KASUWANCI NA
1
Official
By
AsmaBaffa
BISMILLAH
Alhmdllh fans Allah ya kara kawo mu sabon Novel dina KASUWANCI NA da fatan zaku bibiyeni muji yadda zai kasance,Fatana Allah yasa mu karu da juna,Allah yasa masa Albarka ya fadakar ya kuma nishadantar daku.ina matukar Godiya masoyana,masoya novels dina,masu sharhi musamman AsmaBaffa fans club,Taskar fiddausi sodangi,da kuma House of Hausa Novels ina miko dubun gaisuwa ta gareku na gode da Sharhi.
Da fatan zaku ci gaba da Sharhi a kai Kai sabo da shine yake guiding writer ta rubuta muku me dadi da ma'ana,idan ba Sharhi baya tafiya dai dai,Dan Allah a dinga Sharhi fans ana nishadi musamman yan gp na.
Akwai gps da dama da basa Sharhi ko tnx baza suyi ma ba,zaka ta musu posting shuru,sai ranar da ba ayi posting ba sai a fara neman novel ci gaba.duk gp din da basa cewa ko Hi zan daina musu posting wlh,da nayi daya biyu naji duf to shike nan sai suji duf nima๐คฃ๐คฃ
Wannan page na farko na Sadaukar dashi gareki sweet frnd FLOWER.
Kudin cinikin awarata nake irgawa duk da ba kudin arziki bane amma dukkansu daga yan goma sai yan biyar sai ko ashirin,kanwata na shiga kwalawa kira MEENAT wai baza ki fito ba sai na shigo na mareki,Maganar AMMA naji tana daga gefena a kwance saman yar tabarma tace Haba MUFEEDA ta wannan wacce masifa ce haka dan Allah ki dinga dagawa yaran nan kafa kannenki ne fa,Amma kina dai jin tun dazu nake jiransu su fito su tafi Islamiyya amma sai nauyi sukeyi kuma sun San cewar anjima zan soya Awara,gashi gobe zasu zo suna takura mana a basu kudin Break, to ai sai bisu a hankali dan Allah kinga ni ba lafiya ce dani ba kece komai nasu kece uwarsu kece Ubansu Mufeeda kece komai dinmu,Zuciyata ce tayi rauni nace to Amma ba komai na Dena kiyi hakuri Allah zai baki lafiya kinji,ga kudin nan Amman mu bari na gyara gidan na daura mana tuwo naga muna da ragowar garin masara,Murmushi Amma tayi tare da kallona tace Mufeeda Allah ya miki albarka Allah ya baku miji na gari,ya baku yara su rama muku abinda kukayi mana na alkhairi,Mufeeda yau shekarar babanku Sha uku da bacewa,har yau ina Sa ran watarana zai bayyana da Zanfi kowa murna ya ganku Ku uku kun Zama yan mata gaku kyawawan gaske kamar indiyawa,musamman ke Mufeeda kunfi kama da Shuwa sosai mahaifinku kika biyo domin shine fari kamar balarabe haka yake har kin fishi Hasken fata ma,su kuma su Meenat sune masu kalata wato su ba farare ba su kuma ba wanda zai kira su bakake duk gaku Allah ya bani Ku kyawawa farare daku amma duk kyan nan sabo da talauci ko Sallama ban taba ji ance ana sanku ba,wanda na tabbata da masu kudi ne komai muni auruwa sukeyi,musamman ke Mufeeda kin kai har 16yrs amma nafi so na aurar dake tunda ba makaranta kike zuwa ba,Baki na turo gaba tare da sakin shagwaba ina shure shure kamar yarinya ina kukan sangarta Allah Nidai Amma bana son aure kuma ma nawa nake,hmmm Mufeena Mufee tawa ai gashi nan kin fara girma har da Irgan dangi,Ammah mene Irgan dangi? tace gasu nan a kirjinki Kin fara Nono Mufeeda akwai maganar da za muyi anjima idan yaran nan sunyi bacci,kunya ce ta kamani nace to Ammah Allah ya kaimu bari na gama aikin ko kina da bukatar shiga bayi na taimaka miki? Ae rikeni muje Mufeedata Allah ya miki albarka,
kama Ammah nayi da kyar tana rike da sandar karfe wacce a asibiti aka bata ita na kaita har bayi ta tsuguna tare da Dafe jikin bango,sai na fito bayan ta gama abinda zatayi ta kwala min kira na koma nace Ammah ko na goyaki? Dariya tayi tare da cewa na gode Yata baki ji me Doctor yace ba?na dan dinga takawa,murmushi nayi wanda yasa hakorana kanana farare suka bayyana,dimple dina ya lotsa riketa nayi muka fito tare,sai Lokacin kannena MEENAT da MA'EESHAH suka fito cikin shirin makarantar Islamiyya,na kallesu cikin tsafta kayansu yasha guga,sun bani sha'awa naji inama nima haka nake zuwa kullum amma ina bazan samu dama ba,amma Alhmdllh tunda kannena suna zuwa ba matsala.Amma ce ta kalleni cike da tausayawa tace Mufeedata? Da sauri na dawo daga tunanin dana lula na kakalo Murmushin dole nace Ammah ki huta bari na gama aikin naje na siyo kayan alewar madara,kinga gobe kuma da safe Kosai yana jira shima,amma ni naga awarar tafi riba ma,Ammah tace Mufeeda wannan satinfa naji zuku yi Allurar polio vaccine da kukewa yara,Mufeeda tace wlh Ammah ba sauki abin ni haushi na ma gidan masu kudi kantama kantama na GRA Ammah ayi ta wulakanta mu da kyar mukeyi muna Shan wahala,wani gidan ma kafin ka shiga tashin hankali ne ko ina securities ne,aikina naci gaba da yi muna hira da Ammah mahaifiyarmu,saida na gyara gidan tas na kunna turaren Wutar kamshi duk da gidan ba wani me kyau bane amma ita tsafta bata buya,Allah ya haliccemu da tsananin Tsafta wanda duk Bala'in mutum bazai ce gidanmu akwai digon wani abu na kazanta ba haka muke gaba dayanmu,miyar Kubewa busashiya na kada,na tuka tuwon masara na kwashe cikin wata tsohuwar Cooler dunmu,nayi wanke wanke da wanka na shirya cikin kayan gwanjo na Riga blue me layi layi na fari,tare da skert shima ruwan goro,farar Powder na shafa da Vaseline a lebena,Hijab me hannu nasa wanda ya wuce gwiwata nace Ammah bari na siyo kayan nan nazo na fara soya Awarar dare kinga magriba ta gabato,Fadada murmushinta Ammah tayi tace a dawo lfy Allah kiyaye hanya.
Ameen nace tare da fita waje ina dan wasa da kudin dake hannuna cikin unguwarmu layinmu na bari nayi tafiya me Nisan gaske Allah yasa ma ba rana sai da na gaji sosai kafin na karasa wata yar kasuwa karama da ake saida kayan abinci da fruits etc, inda na saba siyen waken kosai da sauran kayan Sana'a ta na karasa da fara'a dukkanmu munyi sabo da juna sabo da yau da kullum,kudin na mika ina bi ko wanne layi duk na hada abinda nake bukata kaf aka hado min a wani katon buhun bacco na fito da kyar nake dagawa ina nishi haka nake tafiya a hankali, wani dattijo ne yace yarinya kawo a daura miki a kai ai zaifi ko? Murmushi nayi masa ya amsa ya daura min na masa godiya naci gaba da tafiyata da kyar,sai da nayi nisa na shiga wani layi wanda manyan gidajen masu kudi ne na gani na fada,GRA ce ta masu kudi nabi ta ciki sabo da kullum ta hanyar nake wucewa ko sabo da nasha kallon hadaddun gidaje tare da Lambu masu kayatarwa duk kuwa da cewa na saba shiga sabo da rigakafin polio na nake aikin dole muna neman Izni mu shiga sabo da tare da masu Unguwanni muke yin rigakafin dole su yarda a shiga ko Police su kama me gidan haka aikin yake.
Wasu motocine a kalla sun kai guda takwas a jere dankara dankara ban taba ganin irinsu ba sai yau da suka shararo da uban gudu kamar zasu tashi sama cikin layin,dai dai wani gida suka Parker wanda gidan yafi kowanne kyau a layin da gudu na matsa tare da rakubewa a jikin ginin gidan ina kallon ikon Allah,
da sauri naga sojoji sun fito daga sauran motocin tare da zagaye wata uwar shahararriyar mota me kyau da tsada na fitar hankali,wani dattijo ne ya fito fari kar dashi yana sheki da Alama kudi sun ratsashi a matukar hasale ya fito daya bangaren ma wani wani mashahurin matashi ne ya fito da sauri a matukar hasale cike da isa hade da Izza Saurayin kamar balarabe ko Bature haka yake duk Haske da kyau na da ake fada sai naga wannan ya wuce nawa ya zartani a komai nan take na raina kaina musamman yanda na kalli shigata babu maraba da Almajira mara gata.
Saurayin bazai wuce 35years ba ya kai karshe a haduwa gashinsa abin kallo kansa style din askinsa abin kallo ne abin birgewa da sha'awa,idonsa ya bude,ban San sanda nace wow a raina ba idonsa kamar madara yana wani lumshewa gasu Dara Dara,girarsa har kamar zata hade,ga wani dan saje da gemu masu matukar kyau da suka kawata fuskarsa,hancinsa me matukar kyau kuma baiyi tsini da yawa ba,dan bakinsa wow masha Allah ga wasu pink lips duk da cewa nima bakina kamar cokali bazai shiga ciki ba gashi lips dina jajir dasu amma sai naga wannan kam nasa sunfi nawa komai,kuma sai na tashi me duhu a kansa ko dan shi Hutu da Naira sun ratsashi ne oho, Kana nan kayane a jikinsa wandon pencil Jean brown color,rigarsa fara tas da top Brown ya daura sama takalminsa fari half cover flat shoe,shi ba gajere ba shi ba dogo da yawa ba,haka ba ramamme ba kuma bame kiba ba,kai masha'Allah da a mafarki na ganshi ba shakka Aljani zance.
Dattijon cikin farar shadda kar cike da Fada yake magana da alama da Saurayin yake,AAYAN will u hear me out pls,da sauri Saurayin ya bata rai cike da fushi yana shagwaba kamar dan yaro cikin muryarsa da ta girgiza ni sabo da dadinta yace pls Abbi I knew it just leave me alone For God sake,Hajja she is ur mother not mine so Abbi kaine ya dace kabi Umarninta ba ni ba,taya zata dinga takura min ni kadai ne jikanta gasu nan da yawa maza da mata,ko kawai dan ni bani da Mahaifiya bata raye,sannan mahaifina bashi da lafiya bakwa kaunata shi yasa ni kadai ake ma haka yanzu ina Abuja kace dole sai na dawo Kano da Zama kusa da Ku,ban taba wani rayuwa a kano ba ka sani sabo da kana matsayin mahaifina nake maka biyayya,sabo da gudun saba maka na bar muku gidanku,bana amfani da sisin kudinka,Allah ya bani nawa Abbi har na fika ma maybe kudin,But why me,why are u doing this to me,kowa a Family kaf maza da mata nine ba a so me nayi musu?idan sabo da Umma ne bata raye sai na huta,Abbi ban shirya aure ba kunsa nayi ba muguntar da ba ayi min ba,haka mun rabu,kun kara aura min wata itama mun rabu sabo da matsalar dake damuna na rashin lafiyar haihuwa Abbi kun San bani da lfy bazan iya Rayuwar aure da mace ba akan me zaku ce na kara auro wata so kuke mata su kasheni bazan iya musu amfanin komai ba,dalilin bacin rannan da nake Sha kasan yanzu Hawan jini gareni me karfin gaske ko wanne lokaci zan iya rasa raina,sannan kasan Ina da diabetes dalilin Hawan jini yasa ya kamani tawakali da addua nakeyi,Abbi why not bakwa tausaya min,bakwa tausayin rayuwata tun tasowata a wahala na tashi a duniya,wannan yasa na tsani mata wlh Bana kaunar duk wata budurwa komai kyau da hankalinta,dalilin haka bana Hulda da kowa family da frnds etc ni kadai nake rayuwata sabo da bakin ciki da halin da nake ciki shi yasa nayi nesa da kowa,gwiwoyinsa ya dire a kasa hawaye na kwarara a idonsa kamar ruwa tare da rike kafar dattijon yace Abbi ka fadawa Hajja zan zauna daku amma pls kar ayi min aure again ko me kuke so wlh zanyi amma yanzu banda aure,Abbi ka tuna kusan mutuwa nayi yanda mata suka ci min mutunci.
Kallonsa Dattijon yayi tare da cewa tashi Aayan,zan yi shawara da yan uwana, muyi deal duk abinda mukace zakayi ka yarda? Ba tare da yayi tunanin komai ba Yace ae Abbi na yarda indai bazanyi aure ba shike nan,Abbi yace an gama ko ka samu Lfy kana haihuwa sai na yarda zakayi aure ka tabbatar?Kuma ko kaga wacce kake so baza ka aureta ba har sai in mune muka yarda?cike da murna yana murmushi ya daga kai alamar yes ya Amince,Abbi yace Good for u,kar kaga bani na haifeka ba kace zaka min butulci zan iya yi maka abinda baka tunani,ka dinga tunawa da halina kasanni sarai zan iya yi maka ko mene ne ba ruwana,Shi dai Bayan murna yake yace ya yarda,Tashi muje daga yau ka dawo Kano gida daya zamu zauna sai dai jefi jefi kaje Abuja harkokin business dinka shima sai idan da yardata idan kuma kaki zan iya haram tama Business dinka gaba daya kasan nasan komai akan hanyoyin da zan lalata duk dukiyar daka mallaka,
Aayan ne yayi murmushi tare da cewa Abbi matukar baza kuyi min aure na zauna da mace ba zan iya mallaka muku komai nawa,na tsani mace a duniya ni bana son Zama dasu wlh ko yan uwana banso,kallon tsana Abbi yayiwa Aayan tare da cewa dan kawai baka da lafiya ne Man amma wa yaki mata?ai mata sune jin dadin duniya,kaga duk son kudina?Saurayin ya daga kai yana murmushin takaici,Abbi yace to duk kudin da nake nema sabo da mata nake nemansu,mata mutanenmu in ba su mene amfanin kudi.
Kai Aayan baka da amfani a duniya fa da kai da gawa daya kuke Banga Amfaninka ba sam,to kai baka haihuwa,baka iya Yiwa mace komai me kakeyi kake wahalar da kanka wajen neman kudi,gaka a haka kamar Namiji Amma na tabbata in dai ba mune muka zaba maka mace ba irin almajira ko talakawa sune suke neman kudi sune yan wahala sune wahalallu wanda basu san kansu ba,basu san me duniya ke ciki ba,basu da wani amfani da irinsu ya dace a nema a aura maka sune watakil ka samu me son kudi tayi kasuwanci da kai ta samu kudi ta zauna da kai da hakuri.
Aayan yaji matukar zafin kalaman Abbi wanda gaba daya ji yayi kamar ya mutu Sabo da bacin rai,haka ya hakura ya danne bakin cikinsa Amma idonsa ya kada yayi jajir,sai da Abbi ya gama gasa masa bakaken maganganu masu zafi sannan yace tashi muje ciki kasa a kawo ma motocinka kasan ko aron nawa ko na gida babu me baka kamar yanda kace kowa yayi amfani da kudinsa,Aayan yace ai duk new nayi Order an siyar da wancen saban yayi za a kawo min gobe,dariyar mugunta Abbi yayi tare da cewa kana kokari fa wlh ni da kai da gawa haka nake kallonka baka da amfani a duniya me zaka amfanawa wani?ko mace baka amfana mata komai ba sai wa? Bakin ciki ya tokare zuciyar Saurayin yana tsaye a gate har Abbi ya bawa Sojojin da suke can gefe dasu Umarnin su shigo da motocin gida,nan suka bar Aayan wanda ya dafe saitin zuciyarsa da hannunsa,har suka shige da motocin gidan,suna rufe gate din ya fadi a wajen ya sankame kamar ya mutu,gashi unguwar shuru ba kowa bare a taimaka masa.
Ni da nake Rabe ina jin komai da Sauri na jefar da kayan dake kaina nayi kan wannan Saurayi cike da tausayawa,tunani na sumewa yayi,na rasa ya zanyi na tasheshi robar ruwa dake hannunsa na Eva na fisgo da Sauri hannuna na rawa na bude tare da kwara masa a fuska Amma shuru bai tashi ba,hannayena biyu na daura saman kirjinsa ina dannawa kamar yanda nake gani likitoci nayi,yi kawai nakeyi ba ji ba gani danna kirjinsa nakeyi sosai ina nishi,a rude na kara kwara masa ragowar ruwan na sunkuya a kansa kamar zan shige masa ciki,kamshin turarensa yasa kamar na sume Sabo da dadi,fatarsa laushi kamar auduga lumis,wukil naga ya bude ido mun hada ido dashi kafin na kifta ido naji an sharara min uban Mari sai da na daina gani na wasu yan lokuta,kafin na dawo hayyacina yasa kafa ya harbar dani da mugun karfin da sai da nayi uwar Sufa na tuntsira naci ta ka na kife can gefe yaraf,nan take lebena ya fashe fuska ta ta kumbura,sabo da rashin Imani bai kyaleni ba takowa yayi har inda nake ya kara Sa kafa yayi ball dani sai da kaina ya bugu da wata yar bishiya,kafa yasa ya take hannuna dake yashe kasa ya murza,idonsa yayi ja da hannu daya ya damki wuyana ya shake tare da rabani da kasa ina kakari,Mari ya shiga yarfa min ban san iyakacinsu ba sannan ya jefar dani kasa kamar wani kayan wanki,Kuka me karfi na saki duk dauriyata ban san inda kaina yake ba,tunani na mahaukacine dama ashe,ina ta kuka a wajen Fuskata ta kumbura sosai jikina duk wani wajen ya farfashe Sabo da ball da ya dinga yi dani,tsorinsa ya shigeni ina nan wajen har ya shige cikin gidan da motoci suka shiga,Allah ne ya taimakeni wani dattijon kirki yazo wucewa a motarsa yace yarinya motace ta bigeki?Ban san me zance ba kawai sai nace kare ne ya biyoni shine na dinga faduwa,mutumin bai yarda ba Amma ya Kira Driver dinsa yace ka dakko mota ka kai yarinyar nan asibitina ka samu Sajeeda tayi mata dressing ka maidata gidansu kayi Sauri dare ya fara,godiya nayi masa ina kwance a kasa ina tunanin zalincin da Saurayin nan ya gwada min tare da rashin Imani daga taimako sai naci Dukan tsiya,
haushinsa naji sosai a raina ga tsoronsa da ya dasu a Cikin raina bana fatan sake ko kallonsa Sabo da tsoronsa nake ji yanzu.
Ina tunani a kwance Dattijon Driver ya karaso tare da bude min mota da kyar na iya shiga motar,Driver ya saka min kayana a Cikin motar wanda na siyo a kasuwa,wani hadadden asibitin kudi ya kaini nan take akayi min komai da ya dace aka bani magunguna da Alama asibitin dattijon mutumin ne da ya Bada motarsa a kaini gida,Driver na gwadawa gidanmu ya kaini har kofar gida sannan ya miko min dubu biyu yace na sha Maltina inji Alhaji me gidansa,da kyar na yarda na karba,shima sai da Driver ya nuna baiji dadi ba sannan na karba tare da zuba godiya na dauki kayana na shige gidanmu shi kuma yaja mota ya tafi,ina shiga gida Kannena Meenat da Ma'eeshah har sun yanka awarar suna jirana da gudu suka taso suna Sister Mufee me ya sameki?lfy?hatsari kikayi ko motace ta kadeki,kinga yanda kika koma kuwa,Da Sauri Ammah ta fito da Rarrafe kamar zata kifa Sabo da rudewa tana Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un shine Abinda Ammah ke furtawa tana Hawaye tare da cewa me ya samu Mufeedata?Me ya samu katangarmu? Kuka na fashe dashi me karfi tare da Rungume Ammah ina cewa ba komai Ammah a wani layi ne kare ya biyoni na dinga gudu na fada cikin kwalabati da kyar wani ya taimakeni ya kaini asibitinsa kinga an bani magani harda kudi dubu biyu na shan Madara da Maltina,Ammah tace wannan waye me kirki haka?Wlh Ammah wani ne Doctor ne Babban mutum ya sa Driver dinsa,to ku dai kiyaye da mazan zamani a tsare mutunci,Alhmdllh tunda komai yazo da sauki,Meenat ki dafa mata ruwan zafi ta gasa jikinta taci abinci tasha maganin ta kwanta,ke Ma'eeshah jeki kofar gida ki fara soya awarar kafin yan siya su fara taruwa, mikewa mukayi tare da aikata abinda Ammah ta ce.
Bayan nayi wanka na gasa jikina Mai na shafa sannan na Sa doguwar riga mara nauyi itama yar gwanjo ce,abinci na dauko tuwon da nayi dazu naci na koshi domin ni cuta bata hanani cin abinci,komai rashin lafiya sai naci na koshi nayi luf,bayan naci Ammah ta dinga ballo min maganin tana bani ina sha har na gama,tace kawo na shafawa na shafa miki,Ammah zan shafa ki barshi kinga ke ba lafiya gareki ba, bayan na shafa jikin Ammah na koma na kwanta ina tunanin Saurayin dazu tare da maganganun da naji sunyi nake ta faman tunani shi kuwa mene tarihinsa me mutanen nan suke nema dashi ne haka,tunowa da nayi irin rashin Imaninsa nan take na firgita tsoronsa ya kara shigata na kankame Ammah har bacci ya kwashe ni,. Washe gari da asuba da kyar na tashi na gabatar da Sallah tare da Azkhar kamar yanda muka saba gaba dayanmu,Bayan gari yayi haske naje da Sauri na hada wutar itace na daura ruwan zafi yana tafasa na dama koko sannan na kafa daya kaskon gefe daban na fara suyar kosan siyarwa ta,ana sallama ana siya sai kuma ruwan zafi ya tafasa na kwalawa su Ma'eeshah kira suzo suyi wanka su wuce schl,da Sauri sukayi wanka suka shirya tsab cikin Uniform dinsu wanda yasha wanki da guga,Kokon dana dama musu suka eba tare da kosan suka ci suka koshi sannan suka kaiwa Ammah nata itama,Nima ina aikin Suya kosan siyarwa ta ina shan koko da kosai na ,Sister ya jikin naki gashi kumburin ya baje,murmushi nayi tare da cewa Alhmdllh kuje kar kuyi late ayi karatu da yawa banda wasa,bani da burin da ya wuce naga kunyi karatu sisters ku dage cikinku mu samu lauya da Doctor dariya suka dingayi Ammah ma tana tayasu cike da tausayawa Mufeeda,kudin Break na mika musu nace gashi yau ba ashirin za a baku ba Hamsin Hamsim zan baku kuci me dadi,murna suka dinga yi suna tsallen murna tare da godiya,Nace kuje mana Gashi karbi Meenat kece babba kuyo mana Cefane muyi miyar egusi da tuwon shinkafa ki taho da nama na dari Uku muma muci dadi ko Ammah? Murmushin farin ciki Ammah ta saki tare da kallona tace Allah ya muku albarka dai yaran nan,
bayan sun tafi na gama siyar da kosai na ya kare kaf ,ina ta faman murna na lallaba jikina na gyara gidan fes na tattaro kayanmu har na Ammah da kannena na wanke su fes na shanya,Ammah wacce ta rarrafo ta zauna saman tabarma tace Mufeeda me za a dafawa yan makarantar ne yau? Na gaji taliya zan dafa da mai da yaji kafin dare sai muyi tuwon,eh hakan ma yayi ai tunda muna samun na sawa a bakin Salati ba kamar lokacin baya ba,tashi ki kokarta ki gama ke ma ki kwanta ki huta idan sun dawo yau ba Islamiyya sai suyi girkin daren,amsawa nayi da to na mike nayi abinda ta Umarceni,na hada mata ruwa na kamata har Nayi tayi wanka fes na koma na riko ta muka dawo naa tayata shiryawa tsaf muna hira.
ina gamawa na hada yaji me dadi yasha hadi na soya manja,na gyar dan kitchen dinmu wanda yake na karfen langa langa ne,Ammah na zubawa na kawo mata tare da ruwa,taimaka mata nayi ta zauna nima nasa hannu muka ci muka koshi muna Bada dunkulen Maggi star,Sallah muka gabatar ta Azahar,sai ko mukaji Sallamar Yan makaranta su Meenat,da gudu suka shigo suna sallama suka rungumeni,Ido na waro mene hakan? Sis wlh wani ne yace yana son Ma'eeshah mu kuwa muka zabgo da gudu,ke kin ganshi wlh in banda wari ba abinda yakeyi wai yanzu Ammah duniya ta lalace me kudi bazai Hulda da talaka ba komai kyanka indai ku talakawa ne babu me kulaka sai talaka dan uwanka,Ammah tace ai duniya haka ta koma idan da gate a gidanku to me mota ne zaizo idan babu kuwa sai dai dan uwanka talaka,Yanzu kalli irin kyawu da Allah ya zuba muku Amma babu me zuwa wajenku talakan ma ya gagara sabo da talakan ma gudun talakawa yake Allah kayi mana magani,dan baki na na turo Ammah ke komai kice aure wai shekarunmu nawa,dan gidanku gata nake nema muku yanzu ko idan da kunyi aure ai kuna da yancinku ko ba komai sai kiga kun huta shine burina,Ammah wa zai kula dake to aini aure bai taso ba a wajena Ammah wlh Bazan iya aure na barki a haka ba ko da kuwa zan dawwama ba aure ne a duniya,ki daina zancensa indai kina so hankalina ya kwanta,Maeeshah tace Sis manya bari muyi girkinmu,harararsu nayi nace kuje dai ku cire Uniform kuci abinci kuyi sallah ku huta sai kuzo ku fara aikin,ni yanzu kun san kasuwa zanje siyo kayan da nake siyarwa citta,kaninfari,barkono,wake,kanwa,Sabulu,omo,maggi kala kala,har su Aya duk siyarwa nakeyi duk wasu kana nan Abu na amfaninmu kayan girki ina siyarwa a gidanmu,haka ina saida su Aya,ridi,kantu,alewar Madara,albishir etc su Ma'eeshah nake sarowa suna Tafiya min dasu makaranta su siyar min,ina kosai na siyarwa,da rana na siyar da su Zobo kunun zaki da dare kuma nayi Awara,ina kitso da zanen lalle sosai kudi idan sunzo zanyi na karbi kudina,sannan ina cikin masu polio rigakafi,duk wani neman kudi na Sana'a kanana na gida ina yi,kusan komai ma siyarwa nakeyi,kullum bani da lokaci bana zama sam sai neman kudi dashi muke ci muke sha,muke Sutura tare da makaranta,
biyawa Ammah kudin magani,yanzu kasuwanci a duniya shine buri na wanda har ya kai ga dasa min matsiyaci son kudi tare da tattali,iya lissafi da planning,sabo da yawan Hulda da mutane yasa na kara gogewa na waye sosai,akan kudi ba mutunci ko bashi ya shiga tsakanina da mutum akan dan Kasuwanci na to fa zan iya rufe ido dole a bani ma,kamar zanyi sata haka nake matukar neman kudi.
Yau Monday Su Meenat suna schl na gama komai na fita naje wajen saro kayan Yara na sha,ina siyowa kala kala har su tuwon madara na wuce schl na kaiwa su Ma'eeshah domin su siyar,ina zuwa na hango Malam ya sa Ma'eeshah kamun kunne ya hanata ko shiga aji wai sun makara.
Ina matukar Jaje gareku fans da raguwar shekaru da muka samu domin ba karuwa shekarunmu suka yi ba raguwar suka yi,ana ta happy new year a daina addua ya dace muyi Allah yasa mun shigeta a Sa'a tazo lfy ta wuce lfy,Allah yasa ta Zama shekara me amfani a Rayuwar mu,ta zame mana farin ciki da samun ci gaba a cikinta,Allah ka kara mana lfy da Nisan kwana me amfani,Allah ka kara mana imani,Allah yasa muyi karshe me kyau idan tamu tazo,Allah ya azurtamu da mutuwar shahada,Allah ya rufa mana asiri duniya da lahira Ameen.
AsmaBaffa
[1/1, 10:20 PM] Asmabaffa: ๐๐๐๐
๐๐๐๐
KASUWANCI NA
2-5
Official
By
AsmaBaffa
Wannan page naki ne HUMAIRA Allah ya bar kauna.
Wajen malamin naje da kyar na rokeshi ya kyaleta yace tayi Sauri ta karbi sakon ta shiga aji, nima ina mikata mata na kama hanya sai gida,washe gari kuwa da sassafe na shirya na barwa su Ma'eeshah suyar kosai da Komai nayi shirin Tafiya rigakafin Polio dama indai ina rigakafin nan to dole Meenat ce zata zauna tayi dukkan abin da nake siyarwa har na gama Polio sannan taci gaba da zuwa,Sabo da Ammah bata yarda da talla ba shi yasa Sam bama fita talla a gida muke sana'armu, Ma'eesha kadai ke zuwa yanzu kafin na gama Vaccine.
Inda muke haduwa da ma'aikatan unguwar da mukeyi naje na samesu cikin Napep na sauka cike da fara'a da murna muka gaisa da juna,sannan na dauki akwatin da kwalaben Allurar suke ciki ga kuma supervisor dinmu da sauransu,sabo da box carrier ce ni ba a biyanmu da yawa dubu hudu da dari biyar muke dauka idan an gama,bani da ilmin da za bani Babban matsayi,haka mune da wahala mune muke daukan kudi kadan,a kafa muke Tafiya muna shiga gidaje ana house marking,sai 2pm muka tashi,washe gari ma bangaren unguwan da mukaje daban,a kwana na Uku kuwa da muka fara GRA din nan da na taba ganin Saurayi Aayan ya zaneni yau gidajensu zamu shiga aikin Vaccine duk da cewar ban taba shiga gidan ba,amma bana fatan shigarsa,ina ji ina gani muka zo jikin gate dinsu,
takadda aka rubuta sannan akayi knocking,Sojoji sunfi biyar ne suka fito kamar zasu masgemu,sai da aka basu takardar cewar yan Polio ne suka zo ga me unguwa a tsaye kuma dole sai an digawa yaro dan kasa da 5years,takardar suka karba sannan suka koma ciki zasu nunawa me gidansu,tunda suka shiga muna tsaye a wajen gate har sai da suka kwashe fin hour guda sannan suka fito sukace ance mu shiga,ma'aikatan sai murna suke zasu gano haduwar gidan,ni kam cikina ya duri ruwa bana fatan shiga Amma ba yanda zanyi haka na fara binsu kamar kwai ya fashe min a ciki sanye nake da red hijab dina me hannu har kasa duk da cewa nayi kyau Amma sam na raina kaina,
Muna shiga muka firgita domin ma'aikata da Securities ne ko ina,gidan ko ina kamshi ke ratsowa yana sheki,ga wasu motoci sunfi ashirin a gidan lafiyayyu,har round ne a gida kamar wani Babban titi tsakiyar youturn din ruwa ke tsiri sama yana shararowa a kasa kuma yana komawa kasan yana fesowa,a film ake ganin irin wannan gida jen,can gefe ga wasu sweeming pool har kala biyu,ko ina flowers ne a gidan,duniya guda ce a gidan domin wani part din ma ya dace ka hau mota sannan ka Isa in kuwa ba haka ba zaka gaji,wani soja ke mana jagora muna binsa a baya har muka zo wani garden ba abinda babu a garden din nan domin har da filin ball da Sauran wasanni iri iri,kida ne na wakokin Naija ke tashi har tsakiyar kai a manyan speakers,yan mata su Uku kyawawa yan gayu ne sanye cikin English wears Wando short da yar vest suna ta faman taka rawa ,hannunsu rike da kantama kantaman wayoyi,gefe wasu Yara ne sunkai su hudu mace daya da Maza su Uku sun sha kyau cikin kana nan kaya yan yayi suna ta faman buga ball, abin mamaki ko kallon inda muke basuyi ba kamar ma basu san mutane sun wuce ba, haka muka ci gaba da Tafiya muna yin gaba kadan sai ga wasu Maza zaratan samari suma hadaddun gaske baza su wuce 29 yrs ba su uku suna zaune a wasu kujeru masu malafa a sama game kawai suke bugawa suna dariya,ko wanne yasha kyau cikin kana nan kaya kamar a England,kaina nidai yana kasa Amma suma samarin inda muke ma basu kalla ba balle musa rai za a kula mu,tafiya dai muke muna bin Soja can wani wawakeken fili ne fetal yasha tsari da haduwa carpet dan gaske ne a kasan wajen da wasu manyan pillows ko ina yasha flowers ga wasu grass carpet wata mashahuriyar Dattijuwa tsohuwa tukuf muka hango kwance tayi kwanciyar Isa kamar sarauniya fatarta lumis fara kar duk da cewa ta tsufa Amma akwai hutu kayan marmari sun ratsata.
Mu matan da muka shigo dama mu Uku ne,da hannu tayiwa Soja Umarni nan muka ga yace gasu nan yayi gaba abinsa,har kasa na durkusa na gaisheta cike da girmamawa,su kuwa sauran matan cewa sukayi ai ma'aikata ne wlh baza su durkusa ba duk wulakanci da akayi musu ba wanda ya musu ko sannu bare kallon arziki,gata ita wannan ta tsufa ma Amma bata saduda da duniya ba har wani jin dadi take.
Kallonmu tayi tsohuwar ko amsa gaisuwata bata yi ba tana yatsina fuska tana kebe baki tare nuna Isa ta fara magana kuje dan Allah kun tsaya min a kai wari yana hawa min kai,da mamaki muke kallon ikon Allah,can ta jawo waya ta danna kira tana jan tsaki,sai ga wata da Alama yar aiki ce harda Uniform dinta dauke ta fito da ruwan roba tare da wani liquid soap me kamshi tace kuzo muje ku wanke hannunku sai a diga musu polio,Tsohuwar nan cike da izza tace wlh badan Hukuma da suke hadawa da ita ba baza a digawa jikokina ba sam,kazanta abinda ana kaisu asibiti ayi musu me kyau ko kasar wajene ma sai suje a diga musu Amma a dinga turo mana kazamai gidaje jasu can kuje,ina jin haka na daga kaina ina kallon sararin samaniya tare da kallon tsayi da girman building din nasu kamar baza a mutu ba katanga ma tayi tsiri sararin samaniya kai kace Mala'ikan daukan rai bazai iya tsallakawa ba,a raina nace to yaje har fadar shugaban kasa ma ya dauke Yar Adua,yau Ina sani Abacha?
Ina wannan tunani sai ga wasu dattijan Maza farare suma su Uku sun fito harda Abbi wanda na taba gani zama sukayi kusa da tsohuwar suna magana,lokacin mu kuma an jamu part din yan aiki nan aka dinga dirje mana hannu sannan suka fito damu, wajen yaran dake Garden tare da yan matan nan masu rawa da Wando 3qtr muka koma,nan fa da kyar aka jawo mana yaran ana cewa Hajja ce tace ayi musu suka bude bakin su tas dasu cikin taka tsantsan na diga musu yanda akeyi sannan nace to Alhmdllh mun gama mun gode,me rubutu ta cike talley sheet din,muna jiranta tana rubutu yan matan nan dake rawa dauke da cup a hannu suna shan lemo suna rawa suna bige mu Amma ko kallon mu basayi bare mu Sa ran ko Sorry zasu ce,gefe dasu muka matsa,wata ce ta fito cikin shiga ta alfarma zata kai 40years da Alama da yaranta a ciki domin munga suna daga mata hannu bye Mum,tayi murmushi Tare da shigewa mota Driver ya jata ta daura kafa daya kan daya tana karanta Jarida,Numfashi ne ya kusa daukewa sakamakon wasu motoci da suka keto cikin gidan a kalla sun kai guda biyar suka Parker zunzurutun Securities ne suka fito tare da zagaye motar kamar wani Shugaban kasa ne zai fito,bude motar sukayi muna tsaye muna shan kallo Wani arnen takalmi ya zuro waje nan take kamshinsa ya cika gidan me dadi,ya dan jima a haka kafin daga bisani ya fito cike da takama kamar wani Sarki,cikin kana nan kaya yake yau ma farin Wando pencil sosai rigarsa Silver color da Golden rubutu,takalminsa Silver yasha masifar kyau,duk wanda ya ganshi zai rantse ba mutum bane Sabo tsabar baiwar sura da kyau,ga iya daukan wanka yanda yake matukar kyau,yan matan nan ne muka ji sunce Hi Ya Aayan,ko kallonsu baiyi ba sai ma wani kallon Banza da muka ga ya watso musu kamar yaga kashi,sabo da nima gwanar mugunta ce a raina nace Allah ya kara shegu ga ubanku a girman kai gwara haka,
Matar da muke aiki da ita wato Salima itace ta kalli yan matan tayi dariya wai irin ta tura musu haushi,ai kuwa ba zato muka ji karar Mari a fuskata domin suna rawa tunaninsu nice na musu dariya shine daya a ciki kawai ta daukeni da shegen mari wanda ya jawo hankalin wannan Saurayin da Sauran Ma'aikata kaina,Kuka na fashe dashi a wajen nan take na fadi a wajen na dinga shure shure,wanda muke Polio ne suke bani baki kan nayi shuru mu tafi,cikin kuka nace Wlh sai na rama mikewa nayi a hasale na cakumo daya a Cikin yan matan wanda ban san wace ta mareni ciki ba nidai na kama daya tare da makalkaleta na cisgo gashinta na murde na ja da karfi,sannan na dalla mata mari har biyu na sake ta na zura da gudu domin sunyo kaina da kwaben lemon me tsada da suke sha zasu fasa min a kai,daya ciki ta jawo Hijab dina ta baya,Securities sun taho Saurayin nan ya dakatar dasu cewar a kyalesu,suna kallo sun rike min Hijab na sunkuya tare da zare Hijab dina na bar musu a hannunsu na Arce jikin gate ina rokon a bude min,Saurayin nan yace kar wanda ya bude min,Har yan matan nan suka zo kaina na kara runtumawa da uban gudu amma saida suka kamani suka rufarmin suka dakeni sosai naji jiki sai da suka gaji dan kansu sannan suka tafi ina yashe a kasa,sai Hawaye nakeyi abokan aikina suka dagani da kyar sannan naga wannan Saurayin yace a bude mana mu bace a ganinsa ya tsani mata ko da yan uwansa ne baya kaunar ganinsu,sai da na tabbatar an bude mana nasa kafa ta daya ciki daya waje sannan nace kai yan mata?duk kuwa suka juyo suna kallona nace Allah ya Isa kuma sai na rama watarana idan kanwata ta zama Doctor ko Lauya,kallon banza suka min tare da tabe baki,nace zaku gani wlh kyaleki nayi dan ba a kan KASUWANCI NA kuka tabo ni ba,rigimar ba akan kudi bace Amma da akan kudi ne ai da sai daรญ a mutu a gidan nan shegu,tsinannu tambadaddu,arna,jahilai,dabbobi kuma dukkan yan gidan nan na zaga na nuna Saurayin nan dake tsaye nace harda kai da wannan tsohuwar dake zaune a carpet a sanar mata dazagina da iyayenku baki daya,sannan kuma ina tunatar muku Mala'ikan mutuwa na nan zuwa watarana,sojoji ne suka yo kaina na Arce da uban gudu tare da cewa Allah ya isa dana gaishe da tsohuwar nan kekakashashiya,na dinga zura uban gudu Allah yasa time din tashinmu yayi kawai na fada Napep ina haki sai gida tazarce kawai tun daga Cikin gidan nake gudu har nazo bakin titi na hau Napep,su kansu abokan aikin nawa dariya suke min da kyar wani cikin wanda ke jiranmu a waje ya karbi box din hannuna Sabo da uban gudun da nake kamar na fanfalaki.
Bayan na koma gida sallah na gabatar tare da fara harkar kasuwancina har Awara nayi ta dare bayan na siyar na gyara komai tare da irga kudin na cire ribar na zuba cikin asusun da nake tarawa Ammah kudin asibiti na magani tare da ware na gida da yan abubuwa,washe gari haka muka je wata unguwar mukayi polio abokan aikina su Salima sun sani gaba suna min dariyar abinda ya faru damu a gidan masu kudin jiya,sai dariya muke muna Bada labarin,Salima tace ammafa sun hadu da yawa a gidan kowa me kyau ga iya kwalliya musamman dan Iskan da yasa aka dakeni domin ni tunanina shine yasa a Zane ni tunda shi ya hana a bude min gate,Salima tace lalle Mufeeda ashe haka kike da rashin kunya idan an tabo ki,kina da Silent falava wlh,u like too much falava,murmushi nayi kawai domin bana jin wani turanci ni kam,karatun Hausa da Arabic kawai na iya Amma Ilmin turanci sai dai kalmomi dai dai domin bani dashi,h akan ma don ina dagewa ne su Meenat suna koya min amma da ba karamar dakikiya za ayi ba ni kam.
Yau cikin nishadi muka gama Polio na dawo gida da Sauri naci abinci na shirya sai kasuwa siyayya ina tsoron bi ta cikin GRA Kawai sai na hau Napep naje na dawo lfy, bayan mun gama suyar Awara mun siyar wanka muka kara yi tare da Sallar Isha,Su Meenat Assignment sukayi na schl tare da karatu nima na zauna suna koya min karatun turanci da rubutu haka Arabic ma duk da ina da Ilmi domin Uzu na ashirin cif haka wasu litattafan duk nayi wanda Kannena su Ma'eeshah sunyi Sauka tuni littafin da suka sani kam ko kafarsu ban kama ba danma ni gwanar jin wa'azi ce nasan duk wasu hukunce Hukunce na addini da dama Amma su suke koya min karatun,da badan haka ba da anyi kungurmar Jahila ni,
Part of speach suke koya min common adjective sun sha fama dani kafin na iya fada Sabo da ba laifi kwakwalwata da saukin ja tunda ni dai iyakacin Jss 2 makaranta ta gagareni Allah ma yasa Makarantar Arabic da boko mukeyi a hade shi yasa muke dana addini,su Meenat kuwa ai akwai Ilmi,shi yasa da munyi fada zasu ce to Sis me kika sani ma in ba neman kudi ba musamman Meenat uwar iyayi da son kwalliya domin duk wata kwalliya ta yan Zamani ta iya ta komai nata na harkar son gayu,Maeeshah ma haka suyi ta faman iyayi ni kuwa sai dai na siya musu kayan yi suyi ta zuba kwalliya ina kallo tunda har cosmetics na talakawa ina siya musu iri iri,kayan wanke gashi na talaka ni dai barni da jarabar tsafta amma ba ruwana da wata kwalliya gani nake bata lokaci ce kawai kudi nake nema dan mi tsira da mutuncinsu,
ni kullum sai daรญ na labta Hijab na fita neman kudi ba sauki wanda yanzu Unguwarmu sun samin suna Yar Kasuwa,sabo da bani da lokaci sai na neman kudi akan kudi ba daga kafa.
Duk inda naji wata Sana'a ko harkar samun kudi to fa yanzu zan cusa kaina ciki dole sai na samu domin mu samu na ci da sha tare da Sutura,ina da karancin wannan shekarun Amma na shaku da kudi,yanzu abinda ya dameni bai wuce kai Ammah Hospital ba domin dubu Sittin da biyar zamu je da ita za ayi mata wani aiki a Ciwon dake kugunta zuwa kafafunta shi yasa na gigice yaki Halak yaki Haram haka nake tara kudin,
Akan wannan yanzu kam na koyi ha'inci a Sana'a ta domin Awara da ina yinta me kyau da dadi Amma yanzu dan na samu riba da yawa na daina alkintata idan na tashi tacewa Bazan matse ruwan da yawa ba,kadan nake dan matsewa kana ci zaka ji ciki lumtsum da ruwa da mai,haka yajin na daina me dadi sai na gabza uban gishiri a ciki dan yayi yawa,haka ake siye Sabo da tsaftarmu Amma sun daina karba da yajinmu,haka kosai na ma da wata taba da ha'inci ya taso min sai na siyo garin kwaki tare da jar kala bayan na dauko markaden saina zuba garrin kwaki a Cikin markaden waken kosan nawa tare da jar color yayi wani jajir sannan kosan ya kumbura yayi sutu sutu dan na samu riba na samu kudi sai kiga ana ta siye Malam kosai yasha kayan miyar color gashi har wani Danko yake Sabo da yaji garrin kwaki ciki ba a sani ba ayi ta siye ina samun riba tunanina dai dai duk kuwa da cewar nasan ba kyau sai daรญ nayi Istngifari domin ko Ammah da kannena basu san tabar da nake aikatawa ba gara awarar gida idan zan soya musu daban nake tace ta tas tsam ba ruwa sai su zata ma wacce ake siya haka take.
Hattana Alewar madarata dasu kwakwimeti tare da kafi tsire in dai zanyi sai na san tabar dana yi a ciki Sabo da kawai na samu riba me yawa,gullisuwa idan zanyita sai na tankade garrin masarara me Laushi na kara a cikin Madarar Sabo da tayi yawa,haka ma Zobo na siyarwa sai na samu jar color na tafasa zobon kadan na narka uwar Color a ciki nayi hadinsa a ganshi kamar gaske ayi ta zuka ba a san rabi color ce kawai da ruwa ba,kuma bana sa sugar dan zaki wato sugarin nake dan yafa kadan sai kaji zaki cai.
Ina zaune kusa da Ammah ina tufke mata gashinta muna sauraren Radio kawai sai muka ji cewar Gomnati zata raba tallafi ga marasa karfi Naira dubu sha biyar biyar tare buhun shinkafa da taliya sugar da man gyada tare da waken Suya a ja jari,nan take na mike zumbur naji kudi,Ammah ta kalleni tace sarkin neman kudi dan Allah ki hutawa kanki zafin nema baya kawo samu haka duk kin damu kanki Allah yana rufa mana asiri dan Allah ki rage takurawa kanki ayi amfani da abinda ya samu,baki na turo Ammah kina gani kudin maganinki har yau basu hadu ba fa,to ta wacce hanya zaki bi ki samo mana tallafin? Ammah wajen counsilor din Unguwarmu Adamu zanje na nemi Alfarma ya nemo mana hanya,ai yana da kirki Amma fa kija mutuncinki duk da nasan irin tarbiyyar da nayi muku ki kiyaye Mufeedata sannan kinga girma ya fara kamaki idan kika bari Namiji ya rike miki ko yatsa shike nan kinyi ciki an gama,da Sauri na zaro ido waje a tsorace nace Ciki Ammah?ae ai indai Namiji ya rike maka ko farcene to shike nan ciki ya shiga,da tsoro na firfito da ido waje,nace Ammah su Meenat nake tsoro bari su dawo na fada musu gaskiya kar suje su yarda da Maza su rike musu hannu.
Su Meenat suna dawowa na taresu da Sauri tare da jansu dan Bedroom dinmu nace dan ubanku karku bari Namiji ya rike ko yatsanku,Meenat tace Sabo da me?ba kyau kuma Ammah tace ciki ake dauka,Dariya naga Meenat ta kyalkyale tare da cewa Allah ya bamu kudi Sis ki koma schl kema wlh ba haka bane ke baki da labarin abinda ake a aure ana samun ciki,ai Ammah wayo ta miki kar mu kula Maza mu lalace shi yasa ta fada haka Sabo da taga mun fara girma,shuru nayi ina Nazari Amma naki yarda da Meenat Sabo da nasan Ammah baza ta fada mana karya ba,kyalesu nayi kawai na fita abina naci gaba zuba kwakwimeti na ร leda,bayan na gama na fara daura su citta dasu kanwa,kaninfari etc,kusan duk makwaftanmu a wajena suke siyen kayan miya,idan suka siya kawai sai su zauna a gidanmu suce bari su daka kayan miyar ko jajjage da sun shiga gida kawai sai daรญ su fara girki,sabo da son kudi na nace to daga yau na kafa doka cewar ko wacce idan zata yi daka a turmin gidanmu to sai ta bayar da Naira goma kudin turmi,ganin haka yasa Bazan basu tabarya ba sai an miko goma shike nan suka daina daka a gidanmu,Muna da wata Kura da yake gidan mu akwai rijiya idan guganmu ya fada da ita muke amfani mi Ciro gugan,mutane suna zuwa aro sosai nan ma nace kudin aron Kura Naira talatin wasu haka dole suke bayarwa suna dauko Guga,Ammah ta hanani Amma naki ji,su Meenat ma dole suyi abinda nace ko bana nan idan aka zo to fa sai an Bada kudin nan,komai nawa idan zaka taba na kudi ne.
Haka na kama kafa naje har gidan Adam counsilor neman Alfarma a sani cikin masu tallafi,yace Mufeedata ki. Makara wlh an gama daukan sunaye amma na miki alkawari akwai na wani watan kizo Office ki sameni a secretariat zan sa sunanki a wasu da za fara bayarwa na manoma,ban kawo da wata manufa ba kawai na dinga Murna ina godiya cewar zanje in Sha Allah.
Bayan kwana goma Zaune muke gaba daya tunda anyiwa Su Meenat hutun schl muna ta Hadin Zobo nan nace suje su ebo robobi a wanke suna Tafiya na watsa Maroon color tare da makawa Zobo ruwa na hadashi da su Flavour yasha uban Barkono a ciki,sabo da aji yaji sosai sai na zuba citta da kaninfari kadan na ebi Barkono na watsa a ciki na tafasa dashi Sabo da aji yajin ya fito sai ka rantse yajin cittane da kaninfari me uban yawa,gaskiya na iya taba sosai ni kaina ina jinjinawa kaina yanda nake tabka tsiya a sana'oi na ba a magana watarana nakanji haushin kaina nima ba da son raina nakeyi ba Amma Sabo da neman rufin asiri,su Ma'eesha suna kawo robobi Meenat tace sis wannan uban zobon fa dazu fa dan kadan ne bai kai rabin botiki ba amma yanzu ya cika botiki,Maeeshah ma tace nima haka na gani kamar na Aljanu,Harara na zabga musu sannan sukayi shuru.
abin takaicin da kyar na hada dubu Sittin da Bakwai kudin Ammah na asibiti,haka nace su shirya mu tafi,har kofar gida na kira Napep muka hadu tare da daukan Ammah muka sata cikin Napep muka kulle dan gidanmu da yar kofar da ta kusa ballewa ma haka na zarge ta muka shiga Napep Sai Asibitin Murtala na cikin Kano,Munje Dr Naseer ya duba lafiyarta ya dinga fada me yasa ba a kawota da wuri ba tuntuni yace a kawota ayi aikin to gashi ciwon nata ya kara karfi yanzu dole wasu magunguna zasu rubuta mana mu siya na dubu Hamsim da biyar sannan idan ta shanye bayan sati Uku mu dawo da ita za ayi mata aiki.
Bakin ciki da tsoro tare da firgici suka kamamu gaba daya,nayi Zuru Zuru kamar wacce ta shekara taana zawo haka na koma nace Doctor yanzu nawa ne kudin aikin? Yace ai kudinku da yawa,likitan da zaiyi mata aikin nan baya zama a kasar nan sam Sabo da aikinta zaizo yayi mata ya koma,don haka idan yayi muku sauki ku biya dubu dari takwas da Hamsim domin ciwon ya girma,da ace tun farko kun kawota da tuni baifi ku kashe dubu dari ba Amma yanzu danma da wannan Doctor dinne Amma wannan aikin kasar waje muke tura mutane masu irin cutar ayi musu aikin anfi dacewa,a nan kuwa sai dai mu dage da addua,kuje ku dawo lallai nan da 3wks tare da kudade in ba haka ba kuna kallo wlh zata kasa ko motsa yatsa dake gabarta nan gaba sankamewa zatayi ku daure ku dawo ayi mata aikin kunji.
Likita na bayani Hawaye na sintiri a fuskata tunanina ina zan nemo kudin nan ko kaina zan siyar wlh bazan yi wannan kudin ba,Innalillahi nake maimatawa Doctor kuma na kwantar min da hankali yana cewa cuta jarabta ce daga Allah,idan Allah ya jarabceka sai hakuri aci gaba da addua Amma tana cikin hadari,Meenat dake kusa dani itama Hawaye takeyi,da kyar na Lallashi kaina nice babba Amma kuma nice me raguwar zuciya bana iya rike Hawaye na saurin kuka gareni ammafa a bangaren abin tausayi,ko ya naga abin tausayi yanzu zan yi kuka,kanmu da Ammah nake tausayawa kawai,Meenat karki fadawa Ammah me Doctor yace kawai kiyi shuru da bakinki Sabo da bana so hankalinta ya tashi,muce kawai aiki za ayi mata nan da 3wks sai kudin zamu fada mata,amma karki fada mata Doctor yace zata iya rasa ranta ba lallai ta tashi ba kinji,ok Sis Bazan fada ba cewar Meenat dake shesheka,hawaye na share mata nace muje kawai muk ayiwa Dr sallama muka tafi,Ma'eeshah da Ammah suna jiranmu a can waje, magunguna muka siya sauran kudin na siyo mana wasu kayan abinci da Cefane,Su Meenat kuwa tuni na hadasu tare da Ammah nace suje gida zanzo daga baya,Ina cikin Napep kawai tunani nake ta ina zan samu kudin nan,lallai Zafin nema baya kawo Samu,gashi dai na gama Ha'incina a sana'ata na cuci mutane da dama ta hanyar siyar musu da gurbataccen abun ci kuma karshe kudin anfaninsu kadan ne a wajenmu abinda nayi don shi ba a dace ba,amma duk haka ban hakura ba kuma ban damu ba matukar zan samu kudin da Zan nemawa Ammah lfy.
Tunani nake bana ganin komai bana ji har Napep ya saukeni a gida na shiga da kaya Niki niki,Meenat ta karba ta shigar dasu ciki,tsabar bakin ciki da muke ciki yau bamu iya daura kaskon Awara a kofar gidanmu ba,duk muna zaune kowa da tunanin da yake banda Ma'eeshah da yake ita ba wani girma da hankali tayi ba sosai bacci ma takeyi,abincin da muka dafa ba wanda ya iya kai ko loma daya bakinsa,musamman ni gaba daya na rude na rikice,idan kuka ya taho min sai na shiga toilet naci uban kuka na wanke fuskata na fito haka na kwana inayi kafin Safiya tayi idona ya kumbura yayi jajir, ga addua muna tayi, mura ta kamani muryata har ta dashe Sabo da Hawaye na kawo Mura yawan kuka,da sassafe kamar me aikin Gomnati 8am nayi shiri da kumburarren idona tare da jansa na maka hijab kowa ya ganni yasan ba lfy,tunani nake ina zanje neman kudi Office din yan siyasa ko gidajen masu kudi?ko kuma kasuwa zanje wajen masu kantina,domin banyi tunanin kaiwa gidan Radio ba ko wani waje,kaf makwaftanmu haushina sukeji Sabo da kan Sana'a ta ba mutunci idan maganar kudi ce ba kawaici don haka ba da wanda muke shiri sai daรญ daiku duk sunfi jin haushina,don haka babu me bamu shawara ko gidan Radio ko wani waje to idan ba business ba babu abinda ke hada mu dasu Sabo da ba a kula mu ance dan munga muna da kyau sai mu dinga yanga mu ba yayan uban kowa ba,sannan tunaninsu ma ni yar Iska ce Sabo da yawan fita da nake kullum ina gantalin neman Kudi tunaninsu ai iskanci nakeyi kullum ina titi,haka suke zagina ba abinda ba ce min.
A fusace na fito daga gida ka Rantse mutanen garin ne suka min abin haushi domin kowa haushinsa nakeji kamar zan make mutane haka nake tafiya fuuuuuuu fuska ba annuri,duk motar dana gani sai na harareta na harari na ciki dake tuki irin ga mutane da kudi ba taimako,common arna ko church kaje a tallafa ma amma musulmai ko a masallaci basa iya bada Sadaka me tsoka sai biyar,goma,ashirin katon me kudi kaga ya mika Hamsim,mafi akasarin Hausawa haka suke bare har wani ya dauki nauyin karatun wasu ko ci da Sha bare na magani sai dai dai ake samun masu haka,amma arna sai kaga mutum daya ya kwashi yan unguwa da yawa ya fitar dasu kasar waje karatu etc.
AsmaBaffa
[1/1, 10:20 PM] Asmabaffa: ๐๐๐๐
๐๐๐๐
KASUWANCI NA
6-10
Official
By
AsmaBaffa
AUTA kema wannan page Sadaukarwa ce gareki.
Tafiya nake ina tunani har na Isa bakin titi ina jiran na shiga Napep shuru shuru ba taxi ba Napep kowacce a cike suke,wata dalleliyar motace tayi parking a gabana tunanina Namiji ne irin samari yan iska masu ragewa mata hanya a nemesu nan take na kara tamke fuska na dauke kaina na kalli can gefen hanya,wani kamshi naji ya cika wajen sakamakon bude murfin motar dake Saitina da akayi sai lokacin na kalli me fitowar ba kowa bane face yan matan nan na gidan Saurayi Aayan wanda suka min dukan tsiya sune su biyu suka fito a zafafe kida na tashi a motarsu sunci uban kyau ko ina zasu je oho,ina cikin wannan tunani sai ji nayi an sharara min ruwa a jikina me sanyi,a firgice na kallesu da mamaki,nan suka sheke min da Dariya dayar ta fusgo min Hijab tare da shakeni,dayar ta duro min ashar tare da cewa ubanwa kika zaga har gidanmu?dama nace wlh duk ranar dana ganki sai kin San wa kika yiwa rashin kunya wato har iyayenmu ko?
Dayar data shakeni ta tsandara min mari tace Wai ke face to face harda zagin ya Aayan ke din banza kucaka yar matsiyata kin San su waye ubanmu har zaki bude rubabben bakinki ki zagi kakarmu who are u me kwakwalwar dusa banza gaja.
Wani bakin ciki da bacin rai ya taso min duk saurin kuka na haka na danne shi,dama cikin haushin masu kudi nake ga bacin ran halin da muke ciki,nan take na kasa hakuri nima nace kune dai gajoji yan iska tsinannu na shaki wacce ta shakeni nima na zuba mata Mari me lafiya,nan take ta shakeni tare da Dafe kuncinta, dayar ta taso a fusace kafin ta karaso na tsuguna tare da kwaso kafafunta ji kake Tim ta fadi gefen titi,na bita kuwa tare da jawo kafarta kaiiiii kowa yana kallo ina janta a kasa tana ihu,na hau kanta tare da Zama daram na rufeta da duka tako ina,wacce na mara kuwa da sauri tazo kaina itama ta hau dukana,muna ta faman yi,ga yara da mutane sun taru ana kokarin rabamu amma Sam munki Hakura yi kawai mukeyi,
Wata motace dalleliya ta kara parking a gaban ta yan mata wata budurwa itace wacce muka samu tare suna rawa ranar da muka je gidan Polio da gudu ta taho tana yiwa yan Uwanta magana Ku kyale matsiyata Ku zo mu tafi pls wannan ba Class dinku bace Ladies pls,babu wanda ya kulata da takalminta me shegen tsini,gani tayi babu me hakura kawai ta daga waya ta kira Babansu tare da fada masa Address din inda muke,Nan take sai ga arnayen Motocin Aayan sunyi parking sun kai su bakwai da securities,yana zuwa ya fito cikin Takun mashahurin Namiji yau sanye yake cikin farar shadda dinkin fitted dai dai jikinsa ya dau matukar kyau ga wani arnen glass Brown a fuskarsa ba karamin kyau yayi ba,ganinsa yana tahowa nayi matukar firgita kamar zanyi fitsari sabo da na tsorata bazan manta da dukan da yayi min ba,ban San sanda na hantsilar da dayar daga jikina ba na tashi daga kan dayar da nake zaune na gyara hijab dina na kwashe da uban gudu kamar zan tashi sama,ina danyin nesa dasu na tsaya ina maida Numfashi,shi kuwa baima tunani ba Sam bai gane ni ba amma ya tabbata ya sanni.
Ina kallonsa ya karasa wajensu ya kama yan matan nan ya dinka kwada musu mari ba ji ba gani yana ball dasu sai da ya canja musu kamanni sannan ya fada mota yace Securities su kamo ni,banyi tunanin wajena zasu zo ba ina ta kokarin tare Napep amma babu,kawai sai motoci na gani sun zagayeni,kafin kace me Sojoji sun zagayeni ba hanyar guduwa.
Saurayin ne ya fito cike da jin kai ya kalleni da kyawawan idonsa,kwarjininsa da haibarsa sun cika min zuciya nayi kasa da kaina har gabana ya matso tabbas nice ya gane nice naje har gida na zagesu da Iyayensu,nan take yace a sa masa ni a mota ko ta wanne Hali,Kuka na fashe dashi me karfi ina rokonsa wayyo uwata wlh ni ba yar uwarku bace baka da dalilin hukuntani,yana jina ko kallona baiyi ba nan take suka jefani a mota suka figi motocinsu dani a ciki,Su kuma yan matan da kyar suka shiga mota daya me jarabar son girma ta jasu sannan tayi waya aka zo tare da daukan motar tata da ta bari gefen titi,Hospital ta wuce dasu aka yi musu Dressing tare da magani sannan suka tafi gida.
Ina cikin bayan wata mota Sanyin Ac sai kadani yake na dunkule waje daya ina ta faman Rusa kuka cewar an saceni za a yanke min kai,ta window naga mun shigo wani katafaren Building na gasken gasken komai glass ne fadin tsaruwar wannan building bata baki ne ashe wai Office din wannan hadadden saurayin ne,harda su Lifter, ko ina Flowers kamar wani Hotel don a Hotel din ma sai shahararre,ina kallo suka sa Lock tare da kulleni ni kadai a motar tun 9am suka shige ciki ina ta sa ran zasu fito gashi motar taki budewa,na rasa yanda zanyi,11am shuru,12pm tuni nayi bacci a cikin motar,3pm dai dai na farka daga baccin daya saceni a cikin motar tun 12 na fara baccin,yunwa taci har ta cinye amma banga Alamar zasu fito ba Sam,tun ina kuka har na hakura gashi banyi ko Sallah ba ni da bana kauna na hada Sallah sabo da gaskiya Allah yasa min son Addini sosai,ganin basu da niyyar fitowa kawai na fara karatun Qurani a hankali sai da nayi ya kai izu biyu sannan na koma tasbihi da sauran Zikhri dana iya,ina ta yin abina bilhakki da gaskiya ina adduar Allah ya kawo silar samun kudin asibiti na Ammah kuma Allah yasa ta warke,yunwa ta addabeni da kishirwa,5pm naga hadadde ya fito cikin shigar 3qtr fari da riga Armless red kamar ka saceshi ka gudu sabo da haduwa ta ko ina,kallonsa nake tayi ina tasbihi ga yanda ya zubawa wannan Saurayi baiwar kyau,sura, ga iya daukan wanka,uwa uba ga nutsuwa Kwarjini da haiba,Securities suna take masa baya yana gaba da robar ruwa a hannunsa,da sauri suka bude masa mota ya shiga ga yan Jarida suna binsu da gudu suna jefa masa tambayoyi amma ko bude baki baiyi ba bare ya basu amsa haka aka bude masa mota ya shiga sannan Securities suka shiga nasu harda motar da nake ciki suka figa muka bar wajen,ina ta mamaki ko ya manta dani gashi nasan Ammah da yan uwana yanzu sun shiga wani a kan rashin dawowata,
Wata katafariyar Unguwa ta masu Hanu da shuni muka nufa ina mamaki nan kuma kamar a turai wacce GRA ce wannan haka?domin nasan Ba Unguwarsu bace wannan,Harga Allah wannan Saurayi wato Aayan ya manta dani a cikin mota,direct Gidansa wanda babu wanda yasan dashi nan ya nufa,gidan fadin haduwarsa da tsaruwarsa bata baki ne ya wuce duk inda ake tunani,gidane na fada wanda kafin a sami irinsa sai dai ko a turai ko Abuja watakil,sunayin parking a compound duk suka firfito aka bude masa ya kallesu tare da basu Umarnin su kwashe motocin su kaisu main Family House tunda yana da motoci iri iri a cikin wannan gidan kalarsu daban masu shegen kyau jibga jibga,daya daga ciki ne ya sanar dashi yarinyar fa? Sai lokacin ya tuna da ina ciki,tsaki yaja sannan yace a fito masa dani su kuma su tafi Gida.
Nan take aka yo waje dani suka figi motoci suka bar gidan daga ni sai wannan Matashi Aayan me cikar zati da kwarjini.
Shuru nayi tare da sunkiyar da kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna jikina yana bari kamar mazari,Kallo daya yayi min wani na mugun wulakanci tare da rainin hankali yana yatsina fuska kamar yaga kashi,nayi mugun raina kaina domin bani da maraba da Almajira mara galibu,juyawa yayi cike da takama hannunsa cikin aljihun wandonsa daya hannun kuma yana latsa waya yace let's go,bana jin turanci amma na gane go din kawai nabi bayan sa kamar Munafuka burina kawai ya kyaleni na tafi gida abina.
Code number ya danna nan take kofar ta bude ya shiga nima haka,Wow ai ciki Aljannar duniyace kawai komai na Alfarma abin ba a cewa komai domin shagala nayi wajen kallo ina mamakin kudin wannan matashin komai Allah ya bashi.
Steps ya hau na bene,har na taka zan bishi ya daga min hannu alamar na tsaya tare da zabga min uwar Harara yana tsaki,a tsorace na kame a wajen,tunda ya shiga ya mugun dadewa har ana shirin Magrib sannan ya fito sanye da farar jallabiya fara fitted a jikinsa yana sheka uban kamshi,ina tsaye kamar gunki yazo ya wuce ni kamar Allah bai halacci dan Adam ba haka ya wuce ya fita daga palon sai karar mota naji da alama ya fita Ashe Sallah ya tafi masallaci,nan take naga tsaiwa baza ta kaini ba kawai na fara duba dakuna gaba daya dake cikin palon kasa Allah ya taimakeni ina bude wata kofa na hango makeken daki dauke da lafiyayyan gado da mudubi tare da sip na Alfarma komai milk and Brown color ne a dakin,kofa na gani a cikin Bedroom din nan take na Murda Handle din toilet ce ta yan gayun gaske ban taba ganin irinsu ba dan Allah yasa a birni muke da bazan iya gwada yanda ake kunna tap din ba,ina shiga wajen sink na nufa abin mamaki ina mika hannuna sai ruwa ya fara zuba shaaa idan na janye hannuna sai ruwan ya dauke haka shower ma kai abin kamar Aljanu,ban San lokaci ya ja ba na shagala na manta da kowa ina ta tabe tabena har na gaji nayi fitsari da tsarki sannan na daura Alwala na fito Palo da sauri dan kar mugun ya dawo ya isheni na shigar masa wani waje,ina fitowa na duba gabas na shimfida dankwali na sai na fara jero salloli,Magrib na fara yi sai la'asar da Azahar ina zaune ina azkhar na Mike na gabatar da Sallar Isha da kyar kasancewar yunwa taci karfina gaba daya a kasa a zaune ina adduoina.
Motarsa naji da Alamar ya dawo lokacin ina yanda nayi Sallah ina adduo ina wanda ban san ma a fili nakeyi ba ina fadawa Allah ciwon Ammah da halin da muke ciki Allah ya yaye mana,kamshinsa naji alamar ya shigo da mamaki ya kalleni da alama Sallah nayi karfa ko Bedroom na shigar masa,wata mahaukaciyar tsawa ya buga min da tasa nan take na saki kuka,Keeeee a ina kika samu Ruwan Alwala? Jiki na rawa na nuna masa Bedroom din dana shiga da yatsa na, tsaki yaja tare da cewa Allah ya taimakeki wata leda ya wurgo min a jikina sannan ya haura Sama da nasa a hannu.
30 mnt ya fito da lemon gwangwani a hannunsa yana korawa nan ya fada saman kujera tare da nutsewa a ciki ya dauki remote yana kunna Tv ya kamo tashar wakokin turawa na yan Iska kusan ma kamar tsirara ake nuna su su Nicki Minaj etc.
Da kyar na Mike na karasa kusa da kafafunsa a hankali cikin ladabi da kwantar da murya nace Sir....Shuru ya min kamar bai San ina magana ba,Nace Sirr.....shuru,Sirrrrrr.....da wani mugun Bala'i ya juyo ba tare da yace komai ba,nan dai na daure da kyar sabo da kwarjininsa nace Dan girman Allah kayi Hakuri ka barni na tafi gida dan Allah,Ammah ta tana gida bata da lfy da kannena yanzu suna cikin damuwa dan Darajar Allah Sir,idan ma baza ka barni na tafi ba to ka kira min su a waya ka hadani dasu na kwantar musu da hankali kafin Lokacin da zaka barni na tafi.
Shuru naji yayi kamar ma ba dashi nake magana ba,na daure ina hawaye nace Sirrrr....sai lokacin ya juyo ya kalleni tare da dauke kai can yace me kike so kice? Wato duk maganar da nayi ma bai ji ba,wani bacin rai ya kamani cike da fushi na hayayyako masa nace ka barni na tafi idan baza ka barni ba ka kira min sis dina na fada mu......wani gigitaccen Mari naji a kumatu na,kafin na bude Ido ya kara min wani marin me masifar Radadi nan ba shiri na barke da kuka,mikewa naga yayi sai gashi ya fito da dalleliyar wuka a hannunsa,a wuyana yasa ta yace will u close tht ur dirty mouth or...kafin yayi Magana na hadiye kuka na sai shesheka duk da bana jin turanci amma na gane Close da mouth tunda Su Meenat suna koya min.
Dan kinga ban miki komai ba shine zaki raina min hankali am I ur mate or what?,baki da tarbiya na gama ganewa dama ina nemanki ke gaki marar kunya ke har kin isa ko kalleni ki zageni har gida,kin San ko ni waye who do u think u r? Murmushin takaici yayi tare da cewa dama bari nayi naga karshen rashin kunyarki,har kina min fada ni zaki kalla ki min maganar banza bayan kina hannuna ko yankaki nayi na yanka banza, shi dama Aayan haushin mata yake ji har jira yake mace ta masa abu yaga ya ci mata mutunci domin mata sun masa abinda bazai manta ba.
Ina gefe nayi mukus fuskata tayi jajir sai yatsunsa kwance a fuskata,wancen abincin ubanwa zai ci miki?da sauri na rarrafa na dauka na bude ledar jiki na mazari na bude Fried rice tasha hadi tare da kaza sai lemo,ruwa da Yogourt a ciki nan take na bude na kai lauma da bismilla kamar mayunwaciya haka nake afka abinci 5mnt kamar waccen ta zubar har na lashe abincin na shanye yogourt tare da lemon sannan na daga ruwan na shanye du,yana zaune mamaki ya rufeshi yana kallon ikon Allah ci kamar jaka,ya tabbata ko da yunwa ya kwana bazai iya cinye abincin ba,na gefensa ya kara jefo min a jikina nufinsa na cinye,ni ko dama ji nake kamar banci ba domin ba laifi akwai ci,haka na dauke na kara budewa yana bude baki da mamaki yaga na kara cinye nasan ruwan ne kawai ban Sha ba amma har yogourt din na shanye ta,da hannu ya min Alama na mike,zumbur na Mike tsaye,yace naje can bangon na dawo haka da sauri naje na dawo,yace yi tsalle na gani nayi tsalle ba shiri sabo da tsoronsa da nakeji,shi tunaninsa bazan iya tashi ba wannan uban abinci dana cinye amma sai yaga ras dani,a zuciyarsa yace bari ya kara gwadawa ya gani,nan ya Mike ya shiga kitchen ya fito dauke da fura tasha hadi a katuwar roba tare da Fruits a wani bowl,nan take yawuna ya tsinke naga dadi ban saba cin irinsa ba amma da shinkafa da wake ce ko plate daya bazan iya cinyewa ba,ko tuwo bazan sauraresu ba amma wannan kayan dadi haka ina zan barsu ko cikina zai fashe bare wannan dan abinci na take away kamar an roko gaba daya bazai plate daya ba,
Furar ya miko min ya tamke fuska yace shanyeta,da mamakinsa yaga na dauke da sauri har ina murmushi don ina son Fura a duniya,kawai na fara Sha cikin nishadi har lumshe ido nake ina addua ga Allah ina inama Ammah na kusa,ina Sha ina Santi a raina gata tayi sanyi a raina nace ah lallai wannan yana so aci a koshi Ashe ma bai cika mugu ba yo ni badan su Ammah ba ai da na rokeshi ya dauki rikona a gidansa,ina ta santina sai gashi na shanye harda lashe spoon din,wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke abinfa ya daure masa kai karfa ko Aljana ce,Nan ya mika min Bowl din Fruits dama su nake kallo cike da kwadayi nan ma na karba harda godiya na koma gefe na fara lunkuma su kankana a baki nace kai Allah me iko na yini banci ba Ashe tanadi Allah ya min harda kara'i yana kallo yaga na tashi Fruits tsaf,karkuce abubuwan masu yawa ne basu da wani yawa kun San dai Harkar yan gayu komai kadan kadan ba dole na cinye ba.
Yau kuwa yace sai ya kure yarinyar nan mayya,ya Mike ya koma kitchen sai gashi dauke da kaza tasha hadi tana tiriri da Alama warming dinta yayi ya turo min gabana,kamar nayi kuka sabo da dadi yaushe rabon naga kaza guda a gashe sabo da murna ban san sanda na kalleshi ba nace Dan Allah ka daukeni aiki ko share share da goge ne a gidan nan,wata uwar Harara ya zabgo min ban san sanda nace yi hakuri na fara yagar kazata ba ina aikata cikina,gani yayi fa da gaske zan iya cinyewa kawai yace karta je ta barke min da Zawo a gida kawai ya taso ya fisge plate din tare da cewa Mayya.
Yana dawowa ya mika min faskekiyar wayarsa nufinsa wai nasa Number na kira gida,ban iya ba amma gudun laifi na karba haka nan take nayi kamar zan iya na zuba yatsuna guda biyu na fara birkita screen din,naga Sam ban gane ba nasa yatsuna guda hudu na fara dirzawa a fuskar wayar,na juyata na juya na dukufa kamar Idona zai zazzago sabo da yanda na zarosu ni a dole me danna waya,shi kanshi da ya kalla yayi tunanin wannan yarinyar Aljanu gareta ko mahaukaciya ce bai San tsabar rashin zaman aji ne da rashin shiga mutane daga siye sai siyarwa, gani yayi zan masa barna ya fisge abarsa tare da cewa fada min Number cikin hasala kamar zai dakeni,to mu dai a gidanmu babu waya dama akwai wani Shehu me Kanti idan wani abu ya faru shi Muke kira a waya sai ya kai gidanmu ayi magana don Number dinsa na kaina,na iya da turanci amma wai dan kar nayi mistake ya dakeni sai naji tsoro nace gwara na fada da hausa nan na fara cewa
sifili takwas sifili...wait wait ths is bull shit ban san wannan abun ba,nan nace yi hakuri bari na Canja na firgita kawai maimakon na fada da turancin sai wai dan yafi ganewa sai nace..tayar mota.. takwas..tayar mota,wai gani nayi Zero (O) yana kama da tayar mota shine dan yafi ganewa nace haka,wani mugun dariya ce ta kamashi da ya gano me nake nufi da Zero ne Tayar mota lallai wannan yarinya dakikiyace amma sai ya daure fuska yace wlh zan kwada miki mari zan miki abinda baza ki manta ba,nan take nace 080 sannan na fada masa Numbers da turanci,yace amma ke dan Iskanci zaki raina min hankali kin iya fada dai dai nonsense tare da Jan tsaki yana dialing bugu daya aka daga ya mika min wayar nace Hello...Shehu Mufeeda ce,dan Allah dan kaiwa Ammah wayar mana minti daya,nan Shehu yace to Mufeeda ya fita da sauri yayi Sallama gidan tare da gaishe da su Ammah dasu Meenat suka gaisheshi suna cikin wani Hali sunyi jirim suna jimamin Ina Mufeeda ta shiga tun safe har dare hankalinsu ya tashi,Shehu yace gashi inji Mufeeda tace za kuyi magana ai da sauri Ammah ta karba jiki na bari,Mufeeda tace Ammahna kuna lfy? Ya jikin naki? Ammah tace ba ta wannan nake ba kina Ina Mufeeda lfy iceko,dariya ni Mufeeda na kakalo tare da cewa lfy lau Ammah kin ganni a gidan wannan kawar tawa wacce kika sani Naeema yar gidan me kudin nan kin San ai da sun tafi kasar waje to sun dawo shine muka hadu a kasuwa tace muje naga gidansu,
shine ma mamanta take tambayata ke nake basu labarin cutarki da aikin da za ayi miki shine Maman tace mijinta yayi tafiya gobe ko jibi zai dawo na zauna kar na tafi na jira zai iya biya mana kudin aikin da za ayi miki,kinga ai bazan taho ba shine na zauna ina jira kuyi addua Allah sa a dace,nan take Ammah wani farin ciki ya lullubeta tace Mufeeda kin tabbatar haka zancen yake ba karya?nace tabbas Ammah ai kin San halina dai ko kin San kuma dalilin fita ta Allah watakil ya amshi adduar mu,Ammah kinga dadin da naci harda Kaza da Yogourt,kuyi addua amma yau Ni ina cikin daula ina su Meenat bani su,nan ma aka bawa Meenat suka Sha labari aka mikawa Maeeshah ma tana Anty jambaki pink ya kare ki siyo min wani,kuma takalmi na ya tsinke Sis nace to Maeeshah zan siyo bawa Ammah,nan nace Ammah aci gaba da kular min da Kasuwanci na dan Allah Meenat tayi komai,Ammah tace kin San basu iya kosan sosai ba,Nace Ammah suyi haka koma yane a tara min kudin in na dawo za muyi magana sai goben idan ya dawo me gidan zan sanar dake idan Bai dawo ba zan fada miki komai dai,Allah yasa a dace cewar Ammah ta mikawa Shehu wayarsa Mufeeda tayi masa godiya ta kashe shima ya musu sallama ya tafi,nan Ammah tace Meenat ta kulle musu gida ta rufe suka yi kwanciyarsu cikin farin ciki.
Ni kuwa ina gamawa hankalina ya kwanta nan na saki ajiyar zuciya,shi kuwa da mamaki yake kallona yanda na iya fesa karya haka,lallai suna da matsala amma ina ruwansa,ni ko dama su Ammah nake ji kuma na gyara komai,idan na koma nasan karyar da zan kara shimfidawa, baki ya tabe nan take ya fisge wayarsa tare da wucewa samansa,ni kuwa yana tafiya na koma saman 3seater na kwanta a tsorace har bacci ya saceni, tunda ya shiga bedroom ya rasa wannan mugunta zai min wacce bazan manta ba ina cikin bacci naji ya harbo ni kasa daga saman sofa,a firgice na tashi, ba Imani yace sai nayi Kamun kunne,haka nayi na Dade ina yi har sai da na saki Kuka,sannan yace nayi kneel down sannan Hands up nan ma na fara ina tayi haka yayi tafiyarsa ya barni ina ta abinda ya sani har bacci ya kwasheni na bingire a wajen,ban farka ba sai da gari yayi haske na Mike a firgice tunawa da banyi Sallah ba yasa na Mike da sauri na fada bedroom din da nayi Alwala jiya,komai na kayan wanka da amfani a kwai a toilet din masu tsadar gaske,ba bata lokaci tube kayana na kai hannuna ruwa me dumi sosai yana zubowa gwanin dadi ban san sanda na fara wanke kaina da shampoo me kamshi da tsada ba,ina gamawa na dauki liquid soap na sheka wanka sai kamshi ina ta washe baki,ina dubawa naga harda sababbin tooth brushes da toothpaste na dauka kuwa na wanke bakina tas abinka da abu me tsada hakorana suka kara haske da kyau Malam nayi wani Fresh dani,Towel nasa tare da goge jikina tas,sa nan na daura Towel na fito ina kara tsane gashina,mirror ba abinda babu na shafawa masu tsada,na dauki lotion na shafa a jikina,babu powder sai wata fara kawai na shafa abata na dauki lipgloss na shafa me kyau red,ban san jagirar waye ba na dauka na zizara a Idona sai gashi nayi kyau sosai.
Gashi na wanda ya bushe na taje na shafe shi da Maya Mayan gashi yana sheki da kamshi dama gani Allah ya bani tsayin gashi,Daure abina nayi nan take nayi acuci da gashina sannan na shafa roll on tare da turaren jiki dana gani me arnen kamshi,kayana na kwaso na saka haka ina so na wanke pant dina amma ba dama kawai na maida abina sai lokacin na tuna banyi sallar Asuba ba da sauri nayi tare da Azkhar sannan na fito Palo cikin Jin dadi na zauna,ina jin motsi na sauka kasa tare da kneel down na daga hannu sama wai dan yace a haka na kwana inayi,kallo daya ya min yasan Lallai har wanka nayi,ko kallona baiyi ba ya fita,15mnt sai gashi ya dawo tare da take away leda hudu,ya zauna a saman Sofa tare da miko min leda uku da sauri na karba dama yunwa nake ji nan na zauna daram tare da bude ledar sai ga kwai da chips tare da gashashiyar Hantar rago, haba Malam nan na zaro harshe na lashe labbana na fara dagargazar Harka yi nake ba ji ba gani,nan na kau da Leda daya na bude daya na lashe na jawo ta Ukun na cinye komai tas tare da daukan ragowar ruwana na jiya na shanye tas nace Alhmdllh tare goge hannuna da tissue din dana gani ciki.
Mamaki ya gama kashe Aayan har firgita yayi yana mamakin a ransa kuma cikinta baya lalacewa,yana kallon TV yace tashi ki gyara gidan nan kaf yayi maganar kamar bada ni yake ba,Zumbur na Mike na kayan aikin,kitchen ya nuna min da yatsa ina shiga na gansu a shirye na hado da kayan mopping,yace na biyo shi haka yasa na gyara samansa Kas Kas, ko ina yana kyalli har su toilet,abin ya bashi mamaki baiyi zaton zan iya gyara haka ba,muka dawo kasa ko ina na gyara har room din da nayi wanka da toilet,haka ya dinga nuna min wasu sashen har wajen motsa jikinsa sai da na gyara tsab,ta window na hango maza suna ta aikin gyaran compound flowers tare da goge windows ni kuma na gyara ciki, nayi matukar jigata nasha wahala,yace sai na shiga kitchen haka na shiga na wanke na goge na gyara komai neat har store,haka fridge ma ya fitar da abinda suka lalace yace na gyara ciki tare da bani wasu abin na gyaran Fridge haka na gyara fes na kara Mopping kitchen din na wanke komai na shanya su sannan na fito,ina fitowa yace naci gaba da Kamun kunne ba Hutu,inayi ina kuka,sai da na kai 1pm sannan yace naje nayi Sallah na bar masa gida,cike da Murna na Mike na gyara jikina tare da Alwala nayi Sallah ta saida na kara gyara fuskata gudun tuhuma wajen Ammah sannan na fito tare da yin hanyar waje,Keee naji muryarsa me sanyi,juyowa nayi a rude nan naga ya daga waya yana magana Hello Abbi ka tashi lfy,ta ciki naji Muryar Abbi yace zo ka bude min kofa ina son magana da kai gani a gidan ka wato ni zaka rainawa Hankali ko,nan take ya firgita amma dake namijin duniya ne sai ya maze bai kawo komai ba ya raba ta gefe na wani kamshi ya dakeni nan take jiki na ya mutu na lumshe ido,kofar ya bude kawai sai ga Abbi ya bayyana a gabana da sauri na tsorata tare da ja baya.
Salati ya saki da salallalami yace dama nasan wlh ba abin kirki kake aikatawa a wannan gidan ba shi yasa nazo da kaina,ashe baka da kunya baka da mutunci ai jiya na tambaya ina ka kwana ance ba a sani ba nasan kana nan,ashe abinda kake aikatawa kenan munafiki ka nuna Sam kai baka kaunar mata Ashe abinda kake kenan,karuwai kake kawowa gidanka,ashe shi yasa baza ka iya zama da aure ba,wannan yaro kwai tsinanne in Allah ya yarda Cutar kanjamau ce ajalinka,baza ka jawo mana abin kunya ba wlh dole yau Hajja taji zancen nan kuma aure dole kayi zaka ga abinda zai biyo baya,nan Abbi ya min kallon Banza ya fice a fusace.
Shi kuwa Aayan ko a jikinsa haka ya nuna amma yaji zafin sharrin da Abbi ya masa,ni kuwa tausayinsa naji sabo da na tuno maganganunsu farkon ganina dasu,Driver ya kira a waya sai gashi yazo umarni ya bashi jeka wannan zata gwada maka gidansu ka,ka kaita can.Nace na gode wata uwar Harara ya balla min nan take nayi mukus tare da bin bayan Driver na shiga motar sai muka bar gidan ina jin dadi na rabu da jaraba.
AsmaBaffa
[1/1, 10:59 PM] Asmabaffa: ๐๐๐๐
๐๐๐๐
KASUWANCI NA
11-15
Official
By
AsmaBaffa
Ths page is for u MARCYCOOL.
ina matukar Godiya da jinjina fans masu Sharhi aci gaba da gashi kuna birgeni.
Allah ya taimakeni Driver na da kirki cikin mutunci ya kaini har kofar gidanmu wanda kaf mutanen unguwar mamaki sukeyi na wannan arniyar mota amma wai sai suka ga Ni Mufeeda yar Kasuwa yar talakawa fitik wai ni aka sauke a wannan mota, ai fa sai mutane suka fara guna guni ga zahiri ai karuwancina ya girmama ni kuwa Allah sarki ban san ma sunayi ba, wata kawata a makwaftan mu Nawwara itama dai Nawwara yar malam Shehu ce talakawa amma sun fimu rufin asiri ita kadai ce kawata sai kuma wata yar gidan masu kudi Na'eema amma ita yanzu sun koma Kasar waje da karatu har iyayenta suna kasar waje abinsu,
A hanya Nawwara tace Mufeeda kece a wannan zundumemiyar mota haka duk da bana zarginki ki kiyaye ko sabo da sharrin yan Unguwa,Murmushi nayi tare da cewa Allah kadai nake tsoro ni,Allah yaga zuciyata.
cike da farin ciki na shiga gida da Sallama dauke a bakina,da fara'a suna min Oyoyo sannan na wuce wajen Ammah tare da gaisar da ita,tace Mufeeda kar ki kara yin irin wannan tafiyar kinji na fada miki,wannan ya Zama na karshe da zaki tafi wani gida ki kwana ba tare da Sanina ba sai dai ki bugo waya,bazan yarda da wannan shirmen ba,karki ga na yarda dake kice zakiyi abinda kika ga dama ko dan kina ci damu etc kice zaki juya ni baki isa ba,ni ba irin iyayen nan bace masu son abin duniya akan yara ne ke ci dasu sai su zauna yaran na juya su sai abinda suka ga dama zasu yi,ki nutsu wlh akan haka gwara mu daina karbar abin hannunki bana so neman Kudi ya kaiki ga halaka ko sabawa Allah,naji matukar ciwo da sai dare ma zaki bugo ki fada min ni har ga Allah ban yarda da zancenki ba kawai dan naji lafiya kike yasa na dan samu nutsuwa,nan Ammah ta dinga fada ba ji ba gani ina bata hakuri harda kuka na,nace bazan kara ba kiyi hakuri abinda na tsaya nema ma ba a dace ba domin me gidan yayi tafiya kasar waje nan ma na kara mako karya ta na fada,aiko nasha fada wajen Ammah,ni dai hakuri nake bayarwa har ta hakura.
Bayan kwana biyu tsakani naga sana'ar tawa ta danyi kasa don haka na tattara ragowar kudin dake hannuna na siyo kajin Hausa da Akuya guda daya wai zan gwada yin kiwo ko za a samu suyi albarka,Kaji biyu yan budurwa na kawosu,akuya tana meee...mee na samu na daure ta can karshen gidanmu,lokacin wake beans yana araha kawai na auni kwano biyar na boye ina jira yayi tsada na siyar naci riba,sannan na dan siyowa su Meenat kayan kwalliya tare da kayan makaranta Uniform na dinka musu sabo idan an koma schl suma su sa sabo,haka na siyo mana Atamfa muka raba yadi biyu kala Uku akayi mana dinki me kyau na talauci domin rabi wasu yadi ne na adon Atamfa akayi mana kari dashi,sai suka ba da ma'ana,dama bamu da kudin dinka shadda daga atamfa sai materials sai kuma kayan gwanjo da muke sawa,suma dinkin atamfar na talauci duk bamu da riga da zani ko daya daga skert damamme sabo da yadinma bai isa ba bare tela ya maka mana dinki dole sai dan fitted,sai ko dogayen riguna baza ka gammu cikin Tsumma ba Sam sabo da ina yawan yi mana dinki tare da yan takalma na roba yan Dari hudu zuwa biyar muna dasu da yawa dasu muke too match,haka mayafai ma ina siya mana da hijabai zaka ga muna canja abinmu iri iri mata sai da gyara ai,bani da burin da ya wuce naga Ammah cikin farin ciki Tare da kannena duk kudin da nake nema sabo da su nake nema.
Asalinmu
Sunana Mufeeda Adam Fatima, Asalin Shuwa Arab ne Babanmu,a Borno state suke da Zama tare da Family dinsa gaba daya,Bashi da Ilmin Boko sosai sai kasuwanci da yake y,Babanmu Adam yana da dangi da yawan gaske wanda mu bamu San dasu ba Sam,Iyayensa sun Dade da rasuwa tun yana yaro domin shi kadai suka Haifa Allah ya musu rasuwa ya taso a maraya,shi yasa ma ya taso da neman Kudi har Allah ya kawoshi Kano state,yana shiga kauyuka saro kayan Noma ya kai kasuwa,Har ya shiga Kauyen Ammah wato Kauyen Rimin Gado can rigar Fulani,Nan yaga Ammah cikin halin rashin gata tana Shan wahala hannun matar uba sabo da bata da Uwa sai Uba,danginta kuma fulanin tashi ne basa Zama Sam kullum a yawon daji suke basa Zumunci,bayan Adam Abban mu ya auri Ammah da shekara daya Allah ya dauki ran Baban Ammah wato Sulaiman,Haka Abba yaci gaba da kula da Ammah suna zamansu lfy a cikin birnin kano gwale,ko sunje kauyen ma ba wasu dangi sun tafi yawon Shanunsu har Ammah ta daina zuwa ma tunda duk yan Uwanta sai wanda suke uba daya kuma basa kulata sai ta kyalesu kawai amma duk da haka tana kaimu muna zuwa itama kafin lalura ta sameta tana zuwa musu.
Mu kuwa ganin basa zuwa basu damu da mu ba ko tace muje sai muki zuwa idan munje ma basa ganinmu da daraja,Shekarar Ammah da Abba biyu da Aure ta Haifeni aka sa min suna Mufeeda kowa yana yabon kyauna,sai da na cika shekara biyu sannan aka kara haifar Meenat,itama After 3years sai aka Haifi Ma'eeshah,Lokacin Babanmu ya samu wadata sosai ya siyi gida kato cikin Rijiyar Zaki muka koma ciki yana Business sosai sannan ya zana waec da Neco ya koma makaranta yayi NCE ya gama,lokacin tuni ina zuwa Primary schl amma ta Gomnati sabo da ba masu kudi bane mu sai rufin asiri domin munfi karfin ci da Sha bare sutura,ina primary 3 aka saka Meenat da Ma'eesha suma muna zuwa nice Babba, Da yamma muje Islamiyya, ina kula dasu sosai domin tun ina yarinya Allah yasa min son iyayena da yan uwana fiye da kaina,mun taso cikin kulawa da tarbiya muna jin dadinmu har na kusa gama Primary
sai kuma muka ga Abbanmu sam ya daina kula Ammah sai wulakantata yakeyi,ba irin wulakancin da Ammah bata gani ba a hannun Abba,idan suna fada har Kuka mukeyi,amma duk lokacin bamu da wayo bamu San akan me suke fadan ba,muna dai ji yana cewa idan ya gaji korarta zaiyi,tun abin baya damun mu har muke damuwa muna bashi hakuri,bamu San dalili ba dai sabo da Ammah bata bari mu San halin da suke ciki,sai dai muga tana kuka watarana Abbah yace zai fita wata state dake Kudu Abia state neman Kudi tun da Allah yasa ya tafi bamu kara Jin labarin Inda yake ba ko a waya.
Mun shiga damuwa me tsanani,Amma taje har garinsu wajen danginsa tare da mu amma sukace suma basu da labarinsa,haka abokanansa na business da sauransu duk an nemesu shuru suma basu sani ba,munyi kuka munyi bakin ciki har aka kwashe shekara guda lokacin na gama primary,anyi cigiyar Abbah har gidan Radio amma ba labari haka Ammah ta fara Sana'ar kosan siyarwa da Awara tare da sauran kanana nan sana'a gida dasu take mana komai na rayuwa,har na shiga Jss1 na gama na shiga jss 2,Katsam lalura ta samu Ammah haka kawai bata iya motsa kafafunta daga Hips zuwa toes,munci kuka gashi nice Babba ga karancin Shekaru haka makwafta suka taimaka mana muka kai Ammah asibiti mafi sauki,da yan kudin da Ammah ke Tarawa muka sai mata magunguna sannan suka ce dole akwai wani aiki da za ayi mata nan gaba,tun da muka dawo Ammah ta dan samu sauki ni kuma dama duk sana'oin nata na iya su sai naci gaba da yi na daina zuwa schl nake biyawa su Ma'eesha suna zuwa,ni ke kula da Ammah da gidan baki daya,akan sana'ar ma sai na kara wasu da yawa ina yi iri iri komai siyarwa nakeyi ba sauki,har Allah yasa Meenat na Ss1 Maeeshah na jss2 ga Islamiyya suna zuwa ni kuwa komai ya tsaya min sai neman kudin jaraba kamar zanyi sata.
har yau munyi munyi da Ammah ta fada mana fadan dake tsakaninta da Abba kafin ya bace amma taki fada mana sabo da haka muka kyaleta sannan muka kara tsanar Abba da ya gudu ya barmu,dan ni ko zancen wani Abba bana yi sam bama na so a ambaci Sunansa shi yasa a makaranta ma Sunana Mufeeda Adam Fatima sabo da sunan Ammah Fatima kawai nace ai bazan sa Kakanmu ba Ammah ta zan sa,haka Meenat Adam Fatima tare da Maeeshah Adam Fatima haka duk muke Amfani dashi da ace da halima sai dai nasa Mufeeda Fatima Adam to kawai dan da uba ake ado shi yasa ba kyau dole nake Sa Adam.
Za muji nan gaba Ina Abbah ya boye oho,ko da gaske ya bata,ko yana raye,ko yan Mafiya ne,mene ya hadasu da Ammah suke fada,wacce lalurace a jikin Ammah haka? Oho dai.
Ci gaban labari
bayan kwanaki kadan na yanke hukuncin zan fara zuwa gidan yan siyasa tare da yan kasuwa da sauran masu kudi na fara neman taimako ko Allah zai sa a samu me Imani ya tallafa a biyawa Ammah kudin magani,bayan na gama kosan siyarwata tare da gyaran gidan haka nayi girkin rana na kwashe a cooler sannan na fara daka lallen da nake siyarwa ina daurawa a leda ina saidawa ashirin,lallen ma ban barshi ba sai dana yi masa Algus na hada da gayyen bishiyar sabara na daka ya kara yawa na daura na ajiye,idan mutum ya siya lalle sai yaga lallen yaki yi masa ja yadda yake so to anyi masa Algus da wasu gayyen,wanka nayi na shirya cikin skert dina dan gwanjo tare da T-shirt dita nayi kyau nasa Hijab dina me hannu sunsha wanki da guga,ban shafa ko Powder ba na yiwa Ammah Sallama nace na tafi kasuwa siyo kaya,tayi mun a dawo lfy,ban zarce ko ina ba sai gidan Chairman din local government dinmu,ban san gidan ba da tambaya aka nuna min ni da me Napep,bayan na sauka mutane damkam a kofar gidan har da yan Sanda masu gadi gida me kyan gaske,maza yan siyasa sai kallo na suke domin sunga baiwar kyau wajena,da gani kuma sun San ba yar siyasa bace ni kamilalliyace ni yar mutunci,salamu alaikum nayi musu sallama tare da gaishesu sannan nace Dan Allah yau Hon yana nan? Suka ce ae kinyi sa'a yana gida muma shi muke jira,amma tunda ke macece bari mu rokar miki masu gadi ki shiga kice wajen matar Hon kika zo,ai kuwa haka akayi nan take yan Sanda sunga kyau suka ce na shiga,
nayi godiya na fada gidan cikin nutsuwa,wata yar aiki ce ta nuna min kofar shiga ciki,nace tayi min jagora zuwa wajen Hajiya,har nan ta kaini sannan ta shiga tare da sanarwa Matar Hon,cikin Sa'a aka ce na shiga har ciki yar aiki tayi min iso,matar Hon yarinya baza ta wuce 24yrs da ganin irin kyau da Allah ya min yasa ta tsaneni kar na kwace mata miji,nan take naga ta canja fuska ta Mike tare da miko min Dubu biyu tace na tafi an sallameni,babu bakin magana jiki ba kwari na karba na dau hanyar fitowa kenan kicif sai ga Hon ya sakko daga sama da katon cikinsa yana shafa tumbinsa,ya kalleni nan take ya lashe bakinsa tare da yi min signa da Ido kamar kwarto,ni dai na fice da sauri daga palon.
Matar Hon tana Alhaji ga abincinka amma tuni yace Hajiya na fita Office ana jirana ya fito da sauri yazo kusa dani a bakin gate,da sauri na durkusa na gaisar dashi sannan na fada masa abinda ya kawoni nan take yace ai karamar matsalace wannan ya bani card dinsa yace na samesa a guess house dinsa,na tsorata amma dai na karba nace sai nazo na fito daga gidan na tafi gida ina murna ta.
Ban fadawa Ammah inda naje ba nasan fada zata min kawai nayi shuru,washe gari kuwa dama yace 5pm zanje gidan da yace,ba tsoro na shirya na tafi ba wahala na gane gidan na fita daga Napep,Naga gida rafkeke na kwankwasa sai ko ga me gadi ya bude yana ganin budurwa yasan irin matan da Hon ke Tarawa kullum ne da fara'a ya tarbeni yace shiga yana ciki,nan ya min iso har cikin palon Hon,sai lokacin tsoro ya kamani,lokacin na hango Hon daga shi sai Singlet da gajeren wando yana latsa waya,da fara'a yana washe baki yace zauna mana kyakyawa me kyan sura,Nace ba sai na zauna ba idan zaka taimakeni to ka bani dan Allah,dariya yayi yace zo mana ke ya kike abu kamar bagidajiya ina ganinki wayayya zo muji dadi mana sannan na baki kudin a wuce wajen kawai,tsorata na karayi na fara ja da baya nace ni ance ba kyau namiji ya rike ma mace hannu nidai zan gudu,Hon yayi dariyar Kuruciyata yana lallabani yana hure min kunne amma naki matsawa ko kusa dashi,tasowa naga yayi ya taho jikina ya fara shafa min fuska yana kokarin cire min Hijab,yana sakin wani Gurnani ai da gudu na ja baya a rude na bude kofar na fice da gudin tsiya ko me gadi gani yayi kamar walkiya na bude kofa na fice wufff.
Ina Haki na fito da matsiyacin gudu na cukwikwiye Hijab dina na tattara skert dina ba takalmi a kafata tuni na watsar dasu,Na samu gefen titi kawai na Mike na dinga tsinka uban gudu ka rantse yan Mafiya ko Zaki ne suke Bina,ga unguwar shuru irin ta masu kudi ba kowa ba a ganin ko mota a titin,can naji karar mota ta bayana tunanina Hon ne haba ai sai na kara karfin gudu na yi nake kamar numfashina zai fita,a hankali motar take tafiya a saitina sai lokaci ina gudu na dan kalli glass din window din an sauke glass din ana ta min magana ta ciki gudu nake iya karfina da karfi nace wlh bazan tsaya ba Hon tsinanne dan Iska ina ta zagin me motar ji nake Hon ne ashe Aayan ne yake ta Bina da motar yana sheka dariya yanda yaga ina uban gudu kamar na tashin kiyama,tsabar mugunta sai yaki yin magana kawai yake ta Bina da mota duk inda nasha kwana sai yasha da motar yana ta dariya har sai da karfina ya kare tas na fara kokarin tsayawa Ashe ban sani ba idan gudu ya cika yawa yakai wani limit mutum kasa tsayawa yake da kansa sai an rikeshi kawai zai ta gudu ne,ina so na tsaya ina kokarin tirjewa amma ina gudu kawai nake falfalawa na fashe da kuka kuma ina ta gudu na kamar masifa har dai da kyar na samu na rike wata bishiya sannan na zube a kasa wajen ina maida numfashi,Dai dai lokacin Saurayi Aayan yana ta dariya harda kwalla sannan ya take birki a inda nake Kuuuuu yana ta dariya yana rike ciki,sai da na Huta sosai da sosai sannan na tashi tsaye ina karkade jikina,sai lokacin na hangoshi cikin motarsa Ashe shine ba Hon ba,kawai nima abin ya bani dariya kamar sabuwar Kamu na dinga sheka dariya harda kwalla,a ransa yace lallai yarinyar nan da alama mahaukaciya ce ko Aljanu gareta,na kalleshi saitin window na daure fuska sannan na maka masa harara,ai ko ya fito a fusace na firgita ba damar guduwa dan na gaji ina ji ina gani ya fito ya zabga min Mari sannan ya jefar dani a kasa keee ya daka min tsawa ba a min ko kallon Banza mind ur fucking Business,bana jin turanci tunanina yasan Business dina dana keyi a gida kawai sai nace dama ai ni Kasuwanci na nakeyi ina ruwanka dani haka kawai sai ka dinga cin zalina dan kaga bamu da kudi,ai kudin naku bana tsoron Allah bane tunda ba a taimako sai yawo a mota ana zalinci,tsaki yaja me karfi cikin takama ya koma labebiyar motarsa fuuuuuuu ya figi abarsa.
Ni kuwa na turo baki tare da cewa Allah ya isa wlh duk ranar daya mareni again Allah sai na rama za a gani ai,nan na gama Kuri na sannan na tafi gida abina.
Washe gari ban tsorata ba na kara shiri na tafi gidan Vice Chairman neman taimako amma haka na yini ban samu ganinsa ba sai yaronsa,Nace dan Allah wajen Vice nazo idan baza ka damu ba ka min hanya na ganshi,cikin daure fuska kamar zai bigeni ya hayayyako min da masifa ke malama an fada miki ya tafi Umrah bazai dawo yanzu ba,irinku dama yan mata makaryata da Iyayenku sabo da son abin duniya sai ku fara karya kuna zuwa Maula daga nan a lalata Ku yan iskan yara,har nawa kike amma har kinsan yawon Maula,nan dai yaron Vice ya min tatas na baro kofar gidan da takaici.
Ban dai kara hakura ba washe gari haka na kara shiryawa na nufi gidan wani Commissioner na Ilmi,a bakin gate kofar gidan na yini ina jira ko za bani dama na shiga ciki amma masu gadin ko kallona ba wanda yayi,har zan tafi sai ga wani ya taho da Jibgegiyar mota kida na tashi Malam nan take mukayi Ido hudu da wani Saurayi black Handsome dan gayu,sai kallona yake,ina tsaye aka bude masa gate,sai wani kallo yake Bina dashi kamar tsohon maye,nan take naga ya sauke glass yana murmushi tare da yafito ni da hannu wai naje,da sauri na karasa,sai kallo yake kare min tun daga sama har kasa yace yan mata wa kike nema?nace wajen Babanka nazo Commissioner na Ilmi da alama kai dansa ne ko?murmushi ya kara saki yana min kallon irin na yan duniya,yace ae dansa ne ni ya akayi?Nan na sanar masa taimakon da nake nema akan rashin lafiyar Ammah yace wannan ai karamar matsala ce Beauty,kawo na sa miki Number ta,nace ni bani da waya mu talakawa ne,baki ya tabe tare da dauke kai yana cewa ai kuna da amfani ta wani fannin,ban gane me yake nufi ba kawai naga ya miko min wata waya sabuwa dal a kwalinta amma karama ce Nokia me kyan gaske,yace kinci sa'a Baby na siyo wa yaron Mama waya karbi ki rike wannan ga sim card sabo bari na sa miki zamu dinga magana ta waya kafin Abba ya dawo sai a kaita asibiti.
Tunanina da gaske ne ba tunanin komai nace nidai ka bar wayarka amma ka bani Number dinka zan nemeka kaji,yace karbi karki damu kyauta na baki yan mata kamarki ba waya ai abin kunya ne,cike da tsoro dai na karba hannu na rawa garin zai miko min sai da ya shafi hannuna yana sani harda lumshe ido,da sauri na dauke hannuna ina godiya,da kansa ya hada min wayar da komai ya sa min Number dinsa ciki ya dauki number ta sannan ya miko min Dubu biyu wai na hau Napep,naki karba kawai sai ya zubar min da kudin a kasa yana shu'umin murmushi ya figi motarsa ya shimfida cikin wannan gida na alfarma,na dade a tsaye ina tunani kawai dai nace Allah gani gareka na kwashi kudin nayi gaba abina.
Danaje gida Ammah dan kar ta hanani amfani da wayar sai nayi karya nace Ammah yau dai na karbi kudin adashina na gidan Haule kinga na siyo waya sabo da baza a ace a gidan nan bamu da waya ko daya ba,nan suka dinga murna da tsalle,Ammah harda sa albarka tana murna dama yaran Zamani badai zuba karya a kifar da iyaye a corner can.
Next day ban hakura ba dai sabo da ina tsoro kar fa nazo ba a samu tallafi wajen Dan Commissioner ba kawai na shirya na Tafi gidan Dan Majalisa na tarayya da suke Zama Abuja,ni dai nasan ba lallai na sameshi da family dinsa ba domin wasu ma ba a Sanin inda gidansu yake buya suke su canja unguwa ko state dan kar a je musu Maula,ni kuwa tsabar jaraba sai da na kwakwulo gidan da tambaya tun daga unguwarmu nake bin gidajen manya ko wani ya sani,idan ance me zaki yi sai nace sako wasu zasu kai gidan da haka aka gwada min gidansa amma fa basu cika Zama a kano ba kawai dai zanje na gani ko me gadi na samu contact Dinsa ya min hanya, haka na fada Napep sai gidan Dan Majalisar tarayya Abuja,gidan kansa abin kallo ne sabo da ya hadu karshe.
Securities ko ina a gidan harda mutane a kofar gidan Yan maula,haka na kutsa kai cikinsu tare da tambaya ko me gidan yana nan suka ce ai rabon da yazo kano ma yau Shekara biyu kenan.
Baki na bude tare da mamaki wani ciki yace sai dansa Yarima Bobo da ake aikowa da sakon yan siyasa ana kawo musu,yanzu ma shi muke jira ya fito kin San shi a kwai gadara da wulakanci sai yaga dama yake fitowa ya bamu sakon Hon Rep,
Nan take nace aiko sai na jira dan nasa dan Ubansa ko shi waye,ina nan tsaye na gaji da jira har 2pm a wajen nayi Sallah saman dankwalina wata me tallan Fura tana zaune a kusa nace ta dama min ta Hamsim,haka ta dama furar tasha Nono me kyau da sugar, nace juye min ita a leda ki kulle,haka ta bani katon Dauri a farar leda na Fura da nono na bata ,sannan na siyi yogourt yar hamsim a leda tayi kankara,ina fara sha sai ga wani dan sanda yace Yarima yace Ku shigo ya ganku zai wuce Flight dinsa ya kusa tashi,da sauri mazan suka fada gidan yuuuuu,ni kadai ce mace haka na danna kai ciki ina Shan furata a leda yanda nake zuka kamar jariri ya kama Nonon uwarsa haka na lumshe ido ina tsotsa Malam ba ruwana.
Muna shiga ciki nan na hangame baki wajen kallon irin haduwa na gidan ba a magana,Saurayin muka hango chocolate dashi ya hadu sosai ga kyau ga iya wanka abin kallo yana kamshi yasha light blue shadda yana sheki ga motoci a gidan birjik,muka karasa gabansa yana zaune a wata farar kujera yana faman yanga da gadara,ido muka hada dashi yasha mamaki ganin harda yarinya haka,dan a wajensa bana Sahun yan mata
Ya fara sauraron wasu kawai muka ga Securities sun wani gigice sun nutsu waje daya tare da bude gate jikinsu na rawa,sai ga wasu motoci dalla dalla sun shugo gidan sun kai biyar kamar nasan motocin,ashe kuwa shine domin Saurayi Aayan ne me tashen kyau da Naira.
Gani mukayi Yarima ya fadada fara'arsa tare da mikewa ya tarbi Aayan da alama abokaine harda wani tafawa suna dariya,Yarima Bobo yace amma kai dan Iska ne Aayan tun safe kace zaka zo kasan yau zan koma Uk amma ka bata min time yanzu na daga flight dina sai 12am na dare,Murmushi Aayan ya saki cike da izza ya dage masa gira daya kana yace to ya akayi ne man sauri ka gama da mutanen nan naku kasan ban son jira,Yarima yace ai kai dan Iska ne ga sit can,kusa da mu ya zauna can nesa a wata kujera ta yan gayu,Juice aka kawo masa yana korawa,a raina nace Allah sarki talakawa mu ko ruwa babu me bamu.
Yarima yana ta ganin mutane yana sallamarsu da kudi,sai yace pls Ku mazane kuyi hakuri na sallami yarinyar can tunda macece,a raina nace Ashe yana da kirki,nan yace ke zo naji na sallameki sai lokacin Aayan ya kalli inda nake muka hada Ido,da mamaki ya kalleni lallai yarinyar nan wato har maula take zuwa gidan masu kudi sabo da son kudi,ko dai bata da iyaye ne oho,yana gani na karaso gaban Yarima ba tsoro na durkusa gaban Yarima tare da cewa ina yini?yace lfy tashi tsaye ki fadi abinda ya kawoki sauri nake ina da bako,ina durkushe a gabansa kaina a kasa kuma ina ta zukar Fura ta kamar yarinyar yaye,idan nayi magana daya biyu na zuki furata,babu wanda baiyi dariyar abinda nake ba kowa yana ganin ai yarinya ce,shi kuwa Gogan Aayan a zuciyarsa yake Dariyar kwadayi na,kuma sabo da kuruciya a gaban kowa ina mace ko dai bani da hankali ne. na karanta masa ciwon Mahaifiya ta,yaji tausayina kuma lallai yaga mu abin taimako ne,sai yace jirani a gefe bari na sallami sauran,
nan na Mike na koma gefe,Aayan ko kallona bai kara yi ba har Yarima ya gama da mutanen kaf suka tafi ya rage daga ni sai Aayan sai Yarima,yace zo ke,da sauri na karasa gabansu su biyu,yace ina babanki ko ya rasu? Bana so na fada a gaban Aayan wanda ke latsa waya,sai nace Sirri ne sai dai idan zamu koma gefe na fada ma,murmushi ya saki yace to ya Mike ya taso na kara kasa da murya da rada nace bacewa yayi ba a San inda yake ba,kawai ko guduwa yayi wa ya sani,dariya Yarima yayi yace to shike nan ki kawo takaddun asibitin naki mu gani,nace to ai naji ance zaka yi tafiya,no ki jira zamu fita da frnd dina sai mu saukeki ki dauko takardun,a tsorace nace tab wancan masifaffen ne zai yarda,kin sanshi ne?ya tambaya,nace ae na sanshi kullum sai ya mareni idan ya ganni,murmushi yayi yace to ki jira ai motata zaki shiga,murmushin da nayi shi ya tafi da Imaninsa ya tsaya yana kallona,sai can ya dawo hayyacinsa yace ina zuwa ya koma wajen Aayan dake ta faman cika yana batsewa,Yace kai Yarima kasan fa ban son jira wlh zan tafi ka tsaya kuyi hirar,ba class ba komai,Sorry let's go,Aayan da mamaki yaga na shiga Motar Yarima shima cike da takaici ya shiga nasa motar suka ja muka bar gidan cikin zugar motocinsu,sai da aka zo kusa da gidanmu suka tsaya,Yarima yace yarinya yisauri ki dakko mana na gani,ina fita na kwashe da gudu na karasa gida na fada daki na ebo kamar kiftawar Ido na fito da wani gudun kowa ya ganni sai ya tsorata ko wani abu ne ya biyoni,da gudu ina Haki na kawo masa takaddu ya sauke glass kasa ya karba ya gani tabbas da gaske nan ya miko min card dinsa yace ga Number ta na Nigeria dana waje ki kirani kiji,da sauri na daga kai sama,ya zaro Dubu goma ya bani yace gashi ki siyawa marar lfy ko ruwane,godiya nayi na karba, Yarima yace ki daina gudu kinji yarinya ba kyau mace tana gudu,da ladabi nace to na daina ai tsoro naji kar Ku tafi sannan na juya na dau hanyar shiga gidanmu,sai da naje bakin kofar gidanmu zan shiga na juyo baya sai naga Motar Yarima sunyi gaba sai Na Aayan yana kallon inda zan shiga kamar Munafuki muna hada Ido suka figi motarsu fiii suka kara gaba abinsu nima na shige gida.
Still ban gamsu da taimakon Yarima ba sabo da yan siyasa basu da tabbas ayi maka karya ka dauka gaske ne kayi ta jira ana ja ma rai,don haka kwana nayi ina tunanin cewar wanne gida kuma zanje nan take na tuno da wani dan kasuwa Hamshakin me kudi a GRA unguwar su Aayan,har matsuwa nayi gari ya waye na tafi,ga kuma gidan wata Mata nan ma Naji ance tana taimakon Talakawa.
Sannan Zan biya sakateriya ta unguwarmu wajen Kansila Adamu me tallafi ko Allah zai sa ya shigar da sunana cikin masu karbar tallafin Manoma na Gomnati.
Kuma duk a gobe zanje wani Training shima ko zan samu a dauki sunana cikin masu koyon sana'a idan ka gama a baka jari.gaskiya gobe ina da tsare tsare da yawa,don haka kosai ma kadan na soya na barwa su Meenat komai tare da shiryawa yau ba Hijab nasa ba mayafi na yafa nayi kyau yau doguwar rigar material nasa red and green mayafinta green da takalmin robata baki,Ammah nayiwa Sallama ta zuba min addua sannan na fita da addua a bakina.
0 comments:
Post a Comment