BINTU Part 005
BINTU Part 005 . Ta bud'o hoton tana kalla. Yana zaune cikin motarsa a mazaunin direba. Ya juyo har da wani tankwashe k'afafu, hannunsa na dama dafe da ha6arsa yana murmushi har da wani k'ank'ance idanu. Ya gama had'ewa cikin lemon-green na shadda ta sha aiki. Farar hula ce mai adon lemon-green a saman kansa. Ta bishi da kallon tsaf, tasan yanada kyau, bayan wannan ma, yana da wasu nagarta na mutunci da yake nunawa jama'a da dukkan wad'anda yakeso kad'ai, amma idan bai k'aunar mutum, to fa anan ka shiga uku. (Atunanin Bintu kenan). Sai kuma ta tsinci kanta da fad'awa kogin tunanin wanda ya d'aukeshi hoton. Ta k'urawa hoton ido, anan ta gane alokacin Ma'aruf da k'ibarsa wuyansa a cike ba kamar yanzun da ya rame ba. Hoton zai dan kwana biyu da alamu. To kodai Hashim ya d'aukeshi? Sai kuma ta girgiza kai, ba zai kashewa Hashim idanu haka ba. Ta yi jim, sai kuma ta ja tsaki ta kashe wayarta. Me zai sanya ta damu kanta da tunanin abinda bai dameta ba. Ta lumshe ido a haka bacci yayi awon gaba da ita. Abinda ya bata mamaki bai wuce yanda tayi mafarkin Yaya Ma'aruf ba, wai gashinan ta tsareshi da tambayar wacce ta daukeshi hoto har ya kawo mata duka. . Koda ta farka, sai mafarkin ma ya bata dariya da haushi. Lallai jiya ta ci ta k'oshi. Washegari ya kama asabar babu makaranta, wannan yasa dukkansu babu wanda ya taka waje. Lokacin k'arfe sha biyu na rana ta kusa saidai Ma'aruf ko falon bai lek'o ba, haka itama Bintu, tana kammala gyare-gyaranta ta koma d'aki abinta ganin bai tashi ba ballantana ta gyara. Sai wajejan sha biyu da rabi ta ji fitowarsa falon. Anan kuma ta ji yana kwala mata kira. Ta ajiye wayar da take dannawa ta fito. Yana zaune ya hard'e kafafunsa a saman tebur, yayi wankansa yana sanye cikin riga ja da wando fari na jeans. Kallo d'aya yayi mata ya had'e rai. "Wai ban hanaki yin shiga anyhow a gidannan bane?" Ta dubeshi sannan ta dubi abinda ke a jikinta. Doguwar riga ce 'yar kanti saidai tana da fiddo halitta kwarai. Ta turo baki kad'an sannan ta zauna tana dubansa kad'an. "Wallahi Yaya kaima kasan manyan kaya suna takuramin a rayuwa. Ko a gida bana sanyawa." Ya furzar da iska kawai, bazai iya fitowa ya sanarmata dalilinsa ba. Shi kansa yana jin ma kunyar tuna wai surar yarinyar da ya raina ke d'an hargitsa shi ba. "Kawomin breakfast." Ta saci kallonsa tayi murmushi lokacin da ta mik'e. Ai tasan manufarsa ta hanata sanyawa. Ita fa ba yarinya bace. Tana shiga kicin tayi kwafa. "Lallai zakayi ka bari." Ta ayyana a ranta. Ta k'udurta a ranta ba zata bar shiga irin yanda ta so ba don ko a can gida ma bata fasa ba. Ta had'omishi kayan kari ta fito. Ya sauke k'afarsa saman teburin ta ajiye sannan ta koma ta zauna. Ya d'an dubeta kawai ya basar, ya soma k'ok'arin had'a tea. "Yaya, baka kewar Hanif? Don Allah ka rok'i Mami su dawo nan." Ya d'an ji sanyi a ransa. Kamar bazai amsa ba sai kuma yayi magana. "Munyi magana da ita jiya, zan iya tahowa da shi a yau." Haba Bintu ta hau murna har tana washe hak'ora. Yana lura da yanda tayita faman shige da fice, daga d'akin da Ma'aruf ya tanada don d'anshi kad'ai wanda aka k'awata da kwalliya da ya kamatu a d'akin yaro. Can kuma sai ta nufi kicin ta d'auko duster ta goge. Kallonta kawai yakeyi, hakanan kuma ya ji ta burgeshi. Yana so yaga ana son d'ansa Hanif. D'an soyayya kenan. Bintu kuwa, a wannan 6angaren ya tabbatar ba shi da matsala ko kad'an da ita. Tana son d'anshi. Yana kammalawa ya fice gidan. Sai wajejan biyar na yamma Aisha ke tabbatar mata yazo ya taho da Hanif, zuwa lokacin ya sallami Atine da goma ta arziki, Atine har kuka tayi saboda murna. Ai kuwa nan Bintu na jin sun taho ta mik'e ta fad'a kicin, har ta kammala tuk'a tuwon semovita miyar ku6ewa babu labarinsu. Can kuma sai ta ji k'arar bud'e gate wanda ya bata tabbacin shine. Ta bud'e k'ofar, bayan yayi fakin ya fito yana rik'e da Hanif a hannu. Yaron ya k'ara narka uban k'iba, ya k'ara wayo. Ga shi fari k'al da shi kamar mahaifinsa. A kammani kuwa, zuwa yanzu sai ka kasa bambance kamannin wanda yafi rinjaye, tsakanin babansa da mamarsa. Sunayin sallama ta amsa da saurinta ta kar6i Hanif ta cillashi sama ta cafe tana dariya. Shima Hanif d'in ganin haka ya kyalkyale da dariya. Tuni ta juya ciki tana fad'in. "Oyoyo d'an Mami." Ya shigo da 'yar jakar Hanif ya rufe k'ofar. Kallonsu yakeyi domin kuwa alal hakika sun burgeshi. Yana zama ta dauki jakar yaron sukayi d'aki. Ya shafi sumarsa yana murmushi, lallai Bintu ba k'aramin so take yiwa Hanif ba Bintu fa ansamu abokin hira. Ai kuwa bata fito falon nan ba sai bayan sun gama wasa da Hanif. Tayi mishi wanka ta chanja mishi kaya bayan ta shafa mishi hoda a jikinsa da fuskarsa, sannan ta sanyamishi riga da wando jikin cotton, na baccinsa. Ta dubeshi tana dariya irin wacce ake yiwa yaro na wasa. "Inye, kaga bebina yayi kyau. Zo muje falo muci abinci." Ta d'aukeshi, yana rik'e da d'an ball sai ihu yakeyi yana sanya bakinsa a jiki. Tayi mamakin ganin Ma'aruf zaune saman carpet ga filet a gabansa har ya kammala cin abinci ma. Ya hard'e k'afa yana kallon The Dr's a Mbc4. Ganinsu ya sanyashi juyowa. Nan ya mik'awa yaronsa hannu yana murmushi. "Come to me my boy." Bintu ta dire mishi yaron sannan ta d'auki filet tayi kicin. Jimawa kad'an sai gatanan ta fito rik'e da faranti itama ta zubo tuwo. Ta ajiye ta koma ta d'auko ruwan roba saboda Hanif, marar sanyi. Itama ta d'aukowa kanta pure water mai d'an sanyi-sanyi. Ta dawo ta zauna. "Zo mu ci abinci." Ma'aruf ya tankwashe k'afafu. "Juyo da abincin nan zan ba shi." . Ta dubeshi, kai har takan yi mamakin irin wannan so da yake yiwa d'ansa. Ba musu ta juyo da filet din. Tana ci a yangance ne saboda wai tana gaban miji, ta ji ance ba'ason yin loma babba. A gida ma bata fiye yi a gabansa ba saboda tsoron fad'ansa, da dai Rufa'i ne, to shi kam babu kalar lomarta da baisani ba. Bayan ta kammala ta ja baya tana shan ruwa. "D'aukomin tissue a d'aki." Ta mike zuwa d'akin. Ta k'ara k'arewa d'akin kallo tamkar bak'onta. Zata d'auko ne, ta hangi BlackBerry dinsa da ke jone a chaji tana faman (vibrating) alamun dai kira ya shigo. Ta nufi wayar ta duba. "Lawisa" Shine sunan da ta gani kawai, babu wani sakaye. Ai kuwa bata manceta ba, k'awar Yaya Abida yayar Ma'u dake yawon zuwa gidansu neman soyayyar Ma'aruf tana fakewa da duba d'ansa. Ta rik'e k'ugu, yau zatayi maganin shegiya ashe. Ta d'aga. "Hello." Bintu tayi shiru. Sa'a ta k'ara magana. "Haba Ma'aruf, so fa ba hauka bane da zaka dunga wulakantani, don kayi aure shikenan sai kuma ka daina kulani gaba d'aya. Me zakayi da yarinya wacce batasan rayuwa ba?" "Uwarki da ubanki zaiyi dani." Cewar Bintu a zuciye. Lawisa tayi shiru kafin tace. "Ni zaki yiwa rashin kunya? Ina mai wayar?" Bintu ta dubi k'ofa babu alamun mutum, ta cigaba da magana a hankali. "Ya shiga wankan sunnah. Ke wai bakyajin kunya ne Lawisa, don yau bazan kiraki antin ba. Babba dake, iskancinki ya rasa kan wa zai fad'a sai tatta6a kunnenki(cewar bintu, don Lawisa bazata fi talatin da wani abu, ta girmewa Ma'aruf). Toh wallahi kika k'ara kiran mijina sai na bazaki a duniya na kiraki karuwa. Ai ina sane cewar ba son Allah kikeyimai. Idan kuma don wannan ne, karki damu, mace mai karfin mata goma ce ni." Ta katse kiran da sauri jin Ma'aruf ya kwalamata kira. "Na'am!" Ta amsa murya a d'age, a fili tace. "Shima Yaya Ma'aruf, ya rasa wacce zai kula sai Lawisa. Ai wallahi ko ni mace banga abin burgewa awajenta. Idan Yaya dan iska ne ya k'are a Lawisa ya ci baya wallahi." Ta zari tissue ta fito tana masifa a zuciya, a gefe d'aya kuwa, ta ji dad'in yanda ta ci mutuncinta, daman ba tun yau take dakonta ba. Ya jefata da wani irin kallo. "Me kika tsaya yi?" Fuskarta a sake tace "Babu komai." Kamar yayi magana, sai kawai ya fasa. Ya kar6a ya gogemishi inda ya 6ata a jikinsa da baki. Ta dauke filet d'in ta maida kicin sannan ta kawo ruwan wanke hannu. Bayan sun wanke ta kai kicin ta zubar. Ta tsaya tana dubansu, babu alamun dai Hanif yana jin bacci. Ita kuwa Allah Allah takeyi ta shiga makwancinta kafin ta6argazar da tayi ya fito. Ta zauna don tasan sai an kammala koda zai shiga d'aki. Hanif ya rarrafo wajenta, nan kuma tabar batun kallo ta k'ara shagaltuwa wajen yi mishi wasa. Ta dubi Yaya Ma'aruf wanda yake satar kallonsu. "Yaya, wallahi yanzu na rasa da wanda Hanif ke kama, idan na hango kamanninka sai na hango na mamansa." Ya lumshe ido ya bude da murmushi saman fuskarsa. "Kamannin wa kika fi hangowa?" Yayi furucin hankalinsa na ga tv. Ta k'urawa Hanif ido, sai kuma ta dago tana yiwa Ma'aruf kallon k'urillah. Sannan ta maido dubanta ga Hanif. "Kaga hancinku d'aya, bakinku ma haka, duk k'aramin baki gareki. Idanuwan ne dai kamar na Mamansa." Ya kwantar da kai jikin kujera yana dubanta da murmushi, Ma'aruf bai fiye hayaniya ba sai akan Bintu wacce ke sanyashi dole don muddin bazata kiyaye abinda baya so ba, to fa za tayita wahala a hannunsa. Ta kauda kanta ganin ba shi da niyyar magana. "Ai dole yafi kama da ni don na fi sonshi akan mamansa dama." Bintu ta amsa. "Allah Yasa dai kada ya dauko halinkuuuu. Allah Yasa da halayen Annabinmu (s.a.w) zaiyi koyi." Abinda ta fada a farko ya fusatashi saidai jin kalamanta na k'arshe yasa ta d'aureshi, babu abinda zai iya ce mata. Ganin ta tsira yasa ta yi mishi saida safe. Zata shige ya dakatar da ita. "Ki kula, nasan kalar baccinki, muddin na lek'o naga kin danneshi ni da ke ne." Bata ce uffan ba ta fad'a dakinta. Bayan ta ajiye Hanif ta fita ta dauko jakarsa da ruwan zafi a flask wanda ta dafa saboda shan firisocrim dinsa. Kulle k'ofarta tayi harda mukulli, tasan yau ya shiga d'aki ya dauki wayarsa to babu abinda zai hanashi kusan ci mata zarafi. Acan kuwa Lawisa an k'ulu an kuma ci alwashi akan Ma'aruf ko babu aure! Daman kamar Bintu ta sani, abinda ta fi bukata kenan da shi bawai auren ba. . A 6angaren Ma'aruf kuwa, yana shiga d'akin ya ajiye wayarsa k'arama marar tsada sosai k'irar Samsung, da ruwan shan da ya shigo da shi. Ya rage kayan jikinsa ya fad'a wanka. Bayan ya fito ne ya shirya cikin riga mai hannun singilet da wando iyaka gwuiwa na bacci. Alokacin ne kuma ya zare wayarsa daga chaji. Yayi mamakin ganin kira rututu na Lawisa. Kamar bazai kirata ba sai kuma ya kira, don baisan dalilin wannan yawan kiran ba duk da ba yau ta saba kiransa ba saidai muddin ta kira sau d'aya zuwa biyu bai d'auka ba bata matsawa kanta. Bayan ta d'auka, yayi mata sallama, ta amsa. Kafin ya kai ga tambayar ko lafiya ta hau magana. "Ka gargadi matarka ta kiyayeni, domin nafi k'arfin wulak'anci." Yayi shiru kad'an, menene had'inta da Bintu kuma? Ya had'e gira. "Idan zakiyi magana yanda zan fahimta kiyi, idan kuma bazakiyi ba, lokacina ba na shirme bane ok?" Nan ta shiga zayyane mishi dukkan abinda ya had'asu. Kusan dariya ya so yi sakamakon kalaman da Bintu ta jefata da su. Har yakai ga murmushin mamaki. Wato har tasan wani wankan sunnah? Hum. Shi fa yana yi mata kallon wacce batasan komai ba. "Kana jina kayi shiru!" Ta fad'a ranta a 6ace. "Duk abinda matata ta fad'a hakane anyi, kiyi hakuri banji dai dadin zagin da tayimiki ba, zan gargad'eta. Ya dace zuwa yanzu ki bar rayuwata Lawisa, ni na gayamiki bazan iya biyayya ga abinda kikeso ba, ba kuma zan iya aikatawa ba. Lokaci yayi da zaki kyaleni, daman ina kulaki ne ba don komai ba sai don girmemin da kikayi da kuma kaunar da kike nunawa d'ana kafin ki 6ullo da wannan batun naki marar kyawun ji. Kiyi hakuri Bintu bata kyauta ba da ta zageki wannan kuma zan gargad'eta." Tayi shiru don takaici, kawai ta kashe wayar. Ya ta6e baki ya jona Samsung d'insa a chaji. Kamar ya je yanzun ya samu Bintu, saidai ya hak'ura zuwa gobe. Haka ya kwana zuciyarsa babu ko d'igon damuwa. Washegari tun tashin Bintu da asuba bata samu damar komawa ba adalilin Hanif, bataso ya tashi neman abincinsa. Tasan mai yiwuwa ya tashi cikin dare amma nauyin baccinta bai barta ta ji ba ballantana ta had'amishi abincinsa. Tana farkawa ta had'a ta ajiye yanda zai d'an huce kafin ya farka. Ta mik'e ta koma falon ta tsaftace har kicin, saida ta kammala komai misalin takwas da rabi ta d'ora abin kari. Kafin ta kammala Hanif ya tashi, ta koma gareshi, tana d'aukarshi tayi bandaki, daga zuwa cire famfas ta 6ige da yi mishi wanka, suna fitowa ta tuno da ruwan da ta dora. Da gudu ta direshi saman gado ta nufi kicin. Har ya k'one sauran kad'an, haka ta k'ara wani ruwan akai da Lipton. Ta fito tana jinjina kokarin mata. Haka suke fama ashe. Ta koma dakin ta shirya Hanif cikin riga fara mai adon purple da bakin jeans bayan ta sanyamishi wando. Ta sanya mishi safa mai fari da purple itama. Ta d'ora mishi bif a wuyansa gudun kada ya 6ata jikinsa. Haka ta daukeshi suka fito falon. Anan k'asa ta zaunar da shi, ta koma ta dauko abincinsa da ta dama ta ajiye saman tebur sannan ta fad'a kicin ta kashe ruwan zafi ta juye a flask. Daman shi kadai ya rage mata tayi. . Ta jera komai saman faranti ta kawo ta ajiye saman tebur. Sai lokacin ta samu nutsuwar dawowa ga Hanif ta shiga ba shi a baki. Ai kuwa ya hau sha da sauri. Ya bata tausayi, ta tallafi kumatunsa. "Sorry bebina, na barka da yunwa." Fatansa ta cigaba da ba shi. Saida ya shanye tas har yana gyatsa sannan ta bashi ruwa ta gyara mishi bakin ta cire bif din. Bayan ta kammala ta mik'e. Saida ta gama gyara komai a kicin ta dawo ta daukeshi zuwa d'akinta, kayan wasanshi ta dauko ta dire mishi kayan wasa kala-kala. Nan kuwa ya rikice yayita iface-ifacensa yana wasa. Ganin haka ta hau gyaran gado ta kwashe kayan wankinsu, saukinta akwai mai wanki. Ta ware na Hanif tunda kala d'aya ne bazai gagareta wankewa ba, ta hada nata a inda ta saba sati-sati ake wankewa. "Bari na shiga wanka bebina, banda rigima." Baimasan tana yi ba, sai wasansa yakeyi yana jik'a kayan wasan da miyau. Ganin su biyu ne kuma batason yayi rigima yasa ta bar band'akin a bud'e. Duk kuwa da cewar bata hangoshi, amma tafison ta dunga jinsa kada ya hau kuka. Saida ta kammala wankan ta hau wanke mishi kayansa da ta cire. Bangaren Ma'aruf kuwa, tara da mintuna ya tashi. Wanka ya soma yi ya zura jallabiya mai hula irinta 'yan Morocco sai dogon wando daga k'asa marar nauyi. Ayau kam koda zai fita baya tunanin fita da wuri. Yana fitowa falon ya shak'i iska mai dadi, a 'yan zaman da sukayi ya tabbatar Bintu ba yanda ya d'auketa take ba, ba mai son jiki bace wajen kula da gida. Ya hangi kayan kari a saman tebur, saidai kuma jin iface-ifacen yaronsa yana wasa ne ya sanyashi nufar d'akinta. Anan tsakar d'akin ya tarar da shi yana wasa, ya k'arewa d'akin kallo, kafin ya sanya hannu ya dauki yaron ya cillashi sama yana dariya. K'arshe ya sakar mishi kiss a le66ansa. Yaron sai k'amshi yakeyi. "Hey, ina Mamanka?" Ya tambaya cikin kunnen yaron. Hanif sai dariya yayi kawai. Jin dariyarsa yasa Bintu fitowa rik'e da rigarsa da ta matse, daga ita sai tawul, bai kai ga rufe cinyarta ba. Ido hud'u sukayi da Ma'aruf, tayi azamar komawa ciki. "Au Yaya kaine?" Bai amsa ba don babu k'arfin amsawar, ya juya kawai ya fita daga d'akin zuwa falo. Ya tsinci kansa cikin wani yanayi, lallai shi d'in bai zamo dutse ba, yana da buk'ata. Ganin Bintu a haka ya dagula lissafinsa, babu laifi yarinyar tana da abin gani a fad'a a jikinta. Ya kai kusan mintuna biyar anan yana waya da Abba da Maminsa kafin ta fito, ajiye wayar kuma yayi daidai da fitowarta. Kallonta ya jazamishi jin wani irin shock tun daga tsakar kansa har tafin k'afarsa. Ya gaza d'auke idanunsa daga kanta. Wata shegiyar riga ce a jikinta wacce ta matseta. Hannun rigar d'aya irinta vest, d'ayar kuma hannun 3-quarter. Ruwan toka ce rigar, sai wando shima iyaka gwuiwarta bak'i mai kamar roba, hakan yasa ya kamata ya fiddo da zahirin halittarta. Sai hula da ta rufe kan da shi. Ta sakarwa Hanif dake gefensa murmushi tayi kamar bata ga kallon da Ma'aruf ke binta da shi ba. "Bebina, bari na shanya kayanka ko?" A haka ta nufi hanyar waje. Sai lokacin ya dawo hayyacinsa. "Baki da hankali zaki fita a haka?" Ta tsaya, saida ta kammala murmushinta kafin ta juyo ta yi mishi wani irin narkakken kallo... . "Ya Ilahi." Ya fad'a a ransa. Baisan lokacin da muryarsa ta sanyaya ba. "Kada ki fita haka please." "Please?" Ta maimaita a zuciyarta da mamaki. Yau kuma Ma'aruf ke bata oda harda rok'o. Sai kuma ta ji jikinta yayi sanyi. "To a ina zan shanya?" Ya kauda kai ga dubanta. "Jeki zan sanya a shanya. Sannan please ki ringa suturta jikinki saboda aljanu." Ta yi murmushi kawai sannan ta koma d'akinta. Tsalle tayi ta fad'a saman gado kafin ta tuntsire da dariya. Yaya Ma'aruf kenan, yana wasa da ita. Ta yi kwafa. Zaiyi bayani ne. Ganin ta soma jin yunwa ne yasa ta mik'ewa dole ta chanja shiga zuwa doguwar riga ta shan iska, jallabiyar mata. Ta fito, baya falon saidai ya sauke Hanif daga saman kujera. Abin ya bata dariya, ta had'a tea abinta ta soma karyawa tana yiwa Hanif wasa. Ranta fari sol, ganin mazan sun soma russuna, ashe ma abin a baki ya tsaya? A d'aki kuwa, Ma'aruf ya shiga wani hali, dole saida ya had'a da fad'awa band'aki gami da sakarwa kansa ruwa. Kusan shekara kenan, shi d'in dai mutum ne kuma mai lafiya. Tunaninsa ya soma kuncewa akan Bintu. Ya soma jin wani abu a ranta yana tunani. Eh! Tunani kawai yakeyi, don ba shi da tabbas. Kawai ya dauki abinda yakeji da wani suna na daban wato sha'awa! Banda haka babu wani abu. Acewar Ma'aruf Abdullahi. Wannan ne silar share maganar Lawisa baiyiwa Bintu ba. Da daddare tana ji tana gani ya shirya maida Hanif wajen Mami, ranta bai so ba saidai jarabawa zasu soma a makaranta gashinan babu mai rik'o. Akan hakan yace Mami ta nemar musu yarinya da zata iya rik'eshi su je makarantar tare ko su zauna gida har Bintu ta dawo. Tun faruwar hakan sai ya zamana Ma'aruf ya rage zaman falon lura da yayi na zata fasa shigar kananun kaya ba. Ita kuwa wani sa'in ba da gayya takeyi ba, sai don hakan ya zame mata sabo. Tun bata rufe kanta har ta zo ta saba adalilin yawan tunasar da itan da yakeyi ta hanyar rankwashin kan. Watarana tana zaune a falo, fitowarta kenan bayan ta idar da sallah. Ranar ya kasance juma'a. Sai ga shi shima ya shigo dawowarsa daga masallaci kenan. Tayi mishi sannu da zuwa. "Shirya zamu fita." Wani sanyi ya mamayeta, daman zaman ya gundureta. Tayi shiga ta manyan kaya. Leshi ne light blue dinkin riga da siket ya zauna d'abas a jikinta. Ta k'ara gyara kwalliyar fuskarta sannan ta yafa mayafi dark blue hakanan takalminta mai d'an tsini shima dark. "Kina ina?" Jin muryarsa yasa ta saurin d'aukar jakarta wacce ta yiwa ciko sai wayarta. "Gani nan." Tayi mishi kyau kwarai, to babu damar nunamata, ya soma tafiya. "Muje." Ta rufe gidan ta bi bayanshi. Gaban motar ta zauna shima ya shiga ya tayar. Ta saci kallonsa, sai kawai ta ji ya burgeta ganin kamar yau din yana cike da nishad'i. Tunaninta ya tafi a inda zasuje, sai ware ido takeyi. Shima baice mata uffan ba. Ganin sun shiga layin gidansu ta saki ihu murna. "Ke banason hauka!" Ya fad'a cikin fad'a-fad'a. Ta nutsu tana dariya. "Wallahi Yaya wani dad'i ne ya rufeni." Yayi murmushi kawai batare da yace uffan ba. Ji takeyi kamar ta 6alle murfin motar ta fad'a ciki tun kafin maigadinsu ya bud'e gate. , Ai kuwa yana shiga da fakin ta bud'e murfi ta fita da saurinta ko waigowa batayi ba ballantana ta rufe mishi k'ofar motar. "Mamina! Mamina!!" Ta hau kwala kira. Da Aisha suka soma cin karo kuwa, duk da cewar sun saba ganin juna a makaranta, amma yau ganin na gida daban yake da na koyaushe. Fitowar Mami ya sanya Bintu runtumawa a guje ta rungumeta. Mami itama rungumeta tayi tana mai cike da tsantsar farincikin ganin yanda d'iyarta ta k'ara k'iba da kyawu. Ma'aruf da Aisha sai abin ya burgesu, wannan k'auna da Mami da Bintu ke yiwa juna daga Allah ne kawai. Can kuma ta saketa tana dariya gami da kwantar da kai a kafad'arta. "Wallahi Mamina nayi kewarki da yawa." Mami ta rik'e hannunta suka k'arasa suka zauna. "Nima nayi Bintuna, amma nagode Allah da yanda na ganki kinyi kyau." Ya k'araso ya zauna gami da gaida Mami. Ta amsa cike da farinciki. Yau wani dadi takeji. Nan fa suma masu aikin suka hau murnar ganin Bintu abokiyar hirarsu. Abba ma yana shigowa ya zauna a falon ransa fari k'al. Hira sukeyi kamar ba surukanta ba. Bayan Abba da Ma'aruf sun shiga falonsa ne Mami ke labarta mata cewa ansanya ranar bikin Aisharta nan kusa. Baki ta saki da mamaki. "Amman Aisha bata gayamin ba?" Aisha ta harareta da wasa. Mami ta amsa tana murmushi. "Kwana uku kenan da kawo kud'in, nan da watanni uku za'ayi." Kai, ranar Bintu ta yi murnar da ta jima batayi ba. Idan ka ganta da Ma'aruf a gaban iyayen saika rantse babu wata 6araka a tsakaninsu. Har takwas na dare tana gidan. Lokacin ne kuma Ma'aruf ya dawo daga 'yar unguwar da ya je. Ya zauna yana duban yanda ta yi filo da cinyar Mami ta d'ora Hanif akan ruwan cikinta tana shan cakulet tana lasa mishi suna hira a haka. Ya girgiza kai yana duban Mami. "Mami kina son sangarta yarinyar nan, bansan dalili ba." Ta shafa kan Bintu tana murmushi. "Sunanmu d'aya, bani da kamarta." Bintu ta lumshe ido ta bud'esu akan Ma'aruf. Ya ji wannan ya basar. "Hakane. Sai ki taso mu tafi." Ta nark'e murya. "Kai Yayana tun yanzu?" Ganin gaban Mami ne yasa shi yi mata murmushin dole. "Au, da kwana zamuyi?" Mami ta sanya baki. Haka Bintu ba don ta gaji da ganin Maminta ba ta shirya suka tafi bayan Mami ta yi mata alk'awarin zuwa. . A mota suna tafe ya dubeta. "Kinason Mami." Ta numfasa da murmushi dauke saman fuskarta. "Tana sona shiyasa." Kamar yayi mata wata tambaya sai kuma ya share. Ya dubeta. "Zakiyimin rakiya zance ne ko na mik'a ki gida?" Tambayar ta zo mata iya wuya, shima d'in ya fad'a ne don ya ga yanda zatayi. "Kaini gida." Ta fad'a kusan a k'ufule. Baice uffan ba ya kad'a kan motar zuwa gida. Tana ganin tamkar wasa yakeyi, saidai kuma ta gane lallai dagasken yakeyi don a k'ofar gidan ya faka motar gami da dannan mabud'i ta gefensa. Dubansa tayi, bai dubeta d'in ba, saidai murmushi da yakeyi na mugunta. Ta bud'e a fusace ta fice. . Saida ya ga shigarta sannan yayi dariya kad'an ya d'agawa Audu maigadi hannu. "Ina dawowa yanzu." Daga haka ya bar layin. Wasa yakeyi mata domin kuwa abin motsa baki yakeson zuwa siyomusu. Bintu a fusace ta k'arasa ta bud'e kofar ta shiga. Ta kasa ta6uka komai, ta shiga safa da marwa falon bayan ta yar da jaka da mayafi da dankwali. A haka ta soma rage kayan jikinta. Ina Ma'aruf yaje? Wajen sauran cocaine(Sa'a) ko kuma Lawisa? Ran Bintu fa babu dad'i ta shiga wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa. To me hakan ke nufi? Me zai dameta da fitar Ma'aruf zance? Ta zauna daga ita sai undies, a fili kuma tayi furucin. "Ai ba wani abu tsakaninmu, me zai dameni?" Ta kusan mintuna uku, ta kasa hakuri ta fiddo wayarta a jaka. Ta lalubo wayarta ta nemo lambarsa. "Angrybird." Shine abinda ta rubuta a sunan Ma'aruf. Haka ta danna kira. Lokacin yana hanyar gidan, ya d'auko wayar ya duba. Baisan lokacin da ya dara ba ganin Bintu ce. Bai d'aga ba har ta yanke. Sai lokacin Bintu ta ji haushin kanta sosai, ta ja tsaki gami da tattara kayanta zuwa d'aki. Haka kawai baya sonta sai ya zama ya dunga wulak'antata. Kawai ta soma zubar hawaye. "To me zai dameki wai?" Wata zuciyar ta k'ara jefomata tambayar da ta sanyata share hawayenta gami da mik'ewa. Wankan ma bazatayi ba, kawai ta bud'e cupboard d'inta ta d'auko rigar bacci doguwa har k'aurinta mai k'aramin hannu. Tana da (top) saidai ko bi ta kansa batayi ba, haushi da wani mugun abu da batasan ko menene ma ya tokare wuyanta. Duk da 'yar yunwar da take ji, haka ta nemi makwanci. Babu yanda Mami batayi ba akan su tafi da abinci ya k'i, ashe don ya shiryamata mugunta yayi hakan. Tayi kwafa, zuciyarta tayi wani irin rauni, yanzu shi yana can yana dariya a gaban budurwarsa. Hawaye ta ji ya silalo mata. Ba zato kuma ta ji hon d'in motarsa. Ta mik'e da sauri ta lek'a, ganin dagaske shi d'inne yasa ta sauke ajiyar zuciya gami da goge fuskarta. . Tana ji yana bugun k'ofar, saida ta d'an yi jim sannan ta mik'e ta fita ta bud'e. Ya had'e fuska gami da mik'amata ledojin hannunsa. "Au, daman kina ji kika shareni?" Batace uffan ba, ta kar6i ledojin ta ajiyesu zata shige d'aki. "Ina zakije? Na sallameki ne?" Ya fad'a yana dubanta. Dole ta dawo ta zauna tana 6ata rai. Dakinsa ya shige. Saida ya gama abinda zaiyi sannan ya dawo falon har ta kai k'ololuwa wajen 6acin rai. Zama yayi yana k'aremata kallo, lallai zaiyi maganinta tunda ba zata gaji da tsokanoshi ba. "D'aukomin filet da kofi." Ta tashi tayi gaba, cikin sauri take tafiya a fusace wanda ya ba shi damar k'arewa halittar kallo. Murmushi yayi, yasan hirar da yace zai tafi ne ya 6ata ranta. A ganinsa ko hirar ya je, me zai takura zuciyar d'ayansu? Bayan dawowarta ya umarceta da bude ledojin, ta ciro kaza wacce aka nad'e a foil paper, ta juye. Ta fiddo youghurt din data gani sai lemu. Tana kammalawa ta juya zata tafi, ji tayi mutum ya fisgota jikinsa. Ta ware idanu tana dubansa a tsorace, hakan ya k'ara fito da manyan idanunta masu kyau tana dubansa. Shi d'inma ita yake duba, zuciyarsu na bugu da sauri-sauri. Ta soma kiciniyar zillewa, babu dama. Ya d'ago ha6anta, cikin k'aramin muryar ya soma magana. "Hey, ba dai kishina kikeyi ba ko? Ban hanaki yimin shiga haka ba?" Ta ji gabanta ya fad'a, saidai kusancinsu yasa batason cewa uffan. Gaba d'aya ma jikinta rawa yake, abu ne da bai ta6a faruwa gareta ba, wai namiji ya rik'eta har haka. Da ace anan abin ya tsaya da saukinta ne, saidai kuma batayi aune ba ta ji ya soma isar ga sak'onsa a cikin mataunar abincinta(hhhhh.. Inji Tasleem. Lol). , Bintu ta rasa a inda take, gaba d'aya ta tsorata, jikinta kamar ana kad'awa. To ba ita d'in ba, shi kansa bai tsira ba. Da k'arfi ta fisge jikinta ta ja baya, da gudu kuma tayi d'aki ta rufe gam! Shi kuwa saman kujera ya zauna ya dafe kansa, idanunsa a lumshe. Ya kwashi tsawon mintuna a haka kafin yayi baya ya jingina da kujera. "Oh Allah, what's about to happen?"(Meke shirin faruwa?) "Very soft." Ya fad'a a ransa lokacin da hancinsa ya k'ara shak'o k'amshi na jan bakinta. "Kai, Bintu ce fa!" Wani sashe na zuciyar yayi mishi tuni. Ya bud'e idanunsa da suma suka chanja. Eh Bintun ce! Ai halaliyarsa ce. Ya bawa kansa wannan amsar cike da jin kwarin gwuiwa da kore kalmar da na sanin da wani sace na zuciyarsa ke k'ok'arin tursasashi wajen yarda. Saidai ba zai kashe kansa ba, ya shirya dambe da borin kunyar, har ya samu abinda gangar jiki da ruhinsa ke so suna kaiwa kasuwa. Don me zai bari shaid'an ya kusan cin galaba akanshi har ya ji zai iya amincewa da buk'atar Lawisa ya kai mata ziyara? A'a, shi d'in bai kasance cikin mazinata ba, don haka dole ayi d'ayan biyu. Gudanar da zaman lafiya tsakaninsa da matarsa, ko kuma auro wacce zata iya da buk'atunsa. Dakyar ya saita kansa ya rufe wannan tashar, zama yayi ya soma cin kazarsa hankalinsa kwance. Saida ya ci mai isarsa sannan ya sha youghurt ya d'ora mata sauran saman firij sanin da yayi na cewar dole zata buk'ata. Daga haka ya dauki ruwa ya kashe fitilu ya fad'a d'akinsa. * * * A daki bintu tana shiga taji wani bakin ciki abinda yayiwa mata a zuciyarta hawaye hawaye hawaye hawaye hawaye hawaye hawaye hawaye hawaye suka dinga zubowa karshe ta shiga ta shiga kitchen ta dauko wuka ta cakawa kanta a ciki take nan ta fadi ta mutu Ma'aruf Yana daki YA jiyo kara shima YA fito da gudu yayi kitchen yama zuwa yaga bintu ta gadi cikin jini YA dinga kuka YAna jijigata amma inaaa ta muta shima sai yayi tunanin mai zaije YA cewa mommy kawai shima YA dauko wukar YA cakawa kanshiiiii shima ya fadi mutuuuu. Kurunkus angama bintu . A hankali ta zauna a k'asa ta jingina da gado yayinda ta takure k'afafunta da hannuwanta wuri d'aya. Har lokacin jikinta yana kyarma. Ta k'ara kai hannu ta share bakinta. Sai kuma ta fashe da kuka marar dalili. To ita kanta batasan abinda ya janyomata zubar hawayen ba, tasan dai ta tsorata sosai da irin abinda ya wanzu tsakaninsu. Can kuma ta mik'e ta koma kan gado gami da goge fuskarta. Lumshe ido tayi tana maida numfashi sannu-sannu. Abin mamaki sai kuma ta tsinci kanta da yin wani murmushi. Yaya Ma'aruf ya had'u, shine kawai abinda ta ayyana a ranta. Abubuwa da yawa sun tsaya mata a rai a d'an wannan rik'on da yayi mata da sak'on da ya isar. "Ban hanaki yimin shiga haka ba?" Abinda ya fad'o ranta kenan, ta mik'e tsaye da saurinta ta nufi gaban madubi tana k'arewa jikinta kallo. Rigar kam babu laifi, da a gidan Mami takeyi ba zata barta ta sanya ba duk da cewar ita bata ga aibunta ba, amma ba laifi tayi shara-shara. Ta dauki top d'inta ta d'ora akai gami da zama a gefen gadon ta rik'e cikinta da ke wani irin kuwwa sakamakon yunwar da ta ji ta motsa mata. Saidai kuma batajin zata iya fita yana a falon, wai Bintu ce da jin kunyar Ma'aruf yau? Abin da ya bata mamaki kenan har yasa ta murmusawa. Haka ta zauna tana sak'e-sak'en zuci. Ta rasa yanda zata fassara hakikanin matsayin da ta ajiye Ma'aruf. D'an uwan ne ko Mijin? To ai kuwa tuni a matsayin mijin yake ko ta k'i kuwa. Saidai fa bata sonshi, shine babbar hujjar da ta kafawa kanta har take tak'ama da shi. Ya za'ayi ta mance munanan kalamansa a kanta? Ai ya nuna ita d'in yarinya ce babu abinda zaiyi da ita, to kuwa zai yi nadamar furucinsa, shiga kuwa na English wears, yanzu ta soma. Jikinta ne kuwa, ta daina bari ya maimaita wannan abu da yayi. Ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru tana jira ya bar falon. Ta jima zaune kafin ta jiyo motsinsa wajen kicin sai kuma da jimawa ta ji ya rufe k'ofarsa. Saida ta bari aka d'anyi mintuna ta lek'o, ganin duhu a falon ya tabbatar mata lallai ya kwanta kenan. Kunna fitilar ta yi ta ware ido, babu ledojin a tsakar falo hakan ya sanyata nufar kicin, nan ta ci karo da su a saman firij. Haka ta koma dakinta ta rufe gam da mukulli bayan ta dauki komai na bukatarta. * * * Washegari ya kama Asabar, abinda ya sanya Bintu jin babu dadi, tana son gasa shi, saidai ta lura ta soma d'an jin nauyinsa don abinda yayi, ashe daman da gaske ne da ta ji ana cewa ana samun wani sauyi a jiki idan irin hakan ta faru a lokacin? Ita kam sai yanzu ta gaskata. Bata mantawa akwai sadda suke hira da Aisha akan ire-iren lamuran nan, ta 6alli rakenta tana tsotsa gami da lumshe ido. "Banza kawai, jeki haukan soyayya ya kasheki kawai, gwara miki shan rake kullum kiyita sha kina nishadi abinki, da wata soyayya." Bata manta amsar Aisha alokacin. "Hum, bakisan menene ma'anar kalmar ba, kedai Allah Yasa wataran ki ji yanda..." Bata manta yanda ta toshemata baki wai kada tayi mata mugun fata. Aisha ta fisge hannunta tana dariya kafin tace. "Wallahi akwai abinda idan anyimiki ba zaki iya magana ba. Ke bakinki mutuwa zaiyi, zaki fahimci shegen kuri ne kawai kikeyi." Dariya tayi ta cigaba da shan rakenta kawai. Bintu ta numfasa ta mik'e cike da kwarin gwuiwa, ba fa zata bari tayi saurin karaya ba, lallai idan ta nunamishi sanyi da kuma nauyinsa da take ji zai fahimci yayi nasara akanta. Har alokacin tana jin 6acin ran zancen da yaje. Har ta fito ta kammala komai bai fito daga d'akinsa ba, daman bata tsammatar hakan tunda yau babu aiki. Ta koma d'akinta tayi wanka, har ta dauko kananun kaya sai tayi murmushi ta mayar, gaskiya a yau dai ba zata iya sanyawar ba amma hakan ba wai yana nufin ta bar alak'a da su bane tunda sun zame mata kamar atamfa. Ta sanya doguwar riga ta atamfa, hoda kawai ta shafa sai man le6e. A falo tana zaune tana karyawa sai gashinan ya fito. Ko wanka baiyi ba, daga shi sai riga da wando dogo na bacci na (pyjamas). Ya zauna saman kujera. Bata ko kalleshi ba sai ma ta had'e fuska. Ido ya zubamata, haka kawai ya ji ta burgeshi yanda ta had'e fuskar. Ya bi d'an bakinnata da kallo kawai, shi kansa a yanzun sai yakejin kunyarta amma kasancewarsa namiji, ya maze har da wani had'e gira kad'an. "Ina kwana." Ya gaisheta da gatse. Sai kuma bataji dadin gaidashin da bata yi ba. Ta gaisheshi, ya amsa kafin yayi umarnin ta had'amishi abin kari. Babu musu ta had'a ta ajiye a gabansa. Yana wani muzurai yana shan tea shi a dole kada yarinya ta ga fuskar rainashi. (Ikon Allah) Har ta kammala ta mik'e babu wata magana da ta k'ara shiga tsakaninsu. Ya bita da kallo, sai yaga kamar ma atamfar ta fi yi mata kyau sosai. Ya kawar da wannan tunanin kamar yanda ya saba kaudawar duk lokacin da ya taso. Haka suka ci hutun karshen satin kowannensu na kokarin nuna jarumtarsa a fuska, alamun fa babu wani abu a zuciya. Ranar litinin tana zauna a falo bayan ta dawo daga makaranta, bayan ya dawo aiki yake sanarmata da tafiyar da ta kamashi zuwa Lagos, bisa wani aiki da zaiyi a karkashin branch na kamfaninsu dake can. Ai a take ta soma washe hak'ora. "Yaushe ne tafiyar?" Ya zauna yana dubanta fuska a sake. "Oh, wato murna ma kikeyi?" Ta rufe baki adalilin dariyar farincikin da ya taho mata. "A'a, ai idan dadi yayi yawa kuka akeyi, nima bakinciki ne yayi yawa shiyasa ni darawa." Ya jinjina kai ya dubi gefe yana murmushi mai bayyana hak'ora kafin ya dubeta. "Bansan lokacin da raininki gareni ya k'aru har haka ba." Ya mik'e tsaye, ya soma tafiya hanyar d'akinsa. "Gobe zan wuce in sha Allah, mungama magana da Mami, Aisha zata zo ta tayaki zama." Wani ihun murna ta saki wanda ya sanyashi juyowa. Da sauri tayi narai-narai da fuska. "Toh Yaya, Allah Ya kiyaye." Ya d'an zubamata ido sai kuma ya juya ya shige. . Murna bai barta ta k'arasa abinda takeyi ba, ai gwara ya d'anyi k'aura daga gidan ko ta sha iska. Haba, Kullum mutum yana gida idan ya taso ofis sai kace ba shi da abokai. Ta ja k'aramin tsaki kawai. Shi kuwa mamaki ta ba shi ganin yanda take murna da tafiyarsa, wannan na nufin Bintu bata damu da shi ba? Ya tunano a baya idan wata 'yar tafiya ta sameshi yanda Ma'u ke damuwa har ta kai ga zubda ruwan hawaye na rashin son tafiyarsa. Amma yau ga Bintu ta zo matsayin matarsa, bata jin ko d'ar na tafiyar da zaiyi. Jikinsa ya d'anyi sanyi, haka kawai baiji dad'in yanda ta nuna d'in ba. Ya damu iyaka damuwa har saida ya gaza jurewa a ranar da zai tafi ya dubeta. "Meyasa bakiyi bakinciki da tafiyata ba?" Ta ji tambayar babu zato, sai kuma ta yi murmushi. "To ai kaima zaka huta da ni, tunda kace ina matsawa rayuwarka. Kuma kace ni ba komai ka d'aukeni ba ko?" Ya rasa kuma bakin magana. Ya watsamata wani kallo mai nuni da jin haushin kalamanta sannan ya sanya kai ya fita jaye da Trolley dinsa. Ta dafe bango da hannunta tana binsa da kallo gami da doka uban hamma. A hankali tace "Allah Ya kaika lafiya. Bari nayi baccina har na gaji ba takura." Ta rufe k'ofar ta koma ciki, lokacin bakwai da mintuna na safe. Abin ya yi mata dadi don kuwa bata da paper.
0 comments:
Post a Comment