Suna shiga lobby ya waiwaya ya dubeshi,zuwa sannan fuskarsa harta fara yin ja,musamman hancinsa,abinka da farar fata
"Ka kiramin dukka wadanda muka shigo wajen nan tare,su sameni a living room now!" Yana fadin haka ya qara sauri ya wuce zuwa elevator.
Da sauri matashin daya bari zaune cikin living room din ya daga kai yana dubansa,yasan yana da matuqar zafi da rashin fara'a,amma yana saurin gane canzawarsa idan wani abun ya sameshi,kamar dai yanzun daya kasa zama,sai iska mai zafi da yake furzawarwa daga bakinsa
"What's going on?" Ya jefa masa tambayar yana binsa da kallo,kai ya girgiza masa ba tare da ya iya ce masa komai ba
"Come on please,take it easy mana man" yayi maganar yana sauke qafafunsa dake harde qasa,tare da yunqurin cooling temper din da hanga cikin idanunsa,dai dai lokacin da aka nema izinin shigowa living room din.
Dukkansu suka dinga shigowa daya bayan daya,kowanne a yanzu wasu kayanne a jikinsa ba baqar suit din dazu ba,da alama kowanne yana dakinsa ne yayi shirin kwanciya. Da wani zazzafan kallo ya bisu,dakin ya dauki shiru na wasu yan daqiqu,sannan ya buda bakinsa da zuzzurfar muryarsa data qara nauyi saboda bacin rai
"i regard one of you was betrayal" yayi furucin da gasken gaske,babu alamun sassauci ko wasa ko kadan saman fuskarsa. Tsit dakin yayi,jikin kowa ya amsa,aka rasa me motsawa bare ya bashi amsa
"Who told her I was there?" Dif dakin ya sakeyi,yayin da yake sake bin fuskarsu da kallo daya bayan daya,yana hucin bacin rai yana fita daga fuskarsa,ya dauke kansa daga dubansu,ya maida hannayensa cikin aljihun wandonsa ya soma takawa a hankali zuwa gaba
"I will not repeat my question....." Ya fada bayan ya basu baya
"Nine" daya daga cikinsu dake rakube acan gefe ya fada,zufa tayi wani irin wankeshi,yasan sakamakonsa,babbar asarar ce zata sameshi wadda ba lallai ya maida gurbinta,sai ta ninka abinda ya samu daga gareta bayan dogon lallashin data masa ta ciyo kansa ya shaida mata sun sauka a bristol din.
A nutse ya waiwayo ya kuma zuba masa idanu,zuciyarsa tana tafasa
"All this while......." Sai kuma ya kasa qarasawa saboda bacin ran dake sake taso masa idan ya tuna yadda ta rungumeshi,yanajin kamar ya zauna ya daye fatar wajen,ko ya maido da lokacin ya goge faruwar hakan
"You're fired!" Ya fada kawai bayan ya duqa ya dauki wayarsa yana nufar qofa
"Anyone who deliberately does what he has done deserves to be fired from his job" statement dinsa na qarshe kenan,yasa kai ya fice daga dakin ba tare daya sake waiwayar kowa a cikinsu ba.
A nutse saurayin SAJJAD ya miqe yabi bayansa,yana shiga dakin shima yana sanya qafarsa
"Me kake aikatawa ne TAUFEEQ?,firing a person from work is not a joke"
"Did I tell you I was kidding? I really mean what I said,i dismissed him,idan kuna tunanin wasa ne na ganshi cikin maaikatana gobe" yayi maganar yana bude fridge,ya cire ruwa me sanyi ya balle murfin gorar yana tuttulawa cikinsa ba tare daya nema koda cup ba.
Da kallo SAJJAD ya bishi,tabbas shan ruwa me sanyi sam ba dabi'ar taufeeq din bane,idan kaga hakan ya faru to alamu ne na tsananin bacin ransa,ko meye zai gaya masa a yanzun bazaiyi tasiri ba,sai yaja qaramin tsaki
"since that's how you choose to be,sai kaci gaba,sai da safe"
"Ka sallamesu ka rufemin qofofina" ya fada masa a taqaice yana cillar da robar ruwan gefe,ko a jikinsa na fushin da sajjad din yayi,bazaita zama bai takawa yarinyar burki ba ita da duk wanda yake bata information na wanzuwarsa a waje ba,tabbas muddin akaci gaba da haka to babu shakka watarana zata zubar masa da mutunci kima da kuma martabarsa,tunda har ta farajin takai hannu jikinsa,the worst part ma a waje na jama'a irin wannan,daya daga cikin dalilan da yasa yake sake tsanar mata a ransa,zasu iya yin komai.......zasu iya aikata komai da gajeran tunani da qwaqwalwarsu.
Qarar wayarsa ce ta dakatar dashi,ya fidda hannayensa daga aljihunsa ya taka a hankali zuwa inda ya ajjiye wayar,kiran dake shigowa ta cikin wayar me muhimmanci ne,ya ajjiyeta ne kawai saboda ire iren kira masu muhimmancin da suka shafi family dinsa.
Wani abun mamaki qaramin murmushin daya ratsa murtukekkiyar fuskarsa har labbansa suka motsa,wani irin sirrintaccen kyau ya bayyana kan fuskarsa,ya dauki wayar yana daga kiran
"Daddy" siririyar muryar qaramar yarinyar ta bayyana cikin wayar,ta kuma ratsa kunnensa,ya lumshe idanunsa ya budesu a hankali,yana jin duk wata damuwa da bacin ransa suna narkewa
"Daddy's angel" ya maida mata a tausashe
"Wai da gaske kazo?"
"Ki fara gaisheni tukunna" ya gyara mata bayan ya bude dukka idanunsa yana kallon gabansa
"Good evening daddy"
"That's my girl......kina lafiya?"
"Lafiya lau daddy,da gaske kazo?" Gyara zamansa yayi ya zauna sosai sannan ya amsa mata kanshi tsaye,don bai saba yi mata qarya ba,bare ma kwata kwata shi din yana cikin jerin mutanen da komai tsanani komai wuya basa barinsa yayi qarya,tun daga yarinya har kawo yau,komai girman situation din da za'a shiga
"Na dawo angel,but wani aiki ya riqe daddynki,i really miss you, I can't wait to see you,but in sha Allah gobe komai dare,you will be next to your daddy,please apologize me" dariya ta qyalqyale dashi cikin nishadi da siririyar muryarta sannan tace
"Apology accepted daddy"
"Thank you princess" ya fada cikin nuna kulawa.
Sosai zakayi mamakin yadda ya saki jiki yana hira da ita cikin kulawa,a hankali kuma bacin ransa yana narkewa,ita din duniyarsa ce,wata qwayar halitta guda daya dake da mazaunin komai na rayuwarsa,baya wasa da dukka abinda ya shafeta,matsayinta da qaunarta a ransa ta zarta komai. Bugu da qari lalurar dake tattare da ita tana sake sanya masa wata qaunar yarinyar tare da mugun tausayinta,tattalinta da kuma bata dukkan kulawar daya kamata,idan ba tayi mugun takewa ba,baya bari ko kadan yayi nisa da ita.
*_F R I D A Y_*
K'arfe d'aya da rabi na rana suka fito daga town hall meeting,wanda ya sake maida kowanne ma'aikaci cikin nutsuwarsa,ya kuma girgiza zukatan duka wasu marasa gaskiya. Iya abinda aka tattauna a gurin kawai tsaiwarsa da yadda ya tsara abubuwa ya tabbatarwa da kowa ba wasa yazo yi ba,daga nan suka wuce sallar juma'a da dukkan Wani ma'aikaci musulmi,sannan ya sallami kowa da zazzafan gargadin haduwarsu da fara aiwatar da komai ranar litinin.
Suit coat dinsa ya cire yana ratayeta,sannan ya jawo kujerarsa ya zauna bayan ya nade hannun rigarsa zuwa sama kadan,yakai hannu ya dauki drink din da jibril ya ajjiye masa yana duban mutum biyun dake zaune,ya tsaya ya saurari dayan ya sallameshi,sannan ya maida dubansa ga sajjad
"Who is my new president?"
"she didn't come" komawa yayi baya yayi relaxing jikin kujerar,idanunsa a lumshe yana jin kansa ya dauki caji da yawa
"Is she a female?"
"Eh" ya amsa masa yana kallonsa,don yasan anzo gurin,idanunsa ya bude tarwai,ya zubesu kan fuskar sajjad
"A female president? why?"
"it's dad's choice" shuru ya danyi,kamar bazai sake magana ba,sajjad ya kafeshi da ido,sai ya janye nasa idanun,ya janyo system dinsa yana budewa
"If she is not ready to work with us, we will replace her with someone else,let her know,dole ta zama serious,ba zamu dinga biyanta tana abinda taga dama ba"
"Za'a gaya mata,but wannan dogon statement din yayi yawa sir" ya fada yana bincika jerin sunaye da address phone number da email address na ma'aikatan dake hannunsa,duk wasu ayyukan ba nasa bane basa a wuyansa,amma sanin hali ya sanya abba ya hadashi dashi,yace kuma ya dinga zama by his side lokaci lokaci,yana monitoring wasu abubuwan,yasan taufeeq din da zafin kai qwarai.
Bazai iya challenging daddy din ba,amma tabbas da ya sauya ta da namiji,matsayine da yake ganin mace sam ba zata iya riqeshi ba,koda zata iya din ma,zuciyarsa bata basu wannan amincin na riqe babban matsayi har haka ba,rashin amanarsu kadai ya sanya baya qaunar wani hulda a tsakaninsu,bare har akai ga zama na aiki da musayen ideas.
Kwata kwata ma basu cancanci dukka wata mu'amala data qunshi aminci ba,yana musu kallon wata halitta ta daban,KUDI shine abinda sukafi bawa daraja kima mutunci da muhimmanci,zaifi kyau su tsaya iya nan.
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*H U G U M A*
_*TABARMAR ƘASHI*_💔
*Arewabooks: huguma*
https://arewabooks.com/u/huguma
Page 12
Tunda yaa zaid ya sauketa a jiyan abun yaqi barin ranta,kusan zata iya cewa dashi ta kwana,wanda ya haifar mata da wani irin bacci mara dadi,da mafarkai barkatai wadanda suka shafi wasu al'amura dake da alaqa da rayuwarta. Cikin dare ciwon kai ya saukar mata,wannan ya sabbaba mata makara a sallar asuba,kuma ko bayan tayi sallar wani baccin ya sake daukarta,sam ta mance da batun fara zuwa aikinta a yau,wanda dama zataje ne kawai don ta fara karantar yanayin yadda abubuwan suke.
Kwata kwata bata tashi farkawa ba sai qarfe goma na safe,ta tashi da sauqin ciwon kan,ta miqe daga gadon tana shirin shiga toilet akayi knocking qofarta.
Maama ce ta shigo,cikin kamalar nan tata wadda kusan a nan da wajen abba sãahar din ta gadota
"Kina lafiya kuwa?" Tayi mata tambayar tana kallon qwayar idanunta tare da fatan ba damuwarta ce ta sake motsawa ba
"Ina kwana maama" ta maida mata da gaisuwa
"Lafiya qalau,kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillah,na dan tashi da ciwon kaine,bayan asuba kuma saina samu bacci"
"Subhanallah,Allah ya sawwaqe,ko zaki asibiti?,banason zama da ciwo" ta fada cikin damuwa,saboda tasan yanayin ciwon kan sãahar din,baya yi mata da sauqi idan ya tashi,saboda ciwo ne da ya samo asali ta Wani dalili,ba hakanan ta sameshi ba
"Alhamdulillah naji sauqi yanzu,wanka kawai zanyi na sauko"
"To alhmdlh,yayanki ne ya dameni da waya tun dazu,yace yana kiran wayarki bata shiga ba"
"Ya muhyi" ta fada kai tsaye,tasan yanason jin ta fita aikinne ko kuwa
"Zan kirashi idan na fito a wanka"
"To madalla,yayi" saita juya tana shirin fita
"Abbanku ya fita,amma shima ya tambaya kafin ya fita din"
"Zan kirashi shima" ta sake fada tana yunqurin zare rigar baccin jikinta
"Don Allah maama,baba rabi ta kawomin ruwan dumi a cup"
"Shikenan" ta amsa tana qarasa fita a dakin.
Da ruwa me dumi sosai tayi wankan nata,ta fito fatarta na wani irin sulbi da qamshi daya hade da tururin ruwan dumin da tayi wankan,ta fito ta tsaya gaban mudubi tana kallon fuskarta dake subul kamar ta jariri,babu tabo babu komai,sai tsananin taushi da sulbi da take sakeyi,alamun product din da take amfani dashi ya karbeta. Tasa hannu ta dauki mug din ruwan dumin da baaba rabi ta kawo mata ta aje ta soma kurba a hankali,saboda muhimmancinsa a jiki bata skipping shansa kowacce safiya kafin taci komai,koda kuwa ta makara bata tashi da wuri ba.
Da wani irin sauri sautin marin jiya ya gilma a kunnenta,ta runtse idanu kamar a sannan abun ya faru,ta cire cup din da takai bakinta a hankali ta ajjiye saman madubin sannan ta bude idanunta tarwai tana kallon fuskarta. Tsantsar rashin sanin darajar dan adam ta tabbata ga duk mutumin da zai iya shimfida yatsunsa akan muhallin da yafi ko ina daraja a jikin dan adam,wani abu yazo ya tsaye mata a wuya,ta saka hannuwanta biyu saman kuncinta,tana tuna wani lokaci can baya daya wuce,tana tuna marukan da tasha saman fuskarta,wanda batasan iya adadinsu ba.
Sauke hannuwanta tayi taja da baya tana barin gaban madubin ganin bacin ran da bataso tana yawan ji yana qoqarin taso mata,sai ta koma gefan gadonta ta zauna tana hadiyeshi,idanunta suka sauka kan ledar siyayyarta data shigo da ita jiya,ta miqa hannu ta janyota,ta fara buda kayan ciki tana sake dubawa,bawai don batasan me ta siya din ba,a'ah tanason kore bacin ran dake taso mata ne.
Sai data shirya kayan cikin walking closet dinta sannan ta fara gyara jikinta,ta shirya kanta cikin wata sassauqar gown fara,alamu suna nuna ita din ma'abociyar son fararen abubuwa ne,musamman kayan zaman gida da qananun abubuwan amfani irin haka. Cikin qasa da awa daya ta sauko qasan riqe da system dinta tana amsa wayar afifa,ta saka system din a chargy,ta leqa ta gayawa maama ta fito wadda ke saman abun sallah zata tayar da salatud duha(sallar walaha),sannan ta nufa kitchen ta samo abinda zata iya ci.
"Barka da fitowa" baba rabi ta fada cikin girmamawa,tadan murmusa kadan,baba rabin ba zata taba daina gaisheta ba
"Ina kwana?"
"Kin tashi lafiya farar d'iya" suna ne da takan kirata dashi lokaci lokaci
"Lafiya qalau,me zan samu?" Fara bude mata abubuwan da suke dashi da safen a kitchen tayi,kusan duka ba cimarta bane,amma batason bawa kowa aiki da safen nan,ita kuma qyuyar aikin yau takeji,don haka sai ta jawo plate ta tsakuri iya abinda take ganin zata iya a plate daya,ta fice zuwa Parlor din.
Tana cin abincin kamar wasan yara ta kunna laptop din nata,gidan gaba daya ya mata shuru ba dadi,afifa bata dawo ba kwata kwata wannan satin,shi yasa takeson yara,bata rabo da dauko 'ya'yan yayyen nata,to wannan karon su fadil suna umra duka gidan,khalifa na exam,aleena tayi qanqanta don ko yayeta ba'ayi ba,ya zaid kuma ya maidasu na'eem canada,cikin satin nan shima zai bisu,dole ta zauna zaman kadaici,idan taji ta matsu da yawa kuma tabi afifa.
Sai data gama duk uzurinta sannan ta shiga ma'ajiyar saqonnin email dinta da nufin share saqonnin da suke kai ko zata ragewa computer din nauyi,har ta fara marking idanunta suka kai kan sabon saqon daya shigo mata daga MT GLOBAL COMPANY,ta dan tsaya tana tunanin inda tasan sunan,kafin daga baya hankalinta yakai kai,takai arrow din kai tayi clicking ta shiga.
Dogon tsaki taja bayan ta gama karanta abinda saqon ya qunsa,and so what don zasu canzata da wata muddin bata shiga aiki ba on Monday,ko an gaya musu aiki da su damuwarta ne?,ko basusan alfarma zatayi musu ba saboda darajar masu daraja?,cikin jin haushi ta soma rubuta musu reply na basu damar sanya watan,cikin ranta tana jin ta samu hanya mafi sauqi ma da zata sabule wannan alaqaqai din aikin,saidai tana kammala rubutawa kafin ta tura taji muryar yaa muhyi yana magana da masu aikin gidan dake harabar gidan,saita dora hannuwanta saman fuskarta tana jin ba dadi,a sanyaye tayi highlight na duka rubutu tayi cutting dinsa,ta goge email din ta sauka daga ciki,tayi shutting down na system din,dai dai lokacin ya sanyo kansa cikin parlor din.
A nutse ta amsa sallamarsa,tayi masa barka da safiya sannan ta miqe ta yiwa maama magana,ta kuma wuce kitchen ta hado masa dan abin motsa baki,ta kawo ta ajjiye masa
"Ya na ganki gida,nayita kiran wayarki kuma bakiyi picking ba,kada dai ace tun ranarki ta farko kin fada wasa da aikinki?" Yaa muhyi ya fada yana kallonta hadi da dan kada key din hannunsa.
Fuskarta ta tattare tayi alamun tausayi ta zauna daga kujerar dake gefansa
"Da ciwon kai na tashi yaa,kuma ma Allah......" Kasa qarasa masa tayi,tadan lanqwasa yatsun hannunsa
"Eheenn,Allah me?" Ya tambayeta kai tsaye yana dubanta bayan yadan tsuke fuskarsa kadan,don bayason jin wani zance sabanin wanda sukayi da ita
"Yaa ko zaka taimakamin su sauyamin position din da suka bani,bana son president din nan wallahi" ta qarashe fada tana narke murya. Ajiyar zuciya yadan sauke yana furzar da iska daga bakinsa sannan ya sake maida dubansa kanta
"Dr yana da matuqar kirki da sanin ya kamata,haka d'an nasa,yana da kamewa da sanin ya kamata,na tabbatar ba zaki taba fuskantar wata matsala wajen yin aiki dasu ba,inda nasan akwai matsalar kema kin sani,bazan karba miki ba,so please accept it,kiyi aiki tuquru,ko don saboda ni" qas tayi da kanta,tanason tilastawa zuciyarta da har yanzu taqi jin nutsuwa aminci wa aikin kan ta karba buqatar dan uwanta,sake gyara zamansa yayi sannan yace
"Shi da kansa Dr yin ya zaba miki position din,ya fimu shekaru da hangen nesa,yana ganin kin cancanta ne,ko abba dana gaya masa baice wani abu ba,kuma koni din nasan you can do it,so please kada kiyi discouraging kanki,you will made it in sha Allah" Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya qasan ranta,bai fahimceta bane,bawai ba zata iya bane,ita sam harkar da duk zai hadata mu'alama da jama'a ne bataso. Ganin ta shiga tunani sau ya katse tunanin nata ta hanyar miqa mata key din mota
"Gashi,gift na fara zuwa aiki,daga ni da kuma Saifullahi" hannu biyu tasa ta karba tana masa godiya,saidai sanda ta duba sunan motar sai da zuciyarta ta tsinke,motace sabuwar qira me kyau ta mata,tana kuma da dan tsada,lallai da gaske sukeso sai tayi aikin nan,zatayi addu'a ta kuma roqi Allah ya dafa mata,kada ya bata ikon watsa musu qasa a ido.
***********Duk daga inda ka daga kanka cikin layin,daga farko ne qarshe gaba ko baya na layin kana iya hangen katafaren ginin mansion house din daya amsa sunansa ta kowacce fuska a idanun me kallo,saidai daga ainihin cikin zuciyar gidan akwai naqasu me tarin yawa a ciki,birnannen tarihi da memories masu daci tsananin quna da soya zukata,memories da suka dakushe jin dadi da walwala mafi rinjaye ta dukka mutumin daya shafi gidan,gefe guda kuma akwai wani boyayyen muhimmin al'amari wanda yake sarrafa duk wani motsi da rayuwa ta al'ummar gidan.
Idan nace al'ummar gidan kada ka dauka wasu jama'a ne masu yawa,a'ah......dai daikun mutane wanda rayuwa cikin gidan ga zame musu lazim.
Kamar kowanne lokaci,qarfe takwas da wasu mintuna na dare,lafiyayyun hamshaqan motocin nasa suka tsaya babbar gate din gidan me kama da qofar masarauta ko shiga wata kasuwar duniya,cikin qasa da second biyar aka soma motsa qofar gate din bisa sahalewa da sarrafawar daya daga ckin security din gidan dake tsaron qofar,wanda ke tsaye daga gefe kusa da na'urar dake tura gate din cikin uniform din da dukka ma'aikatan gidan suke amfani dashi,wato baqin wando da farar riga,sai baqar hula me kama da hular 'yan sanda.
A nutse suka kutsa kai lafiyayyar harabar gidan me matuqar girma da tsari,wadda aka qawatata qwarai da shuke shuke,fitilu masu tsananin kyau da haske,da kuma ainihin fuskar gidan dake manne da wasu gilasai tamkar dasu akayi bangon gidan. Tun daga harabar tsarin gidan zai fara tafiya da imaninka,tsaftatattun tsirrai masu bada wani irin iska qamshi da koke koken tsintsaye daban daban,wasu siyansu akayi aka ajesu don bawa gidan dukkan ni'imar data kamata,wasu kuma daga Allah ne,sukanzo su wuce,kosu samawa kanau gurin kwana cikin tsirran dake wajen wadanda suka dace da tsarinsu,hakan sai ya sake qawata wajen,ya wadatashi da wani irin yanayi me sanyaya zuciya.
A nutse ya fito daga motar kamar kowanne lokaci cikin tsananin kamewa da izza,yauqi da aji irin na hadaddun mazan da suke ji da kansu suka san kuma waye su. Yana sanye da wani yadi da aka samar dashi daga merino wool dan asalin qasar spain me asalin kyau da tsada,wanda wani qwararren telan ya zauna ya shiryawa dinki na zamani daya sake qawata yadin fiye da kima,ya kuma qawata kwalliyar mamallakin suturar. Yana daya daga cikin jerin mutanen dake da tsari da kuma zabi a dukka sutturar da zasu sanya,hakan sai ya cakudu da baiwar dacewa da kowacce shiga keyi da jikinsa,koda kuwa pajamas ya sanya,duk da wasu matan dake da qarancin kunya a idanunsu......sun sha gaya masa yana da kyau ne,hakanan komai nasa me kyau ne,wannan ya sanya kome zai raba a jikinsa yake dacewa dashi,ya kuma sake qara masa kwarjini da cikar haiba da kamala.
Daya daga cikin yaransa ne ya matso da sauri yana masa bayanin wasu tarin takardu dake hannunsa,sai ya masa nuni da matashin dake tsaye a gefansa,yayi handing over dashi sannan ya taka a hankali yana nufar ainihin main entrance na gidan,ya barsu a wajen kowa yana qoqarin hattama aikinsa na ranar.
Duk taku daya yana jin yana qara masa kwadayin isa gareta,zuciyarsa ce ita,rayuwarsa ce,hakanan farincikinsa.
A nutse ya buda qofar lafiyayyen falon farko da zaka soma tararwa,falon da dukka kalolin kayan ado da qawa da aka zuba masa warm beige color ne da ratsin rusty red,tun daga manya manyan curtains na alfarma,kujerun da aka zuba carfet da aka malaleshi dashi ac da paint na ainihin bangon,hatta da frames dake parlor din masu dauke da ayatul kursiyyu falaq da nas da sauran ayoyin tsari color din dake jikinsa kenan,sai ratsin gold kadan a jiki.
Iya dubansa tsaf ya qarewa falon,ya sanya qafafunsa a hankali ya saka kai ciki hannayensa cikin aljihun wandonsa yana ratsa falon,wani yanayi yana saukarwa gangar jikinsa har zuwa zuciyarsa,wasu emotions da baisan yadda zai raba kanshi dasu ba,yayita kokawa da kansa yana danne fushin dakeson motsa masa yana ci gaba da saka kai ciki.
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*H U G U M A*
_*TABARMAR ƘASHI*_💔
*Arewabooks: huguma*
https://arewabooks.com/u/huguma
Page 13
Wani Parlor din ya tarar wanda baikai wannan girma ba,duk da dama abinda ya rabasu da wannan din babbar qofar glass ne da zaka turata,sai kuma labulaye na alfarma da aka zubawa qofofin duka,saidai wannan Parlor din nashi kalar daban da wancan,don komai da aka shirya a cikinsa minty blue green ne da ratsin creamy white. Dan matsaici ne da bai cika girma sosai kamar wancan ba,amma ya tsaru yadda jiki da zuciya zasu samu hutu yadda ya kamata. Shima shuru yake babu kowa,saiya taka zuwa hannun damansa,ya yaye labulen daya sadashi da wani tsararrren corridor wanda ya qawatu da wasu gold leaf picture frames,fentinsa olive green ne saboda qarawa idanu qarfin gani,kalar kuma ta dace da wajen sosai daya qawatau da fitilu masu haske tarwai,sai flowers a maqale a kowacce corner daga jikin bango,wanda suke bada qamshi na musamman da kuma samun kyakkyawar iska fiye da iskar da na'urar bature dake kafe a wajen zata bayar.
Qofofin dakunan bacci ne guda hudu a wajen,kowacce da dan taqi kadan daga qofar dake kusa da ita,biyu na kallon guda biyun,sai yaci gaba da takawa a nutse kamar mai nufar full length mirror din dake maqale a bangon qarshe na wajen,ya isa qofa ta qarshen dake daura da madubin daga hannun damansa,yasa hannu ya murda ya tura sannan ya shiga.
A nutse yake qarewa dakin dake a tsaftace kallo,yana watsa idanunsa tare da laluben daga inda zai hangota.
. Daga saman gadonta ya hangi tattausan bargonta milk color me matuqar taushi cure waje daya,ya zubawa gurin ido sosai,alamun motsin da ya gani shi yaja hankalinsa,ya daga qafa da wani irin hanzari ya isa bakin gadon,bai tsaya jiran komai ba ya sanya hannu ya yaye bargon take ta bayyana.
Kyakkyawar yarinya ce da duka duka shekarunta ba zasu haura biyar zuwa shida ba,fara ce qal siririya sosai,gashinta me tsaho da sulbi yana daure tsakiyar kanta da wani siririn ribbon pink color,kalar riga da wandon dake jikinta kenan. Cure take waje daya,ta qanqame ilahirin jikinta kamar wadda taga wani mummunan abun tsoro,saidai yadda bakinta yake rawa kawai ya isa gaya maka ta hadu ne da mummunan zazzabi.
Da hanzari ya haura gadon gaba daya,jikinta na rawa,lokaci daya tashin hankali da rudewa suka bayyana qarara saman fuskarsa tamkar ba ingarman namijin nan da yanzu yanzu yake shigowa cikin gidan ba,cikin takun dake cike da karsashi ba.
"Ya salam......ya salam" ya fada fuskarsa na wani irin sauyawa,tare da rungumota gaba daya zuwa jikinsa yana fadin
"Zazzabi ne a jikinki fadeela?,ina baaba rabi?" Ya fada yana lullubeta cikin jikinsa tamkar yana shirin maida ciwon jikinsa ne. Bude qofar dakin sai ya zama kamar amsar tambayarsa,kamilalliyar matar tayi sallama,wankan tarwada ce,sanye take da atamfa riga da zani,sai kakkauran mayafi data yane kanta dashi,hannunta dauke da carbi
"A'ah lafiya?,me ya sameta?" Ta fada cikin nuna tsantsar kulawa,itama fuskarta na nuna zallar alhini tana matsowa zuwa bakin gadon
"Yanzu yanzu na fita nayi sallah,na barta tare da julia tana qoqarin bata kayan bacci ta saka" baaba Rabi ta fada cikin tsantsar alhini tana qoqarin karbar fadeela daga jikinsa,saidai yaqi sakar mata ita
"Itace sabuwar nanny din da aka kawo?" Ya jefawa baaba rabin tambaya yana kallonta da idanunsa da suka kada suka canza launi,cike fal da wani irin zazzafan bacin rai
"Itace" ta amsa masa dukka hankalinta yana kan yarinyar,kafin yace komai aka buda qofar dakin aka shigo.
Matashiyar budurwa ce 'yar qabilar yoruba,sanye da uniform irin na ma'aikatan kamar kowanne ma'aikaci dake aiki cikin gidan. Cikin mugun razana taja da baya tana sauke idanunta qasa,gabanta yayi masifar faduwa,dukka jikinta ya dauki rawa,cikin matuqar kaduwa ta sulale ta duqa a wajen
"You are welcome sir" Idanunsa fal da masifa da kuma tashin hankali yake kallonta,ya zare yarinyar daga jikinsa ya miqawa baaba rabi ita,cikin harshen turanci ya fara magana cikin masifa tamkar zai bugeta,saika dauka bai cikin hayyacinsa
"Kin fadi adadin abinda kike da buqata na kudi,nasa an biyaki amma hakan bai hanaki kiyimin sakaci da rayuwar yarinya ba?,zaki barmin ita har zazzabi irin wannan ya sauka a jikinta ba tare da kin sani ba,banga amfaninki ba,ki tattara komai naki kibar gidan nan,na sallameki" ba ita kadai ba data rasa aikin da tayi mugun saka a rai kanshi ba,hatta baaba rabi tayi mugun kaduwa da hukuncin nasa,julia itace me aiki ta goma sha daya daya kora cikin qanqanin lokaci,kwata kwata baya daukan sakaci akan yarinyar,komai qanqantarsa shi ganganci ne a wajensa,duka masu aikin basa wuce sati daya suke rasa ayyukansu,masu nisan zango ne sukeyin sati biyu.
Yana da mugun kwarjini da haibar da bazaka iya tsaiwa roqonsa ba,don haka tana share hawaye cike da baqinciki rasa aiki me gwabi da tarin albashi me tsoka,da kuma fita daga daular wannan gidan,wanda iya cima da AC din dake karakaina a lungu da saqo na gidan kawai ta isa sanyaka ka mallaki lafiyayyar fata me sheqi,ba tare da kana amfani da mai ko sabulu ba.
Wayarsa ya ciro a aljihunsa cikin hanzari yayi kira na wasu sakanni,sannan ya matsa da sauri ya dauke yarinyar cak daga cinyar baaba rabi ya rungumeta cikin jikinsa,ya juya cikin kamewarsa da fushi ya bayyana a tsakiyarta yana fita a dakin.
A nutse yake takawa da ita zuwa sashensa,yana jin kamar ya maido ciwon jikinsa,tana ruqunqume dashi itama duk da zafin zazzabin jikinta,yana takawa idanunsa na sauya launi,wani abu da yafi kama da bacin rai yana motsa zuciyarsa,yana jin wata qaqqarfar tsana ta wata halitta na sake haifuwar sabuwar yabanya a zuciyarsa.
Da hannu daya ya bude qofar bayan ya ratsa wani hadadden balcony da aka qawatashi matuqa fiye da tunani,kyakkyawan falo ne na alfarma wanda ya kerewa dukka falukan gidan,komai da komai na cikin falon,hatta da door mat dinsa kalar creamy white ne me matuqar daukan hankali da burgewa,fararen fitilu qal da suka haska falon tarwai kamar safiyar da aka tashi da tsananin hasken rana sun taka rawar gani wajen qawata falon,tako ina qyalli yake,komai fes qal kamar rai bata rayuwa a ciki,duk inda ka waiwaya sai kaga kamar zaka ga fuskarka. Ba abinda falon yake bayarwa sai Wani irin ni'imtaccen qamshi dake cakude da qamshin air conditioner din dake tsaitsaye a kusurwoyin falon yadda zata wadaceshi tako ina saboda girman da yake dashi. Tsaf ya laqume saitin kujeru biyu na alfarma,iya wanzuwarka cikin falon ya isa ya baka wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali,saidai banda taufeeq wanda babu abinda ya sauya daga abinda yakeji cikin zuciyarsa.
"Welcome sir" ma'aikatan dake aiki a sassansa mutum biyar dukka maza suka fada cikin rusunawa da kuma girmamawa,baiko amsawa kowa daga cikinsu ba,sai hannu daya daga musu alamun ya sallamesu,suka juya da daya da daya suka fice a parlor din bayan kowa ya tabbatar aikinsa ya kammala,jibril ne qarshe,ya zube files din hannunsa da komai da komai ya juya shima ya fice.
Ta hannun damansa ya bulla wani matsakaicin hallway da aka qawatashi sosai shigen na daya sashen,ya tura qofar dake a wajen,babban bedroom ne shima da komai na cikinsa creamy white ne kamar falon,tsararrren gado dan qasar italia da yasha shimfidu da lallausan farin zanin gado saqar qasar dubai,qarasawa yayi ya kwantar da ita akai cikin tsananin tausayawa,shi da itan duka yana jinsu shi da ita tamkar marayan da mahaifinsa ya rasu kafin haihuwarsa,mahaifiyarsa kuma ta rasu ta barshi yayin haihuwarsa,yakanji duniyarsu tayi musu fadi kamar babu wani me jibantar lamarinsu,bawai don sun rasa masoyan dake nuna kulawa da soyayya mara iyaka a kansu shi da ita ba,a'ah.....akwai wani boyayyen abu,wani internal love da dukka su biyun suke buqata,wanda suka rasashi,kuma shine sila sannan musabbabiyyar jin wannan kadaicin dake lasar zukatansu ta can ciki.
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*H U G U M A*
_*TABARMAR ƘASHI*_💔
*Arewabooks: huguma*
https://arewabooks.com/u/huguma
Page 14
"Daddy" ta fada da siririyar muryarta da zazzabi ya jigata ta qara laushi ainun,Hannuwansa yaji ta kama ta riqe tsam,sai ya waiwayo ya kama hannuwan nata ya sanya cikin nashi,idanunsa suna canza launi saboda bacin rai da damuwa,ya miqa hannunsa zuwa gefen wuyanta don sake jin adadin zazzabin,har yanzu dai kamar dazun
"Am sorry angel,yanzu likita zaizo ya dubaki,zaki samu sauqi in sha Allah" da ido kawai take binsa,ya durqusa a tausashe yayi kissing bayan hannunta yana sake riqe hannun nata da kyau,yanajin kamar ya maidata cikinsa. Qararrawar falo ce tayi qara dai dai sanda wayarsa tayi qara itama,ya fara duba kiran
"Ku shiga dashi waiting room" ya fada a taqaice,sannan ya zare bluetooth din kunnen nasa ya ajjiye,ya sunkuya ya sake daukan fadeelan suka fita.
Qaramin clinic ne da ya kasance mallakin gidan,wanda ke dauke da dakin magunguna,dakin jinya guda biyu da gadajensu,da daki guda na gwaje gwaje da sauran ayyuka wato mini laboratory,kusan duk wani qaramin ciwo da zai samu iyalin gidan a nan ake dubasu bisa jagorancin likitan gidan wato Dr anwar ko kuma Dr raheema. Dukkan wasu kayan amfani da suka shafi magunguna na clinic din ana yawan dubasu da sabuntasu qarqashin jagorancin likitan amana Dr anwar bisa kulawa da kuma qwarewa,zallar karamcin MT jarma ya shafe idanunsa,ya kuma bashi dukkan wani matsayi da martabawar da baya iya tsallake kiransa shi da dr raheema kowanne irin aiki sukeyi,matuqar bai wuce gaban tasu buqatar ba.
Cikin lokaci qanqani ya gama checking dinta,ya soma hada allurai zaiyi mata
"Yanzu yanzu zazzabin zai sauka in sha Allah,ba wani ciwo bane me zafi,don't bother sir" a nutse ya gyada kansa,dukka idanunsa da damuwarsa suna kanta.
Mutsu mutsu ta fara yi,qaramin murmushin da bai shirya zuwansa ba ya kufce masa,yasan anzo gurin dama,muddin idanunta suka qyalla akan allura to yanzu zata daga hankalin kowa,a tausashe ya matsa kusa da ita,ya dagata cak ya sanyata a jikinsa,ya dora hannunsa saman lallausan gashinta yana shafawa a hankali
"Relax angel..... relax,bazaiyi miki da zafi ba" ya fada yana tausasa muryarsa sosai,saita tsaya cak din,ta runtse idanu tana jin shigar allurar a jikinta,ta kuwa matseshi gam har aka gama.
Da kansa ya isa dining room bayan zazzabin ya saukar mata,ya dudduba abinda cook dinsa ya dafa,ya zari plate ya debo dai dai iyakar abinda yasan tanaci.
Cikin tsantsar kulawa ya zauna ya dinga diban abincin da spoon yana bata,yana yi yana janye tab din hannunta,don daga saukar zazzabin har ta yiwa game dirar mikiya,tana masifar qaunar game,babu abinda yake bata nishadi kamar ita,idan ta kalleshi ta tabe baki zata sa masa kuka saiya kada mata yatsansa alamun a'ah. Yafi fahimtarta fiye da mahaifiyar data haifeta,ya gama haddace duk wani abu data fiso da wanda bai dameta ba,harma da wanda bataso,sai daya tabbatar ta qoshi sannan ya barta,ya miqa mata tab din yace mata zaije yayi wanka,ta gyada kai ta kuma waving masa hannayenta alamun bye
"See you soon dad" qaramin murmushi ya fita a fuskarsa,ya kada mata nasa hannayen,sannan ya juya a hankali ya wuce bedroom dinsa,hankalinsa da tunaninsa yana kanta.
Kayan jikinsa ya fara ragewa,yanayi yana kokawa da tunaninsa,hutu yake da buqata a yanzu,bawai tuna wasu tarkacen abubuwa marasa muhimmanci ba,tunasun da bazai haifar masa da komai ba sai zallar bacin da kwana cikin damuwa,damuwar da a wannan yanayin da al'amura suka cushe masa abubuwa sukayi masa yawa bashi da buqatarta,gobe ranar hutunsa ce,yana da buqatar ya wuni tare da ita,ya debe mata kewar data jima tanayi tasa. Babban towel fari qal ya daura iya qugunsa,faffadan qirjinsa dake cike da gargasa da murdaddun damtsensa ya bayyana sosai.
*M O N D A Y*
Tun qarfe biyar na asuba data kammala salla tana saman abun sallarta,koda ta gama azkar dinma saita samu kanta da sanyin jiki da kuma sanyin gwiwar kasa tashi tabar wajen,don haka ta buda qur'ani tayi tilawar wasu shafuka daga ciki sannan ta maida ta rufe. Agogo ta kalla,har yanzu akwai sauran lokaci kafin fitarta,sai ta jawo wayarta ta kunnata daga kashetan da tayi. Har yanzu cikin jikinta tana jin wani yanayi mara dadi,wanda duka baya rasa nasaba da fara fitarta aiki.
Saqon barka da asuba daga wajen mahmud gana ta fara cin karo,ko da wasa bata taba gwada saving number dinsa cikin wayarta ba,to amma yadda yaketa binbininta,da yawan cikata da yakeyi da saqonni safe rana dare yasa ta fara shaida number din tasa a idanu. Qaramin tsaki taja,bata koda bari ta buda saqon taga cikakken abinda ya qunsa ba ta shareshi daga wayar tata gaba daya,kusan hakance take faruwa dama,duk sanda saqonsa ya shigo wayarta bata tsaiwa dubawa bare ta karanta,ta riga ta quna daga lamarin maza,batajin akwai wani abu nasu guda daya da zai burgeta,dukkansu a wajenta tamkar hankaka suke,gabansu fari bayansu baqi,kamar hawainiya dake iya canza ainihin launinta zuwa dukka launin da takeso,babu wani abu daga garesu da yayi saura wanda zai dauki hankalinta ko yaja ra'ayinta,tafi ganewa ita dasu din ya zamana kowa yana daga nesa yana sabgarshi.
K'arfe takwas saura ta fito a wanka,tadan makara kadan saboda wani littafi data soma dubawa wanda ya dauki hankalinta har taso gota lokaci,babban towel ne daure ajikinta daya bayyana fararen fatar dake qirjinta zuwa bayanta da kuma sambala sambalan hannayenta. Gaban madubi ta tsaya tana tsane jikinta da towel,sannan ta saka hannu ta zare shower cap din dake kanta,take gashin kanta ya warwatsu a kafada da kuma gadon bayanta,ta ajjiye towel din,ta jawo wata qawatacciyat stool ta zauna a kai,sannan ta jawo cream dinta ta fara shafawa. Batayi nisa da shafan man ba kiran afifa ya shigo,wanda shi ya qara mata nauyin shiryawar,sai data cinye kusan awa guda sannan ta kammala komai.
Ta fito d'as cikin wani atamfa me asalin tsada da taushi,wadda ta yane atamfar da wata tsadajjiyar laffaya ruwan golden yellow da brown,kalolin da suka hadu sukayi masifar fidda kyanta.
Kanta irin daurin nan da ake kira zahra buhari ne,wanda ya baiwa gashinta data nannade damar fitowa ta qasa,tsadadden agogon rolex ne a hannunta da wani sisirin zobe me qananun fararen duwatsu masu walwali,ta zura fararen qafafunta cikin wani lafiyayyen takalmi me matsakaicin tudu qirar kamfanin gucci mahadin qaramar handbag dinta. Bata wani tsaya batawa kanta lokaci wai ta duba komai yayi perfectly fine ba ta fesa lallausan turarenta ta dauki wayarta ta fito.
Kamar ko yaushe muddin bawai baqi ne dasu ba falon gidan nasu shuru yake,ta duba agogon hannunta taga dai dai yake aiki da na falon,saita maida dubanta ga dining dinsu. Dan qaramin murmushi ta saki,baaba rabi kenan,komai ta shiryashi cif,saboda tasan yau zata fara fita aiki,duk da cewa tasan ita ba ma'abociyar cin abinci bace koda rana tayi ma sosai bare yanzu da sassafiyar nan,don ko tara na safe batayi ba.
Tana shirin bullawa sassan maama,idan bata sameta ba ta qarasawa wajen abba don tasan bata wuce can saiga baaba rabi
"Allahu akhbar kabiran,dawisu gwanar ado,ummin abba uwar masu gidan,wannan kyau wannan kyau,hohoho" ba kasafai takeson wannan kodatan da baaba rabi takeyi ba,to amma ya zamewa baba rabin sara da dabi'a yabi jikinta,uwa uba kuma suna martabata saboda dadewarta dasu,suna bata wani girma na musamman
"Barka da warhaka baaba"
"Barka kadai uwarmu,an fito kenan,to ubangiji yasa a fara a sa'a,ya kauda dukkan abunqi,ya kuma kade fitina"
"Ameeen ya hayyu ya qayyumu,maama fa?" Ta tambayeta har cikin zuciyarta tana jin dadin addu'ar da tayi mata
"Ta shiga wajen alhaji" saita juya a nutse tana nufar can.
Sai data tsaya ta ware igiyar takalminta a nutse tayi sallama ta shiga falon. Dattijon da fuskarsa me cike da kamala da kwarjini yana zaune cikin couch,hannunsa riqe da takardun qur'ani da yake zuwa pieces. A gefe ya ajiiye qur'anin cikin martabawa,ya daga kai yana dubanta tare da amsa sallamar tata,qaramin murmushi na fita saman fuskarsa,can qasan zuciyarsa kuma cike yake da fata,fata da buri me tarin yawa akan rayuwarta gaba daya.
Daf da qafafunsa tazo ta rusuna har qasa
"Barka da safiya abba" gyara zamansa yayi yana dubanta
"Barka kadai ummin abba,an tashi lpy?"
"Alhamdulillah abba ya qarfin jiki?"
"Muna godewa Allah"
"Allah ya qara lafiya da nisan kwana me amfani"
"Ameen don nabiyyur rahmati,an fito aikin kenan?" Kai ta gyada a sanyaye
"Eh abba"
"To Allah yasa a fara a sa'a,yasa ya zamewa dukiyarki da lahirarki alkhairi,ki kare mutuncin kanki da kyau,don ke din ba yarinya bace qanqanuwa,duk da bani da haufi akan tarbiyyarki,amma dan adam saida tunasarwa da nuni,ki tsare gaskiya da amana,ki riqe aikinki da muhimmanci sai Allah ya dafa miki"
"In sha Allah abba,na gode Allah ya qara girma" kafin wani a cikinsu yace wani abu an turo qofar falon an shigo,maama ce da afifa da alama wani saqon ta kawo mata suke magana akai. Tayi mamaki da taga afifa din,ta dauka da wasa take mata sanda tace ita zata zo da kanta ta kaita office a ranarta ta farko,ta duqa gaban maama suka gaisa,al'adarta ce ba kasafai take iya gaida babba a tsaye ba,musamman mahaifanta,saita juya ga afifa daketa kallonta,bakinta fal da magana,idanun su abba ne kawai ya hanata cewa komai,har zuwa sansa suka fito.
Bayan sunyi addu'a sun shiga sabuwar motar sãahar din saita waiwaya tana dubanta
"Bestie,kinga kyan da kikayi?,don Allah ki sassauta,karkije ki dinga hada ma'aikata fada a kanki" sosai sãahar ta tsuke fuska,saita sauke madubin gaban motar tana kallon kanta. Tabbas tayi kyau qwarai,komai data saka ajikinta ya haskata sosai,sai kawai ta sanya hannu zata balle murfin motar. Da sauri afifa ta tayar da motar tana dariya,saboda ta gama karantar abinda take da nufin yi
"Kome zakiyi,ke koda kashi zaki shafawa jikinki hakan bazai hanaki yin kyau ba sayyada" harara ta watsa mata
"Kinzo ne to spoiling my whole day afifa da maganganunki?" Ta fada manyan idanunta dake kan afifa kamar zasu fado. Kai ta girgiza tana dariya
"Ni na isa?,kefa yanzu amanar mahmud ce a wajena" fuska ta tsuke sosai tana kallonta
"Waye mahmud?,amanar me?"
"Ba zaki gane ba,amma dole na kula dake don amana ba wasa bace" ranta ya sosu sosai,saidai afifa tafi gaban haka
"Wai kasuwanci na kika fara afifa?" Dariya sosai afifa ta qyalqyale dashi har tana dan duqawa ga sitiyarin motar
"Idan ma shi na fara aiba laifi bane,tunda hankalinki yaqi dawowa gangar jikinki har yanzu" rasa me zatace da afifa tayi,sai kawai ta dauke kanta ta maida gefe tana kallon hanyoyin da suke wucewa,hanyoyin kano da safe wandada suke da qarancin kai kawo na jama'a,maganar duniya afifa tayi mata amma 'yan miskilancin sun motsa,taqi koda waiwayowa bare ta tanka mata.
*************
Kamar ko yaushe daya bayan daya motocin masu kama daya suke kutsawa kan titin da zai sadasu da katafaren kamfanin MT GLOBAL COMPANY,duk da cewa cikin combo suke,amma mota guda dayaa a ciki ta fita zakka,mercedes maybach s580 sand color dake masifar daukan hankulan jama'a duk inda ta gifta.
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*H U G U M A*
_*TABARMAR ƘASHI*_💔
*Arewabooks: huguma*
https://arewabooks.com/u/huguma
Page 15
Kofar tafkeken gate din kamfanin suka tsaya,kafin sukai ga sanar da isowar CEO OF MT GROUP OF COMPANY har jami'an tsaron dake kai kawo a qofar company din sun ture musu gate din gefe,sannan suka qame dukkaninsu suna sara musu har zuwa sanda suka gama shigewa tsaf,suka maida qofar suka rufe.
Cikin nutsuwa da sanin doka da order dukkaninsu suka faka a matsayar motoci ta company din,saidai daga gefe guda dake nuna waje ne kebantacce saboda ajiyar ababen hawa na musamman,don akwai qarfen daya raba tsakaninsa da ragowar filin ajiyar motocin.
Yadda motar ke daukan hankalin kowa haka ta dauki hankalin afifa data taqarqare a dazun tana zubawa sãahar bayanin da yasa takw kallon afifan kamar wata statue
"Wai ta riqe amanar mahmud?,to shi mahmud qanin maama ne ko qanin abba?,yaushe ta karba amanar tasa da har zatayi mata roqon riqewa?,banda afifa duk duniya ba wanda ya isa yayi mata wannan zancan ta barshi tana kallonshi haka.
Saida suka gama fakawa sannan ta maida dubanta ga sãahar
"Kinga abinda na gani kuwa?" Ta jefawa sãahar tambayar cikin zallar mamaki,da kuma tafiya da hankalinta da motar tayi.
Ido kawai sãahar din ta lumshe tare da budesu lokaci guda ba tare data amsawa afifa ba
"Wow....wow.....mybatch vigil abloh fa?,kinsan mutum 150 ne duka duka suka mallaketa a duniya gaba daya?"
"Zan iya tafiya?" Sãahar ta jefeta da wannan tambayar,cikin bawa maganarta rashin muhimmanci,saidai afifan ci gaba tayi da koro mata bayanin zallar tsadar motar da darajarta,sai kawai tasa hannu zata buda motar.
Caraf ta riqo tsintsiyar hannunta
"Don Allah ki barni naga wanne me sa'ar ne ya mallaki wannan motar,wanne DON dinne?" Idanu ta kafe afifa dashi tana mamakin qaunar da afifa kewa motar,already tasan halinta,she's a classy ladie,amma me yaja hankalinta haka?. Ido ta zuba mata tana kallon yadda ta natsu tana mata bayani tare da kallon sashen da motar take.
A qalla an kusa kwashe minti biyar bayan fitowar duk mutanen dake cikin sauran motocin kafin motar ta bude a hankali ya kuma zuro jikinsa zuwa waje,zuwa sannan idanun sãahar nakan wayarta tana dannawar dole,saboda ta cika maqil da takaicin afifa data hanata fita,ga saukar yayyafi da aka fara samu siri siri,wanda ita kuma kwata kwata bata qaunar ruwa ya taba jikinta
cikin shigar wata lafiyayyar suit ta zallar cashmere wool,charcoal color yake,idanunsa manne da baqin eye glasses,wanda zaiyi wuya ka iya ganin qwayar idanunsa,hannuwansa duka cikin aljihun wandon suit din,yana takawa da sassarfa sosai yana kuma magana a waya ta Bluetooth din kunnensa.
"Tabarakallahu ahsanul khaliqeen,don Allah dago ki tayani ganin wani kyau a nan" afifa ta fada tana tabo hannun sãahar,tana kuma qunshe dariya a cikinta,ya tafi da ita matuqar tafiya,amma tanasl ne itama ta rama ta qunsa mata takaicin yin shuru da tayi sanda taketa babatun mata batun mahmud.
A maimakon ta kalla inda afifa keson kalla saita kallo afifan
"Na kalli me?,kedai da kika zabawa kanki ganin kyan dan maciji na d'a namiji ai sai nace miki bismillahi,Allah ya bada sa'a" ta fada wani fushi yana motsawa daga qasan zuciyarta,kai afifa ta girgiza
"Ba haka bane sãahar,ban taba ganin irin wannan a zahiri ba Allah i swear,there was no denying that the handsome man was charming,he was elegant in every way Allah,don Allah ki kalla ki gani,zaki tabbatar ba qarya nakeyi ba" haushi ya sake qure sãahar,takaici da bacin rai yasa ta daga kai zuwa sashen da take roqarta ta kalla din,dai dai sanda yake wucesu cikin tarin ma'aikata zuwa main entrance na building din kamfanin.
Siririn tsaki sãahar taja,ta kuma watsawa afifa harara
"Wai me ya shiga kanki ne yau?,lallai ya zama dole na gayawa su maama suyi gaggawar aurar dake,tunda kin fara sumbatu"
"Ba sumbatu nake ba,don Allah bakiga abinda na gani ba?,haduwa iya haduwa?,he was striking,no one could take their eyes off his good look"
"To ina ruwana?" Ta fada tana jin ta fara hasala,sai afifa ta qwace da dariya,tasan tayi mata abinda tafi tsana a rayuwarta,zancan d'a namiji,kuma har ta zauna tana kodashi haka,duk sa cewa YES wannan din yakai ya wuce ma yadda idanun me kallo zai ganshi,yana da wani irin kyau me sanyi haiba da kuma kwarjini na musamman.
Kafin afifa ta sake cewa komai sãahar ta buda murfin motar ta fice abinta
"Zan wuce da motar,zan bayar a dawo miki da ita sanda zaku shiga lunch break" gyara yafen laffayarta tayi kawai,ta soma takawa a nutse zuwa ciki ba tare data amsa kota waiwayi afifa ba,yayin da afifan ke binta da kallo,murmushi na fita akan fuskarta. Komai na 'yar uwarta me kyau ne,komai na 'yaruwarta me aji ne,iyakar dukka inda mace takai ga aji da kyau takai,amma abu daya ya tsaida duniyarta cak,saita girgiza kai ta tashi motar bayan taga shigewarta building din.
Cikin nutsuwa da kamewarta take takawa,a nutse kuma ba kai tsaye ba tana karantar yanayin kamfanin da kuma inda take takawar,tun daga wajen ta sake karantar girma da tsarin kamfanin,kusan kowa ya duqufa yana aiki sosai,tun lokaci baiyi nisa ba,amma kowa yana mazauninsa ya riqe aikinsa.
"You are highly welcome madam" taji an fada daga gefanta,saita waiwaya a nutse. Matashi ne sanye da shirt da trouser lime green da baqi,yayi maganar cikin zallar girmamawa yana dan rusunawa kadan
"Fourth floor zaki sauka,akwai ma'aikatan dake jiranki a can,zasuyi guiding naki akan komai" ya fada cikin girmamawa,saita jinjina kai ta kuma taka zuwa bakin elevator,ta danna ta shiga,tayi kuma selecting number din floor din da takeson sauka,sannan ta koma daya daga cikin corners din dake cikin elevator din ta goye hannayenta a qirji,idanunta qyar akan numbers din dake jere daga bakin qofar shiga na'urar, zuciyarta na fara ayyana mata ko yaya zamanta cikin wannan babban company zai kasance?.
A second floor elevator din ya tsaya,da alamar akwai wani dakeson shiga shima,idanunta akan bakin qofar,har zuwa sanda ta bude. Fes ya bayyana daga gaban qofar,fuskarsa na kallon gefansa yana magana da wani cikin nutsuwa da kamewa,duk da cewa baka iya jin abinda yake fada,amma yadda yake maganar cikin izza da kamewa zai gaya maka umarni yake bayarwa.
Yana gama maganar yayi taku biyu don isa cikin elevator din,karon FARKO idanunsa ya sauka a kanta,kamar yadda itama karon farko nata idanun suka shiga cikin nasa,tsahon tsaiwar da elevator din yayi sai a sannan ta dubi wanda ke bakin qofar da nufin shigowa ciki suyi tarayya na wasu sakannin da zasu kai kowa inda yayi nufin zuwa. Lokaci guda kuma a tare kowa ya janye idanunsa,ta kauda kanta gefe guda tana tsuke fuskarta,ta gane fuskar,fuskar mutumin da a dazu afifa ta cikata da zancansa,saita sake tsuke fuskartata,tana jin qyamatar hada guri dasu,kamar yadda takeji a ranta game da duk wani DA NAMIJI.
Sanda taji anyi releasing elevator din ya wuce ba tare da an shigo ba sai taji mamaki kadan ya kamata,ta maida dubanta ga qofar taga taci gaba da hawa zuwa saman,saita yarfar da hannunta tare da tabe bakinta,ita dama hakan takeso,bata buqatar hada numfashi da jinsi irin nasu.
Fitowarta daga ciki yayi dai dai da matsowar sajjad dake cikin aiki kace kace,amma Dr girema ya tasheshi takanas saboda ya marabci sãahar din,ya kuma tabbatar ya bata duk abinda take da buqata da zai sake jin ta gamsu da aikin da kuma kamfanin gaba daya.
Kamar wancan data baro a qasa haka shima yayi welcoming nata,sannan cikin sanin kima da darajar dan adam daya sanyata tadanji zuciyarta ta saki kadan yace mata
"If you don't mind......i will show you your office" kai ta jinjina kadan,yayi gaba tana biye dashi,sannan sauran ma'aikatan da suke qarqashin kulawar office dinta.
Kusan kafin ya fita sai daya gabatar mata da komai da take da buqatar sani,tana zaune saman kujerar da sai da tayi addu'a sannan takai ga zama,ta bada dukka hankalinta ga bayanansa,abinda zai nuna maka zallar seriousness dinta,yanayin yadda kyakkyawar fuskarta ke a tamke ya isheka shiga taitayinka da tabbatar maka ba zata dauki wargi ko wasa ba,har ya kammala,saita dan lumshe kyawawan idanunta kadan sannan ta budesu
"Inason a sanarwa suk department din dake qarqashin wannan office din akwai general meeting a gobe"
"In sha Allah" ya fada sannan sukayi mata sallama suka fita don bata damar duba ayyukan da aka tsaya akai don ta dora.
A nutse ta fara buda computer din dake gabanta,ta soma aika saqon email zuwa ga sauran department dake cikin kamfanin da sauran dukka board members,tare da introducing kanta,email guda daya daya rage zata turama,wani saqo ya shigo mata ta email,abinda ya janye hankalinta kenan ta shiga Wani aikin daban,sai kuma ta shiga binciken dame dame aka aiwatar cikin office din.
Cikin qwarewa tare da amfani da zallar basira take sarrafa na'urar,da wani irin qwarin gwiwa da karsashi da batasan ya sauko mata ba. Ta kusan kashe awa biyu cur,kafin ta zame hannunta daga kan computer din,ta kuma maidasu saman fuskarta ta rufe fuskartata da kyau tana fidda numfashi me dumi daga bakinta. Ta fuskanci akwai jan aiki a gabansu,da kuma wasu al'amura na rashin gaskiya masu tarin yawa da aka aiwatar,wadanda sune suka taka rawar gani wajen kawowa company din naqasu da kuma koma baya,ta tura kujerar ta baya tana hade yatsunta da suka gaji guri daya ta lanqwasasu da kyau,dai dai lokacin kiran afifa ya shigo wayarta.
Har ta saka hannu zata daga wayar saita fasa,ta jefawa wayar harara kamar itace afifa din,saita miqe bayan ta zare takalman qafarta,ta taka saman lallausan carfet din da zai sadata da qawataccen fridge din dake office din tana sake nazartar office din,komai an shiryashi base on her favourite colors,har ta soma zargin anya ba tare da yaa muhyi aka zuba furniture na office din ba?.
Komai an tanadeshi,don hatta fridge din cike yake da kalolin drinks,ruwa kawai ta dauko,ta dawo ta zauna saman couch masu laushi da aka shirya daga gaban table dinta bayan ta dauko wayarta.
Sms guda biyu ne suka shigo kusan lokaci daya,na afifa ne a sama,shi ta fara budewa
_"I hope you are enjoying your work?,god bless you dear,All the best"_. Dole murmushi ya subuce mata,afifa ta wajenta,ayi dadi ayi tsiya,saita maida mata amsa a taqaice
_"All is well bestie,thank you"_. Komawa tayi ta duba saqo na biyu
_"assalam gimbiya,iam wishing you a joyful day,i hope you will remain blessed,fatan nasara,mahmud A gana"_ dogon tsaki taja kamar zata tsinke harshenta,saita goge saqon kamar yadda ta saba,ta bude gorar ruwan ta zuba a glass cup ta fara sha tana tunanin next abinda zata aiwatar.
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*H U G U M A*
_*TABARMAR ƘASHI*_💔
*Arewabooks: huguma*
https://arewabooks.com/u/huguma
Page 16
Dogon tsaki taja kamar zata tsinke harshenta,saita goge saqon kamar yadda ta saba,ta bude gorar ruwan ta zuba a glass cup ta fara sha tana tunanin next abinda zata aiwatar.
Tun daga sama zuwa qasa ta tsaya ta qarewa kanta kallo da kyau,tayi taku biyu gaba ta sakeyin taku biyu zuwa baya,taja rigarta baya kadan yadda zata dauki hankalin duk wani daka iya kallonta ko yakai idonsa kanta bisa tsautsayi ko kuma dace. Ta waiwaya kadan jikin wata qofar glass dake baka daman ganin fuskarka tamkar madubi,ta fito full hakanan dressing nata,saita saki siririn murmushi tana maida gashin kanta baya wanda tasa gantalallen scarf ta lullube rabin gashin dashi.
A nutse ta koma ta zauna saman kujerarta ta zauna tana sake sakin murmushi,ita kadai tasan farincikin da takeji cikin ranta,tayi matuqar samun sa'ar da bata zata ba data zama secretary dinsa,bayan dogon hanyar da tabi me cike da tangarda kafin cimma muradinta. Tasan cewa a gata dukiya ilimi da kuma kyau na halitta da take dashi dukka tafi qarfin matsayin zama secretary,to amma....muddin akan MUHAMMAD TAUFEEQ ne,ta shirya zama massinger ma bawai iya secretary kawai ba. Maida qafarta tayi ta harde daya saman daya,ta bude computer din ta soma sarrafata.
Cikin qasaita da izzar nan tasa data zame masa jinin jiki ya sanya kai zuwa babban office dinsa daya kasance na daya duk fadin company din,sauran ma'aikatansa da na biye dashi.
Jibril ya buda qofar,dukka suka dataka ya fara shiga sannan suka rufa masa baya. Da sauri ta daga kanta tana duban qofar,saita miqe cikin sauri saidai kuma cikin salo na yanga da yauqin da take amfani dashi wajen farautar hankulan maza. Gabanta na wani irin faduwa,zuciyarta tana bugawa da qarfi sanadin ganinsa da tayi.
Mamaki ya kusa daskarar da ita sanda taga baiko kallo koda sashen da take tsaye ba,tamkar ma baisan da wanzuwar wata halitta a wajen ba,dole ta tattare guntun iyayin kalamanta data tsara yi masa magana dasu,ta zare jikinta daga kujerar tabi sauran ayari zuwa cikin office dinsa gaba daya,gabanta na faduwa,tana fatan duk wani shiri nata ya dinga zuwa mata da sauqi fiye da yadda take tsammata.
Kamar wanda tsaiwa ta zamewa dabi'a,ba kasafai ya fiya damuwa da zama saman kujera ba,yanzunma haka ce,daya bayan daya ya sallamesu,ya rage saura sajjad da jibril. Jibril din ya duqufa da duba wasu takardu,yayin da sajjad suke magana qasa qasa da ita,duk da cewa gaba daya hankalinta yana a kanshi,yayi mugun tafiya da ita,shigarsa ta yau ta dabance dake nuna aiki zallah.
"Ehnnnn" ya fada a taqaie yana jingine da mulmulallen table dinsa dake tsare da files da suke jiran isowarsa,ya zuba duka hannayensa a aljihun wandonsa,yayin da yayi crossing qafafunsa.
Da sauri jibril ya dago kansa,sannan ya fara magana
"Sir,muna expecting ziyara daga gurin Dr at any moment" kyawawan idanunsa ya lumshe yakuma budesu a lokaci guda
"Okay,the meeting has been postponed,a canza date zuwa gobe"
"Zan sanarwa kowanne department" tayi caraf da zancan,ganin cewa dukka wannan abun aikinta ne,ita ya kamata ta sanar masa da kowanne tsari,amma jibril yana aiwatarwa,hakan na nufin ita 'yar kallo zata zama kenan?. Ta yiwa kanta tambayar da bata da amsarta.
Har yanzun bai nuna alamun yasan da wanzuwarta a wajen ba,bare maganar da tayi,yaci gaba da magana da jibril ya sallameshi. Sajjad ma ya ajjiye masa dukka files din daya kamata ya juya ya fita,cikin zuciyarsa tausayin SAIMA yana kamashi,tabbas SON MASO WANI qoshin wahala ne,yayi imanin babu abinda zata tsinta daga wajensa face tsantsar bacin rai da kuma batawa kai lokaci,inda zata dauki shawararsa,abu daya zaice da ita,ta kama kanta,ta kuma kama martaba da kimarta ta diya mace,shine kadai abinda zaisa ta tsira a idanun TOUFEEQ din.
Kujera yaja ya zauna har yanzu dai bai bata hankalinsa ko da na second guda ba,wannan duka bai sanya ta sare ba,ta tako zuwa gaban table din a hankali ta tsaya,dai dai sanda yake rubutu saman wani file
"Sir.....akwai wani abu da kake buqata?" Tayi maganar tana dan zame rigarta kadan don ta bawa qirjinta damar fitowa,ko Allah zaisa ya daga kansa gareta,sai daya bude page din gaba na file din sannan ya fara magana,cikin muryar sa din nan dake cike da zallar qasaita da kuma izza
"Banason yawan magana,bana kuma son shishshigi,kiyi qoqarin cire kanki daga dukkan abinda ban gayyatoki a ciki ba,karki soma wuce limit dinki,any moment kuma kamfani zai iya sauyaki idan aikinki baiyi ba,these are my conditions,you can go". Wani abune yazo ya tsaya mata a wuya,ta dan zuba masa ido tana jin sonshi yana ninkuwa a ranta,amma bata taba kawowa zaiyi mata irin wanna yankan qaunar da wuri ba haka,tasan halinsa,fes zai iya yanka mata jan card idan ta tsallake abinda ya gaya mata yanzun,dole ta miqe jiki a salube ta fita a office din,tana saqawa ranta abinda zai fishsheta,ba zata taba iya jure irin zaman da shi ya tsara zasuyi ba.
K'arfe daya na rana zuwa biyu shine lokacin break na kamfanin,masu cin abincin rana da masuyin sallah ga musulman ciki,wannan kuma duk umarni ne na CEO,ya sauya fasalin abubuwa da yawa cikin sati guda a kamfanin,da yawan ma'aikatan abubuwan sun musu dadi,amma ga wadanda sharholiya kadai suka sanya a gabansu wasu abubuwan basu yiwa tsarinsu dai dai ba.
Bata da ra'ayin zuwa kitchen,wanda aka tanadeshi musamman saboda manyan offices kamar nata,don haka ta umarci miss sameera ta samo mata coffee kadai. Ba kasafai take sakewa taci abinci ako ina ba,shi yasa ma baaba rabi taso shirya mata wani abun ta taho dashi,duk da tasan babu lallai ta maida kai taci yadda ya kamata.
Cikin toilet dinta dake office din ta daura alwala,ta dawo corner ta musamman da aka tanadarwa office din don yin sallah,ta gyara lullubinta ta tayar da sallar. Kafin ta idar miss sameera ta dawo,ta ajjiye mata coffee din,ta koma ta tsaya tana jiranta ta idar da sallar.
Cikin girmamawa ta matso bayanta kadan bayan ta idar
"Akwai email da aka turo miki daga ceo office,kusan minti talatin kenan,ina kyautata zaton baki gani ba" kai ta gyada mata a nutse tana dubanta
"Boss ne ya iso,yana office na ceo,he wants meet you" jim tayi na wasu 'yan mintuna,sannan ta maida dubanta ga miss sameera,kai ta gyada mata a natse,ita kuma ta jinjina kai ta juya ta fice.
Fuskarta da daurinta ta gyara kamar yadda yake,kamar bata sanyawa fuskarta ruwa ba,tanana da qyallin nan da gogewar fatarta,saika dauka tayi amfani ne da powder. Ta gaban table dinta ta tsaya ta danyi sipping coffe din,bata ma iya shanyewa ba ta fito ta cimma miss sameera na jiranta a farfajiyar data fi kama da parlor wadda zata sadaka da office dinta.
A nutse take takawa cikin shigar tsadaddar laffayar data lullube ilahirin jikinta,duk inda ta gifta sai tayi gaba da hankula da kuma idanun kaso mafi yawa na ma'aikatan kamfanin,walau maza ko mata,ko ina akwai shige da ficen ma'aikata,kasancewar lokaci ne na hutu. Ko daya babu wanda ta baiwa hankalinta,cikin kamewa da nutsuwa har suka isa qofar office din,mr sameera ta tura qofar tayi gaba,sãahar tabi bayanta.
Wani irin katafaren office da babu irinsa kaf kamfanin,wanda ke dauke da sassa biyu zuwa uku,waitin parlor wanda saima ke ciki ita da tarin takardu da kujerun da aka qawata gurin,sai rest room daura dashi kuma main office din da zaka gudanar da ayyukanka. Idan ka kira office din da aljannar duniya akai tsaye sam bakayi laifi ba,saboda ya amsa sunan,wasu irin colors da design me matuqar tsari da aka qawata kowanne sashe na office din.
Sallamar miss sameera ya sanya saima daga idanunta daga kan computer,maimakon idanunta su sauka kan sameera,sai suka fada kan sãahar dake qoqarin daga kiran daya shigo wayarta
"Zaki iya sanarwa da sir isowar president?" Sameera ta yiwa saima tambayar,lokacin da ta tattara dukkan hankalinta akan sãahar da nata hankalin yake kan khalipha dake mata complain na tafiyar da tayi baya nan,lallausan murmushin dake masifar qawata mata fuska ne kwance saman fuskartata,har jerarrun fararen haqoranta da suka zama tamkar hasken lu'ulu'u suna fitowa,wani luguden abu taji ya saukar mata,tana da labarin dukka sabbin ma'aikatan kamfanin a yau zasu kama aiki kamar dai ita,tabi diddigin kowacce mace dake cikinsu,musamman wadanda ya zamana mu'amala zata iya hadasu da office din TOUFEEQ dinta,to amma ita din ita kadai tak! Ta kasa samun komai a kanta,ta gaza cimma wani bayani daya shafeta har zuwa lokacin data taka qafarta ciki kamfanin,sai yanzu,karo na farko
"Excuse me,ko ta shiga ne?" Sameera ta fada cikin girmamawa da kuma zaquwar ganin yadda saima ta kasa amsa maganarta ta farko.
Iska taja sosai a cikin hunhunta,ta qanqance idanu tana duban sameera,duban da zataso ace president din da kanta ta yiwa shi,saidai ba zatayi garajen aikata hakan ba,don batasan wace ita ba,kada ta aikata abinda zai zame mata matsala,ya kuma zama silar cisgeta daga bigiren data dora buri akai
"Sir yana tare da babban baqo wato mahaifinsa,saidai ku dawo wani time din,kafin lokacin na sanar masa" tayi maganar tana ci gaba da dannan system dinta,dai dai sanda sãahar ta gama wayar,ta zameta daga kunnenta tana kallon sameera dake jiran ta kammala wayar tayi mata bayani. Kafin tace wani abu sãahar ta rigata
"Thank you,na gode da rakiya,zaki iya komawa office" tayi maganar kanta tsaye tana kyakkyawar qofar da a samanta take liqe da takardar dake bayanin inane nan gurin ba tare data waiwayi saima ba.
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*H U G U M A*
_*TABARMAR ƘASHI*_💔
*Arewabooks: huguma*
https://arewabooks.com/u/huguma
Page 17
Wani abu ne ya tasowa saima,yayi mata tsaye a wuya,ta riga ta saka hannu kan dokar yin biyya ga wanda yake sama da office dinka,me yasa bata nema matsayin president ba?
"Neman kusanci da taoufeeq" zuciyarta ta bata amsa kai tsaye,ajiyar zuciyar baqinciki ta sauke,ta koma tayi relaxing cikin kujerarta tana qarewa qofofin guda biyu dake facing dinta kallo, zuciyarta na wani irin tsalle cike da luguden kishi,har tsahon wani lokaci toufeeq din zai kwashe kebance da wannan kyakkyawar halittar data bar mata sassanyan turarenta na yawo cikin dukka qofofin hancinta?.
Cikin nutsuwa kuma dauke da sallama ta tura qofar office din. Kyakkyawan dattijone da shekaru sam basu samu nasarar ture kyakkyawan fuskar da Allah ya mallaka masa ba,fari ne sol,farin dake gwada tashen kyau da farin daya zuba zamanin quruciya,yana zaune saman sofa qwaya daya dake cikin office din,ya dora qafarsa daya kan daya,system dinsa na saman qafar tasa yana dannata cike da qwarewa.
Cikin kamala ya waiwayo yana amsa sallamar tata,idanunsu suka gauraya,kwarjininsa da kuma kamalarsa suka cika idanun sãahar,yayin da murmushi ya wadaci fuskarsa
"Lale maraba da 'yata,president dinmu" dattijon da shekarunsa suka suka rufa sittin ya fada yana sauke qafafunsa qasa. Da dan sauri ta daga kanta daga sunkuyar dashi din da tayi da farko tana duban dattijon duba na mamaki,ita dai zata iya cewa kaf rayuwarta yaune karon farko data fara ganinsa ma gaba daya,sani kuwa saidai na fatar baki kawai wajen yaa muhyi,to amma shi din ya akayi yasan wace ita
"Daina mamaki diyata,kamanninki da d'ana muhyiddeen ta bayyana sosai a fuskarki....." Cikin girmamawa qaramin murmushi ya subuce mata,bata taba jin ance suna kama da yaa muhyi ba sai yau,tana shirin gaidashi ya tareta
"Koma ki shiga resting room ku jirani keda d'an uwan naki" ya fada cikin kulawa.
"Dan uwana?" Ta tambayi kanta cikin mamaki,waye cikin gidansu yazo company din ba tare data sani ba?,kodai yaa muhyi ne bai nutsu ba sai daya biyota?,bata sani ba,saita juya a nutse taja masa qofar ta fito.
Qofa ta biyun ta dosa tana takawa a nutse,zuciyarta na qawatuwa da karamcin tsohon da kuma kirkinsa. Tsaiwa ta danyi kadan tana sauraren muryar dake fita daga dakin,wata irin husky voice me zurfi da wani irin amo,cikin fada da kuma tsawa muryar ke fita,saidai kuma a nutse sautin yake fita kuma a jejjere,cikin ginshiri da wani abu da yayi kama da QASAITA.
Hannunta ta sauke daga kan handle din,tadan yamutsa fuskarta kadan,zuciyarta na mata fatan Allah yasa ba halittun maza aka tara a dakin ba,muddin hakan ta kasance bata jin zata iya dogon zama a tattaunawar tasu.
Cikin bawa kai qwarin gwiwa ta sake dora hannunta saman handle din,kalmar da taji ta fita a bakin mamallakiyar fusatacciyar muryar me zurfi yasa ta sake dakatawa
"You are fired,stupid woman" cikin qasa da second biyar qwaqwalwarta tayi mata rewinding,sak irin muryar da taji tana magana da wata mace cikin tsawa a bristol palace kwanakin da suka wuce,daga bisani kuma qarar mari ya biyo baya,qarar marin da ko a yanzun sai data sanyata rintse idanunta kamar a lokacin ake yinsa,ta kuma damqe hannunta abinda ya sanyata murda handle na qofar ba tare data shirya ba,saiji tayi ta tafi kai tsaye zuwa cikin dakin.
Cak ta tsaya daga bakin qofar,idanunta yana nutsawa ga tsakiyar dakin. Kallonta bai sauka a ko ina ba sai akan budurwar dake sharban kuka,kyakkyawar budurwa wadda zubin dressing dinta ke nuna zallar iya gayunta da kuma wayewarta. Dauke idanunta tayi daga kanta tana jin zuciyarta na zafi,ta sauke a hankali a kansa. Tsayyayen namiji sosai mai cikar haiba izza da kuma kamala,hannunsa daya yana sanye a aljihun wandon suit dinsa,daya hannun kuma yana danna wayarsa da zafi zafi. Dai dai sanda yake sanya wayar a kunnensa ya juyo,idanunsu suka sarqe guri daya.
A tare suka sake janye idanunsu kamar dai wancan karon,zuciyar sãahar cike da wani irin tsanarsa da kuma jin haushinsa,ko kadan maza basu da tausayi bare imani,suna amfani da raunin mata suna cutara musu,hakan wani karatu ne da take yawaita bitarsa a kwanyarta a duk lokacin da taga ire iren wadan nan rashin imanin na maza akan mata,saidai a yanzun shi din tamkar yana sake jaddada mata cewa haka tunaninta yake,karo na biyu data taba saninsa a rayuwa,amma duk sanda zata ganshi din cikin wulaqantawa da wofantar da kimar mata yake
"Ka sallameta da albashinta na wannan watan,ka hada dana watan gaba,banason ka nemeni akan wannan issue din,case closed" ya fada da murkakkiyar fuskarsa wadda ko kusa batayi kama data mutumin daya taba gwada yin dariya ba arayuwarsa,ko da yake a wajen mutane da yawa da suka sanshi haka suke kallonsa,sukan tambayi kawunansu harma da abokan huldarsu
"Wai shin yana dariya?"
"Shin wai ya taba dariya kuwa?"
"Ka taba ganin dariyarsa?".
A nutse ta taka ta yiwa kanta mazauni saman daya daga cikin couches din dake zagaye da qawataccen dakin,wanda aka yiwa tsari me ma'ana da baiwa ruhi kwanya harma da zuciya hutu. Dai dai lokacin daya kammala wayar,a karo na biyu ya sake daga kai ya sauke sexy eyes dinsa a kanta,wani fushi ne ya sake taso masa,wacece ita da har zata shigo masa dakin hutawa a sanda yake da buqatar hutu ba tare da izininsa ba?,wacece ita da zata shigo dakin da ba kowa yake baiwa izinin shigowa ba,har ta yiwa kanta da kanta mazauni ba tare data nemi yardarsa ba?,me ta dauki kanta?,dukka wadan nan maganganun dake ransa,shigowar Dr mahmud JARMA ya datsesu daga kwanyarsa,sai ya maida dukka hannuwansa cikin aljihun wandonsa,ya tattara hankalinsa ga mahaifinsa.
Sosai yake mata kwarjini da wani irin haiba dake bayyana a fuskarsa,don haka ta miqe tsaye sanda yake shigowar,cikin nuna girmamawa
"D'iyata ina fatan ban bata lokacinki ba ko?" Kanta a qasa tana murza zara zaran yatsun hannunta,cikin siririyar muryar nan dake da wani irin taushi da amo tace
"Babu komai abba" a hankali ya lumshe idanunsa yana zuqar numfashi da kyau zuwa hunhunsa,lokaci daya yaji wani abu me kama da rashin jituwa ya darsu a ransa,fitar sautin muryarta kawai yaji a ransa yarinyar batayi masa ba kwata kwata
"I hate it" ya fada can qasa yana sauraren muryar tata sanda take magana da abban nasa a karo na biyu. Haka kurum yaji zuciyarsa tana zafi,sai ya koma a hankali ya yiwa kansa mazauni akan daya daga cikin kujerun da aka tanadesu domin hutawar,wadanda zasu bawa gangar jiki qafafu da kuma baya daman zama Sosai su samu nutsuwa.
Yana jinsu sanda dr mahmud yake zama saman daya daga cikin sofa din dake dakin,har zuwa sanda yake umartar sãahar data zame ta zauna saman lallausan carfet din da aka ajjiye tsakanin kujerun
"Tashi ki zauna saman kujera mana,wannan meeting ne zamuyishi tamkar sa'anni,bawai na uba da 'ya'yansa ba" yayi furucin sãahar din na sake shiga zuciyarsa,d'a'arta nutsuwarta da tarbiyya girmama na gaba data samu suna sake saka mata qaunarta tare da jinta a zuciyarsa tamkar TOUFEEQ dinsa. Murmushi ta danyi kadan,sannan ta koma saman kujerar kamar yadda ta buqata.
A nutse ya waiwaya ya dubeshi,sai ya zuba masa idanu,yadda yayi kamar baya gurin da lumsassun idanunsa da eyelashes suka yiwa ado ya tabbatar 'yan halin sun motsa ko suna kusa,don haka yayi gyaran murya,ya kuma kirayeshi da sunansa na aihini
"Muhammad" kiran sunan da ya sanyashi ware idanunsa a hankali,a nutse ya rabo bayansa da jikin kujerar,ya zauna sosai hadi da crossing qafafunsa dake sanye da wata shiny black socks guri daya
"Ga khadijatou,itace sabuwar president na kamfanin nan da zakuyi aiki a tare,nake kuma fatan zaku kai kamfanin zuwa tudun mun tsira,inaso ka dauketa tamkar NADEEYA,infact....na damqa amanarta a hannunka kamar yadda yayanta na damqamin" idanunsa yadan lumshe kadan sannan ya budesu lokaci guda,yana jin maganar abban nasa wani iri,ba aiki tazoyi don a biyata ba?,ko raino aka kawota da za'a buqaci a bata kulawa?,kudi tazo nema fa,an yarda za'a biyata ita kuma ta yiwa kamfani aiki,fine.......ba shikenan ba?.
"Na yarda da kaifin basirarta,na tabbatar kuma idan kuka hada gwiwa,kuka hada qarfi da qarfe za'a samu kyakkyawan result din da akeso" maganar abban a gaba ta biyu ta sake katse masa tunaninsa. Baiko tsaya din ta bakinsa don yasan halin kayansa,ya waiwaya ga sãahar data nutsu tana sauraren maganganun dattijon,duk da tafin hannunta take murzawa a hankali
"Khadijatou,ga MUHAMMAD nan,a matsayin yayanki yake,kada kiji nauyi,idan kina da buqatar wani abu,koma meye ki tambayeshi,bashi da maraba da muhyiddeen,kinji ko?" Kai ta gyada masa,a taqaice tace
"In sha Allah,we will do our best"
"Barakallahu lakuma,zanyi alfahari da hakan".
Duk su biyun ya saka a gaba yana nuna musu wasu muhimman abubuwa da suka shafi company din wadanda su basusan dasu ba,toufeeq na hannun damansa,ita tana daga hagunsa,a lokacin idan ka shigo zaka dauka duka 'ya'yansa ne,shi kansa cikin zuciyarsa sai daya ji hakan.
Tsahon wasu mintuna kusan arba'in da wani abu sannan ya dakata yana dubansu bayan ya kalli tsadajjen agogon hannunsa,ya dan saki murmushi saman dattijuwar fuskarsa
"Inajin a nan zan tsaya,kusan muhammad kasan komai,zan barka da khadijatu,sauran abinda ya rage saika qarasa nuna mata kayi mata bayani,for the first time zatayi aikin kamfani,but tana da talent sosai,zan wuce kada nayi missing flight" ya furta yana miqewa. Dai dai lokacin da daya daga cikin guard dinsa yayi knocking qofar bayan ya samu alert dake nuna Dr din yana buqatarsa. Komai ya tattarawa uban gidan nasa,dr ya miqe yana duban toufeeq da shima ya miqe
"Koma ka zauna,ku qarasa kada lokacin tashi yayi" yadda yayi masa sallama haka itama sãahar,cikin girmamawa da ganin kimarsa,ya juya ya fita a office din,yana jin farinciki har cikin zuciyarsa.
Shuru ne ya ratsa office din tamkar babu sauran wani me rai,shi din yana daga saman kujerarsa,yayin daya dora sambala sambalan qafafunsa akan leg rest na jikin kujerar,yana kuma sarrafa computer dinsa cikin qwarewa da hannu daya. Ko sau daya bai dago kai ko yayi wani motsi da zai nuna yasan da mutum cikin office din ba,dai dai lokacin da sãahar ke zaune don cika umarnin dattijon,wayarta itama take sarrafawa,lokaci lokaci tana duba agogon hannunta,tana jiran kuma lokacin data dibawa kanta ya cika tabar masa office dinsa.
Kowanne a cikinsu jin kansa ya hanashi ya fara tankawa dan uwansa,cikin zuciyar sãahar tsanarsa da haushinsa ne fal suka danqare mata,ba tun yau ba tasan baisan darajar diya mace ba,bai martaba kimarta sam,a nasa sashen kuma ji yake sam batayi masa ba,tunda suke da Dr bai taba ganin mutumin daya jawo jikinsa har haka ba,farat daya ya maidashi tamkar ahalinsa,ya bashi dukkan yarda ya bude masa sirrinsa,yasan halin mata sarai,basu da kirki ko kadan muddin suna da wata manufa akan abu......tofa basa ji basa kuma gani harsai sun cimma muradinsu,suna iya komai,hakanan suna kuma iya jure komai har sai sun cimma gaci,musamman akan KUDI DA DUKIYA,suna sa masifar son kudi,tamkar wata halitta ce aka dasata cikin jininsu,basayin komai don Allah,bayason shi ko wani nasa ya sake fadawa MASIFA DA TARKON MACE,wannan wani HUKUNCI ne nashi da ya jima da yankewa akan kowacce mace idan ka debe MUTUM UKU RAK cikin rayuwarsa.
Sai da ya mula don kansa sannan ya janye hannuwansa da idanuwansa duka daga kan computer din,ya sarqe yatsunsa cikin na juna yana fitar da sassanyar siririyar iska daga bakinsa,ya maida shanyayyun idanunsa dake da wani irin qarfin fusgar hankali a muhallin da take sai kuma ya janye yana jin wani qyashi yana kamashi,dai dai sanda take miqewa a nutse cikin nata jin kan,ta zura takalmanta a nutse ta fara takawa zuwa bakin qofa
"Hey,da alama bakisan policies na aikin kamfani ba" ya jefa mata magabarya nutse ba tare daya kalli inda take ba,tsaiwa tayi cak,sautin muryarsa data tsana tana ratsa kunnuwanta,kamar tayi gaba,sai taga ya kamata atleast ta tsaya ta fuskanci wannan izzar tasa,don haka ta waiwayo cikin nutsuwa ta zube idanunta fes cikin nasa
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
*Arewabooks:Huguma*
https://arewabooks.com/u/huguma
Page 18
"Eheenn" sãahar ta furta a taqaice da alamun dake nuni da neman qarin bayani takeyi,sake zare hannunsa yayi daga kan system din,ya sanya idanunsa cikin nata a hankali kamar masu narkewa,wani abu me kama da fushi yadan ratsa ta tsakanin zagayayyun qwayar idanunsa
"Waye ya sallameki?" Ya fada kansa tsaye yana qanqance idanunsa cikin nata. Sai data kalli agogon hannunta sannan ta amsashi,tana jin kamar ta bude idanu taganta ba cikin office din ba,inda yasan yadda ta tsani hada hulda da maza da bai bari ta zauna tsahon mintunan da tayi a tare dashi ba,tana qoqarin hadiye fushinta ta amsa masa,saidai hakan bai boye tata izzar ba
"Lokacin daya kamata naci gaba da zama ya cika,inajin babu wani sauran abinda ya kamata na sani,inda akwai da ka sanar dani din" yadda take maganar with confidence ya bashi mamaki,karon farko da wata diya mace ta taba tsaiwa a gabansa cikin nutsuwa irin wannan ta bashi amsa takai tsaye,ta kuma amsa masa da abinda ya fito kai tsaye daga zuciyarta. Hannu yasa ya jawo wani file dake gefansa
"Inason nayi alerting naki abu daya,ki tsaya iya matsayinki,kada maganganun Dr ya rudeki,kina da naki limit din,so do not exceed that limit,right?"
"Don't bother" ta amsa masa a taqaice,duk da tanason ta gaya masa sama da hakan,to amma a yanzun bata da buqatar doguwar magana,sannan bai kamata ta take maganganun dattijon da bai dade da gama gaya mata su ba,bata sake bata koda second biyu ba ta juya ta fice abinta ba tare data tsaya jiran abinda yakeson gaya matan ba.
Sanda ta koma office sai abubuwan suka yita dawo mata,tanason taci gaba da aikin,amma kuma abinda ya faru cikin office din yana ta dawo mata a rai,a hankali sai zuciyarta ta fara zafi,ta dinga jan tsaki a jejjere,daga qarshe ta tabbatarwa kanta ba zata iya ci gaba da aikin ba,sai ta ture komai ta fara hada tarkacenta,ta dan debi wasu files da take tsammanin may be zata iya dubasu a gida,tabar office din bayan ta yiwa miss sameera umarnin ta rufe,ta dan bita da kallo tana mamakin yadda ta tashi abinda duk da lokacin tashi baiyi ba,bayan qaqqarfan jan kunne da CEO ya ajewa kowanne ma'aikaci akan makara da kuma tashi kafin cikar lokaci,a taqaice ma dai a kwanakin kusan kowanne ma'aikaci yana d'ara lokacin tashinsa,saboda yadda kowa ya maida hankalin wajen kawo daidaito da gyaruwar lamuran kamfanin.
Tana driving a hanya zuciyarta tana dada yin zafi,ta yaya zata iya aiki da wannan mutumin?,ta yaya zata jure aiki dashi?,kwata kwata nashi da manners,baisan darajar mutum ba,koda wayeshi,kowanne irin matsayi yake dashi,itakam ba zata taba jure ya takata ba,ba zata dauki kowanne banzan hali daga wajen kowanne d'a namiji ba yanzun.
Da wannan fushin da zafin zuciyar ta isa gida,tayi parking ta fito tana tattaro files din data taho dasu,fuskar nan a dinke na walwala taji takun afifa.
Ta cikin motar ta daga kai ta dubeta sanda take tahowa tana amsa waya,sanye da wata free gown,da alama tun dazun ta taso daga nata aikin,saita maida kanta taci gaba da abinda takeyi.
Tana isowa gurin ta gimtse wayar tana dariya qasa qasa
"Oyoyo mr president,bari na kwashi tabarraki" ta fada tana murmushi tare da qoqarin karbar folders din hannun nata,batayi jayayya ba ta sakar mata,ta fara kulle motar,afifa na gyara zaman folders din a hannunta tace
"How was your day today?" Yi tayi kaman ta cilla mata harara amma sai ta fasa,ganin cewa ba ita takar zomon ba,don haka ta amsa mata cikin miskilancin nan nata
"Bad" ta fada a taqaice tana soma takawa zuwa ciki,afifa tabi bayanta da hanzari
"Kaman yaya?,your first day at work fa" kai ta jinjina mata kawai tana lumshe ido ba tare da tace mata komai ba,sai afifan itama bata qara tambayarta ba,sukaci gaba da takawa zuwa ciki.
Maama ce zaune cikin falon,saman cinyarta wani dan bowl ne dake dauke da strawberry tana gyarawa,cikin kulawa ta amsa sallamar tasu idanunta akan fuskar diyar tata
"Barka da gida maama" sãahar ta fada tana isowa gabanta gami da duqawa,ta kuma dora saman cinyarta kadan. Murmushi ta sauke tana dubanta,gaba daya jiki da zuciyarta sun nuna gazawa xda gajiyawarta,saita zare hannunta daga cikin strawberry din ta dora saman kanta
"Barka kadai president dinmu,ya aikin?" Tabe baki tayi kamar wadda zata saki kuka,itako sunan batason a tuna mata,don da alama yaa muhyi ya bata aiki me wahala qwarai
"Ba dadi maama,ya muhyi yayi punishing dina ne kawai da wannan aikin" dariya afifa ta saki yayin da maama tayi murmushi
"Ba haka bane,da sannu dai zaki saba,qila ma ki dinga jin dadin aikin nan gaba kadan fiye da yadda muke tunani" miqewa tayi tana dan tura baki
"Anya maama zanso wannan aikin?"
"Ba wanda yasan gobe sai Allah" kai tadan jinjina
"Abba bai iso ba?"
"Ya kusa,inajin sai an idar da sallar magrib".
Zasu wuce baaba rabi ta iso zata karba strawberry din da zata markada,cikin fara'a da girmamawa ta amsa barka da gidan da sãahar tayi mata
"Barka dai farar d'iya,tun dazun nake dakon isowarki,abincinki ya kammala"
"A shiryamin dan kadan,bamai yawa ba,ina fitowa yanzu"
"A fito lafiya ummin abba" ta fada cikin nuna kulawa,maama dake zaue ta kalleta
"Rabi kece kike sake sakalta sãahar naga alama"
"Idan bamu tattalawa alhaji diya ba hajiya ai bamuyi halacci ba" sai kawai maaman ta bita da murmushi,kasancewar itadinma ba maison yawan magana bace.
Tare suka shiga dakin ita da afifa,ta zube mata takardunta a kyakkyawar kusurwaf da aka shiryama wani kyakkyawan table da kujerarsa,dan qaramin study room a maqale da bedroom din nasu,gurin an masa shiri na musaman da zaiyi dadin karatu,ta koma parlor ta barta a dakin.
A nutse ta cire kayanta ta watsa cikin laundry basket,ta daura wani lallausan farin towel,gab da zata shiga toilet din wayarta ta soma tsuwwa,dakatawa tayi tana duba number dake yawo saman screen dinta,zubawa numbers din dake jere reras idanu tayi,sai taja da baya ta wuce bandaki abinta,saboda number tayi mata kama da number mahmud,wadda a qalla kusan kullum tana ganin gilmawarta cikin wayarta da tarin saqonninsa da ko sau daya bata taba tsaiwa dubawa ba bare ta bashi amsa.
Mintina kusan ashirin da biyar sannan ta fito,ta tsaya gaban madubi ta tsane jikinta,ta shafe lallausar fatarta me sulbi da mayuka sannan ta mutstsike jikinta da turarukanta masu taushin qamshin da kwantar da zuciya.
Wani budadden cotton trouser ta saka,da wata free over size shirt me taushi,ta kama gashinta ta daure da band,idanunta suka sauka ga fuskarta da tayi wani irin fresh,babu alamun tabo ko qwarzane ko daya a kanta
_"ki tsaya iya matsayinki,kada maganganun dr ya rudeki,kina da naki limit din_" ido ta lumshe tana jin maganar na mata zafi kamar yanzun ya furta mata su,waye ya gaya masa buqatar kanta ce wai ta kawota companynsu?,baisan aikin tamkar wata tursasawa bane da karan tsaye ne da aka yiwa rayuwarta ba?,batason shafe maganar dattijon,hakanan batason zubda yaa muhyi a idanunsu,dole wani abun ta kauda masa kai,amma bafa komai ba,kuma muddin zasuci gaba da hada hanya da guy din ta tabbatar babu jimawa zasuyi batacciya,don ba zata iya shanyewa irin wadan nan halayen nasa ba,yadda yakema mata ita ba zata iya dauka ba,don ba abinda take nema daga wajensu.
Dogon tsaki taja,sannan ta juya tana fita a dakin bayan ta dauki wayarta,ta kuma goge duk wani miscall na mahmud da saqonsa da ya shigo bayan taqi daga wayar.
Still maama da afifa na zaune suna hira a parlor din,saita wuce saman dining tana duba abincin da baaba rabi ta ajjiye mata. Cikin wanda ta zuba din ta sake tsakurar wani,duk da bashi da yawa amma ba zai iya shiga cikinta duk ba,hakanan yanayinta yake,sanda tana qarama maaman tasha kaita asibiti,ayita bata multivitamin ko cikinta zai bude a samu cin abincinta ya qaru,saidai babu wani ci gaba,dole aka rabu da ita hakanan bayan sun fahimci halittarta ce a hakan.
Sanda ta kammala itama qasan ta sauko ta saka baki a hirar tasu,duk da kusan rabin hankalinta yana kan wayarta,ta shiga Instagram account dinta tana dubawa.
Har ta gota wani post saita dawo da baya a hankali. Hoto ne da aka yiwa cikakken daukan daya bala'in fita tarrrr,kana ganin hoton zakasan cewa da babbar waya akayi,irin wayoyin da sukasan haqqin fidda hoto da kyau.
_i'd never met anyone so quiet and beautiful simultaneously like him,his personality match his beautiful face MT JARMA_ Rubutun dake qasan photon kenan,sai tarin comments rututu,wanda kusan rabinsa na mata ne.
Wani bacin rai ne yazowa sãahar iya wuya,ta fita gaba daya daga Instagram din,wasu abubuwan ba shakka laifin mata ne,irin comment data dinga gani a qasan photon kwata kwata babu tsari babu kuma aji bare kamun kai irin na 'ya'ya mata,kamar a duniya shi daya Allah ya bawa baiwar kyau?,ba dole ya dinga buga wannan iskancin ba, muddin a zahirance irin wannan rawan kan da digimin matan suke masa,ranta ya baci sosai,har afifa ta kula ta tambayeta,amma sai tace ba komai,ta jawo saman wayar ta kashe data dinta gaba daya,dai dai sanda yaa zaid yayi sallama cikin falon,yana riqe da jakar abba,abban yana biye dashi a baya.
Cikin girmamawa kowa ke qoqarin masa sannu da zuwa,mutum me cikar kamala da kuma nuna qauna da sakewa da iyalinsa,yana da faran faran sakin fuska da kuma barkwanci,amma muddin zakayi ba dai dai ba da gangan da ganganci to fa baya lamunta,a nan ne zaka ga aihin Color dinsa.
Sassansa ya wuce daga nan ta qofar data hada sassan biyu,maama tabi bayansa ta barsu da zaid din yana tambayar sãahar ya aikin
"Lafiya" ta amsa masa a taqaice shima,afifa dake zaune daga gefanta dariyar da taketa dannewa ta taso mata
"Adai dinga jin tsoron Allah ana fadin gaskiya,atoh" waiwayawa tayi ta kalli afifan,kaman zatayi magana saita fasa ta maida idanunta ga wayarta
"Tell me,me ya faru?,da alama akwai magana tunda permanent assistant dinki ke dariya" shuru ta danyi kamar ba zatayi magana ba,sai kuma ta buda baki sound na bacin rai yana dan fita kadan a muryarta
"Bashi da kirki yaa zaid,he was trying to insult me as kamar ina neman wani abu da kamfaninsu" dan zuba mata ido zaid yayi sannan ya saki murmushi
"Try to relieve your anger dear,ki nutsu ki fuskanceshi,ki kuma fuskanci aikinki,ba don shi kadai kike zaune a kamfanin ba right?" Kai ta gyada
"So no need ki damu kanki,do all the right things,amma don't be rude to him,ya girmeki,show some respect zaki samawa yaa muhyi din mutunci,ki zama me kawaici yadda na sanki,kada ki bari qananun abubuwa su dinga bata ranki,kin fahimta?" Nutsuwa taji tana saukar mata,Allah ya sani yadda yayyenta suke nuna qauna da kulawa a gareta ya sanya itama take qaunarsu,take kuma qoqarin bin dukka umarninsu,yanzun maganar da sukayi da yaa zaid din ya samar mata da relief sosai,sai ta dan sake sukaci gaba da hira,har zuwa sanda akayi kiran magrib,ya fita masallaci shida abba,su kuma suka wuce ciki ita da afifa.
Ba kasafai take tashi daga saman abun salla da wuri ba duk bayan sallar magarib har sai tayi isha'i,kamar yadda takeyi bayan asuba har alfijir ya keto,saboda gurabene na amsar addu'a sosai.
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
https://arewabooks.com/u/huguma
Page 19
_____________________________
*_TAHO KI GANI_*👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
_shin kinsan da zaman wannan kuwa?,ko kina can kina bulayin neman inda zaki samu ingantattun kayan mata da SUPPLEMENT masu inganci cikin musulmin farashi?_
*Turqashi,ga biyan buqata ga sauqi*!
*ZAHRA DANGE* 👉🏽 _face behind LADY APHRODISIAC AND MORE_
*dealer in all kind of supplement and herbal aphrodisiacs kayan mata*
*Kayan mu will make you last on bed and permanently end the pain and embarrassment of weak eraction and premature ejaculation*
*Muna hadin bridal package*
*postnatal combination of natural herb's and supplement*
*Akwai hadin uwar gida mai da tsuhuwa yarinya*
*Akwai hadi na infection (sanyi herbs)*
*Akwai Zuma Mai saukar DA niima nan take tare da dandano Na mussaman*
*Muna kalolin gumbar Kamar gumbar madara, gumbar Aya, gumbar ridi, gumbar kasko, yar kicihi, Alhaji ba nan kake ba d.s*
*Akwai kalolin tsimi kamar Dan la'asar, tabaje, tsimin yar gata d.s*
*Muna DA kalolin gari nasha kamar sa buzu kuwa, sinadarin aya, abin sirri ne, emergency, rakumi DA akala, runbun dadi, kinfi Amarya d.s.*
*Muna special kaza, danbu,ciccibi, Yan shila,zuciya d.s*
*Akwai Na matsi different types DA sabulu na tsalki.*
*TA BANGAREN SUPPLEMENT*
*muna da na gyaran skin da kuma herbal aphrodisiacs supplement*
*Akwaisu Juliet eve, royal jelly, ultimate maca, suprodine, frozen detox, frozen collegen, majakani,amirna, khusus, dara,cantik ayu, pesona d.s*
*We have capsules, pills, chocolate, and different coffee that will make you sweet, firm, tight, young, beautiful and healthy.*
*Akwai different oils both siyan d'aya ko sari*
*Muna nan a garin SOKOTO sannan muna tura kaya ko ina a fadin duniya yaje maka cikin aminci IN SHA ALLAH*🌐
*_ZAKU IYA TUNTUBARTA KAI TSAYE TA WANNAN NUMBER WAYAR_*
07034400732
*_SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA_*👌🏽👌🏽👌🏽
*Tasted and trusted*💪🏽💪🏽💪🏽
_______________________________
Afifa na kwance rub da ciki a saman gadonsu,tana kallo ta system din sãahar din,furera mataimakiyar baaba rabi ce tayi knocking,afifa dake kallo tayi mata izini,ta turo qofar dakin a shigo,cikin girmamawa tace
"Maama tace a gayawa ummee,alhaji yana nemanta a sassansa" sãahar da takai ayar qarshe cikin surar da take karantawa ta maida qur'anin ta rufe
"Gani nan zuwa" ta amsawa furera,ta miqe zata fice,afifa ta nuna mata plates din da sukasha kankana tace ta wuce kitchen dashi.
Qur'anin ta mayar gurinsa,ta nade abun sallar sannan ta zura wasu slippers masu taushi a qafafunta tana mamakin kiran abban a irin wannan lokacin. Ko hijabin jikinta bata cire ba ta juya ta fice,afifa ta bita da kallo tana dariya qasa qasa,yau akwai daru kenan,sai ta gyara kwanciyarta sosai tana jiran dawowar rigimammiyar tata.
A nutse tayi sallama abban ya bata umarnin qarasowa,ta zare slipper dinta ta shigo,ta zauna daga qasa gefe guda. Dubanta yayi ba tare da ya ajjiye wayarsa dake hannunsa ba
"Ummin abba,ki duba setting room,kina da baqo". Jin maganar tayi kamar anyi jifa da abu ne nauyi cikin zuzzurfan rami,ya fada kansa tsaye ne ba tare da wata damuwa ko ganin nauyin maganar a tattare dashi,saita shiga ko kwanto,kodai bataji da kyau bane
"Na'am abba?,afifa dai ko?" A natse ya dago ya kalleta sosai wannan karon cikin idanunta
"Khadijatou nace" jikinta ne ya sanyaya gaba daya da yadda abban ya kira ainihin sunanta,wanda ta manta rabon daya kirata hakan,dukka gabobinta kamar an bi an doddokesu haka taji,ta tattara dukka qwarin gwiwarta,ta samu ta yunqura ta miqe,tana jin kamar iska na yawo da ita daga hagunta zuwa dama,daga gaba zuwa baya. Har takai qofa muryar abban ta sake cimmata
"Idan kinje ki dawo zamuyi magana dake" kai ta gyada masa kamar me ciwon baki,ta zura takalminta da a yanzu takejin kamar qafafunta ba zasu iya riqesu ba ta fice.
Minti daya ma ya isa ya kaita setting room din gidan,wanda babban qayataccen parlor ne dake farfajiyar gidansu,wanda a nan abban ke ganawa da baqinsa,to amma a yadda jikinta ya zama wani matacce,sai data debi mintuna biyu harda doriya sannan ta qarasa,zuciyarta cike fal da mamaki da kuma tunanin waye wannan?,me kuma yazoyi mata?.
Muryar ya zaid ta fara ji sanda take dage labulen parlor din,suka hada ido dashi,yana zaune hannun kujera suna hira da baqon dake saye cikin wata dakakkiyar shadda,qamshin turarensa ya cika falon,a sake sosai suke hira da ya zaid kamar sun dade da sanin juna,suna hada ido ya miqe
"Gata nan ma ta iso,sai nace ka gaida gida" ya furta yana miqa masa hannunsa sukayi musabaha,sannan ya zagayeta ya fice daga parlor din.
Shuru parlor din ya dauka,yayin da taci gaba da tsaiwa a wajen kamar an dasata,bata fita ba bata kuma qarasa shigowa ba bare ta samu muhallin zama. Hakan ya baiwa mahmud abba gana damar kallonta da kyau,duk da cewa cikin hijab take amma sassanyan kyawun nan nata bai gaza fitowa fili ba muraran,wata qaunarta ta qara linkuwa cikin ransa,batayi laifi ba idan tayi jan aji me yawa,ta cancanta,tako ina ta cancanci dukkan wata izza da ginshira,saidai inda dubban matan dake binsa zasuya wahalar da yakesha akanta,tabbas da sun dara,da kuma yasha kunya
"Me kake buqata?,me kake nema a gurina?" Ta tambayeshi kanta tsaye,don ta gundira da kallon da yake mata,kamar yadda taji ta tsani zaman falon.
Murmushi ya saki sannan ya miqe tsaye yana mata nuni da kujera
"Inaga zaifi kyau ki samu guri ki zauna,karki gaji da tsaiwar" ya fada yana murmushi,har cikin ransa yana jin dadin ganinta da wanzuwarsu guri guda
"Kada ka damu da tsaiwata ko zamana,kai tsaye ka fadamin abinda kake ya kawoka, inason komawa ciki,nabar ayyuka da yawa " murmushi ya saki yana goye hannayensa a qijinsa
"Ayyah,sorry,ina fatan ba aikin office ne ya gajiyarmin dake ba" idanunta tadan lumshe sannan ta budesu,ta gundura matuqa,da zai taimaketa daya taqaita komai da komai ya sallameta ta wuce ciki abinta
"Have a seat please" ya fada yana karyar da murya. Bata fiyason ayita roqonta abu ba,hasalima tun asali mutum ce da bata qaunar mita da kuma jan magana,don haka ga qarasa ta zauna a hannun kujerar da ya zaid ya tashi a kai
"Na gode" ya fada yana jin dadin yadda ta girmama buqatarsa,sai ya koma kan kujerar da ya tashi shima,idanunsa a kanta,abinda ya fara sanya ranta baci kenan,batason yawan kallo kwata kwata.
"Basai mun dawo da doguwar magana ba, tunda na fuskanci abinda bakeso kenan,kaina tsaye zan gaya miki,sonki nakeyi sãahar,so kuma irin na aure,qauna ta fisabilillah,bance ki soni yanzu yanzu ba,a'ah ina son ki bani dana zuwa wani lokaci,har zuwa sanda zaki aminta a karan kanki da soyayyar da nake miki,ki kuma gamsu da cewa ke din zaki iya aurena" ya fada yana hade tafukan hannayensu biyu waje daya,kamar me neman gafara.
Ji tayi kamar ya sanya wuqa ya yanki naman zuciyarta,tun bayan rabuwarta da adam yaune karon farko data zauna har kunnuwanta suka saurari kalmar soyayya daga bakin wani namiji,kalmar data jima dayin jana'izarta a kaf littafin rayuwarta,kalmar da takeji a ranta zuwa yanzu cewa qarya ce,babu wani so na gaskiya,saidai SON RAI da SON ZUCIYA da kuma SHA'AWA,sune zallarsu,ake musu ado da fenti a kirasu da soyayya.
A ranta taji kawai mahmud din yazo ne don ya bata mata lokaci,eh....bata lokaci mana, tunda bazai taba samun abinda yakeso daga gareta ba,sai ta miqe tsam
"Zanyi shawara" tayi furucin don ta samu ficewa a dakin,bawai don tana nufin yin shawarar bane da gaske,shawara akan abinda baida muhimmanci?,abinda ta riga ta sani ko sama da qasa zasu hadu bazai samu wannan buri nasa daga gareta ba
"Alfarma ya biyu,don Allah badon ni ba" yayi hanzarin fada ganin ta doshi qofar fita,dole ta tsaya ba tare data waiwayo ba
"Ko sau daya ne tak a rana ki dinga daga wayata"
"Banyi alqawari ba" ta fada kai tsaye tana qarasa ficewa harda 'yar sassarfa wannan karon,kamar wadda akace za'a kama.
Hanyar yabi da kallo harta bace masa,ya dunqule hannunsa ya kaiwa iska naushi,saidi fuskarsa murmushi ne a kwance,ko iya hakan yaji dadi a ransa,koba komai sunyi musayar kalamai duk da ba masu tsayi bane,a qalla an samu improvement ko yaya yake,zaici gaba da trying,bazai gaji ba,ya daga tsadajjen agogon rolex dake hannunsa ya duba lokaci,sai ya taka yana fita daga setting room din,wanda kafin ya iso tuni ya yiwa guard dinsa umarni sun shigo da uban siyayyar da yayo dukka domin sãahar din,karon farko daya fara tad'i da ita a cewarsa.
Rana ce da kuma lokaci na musamman a rayuwarsa da bazai taba mantawa da ita ba,duk da ba wani abun kirki ta gaya mishi ba,bai samu hankalinta da lokacinta yadda yakeso ba.
A wani mugun quntace take komawa zuwa falon abban,gaba daya ta shiga rudani da firgici,hankalinta a tashe yake kamar wadda wani mummunan abu ke shirin samunta.
Tana sallama dr mamman ya zuba mata ido bayan ya dauke kansa daga kan takardar dake hannunsa kafin yakai ga amsa sallamar tata,yana sauke qafafunsa dake harde waje daya qasa tare da binta da idanu,yanason karantar yanayinta da gaske.
Kanta a qasa ta tako lallausan carfet din dake shimfide a falonsa,madadin marbles din da aka qawata fiye da rabin qasan ginin gidan,ta zame a hankali cikin matuqar mutuwar jiki da wata fargaba ta zauna daura dashi
"Gani abba" zama ya sakeyi sosai,ya ajjiye takardar yana dubanta
"Ina kyautata zaton ba yau ne karon farko da kika fara ganinsa,nasan kuma zakiyi mamakin yadda akayi ya samu izinin ganinki direct daga wajena.....ya nema izinin soma ganawa dake ne kamar yadda shari'a da kuma al'ada ta tanadar,ya cika dukkan sharudda da akeson mai neman auren diyarka ya cika,wannan ya sanya na bashi izini,zaici gaba da zuwa har zuwa lokacin da zaku daidaita kanku,ku kuma aminta da junanku,kije kiyi addu'a,Allah yayi miki albarka" ya qarqare maganar ba tare daya bata damar cewa komai ba.
"Ameen" tayi qarfin halin kalato jimlar daga kowanne sashe na bakinta ta hadata sanann ta furtawa abban.
Sai da tayi namijin qoqari sannan ta yunqura ta miqe,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,haka ta dinga ji tun daga zuciyarta zuwa gangar jikinta a birkice.
Kasa qarasawa tayi cikin gidan,ta biyo ta farfajiyar gidan,sanna a hankali ta karkata zuwa sashen hagu na gidan,inda aka kebance wajen da wasu qawatattun kujeru domin hutawa musamman da yammaci,irin yammacin da zafin rana ke damun dan adam.
Kujera daya taja ta zauna akai,daidai sanda take fidda wata ajiyar zuciya me nauyi da zafi,tasa dukka hannayenta biyu ta dafe kanta da taji yana niyyar fara mata ciwo saboda nauyin da maganar ta yiwa qwaqwalwarta. Ko da wasa bata taba sanyawa a ranta mahmud zai iya zama saua daga cikin matsalolinta ba a rayuwa,kwata kwata ma bata taba daukar batunsa da muhimmanci ba,shi yasa bata ja masa layi tunda wuri ba,ashe tayi sake,gashi yayi mata shigar burtu,yakai wani guri da idan batayi da gaske ba zai iya sawa a tanqwarata tayi abinda bata da niyya ko lissafin yi.
Shurun da afifa taji yayi yawa sãahar din bata dawo ba,shi ya sanyata kashe laptop din ta sauko daga gadon,dakin maama ta leqa,ta sameta ta fito a wanka tana shiryawa
"Bata shigo ba,tunda kuka wuce daki tacemin ta taho da ayyuka daga office zata rage banga ta sake fitowa ba" sai afifan ta juya zata fita,har takai qofa maaman ta kirata
"Ko abbanku yayi maganar da ita?" Kai afifa ta gyada
"Haka nake tunani maama" jinjina kai tayi fuskarta na bayyanar da damuwa
"Dubata don Allah" juyawa afifan tayi ta fice itama jikinta yana bata lallai akwai damuwa.
Ta jima lausasan tafukan hannuwanta kife saman fuskarta,tanason ta daidaita yanayinta ne ta kuma ragewa kanta damuwa kodon ayyukan data debo masu yawa daga office. A nutse taji an dafa kafadarta,ko bata juyo ba tasan wacace,amma sai tayi burus,a wannan gabar itama afifan ta shafeta,haushinta takeji sosai,ko banza ta taka muhimmiyar rawa wajen faruwar wannan abun,tasan babu ta inda mahmud zai samu cikakken information a kanta sai wajen afifan,inda ta barshi kamar yadda ta bashi tsaye a wajen..... tun a ranar,da tuni an wuce wajen,batajin zata sake bashi damar ganinta ma bare wani abu makamancin wannan ya biyo baya.
Zagayowa tayi ta zauna ganin taqi waiwayowa gareta duk da ta tabata,tasan fushinta akanta,wannan din kuma da tayi alamace na tayi fushi. Sai data zauna sosai sannan tayi kiran sunanta,tsahon wasu sakanni ba tare data motsa ba,kamar bata jita ba,daga bisani kuma ta fara sauke hannuwan nata idanunta fes akan afifa.
Kallon kallo suka yiwa junansu,kafin ta miqe a nutse tara ture kujerarta baya
"Don't say anything......kinsan kome tunda kece silar faruwar komai din" ta fada calmly tana niyyar wucewa. Murmushi ne ya subucewa afifan,amma tasan cikin bacin ran da taketa kokawar dannewa take,don haka bata bari taga murmushin nata ba,ta miqe kawai tabi bayanta
"A shirye nake na fuskanci kowanne irin hukunci,nidai na shirya sauya rayuwar 'yar uwata ta kowacce hanya me kyau,wannan karon tare nakeson a daura mana igiyoyin aure uku" kamar ta sanya waigi ta tsaida sãahar din,ta dakata da tafiyar da takeyi,sannan ta waiwayo ta zubawa afifa fararen idanun nan nata,ta motsa siraran labbanta a hankali
"Aiba watanni shida masu zuwa ba,nan da shekara shida ma,ki rubuta ki ajjiye nan daura damaran yin aure ba" dukka girarta biyu afifa ta dage cike da tsantsar mamakin yadda kullum take dada zurfafa wajen tsanar maza,da kuma nisanta kanta da yin aure
"Ahhh.....kice mun kusa bada sadakar wata yarinya a gidan nan"
"Bismillah" ta fada a taqaice ganin afifa nason maida batun wasa,bata tsaya saurarenta ba ta wuce ciki.
Aiki biyu ta hadawa kwanyarta kusan lokaci guda,damuwa ga aikin office din data debo,haka ta yita yaqi da kanta,har Allah ya bata nasarar wancakalar da wancan batun,tunaninta da hankalinta ya karkata sosai ga files din da take dubawa,tanayi tana hada wasu bayanai a system dinta tana saving. Ba ita ta tashi a wajen ba sai sha biyu saura,ta fahimci abubuwa masu yawa tarin naqasu da kuma gyare gyare,tana kuma saka ran daga gobe zata fara gudanar da aikinta da dukkan fikira da baiwar da Allah ya bata,kafin ta kwanta ta hada dukkan wasu bayanai masu muhimmanci,printing dinsu as document zatasa kawai ayi idan ta isa office.
*_W A S H E G A R I _*
Ta tashi a miskilarta sosai,har ta kammala shirinta,yau dimma cikin wata lafiyayyar lafaya me bala'i kyau da asalin tsada,wadda ta dace da takalmi da qaramin band bag dinta samfurin kamfanin Hermes,tayi wani masifar kyau,daurewar fuskar tata ta sake qara mata kyau da kuma kwarjini na musamman,tayi wani irin sassanyan kyau,sulbi da laushin fatarta a ido kawai kana iya fahimtarsa. Sarai afifa ta fuskanci fushi takeyi da ita,yau da alama 'yan miskilancin har a kanta suka sauka,don haka tana tsaka da nata shirin fita gurin aikin,hannunta riqe da towel tana goge jikinta
"A sister like no other" ta fada tana kanne ido alamun tsokana,duk da cewa so take ta tsokaneta,amma har cikin ranta shigar ta sãahar tayi kyau sosai. Waiwayowa tayi ta jefa mata harara
"Ki samu wanda zakiwa dadin baki" qaramar dariya afifa ta saki, sãahar ta gama daura agogon hannunta,tana fesa lallausan turarenta afifa ta sake cewa
"Ki duba mudubi sosai fa kafin ki fita,gudun samun matsala" ta qarasa maganar tana qunshe dariya,datakawa sãahar tayi daga zuge zip na hand bag din nata,ta juyo tana duban afifa
"Matsala?,kaman yaya?"
"To ai wabillahi any moment za'a iya samun matsala,wannan kyan dake fita daga fuskarki kowacce safiya,kina zaton akwai namijin da zai iya gani ya kau da kai karon farko bai kawo kanshi ba?" Maganar ta fusgi hankalinta,saita waiwaya tana duban kanta da kanta a mudubi,tsahon wasu sakanni sannan ta dawo da dubanta ga afifa dake danne dariyarta,yanayinta yayi wani irin sanyi,kamae wadda ke shirin sakin kuka. Dukka kafadunta afifa ta dage ta yarfar da hannu
"No way out fa malama,indai ba shafa kashi zaki koma yi ba,just kawai ki bawa mahmud kai bori ya hau,shine zaki zama cikin aminci"
"Saiki auramin din mamata" ta fada adan fusace tana fusgar jakarta ta nufi hanyar fita,afifa ta saki dariyarta sosai
"Yo kwana nawa ne" banza tayi da ita,tabbas da biyu afifa ke mata hakan,amma inda tasan yadda maganar ke sanyata cikin firgici da razani da bata dinga tsokanarta da hakan ba.
Kamar kowacce safiya,a sassan abba ta samu maama,saidai ta taras ya Saifullahi yazo,suna breakfast tare da abban,ganin tayi musu sallama zata tafi bataci komai ba ya Saifullahi din ya tsaidata kan lallai sai taci wani abun,tsaiwar da zatayi tayi breakfast din zai iya bata mata lokaci,tana kuma son su shiga meeting din akan lokaci ko don cikar martaba da kamalarta,to amma sam ba zata iya ce masa a'ah ba,dole ta ajjiye hand bag dinta,taja kujera daya dake kusa da abban ta zauna ta hada tea.
_____________
https://youtu.be/y6YMU120RZI
Please subscribe to Rukayyat khalid YouTube channel fisabilillah. I only uploads videos na karatun Qur'an a tashar Please help me reach 1k subs soon insha Allah *RUKAYYAT KHALID*
*Assalamualaikum warahmatullah*
*Yar uwa shin mene amfanin wayar hannunki da bazaki koyi sana a da ita ba?*
*Kullum kina yawo a social media irin su Facebook, WhatsApp, tiktok,Instagram, twitter da ma sauransu.*
*Kina asarar data a banza kina zuba adashinda babu ranar dauka*
*bakya chas bakya as? Se chart kika iya 🤔*
*kin damu mijinki da BANI BANI?? Kizo nan ni* *~Graphics by Rukayyat~* *zan koya miki sanaar Graphics design wanda zaki samu abin dog dogaro da kai. Kina zaune daga gida kina sanaarki.*
*Ga mai bukata a masa design ko wani iri, munayi insha Allah*
SERVICES PROVIDED
🌹Logos
🌹Flyers
🌹data flyers
🌹Pos banner
🌹Book cover
🌹 Invitation Card
🌹 Business Card
🌹 Banner
🌹 Save The Date
🌹 Bank Sticker
🌹 Video Invitation card
🌹 Birthday Videos
🌹Business logo
🌹graduation poster
🌹e t c
Muna kowani design a farashi mai kyau idan training kikeso ma munayi shima a farashi mai kyau insha Allah kedai kimin magana ta wannan number 👇🏻
*DM FOR ANY ENQUIRY*
07084515410
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
https://arewabooks.com/u/huguma
Page 20
_____________________________
*_Wai wai wai_*
_wani kaya sai amale,don raqumi bazai iya dauka ba_
*MAAB LUXURY* _GIDAN ADO DA KECE RAINI_
*MAAB LUXURY* _DUNIYAR QAWATATTUN KAYAYYAKI_
*MAAB LUXURY* _TUNQAHON GIDA DA GININ GIDAN GABA DAYA_
_IDAN NACE ZAN LISSAFO BAZAN GAMA BA A NAN KUSA,DON SUN CANCANCI KOWANNE IRIN SUNA_
*DAME DAME SUKE SIYARWA NE?*👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
_SUN KAWO MUKU DALLADALLAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAWATARWA DANA KITCHEN MASU HASKA DAKUNAN GIRKI… KWASHA KWASHA_
_SU DIN KARSHE NE A DUNIYAR KAYAYYAKIN GIDAH DANA KITCHEN NA KECE RAI NI… INA UWAYEN GIDAH, AMARE? ANTOCI, KAWUNNI, YAYYU MAZA, KANNE DA MA IYAYEN MU MAZA?_
_KU ZO A DAMA DA KU A WANNAN DAMAR ME DAUKE DA DIMBIN KAYAYYAKI MASU KYAU A KUDI DEDE MISALI WANDA KOWANE ZAI IYA MALLAKA IYA KARFIN SA_
_KU ZIYARCI SHAGON DA KE A KANO.. TITIN AHMADU BELLO WAY_
_KO KUYI ORDER DA GA SHAFUKAN SADARWA TA INSTAGRAM: @Maabluxuryhome_
_FACEBOOK:@maabluxuryhome_
_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH,, INGANCI DA RAHUSA, KYAU A DADE ANA AMFANI DA SU SAI KAYAYYAKIN MAAB LUXURY HOME_
_A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY ORIGINAL HOME DECORS AND KITCHEN UTENSILS_
_MAAB LUXURY HOME GOT YOUR HOME AND YOUR KITCHENS COVERED… JUST A VISIT/CALL/DM AWAY_
_08034631010 MAAB LUXURY HOME👈🏽_
_______________________________
K'arfe tara saura mintuna goma na safiyar ranar motocinsa suka isa gurin ajjiye motoci na kamfanin,cikin hanzari cika aiki da sanin makamar aikin,daya daga cikin guards dinsa ya buda murfin motar,a yau din ba tare da wani tsaiko ba ya zuro baqi sidik din takalminsa kafin gangar jikinsa dake sanye tsadaddar suit charcoal color ta biyo baya,kunnuwansa manne da waya,ya waiwaya yana miqawa jibril daya wayar tasa,sannan ya fara takawa zuwa cikin kamfanin,cikin takunsa dake nuna zallar kuzari da kuma izza ta cikar mazantakar d'a namiji.
Duk inda ya gifta ma'aikatane ke zubewa,kowa yana qoqarin miqa gaisuwarsa cike da girmamawa,saidai har a sannan waya yake amsawa,baya samun damar amsa gaisuwar tasu,hakan kuma bai sanya sun daina ba,har ya isa ga elevator,ya shiga shida jibril da mr samson,sauran kuma suka suka biyo bayansa.
Har ya isa ga office din nasa waya yakeyi,wayar dake hannun jibril dince ta dauki tsuwwa,ya duba kiran sanna ya miqa masa da hanzari,sunan dake saman screen din yasa ya katse waccar wayar da yakeyi ya daga daya wayar,yana musu nuni da hannu. Rusunawa sukayi sannan suka juya cikin girmamawa suka fice.
Yadda ya sake yana wayar kadai ya isa ya gaya maka da mutum me muhimmanci yake wayar,ya bata a qalla mintuna goma kafin ya lallabata sukayi sallama,ya sake kallon fuskar wayar yana furzar da iska daga bakinsa,a duk sanda zaiji sautin muryar yarinyar,sai qauna da kuma zallar tausayinta sun cika masa zuciya,inama ace ana iya sauyawa mutum uwa,ba shakka da tuni ya biya,komai tsadar uwar muddin zata maye gurbin waccan,zata shafe sunanta,jininta zai fita daga nata jinin fita ta har abada,lallai da zai iya sarayar da dukka abinda ya mallaka indai hakan zata tabbata,saidai inaaaa...... KADDARA TA RIGA FATA. Wannan tunanin kawai ya motsa zuciyarsa qwarai da gaske,har sai daya fidda baqin glass dinsa ya sakaye qwayar idanunsa a ciki,cikin hanzari kuma ya danna kiran jibril,gwara yayi hanzarin aiwatar da dukka schedules dinsa na yau kafin tunanun yaci galaba a kansa.
Tsam saima ta miqe ta biyo bayan jibril dake yunqurin shiga office din,bata jin zata bari tayi asarar dare da wunin data bata taba zaben kaya da shigar da zatayi yau,ta lura,ko lokacin da ya shigo office din tana welcoming nasa,amma ko kusa ko alama bataga alamun ya ganta ba,bare ta sanya ran yaga dressing dinta.
A nutse ya motsa labbansa yana amsa sallamar jibril,idanunsa sunga saima din dake biye dashi,kallo daya yayi mata ya janye qwayar idanunsa ya maida ga system din,yana qoqarin binciken ganin kowanne department sunsan da meeting din yau?.
"Banason meeting din nan ya wuce nine thirty,a sanarwa dukkan board members din,banason makara,ina buqatar kowa a wajen on time"
"Yes sir" jibril ya amsa yana rusunawa,sannan ya juya zai fice
"Sir,am sorry,sai nake ganin dukka aikina ne fa?,so no need ka dinga kiran jibril,i can do it" ta fada gabanta yana dan faduwa,tana tunanin kalar amsar da zata samu daga wajensa.
Kamar baiji abinda ta fada ba har jibril dinma tuni ya fita,dauke hannunsa yayi daga kan system din,ya zare gilashin idanunsa,qwayar idanun nasa da suka dan canza launi ta fito tarwai,ya kuma zube dukka wani nauyi da uban kwarjinin dake cikinta saman fuskar saima,wadda a take taji tana neman faduwa,cikin dabara ta qarasa ga ma'ajiyar kayan sanyi dake office din ta jingina kadan don hanawa qafafunta rawar da suka fara yi
"Bake zaki tsaramin abinda ya kamata da kuma wanda bai kamata ba,aiki kika nema kuma an baki fine......wannan ya zama karo na qarshe da zanyi warning dinki,duk ranar kuma da kika sake......ki irga kanki a mazaunin korarriya" iya abinda yace da ita kenan ya maida gilashi fuskarsa ya sake tattara hankalinsa ga abinda yakeyi,kai ba zakace shi yayi wannan maganar ba a yanzu.
Mutuwar tsaye tayi,kafin ta samu ta tattara dukka qwarin gwiwarta,ta juya a hankali ta fice. Cikin tsananin bacin rai ta zauna da qarfi saman kujerarta tana maida numfashi,sai kuma ta jawo jakarta dake saman teburinta ta ciro mudubi takai ga fuskarta,so take ta hango wani aibu nata da ya hana taoufeeq bata koda lokacinsa ne bare akai ga hankalinsa,tanason gano wanne irin naqasu take dashi da har ta gaza samun kansa,ta kasa samun soyayyarsa.
Ba abinda ta hango sai doguwar fuskarta ne dauke da siririn hanci da kuma manyan idanu masu girma qwarai,ita kanta tasan tako ina bata da wani makusa ko aibu,KE KYAKKYAWA CE,kullum abinda tarin mazan da take tare dasu suke gaya mata kenan,taji hakan daga bakunansu ba sau daya ba ba sau biyu ba,amma a yau dukka wannan kyan nata ya gaza amfani a kansa?.
Maida dubanta tayi ga shigar jikinta,kayan data kashe kudade masu nauyi ta siya,tasa aka zauna aka tsara mata dinki na jan hankali,amma ko sau daya,ko bisa kuskure bai kalli gangar jikinta ba bare tayi tunanin ya kula har hakan yaja hankalinsa. Madubin ta wurgar cike da bacin rai da kuma zallar takaici,ta kifa fuskarta saman jakar tata,tana jin kamar fa fashe da kuka ko zata samun sassaucin wannan musibar.
Tare da miss sameera secretary dinta suka shigo office,ita ta riqo mata jakarta har ciki,tana shirin zama cikin dan sakewa tayi magana da sameeran
"Ina fatan kowanne department a shirye suke?,qarfe goma dai dai zamu shiga" kai ta jinjina
"Abinda na fara yi kenan ina shigowa office"
"Alright,ki tattara dukkan bayanan nan ki fidda minsu as document,ko basu samu duka kafin lokacin ba ina da buqatar mafiya rinjaye"
"Ok madam" sai ta amsa ta fice,yayin da sãahar din ta soma rage wasu ayyukan kafin cikar lokaci.
Cikin girmamawa jibril ya dawo,yayi sallama ya amsa masa ba tare daya daga kai daga abinda yakeyi
"Sir,akwai wani taron daga office din president,all employees daga dukkan departments,ten o'clock" da mamaki ya tsaya da abinda yakeyi din,ya zubawa jibril idanunsa
"Akwai wani meeting da za'a yi irin wannan ba tare da an shaida min ba?"
"May be an tura email zuwa ga secretary,shaida maka bane batayi ba" a nutse ya maida bayansa ga kujera ya jinginar,a yadda yasan halinta ya tabbatar ba zata kasa gaya masa ba
"Koma daga office din waye a sanar nayi cancelling dinsa,wannan taron shine most important"
"Yes sir" ya fada sannan ya juya ya fita don ya fara sanarwa saima,dole idan suna buqatar isar saqon akan lokaci ta tayashi tura sanarwar.
Siririn tsaki yaja,ya tsani wannan power din da Dr ya bata,a wajensa kamar bata cancanceta ba,a matsayinta na baquwa,wadda batasan komai akan aikinsu ba,batasan kuma komai da ya shafesu ba,sai ya miqe yana cire suit jacket dinsa,yayi hanging dinta,sannan ya taka zuwa bakin qawataccen books shield da aka jera takardunsa da kuma litattafan cikinsa a tsare gwanin burgewa,ya zuge ya debo wasu takardu,dai dai sanda sajjad ya shigo.
A nutse ya amsa sallamar tasa ba tare daya waiwayo ba,ya dauki abinda zai dauka ya rufe sannan ya tako zuwa inda sajjad ke tsaye. Hannu kowa ya dunqule ya miqawa dan uwansa kamar zasu daki juna,wani salon gaisuwa da suka saba yi a tsakaninsu,kafin daga bisani kowa ya ware hannun sukayi musabaha sosai,ya fara takawa zai koma kan kujerarsa
"Tun jiya naga sanarwar general meeting daga office na president,yau kuma katsam sai gashi kayi cancelling ka maye gurbinsa da naka" sai daya zauna sosai sannan ya aza zagayayyun manyan idanunsa a kansa
"Yes,anything else?" Kafada yadan dage yana samawa kansa gurin zama
"Eh......kamar bai dace ba,bai kamata kayi cancelling ba dab da lokacin yin meeting din" ya qarashe maganar yana daukar wata calendar dake dake gefansa yana dubawa,baiyi maganar dama don ya bashi amsa ba,don yasan dama ba lallai bane ya amsa masa din.
Shuru tayi tana duban Miss sameera bayan ta shaida mata anyi cancelling meeting nasu gaba daya daga office din CEO,an kuma maye gurbinsa da board meeting,ranta yadan baci kadan
"Amma for what reason ne sameera?"
"Madam,ban gani sun fada ba,amma dai i think wani babban uzuri ne ya taso" shuru ta sakeyi kafin daga bisani tace
"Alright,ki shiryamin takardun da zan fita dasu" ta amsa mata a aladabce ta fice.
Delay din da aka dan samu kafin miss sameera ta gama hada komai,shi ya kawo tsaikon fitarta on time,ta tsaya ta gyara yafen laffayarta,ta dauki wayarta da system dinta sannan ta fito,sameera na biye da ita
"Madam,idan ba damuwa zan rigaki isa gurin" ta fada cikin girmamawa,kai sãahar ta gyada mata,dom ta fuskanci me take nufi,miss sameeran hard worker ce sosai,hatta da yanayin tafiyarta irin me gab gab din nan ne cike da sauri,ita a iya nata yanayin halittar iya saurinta kenan,amma ta tabbatar ya yiwa sameeran kadan,shi yasa ta bata wannan damar.
A floor din dake qasan nasu za'ayi taron,ta isa gaban elevator ta bude ta shiga,ba kowa a ciki sai ita daya,wannan ya bata damar sakewa. Saidai qofar na shirin rufewa,sai taga ta tsaya,abinda ya sanyata dago kai kenan a nutse tana duban bakin qofar.
Kafarsa dake saye cikin rufaffen baqin takalminsa ya sanya daga bakin qofar,abinda ya hanata rufewa kenan saboda na'ura na aikata da saqon akwai mutum dake shigowa ciki,duk da cewa yana magana da wani dake tsaye a bayansa,amma hakan bazai hanaka ganin gefan kyakkyawar fuskarsa wadda ke kwance lamban da suma ba,sumar dake baki sidik ta kuma kwanta da kyau saman farar lallausar fatarsa,sassanyan qamshinsa dake kai kawo har zuwa cikin elevator din ya karade gurin.
Ido ta janye a hankali tana goye hannuwanta a qirjinta,ta lumshe idanun nata can qasan ranta tana addu'ar idan ya ganta ya koma kamar yadda suka saba,duk yadda takai ga qin hada hulda da maza,ba kasafai takejin tsanarsu ba indai ba harkarta suka shiga ba,amma shi wannan din,tana jin tsanarsa ne naturally daga qasan ranta,banda yana tsaye ne ta bakin qofar,ita kuma tana jin qyashin ce masa ya matsa,da tuni ta fice daga elevator din,ta gwammace ta jirayi wata,koda zata sake bata lokaci fiye da wanda ta bata dazun.
Dai dai sanda tunaninta ya yanke ya kammala magana da mutumin,ya matso da niyyar shigowa idanunsa ya fada a kanta,ta karkatar da kanta daga fuskantar qofa ta maidashi left side dinta kamar me kallon wani abu na daban,sai ya janye shanyayyun idanunsa,yana tsuke fuskarsa da kyau,cikin ransa yanajin ya kamata a raba elevator din maza da mata a company,bai kamata aci gaba da cudanya haka ba,ya isa ga madannin ya bata umarnin inda zata saukeshi.
Ganin ya gama shigowa kuma qofar bata kai ga rufewa ba,saita sauke hannunta,ta kuma nufi qofar da niyyar ficewa ta sauya wata,sarai ya ganta,ya kuma fuskanci fita zatayi saidai hakan bai dakatar dashi daga dannan madannin ba,wanda gab da zata fita qofar ta rufe ruf,sannan kuma ta fara sauka dasu zuwa qasan da sasarfa cikin cika umarnin da aka bata.
Saukar data fara yi cikin ba zata babu zato wani jiri ya fusgeta,qaqqarfan tsoro ya mamayeta,ta runtse idanunta cikin hanzari ta dafe qarfen dake kusa da ita,tun asali ita ba me yawan son hawa lifter ko wani iri bane,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya tana sauke numfashinta a hankali,har zuwa sanda taji tsaiwar elevator,saidai abun takaicin tun bata bude idanunta ba taji floor din da suka sauka ba nan zata je ba,ta bude idon a hankali ranta yana baci. Daga bakin qofar ta ganshi a tsaye yana magana da daya daga cikin guard nasa.
Sosai ranta ya baci,do meye zai maida elevator din jirgin yawo?,bayan yasan bashi kadai bane a cikinta,koda baiyi hakan ba already tasan shi din ba mai sanin darajar dan adam bane,yana da izza, izzar da a kallo daya zakayi masa ta karanceta tasss saman fuskarsa da motsinsa.
Bata sake motsawa ba daga gurin,ta bawa banza ajiyarsa har ya gama abinda zaiyi,ya sake takowa ya zabi floor din da zata ajjiye shi tamkar baisan da mutum a ciki ba. Tana iya jin sanda kira ya shigo wayarsa,ya daga ya kara a kunnensa,saidai bata iya jin abinda yake fada clearly,taja tsaki qasan ranta kamar zata tsinke zuciyarta saboda haushi da kuma takaicinsa.
0 comments:
Post a Comment