Masifa na fara wacce mafita uban wa yace muku mijina nada matsala idan banda ta Family nifa bana son Sa ido Meenat ku kiyayeni,Allah baki hakuri ai gani mukayi mu da ke duk daya ne ba wanda ke boye maganar dake damunsa yaushe Mama Mufee ta dawo mana haka bamu sani ba bayan Ammah ta bar mana wasiya rike zumuncinmu,yau miji yafi mu daraja shike nan.
Jikina yayi sanyi nan nace ai kune wlh bakwa ji sam Amma akwai matsala Meenat,lokacin Aayan yana can yana ta faman jira nazo muyi baccin mu Amma shuru shuru sai tsaki yake faman ja yana juyi.
hannun Meenat na rike muna kwance nace Meenat kuji ni ina cikin neman taimako na addua Asara ta hauni,na tafka babbar asara,jikina da kyauna duk nema yake ya kare a banza,jibi uban Hips dina,kalli tun ina karama Allah ya hore min na shanu masu kyau da birgewa,kalli skin dinmu,amma a haka aka ce idan kana da kyau ka kara da wanka kalli yanda nake zabga uwar kwalliyar da shiga iri iri a gidan nan,yanda nake kashewa jikina kudi bai tsaya a nan ba sai da na dangana ga zuwa gidan gyaran jiki na biya makudan kudi an tsunami nasha an gyara skin,lungu da Sako anyi masa filla filla Amma ku kanku da kallona kun san na kara kyau da canjawa,kalli yanda nake sheki da walwali,kalli yanda nake kamshi ko abu na rike sai ya tafi da kamshi na,kalli ku kanku yanda kuka rude da kyauna gashi komai ya kara cika duk da cewa kun sanni Amma sai da kuka Koka yanda nake sheki da uban kyau,
Meenat tace mun gane,to asarar tayi muni da kashe kudina yayi yawa Amma kun san Aayan asiri na jikinsa har yau bai warke ba,bazai iya komai ba sai tabe tabe,kinga ko ba komai Sabo da lafiyarmu ma ya dace ace an daina taso da sha'awa kuma taki kwanciya,kamata yayi ace mijina yana alfahari dani kamar ko wacce mace,amma ni kaina nake zargi ko nice ban iya yanda zansa yayi amfani dani ba,bayan wannan asarar kudin gyaran jiki so nake nima ace kwalliya ta biya kudin sabulu ace mijina yana yabo na yana susucewa a kaina,amma ace ina sheka Ado bana ganin ya zauce ina kanta.
Dariya Ma'eesha tayi tare da cewa wlh ya susuce kece bakya ganewa kinga yanda yake binki da uban kallo duk inda kika Gilma,kuma kin gama zautar da shi,bakya ganin yanda yake kishinki me kike so kuma? Meenat tace akwai matsala ace mijinka bazai biya bukatarsa da kai ba,kuma ribar soyayya da aure a hayayyafa,to ki kwantar da hankalinki kinga Wani Saurayina a Maiduguri dan gidan gawurtaccen malamin Sunna ne Malamine na Sunna basa tsafi ko shirka addua zasu baka kayi suma su tayaka kuma ba kwandalarku ana dacewa,Maeesha kin tuna Masa'udu Shekare wanda akace yayi shekara da shekaru a Cikin Uwarsa kwantacce kafin a haifeshi? Wanda ke zuwa kusan kullum yana damun mu da Fassarar Hadisai? Ma'eesha tayi dari tare da cewa au wai Shekarau kike nufi? Dalla Shekare yake ba Shekarau ba,ae gaskiya ne kam malamai ne,ni kuwa nayi tsalle na dire cewar Bazan tonawa mijina asiri ba gaskiya,Meenat tace to kin gwammace ya zauna da cutar wani abun sai ana fada ake samun mafita,ai ba wanda yafi karfin cuta a duniya ba a kunya a cuta gwara a daure a fada muji shawara ina da Number su,kinga ko a nan talaka cikin Samarin za suyi rana,shi yasa ba a raina dan Adam kowa da ranarsa kuma da baiwarsa,nace haka ne Meenat Allah ya kaimu gobe sai a kirashi.
Da haka muka fara baccinmu bilhakki,Aayan yana can yana fama da rashina,sai faman jirana yakeyi har ya gaji da latsa waya da laptop ya mike nan take ya sakko kasa tare da nufo dakin su Meenat,Yana zuwa knocking ya shiga yi yaji shuru sai da kyar Meenat ta farka taji tsoro ko abin cutarwa ne tace Mufee ku tashi yan Fashi ne,Da Sauri na fada lungun Bed nayi flat,Maeesha ta fado kaina itama,Meenat ta mike tare da bude sip ta shige ciki ta dunkule waje daya,jikinmu na rawa gashi sai bugawa akeyi,Da kyar nace waye? Nine naji Muryar Aayan,Nan Naja tsaki ina tsinewa Meenat dake fitowa daga Cikin Sip,Maeesha tace Amma kin cuce mu saura kadan hawan jini ya kamamu,a hankali na bude kofar kawai naji yayi sama dani ya tura kofar da kafa ya daukeni kamar Jaririya haka muka je har Bedroom dinsa, nace me ya faru muna baccinmu wlh ka Tsorata mu,Murmushi yayi tare da cewa akwai wani babbar kyauta da zan miki amma ba yanzu ba,tunanina kudi ne na fara Murna nace sai yaushe? Hararar wasa ya min tare da cewa nasan kyautar tafi kudi tafi komai na duniya a wajenki Amma sai ranar nima da nake cikin nishadi wanda soon nake Sa rai,a kirji na cijeshi kadan tare da cewa Allah ai ni babu abinda yafi kudi a wajena a yanzu ko mene shi tunda ba kudi bane na daina murna.
Murmushi yayi me sauti tare da cewa wannan kayan baccin fa? Karki kara Sa min su sunyi nauyi da yawa gashi sun matseki sosai Bazan iya ciresu da wuri ba,Ai yau banyi niyyar kwana nan ba dumin yan uwana nake ji, a kunne ya rada min pls ciresu ni ki daina Sa su bana sonsu kawai,suna miki kyau Amma wahalar cirewa zasuyi harda wani Wando me tsayi fa, kunya nake ji bana son na cire sai na daga zan cire sai na fasa shi kuma ya kafe ni da ido yana faman kallon kirjina tun kafin na cire ma,nace ka kashe light to na karasa a shagwabe kamar zanyi kuka,Kara wani kishingidewa yayi kamar Sarki yana kallona dai dai tare da murmushi,a hankali naji muryarsa yace Babyna kin san me? Nace a'a sai ka fada yace Kinfi kowa kyau a duniya wanda na taba gani komai kin hada Allah ya baki,Murmushi kawai nayi nace hmm tun baka je Palace din ba kenan ka gano haka,Baki ya bude dan baiyi tunanin nasan harkar ba ma,idona na rufe ina dariya hannuwa na biyun ya rike kam yana kare min kallo harda wata Palace da ake zuwa dama? Nace uhm am just kidding u fa,Sai kin fada min naji,Nace to kaima ka sani ai Kingdom kenan ai me matakan tsaro,au wani sunan ne wannan? Nace ai Baza ka gane ba sai ka tsallake border Amma ai kaima yaron ne tunda ba sani kayi ba sai lbr kamar ni.
Ido ya dan ware kadan tare da cewa bacci nake ji pls cire kayan mu kwanta,jikinsa na kalla daga shi sai Boxers dan gutsul,Haka cike da kunya na fara zare rigar tun kafin na zare ya fara Murza Albarkatun Kirjina.
Abbi an dawo ana jiran Boka Shakylgancy ya aikata Aiko sai waya da sukeyi,Cikin dare Boka ya Cillo tsafinsa zuwa jikin Mufeeda sai akayi dace Aayan yasa munyi wankan tsarki don shi ba a ko kara 1hr da najasa a jiki ko na Sunna ne,Yace to Ki daure muna Nafeela ko raka'a biyu ne duk dare mu daina bacci ,Mufee ba musu na bi bayansa muka fara Nafeela,lokacin Boka yana ta jefo tsafinsa baya Tafiya,ya buga ya buga shuru,bayan mun idar sai da sukayi dogon Azkhar lokacin boka yana ta faman jefo bala'insa Amma shuru,Har ya hakura yace sai gobe zai kara yi.
Washe gari da sassafe ya fara tsafin irin ko muna baccin Safe kawai lokacin nan ma azhkar mukeyi na Safiya,da rana bai samu nasara ba lokacin karatun Qur'ani Meenat take kara min,yamma ya gama shiri tsab lokacin kuma Azhkar na yamma nakeyi zuwa Magrib,still daga Magrib zuwa Isha duk bashi da sa'a.
Kwana na biyun kuwa na fara period Amma ko yaushe ina da Alwala,ga addua a bakina har kitchen ni ba wake wake nakeyi ba sai addua nan ma boka ba labari,lokacin kuma mun kira Saurayin Meenat Shekare ya hada mu da babansa na bashi labarin komai nan Malamin ya bamu adduoi ta waya da yanda zamu yisu, na fara ma yau kuma Ma'eesha ta tuna min zamu je gidan kawarsu ana bikin yayarta,haka na damu Aayan ya barni naje da kyar ya yarda yace Amma sai daΓ Ameer ya kaimu,Haka muka ci uban kwalliya bana cikin sahun matan aure,a gaban Aayan sai nasa Katon gyale Amma muna shiga mota na cire gyalen na ajiye a bayan motar Ameer gashina na saki jelarsa,abinda mata keyi yanzu kenan Ba a gane wace matar aure,nima sai na birge kawai,muka je Dinner wurin 9pm ana ta rawa da kade kade,Har wurin 11pm muna ciki ana cashewa na manta da wata addua ma gashi nasan mijina bai so a kalle masa ni,amma na zalunceshi bai sani ba na bari Maza na kalle min sura tare da gashina wanda nasa ne shi kadai Allah ya halitta masa,tunanina na masa wayo ban san kaina nayiwa ba,har shiga filin rawa nake muna gogaggaya da matan manya kowa ya ganni yasan matar hamshaki ce ni ko yar gidan wani ce yanda nake zubar da Naira.
Abin haushi Boka shi aikinsa yakeyi dama aikinsa ne kullum ta nan yake samun kudinsa kamar yana Office ne,kuma basa saurarawa kullum aiki sukeyi suna gwada sa'arsu ko zasu samu wata dama daya tak su samu nasara musamman yare da zaka ga sunfi Musulmin bahaushe Amana basa karya alkawari.
Wufff Ya turo min Aljani ta tsafinsu yana zuwa yaga na shagala ya samu dama nan yayi wuf zai shigeni Amma ba ta inda zai iya shiga jikina da wuri ai tuni ya ankara cewar Gashina gashi nan a waje nan fa yayi wuf ya bi ta gashin ya shiga jikina,nan take naji kaina ya fara ciwo sosai sai nayi tunanin ko Gajiya ce,kawai nace suzo mu tafi,haka muka dawo gida ina fama da ciwon kai me tsananin gaske kamar kaina zai tarwatse,na fara Hawaye na samu Aayan a daki yana jirana yana ganina haka yace mene lfy?,nace kaina ciwo kin gani ko sai da nace karki je kika ki yarda,zo ki kwanta na baki magani,kafada na make tare da cewa Bazan sha ruwan gidan nan ba,indai ruwane na gidan nan Bazan sha ba,Aayan ya zata tsokanarsa nakeyi yayi dariya yace kwanta,nace na rantse Da Allah me Rahma in na kwanta a gidan nan yau Allah ya tsine min albarka,bude baki yayi yaga fa da gaske ne dan ba alamar wasa a tare dani,yace to ina zaki kwana nace wani gidan Amma ba wannan ba,kaina na dafe nace wlh ni a fitar dani daga gidan nan idan na zauna a gidan nan shegiya nake,wlh in dai na kara kwana a gidan nan Allah ya tsine min albarka wannan tsinannen gidan dukka ma tsinannu ne ku yan gidan,Aayan ba a kanta ya fara ganin hakan ba tunda Mommynsa tayi da suka mata asiri haka matarsa Nafisa tayi itama da Ruky, Amma ai munyi alkawari dake baza ki bar gidan nan ba,Alkawari? Amma ka cuceni Allah ya Isa me zanci da wannan gidan,nan na sauka kasa da gudu na fara hado kaya ta ko ina,nace Meenat ku tashi mu tafi,sis lfy? Zanci kutmar ubanku dan uwarku dan ubanku ku tashi mu tafi wlh idan baza ku taho ba ku zauna,Ba yanda su Meenat basuyi dani ba Amma zagi kawai suke sha iri iri,haka Ma'eesha tace mu Bita Meenat kar a samu matsala ta fada hannun bana kirki ba,haka suka kwashi akwati har Uku,Aayan tuni ya fito ya nemi Ameer ya kora masa bayani,nan Ameer yace shawara ka bawa Meenat key din Wani gidan naka can daban sai na kaisu can su zauna,Haka Aayan a gigice ya mika masa yace kuje dayar sabuwar GRA ka gane gida Dana siya last wk pls ko me Mufee na take so a bata, kar ka dawo gidan nan ku zauna ka kula dasu kafin nazo,Ameer yanda yaga Aayan ya fita daga hayyacinsa gaba daya abin ya bashi tausayi kamar ya masa kuka ya ma rasa me zaiyi gaba daya baya hayyacinsa za a rabashi da Mufee dinsa wayyoo.
Yana gani Yanda Mufee ta gigice sai gumi take hadawa ta fita da gudu har Jikin mota hakanma da kyar Ameer ya lallaba ta hau motar tasa cewa tayi in dai motar ta gidan ce baza ta hau ba,Aayan ya Kira Meenat da suke kuka ganin abinda Mufee keyi ya zarta hankali,kwantar musu da hankali yayi tare da cewa karku kara kuka kinji ko,kai kawai Meenat ta daga Masa Kudi ya mika mata masu yawa yace rike zanzo ltr kuyi amfani dashi.
Meenat ta karba ta fada Mota suka tafi,Abbi yana Saman Bene yana dariyar mugunta dan sunyi waya da boka,Aayan Innalillahi yake maimatawa kawai sai Hawaye sharrrr ya kwararo masa da kyar ya lallaba kansa ya mike,ya fito a fusace fuuuu sashen Abbi ya farayi yana shiga ya shaki wuyan Abbi ya bugashi da Bango nan take idon Abbi ya firfito ya shakeshi iya Shaka sai kakari yakeyi,su Haneefa suka fara ihu nan fa su Hajja da kowa ya hallara ana kokarin cire Aayan Amma an kasa Abbi na neman shekawa Lahira,Hajja ta fashe da kuruwa za a kashe mata da ta fara Dukan Aayan,Aayan ya make Hajja ta fadi kasa dabar yace wlh akan a taba Mufee gwara kowa ya mutu a gidan nan bana ubanku bane,ku bar min gida, nan ya saki Abbi ya shiga daki daki yana watso musu kaya tun daga Sama zuwa kasa komai nasu jefowa yakeyi,nan take yace Duk na kwace aikinku kar na kara ganin kowa cikin ku a Company na kuma duk dukiyar bata Daddy bace bare kuce dan uwanku idan baku sani ba ku tambaya kuji kudina nane dukiyata ce gaba daya,Nan fa suka rude harda Hajja sun san tasu kuma ta kare yace wlh wlh ko mota daya baza ku fita da ita ba,nan take yace na baku 15mnt ku bar gidan nan,Nan ya Kira Sojoji har mota biyar suka zo da igwa ta feshin ruwan zafi tafashashe,ba shiri suka tattara kayan da zasu iya dauka na sawa suka fara fita manya da Yara daya bayan daya Maza da mata suna kayi hakuri mun tuba zamu karya asirin,Aayan yasan karya sukeyi kawai yasa Sojoji suka rakasu kaf suka bar gidan,Abbine bai fita ba wai zaiga Daddy haka Hajja ma tace dole zamuyi magana da Dana ehe,nan ma Aayan yasan so take Daddy ya tursasa shi dole ya Barsu kawai yace ba inda zasu Sojoji suka tasa keyarsu sai da suka hau Taxi har guda hudu sannan Aayan ya sallami Sojojin ya koma part din Daddy.
Tunda Daddy ya ganshi gabansa ya fadi yasan ba lfy ba,Gefen Bed din ya dire gwiwoyinsa tare da daura kansa saman Bed din da Daddy ke kwance ya fashe da wani kuka me tsuma zuciya,Daddy ma tunda yaga Aayan yau yana kuka haka to matsala ta afku babba ma kuwa,a hankali yace me ya faru ne My Son? Nan Aayan ya sanarwa Daddy komai,Daddy murna ya fara yi Aayan yanzu yana son matarsa,amma bai ji dadin abinda ya Samu Mufee ba Amma yasan Allah na nan kuma da saninsa, Daddy ne ya kalleshi be a Man Aayan kamar mace ba abinda zai faru Insha'allah muna addua karka damu nan Daddy ya shiga lallashinsa sosai yana kwantar masa da hankali har ya hakura yace Daddy bari a rufe gidan nan kawai mu koma wancen,sai lokacin Daddy ya san Aayan ya kori duka danginsa har Hajja mahaifiyarsa,fada ba irin wanda baiwa Aayan ba ko ba komai ai Uwa Uwa ce sai na bita zan shiga Aljanna,Aayan yace ai zan dawo dasu Amma ka kyalesu Daddy su dandana wahalar,shi dai Daddy masifa ya dinga yi Amma Aayan yayi mursisi dashi haka yasa masu kula da Daddy suka daukeshi har mota suka koma sabon rantsatsen gidan Aayan wanda su Meenat ke ciki yanzu,ni kuwa sai da muka fito daga gidan hankalina ya dawo jikina,sannan na samu nutsuwa ko ciwon kai bana ji sai ma hira data barke a tsakaninmu dasu Ameer.
Gaskiya gidan ya hadu fadar kyansa da haduwarsa bata lokaci ne,nan Ameer ya zabi Bedroom,haka su Meenat ma,nima sai da na zabi nawa sai yanzu nake tunanin ina mijina Aayan ina ya shiga? Ameer banga Aayan ba lfy? Ameer yace yana nan yanzu zai dawo unguwa yaje,nace Ok to Amma bai fada min ba,Ameer ne ya shige Room ya Kira Aayan yana sanar masa me nace murna Aayan ya farayi yace gamu nan zamu karaso,Aayan suna karasowa yasa suka kai Daddy can part dinsa daban tare da abincinsu gaba daya sannan ya wuce Direct part din da muke gidan baya bukatar gyara ko ina fes yake Sabo da ma'aikata ne ke yi kullum,wanka nayi da ruwa me zafi daga ni sai towel na gama shafa turaruka na masu azabar kamshi ina taje gashina cike nake da tunanin ina Mijina ya boye,ina haka sai ji nayi an rungumeni ta baya wani shock naji da ban taba jin irinsa ba a duniya, da Sauri na juyo tare da rungume Aayan a jikina ina kare masa kallo yanda duk ya wani hargitse me ya faru Muka dawo nan gidan My Man? Kallona yayi yace kece kika ce bakya son wancen sai na canja mana nan,na cika da mamaki sosai Hawaye ya zubo min sharrr,A hankali ya girgiza min kai tare da kawo fuskarsa saitin tawa sannan ya fara lashe min Hawayena da suka ki tsayawa,saki na yayi ya shiga toilet da Sauri,ni kuwa ina nan tsaye inda ya barni ina Hawaye har yayi wanka da Komai ya fito da towel yana goge jikinsa,Sai da ya gama feshe feshen turarukansa tare da shafa Lotion sannan yasa Boxers still ina tsaye ina ajiyar zuciya na Kukan da nayi,Har gabana ya karaso sannan ya tsaya kamar zai shiga jikina a hankali cike da nutsuwa ya hade hancinmu waje daya yana gogawa a hankali ya ciji kunnena kadan,nayi yar kara tare da murmushi kadan yanda nake jin sha'awar yau ta wuce hankali ban taba jin irinta ba ban san dalili ba,shima a wajen Aayan hakan take Amma yasan ba lafiyayye bane,Bakinmu ya hade waje daya kalar numfashin da muke fitarwa ya zarta hankali,a hankali ya zare min Towel dina tare da jefar dashi gefe ba tare da na sani ba sabo da dadi, Saman Bed ya daura ni shima ya kwanta yana min abubuwa masu rikita tunani yau a Romancing dinmu yafi na kullum da mukeyi mun kasance cikin Nishadi da jin dadi, yanda Aayan ke Surutai ka rantse babbar Harka ake bugawa,cikin kalamansa yace My wife pls love me, say u Love me,do u love me?,sabo da na tsokaneshi nace a'a ni dai,cik ya tsaya da tsotson albarkatun kirji na tare da shafasu,why Baby nan da nan naga ya birkice min,cike da shagwaba kamar zan narke nace ai baka so na tunda ko yabona bana ji kana yi,kuma ma ai ni baka lallaba ni kana ji dani kamar kwai,duk ba wannan ne zai hanaki so na ba sweetheart,Tunda bakya so na Bazan miki dole ba yana gama fadar haka ya mike zai bar saman Bed din, na riko hannunsa ya dawo saman Bed tare da cewa da cewa Lfy? Bana so na takura miki ne, a hankali na kara bakina a saitin kunnensa tare da cewa I love u My Man nayi shuru tare da rufe fuska da tafukan hannuna.
Cike da farin ciki kamar an masa Bushara da Gidan Aljanna yace Are u serious Baby?yeah My Man,harshena kawai naji ya cafko yana aika min da sakonni masu zafi nima na shiga maida mishi da martani,kukan dadi kawai mukeyi abin ba a cewa komai Haushi nake ji nayi asarar kudina na gyaran jiki nasan bazai iya yi min komai ba, nace Allah ya baka lfy My Man banyi tunanin yaji ba ashe yaji a kunnensa,nan take ya shiga neman Hanyarsa ni kuwa na saki ma jiki bazai iya ba tunda bashi da lfy sai dai naga yau yanayinsa daban yake da kowanne,a hankali yace kin shirya Mufee na? Murmushi nayi da kyar nasan bazai yuwu ba nace why not am Ready, wani Radadi naji marar misaltuwa a kasa na kamar an zuba min Attaruhu a Cikin gabana,cike da Rauni nace wayyo....Allah....zafi.....Amma Aayan baya gane me nakeyi gaba daya aiki yake yi bilhakki,sambatu da Kukan Dadi kawai yake min iri iri wanda ni Sabo da zafi bana kulashi Amma kuma banyi kuka ba,har naga an kwashe lokaci me tsawo yana aikinsa bai gaji ba,kamar raina zai fita haka nake ji,sai da ya dade Sabo da gwarzontaka kuma shima yasha wahala yaune na farkonsa, sai da ya kawo sannan ya wani ki zare jikinsa wai a kasance a haka har abada kawai ya kwanta a kaina da zafi da wahala gashi a jikina ya kwanta,sai da ya huta sosai sannan ya zare jikinsa ya koma saman Bed ya kwanta sai kuma naga ya kara dawowa ya makale a jikina,Aayan yafi mace son jiki,sai murna yakeyi ya rasa inda zai Sa kansa yace ashe alheri ne da muka bar gidan can? Sannu Babyna Allah miki albarka na wahalar dake gashi ban san zamuyi ba ko sallah bamuyi Nafeela ba ta Sunna,amma tunda nayi addua ai ba komai ko Ya karasa yana kallona Sabo da ya kunna haske,nace uhm shike nan dai ai za muyi ltr,amma kin bani mamaki Mufee na bakiyi kuka ba sannan duk kin jure wahalar da karfina,a hankali nace kwalliya ta biya kudin sabulu yanzu banyi asarar kudina ba,ai dama ni asarar kudin ce bana so ayi,kuma gashi kaji dadi Alhmdllh Allah yasa ka warke gaba daya,kasana ya kalla har jini yake Sabo da raunin da yaji min gashi farkon mu ne,yace Bari muyi wanka nace to Amma kaji dadi? Babban yatsanta ya daga min tare da cewa babu wacce za a samu kamarki Baby ni a wajena Bazan ma samu ba,,ai kinga yanda na zauce ke dai bari ba a magana,ni kadai nasan kyautar da zan miki,duk zafin da nakeji sai da nace kudi? Yace ae harda abinda yafi kudi na washe baki nace kayan dadi ne? Yace ae harda su kullum daga yau zaki samu,ban gane ba nace tam Allah ya kaimu zanji dadina,wani kallo yake bina dashi na musamman wanda sai kin cika mace Namiji zai yi miki irinsa,Na daure nace ya dai? Yace Carkwai matsagwai sarkin dadi,Allah ya taimaki Mufee,Allah ya taya miki,Allah ya rika miki kuma Allah yaja zamaninki Mufeedan Ammah Amma yanzu ta Aayan ce,ban san sanda na fara sheka dariya ba yanda yake ta yi min kirari harda daga hannu kamar yana gaban Sarki, kamar ba Aayan ba ban taba sanin haka yake ba sai yau.
A raina sai dadi nake ji yanda naga Aayan ya wani rude ya gigice sai tarairayata yake kamar zai cinye ni,a raina nace dole na ci gaba da bashi hadin kai yana nuna min so haka,dauka na yayi da kyar na bari ya gasa ni sosai sai shagwaba nake masa har yayi min wankan Sabulu nayi na tsarki shima yayi ya dauko ni muka fito,take away din daya shigo dasu dazu ya bude mana kaji gasassu sun sha hadi,ga kayan sha iri iri ya hada min ruwan tea me kauri,bayan mun shirya jikinmu Sallar Nafeela mukayi tare da addua tunda dazu bamu yi ba,sannan nace yunwa,zaman ma da nakeyi sai da dabara da kansa yayi Feeding dina naci na koshi shima haka,Brush mukayi sannan muka kwanta nan ma yaso yayi kari da kyar na lallabashi sai gobe da sassafe,bacci ya kwashe ni shi kuwa farin ciki da murna da kyar ya samu yin bacci yana tunanin me zai min a duniya ya faranta min.
Abinda ya jawo Aayan ya warke shine asirin dasu Abbi suka masa a wancan gidan sukayi sun haka rami suka binne,shi yasa malamin nasu yace bazai masa tasiri ba sai in yana wancan gidan,amma idan baya wancan gidan sha'awa ta motsa masa me karfi to zai iya saduwa da matarsa,shi yasa suka zuga Hajja kan Aayan ya dawo su zauna tare,duk kuma matan nasa dama bai gwada saduwa da su ba sai niyyar ya fara kuma aka samu akasi,yanzu sun manta da hakan burinsu su raba Ni da gidan tare da kannena sai gashi ta wani bangaren Ashe alkhairi ne.
Hajja basu tsaya ko ina ba sai gidan Abbi dake Na'ibawa can cikin yorubawa dake zaune a unguwar,gidan kuma karami ne rashin dabara yasa suka kasa yima kansu planning su mallaki gidaje,motoci etc gaba daya sai suka dogara da Arzikin Daddy suna ganin babu abinda zai Sa a raba su da wannan katafaren gida,Abbi ne kadai yayi karfin Halin siyen karamin gida a Na'ibawa gidan kuma ba wani babba bane ba kuma me kyau bane can,gashi duk Aayan ya kwace motocinsa,Sai Gold din matansu kawai da suka mallaka gashi basu da aikinyi,Khaleel da Mujaheed suka ja tsaki tare da cewa Ameer yayiwa kansa gata gashi yana can cikin daula. Abbi da yan uwansa sai bige bigen waya suke yi,haka Haneefa dasu Sajeeda sai hararar Hajja suke kan wai dole ta tursasa Daddy ya dawo dasu,Hajja tace gobe zamu koma Insha'allah Allah zamu je mu sameshi dole zai barmu.
Hajja bata san basa gidan ba sun barshi kuma basu san sabon gidan da suka koma ba,g ashi duk wayoyin basa shiga .
AsmaBaffa
[1/30, 1:28 PM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
103-104
Official
By
AsmaBaffa
❤Kai Fans Masoya wannan Novel nawa sunyi yawa wai wa zan bawa page ne ma a cikinku ko wanne Gp gaku nan da yawa,ina Godiya fans dina wlh ina matukar jin dadi kuna birgeni.
Kuma ina rokonku dan Allah ko wata tayi min magana taga banyi reply da wuri ba,ko ta kira ban dauka ba dan Allah ayi min Uzuri ba yanga bace kuma ba wai wani abu bane sai in bana kusa ko ina wasu aikin,sannan Dan Adam ajizi ne a dinga hakuri da Halina,ko a gp za ayi comment aga banyi magana ba ayi min Uzuri kwana nan bani da time sosai ne.love u all.
Wannan page kacokan na yan albarka ne YAN NIGER naku ne Masoya na yan Niger band yan Nigeria.π
Koda gari ya waye da kyar Aayan ya iya fara farkawa ya lallaba yayi alwala ya fara Sallah ya idar azhkar din ma kadan yayi ya koma ya kwanta kawai tare da kara kallona yana murmushi nan take ya kara makaleni a jikinsa sai baccinsa, jin laushin jikinsa yasa nayi mika tare da kara shigewa jikinsa harda Kukan shagwaba shi kuma yana wani jijjigani kamar Jaririya,haka har bacci ya sace shi again,bacci muke ba ji ba gani.
Meenat tace Ma'eesha abin nan na Mufeeda na lfy ne kuwa? Kema kya fada gashi har mun gyara ko ina yan aiki har sun gama nasu suma sunyi gaba,Ameer da Alama yunwa yake ji muna ta jira muji me zamu dafa kin santa sai tace mijinta baya ci sai an sake wani kalar,Meenat tana dariya tace muje muyi iya namu kawai,Suna kitchen sai ga Ameer ya fito a birkice daga gym yake ya motsa jiki sosai kamar zai fadi Sabo da yunwa,gashi bai iya shan fresh milk ba Amai take sashi idan ya sha da Safe,
Gefen Meenat ya tsaya tare da cewa ya akayi ne ta Tsito? Harara Meenat ta aika masa,Maeesha bata ma san me suke ba tana can tana fama da tunanin Handsome Yarima da yake kasheta da kalamai masu dadi ita kadai take murmushinta.
Meenat tace Ameer da kasan kyau irin na Tsito da baka yi magana ba,Ameer ya tabe baki tare da cewa ai dai nasan kaf kauyen su Tsito basu da kamata yarinya bare ki min gori,Handsome kamata kema dan kin sanni ne kina ganina a banza kije kiga yanda yan mata suke rubibi na kulasu,da ace baki sanni ba da tuni kin mato a kaina,Allah ya kiyaye ai ni shekarunka sunmin kadan yaro dakai, Wukar da nake fere dankali ya karba ya fara taya mu yace ku matsa so kuke yunwa ta kashe mu a gidan nan, hmm Mufee ce taki fitowa ko lfy? Cewar Ma'eesha,Uwar Sa ido ina ruwanki dan bata fito ba mace da Mijinta ya kamata a aurar daku kuma ku daina sawa mutane ido,Maeesha tace mu ina ruwanmu dan tani su shekara a Bedroom in dai lfy shike nan, wurin 11am da kyar Aayan ya tasheni nayi wanka tare da Brush na sake gasa jikina na daura alwala tare da tayar da Sallah,Lokacin Aayan ya shirya cikin wani yard me Laushi Dark arsh color,Ina kallonsa yanda yayi kyau ya zarta kwatance, nayi adduoi na mike a hankali kamar yar kaciya na lallaba na shafa Lotion da turaruka tare da Sa Gown me kyau simple English wear doguwace har kasa sama ta dan dame kasa ta bude pink color nayi kyau sosai,powder kawai na shafa tare da lipgloss red sama sama na yafa dan siririn gyalena a kaina,uban gashina nayi acuci dashi.
Aayan sai bina yake da kallo so yake sai ya kara yi Amma na ki yarda ko fuska ban bashi ba,na dan dingisa har gabansa na zauna gefensa a saman Bed na kwantar da kaina a cinyarsa ina kallonsa nace ina kwana ya rufe min baki da Sauri tare da cewa ni ya dace na duba lfyr ki My Dear,ya jikin?Nace da sauki yunwa nake ji kasan bana jure yunwa ni,Ki kwanta bari na kawo miki abincin da kaina nasan su Meenat sunyi ma yanzu,Yatsunsa nake wasa dasu nace so kake su gane sai yanzu ka angwance gashi sai murna kakeyi kana fita zasu gane tunda ka kasa boyewa jiya ka kwashi dadi,Dariya Aayan yayi ashe dai matar tawa bata da kunya da yawa,fuska ta na boye a kirjinsa,tashi muje Amma tafiyarki ta canja ya za ayi kawai ka rikeni sosai irin soyayya ce,haka za ayi.
Hannunsa ya zagayo ta kuguna ya manneni a jikinsa tare da rikeni sosai muka fara Tafiya a hankali,nace wash Allah ina famuwa wajen da zafi kawai ka daukeni Bazan iya bin Steps ba.
Ba musu ya daukeni kamar Jaririya tare da cewa kin tabbata baza kiji kunyarsu ba? Nace waye bako na ciki,Ameer ne kuma shi baya shiga sabgar wani bazai ma kalle mu ba.
Suna Dinning suna Break suka hango mu muna sakkowa,Meenat ta Radawa Ma'eesha sabon Salo yau suka canja,Maeesha ma a kunne tace Mufeeda yanzu ko kunya bata da ita,Ameer yace nima dan rada min naji,Dariya sukayi Ma'eesha tace Bada ni ba,Meenat tace dole kai sai kaji nan a hankali ta karkata gefen Ameer tace Sabon salon su Aayan muke kallo a sama ko kunya babu kallesu,Ameer yana dariya ya dan Saci kallon yace uhmm wannan harka tayi nima Allah ya kawo ranata har sun tayar min da tsohon tsumina.
Suna ganin mun karaso suka daina kuskus duk na tsargu nasan halin Meenat.
Aayan suka fara gaisawa sai ni,sun saba kullum faran faran ina jansu da wasa Amma yau suka ga shuru sai dai na kwanta jikin Aayan lagwaf, Aayan yace ina abincin fa naga Table sai kadan? Meenat tace bamu dafa daku ba Sabo da Sis sai tace baka cin Kaza da Kaza shi yasa muka yi iya namu in ta fito sai mu tayata tayi muku naku.
Aayan ya janye na gaban Meenat ya mikawa Mufee,ya janye na gaban Ma'eesha da Ameer ya mikawa Mufee Amma na Ameer shi ya cinye da kansa matarsa baza taci ragowar wani ba,Meenat baki bude take kallonsu hankali kwance suke cin chips and Egg dinsu harda tea din,Aayan yace kuje ku dafa wani ku in kun gama kuci,Mufee ko magana banayi cin abincina nakeyi duk Aayan ya wani rude ya rasa inda zai Sa kansa ya rasa ina zai sani ko me zai min bakinsa a washe yau shi kadai yake ta hira a Dining Ameer mamaki ne ya kamashi dan shima bai san Aayan haka yake ba da surutu gashi ya kwace musu abinci sun cinye musu,Meenat ya kalla da suke ta kallo na yace kuje ku dafa ma kanku wani abun,Darling me zaki ci? Ko kin koshi yanda yake min maganar ma a hankali kamar Jaririya sai da naji kunya,ido na daya na kashe masa sannan nace farfesun Kifi nake so da dambun naman Kaza,Aayan yace to Kunji ayi mata yanzu da wuri kar a dade kai Ameer kuje ko wanke wanke ka tayasu,Dariya Ameer yayi tare da cewa Yaya harda ni ina namiji kasan ni ban iya shiga kitchen ba bayan haka ma Meenat ta gama rainani a gidan nan zagina takeyi,Meenat tace wlh sharri yake min ni ko hararar Sa ban taba yi ba fa, Ma'eesha tace dan Allah muje muyi Sauri zanyi bako ni anjima,Meenat ta kalli Aayan Ya kasan Bakon nata? Aayan yace pls kuje mana kun dameta da surutu kanta zai fara ciwo,ina jinsu sai dai nayi musu Alama da hannu kamar wata sarauniya wai ni ga me miji ana so na nace kuje pls da kyar na furta hakan cike da yanga.
Kitchen suka wuce har Ameer din shi abin ma dariya yake bashi na Aayan to yau me Mufee ta bashi ne haka,Maeesha sarkin kida bluetooth speaker ta dakko ta ajiye a kitchen tare da hadawa da wayarta ta fara Sa musu kida sun cika kitchen da kida, Ameer da Ma'eesha sai bin wakokin sukeyi dama sune sarakan waka,Maeesha ita a wajen rawa ba kunyar uban kowa takeyi ba rawarta take cashewa suna aikin,Ameer kuwa Babban yaro ne sai dai yayi Alama da hannu,Meenat kallo take kawai tana dariya suna girkin suna cinyewa duk dambun naman sun cinye rabi dama kadan sukayi,Farfesun kifin ma haka,Ameer yana ma Meenat magana a daina cinyewa bata ji sanda yayi maganar ba ya dauki spoon daga Cikin farfesun ya dau zafi sai da ya dan tsaya yanda bazai Konata ba Amma zata ji zafi ya daura mata a bayan hannu,a zabure Meenat ta juyo tana yarfe hannu nan take ta koma gefen sink Bowl dauke da ruwan da suka wanke kifi da nama hannayenta biyu ta tsoma ciki ba tare da Ameer ya sani ba sai jin tafin hannayen Meenat biyu a fuskarsa gefen sajensa tana shafa masa kamar me shafa mai, karni yaji da Sauri yaja baya yana dauke numfashinsa ga Ameer da tsantsami baya son karni ko kadan yanzu zai fara Amai,Meenat bata sani ba har sumarsa ta bi ta shafa masa ta karfi yana zillewa.
zuciyarsa har ta fara tashi da Sauri taga Hankalinsa ya tashi ya fito da Sauri tare da wuce mu a Dining ya fada Bedroom,tunaninmu da Meenat sukayi fada Aayan yace Meenat ce ta bata masa shi kuma ga fushi wlh aure zan daura musu,Dariya nayi nace hmm Ai Ameer ke tsokanar ta.
Ameer yana ciki sai wanka yake shekawa kamar zai cire fatarsa ya dade yana abu daya ya fito zuciyarsa na tashi still haka ya shafa Lotion yayi sabon shiri kayan da ya cire a leda ya zuba su tare da fitowa ya wuce mu ya jefa su a dustbin na Compound,Ya kara dawowa Bedroom da Sauri sai kakarin Amansa muka jiyo,Kaji kamar Ameer Amai yakeyi,Aayan yace wani abu ya gani na kyankyami ko karnin kifi yaji haka yake yi,Amma kasan haka kace ya taya su? Na manta ne sai yanzu na tuna Amma tambayi Meenat ko dama bashi da lfy ne.
A hankali na mike da kyar nake Tafiya har kitchen nace Meenat me ya samu Ameer,ba komai spoon me zafi ya Dora min a hannu shine na shafa masa ruwan kifi a fuska,Maeesha tace wlh har sumarsa ta shafa masa,fuska na bata baki da kunya dalla jibeki ta Tsito kawai sai kije kiyi jinyarsa gashi can yana ta sheka amai a toilet Aayan yace baya son Karnin kifi danye baki kyauta ba,Kirji Meenat ta dafe tare da cewa wlh ban sani ba Sis Allah Sarki to me zanyi in na je ma? Harara na watsa mata ki wanke toilet ki gyara ko ina.
Lokacin Aayan ya shiga wajen Ameer dake toilet yana ta faman Amai,Doctor ya Kira tare da sanar masa nan take Doctor yace ga magani nan ya bayar a kawo,15mnt wani Nurse yazo a mota har gidan dake Aayan duk ya sansu suka gaisa ya Bada magani a leda tare da yanda za a shasu ya tafi,ni kuwa uwar son abin duniya har Dustbin naje na zakulo kayan Ameer da ya jefar nace wannan ai fariya ce na bawa me wanki nace ya wanke su ya goge idan ma Ameer baya so sai na kaiwa Shehu me kanti na tsohuwar unguwarmu wanda muke buga masa waya ya kaiwa Ammah.
Meenat Zata shiga Bedroom din Aayan yace ai sai kinyi wanka sosai zaki shiga Sabo da kina zuwa kusa dashi yaji wani karnin amai zai kara yi,Cike da tausayi Meenat ta wuce Dakinsu a ranta tace shi yasa suna fara taba kifi yaja baya ya koma karshen Kitchen ya zauna a can,amma kuma yana cin kifi kadan kadan kawai danyen ne bai son karninsa kuma.
Ma'eesha ce ta karasa komai tare da shirya Dining ta gyara kitchen da komai ta wuce Bedroom lokacin Meenat har ta gama hadewa cikin Lace Sky blue riga da skert tasha kyau ga iya kwalliya,turare tayi ta shafawa iri iri Sabo da kar taje Yiwa Ameer Sannu yaji Karni a jikinta ya fara Amai,ta fito Aayan ya mika mata maganin ki tambayeshi me zaici ki bashi,ina kwance saman cinyar Aayan nace Meenat kar ki sake wlh ki masa rashin kunya Kinji na fada miki,Dariya Meenat tayi sannan tace to ni ina ruwana dashi?
Shiga dakin tayi da mamaki yanda Dakin yake komai Neat kamar na mace,saman Bed ta hangoshi ya dukunkune cikin bargo yana rawar Sanyi,Meenat ta karasa gefensa da Sauri tace Sannu Ameer kayi hakuri ban san Baka son Karni ba,duk da ciwon nasa sai da yace ta Tsito in ba shirmenki ba wa yake son Karni? Murmushi nayi me zaka iya ci yanzu? Ba komai,to tashi kasha magani inji Ya Aayan,haka yace ai sai dai ki hauro saman Bed ki bani Bazan iya tashi ba, farko dai Dan zuba min ruwan tea me zafi ki zuba zuma spoon Uku sai ki matsa lemon tsami kadan ki kawo idan na sha sai na iya shan maganin,dan da nan tayi yanda yace ta Hau tsakiyar Bed din sannan ta bude blanket da kyar ya fito tare da dan Zama kadan,ta daura masa cup a baki ya shanye zumarsa tas,sai ta mika masa ruwa da magani kala biyu ya shanye sannan yana rawar sanyi ya koma ya kwanta, Amma ba amai kawai ya saka harda zazzabi ba? Meenat ta tambaya, Ameer wanda yasan shi dama ciwonsa na Sha'awa na motsawa sama sama to harda shi yau,Yace baza ki gane ba Meenat ciwon biyu ne suka hadu,Da tausayi Meenat tace Sannu Allah baka lfy.
Ameer ya dan kalleta kadan yaga zata bar dakin nan take ya fara nishi yana ohhh wash cikina da Sauri Meenat ta dawo gabansa a gigice ta haura saman Bed din tana ciki kuma again?ko maganin ne ai Ameer fari ya kama yi da ido wai ya sume,Meenat ta rude harda kuka tana dan Allah ka tashi karka mutu kaji tana jijjiga Ameer ya kara lumshe ido Meenat taga fa kamar ma ya dauki hanyar mutuwa gashi ya wani kankame cikinsa dai dai mararsa ya dafe wajen kam kam,Meenat da kyar ta iya cire hannunsa saman Marar ba riga a jikinsa sai Wando 3qrt Shakewa taji yayi yana shidewa kawai sai taa maida hannunta saman Marar tasa tana latsata ko ina ba tare ma da tasan me take ba,Ameer dadi ya gama kasheshi sai nishin dadi yake da numfarfashin dadi, a ransa yace Hajja ma na girmi wayonta bare ke,zaki kasheni ban shirya tafiya ba, ita kuma tunaninta zafin ciwo ne sai ta kara dagewa tace kana jin sauki?Yace da kyar banji me kika ce ba fada min a kunne na,so yake kawai tayi masa magana ya kara Jin sweet, haka ta kara bakinta a kunnen Ameer tare da cewa kana jin sauki? Wani sanyin dadi yaji nan take kafin kace me Ameer ya wani rike Meenat gam gam yana shidewa Meenat ana kukan Tausayi wai yana jin jiki, sai ga Ameer har ya warke ras ya samu nutsuwa zazzabi ya sauka sai gumi ke keto masa Sabo da dama cutar tasa ta Sha'awa ce kuma garin latse latse ta sauke masa ita ya dawo hayyacinsa.
Muryarsa taji yace ba kyau Allah ya hana taba mutumin da ba muharraminki ba kin jawo min Allah zaiyi fushi dani ki tafi zan fito naji sauki na gode,da Sauri Meenat ta cire hannunta daga Cikin Ameer tana Harararsa ta sauka daga Saman Bed din da Sauri tayi waje abinta ta bar Ameer yana dariyar jin dadi yasan yau daba dan Allah ya kawo Meenat ba da maybe mutuwa zaiyi da ciwon Sha'awarsa tuni dan rage zafin ma da yakeyi da mata ya daina,yanzu ya tuba baya kula ko wacce ya mace Sabo da yaga duk bata lokaci ne.
Meenat na fitowa ta tarar na zauna daram a cinyar Aayan yana bani farfesu ina ci,sai shagwaba nake masa ina Hawaye yana lallashi, tunanin Meenat zanji kunya kawai sai taga nayi mursisi ko a jikina sai ma kara lafewa da nayi a jikinsa ina shakar kamshinsa,da Sauri Meenat ta fasa wucewa ta koma dakin Ameer Sabo da wai taji kunya, dariya nayi kawai,Meenata a ranta tana to wai Sis me aka yi mata yau ne komai kuka shi kuma yau ya Zama maye a kanta gaba daya lfy kuwa?
Ameer lokacin ya shiga wanka Meenat ta dan jira wai ko zata ga mun tashi Amma sai ta dan leko ta kofa taga muna nan muna Holewa haka ta hakura ta fito da Sauri ta shige Bedroom,Maeesha kuwa tana palon baki tare da Yarima suna hira.
Aayan ne ya daukeni tare da cewa an koshi haka muje ki kwanta zanje wurin Daddy, ka gaishe min dashi sai na warke zanje,h ar Saman Bed ya kwantar dani tare da rufa min Blanket bai dade da fita ba bacci me nauyi ya kwashe ni.
Yau Daddy kansa yasan Aayan yana cikin farin ciki me tsanani,Daddy ya kalleshi tare da cewa fada min Son wanne abin farin ciki ne ya same mu?Aayan ya fara dariya wacce Daddy ya rasa gane ta mene,Aayan nasan baka boye min komai sanar min mene? Daddy kunya nake ji fa abin kunya ne,Sanar min naji muyi farin cikin tare,Daddy na Warke jiya ya fada tare da rumtse ido wai kunya,Murmushi Daddy yayi na jin dadi tare da cewa Alhmdllh Son Allah ya kara lfy me dorewa da nisan kwana, jeka tunda yau kunyata ka koma ji,da Sauri Aayan ya bar part din Daddy ya dawo namu,kayansa ya cire da Sauri daga shi sai boxers ya shigo blanket dina ya shige jikina sai bacci.
Sai wurin 3pm na farka na ganshi a jikina kara lafewa nayi a jikinsa ina shakar daddadan kamshinsa me sanya nutsuwa,hannunsa ya daura saman kirjina yana baccinsa cikin nutsuwa,tunawa nayi bamuyi Sallah ba ga La'asar ta kusa fuskarsa me matukar kyau tare da sajensa na shiga shafawa a hankali,shima a hankali ya bude idonsa ya saukesu a fuskata me cike da nishadi,bamuyi Sallah ba muna ta faman bacci na karasa ina sauka daga Saman Bed din sai toilet, nayi brush tare da wanka nayi alwala na fito sai lokacin ya shiga shi ma,ban jirashi ba na fara yin sallah sannan na shafa Lotion tare da turaruka nasa kayana lokacin ya fito La'asar tayi na yi Sallar sannan na zauna gaban Mirror na tsantsara kwalliya tare da Sa Atamfa green riga da skert nayi kyau na mamaki,ina gyara Bedroom din ya idar da sallolinsa tare da addua,na gyara room din har toilet komai Kal kal duk da ba wani lfy ce dani ba Amma Haka na daure na yi.
Hajja ce Tare da Abbi suka shigo gida sun dawo daga gidan ko zasu ga Daddy Amma gidan an kulle ba kowa haka suka dawo jiki ba kwari,takaici ya damu Hajja,Abbi yace yanzu ina zamu gansu? Hajja bakin cikinta bata dauki kudi ko sisi a gidan ba,yanzu bata da ko kobo,haka kowa na gidan babu me shi,Gold din matan su Abbi ma iya na kunnensu ne da abin hannu basu da komai,ga ba abinci,har Companies na Aayan sunje bai je aiki ba kuma an hanasu shiga,zama sukayi kowa yayi jugum jugum,Abbi sani yace Hajja bafa aci ba,me zamu ci a gidan dole ciki sai ana bashi hakkinsa,Abbin Ameer yace idan fa na gaji wlh zan tsinewa Ameer na huta yaro dan iska tambadadde ya barmu ko kallonmu baya yi yana can yana jin dadinsa, dama Hajja tana cikin fushi ai ko ta hayayyako da masifa rufe min baki dan Iska da bayanka me zubin na Kwadi, Ameer din nawa zaka la'ana ahir dinka duk jikokina nafi sonsa, Mujaheed yace ai ba shi ya kar zomon ba,duk ba kece kika jawowa kowa ba yaja tsaki,Hajja ta Harare shi da gogoronta irin na yorubawa tasha bakin kwalli a ido bajagau,Khaleel yace mu kawai a san yanda za ayi damu muci abinci,Umman Ameer tace ga dankunnen Gold dina a siyar a siyo abinci,Haka ma matar Abbi Mustapha,da Abbi Sani sai Matar Abbin Yara duk sun Bada nasu,Hajja tace Kai Sani kaje ka siyar dasu ka siyo kayan abinci,sannan ka kawo min dubu goma a ciki zan ajiye a aljihuna kasan zama ba kudi masifa ne,Abbi yace haba Hajja ko masu dankunnen ba a bawa ko 1k ba sai ke za a baki har 10k kin san fa abinci har kayan girki sai an siya,Haneefa ta bude Jakarta tace ni gashi na taho da 10k gashi a bawa Hajja mu huta,da Sauri Hajja ta fisge kudin ba ko godiya,Sajeeda tace dubu biyar gareni kwandala Bazan bawa wata katuwar tsohuwa ba gashi Mujaheed da Khaleel ku rike a hannunku,haka Meenal duk cikin yan matan tace ga Wata 3k Ni Abbi Mustapha zan bawa nawa Sabo da shi ke bani kudi idan na rasa ku kuwa dazu duk ni na siya muku Waina da miya kuka ci kuka koshi Bazan kara muku ba.
Hajja tace Allah sarki duniya Aayan da Daddy tunda suke mana komai basu taba yiwa kowa gori ba.
Wani dan yaro Sabeer yace Mommy ruwa zan sha babu,Hajja ta taso da Masifa zaka ci ubanka kai baka san babu ba ance ba ruwan roba a nan ko purewater babu dan Iskan yaro matsiyaci,Sajeeda tace kaje ka balle kan pampo yaro ka kwankwadi ruwa idan typoid ta kamaka ne hanji ya bule ka sheka lahira dan ni nasan wlh indai a haka zamuyi rayuwa ba shakka mutuwarmu ta gabato cututtuka kadai sun ishemu ruwan pampom ma wasu gurbatattun abu ke fitowa ta ciki.
Haneefa ta sosa cinyarta tace karzuwa ce zata kamani kwanan nan ,Meenal tace ya Ilahi muna karbar rayuwa,Mujaheed ya sheke da dariya tare da cewa ths is just the begining matukar Hajja na raye,kwana biyu kacal, dundu Hajja ta zuba masa a baya.
Kuka akaji Hajja ta saki tana komai ace nice Allah ya Isa abin ya kai har mutuwa ake jawo min da lfy ta da kwari na, Abbi yace kiyi hakuri baza su kara ba,Hajja ganin yayanta Maza na wajen ta fara shure shure tana mutuwa zo ki daukeni na huta ga jikoki birjik suna ji sai Khaleel ne yaja tsaki tare da cewa wuya kika ji shi yasa kike kiran mutuwa da sanda muna gidan daula da jin dadi me yasa baki nemo mutuwar ba,ki rufawa kanki asiri wlh karki mutu yanzu sai kin tuba idan ba haka ba Ki ci duka wajen walakiri da bulalar wuta, Hajja tana Hawaye tace ubanka da uwarka ka fadawa haka Mutuwar tazo ya fiye min wannan rayuwar ta talauci.
Su Abbi an dan siyo kayan abinci matan suka siyo kayan girki tare da na cin abinci duk na talauci haka gidan sai Abbi ne yaje ya karbi bashinsa hannun wani da yake bi Dubu Dari sune ya samu ya siyawa kowa katifa karama sannan aka sawa gidan kaya da sauran kaya haka na talaka,kitchen ma aka kara yan kayan cin abinci da kayan abinci ana dan cin garau garau, duk yanda suka so ganin Aayan ko Ameer ya gagara,har Yarima sun nema yaki saurarar su,ganin haka Hajja tace su hakura ai indai Daddy ne zai nemeta tunda uwarsa ce kuma yana yi mata biyayya su danyi hakuri na dan wani lokaci,gashi yan samari da yan mata sun hana a siyar da wayoyinsu manya tare da laptop dinsu sunce a mutu da yunwa akan a siyar gashi abincin da yan makaranta duk sun cinye kudin su Abbi,a bincin ma sabo da suna da yawa da wuri ake cinyeshi gashi babu me aikin yi ko fita basa yi a unguwar yaran ne kadai ke zuwa schl Abbi yace kudin makaranta na karewa sai dai a maida su ta Gomnati,Mujaheed da Khaleel kuwa su Abbi sunyi sunyi dasu su karkade takardunsu su fara fita neman aiki amma sunki Sam,sabo da ba a musu tarbiyar neman na kai ba,ba a nuna musu tun farko cewar ka nemi naka yafi akan ka dogara da kudin wani ko na ubanka,basu san wahalar duniya ba.
Su Haneefa yan mayuka masu kyau duk sun kare an fara duhu duk da cewa suna da haske amma sabo da ba irin rayuwar da suka saba ba kenan duk sai suka fita daga hayyacinsu sai masifa da rashin kunya da suke yiwa kowa a gidan musamman Hajja da suke ganin laifinta ne. Saurayin Meenal ne ya bata Dubu ashirin suka samu aka sa carpet a Palo da bedrooms,shima sai da ta dinga rokar shi ta zubar da ajinta sosai ya dan Sha minti da ita sannan ta samu kudin.
Matan su Abbi kuwa yanzu yar biyayyar da sukewa su Abbi Ashe duk ta kudi ce yanzu fada da masifa kawai ke tashi a gidan babu me Zama lfy,Hajja da tayi magana su zageta,Hajja ba kudin zuwa wajen bokaye sai cin goro da take tashen yi ba dare ba rana.
Tun daga wannan Rana Hajja Sabo da bata son talauci take kiran mutuwa ko a dakinta sai kaji tace mutuwa kizo ki daukeni da wannan rayuwa,tace to yaran wai ina suka buya haka ko ina an kasa ganinsu da ace sun bude mana gidan ma sai mu kwashi yan kadarorinmu da kudadenmu ko banza ma kafa kanmu cewar Hajja,Haneefa tace ah Hajja kiwa Daddy da Aayan baki mana wlh da nice ke tsinewa Daddy kawai zanyi.
Harara Hajja ta zabga mata tare da cewa to ai yafi ubanki dan uwarki ubanki Abinci kadai ya kasa daukan nauyinmu bazan tsine masa ba idan uwata ce ke sai kisa na tsine masa munafuka da hakora kamar na gafiya.
Kullum yan gidan Hajja ta Gallabesu da kiran mutuwa kawai sai dan Matashi Sabeer yau da dare ya shirya cikin fararen kaya tas,komai fari yasa tare da shafa chalk a fuskarsa ya koma kamar dodo,ya shiga dakin Hajja cikin tsakiyar Dare ya wani tsaya a kanta tare da canja Murya yace Hajja.....firgit ta buga ihu daga kwance taga haka tunaninta Mala'ika ne ko Aljani,yace kin dade kina kiran mutuwa yau gani nazo nine Mutuwa yanzu zan daukeki,Hajja sai ta fara ihun Kuka tana bada hakuri,Sabeer ya fice da gudu ya boye a dakinsu ganin Hajja zata tara masa jama'a.
Tun daga wannan rana Hajja bata kara ambatar sunan mutuwa ba.
Abbi cikin su uku kowa yana da daki shi da matarsa,sai na Hajja daban,Yan matan gidan kuwa manya da yara gaba daya daki daya suke gwamitsa wurin su takwas,kowa da shimfidarsa anyi kwanciyar kai da kafa,Haka mazan ma Kowa a daki daya jal manya da yara haka kullum Suke fada da masifa ba ji ba gani ba zaman lfy a junansu sai dambe,Hajja ma ta Bullo da rigimar ta gaji da zaman banza gwara a siyo mata taskira hhhh irin ta tsofaffi da Mazarin kadi tare da Alli zata fara kadi tana murza Mazari tana saka zaren auduga,Khaleel suka dinga dariya tare da cewa anji wuya za a kare a taskira kuma wato yanzu kin yarda kin tsufa har zaki hada Taskira guda ana tauna goro anci goggoro ana kadin Zare,hhhh yaran kowa yana dariya wa Hajja,Hajja anji wuya cewar Meenal sanda ake goge hakora da Cinyar kaji ba a gode Allah ba sai yanzu da ake gogesu da goro,Nan take Hajja ta fashe da kuka amma ko kiran sunan mutuwa ba a ji tayi ba kus kake ji sai hawaye.
Aayan kuwa shi tuni ya hana Ameer fita kuma kar ya kunna wayarsa yanda su Hajja baza su samu ba,yace sunyi hutun zuwa Office ba me fita ba me shiga sai ya gama Amarcinsa zasu tafi Abuja,Yarima kadai ke zuwa wajensa ko wajen Ma'eesha,Daddy kuwa shi kanshi yanzu hankalinsa yafi kwanciya yafi jin lfy ma a jikinsa amma duk da haka indai Aayan zaije wajensa sai yace ya maida Su Hajja gida sai yace to amma yayi shuru abinsa.
Aayan ne ya sameni a Bedroom ina karanta Novel a waya yau kwana uku kenan naki yarda Aayan ya kara ko kissing dina ba yanda baiyi ba naki yarda, gefen bed din ya zauna jikinmu na Gogan juna wayar ya karba a hannuna tare da ajiyeta can gefe yana kare min kallo na maita,Kunyace ta kamani duba da kayan dake jikina riga ce me dan fadi me hannun vest iya cibi tsayinta sannan sharashara komai a na gani kamar mataci,sai wando Jean white pencil nasha kyau gashina kamar na Baturiya.
Hannun Aayan naji na yawo a kirjina yana murzasu,ban hanashi ba sabo da nima wani dadi nake ji sai dai shagwabe fuska da nayi kamar zanyi kuka.
ππππ
Afwa fans abubuwa kwana biyu ne suke dan min yawa shi yasa zaku ga bana baku pages a kai a kai ba haka na so ba.
❤❤❤❤❤
Typing error ko kuskure ayi hakuri idan an gani.
AsmaBaffa
[1/31, 10:53 PM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
105-106
By
AsmaBaffa
ZAINAB ATIKU SALAMA ths page is for u tawajena.
Shuru nayi sai ma kara gyara masa nayi ina so na hanashi amma bazan iya ba gaskiya,bazan iya shanye wannan shagali ya wuce ni ba banma san sanda na fara mayar masa da martani ba cikin salo da birgewa,muryarsa naji da kyar yana I need u Babyna pls ki yarda a hankali zan miki ba zafi,Yanzu Yamma tayi ka bari sai dare maybe na yarda,no ni ban yarda ba yanzu nake so sai dai idan baza ki bani ba dama tunda ni bakya so na,Haka nace ma bana sonka? to in kina so na ai zaki ji tausayina amma ke ko daya babu a idonki, murmushi nayi sabo da ina sonsa bana son na yi masa laifi ina ji ina gani cike da tsoro nace to ka kara yi kadan amma,yace dan mitsili zan yi,nace to tunanina da gaske dan mitsili din zaiyi,jikinsa na rawa ya fara sarrafani a Fagen sarrafawa sai dai mu sarrafa juna sabo da ta nan ba a bari na a baya sabo da dadi ne ke kwasata kawai nima naji na iya na fara nuna kwarewa ta,a hankali yake bi dani har ya samu Hanyarsa Yanda nake da Niima sai dai a shafa Fatiha, Kai..kai..yau ma da zafi Allah ni bazan yarda ba,Aayan a lokacin yayi nisa kara kankameni yayi ba ta inda zan iya motsi,a hankali yake aikinsa ina ihun Zafi bakinma toshe min yayi da nasa sai Sambatu yake iri iri,in nace ya dagani sai yace dan Mitsili zaiyi sai da ya mugun dadewa sannan ya samu nutsuwa,ya gamsu sosai.
Kukan Shagwaba nake masa yana ta lallashina tare da rada min dadadan kalamai,yau ma naji jiki a hannunsa,nace aka sake Allah Hijira zanyi na bar garin,Dariya yayi ina zaki koma? Can yankin Mambila sai muyi Hijirar tare kafata kafar matata,Ina shafa kirjinsa nace ai bazan je da kai ba tunda kai zaka jawo nayi Hijira, Do u knw what? Sai ka fada, I love u,i love ur everything,u r so sweet Baby ban ma san yanda zan miki bayanin ba, kwanciya ta na gyara tare da juya masa baya,Juyowa dani yayi tare da cewa wa yace miki ana juyawa me gida baya? Mantawa nayi shi yasa wanka za muyi haka ya daukeni har toilet na Sha gashi sannan mukayi wanka tare da tsarkake jikinmu.
Sai da muka kwanta har bacci ya kwasheni naji Aayan yana shafani sai Shan albarkatun kirjina yakeyi,a hankali na tsinci muryarsa yace My Mufee pls dan Dis nake Needing,baki na turo kamar zanyi kuka haka dazu kace Dan mitsili yanzu kace Dan Dis Allah akwai zafi in ba so kake wajen ya samu matsala ba,Insha'allah bazai samu ba dole na hakura ya kara yin na biyu.
Amma wannan kam kasa hakuri nayi kuka nayi ta barkawa sabo da zafi,na tabbata da ace akwai wasu kusa damu sai sunji irin yanda nake Magiya da kuka,Aayan shi baya gajiya ko kadan Sambatunsa kawai yake yi wanda bai ma san inda yake ba.
Washe gari ma again da safe kasa tashi nayi sabo ya min raga raga jiya,Shi ya min komai da komai ina jin Brush kawai nayi da kaina sabo da duk kakale kakalena Aayan uban gida nane kamar zai cire makoshi ni ko nace ya bani nayi, har shafa mai tare da sa kaya shi yayi min mukayi sallar Asuba da Azkhar ya kara gyara Bedroom din sannan muka koma bacci sabo da Bala'i kari naji zai nema kawai nayi baccin karya daga haka na gasken ya daukeni,shima yasan idan ya sake nema baiyi adalci ba haka ya danne jarabarsa yayi bacci da kyar.
Meenat ma yau shuru suka jini sun kasa gane kaina kwana hudun din nan,yanzu basa jirana ma Kansu suke mawa girki in na fito aci damu idan bana ci su dafa min wanda muke so ni da Aayan,Ameer kadai suke kira suci abinsu.
Suna kitchen duk kusan Meenat ce ta gama komai Ma'eesha waya takeyi da Yarima da safen nan tana yanga tare da kashe murya.
Hello Dear cewar Ma'eesha,yeah ina jinka,Yarima ya wani yi juyi saman Bed tare da cewa am just missing u,Maeesha tayi wani murmushin jin dadi Miss u much more Dear,me kikeyi yanzu,Ina kitchen,wow shi yasa naji kamshi cewar Yarima, uhmm kai ina wani kamshi a girkina na yan koyo,Ba wani yar koyo ai Ameer yace duk kun iya girki kinga na huta.
Dariya kawai Ma'eesha tayi sannan yace ltr,ok Allah ya kaimu sukayi Sallama lokacin Meenat ta gama komai har gyaran kitchen.
Tace gashi nan Ma'eesha ki shirya Dining ni kuma bari nayi wanka,wa zakiwa wanka yanzu ki Bari muci sai kiyi ke wai ko da saurayin ki a gidan nan ne?bakya ko fitowa Palo sai kin yi kwalliya.
Meenat jin sharrin da Ma'eesha zata kulla mata ta fasa zuwa tayi wankan,doguwar rigar ta bari Blue a jikinta da dan siririn gyalenta tace muje to mu karya.
Sun Zauna Dining kenan sai ga Ameer yaci uwar wanka kamar zaije wajen Daurin aure shadda light blue tasha aiki dinkin kamar a jikinsa aka dinka das das dashi sai kamshi yake bulbulawa yayi wani Fresh sumarsa me yawa sai sheki take ga gemu na matasa dan firit tare da saje kadan.
Ma'eesha tayi dariya tace gaskiya yau kayi fa, kafi ko yaushe kyau amma Yarima ya wuce ka,Meenat kuwa na kallon Ameer sai ko tayi sauri ta tsuguna a kasan Dining ta buya gyalenta tasa tana ta goge fuskarta wai kar aga maiko, Ameer yace Yarima Din me yarinya Bobonki bai kaini haske ba,amma dai baza kace baki ko chocolate bane ka sani dai ga Hanci kamar biro dan gayu na karshe,Dariya Ameer yayi yace ke kika sani kuma wannan.
Kamar naga Meenat a nan Ameer ya furta,Maeesha tace tana kasan Dining yau aljanunta ne suka motsa tsoron mutane take ji,daga nace wa zata yiwa kwalliya da safe shine taji tsoro na ta fasa fita,Yanzu kuma tana ganinka shine ta buya kasan Nan wai tsoronka take ji,Aljanun tsoro ne suka shigeta,Dariya Ameer yayi tare da tsugunuwa kasa ya leka sai ko Meenat ta kara yin kasa tare da boye fuskarta,yace yau sai naga me kike boyewa yayi kamar zai kamota ta fito da rarrafe ta Mike da sauri ta koma Bedroom,Meenat ta saba da kwalliya idan bata yi ba bata Jin dadin rayuwarta,wanka tayi ta shirya cikin Doguwar rigar Lace tayi kyau matuka,sai lokacin ta fito suna ta cin abincin su ma sannan itama tazo ta zuba nata ta fara ci,Ameer ya kalleta ya kara kallonta sannan yace baki gaisheni ba yau,Ina kwana?ka tashi lfy? Yace lfy lau, u?tace lfy yace good kin kyautawa kanki da badan haka ba yau da sai kin fadawa yan garinku,dariya suka yi gaba daya.
Meenat yau ta fita zuwa Islamiyya schl dinsu ta kai wani kudi tana kan hanyarta ta dawowa gida da yamma wani Saurayin matashi wanda bashi da makusa ta ko ina cikin dalleliyar motarsa ya dinga bin Meenat ta saurareshi amma taki sai da suka zo har gida,Matashin ya firgita da ganin irin wannan katafaren gida,A ransa yace da gani dama kalar masu kudi ce, haka yake ta kallon gidan da Meenat ta shiga da yake Islamiyyar ba nisa da nan gidan,Me mota dai haka yayi shahada ya tura daya daga cikin ma'aikatan gidan cewar dan Allah ya kira masa waccen yarinyar,Me gadi yace Meenat sunanta ai bari a fada mata,Ina Palo muna tare da Ma'eesha dake chat sai Ameer,Me gadi yayi Sallama tare da cewa Meenat kinyi bako yana waje wani me jar mota,Nasan wannan me nacin ne,Ameer yace kina ji fa Kije maybe yayan Tsito ne,wani haushin Ameer Meenat taji da ta rasa gane na mene kawai tace kace ina zuwa, Meenat ta Mike ta shiga daki Don ta kara dan gyarawa ta fita,Kafin ta fito Ameer ya fita wajen Saurayin kawai yace yayi hakuri an kawo kudin auren Meenat shi Yayanta ne, saurayi yace ba komai Allah tabbatar da alkhairi ya shiga motarsa ya tafi yana cike da jin haushin Ameer ko karya ma yakeyi oho a ransa yace suje da yarsu dan Ubansu an fasa aura wannan abu na rufawa juna asiri.
Ameer ya koma inda ya fito ya zauna yayi mursisi,Sai ga Meenat ta fito anci uban gayu kamar zata je Dinner Ameer yana boye dariyarsa Meenat ta wuceshi da yanga tare da Galla masa harara dan ta ganeshi dariya yake mata,ta fita tana kunkuni tace Sa'idini kawai,Sai da taje taga wayam ba kowa,har waje ta leka,Me gadi yace ranki ya dade ya tafi yarsa ina daki naji karar motarsa ya figeta a fusace,ko dan kin dade ne yayi fushi,su kansu Masu aikin basu ga sanda Ameer ya kori bakon ba,Meenat a ranta tace yayiwa kansa, gaba ta kaini tuntuben me choge.
Tana shiga Palo ta zauna gefen Ameer, har ya tafi? Meenat tace ae mun danyi magana sama sama,Ameer yace da Alama kina sonsa? Meenat tayi banza dashi tana latsa waya,sai daga baya tace ya Ameer dan Allah ka kaini gidan kawata da yamma mana kaji? Driver dinku me yakeyi? Sis Mufee tace yaje ya duba Iyalinsa can kauye sai mun koma hutun schl zai dawo,Ya Aayan ya hanamu fita sai nan da wani lokaci ki Bari idan mun tambayeshi ko zai yarda sai na kaiki.
Ok to kana gani tun safe sunki fitowa abincin ma Shi yazo ya daukar musu na kasa gane meke damun Mufee, Aayan kuma sai nishadi yake kullum cikin farin ciki sai wani kiba da kyau ma yake karawa,Ameer baka fahimci komai ba? Ameer shi yasan dalilin komai Aayan warkewa yayi shi yasa yanzu angwanci yake yi su Meenat basu gane ba. Kallon Meenat Ameer yayi tare da cewa ki Bari kije ki tambayeta da kanki kiji tunda ke bakya gani ki kyale sai kinji dalili.
Aayan ne da Misalin 5pm ya shirya tsab ya fito zaije wurin Daddy ni kuma na danji sauki haka na gyara toilet kal kal tare da Bedroom din yana kamshi ta ko ina,nayi wanka da ruwa me Zafi na shirya cikin kaya marasa nauyi,Meenat ce da Ma'eesha suka shigo da Sallama,Lokacin ina Jikin Mirror ina fesa turaruka,Maeesha tace kinyi kyau Mufeeda,Tnx ya kuke? Lfy sis bakya fitowa kamar baki da lfy muke ganinki Meenat ta furta,Wani kuka ne ya taho min sabo da Aayan kullum baya daga min kafa ko kadan na damu gaba daya yaki bari na dan warke ma,Meenat tace subhanallah me akayi miki kuma kuka? a jikin mirror na kifa kaina ina ta kuka da shesheka suna kallona duk sun shiga damuwa.
Dan Allah ki fada mana mene ne?meke damun ki?me ya faru? Ina hawaye nace Ina so na fada muku amma Allah ya haramta ba kyau dole bazan fada ba wai sai dai nayi shuru, Meenat tace to wai tafiyarki ce duk ta canja mu bamu gane ba,nace Aayan ne yake ta abu daya ni wlh bazan iya ba gwara ayi asarar kudin gyaran jikin,ni da nasan hakane bazan yi gyaran ba,Sai yanzu Su Meenat suka gane me yake damuna,Dariya sukayi tare da cewa uhm wannan kuma tsakaninku ne wannan fadan ba ruwanmu babu me iya miki maganin abun sai dai muce aci gaba da hakuri kafin ki saba muji kinfi ma Aayan din maita suna ta dariya,nace
Dan uwarku Ku fitar min a daki tunda dariya kuka zo yi min,Ficewa sukayi suna kuskus.
Hajja ce take rera wakarta tana gaguda kwalli a idonta tana Yareye iyee nanaye...Ayyeee riyalle duniya.....Haneefa dake kusa da ita tayi lamo a gefe sai yanzu take tunanin aure,da can me yasa bata samu cikin samarin ta masu kudi ta fitar da miji an mata aure ba ta zauna tace ita karatu sai tayi Masters, yanzu ko mijin ma ta fito dashi wa zai mata kayan daki? Mikewa tayi ta bar wajen Hajja ta koma dakinsu inda ta tarar da Su Meenal tare dasu Sajeeda sunyi jugum suna tunani,Kallonsu tayi tace ya akayi ne yan mata? Meenal tace hmm ke dai bari Wai yanzu Abbi yazo duk mu cire layin wayar mu mu basu harda masu computer kowa ya kawo tasa wai za a siyar a siya mana kana na Irin su Dagani Gara, harda wata waya Dagani Gara kuma? Ae mana tana nan wata me uban nauyi yar China ko Camera babu,Yanzu dan danna wayar ma da muke tana ebe mana kewa karbesu za ayi kwarai kuwa dan har an kwace ta yan mazan gidan nan tare da Sauran yara kaf za a siyo kayan abinci me yawa wanda zai dan Dade ana ci,Abbi kullum suna fita neman aiki duk tsufansu amma ba a dacewa.
Khaleel ne ya fito daga wanka ko Vaseline babu a dakinsu dakin su Haneefa ya shigo da gajeren wandonsa kai Ku miko min Vaseline na labta a jikina,Sajeeda tace kamarka da shafa Vaseline,to ya zanyi kawai a bani na labta haka,kune ance Ku samu aiki kunki ai da mun huta,Khaleel yace baki da hankali in mutum yayi aikin ma ai sai abinda Hajja tace wlh akan nayi wannan tsohuwar ta Dameni gwara na bar gidan nan na koma gidan frnd dina. Haneefa suna dariya tace nayi mamaki da yanzu kowa baya ragawa Hajja to ko dama wai tsafin nata can gidan ta binne su ne? Ita ta sani ai gashi tun ba a je ko ina ba sun jawo mana muna gane kurenmu gaba daya me yafi zaman lfy dadi Ameer tun wuri ya shiryu gashi ya huta Allah sai ya zareshi a cikin mu suka koreshi Ashe gata suka yi masa aikin banza ni dama ni suka kora wlh da wannan wahalar,Khaleel sai masifa yakeyi yana shafa mansa a dakin ya gama sannan yace to Ku ban aron Cumb,Meenal tace Cumb daya tal a gidan nan na Umma da ta zo dashi a jakarta shi yake yawo a gidan nan kowa dashi yake taje kansa mata da maza bari na karbo ma, yanzu wannan Sumar dana tara ta common Cumb ba bu bare man gashi da sauran kayan gyaranta ai kamar mahaukaci ma zan dawo soon zanje wajen me aski dole na sauketa, Sajeeda tana dariya tace haba gayu tana ma kyau, gyara ne yasa yanzu da babu zaki gani very soon dole ina ji ina gani na sauke ta, gaskiya Aayan baida mutunci Allah wadaran sa daya kore mu akan shegiyar Mufeedan nan,
Khaleel yace ah lallai baku fara nadama ba me tayi muku yanda haka kawai muke biyewa su Abbi da Hajja muka sasu a gaba musamman Ku,Aayan ko wacce shara shi ake turawa,tun bai San kasar nan ba Hajja ke tura masa asiri tun muna yara har muka girma,ki tuna takura da akayi masa shi da Ubansa,kalli matayen da aka sa ya aura kuma aka sa ya sakesu,kalli irin yanda ake nuna masa shi da Ubansa ko makiyinka ai baka yiwa haka ba bare dan Uwa na jini,Allah wadaran halin Hajja me zuciya kamar ta fir'auna danka da jikanka ka jefa su a wani Hali duk sabo da son kudi.
To mu ba irinku bane Sajeeda shekaran jiya dukkanmu Maza muka zauna muka tace tare da tankada mukayi rairayi munyi lissafi ya bulle dai dai dan haka mu Maza duk mun tuba wlh Allah ya ganar damu gaskiya kuma Aayan bashi da laifi yama yi kokari yayi biyayya,yana da damar da zai tattara su koma kasarsu amma ya zauna damu yana Shan bakin ciki,to mu dai yanzu ma Istingifari mukeyi ko mu nan ance miki Hajja haka zata barmu ba tare da ta asirce kowa ba, tunda tayiwa danta da ta haifa wa zata kyale kuma Uwa fa guda, yanzu kalli inda su Mommy suke mata rashin kunya kin San kuwa asirinta ne yake ta karyewa zai tonu,gamu dan muma mun gano gaskiya,da ai bamu gane ba musamman Ku mata masu karamar kwakwalwa,mu dai sai Aayan da Mufeeda,Allah ya bar mana Anty Mufee sai Mufee.
Sajeeda tace kato da kai kana kiran wata yarinya karama da Anty anji kunya,ai ke bakin cikin naki harda Hassada cewar Khaleel kinga tafi ki kyau,ta auri Aayan sannan Ameer ma maybe Kanwarta zai aura,Me yasa yanzu samarin naki yan iska basa zuwa? Duk sun gujeki wlh tun wuri ki gane gaskiya,Haneefa tana ji da sauran mata duk sunyi shuru Khaleel ya gogesu tas ya kara gaba abinsa.
Gaba daya sun hallara a Palo ana cin shinkafa dafa duka tasha manja tana tiri tiri sun saba da cin girkin yan gayu duk sai suka ji wannan ba dadi kowa turawa yake da hakuri,Abbi mamakinsa daya shine dare daya suka koma talakawa me yasa basu yi planning sun mallaki kadarori ba,a ransa ya tuna da fa talakawa ne su sai rufin asiri kuma aka samu Daddy ya basu aiki suka koma gidansa da zama,da sun San haka ne gwara a ginawa kowa gidansa daban da yanzu ba ruwansu,duk kudin kuma da suke samu a wajen bokaye suke karewa aikinsu kenan,kawai kudi suke kwasa a Companies suna abinda suke so basa tunanin su tattala sabo da gaba sai burin kawai su kwace Dukiyar Aayan data Daddy,Hajja kuwa ko a jikinta bata da niyyar tuba sai ma kwantar da hankalinta da tayi tasan dole Daddy zai nemeta ta dawo dasu dole su dora daga inda suka tsaya.
Meenal ce a palon tace duniya budurwar wawa,Abbi ya harareta tayi shuru,Abbi sani kuwa kallon Khaleel yayi tare da cewa dan ubanka baza ku aske Sumar nan ba ko sai kace kan mahaukata,Khaleel yace haba Abbi yawa kuke ba kudi ba komai me kuke so yan mata su gani a kanmu mu birgesu dashi yar wayar duk kun kwace kuma ya kuke so muyi shike nan mu baza muyi nishadi ba kenan, Mujaheed yace ni wlh aka sake barin gidan nan zanyi me ake min sai fada safe da rana da dare.
Hajja ta Galla musu Harara ba wanda ya kulata wanda ta tabbata da ace da ne da tuni sun bata hakuri,Hawaye Hajja ta fara tare da cewa an rainani bani da iko da kowa,shuru ba wanda yace mata kala,ta mike tsaye tare da cewa ai bani na dora muku talaucin ba da zaku tsaneni me nayi muku? Wlh in na gaji bar muku gidan zanyi,sai nayi magana ayi Banza dani wata tsiyar nayi muku da za a dauki karan tsana a dora min,to duk Wanda ya fasa baya kaunar uwarsa da ubansa,Abbi yace me akayi miki kuma wai? Gasu nan bani da iko nayi magana sai cin mutunci to wlh zan bar muku gidan nan, Hajja ta fashe da kuka, yaran gaba daya tsaki suka ja tare da mikewa daya bayan daya suka bar palon su Abbi ne ke bata hakuri.
Zaune nake a palon Sama na Aayan,naci uban kwalliya cikin English Gown iya cinya nayi kyau,Yau na samu Salama Da kyar Aayan ya fita zuwa wajen Yarima yana nemansa yace bazai je ba da kyar na lallabashi sabo da ya Dameni da fitina ko kasa bana sauka sai dai su Meenat ke yin komai kullum sai ya sani kuka yace zan saba ni dai yau 1wk kenan ban saba ba.
Abin mamaki 40mnt sai gashi naji sallamarsa har ya dawo, duk da damuna da Aayan yakeyi bana ganin laifinsa kuma bana jin ya isheni ko naji haushinsa Sam bana jin hakan sabo da sonsa da yayi min yawa bana jin akwai abinda zai nema na hanashi a duniya,Da ya fita ma duk sai naji ba dadi gidan amma jin sallamarsa wani Sanyi da dadi ya ratsani har na kasa boye farin cikina,. Tsayawa yayi yana kare min kallo yanda yaga na wani yi mugun kyau kamar a sace ni,murmushin da nasan yana kara min kyau na sakar masa tare da walwali da Idona cike da jan hankali ina daga zaune na bude masa Hannu ya kuwa karaso a hankali tare da shigewa jikina a hankali na mayar da hannuna tare da rungumeshi gwiwoyinsa suna kasa,Hannayena nasa tare da tallafo fuskarsa muka hada Ido nace sannu da zuwa kana na shiga tsotsar bakinsa kamar na samu Alawa me dadin gaske.
Hannu na daya na sa a cikinsa nace muji ko kana jin yunwa dariya yayi sabo da yanda nayi kamar irin dana din nan, ina Sonki My Queen ya furta yana dariya sabo da yanda nake masa cakulkuli a cikinsa, mikewa yayi tare da kwanciya saman doguwar kujera ya daura kansa a saman lumtsumemiyar cinyata wacce ke sheki da santsi ga tsoka da girma sai kamshi takeyi ta ko ina,Yar rigar dama guntuwa ce,Hannu yasa ya wara cinyata wai bude min Kingdom din taki na gani ya warke jiya fa sau daya kika bani tal, shagwaba na fara
nace Allah a'a amma ai ya dace ka dinga danne maitarka kullum ba fashi ka bari na warke sai na baka amma kullum kace Dan Dis,gobe kace dan Mitsili,gata kace kadan,nasan yau kuma cewa zakayi....kafin na karasa yace Dan Kucili, dariya mukeyi gaba daya yace tunda nake koyan hausa in baki labari wannan words din ne suke bani Wahala da dariya,abin dariya,wai Dan Kucili,dan mitsili,dan dis,dan kadan,dan Kis,Dariya mukeyi nace ai har dan Kucilili ana cewa,yana dariya yace to na yau Dan Kucili zanyi,nace naki sai na warke 1wk sai next wk,Ido ya zaro waje tare da cewa kawai mutuwa kike so nayi ni bazan iya ba,Ina wasa da gashinsa nace gidanmu na gado wai ya za ayi dashi ne? Aayan yace ki Bari kawai a gyarashi a sake sabon Gini sai a sa yan haya mu jira muji nan gaba ko Abbanku yana da rai ko ya rasu dole bincike za ayi first,nace to Allah ya kaimu,Ameen yace sai me kuma?nace uhm...uhm.. da dai zan fada kar kace ina da son kudi ne,fadi mana idan ma kina so waye baya son kudi kuma ai kudin mijinki kije so ko? Kai na daga ae,Lefe ni fa ba ayi min ba,dariya yayi tare da cewa duk kayanki? Ai wannan kawai siya mana kayi kuma ma ai har su Meenat lefe kuwa iya Amarya akewa, Ki kwantar da hankalinki idan ma har biki kike so sai ayi miki,nace a'a ni bana son biki ko wata Dinner kawai lefe nake so sannan ayi min Kamu, mene kamu kuma? Kamu da akewa Amarya idan ana gobe za a daura mata aure a sata a lalle,to ai gwara Dinner dashi,nace a'a ni duk wannan basa birgeni kawai Kamu za ayi min nima shine yake birgeni a duniya bazai yuwu ace ni har abada baza ayi min ba,kullum burina naga anyi min Kamu a biki sai kuma haka ta faru to duk da haka ban makara ba shi yasa nake jin tsoro kar na samu ciki ba ayi min Kamu ba,idan na haihu ai magana ta kare kuma na haifi dan dakan Kuka,Dariya Aayan yake tayi tare da cewa lallai har yau Kuruciya na nan,Dan dakan kuka kuma shege fa kenan,Dariya nayi nace ae ayi min Kamu ni dai ko idan na haihu nace dan dakan Kuka na haifo.
Jibi Birthday na sai a hada da kamuna,Waye zaiyi Kamun to? Zakiyi Birthday party ne? Nace a'a ba wanda zan gayyata Meenat da Ma'eesha sun isa su sani a lalle,ga Ameer da kai kuma Ango kun isa shike nan,Aayan yau dariyar Mufee kamar ta kasheshi da shirmena,yace to sai na gayyato Yarima ma yazo ayi dashi ko,nace to Allah ya kaimu,Aayan ya kalleni yace Amarya an kusa saki a lalle,nace haka yake next wk zamu koma schl ma,Nan Aayan ya hade rai yana jin haushin schl shike nan bazai dinga gani na ba sai yamma,yace a bari sai nan da 2wks ki koma kinga kin kara 1wk kenan ko? Nace ae Allah ya kaimu,Bazan iya yini ban ganki kusa dani ba, schl ta wani dawo ya furta tare da sauke ajiyar zuciya .
Na kalleshi nima nayi shuru sabo da bana so mu rabu ko na 1mnt,hannunsa naji ya tura cikin rigata yana Murza kirjina, sakon dai dai yake shigata babu gargada ban san sanda na shiga Maida masa da martani ba,daukana yayi cak yana rada min dan Kucili za a bani,banyi musu ba sabo da bana son na bata masa kuma kar ma yace na fiye Complain ba dama miji yace zaiyi wani abu sai mace ta fara Complain sai ki ga yana jin tsoron neman hakkinsa yana danne sha'awarsa sabo da yawan Complain,ko miji ya dinga zargin kansa Shi ba namiji bane ko bai iya komai ba baya sa matarsa taji dadi dashi sai kiga duk ya shiga damuwa da tunani baya birge matarsa shi.
Meenat ce zaune Saman sofa tana Shan ice cream dinta tana kallon American film a Tv,Ameer ya shigo ya zauna gefenta shima sanye da riga me gajeren hannu da 3qtr sai kamshi yake yi,yace San min na Sha Ice cream din,Dazu ya Aayan ya kawo mana da yawa yana fridge,bana iya Sha da daya ni kawai in zaki bani a naki ki bani,Meenat ta turo baki haka ta ebo a spoon tace duk zaka rage min quantity ni ungo ni karbi ya bude baki kuwa Meenat ta zuba masa ya shanye tana Sha tana bashi sai da suka shanye robar guda sannan Meenat tace kaji dadi hankalinka ya kwanta mun shanye da kai,karo wani mu shanye again ,au dama kana iya Sha da yawa dan kar nasha nayi kiba kazo ka raba ni dashi, Ma'eesha ce ta cakare ta fito kamar zata je Dinner,Meenat kawai sai ta hade rai tam, Ma'eesha tace Sis zanje wurin Yarima yana palon baki,Meenat sai lokacin ta saki ranta tace to maza ayi sauri a dawo lfy ki gaisheshi..me Meenat ke nufi da fushinta da farko? oho.
Kallon film dinsu suke yi sai katsam budurwa da saurayi suka fara kissing din juna a haukace,Americans ba kunya sai gashi ana tube kaya za a fara Sex,Meenat duk kunya ta rufe ta da sauri ta dauki remote zata canja Chanel,Ameer yace mene haka sai da kallo ya dauko dadi ai nan shine ainihin film din Horror movie ne ki tsaya ki gani abinda zai faru mana,Meenat tace ni ba yar Iska bace tana Satar kallon Tv kuma,tace haka kawai mu dan Allah ka kawo remote a canja ka wani kwace basai mutum zai kalla ba, Meenat taji ana shidewa a Tv Ameer ya ba da Amanna yana kallo ta dan kallo ta dauke kai tace yan iska kawai sai taga Masoya sun koma abin tsoro dama Horror film ne sai suka koma fada da zako zako hakora,mace ta bude bakinta wommm...Sai da Meenat ta buga kara tare da fadawa jikin Ameer, Ameer yana Jinta dan munafuncin Sa sai yace ai film din nan abin tsoronsa yayi yawa yanzu zaki ga ma sun koma kamar Dujal ance har mafarkinsu akeyi, na gani a BBC wani Horror rannan ana kallo a wani gida ya fito daga TV ya shiga jikin matar kin San Aljanune, Meenat ta kara kankameshi ta boye fuskarta a jikinsa taki dagowa,Ameer yana jin dadi a ransa a fili yaci gaba da cewa ai ba a barin irinku su kalli wannan sabo da idan suka ganku sukan iya Faso TV suzo wajenku,ni tsoro nake jiye miki dan yanzu zan fita sai ke daya bari na Canja Chanel,ya canja Chanel ya fara kamar zai Mike Meenat ta rikeshi kam ta makale a jikinsa tana roko Karya tafi,yace to sai dai ki dakko Ice cream ki dinga bani a baki sai na zauna idan ba haka ba tafiya zanyi.
Da sauri Meenat ta dakko tace bari na baka idan Ma'eesha ta dawo sai ka tafi kawai,nan ta zauna damfamfam tana bawa Ameer Ice cream a baki yana sha yana latsa wayarsa ya Zama dan gata,a ransa yace wlh aure zance Aayan ya min kwana nan na huta nima.
0 comments:
Post a Comment