"Ranka ya Dade gurinka nazo tin safe an hanani ganinka a waje na wuni tsaye har Rana ta fadi akaina,
Alhaji ka saurareni maganar danake tafe da ita Mai tsananin girma da mahimmanci Ce sbd maganar Rai da mutuwa akeyi data shafe ahalinka da nawa ahalin."
Kalmarsa ta qarshe Ce ta Saka Dd babba waiwayowa ta kallesa tinda ya fara magana bai juyoba,
"Maganar Rai da mutuwa tsakanin ahalinsa dana kaantes?
Daga Ina wannan din yake?
Lafiyayye ne ko kuwa?" Shine kallan da Dd yayi wa shugaban securities na gidan nasu kafin ya maida kallansa kan Ababa Dake a shirye qyam zantikansa a tsare tsaf cikin ransa da zai jero.
Ganin kallan da Dd ke masa yasa take yayi fuskar tausayi da bacin Rai tareda bayyanarda baqin cikin rayuwa na tareda shi kaman Wanda yayi rashin uwa da uba da kowa na duniya.
Cikin nutsuwa Securityn ya Dan matsosa Yace
"Bismillah malam ko¿Mu Dan je daga waje sai naji abinda ya kawo ka zaa duba matsalarka,muje Bismillah.
Girgiza kai Ababa yayi cikin sake bayyanarda Yana cikin balai da masifar rayuwa Ya sake Maida kallansa kan Dd babba dayake shafa adduarsa daya gama Yace
"Ranka ya Dade Dan Allah ka saurareni,
Kai kadai ya kamata yaji matsalar data kawo ni,
Ina cikin tashin hankali da masifar da bazan iya kallan jamaa ba,
Ni nawa mutuncin ya Riga ya fara rauni a idan duniya,
Banda zabi ne shiyasa nazo Dan kaima kasa muguwar tsautsayi ko kaddara zance data faru tsakanin 'dan gurinku da 'ya.....
Bai qarasaba Dd ya juyo ya zuba masa idanuwansa masu kwarjinin arziki da dattako sbd a duniya idan akwai abinda Dd babba ya tsana Ji shine hada Kalmar
"wani abu ya faru tsakani"
Ababa kuwa sake qasqantar dakai yayi idanuwansa na bayyanarda hawaye masu bayyanarda radadi da zafi tareda quncin rayuwar tsaka me wuyar dayake son nunawa Dd babba Yana ciki.
Shiru Dd babba yayi tsawon mintina Yana nazarin Ababa da kukan dayake Yi a matsayinsa na dattijo kafin ya dago kalli Securityn Dake tsaye a kansu cikin nutsuwa Yace
"Ba komai kaje kawai"
"Yes Sir" Yace tareda kallan Ababa ya juya ya bar gurin ya fice masallacin gabaki daya.
Saida securityn ya fice gabaki daya
Dd babba ya Dan sake kallan Ababa Bai basa Daman magana ba sukai shiru sai da limamin masallacin ya gama nasa lazimin ya fice ganin alaman magana zasuyi Kila Mai mahimmanci musamman duk Wanda yasan Dd babba yasan baya wasa da tattali da Hana kowa yaji sirrin ahalinsa,
Bai yarda ko yayane wani yaji sirrin kaates ba sbd a yanda suka kafu Allah ya girkasu da sanin sirrinsu Kawai zaa iya ganin an rusa su,
A baya hakan yaso faruwa dasu Amma ya tsaya tsayin daka Allah ya taimakesa ya Hana matsalar rusa ahalin daya wahala yagina,
Ginin da har jikokin jikokinsa inshallah bazasu San meye talauci wahala da quncin Rashi na arziki ba saidai wata jarabawar ta rayuwa daga ubangiji.
Kalman Ababa ta cewa "wani qaddara ko tsautsayi tsakanin ahalinsa na kaantes da nasa" ya sakasa basa Daman sauraransa dan farajin koma menene idan ba mahaukaci bane lullube a cikin kaya Bai sani ba.
Bayan ficewan malam liman Dd babba ya Dan sake kallan Ababa daya share hawayensa hannuwansa na rawar tashin hankalin dayake tattare dashi da damuwa ya sunkuyar da Kai cikin rawan murya wani kukan na son sake zuwar masa Yace
"Ranka ya Dade 'dan gurinku Alh Bilal kaante Yana soyayya da 'yata bansaniba sai cikin qaddara kwatsam muka tsinta a jikinta,
Ranka ya Dade ku taimakeni kumin Rai wlh mutuwa zanyi idan ta haife wannan cikin a gida,
Bazata taba samun mijin aurena rayuwarta ta lalace,ta gurbace,ta nakasa,ta.....Jin shiru ba motsin Dd babba ba maganarsa ya Saka Ababan dagowa Ya kallesa kafin yaci gaba da bayaninsa.
Kallansa Dd babba keyi cikin wani irin yanayi na mamaki da Hana zancen kaiwa zuciyarsa bare shiga cikinta,
Yama rasa yanda zai juya zancen bare ya karba cikin Kansa Dan haka ya Dan sauke numfashi a hankali Yana Dan gyara zamansa sai alokacin ya Bude Baki cikin nutsuwa yace
"Meye sunanka?
Daga Ina kake?
Kasan Bilal kaante din Da kake magana akansa?
Ka taba ganinsa a zahiri?
Maana ka taba ganinsa tare da 'yar taka?
Wani zufa ne ya yankowa Ababa Amma Kuma a yanda ya zo ba gudu ba ja da baya wlh sai ankarba cikin yarsa ko kowa yasan Dan kaantes yawa yarsa fyade.
Dan haka sake tattaro nutsuwa yayi cikin daidaita murya Yace
"Sunana Ababa Sulaiman,
Daga kauyen bairi iyayena suke ni anan na tashi anan nake zaune da iyali na,
Alhaji Bilal din Kuma ban taba ganinsa ba a zahiri,
Amma ita ta san shi farin sani,
Ni dai rokona A yimun adalci ya duba lamarin sbd nine a cikin cutatarwa da qunci da bacin Rai,
'yata na asibiti yanzu haka Rai hannun Allah..
Shiru Dd babba ya sake Yi sbd zancan yafara basa mamaki da shakku Kuma,
Meye hakan yake nufi?
Ciki Bilal yaiwa wata ko me?
Sam ba halinsa bane,
Baya kula mata ma bare nemansu da fasiqanci,
Tayaya Rana tsaka haka kawai kaman almara kokuma aikin rashin hankali azo masa da zancen bama yanzu ne ake zarginsa da laifin kebewa da macen ba aa cikin ma gabaki daya aka zo da zancen har ansamu,
Wani nannauyan numfashi ya sauke zuwa lokacin zuciyarsa tafara sauyawa duk da haka dai zancen sam Bai shigesa ba bare karbuwa
Yafara saka Ababan a jerin batan hanya yayi kokuma ansamu kuskuren gurin zuwa sbd sunan Kila yazo daya da wani Bilal din ba nasu ba.
Amma baya garage Sam a rayuwarsa Dan haka komai nasa yake yinsa a tsari da lissafi Shima kaman Ababa saidai nasa lissafin daya baya wasa dashi shine akan suna da mutuncin ahalinsa, sbd yayansa uku duk Maza Babu qaramin mutum a cikinsu,har senator akwai aciki hakama jikansa daya Minister ne tayaya zai bari mutuncinsu da sunansu ya tabu daga shi har 'yayansa qasa zasuyi Harma da sauran jikokinsa Dake dake cikin lokacin nasu sunan da mutuncin tinda sun zama Manyan mutane suma Dan haka lissafi indai akan ahalinsa ne baya batan lissafi ko garaje.
Kallan Ababa yasake ya sake sauke numfashi Mai dumi kafin Yace
"Ba damuwa naji zancenka,
Zaa warware Maka kuskuren fahimtar da aka samu akan lamarin duka,
Bilal kaante dakake Ji daban Wanda yanzu kake magana akansa daban,
Allah ya tsare gaba ya kare Yakuma shirya mana yayanmu duka,
Wannan sabanin fahimta ne kayi.
Da sauri Ababa ya Bude Baki zaiyi magana Dd babban ya dakatar dashi sbd shi ko sunan zancan baisan ana dangantawa da Bilal din dan ma dah da DD aka danganta zancen bazai iya danne bacin ransa ba ko Hana fushinsa bayyana akan wannan mutumin.
Miqewa yai tsaye a hankali cikin nutsuwa Yace Ababan ya biyosa
Suka fice masallacin zuwa cikin gidan Kaantes din.
Abinda yasa zai tafi da Ababan dan warware masa fahimtarsa da tinaninsa akan ya cire zancen sunan kaante ne kwata kwata acikin zancen basuda alaqa ko daya da maganar.
Securities na ganin Ababa bayan Dd babba suka Dan taso Dan dakatar dashi Amma Dd ya dakatar dasu Yace su barsa kawai zai gansa ne.
Ciki suka shige Kai tsaye
Gate din na farko yasa hankalin Ababan tashi suna shiga gate na biyu asalin Inda harabar gidan take makekiya komai a tsare da kyau da aji kaman ya baro qasarsa yaji,
Motocin dasuka kunce masa lissafi yake kalla idanuwansa kaman zasu fado qasa,
Take lissafinsa gabaki daya kwata kwata ya kunce wlh bazai yarda ba cikin nan ya zube,
Idanma ya zube bazai yarda ba sai anbiyasa diyyar keta haddin yarsa da dirka mata cikin farko ba aure.
Wata firgita ya sake Yi lokacinda suka Isa office din Dd babban Dake cikin gidan Dake gefe daya daga bangarensa dayake farko farko.
Sanyin Ac daya tarbesa yasaka shi Saka lissafin Ac take a budget dinsa na gaba cikin abinda zaa kasafto masa.
Italian office set din dasuka qayatar da palon yake kalla Yana sake kokarin yaqi da Hana zallan zalamansa fita ya danne Kansa da nutsuwa da kame Kai.
Gurin zama Dd babba ya nuna masa daya daga cikin kujerun alfarmar Dake jere.
Zama yai Yana sake Satan kallan wata drawer dafi komai tsayi da wani glass a office din zuciyarsa na kissima masa Kila uwayen daloli ne a ciki.
Numfashi Dd babba yasake sakewa a karo ba adadi tin farkon Jin zancen dake tafe da Ababan kafin ya miqa hannu kan wayarsa Daya bari kan stool na set din kujerun dakin dazai fita sallah take ya nemo numbern Bilal ya Saka kiransa.
Yana dauka Kai tsaye Yace ya samesa Daman yasan da dawowansa Bai nemesa bane Dan ya bari ya huta kafin su zauna maganar aikin dayayo acan tsawon watannin biyu.
Jin Bilal aka Kira yasa Ababa Jin fargabarsa ta fada Dan kuwa gwara ayita ta qare din
Dan tin farko da yasan ya dawo ai shi zai fara tinkara kafin su qaraso gurin Dd din.
Shiru sukai Babu mai magana kowannensu yayi Nisa a nasa tinanin da shakkar yanda zata kasance.
Shidai Dd babba fatansa daya kawai duk tsanani kada ma ya kasance Bilal yasan wanna mutumin bare 'yarsan dayake magana Akai,
Zaifi farin cikin ace anzo masa da labarin sunyi asarar miliyoyin kudi masu yawan gaske akan wannan labarin ya sake kasancewa a zuriarsa,
Ya karbi jikan farko ta wannan hanyar bazai yarda ya rungumi tattaba kunnen farko ba ta wanna qaddarar sbd wani tabo da ciwo ne Mai qarfin gaske da haryanzu yake dandana ciwonsa duk da qaddarar ta banbanta da wannan.
Ya kasa karba Bilal zuciya Dari bisa Dari sbd baida shedan auren da 'dansa ya daura boye da mahaifiyarsu Bilal din farko har aka samu cikin,
Madaurin auren ya mutu masu shedan auren sun mutu tayaya zai yarda da auren nasu?
Ya kwato mutunci da sunansa daqyar yayiwa zancen lullubi da wata irin dukiya Mai yawan gaske da har kullum yake shakkar fitarsa sbd baisan ta wace fuska mutane zasu karbi matsayin Bilal din ba jikansa na farko,A matsayin Dan gaban fatiha ko a matsayin Dan Sunna.
Wannan dalilin nasa yasa har ko yaushe DD ne asalin Wanda zuciyarsa ta karba ta riqe bari bisa Dari fiyeda duka sauran jikokinsa sbd Saida ya sake daura auren Fatima da dayyab din tukuna hankalinsa ya karbi auren nasu kafin haihuwa DD da sauran kanwarsu.
Ta Ina yanzu zai fara da wannan Shima idan ya tabbata cikin ne daga ahalinsu wannan mutumin yake magana.
#MAMUH#
For more pages Kuyi joining VIP or Arewabooks
#DD KAANTE
#BENA ABABA
#CRAZY
#LOVE/MARRIAGE/ROMANCE
#SUMAYYAH ABABA
#BILAL KAANTE
#ZAFIN KAI
#MAMUHGEE
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
29
Zaman shirun yake sake girmama tinani da burikan Ababa game da lamarin komai ya sauya na lissafinsa Kuma,
A yanzu baida burin daya wuce su karba cikin kawai ya Dora sharidansa kai tsaye ba batawa juna lokaci.
Dd babba zuwa lokacin jininsa yafara kokarin Hawa Amma dayake jajirtaccen mutum ne Mai qarfin zuciya da Iko sai ya danne ya Hana Kansa karban zancen Tako Ina daga zuciyarsa har cikin Kansa.
Bilal kawai yake jira a datse zancen ya sallami mutumin tareda gargadin ko sunansu karya sake shiga cikin zancen ko gun Bada labari ne na yayi sabanin fahimtar zuwa gurinsu.
Knocking kofar da akai yasa gaban Ababa daka tsalle zuciyarsa na tsinkewa take shakku da fargaba Kuma Mai tsanani yashigesa na abinda Bilal zai fada akan cikin yanzu shine zai tabbatarda matsayin samunsa da rashinsa yanzu kam,
Dan idan Bilal Yace Bai san sumayyah ba kokuma cikin to tabbas ta tabbata daga yau yakoma Nobaba,
Idan Kuma Yace yasan da sumayyahn ko Bai san cikin ba wlh sai sun karba Dan ko ba nasa bane sai ya maqala musu kafin ya koma gida su fuskanci juna shi da sumayyahn Harma da uwarta da Benazir.
Shi kansa Dd babba sai daya sauke numfashi ahankali Mai sanyi kafin ya Bada izinin shigowar.
Kaman yanda suka tsammata Bilal dinne
Gabaki dayansu idanuwansu akansa suna kallansa a tare kowannensu da fata da abinda yake buqatan Bilal din ya tabbatar.
Shi kuwa Bilal hankalinsa akan Dd babban yake sbd baisan Ababan ba Dan Bai taba ganinsa ba sai so daya Kuma da yamma ne daga nesa Dan haka Bai qarar da kamanninsa ba dan haka Yana shigowa cikeda nutsuwa da ladabi ya qarasa ciki ya Isa gaban Dd ya zauna ya gaidasa cikin girman da nutsuwa kaman yanda ya saba.
Numfashi Dd ya sake saukewa kafin ya amsa gaisuwar cikin kulawa ya masa barka da dawowa.
Amsawa yayi Yana kokarin danne tasa damuwar da tashin hankalin dayake ciki na zancen sumayyahn sbd baisan ta inda zai bullo ba Dan yasani Babu maganar karban wannan qaddararriyar maganar a cikin dictionaryn Kaantes din Dan haka yake cikin tsaka me wuyan da baisan Ina zai Saka Kansa Harma da sumayyahn ba.
Gyara murya Dd babba yayi da kyau cikin nutsuwa kafin ya fara da cewa
"Ga bako Nan a bayanka zaune ka duba da kyau ko ka Sansa Dan bakon kusan na ke."
Juyawa yayi cikin nutsuwa ya kalli Ababa ya gaidasa jiki a mace tareda dawo da kallansa ka Dd babba Yace
"Ban Ganesa ba gaskia sai an tinatar Dani."
Magana Ababa zaiyi Dd babba ya daga masa hannu fuskarsa ba sauki ko sakewa ko kadan
Take kwarjininsa ya cika masa Ido gabaki daya dan haka dole yayi shiru zuciyarsa na sake tsinkewa da zancen da Bilal yafara dashi.
"BILAL" Dd ya kirasa Yana kallansa Kai tsaye da son tabbatar masa mahimmanci maganar da zaiyi masa.
"Na'am"
Shima ya amsa cikin nutsuwa da jikinsa dayake bayyanarda sanyinsa a yanzu.
"Bilal wannan bawan Allah gashi Nan yazo tin safe Yace Yana son ganina bai samu damar ba sai da magrib ya Dana fita ya sameni a masallaci da wani babban zancen daya sami yarsa,
Magana yakeyi akan 'yarsa ta hadu da tsautsayin qaruwa ta juna biyu Kuma Wanda yakeda alhakin hakan sunansa Bilal.,
Yazo ne Nan akan Kai Bilal din yake zargi da hakan kokuma Nace yazo ne kan 'yar tasa ta basa tabbacin ka Bilal kaante din ne yayi mata wannan cin mutuncin.
Tinda Dd yafara maganar maqoshin Ababa ke motsi kaman ya karbi zancen ya qarasa sbd ganin Dd babban yakasa fitowa ka tsaye yai maganar data Tara su din sai alokacin da yakai qarshen maganar Ababan ya saki ajiyar zuciya a boye Yana zubawa Bilal idanuwansa kirjinsa na harbawa da jiran amsar dazai Bada.
Sunkuyar da Kai Bilal yayi ahankali a karo na farko dayaji kunyar Kansa data Dd babba Harma data iyayensa da basa gurin,
idan har wannan shine Ababa mahaifin sumayyah to tabbas komai ya Riga ya bayyana gaban Dd Babu sauran tsimi Babu dabara.
"Sumayyah sunanta,nine Ababa mahaifinta"...suka Ji muryar Ababan Yana fada Shima muryasa na rawa sbd matsiwa da fargaba.
Wata sabuwar kunya da damuwa Mai qarfin gaske Ce ta lullube Bilal a gurin Dan kuwa ya tabbata dai Ababan ne yazo gurin Dd babba da zancen.
"Innalillahi wainna ilayhi rajiun"
Wannan shine iya Kalmar da ya iya furtawa cikin zuciyarsa Dake harbawa da karfi.
Jin shirun Bilal da yanayinsa daya bayyanar da tsananin kunya,Dana sani da baqin ciki ya kasa dagowa ya kallesa yasa Dd babba tsayar da kallan sa akansa Yana jiran amsarsa.
Cikin kame murya fiyeda farko wannan Karan dan sirkin zafi kadan a sautin Yace
"Kayi magana a sallamesa ba zancen batawa Kai lokaci tinani bane,
Idan baka sansuba ba buqatan tsayawa nazari ko wani tinanin
ka fada Kai tsaye a sallamesa."
A karo na biyu ya sake Jin hawaye game da kaddara sun ciko idanuwansa duk da kasancewarsa babba bame qananun shekaru ba Amma Kuma tinda komai ya zo a qaddarawan ubangiji baida kaucewa bayan fadan gaskiar.
Ba iya dago Kansa ba yakalli Dd babba ya Bude bakinsa cikin Rauni Yace
"Na Santa,Kuma qaddara Ce ta gifta Banda niyar cutatarwa ko keta mutuncinta,
Da niyar zan aureta na bibiyeta tin farko,Ina matiqar Dana sani da Bada hakuri ga wannan qaddarar data shigo.
A jejjere Ababa ya ringa jero ajiyar zuciya a boye Yana hamdala kala kala ga ubangiji Yana Jin wani farin ciki da sanyi na mamaye ransa.
Bai taba sakawa sumayyahn albarka ba sai yau din yaji zuciyarsa na Saka mata albarka da Bata fada masa karya ba,
Tinda dai Bilal ya tabbatarda ciki nasa ne ai komai ba zai zo da sauki.
Dd babba kuwa shiru yai Bai iya cewa komaiba
Suma duk sukai tsit gurin ya dauke sauti ko motsi Babu.
Minti kusan hudu a hakan kafin Dd ya motsa ahankali ya dauki wayarsa ya Saka kiran Abbakar yaransa tin na shekaru har yanzu.
Abbakar din na dagawa Dd Yace yazo yanzun nan.
Ajiye wayar yai Yana kokarin Hana Kansa bayyanarda attack din daya riskesa take a gurin Saidai daga muryarsa Bilal yagane ya samu attack take ya miqe da sauri yai Kansa Yana Kiran sunansa cikin kulawa
kafin wani yunqurin tini numfashin Dd din ya fara kokarin daukewa saiga Abbakar Yana ganin hakan hankali tashe yayo Kansa Shima.
Ababa ma hankalinsa tashi yayi ya miqe tsaye Yana fatan kada komai ya samu Dd babban a samu matsala Dan haka dashi aka hau yi masa firfita Bilal kuwa likita ya fara kokarin Kira hankalinsa a matiqar tashe.
Cikin mitinan da Basu wuce qalilan ba tsohon yake Neman rasa ransa Dan haka kasa jira sukai take Akai kaante specialist dashi.
Ababa kuwa silalewa yayi dole ya tafi gida bayan an dakatar da kowa shiga Inda Dd babban yake.
Kai tsaye gida ya wuce Baima samu biyawa asibitin ba Dan jikinsa koina ciwo yake Shima yau din yaci wuya Amma tinda dai buqata kusan ta samu shiga komai yazo da sauki.
Anne data kusan haukacewa a kwana daya da wuni biyu sbd rashin ganinsu benazir da rashin sanin wane Hali sike ciki yasa gabaki daya Bata hayyacinta gashi Ababan yaqi fada mata komai bare taji dan sanyi aranta.
Dan haka ma da Daren yana shigowa ya shigewarsa ko abinci Bai samu damar ci ba ya kwanta sbd gobe sammako zaiyi zuwa asibiti da Kansa zaiyi jinyar sumayyahn shi da Benazir.
******A asibiti kuwa sumayyah da Benazir sun Dan samu sassaucin zuciya Dana jiki tinda basa aikin komai sai zama da bacci,
Tinanin Anne ne kawai yake tsananin damun benazir ita datasan halin data barota
Amma koma yayane tinda bataji Ababa Yace ta mutu ba to tasan tasamu tsira kenan.
Sunyi ta zuba idon dawowan Ababa Basu gansa ba har suka kwanta dan haka suka fara addua da fatan Allah yasa lfy ba wata masifar Ce acan gida annensu take Sha ba.
Jinin da aka Saka mata ishashe da magani masu kyau da lafiyayyan abinci wadatacce Harma da gurin kwanciyar me kyau yasa jikin sumayyah samun sauki Sosai tanata samun bacci.
Benazir kuwa ganin samun saukin sumayyah yasata Jin samun saukin zuciya itama dan haka suka dasa jiran tsammanin mekuma zai faru gaba.
Qarfe Tara na safe Ababa ya shigo dakin nasu da aka sauya musu wata nurse ta rakosa tana fada masa Wanda ya Saka a sauya musu dakin sbd Bai saniba shi bayanan.
Dakin yaqarewa kallo Yana mamaki da lissafin kudin da Bilal din ya kashe musu daga jiya zuwa yau din.
Baqin ciki da takaici ne yazo masa wuya ya tsaya wato dai ta tabbata yaran na sun jima suna cin arzikin Bilal baida labari.
Benazir data miqe daga zaunen datake ta gaishesa kanta qasa ya jefawa wani irin kallo zuciyarsa na tafasa ya jefeta da ledan ruwan tea da bread din daya siyo musu Dan karyawa.
Tanaji ruwan zafin ya Sauka qafarta Allah yasa ledan Bai fashe mata a kafa ba dan haka ta durkusa ta dauke ledan tana sunkuyar da Kai.
Sumayyah na ganin hakan ta rakube kan gadon tana jiran nata jifan,
Zaiyi magana aka bubbuga kofar dakin aka shigo.
Sulaiman ne tareda maaikancin babban hotel din kaante bangaren restaurant dauke suke da Manyan ledojin abinci Harma da cikin basket ankawo musu abinci masu Rai da lafiya tareda inganci.
Kallansu Ababa keyi suna ajiye kayan suna gaidasa kai tsaye Yace
"Daga Ina?"
Cikin girmamawa Mai tsanani duka su biyun suka Ce masa daga hotel din kaantes ne Sir Bilal yabada umarnin kawo abincin safe Rana yamma da dare kullum tin jiya.
Kallan kayan da aka jere din yai Yana Juya zancen cikin ransa kafin ya dawo da kallansa kansu sulaiman din ya Dan saki fuska Yace
"Auyo eh lallai hakane
An kyauta to ngd sosai".
Sallama sukai masa cikin girmamawa kaman shine Bilal din Wanda hakan yasa Ababa Jin Kansa na qara daukan zafi.
Suna ficewa ya zauna hankali kwance kan kujera yasa Benazir ta Bude kayan yaga abubuwan da suka ake tabbatar masa fa daga yanxu duniyarsa ta Riga ta sauya zuwa wani matsayin dan kuwa ta Bude sabon babin rayuwa cikin masu daloli irin wainda yake buri da muradi.
Daman Bai tsaya ya karyo ba Dan haka Kai tsaye yasa akai masa wani hadadden combination na abincin da aka kawo ya fara ci zuciyarsa fes hankalinsa na kwanciya.
Kuma Yana gamawa zai nufi asibiti duba Dd babba Dan karma ya manta da waye sila kokuma meye silansa kwanciya asibitin.
Saida yaci ya koshi da abinda bazai iya Saka kudinsa ya siya yaci ba Dan ganin kaman yayi Riya Amma daga yanxu yasan komai ya canja.
Sauran yabar musu ya miqe ya fice bayan ya tabbatarda koma baya damun sumayyahn yanzu Tinda ance ansaka mata jinin Bilal.
Yana fita benazir ta zubawa sumayyah abincin sukaci tare Suma suka bar sauran kafin ta tattara gurin Mai gyara dakin ta sake shigowa a karo na biyu Dan gyarawa.
##MAMUH#
#HOTLOVE
#BENAZIR ABABA KAANTE
#DD KAANTE
#SUMAYYAH
#BILAL KAANTE
#AMNAH KAANTE
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
30
Ababa na fitowa daga Asibitin Kai tsaye Asibitin su alh Bilal din ya nufa Yana addua da fatan dd babba ya samu sauki ya Dan dawo Kansa.
Yanda ya dauka Asibitin ba Hakan ya sameta ba sbd tin a gate ake Hana shiga saika Fadi Abinda kazo Yi,
Idan Kai patient ne bangaren da zaa nuna Maka kabi daban,
Idan dubiya kazo Kuma in ba time na dubiyan bane baa barinka shiga sai time na dubiyan yayi.
Ma'aikatan Asibitin ne kawai ake budewa Kai tsaye su shige harma da barka da zuwa sbd Asibitin kusan duka manya da masu abin duniya ne sukeda files da kati a cikinta.
Dan haka tin a gate Bai samu shiga ba bare qarasawa gurin dubiyar dd babba.
Guri ya nema Yana kokarin zaunawa zaman Jira securities na Asibitin suka hanasa Dan haka baida zabi dole sai komawa gida yasha baccin Rana kafin da yamma ya sake shiryawa ya fito ya nufi Asibitin Dan yasan ankai abincin Rana daga hotel din kaantes shiyasa Bai tsaya yaci abincin gida ba ya fice.
Kaman yanda suka San halinsa da Abinda zai iya biyowa baya idan suka taba duk Abinda zaa kawo batareda izininsa ba tinda yanzu yasan komai yasa tinda aka kawo Basu taba ba Yana Nan aje sai Ababan yazo yabasu Wanda zasu ci.
Yana zuwa kuwa abincin yafara sakawa benazir ta zuba masa yaci ya koshi kafin ya bar musu sauran Suma suka ci anan yace su Basa numbern Alh Bilal ta waya tinda yasan bazasu riqeta Akai ba tinda sun Dade da zama tsofin munafukai akansa.
Shiru sukai suna shakkar fada masa Basu da ita,
Benazir data shirya daukan marinsa ta Bude baki ahankali tana Dan sauke Kai qasa tace
"Bamu San numbernsa ba,bamu taba karba ba."
Kaman yanda suka sani su dukan harbeta yayi da qafa Saida tayi baya Amma Bata Fadi ba
Cikin takaici yace
"Kwadayi kawai Kuka iya ya Baku kayan Dadi kuci ku shiga motarsa
Gashinan kun kwasa mana kayan wahala ko?"
Shiru sukai cikeda kunya da radadin kalmominsa babu Mai iya ko dagowa.
Yana cikin fadan aka buga dakin aka shigo ga mamakinsu su duka Alh Bilal dinne gabaki days sauya a cikin dare Daya damuwa Mai tsanani da rashin sanin mafita yasa idanuwansa har Wani zurfi sukai sbd kaman komai ya lalace masa ne.
Ababa na ganinsa ya miqe tsaye Yana masa barka da zuwa fuska a Dan sake kafin daga baya yakoma kalan jimami Yana tambayar ya jikin dd babba.
A hankali ya amsa masa tareda tambayan ya jikin sumayyah.
Kai tsaye Ababa ya amsa da tanajin sauki itama.
Sumayyahn Bilal ya kalla ta kasa dagowa ta kallesa daga ita har benazir sbd Ababa dake gurin.
Shi Kansa bazaiso su dago su kallesa ba a wannan yanayin Dayake ciki na rashin kwanciyar hankali ko Daya da tsananin damuwa.
Shiru dakin ya dauka har Ababa Mai son yin magana kasawa yayi yai shiru sbd sosai da gaske Bilal din yake cikin mawuyacin hali a bayyane.
Ajiyar zuciya Bilal ya sake bayan tsawon lokaci da shirun ya ratsa dakin zaiyi magana Ababa ya katsesa da kora benazir waje Shima ya fice Dan bawa Bilal din Daman magana da sumayyah
Suna ficewa sumayyah ta dago ahankali ta kallesa da idanuwanta dake cikowa da hawaye a duk lokacin da zata gansa sbd batasan meye matsayarta ba,
Ina rayuwar zata kaita da wannan cikin na jikinta,
Yaya alumma zasu karbeta da Abinda zata Haifa,
A wane matsayi Abinda zata Haifa yake da mahaifinsa.
Kallan datake masa idonta na cikowa da hawaye Shima shi yake mata idanuwansa na cikowa da hawaye sbd Wani radadi ne shi da Abinda zaa Haifa masa zasu kasance aciki Mai kaifi,
Dd babba bai taba karbansa kaman yanda ya karbi sauran jikokinsa,
Bai taba kaunarsa kaman yanda yake kaunar DD,
Baa taba basa matsayi da mahimmancin da aka bawa DD ba tin suna Yara har suka girma matsayin DD daban yake dashi,
Duk Wani aikin wahala da rashin Hutu shine ake damqawa ahakan baa taba nuna godia ko Yabawar da zata saka yajisa Dan asalin kaantes ne Shima,
Ya taso da girmamman tabon rashin soyayyar gaskia ta asalin Dan gadon iyayensa a cikin kaantes,
DD shine hasken idanuwan dd babba,
Shine abin alfaharinsa,
Shine Wanda dd babba kadai kejinsa cikin tsakiyar zuciyarsa fiyeda ma yayansa duk da kasancewarsa jika,
Tin suna qanana banbancin da ake nunawa tsakaninsa da DD a bayyane yake Wanda Hakan Bai taba damunsa ba sbd irin kaunar da DD ke masa tana rufe gurbin da ake bar masa a zuci na nuna masa shi din 'dan gaban fatiha ne bayan iyayensa nada tabbacin da aure suka haifesa.
A duniyarsa kaf tin tasowarsa mahaifiyarsa ce kawai sai DD suke masa Wani irin son Dayake basa qwarin gwiwan ci gaba da rayuwar cikin jarumta da karfin halin da a bayyane kawai yake dashi Amma a zahirin zuciyarsa shi din me tsananin rauni ne Wanda yake saka sa Jin duniyar na isarsa lokuta da dama,
Tin Yana qaraminsa ya taso cikin mawuyacin halin samun tinanin daidai na yanayin da aka sakasa,
Har girmansa Yana cikin wannan yanayin shiyasa tin daga ranar Daya fara kaunar sumayyah ya fahimci kusan ciwo Daya ke damunsu,
Nata ya shiga kwakwalwanta sabanin nasa da Bai shiga ba Amma dai ya sakasa cikin rauni sosai na zuciya.
A yanzu da wannan abin ya faru yasani ya qarasa ficewa ne a ran dd babba hakama zai saka mahaifiyarsa damuwa da kunqi DD kuwa zaiyita samun sabanine da mahaifinsu harma da dd babba sbd bazai taba yarda a tozartasa ba ko kuntata masa akan Abinda yayi.
Gangarowan hawayensa kan kyakkawan fuskarsa yasa sumayyah Kai hannunta hawayen ya sauka hannunta tana Jin zuciyanta narkewa
Take nata hawayen suka gangaro ahankali itama batareda ta iya cewa komaiba sbd basai yayi magana ba daga ita har shi tasan kowa na cikin mawuyacin halin da basusan meye makomarsu da Abinda zasu haifan ba.
Hawayensa Daya kasa riqewa ne suka koma Kuka ahankali mara sauti sai dai radadin zuci da jikinsa Daya gama sanyi da mutuwa.
Itama kasa tiqe nata Kukan tayi ta sunkuyar da Kai tana tsiyayo hawaye masu zafi.
Ahakan suka share lokaci Mai Dan tsayi babu Mai magana sai Kukan dasuka sha kafin ya Ciro handkerchief ya share hawayensa ya goge fuskarsa ya Ciro glass dinsa ya saka kafin ya share mata nata hawayen ya Kalli cikin idanuwanta ya Bata tabbacin inshallah komai zai tafi daidai,
Duk tsanani bazai taba rabuwa da itaba zai Samar musu rayuwar kwanciyar hankali Koda babu kowa acikinta.
Tambayanta yayi babu matsalan Dayake damunta ko babyn
Ta gyada masa Kai tana kallansa kaman Wainda ke bankwana sbd kukansa ba qaramin Bata tabbacin suna cikin tsaka Mai wuya yayiba.
Juyawa yayi ya fice a dakin bayan ya ajiye mata wayarsa Daya da layinsa da komai aciki.
Yana fitowa Ababa dake tareda benazir a zaune miqewa sukai tare tsaye Yana cewa harya fito.
Kasa kallon Ababan yayi sai kawai yace benazir tazo suje yabada Sako Koda zaa nemi Wani abin baya kusa.
Kasa motsawa tayi sbd Bata ma fahimci me yake nufi ba dan haka Ababa ya kalleta yace
"Kije ki karbo Sako akace".
Bayan Bilal din tabi babu Mai magana a cikin su
Suna Isa ya Bude motar ya shiga ya Ciro rafar 1k guda biyu ya miqa mata yace yabar waya a hannun sumayyah duk Abinda ake buqata benazir din ta kirasa.
Yana barin Asibitin ta juyo ta dawo ciki,
Tana shigowa dakin a tsaye ta tadda Ababa Yana jiranta.
Kudin ta Ciro Kai tsaye daga cikin hijabinta ta miqa masa.
Karba yayi yana sakawa aljihu sbd yasani Kai tsaye dubi Dari biyu ne.
Wayar da Bilal din ya bari ya kalla yana kokarin Hana zuciyarsa fasa wayar sbd shi Sam bazai dauki wannan wayar dayakeson su rinqa Yi ba Amma zai Basu kwana biyu daga Nan zai dakatar sai yasan matsayarsa da cikin jikin 'yarsa tukuna Dan shi a mutu a dawo so yake tabbas tinda Akai mata cikin sai sun aureta,
Sai sun shiga cikin ahalin kaantes Suma da yardar Allah.
Barin Asibitin yayi Bai sake dawowa sai dare ya sanmusu abincin Daren da aka kawo sauran yayi gida dashi acan yaci ya koshi har hande ta samu taci ciki itama Anne Kam saidai ta wanke kayan da akaci abincin dashi.
Washe gari Koda Ababa ya iso Asibitin an sallamesu Dan haka Yana zuwa kwasowa sukai suka dawo gida.
Anne gurin rawar jikin farin jikin ganin 'yayanta har faduwa tayi taji ciwo a Dan yatsar qafa Amma Bata damuba,
A rayuwarta Bata taba farin cikin ranar ba sbd sai yanzu ne ta sake tabbatarda bazata iya rayuwar babu su ba Dan haka suna shiga dakinsu ta fasa Kuka ahankali da batasan ko na menene ba Amma dai tasan ganinsu ya dawo mata da rayuwarta ne.
Su kansu jikinsu mutuwa yayi ganin yanda tayi wata mummunan rama kaman wadda ko ruwa Bata taba sha ba tinda suka tafi.
Rungumeta benazir tayi tana sauke numfashi ahankali sbd ita yanzu haka kawai taji batajin Dadin komai,
Yanda zasu Rena babyn kawai take tinani
Idan Kuma su Bilal suka karbe babynsu Yaya sumayyah zata rayuwar batareda ciwonta ya dawo ba,
Nakudar haihuwar kawai tayar mata da hankali takeyi sbd radadin ciwon kawai zai tayar da ciwon sumayyahn.
Dan haka benazir ta shiga Wani tinani daya sanyaya jikinta tinda ta lura Ababa yanzu akan cikin babu Abinda bazai iyaba tasan sumayyah data Rai ko lafiya baida baqin cikin ko Daya.
*******Ahalin kaantes gabaki Daya hankalinsu ya tashi da Jin ciwon dd babba katsam Kuma wai attack ya samu,
Take duk na kusa Dana nesa suka hallaro a cikin kwana biyu Kuma har lokacin Yana Jin jiki sosai gashi an rasa meya samesa sbd Bilal ya kasa fada Dan haka yafi kowa shiga damuwa Daya San shine sanadin
Fatansa dai kada Wani mummunan abin ya faru ya zama Sila.
Lokacin da labari ya Isa ga DD kaante Kai tsaye yasan ba qaramin abu bane ya bawa dd babba attack sbd jajirtaccen tsoho ne Mai tsananin karfin zuciyar Dan haka koma menene yasan babba ne.
Take ya saka su ummensa fara Shirin tafiya zasu taho a cikin satin Suma sbd zuwansa kawai zaisa dd babban Jin sanyi ya sani Shima.
#MAMUH#
#DD KAANTE
#BENA ABABA
#SAFNAH ABABA
#CRAZY IN LOVE
#MARRIAGE
#AMNAH KAANTE
#ZAFIN KAI
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
31
Dd babba tinda ya dawo hayyacinsa numfashinsa da bugun zuciyarsa Daya dawo daidai ya farka Bai ko Kalli gefen da Bilal yake ba sbd Sam ko ganinsa baya son Yi Dan ciwonsa zai iya dawowa harma fiyeda na farkon,
Duka yayansa da daidaikun jikokinsa da suka samu zuwa babu Wanda baiyi kokarin son sanin meya kawowa dd din samun attack a take bayan kowa yasan lafiya yake,
Hakama dad kaante da ko a yammacin ranar sunyi waya lafiya kalau baisani ba Kuma baiji alamar damuwa ko Wani ciwon a yanayin dd babban a lokacin ba.
Dan haka suketa shiga damuwa da mamakin Abinda ya samesa Amma Sam yamaqi yarda ya bayyanarda ko kafa Daya dazata bayyanarda akwai Wani abin ya sanar dasu zuwan kaddara ne kawai Allah ya Aiko masa da attack din.
Dole kowa ya bar zancen aka Maida hankali gurin kulawa dashi sosai.
Bilal Daya fahimci ko kallansa dd bayayi sai jikinsa ya sake mutuwa yayi sanyi ya sake shiga damuwa da mutuwar jikin yanda zancen zai bayyana ga sauran familyn.
Kwana biyi dd yayi a Asibitin ya sa aka sallamosa suka dawo gida a qarasa jinyar a can duk da zuciyarsa ba saukin zata samu sbd shi kadaine yasan tsananin zafi,bacin Rai,baqin ciki da damuwan Dayake ciki akan babu Wanda yasani daga shi sai Bilal sai Allahn su.
Bayan dawowa da jinyar dd babban gida sosai kaantes ke karban baquncin manyan mutane masu riqe da qasar dake zuwa duba dd daban daban,
Dan haka har lokacin dd Baiyi lokacin Bilal ba.
Babu Wanda ya fahimci Wani Abu ko rashin kulawan da dd babba kewa Bilal sbd anriga an Saba da sanin babu wata shaquwa Mai zurfi Ra girma tsakaninsu Dan haka babu Wanda ya ankara da rashin kulasan da dd babba kewa Bilal din.
Damuwa tasako Bilal din gaba sbd babu inda a yanzu yakejin saukin rayuwar,
Komai ya lalace masa ya tsaya masa cak,
Mahaifiyarsa da DD ne farin ciki da sanyin idanuwansa sai 'yar qanwarsu
Gashi duk Basa tare dashi.
Sumayyah Kuma Ababa ya hanasa zuwa ganinta yace sai dd babba yaji sauki asan matsayar magana.
Ababa ya Hana Bilal din zuwa ne sbd rashin zuwansa yasa yake aikowa Ababan kudi kaman Bai San zafinsu ba Dan kada sumayyah dasu benazir su nema komai su rasa na kulawa da baby da lafiyan sumayyahn.
A bangarensu benazir kuwa a yanzu da babu zabin Daya wuce musu karban ciki su hau renansa su Haifa komai menene yazo duniyar yasa suka Maida hankali gurin kulawa da sumayyah sosai.
A dayan bangaren Kuma a rayuwar da suka Saba suka taso cikinta babu Abinda ya sauya musu.
Wahalarsu,bautarsu,qunci da damuwansu babu Abinda ya ragu ko aka dauke musu.
Aikin a yanzu ma yafi na ko yaushe ga benazir sbd wankin shagunansa duka itace take yi hakama ayyukan gida da kulawa da dabbobi
Ga karatinta Dayake baya sbd rashin lokaci da wahalarta data qaru Dan haka duk ta forgice tafara ficewa hayyacinta itama ta rame Takoma kaman itace me cikin.
Anne ma ciwon tsufa ne yake Neman kamata ya rufeta sbd ayyukan sun mata yawa da nauyi itama Dana haka daga ita har benazir babu Mai hutun zuciya dana gangar jiki.
Sumayyah data ga wahala na Neman illatasu qarfinsu ya fara gazawa dole itama ta sakawa kanta qarfi da jarumta ta koma kan aikin itama kaman yanda suka Saba a baya.
******Dd babba tini ya warke ya sake saidai ciwon dake cin zuciyarsa Bai warke ba ko kadan
Tin ranar da abin yafaru baya iya bacci kowane dare tinanin yanda zai kashe zancen yayi Rami ya birne ya rufe yake,
Fushinsa da Bilal Yana qaruwa ne a duk lokacinda ya Tina cikin Yana girma ne yana sake kusantar lokacin haihuwa.
Danne zuciyarsa dd babba yayi ya sake Neman Ababa wannan Karan da Kansa ya gayyatosa Dan suyi magana.
Da qarfe 7 na bayan magrib ya iso Dayake Abbakar ya San da izinin da dd babba ya bayar na ganin Ababa yasa yana babban gate din farkon har Ababa ya iso da Kansa yayi masa barka da zuwa yayi masa iso.
Wannan Karan ma Ababa gidan sake shiga ransa da qwaqwalwansa yake Amma Dayake yafara hangowa Kansa dahir na zamowa Shima Dan haka ya Maida hankali kan dd babba da zai Gani.
Har cikin palon baqin dd babba Abbakar ya rako Ababa ya nuna masa gurin zama ya juya ya fice Dan tsare kofa sbd duk tsananin babu Wanda zaiji me dd babba zai tattauna da Ababan ko ganinsa dd babba yace kada ko Daya a ahalin suyi,
Magana ce zaiyi dashi sukai karshe a rufeta batareda kowa yaji ko yasan komaiba Koda tsautsayi.
Numfashi Mai sanyi da nutsuwa dd babba yayi kafin ya amsa gaisuwar da Ababan ke masa tareda ya karfin jiki.
Bayan ya amsa dagowa yayi ya Kalli Ababa da nutsuwa tareda son nufar maganarsa Kai tsaye,
A natse yafara da cewa
"Malam Ababa daga Kai har mu bama buqatan maimaita zancen baya mara Dadi da bacin zuciya Dan haka Ina Mai baka hakuri da Abinda ya samu yarka,
Allah ya tsare gaba ya yafe musu damu gabaki Daya,
Maganar ciki Dayake jikinta Kuma aikin kaddara ne data Riga fata Dan haka dai Ina sake baka hakuri.
Shigowar Bilal ne Daya saka Abbakar kira masa yasan ya shi dagowa a Karan farko yayi masa Wani Kallo ya Basa izinin zaunawa Shima.
Cikin sanyi da girmamawa Bilal ya gaida Ababa da tini ya fara Jin Kansa Wani ya amsa cikin yar kamewa.
Kallansu su biyun dd babba yayi kafin ya sake Dan yin shiru zuciyarsa cikeda nazari da Abinda ya Yanke akan lamarin Dan haka ya kallesu Kai tsaye ya sake fara da tambayar watannin cikin zuciyarsa na daci.
Ababa ne ya amsa Shima Kai tsaye da fiddo takardar scanning din dake aljihunsa ta cikin ya miqawa dd babban.
Kallan takardar yayi batareda ya amsa ba mamakin Ababa na fara shiga ransa sbd zuwa yanzu babu Wani ciwo ko baqin cikin lamarin a tattare da uban da 'yarsa ke dauke da cikin da bana aure ba.
Bai karbi takardar ba ya buqaci sanin watannin cikin kawai.
Bilal ne ya amsa masa Kai tsaye cikin sanyin jiki sbd sanin dd din baya son tambayar da yayi Maka dabam amsar da zaka Basa daban.
"Wata shida cikin yanzu Inshallah"
Shiru palon ya sake dauka Dan kuwa dai ta tabbata cikin haihuwarsa zaayi.
Ababa dd ya kalla yace
"A yanzu tinda qaddara ce ta shigo babu Abinda zamu iya Yi face zamu Bada muhalli,kudi da rayuwa me kyau da uwar da Abinda zata haifa inshallah bazamu gasa ba har lokacin da uwar zata samu miji tayi aurenta Amma bazamu karbi Abinda zaa haifa ba,
Komai ake buqata har Wanda baa buqatan ma zaa Baku.
Maganar dangantakar ciki da kaantes kuwa Sam babu maganar,
Ba'a ma yita ba,Bata taba yinta ba zancen anrufesa anan karya taba fita har abada...
Daga Ababa har Bilal cikin rashin hankali da firgici suke kallan dd babban sbd babu Wanda ya taba tinanin zaice a rufe maganar 'dan mutum har abada kar a sake tayarwa hakama shi Bilal tayaya ake tinanin yayi rayuwa ya binne zancen har abada bayan Yana sane da Yana 'da ko 'ya?
Tayaya ma zai iya rayuwa ba sumayyahn da Abinda take dauke dashi nasa?
Ababa Wani zazzafan zufa ne ya yanko masa ya Bude baki cikin maqoqon baqin ciki zaiyi magana dd babba ya katsesa da cewa
"Miliyan nawa?"
"In nairas ko in dollars?
"Cash ko wiring?
Rikicewa Ababa yayi Wani zufan na keto masa Tako ina
Take bayanin yake Neman qwace masa Jin bayanin ddn.
Hankali tashe Bilal yake kallan Ababa Yana jiran bayanin amsar da Ababa zai Bada Dan kuwa idan har shi din Uba ne bazai zabi kudin banza akan farin ciki da kare martabar yarsa ba harma da rayuwarta ta gaba sbd Yana karban kudin ya yarda da har abada bazai alaqanta cikin ko babyn da sunan kaantes ba.
Nazari Ababa ya shiga zuciyarsa na tsalle tana rikicewa,
Saidai Kuma duk son kudinsa a lissafe yake Shima,
A yanda yasani Kuma a yanda Alh dd babba da Kansa ya Basa zabin nawa yakeso da Kansa ya tabbatarda ko miliyan nawa ya fada Basa zaayi,
To Amma idan ya karbi miliyoyan kudin qarewa zasuyi komai daran dadewa sabanin idan ya tsaya tsayin Dakan da 'yarsa da jininsu ta shiga ahalin to famfon arzikin samun kudinsa bamai yankewa bane har sai inda arzkin kaantes ya tsaya.
Dan haka take ya fizgo hankalinsa ya dawo hayyacinsa daidai ya Hana Kansa zaban kudin dayasan ko agurin Bilal zai ringa yagarsu gwara dai ya shiga kaantes tsundum ayi dashi Shima.
Dagowa yayi ya Kalli dd babba dake kallansa tini Yana sake nazartarsa take ya gano akwai kwadayin arziki a tattare da Ababan Amma bari ya tabbatarda halinsa ta hanyar zabinsa tukuna.
Zufa Ababa ya share da handkerchief dinsa sbd a rayuwa bai taba shiga tsaka me wuyar zabi ba irin wannan ranar,
Dollars fa akace zaa sallamesa dasu
Amma Kuma akace idan zaka Sha giya ka Sha ta dubu,
Gwara ya shigo daga ciki saiyafi samun manyan dololin akan wainda zaa qirga yanzu a Basa.
Numfashi ya sake ya Kalli dd babba yace
"Ranka ya Dade kudi bazasu Hana bayyabar zancan Nan ba har abada sbd mutum zaa haifa Kuma dole wataran sai Anso sani kokuma sanin ma waye asalin Ubansa duk da kasancewarsa Dan kaddara".
Me zai Hana idan adalci zaa mun Nima Amin yadda akaiwa iyayen mahaifiyar shi Alh Bilal din...........
Cikin Wani mummunan tashin hankali da bugawar zuciya Bilal da dd Daya kasa gasgata Abinda kunnuwansa suka ji masa suke kallansa cikeda mamakin Da hankalinsu duka ya kasa dauka.
Ababa kuwa ganin ya buga daidai kan ga'ba yasa ya sake Jin karfin zuciya dana hali Dan kuwa gwara suyi su gama a rufe babin su fada babin gaba.
Ganin duk sun dauke wuta yasashi sake Dan gyara zama yaci gaba da cewa
"Ayi hakuri ranka ya Dade Nima a bani adalcin daya kamaci 'yata da ni Nima,wlh Banda inda zan saka kaina idan aka barmu da wannan Abinda zaa haifa din.
Ni kaina bazanzo a sani ko aji haihuwar kaddarar da zaayi a cikin gidana ba Amma idan aka haihun babu Wani lullubi da zaayiwa zancen dazai hanasa fita har abada,
Kaddara ce hakuri zamuyi mu dauka a rufawa juna asiri kaman yanda babu Wanda yasan waye Alh Bilal haka Nima idan aka rufa aka karba 'yata har abada wlh nayi alqawarin babu Mai ji.
Yana Kaiwa karshen zancen ya sauke nannauyan boyayyan numfashin karfin zuciyar Daya maqalawa Kansa ya iya furta kalaman a gaban dd babba sbd yasan ba qaramin ganganci Mai hade da ban mamaki yayi ba saidai wannan sarar kawai zai aikawa dd babba a karbi yarsa ba wahala.
#MAMUH#
#KAANTES
#ABABAS
#FAMILIES
#MARRIAGE
#CONTRACT
#CRAZY IN LOVE
#LTRIANGLE
#ZAFIN KAI
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
32
Tsit palon ya dauka kusan kowanne tsakanin dd babba da Bilal sun dauke wuta da mamaki tareda firgicin zancen da Ababan ya zaro,
Bilal Kansa ya sauke cikin baqin ciki da damuwa Mai tsananin gaske tareda sanyin jiki sbd tin zuwansa duniya ko dd babba Bai taba fitowa Kai tsaye ya tinatar dashi ko shi din wayeba,
Iyayensa da suka haifesa dinma daga ranar da aka daura musu aure ko a tsakaninsu Basu sake tayar da zancen ba sbd umarni da qaqqafar rantsuwar da dd babba yayi Akai Amma ayau Rana tsaka Kai tsaye a gaban idon dd babban ga Wani Yana fadan maganar Kai tsaye batareda mutunta shi Bilal din ba.
Dd babba kuwa shiru yayi batareda iya cewa komaiba tsawon mintina kafin ya dago ya sakewa Ababa kallan tsaf na mintina,
Ayau Rana ta farko da Wani yake zaune gabansa ya fada maganar da zata iya sakawa yasa a batar dashi da labarinsa,
Ko a cikin familyn kaantes ba kowa ne ba yasan asalin Tayaya aka haifi Bilal din ba bayan shi da Kansa sai Mahaifin Bilal da mahaifiyarsa sai Dawood da Kuma kanin dadynsu Bilal din da matarsa.,
Bayan wainnan babu Wanda ya sani a familyn sai dangin mahaifiyar Bilal Suma kawunta da matarsa ne kawai suka sani Kuma kawun ya rasu matarsa da yayanta Kuma sun koma asalin garinsu sunbar Nan din gabaki Daya Wanda dd babba da Kansa ya Bata Abinda zatayi nesa dasu kada ta dawo har abada saidai Fatima takai musu ziyara sbd kawai kada ma zancen ya iya fita wataran ta hanyar matar kawun.
Tabbas Ababa yazo da zance Mai girma,
Idan ya fahimci zancensa da yanayin yanda ya isar da zancen cikeda sakon nufin
"Ko a karba yarsa da cikin itama ko ya fallasa zancen cikinta Dana uban cikinta."
Kan Bilal ya Maida kallansa sbd a yanzu kam ya sake tabbatarda illar zamtowar Bilal cikin ahalin kaantes.
Basai dd ya fada ba Bilal da Kansa yasan wannan tinanin ne acikin zuciyar dd babba yanzu akansa Daman Kuma tin ba yanzu ba yasan da Hakan.
A Karo na farko bayan zancen dd babba ya Bude baki yacewa Ababa
"Yama kace sunanka na gaskia malam Ababa?
"Abubakar nake" Ababa ya fada Kai tsaye.
"Malam abubakar a ringa kulawa sosai da aibin harshe,
Maganar 'yar ka Kuma kaje kawai zan sake nemanka.
Magana Ababa zaiyi ddn ya kira Abbakar Sam ko kalma Daya baa bari ya furta ba aka fice da dashi Yana waiwaye sbd Bai fahimci me Hakan ke nufi ba.
Ana fitowa dashi Abbakar ya sallamesa har gate din waje ya koma.
Gida ya nufa Yana shiga nazari saidai Kuma bazaiyi qasa a gwiwa ba zai tsaya tsayin Daka a maganarsa kokuma a mutu har liman.
Bilal kaante ranar yau na cikin ranakun dasuka wuce masa a baya na radadin zuciya sbd maganar Ababa ta sosa masa tabon Daya jima cikin rayuwarsa Yana dannewa,
Bayan tafiyar Ababa shi Kansa ya sosa masa maganar data sakasa rufe Kansa a part dinsa ya zubar da hawayen da suka dawo masa da ciwo da radadin zuciyar Daya jima da dannewa.
Haka damuwarsa tin ta yarinta Mikn ya dawo masa sabo fil baida Mai zaunawa kusa dashi ya sanyaya masa kaman baya da mahaifiyarsa da DD ke zaunawa gefensa su rungumesa.
Kaf ahalin gidan babu Wanda ya asan meyake faruwa sbd gargadin dd babba na kada ya sake kowa yasan da zancen.
Dad dinsa baisan Abinda yake faruwaba tsakanin dd babban da Bilal sbd ko a fuska baka Isa ka Gane akwai Wani abin ba a qasa.
A tinani da hukuncin dd babba so yke ya dakile zancen ya rufe batareda kowa ma ya san da wannan qaddarar ba Amma Kuma da alama Ababa bazai lanqwasu da sauki ba.
Ta bangare Daya Abbakar ya saka yayi masa bincike Mai zurfi akan Ababan da duka huldodinsa.
Karan farko ana gama sanar dashi waye Ababan ya fahimci Yana Hana Ababan Abinda yakeso zai Bata musu sunan Daya debo shekaru masu tsayin gaske Yana ginawa.
Yanada plans me kyau akan rayuwar jikokinsa Dan haka bayajin zai iya hada iri ko zuria da Ababa sbd a halayensa babu na gari to Amma idan har karban yarsa shine maslahar Hana fidda sirrin A kaantes suna yayan gaban fatiha zai sake dubawa ya Gani.
Sake kiran Ababa yayi wannan Karan dukiyar da yayi masa alqawarin Basa harta fita lissafi Amma Sam Ababan ya tsaya akan sai Bilal ya auri yarsa tinda idan an barsu da 'yar baisan yanda zaiyi da ita ba.
Wannan Karan ran dd babban ya tsananta Baci Dan haka ya sauke fushinsa a sirrance kan Bilal ya dakatar dashi daga wasu hildodin ya hanasa ko fita daga kaantes din sbd lura da Bilal din zai iya sallamawa ya zabi yarinyar da ake maganar Wanda Hakan zai iya kawo tonan asirin maganar ga family dama duniya gabaki Daya.
Iyakance Bilal daga komai yasa Ababa qara kafewa sbd da alama dai waton ko Bilal din ya zabi sumayyah ba wasu dalolin arzkin zai samu daga gunsa ba tinda zaa iya dakatar dashi daga komai na dukiyar kaantes Dan haka ya sake tsayuwa akan raayin sai Bilal ya auri 'yarsa kokuma yayi qara.
Akwai matakai da hanyoyin daukan mataki me kyau da sabaninsa da suke dashi akan irinsu Ababa Amma a zuciya da halin dd babban Yana dakatarwa ne sbd duba da yarinyar dake dauke da juna Biyun Wanda rayuwarta tabbas an Riga an lalata mata,
Sunada 'yaya mata da jikoki Wanda ya tabbatarda idan aka cutatar da wannan yarinyar Allah zai iya jarabtarsu tinda ba kudi ko dubarar bace zasu tsare Maka yayanka daga Hakan,
Shi kuwa a duniyarsa da irin qaddarar Hakan ta samu 'yayansa ko jikokinsa koma ahalinsa gaba Daya mata gwara Allah ya dauki ransa ya bar duniyar.
Ta bangare Daya Bilal ya qasqantar da Kansa a gaban dd babba ya rokesa akan yabarsa ya auri sumayyahn sbd Yana kaunarta har lokacin harma da duk Abinda zata haifa,
Yayi alqawarin zaiyi nesa da ita inda zasu Rena Abinda zata haifa batareda kowa yasan Tayaya suka haifesa ba,
Bazai taba barin sunan zuriarsa ta lalace ba sbd shi.
Da fari dd babba kasa karban wannan rokon yayi Amma ganin yanda Bilal yake qasqantar da Kai akan Hakan dakuma zaunawa da yayi ya duba tafiyar Bilal din zata ankarar da mutane a iya sani hakama Ababan Nan ba abin yarda bane matiqar suka barsa a Raye to zaa iya sanin gaskia Dan haka zai amince da auran yarinyar ta yanda zasu batar da zancen su Hana a fahimci ansamu wata qaruwar Bata hanyar aure ba daga baya zaisan yanda zaiyi da Ababa.
Saidai ya gindaya manyan sharuddan da daga Ababa har Bilal jiki na rawa suka amince aka bar maganar a rufe akan ana haihuwa zaa daura musu aure a rufe maganar haihuwar ta dawo kaantes.
******Amincewar dd babba yasa Ababa Jin duniyarsa gabaki Daya ta dawo sabuwa sbd farin ciki da samun biyan buqata cikin sauki,
Bilal ma samun Kansa yayi cikin samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya duk da Sam dd babba ya hanasa zuwa ganinta sbd kada aga Yana zuwa gidan Amma suna magana a waya duk bayan kwana biyu Shima da wayar Ababa sbd Ababan ya mayar masa da tasa wayar Daya bata.
Ta bangare Daya Kuma bakin aljihun kaantes aka budewa Ababan na kulawa da sumayyah wadda basusan meyake faruwa ba Dan kuwa wahalarsu sai Abinda ya qaru ba sauki.
*****Zuwa yanzu rayuwa ta sake yiwa su benazir wahala sbd rashin isashen hutu da yunwa harma da karatun benazir din Dan ita sumayyah tini aka watsar da nata karatun.
Gabaki dayansu sun bushe sun koma kaman wainda ke rayuwa a cikin Sahara sbd daidaicewar yunwa da wahala,
Sumayyah kuwa a yanzu cikinta ne kawai mai tsoka a jikinta,
Komai na masu ciki Tin daga cima har hutu da magani Bata taba samun ko Daya ba tinda ta baro asibiti.
Hande a yanzu tafi koyaushe tsangwamarsu sbd ita kam har lokacin tsanar cikin takeyi harma dasu gabaki Daya Dan ganin takeyi sun haukatar mata da Ababa sbd yanzu duk ya sauya babu Wanda yake Gane Kansa.
***A haka suka ringa gangarawa har cikin ya shiga wata Tara Wanda shigarsa ya saka rayuka da dama shiga tashin hankali da fargaba,
Ababa hankalinsa a yanzu data shiga wata Tara ya tashi cikin fargaban me zaa haifa hakama da fargaba Mai tsanani kan a haihu lafiya ba tareda matsalar komaiba Dan a yanzu haihuwar itace zata tabbatarda hayewarsa zuwa Ababansa ko faduwarsa zuwa Nobaba.
AFUWAN BA YAWA.
##MAMUH#
#AMNAH
#BENAZIR KAANTE
#DD KAANTE
#ABABA
#ZAFIN KAI
#MAMUHGEE
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
33
Acan bangaren Familyn kaantes tini Dd babba ya sanar da 'yayansa yayiwa Bilal matar aure Kuma ba lokaci zaa dauka ba zaa daura musu aure kawai ba buqatan wani biki ko wata bidiar kawai daurin auren alfarma zaa daura musu shikenan.
Da mamaki kowa yake son sani 'yar waye aka nemowa Bilal aurenta haka har cikin qanqanin lokaci zaa Ce zaa daura auren?
Dad Kaante yaso sanin 'yar gidan wace Amma Dd babba sam Yaqi barin tambayoyinsu da zancen ya zurfafa har su fahimci auren na manufa ne da akwai dalilin yinsa,
A yanda yakeso kada kowa ya fahimta ko yasani sai 'yar ta shigo hannunsu sai su taru su rufe zancen cikin gida bame sani sai an shakara da auren a bari duniya tasanta dacewa 'yarsu Bilal din Ce ta yanda ba kowane zai tsaya lissafin yaushe Akai auren yaushe aka haihuba.
Umminsa da zancen auren Bilal ya risketa kaman zata shide Dan farin ciki Mai tsananin gaske sbd matar aurensa Ce kawai zata iya Saka mata Bilal dinta cikin farin ciki su taru su goge masa tareda maye masa gurbin so da kaunar dayake rasawa a cikin familynsa.
Zancen auren Bilal Babu abinda ya qara mata sai tsanani na buqatan Shima Dawood yayi auren sbd tini Shima anan din tai masa matar datake tsananin so itama.
Qaninta 'dan kawunta daya jima da yin nasa arzikin Shima tin tsawon shekaru Ashirin har da yan kai daya Rabu da matarsa ta fari baya tayi barin ciki kafin rabuwarsu
yayi aure har so biyu Amma Bai taba samun haihuwa ba ko barin baa taba sake samu gidansa ba gashi Shima yafara manyanta Amma ba 'yaya ga tarin arziki ya Tara Babu magada.
Daga ita ummen har hajiya Mahaifiyarsu suna cikin damuwar hakan da tausaya masa shiyasa aketa sake auro masa wasu Matan ko Allah zai basa wata ran idan akwai Rabon samun.
A wannan yanayin ne suna cikin fata da adduoi koyaushe da sadaka da komai sai gashi Allah ya share musu kukansu ta hanyar dawowar tsohuwar matarsa da 'yar qaramar budurwar 'yar da Bata Gaza shekaru Sha uku zuwa Sha hudu ba Ashe cikin daya bare kafin rabuwarsu Yananan Bai qarasa zubewa ta haifi 'yar harta girma.
Duk da basa kaunar tsohuwar matar tasa daga ita har hajiya Mahaifiyarsu sbd son Rai da kwadayi tareda rashin girmamawa Harma da iya yin komai akan kudi da rashin godiyar Allah yasa suka rabun dakuma a lokacin Yana talakansa ne baida komai.
Amma dai tinda Allah yasa takawo musu Rabo na haihuwar da suke fata take suka manta komai suka hau tsananin farin ciki da nunawa 'yar so mai tsanani.
Da farko hajiya dashi Kansa hankalinsu bai wani kwanta ba Saida akayo DNA Wanda a asibitin qanin tsohuwar matar tasa Akai komai Kuma suka samu sakamako na tabbacin 'yarsa Ce jininsa Ce Dan haka tini suka hau farin ciki da murnar da bazasu iya kwatantawa ba.
Shi kansa Alh Basheer bulama a wannan lokacin tsananin so da kaunar 'yarsa ya shigesa fiyeda komai da kowa,
Kauna da soyayyar da ake nuna mata tareda halaye da tarbiyar da mahaifiyarta take Dora yarinyar yasa cikin qanqanin lokaci ta sauya daga wuya da talaucin dasuka fito da uwar na rayuwarsu duka ta baya su biyun suka fara kokarin shimfida rayuwar da sukeso ta yanda sukai raayi.
A lokacin matansa biyu ya Rabu da sauran Dan haka ba ja 'yarsa tasa ya sake daura aure da mommynta cikin shekarun da Basu Gaza biyar Ba da auren suka sauyawa Hajiyarsa da yan uwansa shi bayaji baya gani idan akan lamarin 'yarsa ita Kuma 'yar komai mommynta take sakawa Yana yiwa sbd ita Kuma mommyn da 'yar take amfani tana rayuwarta yanda takeso a cikin dukiyarsa.
Har wannan lokacin hajiya da ummin kaante kaman yanda take Kiran yayar mahaifin nata haj Fatima kaante suma basu taba Jin so da kaunar ta ya Sauka a ransu ba dan haka Tako Ina yarinyar ta samu gatan daya lalatata kusan gabaki daya dan kuwa tini ta rufe kowane Babi da ake cewa babin Tina baya.
Da karatun SS 1 ta fara bayan dawowansu hannun Daddynta tana gama secondary school ta fara karatun jamia a Lagos Amma shekara daya kawai tayi dad dinta ya cireta ya maidata Malaysia dayake Daman mummynta itama tai bokon Sosai tare suka koma can da zama itada mummyn dan bazata iya barin 'yar tata ita daya ba can tinda ita din Bata komai a Nigeria din Kuma 'yar tamkar mukullin juya rayuwar Alh basheer ce a hannunta shiyasa Bata wasa ko nesa da ita.
SBB shine sunan da ake kiranta tinda ta waye rayuwarta ta sauya gabaki daya,ita din 'yar gatace a yanzu gaba da baya, 'yar masu tarin arziki Ce,
Babu abinda take nema ta rasa Daddynta Bai mata shi ba,
ta gama karatunta ta sake fadawa wani Dan zurfafawa, tsawon shekarun da Sukai a qasar ta waje tini suka bar Malaysia Takoma Zurich mommynta kuwa Takoma Nigeria Amma kusan Akai Akai tana zuwa Dan akwai shaquwa da kauna Mai tsananin gaske tsakaninta da mummyn.
Wayewarta tayi yawan da yawanci acan gida Nigeria idan tazo sauran dangi na mata kallan mara tarbiya kokuma tashin turai da bayan rayuwarsu Bata iya rayuwar 'yayan Nan. Shekarunta a yanzu sun haura Ashirin da biyar zuwa da shida ko da bakwai ma Amma gata da rayuwar Datake yasa koyaushe a yarinya sharaf iyayenta ke kallanta.
Bata taba sanin DD kaante 'dan ummen kaante ba duk tsawon shekarun Saida ummen tazo qasar ranar data je gurinta a ranar idanuwanta da zuciyarta sukai kyakyawan Gamo dashi,
idan tace tafada soyayya to ta ragewa zancen karfin gaske Dan haka ba soyayya ta fada ba Kai tsaye ta kamu da mahaukaciyar soyayyar da zata iya yadda ta mutu ba aure matiqar ba Dawood Dayyab dauda kaante zata samu ba.
Bata kula kowane namiji a rayuwarta da sunan soyayya sbd Sam ita tama manta da ana tsayawa Ayi soyayya da aure gaba,
Tin a Malaysia datai wani saurayi Dan qasar yaso aurenta Amma yanaso su ringa qwanciya tare taqi sai hakan ya lalata soyayyar tasu duk da suna son juna Amma shi yafi buqatan ta dawo gidansa da zama.
Soyayyar DD kaante a rayuwarta tasan abu ne Mai wuya kafin ta samu Amma tinda umme na sonta kaman yanda take son Zeenah yasa Bata boye ba Dan batasan wata kunya ba a yanzu ta bayyanar da soyayyarta a Fili Kuma ta samu Goyan baya tareda bayyanarda farin ciki sosai da amincewa daga ummen.
Hakan yasaka kusan kullum tana gidan Akai Akai danma taso dawowa gidan gabaki daya Amma qa'idar DD ce bayason mutane a gidansa baya iya rayuwa da wasu a guri daya,su ummen ma Dan mahaifiyarsa Ce Bai hadata da kowa ba sai qanwarsa dayake jinta cikin tsakiyar ransa itama Bai hadata da komaiba dan haka su baida damuwan zamansu a gidansa duk da ummen tasan Dan Yana son su fiyeda komai ya barsu Amma ba wai dan Yana sakewa da hakan bane ta sani.
DD a rayuwarsa bayan baturiyar budurwarsa lizz Shima Bai taba soyayya da kowace mace ba sbd bama zai iya Tina wace macen bace yayiwa kallan tsaf da har zai iya soyayyar da ita
Zuwan ummensa Zurich ta rabasa da Lizz dan tsoran kada 'dan nata ya fada Zina sbd ganin yanda Lizz din ke maqale da hannunsa ko yaushe Idan tazo gidan batareda damuwa da ita uwarsa tana gidan ba.
Babban Saa da Daman da Sbb ta samu shine maganar ummensa kaman yankan wuqa ne Bai taba musawa ba Dan haka tana rabasa da Lizz ta fara Saka masa zancen yai aure tinda zaman a haka ya Isa. Bai taba tinanin aure a yanzu ba Amma sbd bayason ana maimaita magana a rayuwarsa yasa ya barwa ummen zabin komai Dan tasan kalar matar da bazata taba binsa tadamesa ba zata zabar masa.
Sbb na ganin zancenta da DD ya tabbata yasata Jin duniyarta ta sake sauyawa gabaki daya, ita 'yar millionaire zata auri 'dan billionaires Shima Kansa billionaire.
Daga lokacin tafara Jin kanta qarasa juyewa gabaki daya a sonsa Bata Ji Bata gani Bata ganewa duk zancen da babu sunan DD kaante dinta aciki.
Duk wannan bidirin Bai taba tsayawa ma yasan asalin kamannintaba bare tantance muryarta sbd Bai taba maganar data wuce ta minti daya zuwa biyu Ba da ita Amma a hakan taji tagani ta amince.
********
Zancen maganar auren Bilal ya sanya umme ta yiwa Dad kaante magana dan a hade auren Dana DD tinda tare zasu dawo,
Shima Dad kaanten yanason dawowar DD din da zamansa anan Dan haka wannan shawarar tai masa daidai dan haka da kansa ya samu Dd babba da maganar dayake Alh Basheer bulama nasu ne babban mutum ne sosai Shima gashi akwai sanayya Dan haka aka yanke shawarar Neman auren kawai a hade Dan kuwa Dd babban Yana buqatan dawowar DD a kusa dashi suna buqatansa.
Da wannan Shirin aka fara Shirin auren DD da Bilal lokaci Daya.
******Benazir zuwa yanzu rayuwar ta sake matse musu babu sauki sai a gurin ubangiji,
Sumayyah lafiya tafara qaranci sbd rashin Cima Mai lafiya isassa da yawa aikin wahala.
Anne ma depression ya fara tayar mata da ciwonta itama yau lafiya gobe sai ahankali Dan haka benazir ta 'daidaice Takoma abin tausayi,
Sumayyahn ma nata ciwon Yi yakeyi Yana kokarin tashi ga cikin jikinta yayi girma sosai kaman me cikin 'yan biyu.
Tashin hankalin benazir a yanzu shine yanda zata iya karban haihuwar sumayyahn sbd da alama Anne sai ahankali,
Hande Kuma ko sumayyahn zata yage gurin haihuwa bazata taimaka musu ba a yanda ta tsani cikin da su gabaki Daya akansa.
Ta bangare Daya ga karatunta suna kokarin fara exams a satin.
Abinci ta koshi ta manta rabonta da Hakan sbd kullum barwa sumayyahn dake dauke da juna Biyu sukeyi saita koshi suci sauran Wanda itama sumayyahn bawai cin takeyi ta koshi ba tana Dan ci zata ce ta koshi sbd tabar musu itama su samu suci.
Lokacinda benazir suka fara exam lokacin tini depression Mai tsanani yafara kokarin juyar mata da Kai itama sbd Anne da ciwonta ya tashi sai tayi fiyeda kwana nawa kafin ta dawo daidai
Hakama sumayyah sai ahankali itama Dan haka hankalinta ya rarrabe cikin damuwa da rashin sanin madafa,
Bata iya karatun Daya kamata,
Ga aikin gida ga wankin shagon Ababa Idan ankawo wuni takeyi ta raba dare tanayi harda guga,
Ga kula da Anne da sumayyahn wadda a yanzu cikin takejin kaman zai kasheta sbd numfashi ma gagararta Yi daidai yake sbd cikin.
0 comments:
Post a Comment