BINTU Part 004
BINTU Part 004 . Rufa'i ya dubi Maminsu. "Nadai lura 'yarki batason muna kiranta da wannan sunan ko Aisha? Kuma ai girman kujerarta ne." Ya k'arashe yana maida dubansa ga Ma'aruf wanda yaji maganar k'aninnasa tamkar an soka mishi allura a k'ahon zuci. Ya maze kawai, babu damar ya bar musu falon saboda Mami ta nuna tanason magana da shi. Maganar Mami ta katse tunaninsa. "Nikam zan hanaka zuwa gidannan Rufa'i, ka girma amma bakasan ka girma ba baka da aiki sai tsokanarmin 'ya?" Suna dariya hakan ya yi daidai da fitowar Bintu daga kicin. Mami kirata. Ji tayi kamar ta d'ora hannu a ka ta fasa, meyasa Mami zatayi kiranta a gaban wannan mutumin? Kodayake gaba d'ayansu ma haushinsu takeji ganin yanda suke faman dariya wato su kenan duniyar dad'i take musu. Tana mai tur6une fuska ita wai shagwa6a ta k'araso ciki, kai tsaye jikin Mami ta kwanta. Ma'aruf bai ko k'ara kallonta ba tun daga kallon da yayi mata fitowarta daga kicin d'in. A ransa har tsaki yayi, yarinyar kowane shiga ma idan ta so yin abinta takeyi babu wata damuwa kan hakan. Haka kawai baisan dalilin jin sosuwar rai ba. "Zaki fara ko? Aure fa muke shirin yi miki." Cewar Rufa'i. Ina, tuni Bintu ta kai wuya, ai kuwa ta fashe da kuka. Mami ta rungume kafad'arta, nan ta shiga yiwa Rufa'i fad'a, tace ya bar mata gidanta bazai zo ya hana 'yarta sakewa ba. Rufa'i jiki yayi sanyi ganin Bintu na kuka, shi kam gogan, ba zaka gane komai ba a fuskarsa. K'arshe ma ya mik'e ya ja gefe yana amsa waya. Nan Rufa'i ya hau bata hakuri. "Haba tawan, kinsan bama haka dake. Ai ke tawa ce." Da ire-iren haka ya samo kanta. Ma'aruf na waya saidai jefi-jefi idanunsa kan sauka akan Bintu, har haushin kansa ya soma ji don bai ma san lokacin da yake kai duban gareta ba. Ganin zaman falon bazai mishi bane, yasa ya d'auki wayoyinsa. . "Mami zan d'anyi wani aiki kafin wadannan su barmu muyi maganar." Anan ne Bintu ta saci kallonsa. Yayi kyau kam don kyau, saidai mamakinta bai wuce yanda batajin soyayyarsa ba kamar yanda Aisha ke son Ashir d'in. To kodai wannan 6ace 6acen ran da takeyi shine so d'in? "Oho." Ta bawa kanta amsa. Ashe batasani ba har ya fice. Dariyarsu Aisha ta maidota cikin hankalinta. Ta mik'e zaune sosai cike da masifa tace. "Wai ke Aisha banason rashin mutunci fa, ai Yaya Rufa'in zai tafi ya barmu a gidan wallahi sai na rama." Aisha ta had'iye dariyarta sanin halin Bintun da son ramuwar gayya wanda babu kyau. Gashi kuma tayi rantsuwa, tasan Bintu bata wasa da rantsuwa. "Allah Ya huci zuciyar..." Kafin Aisha ta k'arashe, Rufa'i ya amshe. "Matar Yayanmu." Aisha ta dubeshi ita kam ba abinda ta so fad'a kenan ba. Dariya suka sanya, a fusace Bintu ta fice daga falon zuwa can baranda wajensu Sadauki. Mami ta nunawa Rufa'i k'ofa. "Tashi ka barmin gida." Ya mik'e yana dariya, daman ficewar zaiyi don a wannan karon ya daure ya bar Sadauki ya kwana." "Ayi hakuri Maminmu." Da haka ya fice bayan ya d'auki ragowar ruwan robar da ya sha. * * * Da daddare misalin tara. Bintu na kwance a d'akin Hanif, tana yi musu wasa tare da Sadauki, a rayuwa tanason yara. Idan Hanif ya kyalkyale da dariya itama ta dauki dariyar marar sauti saboda Mami ta haneta dariya mai k'ara ko yawan nan. Can kuma ta tsinci Sadauki a gefenta ya watso mata tambaya. "Anti, ai dai zaki tafi da mu gidan Uncle idan kunyi aure ko?" Ta dubi yaron da baifi shekaru biyu zuwa uku ba da mamaki. "Waya gayamaku zan je gidan Uncle?" "Daddy." Ta numfasa yayinda haushin Rufa'i ya k'ara kamata. Batace komai ba ta bagarar da zancen. Ga Ma'aruf kuwa, al'ardarsa ce baya kwanciya batare da ya zo ya ga d'ansa yayi mishi addu'a ba. Wannan na d'aya cikin burikan da Ma'unsa ta ci idan har ta haifi bebinta. Burinta duk dare ta tofe yaranta da addu'a kafin bacci. Har kishi ya kamashi alokacin da tayi wannan furucin shi a dole yafiso ta so shi sama da komai don ya lura tun samuwar cikinta magana d'aya biyu, to fa zata sanyo abinda zata haifa Hakan yasa shi k'ok'artawa wajen cikamata burinta, duk kuwa da cewar wani abin sai mace. Yayi sallama batare da ko a ka ya kawo zai isketa a d'akin ba. Ai kuwa sukayi ido hud'u tana kwance ta d'ora Hanif saman k'afafunta tana mishi wasa. Doguwar riga ce mai kauri ta bacci a jikinta. Kan babu kallabi. Kusan lokaci guda suka kauda kansu. Ta ajiye Hanif saman gado, da gudu ya rarrafa ganin zai fad'o yasa Ma'aruf d'aukarsa. Bintu ta mik'e zata fita, ya dakatar da ita ta hanyar jifanta da tambaya. "Ina Atine ne?" Ciki-ciki ta amsa. "Ta je kicin dafa fidar Hanif." Tana k'ok'arin sa kai ta fice ya k'ara tsaidata. "Ke zo nan." . Ranta yayi wani bak'i, ita fa ko ganinsa ma batason yi, mugu da shi. Saidai dolenta ta dawo baya batare da ta zauna ba. Haushin kansa ya ji a fusace ya soma magana. "Wato tun yanzu raini ya gilma tsakaninmu, banda kin raina mutane ya zanyi kiranki ki tsayamin a ka?" Ta had'iyi miyau na takaici kafin ta zauna. Yayi shiru yana duban Hanif kafin yayi kwafa a fili ya dubeta. "Shine kika cewa su Abba ni kikeso ko?" Ta zaro ido ta dubeshi, idanunta ya kawo ruwa. "Lallai ma, wallahi ni ban ta6a ma sonka ba, ni kawai..." Ta soma hawaye. Ya harareta, yarinya sai tsabar iyayi da yarinta. "Idan ba ke kika nunamusu kin amince da aurena ba, ta yaya zasuyi tunanin had'amu? Wai ke bakiga irin 'yan matana ba ne? Kin ta6a cin karo da mai shekarunki?" Ya d'an fasali kafin ya cigaba da magana bayan ya lalla6a Sadauki ya bar d'akin gudun kada ya kwashi rahoto don lura da yayi yaron akwai wayo. "Me kika sani a aure ne? Bana tunanin ko girki da gyaran gida kin iya don ban ta6a ganin kina yin d'ayansu ba." Sai kuma ya d'an ja tsaki. "Kin d'ebo ruwan dafa kanki Bintu, ina tausayinki a gidana. Sai na kunce miki wad'annan notinan na kanki na saita miki su. Sannan daga yau na k'ara ganinki cikin shiga irin na d'azu sai na 6allaki, hakanan na kafa miki dokar d'ankwali, koda wasa na k'ara cin karo dake babu d'ankwali zaki d'and'ana kalar azabata." Ta mik'e ta goge fuskarta, gaba d'aya ta gama k'uluwa. Har zata fice sai kuma tayi tunani, ai idan ta barshi batare da ta ya6a mishi ba to fa bazata ji sanyi ba, gwara ta dunga ramawa kafin azo lokacin da ya riga ya zama miji gareta. Hakan yasa ta dawo da baya. Ya dubeta, ta kauda kanta gefe, ita ko kusa batason yawaita kallon kwayar idanunsa. Ta tsuke baki wanda ta saba yi idan zatayi rashin ta idon. "Dad'in abin dai nima k'ak'abamin kai akayi ba sonka nakeyi ba. Ni da ace zaka taimaka ka samu su Abba kace bana sonka da nafi kowa jin dad'i. Kaima kasan nafi k'arfinka. Maza nawa ne suke sona don ma soyayyar ba damuna tayi ba? Yanda kake shiryamin uk'ubobi nima haka nake shiryamaka don wallahi bana sonka, mugunta kawai kasani ba komai..." Mik'ewar da ta ga yayi ya sanyata fita a guje. Ran Ma'aruf ya 6aci ainun, tunda yake bayajin akwai macen da ta ta6a gasa mishi maganganu irin haka. Shakka babu Bintu ta k'ara rura wutar k'iyayyarta a zuciyarsa. Sai kuma alokacin ya k'ara jin wani kwarin gwuiwar aurenta, acewarsa, wannan kad'ai ne hanyar k'untatawa rayuwarta. Ya d'auki d'ansa ya fice zuwa sashensa. Da gudu ita kuma ta k'arasa d'akinsu. Anan ta tarar da Aisha dake faman laluben wayarta. A firgice Aishar ta dubeta. "Lafiya?" Bintu ta zauna bakin gado. "Oho. Kekuma lafiya kika wani rikita mana d'akin?" Aisha ta ja tsaki. "Yauwa, bakiga wayata ba don Allah? Nasan Ashir yanata kirana bai samu ba." Bintu ranta yayi fari k'al. A fili kuwa ta ta6e baki. "D'aukar miki waya nakeyi? Bangani ba." "Bani aron naki nayi kiransa." Ta harareta "Kud'ina bana banza bane." Aisha ta ji haushi. Haka ta gama lalubenta, Bintu ta zura wayarta a cikin filo bayan ta kasheta ta kwanta ta rufe idanu. A ranta tana fad'in. "Yi iyakar bincikenki. Gobe kya k'ara kirana Matar Yaya." Tun tana sauraron shige da ficenta, har baccin gaske yayi awon gaba da ita. Sai a washegari ta damk'a mata da zasu fice zuwa makaranta. Bintu bata k'ara yarda sunyi arba da Ma'aruf ba, saidai fa acewarta ba tsoro bane! * * * Bayan Wata d'aya da sati biyu....!! . Biki fa ya kankama, sai shirye-shirye kawai mutanen gidan keyi. Mami babu zama, itace can itace nan. Bintu kallon kowa kawai takeyi da ido, gaba d'aya ta rame saboda bata ta6a kawowa a ranta zatayi aure nan kusa ba. Tuni aka kammala had'a lefe da kayan kunshi da komai da aka sani na al'ada aka rankaya Rano. To abu na gida, babu wanda bai taya Fatima Bintu murna ba, a k'arshe Inna da kanta tace a mayar can Kano, Mami ai itace uwar amarya ita kam ango ne na wajenta. Haka da dariya da komai 'yan uwan junan suka rabu. Ga ango da amaryar kuwa babu wanda zai saurin d'ago wani abu tsakaninsu. Aisha dai tuni ta harbo Bintu, saidai ta san komai zai wuce bayan aure. Babu abinda yafi k'ular da Bintu kamar yanda Ma'aruf ya soma nunawa lallai dagaske sonta yakeyi agaban 'yan uwa. Ta k'ulu iyakar k'uluwa ta tabbatar sabon salo ne ya d'auko domin k'untata mata ga shi a wannan ga6ar ta rasa abin da zai zame mata ramuwar gayya. Ganin bata da mafita yasa ta ke k'auracewa duk wajen da yake. Ta yankewa kanta shiga d'akin Hanif, hakanan ta rage zama falon Mami saidai ta shige k'uryar d'akinta tayi zamanta. Ana sauran sati bikin ne, aka soma yiwa Bintu gyaran jiki, Mami ta tilasta ta sanya hijab da nik'ab idan zataje makaranta har ma da safa saboda kada rana ta 6ata gyaran da akeyi. Ana sauran kwana uku ne kuma ta daina zuwa makarantar acewar Mami ta bari a mik'ata d'akinta tunda ba jarabawa sukeyi ba. Ana gobe za'a soma biki, suna zaune a d'akinsu ita da Aisha, da Hajara harma da Jalila da Atika(yanuwansu wadanda suke sa'anni, suna zama a Rano). Amarya Bintu ansha lalle da kitso siri-siri. Hajara ta kama baki. "Kai nifa nafi mamakin ramar da yarinyar nan keyi, daman akwai abinda zai ladabtar da Bintu haka? Kamar ba wannan shak'iyiyar ba." Bintu ta kallera kawai saidai batace uffan ba. Su Aisha suka kwashe da dariya. Atika dake cin meatpie ta dubeta. "Wallahi ni kunsan me yafi burgeni? Bai wuce yanda naga Yaya Ma'aruf ke nan nan da ita ba. Ku duba kugani, yana ganinta zakuga ya soma zolayarta da amaryata amaryata. Hum, wannan a gidansu akwai kallo." Bintu ta harareta, me zasuyi ba dariya ba. Ta ja tsaki, kamar tayi magana, sai kuma ta fasa. "Yi maganarki, yar duniyar k'arya kinaso kina kaiwa kasuwa. Kodayake kin gama ciki bakin ke bakya soyayya." Cewar Jalila. Tsam ta mik'e ta koma wajensu Mami da iyayensu Atika wadanda suka kasance, 'ya'ya ga kishiyar uwar su Mamin. Nan kuwa babu mai tsokanarta saima hirarsu da sukeyi. Washegari aka soma shagalin biki. Can na hango masu aikin abinci, ciki har da Fauza ga Ummu Abdool a gefenta suna ta juya farar shinkafa a k'atin warmer. A gefe ga dangin Taskira suna ta wanke kwanukan rabo. Can kuwa, Su hanne da Batool kai harma da Sholingaye ke faman kula da miya. Can na hango Bingel da Faharty na fad'a akan k'ashi ganin Bayarabiya Asal mai d'aukar bidiyo ta nufo wajensu ne ya sanyasu nutsuwa. Kai group na matan aure suma sunyi gefe suna hirar yanda zata kaya a gidan amarya Bintu wacce suka gama had'ata suka suburbud'a mata lakcoci acan falon Mami. Bintu ta sha kuka yanda manyan nan suka sanyata a tsaka suna faman yi mata maganganun da suka girmi kunnuwanta. "Nidai gaskiya banason aure." Su Aisha suka kyalkyale da dariyar jin abinda ya fito daga bakinta. Ango kuwa a yanzu ya share komai, ya lura a hakan da yake nunawa Bintu son k'arya idan sun ke6e kuma ya guma mata rashin mutunci. Washegari misalin k'arfe goma na safe aka d'aura auren Fatima Bintu Muhammad da Ma'aruf Abdullahi...!!! . Idan kaga Bintu, ba zaka ce itace amaryar ba domin kuwa tun safe take kwance saman gadon Mami, daga ita sai Sadauki don su Aisha sun hanata zaman d'akin da zolayarsu, wannan yasa Mami ta lalla6ata zuwa d'akinta. Har kuwa aka d'aura auren bata da niyyar motsawa daga saman gadon. Su Aisha sunason zuwa yi mata bud'i saidai Mami ta yi musu jan ido akan shiga inda take. Kuka sosai takeyi, saida Mami ta yi da gaske kafin ta shawo kan Bintu. Babban abinda kuwa yasa jikin Bintun sanyi bai wuce tambayar da Mamin ta jefomata ba na cewa. "Bintuna kodai bakyason yaron nan tilastawa zuciyarki kikayi?" Wannan ne silar daina zubar hawayenta kafin ta nunawa Mami ba haka bane tana kaunarsa. Bayan ta yi wankanta a d'akin Mami. Mami ta turo Hajara da Aisha domin taimakawa wajen shiryata kafin ango da abokansa su shigo bayan ta gargad'esu akan koda wasa kada su tsokaneta. Aisha ta fente mata fuskarta. Yayinda Hajara ta fiddo mata abin buk'ata. Bintu ta fito tayi kyau fiye da zato, ta had'e cikin shadda fara mai golden surfani. "Masha Allah!" Shine kad'ai abinda ke fitowa daga bakin Aisha da Hajara. Bintu dai ta bisu da ido kawai, ita kanta tasan ta had'u k'arshe. Fatarta ta k'ara murjewa tayi haske sakamakon gyaran da ta sha a kwanakin nan. "Wai ina amaryar ne?" Cewar wata gwaggonsu ta Rano lokacin da ta sanyo kai d'akin tare da sauran tsoffin. Har tsakar kan Bintu ta iso ta sakar mata bud'a. "Ayuiririii!" Haka sukayi mata ca, banda haushinsu babu abinda takeji. Suka ja ta har tsakar falon Mami aka zaunar da ita saman kujera, tuni ta soma ruwan hawaye Aisha ta taimakawa wajen sharemata har itama tana tayata hawayen. Bata ta6a jin tausayin 'yar uwartata ba akan lamarin auren sai yanzu, da kuma tunanin rabuwar da zasuyi, daga yau shikenan bazata k'ara kwana tare da ita ba. Babu abinda ta tunano sai shak'uwarsu da yanda take rayamusu gidan da wasa da dariyarta. Allah Sarki rayuwa. Can kuma sukaji shewar ta juya baya. Ana fad'in ga ango! Ga ango! Har da abokansa kuwa. Yana sanye cikin dakakkiyar shadda fara k'al, sai shek'i yakeyi. Lallausan sajensa ya kwanta luf-luf. Ya had'u har ya gaji, kallo d'aya zakayi kwayar idanunsa ka fahimci lallai ya yi kuka sakamakon kad'awar da sukayi, ba kuwa don komai ba sai don tunano matarsa wacce k'aunarta ko kad'an bai ta6a raguwa ba a zuciyarsa. A yau da aka d'aura aurensa da Fatima Bintu, sai ya ji zuciyarsa tamkar anyi mishi fami. Haka suka kammala gaisawa da dangi, yana shirin ficewa wata abokiyar wasanshi ta janyoshi. "A'a ango ya zakayi mana haka. Zo nan ka zauna sai fa anyi muku hoton tarihi." Wajen akayi dariya. Bintu zata mik'e sai kuma wata ta maidata ta zaunar. . "Zauna, ina zaki gudu? Ke kuma matsa kin zauna kina taya 6era 6ari, kema muna dab da aurar da ke." Aisha ta matsa tana k'unk'uni. Daidai lokacin kuma aka zaunar da Ma'aruf a gefenta. Kusan lokaci guda gabansu ya fad'i, k'amshin turaren kowannensu ya bugi hancinsu. Ta muskuta ta ja gefe cike da jin haushin wad'annan matan. Abin haushi suka bud'emata lullu6i wai za'ayi hoto. Dakyar ta bari akayi d'aya duk ranta a k'untace kafin da gudunta ta kutsa ta fad'a d'akin Hanif kasancewar yafi kusa da inda take. Ma'aruf ko murmushi kawai yayi wanda shi kad'ai yasan ma'anarsa. Haka akayita hotuna da ango da abokansa. K'arshe akayimai da d'ansa fin kala biyar. Bayan Magrib kuwa aka soma shirin tafiya Dinner party wanda Mami ta shirya. Anan kuwa Bintu bata bayar da matsala ba, sosai ta ji fad'an Maminta. Ta gama had'ewa cikin gown lace ne mai adon golden da fari. Ta d'ora golden head sai 'yar jaka had'e da takalminsa da na mayafi. Su Aisha da sauran abokan karatunsu na sakandire da jami'a sai 'yan uwa sun yi ankonsu suma sun fito d'as cikin golden lace, yayinda mazan sukayi ankon farin boyel. Mami ta shigo ta d'ago ha6ar Bintu tana dubanta. Murmushi ta saki. "Masha Allah, Allah Ya kauda idanun mak'iya akanki my daughter. Kinyi kyau, sai ki k'ara kame kanki banason rawa kinji ko?" Bintu ta amsa kawai da to. Ina ta ga wani dama ta yin rawa a auren da ba wani so da d'aukinsa take ba? Aisha ce tayi mata rakiya har motar angon. Ta saci kallon motar. Baka ganin wanda ke ciki, hakan yasa ta maida kanta k'asa. Kafin su k'arasa Bintu ta ja tsaki. "Wallahi taraku nakeyi daga ke har su Anti Hajaran, zan rama d'aya bayan d'aya." Jin abinda ta furta yasa Aisha darawa. "Ashe fa d'an iska d'an iska ne ko? Oho dai, kafin kiyi mana ke muka soma yiwa." Bintu ta yi kwafa. "Lokaci." Daga haka bata k'ara cewa uffan ba tana jin dariyar Aisha. Aisha ta bud'e mata k'ofar ta shiga, wani sanyi ya ratsata had'e da k'amshi. Ta dubi gefenta, ajiyar zuciya ta saki ta kauda fuskarta. Ai 6ata lokaci ne ma idan tace yayi kyau, daman kyakkyawan ne. Saidai a yau kowa ya ganshi zai k'ara son ya k'ara kalla banda ita Bintun. Acewar zuciyarta kenan. Muryar Hashim dake zaune wajen direba ya katse tunaninta. "Ina gaisuwa amarsu." Ta daure ta gaisheshi cikin sassanyar muryar da ya ba shi mamaki, ya saba jin Bintu da karad'i, bata da wani sanyi. Ya dai basar ta hanyar dariya kafin ya amsa ya had'a da fatan alheri. Bata amsa ba, alokacin kuma ya ja motar. Shiru ya biyo baya. Can kuma ta ji wayarta ta d'auki k'ara. Ta ciro ta duba. Text message ne daga unknown number. Ta bud'o ta karanta. "Kin ci nasarar zama matata, ina tayaki murna, fatan baki mance dukkan maganganun da na yi miki a baya ba?" Ta dubeshi kad'an bayan ta kammala, wani shu'umin murmushi ya sakarmata mai k'ara sanya yanmata matowa a kansa. Ta kauda kanta, abin da ya ba shi mamaki ganin batayi niyyar ba shi amsa ba, k'arshe ma ta kashe wayar gaba d'aya ta jefa jaka. Hashim ya danna rediyo nan kuma kid'a ya soma tashi jin da yayi shirun na motar ya isa. Haka har suka isa babu wanda ya k'ara cewa wani uffan sai shi da Hashim da ke d'an ta6a hira. , Sun isa har dab da k'ofar shiga hall d'in sannan Hashim ya faka. "Ku jira kar ku fito, ina zuwa." Ya fita daga motar. Ma'aruf ya dubeta, ba laifi kam ta yi kyau kamar ba wacce ya sani ba, duk kuwa da cewar ya ga wadanda suka fita a kyawun. Ya maida kansa ga kallon wajen. Yayi daidai itama ta juyo tana dubansa. Ji fa, namiji har namiji, amma zuciyarsa banda mugunta babu komai ciki. "Jikina ya bani ana kallona." Ta kauda kanta, a karo na farko tayi niyyar maida mishi martani. "Ni me zan kalla a fuskarsa wanda babu shi a wajen..." Bata kai ga k'arasawa ba sakamakon fisgo kafad'arta da yayi, wannan ya sanya fuskokinsu suka kusanci juna har suna jin hucin numfashinsu. Cikin kakkausar murya kuma mai k'aramin sauti ya soma magana. "Ki bar gangancin gayamin dukkan wasu kalmomi da suka fito daga bakinki, idan kuwa bazaki kula ba zan ladabtar da bakinki wallahi." Ya saki kafad'arta, ta matsa da sauri tuni ta soma k'ok'arin zubda hawaye. Ganin haka ya k'ara magana. "Lallai kukanki na nufin na ci galaba akanki tun kafin a je ko'ina." Jin abinda yace ya sanyata azamar share fuskarta. "Ai ba kuka nakeyi ba. Kuma ma.." Ta had'iye abinda tayi niyyar cewa tunano da abinda ya fad'amata a yanzun. Gane hakan da yayi ne, ya sanyashi murmusawa kawai baice uffan ba. A haka kuma sai ga Aisha tace su fito. Ashe kan 'yan matan da zasu shigar da su aka had'o. Can na hango dangin Rof na whatsapp a sun jeru suma babu wacce batayi anko ba, wannan ne dalilin da yasa dole aka barsu suka shiga jerin masu shigar da amarya. Bintu ta fito, har aka zagayo da ita angon bai da niyyar fitowa. Shi kam hawayensa ya tsaya d'aukewa. Babu wacce ya tuno sai matarsa Ma'u. Masoyiya agareshi, bayajin har abada zai manceta. Allah Sarki rayuwa. Hashim na shirin kwankwasa masa sai ya bud'|e ya zuro k'afafunsa ya fito. Bintu takaici ya hanata ma dubansa, idan yana wani yangar sai kace mace. Ita fa ta lura ajinsa har yayi yawa. Tayi kwafa a hankali kawai. Ba tayi aune ba, sai jin tattausan hannunsa tayi a cikin nata, bai tsaya a rik'on ba har saida ya sark'esu wuri guda. Ta d'aga kai ta dubeshi, sai hasken flasher suka gani, tuni ya soma tafiya ta bishi cikin wani irin yanayi na sanyin jiki da rik'on ya janyomusu duka. A haka suke taku. Da ka gansu sai kayi zaton wasu taurari masu haske fiye da sauran. , Shi Ma'aruf yana takunsa cike da jin isa da k'asaitar shi d'in kyakkyawa ne kuma mai aji kwarai da kowace mace zataso ya kasance abokin rayuwarta. Ga Bintu kuwa, yangar daman ta zamto jiki agareta, haka tafiyarta take saidai ta yau ta bambanta da sauran. Sai wani shan k'amshi takeyi bata ko kallon mutane sosai ballantana ta damu da masu d'aukarsu hotuna. A haka har suka k'arasa mazauninsu. Sai lokacin ta soma k'ok'arin zame hannunta ganin ba shi da niyyar sakinta. Shaf shima ya mance da wai hannun Bintu ya ke rik'e da, ya saki hannun bayan ya kalleta kad'an kawai. Nan aka soma gudanar da shagalin biki, can na hango 'yan matan Zauren Karatu da DM har ma da Classic Ladies suna faman cashewa abinsu, kana ganinsu kasan basu da wata matsala asalima murna kwarai sukeyi game da wannan aure na Ma'aruf da Bintu. Bintu ta ja tsaki, wanda ya dira a kunnen Ma'aruf. Ya matso saitin kunnenta yanda zata ji abinda zai ce. "Kika k'ara tsakin nan tsaka zaki zama." Ta matsa gami da dubansa, ya d'aga mata gira kad'an da murmushin k'ularwa. Ta kauda kanta kawai tana mai tsuke bakin. Can kuma aka tsaida kid'an, akayi addu'ar bud'e taro, kafin kuma a soma hada-hadar cin abinci. Har aka kammala babu abinda Bintu ta sanya a bakinta sai lemo. Shi kuwa gogan babu laifi ya d'an ci abincinsa. A k'arshe aka umarci Ango da amarya su fito domin yanka (cake), ya soma mik'ewa, abin mamaki ya k'ara mik'o mata hannunsa wanda ba k'aramin burge mutanen wajen sukayi. Ga iyalan Mami kuwa, su Rufa'i da Aisha abin ya basu mamaki matuk'a, haka suma su Atine su d'an dolo da suka san rashin d'asawar Bintu da yayanta. Ta dubeshi, kallon idanunsa ne bataso, sanyaya jikinta yakeyi. "Haba Amarya kina yanga, daure ki mik'awa angonki hannu." Cewar mai gabatarwar wanda ya bawa sauran jama'a dariya. Hum! Wai sai ga Bintu ta ji kunya. Ta d'aga hannunta ta d'ora a saman nasa ranta babu dad'i saidai jikin yayi sanyi. Ta mik'e suka soma saukowa. Mami ranta yayi sanyi matuk'a, addu'arta bai wuce yanda ma'auratan nan suka had'u ba, Allah Yasa aurensu yayi albarka. Adda Ummi ce mai mik'a wuk'ar yanka cake, Ma'aruf ya kar6a. Bayan ya yanko ya sanyamata a baki, aka d'au sowa. Itama dakyar ta iya sanyamishi a baki bayan ta daurewa zuciyarta, abinda ya bak'anta mata bai wuce yanda har ya k'ara wani rik'o hannunnata ba. Bayan sun kammala aka tsayar dasu, cikin fili, nan aka soma zuba musu ruwan kud'i. Can na hango matasan DM mazansu da matansu suna 6arin ruwan kud'i. A haka aka tashi amarya ta dage Maminta zata bi. Ba takura kuwa, Mami ta ja ta zuwa motarta suka tafi tare da wasu k'annen Mamin. Washegari aka gabatat da lakca, inda matan DDM da Khairin Nisa'i suka jagoranta. Da yamma aka shirya amarya za'a kai ta gidan mijinta...! . Zo kaga kuka da turjiya wajen Bintu. Ta rik'e Mami da Aisha gam! Har ta kusa sanya Mami kuka, Aisha kuwa ai ba'a magana. Abokiyar hirarta zata tafi ta barta. Dakyar Mami ta ja ta ta sanyata a mota bayan ta k'ara mata da nasiharta akan ta Abba da mahaifinta. Har aka isa gidan kuka kawai takeyi. Haka Bintu tana ji tana gani kowa ya watse ya barta, ko k'awayen amaryar wadanda rabinsu 'yan uwana babu wanda aka bari bisa fad'in Mami. Jin shiru yasa ta bud'e idanunta. D'akin Asma'u a baya kenan wanda ya yau yake mallakinta. Anyi fenti mai kyau, kayanta masu tsada. Ta numfasa, jin tsayuwar mota yasa ta mik'ewa da azama ta rufe k'ofar da muk'ulli. A fili ta furta. "Naga abokan da zaka tattaro min su cikamin kunne da hayaniya." . To shima Ma'aruf d'in babu wanda ya janyo rakiya sai Hashim wanda shi ya tilasta masa suka biya siyo KAZAR AMARCI da sauran kayan sha. Da sallama suka sanyo kai falon. Daman basu tsammaci ganin kowa ba a falon, don haka Hashim ya nemi wuri ya zauna. Ma'aruf ya harareshi ganin hakan. "To me kuma kake nema?" Hashim ya sanya dariya. "Ikon Allah, ka manta bisa al'ada abokan ango ke rakiya suma su tofa nasu addu'ar?" Ma'aruf wanda shima ya nemi wajen zama, ya cire hularsa ya yamutse fuska. "Look, ka tilastamin mun siyomata tarkace, ba kuma zan d'auki wani sabon abu ba bayan wannan kaji ko? Baruwana da wata al'ada. Malam ka tashi ka je Sally tana jiranka." Hashim tun yana d'aukar abin wasa don kuwa a auren Ma'aruf na farko, har Ma'un ya kawo falon idanunta a rufe ya yi musu 'yar nasiha. Ganin haka ya watsar, ya bishi da nasiha daga nan kuma ya mik'e. "To ai shikenan, mai yiwuwa kishi ke damunka. Bari na tafi, Allah Ya sanya alheri. A kuma ji tsoron Allah dai. Atoh." Wani kallo kawai ya bishi da shi baice uffan ba. Ya mik'e yayi mishi rakiya har wajen motarsa. Bintu tana jin dukkan abinda suke fad'a, ta ta6e baki, wai ma? Shi kansa bai isheta kallo ba yanzun balle kuma abokinsa. Ta cire laffayarta ta wurga saman gadon. Wani riga da siket na farin leshi d'inkin ya kamata kwarai hakan ya k'ara fiddo zahirin zubin halittarta. Ta fisge d'ankwalin, tana k'ok'arin zuge zip din rigar ne ta ji an murd'a k'ofar. Jin ta a k'ulle ya sanyashi soma bugawa a sannu. Ta harari k'ofar ta cigaba da abinda ta soma. Shima daga bugu uku bai k'ara ba ya bar wajen, daman ledar zai mik'a mata, haka ya sanyata a firij ya fice zuwa d'akinsa bayan ya kashe fitilu. Ita kuwa Bintu ta chanja kayanta zuwa riga da dogon wando ta nemi makwanci. A gajiye take sosai, hakan yasa ko mintuna uku bata ci ba bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita. Asuba nayi kuwa ta farka, wannan kuma sabon su ne, Mami ta sabar musu da tashi sallar asuba. Tana idarwa kuma ta lafke anan saman dardumar sai bacci, abinda ta kasa horuwa da shi kenan, hak'uri har fitowar rana. Cikin baccin ne ta ji ana bugun k'ofarta tamkar za'a 6alla. Bintu ba dai nauyin bacci ba. Ta mik'e a firgice. Ga rana har ta fito kyal. Ba shiri ta bud'e k'ofar. Ma'aruf ta gani sanye cikin farar jallabiya sai faman huci yakeyi. "Wane irin wulak'anci ne haka ina bugun k'ofa bazaki bud'e ba, banda wannan ma, wanene ya baki damar rufe k'ofa?" Ta turo baki. "Gani nayi d'akina ne." Ya watsa mata mugun kallo. "D'akinki, ni kuma gidana ne. Ki ka k'ara gangancin rufe k'ofa sai na hukuntaki. Ba ki da abinda zan nema." Ta dubeshi kawai cike da tsananin 6acin rai dangane da furucinsa. Ta kauda kanta tana mai tunanin abinda ya kamata tayi domin ramuwa. Ya katsemata tunani. "Ki kunna wayarki, Mami na son magana da ke. Ki kuma yi sallah, don banga alamun kinyi ba." , Ya juya ya fice ya barta tsaye kamar an dasa ta. Ta ci alwashin Yaya Ma'aruf sai yayi dana sanin munanan kalamansa gareta. Tayi murmushi mai fassarori. "Bintu ce fa." Cewar wani sashe na zuciyarta. Ta juya ta koma ciki ta rufe d'akinta, saidai bata sanya muk'ulli ba. Wayarta ta nufa kai tsaye ta kunnata. Kira ta dannawa Mami. Mami tana d'auka kawai sai ta fashemata da kuka. "Haba Bintu, kukan na menene kuma? Meyafaru?" Ta ja ajiyar zuciya. "Mamina kewarku nakeyi wallahi." Ta fad'a a shagwa6ance. Mami tayi murmushi mai sauti. "Muma munyi kewar Bintuna, saidai dole zamuyi hakuri saboda gidan mijinki shine babban gata da rufin asirinki. Shi kuma kad'ai ne wanda zai nunamiki so tamkar mu ko ince fiye da mu. Kinji ko?" Bintu ta share hawayenta, lallai ma Mami, batasan abinda ya yi mata ba yanzun. Amma ai bakomai, Inna ta haneta kai k'ara kasafai. Itama ai ba kanwar lasa bace. Shine abinda ta barwa zuciyarta. A fili kuwa ta nunawa Mami ta gamsu, ta hau rok'on a kawomata hanif amma Mami tace ba yanzu ba sai an kwana biyu. Dole ta hak'ura. Gama wayarsu, ta mik'e ta fad'a wanka. Bayan ta fito ta nufi akwatin da Aisha ta had'omata. Tsaki tayi, Aisha sai a barta, duk ta had'ata da manyan kaya bayan ta sani ko a gida ba damunta sukayi ba. Tayi ta d'age-d'agenta, can dai ta hak'ura ta d'auko wani atamfa ja mai adon fararen fulawoyi manya. Simple d'inki akayi masa na riga da siket saidai ya zauna sosai a jikinta. Ta k'ara fesa turare. Ta dubi kan gadon, kayan da ta cire babu linki, haka ta tattara komai ta linke ta gyara gadon gami da adana kayan sallarta. Har zata fita falo ta tuno da batun d'ankwali, ba k'aramin aikin Ma'aruf bane ya zubamata rankwashi a kanta, ba don ta so ba ta d'auka, saidai koda ta tashi yin d'aurin batayi na kirki ba, sai wani da ake kira da Ture Kaga Tsiya. D'ankunne kawai ta sanya sai zobunanta, babu sark'a da abin hannu. Fuskar fayau babu kwalliyar kirki, acewarta wa zata yiwa? Batayi tsammanin ganinsa a falon ba, saidai ga mamakinta yana zaune saman carpet yana karyawa abinsa. Mamaki tayi kwarai, ta shaida kulolin, daga gidan Mami suka fito. Ya dubeta duba na wacce bata isa ba ya kauda kansa fuskarnan tamkar wanda aka aikowa sak'on mutuwa. Shi fa ba'a kyauta mishi ba, ina shi ina Bintu ne? Wannan ta gama ganinsa ai ta cuceshi. Gwara suyita zaman doya da manja. Ganin irin kallon da yayi mata ne yasa tayi murmushin mugunta. Kicin ta shiga ta d'auko kofi da cokali bayan ta d'aurayesu ta dawo. Ta zauna d'an nesa da shi ta janyo flask na ruwan shayi fuskarta a sake. "Wane irin d'an iskan d'auri ne haka kamar wata ka..." Bai kai ga k'arasawa ba wayarsa ta d'auki k'ara. Saida ta kusan yankewa sannan ya d'aga tare da sanyawa a loudspeaker. "Hello." Bintu ta yagi kwai ta tura a baki batare da ta kalleshi ba. Daga can ita kuma wacce ke akan layi ta fashe da kuka. Kukan da ya sanya Bintu kusan sakin dariya sakamakon wata k'atuwar murya da ta ji marar dad'in sauraro tamkar ba muryar mace ba saidai ta cije. Shi kansa yayi mamakin jin ta da babbar murya haka, ashe kenan idan zasuyi magana da shi ne kawai take ragewa. Yau kam gayun murya babu shi. "Prince ka cuceni, ka ci amanar k'auna. Ashe daman aure za'ayi maka da 'yar uwarka shine baka sanardani ba? Na shiga uku." Sai lokacin Bintu ta gane ko wacece, itace dai wacce ta yi mishi rakiyar dole zance wajenta. Ma'aruf ya d'an rarrasheta ta kasa shiru har ya gaji, ganin zai kashe wayar dole ta sauko. Yace ta kwantar da hankalinta, shi aure ai nufin Allah ne. A k'arshe kuma tayita rok'onsa akan ya shigo tayi mishi kallon k'arshe don itama zata koma Kaduna wajen yayarta. Ya tabbatar mata zai shigo. Bayan sunyi sallama ya kwantar da kansa saman kujera ya lumshe ido kawai. Can ya tsinci muryar Bintu. "Yaya, wallahi wannan matar 'yar yaudara ce. Bakaji muryarta ba? Allah Ya kamata, ranar da na raka ka zance tana ta faman k'ank'ance murya, yanzu kuma dubi yanda ta bud'e murya tana zuba kuka tamkar ana ruwan sama." Yayi cak, ya kuma gaza bud'e idanunsa, gaba d'aya tunaninsa ya tafi ga matakin da yafi cancanta ya d'auka akanta. Ita kuwa wani sanyin dad'i ne ya dirar mata ganin ta kashe bakinsa. Ta kammala ciye-ciyenta a tsanake ta kora da ruwan shayi kafin ta mik'e ta kai kayan kicin. Kafin ta kai ga juyowa, ta ji an cakumi gashinta da k'arfi. Ai tuni ta soma ihu. . Tuni d'aurinta ya kunce. "Wacece mai k'atuwar murya?" Ta sanya hannu ta rik'o hannunsa amma k'arfin ba d'aya ba, ko gezau yatsunsa basu motsa ba. "Zan mutu! Don Allah kayi hak'uri Yaya." "Daga yau kika k'ara kiranta mai k'aton murya ni da ke ne. Ke meye a muryarki?" "Wallahi muryata tafi... Wayyo!" Ta kasa k'arasawa adalilin k'ara jan gashin da ya yi. "Au, ashe bakinki bazai mutu ba? Lallai idan zaman da kika za6a kenan muyi zaki d'and'ana kudarki." . Tuni ta soma hawaye. Ya saki gashin. Ya kama hanyar fita yana fad'in. "Ki kammala ki sameni a falo." Ta tur6une fuska ta bishi da harara. "Duk abinda ka tanada nima shi na tanada gareka." Bayan ta kammala wanke komai ta ajiye ta d'auki d'ankwalinta ta d'ora shi tana fad'in, ba zata fasa murza d'aurinta yanda ranta ke so. Ta share fuskarta, ba fa zatayi saurin karaya ba, yanzu aka fara wasan tsakaninsu tunda bazai gaji da zaluntarta ba. Ta fito da wannan takunnata mai cike da yanga. A haka ta k'araso cikin falon, idanunsa a kanta yana duban ikon Allah. Ta zauna saman kujera. "Ganinan." Ya ja fasali sannan ya soma maganarsa. "Inaso ki kiyaye bakinki. Ki kuma kiyaye dukkan wani abu da zaki janyowa kanki na d'ora hannuna a jikinki. Banason raini, shine kuma babban abinda yafi had'amu kema kinsani. Sannan kina sane cewar Ma'aruf ba k'azami bane ko? Sai ki kiyaye ayyukanki, daidai da d'akina da toilet ban d'agamiki k'afa ba." Yana murmushi ya d'aga mata gira. "Ai amarya ce, bata buk'atar 'yar aiki yanzu." Takaici ya isheta, ta dauke idanunta ta turo baki. "Ni ko a gida fa bana wankin band'aki, Aisha ke yi." Ya harareta. "Gida daban, gidan aure daban. Banason maimaici. Na gama maganata ok?" Ta amsa da toh sanin halinsa. Ta mik'e ta bar falon. Kan gado ta fad'a tana tunanin yanda zata soma rayuwar nan a gidan Ma'aruf. Bata kai ga tunanin komai ba har ta ji tsayuwar mota. Da sauri ta mik'e ta lek'a. Wani ihun murna ta saki ganin wadanda ke fitowa daga motar. A guje ta fito, bata lura ko da mutum ko babu ba a falon, ita dai burinta ta bud'e k'ofa ta ji ta ajikin 'yan uwanta. Ba zato ta ji an dakamata tsawa wanda ya sanyata juyowa ba shiri. "Menene hakan?!" Kafin ta ba shi amsa suka jiyo sallamar mutane tun kafin su k'araso jikin k'ofar. Ta shareshi ta juya ta bud'emusu. 'Yan Rano ne, yanmatansu da iyaye amma duk ciki banda Inna. Da sauri ta rungume Aisha tana murna sai kuma ra fashe da kuka. Wata cikin su, mai suna Gwaggo Sadiya ta kama baki "Haba kekuwa Bintu, menene abin kukan kuma?" Ma'aruf na murmushi ya amsa a kunyace. "Shagwa6ar fa gwaggo?" Suka k'araso ciki suna dariya. Aisha ta ja hannunta zasuyi d'aki saidai wata gwaggonsu ta dakatar da ita. "To kekuma haka akeyi? Baki bari ta gaishemu sannan kuyi sirrinku?" Aisha ta saketa suna dariya. Ta k'arasa ta fad'a jikin gwaggo Sadiya sannan ta gaishesu. "Bintu da son jiki. Ashe sai abinda yayi gaba." Ita dai murmushi tayi kawai. Ma'aruf take duba yanda yake wani sunne kai shi a dole kunya ga surukai. Ya dubi Aisha. "Ke me ya hanaki tafiya makaranta?" Ta sosa kai. "To Yaya ai ba wani abun akeyi ba." Ya harareta. "Kedai kinzo ki takurawa Amaryata da gulmace gulmacenku." Akayi dariya, Aisha dariyarta da biyu ce, har da mamaki. Ta dubi Bintu kallon ashe an shirya. Bintu ta murgud'a baki gefe kawai ta watsar. Ta lura wannan ce sabuwar kissar da Ma'aruf ya 6ullo da ita. Tayi kwafa, ai kuwa zata nunamasa ta fishi iyawa. Ta narke fuska tana mishi wani irin duba. "Allah Yaya ba wata gulma zamuyi ba, kaima kasan tun jiya nake kukan kewarta." Bataji kunyar furucinta ba, sai gwaggonnin ne sukaji, 'yan matan kuwa sukayi makwas suna dariya ciki-ciki. Shi kuwa gogan ya maze, lallai ma yarinyar nan, kawai sai ya mik'e a kunyace yana murmushi kamar gaske ya bar wajen bayan ya jefeta da kallon zamu had'u. Ta bishi da murmushin da ta saba idan tayi wata muguntar. A ranta kuwa tace "Yanzu ka soma gani indai irin salon da ka za6a mana kenan." Bayan fitarsa, yanmatan suka kwashe da dariya, gwaggonnin kuwa mik'ewa sukayi suka zagaya d'akunanta biyu da kicin, daman basu zo ba. Aisha ta samu ke6ewa da Bintu. "Gayamin Tawan, ya lamura?" Bintu tayi murmushi, ai itama tasan me takeyi, ko Aisha bazata bari ta gane komai ba. "Ke na durzu a hannunsa, ashe daman duk wani jan ajin da yakemin na k'arya ne, ban dauka komai zai wakana ba tsakani." . Aisha ta saki baki. "To ya na ganki garau?" Bintu ta ja tsaki. "Kefa 'yar iska ce, wayagayamiki dole sai na kwanta ciwo? Saida fa ya had'a da kuka da magiya na amince. Ya kuma dauki alk'awarin daina musgunamin." Aisha dagaske ta yarda, ai sai tayi wata shewa da dariya. Atika ta dubesu. "Anayi babu mu." Aisha ta harareta. "Maganarmu ce ta aminan juna." Bintu tayi dariya kawai. Wannan Aishar ma karatun litattafanta ya tashi a banza. "Amma da banason fallasa don Allah." "Tsakaninmu babu haka Bintu, don Allah ki k'ara zage damtse wajen janyo hankalinsa. Ga k'ananun kayanki can acikin akwati da sauran kayayyakin ma, na had'omiki. Kada ki yarda ki ba shi (chance) na k'orafi." "Naji karki cikani." Aisha tayi dariya. "Zan taho miki da books." Bintu ta harareta. "Sanin kanki ko a gida bana karatun Hausa ballantana a gidan aure." Aisha ta k'ara numfasawa. "Wallahi mamaki nakeyi, daman fa na zargi yaya yana sonki kawai yana k'ok'arin 6oyewa ne irin abinnan." Bintu ta ta6e baki. "Shiyasani." Aisha tace "Bawani, kukasani dai, kema ai kina so kike wani sharewa." Dariya kawai Bintu tayi. Basu jima sosai ba suka tafi. Bayan tafiyarsu shima ya fice ko sallama baiyi mata ba don dagaske yarinyar ta bashi mamakin furucinta. Har sukayi sati cikin wannan zama nasu na doya da manja. Ta koma makaranta abinta shima ya koma aikinsa. A gajiye ta dawo gidan misalin biyar na yamma, bayan sun gaisa da Audu maigadinsu ta shige ciki. Anan farfajiyar gidan ta hangi motarsa a fake. Wannan ya bata tabbacin ya dawo. Ta k'arasa shiga ciki a zatonta ya k'ulle da muk'ulli saidai tana murd'awa ta ji k'ofar a bud'e. Baya falon, wannan ya bata damar zubewa kawai akan doguwar kujera. "Wash!" Ta fad'a a fili cike da jin wata iriyar gajiya. Ta lumshe ido jin dad'in iskar fankar dake kad'awa. Ta kwashi mintuna kusan uku anan kafin ta mik'e ta k'arasa d'akinta. Ta rage kayan jikinta ta fad'a wanka. Saida ta fito ta shirya cikin riga mai k'aramin hannu T-shirt ja an rubuta Baby a jiki, da wando short bak'i ko gwuiwarta bai k'arasa ba. Wannan karon dai ta samu kitso wajen 'yar wata makwafciyarsu. An yarfa mata su k'ananu. Ta tufke da manyan ribbons biyu bak'i da ja. Hoda kawai ta shafawa fuskarta sannan ta fito zuwa kicin domin d'ora girki. Har lokacin baya falon saidai ta ji muryarsa yana amsa waya daga d'akin. Ta ta6e baki tayi kicin, tasan bazai wuce sauran cocaine ba(Sa'a). Ta rasa me zata girka, a k'arshe dai ta yanke shawarar yin jellop din taliya. Ta soma aikin ne tana yi tana wak'e-wak'enta ta ji kamar motsin mutum a bayanta. Wannan ya bata damar juyowa ta dubeshi. Ganin haka ya nufi firij yana k'ok'arin bud'ewa. "Yaushe kika dawo?" Ta yi kamar bata ji ba. Ya gama shan ruwansa sannan ya juyo gareta. "Ban hanaki yawo babu d'ankwali bane?" Tayi narai-narai da fuska. "Wallahi Yaya d'ankwalin takura gareshi." Ya dubeta duban da ace ba matarsa bace bai kamatu ba. "Nikuma bazan d'auka ba a gidannan, sai ki wuce ki rufe kanki." Kamar bazata ajiye aikin ba, dole ta ajiye ganin ba shi da niyyar barin wajen. Ta giftashi ta fita. Ya sauke ajiyar zuciya, bai bita da kallo ba, don ba shi da jarumtar nan. Saida ya tabbatar ta shige sannan ya fito ya koma d'akinsa. Acan d'inma duniyar tunani kawai ya lula, saidai duk yanda zuciyarsa ta kai ga fahimtar da shi wani abu, sam ya k'i aminta balle kuma ya bata dama. Ya ja tsaki ya mik'e, bayason tunanin abinda bazai amfana da shi ba. * * * . Ta kammala tsaf ta zubo nata a filet bayan ta bar mishi nashi cikin flask. Kasancewar ba sallar takeyi ba, yasa ta zaman cin abincinta. Ta soma ci kenan tana kallon wata tasha da ke hasko wrestling. A haka ya fito da zummar tafiya masallaci. Yayi mata kallo d'aya ya cigaba da tafiyarsa baice uffan ba. Ta bishi da kallo, wataran rashin son yawan magana irin na Ma'aruf yakan bata mamaki matuk'a. Kodayake daman bashi da hayaniya, bar shi dai da son girma. D'an hayaniya sai mutuminta, Yaya Rufa'i. Bayan ya dawo ya zauna a falon alokacin ta kusa kammala cin abincin. Ya dubi abinda take kallo sannan ya dubeta. "Bani remote." Ta narke fuska. "Yaya don Allah ka bari na gama kallo." Ya yamutse fuska batare da ya dubeta ba don baya buk'atar cigaba da dubannata saboda dalilai. "A matan ma bansan sunan da zan baki ba, me mace zatayi da wrestling idan na rashin abin yi ba? Malama bani na kalli abinda zai fissheni." Ta mik'a mishi remote d'in ta d'auki filet tayi hanyar kicin ganin ya kamo Aljazeera. Daman ai ba yau suka soma fad'a akan tashar kallo ba. "Ina abincina?" Bata ko juyo ba ballantana ta dubeshi ta amsa. "Yana kicin." "Kawomin." . Ta had'o mishi komai ta ajiye, zama tayi gami da janyo wayarta. "Malama tashi ki suturta jikinki kafin zuciyata ta tashi." Wani gululun bakinciki ya turnuk'eta, kai bafa zata amince da wannan cin fuskar ba. Dole ne tayi maganin Yayan nan. Ta fasa zaman falon ta koma d'aki. Batasan sadda ta soma hawaye ba, kewar Maminta da Aisharta suka mamayeta. Yanzu da ace tana gaban Mami da duk wani abu da zai mata ba dai yayi a gabanta ba. Gashi kuma babu damar kai k'ara, to tace me? Alhalin ta riga ta nunawa Aisha komai lafiya ke tafiya tsakani. Ganin zata sanyawa ranta damuwar babu gaira babu dalili ne yasa ta janyo wayarta. Whatsapp ta soma k'ok'arin downloading, a baya sam bata chatting, tana ganin yanda Aisha ke haukar karanta books da kutsawa groups na matan aure amma ita ko a jikinta. Wannan karon kam, tayi niyyar somawa don ya d'ebemata kewa. Bayan ta gama downloading, ya kammala updating contacts dinta da komai. Bata d'ora hotonta ba, tabar wajen fayau. Dad'i ya cikata ganin Aisha online, hakanan da yawa daga cikin 'yan uwansu na Rano da 'yan uwan Abban Aisha ma duk sunayi. Kai tsaye ta yiwa Aisha magana. Aisha harda 'yar rawarta na murnar ganinta. Nan ta sanyata a groups, na matan auren ma ta sanya (Admin) ta sanyata ciki. Nan ta soma ganin abubuwa, saidai tafi maida hankali a na 'yanuwansu na Rano. Suka isheta da shewa suna tambayar ya amarci. Ta biyemusu da dariya, koda suka tambayi mijin, sai cewa tayi gashinan yana mata tausa. Nan aka dauki dariya har da masu turo Audio. Kai Bintu ta rasa inda zata sanya ranta don dad'i. Ashe dai wataran zata ga amfanin chatting? Haka tayi ta biyemusu tana darawa. Shima Ma'aruf bai k'ara bi ta kanta ba. Misalin tara ta ajiye wayar ta fito. Fitilun a kashe, sai hasken tv saidai waya yakeyi. Ta fahimci da abokin aikinsa yake yinta, ta wuce zuwa kicin domin d'aukar ruwa. Bayan ta fito ne yayi mata nuni da hannu wato ta kwashe kayan abinci. Kamar bazata tsaya ba, sai kuma dai ta dawo da baya. Yana wayan yana binta da kallo sakamakon hasken tv da ya hasketa. Ita kuwa kamar tasan yana kallonta ta wuce tana wata rausaya wacce da gayya ta yi ta. Ai kuwa har da d'an mik'ewa zaune. Tuni kuma ya soma mance bayanin da sukeyi ta wayar. Ta gabansa ta shige da robar ruwa a hannunta. Ajiyar zuciya yayi, ya runtse ido. Dole ya yiwa abokin aikinsa sallama ya tattara ya kashe kayan kallo ya fad'a d'akinsa. Yarinyar nan zai gargad'eta, don bazai lamunci ta dunga yi mishi yawo da duk suturun da ta so ba acikin gidannan. . * * * Ita kuwa shigarta d'aki ta chanja zuwa kayan bacci doguwar riga mai d'an kauri saidai da kad'an ta wuce gwuiwarta, bata da nauyi. Daga haka ta kashe fitila ta kunna (gwamna ya gaza..lol)ta hau whatsapp bayan tayi male-male asaman gadonta. Kai tsaye group na matan aure ta lek'a, nan ta soma cin karo da sirrika kala-kala da akeson duk mace ta iya ta kuma sansu. Ta soma karantawa tiryan-tiryan. Ajiyar zuciya kawai ta saki, wai ana nufin itama zata iya yiwa Ma'aruf? Ta runtse ido ta bud'e, kai bata fatan har mutuwar aurensu wani abin ma ya had'asu. Ta yarda akwai sha'awa a rayuwa, soyayya ce dai ta kasa gaskatawa yana faruwa domin acewarta ita bai ta6a kamata ba. "Toh idan kuma kika soma son Yaya Ma'aruf fa?" Cewar wata zuciyarta. Ta ja wani iri. Kai Allah ma bazai jarabceta da wannan ba in sha Allah. Me zata so a wajen mutumin da baya sonta? "Ni mugani ma ko yana online." Ta fad'a a fili sannan ta hau lalube contacts. Baya online, hotonsa ta gani a dp hakan yasa ta bud'owa. Saida ta furta "Wow" a fili tun bata kai ga k'arewa hoton kallo ba.
0 comments:
Post a Comment