Tashi tayi ta fito daga daki jiki ba qwari ta nufi toilet tayo fitsari tayi alwala ta dawo dakin,
Sallah tafara Yi ta magrib kafin ta fito ta Dora ruwan zafi ta dawo daki ta hadawa baby Madara ta karbeta daga hannun Anne datayi shiru tana bin benazir din da Kallo duk inda ta motsa tinda tasan itama rabuwarsu tazo din.
Bude fuskan babyn benazir tayi ta zuba mata idanuwanta dake kumbure tana kallanta soyayyar uwar data tsuguna ta Haifa 'da na shigarta akan yarinyar,
Ko Ababa ya fada ko kada ya fada soyayyar datakewa babyn na irin Wanda tasan sumayyahn ma zatai mata ne.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda gyarata jikinta tafara Bata madaran ahankali tana Dan rufe Idanuwanta sbd kanta dake tsakanin ciwon da kaman zai sauka daga jikinta.
Shiru dakin ya sake dauka babu me magana har tagama bawa babyn ta koshi ta miqe ta bawa Anne ita ta tsaftace mata fidan da cup din data hada Madarar ta kaisu inda take adanawa ta ajiye.
Sauran ruwan ta debo ta shigo daki dasu a babban roba Anne ta kama mata tayi mata wanka suka sake shiryata tsaf tini Takoma bacci Dan haka Anne ta goyata ita Kuma benazir jiki ba qwari ta fito tattara gidan da kitchen kafin su shige.
Har ta gama komai ta shigo musu da abincinsu hande Bata fito ba hakama Ababa Bai dawo ba Dan haka Suka shigewarsu.
Da daddare bayan benazir ta kwanta duqunqune da babyn ciki abin rufa sbd sauro da sanyi tayi shiru tareda shiga tinani Mai zurfi jikinta na mutuwa daga kwancen datake.,
Anne data kasa bacci Jin shiru benazir tayi bacci
Ta tashi zaune ahankali zuciyarta na karyewa kukan Datake ta riqewa tin lokacin ya subuce mata Mai tsananin ciwo da quncin zuciya ahankali ta fasa shi cikin qanqanin sauti kada ta tada benazir wadda idonta biyu tana jin saukan sautin kukan Annen hawaye masu dumi suka gangaro gefen idonta batareda ta motsa ba sbd Daman ta sani qunce ne Mai tsanani a ran Annen ta danne Dan kawai tana son fiddata wannan gidan zuwa Wani gidan.
Anne da batasan benazir na jinta ba Kuka sosai Tasha Mai ban tausayi tsawon lokaci kafin ta rarrashi zuciyarta ta kwanta bayan benazir din hawayenta na cigaba da gangara gefen idanuwanta daga kwance,
Benazir dake tsiyayan hawaye daga kwancen itama rintse idanuwanta tayi tana fatan wannan ya zama shine alkhairi ga rayuwarsu su ukun ita da babynta da Annenta.
Washe gari daga Annen har benazir din kasa kallan juna sukai sbd kowannensu fuskarsa da idanuwansa a kumbure suke sbd kukan dasuka kwana Yi mara sauti.
Ta bangare Daya Kuma kowannensu ya dauki dangana da qarfin zuciya ya sake sakawa Kansa Dan haka ayyukan gabansu sukahau Yi Wanda kusan wannan Karan Anne ce tafi Benazir din Aiki sbd babyn da benazir keta dawainiya da ita gashi yau din tanata Kuka daqyar benazir ta samu tayi bacci ta Kwantar da ita taje tayo wanka tana dawowa ta shirya tana Shirin goyata Ababa yace Akai masa ita.
A dakinsa da komai na hutawa yake yasa aka Kwantar da ita kan gadonsa Takoma bacci abinta hankali kwance.
Aiki benazir tazo ta karbanwa Anne suka gama kan lokaci suna shiga daki Akai sallama gidan Wanda ya saka Anne fitowa tana amsa sallaman sbd hande na daki ba lallai ta fito ba.
Budurwar yarinya kyakyawa Anne tagani tsaye a tsakar gidan hannunta riqe da babbar qatuwar leda tana kallan Annen itama cikin muryar me nutsuwa tace
"Sannu Ina wuni."
Kallanta Anne takeyi kafin ta Dan sauke kallanta ta amsa a sanyaye ta Dora da cewa
"Bari a kira hande.
Juyawa tayi zata nufi dakin hande Zeenah ta katseta da cewa
"Nan ne gidan su benazir????
Dakatawa Anne tayi tareda juyowa tana kallan Zeenah din kafin tayi Wani motsin Ababa da hande suka fito lokaci Daya Jin ana tambayar benazir Dan kuwa yanzu bazaiyi wasa ko barin kowance kuskure ba Dan haka ya fito yaga waye ke nemanta Kuma lafiya.
Kallo Daya Ababa yayi mata yaga kammanin zuriar kaantes take zuciyarsa tayi Wani tsalle ta dawo kirjinsa ya Dan saki fuska Yana cewa
"Barka da zuwa,daga Ina?
Benazir kike nema?
Numfashi Zeenah ta sauke ahankali tareda kallan Ababan ta Dan gaidasa a jagarce kafin ya gaida hande itama tace
"Daga kaantes nake baby nazo Gani"
Wani farin ciki Mai girma ne ya rufe Ababa yace Mata ta qaraso ciki
"Bismillah Bismillah"
A palonsa aka sauketa ta zauna ahankali tareda ajiye ledarta hannunta tareda key din motanta da wayarya gefe tana Dan kallan yanayin palon.
Ababa da Kansa yaje ya kirawa benazir yace taje da kanta ta dauko babyn ta kawowa baquwar.
Jiki sanyaye benazir ta shigo palon da siririyan sallama ta qarasa Kai tsaye dakin Ababan dama suna shiga tinda sune masu gyarawa ta dauko babyn dake bacci hankali kwance ta fito da ita hannuwanta da zuciyarta na rawa sbd daga wannan lokacin dai ya tabbata itace tayi cikin Kuma ta haihu,tazama uwa ta zama mahaifiyar babynta har abada.
Rintse idanuwanta tayi ahankali tareda sauke numfashi da ajiyar zuciya Mai sanyi ta Bude idanuwanta daidai lokacin da ta iso gaban Zeenah wadda itama ta zubawa benazir din da babynta idanuwa tanajin hawaye na ciko idanuwanta da tsananin son babyn harma da benazir din da tausayinsu na rashin jigonsu Bilal.
Cikin nutsuwa benazir ta miqa mata babyn bayan sun gaisa kowannensu cikin sanyi.
Hannuwan Zeenah har rawa suke gurin karban Babyn tana amsarta ta rungumeta a hankali tsawon mintina biyu kafin ta Kwantar da ita cinyarta tana kallan fuskarta da babu Abinda ta baro na kamannin kaantes saima sake a girma zatafi yin kama dasu din.
Ahankali ta dago ta Kalli benazir da kanta ke qasa tana kasa kallan Zeenah sbd kunyar qaryat Datake dabaibaiye da ita.
Cikin kulawa Zeenah tace
"Yaya babyn lafiyanta kalau right?
Kema duk Kuna lafiya Amma ko??
Gyada Kai benazir din tayi tana cewa
"Eh alhmdllh"
Ababa na ganin Hakan ya fita yana cewa hande ya biyosa sbd Ababa Zeenah din Daman ganin babyn da kyau.
Suna ficewa Zeenah ta Kalli babyn hawaye na gangaro mata na rashin dadyn yarinyar
ahankali itama benazir nata hawayen suka gangaro na rashin tata yar uwar Amma ba Daman nuna ma tanada yar uwa sumayyah kaman yanda Ababa ya a fada har abada saidai tayi kukan kewanta cikin ranta badai a fili ba.
Ganin hawayen benazir yasa Zeenah kasa riqe kukanta cikin tausayin benazir datai rashin Bilal din itama sai ta ringa rarrashinta sbd kukan benazir da yayi karfi a hankali.
Sun jima a palon su kadai daga Kuka Zeenah ta gabatar mata da kanta tareda Bata tabbacin duka familynsu suna tsananin son babyn kaman yanda suke son Dan uwansu dasuka rasa Bilal.
Hotunan da zata Kaiwa Umme Zeenah ta dauki babyn kafin ta bawa benazir kayan data kawowa babyn kafin su karbeta ta dawo hannunsu.
Zeenah kaman kada ta tafi tabar babyn taji Amma haka ta daure ta tafi tana zuwa gida takaiwa ummensu hotunan wainda suka saka hankalin Umme sake tashi akan sai ankarba babyn Bilal din tadawo hannunsu kokuma kawai tabar kaantes din su koma gidan DD ta Reni jikarta acan.
Wannan Kalmar tata da tashin hankalin datai harma da hoton babyn yasaka dad kaante da ubangayya DD Jin buqatan dawowar 'yar hannunsu cikin gaggawa shi Kansa dd babban baisan Yana son 'yar ba Saida yaga hotonta abin tausayi kayan jikinta ma masu tsananin arha da rashin nauyi ne da zai saka sanyi shigarta ya illatata da wuri.
Washe gari Ababa Yanata Kai kawo tsakanin gida da waje Yana lissafin yaushe Kaantes zasu nemesa sai kwatsam ga Kiran Abbakar akan dd babba na nemansa.
Bai tsaya batawa Kansa lokaci ba ya nufi KAANTES din sbd zuwa lokacin ya matsu ayi me yiyiwa kafin DD kaante ya tattara ya koma inda ya fito lissafinsa ya Kuma watsewa a Karo na biyu.
Yana Isa kaantes Kai tsaye yanzu an tantancesa Yana zuwa ake barinsa shiga Dan haka shida Abbakar palon dd babba suka nufa Yana zaune Shima Yana jiransu.
Gaida dd babba yayi tareda dad kaante dake palon Shima kafin ya zauna a natse Dan Jin meye dalilin nemansa.
Numfashi dd babba ya sauke kafin ya dago ya Kalli Ababa cikin nuna manyanta yace
"Malam Ababa maganar jaririyar dake hannunku ce mun Yanke shawarar karbanta tin yanzu sbd a dauke muku nauyi dama duk Wani Barnar sunan da kuke gudu mu zamu ji da komai ba zaa San 'yarka ta taba haihuwa ba inshallah."
Numfashi Shima Ababa ya sauke Mai sauti kafin ya dago ya Kalli dd babba Bai tsaya kwana kwana ba Shima yace
"Ni yanzu na aminta na yarda sunan nawa Dana 'yata ya lalace kowa zai San ta haihu ba aure ya sani Amma bazan taba raba 'ya da uwa ba,
Yarinyar Nan tazo duniya a ranar da mahaifinta yabar duniya sannan Kuma a rabata da mahaifiyarta?
Harma da tinanin bazata San mahaifiyar tata har abada ba??
Daukan haqqin wannan marainiyar jaririyar 'yar zaiyi yawa,
Nayi alqawarin barinta tareda uwarta tinda ta rasa ubanta inshallah zuwa gaba uwarta zata samu mijin dazai aureta da 'yarta Dan Allah ya rufa musu asiri,
Maganar asan waye mahaifinta har sunanku ya Baci nayi muku alqawarin bama zamu taba bari tasan waye mahaifinta bare danginsa har sunanku ya Baci Dan haka daga yau na hakura zan dauki bacin sunan Amma abarni da jikata zata samu gurin agolanci Mai kyau inshallah.
Da gaskiyarsa yake maganar Yana bayyanarda qunci da damuwarsa akan zancen Dan haka take gabaki Daya palon ya dauki tsit.
Dd babba da dad kaante shiru sukai sbd har ga Allah zancensa da ya shigesu yayi magana Mai maanar da zaa duba idan har zaa yiwa marainiyar jinjirar adalci batareda sun duba sunansu sun cutatar da itaba.
DD kuwa daya shigo alokacin maganar agolancin da Ababa yafada tafi sokan zuciyarsa,
Idan har Yana Raye har abada 'yar Bilal bazata taba agolanci gidan kowa ba.
Ababa miqewa yayi Bai Jira Mai zasu fada ba yace
"Insha Allah gobe zamu bar garin gabaki Daya zamu koma asalin mu acan kauye zamu samun kwanciyar hankali da rufin asirin renanta ba maganganu Dan haka idan Kuna buqatan ganinta ko so Daya ne zaku iya zuwa kafin mu wuce nagode sosai Allah ya saka muku da Alkhairi Yakuma ji qan Alh Bilal ya masa rahama.
kofa ya nufa Kai tsaye zuciyarsa na tsallen Allah yasa maganarsa ta Doki inda yakeso ta doka.
Dad kaante da Dawood ne suka Bude baki a tare suka ce
"Zamu karbeta har uwar idan tayi wayon shekaru biyu uwar ta dawo gida tayi auren......
Katsesu yayi ta hanyar juyowa ya katsesu da cewa
"Aa ni 'yata yanzu zan mata aure bazata zo renan shekaru biyu ba ta qarasa lalata sauran rayuwarta,
Kuyi hakuri mu tafiyar mu ka.......
"ZAN DAURA MATA AURE DA QANIN BILAL IDAN HAR HAKAN ZAI SAKA KA BADA ITA DA BABYN"..
Kalmomin dd babba kenan dasuka saka Ababa dauke wuta Yana juyowa Wani haqayin farin ciki da firgita na fita daga Kansa da kunnuwansa.
Dad kaante kuwa ajiyar zuciya ya sauke Bai shirya sbd shock duk da kusan Shima Abinda ya shirya fada kenan.
##MAMUH#
#DD KAANTE
#BENAZIR
#BABY AMNAH
#MARRIAGE/LOVE/HOT HOT
#ROMANCE
#ZAFIN KAI/ZAFIN KAI
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
42
Ababa Suma ne kawai Bai yiba a inda ya tsaya cak lakacin da kalaman dd babba sukai dirar mikiya cikin kunnuwansa,
Kasa gasgatawa da gasken Abinda yaji yasakashi juyowa ahankali idanuwansa a kafe kan dd babban ya tsaya Yana zaunar da zancen cikin Kansa da zuciyarsa tareda boye shock dinsa.
DD kuwa wuta ya dauke na wasu daqiqun da baisan meyema zaiyi tinani Akai?
Wane qanin Bilal din ake maganar ya auri mahaifiyar 'yar Dan uwansa?
A saninsa bayan shi akwai qannan dangi dasuke dashi Amma dai koyaushe akace qanin Bilal yasan shi ake nufi duk da a cikin familyn ne kawai ake kiransa qanin Bilal Shima daga mahaifiyarsu sai dad kaante Amma kusan babu kiransa qanin Bilal sbd ganin yafi Bilal din samun cigaban rayuwa ta bangaren dukiya da suna.
Muryar Ababa dake rawa Yana damqeta Dan Hana bayyanarda zalamarsa a natse Yana kallan dd babba yace
"Idan har aurenta zakuyi Banda matsala da Hakan a shirye nake Amma dai Reno ko zuwanta zaman Dan Wani lokacin ne ban yarda dashi kwata kwata sbd babu adalci ahakan."
Dd babba numfashi ya sauke Kansa na sarawa da hukuncin Daya Yanke din Amma Kuma basuda zabin Daya wuce Hakan a yanzu sbd suna buqatan karban babyn ta dawo hannunsu Kuma rabata da mahaifiyarta kaman yanda Ababa ya fada cutatarwa ne,
Dad kaante ya kalla Wanda Shima dd babban yake Kallo kafin suka Maida kallansu kan DD a tare Wanda shikuma Sam hankalinsa Bai tashi ba sbd baima dauka cewan dashi ake ba akan maganar kawai dai buqatansa 'daya Daya sani shine 'yar Bilal 'yarsa ce a yanzu halak malak da Bilal baya duniya,
Idan akwai wainda ya Isa ya karbi babyn yayi Iko da to shine Dan haka zai karbi babyn kota halin Yaya sbd sanin dayayi babu inda dukiya Bata magana Kuma Bata Aiki.
Dago kyawawan idanuwansa dasuka Dan fada yayi yaga kalar kallan da dd babba da dad kaante suke masa hakama Ababa Shima kallansa yakeyi Yana Jin kaman ya janyosa ya daura masa aure da benazir a lokacin.
Irin kallan da suke masa ya sakasa Sakin Wani gajeran crazy numfashin murmushi cikin zuciyarsa Yana cewa
"Wane crazy tinanin ne yake cikin kan tsoffin Nan"
A fili kuwa Kai tsaye cikin hade fuskarsa daga mamakin tinanin Dayake gudana cikin kansu yace
"You gotta be kidding me,
Ba Abinda nake tinani ba kuke nufi kenan ba right?
Kallan da dd babba ke masa ya tabbatar masa da Abinda suke tinani
Dan haka shi bai iya boye boye ba baya Yi
so tsayuwarsa ya gyara a natse ya Kalli Ababa dake masa kallan mukullin arzkinsa kafin ya dawo da kallansa kansu dd babba ya Bude baki a natse yace
"Babu raayi ko gurin auran mace biyu a rayuwana,
Dayan is ok so bana buqatan Qarin kowanne macen bayan dayan
Please kar ayi complicating things anan,
Maida kallansa yayi akan Ababa dake jiran matsaya Bai masa kallan tsaf ba Kai tsaye yace
"Zan baka blank cheque lissafinka yafara daga naira milayan 100 zuwa sama ka rubuta nawa kakeso ka kawon 'yata da kanka yau"......
Wani jiri ne ya dibi Ababa ya zubar qasan palon gaban DD din batareda ya sani ba sbd kudin Daya fada shi Koda an auri yar tasa Bai taba lissafin zai samu kudin zasu Kai miliyan darin ba bare zuwa sama.
Zufa ne ya tsatsafo masa ta ko Ina ya karye Yana tsiyayo masa,
Kasa dagowa yayi ya Kalli kowa sbd yaqin dayakeyi da zuciyarsa da hankalinsa dake Neman gushewa akan Jin kudin,
Rawa hannuwansa suka dauka yayi saurin zirasu cikin babbar rigarsa kada a gani asan gushewan hankalin Daya samu na 'dan lokacin.
Girgiza Kansa ya hau Yi Yana Hana kansa bayyanarda halinda yake ciki
Amma idan har wannan kudin zai iya sakasa haka hakama Idan DD kaante zai iya bayarda wannan kudin kaman ba komai bane to idan ya auri yarsa yaya kenan?
Abinda zai samu zai zama nin ba ninkin wannan???
Hummmnn ya sauke numfashi a boye tareda yaqar zuciyarsa ya dago ya Kalli dd babba da Suma duk suka rasa abin fada sbd Tim farko kowannensu yasan waye Dawood da raayinsa da kalan yanayin rayuwarsa,
To Amma a yanzu dukkaninsu suna buqatan 'yar dake hannun Ababan Dan haka suna buqatan sacrificing wasu raayoyinsu Dan samun Abinda suke so da buqatan kaman yanda dd babba ya sauke nasa tsananin raayin.
Ganin kaman Basa hayyacin fahimtar Abinda yake fada ya juya yabar palon may be idan Basa ganinsa su kawo Wani tinanin na Abinda zai yiyu.
Yana ficewa Ababa ma Dayake ta yaqi da zuciyarsa gurin Hana kansa karban kudin Dawood kaante din ya fice zuwa gida Yana hada hanya zufa na sake jiqasa.
Bayan barin Dawood da Ababa palon dd babba Kai tsaye Kiran Umme yayi a waya wadda itama take matse da akirata din Jin zuwan Ababa kaantes taji ya aka Kai karshen magana Dan Bata hayyacinta matiqar ba gabanta taga 'yar Bilal dinta Kuma jikarta ta fari ta dawo ba.
Lokacin da tashigo palon Kallo Daya dd babba yayi mata ya dauke Kai sbd ganin yanda gabaki Daya ta fita hayyacinta sbd ciwon rashin 'danta,
Kaman wadda take kwance jinyar watanni Takoma idanuwanta kuwa sun kasa hucewa daga munin kumburin da sukai na kukan data kasa denawa har yau din na rashin Bilal da tsananin buqatan 'yarsa ta dawo gunta.
Cikin nutsuwa da sanyin jiki dd babba ya Bata tabbacin 'yar zata dawo hannunsu Amma sai idan ta saka Dawood amincewa da auren mahaifiyar babyn wannan shine sharadin Mahaifin maman Babyn idan ba Hakan ba a gobe zai tafuyarsa Subar garin gabaki Daya.
Hawaye masu dumi ne suka gangarowa ummen sbd lalata rayuwar 'danta da ake magana a maimaikon 'yar Dan uwansa da suke buqata su dukan,
Auren Sbb dole ne garesa Badan raayinsa ko buqatan Hakan yake ba Amma ya amince sbd ita Dayake son farantawa Amma tasani Wanda bayason hada ko muhalli da kowa har iyayensa ansamu ya aminta zaiyi aure yanzu tin baayi ba ana sake kawo masa Qarin mace ta biyu.,
Yaya Dawood zaiyi da auren mace biyu lokaci Daya?
Tako wane saqo anshiga haqqin rayuwarsa,
Amma Kuma Tayaya suna Kallo zasu rabu da 'yar Bilal ta tafi tabarsu kaman yanda Bilal ya tafi yabarsu da gibi me girman gaske a zukatansu.
A Karo na biyu zata sake zama uwa Mai son Kai ga Dawood Dan kuwa zata sake shiga rayuwarsa da Qarin wata macen.
Hannu takai ahankali ta share hawayenta tareda jinjina Kai tana Bada tabbacin zata gwada shawo Kansa akan maganar auren.
Miqewa tayi ta fito Kai tsaye part din Bilal da DD din yake ta nufa zuciyarta na karyewa.
Tana Isa a Palo ta taddasa zaune Yana amsa wayar Naseer a hankali Wanda ya kira akan yazo daukansa yau zai koma gidansa.
Jin qarshen wayarsa na tafuyarsa dazaiyi yasaka ummensa kasa riqe hawayenta suka gangaro tayi saurin sharewa da hannunta.
Zaunawa tayi gefensa tareda kasa juyowa ta kallesa sbd kunyar rokon da zata yimasa a Karo na biyu.
Idanuwansa ya dago ahankali ya zuba mata ya karance yanayinta tsaf tsawon mintina kafin ya Dan dauke idanuwansa Yana ajiye wayarsa dake hannunsa gefensa ya kalleta cikin nutsuwa yace
"Umme idan kikace nayi auren Nan Hakan na nufin Zaki janye wancan maganar auren na farko,
Na baki zabin duk Wanda acikinsu kikeso ki zaba Daya zan aura kowace a cikinsu".
Yana fadan Hakan yayi mata shiru sbd babu Abinda zai qara Akai,
Maganar zasuyita Janta ne har sai waninsu ya samu ciwon Daya shigesa na damuwa da maimaicin Abu Daya Wanda Sam Hakan baya cikin Abinda yake buqata a rayuwarsa.
Shiru ummen tayi tana kallansa da idanuwanta dasukai laushi sbd a cikin Biyun yanzu babu Wanda zata iya zaba tabar Wani.
Ajiyar zuciya tayi ahankali sbd da Bilal dinta na Nan da duk bazasu shiga wannan tsaka me wuyan ba daga ita har Dawood da zaa aurawa mata biyu duka badan Yana sonsu ba.
Miqewa tayi ta fito Bata iya zabar ko Dayaba a zancen ta koma part dinta tana shiga tinani da damuwan Tayaya ma zata iya kallan Dan uwanta da hajiyarsu ta fada musu Dawood bazai auri Sbb ba wata zai aura?
Wannan maganar kadai zata iya shiga tsakaninta da Dan uwanta da hajiyarsu komai ya lalace a zumincinsu.
Dad kaante ma da Kansa yaje yayo magana sosai da Dawood din Amma Sam raayinsa ya kasa sauyuwa Saida dd babba ya rokesa a matsayin shine zaiwa alfarmar Benazir,
Idan ummensa ta rokesa ta zabar masa Sbb shikuma ya rokesa ya zabar masa benazir Dan haka Suka sakasa a tsakiya sbd sune mafi soyuwa a ransa su Biyun sai babyn da ayanzu tin batazo hannunsa ba yake jinta cikin ransa ta maye gurbin da Dan uwansa yabar masa.
Tinda dd babba yake babu Abinda suka taba ganin ya kwantarwa Kai sai wannan buqatan tasa ta auren Benazir wadda ta saka kusan sauran yayansa sanin halinda ake ciki.
DD kuwa daya gama fahimtar babu Abinda zai sauya tinanin su dd babban daga maganar auren dole ya amince sbd yasan auren sbd 'yar dasuke buqatan karba zaayisa hakama bayajin zai iya kallan matar da Bilal yagama mallaka a matsayin tasa matar,
Bama zai iya saka kalman aurenta cikin Kansa ba sbd Dan uwansa musamman da haihuwa a tsakaninsu.
A cikin Daren zancen yarda da auren isarwa Ababa,
Da farko kasa yarda yayi da Abinda dad kaante ya kirasa ya sanar masa akan zuwansu Neman auren 'yarsa gobe Saida ya kashe wayar ya sake dubawa yaga tabbas sunan dad kaante ne suka gama magana a lokacin.
Sakin wayar yayi tareda zubewa qasa da sauri yayiwa ubangiji sujjada ya taso ya fito zufa na tsinke masa ya tsaya tsakar gidan ya kwada sunan benazir wadda ke daki zaune tana bawa baby Madara.
Jin Kiran Ababa ya sakata sauke ajiyar zuciya ahankali jikinta sanyi da faduwar gaba ta miqe ta fito kanta a qasa ta tsaya gabansa daga nesa kadan rungume da babyn.
Anne ma dake dake rakube zaune fitowa tayi gabanta na faduwan ta tsaya gefen benazir.
Hande ma da sauri ta fito tana tsoron idan ba mutuwa benazir din tayiba itama yake wannan ihun Dan kuwa benazir na mutuwa wannan Karan zaucewa Ababan zaiyi.
Tinda aka haifesu shekaru masu yawa benazir Bata taba ganin murmushin Ababa akansu ba Dan haka daidai lokacinda ya kalleta ya saki murmushin baya tayi ahankali qafafunta na Neman sarewa da tsananin tsoro da fargaba tana sauke Kanta qasa.
"Benazir kin cika mun burina na shekarun Dana debo Ina wahala daku,.
Kallan yarinyar hannunta yayi yaji zuciyarsa na sake sanyaya da farin cikin ganin wannan ranar
Yace
"Sunan benazir sunan sa'a ta ne a yanzu Dan haka itama na saka mata BENAZIR sbd idan Kuka je Tako ina sa'a tayita fasomin ba kakkautawa,
Aurenki zaa taho nema gobe a satin Nan zaa daura Miki aure.
Anne data ji saukan zancen har cikin zuciyarta ta rintse idanuwanta a hankali tana tilasatawa zuciyarta karban zancen da sanyin farin cikin dole.
Follow me at mamuhgee Arewabooks ko VIP for more pages
09033181070
#MAMUH#
#BENAZIR
#DD KAANTE
#HOT HOT
#MARRIAGE
#LIFE
#DEEP
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
43
Benazir Bata iya dagowa ta kallesa ko Annenta ba sake Yin baya tayi ahankali ta dafa bango idanuwanta na kasa taro ruwan hawaye sbd takai matakin da ko kukan yanzu Bata iyawa Amma dai zancen har lokacin jinsa takeyi kaman almara,
Rabata zaayi da Annenta,
Ya Anne zatayi rayuwa babu kowannensu,
Sameerah ta rasu, Safnah ta tafiyarta, sumayyah ta rasu
Ita Kuma yanzu gashi zata tafi tabar Annen da sunan aure,
Bata tausayin kanta sbd babu inda bazata iya rayuwa ba komai tsanani da wahala da rashin kauna hakama batada sauran Jin feelings a zuciyarta dama rayuwarta gabaki Daya da zata ji komai na duk abinda zata tarar a rayuwar da mahaifinta ya Saidata Akai.
Ababa cikin farin cikin dabai taba Jin irinsa ba ya tinkaro Benazir ya karbi babyn hannunta Yana mata wasa baki a washe Yana saka mata albarka harma da rungumeta Yana Jin kaunarta Mai tsanani wadda yake ganin kaman ta kudin dazaiyi ne sanadinta.
Hande ma farin cikin me tsanani na Jin zasu rabu da 'yar ta washe baki tana cewa
"Barkanmu da arziki daga qarshe dai zamu samu mu aurar da Daya daga cikin haihuwar Anne da babu Wanda aka amfana dashi."
Kalmar hande ta saka idanuwan Anne dasuke danne halinda zuciyarta ke ciki na rabuwa da 'yarta cikowa da hawayen data kasa barinsu saukowa ta hadiyesu suka koma maqoshinta sukai cikinta.
Benazir ma Kalmar sakata tayi qarasa silalewa ta zube qasa zaune tana rufe Idanuwanta dasukai mata nauyi.
Ababa kuwa wayarsa ta fidda babyn na hannunsa ya kira yaronsa Bilymanin yazo take ya fidda kudi ya sako aka bazama siyayya.
Har qarfe goman dare Mai saka Kofa da windows da masu Fenti na gidan Yana sakawa su benazir a dakinsu,
Tsakar gidan da waje kuwa da yamma Akai Fentinsu ba Bata lokaci.
Tinda safe masu qatuwar katifa da fanka aka zo aka saka musu dakinsu harma da labule da sabuwar Ghana must go ta saka kayansu na sakawa,
Hadda sabuwar cerpet din daki aka zo aka shimfide dakin duka da ita sbd sanyin siminti dasuke Sha shekara da shekaru kada ya kama baby benazir.
Koda karfe goma Sha dayan Rana tayi gidan gabaki Daya kaman ba gidansu ba,
Benazir da Anne suna daki zaune ko mamakin sun kasa Dan a yanzu babu Abinda zai Basu mamaki ko tsoro daga wannan rayuwar.
Sabbin kayan sawa masu kyau da maana aka siyowa benazir na jallabiya Mai kyau da yar tsada harma da tirarika masu Dan kudi.
Itama Anne an siyo mata Riga da zani na atampa ready-made masu yar tsada
Ya sakasu cin abinci duk bayan awa data saiyace su sake ci sbd so yake fuskokinsu dasuka Fi kama dana qwarangwal su Dan ciko kafin zuwansu kaantes.
Tin safe yasaka aka gyare koina aka siyo abinci lafiyayye daga restaurant me yawa aka ajiye sunta fama yimasa cin dole kafin Kuma yasaka hande da kanta ta zaunar da benazir tayi mata wankin Kai Dana qafafu duk da Bata cikin qazanta sbd sunada tsaftansu sosai kaman ba wainda ke cikin wahala ba Amma sbd muzantawa hande ce ta zaunar da ita ta Riga zuba mata ruwa tana wanke mata Kai kaman yarinya qarama.
Bata motsaba har handen tayi ta gama ta Bata Daman tashi tkuna ta miqe jiki ba qarfi tabar gurin taje tayo wanka ta dawo dakinsu ta zauna bakin katifar da tsoron Hawa ma sukeyi sbd kada baqin su tafi yace abada katifar yace sun lalata masa Dan haka yasaka ma sun kasa sakewa su hau katifar.
Mai tashafa ahankali jikinta babu me magana a tsakanin ita da Anne har tagama ta shirya cikin kayan da aka siyo din ta shirya baby bena itama cikin kaya masu kyau da nauyi na Zeenah data kawo mata shekaran jiyan datazo.
Anne ma wankan tayi ta shirya cikin nata kayan da aka Bata suka zauna daki jigum jigum kaman wainda zaayi shooting film dasu.
Hande ma fes ta shirya cikin lace Blue da fari ta fito kaman tsohuwar albarka.
Ababa kam Jin yake kaman ranar ce zaa daura auren Dan haka yayi Shirin mutinci da babbar Riga da Hula tareda Wanda ya aminta ya tayasa tarban bakin da Bada auren.
Qarfe hudu bayan sallar laasar baqin suka iso ga mamakin Ababa harda dd babba aka taho da dad kaante sai Hon kaante qanin dad kaante,
Dd babba ko auren yayansa babu Wanda taba zuwa da Kansa nemawa aure sai wannan Karan Wanda Daman alqawarinsa ne shine zai je namawa Dawood aure,
Bai samu yaje ya amso masa na Sbb ba Dan haka ya taso da Kansa Dan nema masa na benazir.
Hadda Umme da mum Khadija akaso sai Zeenah da Siyam kaante autan mum Khadija itama.
Su dd babba kofar palon Ababa ta waje aka Bude musu suka shiga su kuwa su Umme Kai tsaye cikin gidan suka shigo Dan ganin baby Benazir da mamanta.
Hande na ganinsu ta saki fuska tana musu barka da zuwa cikin girmamawa da nuna farin cikin zuwansu.
Anne ma dole ta fito tayo dakin handen sbd a can aka saukesu.
Cikin nutsuwa da sanyi tareda girmamawa ta shigo dakin ta gaidasu tareda musu barka da zuwa.
Umme Datake kallanta a natse ta hango nutsuwa da rashin son kallan mutanen Anne sai taji Dan sanyi yaqara shigarta sbd koba komai mahaifiyar benazir nada nutsuwa Allah yasa hakama benazir din.
Zeenah ce ta Kalli Anne bayan ta gaidata tace
"Benazir da baby fa?"
Cikin nutsuwa da sanyi tace tana daki bari tazo ta kawo muku 'yar.
Juyawa tayi ta fice.
Daki taje ta kirawa benazir da jikinta yagama sanyi Amma babu gudu ba ja da baya ga wannan sabuwar qaddarar Dan haka ta miqe rungume da bena a jikinta ta fito.
Tana fitowa Zeenah na fitowa daga can zata amsa waya Amma tana ganinsu ta fasa ta nufo tana miqa hannu ta karbi little bena.
Gaisawa sukai da benazir da batasan me zata ce suka nufi dakin hande qafafunta na rawa.
Zeenah ce a gaba rungume da baby ta shigo ta nufi su Umme tana miqawa Umme babyn tana cewa
"Ga benazir Nan ta shigo Umme."
Hannu na rawa cikin Jin sanyi da farin ciki Umme ta karbi Babyn kafin ta dago ta zubawa benazir data qarasa shigowa cikin nutsuwa kanta aqasa itama Ido.
Ahankali cikin sanyi da yar rawar murya benazir ta Bude baki ta gaidasu Daya bayan Daya batareda ta dago ta Kalli kowannensu ba.
Ajiyar zuciya Umme ta sauke sbd sai yanzu ne take fahimtar Abinda yasaka Bilal kamuwa da son benazir din,
Bilal na son nitsatsiyar mace Mai tsananin sanyi,
To Amma Dawood total opposite ne na Bilal anan bangaren shi baamasan irin matar Dayake so ba kokuma raayin aura,
Amma ita dai idan har wannan nutsuwar Data ga benazir da mahaifiyarta da ita to benazir din ba Abar qyama ko baqin cikin aura bace.
Kasa zama cikinsu tayi kaman yanda Zeenah taso Dan haka ta silale Takoma daki
Anne Kuma itace ta kawo musu ruwa da abin Sha harma da abinci da snacks masu kyau da akayo order acikin sabbin plates da Ababa yasaka aka siyo.
Itama tana gama Jere musu kayan ta fice sbd bazata iya tsayawa cikinsu ba.
Daki tabi benazir Suka Kalli juna Annen ta qaqalo murmushin da ko kyau baiyi mata ba sbd zamansa na qarya da qarfin hali.
Benazir ganin Hakan ta saki nata murmushin Mai ciwo Daya bayyanarda zafin quncin dake qasan zuciyarta tana nunawa Annen gefenta da hannu ta qaraso ta zauna.
Annen ce a hankali ta sauke numfashi ta Bude baki tace
"Benazir na Amince kuma nayi na'am da wannan auren da zaa dauka Miki har cikin zuciyata a matsayina mahaifiyar data dauko cikinki ta haifeki Ina Miki fatan samun sauyun rayuwa ta hanyar wannan auren,
Allah ya albarkaci rayuwar da Zaki tarar acan keda Benazir qarama hakama inshallah zanyi juriyar da banyi a baya ba,babu Abinda zai sameni sai Abinda Allah ya Riga ya qaddara zai sameni."
Sunkuyar da Kai benazir tayi kalaman Anne na sanyaya jiki da zuciyarta sbd tabbatarda dai auren zaa yimata ta tafi tabar Anne.
Numfashi kawai ta iya saukewa jikinta na sake mutuwa da sanyi a hankali ta furta
"Komai zai zo karshe Anne,
Dukkanin tsanani Yana tare da samu inshallah,
Zaki rayu kiga auren Baby benazir Anne,
Zaki rayu,wahala Bata kisa,komai zai wuce Anne.....riqe hawayen dasuka ciko idanuwanta tayi tana hanasu saukowa sbd baqin dake gidan.
Annen ma kasa magana tayi tana Hana kanta sauko da nata hawayen itama.
Sake kiransu Akai suka fito mum Khadija ta saka Benazir din zama tareda su dole suna Dan tambayanta lafiyan baby da ita kanta tana Basu amsa a taqaice cikin girmamawa.
Ahakan sukaita kokarin Janta da magana kafin aka Sako maganar Bilal Wanda ya saka Benazir kasa riqe hawayenta na rashin 'yar uwarta da hawayen Datake ta dannewa tin a daki sukuwa jikinsu duka yayi sanyi Suma hadda hawayen sbd tinanin rashin Bilal takewa hawaye.
Yanda benazir ta bayyanarda kukanta a fili na rashin Bilal ya sakata shiga ran ummensa dasu Zeenah Dan haka Suka matsu ma kawai ayi auren ta dawo cikinsu su mayar mata soyayyar dasukewa Bilal ita da baby Benazir wadda a take Zeenah ta Dora make AMNAH akan sunan benazir din da aka sakawa babyn.
Da zasu tafi kaman kada su bar mata babyn haka Suka fita suka tafi Anne naji nauyin zuciyarta na Dan raguwa sbd ganin mutanen da Bena dinta zata Yi rayuwa acikinsu.
Sun nema auren Benazir Ababa ya Basu sun Bada kudin aure masu yawa dasu sake qarawa Ababa kaunar baby Benazir,
An saka ranar daurin aure 6 ga watan Sept sati biyu masu zuwa kenan.
*******Maganar auren ta yadu har inda Ababa Bai taba tinanin zaa fada ba Jin yake ana fada,
Kullum sai ya saurari redio da kafofin yada labari Dan kawai sauraron sunansa a cikin sanarwar daurin auren duk da kullum zuciyarsa quna takeyi idan ya Tina mace biyu zaa daurawa Dawood din lokaci Daya Amma tinda dai tasa zata shiga baida matsala hakama Amnah zata sa a Fi fifita benazir akan dayar tinda ita Amnah kowa na sonta.
Sati na zagayowa Akai yankan sunan benazir Amnah Wanda Akai a sirrance batareda ma kowa yasaniba,
Har lokacin Dawood Bai San waye benazir da zai aura ba hakama sunanta takamamai ya kasa riqewa sbd ko maganar ya dakatar da ayi masa buqata kawai a daura auren yarinyarsa ta dawo hannunsa qarqashinsa.
Ranar da Kai sunanta a ranar Zeenah tazo ta dauki Amnah taje da ita kaantes.
A ranar DD yafara ganin ta a hannunsa ya zubawa fuskarta Ido babu Abinda ta baro na Bilal,
Wani irin feelings ne na soyayyar Uba Mai tsananin gaske yaji yanawa babyn,
Shi baya ko daukan Yara sbd Basu damesa Sam baya ma Wani San Yara Kuma kowa ya shedesa da Hakan,
Amma ayau ranar farko babyn farko dayaji tashiga ransa,
Duk buqatan karban babyn Dayake Yi a baki sai Daya rungumi babyn yakejin Abinda ma yafi buqatan ta a kusa,
A rayuwarsa kwata kwata yake buqatanta sbd bazata taba maraicin Mahaifinta ba matiqar Yana Raye shine Mahaifin dazai nuna mata soyayyar Uba,uncle harma da uwa idan ya tafi da ita.
Masu buqatan pages da Akai Nisa sosai follow me at mamuhgee Arewabooks kokuma suyi joining VIP
09033181070
#MAMUH#
#HOT
#MARRIAGE
#ROMANCE
#DBENA KAANTES
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
44
Sai yamma aka Maida baby Amnah gurin mamanta tareda da kayan da saidai aka Kai wasu dakin Ababa dakinsu ba guri,
Ababa kuwa shanun da aka yanka haka ya kama fiyeda Rabi ya siyar sauran Kuma yayi sadakar Rabi sbd Amnah tayi albarka Wanda ya rage kuwa aka Soya suka ringa cin abinsu hankali kwance,
Su benazir din Suma wanna Karan anbasu me Dan yawan dasuka ajiye Dan bazasu iya cin ba,
A cikin damuwa suke da sanyin jiki Dana zuciya na rabuwar da zasuji da juna,
Daga hande sai Ababan ne suke cikin tsananin farin ciki da murnar auren Dan haka yanzu baa musu Horan yunwa abinci yake Basu sosai tareda yiwa Benazir alqawarin idan ta Kwantar da hankalinta a auren take ta zama hamshaqiyar da zata ringa Basa dukiya kaman batasan metake ba shikuma yai mata alqawarin Annenta zatai rayuwar 'yanci da kwanciyar hankali.
Idan ta je ta Saba umarninsa kuwa Annenta ce zata dauki hukuncin babu tausayi ba sauki tasan halinsa.
Abincin dasuke samu ana Basu tareda saka su cin dole harma da kayan gyaran jikin da ake gyarata ya saka Benazir Dan cikowa daga bushen Datake.
Hande kuwa ita dai matse take da ayi bikin su huta Dan haka ta ringa gayyata tana shelan gidan da 'yarsu zatayi auren.
Kayan lefen aure Mum Khadija ita Daya ta kawo sai Zeenah da Siyam sbd Basa buqatan daukaka bikin komai a kaman sirrance zaayi sa
Sai daga baya idan Sbb ta dawo zata tare ayi bikin da kowa zaiji ayi gayyatar da aka San bazaa ji kunya ba.
Lefen da aka a cikin akwatinan lv set ne Dan
situran alfarma da kaf gidan har Ababa baisan kudinsu ba da darajansu aka kawo mata bare ita da batama San wata sitarar ta alfarmar ba,
Breeziers da panties da komai na cikin kayan foreign ne masu tsada designers Dan gashi kusan komai daidai na matashiyan mace ne aka Sako hande naji tana Gani babu abin dauka aciki sai laces data kwasa da atampa kusan guda goma.
Anne kuwa komai batada shaawan mallaka a kayan bare Kuma ma me kayan benazir da kasa ma kallan kayan tayi bayan da dare yayi suka shige.
****Ta bangaren Kaantes babu Wani biki bayan daurin aure Dan haka babi Wani hidiman dasuke Yi sai jiran lokaci.
Umme wata damuwan ta sake shiga a lokacinda Dan uwanta yace a boyewa Sbb maganar auren Dawood da wata bayan nata tinda bata qasar Dan haka Umme taketa Jin damuwa kada Sbb din taji ta tada rigima da tashin hankalin da zai saka hajiyarsu taji ba Dadi kokuma laifin Dawood akan zai auri wata lokaci Daya da Sbb dinsu.
Ita kuwa sbb din acan farin ciki takeyi Mai tsananin gaske Jin zaa daura aurenta da DD kaante kafin daga Baya ayi bikin tarewarta idan ta gama sauran karatun nata ta dawo.
Ango DD kuwa babu Wani Abu na farin ciki ko baqin ciki Dayake ji gameda aurensa,
Abinda ya sani shine aure ne zaa daura masa da matan da babu wadda yake so aciki,
Daya zabin mahaifiyarsa,
Daya zabin kakansa Kuma baby mamah dinsa Dan haka duk Wanda Bata sakawa Kanta tinanin dayafi karfinta ba itace zata zauna kaantes lfy.
Ana sauran kwana daya daurin auren Ababa yaje Kaantes da maganar kayan daki Kai tsaye suka sanar dashi babu Abinda suke buqata nasa bayan benazir da babynta.
Daman yasan zaayi Hakan Dan haka ya dawo yaci gaba da shirye shiryensa cikin farin cikin samun cikar burinsa.
Benazir kuwa kullum dare sai sunyi Kuka sosai itada Annenta na rabuwar da zasuyi da juna Bada San ransu ba,
Duk yanda Annen takeson daurewa da dannewa kasawa tayi Dan haka duk dare take Shan kukanta a boye
Itama benazir duk dare tareda Annen take kukan daga kwance batareda Annen tasan Benazir tasan tana Kukanba kullum.
Ta bangare Daya a Dan qanqanin lokacin Reno tamkar da uwar data haihu yariga ya shigeta Dan idan ba nono da Bata Hawa Amnah ba tini itama ta sakawa ranta itace ta Haifa Amnah kaman yanda Ababa ya fada.
Renon Amnah yasaka yanzu aikin gidan tini aka dauke mata sai ga me Aiki hande ta saka ankawo mata wata bazawa daga kauye.
*****
Ranar Friday 6 ga watan Sept aka daura auren DAWOOD D KAANTE Dana BENAZIR ABABA kafin daga Baya aka sake daura na DAWOOD D KAANTE din da SAFNAH BASHEER BULAMA.
Daga lokacinda aka gama daura auren Benazir da Dawood Ababa a cikin bainar jamaa ya zube qasa yayiwa ubangiji sujjada ya miqe ya sake Yi Yana miqa godiyarsa ga Allah.
Sunan Safnah da aka ambata gurin daura auren ba biyu ya saka Ababa dakatawa daga farin cikin Dayake yi yana Tino tasa Safnar data gudu Yana jin baqin ciki tareda fatan wannan Safnar ta gudu daga auren Nan kaman Yanda Safnar gidansa ba a gudu.
Taron daurin dauren ya hada manyan mutane masu yawa daga garuruwa daban daban.
Fadan Taron da aka samu a gurin bazai yiyuba
Securities kuwa koina na anguwar da kewanta hakama jiniyas na motocin tsaro koina.
Akwai mutanen DD dasuka halarci daurin dauren da damansu Dan haka dole ya tsaya ya amsa adduoin mutane da dama kafin ya bar gurin daurin auren Kai tsaye gidansa ya wuce sbd Yana buqatan hutu daga mutane.
Naseer ne Daya kasa yarda da benazir din Dayake bibiya ce tin makaranta aka daurawa DD aure da ita sbd yasan dai itace Benazir Ababan.
Suna isowa a natse ya fito mota Kai tsaye ya wuce ciki Yana cewa Naseer kada ya bari kowama yasan Yana gida hutawa zaiyi Yana fama da headache.
Shi Kansa Naseer Yana fama da headache din Dan haka kashe wayar DD din yayi ya ajiye masa ita a palonsa ya fito yabar gidan ya tafi gida Shima ya samu Kansa ya warware Shima.
Yana shiga bedroom dinsa kayan jikinsa na sky blue tsadaddiyar shadda ya ciresu gabaki Daya tareda shiga closet room dinsa ya janyo drawer da towels ke jere aciki ya Ciro Daya ya daura a qugunsa da babu kaya a jiki ya nufi toilet.
Komai Dayake toilet dinsa na musamman ne domin buqatansa sbd baya iya sharing toilet da kowa,baima taba ba duk tsanani baya amfani da toilet koina sai gidansa sai kuwa na part din Bilal Dayayi amfani dashi a kwanakin dayayi Kaantes.
Ahankali ya sakarwa Kansa ruwan dumi Yana lumshe idanuwansa ahankali sbd relief dayaji yafara samu daga gajiyansa.
Bai dauki time sosai ba yagama ya fito jikinsa da toilet din gabaki Daya ya cika da sanyin qamshin English pear shower gel na Jo Malone.
Daurin towel din qugunsa kaman yanda ya Saba daurawa a sassake kaman zai Fadi yabarsa ya nufi mirror Bai tsaya batawa Kansa time kaman Wani mace ba body oil na Aesop kawai ya shafawa lafiyayyan fatansa dake daukan Ido kaman baby da baya shiga Rana kwata kwata.
Spray kawai ya fesa Wanda ya sake kashe dakin da sanyin qamshinsa ya bar gaban mirror yaje ya saka black Calvin Klein sleeveless shirt da black quarter trouser da slippers masu taushi ya fito Palo ya wuce kitchen ya Bude fridge ya dauko ruwa mara sanyi ya Sha kadan ya koma daki ya kwantawarsa Daman Bai Wani Yi baccin safen ba sbd daurin auren.
Yana kwantawa sbd rashin damuwa da gajiya take bacci ya daukesa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
*******A gidan Ababa kuwa ranar ce ranar farko da Ababan ya sakawa tasa haihuwar albarka Dan kuwa benazir din ya dinga zundumawa albarka ba kunyar Allah bare ta su Benazir din da Annenta.
Kaman yanda akewa kowace haka Anne ta zauna da benazir da idanuwanta suka bushe sukai jajir Bata iya cewa komai sbd ayau nauyin zuciyarta yafi na kullum,
Bata taba tinanin ta wannan hanyar zata rabu da Annenba,
Kuka takeson Yi na barin mahaifiyarta da itama zatayi su barta a hali da rayuwar ukubar da basusan ya zamu sameta a gaba ba.
Kwata kwata takasa kuka tin lokacinda aka tabbatarda an daura auren,
Jajir kawai idanuwanta sukai suka bushe jikinta ne kawai yake rawa a boye Shima sbd halinda zuciyarta ke ciki.
Ita kanta Annen daurewa kawai takeyi tana Hana rauninta bayyana gashi akwai mutane a gidan,
Kaman marayu daga benazir din har Anne babu me walwala ko kuzari suna rakube a daki cikin mawuyacin hali gashi Basu Saba shiga mutane sosai ba Daman.
Su kansu yan bikin duka mutanen hande ne da wasu daga danginta dasuka zo daga kauye Dan haka baa damu da nemansu ba har sai yamma da Ababa ya dawo gidan lokacin kusan duk an watse ba kowa sai su sai baqin hande na kauye mutum uku da suka taho Kuma suna can sunata faman Aiki kaman wasu injin baji ba Gani.
Ana gama sallar magrib Ababa yayi kiransu take gabansu a tare ya Fadi lokaci Daya Anne tayi qasa da kanta tana hade hannuwanta dake rawa ahankali ta damqe tana kasa dagowa ta Kalli benazir data juyo ta zubawa Annen idanuwanta da take suka ciko da wasu ruwan hawaye masu tsananin zafi.
Anne najin daukan hawayen benazir a hannunta ta miqe tsaye tareda juya baya bazata iya kallan benazir din ba hannuwanta na tsananta rawa tana Hana kanta kukan Dayake yanka zuciyarta fitowa ta sunkuyar da kanta.
Benazir data ga Hakan kukanta ya kufce ta kasa motsawa itama sbd Bata taba Jin radadi irin Wanda take jiba a lokacin ba.
Hande dataji shiru shigowa dakin tayi Kai tsaye Bata Jira komaiba ta kamo hannun benazir ta fara Janta tana kokarin ficewa da ita, sai alokacin ne benazir ta iya Bude baki ta kira sunan Annen a hankali.
Kasa juyowa Annen tayi sbd hawayenta dake saukowa da gudu kan fuskarta zuwa kirjinta,
Bazata iya Kallon a rabata da benazir a tafi da ita ba duk da tanason Hakan tamafi Ababan buqatan benazir dinta ta tafi tasamu 'yanci da rayuwa Mai kyau.
Benazir na ficewa daga dakin ta fasa Wani irin Kuka Mai tsananin ciwo da qarfin gaske tana Jin wannan rabuwar tafi mata ciwo akan ta sauran yan uwanta sbd su tasan mutuwa sukai suka bar duniyar
Annenta kuwa batada tabbacin rayuwar da zatayi a gidan cikin lafiya sbd tafiyarta kawai zata iya tayarda ciwon Annen Kuma babu me iya ko kallanta bare ya taimaka mata.
A palon Ababa suna shiga hande ta dire Benazir din tana cewa
"Kuka takeyi a daki itada uwarta kaman wadda muka siyar gidan wahala."
Tsoki Ababa yayi sbd baida lokacin duk Wani sabon renin hankali ko Bata masa lokaci Dan haka ya Kalli benazir din fuska a daure babu rahama ko kadan yace
"Babu Abinda zan fada Miki
Kinsan daidai sbd ganganci Daya zakiya akan asalin waye mahaifiyar Amnah ki nema mahaifiyarki ki rasa bat zan batar da ita wlh,
Kiyayewanki shine zaman uwarki lfy,
Gangancinki kuwa a jikinta zataji,
Duk Abinda Zaki zama a Nan gaba kada ki manta uwarki na hannuna itace alqalamin juya rayuwarki a duk inda kike,Dan haka bazance komai ba sai Allah ya Bada zaman lafiya da sa'a,
Kuma wlh karki yarda naji ko naga kinje kin zama baiwa ko wata wawuya a gidan,
Kaantes Zaki zama ki koma hamshaqiyan matansu ta yanda zan Riga fada da alfahari 'yata ce a gidan ba baiwa na siyar musu ba mata na Basu."
Masu buqatan pages da Akai Nisa sosai follow me at mamuhgee Arewabooks ko suyi joining VIP
09033181070
#MAMUH#
#MARRIAGE
#ROMANCE
#CRAZYINLOVE
#DBENA KAANTES
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
45
Benazir kasa ko motsawa tayi da maganganunsa hakama Anne data biyo bayansu ta tsaya daga wajen palon tanajin duka Abinda yake fadawa Benazir tayi qasa da kanta tanajin inama itama ta mutu ya rasa Abinda zai juya rayuwar Benazir a gidan aurenta ta samu tayi rayuwar kwanciyar hankali kaman kowa.
Wani Abu me nauyi ne ya tsaya kirjin Annen tana Jin jikinta na sake sanyi tinda masifar Bata qarewa benazir ba kenan,.Tayaya zata taimakawa 'yarta qwalli Daya data rage mata a duniya?
Tayaya zata Hana Ababa juya rayuwar Benazir a gidan aurenta.
Wani numfashi ta sauke ahankali hannuwanta na Dan rawa daga tinanikan da zuciyarta ke Bata.
Benazir kuwa numfashi itama ta saki boyayye Wanda yasakata qarasa sarewa daga duniyan gabaki Daya hakama tinaninta ya koma empty Bata ma iya Gane komai yanzu bayan maganar Ababa dake ta amsa sauti cikin kanta.
Kaman makauniya haka hande ta sake kamata ta tayar suka fito
A lokacin ne suka tadda Anne a kofa wadda ta share hawayenta daga idanuwanta da babu sauran hawaye Kuma.
Ga mamakin hande Anne da kanta ta amsa Benazir ta nufi daki da ita ta shiryo benazir din da itama Bata iya komai sai yanda Akai da ita.
Duk yanda hannuwan Anne ke rawa sosai gurin shiryata Benazir na ji Amma Bata iya ko motsawa bare kallan Annen har suka gama ta itama ta sake shiryawa ta dauki Amnah da ta shirya itama ta dorawa benazir din a jiki ta rungumeta ahankali ta suka miqe Anne da riqe da hannun benazir din Daya suka fito.
Hande kallan mamaki takewa Anne data nuna qarfin hali da juriyar shiryo Benazir ta fito da ita da kanta.
Ababa baiyi Wani mamaki ba Dan yasan dole suyi Abinda yace din,
Baiyi mamaki ba sai lokacinda Anne da kanta ta Bude baki tace zata raka Benazir har gidan aurenta idan anbata dama.
Shiru Hande tayi tana kallan Annen Shima Ababan kallanta yayi Yana Maida kallansa gun hande yace
"Ciwonta Daman ya tashi ne shine baku fadamun ba?"
Lumshe idanuwa Benazir tayi batareda ta motsa ba
Itama Anne Dan rufe idanuwan tayi ta Bude ahankali tareda girgiza Kai cikin sanyi tace
"Bai tashiba lafiyata kalau,kawai so nake na Rakata din sbd bansan yaushe zamu sake ganin juna ba."
Kallanta hande tayi zatayi magana cikin fada Ababa ya katseta da cewa barta ta tafi din tinda Daman ba kowa ne ze raka Benazir din ba ke kince bazaki ba gwara ita ta rakatan.
Da wannan hande tayita fadan waye ya taba ganin uwa ta Raka 'yarta gidan miji sai akan Annen wadda ita ta tabbatarda haukarta ce ta tashi shiyasa,Daman idan bakada hankali komaima zaka iya Yi.
Anne kuwa hannun Benazir kawai ta kama Bata dago Kai ga fadan hande ba suka fito.
A BMW 7-series aka Aiko Abbakar daukan benazir tareda mum Khadija wadda da kanta ta amso benazir Suka shigo mota harda Anne wadda dukkanin jikinta rawa yakeyi da Abinda yake zuciyarta datasan zai iya zama sanadin rayuwarta Amma tayi na'am da hakan Koda ta rasa ranta tasan ta taimaki 'yarta takuma tseratar da ita inshallah ta yanda ko bayan barinta duniyar Benazir zata rayu cikin aminci da kwanciyar hankali.
Har suka Isa babu me ko motsi bare magana a motar.
Tin a gate din farko jikin Anne ta tsananta rawa numfashinta na fita da sauri maqoshinta na bushewa tana Jin kanta na juyawa kaman ciwonta zai tashi Dan kusan duk ta fita Hakan takeji matiqar ba komawa gidan Ababa tayiba.
Daga benazir din har Anne babu Wanda hankalinsa da tinaninsa yake kan aljannar duniyar dasuka shigo sbd kusan babu Wanda yake hayyacinsa cikinsu.
Zeenah ce da wasu baqin suka fito suka tarbi benazir Amnah na hannun Mum Khadija suka karbeta cikin farin ciki sukai ciki suna mantawa da Anne dake mota, benazir Kuma Daman babu Abinda take Ganewa sbd kanta ma Dayake Neman juyewa duk inda Akai da ita can take zuwa.
Anne data kasa fitowa hannuwanta da qafafunta na tsananta rawa Wani busashen yawu ta hadiye daqyar kafin ta Bude baki muryarta na rawa tana kallan Abbakar daya Bude mata motar Yana jiran fitowar ta tace
"Inason zanyi magana da dd babba Dan Allah ka mun iso"
Kallanta Abbakar ya juyo yayi cikin mamaki da tinanin lafiya Kuma bayan anyi musu Abinda suke so an auri 'yarsu.
Kaman zai Bata hakuri akan Hakan sai Kuma dai ya Ciro wayarsa ya kira wayar dd babban ya sanar masa Abinda yake faruwan.
Shi Kansa dd babba shiru yayi Yana nazari sbd baya buqatan ganin kowa yanzu Yana Dan fama da jikinsa da isashiyar lafiya na duk tashe tashen hankalin da akaita shiga a Dan lokacin dakuma auren da aka daura yau Dan haka yace baya buqatan ganin kowa.
Yanda jikin Anne ke rawa tana cikin matsanancin tsoro da ficewan hayyaci ya saka Abbakar cewa ta sanar dashi sakon zai isar mata.
Rawa jikinta ta tsananta ta kallesa tana tattara nutsuwarta ahankali tace zancen yanada mahimmanci sosai dd babban kawai zan iya fadawa gameda gaskiyar haihuwar Benazir ne.
Da sauri Abbakar ya dakatar da ita Yana juyawa koina sbd kada Wani ya jisu yace ta fito ta biyosa.
Kai tsaye palon dd babba ya nufa tana bayansa qafafunta na hadewa cikin tsananin tsoro da fargaba tareda zuciyarta dake hanata Amma bazata iya barin Benazir dinta ta gidan rayuwar aurenta cikin tsoron ranar bayyanar gaskia da Ababa ya ringa juyata kaman babyn roba ba duk da tasan hukuncin Hakan mutuwa ne gareta idan Ababa yaji.
Suna shiga palon Abbakar ya sakawa kofar key ya nuna mata guri ta zauna ya wuce ciki Dan sanar da dd babban.
Zaune take Amma duk sakan zuciyarta dap take da Faso kirjinta ta fado,
Hakama rawar da qafafunta da hannuwanta keyi qaruwa takeyi.
Fitowa dd babba yasakata sauke Kanta qasa Hana Dafe hannuwanta dake qara rawa sosai kirjinta na bugawa.
Zaunawa yayi ahankali cikin nutsuwa Ya dago ya kalleta yana ganin yanda jikinta ke kakkarwa gabaki Daya da alama tana cikin mawuyacin hali na shakkan Abinda zata fada Daya danganci gaskiyar haihuwar data fada.
Shi Kansa zuciyarsa Neman sauya masa tinani takeyi sbd son sanin wace gaskiyar ce take magana Akai.
Daga ita har shi kasa gaisawa sukai da juna ahankali ta Bude baki tafara da fadin Asalin maraicin data taso acikinsa zuciyarta na rawa hawayen Datake riqewa suna cika idanuwanta Amma radadinsu ya hanasu saukowa fuskarta.
Halinda dasuka taso ita da 'yayanta tafara jero masa muryanta na rawa Yana iya Jiyo quncinta da rashin madafarta a muryarta.
Yanda yayanta suka mutu Daya bayan Daya ta fada masa tareda saukowa qasa ta zube gabansa sai alokacin hawayenta masu tsananin zafi suka sauko ta fada masa gaskiyar haihuwar Amnah tareda fashewa da Wani irin Kuka tana rokonsa akan Benazir marainiyar da batada kowa saisu a yanzu ce.
Barazanar da Ababa zai ringa yiwa Benazir da ita ta sanar masa tareda sake fashewa da Wani irin Kuka mara sauti da radadin zuciyar Datake cikin qunci ta rokesa akan Amanar 'yarta benazir.
Tinda dd babba yayi gwagwarmayar rayuwa bai taba ji ko ganin Abinda ya tayar masa da hankali ba kaman abubuwan da yaji daga bakin mahaifiyar benazir ba,
Wace rayuwa take fada tayi itada yayanta kaman dabbobi,
Wane irin Uba ne mahaifi wannan Ababan?
Hankalinsa mummunan tashin dayayi yasaka nasa hannuwan rawa Shima ga Wani sabon tinanin tashin hankalin Daya shigesa akan maganar rasuwar sumayyah da Bilal dasuke dauka shi kadai ya rasu gashi yanzu da ana sanar dashi tareda sumayyah ya gudu,
To Yaya Akai gawa Daya aka Gani a motar,
Meyasa tinda Bilal ya rasu Basu taba ganin drivernsa ba Wanda kusan kullum Yana tareda Bilal din.
Me Hakan ke nufi?
Qaddara ce wanna ko Amanar Benazir ne da Allah yakeson damqa masa a hannuwansa sbd tinda ya karbo aurenta yakejin kaman shine gatanta Dana 'yarta.
Abbakar da Shima duk jarimtarsa Saida ya kasa motsawa daga inda kowannensu yake sbd sarawa Ababa takoina daga kafircinsa gashi a dare Daya Anne ta wargaza masa game dinsa ta shekaru.
Numfashin Dd babba sama sama yake Neman Yi
Da gudu Abbakar ya dauko magani jiki na rawa ya Basa tareda ruwa Yana Dan masa firgita duk da akwai sanyin AC Daya cike palon.
Ajiyar zuciya da numfashi Mara karfi yayita saukewa tsawon lokaci Yana kokarin samun relief na attack dayake kokarin sake samu.
Tsawon mintina kafin ya iya dagowa da idanuwansa dasukai jajir ya Kalli Anne da Abbakar a hankali yace
"Wannan maganar zata tsaya a Nan tsakaninmu kada Wanda ya San gaskiyar ba Benazir ce mahaifiyar babyn Bilal ba sbd zata rasa kaunar data fara samu daga family,
Ni kadai ne nasani Kuma ni kadai zan sani har sai lokacin da nagama bincike akan gaskiyar rasuwar Bilal da sumayyah.....
Kallansa ya Maida akan Anne da ko numfashi Bata iyawa daidai sbd kukan datayi na tsawon shekarun Datake ajiye da maganar rayuwar dasukai da yayanta batada Wanda zata fadawa
Yau ta fada taji Wani nauyi ya ragu a zuciyarta tana fadan Hakan yazama silar samun yancin benazir dinta da 'yarta a cikin Kaantes.
Cikin dauriya da Bata Wani irin radadin da dd babba keji a zuciyarsa game da dukkanin zancen ya sake kallan Anne yace
"Nayi Miki Alqawarin zama gatan benazir Koda auren jikana ko Bada aurensa ba sbd gaskiyar ki da maraicinku gabaki Daya,
Ababa ya rasa benazir har abada bazai sake samun damarta ba matiqar Ina Raye,
Benazir ta Riga ta zama kaantes daga lokacinda na amsa aurenta wa jikana Dan haka kije adduar samun zaman lafiya da mijinta kawai Zaki mata Amma wahalarta ta qare inshallah.
Wasu hawayen da Anne Bata taba yiba masu sanyi ne suka gangaro mata ta kasa magana sai sunkuyar da kanta datayi qasa tana tana tare hawayenta da tafukan hannuwanta zuciyarta na samun sukunin da ko mutuwa tayi yanzu batada damuwa.
Kirjin dd babba dake nauyi da zafi ne yasaka Abbakar Yi Kansa Yana kokarin kamasa
Dd babban ya dakatar dashi Yana cewa
"Ka maidata gida batareda kowa yasan na ganta ba."
Da sauri Abbakar din ya Kalli Anne yace su je.
Hawayen godia kawai Anne ta sakarwa dd babba batareda ta iya magana ba har suka fice.
Bata shiga cikin gidan ba Abbakar ya juya da ita zuwa gida a mota tana hawayen bankwana da Bena dinta da batasan ranar da zasu sake haduwa ba.
Kaman yanda dd babba yace kada kowa yasan sunyi magana dakuma alqawarinsa dayayi mata akan Bena yasa Koda ta dawo zuciyarta na da qwari da sukuni Kai tsaye daki ta shigewarta tana Hana kanta hawayen rashin Bena Amma takasa riqe kanta da fasa kukan yau ta wayi gari yanda tazo ita Daya gidan babu 'yayanta ko Daya a tareda ita.
Abbakar kuwa Yana komawa hankali tashe yadawo gurin dd babba da jikinsa ya rikice gabaki Daya cikin qanqanin lokaci ya sanar dasu dad kaante aka kira likita
Shima Dawood dake gidansa anyi sa'a ya kunna wayarsa lokacin aka sanar dashi dd babban ba lafiya sosai dole ya fito da Kansa ya dauko key din mota ya tuqo da kayan jikinsa na gajeran Nike three quarter da sleeveless hoodie shirt ya nufo kaantes din.
##MAMUH#
#LOVE
#HOTHOT
#DBENA
#BABY MAMAH
#MARRIAGE
#SAFNAH
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
46
Koda DD ya shigo kaantes karfe goma Sha Daya,
Parking yayi ya fito Kai tsaye part din dd babban ya nufa inda kusan kowa na gidan Yana can a Palo suna jiran fitowar likitan Dayake Kansa da nurse Daya.
Yana shigowa dukkaninsu suka dawo da kallansu akansa ya qaraso fuskarsa fresh da alaman ya samu isashen hutun Dayake buqata na hayaniya da hidimar yau.
Kai tsaye gurin ummensa dake kallansa cikin nutsuwa da kulawa ya nufa ya tsaya gefenta tareda Dan zagayota da hannunsa Daya Yana Dan babbugawa ahankali alaman komai zai tafi daidai batareda yayi magana ba.
Zaunawa sukai tsawon wasu mintina suna Jira kafin likitan ya fito ya tabbatar musu da dole zasu tafi da dd babban asibiti Koda awanni ne yayi idan ya dawo daidai sai a dawo dashi gida idan Kuma Basu amince ba ya gayyato sauran likitocin asibitinsu suxo a ringa dubasan a gida.
Kai tsaye dad kaante da DD sukace sun amince din Dan haka babu Bata lokaci Akai Kiran ambulance ta asibitinsu akazo aka dauki dd babban Akai asibiti dashi.
Bayan tafiyar dashi DD kaman hannun ummensa yayi ya kaita har cikin bedroom dinta ya zaunar da ita ya fice yabisu Asibitin a motarsa.
Bayan tafiyarsa fitowa tayi ta nufi dakin Zeenah da benazir da Amnah suke ciki harma da Zeenah din.
Zaune suke Bena na bawa Amnah Madara babu kuzari ko walwala a tareda ita.
Zeenah kuwa tana toilet gurin wanka.
Shigowa ummen tayi tana kallan Amnah tace
"Daman tana Shan Madara ne Benazir?
Ahankali benazir din ta Dan gyada Kai cikin sanyi da nutsuwa tace
"Eh madaran Daman kawai take Sha sbd ba ruwan mamah yaqi zuwa."
Qarasowa gefen gadon Umme tayi cikin damuwa sosai da tausayawa ta zauna tana cewa
"Shine tintina baa fada mana ba da sai ayi wata dabarar da breast milk din zaixo,.Amma gaskia Hakan madaran zallah kawai bazai isheta ba."
Karbanta ummen tayi tana goge mata baki tissue tana Jin tausayin Amnah din na rashin Nono gashi yanzu har anyi kusan sati uku da haihuwa bare ayi wata dabarar.
Fitowan Zeenah daga wanka yasa ummen kallan benazir dake zaune Kai a qasa tace
"Kiyi hakuri ki kwana a Nan din yau gobe zaa gyara Miki naki dakin ne a canja Miki komai kafin a saka ranar tarewan ki idan kin Dan Saba da Nan din Kuma Dawood din sai yaje Zurich ya dawo saiki tare gaba Daya kinji?
Ki sake jikinki inshallah zakiji Dadin zama damu hakama Amnah.
Ahankali hadiye Wani numfashi Mara qarfi ta Dan dago batareda ta iya kallan ummen ba ta gyada Kai tana Bude baki cikin nutsuwa da sanyi tace
"Nagode."
Murmush Mai sanyi itama ummen ta saki cikin mutuwan jikin halinda suketa samun kansu aciki.
Miqewa tayi tareda Kwantar da Amnah din zata fice tana cewa
"Zeenah Kinga ga Amnah Nan da benazir kada ki saki ac da yawa sbd benazir na Bata gama jego ba hakama baby Amnah sanyin zai mata yawa ki kula sosai."
Ficewa tayi tana sake jadaddawa Zeenah wadda taketa cewa to sbd itama tasan bama zata saki ac din sosai ba.
Bayan fitar Umme Zeenah kallan benazir tayi bayan ta gama sauyawa Amnah kaya tayi mata Shirin bacci tace
"Ki Kwantar da ita kema kina buqatan gasa jikinki sbd wannan hidiman dole akwai gajiya."
Benazir da batasan me zata ce ba hakama bazata iya musantawa sai ta Kwantar da Amnah din ta nufi bayan Zeenah datace ta biyota toilet din ta taimaka mata da sabbin abubuwan amfani.
Duk quncin rayuwar dasuka taso aciki da rashin gata da rufin asiri Allah Bai taba saka musu kwadayin rayuwar datafi karfinsu ba hakama sunada nutsuwarsu a duk inda zasu samu kansu shiyasa data shiga bathroom din Mai kama da wata duniyar daban Bata daga hankali ko Damar da kanta ko Jin tana shaawar tsayawa kallan Abinda yake toilet dinba,wankan ma kasawa tayi ta Saida ta jima sosai tana Kukan data rasa Kona meye kafin tayi wankan ta fito sbd idan batayiba ta fito Kila su baa kwanciya a gidan sai anyi wanka ancire datti komai kankantarsa.
Qaton towel din da Zeenah ta Bata shi ta dauro ta fito jikinta rufe da Wani sbd Bata Saba fitowa ahakan ba.
Koda ta fito Zeenah ta rage hasken dakin sosai Wani qamshi da sanyi kadan ne ya gauraye dakin ni'iman qamshi na ratsa kowane numfashi da zaka ja a hancinka.
Kaya ne Zeenah ta nuna mata Riga da wando masu tsayi da kauri sosai da taushi suna qamshi Mai sanyi tace ta saka.
Karba tayi ba musu ta koma toilet ta Sako ta fito sbd bazata iya tsayawa musawa a rayuwar datasan kaman anriga an siyota ne Dan haka batada Wani zabi bayan yin kusan duk Abinda aka umarceta batareda ta tsaya azabtar da kanta ko batawa Wainda take zamansu lokaci.
Tana sakawa Zeenah ta nuna mata inda zata kwanta babu musu tazo ahankali ta kwanta kaman mara lafiya a rakube ta janyo Amnah cikin jikinta tana rintse idanuwanta tana Jin zuciyarta na Neman karyewa da tinanin a wane hali Anne take ciki a wanna Daren da zata kwanta ita Daya babu ko Daya acikin 'yayanta.
Zeenah bata jima ba bacci Mai nutsuwa ya dauketa,
Ita kuwa benazir har kusan karfe Biyun dare bacci Bai ziyarci idanuwanta ba sbd radadin rashin sanin halin da Annenta take ciki.
Amnah ce ta motsa daidai karfe uku Dan haka ta tashi zaune ahankali ta sauko gadon jiki ba qarfi ta hada mata Madara da komai da aka aje musu akan bedside.
Madaran ta Bata ta sauya mata pampas harma da Riga sbd sanyin madaran Daya Dan taba rigar kada sanyi ya shigeta.
Tana gamawa ta Kwantar da ita Takoma itama kaman me tsoron kwanciyar ta kwanta tareda rufe Idanuwanta wannan Karan Bata jima ba baccin ya dauketa sama sama.
Rashin baccin datai da wuri ya saka Zeenah kyaleta dataga tasamu baccin sai qarfe 7 ta tada ita tayi sallah.
Zeenah komawa bacci tayi ita Kuma Amnah tasake bawa Madara tanason mata wanka tana jiran Zeenah ta tashi ta Basu ruwan zafi Dan haka ta zauna kan dadduman datai sallah rungume da Amnah data koma bacci itama.
Tana zaune har qarfe Tara na safe lokacin Zeenah ta tashi ta sauko gadon tana kallan benazir din da mamaki tana shafa wuyanta Dan ya Dan sake tace
"Bena a zaune kikai baccin safen ne?"
Girgiza mata Kai benazir din tana cewa
"Ban koma ba Amnah na bawa Madara"
Toilet Zeenah ta wuce tana cewa
"Duk da hakan ya kamata ace kin koma baccin safe sbd samun Qarin lafiya.
Brush tayo ta fito tana kallan benazir dake jiranta tayiwa Amnah wanka.
Komawa sukai ciki ta Tara mata ruwan zafi Dayake Bata Saba ba a roba suke mata a can gida
Itama Kuma Zeenah din kwata kwata batama San ya akewa babys wanka ba Dan haka dole kusan tare sukaiwa Amnah wanka sbd kasawan da benazir tayi ita Daya anan din.
Duka su Biyun sun gama jiqa kayansu Dan haka Zeenah ce ta fito da Amnah tace Benazir din tafara wankan kawai.
Bata jima ba ta gamo wankan da sabulun Zeenah da qamshinsa ya cika toilet din ta fito ta karbi kayan da Zeenah ta miqa mata na wata dagowan Ashape din embellished English super exclusive purple.
Undies data Bata dasu takasa kalla sbd su Basu Saba da panties irin haka ba gajerun wandina suke sakawa Suma hande idan taje siyowa wasu ma kaman na gwanjo,
hakanan ta saka da sauri kada Wani ya shigo dakin saidai rigar sai takejin kaman ta kamata daga saman tinda Bata Saba saka kaya irin Hakan ba.
Tana gamawa ta zauna ta shirya Amnah wadda tafara Kuka tin tanayi a hankali har tafara Yi sosai duk ta rikita benazir din wadda Daman duk a cikin damuwa da rashin kuzari take.
Umme ce ta shigo bedroom din Jin kukan Amnah din Dayake Neman cika koina.
Shigowar Umme ya saka Benazir sunkuyar da kanta qasa cikin sanyin jiki tana sake rufe kanta da dankwalin kayanta tinda Zeenah bata Bata mayafi ba gashi ita batama San Ina aka Kai nata kayan ba bare ta dauko ciki.
Cikin nutsuwa da girmamawa ta Bude baki a hankali ta gaida Umme.
Amsawa ummen tayi cikin kulawa tana cewa
"Meya faru ne?
Kin Bata madaran kuwa?
Ko kun kwana cikin sanyi Mura ya shigeta ne??
Kasa magana benazir tayi sbd batasan me zata ce ba tinda itama batasan me Amnah din kewa Kuka ba.
Kallanta Umme tayi tace sake hada mata madaran ki kawo mugani.
Ficewa tayi dakin da Amnah tana jijjigawa cikin kulawa da kauna.
Rintse idanuwa Benazir tayi sbd kanta Dayake Neman daukan zafi.
Madaran ta hada ta tsaya dakin ta rasa ina zata dosa sbd Bata Saba wannan free rayuwan dasuke tinanin tayi a gidan ba.
Zeenah ce ta kalleta bayan ta saka doguwan riga mara nauyi tace
"Follow me." Gaba tayi tana latsa wayarta data kunna lokacin benazir ta biyota a baya kaman mara lafiya sbd rashin kuzari da sanyin jiki.
Wani mahaukacin palon Daya gama Jin komai na Jin Dadin da kake buqata a zaman duniya suka fito komai da koina yagama daukan sanyi da qamshin kwanciyar hankali da nutsuwa.
Duk inda ta saka tafin kafarta sanyi ya shigeta sai ta rintse idanuwa ahankali tana qanqame madaran Amnah Dayake hannunta.
Dakin Umme Zeenah ta Isa da ita ta Bude suke shiga Benazir din ta tsaya daga kofa
Zeenah kuwa gurin Ummen ta nufa tana Kiran sunan Amnah dake Kuka har lokacin.
Dagowa Umme tayi ta Kalli benazir din tace
"Qaraso kawo abata mugani idan ba Wani abin yake damunta."
Takowa tayi ahankali ta qaraso ta tsaya daga gefe ta miqawa Zeenah madaran Umme ta amsa tafara Bata cikin sa'a kuwa ta amsa tanasha da sauri.
Gama Bata Akai Umme ta gyara mata jikinta da kanta ta Kwantar da ita take tayi bacci tana sauke ajiyar zuciya ahankali.
Kusan dukkaninsu ajiyar zuciya suka saukar Suma kafin benazir ta silale ta fito ta Maida kanta dakin Zeenah ta zauna qasa a darare zuciyarta ba Dadi Dan batasan Tayaya zatai rayuwa a Nan dinba Kuma,
Duk da alqawarin data daukanwa Anne na zata Kwantar da hankalinta tayi rayuwa me nutsuwa to Amma ta Ina? Tayaya?.
#MAMUH#
#DBENA
#MARRIAGE
#ROMANCE
#BABY MAMAH
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
47
Neman Nisa takeyi cikin tinani da damuwa Akai knocking kofar kafin aka Bude aka shigo.
Masu aiki ne guda biyu suka shigo a tare kowannensu dauke da fararen trays masu kyau dauke da breakfast dinta.
Cikin girmamawa Mai tsananin gaske sukai qasa da kansu suka gaidata.
Shiru tayi Bata dago ba sbd batasan da ita suke ba Dan haka Bata dagoba itama kaman yanda Suma Basu dagoba suka sake gaidata wannan Karan suna Dan dagowa.
Zeenah ce data shigo ta amsa musu tana cewa su Daya a cikinsu yaje ya kawo mata lemon zata ci abinci dashi.
Dayar ce ta fara Jere abincin a gaban Benazir da sai alokacin ta Dan dago ta Gane tin farko da ita suke.
Sake gaidata sukai ta amsa tana Maida musu da gaisuwa itama a sanyaye.
Ana kawowa Zeenah Abinda tace suka fice ta zauna tana kallan benazir data kasa kallan kayan da aka Jere a gabanta qamshinsu na cika hancinta zuwa cikinta.
Chips ne da ketchup da scotch eggs se pepper soup na Kazan da aka cirewa qashi dakuma tea mara Madara me qamshi da zafi sosai.
Bata dauka ita aka kawowa wannan abincin ba saida Zeenah ta sakata cinsa tareda Tayata zuba komai cikin wasu irin plates da suka saka benazir din hankalinta na Neman tashi da wannan rayuwar data samu kanta aciki alhalin mahaifiyarta na can cikin zafaffiyar rayuwa.
Duk yanda Zeenah taso Benazir ta sake taci abincin Bata iya cinsa sosai ba sbd ba cimarta bane irin wannan abincin Dan haka sama sama taci komai taji ya isheta.
Tattara kayan Akai aka fice dasu Mai Aiki ta shigo ta sake gyara dakin ta Kuna humidifier ta fice.
Umme da Zeenah ma shiryawa sukai suka fice zuwa Asibiti dubo dd babba.
Ita kadai aka bari sai Amnah da masu aiki.
Da Rana ma haka masu aiki suka kawo mata abinci aka jera mata
Daqyar ta iya cin kadan tace ta koshi suka dawo suka kwashe.
Kaman mara lafiya haka ta wuni a daki jigum tana renon Amnah duk a sanyaye ba kuzari.
Sai magrib suka dawo har lokacin tana daki zaune ba motsin kirki.
Shigewa sukai kowa yayi wanka suka Dan huta kafin suka fito cin abinci wannan Karan haka aka sakata fitowa zuwa dining Wanda har Akai aka gama Bata iya Sakin jiki ta zauna ko daidaiba bare iya cin abinci a cikinsu.
Dole aka maidata daki aka Kai mata Wani abincin acan Shima Bata iya ci ba saida Umme da kanta ta shigo tace taci.
Yau dinma hakuri Umme ta Bata akan su sake kwana dakin Zeenah kafin gobe.
Wanka sukai kaman yanda Zeenah ta sakata ta shirya ta shirya Amnah suka kwanta.
Yau ma kaman jiya sai kusan hudu ta samu bacci ya Dan dauketa.
Washe garin ranar tana daki masu aiki suka zo aka cire tsadaddin furnitures na dakin dake maqale Dana Zeenah da basuyi komaiba aka saka komai sabo a dakin tareda tsarin abubuwan dakin babys.
Me Aiki aka kawo ranar sabuwa wadda hidiman laluran benazir da Amnah ne kawai aikinta da haka ita aka saka ta Jere kayan lefen Benazir tsaf a closet hakama tarin kayan da aka siyawa Amnah duk ta Jere komai
Duk da babu inda yakeda Wani Abu me suna datti ko qura a dakin Amma Saida Nafisat me aikin ta tsaftace koina ta wanke toilet din da a ranar Shima aka zuba mata toiletries da komai na buqatanta Dana Amnah.
Ac aka kunna tareda qamshin masu Dadi Zeenah ta kawota dakin ta fice sbd wayan da zatayi.
Tinda ta baro gidansu babu Abinda ta dago tayiwa kallan ko sakan uku bare kallan tsaf sai dakin.
Turkish Royal bed ne da set dinsa na komai tareda Wani mahaukacin Katan mirror Daya ci kusan Rabin bangon gefe Daya.
Komai na dakin Ashe ne da fari aka saka sai daukan Idon nuna kudin Dayake cikin siyansa,
A gefen makeken gadon daga qurya gadon Amnah ne fari Mai kyau da tsadan gske Shima hakama da kayan qasan baby a jikinsa,.
Ko beddings dake shimfide a gadon fari ne hakama pillows Akai kusan guda 8 dasuka sakata sauke ajiyar zuciya ahankali jikinta na mutuwa sosai.
Carpet da table dasu stools harma da sauran kayan dakin kusan tsoro suka Bata saidai batada mafita ko tudun dafawa a wannan rayuwar data tsinci kanta aciki Dan haka ta Tako ahankali ta Kwantar da Amnah ta nufi inda take tinanin toilet ne ta shiga Nan Wani firgicin Yakuma cikata ta ringa saukar da hawaye masu zafin tonowa da Annenta tinanin anan ake nufin zatayi rayuwa Annenta na can cikin halin qaqanikayi.
Sosai tayi Kuka jikinta na sake mutuwa kafin tayo alwala ta fito ta tayarda sallah.
Tana idarwa taga har lokacin Amnah na bacci Dan haka ta koma toilet tayo wanka sbd tinanin al'adar da Dokan gidan ne wanka kafin kwanciya musamman ganin wannan gadan tasan bama zai yiyu ta hau musu gadon ba.
Tana fitowa ta dauko kaya inda Zeenah tace mata ta ringa daukowa ta saka doguwar Rigar jallabiya sbd a kwana Biyun datai dakin Zeenah cikin mawuyacin hali tayi su sbd kayan datake Bata tana sakawa Riga da wando.
Tana gama shiryawa Zeenah ta shigo ta zauna tana Tayata bawa Amnah data farka Madara.
Bayan sun gama Zeenah anan ta kwanta Saida Amnah tayi bacci kafin ta fice musu bayan ta nunawa benazir inda zata Kuna wutar dakin da kashewa kokuma rage hasken.
Zeenah ce ta sakata Hawa gadon kafin ta fice Dan haka tinda ta hau take shiru kaman wadda tayi bacci Amma zuciyarta cike take da tinanin inda ta samu kanta a yanzu.
Baby Amnah kaman tasan sunyi dakin kansu ranar bacci tayi sosai har safe ko madaran Bata farka ta Sha ba.
Suna yin sallar Asuba benazir ta gyara gadan ta sauko da Amnah suka zauna kan tattausan carpet din dake gefen gadon suna gyangyadi.
A gurin bacci ya sake dauketa sai kusan karfe Tara Nafisat ta shigo tafara kokarin gyara dakin ita Kuma benazir tayi toilet da Amnah Dan Yi mata wanka.
Yau ma a jiqe suka gama wankan ta kawota daki ta Kwantar Takoma itama tayo ta fito suka shirya suka zauna jiran tsammani kaman kullum.
Breakfast din na yau a dining aka kirawota a dosane tayisa cikin tsoro da rashin kwanciyar hankali.
Suna gamawa ta silale Takoma daki sukuma suka sake ficewa zuwa Asibiti sbd dd babba da zaa wuce dashi Zurich yaga likitan DD.
Dayake tafiyan tareda Dawood din harma da dad kaante zaayi sai Basu Wani tsaya Bata time ba cikin kwanaki 10 aka gama komai suka wuce Kuma tin ranar da aka tafi da dd babba asibiti Dawood Bai dawo kaantes ba sbd kullum a Asibiti yake haduwa da ummensa harma da dad kaante.
******Bayan tafiyarsu dd babba Umme ta samu nutsuwan dawo da hankalinta da kulawanta kan benazir data fara sabo da zaman daki da rayuwar kadaici data sake samun rayuwarta aciki duk da Zeenah na iya kokarinta gurin ganin tana debe mata kewa da Bata kulawa tareda nuna mata wasu abubuwan.
Wata sabuwar meyiwa Amnah wanka aka dauko dattijuwa wadda ita Kuma aikinta kawai na yiwa Amnah wanka ne sbd mura data fara shigarta na ruwan wanka da kullum saita shaqa sbd benazir Bata iya mata wanka toilet.
A jiki Umme tafara Jan benazir sbd lura da akwai tsoron mutane da rashin sabo da mutane sosai a tattare da Bena din,
Mum Khadija ma da bata cika son mutane ba tana 'dan kaunar Bena din sbd fahimtar zatayi biyayya makan baiwa ita Kuma Daman tanasan Wanda zai Basu girma da biyayya ya nuna su dinne a sama.
Zaman daki da qarfi da yaji Umme da Zeenah suke Hana Bena kullum indai zasu fito sai ankirata ta fito.
A dosane take zama cikinsu Bata iya magana idan ba tambayarta ummen tayiba ko Zeenah.
Ahankali mura Mai qarfi ta shigeta ita da Amnah sbd sanyi da wankan Datake musu so biyu kullum tinda tazo sbd tsoron shafawa Wani Abu ko gidan datti ganin masu gidan da gidan kaman saika wanke hannu zaka taba su.
Boye zazzabinta Mai tsananin karfi tayi ta danne Bata bari ansaniba tinda haka Suka Saba gida,
Na Amnah ne yakasa dannuwa sbd rigimar Datakeyi ba sassauci.,
Ta Dena baccin dare sbd ciwon Amnah ga nata ciwon ga rigimar Amnah ga kadaici ga damuwar mahaifiyarta sai kawai tafara Neman zauncewa ciwo ya Kwantar da ita gadan gadan harda Kuma Qarin sauyin cima da muhalli.
Hankali tashe aka kirawo likita har gida yazo ya dubata aka duba Amnah itama.
Wannan ciwon da sukai ya saka jikinta yin sanyi sbd kauna me tsananin dataga Umme nayi mata itada Amnah sai Hakan ya taba zuciyarta akan yaudarar ummen takeyi a matsayin wadda Bilal dinta ke tsananin so.
Wannan tinanin ya sanyayar da zuciyarta daga bushewan da tayi batajin kowane feeling a gidan da mutanen gidan.
Idan zatayiwa Umme adalci Bata cancanta wannan yaudarar da ake mata ba Amma Kuma itama Batada zabi sbd ba itace ta zabarwa kanta wannan rayuwar ba.
A haka dole ta fara sakewa dasu Dan faranta ran Umme Dan Zeenah dasuke nuna mata asalin kauna da kulawa.
Da farko kokarin cin cimar da duk aka Bata tafara tareda daurewa tana cin abincin taredasu a dining kowane lokaci.
Hakama takan daure da kanta ta fito Koda dakin Zeenah ne taje,
Kullum da safe da kanta take zuwa dakin Umme ya gaisheta ta dena Jira sai an Aiko kiranta ta fito.
Hakan data fara ba qaramin faranta ran Umme yafara ba Dan haka suka sake dagewa sosai gurin kulawa da benazir din.
*****dd babba ya samu sauki sosai Amma Dawood ya hanasa dawowa sai ya huta daga tashe tashen hankalin da akaita samu a baya Dan haka sukai zamansu sbd shi Dawood din yanada abubuwan da zaiyi a qasar Kuma ahakan yaqi barin ko so Daya Safnah ta gansa Kuma data kira yace Bai aminta ta samesa ba ta zauna inda take zai nemeta da Kansa.
Wata daya suka share harda sati uku kafin suka fara Shirin dawowa shi dad kaante Daman tini ya dawowarsa yabarsu acan.
*****Acikin wannan watan da satikan rayuwar Benazir a Kaantes ta fara amsa Wani sunan da matsayi na sauyi data fara samu,
Dukiya gaskia ce,hakama rayuwar hutu da daula gaskia ce,
Benazir ta fara samun sauyi na rayuwa Dana fata,
Skin dinta brown ne lafiyayye tin asali,
Su ba maabota yawo bane kullum sune kulle cikin kejin gidansu ahakan suka taso suka girma,
Fara jamiar su kullum jikinsu a rufe yake sbd rashin sitarar arzki da Horan da suka samu
Dan haka fatarta na fara samun hutun kaantes da tsadaddiyar luxury rayuwar da ake Bata yasaka sauyinta fara bayyana a kankanin lokacin.
Cikowar jiki Kuma Daman ita din bamai jikin qiba bace Dan haka bata sauya ba tanan siririyarta Saidai murmurewan data samu.
Umme ta Siya mata waya itada Annenta aka aika mata driver yakai mata Dan haka tana magana da ita idan Ababa Yana gida ya Bata wayar tayi tagama a miqo masa ya aje.
Shima shirun da yayi ya daga qafa ne sbd sanin dd babba da Dawood din Basa qasar shiyasa yayi shiru sai sun dawo an nitsa yafara sanin matsayarsa.
******Qarfe uku na yamma jirginsu ya sauka Abbakar ne yaje daukosu
Shikuma DD Naseer ne yaje ya daukosa daga airport gidansa Kai tsaye ya wuce saiya huta zaizo kaantes din.
Yana Isa wanka yayi yayi sallah baya buqatan cin komai sai ya huta tukuna Dan haka kwantawa yayi baccin yamma sai 5 da Rabi ya tashi yasake Yin wanka ya fito Kai tsaye yayi kaantes.
Koda ya Isa zaayi sallan magrib Dan haka tareda dd babba suka shiga sallar suna gamawa ya fito Abbakar na biye dashi Yana sake masa barka da dawowa suka nufo ciko.
Sashen ummensa ya nufa Kai tsaye Shima Abbakar ya koma.
Zaune suke a Palo dukkaninsu daga ummen har Zeenah da benazir dake gefen Zeenah suna bawa Amnah Madara a tare yauma rigimar takeyi.
Qamshinsa yayiwa palon dip Dan haka a tare Umme da Zeenah suka dago kallan kofar daidai shigowansa
Sanye da black Balmain three quarter jean da hoodie sweatshirt hasken qafafunsa dake bayyane na daukan idanuwansu kaman koyaushe fatarsa kaman ta sabon baby sbd hutu da luxury rayuwar daya taso aciki yake aciki.
0 comments:
Post a Comment