BINTU Part 003
BINTU Part 003 . A kanki nake zaune?" Cikin rashin fahimta ta dubeshi. Bazaka fahimci yanayin da ke a saman fuskartasa ba. "Yaya bangane ba." Ya ajiye gwangwanin Maltina bayan ya kur6a. "Me kika cewa Hafsa?" Gabanta ya fad'i, ashe yayi musu la6e? Oh, yanzu ya zatayi? "Ko baki gane ba?" Ta mik'e tana jijjiga Hanif wanda ke zullo shi a dole sai ta saukeshi. "Saukeshi." Ya fad'a, ta saukoshi ta rik'e. "To ai ni bansan abinda na fad'a ba." Shiru ya biyo baya, sai kur6ar lemunsa yakeyi yana dubanta rik'e da gudan jininsa. A hankali ya sauke ajiyar zuciya. "Munyi dake ki nemamin matar aure ne?" Yanda yayi zancen a sanyaye ya sanya ta d'ago dara-daran idanunta ta dubeshi, wani sassanyar kallo yake yi mata wanda yasa ta jin abinda tun da suke tare bata ta6a jinsa ba. A sannu ta sauke kanta ta maida ga Hanif wanda ke wasa da agogon hannunta. "Baki ban amsa ba, meya kawomiki tunanin nemamin auren Hafsa?" Gabanta ya soma fad'uwa ganin yanda yake maganar a sanyaye, ita fa tafi ganewa maganarsa a sama-sama yanda ya saba yi mata magana. Ta zubawa Hanif ido, tana matukar son yaron. Batasan sadda ta soma fad'in zahirin abinda ke cikin zuciyarta ba. "Tausayin Hanif nakeji. Kowane yaro yana so ya rayu tare da mahaifiyarsa, saidai Allah baiyi Hanif zai rayu da tasa mahaifiyar ba. Na sha gani yana faruwa a wasu wuraren, mijin yaya ya auri k'anwarta bayan rasuwarta saboda ta kula da 'ya'yan 'yar uwarta. Shine dalilina na yiwa Hafsa maganar. Kayi hakuri dan Allah." Ta k'arashe cikin rawar murya. Alal hak'ik'a tana tausayin Hanif, har ta sha fad'a a gabansu Mami, ita kam duk radda tayi aure da Hanif zata tafi. Aisha kan tsokaneta, ya zatayi idan Yaya Ma'aruf yayi aure ya damk'awa matarsa Hanif. "Wallahi idan muguwa ce, labari ya risk'eni ta ta6a lafiyarsa, ke zan biyo gidanki na kwasa muje muyi mata tsinannan duka." Wannan ne furucinta, har ma ya basu dariya. A wannan shirun da tayi, a nan ya samu damar nazartarta. Gaba d'aya bai fahimci kansa ba. A sannu ya kai duba ga yaronsa, bai iya furta komai gareta ba. Can kuma ya samu damar magana. "Nagode da wannan k'auna da kike nunawa d'ana. Amma ina mai gargad'inki, banaso ki k'ara yiwa Hafsat maganar nan. Daidai da Mami banason yaje kunnenta. Ni Ma'aruf bana tunanin aure yanzu, Asma'u..." Sai kuma ya fasa cewa uffan, ransa na sosuwa a duk lokacin da tunanin Asma'u ya fad'o mishi. "You can go." Ta mik'e rungume da Hanif tayi hanyar fita. Ta juyo kad'an ta dubeshi, idanunsa a kanta, tayi azamar d'auke kanta ta fice. Haka kawai ta rasa abinda yasa ta jin tausayin Ma'aruf a karo na biyu bayan rasuwar matarsa. A farfajiyar gidan sukaci karo da Aisha wacce ta yiwa Hafsa rakiya. "Ina kika shiga, Hafsa ta tafi." Ta numfasa, maimakon tayi magana sai kawai ta mik'a mata Hanif tayi gaba. Aisha ta bi bayanta da kallo. Anya kuwa lafiyarta kalau? Ta bi bayanta zuaa d'aki ganin da tayi bata falon. . Ga mamaki, kuka ta tarar tana yi har da sheshshek'a. "Ke lafiya kuwa? Meyafaru?" Bata kulata ba, ganin tana niyyar zuwa kiran Mami ya sanya ta dakatar da ita. "Tsaya, wallahi Yaya ne ya tunamin Anti Ma'u, duk sai ya bani tausayi." Aisha ta numfasa. Bintu ta labarta mata abinda akayi bayan ta rok'eta alfarmar kada ya je kunnan Mami. Aisha tayi murmushi. "Allah Sarki, ai daman za'a sha wuya kafin Yaya ya amince yayi aure. Ashe Abba ma ya yi mishi zancen aure kwanaki, shine dalilin rashin lafiyar da ya yi a satin da ya wuce. Yanzu sai an had'a mishi da addu'a, Allah Ya sanyaya zuciyarsa. Ke nifa banga abin tashin hankali ba, duka-duka ko shekara ba'ayi da rashin Anti Ma'u ba, shima kingani ai Abban shiyasa bai k'ara maganar ba. Hum, wayasani ma ko 'yar gida zamuyi muku." Ta k'arashe da zolaya. Ai tuni Bintu ta mance da kukanta. A harzuk'e tace. "Wallahi yanzu zan d'ura miki ashariya, shegiya. Bakinki ya sari d'anyen kashi. Aka had'ani da Yaya Ma'aruf ai an nakasta rayuwata." Gane inda ta nufa ya sanya Aisha tuntsirewa da dariya. Bintu tayi kwafa. "Kya yi dariya mana, muguwa kawai. Ke kafin ma ayi wani batun, ko hoto akayimana da shi ai an cuceni. Mutum kamar zabiya, tab. Ai wallahi mata ma kad'ai sun isheni." Aisha tana dariya ta amsa. "Kuma bakisan wani abu ba, wallahi har zawrawa sonsa sukeyi. Kodayake ai ke shaida ce. Dubi k'awar Anti Amina, Iklima, da biyu matar nan ke kawowa Hanif ziyara. Mace babba mai shekaru talatin, kusan sa'arsa ce." Kwafa Bintu tayi. A rayuwa babu wacce tafi jin haushi kamar Anti Iklima. Ta lura wayewarta ya yi over, ga afkin bleaching, har fuskarta tayi tabo. Ita a dole son Yaya Ma'aruf take. "Ai ita wannan idan batayi hankali ba, wataran sai na koyamata hankali." "Me zai dameki da ita? Wajenki take zuwa?" Harararta tayi. "Yaya Ma'aruf ai yayana ne inace? Shi kansa na kula baya k'aunarta wallahi. Daga ya ganta yakeyin kicin-kicin, ke dole ma na koyamata hankali." Aisha na murmushi, "Wai anya babu wata tsakanin..." Ashar d'in da Bintu ta lailayo ya sanyata yin shiru da azamar rufemata baki tana jan a'uziyya. "Baki da hankali?" Cewar Aisha. Ta fisge hannunta. "'Rainin wayo kai, na gayamiki babu komai tsakanina da Yaya Ma'aruf, sai kawomin k'abli da ba'adi kikeyi. Bar ganin kin fini jiki sai na zauneki na jibgi banza." Aisha ta ajiye Hanif ta soma k'ok'arin mak'ureta. Ai da gudu ta fice tana dariya, daman sai cika bakin, amma babu k'arfin. * * * [7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶ ©Rufaida Omar (July...2016) <<17>>A kwana a tashi babu wuya wajen Mai Sama, har gashinan an shiga satin bikin Hafsa da Bashir. Nan fa Aisha ta zama busy, koyaushe da ita Hafsa ke shirye-shirye kasancewarta aminiyarta. Da zarar Aisha ta taso makaranta, bata yo gida sai can gidansu. Duk yanda tayi Bintu ta dinga taimakonsu da wani abin, tace ba ruwanta ita bata kalan dangi. Ana gobe za'a soma biki, Aisha ta koma gidansu Hafsa da zama. Bintu ta k'ek'eshe tace ba da ita ba, gad'a a mak'ota. Babu inda zata, dole Aisha ta fice da fushinta. Ko a jikinta, acewarta babu dangin iya bare na Baba, zata dai lek'a bikin. Washegari asabar, misalin goma ba safe, tana zaune a falo tana karyawa kasancewar bata jima da tashi ba. Mami na zaune tana bawa Hanif maganin mura, Ma'aruf yayi sallama ya shigo. Bintu ta dubeshi, ya gama had'ewa cikin tsadadden yadi kalar ruwan toka, hannunsa sanye da agogo ruwan silver sai zobunan azurfansa biyu a kowane hannu. Yayi kyau har ya gaji da had'uwa. Ya gaishe da Mami, ta amsa da murmushi. "Yau babu baccin safen? Ina zuwa haka?" Ya gyara zaman hularsa idanunsa akan Hanif. "Akwai wani abokina ne bai ji dad'i ba kwana biyu, shi nakeson lek'awa." Mami ta gyad'a kai. Sai lokacin Bintu ta gaisheshi, ya amsa ba tare da ya dubeta ba, ta ta6e baki. Yanzu mamakinsa takeyi, tun maganar Hafsa da sukayi, kusan sati da 'yan kwanaki kenan, ya chanja mata. Bai fiye shiga harkarta ba, ko meyasa? Bata da amsar hakan. Maganar Mami ta katseta. "A'a, ga Bintu ku je tare ka sauketa a gidan walimar nan tasu." Hakan yasa ta dubansa, shima ita ya duba kafin ya dubi Mami fuska a yamutse. "Ina direban ya shiga ne?" Mami ta 6ata fuska. "Ai nasan da zamansa nace kuje tare. Ka sauketa, yau ba zai zo ba." Ya dubi Bintu fuska a 6ace sai kuma ya mik'e. "Idan ta shirya tayimin magana." Daga haka ya fice, yana ji Mami nayi mata maganar tayi sauri. Bintu ta mik'e fuska a 6ace, ita kam bataso aka had'ata tafiya da Ma'aruf ba. Ta ci wajen mintuna talatin da wankanta da shirin. Walimar ba ta anko bace, yini ne na 'yan mata. Don haka ta sanya material ruwan k'asa, d'inki mai matuk'ar kyau akayi mata. Ya zauna d'abas a jikinta. Ta murza d'aurin d'ankwalinta bayan ta kammala fente fuskarta da kwalliya. Ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin k'amshi don ko kusa Mami bata barinsu amfani da k'arfaffan turaruka. Ta fito, d'akin Mami ta soma shiga tayi mata sallama, Mami ta bata kud'i ta zura a jakarta. Saida ta shiga d'akin Hanif ta sumbaci goshinsa kafin ta fice. "Kwas, kwas." Take takunta da takalminta mai d'an tsawo, tana son takalma masu tsayi duk kuwa da cewar ba gajera bace. A haka har ta nufi sashen Yaya Ma'aruf. Ta shiga da sallama, yana kwance saman kujera idanunsa a lumshe. Ta zuba mishi ido, kamar wanda aka k'arawa haske da kyau. Ga sajensa ya kwanta luf-luf. Haka kawai ta tsinci kanta da dubansa, a sannu ya bud'e idanunsa suka sauka cikin nata. Da sauri ta kauda idanunta. "Na shirya." Ta fad'a cikin in-ina. Ba shi da niyyar mik'ewa, saidai bai maida idanunsa ya rufe ba, ya cigaba da dubanta. Jin shiru yasa ta jin haushi, ta juya zata bar d'akin. "Ki jirani." Ta bi umarninsa ta tsaya a k'ofar d'akin, ya fito ya rufe da muk'ulli. Suka jero. Abba yana zaune a 'yar barandarsa yana karatun jarida, yayinda Mami ke k'ok'arin zuba mishi ruwa a kofi. Hankalinsa ya kai garesu, a gaban idonsa suka jero har Ma'aruf ya bud'e mota suka shiga. A hankali yakejin wani tunani yana d'arsuwa a zuciyarsa. Muryar Mami ta katseshi. "Abban Aisha, ga ruwan." Ya numfasa ya kar6a ya sha alokacin da maigadi ya maida kyauren ya rufe. Bayan ya kammala sha ya ajiye kofin gami da duban Matarsa da murmushi d'auke saman fuskarsa.... . "Yaranki ne suka ban sha'awa." Cikin rashin fahimta Mami ta tambaya. "Wai Bintu da d'anka?" Ya jinjina kai. "Kwarai na ji musu sha'awar kasancewa tare k'ark'ashin inuwar aure, duba da abubuwa da yawa. Saidai ke d'ince bansani ba ko zaki iya bamu 'yar ta ki." Mami tayi shiru, ita kanta ta jima tana wannan tunanin, saidai sanin halin Bintu da Ma'aruf ne yasa ta danne sha'awarta, ta tabbatar da kamar wuya su amince da hakan. Musamman na ita Bintun. Tunaninta ya katse sakamakon rik'o hannunta da Abban ya yi. "Lallai idan hakan ya tabbata, ba mu ba, har su yaran zasuyi farinciki Fatima. Baki lura da yanda yarinyar ke tsananin k'aunar Hanif ba? Ki sanyawa lamarin albarka. Sauran ki barwa Allah, ni kuma zanyi k'ok'arin fahimtar da yaronnan." Ta dubi mijinta, annurin da ta gani kwance saman fuskarsa ya tabbatar mata lallai da gasken gaske ya d'auki lamarin har gashinan ya gaza 6oye farincikinsa. Batasan irin wannan k'auna da Abba ke yiwa Ma'aruf ba, tamkar shi kad'ai ne d'a a wajensa. Ta numfasa gami da zare hannunta cikin nashi "Zan fi kowa farincikin k'ulluwar wannan al'amari, saidai karatun Bintu fa? A ganinka ita zata amince ta aureshi?" Abba yayi shiru kafin ya dubeta. "Bana nufin tursasa musu, saidai yara mu muke da iko akansu ba su keda iko kanmu ba. Ballantana kuma na yiwa yarannan kyakkyawar shaida Fatima. Ina ji a jikina, in sha Allah, ba zasu bamu kunya ba. Batun karatu, ai aure bazai hanata karatunta ba. Ki bar komai a hannun Allah, in sha Allah zasu fimu jin dad'in wannan had'in." . Mami dai hankalinta ya rabu gida biyu, a gefe guda tana mai jin dad'i idan ta misalta yau gashinan Ma'aruf da Bintu sun amince da auren juna wane irin farinciki zatayi? A gefe idan ta tunano rashin jituwarsu duk sai zuciyarta ta karye, bata hangen yiwuwar lamarin ko kad'an, abin ne da kamar wuya. * * * A can kuwa, Ma'aruf da Bintu babu mai cewa wani uffan tun soma tafiyarsu. Motar tayi shiru ko rediyo bai kunna musu ba. Abinda sam Bintu bazata jura ba kenan, idan baza'ayi biyu ba to ayi d'aya. Ko suyi hirar ko ya kunna rediyo. Batason tafiyar kurame, hakan yasa ta fiddo wayarra ta hau k'ok'arin sanyawa kunnuwanta (Earpiece). "Ke baki iya hira ba?" Ta tsaya jin abinda yace, ta dubeshi hankalinsa na ga titi. Ta kauda idanunta. "To ai bansan abinda zance ba." "Bani labarin Banki da Sarkin Nanaye." Ya k'arashe da murmushi. Itama sai ta d'anyi dariya. Ya dubeta. "Ko ba sunayen nasu kenan ba?" Ta tsuke baki, to ta samu abinda take so. "Yaya ai sune suka fiye naci, na nunamusu bana sonsu amma wallahi sun addabeni. Ai Banki aure ma zaiyi yanzu, Sarkin Nanaye kuma ya gaji ya hak'ura." Ma'aruf na murmushi lokacin da ya sha kwanar da zata kaisu gidan su Hafsa sannan marigayiyar matarsa. "Kina da matsala Bintu, mijinki yana da aiki babba." Ta ta6e baki "Ni bana sha'awar aure fa a yanzu." "Sai me? Keda ga shi har soyayya kin iya kina yi." Tayi dariya. "Wannan sai A'i, ni bana soyayya. Na d'auketa 6ata lokaci wallahi. Shiyasa nake k'ara godewa Allah da bai ta6a sanyamin son wani namiji a rayuwata ba, son aure." Shiru ya biyo baya, can kuma Ma'aruf ya dubeta kad'an ya d'auke kai. "Ai nayi zaton bazaki k'ara shekara ba zakiyi aure. Kodayake banga namijin da zai iya da shiriritarki ba." Ta 6ata fuska. "Kuma a hakan fa wallahi sona ake..." Sai kuma ta fasa maganar ganin kallon da yayi mata. Ta muskuta. "To ai gaskiya ne." "Eh, irinsu Ukasha ba, amma sanin kanki maza ire-irenmu, munfi k'arfin ki." Ta dubeshi kad'an, wai me yake d'aukar kansa ne? Shi kuwa sam bai fad'a da wasa ba, ya fad'i iyakar gaskiyar abinda ke zuciyarsa ne. Baisani ba, furucinsa ya yiwa Bintu zafi matuk'a. Ya faka a k'ofar k'aton kyauren gidan. "Bismillah, jeki." Ta dubeshi lokacin da ta murd'a k'ofa. Kamar ta gasa mishi bak'a sai kuma ta fasa ta fita a fusace gami da banko k'ofar da k'arfi. Har saida ya firgita. Sai lokacin ya tunano furucin lallai zai iya 6ata ran mace mai ji da gayu irin Bintu. Yayi 'yar dariya kafin ya ja motarsa. Ai kam da wuya, su had'u wuri d'aya da Bintu ayi rabuwar arzik'i. Ita kuwa haka tayi ta yiwa Aisha mitar abinda yace. Tun Aisha na sauraro har ta gaji. "Ke wai magana bata wucewa a wajenki? Menene abin jin haushi anan? Ni banga abin damun kai ba, kin mance da bakinki kin sha fad'a babu abinda zakiyi da kamar Yaya Ma'aruf?" Bintu ta numfasa cikin yanayin fushi. "To ai ni a nufina na fi k'arfinsa ne, ba wai yafi k'arfina ba." Aisha tayi dariya kawai, lallai ma Bintu, ta yaya zata had'a kanta da Yaya Ma'aruf? Kodayake ance mace ta fi namiji kyau watakil da wannan furucin na bahaushe take tutiya. Har aka tashi walimar bata saki ranta ba, ta ji haushin abinda yace mata, ta kuma ci alwashin ramawa. . Duk yanda Aisha ta so ta zauna ta kwana, amma fafur fa k'i. Dole haka suka rakota titi suka koma. Tana daf da kaiwa bakin babban titi inda anan take saka ran samun abin hawa, ta ji hon a bayanta. Ko tsayuwa batayi ba ballantana ta juyo ta dubi mai shi. Banda murmushi babu abinda yakeyi, bai so biyowa d'aukarta ba saidai babu yanda ya iya tunda Mami ta kira ta shaida mishi ya biya d'in sanin da tayi Bintu ba zata amincewa kwanan ba. Isarsa ne Aisha ke sanarmishi ko mintuna biyar batayi ba da tafiya, hakan ya sanyashi biyo titin sanin ana wuyar abin hawa a titin cikin unguwar ba lallai ne tayi sa'ar abin hawa ba. Hon da ya cika kunnuwanta ne ya sanyata tsayuwa gami da juyowa a fusace da niyyar yiwa mai shi rashin mutunci. Saidai ganin motar yasa ta fahimtar Yaya Ma'aruf ne. Ya bud'e murfin mota ta fito yana dubanta. "Ke bakyajin hon ne? Taho mu tafi." Ta dubi gefenta, wasu samari ne zaune suna dubansu. "Alhamdulillah." Ta fad'i a ranta. Cikin d'aga murya tayi magana. "Wai kai Malam wane irin naci ne haka? Tun d'azu kake bina, na gayamaka bana sonka, ko dole ne?!!" A fusace ya nufota, tayi azamar d'aga hannu gami da ja baya a tsorace. "Wallahi koda wasa kada kayi gangancin ta6a lafiyata, ana so dole ne? Ba gayamaka bana sonka!" Daga haka ta ja tsaki ta juya, tana jin sa'adda samarin suka kwashe da dariya har da masu fito. Ma'aruf ya rasa abin cewa, gaba d'aya ta d'aureshi da jijiyoyin jikinsa. Ya gaji da binta da kallo kawai ya fad'a motarsa a fusace ya ja. Cikin matsanancin gudu ya wuceta har yana tayar da k'aramar guguwa. "Yau naga ta kaina." Ta fad'a a fili. Anya zata koma gida? Kai babu batun kome, ta gwammace tayi kwanan gidansu Hafsa idan yaso gobe Mami ta tahomata da kayan buk'ata ko ta bayar a kawomata. Amma ai ta riga da tayi musu sallama. Kawai sai ta hau mota, kai tsaye gidan yayanta Rufa'i ta je. Suna zaune da Hajara sai ganinta sukayi kamar an jefota. "Ke kuma lafiya?" Ta zauna, hannu ta kai ta ja ruwan dake ajiye saman faranti akan center table ta kur6a. "Anan zan kwana." Rufa'i da Hajara suka dubi juna. Kafin su tambayi komai, ta kwashe abinda ya faru ta sanarmusu. Rufa'i mamaki ya haneshi cewa uffan, Hajara kuwa banda salati mai had'e da dariya babu abinda takeyi. "Wai Bintu baki da aljanu kuwa?" Bintu ta turo baki. "Lafiyata lau, ai shine ya ja. Cewa yayi fa wai maza ire-irensu sunfi k'arfin ajina." Rufa'i yayi wani murmushi tunano maganar da Mami ta gayamishi d'azun. Lallai akwai badak'ala. "Banda abinki, kema kinsan broda ba shi da rufa-rufa. Idan ya fad'i abu iyakar gaskiyarsa yake nufi. Amma ni kaina ban ji dad'in abinda yace ba. Ai kinfi k'arfin ma ire-irensa." Hajara ta tuntsire da dariya. "Yanzu kin sanarwa Mami kina gidana?" Ta girgiza kai. Ya dauki waya ya kira Mami ya shaidamata. Mami tace babu wani abu. Da kansa bayan ya fita da dare ya biya ya kar6o mata kayan amfaninta. Bai ko had'u da Ma'aruf ba ballantana ya ba shi hak'uri kan abinda Bintun ta yi. * * * . Maimakon ya nufi gida, sai ya zarce zuwa gidansa. A fusace ya shiga falon gani da zama kan kujera ta zaman mutum uku wacce batayi k'ura ba sakamakon yana zuwa lokaci-lokaci yasa d'an dolo ya gyara ko'ina. Ya runtse ido yana huci, a sannu kuma abinda ya faru ya shiga dawowa kwanyarsa. Ba shakka Bintu tayi masifar rainashi. Kasa zaman gidan ya yi ya fito. Iyakar tsawon rayuwarsa, babu macen da ta ta6a yi mishi wannan wulak'ancin sai ita. Wai k'anwarsa, wacce ya d'auketa wata yarinya da batasan komai ba sai shirme da shiririta. Lallai idonsa idon Bintu, hum! Koda ya isa gidan, bai zarce ko'ina ba sai d'akinsa. Har wayewar gari Mami da Abba basu sanyashi a ido ba. Safiyar washegari, bai fito ba sai wajejan goma na safe. Mami na zaune a falon Abba suna hira sai gashinan. Ya shigo da sallama, duk suka dubeshi suna masu amsawa. Ya had'e cikin jeans blue marar nauyi, sai farar shirt, kansa babu hula gashinan nan yayi luf-luf. Zama yayi ya gaishesu har lokacin 6acin ran nan da Bintu ta jaza mishi yana nan mak'ale cikin ransa har ma ya shafi walwalarsa. . "Ya akayi dai kakana? Akwai abinda ke damunka?" Maganar Abba ta sanyashi sakin fuska kad'an, ya zauna ya tankwashe kafafunsa. "Babu komai Abbana." Abba ya gyad'a kanshi. Zaiso a yanzu ya ji ta bakinsa, saidai rashin walwalar da ya gani tattare da shi yasa shi yin shiru. "To, Allah Ya rufa asiri, acigaba da hak'uri da rayuwa." "Amin. Nagode Abbana, addu'arku muke buk'ata koyaushe." Abba ya gyad'a kai cikin jin sanyi a ransa. "Kuna tare da shi a koyaushe in sha Allah." Haka suka cigaba da hirar duniya har Mami ta fita ta barsu. Saida Ma'aruf ya sake sosai sannan Abba ya numfasa. "Kakana, akwai maganar da nakeson muyi." Gaban Ma'aruf ya fad'i, ya soma ambaton Allah. "Ina saurarenka Abbana." D'akin ya d'anyi shiru kafin kuma Abba ya soma magana. Saida ya soma na nasihohi masu nuni da muhimmancin yarda da k'addara kafin ya gangaro zuwa ga abinda yakeson fad'a. "Madallah, a matsayina na mahaifinka, ina mai neman amincewarka wajen had'aka aure da 'yar uwarka Fatima Bintu matuk'ar hakan bazai zamto cutarwa ba ga rayuwar d'ayanku. Ka sani, bani da burin tursasaka, ko a farkon aurenku ma kaida d'an uwanka ban tursasa d'ayanku ba, saidai kowannenki da kansa ya za6i matar aure. A wannan karon ma, ba hakan nakeson ayi ba. Na baka nan da kwanaki uku, kayi tunani ka yanke abinda kaga ya dace. Idan baka k'aunarta, to lallai ka sani, ba zan tursasa maka aurenta ba, hakanan itama Fatima Bintu, dukkan abinda tace akan lamarin, to fa bazan takura mata ba. Daman zumunci na so had'awa." Abba ya d'anyi shiru yana duban Ma'aruf wanda gaba d'aya ya gama shiga hali na rikita. "Kana iya tafiya." Ya mik'e jiki kamar ba nashi ba, haka ya bar d'akin a daddafe. Bai iya k'arasawa falon Mami ba, zama yayi a kujerar dake a barandar Abba ya zubawa farfajiyar gidan ido kawai. Bintu? Bintu fa?!! Ita kuma Abba ya hango mishi matsayin abokiyar rayuwa? Ya Ilahi! Saida ya kwashi mintoci kusan uku kafin ya mik'e ya bar wajen. Abba ya sauke labule ya koma saman dardumarsa ya zauna gami da d'aga hannu ya yi addu'ar neman abinda yafi alheri. Fatansa ya ga wannan aure ya tabbata. A can kuwa, Ma'aruf fa ya shiga tara ba uku ba, kansa ya d'aure matuk'a. Meya kawowa iyayensa wannan tunanin? Su rasa wanda zasu hasko a matsayin matarsa sai Bintu? Yarinyar da kunya bata isheta ba? Ya runtse idanu sannan ta bud'esu, nan da nan suka kad'a. A yau mutuwar Ma'unsa ta dawo mishi sabuwa fil! Ba don mutuwa ta mishi YANKAR KAUNA ba, yaushe iyayensa zasuyi tunanin aura mishi wata Bintu? A yau ya k'ara jin kewa mai d'umbin yawa na Ma'unsa. A gefe guda wani iri tsanar Bintu yake ji. ("Wai kai Malam wane irin naci ne haka? Tun d'azu kake bina, na gayamaka bana sonka, ko dole ne?!!") ( "Wallahi koda wasa kada kayi gangancin ta6a lafiyata, ana so dole ne? Ba gayamaka bana sonka!") Ya runtse ido ya bud'e duk a lokaci guda. Cikin zafin nama ya mik'e ya nufi firij, ruwa ya ciro ya soma kwankwad'a kafin wani sanyi ya ziyarci ruhinsa. Lallai zai koyawa yarinyar hankali, zai tabbatar mata cewar ita d'in marar kunyar k'arya ce. Alokaci guda ya saki wani guntun murmushi. * * * A gidan Rufa'i kuwa Bintu ta sake sai hada-hadar tafiya gidan yini sukeyi tare da Hajara wacce itama zata je. A ranar ne kuma za'ayi Dinner Party, ta kama dole da yamma ta koma gida don kwata-kwata Mami bata had'o mata da ankonsu na Dinner ba. Bayan sun kammala, Rufa'i da kanshi ya saukesu wajejan uku na rana. A can suka iske Mami itama da Atine har da Hanif. Nan ta hau tambayar Binti dalilinta na k'in komawa gida, dariya kawai Bintu tayi bata ce mata komai ba. Ganin bata da niyyar maganar ta kyaleta. Aisha kawai ta sanarwa, saidai alokacin ta fahimci jini d'aya ba wasa ba, don kuwa da gaske Aisha ta ji babu dad'in abinda ta yiwa Yayanta. Bintu ganin haka itama ta watsar da ita, saidai basu ci ko rabin awa ba, Aisha ta sauke fushinta, ita d'in ko kusa bata da rik'o. Da yamma Mami ta had'a Bintu da direba domin zuwa d'auko kayanta na dinner. A karshe Bintun tace zata fito kawai daga nan gidan. Yana sauketa, ya juya wajen Mami don su d'inma zasu halarci Dinner, kasancewar har da iyaye. Ta dubi farfajiyar gidan, wani sanyi ya ziyarci zuciyarta ganin babu motar Ma'aruf wannan ya bata tabbacin baya gidan. Hankalinta kwance ta shiga. Wanka ta soma yi sannan ta d'ora alwala. Saida ta idar da Magrib sannan tayi zaman gaban madubi ta shiga fente fuskarnan nata da kwalliya. A fili take fad'in. "Yau zan kece raini." Ta kammala shafe-shafenta sannan ta fiddo orange lace d'in da sukayi na 'yanmata, d'inkin doguwar riga(fitet gown) ta zura. Nan ta k'ara zaman tafkeken ribbons dinta sannan ta d'ora nad'in da sukayo akanta. Ta saki baki tana duban kanta a madubi, iyakar had'uwa ta had'u. Wayarta dake k'ara tun d'azu tana yankewa, sai lokacin tayi niyyar d'agawa. "A'i ya dai?" K'arar da ta ji ya bata tabbacin sun kama hanya. "Kin fito? Mami tace ki tsaya ga Yaya Ma'aruf zai taho ku fito tare." "Tab!" Da sauri ta katse wayar, ta jera da wa? Ita kuwa me ya kaita wannan gangancin. Da sauri-sauri ta had'a 'yar jakarta ta zura takalminta tana magana a fili. "Hauka nakeyi zan fita da Yaya Ma'aruf? Kasheni kawai zaiyi " Saidai me? . Bata kai ga bud'e k'ofar d'akin nasu ba ta ji hon d'in motarsa. Ai take hanjin cikinta suka kad'a. Da sauri ta fito daga d'akinsu tana lek'ensa ta windon falon Mami. Tana kallo ya kashe motar ya kwashi wayoyinsa, akan idanunta sukayi magana da baba maigadi, batasan abinda suke tattaunawa ba, k'arshe ya yo ciki. Da sauri ta saki labule, kirjinta kamar ana lugude tsabar bugun da yakeyi. Shikenan kashinta ya bushe. Ta fito tana sand'a har ta iso farfajiyar gidan. "Ke!" Ta ji an dakamata tsawa, a firgice ta juyo, yana tsaye jikin windon falonsa yana hangenta. Ta zaro idanunta taba dubansa kafin kuma tayi narai-narai da fuska kamar mai shirin kuka. "Zo nan!" "Shikenan na gama yawo." Tayi furucin a fili. Daga haka ya sauke labule. Dole ta taka ta nufi d'akin, a ranta banda addu'o'i babu abinda takeyi. Ta shiga da sallamarta. Ya amsa a ciki, yana tsaye a tsakar falon. Yayi mata kallon tsanake tun daga fuska zuwa yatsun k'afafunta daga inda yake tsaye. Fuskarsa sai ka rantse bai ta6a dariya ba. Batasan ya akayi ba ta ji ta tsugunna. "Yaya barka da dare." Bai amsa ba. "Ina zaki?" "Di..di..nar Hafsa." Ya d'anyi shiru. "Mami bata ce kiyi jirana bane?" Ya fad'a cikin tsananin zafin rai, gaba d'aya yarinyar haushi take ba shi, ya tsani a rainashi. Abin ban haushin ma, wai ita akeson ba shi matsayin mata, wannan abu da me yayi kama? "Ta fad'a." . "Ok, itama kin rainata kenan?" Ta d'an dubeshi, sai kuma ta sauke idanunta, gaba d'aya jikinta ya d'auki rawa. Fatanta Allah Ya mantar da shi abinda tayi mishi jiya kada yayi mata maganar. Ai kuwa dai alokacin baiyi d'in ba. Ya d'auki wayoyinsa ya shige d'aki. Nan ta zauna zaman jira, tun tana duba agogo har ta daina, idanunta tuni suka kawo ruwa ta soma zubar hawaye. Bakinciki da takaici duk suka bi suka addabeta, yana sane ya shanyata. Ta kwashi kusan rabin awa a zaune saman kafet d'in kafin ya fito daga d'akin. K'amshin turarensa ya daki hancinta, ta d'ago ta dubeshi ranta cike da jin tsananin haushinsa. Saidai kuma wani irin sanyin jiki ya ziyarci zuciyarta ganin yanda ya had'e iyakar had'ewa kai ka rantse injin matso kyau ya shiga. Sanye yake da farin boyel mai tsadar gaske, ya d'ora hula bak'a. Yayi kyau har ya gaji. Saidai ta gwammace bata dubeshi ba, don kuwa bai bita da komai ba sai harara. Baice mata uffan ba har saida ya nemi wuri ya zauna, takalminsa ya soma k'ok'arin zurawa. "Kina sane da laifinki ko?" Ya fad'a ba tare da ya dubeta ba. Ta saci kallonsa, ita kam duk ta tsorata. "Don girman Allah Yaya kayi hakuri." Ta fad'a cikin muryar kuka, bil hakk'i ta tsorata ganin yanda koda wasa babu annuri a fuskarsa. Baice mata uffan ba har ya kammala ya soma kashe futilu, ganin haka ta fito tana sharar kwallah har da sauke ajiyar zuciya duk a hangenta ta tsira. Bayan sun isa wajen motarsa ta kama gidan gaba zata bud'e ya harareta. "Koma baya." Ta koma babu shiri, ai ita ko boot ne zata shiga matuk'ar ba zaiyi mata wani hukunci ba. Ya saki kid'a lokacin da motarsu ta cilla titi. Tana kalle-kallenta a hanya, tun tana saka ran ganin sun iso Afficent har dai ta nutsu ta gane ba ma hanyar suka d'auka ba. Fargabarta ta k'aru, gaba d'aya hankalinta ya tashi. "Yaya ba hanyar muka yi ba kamar." Baice mata uffan ba sai ma ya k'ara volume na rediyo. Ai kuwa ta soma kuka. Ya dubeta ta madubi ya dauke kansa yana mai sakin murmushin mugunta. Bai tsaya ko'ina ba sai a wani k'aton gida wanda ko ba'a fad'a ba, kallo d'aya idan ka yiwa gidan zaka san akwai wani abu wai shi kud'i. Bayan ya shiga yayi fakin ya rage muryar kid'an dake tashi. Wayarsa ya fiddo ya danna kira bayan ya bud'e speaker. "Prince." Wata murya ta fad'a daga can 6arin, yayi wani murmushi na mugunta yana mai duban fuskar Bintu wacce take k'arewa gidan kallo ta madubi amma furucin da ta ji wata tayi ya sanyata maido hankalinta ga saurarensa. "Gani nan a waje." Daga can ta saki ihun murna. "Wow!! Yau lallai ina da mugun sa'a. Ma'aruf da kansa a gidannan?" Ya d'anyi dariya kafin ya amsa. "Kika wuce 5minutes zan juya na koma inda na fito." Ai sai ta d'an d'aga murya. "A'a, na tuba don Allah. Ganinan fitowa." Ya katse wayar. Bintu ta rushe da kukan bak'in ciki, tsabar ma rainin wayo yau itace ta zama 'yar rakiyar zance? "Rufemin bakinnan." Ya fad'a a hankali, dolenta tayi shiru. Ya d'an karkato yana dubanta. "Ko tari ban yarda kiyi ba har mu bar gidannan wallahi, idan kikayi wani kwakkwarar motsin da ta fahimci kina motarnan sai kin raina kanki. Bani wayarki." Da sauri ta mik'a mishi tana kokarin danne kukan da ya taho mata, wata irin tsana da haushin Ma'aruf kawai take ji. Ya kashe wayoyinsu ya ajiye. Mintuna uku kawai, sai ga wata budurwa kyakkyawar gaske. Fara tas da ita, ta ci ado har ta gaji cikin wani rantsesan yadi. Tana taku cike da yanga. Bintu sai kuka ya tsaya cak, shakka babu ta had'u iyakar had'uwa. Ita kuwa budurwar ko kusa bata ganinsu kasancewar gilas din tint. Ta k'araso, Ma'aruf ya bud'emata gefensa ta shigo ta zauna. Nan ta bishi da wani sassanyar kallo. "Prince ka shayar da ni mamaki, na kasa gask'atawa. Don Allah mu shiga daga ciki mana." Ya d'an ja fasali kafin ya amsa yana wani yamutse fuska. "No, kiyi hakuri, ina da uzuri ne banason na jima. Don kin damu da ganina ne na daure na zo yau." Bintu fa ta ga abinda ya fi k'arfinta. Ashe daman haka mata ke yiwa Yaya Ma'aruf? Mamakin da takeyi bai wuce yanda wannan mace mai shegen yauk'i da ji da kanta ba ta marairaicewa Ma'aruf har tana rok'onsa ya dunga kulata ko yayane tunda mai sonka yafi mak'iyinka. Ta saki ido da baki tana duban yanda shi kuwa yake faman shan k'amshi. Gaba d'aya ta samu abin kallo ta mance da batun dinner. Wannan shine karon farko da ta ji Ma'aruf ya burgeta...!! . Yana zaune gaban Abba domin amsa kiransa. Abba ya dubeshi. "Ina sauraron ra'ayinka game da maganarmu ta kwanaki." Ma'aruf ya k'ara yin k'asa da kanshi. "Na amince." Ya fad'a da kyar, Abba ya ji wani farinciki ya lullu6eshi. Ya yi hamdala a fili kafin ya bi Ma'aruf da kyawawan addu'o'i. A k'arshe ya sallameshi. Ma'aruf ya mik'e jiki babu kwari ya bar falon. Kai tsaye falon Mami ya nufa. Tun kafin ya k'arasa ya jiyo dariyar Bintu da Aisha saidai na Bintun yafi na kowa d'aguwa. Takaici ya sanyashi fasa shiga ya juya ya koma sashensa. Wai meya kaishi amincewa auren wannan yarinyar ne? Wane su6utar baki ne haka? Kai gaba d'aya ji yayi ya tsani kansa, ya tsinci kansa cikin yanayin 6acin rai da damuwa matsananciya. Ganin ba wani sauk'i ya sanyashi barin gidan batare da ya d'auki motarsa ba. * * * Bintu tayi shiru tana duban Mami wacce ke k'ok'arin zama gefenta a saman gado. Mamakinta bai wuce na kiran da Mamin tayi mata ba har da rufe d'aki da korar Aisha. Mami ta soma da kiran sunanta. "Fatima Bintu, takwara kuma d'iya awajena." Bintu tana murmushi ta amsa. "Na'am." Shiru ya d'an biyo baya, ita kam tana jin nauyin ma gayamata maganar, saidai ba yanda ta iya tunda Abba ne ya sanyata jin ta bakinta. Cikin hikima irin ta manya Mami ta soma da kwantar mata da hankali da nunamata lallai ita mai k'aunarta ce, ba zata bari a cutar da ita ta kowane hanya ba. Tana k'aunarta tamkar yanda take k'aunar yaranta. A k'arshe ta sanarmata da buk'atar Abba ta son had'ata aure da Ma'aruf har ta k'ara da sanarmata cewa Ma'aruf ya amince da aurenta. Bintu ta ji gabanta ya mugun fad'uwa, Ma'aruf kuma?! Innalillahi!! Meyasa tunanin Abba zai kawomishi hakan? Ya zatayi da rayuwa idan har Ma'aruf ya kasance mijin aurenta? Idanunta suka ciko da kwallah. Mami ta kauda duba daga gareta cikin sanyin jiki tace. "Bazan bari a kwareki ba Bintu, zan jiraki daga nan zuwa kwanaki uku, matuk'ar baki k'aunarsa, kada ki kwari kanki, ki fito fili ki sanarmin, bazan ta6a bari a aura miki shi ba. Ki tsayar da tunaninki wuri guda, ki kuma dunga addu'a." Daga haka Mami ta fita daga d'akin batare da ta k'ara dubanta ba ballantana ta fahimci komai a fuskarta. Bintu ta zame ta zauna dirshan a saman carpet. Yaya Ma'aruf fa?!! Me ya burgesu har sukayi tunanin wannan had'in? A rasa ma wanda za'ayi tunanin had'asu aure da shi sai mutumin da ya k'i jinin walwalarta? Koyaushe burinsa ya k'untata rayuwarta? Abar batun haka ma, ta nunamusu wata alama na cewar aure take buk'ata ne? Eh lallai, sun bi son zuciyarsu kawai zasu yiwa d'ansu gata. To ai itama tana da nata gatan, don haka ba zata k'ara kwanan gidansu ba daga wannan rana, gobe Rano zata nufa. Gaba d'aya tunanin Bintu ya birkice, kukanma babu sai ruwan hawaye kawai. Ranta banda k'una babu abinda yakeyi. Ba Ma'aruf d'in kad'ai ba, gaba d'aya gidan saida ta ji ta tsanesu. A ranar haka ta wuni babu walwala, Mami na lura da ita saidai batace uffan gareta ba. Gaba d'aya itama ta ji ta damu, tayi da na sanin yi mata maganar nan, daman ita tasan da wuya abin ya yiwu. Da dai ace Rufa'i ne, wannan kam tana da tabbacin ba lallai ne Bintu ta k'i ba. Gidan bai musu dad'i ba ko kad'an, daman Bintu ce mai rayamusu shi, yau ita kuwa babu kanta. Fuskarta tamkar an aikomata sak'on mutuwa. Washegari da wuri ta fito, ta lissafa kud'inta zasu isheta hawa motar zuwa Rano. Kai tsaye kuwa inda zata sami motar ta nufa maimakon makaranta. Inna suna zaune sai ganinta sukayi. Nan k'annenta suka hau murna. Umma kishiyar Inna batanan, hakanan Saifu da babansa suna kasuwa. Kallo d'aya Inna tayi mata ta fahimci babu lafiya. Abin akwai mamaki matuk'a. . Ya kwashi kusan rabin awa kafin yayi niyyar tafiya, a hakan ma budurwar wacce ya kira da Sa'a bata so ba, haka sukayi sallama tana rok'onsa da ya k'ara dawowa. Abin har ya bawa Bintu haushi, ta k'ulu iyakar k'uluwa, dubu yanda mace ba kunya take karya murya, shi kuwa sai shan k'amshi, haka kawai ta ji wata muguwar tsanar Sa'a ta dirar mata. Can kuma dai tayi tunanin me zai dameta? Bayan tafiyarta ya juyo ya dubi Bintu wacce sai lokacin ne ta tunano inda suka nufa, ta turo baki ta 6ata rai. Murmushi kawai yayi baice komai ba, ai kwalliyar ta biya kud'in sabulu, yayi ribas maigadi ya bud'e mishi (gate) ya fita. Sun kusa Afficent ya tsaida motar a gefen hanya. Ta dubeshi, hannu yasa ya bud'e mazaunin gefensa. "Dawo gaba, don ba direba kika ajiye ba." Ta yi jim kamar kada ta fito sai kuma ta bud'e ta dawo ta zauna ranta a 6ace. Tsaf ta fahimci manufar kaita wajen budurwarsa, wato dai ya nunamata lallai akwai mata 'yan gayu da suka damu da shi fiye da zatonta. Ya dubeta ya maida kansa ga hanya lokacin da ya sha kwanar da zata kaishi d'akin taron. Suna isa ya mik'a mata wayarta, a fusace ta fice daga motar. Saida ya kammala kunna wayoyinsa sannan ya kashe motar ya rufeta ya shiga. Tun kafin ka k'arasa cikin hall d'in kana jiyo tashin kid'e-kid'e. Tana k'arasawa ciki kuwa ta daburce ganin taron jama'a. Mafi yawansu, dangin Abba ne. Ta dawo baya da zummar kiran Aisha a waya. Sai jin maganarsa tayi a dab da kunnenta sakamakon k'arar kid'an da bazai barta ta ji maganarsa ba. . "Illar 'yan k'auyen kenan, ko shekara nawa zasuyi a birni, wayewarsu, suna ce kawai." Daga haka ya zarce ciki, kai tsaye 6angaren maza ya nufa. Ta bishi da kallon takaici. Ji tayi an dafa ta ta juya, ganin Aisha yasa ta sauke ajiyar zuciya, ta kasa magana kawai sai ta soma kuka. Ganin haka Aisha ta ja hannunta suka nufi waje. "Ke ina kuka tsaya? Ga Mami can cikin damuwa. Me Yayan ya yi miki?" Bintu tayi kwafa. Ta kwashe labarin komai ta bata, Aisha abin ya so bata dariya jin yanda take faman kushe Sa'a, ita kam tasan wacece Sa'a, d'iyar wani d'an majalisa ce, tun kafin ma ya auri Ma'u tana sonsa yanzu kuwa bazawara ce ma mijinta ya saketa adalilin shaye-shayen da takeyi ya zamar mata jiki. Tasan ko a mafarki, Ma'aruf bazai ta6a auren Sa'a ba ballantana kuma a farke. Saidai kuma jin abinda yace mata yanzun ne yasa jikin Aisha sanyi. "Kiyi hakuri, kinsan halin Yaya Ma'aruf, ba yau ya soma ya6amiki magana don kawai ya k'ular dake ba. Ke kika nuna kina da saurin fushi shi kuma anan yake samun damar yi miki son ransa. Ni yanzu ba wannan ba, muje Mami ta ganki hankalinta ya kwanta." Bintu ta share idanunta gami da yin kwafa kawai, Aisha ta gyara mata inda ya 6aci, tana janta da zolaya har Bintu ta saki ranta suka shiga ciki. Mami ta yi murnar ganinta kafin ta hau fad'an meyasa bata hau adaidaita ba tunda Ma'aruf d'in ya biya hira. Bintu tayi shiru da mamaki, ko kusa Ma'aruf baisan yayi k'arya ba babu kwakkwarar dalili. Har aka tashi taron bata sanyashi a ido ba. Tun kafin ma a tashin ashe ya tafi, haka ta ji a bakin Rufa'i sadda Mami ke cigiyarsa. Washegari da yamma aka mik'a amarya Hafsa gidan mijinta. Babu inda Bintu ta je, saboda makaranta, ranar a gajiye ta dawo lik'is. Agaban idanunta Mami suka wuce, tana kwance saman doguwar kujera bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita. Dab da magrib, Ma'aruf ya shigo. Dawowarsa kenan daga ofis, tuni ya yi wanka ya chanja zuwa k'ananun kaya na shan iska. Sam bai ko lura da ita a falon ba, duk a zatonsa, gaba d'aya gidan ne suka fice sai masu aiki ya rage da Atine da Hanif wadanda ya hanesu fita acewarsa, yaron ya gaji, kwana biyu kenan ana fita da shi. Saida ya shiga kicin ya nemi Iya da ta d'oramishi ruwan shayi, sannan ya doshi falon. Alokacin ne idanunsa ya kai gareta. Bacci takeyi, kallo d'aya zakayiwa fuskarta ka fahimci bata da wata matsala. Gashinta wanda ko kusa batason kitseshi ya mik'e tsaye kamar na mahaukaciya, ribon d'in kuwa tuni ya fad'i. Daga ita sai vest da dogon wandon da bai matseta. Ya ja guntun tsaki kafin ya d'auki filon kujera a gefensa yayi jifa da shi saman fuskarta. Bacci na Bintu fa, saida ya gwammace bai jefeta ba, juyin da ta yi yasa shi mik'ewa dole ya bar mata falon. D'ayan falon ya koma ya jinginar da kanshi saman kujera yana mai lumshe idanunsa. Wani yanayi ne, wanda tunawa da Ma'unsa kad'ai kan janyo mishi. Cikin k'arfin addu'a ya bagarar da tunanin ta hanyar buga game a wayarsa. Har Iya ta kawomishi ruwan shayin kamar yanda ya buk'ata. "Ki tashi mai baccin nan, lokacin sallah ya kawo kai." Ya fad'a yana duban Iya. Iya tayi 'yar dariya. "Au, mutuniyarka? Bintu ko rigima, ai saida na hanata bata fasa ba." Ta fice. Ta gabansa Bintu ta shige d'akinsu, bai ko dubeta ba. Bayan ta kimtsa ta k'ara fitowa cikin doguwar jallabiya da hula a kanta. Tayi kamar bata ganshi ba zata fice. "Ke bakisan ki gaida mutum ba?" Har lokacin haushinsa takeji. A ciki ciki ta gaisheshi bayan ta d'an russuna. Bai amsa ba, itama ta shareshi ta fice daga falon. Ya numfasa, har lokacin zuciyarsa ta kasa yanke tayashi yanke abinda ya dace. A gobe ne kuma zai bawa Abba amsa. Shi dai yasan Bintu ba ta daga cikin matan da yakeso, ina zai iya da shiriritarta? Ba k'aramin aikinsa bane wataran ya zaneta yayi mata raga-raga. Saidai kuma yanajin nauyin k'in amincewa aurenta. Da wane idon zai dubi Abba yace a'a? Mami kam, ya sani ba zata ji dad'i ba ko kad'an idan ya k'i jininta. Da wannan tunanin ya kammala ya fito. Zai fice ya hangota daga d'akin Hanif, rik'e da shi a cinyarta tana kai lomar abinci tana d'an lasa mishi miyar a baki, sai kuma ta kyalkyale da dariya. Sun burgeshi burgewa, yasan tana son d'ansa, yana girmamata a wannan wajen. Ya numfasa ya fice jin an soma kiraye-kirayen sallah. . Bayan sun shiga d'aki ta kora yaran zuwa tsakar gida. Bintu tuni ta soma hawaye. "Ke, sanardani meke faruwa? Ina Yaya Fatima, ya na ganki ke d'aya?" Inna ke jero dukkan tambayoyin nan cike da tsananin rud'ani. Bintu ta tsaida kukanta. "Wai Mami ce, wai.." Kuka ya hanata k'arasawa. Inna ta soma fusata. "Ki gayamin mana, me yafaru?" "Cewa sukayi zasu auramin Yaya Ma'aruf." Mamaki ya rufe inna, ta tsaya kyam tana dubanta. "Shi ne kikace musu me?" Ta turo baki. "Gudowa nayi don ni..." Marin da Inna ta shek'a mata ya haneta k'arasawa. Cikin tsananin tashin hankali take dubanta, kamar ba wannan Innar mai sanyin hali kuma mai tsananin nuna k'auna gareta ba. Kallo d'aya ta hangi tsananin 6acin ran dake kwance saman fuskarta. . "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!" Inna ta maimaita har sau biyu. Kawai sai kuma ta kece da kuka. "Kaico wannan rayuwa, ni Dije wane zamani muke ciki da d'an Adam ke saurin manta halacci? Da ace kinsan menene kawaici da girmamawa da lallai baki baro gidan 'yar uwata ba bisa wannan k'aramar maganar. Idan ban ta6a gayamiki ba yau ki sani, Yaya Fatima ko dukkan yarana ta nema na bata ta rik'esu zan iya, babu irin sadaukarwar da bazan iya yi dominta ba matuk'ar bai sa6awa addini ba. Ban taso naga mahaifiyata ba, Yaya Fatima nasani, bayan mahaifina, bani da wata gata sai ita. Idan nace zan tsaya gayamiki ire-iren abubuwa na kyautatawar da Yaya Fatima tayimin a rayuwa zamu iya cinye lokaci wanda bazan so hakan ba. Bazan so Yaya ta ankara da cewar nan kikazo ba, ban haifi d'iyar da zata k'i biyayya ga 'yar uwata ba, yanda banyi ba, to muddin ina raye ba zan aminta da d'ayanku ya aikata hakan ba. Kin bani kunya! Kin kuma shayar da ni mamaki kwarai, ko a mafarki banyi zaton 'yar uwata zata bijiro miki da wata buk'atar ba ki k'i amincewa. Bakisan fa dad'ina ba Bintu, Yaya Fatima ita ta yayeki, itace komai na gatanki. Tana sonki fiye da son da na nunamiki, a tunaninki, Yaya Fatima zatayi abinda zai cutar da ke da rayuwarki?" Inna ta k'arashe cikin sanyin murya. Ta ja majina "Tun kafin na 6ata miki rai nayi abinda ban ta6a yi gareki ba, ki tashi ki koma inda kika fito, idan kuma na isa da ke, ki amince da auren dan uwanki." Bintu ta mik'e jikinta a sanyaye, da alamu dai maganganun na Innarta sun shigeta. Har ta sanya kai zata fice, Inna ta kirawota ta mik'a mata dubu biyu akan ta k'ara kud'in mota. Ta k'ara da fad'in. "Ma'aruf yaro ne da yasan abinda yakeyi, yasan daraja da girman d'an adam. Miji ne wanda zakiyi alfahari da shi. In sha Allah ba zaki koka ba da kasancewarsa miji gareki. Ki koma ki yi biyayya ga uwarki mai k'aunarki. Kada ki sake ki sanarmata kinzo garinnan. Kije, Allah Yayi albarka ga rayuwarku, Ya shiga lamuranku. Ina miki murnar samun miji abin alfahari ga dukkan wacce ta sameshi." Bintu ta dubi innarta cikin zubar hawaye. Sai kuma ta juya a sanyaye ta gyara zaman jakar hannunta wacce ta fito da zummar zuwa makaranta ta yo Rano. Ta fice daga d'akin bata bi ko ta kan k'annenta ba dake yi mata magana ba ta bar gidan da sauri-saurinta. Don tayi sauri yasa ta hawan k'aramar mota peagout. A motar ma hawaye kawai takeyi. Gaba d'aya ta tsinci kanta cikin jin kunyar abinda ta so aikatawa Maminta mai k'aunarta da zuciya d'aya. Lallai ta kusa tafka kuskure babba, dad'in magabata kenan. Duk wanda a duniya ya rasa mai fad'a masa gaskiya shakka babu yana cikin garari na rayuwa. Tayi alk'awarin yin biyayya ga Abba da Mami, zata auri d'ansu ba wai don halinsa ba, saidai domin Allah. "To so fa? Kina sonsa?" Wata zuciyar ta jefomata tambayar da ta hautsina cikinta. Ai ita batasan ma soyayyar ba ballantana ta fahimci komai. Kodayake, a zamanin k'uruciyarta, Aisha ta ta6a shaida mata kad'an daga yanda kake gane ka fad'a son mutum. Fad'uwar gaba, da wani kallon kwayar idanu. Ta ja k'aramin tsaki. Shirme kenan. Tsoro ke kawo fad'uwar gaba kawai, shi kuma kallo, kawai idan mutum yana da kwarjini zaisa ka ji bazaka iya duban kwayar idanunsa sosai ba. Banda wannan, sauran kawai tunani ne na marasa aikin yi da suka yarda suka amince da soyayya har ma suke wahalar da rayuwarsu. A haka tayita tunane-tunanenta har dai suka shigo Kano, kai tsaye tashar unguwa uku suka isa. Mintuna arba'in ne suka kawosu. Ta duba agogon dake d'aure a fatar hannunta. K'arfe uku na rana har da mintuna. Ta fito ta nemi abin hawa tayi mishi kwatance. Adaidai junction na titin Zoo road, wajejan Oasis Bakery motarsu ta tsaya cikin go-slow. Ma'aruf yana daga gefensu batare da zato ko tsammani ba, a gefensa abokinsa ne Hashim suna ta6a hira. Juyowar da zaiyi ya hangeta cikin adaidaita, fuskarta babu walwala, hankalinta gaba d'aya yana ga kallon gabanta, yayi daidai da basu hannu da akayi wanda ya janyo rabuwarsu. Mamaki kwarai ya kamashi. Daga ina take? Wajen wa ta zo a wannan unguwar? Abin mamakin kenan, sam bata da k'awaye ballantana yayi zargin ko wajensu ta zo. Haka ya 6oye mamakinsa ya maida hankali ga abokinsa da ya dage ba shi shawarar yanda zai tafiyar da zaman aurensa da Bintu har ma ya ladabtar da ita. Shi dai Ma'aruf baice uffan ba. Tunaninsa gaba d'aya ya tafi ne ga ganin da ya yiwa Bintun yanzu daga hanyar da zata sadata da unguwa uku. To ko dai Rano ta je? Yayi kwafa a ransa kawai. . Rufa'i ya dubi Maminsu. "Nadai lura 'yarki batason muna kiranta da wannan sunan ko Aisha? Kuma ai girman kujerarta ne." Ya k'arashe yana maida dubansa ga Ma'aruf wanda yaji maganar k'aninnasa tamkar an soka mishi allura a k'ahon zuci. Ya maze kawai, babu damar ya bar musu falon saboda Mami ta nuna tanason magana da shi. Maganar Mami ta katse tunaninsa. "Nikam zan hanaka zuwa gidannan Rufa'i, ka girma amma bakasan ka girma ba baka da aiki sai tsokanarmin 'ya?" Suna dariya hakan ya yi daidai da fitowar Bintu daga kicin. Mami kirata. Ji tayi kamar ta d'ora hannu a ka ta fasa, meyasa Mami zatayi kiranta a gaban wannan mutumin? Kodayake gaba d'ayansu ma haushinsu takeji ganin yanda suke faman dariya wato su kenan duniyar dad'i take musu. Tana mai tur6une fuska ita wai shagwa6a ta k'araso ciki, kai tsaye jikin Mami ta kwanta. Ma'aruf bai ko k'ara kallonta ba tun daga kallon da yayi mata fitowarta daga kicin d'in. A ransa har tsaki yayi, yarinyar kowane shiga ma idan ta so yin abinta takeyi babu wata damuwa kan hakan. Haka kawai baisan dalilin jin sosuwar rai ba. "Zaki fara ko? Aure fa muke shirin yi miki." Cewar Rufa'i. Ina, tuni Bintu ta kai wuya, ai kuwa ta fashe da kuka. Mami ta rungume kafad'arta, nan ta shiga yiwa Rufa'i fad'a, tace ya bar mata gidanta bazai zo ya hana 'yarta sakewa ba. Rufa'i jiki yayi sanyi ganin Bintu na kuka, shi kam gogan, ba zaka gane komai ba a fuskarsa. K'arshe ma ya mik'e ya ja gefe yana amsa waya. Nan Rufa'i ya hau bata hakuri. "Haba tawan, kinsan bama haka dake. Ai ke tawa ce." Da ire-iren haka ya samo kanta. Ma'aruf na waya saidai jefi-jefi idanunsa kan sauka akan Bintu, har haushin kansa ya soma ji don bai ma san lokacin da yake kai duban gareta ba. Ganin zaman falon bazai mishi bane, yasa ya d'auki wayoyinsa. "Mami zan d'anyi wani aiki kafin wadannan su barmu muyi maganar." . Anan ne Bintu ta saci kallonsa. Yayi kyau kam don kyau, saidai mamakinta bai wuce yanda batajin soyayyarsa ba kamar yanda Aisha ke son Ashir d'in. To kodai wannan 6ace 6acen ran da takeyi shine so d'in? "Oho." Ta bawa kanta amsa. Ashe batasani ba har ya fice. Dariyarsu Aisha ta maidota cikin hankalinta. Ta mik'e zaune sosai cike da masifa tace. "Wai ke Aisha banason rashin mutunci fa, ai Yaya Rufa'in zai tafi ya barmu a gidan wallahi sai na rama." Aisha ta had'iye dariyarta sanin halin Bintun da son ramuwar gayya wanda babu kyau. Gashi kuma tayi rantsuwa, tasan Bintu bata wasa da rantsuwa. "Allah Ya huci zuciyar..." Kafin Aisha ta k'arashe, Rufa'i ya amshe. "Matar Yayanmu." Aisha ta dubeshi ita kam ba abinda ta so fad'a kenan ba. Dariya suka sanya, a fusace Bintu ta fice daga falon zuwa can baranda wajensu Sadauki. Mami ta nunawa Rufa'i k'ofa. "Tashi ka barmin gida." Ya mik'e yana dariya, daman ficewar zaiyi don a wannan karon ya daure ya bar Sadauki ya kwana." "Ayi hakuri Maminmu." Da haka ya fice bayan ya d'auki ragowar ruwan robar da ya sha. * * * Da daddare misalin tara. Bintu na kwance a d'akin Hanif, tana yi musu wasa tare da Sadauki, a rayuwa tanason yara. Idan Hanif ya kyalkyale da dariya itama ta dauki dariyar marar sauti saboda Mami ta haneta dariya mai k'ara ko yawan nan. Can kuma ta tsinci Sadauki a gefenta ya watso mata tambaya. "Anti, ai dai zaki tafi da mu gidan Uncle idan kunyi aure ko?" Ta dubi yaron da baifi shekaru biyu zuwa uku ba da mamaki. "Waya gayamaku zan je gidan Uncle?" "Daddy." Ta numfasa yayinda haushin Rufa'i ya k'ara kamata. Batace komai ba ta bagarar da zancen. Ga Ma'aruf kuwa, al'ardarsa ce baya kwanciya batare da ya zo ya ga d'ansa yayi mishi addu'a ba. Wannan na d'aya cikin burikan da Ma'unsa ta ci idan har ta haifi bebinta. Burinta duk dare ta tofe yaranta da addu'a kafin bacci. Har kishi ya kamashi alokacin da tayi wannan furucin shi a dole yafiso ta so shi sama da komai don ya lura tun samuwar cikinta magana d'aya biyu, to fa zata sanyo abinda zata haifa Hakan yasa shi k'ok'artawa wajen cikamata burinta, duk kuwa da cewar wani abin sai mace. . Yayi sallama batare da ko a ka ya kawo zai isketa a d'akin ba. Ai kuwa sukayi ido hud'u tana kwance ta d'ora Hanif saman k'afafunta tana mishi wasa. Doguwar riga ce mai kauri ta bacci a jikinta. Kan babu kallabi. Kusan lokaci guda suka kauda kansu. Ta ajiye Hanif saman gado, da gudu ya rarrafa ganin zai fad'o yasa Ma'aruf d'aukarsa. Bintu ta mik'e zata fita, ya dakatar da ita ta hanyar jifanta da tambaya. "Ina Atine ne?" Ciki-ciki ta amsa. "Ta je kicin dafa fidar Hanif." Tana k'ok'arin sa kai ta fice ya k'ara tsaidata. "Ke zo nan." Ranta yayi wani bak'i, ita fa ko ganinsa ma batason yi, mugu da shi. Saidai dolenta ta dawo baya batare da ta zauna ba. Haushin kansa ya ji a fusace ya soma magana. "Wato tun yanzu raini ya gilma tsakaninmu, banda kin raina mutane ya zanyi kiranki ki tsayamin a ka?" Ta had'iyi miyau na takaici kafin ta zauna. Yayi shiru yana duban Hanif kafin yayi kwafa a fili ya dubeta. "Shine kika cewa su Abba ni kikeso ko?" Ta zaro ido ta dubeshi, idanunta ya kawo ruwa. "Lallai ma, wallahi ni ban ta6a ma sonka ba, ni kawai..." Ta soma hawaye. Ya harareta, yarinya sai tsabar iyayi da yarinta. "Idan ba ke kika nunamusu kin amince da aurena ba, ta yaya zasuyi tunanin had'amu? Wai ke bakiga irin 'yan matana ba ne? Kin ta6a cin karo da mai shekarunki?" Ya d'an fasali kafin ya cigaba da magana bayan ya lalla6a Sadauki ya bar d'akin gudun kada ya kwashi rahoto don lura da yayi yaron akwai wayo. "Me kika sani a aure ne? Bana tunanin ko girki da gyaran gida kin iya don ban ta6a ganin kina yin d'ayansu ba." Sai kuma ya d'an ja tsaki. "Kin d'ebo ruwan dafa kanki Bintu, ina tausayinki a gidana. Sai na kunce miki wad'annan notinan na kanki na saita miki su. Sannan daga yau na k'ara ganinki cikin shiga irin na d'azu sai na 6allaki, hakanan na kafa miki dokar d'ankwali, koda wasa na k'ara cin karo dake babu d'ankwali zaki d'and'ana kalar azabata." Ta mik'e ta goge fuskarta, gaba d'aya ta gama k'uluwa. Har zata fice sai kuma tayi tunani, ai idan ta barshi batare da ta ya6a mishi ba to fa bazata ji sanyi ba, gwara ta dunga ramawa kafin azo lokacin da ya riga ya zama miji gareta. Hakan yasa ta dawo da baya. Ya dubeta, ta kauda kanta gefe, ita ko kusa batason yawaita kallon kwayar idanunsa. Ta tsuke baki wanda ta saba yi idan zatayi rashin ta idon. "Dad'in abin dai nima k'ak'abamin kai akayi ba sonka nakeyi ba. Ni da ace zaka taimaka ka samu su Abba kace bana sonka da nafi kowa jin dad'i. Kaima kasan nafi k'arfinka. Maza nawa ne suke sona don ma soyayyar ba damuna tayi ba? Yanda kake shiryamin uk'ubobi nima haka nake shiryamaka don wallahi bana sonka, mugunta kawai kasani ba komai..." Mik'ewar da ta ga yayi ya sanyata fita a guje. Ran Ma'aruf ya 6aci ainun, tunda yake bayajin akwai macen da ta ta6a gasa mishi maganganu irin haka. Shakka babu Bintu ta k'ara rura wutar k'iyayyarta a zuciyarsa. Sai kuma alokacin ya k'ara jin wani kwarin gwuiwar aurenta, acewarsa, wannan kad'ai ne hanyar k'untatawa rayuwarta. Ya d'auki d'ansa ya fice zuwa sashensa. Da gudu ita kuma ta k'arasa d'akinsu. Anan ta tarar da Aisha dake faman laluben wayarta. A firgice Aishar ta dubeta. "Lafiya?" Bintu ta zauna bakin gado. "Oho. Kekuma lafiya kika wani rikita mana d'akin?" Aisha ta ja tsaki. "Yauwa, bakiga wayata ba don Allah? Nasan Ashir yanata kirana bai samu ba." Bintu ranta yayi fari k'al. A fili kuwa ta ta6e baki. "D'aukar miki waya nakeyi? Bangani ba." "Bani aron naki nayi kiransa." Ta harareta "Kud'ina bana banza bane." Aisha ta ji haushi. Haka ta gama lalubenta, Bintu ta zura wayarta a cikin filo bayan ta kasheta ta kwanta ta rufe idanu. A ranta tana fad'in. "Yi iyakar bincikenki. Gobe kya k'ara kirana Matar Yaya." Tun tana sauraron shige da ficenta, har baccin gaske yayi awon gaba da ita. Sai a washegari ta damk'a mata da zasu fice zuwa makaranta. Bintu bata k'ara yarda sunyi arba da Ma'aruf ba, saidai fa acewarta ba tsoro bane! * * *
0 comments:
Post a Comment