BINTU Part 006
BINTU Part 006 . Zuwan Aisha gidan ya yi musu dadi. Haka zasu zauna suyita hirar duniya idan ba makaranta. A kokarin Bintu bai wuce koyaushe ta nunawa Aisha lafiya lau suke da mijinta ba. Har takan dauki waya tayi kiransa saidai har wayar ta gama rurinta baya ko kallonta. Saidai a wayance tayita zuba zance don burge Aisha. Satinsa d'aya da tafiya, amma ko text bai ta6a yi mata ba, da zummar gaisuwa. A yanzu kuwa ta daina samun layinsa, saidai ta ji Aisha tace yayi kiranta ko kuma Mami. Jikinta yayi sanyi, haka kawai ta tsinci kanta da shiga damuwa. Kodai furucinta ya bawa Yaya Ma'aruf haushi? Ashe zai damu da ta nuna damuwa akanshi? Ta kai dubanta ga Aisha wacce ke kwance rigingine a saman gado tana amsa wayar masoyinta Ashir, sai wani narke murya takeyi da murmushi. Daga inda take ta zubawa wayarta ido kawai amma kunnuwanta suna ga Aisha tana sauraronta. Kawai sai ta ji abin ya burgeta, inama ita da Yaya Ma'aruf su dawo haka? Sai ta ji nauyi, kada dai ta kamu da son Ma'aruf ne? Ta girgiza kai, kokusa bata fahimtar abinda akeyi a group din nasu ta whatsapp ta tsinci kanta da komawa contact ta lalubo lambar Ma'aruf, har lokacin hotonnan ne akai bai chanja ba. Ta bud'o tana duba, a hankali takejin wani abu na yawo a zuciya da gangar jikinta. Tayi nisa a kallonsa ta ji Aisha ta makomata filo. "To 'yar is me kikeyi kika wani nutsu?" Bintu batajin wasa a yau, ta ajiye wayar ta dawo kusa da Aisha ta zauna. "Tashi ki bani wasu amsoshi don Allah." Aisha ta mik'e zaune ganin Bintu dagaske take ba wasa. "Ina sauraronki." Bintu ta muskuta tana fuskantarta. "Ya mutum zai gane ya fad'a tarkon so?" Me Aisha zatayi banda dariya. Ta d'aga hannu sama. "Allah na godemaka da Ka bani tsawon ran ganin wannan rana. Cabd'i!" Ta girgiza kai kad'an tana had'e rai cikin son kauda 'yar kunyar da ta ji. "Malama banason haka, idan bazaki bani amsa ba ki bar yimin dariya." Ganin Aisha bata da niyyar dainawa ya sanyata daukar wayarta a fusace ta shige d'aki. Kan gado ta fad'a tana murmushi, daman tasan hakan zata faru tunda ta riga ta gama cika baki a baya. Tana jin sadda Aisha ta shigo gami da zama gefenta, ta had'e rai. Aisha ta gimtse dariyarta ta soma magana duk kuwa da cewa Bintun ta juyamata baya. "Idan ka soma son mutum, zaka tsinci kanka cikin yawan tunaninsa, haka kuma da zarar ka ganshi kun had'a ido zaka ji kamar wasu kibiyoyi ke fitowa daga idanunsa suna shiga naka har suna haddasa maka wani kasala, har ka kasa jure kallon ka sauke idanunka. Komai na mutum zai dawo yana burgeka, ko muryar mutum ka ji sai ka ji wani sanyi na dadi. Babban abinda ke tabbatarwa ka kamu da soyayyar mutum shine KISHI. Nan duniya zakaji baka kaunar abokin takara a zuciyarsa. Ba kuma ka kaunar wani ya ra6eshi da sunan so. Ko yaya kaga ya sakarwa wani fuska ya kula da shi fiye da yanda yake kula da kai sai ka ji tashin hankali sosai, da damuwa da bakin ciki a zuciya. Matukar kina jin wadannan abubuwan da na lissafa, shakka babu (You Are In Love)." Bintu ta bud'e lumsassun idanunta tana duban fuskar gadonta, ta ji gabanta yana bugu da sauri-sauri. Ta kamu da son Ma'aruf yanzu? Kenan dukkan abinda takeji a ranta akansa soyayya ce? "Kenan alamomin da nakeji akan Yaya Ma'aruf suna nuni da cewar inasonsa?" Batasan sadda ta watsowa Aisha tambayar ba. Aisha ta rasa inda zata tsoma ranta don dad'i, don ta jima da gane cewar babu abinda ya ta6a shiga tsakaninsu kawai dai ta barta a yanda ta so ne. "Idan har kina jin abubuwan da na lissafa akansa, to lallai kin fad'a cikin matsanancin soyayyarsa." Sai kuma ta ji wata iriyar kunyar Aisha, lura da hakan ne yasa Aisha mik'ewa ta fita da zummar d'ora musu girki. Ta sauke ajiyar zuciya ta mik'e zaune. "Inason Yaya Ma'aruf." Shine abinda ta furta cikin siririyar murya. * * * "Ina sonki Fatima Bintu." Cewar Ma'aruf kenan a yayinda yake kwance cikin kujera idanuwa a lumshe yana tunanin Bintu wanda ya zame mishi jiki tun zuwansa Lagos. Gaba d'aya kewarta ta dameshi, baisan ya damu da yarinyar ba sai bayan da ya nisanta da ita. Yana fushi da ita akan ta nuna halin ko'in kula da tafiyar da zaiyi, wato dai bata damu da shi ba. A rayuwarsa yana so yaga an damu da shi. Sai ya kai zuciyarsa nesa yake k'in daukar kiranta, lallai shi yana son tilasatawa ransa ya fiddata. Yanaso yabar tunanin wani abu nata da ita kanta. Yana so ya yakiceta a ransa. Wannan yasa ya yanke shawarar yin wata d'ayan da ogansu yace yayi acan batare da ko sau d'aya ya dawo hutun karshen sati Kano ba. Sanin da yayi ma idan yazo ba wani abun zai samu awajenta ba. Ya numfasa ya mik'e zaune. Kalmar nan ta "So" baiyi zaton zai k'ara furtata ba ballantana ya ji ta a ransa. Sai ga shi zuwa yanzu ya gama tabbatarwa ransa ya fad'a dumu-dumu cikin kogin son matarsa kuma 'yar uwarsa abokiyar fad'ansa Bintu. Sai kuma yayi murmushi sadda ya tunano rashin jituwarsu tun afarkon zuwanta gidansu har zuwa girmanta. Rufa'i ya dannawa kira, ya sanar dashi cewar wata d'aya zaiyi don haka ya dauki su Aisha ya maidasu gaban Mami. Daman ya kammala waya da Abba ya shaida mishi. Ya yiwa Bintu gajeran sak'o babu wani abin jan hankali ciki ya shaidamata su had'a kayansu Rufa'i zaizo ya tafi da su gidan Mami. Ta yi kasak'e tana duban sak'on alokacin suna tare da Aisha tana k'ara koyar da ita yanda zata shawo kansa. Ta sanarwa Aisha kafin su soma shiri. Ranta duk babu dad'i jin zai cinye wata d'aya a garin da basu da wani addini sosai. Haka suka kammala shiri suka nufi gidan Mami. Saidai tana ganin Mami ta mance da batunsa ta hau murna. Ganin yanda ta d'an rame sai Mami tayi zaton ko ciki ne. Ta shiga nan nan da ita. Murmushi kawai sukayi ita da Aisha. . A wannan wata d'ayan, wanda aka ci sati uku kenan da Bintu tayi a gidan Mami, ta yishi cikin kwanciyar hankali, duk kuwa da cewar babu wata mu'amalar arziki dake shiga tsakaninta da Yaya Ma'aruf face gaisuwa da take mik'a mishi ta whatsapp, shima wani sa'in za'a nunamata ya je kuma ya gani amma babu amsa. Sai sadda ta ci sa'a ne yake amsa mata, daga amsa gaisuwar kuma bai k'ara cewa uffan. . Tun tana yi har ta soma gajiya, wani sa'in ta watsar. Shi kuwa ya d'auki hakan kawai a matsayin rainin hankali, tunda gwana ce wajen hakan. Ganin yana neman cutuwa sosai da bukatunsa, ya sanyashi farlantawa kansa azumin litinin da alhamis. Haka kuma da yawaita dauke hankalinsa da wani abu da ba zai jawo mishi motsuwarsa ba. Saidai iyakar dauriya yinsa kawai yake, akwai sadda Lawisa ta kusa cin galaba akanshi. Sukayi doguwar hira a waya mai ta6a sosai, a k'arshe suka yanke zata kawomishi ziyara har Lagos. Koda zuwanta da soma gudanar da abubuwa, tun kafin lamura su 6aci, ya dawo nutsuwarsa inda wata kyakkyawar zuciyarsa tayi mishi tuni da "Bafa matarka bace." Da sauri ya fisgeta daga jikinta ya mik'e yana kiran innalillahi a fili kafin ya fad'a ya wanke jikinsa. Nan ya taddata tana hawaye, bai bi ta kanta ba ya kama hanyar fita sai kuma ya tsaya batare da ya juyo ba, cikin kakkausar murya yace. "Kiyi hanzarin barin gidannan tun kafin na dawo." Yana shirin ficewa yaji ta rungumoshi ta baya, ya runtse ido, kafin ya juyo ya tureta. "Karki k'ara kusantoni! Ki rabu da ni Lawisa, please daga yau ki fita hanyata." Hannunsa ta rik'e a gigice. "Bazan fita ba, ka taimaki rayuwata Ma'aruf kada ka barni ha.." . "Ki kyaleni! Ki kyaleni nace!! Kafin na dawo ki tattara abinda kikasan mallakinki ne ki bar gidannan!!" Ya fad'a a tsawance kafin ya sa kai ya fice. Ranta ya 6aci sosai da wannan wulakancin da yayi mata, ita kuwa ko shine autan maza ba zata k'ara kallonsa ba. Ta dauki wayarta ta kira d'aya cikin mutanenta na Lagos. Nan tayi kwatancen inda take, a take kuwa Alhajin yasa direbansa zuwa d'aukarta. Ko wanka bata tsaya yi ba ta shirya tsaf ta bar gidan. Ma'aruf bai jima sosai ba ya dawo, ya ji dad'in rashin ganinta a gidan, ya zauna ya rik'e kai. Idanunsa sunyi ja sun kumbura adalilin kukan da ya ci, yau ga shi ya kusa tafka kuskuren da da ace ya faru ba zai iya yafewa kansa ba. A gefe kuma ga soyayyar dake azabtar da shi, ya ji haushin yanda ta bar turomishi sak'on gaisuwa ko don baya kulata sosai ne? Batasan cewa yana jin dadin hakan ba? Ajiyar zuciya ya saki, fatansa ya kammala aikinsa yaje ayi wacce za'ayi don ba zai zauna da cuta ba. Acan kuwa, Bintu bata k'ara bi ta kansa ba, ta danne abinda takeji a ranta dangane da shi. Ta nemi zuwa Rano ganin iyayenta tunda sun samu hutu. Kasancewar shima Rufa'i zai kai Hajara ganin gida, yasa Abba bai hanata ba ya kira ya sanarwa Ma'aruf. Allah Ya tsare hanya, shine kawai abinda yace. Farinciki ya rufe Bintu yau zata ga 'yan uwanta. Suma can sun shirya tarbarta sosai. Tare suka je har Aisha. Yan uwa sunyi murnar ganinsu. Inna ta shiga nan nan da su. Kwanansu uku suka soma shirin tahowa don Rufa'i zaizo daukarsu. Inna ta k'ara yiwa Bintu nasiha sosai akan rik'e hakkokin mijinta da sauransu. Ta yaba kwarai ganin Bintun ta yi hankali, ta zama wata mai sanyi da nutsuwa, batasan cewa soyayya ke nukurkusarta ba har ta ladabtar da ita ladabin dole. Aisha ta samu abubuwa sosai a wajen 'yar Rano kasancewar bikinta baifi sati hud'u da kwanaki ba. Haka suka baro Rano cike da kewa. A safiyar asabar ne ta koma gidanta kamar yanda Mami ta umarceta. Tare suka je da Aisha sai 'yar yarinyar da aka samo mata da bata wuce sha uku ba da zata tayata rainon Hanif, har da Hanif din wanda suna isa Bintu ta goyeshi a bayanta. Suka gyara komai don a ranar akesa ran dawowar Ma'aruf kamar yanda ya shaidawa Mamin. Kicin suka fad'a suka hau girke-girke. Suna yi Aisha na k'ara bata shawara. "Kwalliya fa zaki ci malama, irin wanda na gayamiki. Kada ki nunamishi fushinki Bintu. Kiyi hakuri, kece dole wajen yi mishi biyayya, amma fa ban hanaki jan aji kad'an ba, karkiyi yanda zai tsinke." Sukayi dariya, Bintu ta dafa kirjinta. "Bakiji yanda gabana ke bugu ba, a tsorace nake fa. Kinsan Yayanki akwai disgawa." Aisha ta girgiza kai. "Akanki ba, kuma kema kinsan abinda yasa yake miki hakan, kin nuna mishi baki da kunya." Bintu ta harareta. Aisha ta dara kad'an. "Allah kuwa rashin girmamashi sosai ne yasa yakemiki wasu abubuwan. Ki tuna keda kanki kin sha yabon yanda sukeyi da Anti Asma'u, yana sakarmata fuska, wasa da dariya duka, koda kuwa a gabanmu ne. Yana da mutunci wallahi ba wai kuma don Yayana bane. Ita gaskiya fa a fad'eta." "Ya gasamin maganganu fa." "Wannan kuma kinfini sanin ta sigar da zaki rama, saidai ina k'ara baki shawara, kada ki ja aji ta yanda zai tsinke wallahi." Murmushi kawai tayi, suka cigaba da aiki suna hira, anan ne Bintu ke labarta mata yanda sukayi da Lawisa. Me Aisha zatayi banda dariya, har da rik'e ciki. Ta jima tana dariya da k'arawa. "Kai wallahi kinyi daidai. Toh wallahi ko don saboda su ya dace ki bada kai bori ya hau kada kiyi sakiyar da ba ruwa." Aisha ta k'arashe tana mai kwafa. "Bakisan wacece Lawisa ba. Yar iska ce, idan ma nayi kiranta karuwa banyi k'arya ba wallahi. Ki tashi tsaye karki bari su samu k'ofa." Bintu ta girgiza kai da gamsuwa da wani irin tsoro. Bayan sun kammala, Aisha ta yiwa Hanif wanka, itama Bintun ta fad'a band'aki. . Mintuna ashirin da kammala shirinta da komai, ta fito falon inda Aisha da Sarah mai rainon Hanif suke zaune suna kallo. Ba Aisha ba, daidai da Sarah saida ta saki baki wajen kallonta. Wani shegen siket ne bak'i mai shek'i amma ba shi da kyalkyali, tsaga gareshi tun daga gwuiwa har k'asa, sai wata riga ja mai igiyoyi wanda ya tafi X ko kirjinta bai rufu yanda akaso ba, bata da hannuwa sai na vest. Ta rufe kanta da jar hula mai wani laushi duk da hakan, tufkakkan gashinta bai kammala rufuwa ba. Ta rik'e k'ugu ta karkace kai kad'an yayinda ta d'an tsuke baki. "Ya?" Aisha ta had'e yatsunta biyu. "Wow! Kinyi kyau wallahi." Ta k'araso tana mai yin farr da ido. "Nasani." Aisha ta d'aka mata duka a cinya sukayi dariya. "Yau dai da wuya Yayanmu ya d'auke idanunsa akanki." Sai kuma jikinta yayi sanyi. Fatanta kada ya gwatsaleta. "I hope so." "In sha Allah, kedai kada ki damu." Cewar Aisha. . Angonnata basu shigo Kano ba sai bayan Magrib. Tuni Aisha ta tattara ta wuce. Duk yanda Bintu ta so zamanta har zuwa sadda zai shigo amma fir ta k'i. Tana zaune ta rik'e Hanif tana mishi wasa ta jiyo tsayuwar mota. Ji tayi gabanta ya fad'i, ashe daman don batason Ma'aruf ne yasa batajin nauyin yin komai a gabansa? Tayi saurin duban Sarah. "Shiga d'aki." Sarah ta mik'e da sauri ta fad'a d'akin Hanif. Kwankwasa k'ofar da akayi yasa ta nufar k'ofar, Hanif yana rungume a jikinta bata ajiyeshi ba. A hankali take tafiya har ta isa k'ofar ta bud'e. Ido cikin ido suka dubi juna. Kowannensu yana kokarin isarwa d'an uwansa sak'o. Sai kuma ya juya da sauri, Isa direban Mami ya tara gami da kar6ar akwatinsa. "Nagode Malam Isa." Ganin haka, yana shigowa ta sa hannu ta rik'o trolley din, shi kuma yayi amfani da hagunsa wajen amsar Hanif dake mak'ale a hannunta na dama. Wani shock sukaji gaba d'ayansu, ya narkar da idanunsa wajen kallon abinda ya fi tafiya da imaninsa a wajenta. Ita kuwa ta dauke idanunta. Murya na rawa ta furta. "Yaya sannu da zuwa." Baki amsa ba har ta juya ta nufi d'akinsa tana rausayar da batasan yanda akayi ta soma ba, wannan kam yafi (natural) tafiyarta had'uwa da tada hankali. Baiyi k'asa a gwuiwa ba ya tura k'ofar da k'afarsa ya mara mata baya. A daidai k'ofa suka had'u, caraf ya rik'o hannunta ya ja zuwa ciki. Ta dubi yanda ya rik'e hannunnata gam kamar mai tsoron a rabasu, sannan ta dubeshi a tsorace, gabanta na bugu da k'arfi da kuma sauri-sauri. Ya ajiye Hanif a saman gado ya jawota gaba d'aya zuwa jikinsa gami da yi mata kyakkyawan rumfa ruf. Gaba d'ayansu sun ji a jikinsu kuwa. Daidai kunnenta ya yi magana. "I'm in need of you Fati." Yanda yayi maganar da irin muryar da yayi amfani da ita wajen yin ce ta sanya tsintar kanta cikin rawar jiki. Bata ankara ba ta jishi yana cigaba da abinda bazata iya jura ba. "A'a! Bintu, not so fast!" Da sauri ta daddage ta tureshi, bata bi takan Hanif ba ta fice a guje. Sai ma ta ba shi dariya, hakan ya sanyashi murmusawa. . Hankalinta ya tashi, ta fad'a kan gado tayi shiru. Ya akayi ta kasa danne zuciyarta? Ta ji haushin kanta, Allah Yasa dai bai gano lagonta ba. Bata kammala tunane-tunanenra ba ya shigo da sallamarsa. Ta daure ta amsa a nutse batare da ta dubeshi ba. Shi d'inma bai damu ba ya mik'amata Hanif. "Rik'eshi." Ta kar6eshi baki bar dubanta ba ya yamutse fuska kad'an. Kamar yace wani abu sai kuma ya fasa ya fice. Ta bishi da kallo tana murmushin takaici, wasu siraran hawaye suka sirnano daga idanunta. Iyakar saninta, tana da rik'o wani lokacin, amma ta rasa dalilin da yasa zuciyarta ke neman gazawa wajen rik'on abinda Yaya Ma'aruf yayi mata. Magana kam, ya gaggasa mata, saidai ta tsorata da abinda Aisha tace akan matan dake kawomasa hari zasu iya zamowa barazana a rayuwarsu. "Amma bai furta yana sonki ba. Kodai bukatar ce kawai yake nufi?" Ta ji zuciyarta babi dadi da wannan tunanin da tayi. Ta yi ringingine saman gado tana duban Hanif dake wasa da zobenta. Tunaninta bai wuce anya dagaske Ma'aruf yana sonta ba? Tafi bawa zuciyarta kawai bukatarta yakeyi. Ba don hakan ba ma bazai nemeta ba. Da bakinsa ya kushe halittarta, ya nuna mata nan duniya ya k'arfin kasancewa da ita. Ita kuwa ta yaya ma Aisha zatace kada ta k'i bada kai? Ta numfasa ta rik'o hannun d'an kamar shine uban take maganarta a fili. "Kai, bazan yi yanda yakeso da wuri ba, sai naji gaskiyar abinda ke zuciyar babanka." Hanif dai banda ihu-ihunsa da 6angale dariya babu wani abu da yakeyi. Ta d'an kama kumatunsa. "Ni ce fa Bintun Mami! Zamiyi maganinsa ko?" Ta k'arashe da 'yar dariya. Ba ita ta fito daga dakin ba saida ya kwalamata kira. Ta janyo (After Dress) ta zura tana murmushi ta fita. Yana zaune saman kafet yana amsa wayar Abbansa, saidai hakan bai hanashi binsu da kallo ba har suka zauna. Hanif ta ajiye gefe sannan ta mik'e ta dauko komai na bukata wajen cin abinci. Ta soma zubawa ta ji muryarsa. "Fati." Bata amsa ba, ba kuma ta fasa abinda takeyi ba, saidai kiranta da yakeyi da Fati, yana sanyamata jin wani abu. Ya k'ara kiranta da murya da sigar da bazata iya ji ta kyale ba. Dole saida ta yi dagaske wajen saita tunani da nutsuwarta, ta d'ago fuskarta a daure, ba k'aramin namijin k'ok'ari tayi ba wajen dubansa. "Na'am." Ganin yanda ta tur6une fuska sai ya ji haushin kansa. Ya manta da cewar Bintu ce fa, yanzun d'an abubuwan da ya aikata zasu sanya ya janyowa kansa sabon raini. . Ya sosa hanci. "Kada dai ki dauki abin d'azu a matsayin wani abu, haka aure ya gada. Eh, kuma ba zai yiwu gida bai k'oshi ba a bawa na waje. Abar batun nan, ya wajaba lallai a gareni ni da ke mu zamto masu tsoron Allah mu dunga sauke hakkokin juna. Hakan zai fi mana kyau." Shi kam, bak'a sosai yaso yarfamata. Baisan ya akayi ya kasa ba. Anzo ga6ar da zata maida martani, don haka ta tura mishi farantin abincin gabansa, ta dubeshi ta kauda kai tana murmushin mugunta. "Na farko dai ni bani da bukata, hakki kuma na yafe nawa, kuma Yaya ka manta kace babu abinda zakayi da jikina. Ka kuma ce kallona kan tashi zuciyarka. Ni ce fa wannan yarinyar da kake fad'a. To nidai bani buk'atar komai nagode da niyya." Ya rasa me zaice? Saidai ya maze ya sha mur. Kamar yayi magana sai ya fasa ya hau cin abinci yana ta nanata maganganunta a ransa. Lallai ma yarinyar nan, wato haka take da riko? Ya ji ta ba shi haushi, ya d'an dubeta da niyyar fad'a, saidai bazai iya ba, wai wane irin muguwarl soyayyarta ce tayi mishi kamu har haka? Kallonta ma wani nishad'antar da zuciyarsa yakeyi. Ya daure batare da ya kalleta ba cikon sanyin murya yace. "Please leave me alone." Yanda yayi maganar baisa ta nuna tausayinsa a fuska ba, iyakar magana ai ya gasa mata. Ta dauki Hanif har da wani cillashi sama tana dariya. Daga haka ta shige dakin Hanif. Ji yayi ransa na k'una, wato ko a jikinta? Shi kuwa yaya zaiyi ne ta gane zuwa yanzu yayi nadama? Lallai so na sanya ladabin dole. Yau shi ke bin Bintu! Ya runtse ido. * * * Tun daga ranar ya fita hanyarta, duk da cewar ta damu a 6oye, hakan baisa a fili nuna kamar batasan me yake yiwa fushin ba. Ta daure ta cigaba da walwalarta yanda ta saba babu ko nuna wata alama ta damuwa. Ranar da ta je gida wuni, shima ranar yana ajiyeta ya nufi gidan abokinsa Hashim. "Ya akayi ne wai? Please mafita zakaban banason dariyar banza." . Hashim ya tsagaita dariyarsa. "Sorry, mamaki dai nayi ne. Kamar ka ace ka auri wannan ficikar yarinyar har ma ka soma sonta? Abinda ko a mafarki bazakayi kuskuren gani ba kenan." Ya fahimci Hashim na tunano mishi furucinsa ne. Ya lumshe ido kafin ya bud'esu ya dubeshi ransa a 6ace, ya ja guntun tsaki. "Bazaka gane ba, banason tuna baya." Hashim ya numfasa ya gimtse dariyarsa. Daidai sadda Salimarsa ta shigo ta ajiye musu kayan motsa baki. Ta tambayi lafiyar Amarya. Ya amsa da murmushi. "Lafiya, ai kun kyauta tunda shi bai kawoki ba kekuma bakizo ba." Hashim da Sally sukayi dariya. "Tuba nake, zaku ganni very soon in sha Allah." Ya jinjina kai yana shafa sumarsa fuskar dauke da murmushi. Bayan fitarta daga falon, Hashim ya dubeshi. "Kai zakayi wannan yak'in har ka siye zuciyarta." Ya yatsine fuska yana dubansa. "Ta yaya kenan? A tunaninka zan durkusa na rok'eta ta soni? Never! Furuci d'aya nayi mata wanda a yanzu nake (regretting, I'm in need of her)." Hashim ya ja tsaki. "Kana da matsala, dole kuma ka sauke wannan ji da kai ko ince girman kan da kake nunamata wallahi." . Hashim ya dubi abokin nasa da tausayi yace ma'aruff dole ka daure anjuma kaje kayi raping din bintu ko tana so ko bata so ....hehehe lol zuciyarta? Ta ji haushin kanta, Allah Yasa dai bai gano lagonta ba. Bata kammala tunane-tunanenra ba ya shigo da sallamarsa. Ta daure ta amsa a nutse batare da ta dubeshi ba. Shi d'inma bai damu ba ya mik'amata Hanif. "Rik'eshi." Ta kar6eshi baki bar dubanta ba ya yamutse fuska kad'an. Kamar yace wani abu sai kuma ya fasa ya fice. . Ta bishi da kallo tana murmushin takaici, wasu siraran hawaye suka sirnano daga idanunta. Iyakar saninta, tana da rik'o wani lokacin, amma ta rasa dalilin da yasa zuciyarta ke neman gazawa wajen rik'on abinda Yaya Ma'aruf yayi mata. Magana kam, ya gaggasa mata, saidai ta tsorata da abinda Aisha tace akan matan dake kawomasa hari zasu iya zamowa barazana a rayuwarsu. "Amma bai furta yana sonki ba. Kodai bukatar ce kawai yake nufi?" Ta ji zuciyarta babi dadi da wannan tunanin da tayi. Ta yi ringingine saman gado tana duban Hanif dake wasa da zobenta. Tunaninta bai wuce anya dagaske Ma'aruf yana sonta ba? Tafi bawa zuciyarta kawai bukatarta yakeyi. Ba don hakan ba ma bazai nemeta ba. Da bakinsa ya kushe halittarta, ya nuna mata nan duniya ya k'arfin kasancewa da ita. Ita kuwa ta yaya ma Aisha zatace kada ta k'i bada kai? Ta numfasa ta rik'o hannun d'an kamar shine uban take maganarta a fili. "Kai, bazan yi yanda yakeso da wuri ba, sai naji gaskiyar abinda ke zuciyar babanka." Hanif dai banda ihu-ihunsa da 6angale dariya babu wani abu da yakeyi. Ta d'an kama kumatunsa. "Ni ce fa Bintun Mami! Zamiyi maganinsa ko?" Ta k'arashe da 'yar dariya. Ba ita ta fito daga dakin ba saida ya kwalamata kira. Ta janyo (After Dress) ta zura tana murmushi ta fita. Yana zaune saman kafet yana amsa wayar Abbansa, saidai hakan bai hanashi binsu da kallo ba har suka zauna. Hanif ta ajiye gefe sannan ta mik'e ta dauko komai na bukata wajen cin abinci. Ta soma zubawa ta ji muryarsa. "Fati." Bata amsa ba, ba kuma ta fasa abinda takeyi ba, saidai kiranta da yakeyi da Fati, yana sanyamata jin wani abu. Ya k'ara kiranta da murya da sigar da bazata iya ji ta kyale ba. Dole saida ta yi dagaske wajen saita tunani da nutsuwarta, ta d'ago fuskarta a daure, ba k'aramin namijin k'ok'ari tayi ba wajen dubansa. "Na'am." Ganin yanda ta tur6une fuska sai ya ji haushin kansa. Ya manta da cewar Bintu ce fa, yanzun d'an abubuwan da ya aikata zasu sanya ya janyowa kansa sabon raini. Ya sosa hanci. "Kada dai ki dauki abin d'azu a matsayin wani abu, haka aure ya gada. Eh, kuma ba zai yiwu gida bai k'oshi ba a bawa na waje. Abar batun nan, ya wajaba lallai a gareni ni da ke mu zamto masu tsoron Allah mu dunga sauke hakkokin juna. Hakan zai fi mana kyau." Shi kam, bak'a sosai yaso yarfamata. Baisan ya akayi ya kasa ba. Anzo ga6ar da zata maida martani, don haka ta tura mishi farantin abincin gabansa, ta dubeshi ta kauda kai tana murmushin mugunta. "Na farko dai ni bani da bukata, hakki kuma na yafe nawa, kuma Yaya ka manta kace babu abinda zakayi da jikina. Ka kuma ce kallona kan tashi zuciyarka. Ni ce fa wannan yarinyar da kake fad'a. To nidai bani buk'atar komai nagode da niyya." Ya rasa me zaice? Saidai ya maze ya sha mur. Kamar yayi magana sai ya fasa ya hau cin abinci yana ta nanata maganganunta a ransa. Lallai ma yarinyar nan, wato haka take da riko? Ya ji ta ba shi haushi, ya d'an dubeta da niyyar fad'a, saidai bazai iya ba, wai wane irin muguwarl soyayyarta ce tayi mishi kamu har haka? Kallonta ma wani nishad'antar da zuciyarsa yakeyi. Ya daure batare da ya kalleta ba cikon sanyin murya yace. "Please leave me alone." Yanda yayi maganar baisa ta nuna tausayinsa a fuska ba, iyakar magana ai ya gasa mata. Ta dauki Hanif har da wani cillashi sama tana dariya. Daga haka ta shige dakin Hanif. Ji yayi ransa na k'una, wato ko a jikinta? Shi kuwa yaya zaiyi ne ta gane zuwa yanzu yayi nadama? Lallai so na sanya ladabin dole. Yau shi ke bin Bintu! Ya runtse ido. * * * Tun daga ranar ya fita hanyarta, duk da cewar ta damu a 6oye, hakan baisa a fili nuna kamar batasan me yake yiwa fushin ba. Ta daure ta cigaba da walwalarta yanda ta saba babu ko nuna wata alama ta damuwa. Ranar da ta je gida wuni, shima ranar yana ajiyeta ya nufi gidan abokinsa Hashim. "Ya akayi ne wai? Please mafita zakaban banason dariyar banza." Hashim ya tsagaita dariyarsa. "Sorry, mamaki dai nayi ne. Kamar ka ace ka auri wannan ficikar yarinyar har ma ka soma sonta? Abinda ko a mafarki bazakayi kuskuren gani ba kenan." Ya fahimci Hashim na tunano mishi furucinsa ne. Ya lumshe ido kafin ya bud'esu ya dubeshi ransa a 6ace, ya ja guntun tsaki. "Bazaka gane ba, banason tuna baya." Hashim ya numfasa ya gimtse dariyarsa. Daidai sadda Salimarsa ta shigo ta ajiye musu kayan motsa baki. Ta tambayi lafiyar Amarya. Ya amsa da murmushi. "Lafiya, ai kun kyauta tunda shi bai kawoki ba kekuma bakizo ba." Hashim da Sally sukayi dariya. "Tuba nake, zaku ganni very soon in sha Allah." Ya jinjina kai yana shafa sumarsa fuskar dauke da murmushi. Bayan fitarta daga falon, Hashim ya dubeshi. "Kai zakayi wannan yak'in har ka siye zuciyarta." Ya yatsine fuska yana dubansa. "Ta yaya kenan? A tunaninka zan durkusa na rok'eta ta soni? Never! Furuci d'aya nayi mata wanda a yanzu nake (regretting, I'm in need of her)." Hashim ya ja tsaki. "Kana da matsala, dole kuma ka sauke wannan ji da kai ko ince girman kan da kake nunamata wallahi." [7/26, 12:44 PM] +249 99 842 9948: ¶°°BINTU°°¶ ©Rufaida Omar (July...2016) <<44>> Shi kuwa iyakar dauriyarsa kawai yayi, yana son kusantar tafi haka, saidai bayaso yayi gaggawar da zata fassarashi baibai. Watakil ba zata fahimci yanda yake so da kaunarta ba. Ya ji sadda tayi bacci, shi d'in kuwa ya jima kafin baccin yayi awon gaba da shi hakance ta sanya baiji kiran sallar asuba ba. Ta k'ura mishi ido tana kallon irin baiwar da Allah Ya bata na samun mutum mai kyau da kwarjini irin Ma'aruf, ba wayonta ba ba komai ba. Bacci yakeyi hankalinsa kwance, dakyar ta iya mik'ewa ta fad'a toilet. Saida ta kammala tsarki da alwala ta fito. Har lokacin bai tashi ba. . Ta d'ora zani saman rigar baccinta tayi shirin tayar da sallah tsaf sannan ta tashe shi a hankali ta hanyar bubbuga k'afarsa. Ya waro ido yana 'yar mik'a. Ganinta da hijab, ya sanyashi azamar mik'ewa. Saida ya kammala sannan ya fice zuwa masallacin gidan dake kallonsu. Ita d'inma Sarah ta tayar, ta koma tayi nata. Ta jima da gama addu'o'inta da komai, har rana ta d'an fito, tana son ta d'an runtsa saidai tana tunanin Hanif. Zata fita sukaci karo zai shigo, ta tsorata, ai ta dauka babu abinda zai maidoshi. Ta gaisheshi ya amsa kafin ta ba shi hanya. "Ina zaki?" Ta dubeshi. "Aiki zanyi." Ya ja hannunta ya rufe k'ofar. "Aiki da asubar nan Fati? Bari zuwa anjima naga yau dai ba makaranta zaki ba. Bai bari tayi magana ba ya nufi ciki da ita. Har gado ya ajiyeta ya kashe fitilun ya zagayo ya kwanta gefenta. Ta runtse ido jin abinda yakeyi. Ya kuramata idanu yana murmushi. "Fati." Ya kira sunanta cikin sigar da ba zata jura ba. Bata iya amsawa ba. "Look into my eyes, please." Ta bud'e idanunta a hankali ta sauke cikin nashi, da sauri kuma ta maida ta rufe. Yayi murmushi ya soma magana ba tare da ya bar abinda yakeyi mata ba wanda ke kunce notinan kanta. "Zaman da mukayi dake tare yasa na damu dake yanzun, kin samu wani babban gurbi a zuciyata Fati..." Sai kuma yayi shiru. Ba wannan takeson ta ji bani ta so ba, yanda ya soma bi da ita yasa ta soma fita hayyacinta, saidai da sauri ta mik'e zaune ya dubeta da soyayyun idanunsa. Da saurinta ta mik'e kafin ya ankara ta nufi k'ofa. "Tsaya!" Ya fad'a da 'yar muryarsa. Ta tsaya cak, ta sa hannu tana m'ara suturce jikinta, a yanzun shi kuma ya shiga matsanancin damuwa, Bintu bata son shi, shine kawai abinda yasa wa ransa. Hakan yasa shi mik'ewa gami da gyara rigarsa ya nufi inda take. , "D'akinki ne. Baki kamata na takuraki ba." Daga haka ya fice. Ta bishi da kallo kafin ta lumshe ido tana murmushi. Ta yarda ta kuma gaskata cewar Ma'aruf fa yana sonta yanzun, saidai ta so yayi furucin da bakinsa ba wai yayita kwana-kwana ba. Ta koma ta kwanta gami da tattaro zanin gadon da filon da yayi matashi tana shinshina cike da jin sanyi a ranta. K'amshin turare Yaya Ma'aruf kawai ke tashi. Wasu ruwan hawaye suka kwaranyo mata. Ko a mafarki idan ance mata zata fad'a wannan hali na soyayya ba lallai ta gaskata ba, sai gashinan daga ita har Yayannata Allah Ya jarabcesu da fad'awa kogi na soyayyar juna, so mai wahalar da zuciya da gangar jiki kuwa. Shima a can, kasa bacci yayi, idan har bazai samu kan Bintu ba, to zai iya kamuwa da mugun ciwo kuwa don shi kad'ai yasan yanda yakeji a ransa. Yayi amanna cewar bazai iya son wsta ko kusantarta wata d'iya mace ba sai ita. Ita kad'ai yake so yake kuma buk'ata. Ya lumshe ido yana sakin ajiyar zuciya. Bintu kuwa har ta kammala komai ta bawa Hanif abincinsa tayi mishi wanka Ma'aruf bai fito ba. Ta gaji da zaman jira ta bar Hanif a hannun Sarah itama ta fad'a wankan. Har ta kammala ta shirya cikin doguwar riga d'inkin buba ta fito falon, shiru babu labarinsa. Hankalinta ya tashi, ta kasa daurewa kawai ta nufi d'akinnasa. Da sallamarta ta shiga, abin mamaki baya dakin, jin motsin ruwa ya bata tabbacin yana wanka ne. Hakan yasa ta fita. Saida ta kammala karyawa ta fiddowa Sarah keken Hanif baranda ta shiga turashi, ita kuwa zama tayi jugum har zuwa sadda ya turo k'ofar ya fito. Tasan yau babu aiki, to meyasa ya shirya cikin manyan kaya. Zama yayi a gefenta, duk yanda yaso ya nunamata yayi fushi, bai iya hakan ba, musamman ma ganin yanda ta ci ado, duk sai ya raina ajinsa, to ita d'inma hakanne a wajenta. "Fati." Ta narke fuska. "Nidai gaskiya ka daina kirani Fati." Yana murmushi ya jefamata tambaya. "Why?" Ta turo baki "Sunan fa Mami ne, kacemin Bintu na yanda kwa ya sanni da shi." "Ok, Bintuna, had'amin tea." Ta dubeshi ido waje sai kuma tayi k'as da kanta don batason kallon da yakeyi mata, irin kallon da Aisha ke gayamata a baya ta k'aryatashi, a yanzun kuwa ta gask'ata lallai akwai shi. Batayi aune ba ta ji ya tallafo ha6anta da hannunsa na dama kafin kuma ta ankara tuni ya soma mata sak'o. Abinda ya keyi zai tabbatar ya mance a inda suke, wannan karon ba k'arfinta ne ya kwaceta ba sai wayarsa da ta dauki ruri. Alokacin ta ja gefe. Ya duba Abbansa ne, cike da girmamawa ya dauka. Abba ya hau fadan dadewar da yayi bai zo sun wuce ba. Ya bashi hakuri gami da mikewa, a tsaye ya kora tea din kadan sannan ya koma daki, jimawa kadan ya fito cikin yadi maimakon shaddar da yasa a farko. Ta kauda kanta, yana murmushi yace"Saina dawo, zan fita da Abba. Ki shirya tarbata mai karfin mata goma." Ai a guje ta fad'a dakinta, ya fice yana dariya. , (Nagode wadanda sukamin ya jiki, da ma wadanda basuyiba a rubuce amma sun kirani, da ma wadanda basuyi duka ba amma sun damu da hakan. Allah Yabar zumuncinmu..love oll)
0 comments:
Post a Comment