tashi, idanu ta kafeshi dashi, baki yasa ya hura mata iska a idanun yace " kallanfa?"
Bata dauke idanunta ba tace " yayan dan kara fada."
Ya kalleta yace "mene? I miss u?"
Kai ta girgiza tace "a'a d'ayan."
Kallan mamaki ya mata yace " to mene?"
Tace " d'ayan please."
Yace " wai Feenah?"
Kai ta daga da sauri tace "bantabajin dadin sunan ba a bakin wani ba kamar kai."
Idanu ya kanne yace " badai so kike kicemin haka kikesan indinga ce miki ba?"
Shiru tai sannan tana wasa da gashin kirjinsa tace "mene? Bazan iya ba?"
Yace " sosai, dan ni Baby nake san cemiki dan haryanzu u are a baby."
Baki ta turo tace " salan ka faracemin baby daga na haihu ka koma cemin Nafisa?"
Cikin mamaki yace " saboda kin haihu sai kawai na daina cemiki?"
Tace " sosai ma dan nasan abinda na haifa zaka koma cema Baby, haka kawai a fara cemin suna ba wani dadewa a canza."
Kallanta yai yace " to amma?" Sai kuma yai shiru kafin da sauri ya kalleta yace " ba wani dadewa? Ya akai kika san haka?"
Kanta ta cusa cikin kirjinsa tace " ya za'ai bazan sani ba bayan lokaci kawai suke jira?"
Idanu ya zaro cikin tsananin mamaki ya d'agota shima ya zauna akan gadon, ya rike hannayenta yace " Baby me kike nufi?"
Harararsa tai tace " sai nayi dala dala? Agunka fa na koyi murda magana."
Yawu ya hadiya sannan ya kalleta cikin wani yanayi yace " Nafisa bana san........."
Kiss tamai a kunci sannan ta kai hannunsa na dama kan cikinta batace mai komai ba.
Kallanta kawai yake kamar a mafarku yakejin abun, da sauri ya jawota ya rungume tsam yace "Nafisa yaushe?"
Tace "sai da mukai tafiya sannan na sani."
Wani irin tsantsar farinciki ne ke ratsashi ya kara kankameta, cikin zolaya tace " kaga banshirya ba na samu ciki sannan gashi ance a satin nan zafa a kafe mana list na makaranta."
Ashraf ya dagota yace " makaranta?"
Kai ta daga da sauri.
Fuska taga ya canza yace " da babyn nawa za'a dinga zirga zirga?salan karatu yasa a ki kulamin da babyna?"
Cikin mamaki ta kalleshi tace " ban gane ba?"
Yace " ki bari dai sai kin haihu."
Kallan tsantsan mamaki tamai tace "yaya mai kake fada haka?"
Dariya taga yasa yace " me? Kinji haushi? Nima ramawa nai ina murnar zanyi d'a ko 'ya amma kidinga min zancen wai karatu? Nima shiyasa na rama."
Hannu tasa tadan bigi kirjinsa tace " yaya harfa ka tsoratani."
Mikewa yai ya daga ta cak yai toilet da ita yana cewa gwara tsoron ya tsaya daga ke karki kaimin shi ciki."
Yana ajiyeta a bathtub ta kalleshi tace " ka gani ko? Dama nasani ina haihuwa zaka daina sona."
Murmushi yai yace "sorry Feenah dan da alama zan daina kuwa."
Haushi ya kamata ta kafeshi da ido, goshinta ya matso ya sumbata yace " in banda abin ki ai soyayyar da muke ma juna ita zamu yi karo karo mu ba babyn mu."
Ta kalleshi tace " hmm gashi nan har ka daina cemin baby, shi yasa ma nace kar a fara."
Shigayai cikin bathtub dib ya sakar musu shaya ya jawota jikinsa ya rungume a hankali yace " Nafisa bansan irin farincikin da nake ba yau lalai ina cikin farinciki mara misaltuwa, ji nake kamar bayani farinciki a duniyarnan."
Murmushi tai ta kara shigewa jikinsa.
Bayan sunyi wanka dakansa ya shafa mata mai sannan ta saka wata doguwar riga baka dake cikin jakarta sannan sukai order na abinci aka kawo musu.
Shi dakansa ya dinga bata bayan ta koshi sannan shima yaci, ya koma kusa da inda take zaune ya jawota suka kwanta a kan gado, a hankali tace " yaya ya kuka kare?"
Nan fa ya zayane mata duk abinda ya faru Nafi kam tasha kuka kankameshi tai tsam taba kuka tace " Yaya."
Murmushi yai yace " karki damu ai komai ya wuce."
Cikin kuka tace " wace irin rayuwa ce wannan ace duk mutanen dake zagaye dakai ba sanka suke ba? Ace mutum ya fifita dukiya akan jininsa"
Ya sake murmushi yace " _zuciyar kenan ai kowa da irin tasa_, wani akan kudi ba abinda bazai iyayi ba."
Tai murmushin takaici sannan tace " yaya wato da rayuwa ta da taka is so similar inaji tamu kaddarar kenan, bamu da kowa sai junan mu, nima daga mahaifina har mahaifiyata kowa rabuwa yai dani saboda san abin duniya."
Ashraf ya kalleta yace " ya akai naga kamar mahaifiyarki?"
Nan ta bashi labarin abinda ya faru, kai ya girgiza cikin takaici yace " Kaddarar da Allah ya daura mana kenan, ikon Allah ne yankaini garinku har na hadu dake, duk da rashin mutanen da ke sona tsakani da Allah a kalla ina alfahari da matata Nafisa na sona tsakani da Allah."
Murmushi tai tare da goge hawayenta ta kai fuskarta saitin tasa sannan tasa hannayenta ta kare bangare biyun idanunta a rufe suke sai ta bud'esu a hankali tana kallansa, shima kallanta yakeyi tace " nima ina alfaharin kasancewa dakai."
Murmushi ya Mata yace " Nafisa tnx alot 4 not living me."
Wani sansanyan murmushi ta saki sannan ta zare hannayenta ta kwantar da kanta akan kafadarsa tace " zaka cigaba da sona duk da banda komai?"
Murmushi yai sannan yace " zaki cigaba da sona duk da yanda nake?"
Idanu ta lumshe tace " duk rintsi bazaka wulakantani ba?"
Murmushi ya sake yi yace " duk rintsi bazaki gaji dani ba?"
Kallan juna sukai suka saki murmushi Nafi tace " yaya amma Little dita fa?"
Ajiyar zuciya yai yace "sai dai kinje."
Ta jinjina kai tace "yaya nisa fa?"
Kallanta yai yace "tana gun tsohuwarta."
Cikin mamaki tace " amma dai ba wai ka saketa bane ba ko?"
Ya hade fuska yace " kinmanta abinda na fada miki? Banda maganin hana daukar ciki datai dani harda ita fa aka hada baki akaina."
Nafi tai murmushi tace " amma yaya kaima ai kasan yanda take sanka ina sanin da kai tana masifar sanka shi yasa kai amfani da ita gun kama Ya Asim? Da kuma ganin akwatin Kawu?"
Ashraf yai shiru bai ce komai ba, Nafi tai murmushi tace " kabarta ma da abinda takeji plx karka saketa."
Hannu yasa ya tureta ya mike tsaye yace " wato ke ko kishi ma bakyayi, a iya sanina murna ya kamata kiyi."
Tasowa tai ta rungumeshi ta baya tace " ni kuwa nake kishinka shine ma yasa na fadi haka, dan ina kishin komai daya shafeka ciki kuwa harda kishin kar idanunka su rufe ka aikata ba daidai ba."
Kanta ta kwantar a bayansa tace" amma yaya nikam maganar wasiyya ta fa?"
Juyowa yai ya kalleta yai dan murmushi sannan ya bata labarin abinda ya faru.
Dariya sosai tai tace " amma dai ai bai kamata Abba yabi maganar wani mutum ba."
Ashraf yai dariya yace " nima da farko na dauka maganar mutumin nan ce ta sashi barin wasiyyar sai dai yanzu na gane ba haka bane, fahimtar dayai su kawu sune sillar halakarsa shine yasa ya mai wasika akan ya janye maganar aurena da Anisa, shi a tunaninsa kawu zai janye, to fatan Abba shine wasiyyar ta isa gun matar da zan aura."
Nafi ta jinjina kai alamar gamsuwa sannan tace " amma yaya kasan akwai mutane masu baiwar haka kuwa? Duk da bance wannan gaskiya ya fada ba sai dai Allah yana hallintar mutane da baiwa kala kala, wasu in basusan ya zasuyi amfani da baiwar tasu ba sai kaga sun koma harkar duba da bokanci da tsubbu."
Ashraf yace " haka ne, amma bakya ganin ya kamata mu maida Inna gun mijinta ta nemi yafiya?"
Nafi tai shiru, Ashraf ya dagota yace " karki damu ba abinda zai faru, iya kaci inyace baisan aurensa da Inna sai mu dawo da ita nan gida."
Kallansa Nafi tai sai dai batace komai ba, tana matukar tsoron Datti gani take bazai taba yafema Inna ba tunda ta satar mai saniya.
Da yamma sun taso sun iso garin kano, ya kuma sanar ma Mumy hukuncinta, a da taso ta zabi zaman gidan yarin dan gani take bata kyautama Ashraf ba a rayuwa, sai dai shi da kansa yace gidajenta za'a saida a bada rabi shi zai bada rabi a biya kudin, sai dai sam tace bata yarda ba, sai dai a saida duk kadararta a bada bazata taba yarda ya biya kudin laifin data aikatamai ba.
Sun isa gida inda Nafi ta shiga gun Little da sauri, a kwance ta ganta a d'aki ita kadai su Afra suna falo suna kallo, Nafi da sauri ta karasa gunta ta rungumeta tsam a jikinta a tare suka saki wani kuka, kuka suke sosai kafin daga baya Nafi ta shiga ba Little hakuri.
Little tace " Nafisa da wani ido zan kalli Yaya? Da wani ido zan kallu Ya Habibda mumy?"
Nafi ya rike hannayenta tace " Little bakiyi komai ba fa, baki san me ya faru ba, ta yayya zaki daura wa kanki laifin da baki aikata ba?"
Little hawaye na zubo mata tace " ta ya zakice ban aikata ba bayan mutuwar Abban Yaya itace sanadiyyar haihuwata?"
Kai Nafi ta girgiza mata tace " karkiyi sabo Little kaddarace ta riga ta faru fatanmu Allah yasa mu gyara."
Da haka Nafi tai ta ba little baki harta kwantar da hankalinta, nan ta jata bangaren Mumy.
Little na zuwa ta fada kanta tana kuka.
Asim kam tunda ya isa ya samu abinci agun Umma ya hau ci ba kakkautawa, Umma kam tausayin dan nata takeji ganin yanda yake tutura abinci kamar zan cinye har kwanon, sai da ya koshi sosai ya tam sannan tace yaje yai wanka.
Yana fita ta saki kukan takaici itakam ina zata sa kanta, basuda komai sai gun zaman nan yanzu in har Ashraf yace su bar gidan nan fa shikenan tasu ta kare.
**********
Da daddare Ashraf yana zaune ya bugama Nafi waya, ta dauka tare da mikewa daga gun su Inna da Mumy da take, cikin rada tace " yaya ya akai?"
Yace " wai bazaki taho gun mijinki ba?"
Tace " gun mijina?"
Yace " da kina so kicemin a gun Little zaki kwana?"
Tace " naga da acan nake kwana?"
Yace "da kenan yanzu ai kayanki zaki tattaro ki dawo bangaren mijinki."
Murmushi tai tace " ni dai kunya nake ji gaskiya."
Yace " kunya ko? To ni bari nazo na daukeki."
Yana kaiwa nan ya kashe wayar.
Dariya tai tace " in zaka iya kenan ba."
Ta koma suka cigaba da hira, batai minti 10 da zama ba suka ji sallamar Ashraf.
Little tai kasa da kanta, shigowa yai ya zauna kusa da Little tare da dagota yace " kanwata ko neman Habib kike ne?"
Dagowa tai da sauri tace "ni kuma?"
Murmushi yai yace " to ni kike nema?"
Kasa tai da kanta tana murmushi, Ashraf ya harari Nafi yace " malama tashi ko?"
Nafi ta zaro ido ta kalli Mumy da Inna cikin tsananin mamaki, wai keke damun Ashraf? Abinda tafada kenan a ranta.
Mumy tai murmushi tace " Ashraf bafa inda zataje."
Kallan Mumy yai cikin mamaki.
Mumy tace " Nafisa tana bukatar wani shagalin biki dan a kara shaida auranku, mutane dayawa basu san matarka bace, ita kanta kunya ya hanata sanar da kawayenta."
Cikin tsantsan mamaki ya kalli Mumy yace " to ai...."
Mumy ta hade rai tace " mun yanke hukunci da mahaifiyarta nan da sati d'aya za'ai ko yar walima ce sannan ta tare."
Haushi ya kama Ashraf yace "har sati?" ya fada yana kallan Nafi.
B'oyewa tai bayan Little tamai gwalo, haushi ya kamashi ya mike yace " hmm amma da ina tunanin gobe zamuje kauye tare da Inna dan ta nemi yafiyar Datti."
Mumy tace " hakan yayi kyau, inyaso sai Little ta rakaku."
Yace " amma mu biyu ma....."
Mumy ta katseshi zan ma Habib magana shima kila zaiso yaje kauyen kaga sai kuje da armashin ku sai ku dauki babbar mota, gashi Afra nan ma xasuyi rakiya."
Haushi ya kama Ashraf yai waje cikin takaici, bangarensa ya nufa ya kalli yanda ya tsara musu bangarensu yace " har wani sati? Sannan goben ma baza'a barmu mu biyu ba???"
**********
Washegari haka suka shirya suka dauki mota babba, Little, Inna,Nafi, Afra da Amra, Dan Litti Habib da Ashraf suka nufi kauyen su Nafi.
A hanya Ashraf yai musu siyayya sosai duk da Habib ne ya sashi dan shi gani yake bazai iya kaima Datti komai ba, haka suka isa kauyen
A kauyen su Dan Litti suka fara sauka aka saukeshi mutane sai kallansu sukeyi, sannan suka wuce rigar Datti.
Sun samu ba kowa a gidan gidan ma a rufe yake nan fa hankalinsu ya tashi sai ga wani yazo wucewa nan ya sanar dasu ai yana gidansu.
Nan suka shiga mota suka gangara, Datti na kwance a karkashin bishiya shi kadai abin duniya duk ya isheshi yana ganin mota ma ta tsaya amma ko alamar mikewa baiyi ba, mutane suka zagaye motar, nan fa su Nafi suka fito ba wanda ya ganesu gwarama Inna yayan Datti na ganinta ya ganeta.
Sai da aka musu iso suka zauna a ciki sannan yayan datti ya aika a kirashi.
Ba'a dade ba sai gashi nan, nan yaga inna sai dai maimakon masifa gani sukai ya saki kuka yana ce mata " innar Nafi mun shiga uku na saida ma masu yankan kai Nafi."
Kuka yake sosai wanda saida yasa Nafi ma kuka, Ashrad ya kalleshi yace " baka gane ni ba baffa?"
Kallansa yai yanasan gano fuskar sai dai ya kasa, Ashraf yai murmushi yace " mijin Nafi ne."
Nan fa aka dau salati, nan Ashraf ya zayyane musu komai, Inna ta nemi yafiya shima datti ya nemi yafiyar ta data Nafi.
Sun dade kafin daga bisani suce zasu tafi,Datti yace ai auransa nanan da matarsa, jin matsalar data sameshi yasa Ashraf ya ciro kudi masu yawa ya bashi yace ya sai wasu dabobbin, sannan suyi shawara in sunfisan zaman nan to in kuma sunfisan birni sai ya turo a daukosu.
Nan ya musu sha tara ta arziki suka fito, kowa sai sha'awar Nafi yake, nan Hanne ma dataji labari tazo taganta alokacib itakuma 'ya'yantama 2.
Su kadai suka taho dan dan litti yace sai yayi kwana biyu, zai dai dawo lokacin bikinsu da Nafi.
***********
Duk yanda Ashraf yaso su kebe da Nafi abin yaci tura har ranar zagayowar sati, Nafi tayi rabon Iv gida ya cika sai dai Anisa da Umma sukam suna zaune a bangarensu ko fitowa ba sayi.
Nafi da kanta ta sai kusu kayan da zasu sa a cikin kudin dake katin da ASHRAF ya bata.
Ta aikama Anisa da umma.
Hall aka kama, ga innarta ta zo itada mahaifinta da hanne, dama ta shirya musu dinkuna.
Su ferry da Little amara kirjin biki kenan sai hidima sukeyi, duk inda Little ta wuce Habib binta kawai yake da ido, sosai guri ya cika Abdulkadir wanda ke kula da dan siyasan nan shima yazo dan yanzu ya zama babban mutum Ashraf ya bude mai shago babba anan titin Zoo road inda yake saida kayan masarufai yanzo ko motar da yake hawa ka kalla sai ka kuma kallo, tunda ya iso shikuma ya kyalla ido yaga ferry hankalinsa ya tashi, sosai ta birgeshi.
Anyi shagalin biki sosai mutane kowa ya tayasu murna, sai dai Nafi tunda ta zauna Ashraf ya hanata tashi, ko kiranta Dj yai sai yace a mata uzuri haushi duk ya isheta datai magana sai yace wai bazai yarda a wahalar mai da baby ba.
Haka aka gama taro aka watse, Little da Ferry sune suka kai Amarya Nafi bangarenta inda Little tai ta mamakin sanda aka canza komai na bangaren.
Duk yanda Habib yaso suyi magana da Little abin ya faskara, haka suka kai Nafi bayan sun ajiyeta Little ta juya zata tafi Habib yai saurin binta suna fita yace " Little haka zamu dawamma ko magana babu?"
Kallansa tai tace " yaya da wani idon kakeso na kalleka bayan mahaifina shine sillar lalacewar rayuwar Dady?"
Habib ya kalleta yace " amma wannan ba ya wuce ba?"
Kai ta girgiza mai tai gaba zata wuce, hannu yasa ya rikota da sauri ta tsaya cak gabanta na faduwa yace " Little bantaba tunanin ina sanku haka ba sai bayan faruwar wannan abun."
Juyowa tai ta kalleshi tace " nifa?" tafada hawaye na gangaro mata, tace " nifa da nake sanka tun ina yarinya?"
Wani irin kallo suka shiga yi ma juna.......
Ferry kam da Abdul bansan ya akai ba can na gansu tare suna hira mamaki ya kamani nace hmmm lalai......
Shikam Ango ana watsewa ya yaye mayafin dake rufe a fuskar Nafi yace " su Amarya am gama gudun?"
Tai kasa dakai wai kunya, dariya yai yace " au abin Amaren gaske zakimin?"
Ta turo baki tace " ba amaryar bace?"
Yai dariya yace lalai su Amarya bari in kaiki ciki in gwada ingani ko Amarya ce da gaske."
Zatai magana taji ya sureta..........
Washegari da safe taga bangarenta sosai taji dadi sai dai tace ya dawo da Anisa, ya aminta da shawarar sai dai yace sai dai a gyara mata wani bangaren dake cikin gidan dan kuwa inhar ta zauna dasu gaskiya itace a wahale dan kuwa bazai iya adalci ba zai kuma sanar da ita hakan.
Da zai fita zuwa gun Anisa ne ya zaro takarda ya mika mata yace " uwar gida ga wasiyyar ki."
Yai gaba
Kan kujera ta kwanta a hankali ta bude takardae.
_Zuwa ga sirikata_
_Bansan me zance miki ba, ban kuma san dalilina na yin wasikarnan ba sai dai nasan abu d'aya shine ke rinjayata, dan Allah ina rokonki da kularmin da wannan yaron nawa, amanace na baki kisoshi saboda Allah bawai dan dukiyarsa ba, ki nunamai kulawar dazaisa yamanta shi marayane, wannan ita kadaice rokon da zan iya miki a rayuwa._
_Ga nawa gudun mawar na auranku, ba yawa sai dai wannan nine nake daburin baki ba wanda yasan da zamansu sai ni sai ke sai Lawyer na Salim, nagode kwarai._
Murmushi tai sannan tace " Abba zan kula da yaya sosai, zan sadaukar da komai nawa a kansa."
Nanta zaro takardar dake bayan wasiyyar, takardace ta nuna mallakin wani gida da kuma shago, mamaki ya kamata, da alama kuma gida ne babba sosai hakama shagon.
**************
Bayan shekara d'aya, sauri take sosai tana hada breakfast Ashraf da babynta mace wato Zainab suna zaune akan dinning ya daurata a cinyarsa yana bubuga mata kan dinning da cokali wai tai sauri su yunwa sukeji.
Nafi ta taho da sauri rike da plate ta ajiye a gabansa ta sa hannu ta ja kunnensa da karfi yadanyi kara kadan yace " muguntar ta motsa kenan?"
Harararsa tai ta rike kugu tace "Yaya daga nan ina zaka?"
Yace " zama zanyi in huta kadan kafin na fita aiki."
Ta hade fuska tace " dama shigaban Company an bashi damar kin zuwa da wuri?"
Yace " an fara akaina?" ya fada yana murmushi tace " ni kuma fa daga nan ina zani?"
Yace " makaranta zaki."
Ya fada tare da sumbatare Zee, Nafi tai kwafa tace " kai da zaka zauna a gida, mu da zamu fita shine kake min kidan yunwa?"
Ya tabe baku yace " to ya zamuyi Zee ma yunwa takeji."
Ta kalli agoggo ganin lokaci yayi yasa tai daki da gudu ta dauko mayafinta da jakarta ta zo kusa dashi tamai kiss a kunci sannan tama Zee tace "yaya inkun gama wasab naku ka kaita gun Ya nisa."
Ya mata salute yace " yes ma."
Dariya tai sannan tai waje.
Motarta ta fada sannan ta kata key tai gaba.
Little ansa ranar auransu da Habib.
Dan Litti kuma Ashraf ya turashi kasar Spain dan yin karatu.
*ALHAMDULILA*
_Nan ne na kawo karshen littafina na zuciya kowa da irin tasa, darusan dake ciki Allah ya bamu ikon fani dasu, kura kuran da ke ciki Allah ka yafe mana, Ameen suma Ameen._
Godiya ta musamman ga
*Yan Haske Writers Association*
Ina godiya kwarai da duk wani mai kaunar littafin nan, na gode kwarai da kaunar da kuka nunamai, naji dadi kwarai.
Gaisuwa ga duk 'yan gro din da nake ciki dan yawansu bazai sa na zayyanosu ba sai dai ina mika gaisuwa ta Allah ya barmu tare Ameen....
Masoyana na gode kwarai da kulawarku, da kaunar ku, Allah ya karemin ku a duk inda kuke.
*ILYSM*
*URX AYUSHER MUHD*
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
Compiled by Princess Aysha Muhammad
Copied by Umar Dalha
0 comments:
Post a Comment