Baba Malam na zama Saman Daya Daga Cikin kujerun Falon lokaci Daya yana gyara zaman alkyyaban Jikinsa Cikin Nazarin Baba Sa"idu Daya Duka gabansa kamar me neman gafara yace"Sa"idu da wata mtsala ce..!
Baba Sa"idu ya Dago yana kallon Baba Mallam kafin ya maida kansa kasa yana Fadin"Eh Malam...Kun yi mgana da D'an Malam cikin kwanakin nan kuwa..?
Baba Malam na Cire gilashin Dake Idanuwansa yace"Eh mun yi mgana Dashi yace suna tafe cikin Satinan..Sai dai bamu yi wata mgana ba..Ammh in ban Manta ba har alokacin yace min Baba Malam Baba Sa'idu bai ce maka komai ba..?Tun da naji haka nasan Yan"uwan juna sun yi abun da suka saba..Nasan da wani abu Saboda haka ina jinka wani Laifi ya aikata yau kuma ya Labe abayanka..!
Ya fada yana Kayattacen Mirmishi Baba Sa"idu na sosa kansa shima yana Dariya Baba Malam yana da Saurin gano Mutun yasan indai aka Fara wannan Zagayen Zagayen wani abu ne ya Faru asan Sa"idu Dabam ne a wajensa Dashi yaran suke kamun kafa in suka aikata wani abun ko kuma suna son suyi wani abun da suna Tsoron yima Mallam mgana Kai Tsaye.
Baba Mallam ya kara Muskutawa yana Fadin"Uhm ina jinka...Meya faru ko ya fasa zuwa Bikin kennan nasa ne..?
Da Sauri Baba Sa"idu yace"A"a yana nan tafe..yau ma yace ma Jirgin kayansu ya taso zuwa gobe zai kariso nan..!
Baba Malam ya gyada kai yana kallon Baba Sa"idu wanda kansa ke kasa Kafin yace"Dama..Dama yace na Fada maka ne..Abukattab ya basa auran yarsa Sarood shi kuma bazai iya masa Musu ba ya karba..!
Baba Mallam bai Sauya Fuska illah Cewa da yayi"Ina ce ba an Daura auran Jiya ba..,?
Da mamaki Baba Sa"idu ke kallonsa kafin ya jinjina kai bai basa Zarafin mgana yace"Abokina bai Rufeni ba kamar yadda kuka Rufeni..Bai Fadamai bane ammh bai Daura masa aure Yarsa ba sai da Izinina..!
Baba Sa"idu ya washe baki yana Fadin"Allah kara girma Baba..!
Dariya yayi kafin yace"In kunyi waya ka Fadamai nasan komai..Kuma har munyi mgana da Kattab da ita zai zo Gida Taga Dangi..Wannan Abu ne mai kyau kuma Sunnar ma"aiki ne Sallalahu alaihi wasallam,Sannan kuma Kattab ya wuce wannan a wajena ballatana Wajen Umar..Ina Farincikin Shigowar Zuru"arsa Cikin Zuru"ata Allah ya Zaunar dasu Lafiya..!
Baba Sa"idu nata amsawa da Ameen Baba Mallam ya cigaba da Fadin"Ya mganar Katin gayyata Sa"idu ina Fatan ka Tura inda ya Dace..?
Baba Sa"idu yace"Insha Allahu Mallam..Jafar da Nasir suna ta aiki sosai su sukace na basu bangaran Baba mallam..Sannan Mutanen bazanga fa ko Mutum zamu tada zuwa chan..?
Baba Mallam yace"Ba Bukata..Zan kira mai gari Ashiru na Sanar dashi..Ina so kasa agyara bangaran Baki na gidan gona Ba lalle bane gidajenmu na nan ya wadata in bai isa sai ku rage wasu zuwa chan..!
Baba Sa"idu yace"Insha Allahi zan yi ma su Mamuda mgana zasu gyara komai...Sannan Husai tayo waya fa..Tace tana nan zuwa sannan tace zata Kiraka kan tana Rokon alfarma abar Jadwa tazogida Don Allah..!
Baba Malan na Mirmishi yace"Husai Diyata..Ta Kirani Dazu da yammah..Munyi mgana nace Tazo ammh naso sai ta kara shekara Uku bata zo gida ba..Hajiya tasa baki nace tazo Tunda suma Sauran yan"uwan nata suna ta kama kafa wajen Iyayensu mata suna son zuwa Bikin nan. !
Baba sa"idu yace"Ai yana da kyau Mallam..zumunci sai ya kara karfi Tunda in ba irin wannan ba sai adade ba"a ga juna ba..!
Baba Mallam yace"Ai bana son Bidia ni ba Taron mata zan yi ba..Ana Daura auree kamar yadda aka Saba Kowacce Mijinta zai Dauketa ba Shikenan ba..!
Baba Sa"idu na Dariya yace"Adai yi hakuri Baba Malam..!
Shima Dariyan yayi kafin yace"Naganeku..Kai da Hajiya bakin ku Daya..asan duk abunda kuka Saka baki bana iya Ture wannan mganar ko..!Shikenan Allah ya nuna mana Allah yasa kowa yazo Lafiya ya koma Lafiya..!
Baba Sa"idu ya amsa da Ameen kafin su Cigaba da Tattaunawa sai wajen 9 na Dare yayi mai sallama ya tafi Gida sannnan sai alokacin Anty Nasara ita ke da Mallam a wannan Daran kuma ita keda Alhakin Shigo da Abinci anan Falon taci Kwalliya tana tashin Kamshin Tana jifan Malam da Sanyayyar Mirmishinta yana Girmama Nasara saboda Kaifin Tunaninta da kuma Sanyinta.
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo(Besty) Alherin Allah yakai miki aduk inda kike*
*🅿️07*
A kimanin Lissafi Saura Sati Hudu Bikin su Ya Zulaihat,Ta kowani bangare ana Cigaba da Shirye Shirye daga Duka gidajen guda Biyu duk da ba wani Sha"ani ake yi sosai ba Baba Malam ya hana anayin gayya dai makota da abokan arziki su zo su tayasu Murna,Walima kadai Baba Malam ya yarda ayi ana yima Amaran ne ana Gobe Daurin aure Ranar Daurin aure kuma ayi Taron mata na Cikin Gida da Safe zuwa yammah Sannan a Dokarsa Daga manya har yara Bamai Raka Amare Dakinsu Haka Tsarinsa yake ko su Ya Jadwa ba wacce aka Raka da an Daura aure zai Damkaki Hannun Mijinki bayan yayi muku Nasiha,ku tafi kin Riga kin zama nasu Jere ne dai ake zuwa ayi kafin Biki aga inda zaki Zauna kuma ko bayan Biki irin kannen Amarya suje wajenta Baya cikin Tsarin Gidan nan da kin tafi shikenan sai kuma Waya zuwa ma sai da Dalili mai karfi.
Gidan Baba Malam ba"a kai Amarya bai yarda ba baya cikin Tsarinsa ba"a Taba ba kuma baza"a Fara ba kuma Daga Washegari Taro zai tashi Baki Duk zasu koma Gidansu komai nashi Cikin Taka Tsantsan ne baya yarda yayi abunda zai kaucema Tsarin Addini da Sallah.
******
*Monday..*
10:20am
Gidan Baba Sa"idu..!
Mamanmu Dake kofar Kitchen Tana Gyaran Zogale Awani Faranti mai kyau tana Zaune kan karamar Kujera yar Tsugunno,Yaya kuma na Daga Kofar Dakinta Tana zaune kan Wata Darduma Data shimfada Farcenta Datake yankewa da abun Yanke Kumba,Hira suke da Mamanmu Sama Sama yayinda Amina ke daga Cikin dakin Mamanmu Saman Daya daga cikin kujerun da sukayi ma falon kwanya tana kwance ne tayi kwanciyar Ruf da ciki tana Sanye da riga da sikat na kanti kanta sanye cikin Hula baka Wayar mamanmu ce a hannunta Kirar Nokia tana game din Maciji Cikin kwarewa Amina ce kadai keda wannan Damar bayan ita Mamanmu bata yarda wani ya taba mata yawa suma banda ita bawanda ma ya damu da wayar tunda ba sabawa da ita sukayi ba.
Hamida ce ta fito Daga Cikin Dakinsu Dauke da wani Sikat na Leshi a Hannunta duk ya yamutse tana nuna ma Mamanmu itama Riga da Sikat din ne ajikinta sai dai nata Ja da Baki ne Cikin Mamaki tace"Mamanmu kalli wannan Sikat din..!na Amina ne fa ko gegesu batayi ba duk sun yamutse..
Mamanmu Dake duke ta Dago tana Fadin"Shine me...?tunda bata gyara ba ki gyara mata mana..?kema kinsan Amina bata da kokarin nan ke tunda kina da Himma sai ki gyara mata amfanin Yan"uwan kenan..!
Hamida ta tura baki Tana Fadin"Allah Mamanmu ki daina cewa haka..Tafa iya Tsabar Wulakanci ne irin na Amina ai naga kayan da zata saka Ranar Bikin su ya Zulaihat.!
Mamanmu tace"Eh ko bama haka ba ta isa ta sakaki ai tana gaba Dake..Oya kije ki gyara mata kayan Dirowanta in kuma sun kawo wuta ki goge mata ki adana mata kinji ko Hamida..?
Ta Karishe da Sigar Lallashi Baki tadan Tura kafin tayi mgana Mamanmu ta Katseta da Fadin"Ban sanki da gaddama ba Hamida..Mganar kaya kuma Hajiya Babba tayi muku kayan Fitar Biki Ranar dana shiga na gansu Tace Shamsu zai kai Dinki..!
Jin haka Hamida ta washe baki Tana Murna Amina nadaga Ciki ta Daga Murya tana Dariya Hamida ta Daga Labulen ta Leka Amina na ganinta tayi mata gwalo Lokaci Daya tana Fadin"Kinci Darajan Mamanmu ne yarinya..!
Amina na Dariya tace"Yarinya na bayan Uwarta..Mganin masu sa ido kenan ina Ruwanki da kayana..!Ni inaga naga Lokacin gyara wasu kaya..!
Hamida tace"Kiji Tsoron Allah..Tun yaushe muke gida..?tun gama Jssce din mu bama zuwa makarantar Boko Sai dai Hadda Karshen Sati..!
Amina tayi Tsaki kafin tace"Kinga bana son Hayaniya..ki kyaleni kawai..!
Hamida ta saki Labulen bata kara mgana ba Amina fa yar Ganin damace ko kayanta bata gyarawa sai ta ga Dama Kuma fa suna gida Tun sati Biyu da gama Jssce dinsu su ya Zulahait ne ke zuwa tunda basu gama Neco ba kwafa tayi ta koma Dakinsu ta cigaba da gyaran Dirowarta dana Amina da Mamanmu tace sai ta gyara mata.
Yaya na zaune har suka gama mganarsu bata Daga kai ba Daman Tana da kawaici bata cika mgana kan wasu abubuwan ba Musammab kan ya"yanta Tana yi ma mamanmu kara gwarama kan su Ya Zeena zakaji muryanta ammh baida kan Amina ba sai Ta cikata sannan take mganinta.
Sai da ta gama yanke Farcen nata ta kankare Lokacin Mamanmu ta gama gyaran Zogalen ta shiga kitchen ta Jikata da Ruwa,ta fito kenan Yaya ta kalleta Tana Fadin"Ni ko Mamansu kinsan D'an Malam ko zai dawo Cikin Satin nan..?
Mamanmu ta Tsaya rike da Kugu kafin Tace"Eh naji su Babansu na mganar sannan naji bakin Hajiya dana Shiga wajenta Ranar..,!
Yaya na Fadada Mirmishinta Tace"Yau da asuba ya Kirani mun gaisa ya Fadamin gobe jirgin Asuba zasu taso...Daga Jidda zuwa gata suna gida..!
Mamanmu ta washe baki Tana Fadin"Masha Allah Allah ya kawo su Lafiya naji jiya Babansu na Fadin kayan su har ya iso tun jiya Shi Kadai zai zo ko Harda ita Sakinar..?
Yaya tace"Yace min Har da ita Sakina sannan yace min zai zo da Bakuwa ma..!
Mamanmu ta tsaya rike da Haba tana Fadin"Bakuwa kuma yaya..!
Yaya bata samu Zarafin mgana ba Hanne tayi sallama Lokaci Daya tana Bayyana atsakar gidan.
Mamanmu da Yaya suka juya kanta Cikin Kulawa sai da ta karisa kan Darduman Yaya ta zauna tana Fadin"Mamanmu yaya sannanku da gida..!
Mamanmu tace"Maraba da Hannatu..Hannatun Aminata..!
Take Fada tana Dariya Hanne ma Dariyan take kanta na kasa ta shiga gaishesu suka amsa mata Yaya ta kalleta Cikin Dogon Hijabinta tana Fadin"Hannatu ya wajen su Hajiya..!
Hanne tace"Kowa lafiya..Tace a gaishemku..!
Suka amsa mata kafin ta mike tana Fadin"Mamanmu su Amina fa..?Daman Hajiya ne tace nazo na Kirasu zamu je chan gidan Ya Dan mallam ne mu yi musu yan gyare gyare kafin su iso..!
Mamanmu tace"Amina na cikin Dakina..Hamida na Dakinsu tama gyara kaya..Amina..Hamida..! Baku ji Zuwan Hanne bane..?
Ta fada tadan Daga Murya Hamida ce ta Fara fitowa tana Fadin"Naji zuwanta Mamanmu ina so na karisane Dirowar Amina kamar Dirowar mara rai mamanmu kaya duk sun Yamutse Wlh Amina kin bani da kazanta..!
Hanne tace"Amina jidalinta bazai barta ma tayi abu mai kyau ba Kina ina ne..?
Amina na jinsu sai da taga Dama ta Fito tana Wani Kallonsu Daya bayan Daya Kafin tace"ina jinku...kawai bana son mgana ne..Ya akayi ne..?
Tafada tana Dafa bangon Dakin Mamanmu.
Hanne tace"ai kinji..Hajiya tace nazo na gayamuku ku shirya muje gidan Ya Dan Malam mu yi musu yan gyare gyare kafin su iso..!
Da Sauri Hamida tace"Kai don Allah..?Bari na gama Yanzu na shirya mu tafi Daman nayi wanka..Amina ce batayi ba..!
Amina ta juya Idanuwanta kafin Tace"Ai ba zuwa ma Zan yi ba..Bar Fadin ma ban yi wanka ba..!
Ba su kadai ba Hatta Yaya sai da ta Dago Tana kallonta Mamanmu bata a wajen tana Kitchen bata jisu ba.
Hanne Tace"Saboda mene...?Hajiya ce fa tace nazo na gaya muku..!
Amina ta mele baki tace"Daman bansan Kakam banki bane hanne Hajiyar ai batace Dole sai munje ba..Ke ni fa nagaji ba wani aikin da zan yi ina kannen Matarsa..?su je mana..!
Hanne tace"Wai su Sa"adatu..?to tare zamu tafi da ita fa..!
Amina tace"Ai kaji..Shiyasa ma bazani ba kinsam na Tsani Hada waje da yarinyar nan.balle tana ganin gidan Yayarsu akaje sai ta nemi Budan Hanci ni kuma kinsan Halin Jidalina Kamar Zawo nake bani da Hakuri..!
Hanne tace"ba abunda zai faru..ai ta Daima Shiga shirginki Tun Sanda Baba mallam ya mata mgana..!
Hamida ta Kada kai kafin tace"Kyaleta Hanne in bazataje ba ni zani..Daman in jin Labarin Haduwar gidan nan banta zuwa ba..!
Hanne tace"Nima ban taba zuwa ba..Kinsan Wanchan Dawowar nasu su ya Abida aka tura shima Dakyar..Yau din ma Baba Sa"idu Hajiya tasa ya Kira Baba Malam ya tambayeshi Da yace baxamu je ba sai dai su Ya Shamsu suje su gyara!
Kinsan Baba Mallam baya son muna Fita ko fa gidansu ya Jafar sau daya muka taba zuwa Inajin Hamida..!
Hamida tace"Wlh kuwa shima Lokacin da Anty Shamsiya ke wannan Laulayin ne muka bi su Hajiya Dakyar Shima Daga Cikin gida sai mota Daga Fitowa sai Mota ko dan gari bamu gani ba..!
Sai Lokacin Yaya ta saka baki Ta mike tana Nannade Dardumanta tana Fadi "Sai abarku kuna mata kuma Yawo agari..?ai ina godema Baba Mallam Har gobe ina jinjina ma Hikimarsa..!
Hamida kiyi ki shirya ku tafi..Ku kyale wacce tace bazata je ba..Rashin zuwanta bazai saka afasa komai ba..!
Tafada Ko kallon Barayin Aminan batayi ba Amina da tasan da ita akeyi ta Tura baki kafin tace"Ai bance ba zani ba..Yasin sai naje nima naga abunda za"ayi Ehe..!
Tafada lokaci Daya tana Juya ido Yaya dai bata ko bi ta kanta ba ta Shige Dakinta Idanuwanta sun kawo kwallah ai akwai wanda Hallayar Amina ke sukan zuciyarta Bayan itace ko Sa"idu bai kaita jin wannan Dacin ba itafa uwace wacce tasan Ciwon abunda ta Haifa Sannan Ita ta kadai tasan aibun mgana da Kullum ake yi akan Amina ita Kadai tasan Ciwon Haifar Zakka cikin Tarin ya"yanka sai dai tana amfani da Nasihar Baba Malam da kullum yake Fada mata Ta rika ma Amina Addu"an Shiriya kada ta sake ta bari ranta ya baci akanta Ballatana watarana ta aibatata Duka basa gyara Tarbiya Sai ma kara Fandarewa Addu"a da Nasiha sune Jagora.
Hawayenta ta Share kafin ta Daga Hannu Sama tana Fadin"Allah ga baiwarka nan Amina kai ka Halliceta kuma Kaddaranka ne kayi ta yadda take..ya Allah ka shiryar da ita..Ka Natsar da ita..ya Allah kada ta zame mana Zakka watarana..Allah ka Bata wani bawanka da zai shigo Rayuwarta da Alheri ya SauyataWatarana..!
Tafada Lokaci daya tana kallon Sama alokacin Bata sani ba Kaddaran Amina Rubutattace ne sannan addu"arta an dade da amsarta bata sani ba.
Amina bata bi ta kan Hamida da Hanne dake mata Dariya ba Har suna Tafawa tayi kwafa batayi mgana ba ganin ta isa Gaban Famfo tana wanke Kafa yasa Hanne tace"Amina wai nufinki bazaki wanka ba..?
Cikin Masifa Amina ta Juyo tana Fadin"Eh din bazan yi ba jikin ki ko nawa..Ban son munafunci Hanne ki Kyaleni..!
Hanne tace"Daga mgana..?Tsiya na Dake bakisan gaskiya..!
Hamida ta leko Daga Cikin Dakimsu tana Fadin"Kice dai batasan abun arziki ba..!
Amina Ta Hura hanci kafin tace"Ba"asani ba din..Hamida da Hanne bana som munafunci kowa yayi harkarsa Fakat..!
Basu kara ma tanka ta ba,Hanne Dakinsy ta shige suna mgana da Hamida tana Fadamata Malam yau baya nan yaje Jigawa Saukar Al"qur'ani da wata Makaranta ta gayyaceshi sai ga Amina ta shigo Tana Hura Hanci jira take amata mgana ta Fara jidalisai ta ga Tataga sun yi banzada ita suna Cigaba da Hirarsu.
Tsab Hamida ta Shirya ta saka Hijabinta da Safa Amina ce ta Tsaya sai bata Musu Lokaci take Hanne tace"Amina don Allah kiyi sauri..Dakyar fa Baba ya barmu..Kuma kinsan in muka Dade hukuncinmu..!
Amina ta cika Bakinta da iska kafin tace"kunga nifa bana son ana Damuna..In kunga bazaku iya jira ba Kuyi gaba ban ce Dole wata Cikin ku ta Jirani ba Atoh..!
Tafada Lokaci Daya tana Bude Dirowarta ta kaya Baki ta Washe ganin Hamida ta gyara mata Cikin Shakiyanci tace"Hamidas..Kai mijinki Wlh ya More da gyara baki da kiwuya..wlh irinku ne masu yima Kishiya wanki da guga harda Uwar miji..!
Ta karishe Fada tana Tsintsira Dariya Hamida tayi tsaki kafin tace"Kina da mtsala Amina..!
Amina tace"Nafi gidan Haya..Tsohowar Mota ma nan taganni ta barni don kwal ubanta..!
Amina ce fa sai ta gama bata musu Lokaci kuma amata mgana tace an Dameta in baza"a jirata ba ayi gaba..
Saida ta gajida mgana kana ta shirya sai da taga Hanne ta kusa kuka sannan ta Sauya kaya zuwa Doguwar riga tama mata kadan Gwiwan kafarta a waje ta kuma Sanya Hijabi ko kasa bai kaimata ba.
Hamida ta kalleta Kafin tace"Amina kalli kaurinki a waje..Ki saka Safa mana..!
Amina tace"Wlh bazan saka ba..Ke haka Kurum ana Fama da Zafin nan..Nifa bana son Zuhudu bazan kashe kaina ba. ke dai bakin saka ba. to miye na Damuwa sai na saka..?
Hamida tace"Kafarki fa awaje..Kinsan fa bai kamata ba..!
Amina ta Tsaya Lokaci Daya tana Fadi "Kafata a waje take..A"a kice Tsirara nayi ba kafata a waje ba..Hamida kin fara isata acikin gidan nan in ban kwabe ba nace na fasa zuwa kuce ba sunana Amina ba..!
Da Sauri Hanne tace"Yi hakuri..Don Muje.Wlh in muka bata Lokaci Hajiya zatace mu barshi su Ya shamsu suje.!
Tsaki Amina Taja tayi gaba tana Fadin"Dilla yo Laifina ne..?baga wacce ta wani Dameni da mganar banza ba nan..Ni wlh na tsani iyayi hamida kuma Halinta kenan Shigen Neman suna da son Nuna tafi kowa son Allah..!
Hamida ta kalli Hanne zatayi mgana ta Rufe mata baki tana Fadin"Don Allah ki kyaleta..Kinsan Halin Jidalin Amina bataki a fasa tafiyar na ba ta Zauna tana sauke mana Rashin Mutumta..!
Dole Hamida tayi shuru suka Fice Kitchen suka fara shiga suka ma Mamanmu Sallama Amina ta Bude Tukwinyar girkin tana Fadin"La Mamanmu Zogale kike Dafawa..!
Tana Dariya tace"Zulaihat na Rage ma aiki..Dambun Zogale zatayi inta Dawo Saboda Aba dinku..!
Amina tace"Wayyo Mamanmu..A ijiyemin mai yawa don Allah..!
Hanne ta Harareta tana Fadin"Ke kadai.?kina da son kai mu fa ba mutane bane ko..,?
Amina ta juya ido tana Rumgume Mamanmu ta baya tana Fadin"Saboda ni kadai ce Diyar Mamanmu ko Mamanmu..?
Mamanmu na Dariya tace"Kwarai kuma baki da na biyu a wajena..Kuje zan Dibar muku da yawa saboda Diyata..!
Fita sukayi Amina nayi musu gwalo Dakin Yaya suka shiga suka mata sallama Amina kin shiga tayi Daga waje ta tsaya suka fito Kafin su Rankaya zuwa gidansu Hanne din Shashen Hajiya suka shiga sai Fada take musu rana tayi.
Hanne tace"hajiya Amina fa ta bata mana Lokaci..!
Hajiya tace"ku kuka sani..In Malam dai ya Dawo bazaku je ba..Tun Dazu Na kira Idi na jiranku zai kai ku kuma zai Tsaya ya Dauko ku..Kuna da yawa..Kagaki ga Mamah ga Hamida da Sa"a kuyi hanzari share share ne da goge kunji ko..?bana son Malam ya Dawo baku dawo ba Dagani har ku ranmu sai ya baci..!
Hanne tace"To Ina key din gidam Hajiya..!
Hajiya tace"Na duba na wajena ban gani ba..Kuje shashen Amarya ku amsa wajenta tana dashi..!
Amina saita koma ta Zauna tana Fadin"in kun amso ku gayamin..!
Hajiya tace"In baki je ba..Tafi Haraba wajen Mota Idi na nan na jiranku..!
Ba Musu ta mike suka fice Tare su suka Wuce Shashen Anty Amarya ita kuma ta koma Haraban gidan Inda Idi ke Cikin mota kirar Siana yana Jiransu.
Tafi minti goma da Fitowa sai gasu sun Fito Sa"adatu ce abaya tana wani Bude Hanci Hannunta Leda ne babba komiye aciki oho..?Sai key din gidan tana wani Kadawa Amina Kallo Daya ta mata ta Kauda kai itama Shiga Motar sukayi bayan sun gaisar Idi kamar yadda Tarbiyansu take..
Kai Tsaye daganan bai Diresu ko"ina ba Sai Kofar Arewa,inda gidan Ya Dan Mallam yake.
Tundaga Wajen gidan suka saki baki suna kallon Wannan Tsaruwa kamar a Turai akwai megadin Dake Tsaran Gidan wani Buzu ne,bai ko jin Hausa sosai,Idi megadi yayi Hon ya Bude musu suka Sulala Ciki tun da suka Fito sukayi ta kallon gidan ba wani Babba bane sai dai ya Tsaru matuka Gashi gabadaya Haraban gidan yana Shimdide da Marbels mai Santsi Kalan Ruwan kasa mai Duhun Get din Gidan Fari ne Fentin gidan kuma Ciki da wajensa Mai ruwan pich ne mai kyau da kyalli.
Sa"adatu ce agaba ita adole masu gida Amina ta tabe baki ita Sakarcin Hanne ta gani ita wazai je gidan Ya Jafar yamata wannan Ikon bata ci uban Mutum ba.
Sai da suka Shiga Falon suka san Waje basu ga komai ba Duk da gidan ya Dade a Rufe ammh kuma babu abunda ya Sauya wani Sanyin Dadi ne ya Daki Hancinsu sai da Amina ta Lumshe Manyan Idanuwamta tana kare ma Falon kallo.
Komai Baki da Fari ne duk yadda akayi Mai gidan yana son Kalan sosai.
Sannan Duka kujerun da Dining an Rufesu da Fararan kyallle,Sai Cafet duk an Nadesu waje Daya Komai dai yana Muhallinsa ammh an Killacesa Daman gidan bayan wani Lokaci su Ya Shamsi na zuwa suna gyarawa sannan Sai Karshen Shekara yake zuwa da ita iyalin nasa,ammh yakan zo a shekara su Uku zuwa Hudu kuma agidansa yake sauka.
Falo ne Babba sai Bedroom guda uku sai Kitchen guda Biyu Sa"adatu ita ta Bude bedroom din guda Biyu Bata Bude Dayan ba ta Dago tana kallon Su Hanne Lokaci Daya tana Fadin"Bari na Bude muku kitchen ku fara da Chan kafin mu zo Falo..Ni zan gyara Bedrooms din Anty Sakina..!
Bawai neman Shawaransu take ba Umarni ne take basu Hanne ko ajikinta ta taka ta mika hannu Tana Fadin"Bani key din na Bude Kitchen din..ki gyara chan din Saboda aikin yayi mana Sauri.Ko kuma Hamida ta shiga Dayam ta gyara ni da Amina mu gyaro Kitchen din ko ya kika gani..?
Da Sauri Sa"adatu tace"A"a ku gyara chan gabadaya in kun gama ga Falo.ni zan gyara Duka bedrooms din ai guda Biyu ne Dayan na Yaya D'an Malam ne kuma Key na wajen su ya Jafar..!
Hanne bata kara mgana ba ta karbi key din ta Bude kitchen din ta Juya tana cema su Amina"Bismillah..!
Hamida tabi bayanta Amina kuwa sai da ta gama Tabe baki kana ta Bisu Ciki Sa"adatu kuma ta shige Ciki abunta.
Amina baki ta saki da Hanci tana kallon Tsaruwa da Haduwar Kitchen din Shima Fari ne da baki gabadaya Cabinet din kitchen din Fari da Baki ne Hatta marbels din Dake Kitchen din ma Fari ne yana kyali Kamar ana Gyarssa ba wani Datti sai ku ran da baza"a rasa ba tunda komai na amfanin Girki suna cikin Kwalayensu ne Fridge ma ba komai aciki sai ruwa da Lemo,Hamida na Duba Kitchen din tace"Gidan ma ba wani Datti..!
Hanne na Kokarin Bude Store tace"Ai Dayake su ya shamsu na zuwa suna gyarawa..Sannan Anty Sakina gaskiya akwai Tsabta kafin su tafi sai ta Hada komai nata ta adana..!
Ba wanda yace wani abu har ta Bude Store din Gabadaya kayan abinci ne Dankam aciki Hamida ta Leka tana Fadin"Hanne kayan abincin su basa Lalacewa ne..?
Hanne tace"Suna Lalacewa mana..kamar fa wannan kwananan aka Zubasu ai kafin su koma suna Kyautar da komai kafin su koma..!
Hamida ta gyada kai tana Fadin"Hum..!
Amina dai na gefe batace komai ba sai Kalle kalle takeyi basu bi ta kanta ba suka Fara goge gpge Da kakkabe kakkabe tunda sun ga tsintsiya da Moper anan Kitchen din da Towel din gogen Kitchen Amina na gefe ko Hannu bata saka ba Domin Taga abun akwai rainin Wayau aciki.
Hamida ne ta juya tana kallonta kafin tace"To ke Amina tunda mun kama nan ko zaki je ji kama Gyaran Falon ne..?
Amina ta tabe baki kafin tace"Ni daman nace muku zan yi wani aiki ne..?ke hanne wai nan ba gidan yayanki bane..?
Hanne bata gane Tambayan ba tace"Bangane ba..?
Amina tace"to gani nayi ta zabi Aiki mai Sauki ku ta hadoki da gyaran Kura..ji yadda take bada Umarni kamar gidansu..In tana takama matar gidan yayartace..Ai kema mai gidan ne Yayanki kin fita iko dashi..!
Hanne tace"Sai me..?ni ina komai ne Saboda Allah da Ya Dan Malam ba Saboda wata Sa"adatu ba..Kema don Allah kidaina mgana in baki yi ba ki koma Falo ki zauna nidai muyi mu gama Lafiya mu tafi gida..!
Hamida tace"Ni ban ma ga abun mgana ba Wlh..!
Amina ta ballara mata Harara tana Fadin"Ai bazaki gani ba..!
Daganan ta yi ficewarta Falo ta koma ta Haye gan Dining ta zauna tana Kada kafa Domin daman chan batayi yi niyyar ko Taba wani abu ba Sa"adatun tazo tayi duka mana.
Tana nan zaune Sa"adatu ta fito Daga Dayan Bedroom din suka kalli juna kafin kowa ya Kauda kansa Dayan ta shiga shima ta gyara kafin nan su Hanne sun gama da kitchen din suka Dawo gabadayansu suna gyaran Falon Sai alokacin Amina ta saka Hannu ta yaye abunda aka Lulluben Dining din ta Goge suma Kujerun sun yaye komai sun goge Dayake Sa"adatu tazo da Klin da Turaran Wuta mai kanshi na Tsinke da na Bunner Dayake akwai Wuta suka jona suka Turara gidan.
Ba inda basu share sun goge shi ba Ko"ina yayi tas yana tashin Kamshi Cikin Awa Biyu suka Idar da komai Sai da sukayi salla suka yi shirin Tafiya Alwarma a Sink din Kitchen sukayi ga yunwa sai dai suka sha Ruwa da Lemo Amina ko Ruwa bata sha ba Sallah kadai ta yarda tayi.
Karfe 2:30pm na rana suka Dawo Daganan Amina da Hamida gida suka wuce basu koma gidan Baba Malam ba.
Koda suka koma su ya Zulahait sun Dawo daga makaranta sun gama Jarabawa Ya Jafar tayi ma waya yaje ya Daukosu Tunda Idi baya nan Daman kuma Dokar Malam ce ya Hana su Hawa adaidaita,Ita da Ya Sadiya da Ya Aisha da ya Ikram da Ya Shamsu sune suke Jarabawar Neco su Ya Zeenatu sai da ya maida su Amina yaje ya Daukosu.
Amina tunda suka Dawo ba wanda yaji wata mgana Daga bakinta Da Daddare bayan sun gama Karatu tana jin Hamida nata bama su ya Zeenatu da su Mamanmu Labarin gidan Suna Zaune abaranda suna shan iska ba Wuta kuma Gen yaki tashi sai mai gyara yazo.
Amina na daga Cikin Dakinsu kwance taji Sanda Hamida ke fadin Tsarin gidan Mamanmu na gefe tana Fadin"Ai bama Sakinar ba shi kanshi Dan Malam din dan gayu ne na karshe..Mun je gidan ai tun sanda aka gama ginashi sannan mun ga Hoton ginin a waya Daya Turo ma Aba dinku..!
Kowa saiTofa albarkacin bakinsa yake yi har Yaya ma tana Saka baki Amina na jinsu aranta tana mamakin yadda Yaya take Ji da Dawowar Dan Malan koda yake taji fa ance Dan Dakinta ne har waya suna yi da ita.
Aba yau ya Dade wajen Baba Malan Amina ta fara barci Sama sama taji Shigowarsa kuma tana ji yana tambayanta yaga kowa bai ganta ba Mamanmu ke fadamai inda mukaje Tunda muka Dawo nake kwance nagaji.
Bai ce komai ba,ya wuce Dakinsa Yaya ke da Aba Aranar ita take ta kai da kawon kai mai abinci da abubuwan Dayake so su kuma su Mamanmu na Tsakar gida suna cigaba da Hirar gidan Ya Danmalam sannan suka koma Hirar Biki da kuma Labarin Sati na sama Baba Malam yace za"a jere kamar yadda aka saba daman ba"a kawo Lefe sai dai kayi shi ka sakashi Cikin Dakin Amarya intazo tagani kayan Fitar Biki Daga na Amaran har na Sauran yan gida Baba Mallam ke yin komai Hajiya babba ita keda jagaba kan Komai Tare da Shalelen baba mallam Baba Sa"idu.
Kuyi hakuri nayi baki ne..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo (Besty) Alherin Allah ya kai miki har inda kike Ameen*
*🅿️08*
Ko daga yanayin yadda ake Murna da Shiryen Shirye zakasan D'anmalam na musamman ne,Amina batasan haka yake da Tasiri har agidansu ba sai Ranar da Daddare gabadaya wuni akayi mganarsa,Tana jin sanda Aba suka shigo da Ya Jafar da Ya Nasir,suna mganar gobe da zafe zasu sauka a Kano tun dazu da Rana suka Taso Daga Filin Sauka da Hawan Jirage na Jidda.
Bata kara jinjina Lamarin ba sai da taji da zasu tafi Ya Jafar na Fadin su Anty Shamsiya zasu zo su wuni Zasu zo kawo su yima Ya D'anmalam barka da Dawowa bazata iya Tuna Rabonsu da gidan ba Mallam baya barinsu suna Barin matansu suna zuwa sai da wani Dalili mai karfi ammh sai gashi yanzu zasu zo Anty Shamsiyan Tsohon ciki gareta Haihuwa ko yau ko Gobe,Anty Fadilan ne keda karamin Ciki Sannan gidansu Daya Tare sukayi Gininsu.
Amina na zaune a wajen anata Hira tayi kamar bata awajen Tsaki take ja acikin Ranta Har ga Allah tana so taga wannan Ya D'anmalam din nan Duk da Tasanshi ammh ayanzu bazata iya Nuna sa ba ko ta Tuna da Kamaninsa ba.
Sanin da tayimai Tana yarinya ne Lokacin Jidalinta ne agabanta da kuma ta fara girma in yazo har ya koma basa Haduwa sai dai tana jin Labarin zuwan nasa,Wannan karon Taji tana son ta gansa wanda har Aba a Fuskarsa yana Nuna Farincikinsa.
Ba gidansu kadai ba Har chan gidan Baba Mallam,Dazu da Rana hanne tazo ta jata sujeta tayasu aikin Sinasir da Waina,Saboda Ya Danmallam yana so Amina tayi kwanciyarta taki zuwa Hanne Tagaji tatafiyarta ko ajikinta Tasan zuwa gobe zasu koma Daidai.
Washegari da Safe Amina ke da Sharan Tsakar gida Hamida kuma Wanke wanke tana fa Sane tana Idar da Sallar asuba ta koma barci ba wanda ya Damu sanin ita ba Karatun asuba take yi ba,Su Ya Zeenatu suna Idar da karatunsu suka fara shirin makaranta Ya Zulaiha ke kitchen tana Hada abun kari,Yau basu da Jarabawa suna gida.
Hamida tana gama karantunta ta fita Waje ta fara Hada kayan wanke wanke zuwa wajen Famfo Mamanmu ta Fito Daga Dakin Aba da Hijabi da Carbi a Hannunta Da Sauri Hamida ta gaisheta ta amsa tana Fadin"Bake keda Shara ba Daman..?
Hamida tace"Amina ce ke da Wanke wanke..Jiya tace nayi wanke wanken Ita zatayi Sharan..!
Mamanmu kai kawai ta kada ta wuce Kitchen wajen Zulaiha.
Ya Zeenatu ta fito Cikin Shirin makaranta tsakar gidan ta kallah tana Fadin"Wake da shara ne..?hala Amina ce..?
Hamida na Duke tace"Eh itace..!
Karamin Tsaki taja tana Fadin"Indai Amina ce..Ba"ajin kowa Ranar aikinsa sai ita..!
Tafada Lokaci daya tana komawa Cikin Dakin Amina tayi Daidai tana barci taji An Daga mata Duka abaya Da Sauri ta Zabura tana Fadin"Kan Uba..Wani dan...!
Ta kasa karisawa ganin ya Zeenatu tsaye tana kallonta Lokaci Daya da Hararanta Baki ta Tura kafin ta wani Juya ido cikin kunkuni tace"To wai don Allah me nayi..?
Ya Zeenatu tace"Bansani ba..Nasha Zaki karisa Ashariyan da kika fara ne..!
Amina tawani Tona baki tana kunkuni Tana Fadin"To haka kurum..Ni..!
Zeenatu ta Make bakin Amina da yasa tayi Shuru cikin Bacin rai tace"Kinsan Allah? Da Safan nan zan Dirji bakin ki bana son Rashin kunya..!
Amina Bakinta ta Dafe tana Dubawa taga Danshi Cikin Zare ido tace"Jar uba..Kan bala balagagge..!
Ya Zeenatu tace"Ko kan uban Balan ne...Malama ki tashi kije kiyi mana Sharan Tsarkan gida waje duk datti kin zo kin kwanta kina barci kuma kinsan aikin ki ne..!
Amina kamar tayi kuka bakinta na mata Zugi tace"To ni nace bazan yi bane..!
Ya Zeenatu da har ta juya ta dawo tana Fadin"Me kika ce..?
Amina tace"Toh..nace..!
Ya Zeenatu ta juya tana Kyafci Lokaci Daya tana Fadin"Da kin maimaita da kin sani..!
Wajen gadonta taje ta Zauna tana kokarin saka Safa,Amina na zaune sai Hararanta Take tana kunkuni Lokaci Daya tana Fadin"Haka kurum..Allah ya isa na..ban yi miki komai ba..Allah ya sakamin Wuta balbal Yasin..!
Ya zeenatu na jinta bata yi mgana ba Sanun Halin Amina ko za"a Mutu bakinta bazai mutu ba.
Amina kin fitowa tayi sai da Ya zeenatu ta kara mata mgana ta Zare mata ido tana Fadin"To wai bana ce toh ba..ba cewa fa nayi bazam yi ba..!
Tana jin haka taje ta Fadama Aba yana Zaune ne yana Duba Tarkadun Lissafin kwan kajin da aka Fita dashi Daga gidan gona ya Dago kai yana kallon Zeenatu kafin yace"Kiramin Aminar..!
Tana daga kwancen Zeenatu ta Dago Labule tana Fadin"Ki tashi kije Aba na kiranki..in kin rainamu shi ai bazaki Rainasa ba..!
Amina ta rike baki afili ta Furta"Munafuki dai bai ji Dadi ba..!
Kara Dago Labule ya Zeenatu tayi tana Kallon Amina da Sauri ta mike tana Neman Hijabinta Lokaci Daya tana yar waka"Kan munafiki dai baya gashi..ko yayi sai ya sauke..!
Ya zeenatu tace"Dani kike Amina..?
Sai data saka Hijabinta Na Hadda kana tace"Nifa badake nake ba..Wakata kawai nake ba"aji na ambaci Suna ba Atoh..!
Tafada tana wucewa tana ta kunkuni Ya Zeenatu ta bita da Harara Domin in ta tsaya Biyema Amina sai ta makara.
Fuu kamar kububuwa ta fito sai Dakin Aba da sallama kamar Mutuniyar arziki ya amsa mata kafin ya bata izinin Shigowa.
Kanta na kasa ta shiga chan gefe ta Zauna Sannan ta dago kanta tana Fadin"Ina kwana Aba..!
Bai kalleta yana Rubutu Bisa Takarda yace"Lafiya..Ya akayi akace an saki aiki kikace bazaki yi ba..?
Amina ta yamutsa Fuska kafin tace"Nifa karya takemin Aba..nace zan yi fa..!
Sai Lokacin ya dago yana kallonta Cikin wani yanayi itama kallonsa take yi Cikin Daure Fuska yace"Zeenatun ke miki karya..?Sa"arki ce..?
Amina ta Tura baki kafin tace"Aba har fa Baki ta fasamin..Wannan ai Zalunci ne..!
Aba ya karkace kai yana Kallonta,Yana kara nazarinta Har yau bata Chanza ba Ganin zata ma batamai Lokaci yasa yace"Tashi kije kiyi aikin da aka saki. daga yau in na nakarajin ana Fada Dake kan aikin da kika san naki ne..sai naci Mutumcinki Sannan Gargadi na Karshe kada na kara jin kin kara kiran wani Dan"uwanki Azzalumi kina jina ko..!
Amina tayi kasake tana kallon Aba aranta tana ayyana yadda ba"a taba goyon bayanta Kullum itace bata da gaskiya ganin tayi shuru yasa yadan daga Murya yana Fadin"Kin ji ko baki ji ba. ?
Amina ta Tura baki kafin tace"Naji Aba..Ammh..!
Hannu ya Daga mata bai kalleta ba yace"Tashi ki bani waje....!
Dole ta mike sanin Halin Aba Tunda yace haka bai Bukatar kara jin mganarta kamar Amina ta Buga ita kadai haka ta fito kamar kububuwa Taje ta Dauki Tsitsiya ko Hijabin Jikinta bata Cire ba ta Fara waka da Karfi tana Fadin"Munafuki dai baya gashi..Ko yayi sai ya Sauke.!
Ba wanda bai jita ba Har Yaya Dake Daki Tana Shirya Jawaad kai kawai ta Kada aranta tana ma Amina Fatan Shiriya.
Ya Zeenatun ma tana jinta tayi mata Banza Mamanmu ce ta fito tana Fadin"Amina ki bar wakar nan..Ko kin manta Aba din ku na gida..?kina so yaji ya fito ya saba miki ne..,?
Amina ta Dago tana Fadin"Mamanmu bana son munafunci ne..Cewa nayi bazan yi sharan ba..?an wani je an Hadani da Aba yamin Fada..!
Mamanmu tace"Yi hakuri yi shararki..Kada ki kara tanka kowa zan ma Zeenatun mgana..!
Saboda Mamanmu yasa ta kama Bakunta ta Cigaba da Sharan,Har tazo wajen da Hamida ke tsunggune tana wanke wanke tayi ta yarfo mata Shara da Datti Hamida ranta ya baci ta Dago Tana kallonta Lokaci daya tana Fadin"Bana son Rashin mutumci Amina baki ganni bane..?ai sai kice na tashi ki share ko..!
Amina ta balla mata Harara kafin tace"Dayake baki da ido ne..Kada Allah yasa ki tashi ta kanki zan bi na wuce..!
Tasan zata aikata kuma abokin Jidali take nema yasa Ta tashi Tsam ta bata waje ta Share ammh duk da haka sai da bata mata wasu kwanukan sai da ta kara Dauraye Amina tana gama Sharan ta koma Daki tayi kwanciyarta tana ta kunkunin mgana Har su ya Zeena suka karya ita da Jawaad suka fita Idi na Jiransu da su Abida..
Hamida data ga Amina bata tashi ta yi Breakfast ba,i ta tayi mata mgana sai ta mata Banza ganin haka yasa ta karisa kusa da ita tana Fadin"Amina ki tashi ki karya..Mutuninki aka Soya Dankali da kwai..!
Amina ta Tsaki tana Fadin"Baza aci ba din..Ina ma Ruwanki dani Cikin ki ko Cikina..?
Hamida ta rike baki tana Fadin"Allah ya baki Hakuri..!
Amina tace"Ameen in da gaske kike..!
Ita dai Hamida ta fice zuwa Dakin Yaya ta bar ma Amina Dakin Mamanmu kuma tana Dakin Aba ta kaimai abun karyawa ya Zulaihat kuma ta shiga wanka adakin Mamanmu.
Amina tun tana kunkuni har barci ya Dauketa bata sani ba Bata Farka ba sai da taji Ihun Hanne asaman kanta Lokaci Daya tana Kiran sunanta"Amina..Amina tsshi..!
Amina ta Bude ido ta ga Hanne Saman kanta bakinta Har kunne Cikin Dariya ta rike Hannunta tana Fadin"Ki tashi Ya Danmallan sun dawo..Yanzu su ya Jafar da ya shamsu suka je Airport zasu Dauko su..!
Amina wani Kololon Takaichi ya zo mata wuya batasan Sadda ta Fizge hannunta ba tana fadin"Shine zaki zo ki tasheni ina barcina..?tsakanina Dake Hanne wlh sai Allah yamana Hisabi..!
Ta karishe Fada tana Sakin Tsaki kafin ta juya tana fadin"Ni ina ruwana da wani Dawowarsa..!
Hanne Jikinta yayi sanyi ta kalli Hamida Dake Tsaye da Sauri Hamidan tace"Kiyi Hakuri Hanne..!
Hanne ta mike batace komai tayi yake kawai kafin tace"Na tafi Hamida..Sai kin shigo..?ai zak zo musu sannu dazuwa ko..?
Hamida tace"Sosai ma zan shigo insha Allahu..!
Daga haka ta fice Amina na jinta tana Fadama su Mamanmu a waje tana jin Sanda Yaya ke fadin"maraba..Maraba..!
Tsaki ta kara ja aranta tace"Kamar wani Gold..?ita zata so taga wannan Mutumin nan..da harda Yaya da bata wani Shiga Sabgan mutane tana ji dashi..!
Bayan tafiyan Hanne Hamida ta kalli Amina Dake ta Zakuda Kafada Daga kwancen tana Fadin"Amina ammh kinsan baki kyauta ba ko..?Hanne fa kika ma haka..!
Amina na Daga kwancen ta Dago kanta kafin tace"To uwata..Hadiza ina jinki..?gayamin abunda nayi wanda ban kyauta ba..!
Tafada Lokaci Daya tana Mikewa Zaune kamar abun arziki.
Hamidatace"Koma me zaki ce..Gaskiya ne sai na Fadamiki baki da wacce tafini Amina..bai kamata kima Hanne haka ba kada ki mamta Hanne yadda take awajenki..Ko ni da muke gida Daya ban kai Hanne Daukan Jidalinki ba Amina Tana ta Murna tazo fadamiki Dan"uwanta ya Dawo kalli yadda kika gwasaleta alhalin batayi Fushi da abunda kika mata Jiya ba yau kuma ta dawo..Wlh ban taba ganin Hanne ta Damu da Halinki ba sau yau..kwallah sai da taru acikin Idonta..!
Amina tayi kasake tana jin Hamida ko ajikinta Ganin haka yasa Hamida ta Cigaba da Fadin"Kuma kada ki manta Ya D'anmallan d'an Hajiya da Baba Mallam ne ko domin yadda suke Kaunarki bazaki musu kara ba..?
Amina ta yamutsa Fuska kafin ta mike tana Fadin"Ke kikasan wannan..Sannan wai da gaske kike Hanne Fushi tayi..!
Hamida ta kalleta Cikin jin Haushi kafin tace"Watarana Amina.Zaki Tuna Damu har kinemu mu bamu kusa Dake ballatana mu gayamiki gaskiyan..!
Amina tayi tsaki ta wuce tana Fadin"Ai da nasan Fushi tayi..Da nasani na Dago na kalli Fuskar ta..Tabdijam waya ga kunu In hanne tayi Fushi..!
Ta Karishe Fada tana Dariya Hamida ta Bita da kallon Yaushe Amina zata Damu da wadanda suka Damu da ita ne..?
Abunda bata sani ba Bawai bata Damu bane A"a ita tana da Saurin Shanye abu,Tana ganin ai ba wani abu bane..Zasu shirya da Hanne tasu bata Baci Shiyasa bata Cika Damuwa ba don sun yi irin wannan ba Ta tabbata ko Kowa ya kyaleta Hamida da Hanne suna gefenta Har acikin Ranta ta basu matsayin dasu basu sani ba.
Kitchen taje ta karya abunta Sannan ta Fito ta isa Dakin Mamanmu bata Ciki tana Dakin Aba Amina ta rike Baki ganin Har 10 ta wuce ammh Aba bai Fita Lalle Ya Dan Malan na zuciyar kowa ta tabbata Saboda Dawowarsa ne Aba bai fita ba
Dakin Yaya ta Leka ta iske ya Zulahait na karatun textbook din Biology Lekawa tayi domin ita bata fiya shiga Dakin batace"Ya Zulahat yaya fa..?
Kanta na Duke bata Dago ba tace"Gata na goyata abaya na..!
Amina ta karkace baki tana Hararanta kafin ta yi kasa da Murya tana Fadin"Ta kusa aure..Ta kusa aure an kusa a bar mana gida..!
Tajita tana mgana yasa ta Dago suna Hada ido ta washe baki kafin tace"Ina kwana Yaya. !
Da karfi Saboda Yaya taji kuma tajin tana gyara kayanta ne Ta girgiza kai kawai chan kuma sai ta dan Murmusa Amina tayi wucewarta aranta tace nasan taji ita yayan nan kowa tana mai Dariya bandani Saboda ta Tsaneni..!
Afili ta Furta"Da ace Aba bai auro Mamanmu ba Al"quran wajen Hajiya zan koma ina zan iya..!
Zulaihat kam sai da ta Toshe kunnenta Amina Mtsalace wlh yarinyar nan kamar mai Almatsutsai
Dakinsu ta koma ta iske Hamida ta Shiga wanka gadonta ta Haye harda jan Zani tana wani Lumshe ido Hutu Dadi ita bataki ma akyaleta kada ta koma makarantar ba ina Laifi takai har Jss3 tafi wasu ma kuma ai ta samu na yaki da jahilci.
*******
Ya Shamsu ne ya fara shigowa Shashen Hajiya babba da wata Jaka ta matafiya irin ta yan Saudiya haka,Hajiya na cikin Dakinta Hanne da Ya Aisha afalon suna ganinsa suka Mike gabadayansu Cikin Murna Ya Aisha tace"Shamsu har sun iso..?
Yana ijiye Jakar nan Tsakiyar Falon yace"Eh suna Haraban gida..Ina Hajiya..,?
Hanne tace"Tana Dakinta..!
Juyawa yayi yana Fadin"Ya D'anmalam yace ku gyara Dakin ku akwai bakuwar da zaku sauke..!
Daga haka ya fice Hanne bata Tsaya ba ta Ruga Dakin Hajiya tana Kiran sunanta sun kusa cin karo Cikin Fada tace"Miye haka ke kullum baki abu Cikin Hankali..?
Tana Dariya ta makaleta tana Fadin"Hajiya su yaya sun iso..!
Kwace jikinta tayi tana Fadin"Shi ne me..?kika rikeni kamar zaki gadani..!
Ta fada tana kariso cikin Falon kafin ma tace wani abu Shamsu ya Sake shigowa da irin Jakar Dazu Ko kafin Hajiya ta samu bakin mgana taga ya Bada Hanya yana Fadin"Bismillah..!
Gabadaya Kofar suka Zubama Ido Hajiya tasan ba D'anmallam bane Domin shashen Malam yake fara isa in ya Dawo kasar kafin ya shigo wajenta sannan in Sakina ne kuma Shashen Uwarta take sauka sai Daga baya take zuwa ta gaisheta.
Bata gama wannan mamakin ba wata Farar balarabiya Jajir da ita kamar ka Taba jini ya fito ta bayyana agaban Shamsu Cikin Shigar Doguwar Abaya baka tayi Rolling din gyale asaman kanta irin yadda matan Larabawa sukeyi,kyakyawace sosai ko gasan kyau zata iya shiga kuma taci sannan Doguwa ce mai Jiki kadam Hannunta Dauke da wata karamar Jaka ta mata Hannanyenta sunsha Jan kunshi kwanin Sha"awa da Burgewa Tunda ta shigo Ta saki Fararan Hakoranta da suka kara Fito da kyanta Tana kallonsu Hajiya.
Suma ita suke kallo Cikin mamaki harta Hanne data saki baki da Hanci tana kallon Tsabar kyau yau datake jin Labari yau gashi ta ganin ma Idonta.
Ya shamsu ne ya Katsesu da Fara gaida Hajiya ta amsa tana Dan Boye mamakinta.
Da Sauri yace"Hajiya bakuwa ce..Ya D'anmallam yace na kawota Shashenki kafin ya shigo..,!
Hajiya bata nuna wani Damuwa ba ta Washe baki tana Fadin"Toto..Nifa nace bakin labarawa da Safen nan..Maraba maraba Sannu da zuwa..!
Tafada Cikin Sakewa Duk da batasan me Hajiyar ke fadaba Tunda batajin Hausa sai larabci ance Tabarman Fuska tafi tabarman zama yadda take ta mata Dariya yasa ta gane tana mata Lale ne.
Shamsu ta kalla daya ijiye jakar hannunsa inda ya Sauke Dayan Dazu tace"Shukran..!
Mirmishi yayi mata shima aransa yana Fadin ina Yaya Danmallan ya Samo Balarabiya mai kyau haka sai da bai tanka ba ya Fice Daga Falon.
Hajiya ta kalli SAROOD tana Fadin"Maraba lale..Kariso mana..!
Hanne ta saka Dariya tana Fadin"Hajiya wayace miki tana jin Hausa..?
Hajiya tace"Oh to..To ku da kuke yara yanzu kwakwalwar ku take ku mata mgana da labarci kuce tazo ta zauna ai batayi ta tsayuwa ba..!
Aisha ce taje ta kamo hannunta tana mata Sannu da zuwa Cikin Harshen Larabci batayi mamaki ba Sanin Daman Umar ya fada mata zataji dadin zama a Nigeria Domin agidansu akwai masu jin yarenta
Har kan Daya Daga Cikin kujerin Falon ta zaunar da ita sai dai bata Zauna ba ta Zame ta Zauna akasa Cafet kanta na kasa Umar ya fadamata Shashen Mahaifiyarsa za"a kaita Shiyasa kanta na kasa ta shiga gaida Hajiya da Harshenta Hajiya na jin Larabci tun abaya don ma Shekaru da kuma Rashin yinsa Lokaci zuwa Lokaci.
Cikin jin Dadi ta amsa mata da Tambayan Hanyan ta amsa da Alhamdulillah kanta na kasa Muryanta Dadi Cikin Harshenta.
Hajiya ta kalli su Aisha tana Fadin"Aisha ce mata ta tsshi a kasa..Ta zauna kan kujera..ke kuma Hanne kwashe kayan nan kikai Dakin ku..Ki kuma Shiga Kitchen ki Hado mata Ruwa da Lemo..!
Daga haka ta wuce zuwa Dakinta Aranta tana Tunanin to wacece wannan yarinyar da D'anmallam ya Taho da ita kuma kai Tsaye a bata Masauki a shashenta da wannan Tunanin ta karisa Dakinta bazatayi gaggawa ba koma me ke ciki tasan Malam ya sani Tunda tasan yaronta bazai Taba zuwa da wata garin nan batare da Izinin Malam din ba..!
Kowacce tayi abunda Hajiyar ta sakata Hanne ta kwashi kayan zuwa Ciki Aisha kuma tace mata ta Hau kujera sai taki Mirmishi Kawai tayi.
Kafin Lokaci an cika gabanta da Ruwa da kunun ayan da sukayi Jiya da Daddare.
Bata taba ko Daya ba tana gefe kanta na kasa tana wasa da adon Kwalliyar Dake Cikin Jakarta Hanne da Ya Aisha suna gefe suna kallonta kowacce aranta tana ayyana kyau kamar ita tayi kanta wannan Balarabiyar da Tambayan Ina Ya Danmlam ya samota..?
Hajiya tana Shiga Bedroom dinta Wayarta Dake kan gado na neman Dauki tana Dubawa taga D'anmalam ne,Da Sauri ta Dauka Tana Fadin"Danmallam kun iso Lafiya..!?
Dagachan Falon Baba Malam Baba Sa"idu na zaune akasa kusa da Baba Malam Dake kan kujera Cikin Farin Raawani suna mgana shi kuma yana Daga chan gefe kamar zai bar Falon kansa na kasa yana Shafa Sumar kansa da bata da yawa.
Cikin Tattausan Muryan da ban taba jiba wacce ta Chakule da Labarci Yasa bata fita saosai kamar yana Koyonta yace"Mun sauka lafiya Hajiya..!ya muka Sameku..?
Hajiya tace"Duka muna Lafiya..!
Sai kuma Shuru ya biyo baya Hajiya Bata Damu ba Sanin Halinsa ko Waya ya Kirata sai ya bata Lokaci kafin ya ce wani abu bayan sun gaisa.
Kamar ana Fizgan mganar Daga bakinsa yace"Hajiya kinga Bakuwa ko..?
Hajiya tace"Eh fa..Yanzu na Dawo Ciki Shamsu yace kai kace ya Kawota Shashena..!
Karkaace kai yayi kamar mace kafin yace"Eh Hajiya..Aisha na kusa ko Hannatu..!?
Hajiya tayi mirmishi tace"Suna Falo Tare da Bakuwar D'anmallam ko na fita na kirasu ne..?
Sai da yayi shuru jin bai yi mgana ba yasa tasan yana jin nauyin yace ta kai musu wayar ne yasa ta Nufi kofa tana Fadin"Kada ka damu..bari na fita na kai musu wayar..!
Da kamar yace ta barshi bari ya Kira Sarood din ammh Hajiya Har takai Falon ji kawai yayi tana Fadin"Lafiyanku kuka zauna kuka tasa Bakuwa agaba kuna kallo..?bana son Shanshanci..Ke Aisha karbi Waya yayanku na son mgana Dake..!
Tafada tana mika musu wayar ganin yadda suka wani tasa Bakuwa gaba suna kallon Dariya sukayi harda Hanne yana ji sanda tace"Wlh Hajiya tana da kyau baki gani ba..?
Hajiya ta tsaki kafin tace"Bangani ba..!
Daidao Sanda Aisha tamai Sallama Cikin Girmamawa ta gaisheshi ya amsa Lokaci Daya yana Fadin"Ke da Hannatu meyasa bakuje makaranta ba..?
Da Sauri tace"Yaya ai muna Jarabawa ne.kuma yau bamu dashi ni da Sadiya da Ikram duk muna gida Hanne kuma sun gama Jssce suna gida suma sai an koma Firstime..!
Kansa ya kara shafawa ya manta fa ko Dazu Shamsu ya fadamai haka da sukaje Dutse suka Daukosu Daga Filin Jirgi,Dayake ta Kano suka Sauka Daganan suka Hawo Jirgin Daya kawosu Dutse.
Cikin Muryansa mai Cike da Zati yace"Kunga bakuwa ko..?
Tace"Eh yaya..Mai kyau da ita wlh ya sunanta..!?
Dan Bakinsa ne ya Motsa kafin yace"Sarood..sunanta batajin Hausa ki rika mata Labarci yanzu dai me kuka bata..?
Kai Tsaye tace"Ruwa da abun sha..Muka fara bata yaya..,!
Kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Aisha ki kaita Dakin ku kice mata tayi wanka..Ta huta tukunnah kina jina..?
Da Sauri tace"To yaya..!
Kai Tsaye yace"Mika mata wayar na Fadamata..!
Ba musu ta mikamata tana Kallomta Tace"Yaya..!
Karba kwwai tayi ba Domin ta gane ba tana kara a kunne taji muryansa Nan da nan ta washe baki basu san me ya Fadamata ba suka ga ta mike Lokaci daya tana mika Aisha wayar Ita kuma tayi gaba sai gata tana Binta abaya Har Dakinsu Hanne ta Bisu da kallo kawai
Har Toilet din sai da Aisha ta nuna mata sannan ta Fice ta barta bayan ta ja mata Kofar Dakin Hajiya ta shiga ta Isketa tana Duba wani Turaran wuta da aka aiko mata Daga garinsu Maiduguri duk da yanzu Saboda Rashin Zaman lafiya Danginta duk sun Dawo Cikin maiduguri wandanda suka Rage Mahaifinsu ya Dade da Rasuwa.
Mikama ta wayar Tayi Hajiya ta karba batayi mgana ba ita bata wannan Shisshigi sai Aishan ne tace"Hajiya Dakin mu yace na Kaita tayi wanka ta Huta..!
Kai kawai hajiya ta gyadamata bata ce komai ba ba irin su daya da Aisha ba Abida ba mai Shigen Surutu ba da hannatu,yasa bata Dameta ba ta fice ta barta sai Faman Raba Turarenta take zata Bama abokan zamanta Sauran ta aika ma su mamanmu Dashi haka Hajiya take Ko sun san da abu ko basu sani ba Sai ta Dibar musu wannan Kirkin nata kowa yana Girmamata Saboda shi.
Sanda ya gama wayar ajiyar Zuciya ya Sauke lokaci Daya yana Sauke wayar Daga kunnensa,kusurwan Falon Mallam yake kallo inda Cabet din Jerin Littafansa suke,Tunani yake yi yazai yi ya Sanar da Hajiya ya kara aure..?ga Halin da Sakina take Ciki Tunda ya Fadamata an Daura musu aure da Sarood take kuka taki cin abinci ta Daina mai mgana Har yau da suka so gida Allah ya gani bai taba son Sarood ba ammh Tana da kimar da bai isa ya Wulakantata ba.
Daga Bayansa yaji Baba Sa"idu na Fadin"UMAR Baba mallam na mgana..?yace ko baka gama wayar bane..?
Jin Haka yasa Lokaci Daya ya Dago kansa Tare da Juyowa Ya fara Tako Doguwar Kafarsa Zarara saman Tattausan Cafet din Dake Falon Malam din
Tsarki ya Tabbata ga Shugaban Hallitun Duniya..Domin Tsabar kyau da Zati da kwarjini wajen bawan Allah nan,Shi ba Fari bane kuma ba Baki ba Fatarsa wani irin Fatace mai kalan Haske kamar na yan Moroci Tattausa Saboda jin Dadi da Hutu tana Sheki Dogon Namiji ne wanda ake Kira Ingarma yana da Fadin Kirji Daga Kafadunsa zuwa cikinsa ya Bude,FUSKARSA doguwa ce Sambal masu Dauke da matsaikatan Idanuwansa da Gashin gira dana Ido..Hancinsa Dogo ne ammh ba Sosai ba wanda ya karamai kyau da Zatinsa Sannan Bakinsa Zagaye da Saje baki wanda ke karamai kwarjini Daga kasa kuma gemunsa wanda yabar gemu kadan wanda bau wuce kamu Daya ba.
Wanda ya Dace da Zagayyen Bakinsa mai dan Fadi kadan da Tudu,yana Sanye Cikin Pakistan Riga da Wando na yan Saudiya Rigar Tawuce gwiwansa Sannan wandon bai rufe kwarin Kafansa ba Kansa Sanye Cikin Hula irin ta Larabawa karamar nan wacce iyakarta rabin kansa mai Kulin Gashin Sakan Hulan Daga sama Wanda ya ba Sumar kansa Daga kasa zuwa sama sama Bayayyana Duk da ya Asketa ammh gatanan tayi kwance gwanin Burgewa sannan Goshinsa ga Bakin Tabon sallah nan wanda ke karamai kwarjini da Haiba.
UMAR YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA kenan Namiji kwara Daya Tal da Bayan Sa"idu Mallam ke matukar kauna acikin Ransa a Cikin Jerin ya"ya ashirin din da Allah ya basa mai tarin baiwa da Allah kadai Daya Hallicesa ya sani mai kimanin Shekaru Talatin da Takwas zuwa da Tara aduniya.
Har ya kariso ya zauna Kusa da Baba Sa"idu Baba Malam da Baba Sa"idu basu daina kallonsa ba.
Suna kara yaba kyan zatinsa ko su kansu kwarjini yake musu Tabbas Qur"ani ba karya bane kana ganin Mahaddacinta kake ganewa Saboda Natsuwar dabam take.
Kansa na kasa Cikin Muryansa mai Zaki yace"Afuwan Baba..na kira Hajiya ne..!
Baba Malam ya gyada kai kafin yace"Kace Shashenta ka Sauki bakuwar taka ko..!?
Kansa na kasa ya gyada kai Baba malam ya cigaba da Fadin"Hajiya ko bata san mutum ba ita din mai karamci ne..Zata karramata matuka..!
Baba Sa"idu yace"Sosai shiyasa nace a kaita chan kaawai..!
Baba Malam yace"Da kaji an ambaci Hajiya Jikin ka na rawa ka yabeta..Ina mamakin yadda ZAINABU ta kwacemin SA"IDU NA..!
ya karishe Fada Cikin Zolaya.
Baba Sa"idu na Dariya Danmalam kuma Mirmishi kawai yayi.
Kafin Baba Sa"idu yace"Haba dai..Ai Tsakanin Uwa da d'a akace sai Allah baba..Kuma haka Tsakanin Uba da Dansa sai Allah har Abada Sa"idu na Baba Malam ne ba shi ba duk wadanda ke karkashin sa naka ne Baba..!
Baba Mallam Zuciyarsa kamar Farar takarda ya gyada kai kafin yace"Allah ya albarci Rayuwarka Kai da iyalanka Sa"idu..!
Suka amsa shi da Umar atare,Kafin Baba Malam yace"Ni na hana Sa"idu ya Fadama Hajiya komai..na bari sai ka zo..Ko sauran abokam zaman nata ban Sanar da kowa ba..Ina Fatan ka Fadama ita Dayar iyalin naka ko..?
Kansa na kasa yace"Eh na sanar da ita tun muna chan..!
Mallam yace"Dakyau haka ake so..Allah ya zaunar daku lafiya..Sai ka zama jajirtattacen adalin zama da macen Fiye da Daya sai Adali Umar..Bana jinka nasan bazaka taba aikata wani abu mara kyau ba..Sannan itama Diyar Kattab din indai Halin Mahaifinta ta Biyo Har Abada bazakayi nadama ba..!
Baba Sa"idu yace"Allah ya sa...!
Kansa na kasa shidai bai ce komai ba basu Damu ba Sanin Halinsa Shuru Shuru bai da Hayaniya.
Baba Malam ne ya kalli Baba Sa"idu yana Fadin"Sa"idu ka tafi wajen aika..Nima anjuma kadan zani Gidan Sarki Tun jiya Sakon sa ya isoni yana son ganina..Umar kuma ya shiga Cikin Gida ya gaida iyayensa zuwa anjuma sai mu zauna gabadaya domin a gabatar da Bakuwar data shigo Cikinmu Gabadaya..!
Baba Sa'idu ya jinjina kai yana ma Malam Allah ya kiyaye Hanya.
Tare sukayi mai Sallama suka Fice shida Baba Sa"idu sun Dade aharaban gidan suna jingine jikin Motar Baba Sa"idun suna mgana kafada na gugan kafada Malam na daga cikin Falonsa yana Hangesu ta Wandow Falon Lokaci Daya ya saki kayattacen Mirmishi.
In ka gansu kamar wasu yaya da kaninsa uwa daya uba Daya ya Tabbata abunda bazai iya Fadamai bane yake Sanar da Sa"idu Akwai Shakuwa da Fahimta a Tsakaninsu Yana Daukansa kamar kaninsa Shima yana Daukansa kamar yaya kuma Uba agaresa
Sun dan jima suna mgana kan yana Fadamai bai Tsara Karin aure yanzu ba, sai dai kana naka Allah na nashi ne Baba Sa"idu na ta bashi Wasu Shawarwarin kafin suyi sallama ya Shiga Mota ya wuce Gidan gona yayinda Shi kuma ya Fara takawa yabar Filin Haraban gidan zuwa Shashen Hajiya ammh Kuma Ransa da da Kallonsa na Shashen Anty Amarya yana Tunanin ko Sakina ta Daina kukan..?ya manta Rabonsa Daya ga taci wani abu sai ruwa kawai..!
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*Sadaukarwa ga Halima Yusuf gwarzo (Besty) Alherin Allah ya kai miki a dukkan inda kike*
*🅿️09*
Cikin Tafiyarsa ta natsuwa ya karisa Shashen Hajiya babba kamar yadda yake a ka"idarsa sai ya fara isa shashen Mallam sun gaisa sannan sai ya shiga cikin gidan Daya bayan Daya ya Bisu ya gaishesu.
Hajiya na cikin Dakinta har alokacin Daya shigo Aisha ce da Hanne har Lokacin afalon yana Shigowa Cikin Sallamarsa da Muryansa mai Zaki da Sanyi a koyaushe,Lokaci daya da kamshin Turaransa na Arab yayi musu Sallama..!
Gabadayansu suka mike Cikin Fara"a da Murnan ganinsa domin sun Dade basu gansa ba Tun Karshen wanchan Shekara sanda yazo Lokacin Duba Hajiya ce Datayi ta Fama da Kafa suna makaramta basu gansa ba kuma Kwana Biyu yayi ya koma.
Hannayensa duka Sanye Cikin Aljihun wandonsa ya Kariso Tsakiyar Falon gabadayansu har suna Hada baki wajen gaisheshi da yanayin Natsuwarsa ya kallesu yana amsa gaisuwarsu yana kara ganin girmansu acikin Idanuwansa.
Kai Tsaye yace"Hannatu Aisha meyasa baku je makaranta ba..?
Da Sauri Aisha tace"La yaya bana Fada maka ba..!
Sai Alokacin ya tuna da Sauri yace"ohm.Sorry na manta..Allah ya bada sa"a..!
Suka amsa da Ameen gabadayansu sai kuma yayi shuru yana kara nazarin Falon kamar me neman wani abu basu Damu ba Sanin Halinsa Sannan babu wani Shakuwa sosai a Tsakaninsu Tunda shi Babba ne sannan Lokacin da suka taso baya kasar yana Madina so zamansa Dasu bashi da yawa ammh duk da Haka yana da Kwarjini da baiwar da kowa ke girmamasa,ba Duka yake yi ba ba kuma Fada ba,Shi ina ma ya zauna ballatana yayi Hukuncin ..?in yazo kuma bai wani Dadewa yake komawa sai dai AllAh ya riga ya bashi wannan girman kuma ya Dauka kamar yadda In mallam yayi mgana bamai Musamai haka shima mgana Daya zai yi Cikin kwanciyar Hankali da Salama kowa zai shiga Taitayinsa bawai bashi da Sakewa bane, bai da yawan wasa da Dariya sannan bai da mgana ballatana Hayaniya yana da Matukar Sanyi Sosai a lamuransa.
Kamar ma ya manta daasu acikin Falon Saboda yadda yayi Shuru bai kara mgana ba sai chan ya kalli Aisha kafin yace"Ina bakuwar ku.?
Da Sauri tace"Na kaita Dakinmu na nuna mata Tiolet tana ciki na barta Tun dazu..!
Kai ya gyada kadan kafin yace"Ina Hajiya..?
Wannan karon Hanne ce ta nuna mai Dakinta tana Fadin"Tana ciki Yaya..!
Bai tsaya kara mgana ba ya Kama Hanyar zuwa Dakin Hajiya Cikin Natsuwarsa kannensa suka Bisa da kallon Sha"awa Duk cikin gidan nan ba kamarsa Sai dai abiyo bayansa.
Sai da suka Tabbatar da ya shiga Dakin Hajiya sannan Hanne ta Juyo Tana Fadin"Ya Aisha kinga yadda Ya D'anmalam ya kara kyau kuwa..?Wlh nima ina son naje Madinar nan Watarana..!
Aisha tana jinta batace mata komai ba illah ta Cigaba da Duba Littafin Dake Hannunta Hanne bata Damu ba Sanin Halin Aishan itama din mai Sanyi ce.
Hajiya na Tsaka da kasafin Turaranta Taji Sallamarsa Cikin Sanyi da Haiba Lokaci daya da Kamshin Turaransa mai Sanyaya Zuciya batasan Lokacin data saki Mirmishi ba Cikin Farinciki ta amsa sallamar tasa tana jaye kayan gabanta Lokaci Daya tana mai maraba.
"Maraba..Maraba..Maraba da Danmallam maraba da bakin madina Bakin Larabawa..!
Sai alokacin hakoransa kadan suka Fito yana Mirmishi gaban Hajiya ya Duka kansa na kasa yace"D'anmallam dai Hajiya..?Har yaushe ne zaki Fara Kirana da Umar ne..?Alhalin Baba Sa"idu Sa"idun sa kike kiransa Hajiya..!
Hajiya na Dariyan Farincikin ganin Yaronta ta kauda mganar da cewa"Masha Allah..Danmallan me kuke ci a Madinar ne.?gabadaya ka Sauya ka koma kamar Balaraben chan..!
Kai kawai ya gyada yana Shafa Gemunsa kafin yace"Hajiya bakomai..Sai nasaran addu"an ku gareni..!
Hajiya tace"Hakane..Allah ya kara Tsareka Allah ya Dafa maka Allah ya albarkaci Rayuwarka..!
Ya amsa da Ameen kafin ya Dago yana Fadin"Hajiya baki ce Allah ya bani Zuru"a ta gari ba..!
Hararansa tayi kafin tace"Ko ban Fada ba..Ina maka wannan addu"ar D'anmallam..!
Daman yasan haka zatace yadda Hajiya ke kunyarsa ko Ita Bafullatanane sai haka Tambayan kowa da kowa yayi tace duk suna Lafiya,Shuru ya biyo baya shi bai ce mata ba itama yasan bazatace ba Hajiya nada wannan Halin bata matsa ma Mutum akan abunda tasan Dole zata saani Shiyasa bata ce masa komai kan Sarood ba shima bai ce mata ba.
Kansa na kasa yana Duke ita kuma tana Cigaba da Zuba Turaranta Ganin Yaki zama kuma yaki tashi yasa ta kallesa tana Fadin'Ka zauna mana..Kada Tsugunnen ya gajiyar Dakai..!
Kai ya girgiza kafin yace"Hajiya Ina da gajiya ajikina..So nake na shiga na gaisa da su Hajiya uwa..Kafin naje nayi wanka na Huta..!
Kai ta gyada kafin tace"Hakan ma ya kamata..Mallam ya fitan ne..?
Kansa na kasa yace"Bai riga ya fitan ba ammhh yace yanzu zai fitan..Muna ma nan Haraba ni da Baba Sa"idu yanzu ya wuce gidan gona..!
Hajiya tace"Sa'idun Zainabu da Malam..ya shigo mun gaisa tun zuwansa..!
Bai yi mgana ba ita kuma ta kallesa tana Fadin"Dame zaka Karya..?nasa dai yaran sun yi maka Sinasir da waina..Bansan kuma me zamu ba wannan bakuwar ba kasan ku achan ba irin Cimar mu bane naku..!
Sai alokacin ya Dago kafin yace"Da kuli Hajiya..?
Kai ta gyadamai tana yar Dariya shima Mirmishin yayi yana Fadin"Yaushe Rabona da waina da kuli Hajiya..?Naji dadi sosai su dafamin ruwan Tea da na"a na"a,su hadomin da waina din ita kuma Sarood su hada mata Tea su soya mata Kwai is ok..!
Hajiya bata wani Damu ba tace"Shikenan.Ammh a Shashen mallam zaka Huta..?ko yanzu zaku isa gidan naku..?
Da Sauri yace"Sai Dare hajiya..Dakin su Shamsu zan yi wanka na Huta zuwa an juma..!
Hajiya tace"Na manta ne da na saka su Akilu sun gyara maka Dakinsu Nazem ka Zauna aciki..!
Kai ya kada kafin yace"Bakomai Hajiya nan din ma ya isa..!
Hajiya tace"Ai shikenan..!
Yana kallonta Kafin yace"Hajiya Turare kika fara saidawa..?
Hajiya tace"A"a Goggonku Yakura ta aikomin dashi shine nake rabawa zan aikama sauran iyayanka Sauran kuma na matan Sa"idu ne..!
Danmallam ya Murmusa kafin yace"Su yaya suna Lafiya..!
Hajiya tace"Duka suna Lafiya..!
Daganan sukayi shuru hirar ta kare ya Dade kafin ya tashi ya mata sallama ya Fice,Bayan ya fito su Hanne sun zata zai nemi Sarood sai dai bai ce musu komai ba ya Fice bayan Fitarsa Hajiya ta leko tace Hanne ta Dafa Ruwan Tea ta soya kwai ita kuma Aisha taje wajen Shamsu ta karbi key din Dakin Su Nazem ta dan gyarama Danmallam ya samu wajen da zai karya ya Huta.
Dukkansu da toh suka amsa Aisha tatashi ta saka Hijabi ta Fice,Hanne kuma ta shiga Kitchen.
Daga Dakin Hajiya Shashen Hajiya Uwa ya isa Tana ganinsa Cikin Fara'arta ta fara mai maraba itama Dukawa yayi yana gaisheta ta amsa tana Fadin"Umaru basai ka jira mu zo sannu da zuwa ba..!
Kansa na kasa bai ce komai ba tayi Dariya ya tambayeta yaran tace kowa Lafiya sai ga Umaima ta fito ta gaisheshi ya amsa yana kallon Hajiya uwa kafin yace"jikinta ya daina tashi ko..?
Hajiya Uwa tace"To ya dai yi Sauki Umaru..!
Kai ya jinjina kafin yace"Allah ya kara afuwa..Nazo mata da wasu manganuna in na Huta zan kawo mata ta fara amfani dashi mu gani..!
Hajiya Uwa ta fara mai godiya yana amsawa Har ya fice tana Rakasa da addu"an haka take ita tana da Kirki kamar Hajiya take.
Daganan sai bangaran Haj.Nasara itama ta karbesa sosai suka gaisa da Tambayan bayan Rabuwa Ikram ya gani tazo ta gaisheshi ya amsa yana kallonta ganin ta girma har zai tambayeta meyasa bataje makaranta ba sai ya tuna da mganar Aisha sai ya Fasa Yana Shirin Fita ne Take tambayansa ko da ba Sakinar suka zo bane..?
Cikin Haibarsa yace"Tare muke da ita..Tana bangaran Anty Amarya..!
Baki ta tabe batace komai ba yayi mata Sallama ya fice yana fita tace Ikram ta shiga Kitchen ta Dafamai Tea da soya kwai,Saboda Umar Domin in yazo garin ba wacce bata kokarin kyautatamai kamar yadda zata kyautatama Malam.
Kai Tsaye Daganan sai Shashen Anty Amarya ita kam koda ya Shiga bata Falon Sa"adatu kadai ya gani Tana Kwance saman kujera ko Sallamarsa ma bataji ba sai dai ta gansa saman kanta Cikin Muryansa yana Fadin"Ke baki jin sallama ne..?
Kamar ta kifa haka ta sauko daga kan Kujeran tana Raba ido Cikin Kifta ido Tace"Sannu da zuwa ya D'anmallam..!
Bai amsa mata illah Falon Dayake bi da kallo kafin yace"Ina Anty..?
Da Sauri ta mike tana Fadin"Tana Dakinta ita da Ya Sakina..!
Baima ce ta Kirata ba yaga ta wuce sai bai kirata ba Hannayensa Cikin Aljihun wandonsa ya kurama waje Daya ido kamar mai nazari.
Sa"adatu sai da tayi knooking Domin Tun isowar Sakinar tana kuka suka Kule Cikin Daki ita da Anty basu Fito ba,Kuma sun kulle kofar Daga ciki Anty Amarya da Ranta ke bace domin ta gaji da Lallashi da Tambayan Sakina meke Damunta taki gayamata gabadaya Tunda suka iso take kuka taki mgana ballatana tasan meke Faruwa..
Dagachan tace"Waye..?
Da Sauri Sa"adatu tace"Nice Anty..!
Tashi tayi taje ta Bude Kofar da Sauri Sa"adatu tace"Anty Ya D'anmallam yazo yana Falo..!
Da sauri tace"Yazo .?
Ta daga kanta Sakina ta juya tana kallo wacce ta Dunkule kan gado tana kuka kafin ta Dawo da kallonta kan Sa"adatu tana fadin"Kice mai gani nan zuwa..!
Daganan Sa'adatu ta juya ita koma ta maida kofar ta Rufe ta Dawo bakin makeken gadon Dake Bedroom din inda Sakina ke Dunkule ta Dade tana kallonta kaf ta gama Hasashenta bata hango abunda zai sa Tunda suka iso Sakina ke wannan kukan ba ta kuma yi Tambayar Duniyar nan Sakina taki Mgana.
Kai ta kada Kafin tace"Ai shikenan Tunda bazaki mgana ba..ga Umar din chan yazo..Bari naje na tambayesa kila shi ya fadamin abunda ke faruwa..!
Har ta bar Dakin bata Dago Daga kukan datake yi ba ballatana tasaka ran zata kalleta
Ta iskeshi Tsaye bai ko zauna ba Sadiya ta fito sun gaisa Sa"adatu ta shiga Dakinsu ta Fadamata zuwanshi.
Yana ganin Fitowarta ya Rage tsawonsa ya Durkusa kan kafafunsa yana gaisheta ta amsa Lokaci Daya Tana zama kan Daya daga cikin kujerun Dake Falon.
Daga gaisuwan ne bai kara cewa komai ba kansa na kasa yana kallon adon Zanen jikin Tattausan Cafet din Dake Falon.
Anty ta kalli su Sadiya kafin tace"Ku tashi ku shiga ciki..!
Ba musu suka mike zuwa Dakinsu sai da taga Shigewarsu kana ta maida Hankalinta kansa kafin Tace"Umar meke Faruwa ne..?ko kun samu Sabani da Sakina ne .?Tunda kuka iso take kuka gatachan kwance kuma nayi Tambayan Duniyan nan tayi banza dani har yanzu taki cemin komai..Shine nace bari kai na Tambayeka meke faruwa ne .?
Kansa na kasa bai Dago ba abu Dayane ya kara bashi mamaki me Sakina ta Dauki kanta ne..?tana Tunanin kukanta da Rigimanta zai sa afasa komai..?ai ta makaro Domin bakin Alkalami ya riga ya Bushe..Sannan bata isa yasa ya Sauya abunda Allah ya Tsaramai ba Duk da karin aure bai Cikin Tsarinsa.
Yasan yana da Sanyin Hali baya son Damuwa da Hayaniya ammh tasanshi Yana da zuciya mai karfi wanda in yagaji da baka baki bazai biyema iskancinka ba zai Fita batunka ne kamar ita yadda tayi mai tun suna Madina yake bata baki ganin yadda Hankalinta ya tashi bayan ya gayamata bayan an Daura auran Abunda yasa ya Biyemata yana ganin ya bata mata Tunda shima abun Daga sama yazo mai ammh akallah ba Dadi Kaji Mijinka yayi aure Lokaci Daya sai dai ya gaji da Lallashinta zai kyaleta In ta gama kukan don kanta ta Hakura shi bai kuma san da wani Kalma zai kara lallashinta ba.
Anty Amarya ta gaji da jiran amsar sa bai ce mata komai ba gabanta nata Faduwa kada matsalan yazama babbace Fiye da Tsammaninta.
Yasa ta gyara zama tana Fadin"Kayi Shuru..!?Ina fatan Allah yasa abun bai kai ku ga Saki ba..?
Sai alokacin ya Dago yana kallonta bata ga wani abu a Fuskarsa ba Illah Haibarsa da Zatinsa Cikin kakkausan Muryansa mai Cike da Sanyi yace"Babu ma mgana makamancin wannan Anty..!
Ajiyar rai ta sauke na samun natsuwa kafin tace"To me ke faruwa..?
Nan ma Shuru yayi mata ta kara kallonsa tana nazarinta har ta Fidda rai da zai yi mgana sai chan taji yace"Tunda bata gayamiki ba..Bakomai kenan..!
Kai Tsaye ya fada batare da Tunanin wani abu ba ya mike yamata Sallama ya Fice Daga Dakin tana Binsa da kallon mamaki.
Aranta tana ayyana wani abun Meke Faruwa..?meyasa Sakina taki mgana..?tana ji ajikinta koma miye babban al"amari ne sannan ta godema Allah daya kasance ba Zencen Saki bane Komai miye ai zai zo da Sauki.
Tashi tayi ta koma Dakin ga mamakinta sai ta iske Sakina ta shiga wanka sai taji Dadi,Yasa ta fita da Sauri zuwa Dakin su Sadiya tace su tafi Kitchen su sama ma Sakina abunda Zata karya dashi Dakin ta koma ta iske Sakina ta fito Fuskarta Duk ta kumbura idanuwanta duk sun shige Saboda kuka.
Anty Amarya ta kalleta tana Fadin"Ko kefa Sakina..?
Dagowa tayi ta kalleta Fara ce kyakyawa Daidai Misali sannan ita din mai matsakaicin Tsawo ce Tana da Jiki kadan da Jikin mata.
Kai Tsaye tace"Ya gayamiki wani abu..?
Anty tace"Kema kinsan bazai yi mgana ba..Umar yafi Ubansa Miskilanci da kyaluwa..!
Dan Mirmishin Fatan baki tayi Lokaci Daya tana Cije bakinta Towel ne Babba ajikinta taja Kujeran gaban madubi ta zauna ta Fara Shafa mai,Acikin Ranta tana jin kanta yayi mata Girma kamar zai Rabe Biyu Saboda Tsananin Kunar da zuciyarta ke mata.
Tana gama Shafaa mai ta Sauya kaya Cikin Wata Riga da wando Saukakku,Lokacin Sadiya ta shigo mata da Faranti shake da kayan karyawa Tea kadai ta sha bata iya cin komai ba,Bakinta ba Dadi Saboda yanayin Datake ciki.
Tagama kenan sai ga Anty Amarya ta shigo Dakin tana kallon Farantin Dake gabanta take fadin"Ya haka..?naga baki ci komai ba..?
Sakina na Sake komawa kan gadon tace"bakina ba Dadi Anty..!
Anty ta waro ido kafin ta karisa gefen gadon ta zauna tana Dafata Lokaci Daya tana Fadin"Ke na tabaki da Alheri Sakina..Allah yasa abunda muka Dade muna jira ne..?
Cikin Mamaki take kallonta kafin tace"Me kenan..?
Kai Tsaye tace"Ciki mana Sakina..Naji kince bakin ki baya Dadi..shine nake Tunanin kodai kodai..!
Da Sauri ta katseta ta fadin"Ba ciki bane Anty..Wannan al'amarin yafi gaban na..Rufo kofa kizo kiji..!
Da Sauri tatashi ta Rufo kofar ta Dawo ta Zauna kusa da ita kamar wata kawarta.
Sakina ta Fara matsan kwallah kafin tace"Anty Umar fa aure ya kara..!
Anty tayi wani Sansarai rai kafin tace"Aure wani irin aure kuma..?
Sakina ta ballo Hawaye saman kumatunta kafin tace"Aure da kika Sani Anty..Abun bakin cikin ma bai Fadamin ba sai da aka Daura auran. !
Anty Amarya ta Dafe Kirjinta kafin tace"Daman da gaske kike yi Sakina..!Wani irin aure kuma ana Zaune kalau..!
Sakina tace"Uhm yadda kikaji haka naji Anty..Ni ba komai yafi Tadamin Hankali ba..Irin matar daya aura..Anty Balarabiya ina ni ina kishi da Balarabiya..?
Ta karishe fada tana Kuka Wiwi Anty Amarya ta Dora Hannu akanta tana Fadin"Na shiga tara ni Marliya..?wannan wani irin kaddara ne..?
Sakina ta kwanto da kanta Saman Cinyar Anty Amarya kafin tace"Kaddara mai muni ma Anty..Kinga kyan yarinyar..?wlh ko gasar kyau ta Shiga sai taci..Tafini komai da komai ta bangaran kyau da Zati da nasaba da asali Wlh Anty wannan suka fara zama da Umar ni Bora zan zama..!
Ta karishe Cikin gunjin kuka Anty Amarya gabadaya jikinta rawa yake yi Cikin Tashin Hankali tace"Wai garin Yaya haka ta faru...?Diyar wacece ya auran..?
Sakina tace"Diyar abokin Baba Mallam ne..!
Anty Amarya tace"Kattab..?
Da Sauri ta Daga kai kafin ta cigaba da Fadin"Ita..Diyar su din nan kwara Daya Sarood..yadda Umar din yace min shi Abu kattab din ne ya bashi Auran kuma bazai iya kin karba ba..Ni ban sani ba saida aka Daura auran a Satin da zamu taho..!
Anty Amarya gabadaya Hankalinta baya Jikinta Har Sakina ta cigaba da Fadin"Tashin Hankalina Daya Anty..In tazo ta Haihu fa..?wlh Bora zan zama a idon Umar da Danginsa na zama bani da wani amfani..!
Da Sauri Anty Amarya tace"Ina.karya ne..Ba wanda ya isa wlh..!
Ta fada Lokaci Daya tana Ture kan Sakina Daga Jikinta ta mike tana Mazari Cikin bacin rai tace"ba wanda ya isa ya maidake baya Sakina..Kamar yadda ban zama baya ba..Wani Cikin ya"yana bazai taba zama baya ba..!
Take Fada tana Huci Sakina ta Mike Zaune tana Sharan kwallah kafin tace"Nama zama..Domin da ita muka zo kasar nan..!
Da Sauri ta zaro ido tana Fadin"Eyee...!
Sakina ta Daga kai tana Fadin"Eh tana ma Cikin gidan nan..Inaga Shashen Hajiyarsa yace shamsu yakaita..!
Anty Amarya ta rike Haba Kafin tace"Kenan iyayen nasa sun san da Labarin auran shine mu bamu ji ba..?
Sakina tace"Ni bansani ba..Ammh dai Malam ya sani Da Baban su Jafar tunda naji suna mgana tun muma chan..!
Anty Amarya ta Lailayo Ashar ta Dankara kafin tace"Sa"idu...Sa"idu..Ko bai kira Malam ba..Ina mai Tabbatar miki Sa"idu zai fara kira..Sa"idu ne ja gaba kan komai..Ko Malam da Hajiya basa tsallaken Shawaran Sa"idu abunda yace shi akeyi acikin Gidanan Sakina..!
Sakina ta Sharce majina tana Fadin"Anty ya zamu yi..?wlh karki so ki ganta Kinga kyanta..?
Anty Amarya Haushi ya kamata ta Ballama Sakina Harara tana Fadin"Kyan me..?kyanta na banza..Takai ki wayau ne..?Kyan ne kawai ammh batakai Budewar ido ba ..ina taje ina ta taka..?Irin wadanan kyan ne kawai da zaman waje Daya na Tabbata bata samu wata Sakewa ba..!
Sakina tayi shuru tana kallonta kafin tace'"Eh kam..kamar sakara haka take..Sai dai namiji ba ruwansa da wannan..!
Anty Amarya tayi Mirmishi kafin tace"Kada ki damu kanki..Ki Share Hawayenki kada ki kara kuka..Waannan auran wani matakin Nasarmu ce Sakina..!
Sakina tace"Taya ya..?
Anty Amarya ta kama Hanyar fita tana Fadin"kidai ki saka ido kawai..Mu zuba mu gani..!
Shege ka fasa..!
Daga haka ta Bude Kofar ta Fice tana Tafe tana Mirmishi ita kadai kamar an ce mata an biya mata aikin Hajji.
Falo ta koma ta Zauna ta Dora Kafa Daya kan Daya tana Kadawa kamar wata yar yarinya yar shekara Goma sha.
Sakina kuma tana Fita ta koma ta kwanta Damuwarta ya ragu,Saboda tasan duk abunda Anty tace kada ta Damu to tasan cewa kada ta Damun komai zai zama Daidai,Daman ga Rashin barci ga Damuwa yasa batasan Lokacin da barci ya kwasheta ba Cike da Mafarkin yadda makomarta zai kasance Tsakaninta da Umar da Sarood.
******
Amina sai gabda Azahar tatashi Daga barci tana mika Hamida bata Dakin yasa bata damu ba tatashi ta shiga waanka Lokaci daya ta Dauro alwala sai da tazo tayi Salla kana ta Sauya kaya ta saka Riga da Sikat na wani leshi da Mamanmu ta Dinka musu ita da Hamida.
Sannan ta fita Tsakar gida ba kowa ko'ina tsit,Kitchen ta Zarce ta iske ya Zulahait ta gama abinci Kuskus da Miya da nama Amina tayi Dariya kafin tace"Mijin ya Zulaiha zai ja kaya Wlh...!
Haka take fada tana Dariya kafin ta Diba iya sonta ta cika nama ta koma gefe taci tayi kat ta koshi,sannan ta fito taje bakin Famfo ta wanke hannu Dakin Mamanmu ta leka ta isketa tana Sallah Tana jin Hayaniyar Hamida a dakin Yaya taki Shiga Daki ta koma ta Sake kwanciya taci ta koshi Takaichinta Daya bata zuwa da Littafin hausa agida iya makaranta take karatunta ko boko ko Islamiya.
Ammh bata zuwa dashi gida ba Domin tana jin Tsoro ba ko wani abu ba, Aron daman iya makaranta ne ana tashi zainab take karba Saboda na mamanta ne take aro mata itama ba"a Sani ba agida.
Yasa barci ya kara Daukanta bata Sani ba sai Bayan azahar ta tashi Shima Mamanmu ce tatasheta tana Fadan ta Daina barcin yammah ba kyau.
Lokacin datasahi ta ga mamanmu Sanye da Hijabi tana Mitsike ido ta Sauko Daga kan gadonta tana Fadin"Mamanmu ina zaki na ganki da Hijabi..?
Mamanmu tace"Gidan Mallam zamu shiga ni da yaya..Danmallam sun iso tun Safe..!
Zamu je maraba da barka da zuwa..!
Amina ta tabe baki kafin tace"Mamanmu sai ku bisa..?bashi zai zo ba..?
Mamanmu na Dariya tace"Basai kin Fada ba zai zo..ammh yana da kyau mu bara zuwa din..!
Ta fada tana Ficewa Lokaci Daya tana Fadin"Ki tashi kiyi sallah tunda ke bazaki shiga ba..Tun dazu hamida tatafi..!
Mamanmu bata tsaya ba ta fice Amina tana so ta tambayeta chan gidan nasa Hamida tatafi ko gidan Baba Malam..?
Bata samu mai bata amsa ba yasa ta Tabe baki ta fito Bakin famfo tayi alwala tazo tayi sallar Ta gaji da kwaciya bayanta har ya gaji yasa ta zauna tana Tunane tunane Zulaihat na Dakin Yaya tun Safe batama zauna adakin ba Tana jin tashin mganar Ya Zeena na tashi,Yau Alhamis ba islamiya Shiyasa suke gida.
Bata fita ba Sanin Yau jidalinta na Saman kanta in taje Bakinta bazai yi Shuru ba kuma baza"a samu Zaman lafiya ba.
Yasa ta Cigaba da zama inda tayi Sallar har ya Zeenatu ta Shigo ganin yadda Amina ke zaune da Hijabi yasa abun ya bata mamaki yasa ta kalleta kafin tace"Amina yau kuma Lazimin yammah aka fara..?
Amina ta kalleta shekesheke kafin tace"Uhmm..!
Daga haka bata kara mgana ba Ya Zeena tayi Dariya tana fadin"Gwara dai kiyi shuru..yau gidan ya Sarara..!
Amina batace komai ba Tunani take taje gidansu Hanne ko A"a tana Shawara da zuciyarta ne Har ya zeena ta Dauki abunda zata Dauka ta Fice ta bar Amina nan zaune tana cigaba da Shawara tasan Hanne Sarai in taje sai ta basar da ita Kafin su shirya.
Tana nan zaune har su Mammanmu suka Dawo bata tashi ba har Lokacin kuma Hamida bata Dawo ba Amina ta Mike tana Fadin"Alqur"an sai naje naga ni..Hamida iyayan gulma ba"a Dawo ba..!
Ko Hijabin jikinta bata Cire ba,Ta fice batare da tace ma kowa gata zuwa ba.
Mazan duk basa nan suna msallaci wajen karatun yammah Da Baba Mallam ke yi,yasa kai Tsaye ta Nufi Shashen Hajiya Babba.
Daga Kofar ta fara kiran sunan Hanne kafin ta shigo tana Fadin"Hanne ni zaki Wulakanta ina ta Kiranki kinyi banza dani..!
Tafada Lokaci Daya tana Shigowa Falon batare data Tsaya Lura da kowa ba,Idanuwanta suka fada kan Hanne da Hamida dake gefe sun hada kai suna mgana Amina ta rike baki Tana Fadin"Hamida an ci amanata..Shine ko ki tasheni sanda zaki taho..!
Tafada Lokaci Daya tana karisawa gabansu Hannu tasa tana jan hannun Hanne Lokaci Daya tana Fadin"Hanne taso kiji..!
Hanne taki tashi lokaci Daya tana Fadin"Ba inda zani..Lokacin da naje ina miki mgana kin manta me kikacemi ..?
Amina tace"Hamida ce zata Hadamu Hanne..?Haba hannenta Hannen Aminene..!
Tafada tana Dariya har tana Jan kumatun Hanne da Duk Dauriyanta sai da tayi Dariya.
Hamida tace"Amina kinzama abun kallo kin shigo baki gaida kowa ba..!
Sai alokacin ta juya tana bin wadanda ke falon Idonta ya Sauka kan Sa"adatu lokaci Daya ta balla mata Harara,Sai kuma wacce ke kusa da ita Tana Sanye da Babban lullube asamaa kanta Sakina ce Anty Amarya ta saka Sa"adatu ta rakota tazo ta gaida Hajiya bayan sun gaisa Hajiya ta shige ta barsu da yara.
Sakina taki tafiya ne tana so taga ta inda Sarood zata fito Saboda ta tabbatar tana Shashen Hajiya,Shi kanshi Umar din bata kara jin motsinsa ba ance yana Masallaci Wajen karatun mallam
Sai ga Amina ta shigo Tunda ta shigo Kowa ya koma kallonta Saboda yadda ta Fado falon kamar Daga sama.
Amina ta Dawo da kallonta kan Hamida kafin tace"Su waye..?
Ta fada tana yamutsa baki Da Sauri Hanne tace"Matar ya D'anmallan ce Anty Sakina..ki gaisheta..!
Amina taja Tsaki da karfi kafin tayi mgana Hamida tace"Amina don Allah...!
Yasa bakinta ya mutu,Ranta bace ta Juya tana Fadin"Ina yini..!
Sakina sai da ta kare ma Amina kallo sama da kasa kafin ta tabe baki tace"Lafiya..!
Lokaci daya tana kallon Sa"adatu kafin ma tayi mgana tace"Amina ce..Ta gidan Baba Sa"idu..!
Sakina ta Tabe baki ta kauda kai ita bata gabanta abunda ke gabanta ya Isheta tana so ta Sako mganar Sarood wajen Aisha sai dai bata so ta Fahimceta sannan Aishar ma Azkar ne a Hannunta tana karantawa bata bi ta kan abubuwan dake Faruwa acikin Falon ba.
Amina ranta yakai kololuwa abaci da karfi tace"Jaruba..Kayyasa..!
Hanne bata bari ta karisa ba ta Tashi Tsaye ta Toshe mata baki lokaci Daya ta jata suka zauna kan kujera tana Mata rada a kunni.
"ke ya D'anmallan yazo da bakuwa wata balarabiya mai kyau baki ganta ba..?
Amina jin gulma yasa ta saki baki tana Fadin"Kice Wlh..?wacece tana ina..!?
Hanne tace"Tana Dakinmu..Bamu san ko wacece ba..Hajiya ma bata ce mana komai ba..!
Amina ta mike tana jan hannu tana Fadin""muje naganta..!
Hanne ta mike tana Fadin"Ke banza batajin Hausa sai labarci..!
Amina tace"Muma mun iya..Kaifa antum ne sai mu sakar mata..!
Sai da Hanne da Hamida sukayi Dariya dukkansu suka Dumguma zuwa Dakin Sa"adatu da Sakina suka Bisu da kallo banza.
*Janafty*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*🅿️10*
Koda suka shiga Dakin sun iske Sarood na zaune gefen gado tana Danna wata karamar farar wayar Dake hannunta ta sauya kaya zuwa Saukakkan riga ta larabawa Sannan mayafin kanta ya zame kadan wanda ya bama Gashinta Daman bayyana har gadon bayanta.
Amina Sakin baki tayi tana ganin Tsabar kyau da zati ita kuma Sarood tana ganinsu ta washe bakinta Hakoranta Farare suka bayanna Ta gane Hanne Hamida da Amina ne bata gane ba ammh ai tasan Kannen Umar ne,Hannu ta mika musu alaman su matso kusa da ita Lokaci Daya tana Sauko da Tattausasun Fararan Kafafunta a saman Cafet din Dakin kafarta kamar ta jaririn da aka Haifa yau bai taba taka kasa ba.
Kamar masu neman gafara haka suka buga Layi agabanta bayan ta saka Hannunta Zara zara da yaji Jan kinshin Larabawa ta matsar da Farantin da Hanne ta kawo mata Fankwasau kuma tacida yawa Saboda mai gishiri akayi.
Daya bayan Daya ta fara tambayansu Sunayensu cikin Harshen labarci wanda sai ma sun Dage suke iya gane abunda take fadi,Amina ce karshen Fadamata Sunanta Lokaci Daya tana mika mata Hannunta alamun musabaha.
Sarood bata da bakunta gata da Sakewa nan da nan ta karbe hannun Amina Cikin Fara"arta,Amina taji hannu kamar auduga batasan sanda tace"Jar uba..Kun ji hannunta kamar Auduga .?ina ga tunda aka Haifeta bata taba wani aiki ba..?kayya sannan Hanne kunga gashinta mai kyau ce Wlh ta Burgeni..!
Har acikin Ranta ta kejin Sarood din ta kwanta mata Har tana Ji dama ace itace matar Ya D'anmalam din da wannan Banzar Sakinar.
Jin abunda Amina tace ne yasa suka rika bata Hannu Daya bayan Daya alamun musabaha su ba gane ma mganar suke ba in tayi musu mgana sai dai su daga kai Amina ce take ji kuma bazata taba nuna tasan ma tana ji ba Amina bayan Baba Mallam ba wanda yasan Wacece Amina A zahirinta.
Tasata sukayi kamar sun samu Tibi suna kallon Duka motsinta Sai dai ta kallesu ta Murmusa Amina ta Raba gefen kunnen Hanne tana Fadin"Hala Budurwansa ne..?
Hanne tace"Kai..Bana Tunani ko kila Diyar abokin Baba mallam ne Dake chan Madina .!
Hamida tace"Zata iya yiyuwa haka din ne..Kila tana so tazo taga kasarmu shiyasa ta biyosu..!
Da haka suka bar mganar Musun ammh acikin ran Amina Tana Tunanin haka kurum sai yazo da ita..?da wata akasa.
Basu da Niyyar Fita sai Hirarsu sukeyi sai dai ta kallesu tunda baji take yi ba, basai ga ya Abida tashigo ba, Amina na ganinta ta kyabe baki a hankali Tace"Ga uwar iyayi ta shigo..Uwar sa ido..!
Ai bata gama mgana ba ta Rike kugunta Tana Fadin"Ji yaran nan..Uban me kuke yi..?kun wani zo kun zauna kun sakata gaba sai kace kuna jin abunda take cewa..?
Hanne ce tace"Mu fa ba Damunta muke yi ba..Muna Hirarmu ne muna kallonta..!
Abida ta saki Tsaki kafin tace"To ku tashi ku fita ku barta ta Sake..Kauyawa kawai..!
Dole suka tashi Amina ta Zumbura baki tana kunkuni fadi take"Mu ba kauyawa bane..Kema ai ita kika zo kallon..!
Tana ganinta sanda take mganganun Yasa tace"Ke Amina da wa kike..?
Amina tace"Ni nayi mgana ne..?
Hanne don Allah me nace..?
Tafada tana gwalo idonta dukkansu suka Hada baki wajen Fadin"Bafa tace komai ba ya Abida..!
Kwafa tayi kafin tatasasu suka bar Dakin ita kuma Sarood sai kallonsu take tana Mirmishi..
Koda suka fito falo ba su Sakina sun koma Shashen Anty Amarya Amina tayi Tsalle ta Dire kan kujera ya Aisha Dake gefe ta kalleta da Sauri tace"yi hakuri ya Aisha..!
Tana kunshe bakinta ganin yadda take Hararanta Fitowar Hajiya yasa Amina ta Mike Zaune tana Fadin"Hajiya ina yini..!
Hajiya tace"Mamah..yaushe kika zo..?
Amina tace"Ban dade da zuwa ba..!.
Hajiya tace"naga zuwan Hamida tun dazu nace kina ina tace kina gida..Sanda su yaya suka zo ma na Tambayeki..!
Amina kanta na kasa tace"Gani nazo Hajiya Lokacin kina Daki ne..!
Hajiya tace"Barka da zuwa Mamah..!
Kafin ta juya tana Kallon Abida Lokaci Daya tana Fadin"Sakina ta koma wajen Amarya ne..?
Ta daga mata kai tana fadin"Sun tafi tace wai in kin fito ace ta wuce kanta ke ciwo zataje ta kwanta..!
Hajiya bata Damu ba ta juya tana Fadi "Hanne ku zo ku karbi Sako ku kaima su Hajiya uwa..!
Daga haka ta shige Ciki Hanne Tajeta karbo Sakon Turaran wutan Har ta juya ta Dawo tana Fadin"Hajiya ina nasu mamanmu..?
Hajiya tace"Yanzu na basu da suka shigo yi ma D'anmallam barka da zuwa. !
Jin haka yasa ta fita zuwa falon tace ma su Amina su taso suje Amina Kirkiri tace ba inda zataje Dole Hanne da Hamida suka fita Shashen Hajiya uwa suka fara zuwa suka kaimata Tana ta godiya sai wajen Haj.Nasara itama tana godiya tana cewa ace ma Hajiya sai ta shigo Shashen Anty Amarya kuwa tana ciki ita da Sakina Ya Sadiya suka bama Sakon sukayi Fitowarsu suka koma Shashen Hajiya suna Hiransu Abida ta shiga Kitchen tana soya kaza Ya Aisha kuma ta koma Dakin Hajiya tana gyara mata sai su kadai afalon suna ta Hayaniya.
Amina ce ta kalli Hanne kafin tace"Wai ni banga ya D'anmalam din ba..?ko yana gidansa ne chan kofar arewa..?
Hanne tace"A"a yana nan gidan..Tun Safe Dakin su ya Nazem aka gyaramai ya yi wanka ya huta..yanzu haka yana masallaci tare da mallam sai Dare zasu wuce gidansu in ji Hajiya..!
Amina ta gyada kai kafin tace"Shi nazo gani gashi ban ganshi ba..!
Hanne tace"Zai shigo ki tsaya don Allah..!
Hamida tace"Nima ina so na gansa..Na dade ban gansa ba wlh Amina mu kara jira mu gani..!
Amina batace komai ba sai chan ta rage murya tana Fadin"Ku jinin al"adarku sau nawa kuka gani..?
Hanne ta kalli Hamida itama ta kalleta kafin tace"Ni tun na Farkon nan ban kara gani ba..!
Hamida tace"Ni ya kara zuwar min Sau Daya wanchan watan..!
Amina tayi tagumi tace"Hanne bamu da lafiya ne..?nima fa daga sau dayan nan fa ban kara gani ba..!
Na tambayi mamanmu tace kada mu damu zai zo haka yake yi..!
Hanne tace"Eh mana kin manta ya Sayyadi yayi mana a islamiya yace in yazo na farko kafin ya kara zuwa ana Daukan Lokaci..!
Amina ta kalli Kirjin Hanne ta kalli nata ta kalli na Hamida kafin ta Bushe Da Dariya Hanne ta Daga mata Duka tana Fadin"Kefa baki jin mgana..!
Amina na nuna kirjin Hamida tana Fadin"Hamida zan siya miki Breziya in muka gani a hanyar makaranta..!
Tafada tana Dariya Hamida ta ji kunya ta juya Baya Saboda ita Nonuwanta sunfara girma har ana gani A hijabi Saboda yanayin Jikinta..sabanin Amina da kirgan Dangi makale a kirji har gwara Hanne ma sun Fara bayyana.
Hanne tace"to ai sa"adatu ma tana Saka abunta..!
Amina tace"ita wannan ai ko uwarta ta siya mata mara kunya ce..!
Na taba gani a Littafin Haussa fa ance maza na son Nono shine in nayi sallah nake Rokon Allah ya bani kada yazo banidashi nayi aure mijina ya karomin Kishiya..!
Gabadayansu baki suka rike suna kallonta kafin su fara kallon kofar Dakin Hajiya ganin ba kowa yasa suka Fixgeta sai Chan lungun Falon atare suka Hada baki wajen fadin"Amina daman baki daina karatun Littafan Hausanan ba ko..?
In akaji labari fa..?
Amina na Dariya tace"Dilla kun cika Tsoro..!
Hanne tace"Na Dauka da ya Sayyadi ya kamaki a makaranta ya Dakeki kin daina..!
Amina ta yi wata Dariya kafin tace"Aminene ikon Allah..Ni duka ai baya sani na fasa abunda nayi niyya..In ma zaku daina wannan Tsoron ku daina ku zo kuma ku fara Wlh Dadi kunga Love..?nace ni ko su ya Zulahait da zasu aure basa wannan Love din da mazajensu koda yake ko waya fa basu da ita ta ina zasu ma kirasu" ta karishe fada tana yar Dariya Hanne tace"Allah ya shiryeki Amina..'
Tace Ameen Hamida kuma ta kasa mgana Domin ta gama Sarewa da Lamarin Amina girma kawai yake karawa.
Suna nan har shidda na yammah Amina ta gaji ta mike tana cema Hamida"Kinga tafiyata in ke baki tashi ba..!
Hamida ta mike tana Fadin"Mu bari bayan mangariba mu tafi kinga yanzu kila su ya jafar suna waje zai mana Fada..!
Amina tace"Allah yasa yankamuzai yi ba Fada ba sai na tafi..!
Hanne tasan bazata tsaya ba yasa taje ta Dauko hijabinta Dakin Hajiya suka je suka mata sallama tana bakin gadonta waya na Hannunta tace"Mamah ku bari Abida ta gama Pepe Chicken din nan mana ta Dibar muku..!
Amina na jin haka tace"Hajiya ko Tafashasshe ne abamu hakanan..!
Dariya suka mata Har da Hajiya kafin tace"Kuje Abida ta baku..!
Amina tace"Ya Abida taf..Hajiya sai dai in kizo da kanki dama yar aljannah ce ya Aisha ..!
Ya Aisha na Gaban wardrope din Hajiya tana gyara mata tana jinta batace komai ba Amina fa yanzu zata yabeka anjuma ta zageka tas.
Hanne tace"Allah yasa ya Abida ta jiki..!
Amina ta Zunguri kafadarta tana Fadin"Ke in ta ma taji fa..?sai nayi abunda na saba nace bada ita nake yi ba..!
Hajiya na jinsu tayi Dariya Amina manya Kafin tace"Kuje dai ku ce mata ni nace..!
Dole suka wuce Kitchen din suna Shiga tana ganinsu ta Fara masifa"me aka zo min Ehe..?ba kwa son aiki sai Ci ko..?ku fita ku bani waje bana son Iskanci..!
Amina ta kalli Hanne itama ta kalleta Hararansu tayi kafin tace"Bana son munafunci lafiya..?
Hanne tace"Hajiya ce tace ki bama su Amina nama wanda baki soya ba zasu tafi ne..!
Abida tace"Bazan bayar ba..Kada Allah yasa su tsaya din..Ke Hamida ki bari na gama in Amina zata tafi ki barta tatafi din..
Sai na gama Duka sannan Wlh zan baku. !
Kyam suka tsaya suna kallonta ta juya baya ta cigaba da aikinta ganin sunki Tafiya yasa ta Juyo tana Fadin"Kuka tsayamin aka..?zaku wuce ko kuwa..?
Amina ta fara juyawa Hanne zatayi mgana ta rike hannunta kofar Kichen din suka Labe Amina na fadin"Wlh sai na Sata tunda taki bani da lalama..!
Basu ma yi mamaki ba Domin Amina bata Fadar abunda bazata iya shi ba.
Hijabinta ta Tattare sai da ta bari hankalin ya Abida na wajen juya Naman dake cikin kasko ta fara Sanda ta shiga kitchen din sai ji tayi kawai an Dumbuzu Naman Daya Rage bata soya ba har Garin Sauri tana Zubar da wani a kasa Abida ta Juyo taga sanda Amina ta Ruga Su Hanne suka mara mata baya suna Dariya fitowa tayi da Gudu da Abun suya a hannunta yana Digan mai tana Fadin"Kai kai..Ni yaranan zaku raina ko..?wlh na kama yarinya sai na Lahira yafi ta jin Dadi barin ma Amina zaki gane dani kike..!.abun ya bata mata rai kamar ita yaran nan suka ma haka su ko juyowa ma basuyi ba Hanyar Fita Amina ta kama Tana Fadin"Ku ka tsaya wlh ta Sauke Haushina Akan ku..!
Ta kawo bakin kofar kenan tana juya baya bata ma kallon gabanta Daidai Lokacin aka Bude kofar Shashen na Hajiya Lokaci Daya da shigowa Amina bata sani ba da karfinta ta juyo Hannunta Damke da naman data Diba sai Gaf taji tayi karo da Mutum ammh kamar Da Icce taci karo Saboda ko gizau na Tsayen bai yi ba sai ma itace ta koma da baya Kamar zata Kifa da Azama da wani Zafin Nama ya ciro Hannunsa guda Daya daga Cikin Aljihun bakin wandon Dake Jikinsa ya Rike hannunta Cikin Tsausatsayi wanda Naman ke Ciki gabadaya maikon da ruwan Tafashen ya gama Mamaye hannunsa..
Ammh duk da haka bai saketa ba sai da ya Dagota da hannu Dayan nan ta Tsaya da Kafafunta Idanuwanta na Runtse domin ta gama Sadakarwa ta Fadi Numfashi take saukewa shima da azama ya saki hannunta yana Bin Hannunsa da kallo ransa nan take ya baci kyamyami garesa Har tsikar Jikinsa na tashi.
Cikin Tatattausan Muryansa ammah Cikin Fada yake fadin"Ke wata irin mara Hankali ce..?kina tafiya ba natsuwa kamar wata namiji..?
Muryan daga sama ta jita sannan kafin ta gama Daidaita Natsuwarta ta Bude Dara daran idanuwanta Daga baya taji Hanne na Fadin"Sannu da zuwa Ya D'anmalam..!
D'ANMALAM..!
DAM gabanta ya fadi kenan da Ya D'anmallam ta ci karo bata sani ba..
Da sauri ta Bude idonta ta Sauke akansa alokacin bama ita yake kallo ba Hannunsa na Sama kamar wanda kashi ya taba yana kallon Hanne yace"Hannatu meke damun ku..?wani irin wasan banza ne wannan..?
Yafada har Giransa na sama yana Hadewa waje Daya ya Abida Daga Kofar Kicthen ranta fes tasan sai ya D'anmallam ya chasa mata su sosai.
Amina batasan ta saki baki tana kallonsa ba Domin kamar mayen karfe na janta haka taji ta kasa Daina kallonsa Duk da bai juyo ma gareta ba Kyau da zati kawai da wani Haiba take gani da Hange da kuma wani Dattako da wajen Baba Mallan kadai tasan dashi.
Hamida jin Hanne tace ya D'anmallan yasa ta gaisheshi ya amsa bai Damu Daya kalleta ba Yasan dai Cikin yaran gidan ne saboda ai ba Duka suka taso agabansa ba.
Hannunsa ya kallah kafin ya Yamutsa Fuska yace"Miye wanna..?wacece ta shafamin wannan kazantar a Hannuna..?
Yafada yana kara kyamatar hannunsa nasa Amina Girman idonta ta Bude tana kara kallonsa Daga sama har ksa Yana Sanye da Jallabiya mai Ruwan Madara,Da bakin wando sai kansa Sanye da Hula irin ta yan Saudiya karama iyakarta rabin kan nasa Fuskarsa tayi wani Haske mai Annuri sosai da Zati Lokaci Daya.
Abida na jin abunda yace ta kariso Tana Fadin"Ya D'anmallan gwara da Allah ya kawoka..Nama suka zo suka Satarmin Hajiya ta sakani suya..!
Cikin mamaki yace"Nama..?
Da sauri tace"Eh ga shugabarsu na..Amina wlh yaya har tana Zubarda Naman a kitchen bata da natsuwa kamar yadda ka Fada kazamar ce..!
Tafada tana nuna Amina wacce ke Tsaye tana kallonsa ga Hannunta Dunkule da Naman data Sato din
Shi ko da suka ci karo ya Rikota bai Tsayama kallonta ba Duk azatonsa Sa"adatu ne ko cikin yaran gidan sai yana kallonta yaci gabansa yayi wani Dif saboda yadda Fuskarta ta Tsaya aransa yana so ya Tuna mai irinta Saboda Tsabar kwarjinsa akaron Farko Amina taji ta kasa Jurre kallon Cikin Idanuwansa Sai da ta sadda kanta gabanta na Fadi haka kurum taji Wani tsaro karon Farko da kunyar da Amina bata taba jin irinta ba.
Ganin yadda ya Dawo da kallonsa kan Abida ne Cikin Alamun Tambaya.
"Amina...?
Da sauri tace"Amina..Diyar Baba Sa"idu ne..Yar wajen yaya ce fa..!
Ga Hamida ma itama duka na gidan Baba Sa"idu ne..!
Sai alokacin ya kara kallonta yasan wannan Fuskar matar dayake ganin kimarta bayan Hajiya babba ne wato yaya.
Shi bai ma san tana da Wata karamar yarinya ba ya Dauka Jawaad ne Autanta Saboda in yazo yana ganinsa Tare da Baba Sa"idu shi bayansu Jadwa sai su Jaleela yaran nan duk ba Saninsu yayi ba.
Hayaniya ce bai so sannan hannunsa kyamkyami ya ishesa yasa yace"Nama kuke sata agidan Baba Mallan..?
Yafada Cikin Sanyinsa a karon Farko Hamida da Hanne basu Dauki Jidalin Amina ba suka Hada baki Wajen fadin"Bamu bane..Wlh Amina ce ta Shiga ta Dauko..!
Suka fada suna Nunata Amina taji kamar kasa ta Bude ta shige saboda kunya tana jin idanuwansa akanta Ga hannunta Dauke da Nama Ruwan maiko na Diga da Sauri ya kauda kai ya wuce da Hanzarinsa cikin Natsuwa
"Ita mace da natsuwa aka santa..Hakane ke bambamta ta da Namiji..Sannan kazanta ko a addini bashi da kyau Hadisi ne guda Ko Sallah bata cika sai da Tsabta..!
Bai ko kara kallonsu ba ya shiga Kitchen din ya tara hannunsa a sink ya wanke har da saka Omo yana jin karnin Naman a Hannunsa karamin Tsaki yaja kafin yace"Kazamar yarinya kawai..!
Suna nan Tsaye kamar an Dasasu ya Fito Abida ssa Dariya take musu suna ganin ya fito Hanne taja hannu Hamida suka fice da Sauri ammh Amina ta kasa gaba ta kasa baya.
Kunya da wani abu data kasa sanin Dalili taji wani abu sunan yau an kunyatata Duk da gaban Hanne da Hamida ne an kirata mai Satar nama kuma kazama kuma mara natsuwa har ana Dangantata da Namiji wadandan kalmomin sun taimaka wajen sata ta cigaba da Tsayuwa a wajen Saboda ji tayi kafafuwanta sun kasa Daukanta.
Tana tsaye a wajen taji yana Tambayan Abida Hajiya tace tana ciki Tana kuma jin Sanda ya fara taku zuwa Dakin Hajiya yana Shigewa Abida ta saka Dariya tana Fadin"Bera mai satan Nama..!.
Sai ga Idanuwam Amina sun ciko da kwallah suna Shirin zubowa.
Su hamida sun fara gaba suna juyowa suka ga ba Amina Hanne tace"Amina bata taho ba..?
Da sauri suka juya suka koma suna Shigowa falon daidai Yana fitowa Daga Dakin Hajiya shi da Aisha yana mata mgana ganin haka yasa suka kasa ma Amina mgana shi kan yama manta dasu sam Aisha Dakin da Sarood take ta shiga ba jimawa sai gata ta dawo tare da ita tana ganinsa ta Nufesa kamar zata Rumgumesa sai ya rike hannuwanta Hanne nata Zungurin Amina duk son gulmarta wannan karom bata Dago ba Domin har alokacin bata gama Dawowa daidai ba.
Mgana suke da harshen Larabci Cikin kwarewar da in ba ka iya Sosai ba bazaka gane komai ba, ba Dadewa ya Dauko waya daga gaban Aljihun jallabiyansa ya bata Sannan ya Saki hannunta Tana Sakin mai kayattacen Mirmishi yana Shirin juyowa Hanne ta Fizgo hannun Amina suka jata suka fita da sauri har suna Bugo kofar Falon da sai ya da maida Hankalinsa wajen.
Ganin bai ga kowa ba yasa ya barsa shima Ficewar yayi suna ganinsa labewa sukayi a wajen Bayan Shashen Hajiya,sai da ya wuce suka Fito Hanne ta kalli yadda Amina tayi zata Rantse da Allah bata taba ganinta Cikin wannan Halin ba
Da Sauri tace"Amina lafiya..?ko wai Fadar sunanki da mukayi..?
Da Sauri Hamida tace"Wlh shi ba irin ya jafar bane..Kinga idonsa kana mai karya sai ya ganeka..!
Amina bata ma Tsaya bi ta kansu ba Naman Dake hannunta ta saki ya Zube a kasa,kawai ta kada kai ta wuce Suka Bita da kallon mamaki suna kwala mata Kira bata amasasu ba.
Suka fita har suna Hadawa da gudu ganin ana ta Haraman Alwala Domin lokacin Sallah ya kusa.
Amina bata tsaya musu ba Har suka iso gidan Ya Zeena na bakin Famfo tana wanki mamanmu na Shimfida Darduma kofar Dakinta Amina ta shigo ba sallama Ya Zeenatu ta dago tana Fadin"In kika gyara Halinki ai ke baki cika Amina ba..ki rika shigowa gida kamar Kafira..!
Mara natsuwa kawai..!
Amina ta jita ta kuma ji sanda Mamanmu kr fadin"Zeenatu bana son haka..?ban ce ki daina shiga Harkan Amina ba..,!?
Ita dai sai da ta danganta da kan gadonta taci kukan data ke rikewa ya zo mata Kamar wacce aka Daketa ta Fara kuka tana jin Hanne da Hamida akanta suna tambayanta tayi kamar bata jisu ba.
Kuma taji sanda ya Zulaiha ta shigo ita da ya Zeena ganin Amina na kuka yasa suka tambayesu sanin halinta ba kasafai take da Saurin kuka ba.
Hamida ta fara maida yar da akayi tazo wajen bayanin abunda Danmalan yace Amina ta Dago afusace tana Fadin"Eh yace min Kazama mara natsuwa ko..?haka kika so kice munafuka..!
Tafada tana Sakarmata Jajayen idanuwanta da sai da ya basu Tsoro.
Sai a ka rasa mai mata mgana har ta Fice Fuu Daga Dakin Zeenatu ta kwashe Dadariya tana Fadin"Ba Duka ba Zagi ashe mgana na Ladabtar da Amina bansani ba..?
Hamida dai da Hanne sun kasa mgana ajikinsu yayi sanyi.
Yasa suka fita suka fara shirin yin alwala Jam'i suka bi Amina na Dakin Mamanmu ta Dunkule kan kujera ko Sallar batayi ba tana jinsu a Tsakar gida suna Fadin yau Yaya Danmalan ya bada Sallar Itama ai taji Sanyayyar Muryansa yana Karatu Karatun da Har ita tayi karya tace bai natsar da zuciyarta ba tana jin Yaya na Fadin"Allah Sarki mun yi kewar karatun D'anmallam..!
Daman in yana nan shike bada Salla har ya koma..!
Amina aranta tana ayyana yadda yau yaci Zarafinta sai taji gabadaya Duhu ya mamaye saninta dashi an sha ce mata mara natsuwa da kazanta ammh yau sai abunda ya Zafeta fiye da koyaushe.
Tana jin sanda Hanne ta ke ma su Mamanmu sallama tatafi gida sai Alokacin Amina tatashi tayi sallar Tana Tura baki.
Ganin yan jidalin na kusa yasa bama wanda ya sake bi ta kanta.
Sai dai tun Safe Hanne ta Dawo Lokacin Amina ta dan Huce Tana zaune bisa gadonta ita da Hamida alokacin Ya Zulaihat bata Dakin ya Zeena na makaranta.
Hanne tace"kunsan wani abu..?
Hamida ce ta girgiza kai Amina kuwa Yamutsa Fuska tayi kawai duk da Hannen na kusa da ita ne.
Hanne tace"Ashe balarabiyar nan mai kyau dinan da ya D'anmallan yazo da ita matarsa ce..!?
Amina ta Zaro ido kafin ta mike tana Fadin"ki bari don Allah Hanne..?
Hamida tace"Nima naji Mamanmu da yaya suna mgana da safe..Wai Aba ya Fada musu jiya da Daddare..!
Hanne tace"Kwarai muma jiya Mallam ya taramu har da ita ya fada mana aka gabatar da ita acikin mu Ashe Diyar dai abokin Baba mallam ne na Madina ya aura ma Ya D'anmallan diyar tasa achan Madinan.!
Amina tace"Ya su Sa"adatu sukayi..?Ina Anty Sakinar..!
Hanne tace"Abun mamaki basu nuna komai ba Anty Amarya tafi kowa ma karban Abun tatashi ta Rumgume Anty Sarood din agaban kowa tana mata maraba..!
Amina tace"Jar uba..Wlh na karya ne..Wannan matar din..?
Hanne tace"Bakisan wani abu bama..Ta kwace ta Daga Shashenmu tace ma Hajiya ita ke Saukan Anty Sakina to yanzu bata Sauya ba ita zata Sauki Anty Sarood jiya ai shashenta ta kwana..Sai da Safen nan suka wuce gidansu kuma Anty Amaryan ta rakasu Mallan yace taje..!
Amina sam Labarin bai kwanta mata Baki ta Tabe kafin tace"Uhmm!
Daganan bata kara mgana ba aranta bata yarda don Allah tayi ba Matar da ko su Mamanmu suna Fadin Rashin Kirkinta sun ce ko Aba bata cika mgana Dashi ba tana jin Haushinsa Sabida Hajiya da Baba Malam.
Tundaga Ranar Amina bata kara yarda ta koma gidansu Hanne ba Duk kuwa da Tasan ya Danmallan yana gidansa ammh ai kusan nan anguwan yake zama Saboda bada sallah haka kurum taji batason su kara Haduwa Ya riga ya gama da ita tunda ya ce mata kazama kuma mara natsuwa bawai ta tsaneshi bane sai dai Acikin Ranta bai burgeta ba,duk da baya Duka ammh kuma yana mganar da zai saka ka kwana kana kuka aran Amina tasa masu sanyin Halin nan ba masu Kirki bane to Danmalam yana Daga cikinsu.
0 comments:
Post a Comment