"Good.....sannan,baki iya addu'a ba sanda mutum yaga abinda ya tsoratashi?"
"Na iya" ta fada a sanyaye
"To daga yau ita zaki dinga ya,kada na sake ji ko ganin kina ihun nan......ki fahimta?" Nan ma kai ta gyada masa,ya jijjiga kai,shuru ya ratsa na second biyu
"Kin yini lafiya?"
"Ina wuni" ta maida masa da gaisuwa da muryarta dake dan rawa har yanzu
"lafiya lau" ya amsa mata yana miqewa
"Ga saqo can daga kano" fadin kano din da yayi ya sanyata warwarwwa ta farat daya,ya bita da kallo sanda yaga ta doshi kedar fuskarta na haske da murmushi,sai ua juya ya fice daga dakin,yanata juya al'amuranta a ransa,raino ne hajiya ta bashi,raino kuma me wuya da baisan sanda zai gamashi ba.
Sanda ya isa sassan hafsat yayi mamakin ganinsa a tsaftace,zai iya cewa ya manta lokaci na qarshe da yaga komai a muhallinsa a sassan nata,baiyi dai magana ba,amma kuma hakan ya masa dadi, zuciyar sa kuma ta sauka,akaci sa'a a yau din ta danyi wankan dare,ta kuma qure adaka da daya daga cikin tsadaddun suturun da yake mata,don tana son ta sake amintar dashi,ta kums kore kowanne zargi daga ransa,uwa uba kuma akwai kudaden da takeson karba daga wajensa a daren.
*********To tsahon kwanaki ukun da sukayi a bauchin widad ita kewa hafsat din dukkan wasu aikace aikacen sassanta,kama daga wanke wanke shara da wankan yara da dyk wata lalurarsu,koda bata shigo sashen ba zata shigo da kanta ta fiddota,idan abbas yana gida yafi zama sashensa,takanntattara ta bishi can,bata fita sai idan yasa qafarsa yabar gidan shima.
Baisan meke faruwa ba,tunda ya sani akwai alamun tsoronsa sosai tattare da yarinyar,bayason ya dinga matsa mata ko takura mata,ganin yadda taje sakewa walwalarta take qaruwa idan tana tare dasu mimi sai ya saki komai shima,wuni take hidimar sassan hafsat din,girki kawai hafsat din keyi,itama widad din taje tayi nata.
Quruciya qarancin shekarunta da rashin wayo ya sanya bata dauki hakan a bakin komai ba, saidai wasu lokutan tana jin aikin kamar yayi mata yawa,amma bata fasa yi mata ba,don a ganinta gaba take da ita,sannan tana samun sassaucin mugun tsoron da hafsat din ta dasa mata a ranta,tsoron abbas din da koda yaushe take zayyana mata abu kaza babu kyau....abu kaza babu kyau,ki tsare mutuncinki,dukka wani halali ta haramta mata shi,tayi amfani da wayo da dabararta da shekaru data daranma widad din.
Ranar lahadi da yammaci suka tattara suka bar bauchin,kamar wancan karon,wannan karonma wani abune ya tsaya mata a rai,ta zubawa motarsu idanu sanda take fita daga gidan,zuciyarta a mugun quntace,saidai taci alwashin tafiyar tasu babu abinda zata bari ya sauya,data koma cikin gidan kuma ta sake qarewa sashenta kallo taga yadda ya fara komawa hayyacinsa,sai taji inama widad din a kadunan take,ta tuna gobe fa itace zatayi dukkan hidimar da widad din ke mata,ga shirin makarantar mimi,ranta sai ya baci,haka ta wuni tana qunci tana kuma jibgar yaran,saboda kwanaki biyun bata saka hannu a hidimarsu,duk wata lalura tasu widad dince,wanka tsarkin kashi abinci da sauransu,su kansu yau din duk sai suka zama sukuku,kada ma mimi taji labari,minti daya biyu saita kira sunanta,saida hafsat din ta fara doke mata baki sannan ta samu salaama.
Tun a mota widad in ta dinga bacci,baccin gajiyar data debo a kaduna na ayyukan wahalar hafsat,koda suka isa gida ma sai daya tasheta,ta murza idanunta ta buda motar ta fito a kasalance tayi sassansu.
Sallar magariba da isha'i kawai tayi ta sake kifewa a dakinta,sanda ya shigo gidan tayi nisa a duniyar bacci,sai ya maida mata qofar dakin nata ya rufe kawai ya sanya ledar takeaway din a fridge don kada ya lalace,mamaki yana dan kamashi da irin baccin da takeyi,kamar wadda bata samun baccin kirki.
Washegari da zai miqa ta makaranta ma kusan a makare suka fita,don sai daya shiga dakin ya tasheta sannan ta samu ta shirya a gurguje,don ko gyaran gidan bata samu yiba sai da aka taso daga makarantar,samuel ya aika ya daukota a motarsa ya ajeta gidan,tana shigowa suna cin karo da maami matar gidan,wadda yaranta duka maza ne,shi yasa ba wanda ke shigowa sashen
"Yaushe kuka dawo haka babu sanarwa?" Ta tambayi widad tana qare mata kallo cikin uniform din da suka bala'in karbarta
"Jiya da daddare ne,uncle yace na shigo na gaisheki ma daman idan an taso daga makaranta"
"Oh....makaranta kenan aka fara zuwa,aji nawa?" Ta sake tambayarta
"S.s one" kai ta gyada,lallai namiji,shan koko daukan rai,banda qalata irin tasa,itadai bataga abun daukarwa kai wannan dawainiyar ba,amma wataqila kyan yake rudarsa
"To Allah ya taimaka"
"Ameen,a dawo lafiya" ta fada tana yin gaba zuwa cikin gidan,ita kuma ta amsa tana shigewa motarta,idanuwanta akan widad din,kamar zata gayawa hafsat sai kuma ta share,don bataga abinda yarinyar tayi mata bama,kawai dai hali irin na mata,taya kishin da bai shafeka ba.
Sallar azahar kawai tayi ta fara gyaran gidan,duk da muguwar gajiyar da tayi,ta tuna sanda take dawowa daga makaranta,ummu tasa an hada mata komai,saidai tayi wanka taci abinci tayi shirin islamiyya,take qwalla ta kawo a idanunta,taji kamar ta watsar amma ba zata iya zama a datti ba,tsahon rayuwarta ko kadan batasan dauda qazanta ko datti ba,ummun nada wata irin mugu muguwar tsafta,kowa ya shaida,hakanan duk matan gidansu babu qazama.
Tana gama mopping taji ana saka key za'a buda qofar sashen,ta tsaya a dan tsorace tana kallon qofar,har ya kammala budewa ya tura ya shigo.
A kanta idanuwansa suka sauka,yayin da kuma ta sauke ajiyar zuciya tana jin tsoronta na zagwanyewa,baisan yadda akayi murmushi ya subuce masa ba,don ya gane tsoron nata taji da taba qofar da yayi,itama sai murmushin ya kubcewa fuskarta,ta kuma ji yar kunya ta kamata,tayi qas da kanta tana tambayar kanta me yasa ta fiya tsoro haka
"Matsoraciya kawai" ya fada a hankali,murmushi ta danyi sannan ta turo qaramin bakinta gaba a shagwabe,kwatankwacin irin yadda takewa ummu,sai ya samu kansa da binta da kallo,batace komai ba shima haka,ya zauna hannun kujerar falon yana goye da hannayensa a qirji,lumsassun idanunsa nakan dan qaramin bakinta
"Me kika ci?"
"Ni?" Ta tambayeshi tana fidda idanu waje hadi sa taba lips dinta kamar mai tsoron wani abun, murmushi ya sake subuce masa
"Eh me kikaci baki ajjiyemin ba?" Fuskarta ta narke a shagwabe
"Nifa banci komai ba uncle,yunwa ma nakeji" ta fada tana shafa cikinta,shafaffen cikin nata yabi da kallo, idanuwansa suka kai har kan qugunta daya fito sosai ta cikin skeet din material na jikinta,ya janye idanunsa yana sauke numfashi,hirar da abokan aikinsa moses jackson da andrew sukayi yau ta fado masa a rai,har a lokacin suka cika shi suka kuma dameshi ya nemi tashi ya basu guri,sai suka dinga masa dariya suna tsokanarsa,ya sansu sarai,su din mayun mata ne,daya daga cikin abinda yasa ko kusa baya bari sukai ga ganin iyalinsa
"Ina zuwa,bari na fito sai naga yau me za'a koya" sosai taji dadi,don har hakan ya bayyana saman fuskarta,tana son taga ta iya kalolin girke girke,saboda zumudi a falon ta zauna tayi jiransa,ba jimawa sai gashi ya fito.
Sauri tayi ta dauke kanta sanda ya fito din,boxer ne a jikinsa sai wata armless shirt farare,kayan sun masu kyau sosai,saidai sun fidda qirar jikinsa.
Har ya kusa isa kitchen din yaji bata biyoshi ba,sai ya waiwayo yana dubanta,tayi hanzarin sake dauke kanta gefe tana turo baki,shi wasu abubuwan idan yayi kamar baijin kunya wai?.
"Ko baki shirya ba?" Ya tambayeta yana tsareta da idanunsa da suka rusuna yau din qwarai,kai ta girgiza ta kuma amsa masa ba tare data kalleshi ba
"Na shirya.....amma.....amma" sai kuma ta kasa qarasawa
"Amma me?"
"Ka saka kaya don Allah mana" murmushin da bai shirya bane ya qwace masa,ya kalli jikinsa sannan ya dawo da dubansa kanta
"Wannan meye a jikina idan ba kaya ba?"
"Amma uncle,kalli gafarka kalli hannunka fa,ummu idan su yaa ma'aruf suka fito haka fada take musu fa" ta fada a shagwaben nan nata kamar zata saki kuka.
Lallausan murmushi ya subucewa fuskarsa,for now yana ganin ya kamata ace ta fara sanin bambancin mutanen gidansu dashi,wannan yasa ya fara takowa a hankali cikin lallausan carfet din falon,bata lura dashi ba sai ganin mutum tayi dab da ita.
Gabanta ya fadi,sai taja baya kadan,bai damu ba ya zauna a gabanta saitin qafafunta yana kallon idanunta dake cike da quruciya,ta kuwa bata fuska sosai,gabanta yanata faduwa
"Akwai bambanci tsakanina dasu yaaya ma'aruf da sauran duk 'yan gidanku,ni mijinki ne,na biya sadaki an daura min aure,ni dake ya halatta muga komai na junanmu,mu taba juna,mu kwana guri daya....muci abinci tare,na ganki a duk yanayin da kike....koda tsirara kuwa....."
"La ilaaaaa" ta fada da qarfi hade da wani irin kuka,idanunta a kansa, tsoronsa yana shigarta,ta kwashe qafafunta ta mayar saman kujerar kamar mai shirin zurawa da gudu.
Wata dariya ta bashi,wadda a wannan karon ya kasa riqeta sai daya dara,hannunsa saman bakinsa yana qoqarin controlling na dariyarsa,he don't know what to do next kuma.....he don't know how to explain her, tabbas goyon kakace ta gaske,kuma symptoms ne na cewa ta samu tarbiyyar qwarai.
"Shikenan,is okay,ya isa,bazan kalli jikinki ba,amma sorry for saying that.... shikenan?" Da qyar ya shawo kanta suka shiga kitchen din,yana hada girkin yana nuna mata kamar yadda suka saba,saidai sam taqi sakewa dashi,yana matsowa take komawa baya,gashi shi ba gwanin hira ba,biyu ta hadu,da haka dai ya dinga nuna mata har suka kammala.
Ita ta zuba abincin a warmers takai dining,ta gyara kitchen din,ko kafin ta fito har yayi alwala ya leqo yace mata ya wuce masallaci,don haka itama tana gamawa alawar tayi,tayi sallah sai kuma ta dawo falon ta zauna, maimakon taci abincin amma sai taji ba zata iya ci ba har sai ya dawo,hakanan ta zauna zaman jiransa,wayarta na hannunta tana game tana dakon shigowarsa.
*Arewabooks:Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*
Page 54
Tana tsaka da game din taji mararta ta murda,ta dakata tana zare idanu jin wani abu mai danshi ya fara fitowa ta jikinta,gabanta ya fadi,kada dai ace wannan jinin ne da bataso yazo mata?,yanzu ya zatayi?,yi na qarshe da tayi suna tare da latifa,hankalinta a kwance yake,ta dinga kula da ita da ciwon mararta.
A tsorace tadan miqe don duba jikinta,sai tayi sauri ta koma ta zauna saboda mararta data murda mata,ta dafe marar tana jin yadda danshin ke biyo jikinta,hankalinta ya tashi sosai,kawai sai kuka yazo mata,tana ganin kamar ba zata iya ba. gumi ya fara yanko mata ya gauraye da hawaye,ta soma jan majina tana raba ido.
Sallamar da yayi cikin falon ya sanyata sake tsorata,sai taji kamar ta tashi ta zura da gudu,idanunshi a kanta,cikin mamakin yanayin da ya ganta a ciki,itama shi take kallo kamar wacce ta aikata wani mummunan abu.
A nutse ya qaraso,hannayensa zube a aljihun wandonsa
"What's happening?,lafiya?" Tsareshi taci gaba dayi da idanu,saidai qwalla ta cika idanunta fal,har bata iya ganinsa sosai,kallonsa take kai tsaye,kamar mai tsoron wani abu dake a jikinsa,maimakon ta amsa masa sai hawayen ya fara saukowa,ta sake dora hannunta saman mararta dake qara murda mata.
"Me ya faru ne?" Ya sake maimaita tambayar yana sake qoqarin karantar fuskarta,hawayen dai taci gaba da fitarwa,a hankali idanunsa ya sauka saman hannunta,yadan kalli wajen na tsahon wasu mintuna,sai ya matsa gaba a hankali yana qoqarin miqa hannunsa,sai kuma ya janye yana duban qwayar idanunta
"Ciwo cikin yake miki?" Kai ta gyada masa,Hawaye na sake saukar mata,sai ya sake matsowa yana cire hannunsa guda daya daga aljihunsa
"Oh sorry....sannu,tun yaushe?"
"Yanzu" ta fada a narke, zuciyarta tana karyewa,saboda komai yayi mata tana kallonsa banbarakwai,don ba haka ummu ta saba mata ba,indai tace bata da lafiya gaba daya komawa take kamar jinjinniya a wajen ummu,ta yita tattarota tana langabe mata a jiki,takanyi kamar ta maido ciwon a jikinta
"Muje kici abinci,sai mu fita na kaiki kiga likita ko?" Kai ta girgiza da sauri,don ita bata qaunar ma abinda zai sanya ayi mata zancan asibiti,bata qaunar magani sam sam sam,babban abinda yake saka a gansu a rana ita da ummu kenan
"Why.....zaki zauna ne a gida cikin yana miki ciwo?"
"Ai zai daina" ta fada muryarta na rawa,saboda yadda ciwon ya fara mata azaba da gaske,wannan shine karo na biyu daya taba mata haka,duk da cewa duka duka period din nata ma wannan shine yinta na hudu.
"it is not possible ki zauna da ciwo,oya......taso kici wani abun ko kadanne idan ma ba zaki asibitin ba" ya furta yana miqa mata lallausan hannunsa mai dumi,wanda ya wadatu da sassanyan qamshinsa.
Hannun ta kalla sannan ta rintse idanunta da gaske tana jin yadda ake kartar mararta,yadda tayin sai ya tuna masa koda wasa ba zata taba yarda intentionally su hada hannu ba,don haka kansa tsaye ya miqa hannu ya kamo.hannunta guda daya,ya kuma dagota gaba daya.
Luuuuu ta tafi jikinsa ba tare data shirya ba saboda wani azabar murdewa da marar ta sakeyi fiye da dazun,kamar numfashin ta zai bar gangar jikinta,take ta zabi bin gangar jikinsa ta yiwa kanta madogara,tana gama samun kyakkyawan masauki saita saki kuka tana kiran sunan ummu,hannayensa ya saka gaba daya ya rufeta da kyau cikin jikinsa.
A yadda ta samu masauki me kyau cikin jikinsa ya sanya hatta da bugun zuciyarta da kai kawon numfashinta tana jinsa sosai cikin jikinsa,kamar jininsa suke bi cikin kowacce bugawa da zaiyi.
Sunkuyo da tasa fuskarsa yayi ta gefen fuskarta dake kwance kan qirjinsa da yake ya fita tsayi sosai ya cusa tasa fuskar yana leqata,wani irin kuka take a hankali hade da sheshsheqa,hucin numfashin ta ya daki fuskarsa,sai ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na tashi,ya sake riqeta sosai zai motsa,saita kuma qanqameshi tana sake sakin kukan,abinda ya sanyashi kusan daskarewa a wajen,gaba daya ta manna masa jikinta da kyau,lallausar fatarta takai ko ina a jikinsa ba tare data sani ba,ita din kuma tayi hakane saboda batason su motsa daga wajen,ta tabbatar ta bata wajen da jini,bataso kuma ya gani,kunya takeji,da wanne ido zata kalleshi?.
"Let's move from here,mu koma daki ki kwanta na fidda mota kiga likita,jikinki shacking yakeyi" yana fada ya sunkuya kawai ya dauketa cak,bata da sauran zanbi sai kawai ta boye kanta cikin jikinsa,bayan ta saka hannu ta riqeshi da kyau.
Bai lura da komai ba sai daya shimfide ta saman gadonsa sannan yaga hannunsa ya baci,ya daga kai ya kalleta,sake saka masa kuka tayi,abinda taketa gudu kenan,ta rintse idanu tana jiran jin fada ko duka daga wajensa,kamar yadda yaa ma'aruf ya taba mata saboda kawai ta kawo abinci ya bata flask din ya riqe hannunsa ya baci.
Maimakon taji abinda ta zata saima jiyo sautin ruwa da tayi a toilet,ba jimawa ya fito da alama wankewa yayi,suna hada ido ta dauke kanta hawayen naci gaba da sauka,ciwo da kunya duka suka hadar mata,ya qaraso gabanta a hankali ya tsugunna
"Dama kina period ne?" Wayyo Allah,ji tayi kaman zata nutse a wajen,ta jawo filo ta cusa kanta tana sake sakin kuka,wannan abun sam bai kyauta mata ba,inda ta san zaizo gida zata dage sai ya kaita.
Sake maimaita mata tambayar yayi amma shuru, ganin da gaske ba zata amsa mishi da komai ba,taqi daga kai ma ta fuskanceshi,sai kawai ya miqe yana murmushi ya fita a dakin.
Da kansa ya gyara wajen data bata din a falo,wajen bashi da wani yawa sosai,ya dauki waya ya kira na 'yan mintuna ya kashe.
Da pad ya dawo mata,ya ajjiye mata yace ta shirya zai fiddo mota suje asibiti,yana zaune a falo ya dora qafa daya kan daya yana amsa waya ta fito tana rab'e rab'e,kunya kamar qasa ta tsage ta shige,wayar na a kunnensa ya waiwaya ya dubeta,can qasan ransa fal dariya,duk da babu ko alamun hakan a saman fuskarsa,ya jima baiga yarinya mara wayo mai tsananin tsoro da kunya irinta ba,iya period kawai data fara ya gani?,inda ace ya karba budurcinta ne fa gaba daya?, Shi kansa daya raya zancan a ransa sai daya sake maimaitawa,sai kawai qaramin murmushi ya kubce masa,ya cije lips nasa na qasa kadan saboda yadda yaji jikinsa ya amsa gaba daya,baisan lokacin da hakan zai faru ba,amma tabbas duk sanda ya kasance qila saita kusa mace masa saboda tsoro.
Wayar ya kashe ya mayar aljihu sannan ya miqe,ya tako kadan gabanta
"Zaki iya tafiya?" Kai ta jinjina masa ba tare da ta iya kallonsa ba
"Muje to na gani idan zaki iya din" ya matsa gefe yana kallonta,ta rabashi a hankali ta fara takawa tana hada hanya,taku uku ya cimmata,ya riqo kafadunta suka ci gaba tafiya,tanason zare kanta,amma hakan da yayi mata saita dinga jin kamar relief yake bawa ciwonta,a haka suka qarasa,ya buda gaban mota ya sanyata ya kwantar mata da kujerar,sannan ya shiga ya tayar da motar suka fice daga gidan.
Da yake private hospital ne basu samu wani layi ba suka samu ganin likita,duk tambayoyin da yayi mata kusan shuru tayi,tanajin kamar ta narke,maza biyu a daki guda suna mata tamba game da period dinta,abinda ko acikin gidansu boyewa take ba kowa yasan ta fara ba, murmushi likitan yayi ganin lokaci lokaci tana satar kallon abbas
"Yallabai,da alama kai din ba yayanta bane na hannun dama,ko zaka bamu waje qilan tafiyin bayani" haka kawai cikin ransa yaji bazai iya barinsu su kebe ita dashi ba,don yaga baima fahimci matar aure bace,yayi yunqurin miqewa da nufin matsawa daga koda zuwa bakin window ne,saiji yayi caraf an kamo hannunsa,ya waiwaya a hankali,itace ke kallonsa tana qwalla
"Kada ka tafi please" hada ido sukayi da likitan,sai ya saki dariya sannan ya miqe
"Ta gaya maka abinda takeji,sai kayimin bayani,ina zuwa bari na samo nurse,za'a yi mata scanning,tunda kace ciwon mara ne" sai likitan ya cire abinda ya saqala a wuyansa ya ajjiye ya fice daga office din.
Cikin kunya ta soma qoqarin zame hannunta daga nasa,amma saiya qara matsowa yana sanya dukka tafukan hannunsa a ciki da saman nata,ya rahe gap din dake tsakaninsu sosai yana dubanta
"Uhnnnn.... tell me,kinga idan ya dawo baki fada ba zan tafi na barku tare" qoqarin tsaida kukan nata take tayi,taja majina sannan tace cikin muryar kuka
"Marata ce take ciwo sosai" ta fadi cikin mugun jin kunya
"dai dai ina?" Ya tambayeta yana kallon qwayar idanunta,sai ta motsa hannunta dake mararta kadan,kamar mai tsoron kada ya taba hannun nata.
Idanunsa ya mayar kan hannun nata,sai yasa yatsansa ya nuna wajen
"Wajen nan kenan?' ta gyada kanta a hankali,sai ya dauke dubansa daga wajen yana fidda numfashi,ya miqe a hankali,yayi taku biyu kenan saiga likitan ya dawo,bayansa wata nurse ce,zata kusa shekaru talatin,ba yarinya bace.
Yana dariya ya tambayi abbas me tace?,ya zube hannayensa a aljihun wandonsa yana duban likitan
"Ciwon maranne dai"
"Ba damuwa,da Allah ki mana scanning,bari naje mota na dawo" ya sake fada yana diban wasu takardu ya fice.
Sanda taga an gama saitan scanning machine din tace kuma tahau sai ta fara zare idanu,ganin alamun tana jin tsoro sai nurse din ta dubi abbas
"Yallabai ko zaka taimaka mata" a nutse ya maida dubansa ga widad din,itama shi take kallo,idanun nan har yanzu qwalla ce kwance a ciki,ya cire hannayensa da tun dazun ke aljihunsa,ya tako a nutse ya iso gabanta.
Sosai ua tsugunna a gaban nata,cikin murya qasa qasa, yadda ba wanda zai iya jinsu ya fara magana
"Kije ta dubaki,few minutes ne ta gama miki,ba ciwo ba zafi,just relax...." Baki ta kwabe tana dubansa
"Tsoro nakeji"
"I promise you ba abinda zakiji,muje na rakaki" yadda take a tsorace yasa bata damu da kama hannunta da yayi ba,ya kaita har kan gadon sannan ta kwanta.
"Dage rigar taki" nurse din ta fada tana dauko cream din da zata shafa mata saman cikinta,sai ido ya sake raina fata,matsawa yayi dab da gadon,yasa hannunsa a hankali ya fara janye rigar jikin nata,da hanzari ta riqe tsintsiyar hannunsa,sai suka hada idanu,ya tsareta sosai da manyan idanunsa masu wani irin kaifi da tasiri,ya girgiza mata kai murya kuma can qasa yace
"Nooo,i said just relax" sosai taji idanun nasa sun mata nauyi,saita kauda kanta gefe,hawayen da suka cika idanun nata suna gangarawa ta gefe.
Kamar wanda aka zarewa laka haka ya dage mata rigar har zuwa saman cikinta, kyakkyawar farar fatarta mai sulbi ta bayyana,ya koma a hankali da baya yana jin kamar iska na yawo dashi,ya jingina da wani qaramin locker dake wajen idanunsa nakan saman fatar cikin nata.
*Arewabooks:Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 55
Da numfashinsa da idanunsa ya dauke lokaci guda sanda taja zanin nata sosai qasan marar tata,har jan pant dinta yana bayyana
"Ya Allah" ya furta yana sake rintse idanunsa,har suka gama bai bude ba sai da yaji nurse din na magana
"Zaki iya tashi?" Ta tambayeta,ya bude idanunsa a hankali ya maida kanta,sai ya taka a hankali zuwa gabanta,ya miqa mata hannunsa,idanunta a qas, karon farko da kunya tayi mata mugun kamu fiye da ko yaushe ta miqa masa hannun nata,ya dagota a tausashe.
Sosai ta zauna saman gadon tana gyara daurin dankwalinta, likitan ya shigo yana qarasawa gaban computer scanning din yana duba scan din data bari a jiki
"Ba wata matsala,zan rubuta mata magunguna,zata samu relief in sha Allah".
Koda suka fito dinma tana riqe a hannunsa,gaba daya ta narke masa,tana ta sharar qwalla,ummu take tunawa da yadda take kula da ita idan bata da lafiya,dan riqetan da yayi sai takejin kamar tana tare da ummun ne,don haka ta narke masa sosai kamar yadda takewa ummu.
Tun a pharmacy din cikin asibitin ya siya magungunan,fruit kawai ya tsaya ya siya a hanya suka wuce gida.
Dakinsa kai tsaye ya wuce da ita,ya shiga kitchen da kansa ya dauko gorar ruwa da cup,ya zuba abinci a plate ya zauna da kansa a gabanta yana dubanta
"Kici abinci,magani zaki sha" kai ta girgiza,fuska yadan hade kadan,ya zama serious,ya debi abincin da kansa yakai bakin bakinta
"Oya....karbi" haka ta dinga bude bakinta yana saka mata abincin,har yanzu hawayenta yaqi tsayawa,duk ta narke,kamar yadda takewa ummu,bai saba daukan shagwaba irin wanna ba,sai ya rasa ta inda zai bi da ita,a haka ya samu tadanci,ya balla mata magungunan ya bata tasha,sannan ya miqe yana kallonta
"Ki huta kadan,sai na rakaki ki kwanta" ya fada muryarsa can qasa,saita gyada kai tana rintse ido,kawai yadda zata tafi dakin ta kwanta ita kadai take hasasowa.
Toilet ya shiga,ya sauya kayansa zuwa jallabiyya mai sulbi saqar qasar india,ya daura alwala,ya dawo cikin dakin ya shimfida abun sallah yana dan duban sashenta,ta sanya pillow daga bayanta,idanunta na a lumshe,amma da alama idanunta biyu,sai ya juya ya kabbara sallarsa.
Tun tana satar kallonsa da kadan da kadan har bacci ya soma rinjayar idanunta,tayita dagewa batason hawa gadon sosai,yana fusgarta tana qwacewa,har yaci qarfinta,ta kwanta riris saman gadon,bacci mai dadi yayi gaba da ita saboda sassaucin ciwon data samu.
Da murmushi akan fuskarsa yake dubanta sanda ya idar da sallar yaga tayi bacci,ya qarasa addu'o'in sa ya sauya kayan baccin sannan ya matso dab da ita,ta ranqwafa saman kanta yana kallon fuskarta sosai da sukayi gab da juna,siraran tausasan labbanta masu kama da an shafa musu ban lebe suka dauki hankalinsa,ya miqa hannu a hankali ya dora saman lips din nata yasa yatsunsa ya shafasu kadan,saita motsa,ta turo baki gaba cikin shagwaba
"Ummu na.....ummu don Allah fa ni...." Ta fadi tana yin juyi,abinda ya sake kawo kusancin dake tsakaninsu sosai har suka fara musayar numfashi,ta haye kusan rabin cinyarsa,ya kalleta yadda tayi relaxing a jikinsa,jikinsa ya bashi idan yace ma zai tasheta ne wata really rigimar ce,don haka kawai sai ya zame ya kwanta,hakan kuwa sai ya zamar mata kamar wata hanya data samu ta shige jikinsa sosai,harda curewa waje daya kamar kwanciyar yaro a cikin mahaifiyarsa,taja hannunsa kuma ta riqe gam tana cewa
"Ummu......na....gode" ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke,da alama mafarki takeyi,hakanan ya samu kansa da sake kusanto da ita cikin jikinsa suna musayar dumin juna,ya lumshe idanunsa a hankali yana jin wani abu yana bin jinin jikinsa,zuciyarsa ta fara sauya tsarin bugunta,sannu sannu numfashinsa ya fara sauyawa,ya dinga fita a jejjere,mode dinsa ya canza gaba daya,yasan me jikinsa yakeso,amma bayajin wannan buqatar zata samu,ta yaya ma daga samun kusanci da yarinyar zuciyarsa zata bijiro da wannan babbar buqatar?,bashi da sauran zabi illa qoqarin zameta daya fara yi daga jikinsa,saidai ta riqeshi qam,daga bisani ma da yayi nasarar zameta din,juyi daya tak tayi ta dawo jikinsa,idanunta a rufe amma kukan shagwaba take saki,yayi shuru yana sauraren siririyar muryarta dake fidda wani irin kuka a shagwabe,wanda yake qara sanya tsigar jikinsa zubawa,ya sake rufe idanunsa da kyau yana sake qoqarin zameta a karo na barkatai,amma saita riqo hannunsa,ta kuma cusa kanta cikin qirjinsa sosai.
Duk yadda yaso yayi controlling kansa ya kasa,komai na jikinsa ya gama amsawa,qwaqwalwarsa kuma ta dauki chargy fiye da kima,dukka hannuwansa ya sanya ya jawota cikin jikinsa,shi da ita suka sauke ajiyar zuciya a tare,a hankali ya nutsa hannunsa cikin sassalkar sumarta dake fidda qamshin man kitsonta mai hade da sinadarin menthol me sanyi,cikin sanyi taushi da nutsuwa ya fara yamutsa shi yana jin dukkan wata gaba ta jikinsa tana sake amsawa,abinda ya sanya widad sake sakankancewa cikin baccinta,zuciya da ranta suna bata tana tare da ummu.
A nutse hannunsa ya biyo tsahon gashin nata daya sauka har zuwa gadon bayanta,yana kaiwa qarshe hannunsa ya zarce ta cikin rigarta dake da faffadan baya,lallausan tafin hannunsa ya hadu da fatar bayanta mai santsi da dumi,ya zura hannunsa a hankali yana shafota,idanunsa suna sake nauyi da kyau,zuciyarsa na sake dugunzuma da dokantuwa da samun biyan buqatar ransa,bai gushe ba yana ci gaba da murza fatar bayanta,duk inda yayi qasa da hannunsa zip din na bashi hadin kai wajen zugewa,har yakai can qasa,ya dora hannunsa numfashin sa yana sake gudu kamar wanda yayi tsere,wannan ya sake sanyashi matsa qaimi,ya birkitata a hankali ya soma sabule rigar tata,ya sake dora hannayensa saman wuyanta,hancinsa yana kaiwa wajen,sassanyan qamshin daya zamewa jikinta kamar dabi'a ya zuqa,qamshin da zai iya cewa tunda yake bai taba jin irinsa a jikin hafsat ba,sai yaji bashi da muradin daya wuce yayi sharing qamshin nata da tasa gangar jikin,don haka yasa fuskar sa sosai saman fatar wuyanta,ya kuma fara gangarowa ga qirjinta a hankali yana sauke wani irin birkitaccen numfashi.
A hankali ya fara isowa ga tudun saman qirjinta,abinda ya sanya shi da ita sukaji tamkar an sanya musu wani irin electric shock,ya qanqameta da kyau yana sake zuqar qamshin turaren,yayin da ita kuma taji kamar ance mata tashi!!!,cak kwanyarta ta tsaya waje daya tana son rarrrabe abinda yake faruwa,sanyin daya fara ratsa fatar jikinta ta fahinci saura kadan rigarta ta sauka qasan qirjinta,yunqurin riqe masa hannu tayi cikun matuqar tashin hankali amma ta gaza,saboda yadda jikinsu take rawa gaba daya ita dashi
"Don Allah.....don Allah" ta fara fada cikin mugun rawar murya da kuma kuka,cak ya tsaya kamar wanda aka sanyawa sarqa,ya zame hannunsa daga jikinta a hankali ya mirgina gefe yana fadin
"Hasbunallahu wani'imal wakil" can qasan maqoshinsa,yayin ruf da ciki yana cusa kansa cikin katifar tare da qoqarin dawo da nutsuwarsa cikin jikinsa.
Tuni takai bango,ta tattare dukka jikinta guri daya,tana riqe da rigarta a hannu qam qam,hawaye sun yiwa fuskarta ado,kuka take sosai cikin tsoro da kuma tashin hankali.
Dakin ya dauki shuru na wasu sakanni,har yanzu kansa na cikin katifar,yana sauraren kukan da take rerawa,wanda ya dinga jinsa har tsakiyar kansa,wani tunani yazo mata,ta soma maida rigarta da sauri sauri,saidai ta gaza zuge zip din,sai kawai ta sauke qafafunta qasan gadon ta miqe ta nufi qofa.
Cikin jikinsa yaji alamun takunta,ya daga rinannun idanunsa da har yanzu basu gama komawa dai dai ba yabita da kallo,duk da dakin ba wadatar haske amma kuma yana iya ganin bayanta daya bayyana sosai saboda rashin zuge zip din,wani irin baya dake dauke da wani shape mai jan hankali daya taimaka wajen fidda shape na mazaunanta da qugunta.
Bayajin koda yayi magana zata fita daga maqoshinsa,don haka ya miqe kawai cikin wata iriyar kasala da mutuwar jiki,kamar wanda yasha abun maye,taku uku ya cimmata,ya isa jikin qofar,ya murza key sannan ya waiwayo ya zube mata idanuwansa gaba daya yana kallonta
"Koma ki kwanta" ya fada da dakusashiyar muryarsa,saita janye gefe tana maqale kafada,bai sake mata magana ta biyu ba,illa hannuwansa daya sanya ya dauketa cak,bai direta ko ina ba sai saman gadon,ya kwantar da ita saman pillow,yaja mata duvet sannan ya sunkuya yana kallon qwayar idanunta sosai
"Sleep......banason na sake jin kukanki,idan kuma kika sake tashi....tom" ya fada yana gyada kansa,alamun akwai abinda zai biyo baya,sai ya matsa yaja da baya,sannan ya juya ya shige bandaki.
Runtse idanunta kawai tayi tana qoqarin danne kukan nata,wani haushinsa da tsanarsa takeji,ashe dan iska ne sosai haka?,tunda take ba wansa ya taba yi mata abinda yayi matan sai shi,boye kanta ta sakeyi sosai cikin duvet din tana share hawayen daketa bulbulowa daga idanunta.
Ya jima cikin toilet din sannan ya kunna ruwan zafi dana sanyi ya daidaita temperature dinsu,ya sakarwa kansa shower,bai taba zaton yarinyar zata kunnashi haka ba,akwai wani irin magnet tattare da ita dake saurin jan zuciya da kuma gangar jiki,yayi shuru ruwan yana gangara a sassan jikinsa,yana tuna qamshi da dumin fatarta,da wani laushi kamar fatar jariri,irin yanayin da yakeso tattare da matarsa,irin yanayin daya jima yana fasaltawa,hannu yasa saman kansa ya sharce sauran ruwan da bai gama diga ba sannan ya fita daga qasan shower din ya samu babbabn towel ya daura ya fito daga bandakin.
Koda ya fito turare kawai ya samu ya shafe jikinsa dashi ya sauya wata rigar,ya koma can daya side na gadon ya zauna yana kallonta yadda take nade waje daya,batayi motsi ba ko kadan,saidai duk da haka ya karanci bacci ya fara daukarta,saidai baccin baiyi nauyi ba,ya sauke ajiyar zuciya ya jingina bayansa da fuskar gadon yana sauke idanunsa kan agogon dake saman bedside yana duba time da date,yana buqatar zuwa bauchi lallai,saidai yau din Monday,zai iya jira har sai ran Friday kuwa?, tambayar da ta masa nauyi,kwanakin kuma yaji sunyi masa nisa da yawa,sai kawai ya jawo wayarsa,ya yanke bari ya kira hafsat din,at least ko hira da zata sake bashi nutsuwa ya samu daga gareta.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 56
Sanda yayi kiran farko har ta katse bata daga ba,bai qosa ba ya sake kira,dab da zata katse aka daga.
Sallama ya fara yi mata,cikin muryar bacci ta amsa
"Badai bacci ba?" Ya tambayeta da muryarsa da ta sake sanyi sosai
"Uhmmm....bacci mana,isan banyi bacci ba me zanyi,ka wuni hidimar gida data yara,kiranka ne ma ya tasheni,da banjin zan tashi har zuwa nan da asuba" idanunsa ya ragewa kaifi kadan,sarkin qorafi da mita,ya kauda wannan a kasalance yace
"Sannu da qoqari"
"Yauwa" ta fada a gajarce
"Ina yaran duka sunyi bacci?"
"Eh" ta sake amsa masa a tsaye
"Good......Allah yayi musu albarka"
"Ameen" ta kuma amsawa a gajarce,shuru na sakanni ya ratsa,ya zaci daga sound dinsa zata karanci wani abu,amma baiga alamun hakan ba,don haka yace da ita
"I missed you, that's why I call you,ko zan samu wani abu special haka who will cheer me up da daren nan" baki ta tabe daga can,zuciyarta na mata zafi,ya ma raina mata wayo ne kawai,me zata masa tunda ya zabi ta zauna a nan?,ai sai kowa ya zauna da lalurarsa
"Kai da kake da amarya?,me zaka nema a wajena?" Duk da baiso ba qaramin murmushi sai daya qwace masa,there is jealousy in her words,bai kuma shirya gamsar da ita ba,don haka yace
"Sister din taki yarinya ce qarama,she can't take all my needs,so dole ki tallafa mata kamar yadda kikacemin zakiyi" idanunta ta runtse tana jin wani ciwo,kamar da gayya abbas din yake gaya mata hakan,yanason ce mata yana samun kulawa daga wajen yarinyar kenan?
"It is better to go back to her" ta fada cikin haqiqancewa
"She's sick" shima ya amsa mata a gajarce,ba dacewa bane ya bata qofan da zata karanci me yake gudana tsakaninsu,wannan wani abu ne daya shafesu su biyu.
Bata shiryawa tashi ta zauna ba amma sai gata a zaune,qirjinta ya buga sosai,me ya sameta?,kodai ya aikata?,indai da gaske bata da lafiya to tabbatar suna tare a yanzu haka,tafi kowa saninsa,yana da tsananin tausayi da kulawa akan iyali,idan baki da lafiya kulawarsa ta musamman ce
"Tana ina?"
"No need ki sani..... just relax me madam" a yadda hankalinta ya daga bata jin zata iya masa komai
"I feel sleepy....so i can't do anything" Maimaita words din data fada din yayi a kunnuwanta sannan yace
"Alright.... good night" sai ya kashe wayar ya ajjiye ta a gefe yana shafa kansa zuwa fuskarsa hadi da furzar da iska,tunani kala daban daban cikin ransa da zuciyarsa,yana ganin kiranta amma sam bashi da interest na dagawa,saboda yana da yaqinij ba ta kirashi don tayi masa abinda yake da buqata bane,wala'alla ma ta kira ne ta bishi da qorafi ko kuma mita.
Kamar yadda ya zata kuwa saiga gajeran tex bayan ta fahimci bazai daga kiran ba
_Na gode da wulaqantani da kayi,ka daga wayar ka bani ita zamuyi magana,i called her,but bata daga wayan itama_
Tsaki yaja ya ajjiye wayar,mamakin halayen hafsat har yau basa barinsa,she call her to tell her what?,a wannan daren?,she refused to do what he wanted amma kuma tana son magana da weedad for what?,baisan sanda zatayi hankali ba da gaske,duk sanda tayi masa irin wannan sake fita takeyi daga ransa,daga qarshe qur'ani ya rungume sannan ya samu bacci ya daukeshi.
*_W A S H E G A R I_*
Ta jima da gama shiryawa cikin uniform dinta,amma ta kasa fitowa,tayi zaune gefan gadonta tana duban fuskarta time to time ta madubi,batasan yadda zata fuskanceshi ba,haushinsa takeji a zahiri,a badini kuma idan ta tuna abinda ya farun jiya sai taji kamar ta nutse a qasa,da qyar ta samu hawayen ta ya tsaya.
Tana jin an taba qofar za'a bude ta runtse idanu,idonsa a kanta,qaramar dariya tana cinsa,yasan wannan rufe idanun duka nasa ne
"Kin fasa zuwa school dinne?" Kai ta girgiza da sauri alamun a'ah,sai ta tashi tana juya masa baya,ta rataya jakarta tayo bakin qofa,a lokacin tuni yabar wajen.
Tayi tsammani Samuel ne zai kaita kamar jiya,sai data shiga motar sannan taga shine ashe,ya tada motar suka fara tafiya,babu wanda ke cewa da dan uwansa komai,har suka isa makarantar,ya cira kudi ya bata
"Ga kudin break,idan an tashi ki jira,idan ban samu zuwa ba samuel zaizo" bata iya hada idanu dashi ba tasa hannu biyu ta karba
"Na gode" ta fadi qasa qasa sannan ta juya da hanzari tana yin hanyar class,yana zaune cikin motar yana kallonta har ta shige sannan ya tada motar yana kada kai da qaramin murmushi kan fuskarsa yayi reverse yabar makarantar.
Wunin ranar sukuku tayishi,don ma 'yan ajin nasu suna da saurin sabo da jan mutum a jiki,nan da nan tadan fara sabawa dasu bayan tasan sunayen wasunsu,da azahar aka tashi,bata tsammaci ganinsa ba still sai gashi,yana sanye da uniform dinsa din nan dake qara masa wani mugun kwarjini haiba da kamala,da suka isa gida ta dauka zaya koma aiki ne,sai taga ya canza kaya ya kirata suka shiga kitchen.
Koda suka gama kowa ya diba nasa,dakinta ta wuce dashi taci a can,bata sake jin motsinsa ba kamar yadda ta wuni a kwance,sai da yamma ya leqo yace tasha magungunta ta shaida masa tasha,hakanan tun bayan magariba daya leqo ya tabbatar tasha maganin dare bata sake jinsa ba.
Wanka tayi tayi shirin bacci kamar yadda ta saba,saidai bacci yaqi zuwan mata,data gaji ta dauki wayarta ta duba,taga tana da kati a ciki sosai,kusan katin tun sanda aka siya wayar yake cikin layin,batasan na nawa ya loda mata haka ba,though dai bata fiya kiran waya ba,mostly saidai ayi kiranta.
Mutanen gida ta dinga kira,ummunta ta fara kira,sai abbanta,anty madina hajjaa sai anty deena,wadda sunfi jimawa da anty deena din,tana ta mata hannunka mai sanda da jirwaye mai kama da wanka akan kula da miji,saidai hankalinta baima wani kawo mata ba,tadai jita ne,sai kusan tara na dare sannan sukayi sallama.
Sam bacci ya qauracewa idanunta,ta dinga juyi ita daya tana tuna daren jiya,rabon da tayi cikakken baccin mai dadi irin na jiya har ta manta,saboda ita din mutum ce da tayi sabo da kwana a jikin ummu,shi yasa a kullum idan zatayi bacci da qyar yake zuwa mata tun bayan tafiyar latifa.
Karar wayarta ta katse mata tunaninta,har tadan tsorata ma saboda ta manta da ita,sunan mommy hafsat data gani ya sanyata tashi ta zauna ba shiri,gabanta yayi mugun faduwa,hakanan takejin mummunan faduwar gaba a duk sanda taga wani abu daya danganceta,kamar sunanta muryarta da sauransu.
Muryarta na dan rawa ta daga wayar tana sallama tare da yunqurin gaisheta
"Kina ina?" Ta tambayeta kanta tsaye ba tare da tabi takan gaisuwar da take mata ba
"Ina daki"
"Wanne dakin?" Ta tambayeta daga can gabanta yana faduwa
"Dakina"
"Abbansu mimi yace baki da lafiya jiya,me ya sameki?" Gabanta ya yanke ya fadi data tuna cewa a dakinsa ta kwana jiya,kuma koda ra farka cikin jikinsa ta ganta,ta fahimci hakanne?,kota gane?
"Ciwon mara" ta amsa mata muryarta nadan rawa kadan,abinda ya sake sanya shakku a zuciyar hafsat din,tsoronta ya ninku
"Kodai wani abun kukayi ke dashi?" Tambayar daketa mata yawo tsakar ka ta subuce ta fito daga bakinta,da sauri ta hau girgiza kai kamar tana a gabanta ne,hawaye kuma suka jiqa mata fuska
"A'ah mommy....wallahi ba komai,ciwon mara ne kawai Allah ki yarda gaskiya na fada miki" boyayyar ajiyar zuciya ta saki,sanin weedad din bata qarya sai hankalinta yadan kwanta,amma saita fuske saboda ta samu nasarar sake dasa tsoron hakan a zuciyarta
"Ohon miki idan ma wani abun kika yarda yayi miki,mutuwa zakiyi.....ina ruwan wani,nima ina gaya miki ne don ina sonki banaso ki mutu"
"Allah mommy ba komai" sai kawai hafsan ta kashe wayar donta qara tsoratata.
Sosai hankalin weedad din ya tashi,tana shirin bin kiran taji ya turo qofar,ta daga kai tana kallonsa,har qasan ranta tana jin haushinsa,ya danji wani iri ganin tana kuka,yana fargabar ko wani abunne ya sameta,yasan yau bai leqota da kyau ba,duka yau ya kulle kansa ne a daki yana aikin tracing din wani criminal a sirrance,abinda yasa ya baro office kenan,bayaso kowa yasan abinda yakeyi
"Yaaya?.....jikinne?" Kai ta girgiza tana turo baki,ta kuma tura masa qeya taqi kallonsa
"To ma sha Allah"ya fada duk da ya fuskanci kamar cikin fushi take,shuru ya ratsa tsakani na sakanni kafin ya miqe
"Ki ajjiye komai ki kwanta" sai ya juya yana shirin barin dakin,binsa tayi da kallo,tana jin kamar ta bishi,amma da ta bishi ya tabata gwara ta zauna a dakinta.
A jikinsa yaji kamar tana kallonsa,don haka ya dakata ya waiwayo,suka hada ido saita dauke kai,kamar xaiyi magana sai kuma ya fasa,ya saka kai ya fita.
Tun bai kai tsakiyar falon ba yaji ihunta,ya juyo da sauri,sai gata sunyi kacibus a hanya har tana fadawa jikinsa,taja baya da sauri jikinta yana rawa
"Mm....mage"
"A ina?"
"Bakin window" ta fada tana duban qofar dakin
"Muje na gani" ya fadi yana sakata a gaba,kafada ta maqale tana sakin kuka,kome zaiyi mata bata jin zata yarda ta bishi,haka tayi tsaye a wajen ya shiga dakin,bai jimaba ya fito
"Bata shigo ba,infact ta wuce ma,zaki iya komawa" waiwaya tayi inda yake,taga da gaske tafiya yake zuwa dakinsa,ta daga qafarta da sauri tabi bayansa.
Batasan ta cimmasa ba sai da suka tsaya suna kallon kallo shi da ita,yana riqe da handle din qofar yana dubanta,itama shi take kallo saidai batace komai ba sai aukin hawayen da take faman zubarwa
"Don Allah...zan karka tafi ka barni"
"Bacci nakeji" ya amsa mata a taqaice,saita sake fashe masa da kuka,hannu ya sanya ya dafe goshinsa
"Oh my goodness" ya furta a hankali,saiya maida manyan idanunsa kanta
"Me kike so?" Shuru tayi kamar ba zata amsa ba,sai kuma tayi qasa da kanta
"Zan kwana a nan" ta fada a hankali gabanta yana faduwa,zuciyarta na gaya mata girman laifinta,ta yaya zata hada dakin kwana dashi?.
Qaramin murmushi ya saki
"Silly girl" ya fada qasa qasa,ga dan banzan tsoro ga shagwaba da sakarci harda na siyarwa,sai ya matsa gefe daya
"Bismillah" ya furta a hankali,ta rabeshi sosai ta shige dakin,ya rufe qofar ya sanya key sannan yabi bayanta.
Ta jima a zaune har ya gama komai na shirin kwanciya bacci tana binsa da idanu,pillow ya dauka ya jefar a qasa sannan yabi pillow din ya kwanta idanuwansa a rufe yana karanto addu'an bacci,ya gama ya shafe jikinsa,ba tare daya bude idanun ko ya dubeta ba yace
"Ki kwanta kiyi kuma addu'a" a takure take sosai saman gadon,duk kuwa da cewa ita daya ce,duk juyin da zatayi idanunta a kansa,har sai data ji saukar numfashinsa a hankali alamun bacci yayi awon gaba dashi,sannu a hankali itama jikinta ya saki,wani bacci me dadi wanda babu fargaba a ciki ya sureta.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:huguma*
Page 57
To tun daga wannan rana kwananta ya dawo dakinsa,saidai tana kammala sallar asuba take komawa dakinta ta shirya shirin makaranta,wani lokaci shike kaita,wani lokacin kuma samuel ko daya daga cikin yaran dake qarqashinsa.
Aikin da yakeyi yasa a yanzun zamansa a gida yafi yawa,wannan ya fara haifar da shaquwa a tsakaninsu,duk da baya barin kowa ya rabi inda yake wannan aikin amma yawancin lokuta suna tare,badai hira sukeyi da ita ba,amma zata dauki littafinta ta zauna a wajen,ko ba komai tana jin motsinsa bata da kewa,lokaci bayan lokaci tana barin karatunta tadan zuba idanu tana kallonsa,idan sun hada ido kuma sai ta basar,murmushi kawai yakeyi ko yayi kamar bai gani ba yaci gaba da abinda yakeyi,aikin nasa ke bata sha'awa yake kuma burgeta,tanason masa tambaya amma kuma tana jin nauyi,don har yanzu bata gama sakewa dashi ba.
A lokacin yayi qoqari matuqa ya koya mata abubuwa da dama,har ya fara sakar mata,don majority ita ke dafa musu abincin rana,kuma ya ciyu saboda gyaran bashi da wani yawa.
Wannan karon ma bai samu zuwa bauchin ba sai bayan sati biyu,tanata hada kaya ta zaci da ita zaya je,sai yace a'ah,tayi zamanta,ta dinga masa kuka amma daga baya dole ta haqura,ya yiwa mai gidan magana matar gidan ta bata 'yar tayin kwana suke kwana tare,friday ya tafi ya dawo sunday da magariba,saita samu kanta cikin murna da farinciki ranar daya dawo din,wanda ita kanta batasan dalili ba,tunda dai ya tafi taji gaba daya bata da sukuni.
Zuwansa bauchi a yawancin lokuta bacin raine,yana zuwa ne kawai don ya sauke nauyin da Allah ya dora masa,ya kuma kwatanta adalci,amma baya ga haka baiga wani alfanu da yake samu ba,hafsat din ta yita mita da nunqufurcin bai taho da weedad ba,don ta tara ayyukanta jingim suna jiranta,gidan ya hada mugun datti da qura yadda ya kamata,to koda yaje ma kusan washegarin ranar a aikin kintsa gidan ya qarar dashi,daga qarshe sassan weedad din ya bude ya kwanta yayi baccin gajiya a falonta,ki sashen nata da babu dan adam baiyi wannan qazancewar ba,da yamma ya fice wajen hajiyarsa,wadda ta dinga jajjabin abinda yasa baizo da weedad din ba,a haka dai ya qare weekend din nasa a gantale babu wata kyakkyawar maraba.
Haka kawai ta samu kanta da son masa gwaninta,yana fita sallar magariba din a gurguje ta shiga kitchen,ta hada masa simple spaghetti jallop,da murmushi yake kallonta sanda ta dire masa ita,taliya ba cimarsa bace,amma kuma sai yaji ta burgeshi dari bisa dari,ko babu komai tafi hafsat din wadda a qalla nata shekarun sun ninka na weedad din,amma ko irin hakan batasan tayi masa ba,don haka yaji bazai iya watsa mata qasa a ido ba,yaja taliyar ya soma ci,taste dinta sai ya bashi mamaki qwarai,har ya kasa jurewa
"Yammata irin wannan abincin fa?,a ina kika koyo shi?" Sunan daya kirata dashi ya bata kunya,saita kifa kanta saman pillow tana dariya,batasan sanda suka fara irin wannan wasan dashi ba
"Kaine ka koyamin" kai ya girgiza yana sakin murmushi
"Wannan kaman ba aiki na ba" kuma ya fada dinne har zuciyarsa,saboda dandanon ya zarta yadda ya koya mata din.
Daya tashi komawa bauchi da ita ya tafi saboda hajiyarsa dake ta tambaya,hakan ya yiwa hafsat dadi,ta sake miqa dukka wasu ayyukan gida ga weedad din,bata samun zama ko hutu saita gama dukka wasu aiki na sassan hafsat din,hakanan hidimar yaran gaba daya ta dawo hannunta,wankansu wanki cire pampers,basu abinci da sauransu,tun tana jin gajiya da wahala har ya soma zame mata jiki ta saba.
Wani zuwa da sukayi,ranar asabar da azahar,tana kitchen din hafsat din tana gogeshi bayan ta gama wanke kwanukan da suka cika babban sink din kitchen din,cikin ranta cike fal da mamakin yadda take barin kitchen ya hada wannan uban datti da kayan wanke wanken kamar na gidan biki ko suna,mimi da nawwara na falon data gama gyarawa suna wasa,ta kadasu can don su barta ta gyara nan din a nutse,a dole ta sake qwarewa ta samu kuma experience sosai akan harkar kitchen da kula da yara.
Sau biyu anty ummee na sallama sai surutansu mimi,har sai data bude qofar falon ta shigo,tabi falon da kallo zuciyarta cike fal da mamakin yaushe hafsta ta koyo tsafta?,yaran da suka ankare da shigowarta suka watsar da kayan wasan suka taho da gudu suka rungumeta
"Ina babarku?"
"Tana dakinta,ta kwanta tace kada a tasheta"
"Babanku yana nan ne?" Kai ta girgiza
"Ya fita a mota"
"Muje cikin" ta fada tana kama hannunsu,har yanzu tana mamakin kintsuwar falon,duk da tazo kwana hudu da suka wuce amma ba haka ta samu falon ba.
Tana kwance male male saman gadonta tana sana'artata wato chart,harta bude baki data ji an bude qofar zata hau masifa,a zatonta weedad ko yaran ne saita maida maganar dake cikinta tana murmushi ta miqe ta zauna saman gadon ganin anty ummee ce
"Daga ina haka ba kira ba sanarwa?" Harara ta balla mata tana samun gefan gadon ta zauna
"Kedai baki da hali,don zanzo gidanki saina gaya miki?" Dariya tayi
"Allah ya baki haquri ba haka nake nufi ba" bedroom din nata anty ummen ta sake kalla
"Nace ba,wai yaushe kika fara tsafta ne?,don nidai banga haka a jikinki ba" tafadi tana kallon jikin hafsat din,wadda ko brassiere babu,sai wata t-shirt data mata yawa da zanin atamfa,kanta kuma tsifa ce rabi da rabi.
Fuska ta tsuke tana kallonta,tasan halin anty ummee idan ya motsa in ba cin mutunci tataba mata ba bata jin dadi
"Ni dadina dake wlh cin fuska,aidai jikin nawa babu qazanta ko?"
"Nima bance akwai ba" ta amsa mata tana boye dariya,sai hafsat din ta gyara zama tana cewa
"Yarinyar nan ce sunzo weekend,ai na gayamiki indai sukazo bani da matsala,nima nawa weekend din nakesha"
"Kina shan weekend dinki amma na ga kanki rabi da rabi,a haka mai gidan yazo ya sameki?" Kan nata ta shafo
"To mene?,kitso naso azo ayimin kuma na kasa qarasa tsifar tun shekaran jiya"
"Allah ya tsinewa qazantarki" anty ummee ta fada cikin ranta,amma a fili saita mirgina kai kawai,tasan kome zata gaya mata abanza,tunda ba yau farau ba,indai akan tsaftane
"Amma dai ya kamata kiyi amfani da damarki duk sanda yazo weekend ya zamana kin qara kawo kusanci tsakaninki dashi"
"Manta da wannan anty ummee,kome zakiyi masa baki taba burgeshi" baki ta tabe
"Ai shikenan,Allah ya kyauta" daga haka ta maida kallonta ga dakin,ta fara bin ko ina da kallo tana neman abinda zata rabauta dashi,ganin haka sai hafsat din ta tsuke fuska da kyau,tasan yanzun zata rabata da wani abu,don haka ta zamo daga gadon tana daura zaninta
"Muje falo anty ummee,kada a shigo gidan babu kowa a daukemin wani ita tana ciki tana aiki bata sani ba" ta fahimceta sarai,bata ce komai ba tadauki jakartata suka dawo falo,amma cikin ranta taci alwashin sai fa ta fita da wani abu daga gidan
"A banza zan dinga baki shawari" ta fadi a ranta.
"Nifa dadina dake rowa wlh,ko ruwa ki kasa bawa mutum?" Anty ummee ta fada ganin sunata zuba zance amma ko ruwa bata mata tayinsa ba,kusan wannan din dabi'ar hafsat ce,bawai wani abu bane a wajenta
"Kai anty ummee,kedai kin cika qorafi wallahi"
"Ahto ai gaskiya ce" daga nan inda take zaune ta qwalawa widad kira tace ta kawo ruwa,ajjiye mop stick din hannunta tayi,ta samu plate ta hado ruwa da kuma lemo babba da qarami me sanyi da cup,kamar yadda ta saba gani a gidansu ummu nayi,ta nufo falon.
Idanun anty ummee a kanta harta qaraso,ta tsugunna ta ajjiye kayan sannan ta gaidata ta miqe ta koma ciki.
Sai data koma sannan ta dauke idanunta daga kanta ta maida ga hafsat
"Hafsatu,ya naga yarinyar nan tana girma ne?,kinga yadda take canzawa?" Baki hafsat ta tabe
"Na gani,nima abun yana dan damuna,duk da dai nayi mata dashen dana tabbatar bazai barsu suyi kowacce irin sakewa ba,kai qarshe ma idan ya matsa nasan rikici za'a yi ba dan qarami ba,namiji kuwa kinfini sanin ba haquri gareshi ta wannan bangaren ba" kai ta jinjina
"Eh da haka kam,amma dole mu sake lalubo wata hanyar kafin ta fahimci duk gaibu kike gaya mata" mugun tsaki hafsaa din taja
"Kuma dai?,ni na fara gajiya,haka kawai kana zaman zamanka banda namiji matsiyaci ne ya dauko abinda zai hanaka sakewa,shi bai amfana ba kai baka sake ba,aikin banza kawai" ta sake fada tana jan mugun tsaki, idanunta har sun sauya launi,da kallo anty ummee ta bita tana fasa lemon da aka kawo mata,a baqin kishin hafsat dinma bata dauka za'a kai warhaka gayyar bata watse ba,saidai tana alaqanta dadewarta akan plan din da morar yarinyar da takeyi.
Bayan ta shanye ta dauki dayan ta jefa a jakar hannunta,don tunda ta samu wannan damar ba zata barta ba,hafsat din kuwa ta bita da kallo cikin ranta tana fadin
"Kwadayayya hadamammiya" yayin da anty ummee din ta waske da cewa
"Karki damu,kafin lokaci ya qara turawa za'a samo wata mafitar".
Sannu a hankali rayuwa ta dinga juyawa,watanni suka fara shudewa,tsakanin widad da abbas yanzun akwai sakewa da sabo ba kamar baya ba,duk da cewa ba wata mai yawa bace,don bata bari ya kusanci inda take sosai,idan ka gansu zakayi tsammanin yaya ne da qanwarsa da yake matuqar bawa kulawa,zuwa sannan weedad din ta fara girma ita a karan kanta tana ganin wasu sauye sauye,ta fannin girki ta iya abubuwan da baza'a rasa ba,sosai kuma takejin dadin makarantar ta,ta fara sabo da mutane,ta kuma fara karantar rayuwa da yadda mu'amala take tsakanin mutane
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*_Arewabooks:huguma_*
Page 58
Tsakanin shi da itan zamu iya cewa wasu irin mutane ne da miskilanci yake gudana a jininsu,saidai duk da wannan hakan bai hana sabo da sakewa a tsakaninsu ba,kamar ko yaushe,safiyar ranar juma'a ce,suna kitchen ita dashi,tana sanye da abaya mai santsi peache color me turuwa kadan,wanda daga cikinta riga da wando ne straight leg,duk da basu matseta ba amma sun fidda aihinin shape nata,shi yasa ya dora abayan a kai,haka kawai tayi sha'awar sanyasu,taga hotunansu cikin wayar wata 'yar ajinsu yayarta ke sayarwa,data duba kayanta taga tana da irinsu,kaf ire iren wadan nan kayan nata suna hade ne a waje daya,bata taba gwada sakasu ba,tana ganin kamar kayan 'yan iska ne.
Manyan kalba da aka yi ma kanta guda hudu masu kauri da tsahon jela,biyu suka zubo gefe da gefen fuskarta,suka kuma sauka mata har kafada,sauran biyun kuma suka sauka a gadon bayanta.
Yau din abbas na saman cupboard a zaune kawai yana latsa waya,saboda tunda suka tashi da safen tana gaidashi tace,saita langwabe kai gefe guda tana wasa da yatsun hannunta
"Yau babu abinda zaka koyamin,I want to surprise you" she is always like a baby,haka take maganarta cike da quruciya,daya daga cikin abinda yasa yakeson yaga tana magana,kota dake da gasken gaske tana zuba wautarta,amma ita a nata ganin a dai dai take komai.
Yadda ta ritsashi da idanu bayan ta gama maganar ya sanya dole murmushi ya qwace masa,irin miskilin murmushinsa da ko haqoransa baka fiya gani ba,ya dage girarsa dukka biyun sama yana kallon tsakiyar qwayar idanunta
"Really?"
"Yes" ta amsa da amsa amo cike da qwarin gwiwa,sai ya girgiza kai yana qaramar dariya
"Zamu gani,in zauna yau abina kenan?"
"Eh mana,na baka hutu" ya fidda sauti kadan,yayi tsalla daya ya haye sama yayi zamansa,saita bishi da ido tana fidda manyan idanunta waje,wasu irin fararen manyan zagayayyun idanuwa da suka dauki hankalinsa a karon farko,har baisan yayi subutar bakin tambayar ta
"What?" Ya fadi yana jin wani abu nason masa tasiri,qaramar dariya mai cike da sakalci tayi
"Tsallae daya fa kayi uncle ka haye?" Murmushi ya sake subuce masa,ya girgiza kai
"Shine kika bude dukka wadan qwala qwalan idanun naki zaki cinyeni dasu?" Baki ta tabe kamar yadda qaramin yaro keyi idan zai saki kuka,abinda ya sake shagaltar dashi da kallonta kenan,siraran labbanta kamar ta shafa musu jambaki
"Qwala qwala fa kace uncle"
"I don't mean qwala qwala marasa kyau,u have a beautiful eyes dear" ya fadi yana duban qwayar idanunta,kawai sai taji wani irin kunya ta kamata,ta saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta,hirar 'yan ajinsu ta fado mata,daya daga ciki dake basu labarin yadda saurayinta yake kodata,haka akeji dama data taba ce musu kunya takeji?.
Zara zaran yatsuntsa data rufe fuskarta dasu yabi da kallo,farare tas,hatta da farcenta fari ne qal babu digon komai a jiki
"Me kike tunani?" Taji ya sake fada
"Ba komai" ta amsa masa da sauri tana sauke hannuwanta daga fuskartata,gani take kamar zai karanto abinda ke cikin zuciyarta
"Kin manta am a police,da tsalle daya muna iya hayewa saman gini dake da tsahon da yafi na wannan,kin tuna?" Kai ta gyada tana murmushi,saita kasa ci gaba da cewa komai saboda yadda yake kallonta tsakiyar idanunta yana sanyata tana jin wani iri.
Shuru kitchen din ya dauka,yayin data buda wayarta tana duba recipe na abinda zata dafa din,tana daukowa daya bayan daya tana ajjiyewa,har ta kammala ta fara aikinta.
Haka kawai ya samu kansa da daga kai time to time yana kallonta,hakan ya sanya duk kai kawonta take yinsa cikin idanunsa ba tare data ankara ba,aiki yayi aiki,taja igiyar rigar ta daureta don tafi jin dadin yin aikin,saidai abinda bata sani ba,gaba daya ta fidda shape na mazaunanta qugunta da kuma qirjinta.
Ya sake dagowa yaga a inda girkin ya tsaya idanunsa sukayi kyakkyawan gani,yaso janye idanun nasa amma sai ya kasa,karon farko kamar an zare masa laka daga jikinsa,yaso ya maida kai ga wayarsa amma sai yaji ya kasa,dole ya kashe abinda yakeyi din,ya aje wayar a gefe,ya jingina da bango ya harde hannayensa a qirjinsa ya zuba mata idanu.
Sam batasan yana kallon ta din ba,saboda ta bada hankalinta gaba daya ga abincin,tanason yayi dadin da zai yaba mata,ta waiwayo zata dauki chopping board har ta juya ta fara yanka albasa jikinta ya bata kamar kallon ta yake,tana juyawa sukayi ido hudu,sai gabanta ya fadi,ta juya da sauri ta saki igiyar rigar tata,ta koma shapeless kamar yadda take idan ba igiyar a jiki,jikinta yadan dauki rawa kadan,ta sunkui da kanta tana yankan da sauri sauri.
Bata son kallo ko kadan,bare shi da a duk sanda ya kalleta sai taji nashi idanun kamar sun banbanta dana kowa,ta fara nisa a tunani,don haka har ya sauko daga inda yake zaunen,ya tako a hankali ya tsaya a bayanta bata jishi ba.
Sosai ya zuqi qamshin splash da jikinta ke fitarwa kadan kadan yana kadawa hagu da dama gaba da bayanta,taku biyu ya qara ya sake rage kusancin dake tsakaninsu,sai a lokacin taji kamar iskar dake bayanta ta canza da wani kalar qamshi na body mist na daban.
Cikin hanzari ta waiwayo,ta manta da wuqar dake hannunta tana datsa albasa,tariga ta dora ashe saman yatsanta ne,tayi wurgi sa wuqar tana yarfar da hannunta gefe daya,saidai duk da zafin da taji kusancin shi da ita yafi daga mata hankali,ta kafeshi da idanu qirjinta na wani irin bugawar da bai taba yiba,ta kuma ja baya sosai har ta qure da jikin kitchen cabinet din.
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin shi da ita,a hankali ya sanya hannunsa ya lalubo hannunta data yanke din ba tare daya janye idanunsa daga cikin nata ba,sai daya sanya hannun cikin tafin hannunsa sannan ya maida dubansa akai.
Kusan lokaci daya suke duban hannun shi da ita,sannan suka kalli juna
"Kinga abinda kikayi ko?" Ya tambayeta da wata shaqaqqiyar muryar,kamar jiransa dama takeyi sai ga hawaye ya cika mata idanu
"Kaine fa ka bani tsoro" dariya taso bashi amma ya dake,saiya langabe kai kamar yadda yaga tayi
"Banda ke banga wadda take tsoron mijinta ba" kamar ya tunzurata,don batason kalmar miji,sai ta fara qoqarin zame hannnunta daga cikin nashi
"Ni ba mijina bane kai"
"To waye ni?" Ya tambayeta yana dage girarsa sama
"Uncle" kai ya girgiza kawai yana sake sakin boyayyen murmushi
"Riqe uncle dinki,banaso,let me treat your wound first" ya fada yana sake kamo hannunta.
Kujera ya saka mata ta zauna akai,sannan shima ya jawo wata ya zauna,har gwiwoyinsu suna haduwa da juna,ya bude first aid kit din ya fada wanke jinin,yana yi tana rintse idanu,ya daga idanunsa ya kalleta,idanuwansu suka hadu waje daya,sai taji hakan ya mata nauyi sosai,ta kauda nata idanun numfashin su yana gauraya da juna.
Har ya gama mata babu wanda ya sake cewa komai,ya sakar mata hannun yana hade kayan waje daya
"Jibi idan Allah ya kaimu zanje bauchi" kallonsa tayi da sauri,hakanan kwanakin nan sai ta dinga jin batason zuwa garin
"Zanje nayi one week,zamu taho da hajiya,the next day zamu wuce umara ni da ita in sha Allah" zuwan da yace hajiyan zatayi taji yayi mata dadi,har zumudinta ya bayyana a fili
"Amma wata daya ya kamata tayi,ko ka dawo da ita nan kawai" ta fada tana langabar da kanta,cak ya tsaya yana kallonta,yaji mamakin jin furucin daga bakinta,abinda bai taba ji daga bakin hafsat ba tsahon zamansu da ita
"Hajiya ba zata zauna ba" ya amsa mata yana miqewa riqe da kit din.
Koda ya dawo sai ya fara rolling hannun rigarsa zuwa sama,tana daga zaune tana kallonsa har ya gama,idanuwanta suka sauka kan lallausar gargasar dake lullube da hannunsa,abar da take yawan burgeta ba tare da tasan dalilin ko kuma amfaninta
"tell me what you are cooking sai na qarasa" idanu ta narke
"Zan iya qarasawa uncle,don't spoil it" girarsa ya daga ya watsa hannayensa
"I will finished it anyway idan ma baki gayamin ba" ya fada yana qarasawa,ya bubbada tukwanen
"Kin kusa gamawa ai" ya fada ba tare daya juyo ba,yana mamakin qoqarin da tayi,kai ta gyada masa.
A nutse yake ci gaba da aikin,har ya kammala,duk inda ya motsa idanunta suna biye dashi,yana ankare da ita amma bai nuna ya ganta ba,har ya kammala,zata karba gyara kitchen din shima ya hada ya gyara komai,mamakinsa sake cikata yakeyi kullum,shi kam baya jin aiki ne?.
************Tana nade saman kujerar falon,tayi lamo kamar 'yar magen data samu waje mai laushi,sanye take da atamfa dinkin riga da skert na atamfa,ta yane saman kanta da dankwalin atamfar,jikinta na fitar da tattausan qamshin turarenta,daga gaba kadan kujerar ta uku daga gefanta,abbas ne a tsaye yana qarasa zuge jakarsa ta tafiya,yanayi yana amsa waya daga office,har ya kammala,ya kashe wayar ya sanyata a aljihu,ya dauki jakar ya rataya a kafadarsa.
Sai a sannan ya waiwayo inda take zaunen,yadan zuba mata idanu yana karantar yanayin fuskarta,duk sanda zayaje bauchi indai bada ita bane sai yaga wannan damuwar a tare da ita,saidai a wannan karon damuwar kamar tafi ta kowanne lokaci.
Yadda tayin kamar wata marainiya ya bashi tausayi da kuma dariya,ya taka a hankali ya tsaya a gabanta,ya miqa mata dogayen lausasan hannunsa.
Hannun tabi da kallo kafin ta mayar saman fuskarsa dake dauke da wani irin haiba da wani sirritaccen kyau da ba kasafai kake iya hangensa farat daya a fuskarsa ba,har cikin zuciyarta takejin wani iri babu dadi,saboda wannan ne karon farko da zaije yayi sati daya,kwana biyu rak yake ya dawo duk sanda ya tafin,idan da itane ma suke kwana uku.
Sake miqa mata hannun yayi,saita noqe hannun nata tana lumshe idanunta hadi da kwantar da kanta tsakanin cinyoyinta.
Murmushi ne mai sauti ya kubce masa,cikin taushin murya yace
"Get up,tashi muyi sallama" curewa tayi waje daya,saita saki kuka kawai
"Ya rabb"ya furta yana sauke jakarsa daga kafadarsa ya ajjiyeta a qasa,sannan ya duqa saman gwiwarsa a gabansa
"Na gayawa hajiyane baki barni inje na daukota ba?,ko na gayawa maman mimi baki amince naje muyi sallama ba?" Furta sunan mommy hafsat da yayi ya sakata zabura,ta kuma daga kanta da sauri,sunanta kawai na sanya gabanta faduwa,hajiya kuwa tana jin nauyi da kuma kunyarta fiye da yadda baki zai furta,dukkansu babu wanda zataso ya gayawa abinda yace zai gaya musun.
Kai ta girgiza masa da sauri,ya lumshe idanunsa ya kuma budesu duka a tare
"Wipe your tears" hannu biyu tasa ta goge hawayen yana kallonta, cikin ransa yana jin wani irin yanayi daya gaza tantance wanne iri ne,a yau apart from hajiyansa,yau ga wata halitta dake amsa sunan matarsa tana jin babu dadi wai don zaiyi nesa da ita,a wajen mutum guda yake ganin hakan..... hajiyan sa,babu na biyun sai a yanxun da yake gani daga wajenta.
Sai daya hilaceta ta dan saki jiki,sannan ya miqe ya dauki luggage dinsa yayi mata sallama ya fice,tana tsaye a jikin window har motarsu ta tashi suka fice daga gidan.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 59
Ranar gaba daya wunin falo tayi,tayi kwance cikin kujera ta kasa hasala komai,,haka kawai take jinta wani sukuku,jikinta duka babu dadi,sai bayan sallar la'asar tana kwance kiran anty deena ya shigo
"Lafiya kike?" Ta tambayeta jin muryarta tayi qasa da yawa,sai ta kama mata hawaye kafin daga qarshe ta gaya mata ya tafi bauchi ya barta ne,abun ya baiwa anty deena dariya,wohoho...... widad har yanzu quruciyar dai tana nan,sai data bata baki sannan tayi mata zancan da yasa ta kirata
"Akwai watsapp groups da za'a saki,inason kowanne idan an sakaki ki tsaya kibi duk hirarrakinsu kinji ko?,akwai qaruwa sosai qanwata"
"To anty" ta fada tana gyada kai,sun jima da anty deena din suna hira,sai data debe mata kewa sosai sannan sukayi sallama.
Washegari haka ta tashi jikinta babu qwari har ta gama shirin makaranta,bayan kowanne minti daya saita kallin dukka wajen da yafi zama ko tsaiwa,sai taji hawaye sun cika mata idanu,tasa hannu ta share da sauri,sannan ta dauki school bag dinta zata fice a dakin,qarar wayarta ya dakatar da ita,ta waiwaya ga inda ta ajjiye wayar saman madubinta,ta koma ta zuba mata ido tana kallon number wayar,sai kuma ta miqa hannu ta dauka.
Lallausar muryarsa ta bayyana cikin wayar,gaba daya kamar wadda aka bigewa gwiwoyinta haka taji,ta koma da baya ta zauna tana qoqarin amsa sallamar tasa,yana jin sautin muryarta ya saki boyayyen murmushi
"Ina kwana?" Ta gaisheshi muryarta na rawa
"Kin tashi lafiya?"
"Lafiya qalau" shuru yadan ratsa sai yace
"Baki kirani kinji yadda na sauka ba,tsakani da Allah ba amana,ni ina nan ina tunaninki" wata irin kunya ce ta saukar mata,har taji kamar gata a gabansa,saita saki murmushi tana qunshe fuska
"Kayi haquri" ta samu kanta da fada,don ko kadan ta kirashin baizo kanta ba,hasalima ita batace ga number dinsa ba
"Yayi kyau,yanzu me kikeyi?"
"Makaranta" ta bashi amsa a taqaice,daga nan inda yake ya kalli agogon dake gefansa
"To a dawo lafiya"
"Allah yasa" ta fada cikin dan karsashin data samu
"Babu komai ko?" Shuru ta danyi,da kamar tace masa gidan babu dadi,kamar tace masa jiya da qyar tayi bacci,kamar tace masa ya dawo don Allah,amma kuma saita kasa ta amsa masa da babu,sukayi sallama ta kashe wayar ta barta saman gado sannan ta fito ta cimma driver suka bar gidan,tana jin ta samu wani karsashi Cikin jiki da zuciyarta.
Wayar yabi da kallo bayan sunyi sallama ya kashe wayar,hafsat data fito daga wanka tayi zaune gaban madubi tana shafa jambakin dole ta sake binsa da kallo ta cikin mudubin,tunda ya fara wayar gaba daya ta tattara hankalinsa a kansa,kusan wannan dabi'arta ce,tanaso ta cinye amma ta kasa,tadan gyara zamanta tana matso jambakin ba tare data shafa ba tace
"Dawa kake waya ne?" Kansa ya daga yana kallon fuskarta ta cikin mudubin,maimakon ya maida kai ga amsa tambayarta,sai duka tunaninsa suka koma daren jiya tsakanin shi da ita
"Hasbunallah" ya furta qasan ransa,bacin ranta ya motsa masa amma sai ya kori shaidan
"Wanka kikayi?" Ya mata tambayar data bata mamaki,a mamakance ta amsa masa
"Eh,baka gani ba?" Kai ya jinjina
"I see,but.....zo muje in nuna miki wani abu" ya fada yana yaye lallausan duvet dinsa sabo fil da dole ta sanyashi daukoshi,saboda yazo ya tarar da nashi anci ubansa,tun kafin yayi magana ma tace masa nawwara ce,haka ya tattarashi a daren ya bawa mai gadinsu yace ya yar,shi kuwa ya kaishi baya cikin murna ya jiqashi zai wanke,saidai shi dinma yana wankewar yana tsinewa qazantar hafsatun a ranshi,saboda wani irin gamayyar hadakar dauda ne a jiki harma da guntun kashi dana fitsari.
Kai tsaye ya shige bandakin,ta ajjiye jambakin ta bishi da kallo,itafa ba wannan takeso ba,bai amsa mata tambayar ta ba,abun yayi mata tsaye a rai tunda taji suna waya da yarinyar,abinda bata taba ji yayi da ita ba,to amma kuma dole ta lallaba a yanzun,bataso suyi tashin hankali,kada ta barar da umrarta,don tunda taji labarin tafiya umarar ranta ya raya mata harda ita a ciki,qilan bai fada mata bane,saboda ya saba,yana da wani irin miskilanci da shan qamshi ta wannan bangaren,ba kasafai idan zai maka abu yake gaya maka ba,har sai dab da faruwar abun,dole ta miqe ta bishi bandakin,zuciyarta nq raya mata dole ta kira yarinyar tabi ba'asi,ta kuma sake kada mata warning,dama ranta a bace yake tunda taga yazo babu ita,don ta hada himilin qazantarta,mai wankinsu ya gudu amma yace mata yana qauyensu,tana ta jira fa taji wayam,dole ta tattara duk wasu tarkacen kayayyakinta takaisu store din bayan gidan ta kulle saboda abbas din,ta tabbatar idan ya gani sai yayi fada,ita batasan uwar daya sanya yanzun sai yayi zuwa biyu baizo da ita ba,ko a yanzun wannan kusan zuwasa na biyun kenan,idan ta bigi cikinsa sai yace mata makarantar ya sanya haka.
Tana shiga bandakin yana tsaye da clipper a hannunsa yana daurata,ya daga tsimammun idanunsa dake motsa mata soyayyarsa koda bata shirya ba ya kalleta
"come closer" ya fada yana kallonta,kamar zata musa masa kota tambayeshi dalili sai kuma ta fasa,ta matso din kamar yadda ya buqata,bata kawo hakan a ranta ba kawai taji ya sanya hannu zai ware towel din jikinta,da mugun qarfi ta kama towel din ta riqe tana kallon idanunsa
"Me zaka yimin da safiyar nan kuma?" Ta tambayeshi ranta a bace,mamakinta ya sake cikashi,yana sane yace mata
"I want to be with you" ido ta zare ranta a bace
"Haba don Allah,duk abinda kayi jiyan bai isheka ba?, al'amuranka are getting worst gaskiya abban mimi, jiyan kamar zan mutu fa" bai amsa mata ba illa hannu daya daya saka ya fincikota,ya ware towel din,ya kunna clipper din ya daga hannunta ya fara kwashe mata gashin hammata,sai tayi shuru tana kallonsa,fuskarsa a hade,kunya ta kamata,ta rasa yadda zata nade masa tabarmar kunya da hauka,har ya gama sannan yace mata
"Kwanta na qarasa miki sauran,tunda bakisan yadda akeyi ba"yafadi ba tare daya kalleta ba yana goge gashin daya bata jikin clipper din, fuska ta bata
"Kawai da ranar Allah saina yaye maka jikina,kai ba zaka ji kunyar kalla ba?" A nutse ya daga kai yana kallonta,ko yaushe mamakinta kasheshi yakeyi,kamar wata jahila ko wadda batasan meye aure ba,ya zuba mata idanunsa da suka sanyata tadan daburce,sai tahau quna quni
"Zanji kunya mana,wannan uwar gayyar da kika tarawa wajen ai dole aji kunyar kallansa" batasan abinda zai maida mata dashi ba kenan,sai zancan nasa yayi mata ciwo
"Me kake nufi?,daga fadin gaskiya zaka mayar min da baqar magana?" Baice mata komai ba,ya qarasa gefanta inda take tsaye ya ajjiye clipper din ransa ya suya,kome zaka.mata a duniya baka iya ba,bakuma zaka fita ba
"Kada ki fito baki kwashemin wannan go slow din da kika tarawa wajen ba" ya fada adan zafafe ya qarasa sink ya wanke hannunsa da detergent ya fita yabar mata toilet din.
Binsa tayi da kallo idanunta na hada qwalla,to wai ina ruwansa da sumar wajen?,badai ta bashi abinda yake nema ba?,why not zai dameta harda baqar magana?,banda tasan halinsa sarai tana kuma tsoron hukuncinsa da ba zata aske ba,tasanshi hukuncinsa bashi da dadi idan ka kaishi bango.
Ko kafin ta fito ma shi tuni ya gama gyaran sassan nasa,suna falo suna breakfast shi da yaransa,wucesu tayi tana shan qamshi,ita ala dole ya bata mata rai,can qasan ranta kuma kunya ce fal bayan ta gama askewar taga uban tulin gashin data tara,taji kuma iska tana ratsata, baibi ta kanta ba shima,don idan da sabo ya saba da irin wadan nan dabu'un nata.
Wankansa yayi ya shirya ya kuma shirya yaran,ya aikasu ta saka musu kaya,taja tsaki
"Wato baima san tanayi ba,ficewarsa zaiyi kenan,me yasa ne duk fushin da zatayi baya iya lallashinta?" Ta tambayi kanta zuciyarta na quna,haka ya figi yaran ta watsa musu wata shadda ta kadasu daga dakin.
Sanda suka shigo sai daya dakata daga taje sumarsa da yakeyi,ya juyo yana kallon kayan jikin nasu sosai,gezner ce mai mugun tsada daya siya musu kwanan nan da aka qara masa girma su da mamarsu,ya kuma biya kudi mai yawa aka muau dinki mai tsada,ita mamartasu tun randa suka fita a hannunsa bai taba ganinta a jikinsa ba,su kuma bai tashi ganinta a nasu jikin ba sai da wannan muguwar kamar,gaba daya ta fita hayyacinta,kamar ma ta soma dafewa,ga wata muguwat squeezing da sukayi
"Allah ya kyauta"kawai ta fadi bayan ya taba shaddar ya tabbatar itace
"Daddy mu tafi,daddy tare zamuje ko?" Mimi ta fada,saiya gyada mata kai,tausayinta na cikashi,sam bata damu da yanayin da kayan jikin nata suke ba
"Muje na canza muku kaya tukunna" ya fada yana hada kansu suka wuce sashen hafsa din.
Gaba daya dakin a qazance yake sannan a hautsine,dama kusan kaso casa'in na gyaran dakin shike musu,idan ya gama nasa gyaran saiya hada da nasu,yana saka ran kuwa ba'a sake bi ta kansa sai idan ya sake zuwa wani weekend din,baya qaunar yadda taje barin rayuwar yaransa cikin qazanta,yara mata ne,wataran dole gidan wani zasu,uwa uba ma lafiyarsu,yana tsoron wata cutar a tattare dasu,haka ya dinga hadiyar bacin ran bayan ya bude cupboard dinsu,duka kayan ma baya ganesu,baya gane masu wanki da wadanda babu wanki,ga kaya cike da cupboard din amma babu na zabe,ya zubo dasu duka,ransa a mugun bace,wai me yake damun hafsat ne?,kayan yaranki kamar na mahaukata?,banbancinsu kadanne?.
Wayarsa ya zaro yayi kiranta,don bayason su hada fuska ma ta qara tunzurashi,tana ganin kiran taqi dagawa,har ya gaji ya tura mimi tayi kiranta.
Sai data mula sannan ta taso,ta tura qofar suka hada ido,saita kauda kanta saboda yadda taga bacin rai baro baro saman fuskarsa,tayi gefe da kanta tana jiran jin tashin boma boman fada,saboda ta hangi himilin kayan yaran daya watso qasa
"Meye matsalar me muku wanki?,bai iya bane?" Ya tambayeta calmly yana qoqarin dannar kansa,duk da can qasan ransa wani irin bacib raine kecin zuciyarsa
"Kawai yaron bashi da mutunci ne,ba kasafai nake bashi wanki ba" ya jinjina kai kawai,saboda yasan ta fada ne kawai don ta kare kanta
"Shi kuma engine wankin gidan fa?"
"Ya lalace wata hudu kenan" wani abu mai tauri ya hadiye,ransa na baci, engine ma ya lalace amma ta buda baki ta gaya masa ba zata iya ba?
"Yayi" kawai yace da ita,saita saki handle din qofar ta juya ta fice abinta
"Ka qaraci jarabarka kai kadai" tafada can qasan ranta tana buga tsaki.
Wayarsa kawai ya zaro ya kira hajiya
"Ka iso ne?"
"Ina dai hanya,muneera zaki turomin gida yanzu"
"To gata nan" ta fadi ba tare data tambayi ba'asi ba,amma cikin ranta tana addu'ar Allah yasa lafiya.
Babu dadewa kuwa sai gata,ya sakata ta zauna ta ware sababbin da rashin tsafta da kulawa yasa suka lalace,sauran kuwa yace dukka ta samu manyan buhu ta duresu ta fita dasu,hakan kuwa tayi,yasa takai waje ta baiwa mai gadi,sauran masu kyan ta saka masa a booth din motarsa ya sakasu a gaba suka fito a dakin.
Jin motsi ya qaru a gidan da surutun yaran yasa ta kasa zaman dakin,tayita kai kawo tsakanin dakinta da kitchen tana kallon qofar dakin nasu tanaso taga waye yazo,dai dai sanda ta fito daga kitchen din muneera ta fitowa da jakar kayan dasu mimi, cikin girmamawa ta rusuna tana gaidata.
Fuskarta kadaran kadaham ta amsa mata tana kallon jakar kayan a hannunta,shikam tuni yayi gaba,sai itama muneera tayi mata sallana tabi bayan uncle din nata.
Baqinciki kamar tayi me,tabi yarinyar da kallo,tabbas shike sake wulaqantata tare da basu damar da zasu gaya mata magana su kirata da qazama,ya kira yarinya har cikin gidanta cikin dakin yaranta ta kwashi kaya an fita dasu,tome za'a je ayi mata da kayan yara?,da wannan bacin ran ta dinga mita da.surutu ita kadai a cikin gidan,banda tana shakkarsa saita tsaidasu tabi ba'asi,kai da babu ma mai daukar mata kaya ya fita mata dasu a cikin gida,saidai ta sani,bacin ransa bashi da dadi,dole tana jiyo qarar motarsa ya tasheta suka fita a gidan.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 60
Wuni tayi takaici yana cinta,amma kuma da sukayi waya da anty ummee ta tilastata sakin jikinta
"Ke da kike jira kiji albashiri din tafiya dake,me ya kaiki dukka wadan nan abubuwan,dole ki taushi zuciyarki ki nuna masa komai ba komai bane,kuma kiyi dako kar kiyi gaggawar tambayarsa,ha sai in shi ya gaya miki da bakinsa" da wannan shawarar tayi qoqarin gyara dakin yaran,ta kuma tsallaka taje ta gyara nasa,dukda gyaran nata ba wani na azo a gani bane,amma bahaushe yace da babu gwara babu dadi.
Cikin kwanakin kuwa ta dunga qoqarin yun dukma abubuwan da tasan yanaso,sai abunuwan nata gaba daya suka zama wanu banbarakwai saboda ba saba yi tayi ba,ita kanta da qyar take kai labari saboda rashin sabo,a wajensa shima abun ya zameasa wani iri,saidai shi din hakan yakeso inda ace zata sauya din.
***********Kwana daya rak amma gaba daya jikinta ya zama week kamar wata mara lafiya,randa ta dawo daga makaranta ma wannan dogon wunin kwanciyar tayi,don haka da dare bacci bacci yayi mata qaura,sai taja wayarta kawai ta soma bin charts na groups din da anty deena ta saka a sanyata,tun abun bai wanu burgeta ko mata dadi har ya fara jan hankalinta,a hankali ta dinga bin topics din da suke tattaynawa daya baya daya,tarin uban saqonni saidai dukkaninsu msu amfani ne ga macen auren dake neman gyara rayuwar aurenta,saidai ga widad fa abun kunya ya zame mata,tana karantawa tana jin kunya ita kadai,musamma idan ta tuna anty deena na ciki.
Bayan tayi nisa ta soma fahimtar wasu abunuwa da suka sanyata cikin nqzari da lissafi,an gadi abubuwa masu yawa da ita bata sansu ba,kuma kallon iskanci take musu,amma kuma taji suna batun lada,dama akwai lada cikin iskanci banda tarin zunubi?,saita maida wayar ta ajjiye gefe tana tuno wasu abubuwa,ta dinga saqa tana warwarewa,wa zata tambaya wanda zaiyi mata bayanin da zata gane da kyau,ta kuma fita daga shakka?,ita kanta anty deena maganganun da taga tayin sai suka weedad ke tunani a kanta,tasan dai anty deena ba 'yar iska bace,to amma.......
Katsewa tunanina yayi sanda wayarta ta soma wani qaramun ringing mai dadi,ta kalli wayar,kamar ta gane number din,ta jawo wayar ta daga ta sakata a kunnenta.
A nutse muryarsa a qasa yayi mata sallama,ajiyar zuciya ta kubce mata ba tare data shirya ba,ajiyar zuciyar data sauka a kunnensa,ta kuma sanya tsigar jikinsa zubawa
"Bakiyi bacci ba?"kai ta gyada sannan ta amsa masa
"Eh"
"Me yasa?" Rasa amsar bashi tayi,saboda dai ba zata iya ce masa ga abinda take karantawa ba
"Me tayin kwanan ta shigo?"
"Eh" ta bashi amsa,don sai da sukayi sallama da ita sannan ta shigo dakinta,saboda ita a falo take kwana,taqi yarda ta kwana dakin widad din
"Yayi,yanzu gaya min dame dame kikayi yau?" Ya tambayeta yana hangen hafsa daga inda yake zaune cikn falonsa,tana nannade wandon kashin da nawwara tayi tana cusashi qasan kujera,ya dauke kallonsa daga kanta ya maida wani gefin,don bayason ransa ya baci.
Sosai ta narke cikin pillow din,zuciyarta tana narkewa,kewa tana sake cikata
"Bayan kaine....kaine kayi tafiyarka ka barni" ta fada a wanu kugun shagwabe,abinda yayi masifar tabashi,tsigar jikinsa ta zuba sosai,ita kuwa ko a jikinta,saboda tana ganin tayi maganarta ne sak
"Am sorry......bazan sake ba" ya samu kansa da fadin hakan ba tare daya shirya ba,dai dai sanda hafsat din ta qaraso wajen,sai taji kamar kunnuwanta basu jiye mata dai dai ba,waye yake baiwa haquri wai?,ta tambayi kanta,ta tsaya cak tana dubansa,yayi kamar bai ganta ba,yaja cup din coffe daya hada kafin ya zauna ya kurba kadan
"Yanzu kiyi addu'a ki kwanta,akwai school gobe"
"Tom.....sai da safe?" Ta tambayeshi a sanyaye,saboda har ga Allah hirar ta mata dadi,bataso yace ta kwanta ba.
Murmushi ya sake kubce masa,a hankali ya furta
"Goodnight" sai ya zame wayar daga kunnensa yana kasheta,dai dai sanda hafsat din ta kasa tsaiwa,ta zame ta zauna a kujerar dame kusa dashi
"Wai da waye kuje waya haka?" Sai daya kashe wayar ya ajjiye sannan ya dago yana dubanta,yadan zuba mata ido na wasu sakanni sannan ya saki murmushi
"Qanwarki ce"
"Qanwata ko kishiyata"shine abinda bakibta taji ya kamata ta furta,to amma tana tsoron kada ta barar da tafiyarta,don haka ta hadiye maganarta,sai gefw da tayi da kanta ta tabe baki
"Dole yarinyar ta dinga tsoronka,ya zaka dinga gaya mata maganganun da sukafi qarfi kanta,a haife fa ka kusa haifarta,tunda ka ninka shekarunta harda doriya" ta qarasa maganar tana dawo da dubanta kansa.
Fuskarsa a sake,saima murmushi daya saki,ya shafa kanshi zuwa kyakkyawan hanarsa dake dauke da gashi baqi sidik daya sha gyara
"Kinason ki gayamin na tsufa kenan fa"
"Kusan haka ne" ta fada tana tabe baki,a nufinta na zare masa karsashinsa da sha'awar komai,murmushi ya sake saki,abu daya ya sani,komai zatayi ba zataji komai daga bakinsa ba,ta manta wayeshi din wajen riqe sirri
"Ki zaro wancan andon kashin ki fita dashi ki wanke,and please.....kada na ganshi a dustbin" ya maida zancan zuwa wani topic din na daban.
Kunya da haushi suka cikata,ba wannan batyn takeso suyi ba,ita batasan ma ya ganta ba,maganar gaskiya babu agender din wanke kashi yanzu a gabanta,amma dole ta miqe rana cewa
"Kadai dinga mata a hankali tunda yarinya ce,bawai wani abu zata fahimta daga gareka ba" da kallo ya bita yana son tantance da wanne irin sound tayi masa maganar,sai ya maida nayansa jikin kujera,ya lumshe ido yana maimaita maganarta,abubuwa da yawa sunzo kansa a sannan wadanda suka sanya dole murmushi ya qwace masa.
Dukka abinda ta karanta a daren washegari ta dunga bitarsu a makaranta,kwatsam ranar sunyi missing periods har biyu,sai ajin ya zamana na surutu da hira,abinda ya sake sanyata daukar wayarta taci gaba da dubawa,saidai tana tsaka da dubawar hirar da 'yan bench din bayansu keyi yaja hankalinta,bata suaje wayarta ba amma ta bada kunnuwanta tana saurarensu,hirace ta aure da yawanci ba'a rasa matasan 'yammata da suke ganun sun fara zama seniors da yinta,fiye da rabin hirar ta zame mata kamar wani mabudi kuma amsa na dukka tambayoyinta,ta dinga saurarnsu tana ciro abubuwa masu yawa tana hadawa cikin maganganun data ji a groups daban daban.
Koda aka tashi daya daga cikin qawayenta ta bata ajiyar hausa novels
"Ki ajjiyemin don allah widad,yayana yazo gutu,doke sai ya koma zan karba,hanani karatun yakeyi,kada yaje garin bincike bincike ya ganosu na shiga uku" a karba din ta tafi dasu gida,da daddare ta buda jakarta bayan ta gama wani assignment zata maida jakar don kada ta manta idanunta suka gano mata litattafan,saita jawosu ta buda tana kallo tare da mamakin meye a ciki da za'a hanata karabtawa,don ita kallon normal kowanne littafi take masa,taji sha'awar duba meye a ciki,ta dauki daya part one ta buda ta fara karantawa.
Ko page daya bata dauka da niyyar karantawa ba,sannu sannu sai gashi har tajai page na wajen biyar,ta saki murmushi saboda labarin yaja hankalinta,saita kife littafin,ta wuce kitchen ta zuba abinci ta dawo taci gaba da dubawa.
Sannu a hankali sai gashi ta raba dare tana karatun,sam batasan dare yayi haka ba,don hatta da wayarta ta manta da ita,taje ta samu miscall na abbas kuwa harda sms guda daya,dare yayi don haka bata kirashi ba,sai tayi addu'a ta kwanta,amma kuma bacci ya qauracewa idanunta,tanata bitar abinda ta karanta din cikin kwanyarta,da gaske akwai soyayya irin haka?,soyayyar jaruman littafin ya tafi da ita,ta dinga kwantanta kanta dasu,kunya ta kamata ita akdai cikin dakin,saita kifa kai tana murmushi.
Washegari babu makaranta good friday ce,wuni tayi tana karatun,wanda a ranar ta gama da part 02 ta shiga 03,sai data qare littafin a ranar ma sannan ta kwanta,nan dinma dai dukka labarin ta dinga tunawa,yadda jarumar ke gudanar da rayuwarta
"Kamar ni da uncle kenan?" Ta ayyana a ranta,da sauri ta girgiza kai,kai anya?,ita kanta wasu abunuwan cikin labarin kunya suka dinga bata,first night dinsu ya dawo mata a rai,sai tsoro ya shigeta,itama wataran haka uncle din nata zaiyi mata?,amma wannan ai iskanci ne,to amma dama akwai ranar da wannan abun zai tashi daga sunan iskanci?,ta tuna haihuwar da jarumar tayi,suna nufin kowacce mace ta haka take haihuwa?.
A daren qwaqwalwa da tunanin yarinya kala kala ta dinga yi,abubuwa da yawa ta watsar dasu tana ganin bazai yiwu ba,ta rungumi abubuwa da yawa da syka dinga burgeta,har ta dinga kwantata gwadawa.
Da safe kuwa ta gwada abunuwa da yawa da ta karanta din,duk da tana wasu qarawa tayi,ta gama komai ta hada breakfast dai dai cikinta,din me tayata kwana gari na wayewa take komawa cikun gida tayi ayyukanta,bata dawowa sai wani daren,ko idan bata da abinda zatayi ta leqota su gaisa sannan ta koma,mayar mai gadin gidan ce,tana da matuqar kirki sosai.
Tana cikin yin breakfast taji sha'awar kiransa kamar yadda taji jarumar littafin tana yi,gabanta ya dinga faduwa sabida rashin sabo,ta dinga jin tsoro tana ganin kamar ba wani abun burgewa bane,saidai duk da haka bata fasa kira ba.
Lokacin ya shiga wanka,hafsat na zaune daga gefan gadon nasa tana dakon fitowarsa,da sauri kamar wadda aka kirayi wayarta ta dauki wayar tana duba mai kiran
"Weedad" ta maimaita sunan data gani a rubucen cike da mamaki,kanta ya daure da kyau,ita dince ke kiran ko kuma dai idanunta ne,ko wata ce mai irin sunan,saita daga kawai kai tsaye.
Shagwababbiyar muryarta data zame mata jiki,ta kuma saba magana da ita,da ita tayi sallama
"Ke tsaya" hafsat ta fada da sauri dai dai sanda take ficewa a bedroom din don kada ma ya jiyota.
Wani mugun faduwa gaban widad yayi jin muryar mommy hafsa
"Ina kwana mommy"
"Da ban kwana na zaki jini?,wa ya sakaki kiransa ko shi din sa'anki ne?" Mamaki ya bayyana a fuskar widad din,ta dauka ba komai,ta dauka momy din zata ce ta kyauta,saita kasa gane yadda abun yake
"Kiransa nayi mu gaisa mommy,jiya ya kirani ban dauka ba" tashin hankali!!, Ta fada a ranta tana jin yadda fuskarta ta dauki wani irin zafi,zazzafan kishinta da taketa qoqarin dannewa ya taso mata
"Yanzu ke har kisan ki kira d'a namiji kusan sa'an babban wanki koma babanki,ashe baki da kunya kwata kwata,to ba sa'anki bane,idan kika sake kiransa ko kuma ya sake kiranki kika daga saina miki mugun duka,ke bakya tsoron abinda zai sameki?,na gaya miki ba'a sakar musu fuska ko jiki,so kike yayi miki ciki ki mutu ko?" Karon farko taji maganar mommy hafsa din banbarakwai,sai taji kanta ya kulle
"Karna sake ji kuma kada na sake gani,kina jina?" Ta tambayeta a tsawace
"Tom" ta amsa mata jiki a sanyaye,sai hafsat din ta katae wayar tana jan tsaki,taso yarinyar na gabanta,amma bari ya fita,zata sake kiranta ta sake jadda da mata.
Jiki a sanyaye ta ajjiye wayar, kwanyarta ta shiga rububin lissafin maganganun hafsat din,zuciyarta taqi amincewa da hakan jikinta yaqi karba kuma ranta yaqi gamsuwa,saboda aduk abubuwan data karanta bataga ta inda aka nuna abune mara kyau ba da har mommy hafsat din zata dinga mata fada haka ba,kusan minti goma ta kasa samun nutsuwa,sai tunani yazo mata,sai kawai ta kira anty deena tace bari ta tambayeta.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:huguma*
Page 61
Kiran farko aka gaya mata user busy,tadan dakata na wasu mintuna sannan ta qara kiranta,cikin sa'a kuwa ta shiga
"Aah,kaga amaren kaduna" anty deena ta fada cikin tsokana,da yake idan taso tsokanarta haka take ce mata,dariya ta danyi ta gaidata tambayarta yaranta,ta amsa mata da suna lafiya,suka dan taba hirar data shafi gda sannan daga bisani shuru ya biyo baya,sai anty deena dince tace
"Kina bibiyar kuwa karatun da ake a groups din nan,kinsan kudi na biya kada ki sakani nayi asarar kudina" dariya ta danyi
"Inabi Allah anty,a ciki ma naga wani abu,nayi kuma to mommy hafsa tanata fada,nace anty ko banyi dai dai bane?" Ta qarasa fada a shagwabe
"Me kikayi kuma?" Antu deena ta tambayeta,bata boye mata ba ta gaya mata komai,anty deena tayi shuru tana nazarin maganar cikin ranta,zuciyarta na hasaso mata wani abu,amma kuma nataso ta dora nata tunajun ko tunanun yarinyar akan hakan,tunda dukka dan adam ajizine,zai yiwu ajizanci ne da kuma yanayi ma kishi da zai iya motsawa kowacce mace a kowanne lokaci
"Bakiyi abu mara kyau ba widadun ummu..."
"Ba wani widad din ummu yanzun fa anty deena ta daina sona,su Aafiya tafiso,kullun mukayi waya sai tace zatazo amma taqi zuwa" murmushi ya kubce mata
"Zatazo weedad,kullum ummu cikin zancanki take,amma kafin sannan.....inaso kome kika gani ance ayi kiyi qoqarin yinsa,zaki yi?" Ta tambayeta,saita gyada kai
"Eh anty deena"
"Yauwa widad dinmu,sannan ko meye kika gani baki gane ba ko ya faru ki kirani,koni ko anty madeena ki tambayemu,ba komai ne idan mommy hafsa tace kiyiwa uncle din naki zaki dinga yi ba kinji ko?"
"Tom anty deena" sun dan jima suna waya tana sake wayar mata da kai a fakaice sannan sukayi sallama,koda suka gama wayar litattafan ta debo ta sake zabo wasu a ciki ta dora da karatunta,itama tama manta d batun mommy hafsa da duk matsalolinta.
Rai bace hafsat din ta goge kiran da widad din tayi masa,sannan ta koma dakin ta maida wayar ta ajjiye ta kamar yadda ta ganta taci gaba da zaman jiransa,amma kuna qasan ranta a quntace yake da abinda ya farun,tana zargi da kuma tuhumar kanta,kwana biyu ta watsar da kiran yarinyar bare taci gaba da saita mata hanya,amma fa tana tsoro,kada ya zamana ta hadu da gogaggu kima wayayyun da zasuyi mata karatun da yafi nata shiga,tunda kaduna badai hadakar gamayyar mutane daga gari da qabila kala daban daban ba,amma zata kira ta binciki hajiya amina taji dawa dawa take hulda.
Koda ya fito daga wankan baisan anyi kiranshi ba,saboda qarar shower ta hanashi jin ringtone din,yana goge ruwan jikinsa tana binsa da kallo,jikinsa luwai luwai, fatarsa mai santsi da taushi sai daukar idanu takeyi, muscles din a hade alamun ya samu kyakkyawan training,ta hadiye wani abu da qyar saboda kishinsa daya tsarga mata.
Waiwayawa yayi suka hada idanu da ita,saiya dauke kansa yana cewa
"Ya akayi?,me yake faruwa?" Qaqalo murmushi tayi sannan tace
"Har yanzu banji kace na fara hada kayana ba"
"Zuwa ina?" Yayi mata tambayar bayan ya isa gaban madubi yaja lotion dinsa zai fara shafawa,wani abu ya tsarga mata amma ta dake
"Umara mana" sai daya kalleta ya kuma ci gaba da shafa mansa sannan yace
"Ban shirya wannan zuwan dake ba,babu kudi a hannuna,ina cewa ma ko wata shida bamuyi da zuwa ba ko?"
"Eh amma ai musulmi baya gajiya da zuwa" kai ya gyada
"Haka ne,amma yanxun bani da kudin da xamu iya tafiya mu duka,ke ni da hajiya" ranta ya baci sosai, zuciyarta tayita qissimata mata abubuwa da yawa da zata gaya masa,a fakaice dai hajiyan kusan duk shekara saiya kaita kenan,tunda itama ai baara iwar haka taje
"Aure ya cinye maka kudin kenan?" Ta tambayeshi tana tsareshi da ido,ya sake waiwayowa ya kalleta,ya kuma karanci yanayinta cikin sakanni,sai ya kuma dauke kansa ya maida ga abinda yakeyi,bayason doguwar magana,hakanan baya qaunar mita da qorafi
"Idanma hakanne ba mamaki bane" tofa,baki yasan me zai fada amma baisan me za'a mayar masa ba,saita miqe a mugun fusace
"Allah yayi mana arziqin da zamuyi ta zuwa babu mai hanamu" sai tayi waje fuuuu kamar zata tada iska.
Ransa ya sosu,amma ko iskar data kwasota bai kalla ba,yaci gaba da shirinsa,kafin ya sanya kayansa ya tsaya ya tsaftace sassansa,ya kuma dafa coffee yasha sannan ya qarasa shiryawa ya fice abinsa,yasan bazai rasa abinci gidan hajiya ba.
Tun daga wannan maganar ta dauke masa wuta gaba daya,shima kuma ya tattarata ya watsar ya baiwa banza ajiyarsa,yana ganin guga koda baiyi tsiran komai ba yayi na igiya,ta yaya zatayi kishi da mahaifiyarsa ko nawa kuwa zai kashe mata?,ita din ai ba tsararta bace.
Duka kwanakin da yayi kowa sabgarsa yake,amma hafsa din ta fishi damuwa,saboda tana da buqatar kudi a wajensa,baya ga haka tanason ya dawo da widad din har su dawo daga tafiyar,a wata dayan da zasuyi tasan zata moreta sosai,zata kuma dora mata karatun da zai zauna daram a kwanyarta,amma girman kai da jin tafi qarfin tayi qasa yasa taji gwara tayi shuru duk abinda ma ya yanke shikenan.
Ta bangaren widad kuwa cikin kwanaki qalilan karatun hausa novels ya shigeta sosai,idan tana karantawa tana jinta ne kamar a wata duniyar ta daban,yana debe mata kewa,tana kuma ganin abubuwan da suke bata mamaki,duk kuwa girki ko drinks din data gani saita gwada,a lokacin kitchen dinta yaga rayuwa,saidai duk abinda ta gwada din idan taga yayi farinciki cikata yakeyi,mai aikin maama(hajiya amina) ke tayata wani bin,tana ganinta kamar latifa saboda kirkinta.
Ranar da zai baro kadunan zai biya ta gidan hajiya ya daukota su wuce,har ya kammala shirinsa tsaf a sassansa tana nata sashen tana baccinta,don tun daga waccan ranar basu qara hada makwanci ba,tana sashenta yana nasa,yaci alwashin ko meye zatayi badai shi da qafafunsa ya bita yayi begging nata ba,yasan abinda takeso kenan.
Tare dasu mimi suka fito,a wajensa yaran suka kwana,tsaf dasu don su kansu sai daya shiryasu ya kuma gyara sasssan,suna riqe da hannunsa ya tura ya shiga,falon a hargitse kamar wanda aka tashi taron biki,harsa pampers din nawwara da yayi imanin idan bana shekaran jiya bane na jiya ne
"Ku zauna nayi sallama da mamanku" ya fada yana kallonsu,sai suka amsa suna hayewa saman kujerar,ya ajjiye luggage dinsa ya nufi qofar bedroom dinta,don ko takalminsa bai fidda ba saboda tsaftar tiles din ma bata gamsheshi ba,duka yayi rod'i rod'i kamar an watsar da ruwan tea ya fara bushewa samansa.
Sau uku yana knocking sannan yaji ana tambayar waye da cunkusashiyar muryar bacci,gyaran murya kawai yayi,ta taso tana turbune fuskarta daya kacame saboda bacci ta buda qofar.
Ido hudu sukayi, doguwar rigar wata kodaddiyar atamfa ce a jikinta da aka yiwa adon net,net din har ya soma bubbulewa alamun dake nuna ya fara gajiya da aikinsa,kanta gashinta ne him daya hautsine kamar ciyawar da aka tara za'a ciyar da dabbobi,abinka da baqar fata idan bai shafa mai ba....duk jikinta yayi fari fari,dakin yana fidda irin abinda jikinta ke fiddawa,da alama ya kama ko ina.
Kansa ya dauke,don takaicinta bazai kasheshi ba,ya fara gajiya da al'amuranta da kullum babu gyara sai gaba da abun yakeyi,ya sanya kai cikin dakin,dole ta kauce masa ya rabe ya shige,sai ya kasa zama,yana kallonta ta tsince pant dinta da bra dake watse a qasa
"Ina kwana?" Ta gaisheshi murya a cushe
"Lafiya....mu zamu wuce" ya bata saqo a gaggauce,saboda qagauta da yayi da wanzuwarsa cikin dakin,ya zura hannunsa a aljihu ya fiddo rafa na kudi ya matsa gefanta ya ajjiye mata yana cewa
"jibi zamu tashi,zamuyi sati uku idan ta kama har hudu ma,saboda inaso zamu tsaya egypt hajiya zataga likita,duk yadda ta kama dai....shikenan babu wani abu?" sai a sannan ta dago ta sake kallon sa
"Daa ka sani ma baka shigo ba,inda wucewarka kayi da hakan yafi" tsareta yayi da idanunsa yana mamakin furucinta
"Hafsa.....magana nake miki ta zanyi tafiyar da babu lallai na sake dawowa fa" gaba tayi tana qoqarin komawa cikin bargonta
"Allah ki yaye hanya" ta fada cikin nuna halin ko in kula taja bargo ta rufa abinta,saidai tuni idanunta sun cika da hawaye,banda qin Allah,da kudin da zataga likitan basai ta haqura ba a biya musu tare,idan suka dawo taga likitan a nan ba,ai duka daya ne,to amma a'ah,wai dole sai an nuna maka iyakarka.
Sai daya bata kusan mintuna a tsaye yana kallonta ta cikin bargon,zuciya na hasalashi amma ya hadiye ya juya a hankali ya soma fice daga dakin.
Wuf tayi ta yaye rufar ta kuma sauko daga gadon,da gudu tasha gabansa
"Au tafiyar zakayi?" Ta fada hawaye yana layi kan fuskarta,kallo daya yayi mata ya kauda kansa,saboda yadda zuciyarsa ke azalzalarsa
"Tun ba yau ba nasan baka damu da damuwata ba dama,ba abinda ya shafeka da baqinciki na ko walwalata,to kaje,amma ka sani akwai hisabi tsakanina dakai,Allah bazai taba yafe maka ba idan ka zalunceni" ido ya runtse yana jin zafin maganganunta,ya budesu a hankali sai suka kan yaransu,mimi da nawwara suna tsaye daga bayanta sunyi carko carko,da alama sun fahimci wani abune mara dadi yake faruwa.
Maganganu ne da yawa a ransa da amsoshin da zai bata,amma sai ya hadiye,muryarsa a sarqe yace
"Naji,Allah ya saka mikin,matsa ki bani hanya" jagale tayi tana kallonsa,sai kuma ta saki qofar ta koma ciki da gudu ta fada gado tana sakin kuka,baiko waiwayeta ba ya matsa zuwa gaba,ya sunkuya yayi kissing goshin yaran sannan ya kama hannunsu zuwa falo ya kunna musu cartoon yayi musu dabara ya fice.
Har suka kama hanyar kaduna ransa a bace yake amma yaketa dannewa saboda kada hajiya ta fahimta,yasan yanzu zata gaza nutsuwa.
Sai da suka shiga garin kaduna sannan ya fara tunanin yadda zasu samu widad ita kuma,abinci da zasuci da sauransu,yau dai ba makaranta yasan tana gida,to amma abinci bashi da tabbacin zasu samu,tunda ga wadda a haife ta haifeta ma bata da wannan tunanin,ina ga ita?,ya yanke kawai idan sun isa yana kai hajiya ciki ya koma ya siya musu abinda zasuci ya hada musu da order din abincin dare,gobe kuma ya samu time yayi musu,da wannan tunanin suka shiga unguwarsu.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:huguma*
Page 62
Tun jiya da ya kirata yace mata gobe zasu taho da hajiya,tayi murna sosai saboda zaman kadaicin ya isheta amma bata kawo wai ta tanadi komai ba,ta dauki littafinta taci gaba da karatunta,tana tsaka da karatun taga inda jarumar littafin ke shirye shiryen dawowar mijinta daga tafiya,abun sai ya burgeta sosai,ta idar da sallah azahar tana saman abun sallah abun ya sake fado mata,saita dauki wayarta ta kira anty deena tana labarta mata
"Kema irin hakan zakiyi, bakiga abincin da aka kiya jiya ba a group?" Kai ta gyada
"To haka zakiyi,ki shirya shi kamar yadda aka koyar ana shirya abincin mutum" daga kan abun sallar kuwa bata koma yin komai ba ta fara practicing abincin,datayi kuma yayi mata yadda takeso,suna da komai ba abinda zata buqata,saita fara shirya komai tun a ranar.
Washegari gari yana yin haske ta gyara gidan,dama ta saba wannan ya fara zame mata jiki,saidai yau har dakinsa ta gyara kamar yadda anty deena tace mata,tana yi tana kiran anty deena ita kuma tana qara mata haske,tana aikin suna video call da anty deena ta watsapp,sannu sannan sai gashi har girkin ta gamashi tsaf,ta kuma zuba a warmer,ta jera,anty deena ta kalla ta cikin wayar,cikin farinciki tace
"Well done qanwata,yanzu saura abu daya" langabe kai widad tayi
"Allah anty na gaji sosai"
"Aikin gama,sauranki wanka,ki dauko kayanki na zuwa gidan biki ki saka,yau duka kayan kwalliyarki ki juyesu a fuskarki" ido widad ta zaro tana dariya
"Kai anty....suna da yawa fa" dariya itama tayi
"Ai wai ina nufin ayi kwalliya da kyau,a saka turaren gida dana jiki ako ina" dan turbune fuska tayi
"Wai anty duk uncle akewa haka?"
"Kai,ai yafi gaban haka ma,ba kinje min litattafai kika samu kina karantawa ba?,bakiga yadda akeyi bane?" Batason tacewa anty deena din eh,saboda wasu guraren cikin litattafan kunya suke bata(tsarkakakkun litattafai wadanda babu batsa a ciki sai qaruwa),kai ta gyada mata a kunyace
"Good,maza kije ki shirya to" cewar anty deena,daga haka suka katse kiran,ta dauki wayar ta wuce bedroom dinta,tana tafe tana hangen dining din kamar wani zai bata mata aikinta,saidai murmushi kawai takeyi najin dadin yau ta qure adaka tayi abinci,gidan kansa yadda yau ta gyarashi ita da kanta yana bata mamaki.
Sai data bata lokaci a daki tana zaben kayan da zata saka,anty deena dai tace mata atamfa,ita kuma babu abinda tafiso irin doguwar riga abaya,don kusan kullum itace shigarta,kamar kuma sunsan zabinta sun sakota da yawa sosai a lefenta,tana kallon abayar ta haqura,ta ciro atamfa riga da skert,blue black mai adon maroon,sannan ta shige bandakin ta hada ruwan wanka ta fara wanke jikinta.
Tana wankan tana 'yan waqe waqenta qasa qasa,saboda yau din nishadi takeji cikin ranta,ta gama cuda jikinta ta shige asan shower ruwan yana ratsata,saita tuna gida,ummu na hanata shiga shower saboda wasa takeyi da ruwa, kuma tana jiqewa har kanta ne,sumarta nada tshao da yawa,yawancin lokaci saidai a saka hand Drayer a busar mata da ita,saita saki murmushi,tana jin ba dadi cikin ranta,ko sai yaushe zata ga ummu?,bata tabq zato a rayuwarta zatayi nesa da ummu har haka ba ta kuma haqura ba.
°°°°"alhamdulillahi" hajiya ta fada tana fitowa daga motar bayan tsaiwar motar tasu a farfajiyar gidan,murmushi abbas yayi
"Yau gaki a kaduna dai" sai tayi murmushi
"Eh nufin Allah kenan" yana janye da trolly dinta, muneera na dauke da jakar hannunta suka doshi sashensu.
"Assalamualaikum mutan gida" hajiya ta fada tana murmushi idanunta cikin falon,wani boyayyen ajiyar zuciya abbas din ya sauke,saboda hango warmers da yayi saman dining din,uwa uba yadda fakon yake a tsaftace ya qawatar dashi,duk da dama bai tana ganin wani abu na qazanta ko qanqani a tattare da ita ba,hasalima yana mamakin yadda bata son taji ta taka datti
"Ki zauna hajiya,inajin tana daki" ya fada yana janye mata pillow din kujerar,tayi bismillah ta zauna,haka kawai taji ranta yana mata dadi,ya juya ya dubi muneera
"Ki samo muku ruwa da lemo"
"Aah,bari dai matar gidan ta fiti tukunna ta shaida xuwanmu ko?" Murmushi abbas yayi
"Peace maker" shine sunan da sau tari yake kiran hajiyarsa,bata qaunar tashin hankali ko kuma husuma ko kadan.
Kayan daya gani baje saman gado yasa hankalinsa yadan tashi,bai kuma ji motsinta ba,ba tare da tunanin komai ba ya murda handle na bandakin ya tura ya sanya kansa.
Dai dai lokacin da take tsaye babu komai a jikinta,sai towel a hannunta tana tsane gashin kanta,mugun zabura tayi ta kuma tsorata matuqa,saidai data waiwayo suka hada ido sai taji kamar zata narke a wajen,saboda tsorata saita jefar da towel din,ta kuma sulale a wajen ta duqe tana cure jikinta waje daya,ko ina na jikinta rawa yakeyi,take ta fash da kuka.
Shi din ma kamar an jona masa lantarki haka yaji,ganinta a hakan ba qaramin al'amari bane a zuciyarsa da kuma gangar jikinsa,ya rintae idanunsa ya koma baya days saut yana mayar da qofar yadda ya ganta,saidai ya kasa sakin hannun qofar,yayi tsaye riqe da handle din yana maida mumfashi.
A hankali yaci gaba da sauke jumfashun nasa ta baki data hanci,ya bude idanunsa a hankali yana jiyo sautin kukanta,yasan yau kam ya taro match,sai ya matsa jikin qofar cikin kasala yace
"Am sorry" shuru bata amsa masa ba,sai ya sake daga murya
"Am very sorry" cakin muryar kuka tace
"Kana sane ka budeni,ai kasan wanka nakeyi" murmushi ya saki tsigar jikinsa na sake zuba a,daga dawowarsa ta masa wani irin kunnawa da yasan bashi da maganinta
"I swear bansan kina ciki ba.....am sorry.... please kiyi shuru mana"
"Allah tunda ka ganni tsirara bazan yadda ba" ta fada bayan ta miqe tana daura towel dinta da sauri,tana tsoron kada ya dawo.
Murmushi mai kama da dariya ne ya kubce masa,shagwabarta tana kasheshi ainun
"To shikenan,let me come inside,sai na cire kayana kema ki rama,kinga shikenan anyi one one"
"Wayyo ummuna....Allah karka shigo,idan ka shigo saina gayawa ummu" ta fada tana gunjin kuka jin yana taba qofar kama zai bude,dariya sosai ta kamashi har sai daya dan sunkuya
"Alright.....alright,shikenan,khalas.....ya isa,am sorry,ki qarasa ki fito,hajiya na falo tana jiranki" ya danja da baya har yanzu fuskarsa murmushi ne kwance akai ya baro dakin,gaba daya bacin ran daya taho dashi babu kaso hamsin cikin dari.
Da sauri ta miqe ta qarasa wankan jin cewa hajiya ta qaraso,ta shirya a gurguje,bata saka komai kan fuskarta ba,saisai jikinta ya wadata da turare,sanon turare ne ta bude cikin kayan lefenta.
Rungume hajiyan tayi abinta tana jin dadi,sai take ganin kamar ummunta ce tazo,ta ma mance dashi a wajen,suna gama gaisawa ta gabatar mata da lemuka da ruwa
"Hajiya na kawo miki abinci?,ni na girka da kaina" ta fadi tana murmushi,ta qagu taci taji me zata ce,dariya tayi
"Bari nayi sallah tukunna widad,nunan bandaki"
Dakinta ta kaita ita da muneera duka harda kayansu,sukayi sallah sannan suka dawo falon ta fara zuba musu abincin,a sannan abbas daya fita salla masallaci bai dawo ba.
Hankali kwance suke cin abincin suna hira,duk yau sai widad takejinta free kamar a gida,babu wanna kadaicin ba komai,har suka gama bai dawo ba,sukaci gaba da hirarsu hajiya na jinsu,yanayin da taga widad yayi mata dadi sosai,saboda ta qara wani irin haske akan wanda take dashi,hakanan ta murje sosai,duk da ba qiba tayi ba,amma fatarta tayi kyau.
Yamma liqis ta sake shiga kitchen ya gwada yin tuwo miyar kubewa,tanata taraddadi kada tayi kwaba,cikin ikon Allah sai gashi tayi shi fes,abinda ya faranta mata ranta,ta gama suka gyara kitchen din,muneera tayi mata wanke wanke sannan ta gabatarwa da hajiya bayan sunyi sallar magariba.
Farincikin da hajiyar ta tsinci kanta a ciki ba dan kadan bane,zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba cin.abincin gidan abbas din ba sai wannan karon,karamcin da yarinyar ta nuna mata ya qara dad'ad'a abincin a bakinta,ya kuma qara mata qaunar widad din a zuciyarta.
Tana ta so tayi wanka amma kuma sai takejin nauyin hajiyan, saboda ba zata iya tube kayanya cikin dakin ta shirya ba,sai ta basar kawai sukaci gaba da hira abinsu.
Ana idar da sallar isha'i dukka suna falo,a sannan yayi sallama ya shigo,hannunsa dauke da leda,dukkan alamun gajiya sun bayyana a tare dashi.
Kusan a tare sukayi masa sannu da zuwa,ya amsa yana zubewa gaban hajiyan yana mata barka da dare
"Ina ka shiga haka?,tun dazu nake taraddadi"
"Wallahi na leqa office ne,akwai ayyukan da nakeso na rufe file dinsu kafin mu wuce,kuma zan dauki excuse ma.na tafiyar tamu".kai ta jinjina
"To Allah yayi.jagora ya dafa"
"Ameen ameen hajiya,kunci abincin dare?" Sai da tayi murmushi sannan ta amsa
"Munci abinci kuwa,tuwo ma,mun qoshi kuma alhmdlh"
"To ma sha Allah" ya fada ransa na masa fari,bai taba zaton zai tadda hakan ba,ya saci.kallonta kanta yana a qasa tana wasa da zaren dankwalinta,har yanzu haushinsa takeji,kunyarsa kuwa kamar ta bace a wajen,musamman idan ta tuno a yadda ya ganta,ko ummu bata zaton ta taba ganinta a haka da wayonta.
"Na gaji fa sosai,inajin kwanciya zan shiga nayi" hajiyan ta fada tana miqewa,sai muneera itama ta miqe,don itama a gajiyen take
"Ya kamata"
"To Allah ya bamu alkhairi,sai da safe" tayi musu sallama suka wuce dakin ita da muneera.
A hankali ya tattaro dukka.hankalinsa a kanta,ya xuba mata idanuwansa yana kallon ta,da gaske ba zata kalleshi ba,har yanzu baku dankwalinta yana hannunta tana ta murzasu,cikin sakanni jikinta ya bata saqon cewa ana kallonta, tasan kuma shine,saboda rashin wanzuwar motsinsa kadai ya isa amsa.
Dan daga kai tayi,sai suka hada idanu, karon farki taji ba zata iya jurewa ba,ta saki gefan mayafin ta yunqurq zata miqe
"Ina zuwa?" Ya jefa mata tambayar,qeya ta juya masa,ya kuma tura baki gaba
"Zanje na kwanta,nima baccin nakeji" yadda tayin ya bashi dariya,amma ya maze
"Haka zaki tafi ki barni,ni baki bani abincin ba yuwa nakeji" ya fada yana karyar da wuya kamar qaramin yaro,shi kansa baisan yayi hakan ba.
Dan jim tayi,sai maganar anty deena ta dawo mata
"Idan ummu taga yayi miki ba dai dai ba ko nuna rashin kulawa,kinsan zataji babu dadi ko?,to kema idan kika masa hakan hajiyarsa ba zataji dadi ba" da wannan tunanin ta juya zuwa dining area don kwaso masa abincin,yabi bayanta da kallo,sosai skert din ya zauna mata das das,ya fidda qugunta dake juyawa sanda duk tayi taku,kamar da gayya takeyin hakan,ya janye gajiyayyun idanuwansa a hankali ya lumshesu yana furta kiran sunan Allah.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 63
Koda ta hado kayan abincin ta dawo bata sameshi a falon ba,amma taga qofar dakinsa a bude,da alama yana ciki,tadan bata fusja kadan,itafa batason haduwarsu sam,ya gama kalle mata jiki ta yaya zata iya fuskantarsa,amma dai babu yadda ta iya,haka ta taka zuwa dakin nasa roqe da tray din data shiryo komai akai.
Sanda tayi sallama ta shiga ya gama fidda kayan jikinta,daga shi sai pant na maza iya cinya,a yadda ta ganshi tayi masifar tsorata,don bata taba ganinsa koda singlet ba,hakanan tsahon rayuwarta bata taba ganin wani namiji haka ba sai a kansa,saura kadan ta zubda kayan hannunta,taja baya da sauri tana neman qofar fita amma sai ya rigata isa wajen,yasa hannu ya maida qofar ya rufe,ta bude baki ya tabbatar ihu ko kuka zata masa,sai yasa hannunsa saman bakinta ya rufe da kyau,sannan yasa daya hannun ya karbe tray din daketa tangal tangal a hannunta zai kife ya aje a qasa.
Dab da ita ya matsa,har jikinsa yana dan gogar nata,sai taji kamar numfashinta zaiyu qaura yabar gangar jikinta,manyan idanunta gaba daya sun fito waje kamar zasu fado.
Magana yakeson mata amma ta maqale masa a maqoshi,qamshinta dake tashi daga jikinta keson rikita masa lissafi,idanunta masu haske da ruwan hawaye ya cikasu suka soma fusgarsa,yayi ta maza cikin taushi da raunin murya yace
"Keep silent please..... hajiya tana ciki fa,so kike tace na miki wani abu?,zata batamin rai idan haka ya faru" ya qarashe zancan a narke kamar yaron dake tsoron duka daga mamansa.
Sake sanya idanunsa yayi sosai cikin nata,itama shi take kallo,wasu irin idanuwa da suka dinga tilasta saukar nutsuwa a jikinta,a hankali yaci gaba da aike mata da wani saqo ta cikin idanuwansa,har hawayenta suka fara bacewa,nutsuwarta ta fara daidaita,kunya ta maue gurbin tsoronta,sai ya sauke hannunsa a hankali daga kan bakinta daya gaji da motsawa yayi laqwas,yaja da baya a hankali ya dauki babbaj towel ya rufe jikinsa sannan ya doshi bandaki,doke sai yayi da gaske,ya cire tsoronsa daga ranta muddin yanason su zauna zama na auratayya mai dadi,sai ya sake kawo kusanci sosai a tsakaninsu,sai ya zama komai nata ya kusanta kansa da rayuwarta,tana da kima da darajar da yake jin dole ya sama mata gurbi a rayuwarsa,saboda ita din kamar isharar mahaifiyarsa abar soyuwarsa ce,ya zama dole ya kimantata ko don farincikin mahaifiyar tasa.
"Ka rufe qofar fa" ta fada bayan ta hadiye wani abu muryarta tana dan rawa,har ya sanya kai a toilet din sai ya fasa ya waiwayo
"Ki jira na fito daga wanka tukunna" sai ya shige.
Jikinta babu kuzari ko kadan ta sulale ta zauna a wajen,wani abu ya fara mata yawo cikin kwanyarta gangar jiki da kuma zuciyarta,a yau daya kusanta kanshi da ita bawai tsoro kadai taji ba,kunya nauyi da kuma wani irin yanayi da batasanshi ya mamayeta,saidai akwai wani irin tsoro nasa danqare a zuciyarta,hakanan yana mata mugun kwarjini mara misali.
Yana goge ruwan jikinsa yadan kalleta,ta takure waje daya,ta kuma qi yarda su hada idanu,ya saki boyayyen miskilin murmushi,yasan me yake damunta,ya matsa gaban mudubi ya fara shafa mai
"Kina sane kenan kika shigomin daki ko?,kin rama nima kin ganni babu kaya" yayi maganar yana kallonta ta cikin mudubin,kai ta daga da sauri,suna hada ido ta mudubin kuma saita maida kan nata ta fara qananun hawaye harda rantsuwa ita batasan ya cire kayansa ba,ita bata kalleshi ba,dariya kamar yayi me,wanann wautar tata da quruciyarta wani bangare ne dake sanyashi nishadi,ya gama shirinsa cikin wata armless fara qal din shirt,sai wando daya tsaya masa iya qaurinsa
"Ai shikenan......"
"Budemin to zan tafi" ta katsi numfashinsa
"To zubamin abincin naci tukunna" da sauri ta zuba masa komai ya zauna zai fara ci sai ya kalleta
"Zauna muci" kai ta gyada
"Na qoshi"
"Bakison tafiya kenan?" Kai ta kada da sauri,saita matso ta sanya hannu suka fara ci.
Suna ci yana kallon idanunta,saidai ko kadan taqi yarda ita din ta kalleshi,yadda cin abincin yayi masa dadi saboda ya saba ci dasu mimi a gida nan kuwa saishi daya.....haka abincin ma yayi masa dadi
"I can't believe ke kikayi girkin nan" abinda take son ji dama taji ya yaba kenan,har batasan sanda ta kalleshi ba tana dan murmushi
"Allah nice nayi,yankan kubewa kawai muneera ta tayani"
"Wow...wow,,nan gaba ina da great cook kenan,na shirya cin abinci da kyau" murmushi ya subuce mata,tayi qasa da kanta,tana jin dadi sosai har cikin ranta.
Ganin ya gama cin abincin yana shirin sake zama sai tace mishi
"Kace idan ka gama zaka rakani fa"
"Oh yeah,muje to" ya furta yana sanya bedroom slippers dinshi,yana gaba tana binsa a baya.
Murda qofar kadan yayi,sai ya waiwayo yana dubanta da alamun damuwa kan fuskarsa
"Ayyah....sun riga sun kulle qofar" kallon qofar tayi sannan ta kalleshi
"Wayyo Allah na"
"Ko ayi knocking ne?" Ya fada da sigar jarrabata,taci kuwa jarrabawar da karon farko.ta qara mata kima da daraja mai dimbin yawa a idanunsa,don kai ta girgiza
"A'ah,ummu ta hana,tace ba'a tashin babba idan yana bacci,hajiya ta gaji tun dazu na gani.....amma saidai....." Sai kuma tayi shuru tana kallonsa.
Wani qawataccen murmushi ya saki,idanunsa cikin nata yana jin kamar suna narkewa ne zuwa sassan jikinsa
"Saidai me?"
"Saidai na kwana a falo?" Kai ya girgixa
"Qwarai kuwa" ya fadi sounding seriously,sannan ya fada takawa yana nufar qofar dakinsa,da hanzari ta taka ta bishi,harda riqo masa hannu ba tare data sani ba
"Da gaske tafiya zakayi ka barni a nan?" Kai ya kada,yanata qoqarin danne dariyarsa
"Yes,da ina zaki bini?" Marairaice masa tayi,harta fara guzurin hawaye
"Please mana,kaji tausayina" badon yayi da gaske ba wannan karon dariyar saita fito
"Oh.... okay,me kikeso yanzu?"
"Ka barni na kwana a dakinka,nan din tsoro nakeji Allah" ido yq zaro kamar gaske
"Dakina kuma?"
"Eh" yadanyi shuru kamar mai tunani
"Matsalar ni gaskiya ba za'a hanani kwanciya a gadona ba,kuma idan muka kwanta gado daya ina da juye juye,zan.iya danneki ban sani ba,saidai ki tasheni idan kikaji haka saina dagaki,kin yarda?" Kai ta gyada da sauri,saboda kukan mage data fara jiyowa
"Fine,muje" tuni tayi gaba suka jera kafada dashi, dariyar kamar yayi ke haka ta dinga cinsa,yana sane yayi mata wannan hikimar,banda haka tubura zatayi masa.
Ta rigashi kwanciya amma idanunta biyu,yana kallonta ta ninka duvet dinsa guda daya ta raba gadon dashi,taja daya ta lulluba, murmushi yayi qasa qasa
"Zanyi maganinki yau kam" ya fadi yana maida dubansa ga takardun da yake dubawa,sai daya gama komai,sannan ya haye gadon,ya jawo wayarsa ya kunna sound na kukan mage,ya saitashi wajen kanta ya koma ya kwanta abinsa.
A hankali kukan magen ya fara ratsata daga baccin daya dauketa,dama kuma ba wani nisa can sosai baccin yayi ba,rudewa tayi gaba daya saboda jin kukan a kusa da ita sosai,batasan sanda tayi cilli da katangar data gina a tsakaninsu ba, hankali kwance yaji ta shige jikinsa hadi da qanqameshi,wanan lallausan jikin nata ma'abocin qamshi ya nutse cikin faffadan qirjinsa,sai ya saki wani tattausan murmushi,cikin sanyi ya kamota zuwa jikinsa sosai ya mata kyakkyawar runguma da har sai da zuciyarsa ta gamsu da hakan,ya dora hannunsa a gadon bayanta yana dan bubbugawa
"Shshhhhhhh.....,zata tafi fa.....yanzu" maganar tasa ta rarrabe saboda yadda ta raba tsakanin cinyoyinsa da qafafunta tana sake shige masa kamar zata koma jikinsa
"Tana qasan gadon,ka koreta uncle" cikin tsoro take fadar haka,tuni ta soma rikitashi,sai ya dora bakinsa saitin kunnenta
"It will be alright"furucin da ya sanya jikinta wani zubawa,abinda bata taba jiba tsahon rayuwarta,yanayin da yasa ta sake maqale masa da kyau,ta kuma sanya fitar numfashin sa sake jirkita,ya nutsa hannunsa gadon bayanta ya hade da ainihin fatar jikinta mai santsi a maimakon rigar dake jirkitanta,taji hakan har cikin qashi da bargonta,to amma kuma tsoro ya hanata motsawa,ji yayi kamar kada ya kashe kukan,amma yadda yaga ta tsorata dole badon yaso ba ya zura hannunsa ya kashe wayar gaba dayanta.
A hankali a hankali ya fara fitar da numfashi da gudu gudu,tun tana tunanin ba komai bane har hankalinta ya kawo kan canzawar da taji yayi,hakanan bugun zuciyarsa sosai yake shiga zuwa ga kunnuwanta dake kwance saman qirjinsa dake shimfide da lallausar gargasa,a hankali ya daga kanta tana duban fuskarsa
"Uncle.....baka da lafiya?" Murmushi ya qwace masa,gumi na saukowa ta saman goshinsa kadan kadan
"Am fine,kwanta kiyi baccinki" ya qarashe maganar yana cije labbansa,saboda yadda mararsa ta murda masa
"Gumi fa kake uncle"
"I know,na sani"
"Ka bari na taso hajiya"
"Aah"
"To akwai magani na dauko maka?"
"Kece maganin" ya fada muryarsa tana rawa,sam bata fahimci me yake nufi ba,don batasan ainihin abinda yake damunsa ba
"Ni kuma uncle?"
"Yes,but.....ki kwanta kawai nace" ya fada da dan kaushi,saboda ciwon da cikinsa ya fara,jiki a sanyaye ta zame kanta daga jikinsa zata kwanta gefe,sai yasa hannunsa ya tarota
"No,don't leave me,stay here,i will be okay" gaba daya sai taji bata da kuzarin musawa,ba wani sauran tsoro tattare da ita,tana jin sanda ya matso da ita zuwa jikinsa sosai,sai taji tausayinsa ya kamata,tana da saurin kuka da karyewar zuciya akan mara lafiya,don haka tasa dukka tafukan hannuwanta biyu a kuncinsa hagu da dama tana masa sannu da muryarta can qasa,abun sai ya zame masa kamar fami,don haka yasa hannayensa ya cire hannun nata,ya kuma jawota jikin nasa still yana cewa
"Kiyi bacci,good night".
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 64
Shi kadai yasan yadda yayi surviving wannan daren,ya azabtu da yawa,daga baya da yaga ba sarki sai Allah dole ya zareta daga jikinsa bayan yaji saukar numfashinta tayi bacci.
Ya dade yana kai komo,zuciyarsa na gaya masa ya aika abinda zai samu sassauci,to amma yana tuna abinda zaije ya dawo,har yanzu ya tabbatar bata gama sanin meye aure ba,bugu da qari rainon zuciyarta yakeyi,baida tabbacin soyayyarsa a ranta,beside ma hajiya na gidan,bai kamata haka ta kasance ba a karon farko.
Sai wajen biyu na dare ya samu kansa da qyar,da kansa ya zabi kwanciya a qasa,zuciya da ruhinsa cike fal da tunani,wannan din ba komai bane sai kasawa da gazawar hafsa,bai taba zuwa mata weekend ko tafiya irin wannan ya samu irin tarbar da yakeso ba,bai taba dawowa sun rabu lafiya lau da ita ba,duk yadda kuwa zaikai gakai zuciyarsa nesa da dauke kansa,ya tabbatar inda ya samu ko yana samun yadda yakeso daga gareta,duka hakan ba zata faru dashi ba,saidai kuma ajizanci irin na dan adam.
Kusan tare suka tashi sallar asuba shi da ita,abu na farko data fara tambaya tun batayi alwala ba shine lafiyarsa,ya jikin nasa,ya saki murmushi yana jin dadi hat xikin ransa,saboda baisan da kalar wannan kulawar ba,yana iya yin ciwo har ya warke hafsat din bata sani ba saboda tsabar rashin kulawa irin nata
"Na warware alhmdlh"
"Sannu uncle,Allah ya sawwaqe"
"Ameen" ya amsata yana murmushi,da gaske yarinyar ce,wadda aka raineta bisa tsaftataccen tarbiyyar da har batasan meye ainihin ma'anar aure ba,batasan sha'awa ko wani abu daya danganceta ba,abu kadan ta sani wanda baikai girman da zai shiga tunani ya lalata mata rayuwa ba, tashin farko da yaji rashin sanin meye aure da batayi ba bai wani dameshi sosai ba,saboda wannan shine yake basji guarantee na cewa ita din mai tsaftataccen tunani ce da batasan komai ba,zaiyi dashensa yayi shukarsa ya kuma yi girbinsa yadda yakeso kenan.
Tana kan abun salla tana tunanin me zata dafa da safen,wayarta da tayi qara ta katse mata tunaninta,ta tashi ta dauko wayar tana duba me kiran
"Mommy hafsa da safen nan?" Ta tambayi kanta gabanta yana faduwa,sai a sannan ta tuna a dakinshi fa ashe ta kwana,ko wani ya gaya mata ne?,wannan tunanin ya hanata daga wayar har ta katse.
Iska mai zafi hafsa dake tsaye cikin dakinta ta furzar,ta daura alwalar amma ta gagara tayar da sallar,ta manta gaba daya gidan daki biyu gareshi,hakan yana nufin hajiya na daki daya,ita da abbas dinta zasu kwanta daki guda shimfida guda?.
Ko yanzun data kiratata bata daga ba, zuciyarta na kissima mata qila a daren jiyan ya samu yadda yakeso ne,babu yadda take shi yasa ta gaza daukar wayarta,wannan tunanin ya tashi hankalinta,ta koma gefan gadon ta zauna ta shiga jera mata kira ba qaqqautawa.
Abin da ya sake tsorata widad kenan ta kasa daga kiran,lallai tasan a dakinsa ta kwana,kuma tambayar da zata mata kenan tunda taketa kira,sai ta ajjiye wayar tana kallonta gabanta yana ci gaba da faduwa,har zuwa sa'ar da abbas ya dawo daga sallah,ya buda qofar dakin ya shigo.
Idonsa akan wayar,don itama ita take kalla,hannunsa zube a aljihunsa ya qaraso,ya dauke idonsa daga kan wayar ya maida kan fuskarta,saita dan dauke kai tsoron kiran da ake mata,da kuma kunyarsa suka hadar mata
"Ina kwana?"
"Kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau ya jikin naka?" Idanunsa ya lumshe ya kuma budesu yana sakin murmushi, lallai quruciya na damunta da gaske
"Da sauqi,na warke" kai ta jinjina masa,sai ya sake duban wayar
"Ba kiranki akeyi ba ki daga" fuska ta kwabe sannan ta girgiza kanta,bai sake cewa komai ba ya matsa wajen kujerar da yakan zauna yayi karatu da asuba ya jawota ya zauna,sai widad din ta miqe a hankali ta nade abun sallar nata,ta nufi qofar fita a dakin
"Ina zuwa?" Waiwayowa tayi
"Xanje gaida hajiya" sai ya gyada mata kai kawai.
Daga inda yake zaunen yana hangen hasken da wayar taketa yi,yadda aketa kira ba qaqqautawa ya bashi mamaki,ba tare daya shirya ba ya miqe,ya isa ga wayar ya dauko,sai yaga sunan mommy hafsat,abun ya daure masa kai,ya juya yana duba wayarsa waiko zaiga miscall dinta,may be ta kirashi ne baya kusa bai daga ba,wani abun kuma ya faru,amma sai yaga babu kiranta ko daya,ya daga wayar ya kara a kunnensa tare da yin sallama.
Jin muryarsa ya qarasa fadar mata da gaba,jikinta gaba daya yayi laushi,ta saki abun sallar a qasa,da gaske suna tare,tare suka kwana,kasa motsawa bakinta yayi,ta riga data samu amsar abinda take nema,don haka ta kashe wayar tare da sulalewa a wajen ta saki wani irin kuka mai tsananin zafi da cin rai,shikenan,ta faru ts qare.
Jin alamun an katse ya sashi daga wayar ya kalli screen din wayar,sai yadan tabe baki ya maida wayar ya ajjiye,har ya taka zai bar wajen sai hoton fuskar wayar ya dauki hankalinsa,ya koma ya sake dauka,ya koma saman kujerar ya zauna,ya buda gallery ya soma kallon pictures din a hankali har baisan sanda murmushi ya dinga kubcewa daga fuskarsa ba,kowanne hoto da kalar quruciyar da za'a nuna a jiki.
Hannunsa ya miqa,ya dauki wayarsa ya buda,yayi marking wasu daga ciki ya tura.
Ranar kaf qin yarda tayi ta sake komawa dakinsa,ko hanya qin yarda tayi su hada dashi,tana tsakanin dakin hajiya da kitchen,bayan sun hada breakfast ita da muneera suka shirya komai a falo,tare sukayi break din har hajiyan,sunayi ana taba hira,da suka gama suka sake gyare gidan tare,shi da hajiyan suna dai falo suna hira,a nan sukaci abincin ranar tare da hajiyan,sannan ya koma daki ya shirya ya fice.
A daren ranar yana zaune daga bakin gadon sa,qaramin littafin addu'o'i ne a hannunsa yana karantawa,ya gama komai,kammala addu'arka ne kawai ya rage masa,amma sam baiji motsinta ba,lokaci lokaci yana daga kai ya kalli bakin qofar dakin nasa a haka har ya kammala addu'ar,ya aje littafin gefen bedside ya zuro qafafunsa ya zura bedroom slippers dinsa ya miqe a hankali ya fito daga dakin.
Babu kowa a falon,amma yaga dakinta a bude,yasan suna ciki,yayi gaba zuwa dakin,ya tura qofar bakinsa dauke da sallama.
Dukkansu suka amsa,hajiya na zaune gefan gado,muneera da widad na saman qaramin carpet din dake shimfide qasan dakin,muneeran na maidawa weedad kalbar kanta da santsin kan ya sanya ta ware kamar ba'a taba yinta ba,bataso a taba mata kai tana ta qorafi muneeran na fadin saita yi mata,hajiya na goyuwa da bayan weedad din.
Kadan ya kalli sashen da suke,ya qaraso ciki,ya samu gefan hajiya ya zauna
"Bakiyi bacci ba hajiya?" Sai tayi murmushi
"Banyi ba,ina dai shiri"
"to yayi kyau,kin hada komai naki waje daya ko?, saboda gobe sha biyu zamu fita"
"Komai a kammale yake"
"Ma sha Allah.....shikenan,dama zuwa nayi nai miki sallama,sai da safe"
"To Allah ya bamu alkhairi ya tashemu lafiya" sai ya juya yana ficewa a dakin,minti biyu hajiyan ta kalli widad
"Maza tashi ki tafi ki kwanta kin baro mijinki,nikam sai da safenku" dif widad tayi,don ita gaba daya ta gama tsarin kwana a nan din,ta dan dubi muneera taga itama ta fara shirin kwanciyar,dole ta miqe,ta dauki siririn gyalen abayarta ta dora saman kanta,ta bude closet dinta ta dauki rigar bacci tayi musu sai da safe ta fita.
A sanyaye ta tura qofar dakin tashiga da sallama,yana zaune daga bakin gado yana amsa waya,haka kawai yaji sanyi har cikin ransa sanda yaga ta shigo din,bandaki ta wuce,ta fidda kayan jikinta tayi wanka,don zuwa yanzu tayi mugun sabo da wankan dare,ta shirya cikin kayan baccin ta fito.
Dim light ne a dakin,yana iya hangen sanda ta fito da kuma hawanta saman gadon,taja duvet ta kwanta ba tare data ce komai ba,qaramin murmushi ya saki,abinda ya faru jiya yana dawo masa,sai ya samu kansa da janyo wayarsa,ya duba wajen music ya lalubo kukan magen jiya ya saka.
Curewa tayi waje daya,tun tana iya ganin zata jure harta kasa,sannu sannu sai gata cikin jikinsa ta cukuikuye shi,ya saki murmushin nasara ya sanya hannunsa ya lullubeta cikin qirjinsa yana sakin murmushi,ita kuna tayi lamo tana sauraren bugun zuciyarsa da nata da kowannensu ke fita da sauri da sauri.
0 comments:
Post a Comment