Me Adda yace "ba maganar banza bace, roofing kwano suka buɗe suka gudu"
"Roofing kwanon ne ba kuyi da kyauba kokuwa?"
"wallahi munyi komai yadda yakamata, ni babban abunda ya bani mamaki be wuce yadda ko iya miƙewa tsaye ba sayi saboda wahala, amma suka iya tserewa, ni yanz....
Alhaji Musa ya katse shi ta hanyar cewa " kaga dalla rufemin baki, na yadda da ƙarewarka a wannan fannin shiyasa na baka aikin nan, amma ka kunyatani, shekara nawa kayi kana aikata irin wannan Aikin? Miyagun ayyuka mawa ka aikata kana Nasara, amma se yanzu wannan ɗan ƙaramin aikin ka bari har suka gudu saboda hauka, wallahi tun wuri ka nemo su na gaya maka"
Ya ajiye wayar tare da yin jifa da ita yana dafe kai, jinjina kai yayi yace "Akwai babbar matsala"
Ramlah ce kwance akan gadon Hotel, se bacci take yi kamar matacciya, ta lulluɓe jikinta da blanket, Fahad na gefenta yana ta busa shisha.
Seda yasha me isarsa sannan ya duba agogon hannunsa, ya miƙe zaune dagashi se gajeren wando, yaye blanket ɗin da Ramlah ke ciki yayi ya ɗagota zaune, ko sutura babu a jikinta, busa mata hayaƙi yayi a fuska, a hankali ta motsa ta fara tari, buɗe idanunta tayi wanda sukayi mata matuƙar nauyi ta kalle shi.
Fahad yayi wani murmushi irin na 'yan bariki yace "baccin ya isa haka, yakamata mu koma gida, kafin yaynki ya fara masifa"
Miƙa tayi ta sake kwanciya a jikinsa tace "ƙarfe nawa ne?"
"Ƙarfe takwas na safe" ya bata amsa, ba shiri ta watsakke tare da zaro ido tace
"takwas na safe, na shiga uku Fahad, wacw irin ƙwaya ka bani haka? Me zan cewa Mummy?"
Murmushi yayi yace "matsoraciya kawai, ashe iskancin naki na ƙarya ne, karki damu baby zance mata a gidanmu kika kwana kawai"
Tayi ajiyar zuciya tace "kuma kasan Mummy tana yarda da maganar ka sosai, har naji daɗi wallahi I love you Fahad"
"Love you too baby"
"Fahad tunda Widad ta ɓata zaka Aureni?"
Ya sake rungumeta yace "idan ban Aureki ba wa zan aura? Itama na yadda da Aurenta ne dan in Aureta in Wulaƙanta ta, Allah ya temake ta wannan abu ya faru, amma a duniya in bake ba wace macece ta dace da Fahad?"
Murmushi tayi tama jin daɗin kalamansa ma yaudara suna ratsa ta.
Saleh ya kamo hannun Yusuf suka fito waje, Saleh yace
" Samun mutum managarci me Amana kamarka abune me matuƙar wahala Yusuf, ka cika mutum nagari abun a jinjina masa, iyakar sadaukarwa kayi ta, ina fatan wannan Auren anyi shi kenan har gaban Abada, duk macen da ta auri namiji irinka yakamata ta gode Allah, nasan kayi haƙuri a baya dan haka ina fatan ka ƙara haƙuri, Widad yarinya ce me tsiwa da girman kai amma zakaji daɗin zama da ita, saboda tana sa sauƙin kai ga wanda ya gane kanta, dan wani lokacin gane kanta se a hankali, nasan zata baka wahala kafin ta saba da zaman garin nan, amma kayi haƙuri a hankali zata saba, babu wanda ta sani a yanzu daga Allah se kai, ka riƙe Amana Yusuf babu tabbacin ku koma gida Widad ta tarar da mahaifinta a raye! "
Wata irin mummunar faɗuwar gaba Yusuf yaji, yace " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, me kake Nufi? "
"tunda kuka ɓata Daula yake gadon Asibiti, kullum zancensa 'ya' yana wani hali suke ciki? An ɗaga taron da suke burin ayi suyi amfani da sunan Daula su damfari biliyoyin kuɗi, yanzu idan suka farga kun gudu akwai gagarumar matsala, maganar da nake maka matarsa ba ita take jinyarsa ba, tana can tana shagalinta, babban ɗanta Anwar shike ta sintirin jinyarsa, sannan an bawa likitansa maƙudan kuɗi sunce yayi duk me yuwuwa kar Daula ya warke, Nayi duk ƙoƙarin da zanyi a rabashi da Asibitin amma ba hali, muddin nayi wani babban yunƙuri komai ze lalace "
Yusuf ya dafe kai ya shiga jera salati,
"Rananar da'aka ɗaukeku ni naje na janye Motar da kuke ciki daga titi na maida ita, aka cire lamabr motar, shiyasa na samu wayoyinku da kuma wannan Akwatunan naku, amma bazan baku wayoyin ba, dan nasan tabbas za'a iya tracking ɗin inda kuke, zan kawo maka ƙaramar waya da sim wadda zamu dinga communicating da kai, mahaifiyarka na gaisheka tana ta samaka Albarka "
Yusuf kasa magana yayi se zuciyarsa daketa faman tafasa, suka nufi turakar megari Saleh yace " Baffa zan koma yau, na bawa ila kuɗi da kayan aiki, zezo yayi musu banɗaki, wallahi nan da kwana uku idan beyi ba, yasan halina, na bashi isassun kuɗi wallahi na dawo beyi ba koya cinye kuɗin sena karya shi, kaja masa kunne"
Megari yace
"Subhanallah zeyima Insha Allah, ɗakin nan da bakomai shi za'a gyara ba wani abu, ai kaine ka sashi zeyi insha Allah"
Saleh yayiwa Megari sallama, Yusuf ya ɗanyiwa Saleh rakiya sannan ya koma.
Gaba ɗaya kamar an zarewa Yusuf laka jin maganganun da Saleh ya gaya masa, ji yake tamkar mahaifinsa ne a wannan haɗarin, wani irin tausayin Widad ya kama shi.
Ya shiga gidan yana takawa da ƙyar, gwaggo ce tace "Malam Yusufa Allah ya Sanya Alkhairi ya baku zaman lafiya, yasa anyi kenan kasan lamarin Aure se anyi haƙuri Allah ya baku zaman lafiya"
Yusuf ya ƙaƙaro murmushi yace "Ameen ya Allah nagode sosai"
Gwaggo tace "sedai akwai ɗan bikin Al'ada da mukeyi anan in akayi Aure, yakamata mu gayyaci mutane mu ɗanyi mu tayaku murna"
Yusuf yace "Allah sarki Mama, base kin wahal da kanki ba, kinga ita Amaryar ma bata cikakkiyar lafiya kuma har yanzu a tsorace take, baki ga ko magana bata sonyi ba, Addu'ar ku da kulawar da kuke bamuma mungode sosai"
Gwaggo tace "shikenan Allah ya bata lafiya"
Yusuf yace "Ameen"
Jiki babu ƙwari ya ƙarasa ɗakin nasu, kayan ɗaurin Auren suna nan a inda suke, da kuɗin sadakin nata, tana zaune ta haɗe kai da gwiwa se rusar uban kuka take.
Dole Widad tayi kuka, rayuwar ta cike take da ƙaddara daban daban, a hankali ya ƙaraso bakin katifar ya zauna, sam bataji zuwansa ba seji tayi ya taɓa ta, a ɗan razane ta ɗago ta kalleshi, ganin Yusuf ne yasa ta maida kanta kan gwiwarta ta cigaba da kukanta.
Yusuf yasa hannu ya ɗagota yana kallon yadda farar fatarta ta koma ja saboda kuka da wahala.
Girgiza mata kai yayi amma yakasa ce mata komai, dan bema san ta'ina ze fara ba, Widad ta cancanci tayi kuka.
A hankali tasa hannu ta ture nasa hannun ta kwanta, tare da ɗora hannunta akan fuskarta tana ci gaba da kukan, A hankali take furta
"Ya Allah, aslihli sha'ani kullahu, wala takilni ila Nafsi, ɗarfatu ainun"
(wuya koda magani ba daɗi, ashe Widad ta iya Addu'a haka 🙄)
Yusuf ya zauna ya zuba mata ido wai a hakama bata san halin da mahaifinta ke cikiba kenan, inaga inta sani.
Yarone yayi Sallama ɗakinsu Yusuf, Yusuf ya amsa, yaron yace "Wai gashi inji gwaggo"
Yusuf ya karɓi ƙwaryar da'aka rufeya da faifai, yace "Masha Allah, kace mata mungode"
Yaron yace to ya fita, Yusuf ya ajiye Ƙwaryar yayi shiru yana kallon Widad da jikinta har rawa yake saboda tsabar kuka.
Yusuf yayi shiru, abubuwa suka cinkushe masa kai, nan da nan kansa ya fara sarawa, ya jingina da jikin bango ya rasa abunda yake masa daɗi.
A hankali Widad ta buɗe idonta, ta kalli inda Yusuf ke zaune yayi shiru, jijiyoyin kansa duk sun tashi, ga idonsa yayi ja kallo ɗaya zaka masa kasan a cikin damuwa yake.
Ta miƙe zaune a hankali, yai saurin juyowa yana kallonta, ta goge hawayenta tace
"me'aka kawo? Yunwa nakeji"
Yusuf yace "ban san me'aka kawo ba bari im duba"
Ya ɗakko ƙwaryar ya duba, fura da Nono ne aka dama, tace "bani cokali a can gurin"
Ya duba ya ɗakko mata, ya bata. Sosai take jin yunwa ta ɗiba ta kai bakinta, ajiye cokalin tayi a gefe ta kafa kai ta dinga sha, tasha ya kai rabi sannan ta ajiye, ta koma gefe ta zauna tana lumshe ido.
Yusuf yace "kin ƙoshi ne?" ta jinjina masa kai ba tare da ta buɗe idonta ba, yasa hannu ya ɗau wadda ta rage ya fara sha, an zuba zuma a cikin furar shiyasa tasha da yawa.
Gaba ɗaya Yusuf tausayi yake bata, beji ba be gani ba ƙaddara ta haɗasj se wahala suke sha tare, duk abunda za'a kawo na Abinci indai zata iya ci, se taci ta rage sannan zeci, kuma seya tabattar ta ƙoshi sannan ko yaya ta rage shima yaci.
Kallonsa take yadda ya duƙa yana shan furar, wadda ba isarsa za tayi ba, ta lura shidai a rayuwarsa be ɗau komai da zafi ba, irin mutanen nan ne da duk yadda rayuwa tazo zasu karɓeta a haka.
Yusuf ji yayi kamar tana kallonsa, ya ɗago kai ba tayi zato ba suka haɗa ido, tao saurin ɗauke nata idon.
Jiki a sanyaye yace "har yanzu dai kukan baki dena ba? Yakamata ace zuwa yanzu kin sawa zuciyarki haƙuri, kukan nan bashi da amfani, kina ƙaramin damuwa akan wadda nake ciki ne"
"Ni nace ka damu dani ne? Don't try to comfort me when ever am crying, kaji da damuwarka kaima"
Yusuf yace "tun daga lokacin da kika fara kuka saboda damuwa zuwa yanzu, maganin me kuka yayi miki? Kuka baya maganin damuwa wasu lokutan sema dai ya ƙara maka ƙuncin zuciya, ina tare da ke a guri ɗaya ta yaya zan zuba miki ido kiyi ta kuka, kina wahalar da kanki da yawa "
" kowa yaji da kansa malam ka dena damun kanka akaina"
Yusuf yace "Ai bazan iya bane, in dai kina kuka nikuma zuciyata rauni take"
Tsaki tayi tace "Se kai tayi ai"
Yusuf murmushi yayi bece komai ba.
Can tace "yanzu kaga death contract ɗin da nake gaya maka muddin zakayi aiki dani ko? Meyasa baka yi tunani akai ba kasa hannu, dukda na gaya maka haka? "
Yusuf yace "saboda shi bawa baya taɓa tsallake ƙaddararsa, Allah ya ƙaddara se haka ta faru"
Shiru tayi ta shiga duniyar tunani, tana cikin tunanin ne bacci ya kwasheta daga nan inda take zaune, ta lanƙwashe wuyanta.
Yusuf ya miƙe yaje da nufin ya gyara mata kwanciya saboda wuyanta, ashe baccin nata ba nisa yayi ba, ta buɗe idonta ta kalle shi, haɗe rai tayi tace "meye haka?"
"yi haƙuri, gani nai kin lanƙwasa wuyanki, kar yayi miki ciwo kuma bana son in tasheki"
"to ina ruwanka inma yayi min ciwon? Dalla cikani kuma karka ƙara taɓani na gaya maka"
(Nikam nace Mamaki 😂 jimin mara kunya, sekace yau aka fara)
Murmushi yayi yace "shikenan Allah ya huci zuciyarki"
Ta kwanta tareda juya masa baya, Yusuf ya ƙura mata ido tare da yin murmushi a ransa yace 'insha Allah sena maye gurbin wannan damuwar taki da farinciki'
Yusuf ji yake kamar bashi ba, wai shine ya Auri Widad, yasan badan ƙaddara ta Ubangiji ba, kamar shi a yadda yake ya Auri mace irin Widad kyakkyawa 'yar me kuɗi haka, sedai wani iko na ubangiji.
Haka nan yake fatan Allah yasa su kasance tare har Abada, Allah yasa idan ta gano waye shi karta guje shi.
Misalin ƙarfe biyu da rabi na dare, Nurat taji motsi a harabar gidansu, ta leƙa ta taga ta hango mahaifinta ya fita shida direbansa, tunani ta shiga yi ina mahaifinta zeje a wannan daren haka? Tashi tayi ta tafi ɗakinsa, ta murɗa ƙofar a hankali ta shiga, ƙarƙashin gadonsa taje ta ɗakko wayarta da ta ajiye ta kunna recording.
Tayi saving ta fito daga ɗakin ta koma nata ɗakin, anan taji wayar da yayi da batun kuɓutar su Widad, da sauri ta miƙe tsaye tana Alhamdilillah, ta dinga kunna recording ɗin tana sake saurara, hankalinta ya koma son sanin me zasu tattauna a meeting ɗin da zasuyi a wannan tsakiyar dare kamar wasu matsafa.
Babban falon Hotel ne suke zaune, sunyi jugum jugum kamar masu jiran tsammani kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin damuwa.
Alhaji Haruna yace "jama'a ayi magana, abubuwa da sun taho kamar abun arziki, amma yanzu komai taɓarɓarwa yake, ta yaya za'ace sun gudu se kace a film, ko wata tatsuniya.
Alhaji Munir yace "nima abun ya ɗauremin kai, ga kuma wannan samu da rashi da muka gani, muna shirya abu amma wai an fasa taron, wannan shegun turawan ne suka ce a ɗaga, na rasa wani baƙin munafukin ne ya gaya musu ba, nifa kaina gaba ɗaya ya kulle"
Alhaji Musa yace "babu yadda za'ayi ace su kasa jim rashin lafiyarsa ko kun manta shahararsa ne? Dole zasuji ai"
Wayar hannun Alhaji Musace ta fara ringing, ya fito da ita ya ɗaga .
"ban samu halartar zaman da kuke a daren yauba, hakanma duk yana cikin shirina ne, yakamata ku maida hankali gurin gane cewar wani yana muku zagon ƙasa, akwai na jikinku wanda yasan siriinku shine yake ta dagula muku lissafi, ku maida hankali gurin gano waye, sannan kusam duk yadda zakuyi ku kama wanda sukayi garkuwa da 'yar gidan Daula ku kashe su, in bahaka ba akwai gagarumar matsala, sannan ko a mace ko a raye ku tabattar an kama yaran nan an kashesu" yana gama maganar ya kashe wayarsa.
Nan fa suka sake shiga wani ruɗanin, tabbas inba wanda yake cikinsu ba babu ta yadda za' ayi Su Widad su iya tsira daga inda aka ɓoyesu.
Alhaji Haruna yace "to kun daiji abunda Alhaji Bukar yace, yanzu abunda za'ayi shine, kusa a binciko mana wanda aka bawa bincike hukumar jam'ian tsaro, ayi karɓo mana sakamakon binciken, hakan ze ƙara haska mana wani abun"
Alhaji Munir yace "wannan kuma aikin Saleh ne, shi'aka ɗorawa wannan ragamar"
Alhaji Musa yace "Na kira shi sam labarsa bata shiga, inaga zan tura ɗan aike a kiramin shi da safe"
Haka suka gama tattaunawa suka tashi ba tare da cimma wata ƙwaƙwarar matsaya ba.
Da safe Hajiya Halima nata safa da marwa, layin Ramlah sam baya shiga, ƙarfe goma na safe sega Ramlah ta dawo, Hajiya Halima tace "daga ina kike?"
Kafin tayi magana Fahad ya shigo, Yace 'Mummy barka da safiya, mun miki laifi ko? Wallahi bayan mun dawo daga cinema ne naga kwana biyu ba taje gidanmu ba, kawai muka zarce can, daga nan kuma mumsy tace seta kwana tunda bata zumunci "
Hajiya Halima tace " Aida ta kira ta gayamin, hankalina ya tashi ince kaddai kuma an sace mana ku"
Ramlah tace "haba Mummy wani irin sacewa kuma, ai an san wanda ake sata, ina tare da Fahad waye yavisa ya saceni"
Sukayi dariya gaba ɗaya, Fahad ya kashe mata ido, sukayi Sallama ya tafi.
Ramlah na zuwa ɗakinta ta jefar da jakarta ta kife akan gado ta cigaba da bacci, saboda har yanzu ƙwayar da ta sha bata saketa ba, kuma ga rashin sabo dama, dan bata taɓa shan kayan maye ba.
Yusuf bayan ya dawo daga sallar Asuba, har ya kwanta ya tashi, ya duba shimfiɗar Widad yaga bata nan, zumbur ya miƙe zaune a gigice yana waige waige, miƙewa yayi ya fito tsakar gidan bakowa, saboda yanayin garin da sanyi kuma gari be gama waye ba, leƙe leƙe ya shiga yi yana nemanta, can ya hangota daga wani ɗan lungu tana tsaye tana leƙa wata taga se murmushi take, hannunta riƙe da brush da toothpaste, kan nan ko ɗan kwali babu, gashinta ko taza babu ta naɗeshi da ribbon ya kwanta a bayanta.
A hankali ya ƙarasa inda take cike da son sanin me takewa wannan murmushi haka?
Jin mutum tayi a tsaye a bayanta, ta juyo a ɗan razane, Yusuf ta gani a tsaye a daf da ita.
"meye haka?"
Yusuf yace "gani nayi kina tsaye kina murmushi, shiyasa nace bari inga abunda ya saki nishaɗi haka? Sannan gari akwai sanyi fa, kalli kanki babu ɗan kwali kar mura ta kamaki, sannan kayan jikinki maza na shiga na fita a gidan nan, kar gari yayi haske suzo su sameki a haka, su kansu matan gidan zasu ga hakan wani iri saboda ya saɓawa Al'adunsu"
"Wai kai meyasa ka fiye shishshigi da takura ne?"
"ba shishshigi da takura bane, kinga yanzu kina da Aure fa"
"kaga wannan Auren fa dashi da babu duk ɗaya, karka ƙara sawa ranka wani Aure mukayi"
Yusuf ya ɗanyi murmushi, cike da basar da zancen yace "kin tsorata nifa, harna kwanta na duba ban ganki ba, shiru shiru kuma naga baki shigo ɗaki ba"
"hmm kayi zaton zan gudune? In gudu inje ina? Ko kana zaton zan gudu da wannan Auren naka a kaina? Idan kaga na gudu ko na bar ƙauyen nan to tabbas ka sakeni ne"
Yusuf yace "idan kuma ban sake kin bafa?"
Juyowa tayi ta saka idonta a nasa tace "me kace?"
Girgiza mata kai yayi alamar bakomai, ta harareshi tace "ban guri in wuce"
Seda ta tafi ya Leƙa me take kallo, ɗakin zomaye ne, an kunna musu aci balbal an rataye ta, se guje guje suke suna haƙa ƙasa, da wasanninsu shine abunda yasa ta nishaɗi ta tsaya take kallonsu.
Yusuf ya koma ya kwanta bacci ya ɗauke shi, ita kuwa Widad data gama brush ɗin komawa tayi ta cigaba da kallon zomaye, seda ta gaji sannan ta koma ɗaki.
Yusuf yayi juyi ya buɗe idonsa a hankali, ya sauke su akan Widad, ta gyara shimfiɗarta sa kanta, ta sauke Akwatunanta tana ta gyara kayan ciki, ta ware masu datti ta tattare Akwatunan ta canza musu guri, duk Yusuf yana kallonta, Widas sam bata son ƙazanta, tana da matuƙar son tsafta a rayuwarta.
Yusuf ya tashi ya kwashe kayan shimfiɗarasa ya ninke, bata kula shi ba sabgoginta kawai take, Yusuf yayi mamakin danganar da Widad tayi, dukda har yanzu bata saba da abubuwa da yawa ba.
"wai babu inda za'a samu inji wanki ne? Ina son a wanke min wannan kayan ne"
Yusuf yace "Ai baki da wani injin wankin daya wuceni, in kin haɗa se in ɗiba inje in wanko su"
Widad tace "kaine zaka wankemin kayan?"
Yusuf yace "eh mana, ko kinga alamar injin wanki a garin nan, tunda muka zo kin taɓa ganin wuta?"
"to gasu nan na haɗa, kaje kace a bani ruwan wanka"
Yusuf ya girgiza kai yace "to"
Ya miƙe ya ɗau bokiti ya fita, Widad ta buɗe Akwatinta ta ɗakko towel ta ɗaura, ta saka hijjabi ta biyo bayansa yadda ana haɗa ruwan se ta shiga tayi wanka.
Mutan gidan sunata hada Hadar yadda za'a haɗa karin kumallo, ga dukkan alamu yau mutuniyar Widas ce da girki, wato Harira.
Yusuf ya durƙusa ya gaishesu, cikin jin nauyi kafin yayi magana Gwaggo tace "Yusufa na ganka da bokiti, ruwan wankan za'a zuba mata?"
Yusuf yace "eh Mama"
Tace "kawo in zuba maka anan, ya jikin nata kuwa"
Yusuf yace "jiki Alhamdilillah"
Tace "Madalla, nikam ya sunan nata ne? Bamu san sunanta ba"
Yusuf yayi murmushi yace "Sunanta Widad"
Hari dake gaban murhu ta juyo da sauri tace
"Bala'i, wannan wane irin sunane? Hudas ko wudas sekace kayan citta da masoro wane irin sunane wannan"
Tsakin Widad ne yasa Yusuf juyawa, yadda ta tamke fuskane ya tabattar maaa sa taji abunda Hari tace, Yusuf kamar yayi dariya Amma ya basar kar suyi faɗa a gaban mutane.
Gwaggo tace "kaga 'yar halak, ana zancenta se gata, sedai ni wannan sunan nata na Larabawa bazan iya faɗa ba, Amarya ya jikin naki?"
Widad a ranta tace "wai Amarya Taɓɗijan"
Yusuf yace "Ana miki ya jiki?"
"Naji sauƙi"
Galala Hari ta bita da kallo tace "Ashe bahaushiya ce, wallahi ganinta nake kamar bata jin hausa, yo aini harna fara tunanin ko kurma ce, ashe tana magana sannu Amarya wudas, ashe kina magana Allah sarki, ya jiki?"
Sake yamutsa fuska Widad tayi, 'ita dai wannan matar bata gajiya da magana, kodai bata san yadda haƙoranta suke bane take buɗesu tana surutu haka, bar wani kore kore ne a jikinsu, ga maganar tsiya da take dashi"
Widad bata kulata ba, aka haɗa mata ruwanta, Yusuf ya kaimata inda take wanka.
Aka haɗa Yusuf da yaro ya rakashi rafin da matasan garin suke haɗuwa suyi wanki.
Amlace ta shiga ɗakin Ramlah, ta dinga bubbuga mata filo, da ƙyar Ramlah ta tashi a fusace tace "Meye haka Amal?"
Amal tace "Anya lafiyar ki kuwa? Ƙarfe biyi fa, amma har yanzu bacci kike, yakamata ki tashi haka ai"
Miƙewa tayi zaune tana miƙa tare da duba agogo, dagaske biyu na rana, haka ta miƙe ta tafi banɗaki tayi wanka sannan ta ɗanji ƙarfin jikinta.
Koda Saleh ya dawo kano, be biya ko'ima ba Asibiti ya fara zuwa duba jikin Alhaji Nasir, amma yanayin jikin nasa se godiyar Allah, Nurses suka gaya masa Anwar yaje masallaci.
Saleh ya zauna a kusa da Alhaji Nasir, wanda idanunsa ke lumshe yake numfashi da temakon Na'urar dakw bashi iskar Oxygen, ya riƙo hannunsa da suka yi sanyi ƙalau, cike da tausayawa ya kai bakinsa daidai kunnensa yace
"Allah ya baka lafiya Yallaɓai, 'ya' yanka sun kuɓuta daga hannun miyagun nan, yanzu haka suna wasu ƙauye na basu mafaka, saboda tseratar da Rayuwarsu, Yusuf yayi ƙoƙari matuƙa ya kula da Amanarka, yana kula da gimbiyarka sosai, Amma munyi maka wani laifi da ban san ya zaka ɗauki abunba, Na wuce gaba Yusuf ya Auri 'yarka, dan kasan bata yadda da kowa seshi, kuma baze yuwu ya cigaba da kula da ita ba, tunda ba muharramarsa bace"
Dukda Alhaji Nasir ba iya magana zeba, da alama yana jin abunda Saleh yake faɗa, ƙara riƙe hannun Saleh yayi gam sannan yayi masa murmushi.
Saleh yace "Amma karka kuskura ka gayawa kowa, kayi shiru da bakinka"
Anwar ne ya shigo bakinsa ɗauke da Sallama, yana ganin Saleh yayi murmushi yace "Saleh sannu da zuwa, naje Sallane"
Saleh yace "bakomai Anwar, ya me jiki?"
Shiru Anwar yayi, ƙwall
0 comments:
Post a Comment