Sosai hankali Aneeesa ya tashi, ta dubi Barrister Mansur ta ce mai, "wai ita wannnan matar ɗin wacece ita da naga har alƙali da aka tashi girmamata yakeyi?
Ta ƙarisa maganar tana kallon Barrister Mansur da Barrister zainab da Espector Idi da sukayi tsuru tsuru ba abun da ake hangowa a idanuwan su sai tsaɓan tsoro da firgici, da kyar Barrister zainab ta iya buɗe baki ta ce ma Aneeesa, "tabbass mun yi tuya mun mance da Albasa domin ina tabbatar miki da cewa Hajiya a tarihin ta bata taɓa shari'a an kada ita ba tun lokacin da da take lauya har ta zo ta zama alƙaliya, saboda tsaban gaskiyar ta da ruƙon amanarta da jajircewa domin ita ko cin hanci bata karɓa hakan yasa aka bata shugaban Alƙalai na ƙasa baki daya, a gurin ta ai Barrister Khasheeefat ta koyi wannan jajircewar da kafiyan da bin ƙoƙƙofi, gashi yanzu munyi ƙoƙari mun kaita ƙasa gashi kuma muna neman ɓallo ma kanmu ruwa domin gwabzawa da Hajiaya tamkar faɗa da aljani ne kun ga kenan faɗa da aljani ba daɗi baza kuma ka tsinci komai ba sai wahala, ni gaskiya yanzu ku cireni daga tafiyar nan ba hannuna."
Barrrister Zainab tana gama maganarta ta ɗauki jakarta ta fice, gaba ɗaya jikin su yayi sanyi Barrister Mansur ne ya kalli Aneeesa ya ce, "Aneeesa ya kamata ki haƙura da wannan ɗaukan fansa ko iya haka kika tsaya kin san Hajiya Hindu taji jiki ni da ke da kowa ma da ke gurin nan yasan ba Hajiya ta kashe miki mahaifiya ba asali ma mahaifiyar ta ki ba ta mutu ba, abun da yafi muhimmanci yanzu shine muyi ƙoƙari mu gano in da aka ɓoye Mahaifiyarki."
"Barrister ka dakata ni Hajiya Saudat ba Mahifiya ta ba ce, domin na riga naji komai a lokacin da Hajiya Hindu take faɗa ma Mallam ɗin unguwar dosa komai dai dai ni kuma lokacin zan wuce na jita, tun daga lokacin naji na ƙara tsanar Hajiya Hindu nake so a yanke mata hukuncin kisa in da kunga ba wanda yasan maganar cewa ni ba ƴar daddy da momy ba ne sai Malam ɗin unguwar Dosa in da shima ya kamata ya mutu domin yana shiga rigar malanta yana tafka ɓarna a doran ƙasa, domin shi ya zo ya sameni kan cewa zamu haɗu mu kashe Momy sannan mu ɗora ma Hajiya Hindu daga nan kuma sai mu raba dukiyar su Daddy biyu ni da shi, bai san ni ko kar nake kallon shi ba, tuni nima na siye wanda ya turo akan yayi kisan akan in ya zo kar ya sake ya soki momy a in da ya san zata mutu ni kuma zan bata maganin barci wanda ko an soketa ba zata sha wahala ba domin duk da ba ita ta haifeni ba ina son ta kuma ina mata kallon mahaifiya, bayan na zuba mata maganin barci a cikin lemu ta sha sai ta fara barci tuni naje na siye maigadi da duk sauran ma'aikatan gidan da kuɗi shi kuma wanda Baba Malam ya turo ya shigo gidan bayan na dakatar da duk wani cctv camera na gidan har sai da ya caka ma Momy wuƙar sannan na ɗauki waya na kira Hajiya Hindu nayi tamkar muryan Momy ina faɗin Hajiya ki zo ki ceceni ina ajiye wayar nayi sauri na fice naje na kunna cctv ɗin gidan na koma ɗaki sai da na tabbatar da cewa Hajiya ta shiga kuma plan ɗina ya tafi dai dai sannan na fito."
Aneeesa ta ƙarisa maganar tana zubar da hawaye, "nayi kewar Momy na mai ƙaunata da gaskiya Allah sarki baiwar Allah ta raini ƴa mare asali ko ya rayuwar nata ɗan ya kasance oho, ni yanzu ba damuwata in ga momy ba damuwata a yanke ma Hajiya Hindu hukuncin kisa.!
Tana gama maganar ta ɗauki jakarta da glass ɗin ta tayi hanyar ficewa, da sauri Barrisster Zainab da take laɓe da abun ɗaukan magana a hannun ta tayi sauri ta juya ta ɓuya, har Aneesa da sauran suka fice sannan itama ta fito ta nufi bakin titi ta tari abun hawa sai Asibiti, tana zuwa ta tarar da Hajiya da Barrister Khasheeefat suna hira, har Barrister Khasheeefat tayi sauri ta kooma ta kwanta tamkar barci takeyi sai taga ashe Barrister Zainab ce sai ta miƙe ta jingina tana faɗin, "a'a ƙawata ya ake cikine to akwai wani labari ne,"
Murmushi Barrister Zainab tayi ta zauna kusa da Hajiya ta fara gaisheta sannan ta dubi Barrister Khasheeefat ta ce, "ai ƙawata komai ya zo last domin duk wani bayani da muke buƙata daga gurin yarinyar gaba ɗaya yau ta warware mun, kin san wani abun ƙarin mamaki kuwa wai ashe ƙanin Mijin Hajiya Hindu wanda suke Uba ɗaya duk shi ya shirya wannan kitimurmuran, bari dai ku ji komai, kunna musu recording ɗin tayi suna ji sai da suka gama ji tass gaba ɗaya suka numfasa Hajiya Madina ta ce lallai wannan family akwai rikici da yawa a cikin ta, kenan yanzu ita Aneesa ta san ba ƴar gidan ba ce shiyasa take son ta yagi rabon ta kafin wasa ya tashi, to ni damuwata ma gaba ɗaya ina ita Hajiya Saudat ɗin, su wa suka haƙota tabbass itama Aneeaasan akwai wanda yake munafurtan ta a gefe."
"Tabbass Hajiya nima ina tunanin haka bayan ni da nake bibiyan ta akwai wasu daban kuma, amma da sannu zamu binciko komai insha Allah ni zan wuce gida ƙawata Allah ƙara lpy."
"To ɗiyar Albarka, Allah ya albarkace ku ya kareku a duk in da kuke ki gaidamun da Umman ta ki."
"Ameeen ya Allah Hajiya, zataji Insha Allah."
*************************
Hajiya Saudat ne ke sauraran duk bayanin da Aneeesa ta keyi a cikin Audio ɗin da aka kunna mata take sauraro, gaba ɗaya hankalin ta ya tashi, to in har Aneeeasa ba ƴar ta ba ce ina ɗan ta yake kenan Momy Hindu ta san komai, aiko ba zata taɓa yafe ma Hajiya Hindu ba, tasa ta raini ƴan da ta zama bala'i a cikin al'umma har take iya tunanin a haɗa kai da ita a kashe wani, ita in da Aneeesan ta faɗa mata ko nawa take buƙata zata mallaka mata, taji bala'in mamaki akan cewa wai har da Baba Malam wanda kaf dangin mijin ta ba wanda yafi nuna mata ƙauna irin shi, kai tabbass sai yau tasan ɗan adam ba abun yarda ba ne, miƙama Hamida wayar tayi ta koma ta yi zaman ƴan bori nan da nan taji zazzaɓi ya lulluɓeta.
*************************
UNGUWAN DOSA
Sosai Baba malam ke cikin tashin hankali tun bayan kallon labaran da yayi shekaran jiya ko barci ba ya iya yi, matar shi tayi mai tanbayar duniya ya ce ba komai, in da gefe guda kuma aka tura mai maganar Aneeeaa ta whatsaaap nan ma ya ƙara kiɗimeeawa.
*************************
NIGERIA KADUNA
Malam ne zaune a ɗakin shi na sirri da wani fai-fai da ke ɗauke da wani ƙasa mai matuƙar laushi yana ta wasu zane-zane a cikin ƙasan da ya zana sai ya goge da ya zana sai ya goge duk ya haɗa uban zufa duk da AC da ke kaɗawa a cikin ɗakin na shi, can ya miƙe a zabure yayi fatali da fai-fan ƙasa haɗi da furzar da wani huci mai zafi yana faɗin, "ina hakan ba zai taɓa yuwuwa ba, ba zan bar hakan ya faru ba kai kai.!
Ya ƙarisa maganar cikin tsananin ɗimuwa da tashin hankali, "in dai ina numfashi zuri'ar Usman ba zata taɓa dawowa ta tafi kenan, taya ma wai za'a ce duk tsawon Shekarun nan Usman na raye amma ƙasa bata taɓa nuna mun haka ba tabbas ƙasa kin ci Amanata kuma kin karya alƙawari,! da sauri ya ƙara duƙawa ya fara tattara ƙasan tamkar wadda ya tuna wani abu.
*************************
"Ina so ki sani Hajiya Saudat ban ɗauko ki nan don in cutar da ke ba sai dai don in tseratar da ke kan sharrin ƴar ki da ƙanin sirikin ki sannan kuma don in ɗauki fansa akan Hajiya Hindu, har abada ba zan taɓa iya cutar da ke ba domin ke ɗin kin kasance mace ce adala mai tausayi da jin ƙai, cikin haka nima kin taɓa taimaka mun game da Mahaifiyata duk da ita ɗin bata cancanci taimakon ki ba, domin mahaifiyata tana ɗaya daga cikin wanda suka cutar da ke a rayuwa, ita ɗin Aminiyar Hajiya Hindu ce ƙut da ƙut domin duk wani makirci tare suke ƙullashi abun na mun matuƙar ciwo inna ga mahaifiyata suna aikata wani abun duk wani biye biyen malamai da bokaye tare sukeyi da Mahaifiyata, sai watarana kwatsam sunje gurin wani boka da Mahaifiyata ya ce buƙatan su ba zata taɓa biyaba sai yayi anfani da ɗaya daga cikin su, Hajiya Hindu ta ce ma Mahaifiya ta taje yayi anfani da ita kasancewar ita ta fita yarinta kuma tayi mata alƙawarin zata bata kuɗi masu yawa, kasancewar mahaifiyata ta kasance mayyan kuɗi akan kuɗi zata iya aikata komai, gashi dama mahaifin mu ya rasu ita take fafutukar ɗawainiya da mu kasancewar dangin mahaifin mu sun watsar da mu, haka mahaifiyata taje suka aikata masha'a da wannan boka wanda shine sanadiyar tarwatsewar rayuwar mahaifiyar mu da mu baki ɗaya, bayan wasu watanni Hajiya Hindu taƙi ba mahaifiyar mu kuɗin da tayi alkawari ta fara mata yawo da hankali, kwatsam mahaifiyar mu ta fara wani ciwo mai matuƙar firgitarwa wasu manya manyan kuraje ne suka fito mata a cikin farjin ta da sun fashe sai wari mai tsanani haka mukaje Asibiti sukayi iya yin su suka rubuta mana magunguna muka dawo gida ta fara sha sai gaba ɗaya ƙurajen suka mutu, a lokacin da ta fara ciwon kwata kwata Hajiya Hindu ta daina zuwa gidan mu tun da ta zo sau ɗaya taga halin da mahaifiyata take ciki ta bani dubu ashirin bata ƙara zuwa ba ko mahaifiyata ta kirata bata ɗauka wataran ma sai ta kashe wayar sosai abun ya ba mama na mamaki bayan taji sauki ta shirya taje gidan ku sai Hajiya Hindu tayi mata korar rashin mutunci ta ce ma masu gadi karsu ƙara barin ta ta shigo ko ta zo, muna cikin wannan hali ciwon mahaifiyata ya ƙara dawowa fiye da na baya don wannan karan gaba ɗaya jikin ta ne, haka muka koma Asibiti, haka muka dunga zarya har gaba ɗaya kuɗin da mahaifiyata take da shi suka ƙare asibiti suka koremu kwatsam sai gaki shine ki ka taimaka mana kika biya kuɗin aka cigaba da kula da mahaifiyata bayan wasu watanni ciwo sai gaba yakeyi ba wani sauki har ƴan kuɗin da kika biya suka ƙare, hakan yasa doctor ɗin cewa su sun gaji zai sallamemu na dunga roƙon shi amma yaƙi saurarata daga baya yace mun in har zan bashi kaina za'a cigaba da kula da mahaifiyata kyauta har taji sauki, saboda shi rayuwan yanzu taimakekeniya akeyi in taimake shi in kashe mai ƙishin shi shima ya taimakeni ya kula da mahaifiyata, hakanan ban da zaɓi na amince tun daga ranan dr Sameer ya maidani tamkar matar shi ko dare ko rana ya buƙace ni haka zai kirani in je tun ina kuka har na zo abun ma ya daina damuna, sai ya kasance ma ko bai nemeni ba ni zan nemeshi, daga nan idona ya ƙara buɗewa sai na fara bin wasu mazan irin alhazawan nan saboda ɓarin kuɗi da suke mun, sai in kwana biyu ban leƙa naga ya jikin mahaifiyata ba, in ko na leƙa a daddafe ina yi ina liƙe hanci, haka mahaifiyar tawa zata bini da kallo tana girgiza kai tana hawaye ni ko ko a jikina a gabanta dr Sameer zai rungumeni ya mun kiss kuma ko damuna hakan baiyi, sai da mahaifiyata tayi shekara ɗaya da rabi tana jinya sannan ta mutu, daga lokacin ni kuwa duniya ta zama mun sabo, rikici muka fara da dr Sameer da naji cewar zaiyi aure bayan ya mun alƙawarin aure, aiko ƙiri ƙiri ya ce ba zai auri raguwar maza ba, maganar tai matuƙar ƙona mun rai alhalin shi ya fara lalatamun rayuwata.!
Hamida ta ƙarisa maganar tana mai sakin kuka, da sauri Hajiya Saudat ta taso ta rungumeta a jikinta tana ta, bata hanata kukan ba sai da tayi mai isar ta sannan tayi shiru, ta cigaba da magana, "shiyasa naƙi barin ki ki fita domin a yanke ma hajiya Hindu hukuncin da zata tozarta a idon duniya na cewa ta kashe sirikarta, amma don Allah ki gafarceni."
Ta ƙarisa maganar tana kallon Hajiya saudat.
"To amma taya akayi har kika san shirin Aneesa, sannan taya akayi kukaje kuka haƙoni.?
"Nasan shirin Aneesa ce ta hanyar ƙawarta wacce ta yarda da ita wato Marry, ita ta sanar da ni komai bayan na bata maƙudan kuɗaɗe, sannan wani yarona da ke mun aiki tare da shi akaje maƙabarta kai ki bayan kowa ya watse shi bai tafi ba yayin da dama mun riga mun sanar da maigadin maƙabartan komai shima mun bashi wasu kuɗaɗe shiya taya yarona suka haƙo ki aka ɓoyeki a maƙaɓartan aka fara baki taimakon gaggawa saboda a lokacin kin zubar da jini sosai, sai da dare yayi muka bar da ke maƙabartan saboda idon mutane."
.************************
"Amma ban taɓa sanin cewa ke butulu ba ce sai yanzu! har ni zaki ci amana Aneesa kin san dai na fiki wayau da komai zan iya zame kai na a cikin lamarin nan sannan in rufta da ke ciki kinga kinyi biyu biyu kenan kuma duniya zata san cewa ke ba jinin mu ba ce.!
"Hhhhh to sai me! na ce sai me to malam yakubu.
NIGERIA KADUNA
Zaune suke baki d'ayan su sun mi'ka hankalinsu da natsuwar su suna sauraran Hajiya game da maganar da take musu, "Khasheefat dole zaki tafi Dubai kiyi mana kwakkwarar bincike game da wadan nan familyn da muka gama kallo, domin jikina ya na bani akwai kwakkwaran ala'ka a tsakanin su da iyalan gidan Mailafiya, domin wancan tsohon da aka daukeshi tabbass hoton shi ne a falon gidan Alhaji Mailafiya."
Nisawa gaba d'ayan su su sukayi, sannan Barrister Zainab ta Fara magana tana fad'in, "yanzu momy kina ganin Harbeebarty zata iya zuwa Dubai ita kad'ai ga shi bata dad'e da warkewa ba,? me zai sa ba zamu tafi tare ba.?
"Zainab ba zaku tafi tare ba, domin kema akwai aikin da zaki mun domin Ina bukatar in san meye dalilin da yasa wancan yarinyar Hamida taje ta sa aka hako Hajiya Saudat, da kuma Ina ta 'boyeta domin shine abun da yafi muhimmanci a yanzu, bayyanar Hajiya Saudat shi zai warware duk wani kulle-kulle na su Aneeesat da shi kanshi Malam yakubun."
"To yanzu Momy yaushe ne Zan tafi Dubai d'in,? bayan kin San yau saura kwana bakwai a koma kotu, sannan kina ganin momy a cikin kwanaki bakwai d'in nan zan iya kammala binciken da naje yi har mu samu abun da muke so.?
"Sosaima kuwa y'ar momy ban San ki da karaya ba, kisa a ran ki zaki iya."
"Shikenan Momy Allah ya taimakemu, zan tafi dare nayi insha Allah gobe da safe zan shigo da wuri sai a shirya komai yadda ya dace, 'kawata Allah ya 'kara lafiya mu had'u a chat anjima akwai labari."
Zainab ta 'karisa maganar tana kashe ma Barrister Khasheeefat ido, harara ta ballara mata, ta fice tana dariya girgiza kai Momy tayi tana ma yaran nata dariya, had'i da mikewa ta shige ciki.
*************************
Kaiwa da kawowa Aneesa take ta yi a dakin, hankalinta a matuk'ar tashe, juyawa tayi ta kalli Marry ta ce mata, "Marry Ina matukar jin tsoron Malam na unguwar Dosa domin shi din ba k'aramin hatsabibi bane ga iya munafunci ko wata macen albarka, gashi har yanzu mun kasa samo in da Momy take."
"To yanzu Aneesa ya kike so ayi, dole fa sai mun gano in da momyn ki ta ke."
Nisawa gaba dayansu sukayi.
*************************
DUBAI.
MAJEED FAMILY.
Bayan kwana biyu da faruwar lamarin, komai ya lafa, kowa ya dawo hayyacin shi, sannan Papi ya tara kowa da kowa domin aji ta bakin kowa, gaba dayansu suna zaune a babban falon gidan kowa yayi shiru da abun da yake sakawa a ran shi, Papi ne yayi karfin hali ya ce, "Sheick ya kamata ka bude mana wannan taron da Addu'a kafin mu fara abun da ya taramu."
Bude bakin sheick Sudaes ke da wuya zai fara magana sai akayi sallama a kofar falon gaba daya suka juya don ganin mai yin sallaman.✍️✍️
NIGERIA KADUNA
Zaune ya ke a cikin wani daki mai cike da tarkace irin na su na masu buga kasa, k'asace a gaban shi ya na ta wani zane-zane a ciki yana gogewa duk ya hada uban zufa, can ya mike ya fara kaiwa da dawowa a cikin daki, yana surutai.
Malam na unguwar dosa kenan yau kimanin kwanan shi uku a kulle a daki ya na bincike game da iyalan Majeed family da ke Dubai, amma ya kasa gano komai saboda kasa ta ki ba shi hadin kai.
*************************
"Hello Hamida kina ji na ko,? Aneeesa ta bude wuta akan binciken lallai sai ta gano in da Hajiya ta ke, kuma ta fara zargina, saboda haka dole a canja salon tafiyar, in da hali ma ki dauke Hajiya daga wannan gidan ki canja mata waje."
"Good Merry aikin ki na kyau karki damu Aneesa ba zata taba gano in da muke ba."
" OK to shikenan ba matsala sai kin ji ni."
Juyawan da Marry zatayi sai jin bindiga tayi a kan ta, a firgice ta dago ido tana kallon Aneesa da ta dora mata bindiga a kan ta, sannan fuskar ta tamkar bata taba dariya ba.
"Kinyi babban kuskure Merry da kike tunanin zaki ci Amanar Aneesa ki zauna lafiya, tabbass sai kin san kin ci Amanata."
"Please Aneesa ki tsaya ki saurareni wlh ban ci Amanarki ba, ni kawai..!
"Keep quiet ki rufemun baki ko in fasa miki kai da bindigan nan.!
*************************
Tafe take cikin wani katafaren mall tana dauke da abun zuba kaya, hannun ta ta kai zata dauki wani turare dai-dai lokacin da Barrister Zainab ta kai hannu ita ma zata dauka hannun su ya hadu da na juna, juyowa Hameeda tayi suka hada ido da Barrister Zainab a tare suka sakin ma juna wani tattausar murmushi, Barrister Zainab ta ce ma Hameeda, "Woww ke ma kina son turaren nan kenan.?
"Sosai ma kuwa ni shi ne turarena, akwai shi da kamshi mai dadi."
"Sosai ma kuwa."
Jerawa sukayi suka cigaba da hira tamkar wanda dama sun san juna, har suka kammala siyayyar suka jero suka fito tare, bayan sun fito ne sukayi exchanging number kowa ta shige motor ta.
*************************
YAU SAURA KWANA BIYU A SHIGA KOTU.
"Momy na samu dai na samu number kuma ta zo gidan mu jiya nima nayi alkawarin yau zanje gidan ta."
"Ok ba damuwa y'ata haka nake son ku Allah ya muku albarka."
"Ameeen Momy, yauwa Momy kin samu kawata Kuwa,? don ni na Kira ta bai zuwa."
"Eh ta kirani da zu kuma ta fadamun kamar da alamun nasara a tafiyar tata."
"To Alhamdulillahi Momy Allah ya dawo mana da ita lafiya."
"Ameeen ya Allah."
*************************
Kwanci ta shi ba wuya a gurin Allah domin yau ne ta kama za'ayi zaman kotu wanda ake sa ran shine zama na karshe da za'a yanke ma kowa hukunci ya girbi abun da ya shuka, ga shi har yau Khasheefat ba ta dawo ba kuma number ta bai shiga.
Kotu ta cika makil da jama'a da yan jaridu an zauna kowa ya natsu a fara gabatar da karan kenan sai ga wata ta shigo kotun kaman an jefota fuskar ta jina-jina da jini tana zuwa tsakiyar kotu ta fadi kafin alkali yayi magana da sauran yan kotun sai ga Barrister Khasheefat ta shigo da wasu mutane.
Kash na gaji amma Inna ji ruwan comment zaku ji ni, da dai nayi tunanin Anya ba Zan maida littafin nan na kudi ba kuwa sbda wasu dalilai domin akwai saura labari da yawa da yuwuwan in mai da shi 1&2 two din ya zama na kudi amma kuma in har naga kun nunamin one love gurin sanbado comment nima Zan nuna muku one love gurin barin shi free.
*************************
KOTU
Hajiya Hindu ce ta zaro ido tana nuna bayan Barrister Kasheefat jikin ta na rawa ta ke fad'in, "Alhaji Usman dama kana raye,,,,? Maganar tata makalewa tayi sakamakon shigowar Barrister Zainab da Hajiya Saudat da Alhaji Mubasshir Mai lafiya, luuuu Hajiya Hindu ta tafi ta sume, yayin da kotu ta hargitse da hayaniya sakamakon bayyanar Alhaji Mubasshir Mai lafiya da Matar shi Hajiya Saudat Mai lafiya, kasancewar shi sanannen mutum ne mai taimakon Al'umma, kuma shekara biyu da suka wuce kowa ya san cewa Alhaji Mubasshir ya rasu, haka Hajiya Saudat ma an san ta rasu, watannin baya wadda ya kasance yanzu akan mutuwar ta ta ce ake tafka wannan rudadden shari'a mai cike da rud'ani, gaba d'aya Aneeesa ta shiga rud'ani sakamakon ganin mahaifin nata da Mahaifiyarta a raye, to in har Daddy bai mutu ba kenan su Daniel sun ci amananta kenan, to tsawon shekarun nan Ina suka b'oye Daddy, bata gama rudewa ba sai da taga ana k'ok'arin d'aukar mutanen da suka sussume zuwa Asibiti don basu taimakon gaggawa, Marry ce ta d'ingiso ta zo kusa da Aneesa ta ce mata, "Madam Aneeesa ya kika ga kalan namu makircin, tabbass kin yi babban kuskuren Amincewa da mu, kin san meye,? Ni da Daniel jami'an bincike ne na farin kaya, ke baki ji mamaki ba a ce kamar mu muna da girman mu muna secondry school,? To ki sani Mahaifin ki shi ya wakilta mu domin mu shiga rqyuwar ki karki lalacewa sai dai kash lokacin da muka fara bibiyanki muka tararr kin riga kin lalacen domin a lokacin ba abun da bakya sha, hhhh Madam Aneeesa kin yi kuskure Babba fa amma lokaci yayi da zaki girbe abun da kika shuka, Officer Arrest her.!
"Yes ma."
Luuuu Aneeesa ta yi zata sume Marry ta tsinka mata wasu lafiyayyun Mari guda biyu wanda yasa ta farfadowar dole, sa mata ankwa akayi aka tasa keyarta, waigowa ta yi tana nuna Merry da hannunta tana fad'in, " ni kuka cuta ko tabbass zan fito zaku gane kuranku dukkanku sai naga bayan ku.!
Ta fad'a cikin karaji, tana wani irin ihu da ya jawo hankalin mutanen da ke cikin kotu, gaba d'aya kallo ya dawo kan ta, haka dai aka tafi da ita tana zage-zage tamkar mahaukaciya.
*************************
*KAUYEN DAN DAURA*
"Wayyo Allah zan fad'a! zan fad'a!.
"Ke Asabe wai lafiyanki kuwa,? Ki ta shi daga barcin Asarar nan da kikeyi kullum ga shi duk in kin kwanta kin dunga ihu kenan kina zaki fad'a."
Wacce aka kira da Asabe ce ta ta shi daga kan wani yagwal-gwal d'in katifa tana murza ido duk ta had'a zufa kashirb'an, kallon tsohuwar da take tsaye a kanta ta yi fuskar ta cike da damuwa ta fara magana, "Inna ina cikin matsananciyar damuwa akan wani abu da na aikata shekara goma Sha takwas baya, Wanda ya zama dole in koma Kaduna domin bud'e abun da ke burne ko na samu salama, hak'ik'a na cuci kawata Tasalla kuma na ci amanar wata mata." tana kaiwa nan a zancen ta sai ta fashe da kuka.
*************************
KADUNA GARIN GWAMNA.
Gaba d'aya kotu fa ta rud'e hakan yasa dole aka dakata da shari'ar da ake sa ran yau za'a kammalata sai ga shi ta k'ara zuwa da wani rud'anin da dole sai an k'ara tsaida shari'an, haka dai Kotu ta watse kowa na fad'in albarkacin bakin shi, yayin da y'an jaridu na gidajen radio, Tv, da na yanar gizo suka Samu abun yad'awa, tuni labari ya watsu a cikin jahar Kaduna da wasu garuruwa da suke makwabtaka da ita na cewar Ashe Hajiya Saudat da Alhaji Mubasshir Mailafiya suna raye basu mutu ba.
*************************
BARAU DIKKO TEACHING HOSPITAL KADUNA
Kasancewar wannan Asibiti yana d'aya daga cikin manyan Asibitoci na gwamnati da ke cikin garin na Kaduna, can kotu ta bada umarnin a kai su Hajiya Hindu da sauran wadanda suka samu matsala na yanke ciki suka fad'i yayin zaman kotun, tuni likitoci suka rufu a kan su don basu taimakon gaggawa.
*************************
UNGUWAR DOSA
"Hajiya Laraba akwai babban matsala,domin da idona naga Usmanu, da Mubasshiru, ke har ma da Hasseenat da Maimunatu,!
"Mun shiga uku! Yakubu har da fa su Maimunatu ka ce, tabbass lokacin tonuwar Asirin mu yayi domin dai kasan Maimunatu ta San duk wani kulle-kulle da mukayi game da kashe iyayen su ita da Haseenat."
"Ni duk ba wannan ba ne ya fi damuna sai dawowar Usman da Mubasshir domin kin san kusan rabin dukiyar su yana hannuna saboda yadda na kwantar da kai na sa matar shi ta yadda da ni, sai da ya zama saura kiris in mallake duka dukiyar Sannan komai zai rushemun, wayyo Allah na kaico na, wannan shine karon farko da na so abu ban samu ba a rayuwata."
"Wai kai Yakubu bakaji me nake cewa ba ne kai ta dukiya ma kake yi,? Maimunatu fa tasan komai."
"Ba abun da zata tuna ni na sani."
*************************
UNGUWAR RIMI.
"Momy kin san wani abu na sha wuya kafin in shawo kan Hameeda fa."
"Ni Abun da ke Ban mamaki wai a Ina kika san Alhaji Mubasshir yana raye.?
"Ka barni in shiga don Allah ranka ya dade ina son ganin Hajiya Saudat ne, akwai abun da zan fadamata."
Tana k'arisa maganar idon ta cike da hawaye, dai dai lokacin da Kaka Mubasshir suka dawo daga Unguwar dosa zasu shiga gida kaka ta hango su suna takaddaman hana wata mata shiga, da sauri ta ce driver ya tsaya, bayan ya tsaya ne kaka ta sauko ta k'ariso gurin ta na zuwa gurin ta zaro ido jikin ta na rawa tana nuna Asabe ta ce, "Asabe ke ce!"
Ita ko wacce aka kira da Asabe bin Kaka tayi da kallo saboda bata ganeta ba, "Asabe wai baki ganeni ba, Maimunatu ce fa ta gidan Alhaji Lawal k'anin Malam Yakubu na unguwar dosa,"
"Alhamdulillah Aunty Maimunatu Ina yaron da na baki, wlh shine sanadin dawowa na garin nan, nayi nadama nayi da na sanin abubuwan da na aikata a rayuwata shiyasa na zo don in bayyana gaskiyan lamarin, amma Ina yarinyar Hajiya Saudat din nan,?
Ba ta k'arisa maganar ba Kaka ta ce, "mu shiga daga ciki Asabe wannan maganar ba ta waje ba ce."
*************************
Bayan sati daya komai ya lafa an sallamo Hajiya Hindu sai dai ta kamu da ciwon barin jiki, wacce yanzu gaba daya Hajiya Saudat da Mubasshir suke kulawa da ita kullum cikin kuka ta ke tana rukon su yafiya, tun ba ma in ta kalli Mubasshir ba sak dabi'un shi irin na mahaifin shi ne, haka in ta juya ta kalli Haseenat da jikokin ta mussamman ma Ayrah da yanzu wani shakuwa ce mai tsanani tsakanin ta da Mubasshir wanda komai tare suke da shi, in da gefe guda kuwa Habibullah bai k'aunar ko ganin Hajiya Saudat, haka dai kowa ya cigaba da zama don jiran tsammanin ranar da za'a koma kotu, in da gefe guda iyayen Maza suke ta cuku-cuku yadda kotu zata sallami Shari'a tun da dai abun ya zama matsala ce ta family, amma kwamitin kotu da lauyoyin gwamnati sun ce ba su yarda ba, haka dai suka hakura akan za'a koma kotu nan da uku ga watan October.
*************************
"Ina so ki sani Laraba banga wanda ya isa ya kama ni ba tare da wani kwakkwaran shaida ba, sannan Ina so ki sani kowa ya ci tuwo da Yakubu miya ya sha."
"Malam Yakubu Ina ga ka samu tabin hankali ko, to bari ka ji jiya da naje gidan Mailafiya ba wanda babu shi a cikin zuri'an shi, sannan ina so ka sani jiya har Asabe na gani wannan mai aikin na gidan Yaya Lawal."
Mik'ewa Malam na unguwar Dosa yayi a zabure ya ce, "wata Asaben kike nufi wacce nayi yunkurin kashewa? Innalillahi wa'innah ilaihir raji'un."
Zufa ne ya fara karyo ma Malam na Unguwar dosa yayi zaman yan bori jikin shi ba in da bai rawa.
*************************
"Marry kunyi kokari sosai gurin ganin an kammala aikin nan, saboda haka Ina bukatar ku tattara gaba daya bayanan saboda uku ga wata zamu koma kotu."
"Ok sir."
Cewar Marry bayan ta sara ma shugaban na su, ta juya ta fice daga office din na shi."
*************************
"Aslamu Alaikum, Sunana Barrister Mansur ko zan iya zama.?
Dagowa Barrister Zainab da Khashefat sukayi a tare suna kallon mai maganar, sosai Barrister Khashefat ta had'a rai, Barrister Zainab ce ta ce mai ya zauna, bayan ya zauna ne ya fara magana, "Ina so ku fad'I ko nawa kuke so za'a baku matukar ba ku gabatar da duk wani shaida a gaban kotu ba."
"Barrister get out of my office.!
Cewar Barrister Kasheefat da ta mik'e a fusace.
"Ok ni kike wa tsawa, fine zaki san kin mun tsawa akan kudi ba abun da ba zanyi ba.!
Ficewa ya yi daga office din ya na karada hannu.
Kallon ta Barrister Zainab ta yi ta ce, "baki jin tsoron mai zai yi, kin san mutanen nan ba imani garesu ba."
"Karki damu kawata da Allah muka dogara."
*************************
KOTU
Yau ta kama uku ga watan October, in da kaf familyn Mai lafiya sun hallara a kotu, in da gefe guda kuma an kamo Malam yakubu da Hajiya Laraba, bisa shaidan takardun tuhuma daga kotu, kowa ka kalla a kotun zakaga ba annuri a fuskan shi, bayan shigowar Alkali da lauyoyi da wasu daga cikin ma'aikatn kotu, kowa ya natsu.
"A yau ne kotu zata cigaba da sauraran shari'a Aneesa da take karar kakan ta bisa kashe mata mahaifiya, in da kuma Shari'a tayi kokarin juyewa zuwa wata shari'an da ban, saboda haka yanzu kotu tana bukatar ganin lauyoyin wanda suke kara da wacce ake kara."
"Ya mai girma mai shari'a sunana Barrister Khasheefat Ahmad lauyar wacce ake kara, tare da ni akwai Barrister Madina Abdulwahab da Zainab Abubakar."
Ta k'arisa maganar tana sunkuyawa alaman girmamawa.
"Sunana Barrister Mansur Tanko tare da ni akwai Barrister Ungozi ekechi da Barrister Lado Zubairu nagode."
Shima ya fad'i haka yana duk'awa.
Bayan alkali ya danyi rubuce rubucen shi sannan ya dago ya na fad'in kotu ta na buk'atar lauyoyi su fara gabatar da hujjojin su a gaban kotu."
"Ya Mai girma mai shari'a Ina son kotu ta bani dama in fara gabatar da shaiduna ga wannan kotu mai albarka."
"Barrister Khasheefat kotu ta baki dama."
"Nagode ya mai girma mai Shari'a, a ranar ashirin ga watan maris ne aka kama Hajiya Hindu da zargin kisan Surikarta Hajiya Saudat, in da a yanzu nake so in wanke Hajiya Hindu daga zargin da ake mata saboda kwararan hujjojin da nake da shi, a ranar talata Ana saura kwana biyu Hajiya Saudat zata mutu, Aneesa ta ziyarci Malam Yakubu a unguwar dosa bayan dawowar ta makaranta ita da kawayenta Marry da Daniel, bayan sun isa ne suka fara maganar yadda za'a kashe Hajiya Saudat a dora ma Hajiya Hindu laifin kisan, bayan sun gama shirya komai sai ta kamo hanya zuwa gida."
"Barrister Kasheefat shin kina da kwakkwaran sahidar da zai bayyanawa kotu cewar Aneesa da Malam Yakubu su suka shirya wannan kisan.?
"Eh ya mai girma mai shari'a tabbass Ina da shi."
Fito da wani madaidaicin recorder tayi ta kunna sai ga muryan Malam Yakubu yana fad'in, "ki saurareni da kyau ki ji ni Aneesa karki bari a samu kuskure domin zan tura killer daren jumma'a ki tabbatar kin kauda duk wani abu na zargi, sannan ki bata maganin barcin da zai sa har a shiga a aikata lahira ba wanda ya sani."
"Ni fa Uncle Yakubu bana so a kashe momy gaskiya, amma ban k'aunar ganin Hajiya Hindu."
"To ki sani dole Hajiya Saudat ta mutu in har kina son ganin bayan Hajiya Hindu, sannan kina son ki samu kaso mafi tsoka a cikin dukiyar mahaifinki dole ki kauda su duka domin kin san komai dadewa in har suna raye sai an san cewa ke ba yar su ba ce kinga kin ta shi a tutar babu, bakiga bayar makiyiyarki ba sannan kin rasa gata da kudi sai ki koma rayuwar talauci."
Nisawa tayi ta ce, "tabbass ba zan iya rayuwar talauci ba dole kam duk su mutu."
Dariya sukayi baki d'ayansu, nan dai suka tsaya akan cewa in an gama da su zasu raba dukiyar biyu kowa ya dauki kashi d'aya.
Bayan tafiyar Aneesa Malam yakubu ya tuntsire da dariya yana fad'in, "yaro man kaza.!
Bayan Alkali ya gama sauraran duk tattaunawar Aneesa da Malam yakubu sai Barrister Khasheefat ta cigaba da magana kamar haka, "bayan an samu labarin mutuwar Hajiya Saudat sannan an dora alhakin kisan ga Hajiya Hindu bisa kamata dumu-dumu da akayi a dakin da akayi kisar dauke da wuka a hannun ta, hakan ya assasa zargin da ake mata, bayan da na fara gabatar da bincike game da kisar sai na fara zargin Aneesa, bisa bibiyanta da nayi da ganinta da nayi zasuje makabarta cikin dare na bibiyesu naga sunje don su hako gawar Hajiya Saudat, sai akayi rashin sa'an basu tarar da gawar a gurin ba, haka dai suka juyo ni kuma tun daga nan sai na gane akwai lauje cikin nad'i hakan yasa na tura k'awata Barrister Zainab ta bibiyeta har ta samu shiga gurin Aneesa, a kwanan nan ne kuma muka gano cewa Hajiya Saudat na raye a boye a gidan Hameedat bayan k'awata tayi iya k'ok'arinta gurin shiga jikin Hameeda bayan da mukaji bayanin sirri daga gurin k'awar Aneesa Merry cewa Hajiya Saudat na boye a guest house din Hameeda saboda tayi haka ne itama don daukar fansa akan Hajiya Hindu, da kyar Barrister Zainab ta shawo kan Hameeda har ta amince ta bamu Hajiya Saudat domin zuwa kotu don tabbatar ma da duniya cewa Hajiya Hindu bata kashe Hajiya Saudat ba."
Bayan duk wadan nan bayanan da shaidun da Barrister Kasheefat ta gabatar sai Alkali ya danyi rubuce-rubucen shi sannan ya dago ya ce, "in Hajiya Saudat na kusa kotu tana buk'atar ganinta."
Tasowa Hajiya Saudat tayi, in da gaba d'aya kotu ta d'auki hayaniya, gefe guda kuma Malam yakubu da Anesa sun jike da zufa jikin su ba in da baya rawa, bayan Alkali ya tsawatar kowa ya natsu ya dubi Hajiya Saudat ya ce mata, "Hajiya ko zaki iya ma kotu bayanin abun da ya faru."
"Eh ya mai girma mai shari'a."
Nan dai Hajiya Saudat ta labarta ma kotu duk abun da ta sani.
Bayan Alkali ya gama sauraranta ya sallameta ta koma mazaunin ta, sai Barrister Khasheefat ta nemi da a kara bata izini ta gabatar da wata shaidan ta na gaba kotu ta ce ta bata dama, gaba d'aya su Barrister Mansur sun zama tamkar yan kallo sun kasa tabuka komai, ko motsi kwakkwara basayi.
"Ya mai shari'a in da kotu zata tabbatar da cewa tsintacciyar mage bata mage shine in har ta ji cewa Aneesa ita tasa likitan Alhaji ya ba Alhaji guba sannan in an kirashi ya tabbatar da Cewar zuciyar Alhaji ce ta buga yasa ya mutu, bayan ta fahimci cewa basu ne iyayenta ba, tare da alkawarin zata bashi makudan kudad'e, shi kuma likita yaga ba zai iya cin amanar Alhaji ba hakan ta sa suka had'a baki da Alhaji aka chanja Alhaji da wani gawa da ban shi kuma Alhaji aka fitar da shi k'asan zuwa k'asar India, yace yayi hakan ne don ya nesanta da bak'in cikin mahaifiyar shi, duk da yana tausaya ma matar shi irin halin da zata shiga."
Haka dai aka kira likita ya zo ya bada na shi shaidar, sannan Alhaji Mubasshir in da in ban da kuka ba abun da Hajiya Hindu takeyi.
Bayan duk gama sauraran shaidu da kotu ta yi Alkali na shirin yanke hukunci Asabe ta mik'e tana fad'in, "ya mai shari'a ai shari'a bata k'are ba."
*************************
"Ya mai girma mai shari'a tabbass Shari'a bata k'are ba nasan mutane da yawa a cikin kotun nan zasu ce meyasa na fad'i haka, tabbass Ina da dalilina na fad'in haka domin Alhaji Yakubu shi ya kashe K'anin Mahaifinsu wato Alhaji Lawal tare da sa hannun y'ar uwar shi Hajiya Laraba, dalilina kuwa na cewa haka shine akwai watarana Hajiya Hauwa uwar d'akina ta aikeni in karbo mata sako gidan Alhaji Yakubu bayan na shiga haraban gidan har na gota in da ake parking motoci sai naji ana magana sama-sama sai na labe kasancewata mace mai son jin gulma, sai naji muryan Alhaji Yakubu da Hajiya Laraba suna fad'ama wani mutumi cewa ka tabbatar ka cire burkin motan da zasuyi tafiyan da shi, bayan na gama sauraran su ne na lallaba na shige gidan zuciyata cike da tunanin suwa Alhaji Yakubu suke so su kashe a iya tunanina na kasa fahimta, bayan kwana uku da jin wannan zance sai Alhaji ya shirya shi da mai dakin shi zasuyi tafiya zuwa Maiduguri sai da ba zasu tafi da Hasseenat da Maimunatu ba saboda Dukan su suna da exam a makaranta, sai suka koma gidan Alhaji Yakubu da zama kafin iyayen su su dawo ashe tafiya ce ba ta dawowa ba, an ce sun tafi ko Abuja basu kai ba motor su tayi had'ari kasancewar kwacewar burkin motan sai gawan su aka dawo da su gida sosai mutuwar ya bigi yaran Alhaji Lawal Haseenat da Maimunatu haka dai rukon su ya dawo Hannun Alhaji Yakubu in da yake nuna musu matukar kulawa ya hana kowa ya rabi yaran, haka dukiyarsu gaba daya yana hannun shi, bayan wasu shekaru masu yawa Ina tare da su Haseenat sai kwatsam Alhaji yakubu ya ce zai Aura ma Alhaji Usman Hasseenat haka ya shiga ya fita akayi auren saboda wani manufa na shi na daban domin sai da yayi duba ya tabbatr da cewa Hajiya Hindu ba zata taba barin Hasseenat ba, bayan Auran da shekaru masu yawa aka nemi Hasseenat aka rasa kowa ya mance da babin ta haka muka dunga rayuwa ni da Maimunatu a wahale a gidan Alhaji Yakubu saukin mu daya mai aikin gidan kawata ce, kuma akwai alakar sirri tsakanin ta da Alhaji Yakubu, akwai watarana na fito daga sashin mu don zuwa cikin gidan karbo mana Abinci na bi ta kofar baya kawai naga Alhaji Yakubu da kawata Tasalla suna aikata Zina wanda hakan yayi matukar gigitani gashi sun ganni tun daga nan Alhaji Yakubu ya samun karan tsana yake fad'amun cewa tabbas na tona musu Asiri sai ya kawar da ni kamar yadda ya kauda Ubangidana hakan ya sa na tsorota Sosai da lamarin shi, bayan wasu watanni da faruwar hakan k'awata ta zo ta sameni da maganar cewa ta na da ciki kuma na Alhaji Yakubu ne ya ce sai ta zubar ko ya kasheta ita kuma ta ce ba zata zubar ba, muna cikin wannan magana ya zo ya samemu ya ce mata wato ba zata zubar ba ko to tabbass da ni da ita duka sai ya kashe mu kamar yadda yaga bayan Alhaji Lawal da Alhaji Usman karaf a kunnin Maimunatu kuma yaga shigowarta hakan ta sa ya kulle mu a d'akin satin mu d'aya ga nakuda ta kama Tasalla da taimakon Allah muka samu hanyar fita daga gidan cikin dare muka kawota Asibiti dai dai an kawo Hajiya Saudat Mai lafiya gashi lokacin bamu da ko sisi da kyar wata nurse ta karbemu da sharadin zamuyi mata abun da take so, bayan tsawon lokaci Tasallah ta haihu tare da Matar Alhaji Mubasshir sai dai Allah ya ma Tasallah Rasuwa ko ganin abun da ta Haifa batayi ba, a gaban Idon mu aka canza shegiya da mai Uba ma'ana aka dauke yar Tasallah aka ba Hajiya Saudat bisa umarnin uwar Mijin ta mu kuma aka bamu d'anta da sunan muje mu birneshi da ran shi, gaba daya jikin mu yayi sanyi domin kuka sosai mukeyi kasancewar Maimunatu ta girmeni sosai a lokacin don da tayi auren wuri irin namu na kauye zata haifi kamata hakan yasa ta ce zata rike yaron nan iya karfinta zata shiga duniya zatayi nesa daga gida domin tsira da rayuwarsu, amma komai dadewa zata dawo d'aukar fansan jinin iyayen ta, haka muka rabu Ina kuka tana kuka a cikin daren kowa ya Kama gabansa ba mu kara haduwa ba sai shekaranjiya."
Jikin Alhaji Yakubu ne ya fara rawa kar ga wani gumi da yake keto mai ya fara nuna Asabe da hannun shi yana fad'in, "kina Nufin kice Aneesa y'ata ce keban....! Luuuuu yayi ya fad'i ya Sume a gurin.
Ruwa aka kwara mai ya farfad'o Alkali ya fara magana kamar haka, "in Maimunatu tana kusa kotu na bukatar ganin ta da kuma ji daga Gare ta."
Tasowa Kaka tayi ta iso gaban kotu ta gabatar da Kanta.
"Maimunatu muna bukatar jin karin Bayani game da Maganar da Asabe tayi shin da gaske ne.?
"Eh ya Mai girma Mai Shari'a da gaske ne, bayan rabuwar mu da Asabe a Asibiti...
*************************
KOTU
"Eh ya mai girma mai shari'a tabbas maganar da Asabe ta fad'a gaskiya ce, bayan mun rabu da Asabe a cikin daren na nufi tashar mota, na hau mota zuwa Lagos, kasancewar akwai dan wasu kud'ad'e da ke hannuna bayan tashin motar mu haka na zura ma jaririn da ko wanka ba ai mai ba gashi Allah ya saka mai hakuri ya na ta barci abun shi ba mu muka isa lagos ba sai gurin karfe shidan yamma, tun bayan saukan mu na rasa Ina zan dosa, can dai na yanke ma kaina shawaran in nemi in da zan siya abinci in ci da ruwa in yi ma yaron wanka nima in yi sannan in rama salolin da ake bina,washe gari haka na nutsa cikin gari neman aikin da zanyi na sha wahala a ranar gashi kud'in hannuna sun kare ga shi yaron na ta kuka na rasa yadda zanyi haka na samu guri na zauna nima Ina kuka wata mota ce ta parker a kusa da mu aka zuge glass din baya wata hamshakiyar mata na gani, ta yafitoni na ta shi cikin hanzari na isa kusa da motan ta ce mun meya sa nake kuka, na ce mata yarona ne yake jin yunwa ga shi bani da kud'in siyan madara, haka matar nan ta taimake mu ta kaimu gidan ta ba abun da bata mana ba ni da Yarona bayan sati daya sai ta ce mun ta na so zatayi tafiya Dubai amma tare zamuje in dunga mata wasu aikace aikace na ce mata ba komai na Amince, bayan zuwan mu Dubai ne na gane cewa ashe wannan Hajiyar mace ce mai zaman kanta kuma safarar y'an mata takeyi dalilin jinta da nayi tana waya tana fad'in Alhaji gaskiya ka karamun farashi domin wannan fa yarinyar mai zafi ce kuma danyar goyo gareta, tuni na fahimci ciniki na akeyi saboda da turanci take maganar kuma ni na nuna mata banjin turanci a daren ranar na gudu daga gidan na ci bak'ar wahala a k'asar da ba tawa ba, har kamani akayi nayi zaman gidan yari ba irin wahalar da ban sha ba, har ta kawo na fara aikatau a gidajen masu da shi a haka na saka Mubasshir a makaranta islamiya da boko."
Ta k'arisa maganar tana mai fashewa da kuka, sosai jikin kowa a kotun yayi sanyi wasu masu saurin kuka kuwa kuka sukeyi sosai saboda tausayin halin da Maimunatu ta shiga saboda Dan da bata haifa, bayan alkali ya gama tattara bayanai gaba d'aya sannan ya fara magana kamar haka, "a yau ne wannan kotu mai adalci zata yankewa duk wanda suke da Hannu a cikin wannan badakala, kotu ta yanke ma Alhaji Yakubu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kwararan shaidu da aka gabatar a gaban kotu, in da kuma aka yanke ma Aneesa Mubasshir zaman gidan yari na shekaru goma sha biyar da horo mai tsanani bisa yunkurin kisan kai da tayi har sau biyu, sannan an yanke ma Hajiya Hindu zaman gidan na wata takwas bisa cutar da jikan ta da kishiyar ta, sannan Hajiya Laraba itama an yanke mata hukuncin zaman gidan Kaso na shekara daya bisa hada baki da ita gurin yin kisan kai, sannan kotu tayi umarni ga Alhaji Yakubu ya tattaro duk abun da yasan na su Maimunatu ne ya basu hakkin su, wannan shine hukuncin da kotu ta yanke, sanan Alkali yana jinjina ga Barrister Khasheefat tare da Barrister Zainab gurin namijin Kokari da sukayi gurin ganin sun fito da masu laifi."
"Ya mai girma mai shari'a muna rokon wannan motu Mai adalci da a bamu belin Hajiya Hindu duba da halin rashin lafiya da take ciki, sannan ni a matsayina na jikan ta na yafe mata duniya da lahira, kamar yadda Mommah Haseenat ita ma ta yafe mata, nagode ya Mai Shari'a."
"Bisa duba da wa'inda akai ma laifin sun ce sun yafe, kotu ta sassauta ma Hajiya Hindu a madadin zaman gidan yari zata ba da taran kud'I naira Miliyan biyar."
Bayan Alkali ya kammala jawabin shi ne ya buga guduma kowa ya mike, aka tasa keyar masu laifi, nan aka turo keken marasa lafiya dauke da Hajiya Hindu wanda kunyar Duniya ta kare mata.
BAYAN WATA UKU
Gaba d'aya ahalin ne suke zaune a kayataccen falo in da kowa ka kalla yana cikin farin ciki, in da tuni Alhaji Usman ya maida Haseenat d'akin ta ya kuma saki Hajiya Hindu in da ita da kanta ta nemi ya sawwake mata.
Alhaji Usman ne ya kalli Haseenat ya ce mata, "Sweetheart yaushe ne zamu tafi honeymoon din mu ne.?
Gaba daya jikokin dariya suka yi suna tsokanar su, "tab waya ga su Mommah ana Honeymoon." Cewar Anwar suka kara kwashewa da dariya.
"Karbi naka Anwaru ku ta shi ku bamu guru,"
Cewar Daddyn Nigeria dariya duka akayi Didi ya ce, "a'a rabu mun da abokai, kunji ku ta shi muje a buga ball nifa yanzu jina nake kamar dan sha tara."
Gaba daya kara wani dariyan akayi, hira suka cigaba da yi cike da soyayya da kaunar juna.
BAYAN WASU SHEKARU
Komai ya dai daita ciki har da Auren Kaka Maimunatu in da ta Auri abokin Daddy a Dubai shi kuma Daddyn Dubai yanzu ya zama bashi Nigeria bashi Dubai, don kasuwancin shi sai kara habaka yakeyi.
ALHAMDULILLAH
A nanne na kawo karshen labarin nan abun da na rubuta bisa kuskure Allah ya yafemun, Abinda nayi dai dai kuma Allah ya bamu ladanshi Allah ka rabamu da hali irin na su Aneesa, ka, ka rabamu da fadin mugayen kalami ga yan uwan mu wanda hakan shi ya jawo ma Hajiya Hindu masifa har ake ganin ita ta kashe surukarta don an ce baki shi kan yanka wuya tabbas na ta bakin ya yanka ta, Allah ka karemu da son Abun duniya irin na Alhaji yakubu ga shi yayi biyu babu.
0 comments:
Post a Comment