.
Haka Khairat tanaji tana gani akayi sunan Fatima batajeba,ranar sunan Hydar yasha daru shide toshe kunnenshi yayi. Kamal yama Fatima bazata domin yaronde sunan Hydar ya amsa,ana kiranshi da Arif wannan kara da yamata ba k'aramin farinciki tayiba, dan tagaza b'oyewa. Jin sunan da aka sawa yaron Fatima Hydar ba k'aramin mamaki yayiba kuma tabbas yaji dad'i ba kad'anba haka itama Khairat ta nuna jin dad'inta.
.
Seda Fatima tayi arba'in sannan Hydar yad'ebesu sukayo kaduna,murna gurin Khairat da Fatima ba'a magana haka dangi kowa murnar ganinta yake. Sunje gidajen dangi ziyara sunraba abin arziki satinsu d'aya suka dawo Abuja cike da sa albarka iyaye. Yau Khairat tun safe take bacci tak'i tashi Hydar yayi yayi ya tasheta amman ina baccinta take abin har tsoro ya dunga bashi dan yasan bata bacci haka,dakyar yasamu ta tashi shima kuka tasamishi akan meyasa yatasheta. Da kyar yasamu tayi wanka abinci ko takeway yasiyo musu suka ci shida su Yasmeen dan ita fafur tak'i cin abincin sede kwanciya. Hydar hankalinshine yatashi don zuwa yanzu harda zazzab'i ajikinta,waya ya d'auka yakira likitanshi bejimaba yazo, Hydar ne yamasa bayanin abinda ke faruwa dan ita bacci take. Fitsarinta likitan ya buk'ata dole Hydar ya d'auketa zuwa toilet yasa tai fitsarin a wata roba da likitan yabasu,dawowa yayi ya kawowa likitan dan ita suna fitowa daga toilet d'in gado tayi hayewarta taci gaba da baccinta. Gwajin farko da likitan yayi yamishi albishir da Khairat na d'auke da ciki, na tsawon wata biyu,murnar da Hydar yayi bata fad'uwa danshi mutumne meson haihuwa har kyautar mota yayiwa likitan sannan sukayi sallama yatafi. Da gudu yakoma d'akin da Khairat take yana zuwa d'agata yayi gabad'aya yafara taka rawa da ita har da y'ar wak'arshi, farkawa tayi taga yana chashewa da ita yana d'ibar shoki da kyar yadireta,tambayarshi tashiga yi akan abinda ke faruwa. "Princess my little princess tazo nanda y'an wasu watanni zamu ganta,Baby cikine dake". Da sauri ta kalleshi dan bata gasgata abinda kunnenta yajiba,result ya nuna mata ayko ba kunya itama tashiga murna dan Tunda taga Arif d'an gidan Fatima taji tana matuk'ar son itama ta haihu don yaron kyakkyawane bame cewa d'an Fatima ne. Tunda ga wannan rana Hydar ya d'auko mata me ayki duk da sunsha daru kamin ta yarda,ko tsinke be amince ta d'aga ba inyana gurin ayki hankalinshi nakanta duk abinda takeso shi take samu, Fatima ma ta tayata murna data sanar da ita. Kwanci tashi ba wuya agurin Allah. Yau ga Khairat a gadon nak'uda kuka take sosai dan kwana tayi tana abu d'aya Hydar shima a tsorace yake yana tsaron kar itama ta mutu kamar matarshi maryam addu'a yinta yake don gaba d'aya ya rud'e, Khairat tun Tana k'ok'artawa har k'arfinta yak'are wanda hakanne ya tilastawa Hydar sa hannu a takardar yimata cs.
.
Anyi aykin cikin nasara inda aka ciromata Baby girl kyakkyawa me kama da ita don yarinyar harta fi Khairat d'in kyau sosai,ana cirota tafara neman abinci hannunta a bakinta tana tsotsa. Koda aka kawowa Hydar princess d'inshi har hawaye yayi na farinciki sabida kyautar da Allah yay masa,murnarsa gaza b'oyuwa tayi. D'akin kwantarwa aka maida Khairat sanda ta farko Babynta tafara tambaya da sauri Hydar ya mik'a mata ita kusa da ita,wani sanyine ya ziyarci zuciyarta kissing d'in babyn take Ta koina. Mutanan kaduna ayari guda sukazo dubata harda Fatima,satinta biyu a Asibitin sannan aka sallameta dan tun wancan satin aka sallameta Hydar ya hana su tafi dan yafiso tak'ara kwari tukuna. Taron suna na gani na fad'a akayi inda ranar suna yarinya ta amsa sunan Fatima suna kiranta da Arfat,fad'in irin bidirin da akayi aranar b'ata lokacine, ranar naira tayi kuka dan Hydar tamkar ba'a tab'a yimasa haihuwa ba haka ya nuna. Anci ansha anyi danasha taro yatashi Lafiya Fatima har kukan dad'i tayi dajin sunanta akasawa Babyn sosai ta dunga yimusu godiya,da zasu koma direba Hydar yabasu yamaidasu bayan yacikasu da abin arziki. Tsohuwa aka d'aukowa Khairat me kulawa da ita, Hydar ko bashi da ayki sena renon Princess d'inshi son dayayiwa Fatima shine ya shafi takwarar tata, bashida lokacin kowa senata Khairat har complain takeyi danko gurin bacci ajikinshi take kwana. Watan Arfat biyar amman ta iya zama sosai kyanta se k'ara fitowa yake,sede wani ikon Allah yanzu sam bata kama da Khairat sede ta jini, gabad'aya kammaninta yanzu sun koma na Yasmeen kamar antsaga kara,anata b'angaran Yasmeen tanason Arfat dan har goyata takeyi,wannan kama da Arfat takeyi da Yasmeen shi yafara canjawa Yasmeen matsayi a zuciyar Hydar.
.
Tun daga wannan lokaci Hydar yakasa gane kansa,kullum bashida ayki sena tunanin Yasmeen yarasa dalili gaba d'aya yabi ya susuce yafita hayyacinshi. Sosai Khairat taga canji daga megidannata wanda tasan da ba haka yakeba, koda ta tambayeshi meke damunshi, murmushi kawai yamata yace shima besaniba amman ta tayashi da addu'a. Khairat bata da zab'in daya wuce ta tayashi da addu'ar kamar yadda ya buk'ata.
.
*Bayan shekara bakwai.*
Al-amura sun Faru da dama aciki harda komawar Fatima da Khairat makaranta inda a halin yanzu sungama degree d'insu Master's sukeyi yanzu. Hydar yabiya musu makkah Fatima da Khairat d'in harda kamal sunje har sun dawo. Rayuwa taci gaba da tafiya inda dukansu sun sake haihuwa duka mata suka haifa,inda y'ar gidan Fatima akasa mata Khairat suna kiranta meemee,itakuma Khairat sunan mahaifiyar Hydar akasa suna kiranta meema. Yasmeen da Iman yanzu sunkai matakin ss2 a makaranta, shak'uwace me k'arfi a tsakaninsu bata wasaba. Hydar kuwa so da k'aunar Yasmeen yanzu sungama kamashi dan beda kwanciyar hankali ko kad'an yaso yacireta aranshi amman abun ya gagara dan yasan duk ranar da zancan ya fito akwai tashin hankali bad'an kad'anba amman ya barwa Allah zab'i Wata budurwa na hango wacce shekarunta basu wuce 16 ba sanye cikin wasu riga da wando farare, wandon and'an yagashi daga dede gwuiwa wato crazy rigar body hug ce itama fara se wata bak'ar boy friend jacket data d'ora asaman kayan takalmin k'afarta dogone irin me igiyoyinnan shima bak'i se farin gyale data nad'a akanta ta rataya bak'ar jaka fuskarta sanye cikin wani k'aton glass irin me rufe rabin fuska,kai me karatu duk yadda zan fasaltamaka kyau da had'uwar budurwarnan bazan fad'a maka daidai ba sede abu guda zan iya cewa, k'arshece gurin had'uwa,ba kowa bace wannan budurwa face *Yasmeen.*
.
Sakkowa take daga step cikin tafiyarta me d'aukar hankali har ta k'araso falon gidan, jikin Khairat ta nufa ta kwanta wacce ke zaune ita da hydar suna tattaunawa game da al-amuran siyasarsa dan tenure d'inshi tak'are har yasake maimaitawa. Tunda Yasmeen tashigo falon gaba d'aya Hydar yay loosing control, hankalinshi nakanta tsawon wannan shekaru da sonta da k'aunarta yake kwana yake tashi, ya jima da amincewa zuciyarshi tabbas son Yasmeen yakeyi,muryartace ta dawo dashi daga tunanin daya tafi. "Aunty zamuje shan ice cream nida Iman kuma we don't have enough money so please abamu don Allah",ta fad'a cike da shagwab'a dan ita koda wa zatayi magana a shagwab'e takeyi ya zama nature d'inta. "Au yau kuma ni zaki tambaya? ki tambayi daddyn ku mana gashinan yana jinki danni ko sisi bazan bakuba, ko jiya about 50k kuka amsa a hannuna zakuyi ankwan k'awarku to yaude kam bazan bayarba". "Tunda bazaki bamuba shikenan munfasa zuwan"Yasmeen ta fad'i ranta a b'ace ta mik'e zata wuce dan ita in akwai abinda ta tsana shine ace tayiwa Hydar magana gaisuwace kawai take had'ata dashi itama bata wuce ina kwana,daga haka bata k'arawa. Wannan hali na Yasmeen shi yake sawa Hydar yarasa taya ze sanar da ita abinda ke damunsa aransa,yarasa gane me yay mata data tsaneshi haka dan tabbas tsanace tunda shi kad'ai takewa hakan.
.
"Au Yasmeen daki tambayi daddy gwanda kifasa zuwa duk wannan wankan sikarin dakika sha?". Ko kallonta batayiba taci gaba da tafiyarta, cikin in ina Hydar yace. "Yasmeen!!!" Cak ta tsaya a inda take don jin sunanta a bakin wanda be tab'a furtawa ba,kuma batajin akwai wani mahaluki daya kaishi iya furta sunan. Shima kanshi yayi mamakin yadda ya iya kiran sunan nata kai tsaye haka, danshi har tsoronta ma yakeji, daurewa yayi yaci gaba da cewa. "Zo muje na siyamuku ice cream d'in kar kiyi Kwalliyar a banza, kyale Auntyn ki so take takashemiki kasuwa don taga kinyi kyau, kyaleta kizo muje dama nima fita zanyi". Ba Khairat da Yasmeen ba shi kanshi mamakin kansa yakeyi,don magana makwatanciyar wannan bata tab'a had'ashi da ita ba,itako Khairat farin ciki ne yakamata yau Hydar ya nuna kulawarsa ga k'anwarta dan sam batajin dad'in rashin kula Yasmeen dayakeyi dan haka yanzu murnarta tagaza b'oyuwa shima yagani. Yasmeen kuwa wani killer smile tasaki,dan yau tayi imani addu'arta ta tsawon shekara takwas tafara amsuwa, seda ta dedeta natsuwarta sannan ta juyo fuska a had'e tace. "Ni nafasa zuwa kabarshi kawai dama kuma Iman ma bata shiryaba"ta fad'i cikin salon datasan dole ta d'auki hankalinsa. "Banason irin haka Yasmeen taya da girmansa zece kizo kuje yasaimiki amman sewani abu kikeyi kamar wani sa'anki, banason iskanci kizo kiwuce kutafi kya tahowa da Iman d'in nata,tunda bata shiryaba, haba,yarinya se shegen kafiyar tsiya"Khairat ta fad'i cikin b'acin rai. Killer smile Yasmeen tasake yi aranta tace,"wow I love that, da kanki kika bani dama gaskiya nagode miki" Amman a fili tafiya tayi da gudu ta rungume Khairat d'in tana dariya tace. "Wayyo my sweet three in one kiyi hak'uri banason ganin b'acin ranki". "Bangane three in one ba, mekenan hakan ke nufi?"inji Khairat. Murmushi Yasmeen tayi sannan tace. "One kece marik'iyata kinga you are my mum, two ke my blood sister ce me sona, three se ranar da aka kaini gidan mijina zan fad'amiki"da gudu tamik'e ajikinta tayi waje tana dariya. Khairat ma dariyar tayi tace. "Kai yaran zamani ba kunya wai Yasmeen ce ke zancan gidan mijinta Allah yakawomu zamani". Mik'ewa Hydar Yayi yana sa hularsa yace, "madam keda wannan sister taki se Allah, bansan Wanda yafi wani son wani a cikinkuba" ya fad'i yana dariya. "Ay gaskiya kam koni bazance ga wanda yafi son waniba a cikinmu, kaje ku tafi karta botsare kasan halinta". Rakiya taimishi har gurin mota koda driver d'inshi yataso key kawai ya amsa, yace dakanshi zeja motar,tuni Yasmeen ta k'ace a gaban mota,duka Khairat ta kaimata tace. "Zaki dawo ki samenine nikike cewa gidan mijinki ko?". Dariya dukansu sukayi Hydar yaja motar suka tafi, Khairat takoma cikin gida zuciyarta cike da farincikin Hydar da Yasmeen yanzu Sun shirya dan batajin dad'in yadda sukewa juna.
.
Tafe suke bamecewa kowa komai Yasmeen se chatting take da friends d'inta hankalinta kwance, shiko Hydar rabi hankalinshi na kanta har suka iso wani ostrich inda zasu sayi ice cream d'in. Yasmeen da zata sakko a motar seda tayi wani juyi wanda ko waye yagani se ya koka,Hydar Kasa motsawa yayi a inda yake seda tayi gyaran murya sannan ya dawo tunaninsa. Jerawa sukayi suka shige gurin basu jimaba suka fito me makon taga yayi hanyar gida setaga yayi hanyar millonium park da ita, bata damuba har suka k'arasa gurin ice cream dinta kawai take sha,koda suka isa gurin bece su fitaba Illa adjusting d'in seat d'inshi da yayi itama mik'a hannu yayi yamata adjusting d'in kujerar wanda hakan ya tilastawa jikinsu had'uwa da sauri ya d'auke hannunshi. jingina yayi da kujerar yana kallon Yasmeen wacce se shan ice cream d'inta takeyi kamar batasan Allah yay ruwanshi agunba,mik'a hannu yayi ya kwace robar ice cream d'in ya rik'e a hannunshi, da sauri ta d'ago tana kallonshi,kwab'e fuska tayi zatayi kuka,tace. "Haba daddy yazaka kwacemin ice cream inacikin sha ko dama ba ni kasiyamawaba?".
.
"Naga ice cream d'in yafini muhimmancine shiyasa na amshe domin inason kibani aron hankalinki zamuyi wata magana". Kallonshi take da idanuwanta masu k'ara sashi fad'awa kogin sonta,tace. "Daddy I hope ba laifi de naimakaba?"ta fad'i harda wani juya ido. "Ba laifi kikaminba".ya d'ora da cewa. "Yasmeen inaso ki fahimceni da kyau karkimin wani kallo na dabam,tunda Allah ya kawoki gidana da zama na fad'a cikin wani yanayi wanda ni kaina tsoronsa nake, na rok'i Allah akan inba alkha'iri bane yacireminshi a raina amman ina kullum kamar k'araminshi ake a zuciyata tsawon shekaru bakwai kenan Yasmeen na kamu da ciwon sonki me tsanani don Allah ki taimakamin". Wani farincikine ya lullub'e duk wani sassa najikin Yasmeen,harta rasa wacce irin godiya zatayiwa Allah,amman afili zabura tayi tace. "What!!!,Daddy kana sonafa kace? kamanta yadda muke da Aunty Khairat ne?gaskiya wannan zancan bame yiwuwa bane yakamata kayi tunani ni don Allah karma kasake furta irin wannan maganar,ashe abinda ke ranka kenan yasa kace inzo kasiyamin ice cream?". Kan Hydar ne yafara d'aukar zafi dama abinda yaguda kenan tun farko shiyasa yak'i bayyanamata,dan yasan bazata aminceba Amman ya ya iya? cigaba yayi da rarrashinta kamar wani yaro yadunga zayyana mata irin son da yake mata,dad'i kamar yakasheta Amman afili se ignoring take. Daga k'arshe de dataga yana shirin zubda hawayene yasa ta turo baki gaba tace, "to naji kabari zanyi shawara abinda nasamu daga shawarar zansanar dakai". "Dawa zakiyi shawara Khairat ko Iman?". "Da zuciyata". "Don Allah yayin shawarar ki kwatantamin adalci, dakwan soyayya tsawon shekara bakwai it not easy pls". Bata bashi amsaba haka yagaji ya ja motar suka dawo gida. Khairat murna kamar anmata albishir da aljannah don murnar Hydar da Yasmeen Sun shirya. Ranar dukansu suka had'u gurin cin abinci Yasmeen da Hydar se satar kallon juna sukeyi har aka gama cin abincin kowa ya watse. Yasmeen d'akin Khairat taje tasameta fitowarta daga wanka kenan tana kwalliya Yasmeen tashigo d'akin, Khairat tayi mamakin zuwan nata adede wannan lokacin dan da zaran anyi magrib basa hawa sama ma bare suzo d'akinta. Tasowa tayi daga gaban mirror ta koma kan godo ta zauna Yasmeen na k'arasawa kan cinyarta ta kwanta tace. "Am sorry Aunty nazuwa gurinki yanzu,wlh wata friend d'inace take cikin mawuyacin hali tanemi nataimaka mata da shawara yazatayi, to nikuma kinsan bawani wayo ne daniba shine yasa nace ta Bari intambayar mata Aunty na". Murmushi Khairat tayi tace.
.
"Allah sarki, shawarar me take nema? Allah yasa na iya bata". "Wlh Aunty mijin marik'iyartane kesonta kuma ba k'aramin soba tak'i amincewa amman inkinga yadda yake mata magiya ko ke sekin tausaya masa kuma itama tanasonshi,amman ganin mijin marik'iyartane yasa tak'i amincewa wlh dukansu suna cikin wani hali abin a tausaya musu,dan cewa tayi inde tarasashi to ita da aure har abada shine take neman shawara". Ajiyar zuciya Khairat tayi sannan ta shafo kan Yasmeen tace. "Wannan ba abin tada hankaline ba inde akwai fahimta ita da marik'iyartata tanasonta tsakani da Allah inaga bazata damuba dan hakan takasance, duba da cewa bazataso taga yarinyar batayi aureba kamar yadda tayi ikirari,inaga ta amince kawai inde marik'iyar nasonta tsakani da Allah bazata hanaba sede zataji zafi amman ba kamar akawo mata bareba wannan shine kawai". Murmushi Yasmeen tayi bayan ta kashe recording d'in datasa tad'au muryar Khairat sanda take bata amsa sannan tace. "Wlh bahaushe yayi gaskiya dayace aykin me shawara baya b'aci,da saura kad'an ta guntulawa kanta,wajan hana zuciyarta abinda takeso, Kai wallahi zama da Manya masu zurfin tunani,masu sowa d'an uwansu abinda suke sowa kansu da dad'i mungode Aunty da shawara kuma insha Allahu zan fad'a mata wannan shawarar,mukwana lfy".ta mik'e da gudu tabar d'akin tana dariya. Khairat itama dariyar tayi aranta tace, "kai Yasmeen wlh akwai hankali bata abu kai tsaye seta nemi shawara Allah de yay mata zab'i da miji nagari". Yasmeen ko tunda ta koma d'akinsu inbanda dariya ba abinda takeyi, Iman har haushi taji dan ta d'auka ita takewa dariyar akan ba'a je da ita shan ice cream ba. WhatsApp Yasmeen tahau tana chatting da k'awayenta cike da farinciki da annashuwa.
.
Washe gari da safe dukansu sukayi breakfast,a tare Hydar se mamakin irin wani kallo da Yasmeen take watso mishi yake, kallone dake nuna tsantsar soyayya. Yanason magana da ita Amman ba hali tunda yau weekend ne yana gida kuma tare da Khairat,dan haka fakar idon su yayi ya Kara hannunshi a kunne,Yasmeen na kallonshi alamar tabashi number wayarta. Ho Yasmeen!!!halinki seke. Tunda ta fahinceshi ay kawai setayi murmushi ta waiga gurin Khairat tace. "Aunty don Allah d'an karantomin number na naga kamar kin rik'e, ni wlh ban rik'eba gashi wanine zanturamawa yadameni da tambaya yanzu haka gashi nan online,kuma kinsan number danake whatsApp bada ita nake receiving calls ba".
.
"Lalle Yasmeen yanzu number nakine baki rik'eba? sannunki da shiririta, niko ko daga bacci kika tasheni zan karantomiki numbar ki danna rik'e"daganan tafara karanto number Hydar yana rubutawa batare da Khairat ta ganeba tana gamawa Yasmeen tace. "Yeeeeh thanks my sweet three in one,you are perfect that's why you deserve a perfect surprise when the time comes". Duka Khairat takaimata tace. "Niko na k'osa naji wannan sabon sunan nawa na ukun, dannasan dole zeyi dad'i tunda my sweet two in one ce tasaminshi". Fuska Yasmeen ta b'ata tace. "Kai Aunty don Allah taya zaki cemin two in one? wlh nima three in one ce a gurinki,ranar dazan sanar dake d'ayan sunan naki kema seki zab'i wanda yadace kisamin, amman gaskiya niba two in one bace a gurinki ba". Sosai Khairat taji dad'in kalaman Yasmeen,rungumeta tayi tace. "Wlh Sis bansan irin sonda nake mikiba komai naki burgeni yakeyi wlh, Allah de yahad'aki da miji na gari daze rik'eminke amana". "Aunty na kenan ay wlh nafi sonki,sabida kinga nide yarinyace ko?to wlh bazan tab'a yarda Inga Daddy yashigo da wata bare a matsayin kishiyar muba, dan in yamiki kishiya ni yayiwa dole mutashi mud'au mataki, shiyasa ma Nafad'i a gabansa dagamu bak'ari inde ya amince to muma mun amince". "Wlh Sis tunda muke baki tab'a farantamin rai irinna yauba,gaskiya nayarda da soyayyarki gareni tunda har bakyason ayimin kishiya gaskiya nagode". Hydar zan iya cewa kusan suman zaune yayi dan abinna Yasmeen yafi k'arfin tunanin shi,cikin hikima tana magana dashi amman Khairat bata ganeba,se shid'in data.keyi dashi shine yaganen,dank'ari lalle akwai bala'i a gidanshi, sede addu'ar Allah ya yayyafa mishi ruwan sanyi. gyara murya yayi sannan yace. "Lalle ma mutanennan wato abin y'ar son kaice?,ina laifinma kuce kun yarda na k'aro wata a wajen bayan ku, Amman seku rik'eni ku kad'ai gaskiya bakuyi adalciba". Yasmeen turo baki gaba tayi sannan tace. "wlh muddin bayanmu kana tunanin k'ara wata to wlh kadena danmu aka yika kamar yadda kaima dankai aka yimu, koya kikace Auntyna?"ta waiga tana kallon Khairat wacce ta d'auki zancan Yasmeen a matsayin irin wasan da akeyi tsakanin miji da k'anwar matarsa cike da farinciki tace. "wannan zance naki gaskiyane my Sister".
.
"To inde hakane yazama wajibi kudage da nunamin so da k'auna kamar yadda nima nake nuna muku,ma'ana kurik'eni amana inde kukamin haka to Hydar nakune ku kad'ai dan lokaci, yayi da zan shida muku kune zab'ina dana jima ina nema yau gashi kun tabbatarmin da hakan, gaskiya innace banji dad'iba nayi k'arya, nagode sosai wlh Allah yabarmu tare yasa mucinye duk wani k'alubale dazamu fuskanta". Da sauri Yasmeen tace,"Ameen Ameen". Oh my God jama'a kuna ina sunmaida Khairat banza. A gabanta suna musayar magana amman bata ganeba, Dan k'arshema da gudu taje ta rungume Hydar dan ita zatonta da ita yake wannan dad'ad'an maganganu shima rungumeta yayi ya Kalli Yasmeen yace. "Wannan shine fatana wata rana"yana nuna mata yadda Khairat ta rungumeshi. Kunyace ta kama Yasmeen da gudu tabar gurin ita da Iman wacce tun d'azu dariya kawai takeyi. Khairat ranar wani tattalin Hydar takeyi da bashi kulawa jin yace daga ita ba k'ari, itako dama ba abinda ta tsana irin kishiya, Tunda ko yace baze mataba itako bataga abinda bazata iya yimasa ba don ta faranta masa. Hydar besamu damar kiran Yasmeen ba seda yafita masallaci, bayan an idar da sallah ya tsaya a garden d'in gidan yakirata a waya,bugu biyu ta d'auka cikin muryarta me kwantar da hankali tace. "Ran hydara na yadad'e,karkayi mamaki, sanin zaka kira shiyasa na kama suna dannasan kaid'inne". Murmushi Hydar yayi sannan yace. "Such amazing My heart,d'azu kin rikitani wlh, wai dagaske kin amince dani to be your husband kode wasa kikemin?". "Bana wasa da abu me muhimmanci kamarka tunda nace na amince I mean it babu wani wasa aciki". Nande infad'amuku, suka kwashi soyayarsu me dad'in saurare, dan basu denaba seda aka kira sallar la'asar,yakashe yatafi masallaci. koda yadawo gida Khairat tacemishi meya zaunar dashi, amsa yabata da wa'azi akeyi a masallacin shine yazauna ji se yanzu aka gama. Kai Hydar, kai tun kafin kayi mata biyun kafara shirgota. Muje zuwa readers.
0 comments:
Post a Comment