Tashin hankali Hadiza tashiga Jin abinda ya fada a firgice Tasha gabansa tana rokonsa cikin mummunan hali na kuka tana rokon ya hadata da 'yarta Ayshatouh Inayah.
Numfashi ya sauke a hankali tareda ajiyar zuciya Mai dumi kafin ya Dan dago ya kalleta kadan cikin nutsuwa kaman Wanda zuciyarsa ba tsananin quna takeba da 'daci takeba yace"
Babban taimakon da zakiyiwa kanki da Abdulsamad shine ki cirewa ranki da kanki tunanin sanin mahaifin Inayah bare ita Inayah din,
Inayah 'yatace Kuma Babu Wanda zaizo Rana tsaka yacemun shine ya haifeta,
Bansankiba Baku nada alaqan komai dake..
Ki nema yarki a Inda kikasan son zuciya yasa kin barta.
Zafi maganganunsa suka farai Mata sbd duk yanda tayi aikin son zuciya abaya Inayah dai yartace Kuma tayi danasani daga ranar data gudu ta barta.
Wlh bazata yardaba taga yarta sannan ya dauketa su bar qasar tasan bazata Kuma ganintaba har abada Dan haka cikin rashin tunani da tauna zancen abinda yafada matan tace"
Har abada saidai ka Kira kanka matsayin mariqinta uban daya raineta Amma bazaka taba sauyata daga nice wadda na dauka cikintaba na haifeta.
Bai tsaya saurarentaba ya fito Kai tsaye yashiga motarsa Yana cewa security a rufe Masa koina.
Cikin zafi ga figi motarsa da matsiyacin speed yabar gurin batareda yajira ganin fitowartaba.
Ikon Allah ne kawai da nutsuwa dayayita kokarin sakawa kansa sbd kada su Inayah su gano halinda yake ciki yakaisa gida lfy.
Yana parking ya fito ya nufi kofar dazata kaisa palonsa na farko direct batareda yabi kofar dazata bi dashi ta palon su Inayah ba kafin ya Isa nasa palon.
Yana Shiga palonsa Kai tsaye hanyar bedroom dinsa ya nufa ya shige tareda Zama kan luxury italian sofa dake dakin ya rintse idanuwansa dasukai jajir.
Ajiyar zuciya yafara jerowa da numfashi Mai zafi yanajin damuwa da tashin hankali Mai tsananin wannan auren da Allah yasa baa dauraba da tako Ina masifun da tashin hankalin bullowa zaiyi,
To Amma babban tashin hankalin da damuwar shine ta yanda Inayah Zata karbi fashin aurenta akaro kusan na hudu.
Tayaya zai iya taro matsalar da Zata iya samunta?
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun.
Miqewa yayi ya nufa toilet ya sakarwa kansa daya dauki tsananin zafi ruwa yanajin zafin kan na tsananta.
Da ruwan dumi yayi wanka ya fito ya saka blue pyjamas sai sanyayyan Chanel na jiki ya kashe wayarsa tareda jefarwa gefe ya hau gado zauna Dan yasan yau koda qyaftawar Ido bazai rintsaba sbd fitina da tashin hankalin dayake jiransu da safe.
Umma Hadiza ma cikin masifaffen tashin hankali da tsoron AA MAJEED yabar qasar da inayah ta iso gida jikinta Babu Inda baya kakkarwa ta silale tashige dakinta batareda kowa yasan fitarta da dawowartaba ta rufe daki tareda zubewa qasa tafara kuka Mara sauti tana cewa"
Ya Allah kagani rashin mafita da madafa da Sharrin shedan ya hanani tawakkali na gudu nabar 'yata badan bana tsananin sontaba ya Allah nayi shekaru cikin qunci da damuwa da tawakkali ya Allah kada kabari wannan bawa naka ya tafi da 'yata wata qasarda bazan Kuma jinsu ko ganinsu.,,ya Allah ka duba maraicina ka hadani da 'yata,
Allah ka kawo Mana sassaucin wannan masifar data kunne Kai da tashin hankalin dazai biyo goben sanadin fashin auren yaran Nan.
Kuka takeyi sosai tana rokon Allah sassauci da mafita.
****Daga AA MAJEED har umma Hadizan Babu Wanda ya rintsa yanda sukaga Rana haka sukaga dare da safiya.
A gidan A MAJEED da zallar farin ciki iyalan gidan suka tashi Dan ko su Anty Hafsat duk a gidan takwana da yaranta gasu Safnah da Neesah dasu Daman tuni suka tare sai Yan uwan umma yaganah guda biyu dasuka zo bikin Dan tayata Murna dakuma samun abun arziki.
Dr farhat dasu Mimi ma tunda safe suka iso gidan kaman dasu aka kwana.
Kowa farin cikinsa bayyananne ne sbd duka aurarrakinta da ake fasawa Babu Wanda yazo ranar Daurin auren sai wannan yau gashi Allah yayi anzo daurin auren a wanni kadan ne suka rage tazamata cikakkiyar matar Heart dinta Abdulsamad salees halak malak.
Cikin kayan baccin data kwana dasu Riga sa wando masu santsi tafito da hula akanta fuskarta da dukkanin fatar jikinta sunyi fresh sai sheqin kyau da gyara sukeyi gashi yanayin data fito din kaman wata qaramar yarinya.
Kai tsaye dining ta nufa tana cewa"
Yunwa nakeji zubbi kawon tea nafara sha.
Tea da doughnuts masu laushi guda uku zubbi takawo Mata tana cewa"
Mint tea din Sir is ready
Zaa shirya Masa ne a dining kokuwa?
Tana Shan tea dinta tace"
No ki shirya zan Kai Masa palonsa yau da mutane a gidan bazai shigo ciki ba,
Harda dessert din kin kammala hada Masa?
Yes Ma.
Ok kije ki hado zan Kai Masa.
Ok Ma.
Juyawa tayi ta koma kitchen din Dan hadowa takawo Mata.
Wayarta ta daga tana kokarin Nemo numbern Heart sai gashi kiransa yashigo wayarta da farin ciki bayyane kan fuskar ta dauka da Yar muryarta Mai shagwaba tace"
Good morning Heart.
Wani sanyin farin cikine yakuma cika ransa sbd ranar yau din daqyar yaga garin ya waye
Cikin wani irin girmammen farin ciki yake Mai nutsuwa,
Allah yau yacika Masa burinsa na mallakar Inayah amatsayin matarsa dazata Zama uwar yayansa.
Ji yayima farin cikin yasaka jikinsa sanyi Musamman data Kuma kiran sunansa da HEART.
Muryarsa a sanyaye yace"
Morning baby,
Kin tashi lfy?
Yaya shirye shiryen da hayaniyar su Anty Hafsat?
Murmushi kawai tayi Tana cewa"
Idan anty Hafsat tajika Zata sa a 'daga tafiyan Amarya yau sai wani satin.
Wat? aikuwa Dana tare a gidan Abbi Nima.
Dariya tayi tana cewa"
Zan kaiwa Abbi breakfast zankiraka idan nafito
Kisses.
Murmushi kawai yayi Yana kashe wayar gabaki daya muryarta ta kashe Masa jiki yayi sanyi sosai,
Jin yayi har zuciyarsa na yin sanyi.
Daukeda tray ta nufi hanyar palon Abbi tana murmushin wayar data Gama da Heart.
Knocking kofar tayi ahankali tareda budewa ta shigo da sallama tana kallon palon da Babu kowa sai Sanyin AC dake aiki da Qamshin turarensa daya Gama Kama koina na palon.
Hanyar bedroom dinsa ta kalla tana ajiye tray din kan table.
Tabaro wayarta bare takirasa ta sanar Masa tana Palo Dan haka tana ajiyewa ta juya ta fice.
Breakfast ta tadda duka kowa nayi wasu a dining wasu a dakin umma yaganah Dan haka tayi joining Dinsu itama tana cin Doyan da aka soya kadan.
Har qarfe Tara ta buga da mintuna Abbi Bai fitoba sbd baisan ta Yaya zaifara cewa su Inayah su shiryaba zasu bar qasar ayau datake ganin ranar Daurin aurentane.
Yarasa ta Ina zai fara,
Ta Ina zai tarbo wannan rikitaccen matsatsen yanayin.
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun.
Gashi jama'a da dama manyan tunanensu sai kiransa akeyi ana tayasa Murna wainda bazasu samu damar zuwaba basa qasar dama wainda suna qasar uzuri bazai basu Daman halartaba.
Kansa Neman bugawa yakeyi,
Duk wannan masifar damuwarsa da tashin hankalinsa na Inayah ne da Zata shiga mummunan hali daga lokacinda aka Kuma fasa aurenta dakuma wannan mummunan labarin da har abada baya kaunar tajisa cewan bashine mahaifinta Wanda ya haifetaba,ko alaqan Jini basuda a taqaicema baisan mahaifinta da mahaifiyarta ba Dan zuciyarsama badan ya tattabar akansaba cewa uwa na iya yafe danta da bama zai yarda da cewan Hadiza ce ta Haifa Inayah ba Dan uwa Bata iya Yar da 'danta
To Amma hakan tafaru dashi sbd tasa uwar ta yafesa sbd zarginsa na aikata abinda Bai aikataba bayajin ma zai taba iya aikatawa.
Tayaya zai Bari Inayah tasan wannan 'datacciyar Gaskiar?
Baya fatan ko kadan ta 'dandana 'daci Mai kaifin gaske da ciwon uwa mahaifiyarka ta gujeka sbd wani dalilin banza Wanda Koda bakada uba tunda qaddara ta Samar da Kai baka cancanta hakanba.
****Hadiza Koda safiyar ta waye tagama fita nutsuwa da hayyacinta,
Bata ji Bata gani matuqar ba 'yarta Ayshatouh AA MAJEED yadawo Mata da itaba,
Tayi gangancin rabuwa da yarta shekarun baya Amma yanzu ko zaisa a daureta asibitin mahaukata sbd arzikinsa wlh bazata yardaba saiya Bata yarta tadawo hannunta ciki kuwa harda Koda Zata qaryata kanta agurinsa da cewa ba itace ta Haifa Abdulsamad ba idan yaso a daura auren su tafi da Inayah Adamawa suna zuwa can ta fada Gaskia a Raba auren 'yarta dai tadawo hannunta.
Wannan rubabben tunanin shedan ya qissima Mata ta tashi hankali tashe Musamman ganin lokaci na tafiya tasan rasai AA MAJEED din zai bar qasar da inayah kafin lokacin daurin aure Dan haka a rikice ta iya watsa ruwa ta kimtsa kanta sbd kada Wanda yagano halinda take ciki na firgici da tashin hankali.
Da mamaki su Haj balaraba suke kallonta lokacinda ta fito dakinta a shirye tsaf harda gilashin fuska sbd kada a gano tsananin kumburin da idanuwanta sukai
Gashi iyaye maza yanne da qannen mahaifinsu Abdulsamad din sun iso yanzu da safen daga Adamawa suna hanyar isowa gidan kafin lokacin daurin auren yaqarasa Amma ta fito tana cewa zataje karbo saqo tadawo.
Kafin Haj balaraba data saki bakin kallonta tayi mgn umma Hadizan ta wuce hannuwanta na rawa sosai keys din motar ma daqyar ta iya damqesu suka tsaya a hannunta ta Isa motar ta bude ta shige da gudu tabar gidan tana kallon agogo.
A daidai wannan lokacin Abbi yagama yanke shawarar tura Inayah da umma yaganah su fara wucewa qarfe goma Sha daya jirginsu zai tashi shikuma zai tsaya ya bawa mutanensa dasuka zozzo hakurin fashin auren batareda Inayah tasan fashin auren akaiba idan yaso Bayan kwana biyu zai samesu acan yasan yanda zai rarrasheta ya fahimtar da ita fashin auren ta wata hanyar.
Dan hakan Kai tsaye yakira umma yaganah a waya ya sanar da ita ta shirya itada Inayah akwai Inda zasu qarfe Sha daya kafin lokacin daurin aure.
Yana fadan hakan ya kashe wayarsa sbd kada tayi Masa tambayar komai.
Agogo ya kalla yaga qarfe goma da kusan rabi Dan haka ya miqe ya nufi toilet yayo wanka cikin nutsuwa.
Daure da Brown towel mai kauri a qugunsa ya fito farar fatarsa sai tsiyayar ruwan wanka takeyi so freaking fresh.
Gaban mirror ya nufa ya tsaya ahankali Dan baya Zama gaban mirror kaman mace saidai ya tsaya a tsaye yayi komai.
Lumin body moisture ya shafa tareda fesa spray din Paco Rabanne
Yayi brushing sumar kansa tareda sauran Shirin daya saba yagama ya wuce closet din tarin kayansa.
##MAMUH#
##MARRIAGE/INAYAH.
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/26, 8:45 PM] Sweet sis: *_29_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Qarfe goma da minti arbain su Umma yaganah da Inayah suka fito tana shirye cikin Tsadadden red Australian lace mara nauyi dinkin fitted gown daya zauna jikinta da kyau
Shafaffen cikinta zuwa hips dinta dake Dan baje sun fito da kyau cikin kayan ta yafo 3D veil dinta kayan touches na lace din.
Zallan qamshi Mai sanyi da nutsuwa take fitarwa
Kyakkyawar fuskarta sai sheqin farin cikin dake ranta take fitarwa.
Suna fitowa harabar gidan Abbi ma na fitowa Sanye cikin wata fitinanniyar farar shadda Mai tsadar gaske da laushi.
Basu taba ganinsa da babbar rigaba sai yau shima sbd Inayah data nace abbin saiya saka Kaya masu babban Riga a aurenta sbd kada mutane da dangin mijinta su ringa cewa babanta Bai manyantaba sosai.
Qamshinsa ne ya gauraya iskar gurin suka zuba Masa Ido dukkaninsu Musamman Inayah dake washe bakin farin ciki tana cewa Abbinta na Musamman ne aduk Inda yaje.
Neesah kuwa dasu Safnah take kowaccensu taji da Abbi matsayin yayan Inayah ne ba mahaifiba Babu abinda zai hanasu aurensa.
Umma yaganah ma cikin kulawa da farin cikin ganinsa cikin Shiri da adon auren Inayah a hankali tace"
Masha Allah laquwata.
Allah yaqaro girma da 'daukaka
Yabaka tsari da kariya
Yayi maka albarka tareda kawo dawamammen farin ciki rayuwarka data zuriarka.
Amin"
Su Safnah dasuka jita suka amsa suna dauke idonsu daga kallonsa sbd grima da kwarjininsa.
Ahankali ya kalli fuskar Inayah ganin farin cikin dake tattareda kowane irin yanayinta,
Ta Bangare daya baisan tayaya zai Samar dasuba qasar zasu Bari yau.
A natse fuskarta daukeda murmushi tace"
Abbi you look handsome,
and...
Katseta yayi a nutse da cewa"
Inayah kuje karkuyi latti Inda zaa kaiku.
Kallonsa tayi a natse tana cewa
"Abbi Ina zamuje?
Dan rufe idonsa yayi ya bude tareda kallonta cikin tsananin kulawa yace,
"Idan kunje Zaki gani.
Da murmushi akan fuskarta tace"
Okay.
Umma yaganah ya kalla sukai gaisuwar safe d basuyiba tunda ba haduwa sukaiba.
Su Neesah ma da Safnah cikin girmamawa sosai suka Masa Ina kwana kafin ya kalli umma yagana a natse cikin Dan takaita magana yace"
Idan kunje komai na hannun Ahmed zai damqa miki komai
Zanzo daga baya.
Tsit suka Dan Yi da mamaki suna kallonsa duk da basu gane komaiba akan Inda zasuje sai jikin umma yagana yayi sanyi taji zuciyarta na Neman shiga wasi wasi.
Inayah ma jikin nata taji yafara sanyi take ta kalli abbin da rauni Amma batace komaiba.
Juyawa yayi yana kokarin Isa motarsa aka bude gate motar CM tashigo ko qarasa rufe gate baayiba motar Dr Abdul ta Sako Kai itama.
Umma Hadiza ce aciki Kuma tanayin parking idonta ya sauka kan Ayshatunta take taji wasu hawayen da tsananin kaunar yarta suna finciko Mata tako Ina,
Kaunace Mai tsananin gaske wadda uwa kewa 'danta Bayan tacire ran samu ko ganinsa har abada.
Hawaye takeyi sosai tana kallon Inayah din tanajin tamkar taje ta rungumota tayita kissing dinta tana fada Mata yanda take kaunarta da qaddarar datashiga akan cikinta.
Wani zafi da tirnikin bacin Rai da tashin hankali ne ya taso Mata ganin suna kokarin shiga mota tasan wlh qasar zasu Bari suna fita gidan yau bazata Kuma ganin 'yartaba Wanda haukar da Allah ya taqaita Mata lokacinda tayi danasani tashiga Neman yarta to haukar zatayi yanzu matuqar takuma rasa Ayshatouh.
Hankali tashe ta fito motar da gudu ta nufosu Inayah tana Kiran sunanta.
Dakatawa umma yaganah tafarayi tana kallon Hadizan kafin Inayah itama ta dakata suna kallonta cikeda mamaki.
Inayah kuma umman na isowa gabansu ta kalleta da kyau taga yanda idanuwanta da fuskarta sukai jajir tashin hankali bayyane kan fuskar umma Hadizan
Wani mummunan bugawa zuciyar Inayah tayi har Saida ta dafa Neesah dake gefenta.
Muryarta na rawa itada umma yagana ma data shiga zullumin abinda zasuji Dan dagani ba lafiyaba murya a hautsine sukace"
Umma Hadiza....
Kasa tambayar abinda ke faruwa sukai sbd tsoron abinda zasuji.
Kai tsaye Inayah taji wani jiri na Neman dibanta kafin tayi kokarin dafe kanta taji muryar Umma Hadiza a hargitse tana cewa"
Dan Allah kadaku tafi wlh qasar zaku Bari kuna fita,
Aurenki Inayah da Abdul bazai fas....
Inayah Bata gama jiba qafafuwanta suka yanke zuciyarta na neman bugawa ta tabbatar fasa aurenta yanzuma akai ko ake neman Yi.
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun"
Mezan gani hakan Ni yaganah,
Innalillahi, innalillahi.
Hawayene ke kokarin gangarowa Inayah Amma tashin hankali yaqi Bari umma yaganah dasu Neesah da duk suka shiga tension din suka fara kokarin kamata sukoma ciki da ita
Umma Hadiza ma cikin tsananin tashin hankali da dimuwa ta ringa maimaita ba fasawa nace anyiba Dan Allah Inayah karki shiga wani hali,
Babu fashi aurenki da Abdulsamad,
Zaa daura zamu tafi dake adamwa zan Baki duk wata soyayyar uwa da Baki samuba,
Inayah, Inayah.
Sam Inayah Bata gane kalma daya da umman Abdul din take fada sbd zuciyarta bugawa takeyi sosai da tashin hankali da attack data samu take Dan hakan komai Bata ganewa sai rawa da jikinta keyi.
Su umma yaganah kuwa take ta fara tunanin daqyar idan umman Abdul nada lafiyar qwaqwalwa sbd duk tabi ta rude da Kiran Inayah da suna biyu.
Abbi da hankalinsa nakan CM dayazo daukansa su wuce daurin auren tare Bai lurada Hadiza ce tashigo a motar Dr Abdul ba Saida yaji salatin da umma yaganah ke qwalawa da qarfi hankalinsu duk yakoma Kai cikeda mamaki da zafin zuciya Mai qarfi ya kalli umma Hadiza Yana kallon 'yarsa dake Neman siqewa cikin tashin hankali numfashinta na neman gagararta.
Cikin bacin Rai Mai qarfi ya qaraso gurin tareda kallon umma yaganah yace"
Ku kaita ciki Dr farhat ta dubata da sauri.
Kan umma Hadiza dake kokarin binsu hankali tashe ya maida kallonsa idanuwansa na Neman sauyawa yace"
Ni Zaki sama da duk abinda kikazo dashi,
Me kika fadawa Inayah yasata cikin wannan halin?
Ganin su umma yaganah Basu qarasa shigewa da Inayah ba yasashi juyawa tabiyo bayansa tana cewa"
Dan girman Allah da manzansa kaban 'yata,
Ka sanar da ita nice mahaifiyarta,
Dan Allah kada ka cutatar da uwar dake cikin qunci tsawon shekaru ta hanyar Hana Mata 'yarta....
Babban palonsa suka shigo ta tsaya gabansa idanuwanta na zubda hawaye sosai cikin mawuyacin hali tafara rokonsa akan ya sanar da Inayah itace mahaifiyarta.
Mamakine ya Kama CM dake tareda A A MAJEED din tako Ina.
Idan ya fahimta Kuma yagane wannan matar Inayah take Kiran 'yartace.
Itace mahaifiyar Inayah?
MAJEED da idanuwansa ke bayyanarda tsananin bacin ransa da fushinsa ya kalla yasan yau kam ransa yakai kololuwar baci tunda ya bayyanarda fushinsa.
Bai iya cewa umma Hadiza komaiba sbd baimasan mezai fada mataba,
Da alama tanada ciwon Kai Dan hakan tako Ina lalata Masa Al'amura zatai.
Cikin kosawa da ganinta gabansa ya bude Baki a gundure yace.
"Me kika fadawa Inayah da har kika data cikin wancan halin datake ciki?
Idan kin sanar da itane matsayinki a gunta kinyi babban kuskuren da....
Cikin sauri da bayyanarda gaskiyarta ta katsesa da cewa,
"Banfada Mata komaiba
Maganar aurenta da Abdul kawai nake fada musu.
Wani irin rufe Ido yayi ya bude cikin baqin ciki da takaici yace"
Kinsan shima hakan matsalar da Zaki haifar mata?
Kinsan halinda Zata iya Shiga akan hakan?
Meysa zakiyi kutse acikin Al'amarin da bakisan Yaya yake tafiyaba?
Numfashi Mai zafi ya sauke tareda fitarda ajiyar zuciya Dan bazai iya wannan tashin hankalinba yanzu.
dauke kallonsa daga kanta yayi a natse yace"
Idan harkina kaunarta a matsayin uwa kaman yanda kika fada kibarta taci gaba da rayuwarta batareda kin dandana Mata 'dacin rashin karbuwa daga uwar data haifeta kokuma dacin hanyar da aka samar da ita.
Maganarsa ta qarshe tayi mummunan girgiza,
Kenan shima daukan yake ta hanyar banza ta samu Inayah tunda yaga ta gudu tabarta?
Wasu hawayen baqin ciki Mai tsanani ne suka gangaro Mata ta dago da jajayen idanuwanta ta kallesa zuciyarta na quna da bacin Rai tace"
Na tsaya rokonkane ka bayyanarwa 'yata nice na haifeta sbd nabaka haqqinka amatsayin Wanda ya reneta da Amana ba cutatarwa bawai Dan narasa damata ta uwa agaretaba.
Kanason nuna dukiya ka rabani da 'yata rabuwar har abada Amma hakan bazai taba karbuwaba gurina.
Wlh bazan yardaba Sharia Zata karbamun 'yata tadawo hannuna.
Mamaki tafara basa ta yanda take iya furta kalamai batareda taji kunyar kantaba na abinda ta aikatawa 'yar a baya harma dashi.
Idan tana maganar qarfin ikone
To zai nuna Mata qarfin iko akan Inayah.
Cikin sautin bayyanarda gajiya da lamarinta yace"
Wannan shine Karo na qarshe da Zaki iya zuwa gidana ko kusantar daya daga cikin iyalin gidana,
Zaki iya tafiya.
Kallon baqin ciki da damuwa lokaci daya take Masa tace"
Zantafi Amma kasani nice uwa dana Rena cikin Inayah nakuma haifeta har abada babu wani ko sunan dazai sauya mun matsayi akanta,
Nice nafi kowa cikakkiyar dama da iko akanta,
Kaikuma damarka da ikonka akan Inayah ya tsayane a matsayin mariki Kuma zai tsaya ahakan ne har abada.
'ya mace ce duk iko da isar da zaka nuna akanta saitabarka har abada sbd aure zatayi take gidan wani Kuma a qarqashinsa Dan hakan idan kafi qarfin hukuma bazakafi na shari'a ba,
Sharia Zata dauke inayah daga hannunka tabani 'yata,
Idanma shariar kafita ikone zamuga wannan sbd duk ikonka akanta bazaka taba aurentaba Dan kuwa aurene kawai zai riqe 'ya mace aguri wani ikon ya kasa dauketa dauketa
Kuma da yardar Allah Inayah bazata rufa wata a hannunkaba saina karba Yana Koda ta hanyar kawo Mata wani mijin auren ne.
Rintse idanuwansa yayi cikin takaici da baqin cikin ganin Hadiza agabansa.
Duk shekarun mace hankalinta da tunaninta na banza ne lokuta da dama,
Sam kansu toshewa yakeyi hat basusan me suke fadaba.
Idan Hadiza na tunani haryanzu akan shari'a Zata karba Mata Inayah a hannunsa to zai sakata a spot dinda ko shariar bazata iya dauke inayah daga hannunsaba a gurin.
Bai iya kallontaba sbd siqewa kai tsaye yace.
Kije Ina jiran shariar.
A fusace da baqin ciki ta juya tana hawaye sbd ba haka tasoba son tayi ya amince ya hadata da 'yarta idan Tai Masa barazana da sharia sbd tasan bazai taba son duniya tasan Inayah ba 'yarsa bace.
CM da kansa yayi matuqar daurewa da daukan zafi kusan yagama gano kan zancen shine Inayah dai ba Amininsa neba ya haifeta Kuma wannan matar itace mahaifiyar tata.
Baisan ya zancen yafaruba Amma tabbas a wannan tsukakken yanayin yasan akwai matsala Babba matuqar wannan Al'amarin zai shafa daurin auren yau.
Agogo A MAJEED ya kalla yaga Sha daya da rabi harta fara wucwa.
Bai iya cewa Amininsa komaiba yace su tafi kawai.
Shima CM tunda ba qaramin yaro bane yasan yanzu ba lokacinda zai tsaya tambayar MAJEED din meyake faruwa bane saidai idan an natsa zafi da dacin ransa ya sauka.
Suna fitowa Kai tsaye yabawa Bosco odar kada akuma barin motar Abdulsamad tashigo gidansa matuqar bashineba aciki.
Kai tsaye babban masallacin dake kusada gidan iyayen CM suka nufa Inda anan ne zaai daurin auren dama.
Mutane ne tako Ina sun cika anguwar ga securities da jamiaan tsaro kusan tako Ina sbd akwai manyan mutanensu dasun iso tuni Dan mintuna goma Sha takwas suka rage ga daurin auren.
Wani irin zafi da 'dacin zuciya yakeji ganin tarin jama'ar dasukazo Dan sheda daurin auren ga dangin Abdul ma da dama sun iso shi kansa Abdulsamad din ya iso gurin cikin shigar alfarma ta angon dake cikin tsananin farin ciki.
Qarfe goma Sha biyu daidai aka nutsu aka fara daurin auren Wanda CM ne da kansa yayi wakilcin Amarya mahaifinsa Alhaji babbah yayi wakilcin Ango sauyin daya faru tsananinsu take agurin.
Kafin iyayen Abdulsamad su Ankara sukaji ana shelar an daura auren ABDULMAJEED ABDALLAH da INAYAH A MAJEED.
#MAMUH#
#AFADA ALKHAIRI KO AYI SHIRU/#MASU YI DANI A BAYANA.
*_ZAFAFA BIYAR_*
*_INAYAH_*
_Mamuhgee_
*_GURBIN IDO_*
_Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/26, 8:45 PM] Sweet sis: *_30_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Kusan da yawan jama'ar gurin Basu fahimci wane ABDULMAJEED din ake nufiba sai Amin kawai suke amsawa da ita suna qarawa da adduar zaman lafiya da albarkar aure sbd sunan Abdul din da aka ambata cikin sunan basu wani bambamceba tunda dai kowa yasan sunan Ango Abdul.
Iyayen Abdulsamad Wakilansa sune suka saki Ido da Baki cikin zallar mamaki da firgici Jin andaura da wani Abdul din daba nasuba Dan Babu Wanda ya tsaya kawo wani rubabben tunanin AA MAJEED mahaifinta ake nufi.
Shi kansa Abdulsamad kasa tantance meyake faruwa yayi saiyafara tunanin ko matsalar fadan sunan aka samu Mai fadar be kila ya rude ya fada sunan mahaifin Inayah a matsayin uba Kuma yadawo ya fada amatsayin Miki Wanda aka daura auren dashi.
Jin zuciyarsa dai takasa yarda sai tsinkewa data farayi yasashi kokarin baro Inda yake Dan zuwa gaban wakilan daurin auren yaji wane rudadden ne Mai sanarwar dazai saka kansa kuncewa da zancensa.
Kusan dai jama'a tsakani da Allah duk Basu ganeba idan ba wainda suke Yan uwan Abdulsamad ba sbd suka Sarai sunji ba sunan angonsu aka fadaba
Sauran jama'a da Basu ganeba tunda ba hankali mutane ke badawa sosaiba gurin daurin aure sai an daura zu amsa da Amin da fatan Alkhairi su tafi Dan haka aka ringa gaggaisawa ana Allah sanya Alkhairi ana neman fara watsewa.
Ciki mamaki Mai tsanani da kokarin danne bacin Rai yayan Marigayi salisu ya kalli CM da Alhaji babbah kafin ya maida kallonsa kan AA yace"
Alhaji MAJEED mufa bamu gane abinda yake faruwaba anan,
Auren da zaa daura biyu ne Daman kokuwa dai Wanda zamu daura dinne aka daura da wani 'dan ba namuba?
Dan idan naji daidai sunan yarinyar dai shine wadda zaa daurawa danmu da ita.
Duk Inda damuwa da 'dacin Rai Dana zuciya suke sune a dabaibaye da A MAJEED,
Bai taba samun kansa a yanayi Mai 'daci da qaqa nikayiba irin wannan Rana,
Ko a wancan lokacin daya hadu da qaddarar samun Inayah baishiga damuwa da quncin dayake cikiba yanzu.
Me zaiyi da auren 'yarsa ta kansa?
Wace mummunar masifa Hadiza ta sakasa daya qare qarshe a auren Inayah 'yarsa??
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun,
Yau shima yahadu da qaddarar Sharrin shedan Dana zafi da yanke hukunci cikin fushi.
Duniyama idan taji shine ya aura 'yarsa zai anyi Allah wadai da tunaninsa.
Gashi garin yanke hukunci kada Hadiza ta ra'bi Inayah har Inayah tasan bashine mahaifinta ba yaje cikin fushi da bacin Rai yayi abinda ba iya Inayah kadaiba da bayason ta taba sanin bashine ya haifetaba duniyama kowa zai sani yanzu Wanda harga Allah yaso riqeta amatsayin ya har abada batareda kowane Dan Adam yasan bashine ya haifetaba sbd daga lokacinda mahaifiyarsa datafi kowa saninsa da tarbiyarsa ta tuhumesa tareda yarda da zai iya aikata Zina harma ya Haihu a hanyar Zina yasaka a ransa ya karbi Inayah amatsayin 'ya dabazai taba barin wani yasan bashine ya haifetaba ciki kuwa harda mahaifiyarsa saigashi Rana tsaka Hadiza ta sakasa a mummunan tarko.
Hadiza itace masifar rayuwarsa yau ya tabbatarda hakan sbd akaro na biyu takuma sakasa masifar da kusan tafi ta baya yaqare da rataya igiyoyinsa na aure a wuyan 'yarsa baisan wane mummunan Al'amarin Zata Kuma kawo masaba a gaba Dan yasa zaifi wainnan zauta Kai da qwaqwalwa.
CM ne yayi saurin kallonsu Alhaji buhari ganin ransu yafara baci sosai sunason Jin bayanin abinda yake faruwa Dan haryanzu sunkasa yarda da auren matar 'dansu aka daura da wani sbd har lokacin Babu Wanda yakawo da AA MAJEED aka daura auren tunda ba abune Mai yiyuwaba uba ya aura 'yarsa Dan hakan kaf gurin Babu Wanda yakawo ABDULMAJEED mahaifinta ake nufi suma su CM da Alhaji babbah sunqi barinma agane wane ABDULMAJEED Dadi da qari kusan duniya da AA MAJEED tasansa bada cikakken sunansaba ABDULMAJEED ABDALLAH.
Cikin qarfin hali Abbin yataso Yana sallama da mutanensa dake wucewa suna Masa Allah ya sanyawa auren 'yarsa albarka Yana amsawa da amin.
Kaurewa da gurin yayi da jiniyar motocin 'yan sanda da civil defense ga yawan jama'a kowa nata kokarin miqa barkarsa ya wuce shiya taimakawa su CM gurin Jan su Alhaji buhari zuwa cikin gida palon Alhaji babbah Wanda shine da kansa ya iya fara tankwafarsu sbd fadan tozarci dasukagani qarara dasuka fara yi.
Alhaji buhari ne mai iya dan danne tsananin bacin ran dasuke ciki su Alhaji kabiru 'yan Nan Hadiza kuwa kasa dannewa sukai suka fara zuba masifar tashin hankali Dan duk Inda ake wulaqantawa an wulaqantasu ankuma tozartasu sun debo jiki tun daga adamawa sunzo Lagos daurin aure ace suna zaune suna kallo kaman wasu gumaka andaurawa amaryar aure da wani koma Dan uban waye ai Basu cancanta wannan tozarcinba.
Abdulsamad a rikice cikin tashin hankalin daya zaburo Masa tako Ina ya ringa kutsa jama'a Yana neman iyayensa maza dasune wakilan Amma Bai gansuba Dan haka ba Shiri ya zare hular kansa Yana Jin akwai gagarumar matsala Mai tsananin girman gaske kuwa.
Saida mutane suka rake sosai aka fara Ankara da abinda yafaru ganin rudewa da tashin hankali da Abdulsamad yake ciki da yawa wainda suka dauka sune basuji sunan daidaiba suka fahimci cewan daidai sukaji Ashe auren ne dai bada Dr Abdulsamad aka dauraba.
Take kurar hayaniya tafara kaurewa daga gurin
Ganin Abdulsamad na Neman zarewa yasa Abbi daya Gama sallamar baqinsa ya Kama hannunsa sukai cikin babban gidan na Alhaji babbah.
Qanin CM Professor Ibrahim shine ya tsaya yaqarasa sallamar sauran jama'ar aka watse wasu nata sake sawa auren albarka wasu Kuma na shiga mamaki da son Jin yanda wannan mugun Al'amarin yafaru hakama wasu take suka ringa maimaitawa wainda basujiba cewan sunan fa AA MAJEED ne aka daura dashi.
Mamaki da firgici wasu suka Kuma shiga Jin sunan Wanda aka daura dashi din aikuwa take tun anan suka fara shigar da gulmar Internet.
An watse tsaf ba kowa Dan hakan Alhaji babbah ya kalli su Alhaji buhari dake cikin mummunan yanayi na bacin Rai da fushi.
Cikin sanyi da taushin murya ga Wanda baa kyautawaba yace"
Alhaji buhari kuyi hakuri nasan baa kyauta mukuba tako Ina Musamman da baa sanar daku komaiba ko fahimtar daku komaiba Saida kukazo cikin baynar jama'a hakan tafaru.
Dr Abdulsamad dake tsiyayar wasu ruwan zufan tashin hankali da fita hayyaci ya kalla duk saiyaji jikinsa yayi sanyi da tausayin Abdulsamad din sbd duk Wanda ya kallesa yasan yana tsananin son Inayah so Mai tsanani,
Tayaya Za'a kallesa ace Masa uwarsu daya,
Uban ne kawai Basu saniba ko dayane tunda A MAJEED cewa yayi uwar kawai yasani itama a bisaga qaddara.
Shi kansa Dr Abdul idanuwansa duka da hankalinsa suna kan Alhaji babbah sbd ya fahimci agurinsa zasuji abinda suke buqatan ji Wanda zuciyarsa ayau harbawar datake yasan ta wuce kowane irin tsari da akeson zuciyar Dan Adam ta buga.
Babu wani yaren dazai gane ayanzu idanba na maganar aurensa da Inayah bane.
Dan jinjina maganar dake bakinsa Alhaji babbah yiyi tareda dauke idanuwansa daga Abdul ya maida kan su Alhaji buhari dasuke manya zasu fahimtarsa a natse yace"
Ita wannan yarinya Inayah wadda mahaifiyar Abdulsamad ke Kira da Ayshatouh 'yar mahaifiyar Abdulsamad ce wadda ta jima da Bata tun jarinta Wanda A jiyan bayan haduwar mahaifin Inayah Wanda yanzu zance mijinta da ita mahaifiyar tasa suka tabbatarda Dr Abdulsamad da Inayah uwa dayace ta haifesu,
Dr Abdulsamad da Inayah uwarsu daya Kuma kaman yanda duk muka sani Babu aure tsakaninsu,
Sauyin Wanda aka daura dashi Kuma wannan nine Nan na tayasa yanke wannan hukuncin sbd kaman barazana da ita mahaifiyar yarinyar takeson tayiwa MAJEED Dan hakan muka yanke hukuncin ya aureta.
Dan haka a taqaice ABDULMAJEED shine ya aura AYSHATOUH INAYAH,
Shine mijinta ayanzu,
Sauran bayanin Inda ita mahaifiyar Dr ta samo yarinyar har suka Zama uwa daya da Dr wannan saidai aji daga gareta.
Wani mummunan shock da matsiyacin zufane ya fesowa Alhaji kabiru zuciyarsa na harbawa da mamaki ya juya ya kalli malam Umar Dan uwansa Wanda harya fisa jiqewa jagab da zufa.
Alhaji buhari daya Gama samun qullewar Kai da mamaki da Yar rudewa yace'
Inayah kuma Yar Hadiza?
Tayaya?
Garin Yaya?
Yaushe?
Shaqewa muryar Alhaji kabiru tayi a Rikice murya na yankewa yace"
Inayah itace AYSHATOUH????
'yar da Hadiza ta Haifa ranarda mahaifiyarmu ta rasu??
Da tashin hankali malam Umar ya karba da cewa"
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun
Tabbas Hadiza ta haifi 'ya takuma saka Mata Ayshatouh.,
Idan har ya tabbatarda Hadiza ce dimun wadda tabar Masa 'ya to tabbas kuwa wannan 'yar ta Hadiza ce halak malak sbd ranarda ta haifeta ranar tabar gida.
Sai alokacin zufa ta karyowa Alhaji buhari Jin dai ta tabbata Hadiza haihuwa tayi ba aure bayan rasuwar salisu.
Da sauri malam Umar daya fahimci tunanin dake zuciyar Alhaji buharin yace"
'yar Hadiza 'yar halak ce
'yar sunna Dan kuwa cikinda salisu yabarta dashine muma sai daga baya muka Ankara da hakan Dan haka 'ya 'yar halak ce
Uwarsu daya ubansu daya da Abdulsamad gashinan zaun....." Ya qarasa fada Yana waiwayawa Inda Abdulsamad ke zaune sai kawai sukagansa zube baya numfashi da alama ya jima da sumewa Basu saniba sbd tashin hankalin da kowa yake ciki.
Arikice Alhaji buhari yayi kansa shida malam Umar suna Kiran sunansa Amma da alama ba sumar kadai yayiba kaman harda attack yasamu.
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun""Alhaji buhari yake fada Yana kamo Abdulsamad din da qarfinsa
Ba arziki Dole zaman bayanin yaqare sukai asibiti dashi hankali tashe.
Bayan fitarsu kallon Abbi Alhaji babbah yayi yana nazarin halin tsananin damuwar dayake ciki da rashin ta Ina zai Kama wannan rakitaccen Al'amarin.
Tausayinsa ne Dana Abdulsamad ma dayafi kowa tausayi yanzu Dan yasan Al'amarin zai daki yaron sosai sudai dama saukinsu da hamdalar dasuke shine da baa daura aurenba da komai yafi lalacewa uwa daya uba daya.
Bayason qarawa MAJEED damuwa da wasu zantukan Dan haka ya taqaita da cemasa,
"MAJEED kaje gida kasamu ka nutsa kanka ya sake kafin shima Abdulsamad asamu lafiyarsa saiku zauna duka kuyi taron fahimtar juna,
Itama yarinyar kada kace zaka kasa karban wannan qaddarar sbd ko ahakan Allah ikonsa ne ya nuna,
Haisawa sukace matar mutum kabarinsa
Allah yayi itace matarka shiyasa Bai baka ikon aureba tun kuruciya har gashi manyanci nason zuwa hakama rabon zamtowarta matarka ya hadaka da mahaifiyarta harta dawo hannunka dan ka tarbiyantar da matarka da kanka Dan haka shi Allah Babu ruwansa idan ya jarabta mutum to akwai tanadin dayayiwa wannan bawan idan har yayi tawakkali yacinye wannan jarabawar.
Allah yasa mudace,
Allah Kuma yabaku zaman lafiya yasawa wannan auren albarka.
"Amin" CM ya amsa adduar ta Alhaji babbah Yana cewa"
Allah yaqara girma.
A natse MAJEED shima yayiwa Alhaji babban godia kafin suka fito.
Dayake da lafiyayyar Lexus din CM sukazo Dole shine ya maidasa gida.
Suna Isa gidan Yana ajiyesa harabar gidan yakira matansa yace kowaccensu ta fito su koma gida sbd yasan ba qaramar rigima zaayiba idan zancen auren ya Isa cikin gidan tunda duk matane bare ita kanta Inayah din
Gwara idan zatai Rigimar ya Zama ba kowa a gidan.
##MAMUH#
#LOVE/MARRIAGE/ROMANCE#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107[10/31, 9:42 PM] +234 703 926 9802: *_31_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Sake Shan jinin jikinsu dukkaninsu sukayi Jin cm yace sufito atafi gida Nan suka sake tabbatarda ba lafiyaba
Amma Kuma bilyamin qanin Anty Hafsat ya tabbatar musu da an daura aure,
To Kuma menene matsalar?
Sudai koma menene suna ganin da sauki idan har andaura auren Inayah da Dr Abdul dinta.
Ita kanta Inayah data dawo hayyacinta tuntuni zaune take tana jiran ta Inda labarin halinda aurenta yake ciki zai bullo.
Lokacinda bilyamin ya sanar dasu cewa andaura auren wani irin Al'amari taji atattare da ita shi ba farin cikiba hakama ba baqin cikiba
Tadaisan jikinta ya mutune kawai Dan haka daqyar ta iya sauya Kaya kaman yanda su Anty Hafsat suka takura Mata sbd Ango na tafe da jama'arsa suyi hotuna takuma gaisa da abokansa da zasu bi jirgi a ranar su koma.
Tafiyar su Anty Hafsat shine ya fara daga hankalin umma yaganah harma da Inayah Dan haka da kanta ta Kira cm din a waya tace Inayah tace Dan Allah abar Mata Hafsat da Safnah har zuwa anjima.
Bai Musa ba yabar Anty Hafsat da Safnah Dan haka gidan yayi tsit daga umma yaganah sai Anty Hafsat da Safnah da Neesah
Dr farhat ma ta tafi gida sai zaa wuce da Inayah din tace akirata.
Babu Mai wata doguwar walwala acikinsu sbd sudai anbarsu a duhu basusan meyake faruwaba sai jiran tsammanin zuwan Ango da jama'arsa suke Amma basuga alamar hakan Zata faruba ga wayarsa da Inayah ke Kira kaman zata zare Amma batama shiga kwata kwata.
Sanin Abbi yadawo yasa ta miqe jiki mace ta nufa gefensa tana sake trying din Abdul.
Kodata Isa knocking daya tayi tabude kofar tashiga daukeda sallama Mara sauti sosai.
Baya Palo da alama Yana bedroom dinsa Dan haka ta zauna kan kujera tana sake trying din Abdul.
Tunanin Kiran ummansane ya shigota ta nema numbern umman aikuwa tafara ringing.
Harta katse baa dagaba Dan haka ta fara rubutawa Abdul text.
Kofar bedroom dinsace ta bude Dan haka ta dakata rubutun tareda dagowa tana kallon kofar.
Sanye yake da ash Lululemon wears navy blue dasuka fidda hasken fatarsa sosai da alama wanka yayi ya shiryo cikin kayan Dan samun nutsuwa,
Qamshinsane ya gauraye palon take ya qaraso da yimata kallo daya yanajin wata qululuwar damuwar auren da aka daura Yana dawo Masa.
Cikin boye damuwarta da Yar sakakiyar murya tace"
Abbi kadawo Ashe tun dazu?
Abbi Ina Heart ya....kasa qarasawa tanajin nauyin qarasa zancen sbd ita wani lokacin mantawa takeyi da kunyar fadan wani zancen.
Dan juyowa yayi kadan ya kalleta ganin damuwa a tattare da ita cikin dan yanayin kawar da zancen Kai tsaye yace"
Abdul na asibiti ya Dan samu attack ne aka wuce dashi asibiti.
Zaro ido tayi cikin tashin hankali da firgici Amma ganin ba fuskar Kuma wata tambayar agurin Abbi yasata miqewa ta silale Takoma.
Koda ta Isa a tsattsaye ta taddasu kowanne ba acikin cikakken hayyacinsaba,
Tashin hankali da firgicin data gani ataredasu duka yasata bude Baki da qarfi cikin firgici tace"
Badai Heart wani abun yasamaba kuma daga asibiti???
Umma yaganah kanta yakasa daukan abinda CM yafadawa Hafsat a taqaice na cewa A MAJEED shine mijin da aka daurawa Inayah aure dashi yau.
Wani irin zufa takeyi tanajin kaman iskar dake gurin Bata isarta Dan haka da sauri Neesah ma dake cikin tsananin shock ta Kama umma yaganah sukai daki taqara Mata AC tareda bude suka windows tana cewa"
breath, just breath kada ki Bari Jan numfashi ya tsaya Miki kiyi kokari kijasa.
Kasawa umma yaganah tayi Saida Inayah tashigo dakin tana kallonsu a haukace tana cewa"
Dan Allah ku fadan abinda yake faruwa,
Wane tashin hankali ne zaisaka umma wannan halin?
Anty Hafsat is crying,
Kema Neesah sai zare Ido kikeyi Kun kasa fadamun komai,
Kuka ta fashe dashi tana cewa"
Idan Heart ne ya rasu Dan Allah ku fadamun.
Kasa riqe maganar bakinta Neesah tayi cikin mamaki da qin yarda da abinda sukaji tace"
Inayah Abbi ne fa ya aureki,
Dashi aka daura auren wai,
Shine mijinki yanzu,
Dama akwai aure tsakanin uba da 'ya??....
A jere take Watso kalaman sbd takai kololuwar kasa danne mamakin firgicin dake ransu ita nata kalaman ne suka Riga na kowa fitowa a hargitse.
Kallon rashin fahimta Inayah ke Mata kafin ta kalli umma yaganah da duk tayi wani iri Dan kuwa CM bazai musu qaryaba,
hakama tafi kowa sanin MAJEED ba jahili bane bakuma mahaukaci bane da iliminsa
Idan harya auri Inayah hakan na nufin bashine ya haifetaba kenan tun asali....to wannan wane irin masifa ce Zata sakasa auran yarinyarda take matsayin 'yarsa Koda ba shine ya haifeta ba tasan Dole ba auran dadin Rai ne yayiwa Inayah ba.
Anty Hafsat ce tashigo tana sake samun tabbaci daga uban mijinta Alhaji babbah cewa Inayah dai ba 'yar MAJEED bace Kuma shine dai mijin daya aureta yau Dan haka suyi kokarin ganin sun tausar da ita batareda taqara Masa tension ba akan Wanda yake ciki yanzu.
Da rikitaccen yanayi Inayah ta maida kallonta kan Anty Hafsat data shigo dakin cikin kosawa tace"
Anty Hafsat meke faruwa dan Allah?Bazan iya daukan wannan shirun da kowa kemun ba,
Maganar Neesah ma Ni Sam bangane itama me take nufiba.
Ahankali Anty Hafsat takama hannunta suka nufi Inda umma yaganah take ta zaunar da ita itama ta zauna suka sakata tsakiya itada umma yaganah ahankali ta kalleta cikin sanyin murya tafara cewa"
Inayah bamusan komai dayasaba kokuma yazama sanadi komai for now Amma dai abinda yake gaskiyar zance shine aurenki da Abdulsamad Bai yiyuba Amma aure kam kaman yanda aka sanar Mana tabbas andaura Miki aure da...
Dan shiru tayi tareda kallon umma yaganah dake saurarenta itama Dan Hafsat din tafisu sani da fahimtar komai da kyau tunda itace tayi waya da mijinta yayi Mata bayanin komai hakama Alhaji babbah yayi Mata bayanin komai qarshema yanzu driver na hanyar zuwa daukansu su duka zuwa gurin Alhaji babbah din Dan shine kadai zai iya yiwa Inayah bayaninda kila Zata fahimta.
Kaman daga sama sukaji Inayah din tace"
Da aka fasa aurena da heart sai aka daura mun da Abbi???
Right?
Shine abinda kikeson fada mun?
Shigowar zubbi da sakon isowar driver daga can family house yasa Anty Hafsat dojewa amsa tambayar Inayah din Dan haka ba Bata lokaci takama hannun Inayah din Umma ba Bata jira komaiba ta sauko gadon tareda miqewa ta zari mayafi suka fito Dan kowa matse yake da a wayar Masa da Kai akan wannan sauyin lamari Mai wuyar ganewa.
Koda suka Isa gidan Alhaji babbah na masallaci sallar la'asar Dan haka Saida suka jira ya dawo a babban Palo Haj mama na sake yimusu nasiha a fakaice Dan ita saima taji tafi jin dadin MAJEED daya aure Inayah Dan kuwa da tun farkoma sun San bashine ya haifetaba baida alaqar Jini tako Ina da ita da tuni sun matsanta Masa ya aureta yafi fashe fashen aurenta da akaita Yi shima Kuma ga lokaci yaja Bai taba aureba ace haryanzu matsayin saurayi yake Dan haka Kai tsaye ya bayyanarda farin cikinta ana fada saidai Kuma ta tausayawa Inayah sosai ta yanda Rana tsaka Zata karbi zamanta ba 'yar mahaifintaba datake tsananin so da kauna amatsayin ubanta ita daya.
Kusan Banda Inayah data kasa fahimta bare yarda har lokacin
Sun Gama fahimtar dai Abbi bashine ya Haifa Inayah ba Kuma shine mijinta a yanzu.
Duk sun gane wannan abinda basu ganeba shine meya Hana a daura auren da Abdulsamad.
Alhaji babbah na dawowa daga masallaci suka dunguma palonsa lokacin har CM ma ya iso Yana gidan.
Zama kowa yayi jiki a sanyaye Musamman Inayah da kusan komai Bata ganewa Takoma kaman wata mutum mutumi.
Ita Alhaji babbah yafara kalla cikeda tausayawa da kulawa kafin ya maida kallonsa kan umma yaganah datake Babba zatafin fahimtar komai Kuma idan ta fahimta komai zaifi tafiya daidai Dan itace Zata ringa dorata a hanya akan auren da haqqoqinsa tunda tare suke rayuwa gida daya.
Gaisawa suka fara Yi kafin ya Dora da fadar"
Haj yaganah ya fama da hidima da jama'a?
Allah yasa angama lafiya yakuma sanya Alkhairi.
To wani babban Al'amari yafaru tsakanin shekaran jiya zuwa jiya da Kuma yau din kafin daurin aure Wanda yasa aka samu sauyi cikin qurarren lokaci.,
Shi aure nufine na Allah Dan haka kada kuyi Wani mamaki da Al'amarin ubangiji,
Inayah dai kaman yanda a da MAJEED shine jigonta yanzuma shine jigonta Kuma ma'ishinta Dan kuwa shine mijinta haryanzu yafi kowa iko akanta.
Basai an tsaya tone toneba anan ko dogon bayani Wanda Zata samu daga baya idan ansamu komai ya lafa
MAJEED dai bashine mahaifinta ba Kuma yada alaqar Jini tako Ina da ita bamu kadaiba duniyama Bata taba sanin da hakanba sbd riqon Amana da Gaskia da yayi Mata da zuciya daya Kuma a wannan duniyar abune Mai wuya samun irinsa Dan kuwa ko 'dan jininka baka riqewa ba Amana irin hakan Amma shi ya riqeta ya reneta da Amana da kauna bai taba barin tasan bashine mahaifinta ba idanba yanzu da hakan ta bullo ba Rana tsaka shima Kuma hakan da yayi yayine duk akanta sbd har gobe itace kulawarsa.
Shi Dr Abdul dai anfasa aurensane sbd uwarsa daya ubansa daya da Inayah Wanda shi wannan bayanin ba hurumin shigata bane
Dan hakan Ina fatan Kun fahimci yanayin da aka shiga dakuma wandama zaa Shiga Nan gaba sbd Koda Wasa karnaji anyi wata fitina kokuma tashin hankali akan wannan auren,
Shima MAJEED din danasan yafi kowa shiga mugun yanayi akan wannan auren nai Masa nasiha Kuma Inshallah Ina fatan ya dauka.
Dan hakan Haj yaganah sai anyi kokari gurin fahimtar dasu wasu abubuwan aure ya wuce mutum yayi Masa daukan dayaga dama,
Allah ya sanyawa auren albarka,
Suma can Allah yabasu ikon warware komai lafiya.
Waiwayowa yayi zaiwa Inayah nasiha akan itama saita dauki qaddara sbd da tashin hankali samun kanka irin wannan yanayin sai ganin sukai tana Jan numfashi alamar attack Zata samu
Kafin suyi wani yunqurin tasamu attack take Dan haka a rikice suka dauketa zuwa cikin gida.
Allah yasa akwai likita taredasu Neesah taredasu Amma bada ita akaje palon Alhaji babbah ba
itace tayi gaggawar fara taimakawa Inayah din wadda takejin kaman zata rasa ranta sbd yanda numfashinta ke Neman yankewa Neesah na taimaka Mata gurin janyosa da karfi.
Ganin kaman Al'amarin zaiyi girma sosai Dole suka Kira Dr farhat wadda kafin ta iso suka dunguma da Inayah din zuwa asibiti sbd tuni umma yaganah takira Abbi ya sanar Masa yace su wuce asibiti gashinan zuwa asibitin.
##MAMUH#
#LOVE/ROMANCE
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/31, 9:43 PM] +234 703 926 9802: *_32_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Private hospital din dake anguwarsu Alhaji babbah aka kaita sbd kafin suce sunje AA specialist wato private hospital dinsu akwai nisa daganan da hakan suka tsaya tanan kusa.
Cikin gagawa suka karba Inayah din
Neesah ma bata barmusu aikinba su kadai da ita sukayi Dan sunada fahimta tana sanar dasu itama likitace suka barta ta taimaka musu tunda dama itace kusan tasaba taimakawa Inayah idan irin hakan ta taso.
Umma yaganah gabaki daya kanta neman sake cakewa yakeyi da wannan Al'amuran daketa faruwa daga wannan sai wannan,
Har cikin ranta takejin kauna Mai tsafta da tsanani akan MAJEED da Inayah sbd sune danginta itace danginsu Dan lokuta da dama sukan mantama basuda alaqar jini da juna.
Badan a yanda yanayin komai ya fallasa kansa ba lokaci daya ba zato ba tsammani da Babu Wanda zai kaita murnar Auren MAJEED datake addua da fatar gani tsawon shekaru.
Hakama auren Inayah wani babban burinta ne shima datake fatan Allah ya nuna Mata ya cika a yau din
sai gashi Allah yacika Mata burin Auren dukansu a yanayinda Babu wanda yataba tsammata,
Ku kansu basuma San farin ciki zasuyiba ko damuwar sanin ba Abbi ne ya haifi Inayah ba.
Anty Hafsat ma zuciyarta kusan Kashi Kashi take kasuwa tana rarraba Mata tunani sbd ayanzu Bayan Jin bayanin yanda Al'amarin yake daga bakin Alhaji babbah taji zuciyarta na farin ciki da auren Dan kuwa Inayah Allah yayimata kyakkyawan sauyin dayafi duka tarin mazan data rasa abaya sbd Abbinta yakai kowanne level da ake kwadayin namiji yakai badan tashin hankalin halinda Inayah tashigaba da a fili Zata fara bayyanarda farin cikinta akan wannan tsintar damu akala da Inayarsu tayi Dan kuwa Abbi kam Masha Allah.
Sbd wadda tasaba ji da matsalarta na kusa yasa ma'aikatan asibitin Basu Sha wuyar taro yanayinta ba tadawo hayyacinta saidai take bacci ya dauketa sbd kusan wannan attack din yafi wainda tasaba samu abaya.
Kwantawa hankalinsu yayi ganin tadawo daidai tasamu bacci Amma kallo daya zakawa fuskarta ka gano baccin na tattareda yanayin firgici data shiga.
Suna zaune a dakin datake anty Hafsat na kokarin daidaita ACn dakin da yayi yawa umma yaganah Kuma na zaune tana kokarin amsa wayarta da Mimi ke Kira saigashi ya iso yashiga dakin cikin nutsuwa sanyeda Lululemon wears har lokacin da alama Bai tsaya sauyawaba zuwa wasu manyan kayan.
Fresh skin dinsa daya bayyana sosai cikin kayan anty Hafsat da Neesah suka kalla suna sake tabbatarda kyau da tsarin da Allah yayiwa Abbin
Take suka sake Jin tabbas ta wannan fannin Inayah Dinsu tagama dacen miji illa kawai baqin cikin dazata Shiga sanin Abbinta datafi so fiyeda komai baida alaqan Jini da ita
Tsintar yayi,kyautarta akai Masa kokuma tayaya ya sameta Allah ne kawai yasani saishi da umman Abdul din.
Cikin girmamawa anty Hafsat da Neesah sukai Masa sannu da isowa
Da qaramin sauti ya amsa Yana dan kallon Inayar kafin ya kalli anty Hafsat sbd umma yaganah na waya yace"
Doctors din sungama dubata ne?
Neesah ya nisan yanayin nata?
Firgici ne kawai data shiga ya daketa sosai Amma Inshallah lafiyanta kalau yanzu anmata allura ne sbd tayi baccinda kanta zai Dan warware ya rage Mata tashin hankalin.
Gyada Kai yayi ahankali tareda sake kallon Inayah datai wani iri cikin lokaci qanqani.
Dan gajeran numfashi ya sauke tareda juyawa yafita zuwa ganin likita Dan bayason ta kwana a asibitin gida zasu koma tunda suna tareda qwararrun likitoci a gidan.
Fitarsa da mintuna biyar sai gasu Mimi sun iso asibitin a gigice sbd tashin hankali biyu,
Na farko Jin auren MAJEED da Inayah dakuma Jin uwarsu daya ubansu daya itada Dr Abdul ga qarin halinda Inayar tashiga.
Jigum jigum sukai a dakin wasunsu na sake Dan jajanta wannan alamari da masu godewa Allah da baa Riga an daura aurenta da Dr Abdul dinba dan da abin yafi lalacewa.
Umma dai bayan taga Inayah ta tashi babu abinda take fata Dan ita kanta yanzu tanajin dacin da Inayah Zata Shiga,.
A sanin dataiwa Inayah kuka da baqin cikin dazata Shiga na zaman Abbi ba mahaifintaba zaifi Mata ciwo da radadi fiyeda auren Dan kuwa tafi buqatan ace alaqar jini suka hada Bata auratayyaba.
Har yamma lis suna asibitin Inayah Bata farkaba sai magriba.
Tana farkawa takasa kallon kowa a dakin sbd yanda duk sukai jigum jigum yabata tabbacin abinda yafaru kafin zuwanta asibitin Gaskia ne haqiqanin Gaskia Kuma Dan haka Batasan ta Ina Zata fara bayyanarda babban abinda takeji tokare da zuciyarta da maqoshinta.
Cikin kulawa da sanyin jikin yanayin da Inayah din ta nuna umma yaganah da Anty Hafsat suka fara kokarin magana saiga shigowar Abbi Wanda Yana shigowa qamshinsa ya gauraya dakin suka tsit suna jiran abinda zai faru Kuma ga Inayah din ga Abbi a amatsayin ma'aurata.
Yanayinsu yasashi basarwa tareda Dan kamewa ya kalli Inayah data dago ta zuba Masa Ido tana Neman fashewa da kuka yace"
Kina farkawa Kuma Zaki fara wani kuka agurin.
Neesah dake gefenta ya Dan kalla yace"
Ku shirya gida zaa koma da ita yanzu.
To" Neesah tace tana kallon Inayah din dake kokarin fashewa da kuka Amma takasa sbd abun datakeji ya girma qwaqwalwarta.
Juyawa yayi ya fice suka biyo bayansa.
Anty Hafsat motar CM zatabi itada Mimi da Safnah
Su Kuma su Inayah din motar Abbi zasubi Dan haka suka nufa motar Kai tsaye umma yaganah na riqe da hannun Inayah dake kokarin zubewa sbd tangadin datake na Bata cikin cikakkiyar nutsuwarta.
Kaman yanda suka Saba fitarsu da Abbin idan takama Inayah ce a gaba Dan haka yau dinma itace agaba sai umma da Neesah a baya.
Bayan sanyin Ac na motar da qamshinsa daya cika motar Yana zagayawa Babu Mai ko motsi acikinsu kaman ba kowa a motar kowa da tunanin daya shiga Banda Inayah da har lokacin qwaqwalwarta Bata fara aiki daidai ba dif take Bata ji Bata gane komai yanzu.
Suna Isa gida Dole Neesah ce ta kamota suka nufi ciki tana kokarin kaita bedroom dinta ta qwace Takoma Palo tana kokarin bin bayan Abbi cikin dimauta tana cewa"
Abbi ne kawai zaifadamun Gaskia na yarda da abinda duk ake fada,
Abbina ne kawai zan yarda da maganarsa.
Da sauri umma yaganah ta riqota tana cewa"
Ki nutsu Mana Inayah,
Me zakije kice Masa yanzu?
Bakiji anfada Miki yanzu mijinki bane,
Qarya zamu taru mu Miki ne?
Alhaji babbah zai Miki qaryane?
MAJEED din dakikeson saiya fada Miki komai Yana cikin damuwa sosai bakya gani?
Zaki sake daga Masa hankali da kukan Nan nakine idan kikace rikicewa zakiyi.
Rikitaccen Kuka ta fashe dashi Mai tsananin qunci tana cewa"
Ni bazan yardaba wlh abbin ne mahaifina,
Banason kowa a mahaifi sai Abbi,
Har umman Abdul din banaso amatsayin uwa Ni Abbi ne kawai uwa Kuma ubana...
Da sauri umma ta rufe Mata Baki jikinta na rawa sbd jikinta daya fara sanyi itama da irin kukan da Inayah din fasawa Wanda tunda take Bata taba yin irinsaba sai yau.
Rirriqeta sukai ta zube qasa tana sake tsananta kukanta zuciyarta na Mata wani irin zafi da radadi...
Idan ba abbine mahaifinta ba ai ita asaran duniya da baqin cikin duniya tana cikin cikinsa da wannan mummunan labarin da gwara ayita fasa aurenta har abada akan wannan labari...
Bazata taba yarda da maganar kowaba sai taji daga Abbinta cewa gaske bashine ya haifetaba.
Dukkanin sautin kukan datake yanajinsu Amma Bai iya zuwa Inda suke dinba Dan kusan yafita baqin ciki da wannan bankadar,
Dan yaso ya tsaya a ubanta na har abada saidai qaddara Bata bar hakan ba Dan kuwa Koda warware auren Nan akayi har abada ita zaa Kira da matarsa ta farko wadda tafara daukan igiyoyin aurensa haka itama har abada shi zaa Kira da mijinta na farko daya fara riqe martabar aurenta.
Kuka Inayah da tashin hankali sosai tashiga lokaci daya Wanda ya gigita umma yaganah da Neesah harma dasu zubbi da Salimat sun Shiga tashin hankali da damuwa sosai ganin halinda Inayah din ke ciki
Ta bangare daya shi kansa Mai gidan babu Wanda yakuma ganinsa har washe gari,
Abincin gidan ranar haka aka daukesa aka fitarwa Bosco ya rarrabawa securities din anguwar abokanansa sbd Babu Mai nutsuwar cin wani abinci.
Da zazzabi Mai zafi Inayah ta kwana Dan kaman yarinya qarama Takoma musu daqyar baccin wahala ya daukeda jikinta da mugun zazzabi.
MAMUH#
#LOVE/ROMANCE
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107*_33_*
*_Arewabook@Mamuhgee_*
Da zazzabin ta tashi da safe Dan haka sallah kawai ta iya Yi Takoma ta kwanta sbd tsananin ciwon Kai Dana kirji,
Ana Gama breakfast umma yaganah ta sallami baqinta aka kaisu aka sanya mota tareda Dan abin arziki gidan yasake daukan tsit.
Su zubbi tuni suka shirya komai a dining na breakfast kaman yanda suka Saba.
Umma dai a dakinta tayi breakfast din Neesah ma bata fito dining ba Dan a daki Tasha tea Danma sunyi sunyi Inayah ko tea din Tasha taqi.
Har lokacin bata daina tsiyayar hawayeba,
Takasa yarda da wannan qaddarar lokaci daya wai ace Abbinta shine mijinta,
Tayaya Zata fara fuskantar wannan maganar,
Har abada bazata taba iya karban Abbi amatsayin mijintaba sbd haramun nema agunta kallon Abbi a matsayin Miji ba uba ba.
Daga Neesah har umma sunyi rarrashi da nasihun harsun gaji Amma Babu sassauci a lamarin,
Gabaki daya fuskarta ta sauya sbd kuka.
Anty Hafsat ma tazo tayi nata rarrashin Amma Dole haka zasu hakura sbd dama bazai yiyu ka karbi irin wannan ba lokaci daya.
Gabaki daya wunin basuga Abbi ba sbd yafita tun safe gurin sallamar baqinsu na nesa dazasu wuce Kuma akwai wainda zaiyi meeting dasu kafin su wuce din.
Da farko mantawa yayi da auren daya rataya akansa jiyan sai daga baya bayanma ya daga waya zai Kira Inayah.
Dan rinte Ido yayi tareda maida wayar ya ajiye Yana fitarda Dan numfashi Mai zafi.
Miqewa yayi ya nufi toilet ya sakarwa kansa ruwan Yana gogawa fatarsa sabulun mountain water soap na Creed.
Sai bayan wasu Yan mintuna yafito daureda blue towel a qugu yafara shiryawa.
Cikin dark blue kaftans yafito da blue hular kube Bai wani shiga can palonsu ya fice daga gidan sbd jiransa da ake.
Sai Bayan azahar Inayah ta iya tashi da daqyar takai kanta toilet tayi wanka.
Sallah tayi tazauna tareda janyo wayarta tana sake saka kiran Heart dinta Wanda yanzu Kuma hankalinta ya karkatane akan taji yanda yake sbd tasan Yana cikin matsanancin halin shima.
Wayarsa har lokacin bata Shiga Dan haka tasake daga hankalinta da wata qarin damuwar.
Dole anty Hafsat da Neesah da umma yaganah sukai Shirin tafiya dubosa asibiti Dan dama suma duk sun damu dason sanin halinda yake ciki din tun iya basuda labarin komai akansa da mahaifiyarsa Kuma mahaifiyar Inayah.
Abbi umma yaganah takira ta sanar Masa zasu tafi dubo Abdul din Bai hanasuba yace suje.
Har Zata kashe Kai tsaye a nutse cikin kamewa yace"
Kar kuje da Inayah ta zauna gida.
Ok shikenan.
Inayah taji lokacinda Abbi yace kada aje da ita Dan haka hankalinta yaqara tashi da sauri tadauki wayarta tareda saka kiransa.
Ringing wayar tafara
Lokacin Yana tareda dasu CM da wasu school mates Dinsu da duk sunzo daurin auren sbd kowa nata kokarin hulda dasu shida CM yanzu sbd ganin sun Zama abokan manya sbd kudi.
Dan waiwayawa yayi gefensa da wayar ke ajiye ya kalli wayar a natse yaga Inayah ce me Kiran yakuma San Sarai roqonsa zatai akan binsu shikuma bazai taba barin ta hadu da Hadiza ba ayanzu Dan haka ya dauki wayar a kame yace"
Yes,Inayah.
A marairaice da alamar kuka tace"
Abbi Dan Allah zan bisu inason dubo Heart Nima,
Abbi Dan Allah kada ka hanani....
Bakida lfy Babu Inda Zaki kina wannan kukan
Kisha magani ki kwanta.
Kashe wayar yayi tareda ajiyewa Yana maida hankalinsa kan maganar dasukeyi.
Hawaye tafara tana kallon wayar
Su umma na ganin haka suka fice suna cemata saisun dawo.
Zaunawa tayi bakin gadon dakinta Tana cigaba da tsiyayar hawaye sbd tana tsananin buqatan son ganin Heart Dan taga yanayinda yake ciki.
Wurgi tayi da wayarta kan gado tana cusa fuskarta cikin tafukan hannuwanta zuciyarta na radadi.
Hannu takeson dorawa akai ta ringa zumduma ihu da birgima ko zataji sassaucin tsananin qunci da damuwar dake ranta.
Tayaya Zata iya cire soyayyar heart daga ranta bayan yayiwa zuciyarta kyakkyawar Shiga?
Tayaya zasu iya rabuwa da juna sbd kalmar uwa daya uba daya da ake dangantasu da ita?
Batada uban daya wuce abbi Kuma batajin Zata daina daukansa ahakan kokuma daina kallonsa ahakan.
Abbinta fa ake maimaita Mata kalmar mini agurinta.
Kasa riqe kukan tayi ta kwanta agurin tafara rero kuka tana sake Jin zuciyarta kaman zata kama da wuta.
***Su umma yaganah kuwa koda suka Isa asibitin da Dr Abdul yake hankalin Yan uwansa da mahaifiyarsa atashe yake sosai fiyeda tunani Dan kuwa Dr Abdul dai jiki ya rikice.
A jiyan da aka kawosa asibiti daqyar aka samu ya farfado ya kalli mahaifiyarsa da hankalinta ya rarrabu cikin tashin hankali masu girma sbd labarin auren MAJEED da INAYAH ya gigitata sosai,
Zancen ya daketa har Batasan lokacinda itama ta zube qasaba jininta na Neman hawa.
Tabbas AA MAJEED ya nuna Mata shi namijin duniya ne,
Ya Sha gabanta ta hanyar aure Inayah sbd baida niyar bata 'yarta,
Tabbas Babu shari'a yanzu Kam da Zata karbar Mata Inayah daga hannunsa Amma Kuma idan har Inayah Bata son wannan auren Koda abinda ta mallaka zai qare duniya kowa ya juya Mata baya saita tsaya Sharia ta raba auren anbata 'yarta.
Su Haj balaraba dasu Alhaji buhari saidai su Alhaji kabiru sukai musu bayanin cikin daya bayyana jikin Hadiza bayan shekaru Wanda yayi sanadin dasuka koreta daga gida
Saidai yanda komai yafaru Bayan barinta gidan shine Basu saniba saisunji daga gareta dashi AA MAJEED din Dan yanzu sune kadai zasu qarasa warwarewa kowa wannan qullin da tunanin dasuka shiga.
Haj balaraba kuka ta ringa rerawa tana yiwa salisu addua suna qara godewa Allah da baa daura wannan aureba da basusan iya Ina tashin hankalin zai kaisuba.
Hajiyarsu suka kira suka Dan sanar da ita komai a taqaice to dayake tasan da maganar cikin da haihuwar bayan barin Hadiza gida daga bakin jama'a Amma tayi shiru ta lafe sbd tunanin ko cikin banzane Hadizan tasamo daga Lagos sbd kada a dangantasu da cikin Tai shiru taqi Kuma barin 'yayanta ko daya yasani dan kada suce zasu karba tunda ba tabbas hakama Hadiza ta sameta takanas da jaririyar Amma shedan yaqi Bari ta amsa.
Tsufa ya kamata sosai yanzu Amma itama haka ta ringa kukan danasani da farin cikin da aka samu Ayshatouh take zancen yafara fita a dangi saidai halinda Abdul ke ciki yafi daga hankalinsu akan murnar bayyanar wadda basuma San da itaba a zuriar.
Dr Abdul mummunan shock din daya shiga ya daki zuciyarsa zuwa qwaqwalwarsa sosai Dan haka ya jima Bai farfado ba Kuma ya a farfadowa ummansa yafara zubawa indanuwansa dasukai mummunan ja yana kallonta cikin karaya da mutuwar dukkanin jiki yace"
Umma since Inayah 'yarki ce itama kece kika haife shiyasa bazan auretaba Abbi ya aureta
Ni nakasa gane komai
So kawai naji daga bakinki idan kece mahaifiyar Inayah tayaya AA MAJEED zai Zama ubanta?
Umma Dan Allah kicemun ba kece kika haifetaba,
Kicemun bakida alaqar komai da ita sai wadda zamu qulla yanzu ta auratayya,
Umma Dan allah kice bakece uwar Inayah ba bakida alaqan komai da ita...umma bazan iya rayuwa Babu Inayah ba kinsani akanta zan iya rasa hankalina da nutsuwata,
INAYAH ce farin cikina,rayuwata da nutsuwata.....umma kice wani abun Dan Allah Amma ki janye maganar kece mahaifiyar INAYAH.
Kakkarwa jikinsa keyi idanuwansa na sake fitowa da tashin hankali.
Saikowa yayi gadon Yana Neman faduwa sbd jiri sukai saurin riqesa umman cikin kuka ta riqosa tana kallon yanda yake kokarin haukace musu tace"
Abdul hakuri zakayi da wannan kaddarar ka runguma sbd bazan iya goge alaqar jinin dake tsakaninka da Ayshatouh Inayah ba,
Kai Dan uwantane na Jini,
Nice na haifeta kaman yanda na haifeka,
Uwar daya ubanku daya Babu Mai iya goge wannan sbd rubutacciyar kaddara ce,
Abdulsamad ma dauki danganar rasa Inayah sbd har abada Babu aure tsakaninku
bazaka taba aurentaba Koda ku biyu zaku rage a duniya.
Dan Allah Abdul ka karbi wannan kaddarar da hannu babbiyu sbd zuciyata bazata iya daukan wannan tashin hankalin dakake saka kanka acikiba Dan Allah Abdul.
##MAMUH#
##KUYI HAKURI AMIN UZURI NASAN CHAPTER DIN IS TOO SHORT.🙏
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107*_34_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Umma Hadiza hankalinta yagama rabuwa daban daban,
Tana buqatan fuskantar MAJEED akan abinda yayi na auren Inayah badan komaiba sai Dan nuna Mata iko akan Ayshatouh..
Ta Bangare Daya tasan Inayah ma na can cikin matsanancin halin itama,
Babbar damuwar Kuma ganin Abdulsamad na Neman zauce musu sbd yaqi sauraren kowa bayan zantukan tashin hankali da qin yarda da uwarsa daya da Inayah kaman yanda itama Inayah batama yarda da tanada wata uwarba Dan ko acikin tarin damuwarta umma Hadizan Bata shigob ita tashin hankalinta Abbi daya zamana ba mahaifinta ba ko auren daurawa kawai akayi batajinsa ajikinta kwata kwata.
Zuwansu umma yaganah yasa hankalinsu Haj balaraba tashi sbd mummunan halinda Abdul yakuma shiga Dan kuka ya ringa yiwa su umman da Anty Hafsat Yana maimaita sunan Inayah cikin karyewar zuciya.
Umma yaganah dayake tanada saurin kuka take itama tafara hawayen tausayin Abdul tana cewa"
Abdulsamad sai hakuri
Jarabawar ubangiji ce duk zaa cinye idan anyi hakuri da tawakkali
Inayah tariga ta Zama ta waninka dole dangana zaa dauka abarwa Allah...
Kalaman umma yaganah suka qara Karya zuciyarsa yaci gaba da zubda hawaye Yana sunkuyar dakai zuciyarsa na Masa wani irin ciwo.
Anty Hafsat ma jikinta mugun sanyi yayi da tausayin Abdulsamad Mai tsanani Dan kuwa Basu dauka abin yayi tsanani hakanba.,
Abdulsamad din dasuka sani Dan gayu da kwalisa shine ya garare cikin kwana daya sbd masifar ciwon rashin Inayah.
Neesah kuwa itama jitayi tausayinsa da Inayah harma Dana Abbi yasa hawaye ciko idonta sbd kowannensu yana cikin matsanancin halin da Babu mafita sai dauka da dungumar abinda ya samesa.
Irin naci da daga hankalinda Abdulsamad yayi nason zuwa ganin Inayah yasa umma yaganah miqewa su tafi sbd ko hauka bazata sakata tafiyada abdul dinba ko basa damar zuwa ganin Inayah ayanzu sbd bayan haqqin mariqi da MAJEED yake dashi akan Inayah yanzu shine Mai gabaki dayanta Dan haka bazatai wannan wuce gurinba ko gangancin zuwa dashi Dan haka suka miqe suka fito jiki a sanyaye Koda,
Inayah ma Babu Wanda yayi musu maganarta sbd kowannensu baimasan me zaiceba akanta Dan haka sukai shiru kafin suga sun fara samun daidaituwar Abdul tukuna ayi zaman wannan maganar dake buqatan iyaye da manya aciki sbd tsanar da MAJEED yayiwa Hadiza Saida manya a zancen zai yiyu.
Abbin ne yarigasu isowa gida Kuma yasan Babu kowa a gidan sai Inayah Dan haka daya dawo direct ta palonsu ya biyo tareda nufar bedroom dinta.
Yana isowa zubbi na fitowa daga dakin daukeda tray din abinci da Inayah din bataci ba.
Zubbi na ganinsa tayi saurin Dan yi gefe Tana cewa"
Welcome Sir.
Tray din hannunta ya kalla ganin Babu abinda aka taba daga abincin.
Dan rintse Ido yayi ya bude tareda cewa a natse,
"Kiyi warming abincin ki dawo Mata dashi.
Ok Sir" tafada tareda barin gurin.
Dayake kofar abude take Koda suke maganar Dan haka Inayah taji Qamshin turensa tasan abbi na kusa sai gashi taji muryarsa a hankali.
Da sallama Mara sauti sosai yashigo dakin Yana kallon yanda take zaune kan gado daga fuskarta har idanuwanta sunyi mugun kumbura gabaki dayama kusan kamanninta sun sauya sbd kuka da tsananin tashin hankali.
Sofa dake dakin ya nufa ya zauna ahankali tareda Dan takaita kallonsa akanta sbd ganin fuskarta ahakan damunsa zaiyi sbd baitaba barinta tun yarintaba tashiga damuwa irin haka.
Yana zaunawa ta miqe tsaye ta nufosa.
Wani kallo yayiwa qafafuwanta dasukai haske sosai ga sai zanen maroon lallen da akai Mata na aure yafito da Babu safa ko bedroom feetwear a qafafun tana kallon ta dakata tareda komawa baya ta dauki feetwear dake gefen gadon masu taushi na bargo ta saka kafin ta nufosa Dan yawo ba feetwear ko safa wani abune da abbinta koyar da ita tun qanqanuwarta
Duk tsafta da kyan gidansu basa da yanda tsarin gidansu yake na komai fes Bata tafiya ba takarmin ko safa a qafarta sbd wasu qananun qwayoyin cuta ta qafa suke saurin shigar mutum.
Gefensa ta qaraso jiki a sanyaye ta zauna tana kokarin yimasa wani kukan Dan dama tun jiya takeson ganinsa tayi Masa kukan dake cinta Amma taqi barin kowa ya gansa ya shigewarsa.
Fara hawaye tayi tana kallonsa tace"
Abbi Dan Allah kada kacemun bakaine mahaifinaba,
Ni Kai nasani Kuma Kai zanci gaba da sani a wannan matsayin
Bazan taba karban kowaba amatsayin uwa ko uba
Dan Allah Abbi kabarni da matsayina na 'yarka ta Jini nafison.
Umma yaganah ce ta bude kofar dakin tashigo Kai tsaye sbd dawowarsu kenan.
INAYAH Bata tsaya da abinda take fadaba tacigaba da cewa"
Abbi Dan Allah kada karka bari a sauya mini wani sunan bayan Wanda ka sanyamin,
Ni banason kowa amatsayin jinina sai Kai,
Abbi Ni Kai kadai ne jinina,
Danasan yanda zanyi na hada Jinina da naka ya gauraya daya da naka Abbi wlh danayi ayau dinnan.......
Umma yaganah dake kokarin juyawa tabasu guri Batasan lokacinda ta tsaya cak ba tareda dawowa da wuri tana buge bakin Inayah din cikin kunyar zancenta.
Shi kansa MAJEED din Dan muskutawa yayi tareda fuskewa sbd Inayah dai idan zatai zance ba ruwanta yanko abarta kawai takeyi.
Lokuta da dama Dan umma yaganah na kwabarta ne Amma zantukan datake yankowa gaban Abbin mamaki suke basa matuqa Dan shi wasu abubuwan na halayen Mata dabai taba saniba sbd Bai mu'amalantu dasuba sosai a gurin Inayah yake ji da saninsu.
Ahankali ya kalleta Bayan ya kalli umma yaganah da bakin Inayah yake Bata takaici wasu lokutan.
A natse cikin yace"
Inayah wannan wata Gaskia ce da Dole zamu hakura na dauka sbd nafiki Jin dacin rashin Zama Wanda ya haifeki Amma hakan Allah ya qaddara.
Wannan kukan kidaina Babu Wanda zai tafi dake koina,
Dr Abdul Kuma idan kin daina kuka kin nutsu zan Bari kije ki dubasa.
Gangaro Mata hawaye sukai tace"
Abbi maganar auren fa?
Da gaske an daura mun aure da......
Sake buge bakinta umma yaganah tayi cikin wani sabon takaicin tace"
Waiki bakinki baya shiru idan bakisan me Zaki fada bane?
Qarya zamu Miki baa shine mijinki ba?
Baice komaiba ya miqe ya fice Yana cewa"
Wannan kukan idan Baki dainaba ko gate bazaki sake fitaba bare zuwa duba Dr Abdul.
Yana fita anty Hafsat da Zata wuce tashigo dakin tana kallonsu,
umma ta zauna gefen Inayah cikin takaici tace"
Ke bakinki baya haila ko?
Kullum Ina kwabar bakin Amma kin kasa iya kamesa ko?
Da kike maganar dakinsan yanda Zaki hada Jini dashi da kin hada ayau
Saurin uban me kikeyi idan a gauraya Jini kikeso ai zaa zo gurin saikiyi bayani da kanki,
Kullum kwabarki nakeyi bakyaji
Yanzu dai mijinki ne idan zakiyi hankali kiyi Dan kuwa bakin Nan naki kaiki zaiyi yabaro tun baayi nisaba ki gane barno gabas take.
Murmushi Anty Hafsat tayi sbd ko baa fadaba tagano kan zancen ta kalli Inayah datai tsit idonta yake hawayen fadan ummsn cikin kulawa tace,
"Yi shiru Inayah
Amma ki koya fadan magana bako wace iriba agaban Abbi yanzu sbd yanzu mijinki ne wata maganar idan kinyi kina tadowa kanki aikine tunda wuri wuri Wanda bazaki iya daukaba.
Kinga shikansa yanzu bai Gama karban yanayin ba Dan haka ki ringa Kama bakinki kisan me zakina fada.
Karma ta Kama taci gaba ita Zata bada labari Ina zaune Ina kallo
Badai gaurayan Jini kikesoba
Zaa gauraya Inda rai kuwa.
Umma Dan Allah ayi Mata hakuri da kyakkyawar manufa ta fada sbd yanayin data samu kanta da Wanda ta dauka mahaifinta ne,
Ita kanta Batasan wata manufar abinda tafada tabadaba.
Duk da hakan Inayah nada buqatan sanin abubuwa da dama na sanin Kai tunda yanzu aure yahau kanta Dan haka Hafsat ke wannan aikin ya sama saiki bada himma gurin ganar da ita.
Da farin ciki anty Hafsat tace"
Umma ai wannan aikin Dole ma kuwa
Musamman angon na Inayah shakkarsa duka muke muma dake yanne Kuma iyaye
Amma ahakan zakisha kallon hudubar da zanwa mutuniyar tawa.
Allah yasa ta dauka idan ba zuwa zatai tana fada Masa abubuwan da kike koya mataba
Wlh databarki da kunyar duniya"
Umma yaganah ta fada tana dariyar abinda zai biyo baya kuwa idan hakan ta kasance.
Dariya anty Hafsat tayi tana cewa"
Dakuwa mun Bata da ita idan tamun wannan gangancin
Yanzu mijine bakomai Zata fada masaba sabanin adah dayake matsayin uba.
Ganin Zata shiririce yasata miqewa Tai musu Saida safe ta wuce sbd anzo daukanta.
Bayan fitar anty Hafsat umma ma miqewa Tay ta wuce dakinta
INAYAH tabi kofar dasuka fice da kallo tanajin sun datse Mata maganarta da Abbi batareda sun gamaba.
Miqawa tayi ta nufi toilet tashige sbd alwalar sallar magrib da ake Kira.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107[11/2, 10:00 AM] It's Queen Meenali👑: *_35_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
*_'YAR ZURU Maman ZEE ZEE Best kayan mata_*
Shin ko kunada labarin Yar Zuru mamar ZEE ZEE Mai maida tsohuwa yarinya wadda ta shahara wurin hada kaya kamar haka ❤️kamar su
Kaza
Zabo
Zakara
Ciccibi
Zuciya
Tsimin kankana d rake
Tsimin tabaje
Zumar dabino d kwakwa
Zumar gorun tula syrup
Garuka masu kama jiki kamar su ❤️
Bita zai zai
Dan wata bakwai
Madarar mata
Bata🤐🤐🤐
Ba kishiya ba Ko mugun mutan d mugun aljani sai sun barki
Matsin kinfi budurwa
Kalolin gumba dsauransu
Address maberar jariri bayan FGC sokoto
Phone 08068526455
Instagram Yar Zuru mamar ZEE ZEE kayan mata.
Karku Bari kuwuce Baku gwada kayan Maman zee zee best kayan Mata ba..
*_35_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Da daddare tun 7:30 sukaci abincin dare Amma banda Inayah dataqi fitowa shima Kuma abbin tambaya daya yayi umma tace Inayan ba yanzu tace zataciba
Baikuma maganaba yagama cin abincinsa ya fice yabar umma da Neesah a table suna sake jinjina taurin Kai irin na Inayah sbd son zuwa ganin Abdul Zata dagawa kowa hankali.
Cikin damuwa da takaici umma yaganah tace"
Babban damuwata akan Inayah
Ga abinda yakamata ta fuskanta wato Wanda aurensa ya rataya akanta Amma Sam ita ko yarda da zancen taqiyi bare bawa zancen mahimmanci hauka kawai ta dauka munayi tunda abokan wasantane mu,
Idan Ni ta rainani ai Alhaji babbah da Abbin nata bazasuyi Mata wasaba ko shirme irin nata datake tunani.
Neesah ajiyar zuciya ta sauke tana ajiye spoon din hannunta tareda Shiga tunani tana kwatanta irin rayuwar da Aminiyarta Zata zuba a cikin gidansu Kuma gidan aurenta da Wanda Koda qazantar mafarki Bata taba mafarkin aurensaba,
To Amma yanxu da hakan ta kasance tayaya zata karba auren harsu samu cika burikan dasuka dauka zasuyi da mazajensu idan dukkaninsu sukai aure.,
Babban qarin abin shiga tunanin shine abbin da kusan baiwani San mataba,
bama kusan ba
Baisaniba kwata kwata tunda bashine ya Haifa Inayah ba to tabbas kenan
"he's virgin" tafada a bayyane tana zare Ido cikin Murna Mai tsanani sbd burin Inayah kenan auren wanda Bai taba sanin kowace maceba sai akanta,,,
""ohh my God, Abbi is still a virgin????
Tafada da Dan farin ciki tana kokarin miqewa zuwa gurin qawarta suka hada Ido da umma yaganah dake sake Baki duka tana kallonta cikeda tsoro da mamakin yanda yaran Nan suka Gama lalacewa basuda masaniya akai.
Wata irin kunya ce takama Neesah tana ganin irin kallon da umma ke Mata tasan itama ta sake layi Dan daga ita har Inayah din bakin nasu wani lokacin ba burki bare ribas.
Dan fuskewa take kokarin Yi ta hanyar komawa ta zauna Dan qarasa cin abincin da Zata Bari sbd zumudi
Umma a kasalance da mamaki tace"
Aa karki koma ki zauna jeki Inda kikai niyar zuwa Dan yanzu Kam na Gama tabbatarda kunfi qarfina yaran Nan Musamman Inayah,.
Yanzu ko kunyar Allah bakwaji zakije kuyi maganar MAJEED Bai taba sanin ma....
Kasa qarasawa tayi tana girgiza Kai cikeda kunya da takaicin fada da bakinta.
Kallon yanda Neesah tayi tsamo tsamo tayi tace"
Jeki kuyi abinda zakuyi din,
Nagamo da ita tana maganar gauraya Jini kekuma gakinan yanzu kema kina Taki maganar banzar,
Allah ya shiryaku ya sakamu kunya irin ta 'yaya Mata Dan kuwa Naga sai mun dage da adduar kunyi nisa,
Ita ansamu tun batai tsamari ba an aurar Saura ke
Kema Kuma hankali na kwantawa zanfadawa Fatima suyi Miki aure.
Kaman munafukar Neesah tabar gurin a ranta tana cewa"
Allah yasa umma yaganah kinawa momy magana ko wata kada na qara Amin auren ai inaso.
Da mamaki umma tasake bin Neesah da kallo jin ta amsa adduarta ta qarshe da cewa"
Amin" a bayyane.
Neesah Kai tsaye dakin Neesah ta Isa tana murmushi da dauke gira daya ta qarasa kan gadon da Inayah din ke kwance tana waya da Abdulsamad wadda sai alokacin suka samu Jin juna tunda wannan abun yafaru.
Tunda ya Kira wayar ta dauka take rero Masa wani irin kuka ahankali tanajin kaman ta bude Masa zuciyarta yaga matsayin sonsa aciki.
Kukanta kawai yake saurara Yana zubda hawaye shima sbd bazai iya magana ba shima,
Daga zuciyarsa har kirjinsa da kansa zafi suke Masa,
Yakasa yarda ko karban Inayah amatsayin 'yar uwa,
Bazai iyaba,
Bazai iya daukaba,
Hakama zuciyarsa bazata iya daukaba bare kwakwalwarsa data gama yamutsewa akan son Inayah tuni.
Ganin halinda suke cikine yasa jikin Neesah sanyi ta kalli Inayah dake kuka sosai har hancinta Saida yayi jajir Bayan idanuwanta da fuskar gabaki daya.
Karbe wayar Neesah tayi tareda dorawa akan kunnenta cikin tausasa murya dakuma damuwa tace"
Dr wannan kaman kuna neman butulcewa qaddarar da Allah yake jarabtarku da itane,
Inayah matar wanice yanzu daga ita har Kai kunsan me ake nufi da hakan
Badan kana matsayin muharramintaba dasai nace wanna haramun ne kuke aikatawa mezaisa bazaku danganaba ku dauki hakan wani babban rabo daga ubangiji ku gode Masa da kuka kasancema Jini daya qarshen kauna,
Shi Abbi Yana baqin ciki da takaicin rashin zamtowarta jininsa kaikuma data zamo jininka kuna Neman batawa kowa da komai Dan wannan lalata komai zaku qarasa yi.
Kashe wayar tayi ta dungurar Mata gefe tareda kallonta cikin fara Dan siqewa da yawan kukanta akan soyayyar Dr Abdul tace"
Inayah can you stop all this stupidity,
Yanzu ke kunya bakyaji ki zabi wani kinata kuka akan wani duk kin kasa tsayawama ki duba babban abinda ya rataya akanki.
Tsoki tayi tareda juyawa tabar gurin ta fada toilet Dan yin wanka sbd ita duk sun fara Bata haushi.
Rayuwa saukine da ita,
Ansan ba abune Mai saukin karbaba wannan yanayin dayazo Amma Kuma ba abinda zaka daga hankalinka bane sbd abbin dai dayafi Mata komai da kowa yasake zamowa nata dukkaninsa ba maganar kukan rabuwa dashi Amma haukan soyayyar wani na Neman rufe Mata Ido waninma 'dan uwanta da aka tabbatar Mata da Babu aure tsakaninsu.
Inayah dake hawaye komawa tayi ta kwanta kawai batareda ta iya magana ba sbd bazata iya cire soyayyar Dr Abdul arantaba lokaci dayaba,
Tafi tausayinta sosai akan kanta na wannan yanayin dasuka samu kansu sbd sanin yanda yagama zurfafa da haukacewa a Sonta.
Aurenta Kuma da Abbi Bata Gama yarda dashi bane sbd tasan abbin ma bazai taba karban aurenba sbd Babu yanda zaayi suyi rayuwa ko zaman aure Dan tamkar haramunce garesu.
Ita maganar uwarta da akeyi Kuma batajin Zata taba iya daukanta a wani matsayin Bayan na mahaifiyar Abdulsamad kawai
Sbd aduk matsayinda Abbi zai dauketa hakan itama Zata dauketa Mai kyau ko sabaninsa sbd har abada Abbinta shine komai nata Kuma maganarsa zataci gaba Dabi har qarshen rayuwarta.
Koda Neesah tafito har lokacin Inayah din takasa daina hawaye sbd yanzu kukan rashin sanin kanta takeyi.
Shin marainiyace ita kokuwa 'yar gaba da fatihan dagaske¿
Yarasa tayaya uwarta Zata jefar da ita kokuma guduwa tabarta kokuma kaita gidan marayu tun jarinta,
Tayaya ta fada hannun Abbinta,
Wace irin tsana uwarta Tai Mata da Zata jefar da ita tana jaririya
ta dauki Abdul daya girmeta Amma ita ta jefar da ita.
Ganin kukan datakeyi yayi yawa Kuma akwai tsananin damuwar abin da quncinsa a bayyane da Inayahn yasa Neesah tahowa ta zauna gefen Inayah din tareda Dan rungumota batareda tace komaiba Dan kada ta katse Mata damuwar datakeson ragewa ta hanyar kukan da tunanin.
Sun jima a hakan kafin Inayah ta janye jikinta tareda zamewa ta kwanta kan gadon tana rufe idanuwanta.
Shiryawa Neesah tayi itama cikin kayan bacci masu gajeran wando tazo ta kwanta gefen Inayah sbd tana period bare tayi sallar ishai.
Tanajin yanda jikin Inayah yayi zafi sosai alaman yauma da zazzabin atareda ita Dan haka ta miqe tadauko Mata magani tabata Tasha suka kwanta tanajin jikinta duk yakuma sanyi.
Washe gari ma Bata fito breakfast shima Abbin Bai fitoba su kadai sukayi daga umma yaganah sai Neesah.
Bayan sun Gama umma yaganah da kanta takai breakfast din abbin palonsa ta jiye ta fito.
Neesah Kuma tayi Shirin na Inayah takai Mata daki itama.
Zazzabinta ya tsananta Dan haka hankalinsu ya tashi Amma dai duk da hakan umma Bata sanarwa Abbin ba sbd kada damuwar suyi yawa Dan haka suka samu suka Dan lallabata Neesah Tai Mata allura bayan awa biyu jikin nata ya Dan saki tasamu qwarinsa tasamu tayi wanka tayi sallar azahar.
Tana idarwa ta zare kayan sallar ta miqe ahankali ta zura slippers ta fito dakin sbd tasan Abbinta baisan batada lafiyaba tunda Bai nemetaba Dan haka Kai tsaye tana fitowa Bata nufi koinaba sai hanyar palonsa jikinta ba qwari tafiyarma ahankali takeyi.
Tsit taji gidan duk da dama basuda wani manyan motsi a gidan Amma tsit taji da alama kaman umma yaganah basa gidan.
A dining yake zaune yana Shan ruwan yakasa cin abincin dake jere gabansa
idanuwansa sun sauya sosai sbd yau wani irin daci ne da quncin zuciya tareda damuwar shekaru suke tasowa suna komawa sababbi fal Kaman yanda komai yafaru alokacin bayan...,
Baitaba sanin zai Kuma fuskantar maimaicin abinda yafaru dashiba alokacinda yake cikin radadi da zafin maraicinsa abayaba.
Rintse idanuwansa yayi cikeda daci Mai tsanani dayake sake cika maqoshinsa...
Qamshin Turaren Inayah duk da Bata wani sakaba da yawaba yasashi bude idanuwansa dasukai jajir Yana kokarin basarda yanayinsa sbd kada tagani ta daga hankali da tambayarsa abinda yake damunsa.
Jin takunta ya nufi wani direction din yasashi waiwayowa ahankali ya kalli hanyar.
Riga da wandone ajikinta na masu Fadi sosai Amma basuda nauyi ko kadan sai suke saka kirjinta da bra rawa qaramar hular kayan ce kawai akanta Bata Gama rufe baqin gashintaba da akaiwa gyaran aure Amma auren baiyiyuba.
Dauke kansa yayi daga kallon gurin tareda miqewa ya nufito ganin hanyar palon dazatakl kaita gurinsa ta nufa Kuma yasan su Alhaji babbah da dangin Hadiza da Hadizan suna ciki sbd maganganun da zaayi...
Shigarta hakan gurin zai iya bayyanarda raunin tarbiyarta ga Hadiza da danginta dake gurin harma da Dr Abdul Wanda zai Mata kallon da zai iya Zama laifi ga ubangiji.
Qaramin palon daya rabasu da palon Abbin ta Isa Zata shige taji anriqo hannunta ta baya.
Batada qarfin razana Amma duk da hakan a tsorace ta waiwayo sbd riqon bana mace bane hakama tasan basuda namiji a gidan dazai shigo har nan bayan Abbinta.
Tana juyowa acikin idon Abbin idonta yafara fadawa akaron farko dataji tsoro da fargaban kallon idon Abbin...
Da sauri ta maida kallonta kansa tana bayyanarda tsoronta da damuwarta tace"
Abbi..
Kasa magana tayi sbd idanuwanta dake kokarin cikowa da hawayen da batamasan na menene ba ita dai tasan Abbinta shagwabarta akansa ta qare Dan haka yanzuma tasan bazata iya dainawa sbd kallonsa kawai nasa taji duniyarta alhmdllh sbd samun tsayayyen uba kamansa sai Mai saa irinta.
Matsowa tayi tana sake riqe hannunsa cikin hawaye tace"
Abbi Dan Allah kayi hakuri idan fushi kakeyi sbd na nace Akan zuwa asibiti dubo heart...
Tun jiya Banda lafiya sosai abbi baka..
Saketa yayi tareda zare hannunta daga riqon datai Masa
Tabisa da kallo tana jin sabon kuka na zuwar Mata sbd ganin kaman fushi yake da ita sbd ta saba riqe hannun mahaifinta ko bayan ta girma Bata daina riqe hannunsa Amma yau din ya zare batareda ya kalletaba.
Juyawa yayi Yana komawa palon ya zauna Yana cewa"
Akwai baqi aciki koma ciki anjima zansa Dr farhat tazo ta dubaki.
Kuka ya fashi dashi tareda zuwa gabansa ta durqusa tana hawaye masu gudu tace"
Abbi Dan Allah kayi hkr idan nayi laifi,
Kamun hukuncin laifin ma
Amma Dan Allah kada kabari a rabani da Heart Abbi.....
#MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[11/2, 10:00 AM] It's Queen Meenali👑: *_36_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Ahankali ya waiwayo ya kalleta
Ganin irin kukan datakeyi yasashi Dan sauke ajiyar zuciya Yana nazarin halinda tashiga duk tabi ta sauya sbd kuka da damuwa da tashin hankali lokaci kankani.
Dr Abdulsamad ne ya sulale daga palon batareda sanin kowaba ya shigo ciki Yana Jin idan ba ganin Inayahn yayiba bazai fahimci dukkanin abinda akeson fadaba a zaman.
Umma yaganah data lura da fitarsa ta miqe ta biyo bayansa sbd fargabar abinda shedan zai iya sawa su aikata shida Inayahn idan sun hadu,
Itakuma yanzu Kam tunda aka daura auren INAYAH da MAJEED batajin tanada abinda yakai Mata wannan auren mahimmanci sbd dai basuda yanda zasuyi aure an daura Dan haka kowa hakuri zaiyi a runguma wannan qaddarar gabaki daya.
Shigowar Dr Abdul yasa Inayah dakatawa daga rokon datakeyiwa Abbi ta zubawa Dr Abdul din idanuwanta tanajin kaunarsa na sake karyar Mata da zuciya..
Meyesa ummansa Bata tashi bayyanaba sai alokacinda zasu mallaki junansu.
Dr Abdul ma kasa riqe hawayensa yayi dukda zamtowarsa namiji agabanta.
Qarasowa yayi ya durqusa gaban Abbin shima tareda sunkuyar da Kai Yana tsiyayar hawaye cikin yanayi na damuwa Mai tsanani da quncin dake cinsa cikin zuciya yace"
Sir Dan Allah kada ka rabani da Inayah idan ta haramta aguna matsayin Mata Dan Allah kabani ita matsayin 'yar uwa tunda hakan Bai haramtaba.
Kukan tausayin Dr Abdul din yakuma zuwarwa Inayah ta kalli abbin dayaqi ko kallonsu yayi shiru cikin nasa nazarin.
Idanuwansu sun rufe suna roqonsa
Inayah roqonsa takeyi akan ya warware auren da aka daura sbd har abada bazata iya karban Abbinta amatsayin mijiba.
Irin kukan datakeyi shine yake Sosa ransa ba girman kalaman datake fadaba,
Har cikin ranta take bayyanarda quncinta na auren,
Bazata iya karban wannan aurenba,
Ta zabi yaci gaba da Zama ubanta har qarshen rayuwarta...
Umma yaganah dataga irin kuka da Inayah keyi ya daga hankalinta sosai Musamman ganin shima MAJEED din yanda idanuwansa suka sauya sosai batareda ya juyo ya kalli su Inayahn ba.
Miqewa yayi tsaye ahankali ganin tana neman shaqewa sbd kuka numfashinta Yana hardewa alamar wani attack dinne Zata Kuma samu...
Idanuwansa ya juyo ya zuba Mata Yana kallon yanda numfashinta ke kokarin rabuwa da kirjinta duk akan aurensa daya rataya akanta,
Meyesa tun farko ya aminta da auren sbd tunanin shine mafitar da Zata Hana kowa karban Inayah daga hannunsa...
A zuciyarsa kusan yafi kowa Jin kunci da shiga matsananci hali akan wannan yanayin dahar yakai ga wannan auren Wanda shima yasan yin auren kawai akai bazai taba kallon 'yarsa amatsayin maceba bare matar da....kasa qarasa tunanin yayi sbd nauyin da dacin kalaman.
Da gudu umma taqaraso tana kokarin kamo Inayah
Inayahn ta miqe da sauri tana sake rarrafawa gaban Abbi tana roqonsa numfashinta ko fita daidai bayayi.
Cikin tashin hankali umma yaganah ta sake tarota tana miqar da ita tsaye tace"
INAYAH kinada hankali kuwa?
Kinsan me kike fada?
Wane auren kikeda qwarin gwuwar cewa araba?
Cikin kuka tace"
Umma yaganah wlh bazan iyaba,
Bazan iyaba,
Rayuwar auren da akeson ayi tsakanin ma'aurata bazan iya yinta da Abbi ba wlh,
Rayuwar auren dazanyi bazan taba yinta da Abbi ba,
Umma bazan iya kwanciya gado......
Suka umma yaganah takaiwa bakin tanajin baqin ciki da takaici harma da tashin hankali sbd yanayin MAJEED duk kannewarsa Yana bayyanarda bacin Rai da griman tasirin da maganganunta keyi a ransa.
Ajiyar zuciya Mai sanyi abbin ya sake Yana kallon yanda numfashinta ke kokawa da Isa yasake sauke numfashi Yana Dan dauke idonsa daga kallon kirjinta dake harbawa sosai sbd halinda take ciki.
Fuskarta ya kalla ahankali cikeda kulawa ya kalleta tareda riqo hannunta daga jikin Umma yaganah ya zaunar kan kujera tareda kallonta Yana nazarin kalamanta dasuke bayyanarda haqiqanin Gaskiar abinda yake ranta.
Cikin nutsuwa da sautin muryarsa Mai nutsuwa da kamewa yace"
Inayah!!!!!
Kasa dagowa tayi ta kallesa sai hawayenta dake gara gangarowa daga Idanuwanta dasukai mummunan kumbura.
Kukan dakikeyi Zaki jawa kanki ciwo akan wannan unnecessary Al'amarin,
Auren ne yasaki wannan halin right?
Gyada Kai tayi wasu zafafan hawaye na Kuma ganganro Mata.
Kai tsaye Bai tsaya komaiba yace"
namiki alqawarin sauke Miki wannan auren daga lokacinda kika yarda da qaddara kika San aure tsakaninki da Abdul ya haramta,
Zan sauke Miki auren ki koma hannun mahaifiyarki da Abdulsamad kimun alqawarin bazaki Bari shedan ya Shiga zuciyarkiba kiyi watsi da tarbiyar Dana Baki.
Dago jajayen idanuwanta tayi da basa iya budewa sosai ta kallesa Jin Zata bar hannunsa Wanda ita Batasan wannan yarenba kwata kwata bazata taba barinsa Koda Zata rasa kowa a duniya.
Juyawa yayi ya kalli umma yaganah zaiyi magana
umma yaganah tayi saurin zubewa qasa tana neman fashe Masa da kuka tace"
Dan girman Allah MAJEED kada ka furta kalma daya data danganci rabuwar wannan auren.....
Rintse idanuwansa yayi Yana sake hadiye yanayin dayake ciki ya kalli Inayah dake kallonsa Ido na tsiyayar hawaye tana jiran kalamansa da zasu warware auren su koma matsayinsu na uba da 'ya.
Tunda umma yaganah take Bata dukan Inayah ba bare ma agaban Abbi sai yau dataji kaman tayiwa Inayah din duka tashi Kisha ruwan gishiri Dan haka Batasan lokacinda ta ringa dukan Inayahn da mayafin Jikintaba tareda damqar hannunta tayi ciki da ita bayan ta kalli cikin tsakiyar idanuwan Dr Abdul dake zubarda hawaye shime ta buga Masa wani irin mummunan gargadin dayasa shi kallon Abbi Wanda yakasa cewa komai sbd kansa daya toshe Yana sake daukan zafi.
Wucewa yayi yabar Dr Abdul din a tsaye gurin Yana bin hanyoyin dasuka bi da idanuwa cikin tashin hankali sbd Koda yasan bazai taba auren Dan Inayah ba zaifi samun nutsuwa da sauki idan yasan ba auren kowa kanta.
Umma na shiga daki da Inayah tayi wurgi da ita tsakiyar dakin tareda kallonta cikin tsananin takaici da bacin Rai tarasa wane irin duka zataiwa bakin Inayahn,
Cikin kuka Inayah ta cusa kanta cikin tsakiyar qafafunta tana jin hankalinta Kuma na tashi da kalman Abbi na miqata ga matarda ake Kira da mahaifiyarta wadda haryanzu basu sake haduwaba tun ranarda tazo gidan komai ya lalace.
Daqyar umma yaganah ta samu danne zuciyarta Takoma palon Wanda dama MAJEED ake jiran yazo afara maganar da zaayi.
Koda Isa palon zaman taron yaqara yamutsewa sbd Dr Abdul da jikinsa ya rikice Dole suka bar gidan.
Umma Hadiza kaman zata Dora hannu akai tayita rusa ihu takeji sbd wannan masifar dake Neman dawo Mata,
'danta daya Wanda take ganin ta Kama qwaqwalwarsa na Neman juyewa sbd son 'yar uwarsa
Gashi tana neman rasashi batareda wannan datake ganin tasamoba Bayan shekaru tazo hannuntaba.
Bataso tafiyaba saita hadu da Inayah Amma MAJEED ya hanata ganin 'yarta sbd yaqara nuna Mata ikonsa akanta.
Bayan barinsu gidan umma yaganah qin zuwa Inda Inayah take tayi sbd wannan karon tayi mummunan Kona Mata Rai.
Matuqar auren MAJEED yabar kanta Bata tunanin Inayah Zata samu mijinda zai kaisa agurin kulawa da ita Dan haka zatai iya kokarinta gurin ganin wannan auren baitaba rabuwaba Koda hakan na nufin da qarfin hali ta cusa Inayah gun MAJEED ya dirka Mata ciki taga yanda auren zai rabu kowama ya huta har Hadizan da 'dan su huta dasu akan raba auren.
Ranar gidan ko abincin dare Babu Wanda ya fito ci sai Neesah kawai data fito itama snacks kawai taci takoma daki ta kwanta.
Acikin daren Abbi yayi booking ticket na zuwa Abuja akwai Wanda zai gani daga can zai wucewarsa Dan Yana buqatan kansa ya sake.
Washe gari qarfe 8 na safe yayiwa umma yaganah txt driver ya wuce dashi airport jirginsu ya tashi qarfe Tara.
Koda INAYAH ta tashi da safe jiki a mace tasan Bata kyautaba Musamman da umma yaganah ta matse fuska sosai Bata wani sake Mata ba
Duk saitaji tasake Shiga damuwa dan haka ko wanka bataiba da Riga da wandon bacci masu tsantsi ta wuce palon Abbinta Dan basa hakuri sbd Bata iya juran fushinsa akanta ko kadan,
Kuma ta wani bangaren gaskiyarta ce tafada bazata iya rayuwar aure da Abbinba sbd asalin life takeso arayuwar aurenta wanda Zata iya nuna soyayyar mijinta agaban kowa Kuma shima zai iya nunawa agaban kowa Dan haka Babu ta Inda Zata iya wannan rayuwar da Abbi Wanda takewa kallon ubanta Kuma uwarta.
Shine ya koyar da ita yakuma Bata tarbiyar fadar Gaskia komai dacin dazata kawo shiyasa koyaushe ake ganin wautarta Dan ita tasaba gaskiyarta take fada daga zuciya ba boye boye ko munafurci.
Kayan jikinta umma yaganah ta kalla lokacinda ta gaisheta tareda juyawa Zata nufa sashen Abbin.
Floral pyjamas ne na bacci ajikinta masu santsi farare,
Babu bra ajikinta Dan haka kirjinta dasuke tsaye qyam suna bayyanarda basa cikin bra din.
Ko hips dinta sosai suka fito a wandon kayan sbd santsin kayan yasa suka Dan lafe a jikinta.
Da adah ne umma yaganah hanata zuwa takeyi gaban Abbinta da kayan bacci sbd kusan rayuwar Inayah din babu ruwanta kusan koyaya tana iya zuwa gaban mahaifinta da towel ne kawai Bata iya zuwa gabansa sai guntayen Kaya Amma Dan kayan bacci dasu leggings duk ba komai bane agunta.
Umman na sane Sarai ta qyaleta ta Kama hanyar palon nasa batareda tace Mata taje ta sauyaba kokuma sanya wani Abu akai.
Ja'irar yarinya Allah ya nunan ranarda wannan bakin naki zai mutu yayi hankali.
Shima MAJEED din da haryanzu yake biye Miki yaqi bude Baki ya magantu dakyau ki dawo hankalinki.
Inayah nakaiwa kofa massage din MAJEED nashigowa wayar umma na cewan yayi tafiya.
Sanyi jikinta yayi tanajin tausayin MAJEED din sbd abubuwan sun Masa yawa gashi wannan Yar banzar na Neman qara zafafa Masa kai da haukarta.
Cikin gatse tace"
Hajiya saiki dawo MAJEED din yayi tafiya yace
Saiki dawo kici gaba da kuka tunda Baki aura Dan rayuwar dakike burin samun aureba.
Maganar umma na cewan abbin yayi tafiya yasa hankalinta sake tashi saidai Bata nunaba sbd umman karta cigaba da Mata wannan fadan na baqar magana Dan haka ta juya jiki mace Takoma dakinta.
Tana shiga daki ta zauna tareda daukan wayarta Kai tsaye tasaka kiransa tana sake Shiga damuwa Mai tsanani,
Abbinta akaron farko dasuka kwana suka wuni basuyi wayaba basuyi maganar arzikiba,
Yanzu Kuma yayi tafiya batama saniba hakama umma yaganah kawai ya fadawa.
Hawaye taji idanuwanta na cikowa dasu indai kuwa akan Abdulsamad Abbinta zaiyi irin wannan fushin da ita Zata hakura dashi...
Tama hakura dashi
Zata bawa Abbi hakuri bazata sake ko maganar Abdul dinba barema ummansa.
Kiran wayarsa tahau yi Amma takasa samu Dan haka taji kaman wani zazzabin na neman kamata Dan haka ta silala tayo wanka ta shirya cikin doguwar Riga breakfast dinma Dan Dole ta fito taci tana qarfafawa kanta sbd Abbi yadawo anjima ya taddata ta sake zaifi saurin yafe Mata sbd fushin Abbi shine abinda Bata taba dauka da wasaba.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107[11/3, 10:19 AM] It's Queen Meenali👑: *_37_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Sukuku ta wuni ranar zuciyarta ba Dadi hakama umma har lokacin ta fuske Mata ga Neesah nata shirye shiryen tafiyarta ga abbin sai Kira takeyi takasa samunsa duk saitaji kaman tayita rusa kuka
Gashi umma na fushi ko tayi kukan tasan ba rarrashinta umman zataiba.
Har qarfe biyar na yamma tana jiran dawowar abbin sbd Bata tunanin tafiyarsa Mai nisace kokuma kwana bare barin qasa dazai tafi Bata saniba tana matsayin 'yarsa daya tal......
Shiru tayi daga wannan tunanin sbd tunowa da auren da har lokacin Batajin ta sauko ta karba auren,
Ta hakura da Dr Abdul sbd kaucewa fushin abbin Amma ita maganar aurenta dashi batajin Zata taba karban wannan.
Ganin zaman Yana neman Cinna Mata hauka yasa ta fito Palo tana kokarin nufar hanyar dakin umma yaganah saiga qarar akwai baqi a kofa.
Duk da tasan ba Abbi bane Amma sbd tana buqatan ganinsa yasa taje da sauri ta bude tana adduar Allah yasa shi dinne.
Anty Hafsat tagani da CM da sauri ta rungume anty Hafsat tana Jin hawaye na ciko idonta kawai sbd Daman tana neman Wanda Zata fadawa kukanta.
Cikin kulawa Anty Hafsat ta dago bayan ta zare jikinta tace"
Muna tareda baqi Inayah behave yourself idan mun nutsu mayi magana.
Fuskarta still da sauran hawaye ta juyo ta kalli baqin.
CM tafara kallo cikin nutsuwa tace"
Daddy Ina wuni?
Murmushi yayi cikin kulawa shima yace"
Lfy kalau Inayah,
Yaya umma yaganah?
Ki gaidata idan Kun shiga bazan tsayaba sauri nake saidai idan nadawo.
Anty Hafsat ya kalla yace"
zanje na dauko Alhaji babbah sbd suma su Haj Hadizan suna hanyar qarasowa nan din kafin su iso akai su hajiya suyi sallah su huta sun biyo hanya.
Juyawa yayi ya kalli farar dattijuwar dake tsaye gefe cikin ash Australian lace da lafaya baqa a nade da ita yace"
Hajiya ku qarasa Bara na dauko Alhaji idan kafin Ku huta.
Gyada Masa Kai kawai tayi ahankali tareda maida kallonta kan Inayah data kasa daukewa Ido.
Cikin nutsuwa Inayah ta kalli matar wadda itama tsura Mata Ido yayi sosai sbd haskenta sosai da Kuma ganin kamanninta sosai da Abbinta Dan kuwa kusan Tama fisa kyau sbd tana mace saidai kawai manyancin datai sosai.
A natse cikin kasa boye mamakinta sosai tace"
Ina wuni?
sannu da zuwa.
Sam hajiyar Bata amsaba Wanda ita Inayah Sam Bata luraba juyawa tayi Takoma ciki tana sake saka Kiran Abbi a wayarta.
Cak hajiyar tayi agurin taqi saka kafarta a palon.
'yarta dake gefenta wadda a shekaru tafi anty Hafsat shekaru sosai ta kalli hajiyar zuciyarta na quna kaman yanda ta hajiyar ke quna Kai tsaye ta bude Baki ba boye boye tace"
Hajiya inaga mu koma gida kowai kokuma kokuma muje gidan Alhaji babbahn shida kikazo sbd alfarmar daya nema ta zuwan naki.
Batareda hajiyar tace komaiba kuwa suka juya
Anty Hafsat ta juyo da sauri tareda binsu a rikice tana bawa hajiyar hakurin su dawo.
Hajiyar tafiyar kawai takeyi Amma zuciyarta a rufe take....
Ciwon hawan jininta Dana zuciya daf yake da tashi sbd dacin da zuciyarta ke dauka..
Kasa jurewa tayi ta tsaya cak tana Dan dafe kirjinta.
Da sauri anty Hafsat da 'yar tata wadda anty Hafsat takira da Anty juwairiyyah suka riqota suna Kiran sunanta da cikin kulawa.
Ganin tana neman faduwa agurin yasa ba yanda anty juwairiyyah ta iya suka Jata suka koma cikin gidan.
Umma yaganah data fito palon Jin ance sunyi baqi Bata ga kowaba tana Shirin juyawa suka shigo da hajiyar a rirriqe.
Da sauri cikin kulawa tace"
Subhanallh,
Hafsat baqin namune ba lafiya?
Bari Akira Dr farhat da sauri kafin Nan Bari Neesah ta fara dubata.
Ciki umman tayi takira Neesah saidai Ashe Neesah din ta fita Dole sai dr farhat suka kira da gaggawa.
Agurin wayar anty Hafsat tace"
Umma yaganah ki sanar da ita umman AA MAJEED ce da kanta da Allah ta iso da wuri........
Wuta umma yaganah ta dauke tareda bude dukkanin idonta tana kallon hajiya.
Sai alokacin taga zallar kamannin MAJEED atareda hajiyar dan haka take jikinta Dana Inayah data fito lokacin mutuwa sbd tsananin farin ciki.
Umma na aje wayar kuwa ta kalli anty Hafsat tace"
Mahaifiyar MAJEED ce kikace?
Eh umma itace.
Maida kallonsu kan hajiya sukai itada Inayah lokaci daya fuskar Inayah daukeda farin ciki Batasan lokacinda ta furta"
Yau Naga daya da cikin kakannina kenan...
Ashe munada dangi muma,
Abbi na ummansa na raye..
Da sauri umma yaganah ta Dan kwabeta kada ta sauka layi
Cikin sakin fuska da bayyanan farin ciki tafara yimusu sabuwar sannu da zuwa tana miqewa Anty juwairiyyah ruwan roba da aka kawo Mara sanyi tace"
Bata Tasha Zata Dan ji dama Dama kafin Dr farhat din tazo.
Daga hajiyar har anti juwairiyyah Babu wanda ya iya magana har lokacin sbd Babu Wanda zuciyarsa Bata cikin dacin rai na shigowa gidan.
Ganin yanayinsu yasa umma datake Babba ta fahimci akwai damuwa Dan haka tace Inayah tayi ciki har hajiyar ta samu nutsuwa tukunna.
Babban dakin bakinsu dake gefen na umma yaganah aka gyara take duk da Baya buqatan wani gyaran sbd komai na dakin fes yake Kuma Babbane da toilet.
Dubari su Anty Hafsat suka ringa yiwa hajiyar ana mata firfita duk da sanyin AC sbd asamu Dr farhat ta iso.
Dr farhat na isowa aka Kama hajiyar aka Kai dakin da aka Gama gyara musu sanyin AC da qamshi sai tashi yakeyi.
Ba wata matsalar bace kawai jinintane ya hau take.
Maganinta da batazo dashiba shi Dr farhat tasa aka kawo suka Bata
Cikin Yan mintuna kuwa sai gashi tadan samu tafara dawowa daidai.
Fita akai aka bawa hajiyar da Anty juwairiyyah guri su but suyi sallah da sauransu tukuna.
Bayan fitarsu ganin yanayin hajiyar yasa Anty juwairiyyah data Gama cika da baqin ciki aranta tun na shekarun Dana yanzu datake gani gabanta yasa bataiwa hajiyar maganar komaiba ta nufi toilet tashiga Dan yin alwala.
Hajiyarma saita huta Zata iya sallar sbd tanajin jiri har lokacin da bugawar zuciya da sauri Dan haka rufe idanuwa tayi daga kwancen tanajin zuciyarta na karye fiyeda shekarun data debo bada ABDULMAJEED dintaba sbd Bata saniba Ashe Yana Nan ya Gina sabuwar rayuwa da sabuwar uwa...Jin tayi hawaye na taruwa acikin idonta Amma kaman koyaushe Bata barin su gangaro sbd zubda hawayen uwa akan danta matuqar bana farin cikiba babbar masiface ga 'da.
Inayah kuwa cikin farin ciki take Neman wayar abbin Amma still Bata samuba sai taji murnarta ta Kai sbd duk Wanda Zata samu a rayuwarta matuqar Bata daidai da Abbinta Bata cikin farin ciki da nutsuwa Dan haka take murnar ta sace Mata ta zauna daki tareda zubawa wayarta Ido.
Umma yaganah kuwa hidima tashiga kitchen da kanta tafara yiwa su hajiyar MAJEED din sbd tasan matsayinsu sun wuce abar 'yan aiki da hidimarsu Dan haka tahau aikin abinci Lafiyayye Mai lafiya.
Saida akai Kiran magriba aka Gama komai aka kwasa a jere da kuloli aka Kai dakinsu har lokacin daga hajiyar har Anty juwairiyyah Babu Wanda ya saki fuska ko nuna sakewa Amma hajiyar taji sauki tana zaune tana waya a sanyaye da babbar yarta.
Umma yaganah Bata damu da rashin sakewarsuba bil haqqi take musu hidima tana sake bayyanar musu da mahimmanci dasuke dashi Mai girma a gidan duk da yau suka fara zuwa.
Acan Kuma Inayah nason magana da anty Hafsat Amma anty Hafsat din ta hana sbd Dr farhat na gidan Bata wuceba Kuma Batasan da MAJEED aka daura aurenba a qataice bakowane yasan meye dalilin fasa auren Inayah da Dr Abdul ba hakama bakowa yasan da waye aka daura aurenba sbd duk har lokacin a uban Inayah suka Sansa.
Dr farhat na tafiya saiga su Alhaji babbah sun iso daidai tareda motarsu umma Hadiza da 'yan uwanta.
Dunguma sukai suka shigo ciki gabaki daya babban palonsu umma yaganah.
Tunda umma Hadiza tashigo take rarraba idon Neman ganin Inayah cikin gidan.
Inayah tunda taji su umma Hadiza sunzo gidan taqi fitowa ko Alhaji babbah tanason fitowa ta gaidar Amma batajin Zata iya barin umma Hadiza ta ganta matuqar bada izinin Abbinta ba sbd shine kawai yakeda iko akanta na yanda zaiyi da alaqarta da Hadizan.
Umma yaganah ma Gaisawa kawai tayi dasu Alhaji babban ta miqe Zata komawarta ciki sbd yanzu da mahaifiyar MAJEED take Nan ba buqatan zamanta agurin dama can Dan tana matsayin uwa ne.
Cikin nutsuwa Alhaji babbah yace"
Yaganah dawo ki zauna ai komai dake zaayi kece MAJEED yanzu tunda Baya Nan.
Dan murmushin yaqe tayi tareda dawowa ta zauna tana dan kallon Inda hajiyar MAJEED take zaune fuskarta ba walwala ko kadan.
Kusan kowa ya zauna ya nutsu,
Alhaji babbah ne da CM a gefe daya
Sai umma Hadiza da Haj balaraba a dayan gefen
Alhaji buhari dasu malam Umar ma dasuka matsu dason ganin Inayah duk suna zaune sai Dr Abdul daya rakube cikin yanayi na tausayi da ciwon dake damunsa.
Hajiyar MAJEED ma da Anty juwairiyyah da umma yaganah sai Anty Hafsat gefensu daya.
Cikin nutsuwa Alhaji babbah yafara magana da cewa"
To dukkaninmu dai kusan bamusan junaba anan MAJEED da INAYAH ne ya hadamu anan,
MAJEED yayi tafiya wadda Nima ban hanasa duk da nasan zaayi wannan zaman sbd Yana cikin yamutsin Kai Dana zuciya
Yaron Yana buqatan nutsuwa sbd abubuwan duk sun taru sun ratayane akansa Dan haka gwara abarsa ya samu nutsuwa kada pressure da damuwa din mahaifiyarsa gatanan data matarsa data hajiya Hadiza dama Tamu duka ta sanyasa cikin wani hali.
Hajiya Asma'u wannan itace hajiya Hadiza da 'yan uwanta gasunan mahaifiyar Inayah 'yar MAJEED da kuka sani a baya matarsa Kuma a yanzu.
Hajiya Hadiza wannan Kuma itace mahaifiyar ABDULMAJEED data haifesa.
Ayanzu wannan taron dai na fahimatar junane dakuma warware duk wata damuwa da qaddarar data Riga ta wuce.
Inayah dai ba 'yar MAJEED bace hajiya kaman yanda kike tunani
Amma dai yanda tazo hannunsa ne Babu Wanda yasani sai Allah saikuma MAJEED din da Hadiza gatanan zaune.
Hadiza ki warwarewa hajiya komai sbd kawarda zargi da Kuma damuwar qaddarorin dasuka gifta abaya data rabu da 'danta akan hakan.
Dagowa Hadiza tayi jiki a sanyaye ta kalli hajiyar cikeda kunyar Zama mugun sanadin daya kawo abubuwa da dama.
Kan su Yaya Umar da Yaya kabiru ta maida kallonta sbd kusan suma sune sanadin komai.
Inayah data tsaya bakin kofar dakin umma yaganah sbd tanason taji yanda tazo hannun Abbinta da kunnenta batareda wani ya fada Mata ya rage Mata wani abun....
SHEKARUN BAYA....
#MAMUH##
#LOVE/ROMANCE/LOADING
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[11/3, 10:19 AM] It's Queen Meenali👑: *_38_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Tana fitowa gidansu rungume da jaririyar tata dake lafe kirjinta tana bacci taji qafafuwanta na Neman sanyi Amma sukasa riqeta sbd wani irin nauyi da kirjinta kemata tareda radadi a maqoshi..
Sake rungume jaririyarta tayi da kyau ahankali kafin ta dago ta kalli hanya da idanuwanta dasuka qafe sukai jajir sbd kuka tuni ya qafe daga Idanuwanta.
Ahankali ta daga qafafunta tafara tafiya tareda kauke kanta qasa sbd Yan anguwa wainda suka lura da ita suke kallonta da ma'anoni da maganganun zunde da zagi.
Bakowane yasan tadwo daga Lagos dinba da ciki saidai sukaji haihuwar tareda rasuwar mahaifiyarta shiyasa kusan duk Wanda ya bude Baki tir da Allah wadai yake furtawa gareta da jaririyar 'yarta.
Ahankali take takawar sbd rashin qarfin jiki dakuma qarin data samu agun haihuwa gakuma rashin abinci ko abinsha Dan haka batada wani babban kuzarin takawa da sauri harta fice daga layin batareda ta waiwayo ba Dan tanajin idanuwan mutane akanta Wanda tasan mummunan fatar rashin ganin me kyau suke Mata a duniyar da Zata shiga.
Kasa hawa titi tayi sbd Batasan Inda ta dosaba,
Batasan gurin waye Zata ba a wannan mummunan halin datake ciki,
Batada uwa Bata uba batada miji waye gareta Mai tsaya mata?
Samun kanta tayi da zaunawa bakin wata bishiya sbd kwakwalwarta datake neman Dena aiki.
Jaririyarta tafara kuka Wanda na tsananin zafin ranar dake dukansu ne
Yaye zanin datake dunqule aciki tayi ta Dan kalli fuskarta taga yanda fuskar tayi jajir take sbd azabar Rana
Sai alokacin taji zuciyarta data daskare tana narkewa da tausayin kanta dana jaririyar Dan haka batada zabi daya wuce ta tunkari gidansu salisu ko ummansa Zata karbesu tunda jikartace su taimaketa ta zauna gurinsu ta Rena Ayshatouh idan ko shekara tayi saita barta takoma gidansu idanma sbd itane su Yaya Umar suka koreta daga gida.
'yar qaramar jakar kayanta ta bude tafara duba kudin datake dasu.,
Dari uku da ashirin tagani take jikinta yakuma mutuwa saidai halinda zuciyarta take ciki Batajin akwai abinda zai fisa daci.,
Miqewa tayi ta qarasa bakin titi Anata kallonta sbd Jin yanda jaririya ke kuka sosai a jikinta Dan haka Bata tsaya juran napep ba ta tsayarda Mai mashin ta hau suka tafi.
Gabanta tsananta faduwa da shiga qunci yakeyi sbd hajiyar salisu ma batasan yaya zata karbesuba...
Mai mashin na ajiyeta kofar gidan ta Ciro dari da hamsin ta miqa Masa ta juya ta shige qaramar kofar gidan tana sake qamqame yarta jikinta.
Tun kafin ta qaraso ciki Yara suka fara Isa gurin hajiyar suka sanar Mata Hadiza tazo.
Dan shiru hajiyar tayi kafin ta kalli yaran ta korasu waje ta dawo da hankalinta kansu balaraba dake gidan ta sallamesu suka wuce inda zasu ta kofar baya batareda sun tsaya Gaisawa da Hadizan ba Dan dama a sama sama suke da ita tun salisu nada Rai bare yanzu da basuda alaqa da ita.
Da wata irin dasasshiyar sallama ta shigo hankali sbd muryarta ko fita batayi.
Da mamaki hajiya ta kalleta idanuwanta na sauka kan jaririyar dake hannun Hadizan.
Idanuwan Hadizan zuwa fuskarta ta kalla dakyau take tagane jegone tareda Hadizan Dan haka ta tattaro hankalinta da mamaki a bayyane kan fuskarta tace"
Hadiza¿
Kece nake gani?
Lafiya da Rana tsaka haka?
Ba zaman karban gaisuwar Aishatu akeba.
Kasa magana Hadiza tayi sbd jirin dake dibanta Dan haka a sukwane ta qaraso ta durqusa gaban hajiyar tareda sunkuyar dakai idanuwanta na sake rinewa.
Sake Shiga firgici hajiya tayi tana qin nuna taga jariri atareda hadizanba tasake cewa"
Hadiza nace lfy kuwa?
Kiyi mgana kikai shiru kina bani tsoro...
Dagowa Hadizan tayi tana kallon hajiyar sbd tasan bazatace bataga abinda ke hannuntaba
Idanma Bata ganiba bazatace batajin kukan da Ayshatouh ke tsalawaba.
Sunkuyar dakai tayi tareda bude jaririyar dakyau agaban hajiyar muryarta na a disashe da tsananin damuwa da qunci Mai daci tace"
Hajiya haihuwa nayi su Yaya Umar sukace nabar gida,
Bansan Inda zaniba sbd ko Abokai banda shine nataho Nan....
Dauke wuta hajiyar tayi daga zaune tana kallon Hadizan Baki sake ko fuskar jaririyar taqi kalla.
Qofa tafara kalla ta leqa tsakar gida taga ba kowa tadawo da sauri ta kalli Hadizan cikin tsananin mamaki, firgici da takaici Kai tsaye tace"
Me Zan Miki anan hadiza?
Haihuwafa kikace kinyi?
Haihuwa ba aure fa?
Wace qaddarace wannan takaiki ga wannan mummunan sakamakon? Shine Kuma Zaki zomun Nan?
Ko kunyar 'danki dake gidan Nan bakijiba kika kwaso jiki da jaririn shege kizomun anan?
To Kinga Hadiza tun kafin Raina ya baci Kuma tum kafin wani yaji tashi ki fice,
Mune mukafi kowa hauka a duniya ne dazamu Baki gurin zaman renon barna......
Rawa hannuwan Hadiza suka fara hankalinta yasake mummunan tashi tana kallon hajiya da idanuwanta jajir tace"
Dan Allah hajiya ki yarda Dani ki fahimceni
Kima kaini a dubani idan ana dubawa wallahi tallahi banyi kowace irin barnaba nasamu cikin Nan,
Wallahi cikin salisu ne......
Wata irin mummunan zabura hajiyar tayi tana kallon Hadiza a gigice sbd mamaki da baqin cikin zancenta Dan ta Gama raina Mata hankali kokuwa dai mahaukaciya ta dauketa?
Amma dai Bari ta tabbatar...kallonta tayi a Rikice tace wane salisun Hadiza?
Muryarta Bata fita sosai sbd shaqewar maqoshi tace"
Salisu baban Abdul....
Kasa magana hajiyar tayi ta rufe idonta daya fara sauyawa sbd tsananin bacin Rai da masifar Rainin da Hadiza tazo dashi Dan haka Bata buqatan ma Jin komai ta nuna Mata hanya tace"
Fice Hadiza kibar gabana Dan Allah.
Dagowa Hadiza tayi ta kalli hajiyar sai alokacin hawaye suka ciko jajayen idanuwanta suka fara gangarowa.
Magana takeson yi Amma zuciyarta tayi nauyi bazata iyaba sai wani irin quntataccen kuka Mai ciwo daya zuwar Mata.
Ganin ba tashi zataiba kada wani yashigo yagantama kokuma yaji haukar datake fada yasa hajiyar Kama hannayenta ta miqar tsaye tareda janta takaita har waje ta Kuma gargadeta akan sake zuwa da wata jaririyar gidan da sunan salisu abakinta.
Kuka sosai Hadiza keyi tanajin wani irin azababben ciwo a zuciyarta,
Jin takeyi kaman zuciyarta zata mutu,
Ganin mutanen dake wucewa sunfara Mata kallon mahaukaciya yasata Jan jiki tabar kofar gidan.
Tafiya kawai takeyi sbd Batasan Inda zataba,
Jin jaririyar tayi baccin wuya itama yasata tsayawa ta goyata taci gaba da tafiya.
Tafiya Mai nisa tayi wadda batamasan tayiba har Saida yamma tayi sosai ta nema bakin wani gidan abinci ta zauna tareda sauke jaririyarta ta saka cikin hijabinta tafara Bata nono.
Kasa Shan nono 'yar tayi sbd tuni ciwon zazzabin wahala ya rufeta sbd ba qaramar Rana sukashaba.
Fara jijjigata tayi tana sake cusa Mata nonon Amma Bata amsaba Dan haka ta maidata ta goya.
Shagon dake gefen gidan abincin ta qarasa ta siyo ruwan roba na sauran canjinta dasuka rage Takoma Inda ta baro ta zauna tasake saukoda 'yar ta bude ruwan ta ringa zubawa a murfin robar tana Bata.
Ruwan ma batasha saidai wasu sun shiga cikinta kadan...
Kuka jaririyar keyi sosai Wanda ya qarasa gigita Hadiza..
Batasan ya zataiba sbd kanta zazzabi da ciwone Mai qarfi a jikinta.
Gabanta radadi yake Mata sbd qarin haihuwa da rashin ruwan zafin gasa gurin ga doguwar tafiya cikin azabar Rana Dan haka itama take a gigice.
Kukan 'yar yasa Dole tabar gurin ganin hankalin jama'a yafara yawa kanta.
Cikin wasu mabarata dake gaba kadan bakin wasu super market taje ta zauna tana sake fama da Yar dake kuka har lokacin.
Nanma bata tsiraba sbd anfara Mata kallon zargi da 'yar
Silalewa tayi tabar gurin kafin ayi Mata dukan Satan 'ya takama hanya taci gaba da tafiya gashi duhun dare yafara Dan har anfito sallar magriba.
Tafiya Mai Dan tsayi takuma Yi taji bazata iyaba sbd radadi da azabar da tsakiyar cinyiyinta ke Mata,
Azabar datakeji tafi Mata naqudar haihuwar datayi sbd gurin ya goge sosai sbd tafiya Dan haka tasamu wasu shaguna da Yan gudun hijira suke ta zauna daga can gefe itama.
Ruwan robar data siyawa yarta itama taciro daqyar ta iya karban kadan ta shimfida zaninta agurin ta kwanta tana fidda numfashi daqyar jikinta na rawar sanyi.
Babu Wanda ya lura da ita sbd suma kowa ta kansa yakeyi Bata wani ba dan kowa agurin abin tausayine.
Yarta na dungule cikin jikinta itama tayi bacci.
Hadiza Batasan inda kanta yakeba sbd kusan suma tayi saida sanyin asuba da kukan yarta ya dawo da ita
Ta bude idanuwanta daqyar tana Neman tashi Amma takasa.
Daga kwancen ta sake rungume jaririyarta ta Ciro nono tasaka Mata a Baki.
Ana Gama sallar asuba duka mabarata da Yan gudun hijira dake gurin suka fara watsewa sbd baa barin Zama gurin da daddare kawai suke zuwa su kwanta da gari ya waye kowa yatafi gurin bara.
Daqyar ta iya daddafawa ta tashi tabar gurin
Tafiya kadan tayi tasamu guri ta zauna sbd bazata iyaba.
Anan gurin ta Rana ta fito ta sameta
Mutanen dake wucewa suka fara Bata sadaka sbd sun dauka Bata takeyi
Dayake tana buqatan taimakon ana bata haka ta ringa karba har Allah yasa ta hada 400 ta tashi daqyar ta siya ruwan zafi gurin me shayi ta Sha na hamsin ta siya wasu na hamsin din ta wankewa 'yarta jiki ta gogeta ta maida Mata kayanta da daudarsu da komai.
Har yamma tana garari a hanya Dan haka tasake komawa gidansu salisu
Hajiyarsa Bata tausayawa mataba tayi Mata korar wulaqanci harda munanan kalamai akan 'yarta Dan haka ta sake komawa Inda ta kwana jiya anan ta Kuma kwanciya.
Washe gari ma haka ta sake zuwa gidansu salisu a karon karshe hajiyarsa tayi Mata mummunan gargadin sake zuwa tareda tabbatar Mata da har abada bazasu karbi shegiyar data haifaba amatsayin 'yar salisu.
Ranar tayi kukan data jima batasamu tayiba sbd maganganun hajiyar dakuma ciwo Mai tsanani daya sakota gaba da 'yarta.
A ranar ko bacci Bata samu tayiba a zaune ta kwana tana kallon yarta wadda da alama sanyi ne yayi mummunan shigarta tana numfashi daqyar.
Gabaki daya duniyar tayi mata zafi,
Qunci da nauyi takeji a zuciyarta Mai tsananin gaske..
Washe gari da safe data samu qarfin jikinta ta tallaba takai jaririyarta wani qaramin asibiti datagani a hanya.
Karon farko ana dubata akace Mata 'yar batada lfy sosai,
Zuciyarta Bata bugawa yanda yakamata hakama sanyi na Neman shigarta.
Gado aka Bata Amma sbd batada ko kudi suka korota ta fito tana bin hanya Ahankali idanuwanta na tsiyayar hawaye.
Yau Bata samu gurin kwanciyaba sbd yan hijirar dasuka qara yawa Dan haka Nesa dasu sosai tasamu ta kwanta.
Hankalinta a tashe yake da Inda ta kwanta din sbd itace a nesa qarshe sosai
Wasu irin sauro da cinnaku suka ringa cizonta tanaji Amma Bata ko iya motsawa sbd zuciyarta data Gama mutuwa.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107[11/3, 7:34 PM] +234 808 746 2576: *_39_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Koda garin ya waye daga ita har 'yarta gabaki daya jikinsu kurajen cizan sauro sun bayyana ajikinsu ita hardana cinnaku dasukai Mata kaman Mai wani ciwon take fuskarta ta kumbura.
Tashi tayi ta nufi Inda suke gyara jikinsu ta gyara ta fito ta miqa hanya goye da 'yar tata.
Kwananta hudu agurin aka rarraba musu kudin sadaka a gurin akan kowa yabar gurin
tana karban nata ta tattara tsumman kayanta ta nufi asibiti takai 'yarta data fara nisa.
Kwantar dasu akai tareda sakasawa 'yar oxygen Wanda ya cinye kudin nata batareda ansamu na siyan sauran maganiba.
Daqyar takai safe cikin tashin hankali Mai tsanani da qaqa nikayi sbd jikin 'yar jaririyarta daya sake gabaki daya.
Rashin Imani da rashin tausayin asibitin haka suka sallameta sbd rashin magani da rashin kudin siyansa ta rungumo 'yarta ta fito tana hada hanya.
Yau kam komai yasake yimata tsananin da takejin mutuwa take buqata Ido rufe.
Uwarta da ubanta da salisu takeson bi Ido rufe sbd ta huta da qunci da baqin cikin duniyar datake ciki.
Kuka aranar tayisa har idanuwanta basa gani sosai sbd kumbura.
Tahau titi rungume da 'yarta wadda take tsoron dubawa ko ta mutu ko tanada sauran Rai.
Mutuwa take Kira take Kuma fata sbd Babu Inda takejin sassauci a wannan rayuwar.
Wani azababben ciwon gaba take fama dashi da ciwo ciki Mai tsanani,
Ta bangare daya qwaqwalwarta tafara kasa daukan tashin hankalin da masifar datake ciki Dan haka wunin ranar attempting kashe kanta kawai takeyi Amma tsananin qaunar datakewa yarta Yana hanata idan ta kalleta.
Tamkar mahaukaciya tafara komawa sbd taba qwaqwalwarta da abin yafara Musamman mummunan infection din daya shigeta sosai sbd rashin kulawa da gurinda ta Haihu.
Tun tana iya controlling kanta akan yanayinta dayake son juyar da qwaqwalwarta haryazo tafara tsoraran yanayinda jaririyarta da itama kusan Rai ne kawai ya rage Mata Zata shiga idan wani Abu ya sameta.
wani masallaci takai 'yar ta ajiye Zata gudu tabarta ko zaa samu Wanda zai tallafeta Amma saita kasa barinta agurin tadauketa tana hawaye tana jujjuyar dakai tabi hanya tana surautai ita kadai.
Batasan ya akaiba sai gata kwatsam takai kanta hanyar Tasha tana tafiya.
Kaduna ne?
Ina zuwa ne?
Kano ne?
Katsina ne?
A kunnuwanta kalmomin ke sauka suna sake yamutsa qwaqwalwarta...
Jikinta rawa yakeyi sosai kanta na sake juyawa sosai.
Ahankali sama sama takejin cikin nutsuwa wani yayi magana a bayanta.
Assalam alaikum,
Malama Zan wuce ko
Zaki Dan matsa.
Waiwayowa tayi da sauri a firgice tareda kallon Mai maganar.
Saurayine matashi Wanda zatai qani dashi bamai tazaraba sosai.
Sanye yake cikin qananun Kaya Riga ash da wandon jeans black.
Cikin sauri Dan tashar masu mota ya qaraso Yana daka Mata tsawa da cewa"
Dalla matsa ki wuce daga Nan
Kinzo kintare hanya
Idan bara zakiyi ki matsa can.
Yallabai Kace gombe Abuja ne ko?
Kallonsa matashin yayi kafin ya kalli Hadiza data Matsa gefe ta rabe rungume da abinda yake sakaran 'da ne sbd yanda ta rungume zanin cikeda so da shauqi.
Hannu ya saka aljihunsa ya Ciro Dubu daya ya miqa Mata cikeda kulawa batareda yace komaiba.
Hannu ta miqa a hankali ta karba tareda kafesa da Ido tana zuba godiya Kuma takasa tafiya.
Cikin qaguwa ya kalli masu lodin motar yace"
Saura mutum nawane motar tacika hanyar kunsanfa bawani kyaune da itaba.
Yallabai Saura mutum uku motar tacika.
Muje zan biya kudin sauran gurin.
Angama ranka yallabai.
Hadiza dake rakube tanajin haka sai kawai tasamu kanta da biyo bayansa tafara kokarin Shiga motar sbd Jin zaa biya koba komai gwara tashiga duniyar tunda hakane qaddararta.
Kokarin hanata shiga motar direba yafara yana cewa"
Ke tsaya, tsaya
Ina zaki?
Wane gari Zaki?
Abuja" ta furta Kai tsaye muryarta na 'dan rawa.
Ina kudinki na mota?
Waiwayowa tayi ta kalli gefenda matashin yake zaune cikin nutsuwa Yana duba wayar hannunsa.
Ganin tana kallonsa ya fahimci batada kudin motar Dan haka yacewa drivern tahau gurin mutum daya cikin kudin mutum biyu daya biya.
Kasa kallonsa tayi bare tasake Masa godia saima sauke kanta datayi qasa tana sake rungume jaririyarta.
Hanya aka dauka aka fara tafiya Mai nisa kowa yayi tsit a motar Yana aikin gabansa masu bacci Kuma nayi.
Ahankali ahankali idanuwan Hadiza suke cikowa da hawaye tanajin wani irin masifaffen ciwon Kai da zabar ciwon ciki.
'yarta take ji,
Ita take tausayi ba kantaba,
Jin kanta na neman juyewa yasa tafara jin kaman tace a tsaya ta sauka.
Yanayin yanda take sake qanqame babynta yasashi Dan dagowa ya kalleta dakyau yaga tarin tashin hankalin dayake ciki kafin ya maida kallonsa kan babyn cikeda kulawa yace"
Ki Dan sassauta riqon
Kina matse babyn sosai Inaga.
Da sauri kaman qaramar yarinya tayi saurin sassauta riqon tareda bube jaririyar gabaki daya Dan Tasha iska.
Wani irin mamaki da firgici ne ya kamasa ganin babyn wadda alamun rashin lafiya sosai da yin nisa ya bayyana atareda da ita,
Gabaki daya babyn yunwa tagama kamata tako ina.
Dauke kansa yayi daga kallon jaririyar sbd zuciyarsa bazata iya jurewa kallontaba.
Tafiya suka cigaba dayi mai nisa da gudu..
Guri biyu aka tsaya siyan abinci Kuma ya siya Mata yabata sbd lurada akwai yunwa tareda ita.
Duk abinda ya siya Mata ya bata bataciba suna jikinta dunqule sbd bazata iya ciba ita kadai tasan tsananin halin azabar datake ciki.
Daga Nan Basu sake tsayawaba a hanya suka cigaba da zuba gudu a hanya.
Qarfe Tara da mintuna arbain da takwas suka isa birnin tarayya.
Kowa fitowa yayi daga motar yana haramar daukan kayansa ya wuce.
Daga shi sai jakarsa dake rataye a kafadarsa ya fito Yana sake saka Kiran Wanda aka aiko daukansa daga gida.
Ahankali Hadiza ta tako gefensa ta kallesa qafafuwanta na 'dan yin rawa.
Tsalle zuciyarta keyi ga abinda zuciyar tata ke ingizata ga aikatawa.
Jin takeyi zuciyarta ta kwanta data barmasa 'yarta ta gudu sbd yanada tausayi da Jin qai Dan kuwa ita batada tabbacin zatakai labari ayanda takejin azaba da radadi cikin jikinta.
Bazataso wani Abu ya sametaba 'yarta ta gararanta...
Jin mutum kusa dashi yashi juyowa da Dan sauri sbd ya Dan firgita.
Kallonta yakeyi da mamaki sosai batareda yace Mata komaiba.
Ganin kallon dayake Mata yasata kallon 'yarta cikin kokarin daidaita kanta tace"
Nagode sosai Allah yasaka maka da Alkhairi.
Amin" kawai ya iya furtawa Kai tsaye Yana cigaba da wayarsa.
Yana aje wayar drivern ya tura aljihun jeans dinsa drivern gidansu yace Saura kadan ya iso.
Jakarsa ya juyo zai dauka daga qasa gefensa idanuwansa suka sauka kan zani kan jakar tasa.
Da sauri ya waiwaya Babu kowa gefensa da bayansa.
Sake jujjuyawa yayi Yana Raba idon matar data bar Masa zanin.
Jakar ya riqe zai dauka ya watsar da zanin agurin sai zuciyarsa ta kasa Dan haka yakai hannu kawai zai janye zanin yaji alamun Abu aciki
Batareda ya taba tunanin ganin komaiba bare 'dan mutum ya bude zanin aikuwa yayi Ido biyu da babyn.
Zaro Ido yayi da sauri tareda mayarda zanin ya rufe babyn zuciyarsa na rawa.
Da sauri tafara waigawa koina Yana zazzare idon Neman Hadiza.
Daukan babyn yayi dan Dole ya rungume Yana sake jujjuyawa Neman Hadiza.
Fara tashi hankalinsa yayi dayaga dagaske yakasa ganin uwar babyn.
Kokarin komawa yakeyi gurin motar dasuka iso sai kawai ya hangota tana sauri zatabar tashar tana zazzare idon kada ya ganta.
Da sauri ya bita
tana ganinsa ta sake sauri ba Shiri ta tare Mai mashin ta haye suka bar gurin da sauri.
Tashin hankali da tsananin mamakine da firgici yasashi Neman wani mashin din ya hau Amma tuni Hadiza da me mashin dinta suka bace Masa.
Me wannan matar tayi ne?
Me take nufi?
Da gangan tana sane ta bar Masa babyn ta gudu fa.
Innalillahi wainna ilaihrrjiun..
Meyasa zatayi haka?
Dama mahaukaciyace Basu luraba?
Meyesa Zata gudu tabar Masa baby ?
Ina zai Kai babyn to?
Yawo ya ringa Yi dame mashin hankaki tashe Amma sun kasa ganin hadiza ko Mai Kama da ita.
Dukkanin qwaqwalwarsa tsayawa tayi cak shima
Ya tsaya rungume da baby ajikinsa Yana Jin jiri na Neman zubar dashi,
Ya zaiyi da wannan babyn?
Bazai iya komawa tashaba sbd baisan wazai bawa babynba,
Baimasan wazai fara tunkaraba a tasha da babyn sbd Babu ruwan kowa babuma Kuma Wanda zai karba.
Innalillahi wainna ilayhirrajiun" yafara maimaitawa dukkanin jikinsa na saki.
Mai mashin ya fadawa Inda zai kaishi
Wata qaramar police station yaje da babyn suka qi karba sukace yace babban station kawai.
Wata station din yakuma zuwa sukuma sukaqi karban 'yar suna zargin kodai yarda Yar kawai yakeson Yi.
Wata sabuwar masifar yakuma Shiga lokacinda yagama yawo da babyn Babu wata mafita ko daya.
Yanayin babyn kawai ya tabbatar masa da babyn sosai tayi nisa batada lafiya Dan haka ya tattara a nufi wani private asibiti yakaita su duba.
Suna karbanta take sukai dakin jarirai da ita.
Fada suka fara yimasa sosai ganin yanayin datake ciki.
Duk abubuwan zasuyi Mata sunyi suka sakata a kwalba sbd ma sai allah Kam idan Zata rayu.
Tashin hankali sabo yakuma Shiga lokacinda suka zayyano Masa cututtukan dasuke cin babyn.
Biyan komai yayi kafin ya samu ya wuce gida yabar babyn anan sbd akwai masu kula da babies a dakinsu.
Koda ya Isa gidansu mahaifiyarsa na ganinsa cikin tashin hankalin rashin daukan wayarsa da rashin ganinsa da driver yayi har kusan qarfe daya da rabi na daren yayi.
ABDULMAJEED..Ina ka shiga daga isowarka?
Lafiya kuwa?
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali idanuwansa na qanqancewa da tashin hankali da damuwa yace"
Hajiya umma kaina kaman zai fashe
Zanshiga nayi sallah tukuna.
Cikeda kulawa tace"
Jeka kayi wanka da sallar ka huta da safe mayi magana.
Juyawa yayi Yana hada hanya ya nufi hanyar dakinsa Yana jin kansa na sake tsananta ciwo.
Zubewa yayi qasa tsakiyar dakin Yana dafe kansa,
Daqyar ya tashi ya qarasa isa ya tube kayansa ya shafa toilet.
Wanka yayi ko zai samu kansa ya Dan sake tareda alwala yafito.
Jallabiya da gajeran wando kawai yasake yayi sallah ya miqe a daddafa ya Isa kan gadonsa ya hau ya kwanta tareda rufe fararen idanuwansa dasuka qanqance sbd tashin hankali da damuwa.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[11/4, 11:05 AM] +234 813 979 4675: *_40_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Babban tashin hankalinsa shine a yanayinda babyn Nan take ciki bazai iya bada ita ga Yan sandaba kokuma gidan marayu sbd tana cikin mawuyacin hali,
Haka Kuma mahaifiyarsa a yanda ya santa mace ce Mai tsananin kishin 'yayanta Musamman shi ta tsani wani ya rabesa Dan haka yasan bazata taba yarda da abar babynba hannunsu harta danyi wayo tukuna akaita gidan marayun
Idanma baa ga uwar babynba kenan Dan zuciyarsa takasa yarda da uwa Zata iya jefar da 'danta ta gudu duk tsananun rayuwa kuwa..
Washe gari tun kafin kowa ya tashi daga masallaci sallar asuba ya fice zuwa asibiti da mota Yana Jin rashin nutsuwa matuqar ba zuwa yayi yasan halinda babyn ke cikiba.
Banyi baccin nutsuwaba sbd Jin yake babyn mutuwa zatayi a halinda dai yabarta.
Tunaninsa gabaki daya ya karkata akan uwarta ta gudu ne tabar 'yar sbd rashin lafiyar babyn da bazata iya daukaba wannda hakan zallar rashin imani da tausayine.
Koda ya Isa asibitin babyn ba laifi tarta fara daidaituwa sbd Madara da aka kwana ana bata duk Bayan mintuna sbd yunwace da tsananin wahala da sanyi suka Kama babyn sosai.
Fes aka shiryata cikin kayan sanyi masu tsananin taushi farare tas daya siya tun jiya a asibitin aka shiryata.
Har Inda babyn take aka Isa dashi tareda kallonsa likita yace"
Ina uwar babyn take ne?
Tayi sakaci da ganganci sosai akan wannan babyn gskia.
Wani irin sanyi yaji zuciyarsa tayi batareda ya dauke idonsa daga kan babynba dake bacci idanuwanta a rufe murya a sanyaye yace"
Batada uwa.
Dakatawa daga rubutu a file Dr yayi yana dagowa dukkaninsa ya kalli ABDULMAJEED din da mamaki yace"
Ka kuwa gane abinda na tambaya?
Mahaifiyarta nake nufi,
Wadda ta haifeta.
Wani daci yaji yakuma cika ransa ambatar sunan uwar babyn...
Yana kallonta tana kallonsa da 'yarta a hannu tahau mashin ta gudu tabarsa da 'ya jaririya Yana yawo tsakar dare nemanta.
Mezaice gameda wannan uwar?
Mezai fadawa kowa gameda uwa irin wannan aduk Inda ze Kai babyn yasan bazaa taba kaunarta ko kulawa da itaba Kamar uwarta Koda kuwa a halin talauci da qunci ne.
Numfashi ya sauke a boye tareda dagowa ya kalli likitan Kai tsaye yace"
Mahaifiyarta ta rasu.
Numfashi Dr ya sauke tareda tausayawa babyn
Saikuma ya dago ya kalli ABDULMAJEED din dakyau
Dan haihuwa Kam ya Isa ya Haihu tunda matashine Amma Kuma yanayin wayewa da hutun daya gani tattareda dashi yasan zaiyi wuya ace yayi saurin aure bare harda haihuwa
A qiyasa bazai wuce 300level hakaba zuwa 400 a karatun jami'a.
Duk tunanin dr iya lissafinsane kawai Dan haka kai tsaye yace"
But you are the Father right??
Yes" kawai yace Masa Dan bayason tambayar.
Sauran abubuwan da baayi bane jiyan aka qarasa yi qarshe dai bai baro asibitin ba sai qarfe goma Sha daya sbd babyn Kam Saida aka hada da Oxygen.
Daga asibiti report yaje yasaka na Neman uwar babyn Wanda yasan zaiyi wuya a sameta tunda tana sane ta gudu ba wai batane babyn tayiba.
Koda ya dawo gida hankalin hajiya umma yagama tashi hakama duk Inda ranta yake yagama Kai qololuwa gurin baci.
Musamman su Anty juwairiyyah dasuka Gama qara hawar da ita akan zancen ABDULMAJEED yafi daukan mutanen waje da mahimmanci akanta.
Hajiya umma wadda asalin sunanta yake AYSHATOUH mahaifiyace ga ABDULMAJEED da yayunsa Mata guda biyu.
Anty juwairiyyah itace Babba sai Anty safiyyah saikuma shi ABDULMAJEED daya kasance qarami Kuma auta.
Son da mahaifinsu da hajiya umma kewa ABDULMAJEED sosai ya zarta abinda Yan uwansa zasu iya dauka sbd bambamci ne afili.
Mahaifinsu justice Abdullahi Isah babban former justice ne a high Court dake Abuja,
Yayi retire tareda barin qasar yakoma South Africa tsawon shekaru kafin yadawo Nigeria sbd ABDULMAJEED dake shaawar karatu da rayuwarsa a Nigeria.
Dagowarsu da qanqanin lokaci akai auren juwairiyyah da wani babban barrister anan Abuja haihuwarta daya auren ya mutu tadawo gida itakuma anty safiyyah dama Bata samu mijinba aikinta kawai takeyi Dan itama aikin mahaifinsu tabi lawyer ce.
Anty juwairiyyah da Anty safiyyah tun ABDULMAJEED dasu suna qanana Allah ya sanya musu kishinsa Mai tsanani Wanda ta wani fannin yake surkuwa da baqin ciki sbd fifici da banbancin da iyayensu suke nuna musu sosai akansa Musamman hajiya umma.
Abbansu Yana iya kokarinsa gurin yimusu adalci da Basu iya tasu kulawa da kaunar Amma Kuma ko yayane baya iya boye fificin kaunar ABDULMAJEED.
Ita hajiya umma nata shine yafi tabasu sosai sbd Babu tunanin illar hakan take nuna nata fificin.
Sunkoma tamkar wasu 'yayan riqo a hannun iyayensu sbd ABDULMAJEED Wanda hakan ya Gina rashin kauna tsakaninsu da 'dan uwansu.
Bayan rasuwar abbansu Haj umma sosai ta sake qwallafa ranta akan majeed Bataji Bata ganin kowa sai shi,
Su Anty juwairiyyah dasuka fara nuna rashin Jin dadinsu a fili sai kawai ta tsana zamansu a gida kullum cikin musu fadan rashin fidda mijin aure takeyi sun fara tsufa a gida.
Wannan kalaman nata ya tsananta duk wata tsanar dasukaiwa Dan uwansu sunajin kamar shine duk wata matsakarsu da baqin cikinsu na rayuwa.
Haj umma tsananin kaunar datakewa 'danta yasa ta kasance cikin irin iyayen dake tsananin kishin 'yayansu
Kishi Mai tsanani,
Sam batason kowa ya rabi 'danta tafison kulawarsa da komai akanta ita kadai,
Shikuma Allah yayisa Mai tausayi da taimako tareda mutunta mutane Musamman marasa qarfi kusan sune mutanensa Dan yafison yayi mu'amala da wainda zasu ringa qaruwa dashi suna samun taimakonsa dan kawar da tasu matsalar.
Mahaifiyarsa kuma hakan ne yasata ta tsani duk wasu marasa karfin dake taredashi sbd ganin sunason samun kusanci dashi,
Ba abinda yake Basu bane baqin cikinta Dan idan duka zai Basu dukiya batada damuwa ita damuwarta kada kowa ya samu kusanci da 'danta Bayan ita.
A American University of Nigeria yake karatunsa badan Haj umma tasoba tabarsa yake karatu a wani garinba sai Dan hakan mahaifinsa yaso,
Burin mahaifinsane ganin yayi karatunda zai mallaki komai nasa ya Gina kansa da kansa.
Fara karatunsa da yanda yake Dan jimawa baya gida yasa su Anty juwairiyyah suka fara samun shiga gurin Haj umma har suka fara kawo sabani tsakaninta da ABDULMAJEED ta hanyar saka Mata zargi Mai girma akan yafara 'yan Mata hankinsa akansu yake Nan gaba ma mace Zata Raba tsakaninta da 'danta.
Hankalin Haj umma tashi yayi sosai sbd yanda idonta ya rufe akan kaunar da kishin danta yasa komai aka fada Mata yarda takeyi Musamman da ABDULMAJEED din yayi budurwa kullum cikin kiransa take Dan tun Kiran Sumayya din na damunsa harya daina damunsa Dole ya saba.
Soyayyar MAJEED da sumayya ta daga hankalin Haj umma sbd sosai yanzu ta tabbarda mace Zata rabata da Dan ta Dan haka ta rufe Ido tamasa kaca kaca da fada takuma hanasa kula Mata saiya kammala karatun ita Zata Nemo masa matanda zai aura.
Ganin yanda ranta ya baci sosai yasa MAJEED din takaita muamalarsa da sumayya kwata kwata baisake bi takanta.
Amma duk da hakan shikenan Haj umma taringa saka Masa Ido takasa yarda dashi.
Wannan yakawo babban gibin dayasa su Anty juwairiyyah qarasa saka zargi da rashin sukuni a tsaninin Haj umma da majeed kusan yanzu kullum cikin fitinarta da fadanta yake akan Yana hulda da 'yan Mata shiyasa yake jimawa a makaranta kafin yadawo hutu gida.
Wannan ne babban matsalar data fara kunno Kai a tsakaninsa da mahaifiyarsa wadda kwata kwata Bata yarda dashi sosai yanzu.
Su Anty juwairiyyah kuwa yanzu zancensune abin yardarta
Duk abinda suka fada mata hawa takeyi ta zauna daram tayita fada
Abbansu baya raye bare ya ganarda ita gaskiyar rashin kyautawa da tunani akan abinda takeyi.
*******Shigowarsa gidan Kai tsaye Palo yashigo lokacin daga hajiyar sai Anty juwairiyyah da rumanah 'yar anty juwairiyyah suna zaune palon anty juwairiyyah na bubbude kayanta dasuka iso daga Dubai yau na tsadaddun laces da abayas datake saidawa sosai.
Ko kallonsa hajiya bataiba lokacinda ya zauna kusada ita Yana riqo hannunta cikeda kulawa yace"
Umma...
Zare hannunta tayi tana juyowa ta kallesa fuska ba walwala tace"
Meya hadaka da asibiti kake warin asibitin?
Tun asuba fa akace ka fita¿
Ina kaje?
Ajiyar zuciya yayi cikin Hana kansa Jin rashin Jin dadin zancenta sbd takasa daina saka Masa dokar duk Ina yaje da Inda zashi saiya fada Mata bayan Shiba yaro bane da girmansa take Masa irin hakan,
Amma Kuma uwace Babu yanda zaiyi da ita bakuma zai iyajin haushintaba sbd yanda take kaunarsa haka yake tsananin kaunarta shima Dan tafiye Masa komai a rayuwarsa.
Ahankali ya bude Baki zai fada Mata abinda yake faruwa saiya dakata sbd tabbas yasan atake zatace Bata yafe yakoma gurin babynba yabarta can asibitin Susan yanda zasuyi da ita.
Ajiyar zuciya yayi tareda sakin murmushin boye damuwarsa yace"
Dubiya naje wani asibiti a kubwa.
Kasa yarda hajiyan tayi tana kallon fuskarsa dake kokarin Tona asirinsa sbd Bai iya qaryaba baikuma taba yintabama.
Miqewa yayi ya wuce dakinsa yayi wanka ya shirya yakuma sulalewa ya fice gidan batareda sun saniba.
Har dare Bai dawoba sai guraren 10 yadawo ya shige ya kwanta.
Washe garima daqyar ya iya tsayawa yasha ruwan tea kawai ya Kuma ficewa zuwa asibiti.
Kwana biyu kowa gidan ya saka Masa Ido ganin duk yabi ya rikice baya wani cikin nutsuwa gashi sai boye boye yakeyi sbd harga Allah bazai iya barin babynba shima hakama mahaifiyarsa yasan bazata taba Bari su dauki 'yar ba Dan haka hankalinsa ya tashi sosai,
Yayi yawon bincike akan gidan marayu Amma Babu Inda yaji bayanin daya kwantar Masa da hankali Dan haka yasake shiga tsaka Mai wuya.
Ta Bangare Daya ya rikice ya haukace gurin Neman uwar babyn harya gaji Babu labari,
Komai yafara tsananta lalace Masa ne bayanda anty safiyyah ta ringa bin diddiqinsa tagano asibitin dayake zuwa kullum harma da babyn dayake jinya mai amfani da sunansa ABDULMAJEEDs.
Hankali tashe cikeda firgici da mamaki takawo labarin gida Inda suka dunguma sukaje suka ganarwa idonsu Kuma suka tabbatarda babyn dai ta ABDULMAJEED dince ta hanyar bayaninda nurse Tai musu shine mahaifin babyn.
Uwar babyn suka tambaya tace musu ta rasu gun haihuwa.
Dayake suma asibitin sun dade dafara gulmarsa akan kila baasan ya haifi yarinyarba shiyasa yakasa kawo 'yan uwansa su tayasa hidimar babyn.
Gida suka koma hankali tashe suka zayyanewa hajiya komai.
Kasa yarda tayi da Abdul dinta zaiyi abinda suke fada kula Mata da aikata Zina harma da haihuwar 'yar gaban fatiha.
Sunsan zaayi hakan Dan haka suka dauketa suka kwasa zuwa asibitin
Cikin saa kuwa suna zuwa suka taddasa rungumeda babyn an jikinsa cikin tsananin kulawa.
Sallamarsu ake tunanin Yi zuwa gobe dan haka yake Jin sanyi ta wani bangaren Kuma tashin hankalin yanda zaiyi da babyn.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[11/4, 11:05 AM] +234 813 979 4675: *_41_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Ahankali Haj umma ta qaraso tana kallon babyn hannunsa a Rikice tace"
MAJEED babyn waye wannan?
Da sauri ya dago Yana kallonta dasu anty juwairiyyah.
Miqawa nurse babyn yayi yana kallon hajiyan yace"
Umma muje gida Zan Miki bayani.
Kasa motsawa tayi sbd fargaba da tsoro tace"
Majeed bazan koma gidaba wlh saikamun bayanin Inda kasamo wannan babyn.
Mezan gani majeed?
Mezan ji?
Ta tabbata kenan fasiki ka Zama har kayi nisa haka¿
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun" zuciyarsa dake rawa tafara karantowa.
Cikin dacin kalaman mahaifiyar tasa ya dago ya kalleta Jin sunan fasiqi data kirasa dashi.
Zuciyarsa na daci ya bude Baki zaiyi magana anty juwairiyyah ta taresa da munanan kalamai tareda kiransa da sunayen mazinatai kala kala.
Kasa dago kansa yayi cikin tsananin tashin hankali da baqin ciki ya dakatar da Anty juwairiyyah da cewa"
Anty juwairiyyah me kika fada?
Sunayen mazinata fasikai kike kirana,
Idanma nine mahaifin babyn akwai yanda zakuyi ne da qaddarar Allah?...
Ba zato sukaji qarar saukan Marin da hajiya tayi sakar Masa tana kallonsa ciki tsananin bacin Rai da baqin ciki tace"
Wallahi wannan 'yar bazamu taba karbantaba idanma Kaine ubanta,
Idan Kuma wani gurin kasamota kayi gaggawar maida ita..
Kai koma Kaine ka haifeta bazaka karbetaba wuce muje gida.
Jajir idanuwansa sukayi sbd baqin ciki da damuwa,
Su Anty safiyyah kuwa ta Inda suke shiga bayanan suke fitaba take hankalin hajiya yaqarasa tashi hawan jinin datake fama dashi yayi sama take
Ba Shiri suka Jata zuwa gida har ABDULMAJEED din Wanda jikinsa yayi dukkanin sanyi.
Isarsu gida Bai qarar da komaiba sai sabon tashin hankali Dan kuwa bayanai ne daga Yan sanda sukazo anga Hadiza Kuma ta tabbatar musu da 'ya 'yarsace.
Kasa yarda da zancensu yayi saida aka kawo Hadiza wadda gabaki dayanta batada bambamci da mahaukaciya sbd yanayin shigarta da rashin lafiyarta.
Saida aka fara tambayarsa ya tabbatar musu da itace mahaifiyar babyn kafin aka sake tambayarta itama tace babynsa ce.
Ganin yanayinta na tabin hankali yasa aka sallameta ta tafiyarta dayake yan sandan sunga gurin samun kudi sai suka Kama MAJEED din akan yayiwa mahaukaciya fyade ta Haihu.
Take Yan sanda suka sauya zancen Kuma suka tabbatarda Hadiza ta tafiyarta sbd karma aci gaba da tambayarta tadawo daidai tafada wani zancen Bayan wannan.
Babban tashin hankali yashiga Yana son mahaifiyarsa kadai ta yarda dashi ta fahimcesa Amma tuni taji tana danasanin fifita sonsa akan sauran 'yayanta.
Kasa danne abinda takeji tayi zuciyarta take tafara Neman bugawa aka kwasheta zuwa asibiti.
Acan station kuwa ba Imani yan sandan suka rufesa tareda cike Masa laifin dabai aikataba.
Zafi zuciyarsa da kansa sukeyi kaman zasu fashe,
Wace irin masifaffiyar qaddara ce wannan?
Tayaya mahaifiyarsa da 'yan uwansa zasu yarda da zai iya Koda kallon wannan matar so ukuma bare iya wani abun da ita sbd tsananin qyanqyamin dayake dashi.
Bai taba kukaba tun girmansa Amma ayau baisan lokacinda wasu hawayen baqin ciki da qunci suka gangaro masaba.
A rufe ya kwana Saida yakuma wuni a rufen kafin alhj jamilu qanin Haj umma yazo yayi belinsa shima ransa amatuqar bace da abinda MAJEED din yayi.
Ko sauraronsa baiyiba yayi Masa diban albarka da maganganun dasuke kaman Yana Masa Baki.
A gidan ma saida ya zubda hawaye ga maganganu marasa Dadi da 'yan uwansa suka ringa jifansa dasu
Mahaifiyar tasa kuwa ko qaunar ganin batayi hakan ta ringa hawaye tana jujjuyar dakai batason ganinsa yatafi yabarta kawai.
Nauyi zuciyarsa tayi ta yanda baisan mezaiyiba,
Mahaifiyarsa ta tsanesa Bata son ko ganin inuwarsa,
Yan uwansa ma sun tsanesa,
Yan uwan mahaifinsa Dana mahaifiyarsa sai Allah wadai sukeyi dashi.
Kiransa akai daga asibiti akan yazo ya tafi da babysa.
Baida wani zabi bayan zuwa ya karbota sbd bazai iya barinta acanba ayanzu da kowa yagama alaqanta shine mahaifinta.
Koda ya karbota ya dade Yana tunanin Inda zai kaita sbd dagashi har ita bazasu taba karbuwa ba a gidansu.
Hakanan ya daure ya iso gidan da ita saidai tun kafin ya shiga ainihin gidan su Anty safiyyah suka tabbatar Masa bazai zauna da 'yar ba a gidan.
Zabi zaka dauka ko ka kaita gidan marayu kokuma kasan Inda zakaje ka raineta Dan bazai taba yiyuba ayi renon 'yar qaddaraba a gaban hajiya sbd baka damu da damuwa ko baqin cikinka ya kasheta.
Bai tsaya ya sauraresuba ya wuce ciki da 'yar a hannunsa rungume ya nufi dakinsa.
Cikin fada sosai da tsawa anty juwairiyyah tace"
Bakaji abinda safiyyah ta fada bane?
Ina zaka wuce ana magana?
Ka fice kakoma tun dare baimaba kakaita gidan marayu idanma bazasu karbaba ka maidawa mahaukaciyar uwarta idan taga dama ta Yar da ita...
Tsananin zafi da quncin da zuciyarsa me Masa yasa tafara bushewa a fusace yace"
Duk abinda zanyi da ita da Inda Zan kaita ba ruwan kowa bane matsalata ne tunda nine nakawota..
Idan sbd wannan 'yar alhakin aketa tada hankali to naji nine ubanta zai raineta daga Nan har girmanta Kuma Babu Wanda ya Isa ya hana hakan.....
Nima ban isaba Amma Kuma na Isa danace kabar gidan Nan da ita tunda gidan bana uban nata bane.
Kai yanzu MAJEED har kayi nisan da yannanka suna magana kana mayar masu Kai me 'ya?
To wlh wallhi wannan 'yar dai bazata zauna a gidan banba,
Banason ganinku daga Kai har ita ka tattara ku koma gidan marayun har Kai sbd kaima kazama marayan daga yau...
A Rikice ya kalli hajiyar idanuwansa na sauyawa
Muryarsa na rawa yace"
umma nabar gida?????
Ban Isa bane?
Ai kakai tunda kazama uba yanzu.
Innalillahi wainna ilaihrrjiun""
Umma........
Daga Masa hannuwa tayi tareda fashewa da kuka Mai ciwo da qunan zuciya tace"
Idan Ina ganinka zuciyata bugawa zatayi MAJEED Dan Allah ka tafi na daina ganinka da 'yar nan.
Kaci amanar tarbiya da tsananin kaunar dana fifitaka akan 'yan uwankw..
Maganganunta dukan zuciyarsa sukeyi suna yamutsa qwaqwalwarsa tareda zafafa kansa.
Daqyar ya daga qafafunsa zai matso gabanta ta Kuma fasa kuka tana ja da Baya.
Wani nauyi ne ya danne Masa zuciya ya juya ahankali ya shiga dakinsa ya tattaro kayan dazai buqata ya zubo a jaka ya fito.
Su Anty safiyyah na kallonsa da mamaki sosai ya fice gidan batareda yasake cewa komaiba.
Yana fita kuwa hajiya jikinta ya rikice Nan tafara numfashi daqyar
Hankali tashe aka kwasheta zuwa asibiti.
Baitaba sanin haka 'dacin baqin ciki yakeba sai yanzu,
Zafi,ciwo,radadi,nauyi da tiriri zuciyarsa keyi duk lokaci daya,
Gidan Alhaji jamilu ya nufa Amma cin zarafin dayayi Masa yafi Wanda akayo Masa daga gida Dan haka yana baro gidansa Kai tsaye hotel yanufa yakamata daki ya kwantar da babyn tareda komawa gefe ya zube Yana riqe kansa dake neman tarwatsewa.
Babban qunci da dacin zuciyarsa yanda mahaifiyarsa da Yan uwansa dasuke jininsa suka zabi aibatasa da kalmomi mafi muni tareda tsanarsa..
Shin idan da gaske shine qaddarar haihuwar babyn ta sama haka zasu gujesa kenan?
Me yayiwa wannan baiwar Allah dazata ruguza rayuwarsa haka?
Kansa dake Neman bugawa ya juyo ya kalli babyn dake bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali..
Wani irin tausayinta yaji tareda qaunarta,
Me tayiwa mahaifiyarta dazata jefar da ita haka ga mutuminda batasaniba,
Batasan halayyarsaba,
Shin idan ga wani mugun mutum ne ta jefarda 'yar Yaya takeson rayuwar wannan 'yar alhakin tayi.
Kansa da kirjinsa sun toshe baida tunani komai.
Alwala yayo yafito yayi sallar magriba da aka Kira.
Yana idarwa babyn ta farka ya taso ahankali ya tsaya akanta Yana kallon yanda take motsawa ahankali tana fidda harshe alaman yunwa.
Numfashi ya sauke a sanyaye kafin ya juya gurin jakar kayan madaranta da nurse ta koya Masa yanda zai hada.
A sanyaye ya hada mata madaran da ruwan roba kafin ya debo ruwan dumi ya saka madaran yayi dumi.
Ajewa yayi gefe kafin ya dauki babyn yafara Bata ta karba take tana zuqa ahankali.
Qura Mata fararen idanuwansa dasuka sauya yayi Yana Jin tausayin kansa da ita,
Meyasa iyayensu zasu zabi jefar dasu akan qaddara?
Meyasa iyayensu suka zabi rabuwa dasu akan abinda suma basune suka samarwa kansuba?
Uwa mace da akafi sani da qawa zucin 'danta Amma su nasu uwayen Mata ne suka fincikesu daga rayuwarsu suka 'yar batareda nazari ko tunanin halinda zasu shigaba.
Shi tasa uwar data fincikesa daga rayuwarsu ta Yar yanada girman dazai kula da kansa Amma ita wannan babyn me tasani.
Har tagama shan madaran tayi bacci bai saniba sbd nisan dayayi a tunani.
Har lokacin sallar ishai tayi Yana zaune rungume da babyn.
Sallar ishai yayi wadda Yana idarwa ya nema guri yazauna tareda rufe idanuwansa yanajin yanda kansa ke tsananin ciwo.
Babban saukin daya samu babyn bamai rigima bace Dan haka har safe batai Masa rigima ba sai Madara datakesha sosai Dan haka baiyi wani baccin safeba.
Garin na wayewa guraren qarfe goma Dole cikin ma'aikatan hotel din yasamu wata ta sauya Masa kayan babyn ta shirya Masa ita ya dauketa suka sake koma gidansu.
Wannan karon Yana Isa babban tsaro yasamu a gate akan kada abarsa ya Shiga gidan.
Kiran wayar hajiyar ya ringa Yi Amma Sam Bata dauka daga karshe aka kashe.
Numbern anty juwairiyyah yafara kira itama bata dauka.
Ta anty safiyyah yakoma Kira itama Bata dauka.
Anan ya kusan wuni da babyn cikin Rana ganin Zata wahala yasa yakoma hotel din.
Washe gari haka yakoma gidan Amma saiya samu labarin sun wuce Lagos gabaki dayansu gurin ganin likitan hajiya.
Tashi hankalinsa yayi Dan haka ya ringa Kiran wayar hajiyar Bata Shiga qarshe ya Kira anty juwairiyyah.
Kalaman data fada masa sune yaka saddaqar da duk wani sauran burinsa na zama cikin Yan uwansa da mahaifiyarsa.
Ta sanar dashi hajiya umma Bata kaunar jinsa ko ganinsa,
Idan yakuma zuwa ko kiranta Zata iya tsine Masa.
Wainnan kalaman sun girgiza duk wata jarumtarsa da karfin zuciyarsa,
Amma Kuma sun daskarar da zuciyarsa data tarwatse lokaci daya,
Tabbas zaiyi nesa da Inda Haj umma Zata gansa bare yazama sanadin mutuwarta da 'yan uwansa suke fada.
Yana barin gidan yakoma hotel ya tattara kayansa guri daya,
Yayi wani irin kukan baqin ciki da maraicin rashin mahaifi a duniya,
Yayi kukan rabuwa da uwa wadda yasan itama tana cikin quncin wannan hukuncin nata saidai Kuma bazai taba Zama sanadin ciwonta ba dakuma tsinuwar data ambata garesa.
gari na wayewa ya nufi Tasha yahau motar komawa Yola.
A motar tun agurin Lodi ya sanar masu mahaifiyar 'yarsa ta rasune zai koma gida gurin danginsa.
Da wannan ya kawarda kallon zargin da ake binsa dashi fa babyn.
Wasu sun yarda wasu Basu yardaba ahaka dai akai tafiyar Amma saida wata dattijuwa ta karban Masa babyn sbd ganin yanda yake fama da babyn.
##MAMUH#
0 comments:
Post a Comment