.
Soyayya fa tayi k'arfi tsakanin Hydar da Yasmeen kullum cikin nunawa juna kulawa suke koda kuwa a gaban Khairat ne,sun iya takunsu babu ta yadda zata gane. Su Yasmeen sun gama makarantar su lafiya ita da Iman, se murna sukeyi Hydar kuwa harda party ya shirya musu,anyi taron tayasu murna lfy gami da musu fatan alkha'iri. Yau asabar kowa yana gida dayake weekend ne zaune, suke a falo suna kallon casset d'in party da sukayi,Hydar ne yay sallama yashigo daga training ya dawo,da sauri Yasmeen ta mik'e taje taryarsa,suka tsaya a bakin k'ofar,tace. "Sannu da zuwa me gidan Aunty na dafatan kadawo lfy?".magana take tana juya ido. "Nadawo lfy Amarya ta, yakike ya Auntynki? dafatan kina kulamin da ita? kinsa itace heart beat d'ina". Murmushi tayi sannan tace. "Ka tambayeta kaji kullum ina kulawa da ita sabida sanin muhimmancinta a gurinka dan itama nasan kullum da tunaninka take kwana take tashi, kaide karik'e ta amana kuma ka gaggauta bata mulki na sarauniyar zuciyarka shine zesa tak'ara yadda ita d'in itace heart beat d'in taka". Khairat ce tak'araso gurinsu tana dariya tace. "Ikon Allah, wlh shiryawarka da Yasmeen ba k'aramin rana tayimin ba tunda gashi a sanadin hakan kana fallasamin sirrin zuciyarka wanda da baka tab'a fad'aminba, yanzu ne nake sanin matsayina a zuciyarka"dafa Yasmeen tayi sannan taci gaba da cewa. "Ay wlh kede Sis sede ince Allah ya rabaki da bak'in cikin duniya da lahira Allah ya d'aga darajarki a idon mijin dazaki Aura fiye da duk wata mace afad'in duniya yazamana yana hannunki se yadda kikayi dashi". Wata shegiyar dariya suka kwashe da ita Hydar da Yasmeen atare suna kallonta itama dariyar takeyi,Yasmeen tace. "Wai Aunty anya wannan addu'ar batayi tsauri da yawa ba kuwa? kide sassauta dan inason inkin tashi bani sunana na uku agurinki kibani me dad'i amman wannan zazzafar Addu'a haka Aunty, ay seki jamin zagi a idon duniya ace na mallakeshi yazama mijin tace". Carab Hydar yace.
.
"Ay ni wlh da za'a kiran mijin kan tacema akan Antynki so zanyi,dan matsayine babba agurina faruwar hakan". Rungumeshi Khairat tayi sabida jin dad'i,tana jikinshi take ba Yasmeen amsa. "Addu'a ce me kyau namiki Sis bazaki san amfaninta ba se ranar dakikayi auran, bazakiso ki koma komabaya a gurin mijinki ba dan haka kedai kawai kice ameen". "Ah to tunda kika ce hakan nasan abune me amfani danhaka ameen ameen Aunty na daddy kai baka tayani cewa ameen d'in ba"ta fad'i tana kallon idonshi. Murmushi yayi yak'ara rungume Khairat sosai ajikinshi sannan yace. "Wacce ameen zance anan nida har a Sallah ina fad'awa Allah yabaki Wanda yake sonki kema kuma kike sonshi kuzauna lfy, amman tunda Auntyn kice tayi addu'ar kuma kinsan irinsu addu'ar su na amsuwa nima nace ameen d'in". Janshi Khairat tayi suka haura sama suka bar Yasmeen da b'acin rai dan ta tsani taga Khairat ta rungumar mata Hydar. Tofa kuji k'arfin hali don Allah. Soyayya kullum se abunda yayi gaba koda wasa Khairat bata gano bakin zaranba, ita ta d'auki alak'arsu a matsayin wasan miji da k'anwar matarsa,ko shan ice cream yanzu duk Sunday se sunfita shida Yasmeen, wani time d'in suje da Iman wani lokacin da Khairat, ko su tafi da meema da Arfat dayake sun iya takunsu bawanda yaganosu. Hydar ne yamatsama Yasmeen akan shifa yanaso tabashi dama yatura gidansu neman auranta,hak'uri tadunga bashi akan yad'an k'ara hak'uri ba yanzuba. To yaude ko shawartarta beyiba da asubar fari ya kama hanyar kaduna shida drivern sa,yafiso ayita tak'are yagaji da b'oyewar dayakeyi shi ba mak'aryaciba Amman duk yagama zama mak'aryaci a gurin Khairat sabida hakan, shiyasa shi yak'osa ayita ta k'are Tunda yasande d'ayan biyu ne ko nasara ko akasin hakan. Tafe suke shide se addu'a yake akan Allah yabashi nasara. Yasmeen yau tun safe takejin gabanta nafad'uwa tarasa dalili addu'a kawai tayi akan Allah yasa alkha'irine,a kitchen suka had'u da Khairat gaisheta tayi ta amsa fuskarta d'auke da walwala.
.
Yasmeen tace, "Aunty yau ina soulmate d'in naki naga kinsakko da wuri haka?". Murmushi Khairat tayi sannan tace. "Wlh yau tun asuba yatafi kaduna shida driver yace ya kwana biyu beje ya gaishesu ba shine yau yatafi gobe ze dawo yace". Hankalin Yasmeen ne yay mugun tashi tabbas tasan zuwan Hydar kaduna ayau nanufin tayi bankwana da farinciki a rayuwarta, meyasa yatafi be sanar da ita ba?. Khairat ce ta tab'ota ganin gaba d'aya lokaci guda ta firgice tashiga damuwa,a rud'e ta waigo tana kallon Khairat,tambayarta tayi. "Lafiya kuwa Yasmeen?meke faruwa haka?daga cewa Hydar yatafi kaduna duk kin tada hankalinki". K'irk'iro murmushi tayi sannan tace. "Wlh dama naso nabishine duk lokacin dazeje shine kuma naji yatafi bansaniba shiyasa kikaga nashiga damuwa amman bakomai wlh". "To kidena damuwa in ze koma wani lokacin sekuje tare kinji my Sis". Kai ta d'aga mata sannan tafice a kitchen d'in takoma d'akinsu,rasa me zatayi tayi addu'a kawai tashigayi dan tasan halin Ummanta in zancannan yafito zata iya nakasata da duka ita yau yazatayi,?wata zuciyarce tashiga k'arfafa mata guiwa da cewa "ay ba ke kad'aice cikin tashin Hankalin ba Khairat ma tana ciki in har da gaske kina da burin fansa a ranki dole kicire tsaron komai a ranki dan dole sekin daure zuciyarki". shawara da zuciyarta ta bata itace ta k'ara mata kwarin gwuiwa yazamana memakwan tashiga tashin hankali sema wata natsuwace take shigarta. Had'a kayanta tayi guri guda tayadda bame ganewa dan tasan zamanta a gidan yakusa zuwa k'arshe data fita ba shiri gwanda ta shirya.
.
Hydar ya isa Kaduna lafiya kai tsaye gidan iyayensa yanufa. Sunyi murna sosai da ganinsa dan ba k'aramin so suke masa ba kasancewarshi shikad'ai Allah yabasu,shiyasa suke tattalinsa, kuma koba dan hakaba Hydar mutumne dayasan daraja da girma na iyayensa dole ko zuciya taso me kyautata mata. Part d'inshi nagidan yasauka, bayan yayi wanka ya kintsa fitowa yayi yanufi b'angaren iyayennasa, gaishesu yasake yi sannan yace. "Alhaji dama akwai wata magana data kawoni inaso kufahinceni kunsan bazan tab'a yin abinda yasab'awa addini ba,shiyasa wannan ma inaso ku d'aukeshi a matsayin k'addarata ce tazo a haka". Natsuwa sukayi suna sauraraonsa dan sun fahimci zancannasa me muhimmancine,cigaba yayi da cewa. "Bakomai bane dama illah inason Yasmeen k'anwar Khairat kuma inaso kashigemin gaba gurin neman auranta". "Innalillahi wainna ilaihirrajiun, Hydar kanka d'aya kuwa?,kasan abinda kake furtawa kuwa?,so kake kazama abokin shaid'an wajan tarwatsa zumunci?ina katab'a ganin haka?to wlh tuntuni inma bacci kake ka farka,wannan zancan bame yiwuwa bane",inji Hajiya wacce ke magana cikin fushi.
.
"Ah Hydar naji duk bayaninka kuma nagamsu dashi tunda nasan a addinancema ba laifi bane,sede Hydar iyayen yaran bazasu aminta subaka aurannanba dan ze tab'a zumuncinsu,kuma in akayi hakan kamar da cutarwa aciki, duba da ganin Khairat itace ta rik'e yarinyar harta girma,bawai nace bazan maka jagora bane aa kod'aya shawarace zanbaka inda hali ka hak'ura da wannan maganar kaji",Alhaji ya fad'a cikin sigar rarrashi. Afusace Hajiya ta amshi zancan. "Au lalle ma Alhaji koda yake ay duk sunanku maza,amman taya zaka goyawa yaro baya akan abinda kasan badede bane? tonide wlh ba hannuna aciki, dan bazan goyi bayan cin amana ba".tana gama magana tabar gurin tana huci. Hawayene suka zub'o a fuskar Hydar na rashin kwarin guiwa, Mahaifiyarsa ma bata goyi bayansaba bayajin iyayen Su Yasmeen zasu amince subashi auranta,Alhaji ne ya katse masa tunani tahanyar dafashi yace. "Haba Aliyu Hydar zakin fama namijin mazaje,karka bani kunya mana, taya akan wannan maganar zaka tada hankalinka?katunafa yak'i kad'auko bedace tundaga farko kanuna ka gazaba, dole seka nuna juriya da jarumta kuma dama su mata haka suke, sekaga abu al-adace kawai amman sesu fifitashi fiye da addini kuma kosu gidan yaran inaga ko za'a samu matsala to daga matanne,kaide kadage da addu'a yanzu katashi kaje da kanka kafara yi musu maganar in yaso yadda kukayi dasu zuwa gobe semuje tare". Maganganun Alhaji sune suka k'ara masa kwarin guiwa, godiya yayi masa sosai sannan ya fita yanufi gidan iyayansu Khairat. Da isarsa k'ofar Gidan Abban Khairat yasamu ya fito daga gida zashi masallaci, da sauri yafito a motor ya nufeshi, shima Abban ganin Hydar ya nufoshine yasa ya tsaya fuskarsa d'auke da fara'a. Hydar tsugunawa yayi har k'asa yagaisheshi,yana d'aya daga cikin halayansa dayake sawa surukannasa ke sonsa shine girmamasu dayakeyi batare da yayi la'akari da matsayinsaba,ruwan alwala Abban yasa aka kawomishi yayi alwalar suka nufi masallacin tare. Bayan an idar da sallah kai tsaye cikin gidansa yaja Hydar d'in suka gaisa da Umman Khairat, daganan sit room suka koma suka zauna aka kawo musu abinci Abban tilastawa Hydar yayi suka ci tare, duk kunyar Abban ta gama kama Hydar bayan sungamane Hydar yace yanada maganar data kawoshi,murmushi Abban yayi yace. "To Hydar ina sauraronka".
.
Rasa Ta inda ze fara yayi gaba d'aya Abban yamasa kwarjini,amman bashida zab'i dole ya furta,cikin rawar murya yafara maganar. "Abba don Allah ku fahimceni wlh k'addarace ta hau kaina bana nufin kawo tarnaki acikin familynku banida yadda zanyine don Allah kugafarceni". Mamakine yakama Abban to me Hydar yamusu da yake neman gafarar su haka. "Hydar ka natsu ka sanar dani abinda yake faruwa, ni mahaifinkane zanmaka duk abinda uba yake wa d'ansa, meyasa kake shayin sanar dani damuwarka?ni na maka alk'awari kowacce irice insha Allahu zanyi k'ok'arin taimakamaka, Danhaka kasanar dani ina sauraronka"Abba yayi maganar cikin yanayin k'arfafa guiwa agareshi. "Abba Yasmeen nakeso ka auramin idan har da gaske kai ubane agurina, inaso kayimin ranar da uba yakewa d'ansa yayinda d'an yashiga tashin hankali"ya k'arasa maganar yana kuka tamkar anmasa mutuwa. Tashin hankali ba'a samaka rana. Abba jiyayi kansa na shawagi a sararin samaniya gaba d'aya kalma ta gudu daga bakinsa gumi se karyo masa yakeyi. Hydar zuwa yayi yakama k'afarsa yana kuka yake fad'in. "Abba naso hak'ura tun kan kuji maganar amman nakasa, wlh Abba inbaka auramin Yasmeen ba zan iya rasa raina, don Allah katausayamin kuma wlh bazan wulak'anta muku y'ay'aba". Dakyar Abba yasamu abin cewa. "Hydar ka kwantar da hankalinka bana tunanin zaka wulak'antasu,kawai zumuncinsu ake dubawa,amman ba komai gobe dama munada family meeting,zamu tattauna maganar a gurin kaje ka kwantar da hankalinka Hydar kanada uba tsayayye,idan har inada iko akan Yasmeen inkuma Allah yayi matarkace koda duka dangi basu yardaba ni zan auramaka ita,kuma inda Hali inaso taron dazamuyi gobe da azahar yazamana Khairat da Yasmeen su halarta". "Insha Allahu zasu halarta Abba nagode Allah yasaka da alkha'iri Allah yak'ara girma",godiya Hydar yakeyi kamar zeyi sujada. Abba k'arfafa masa guiwa yayi sosai gamida alk'awari. Hydar gidan su Yasmeen yashiga suka gaisa da iyayanta sannan yamusu sallama ya wuce gidan iyayensa.
.
Hydar yana isa gidan iyayensa yakwashe yadda sukayi da Abban yafad'awa mahaifinsa,fatan alkhairi yamasa sannan yak'ara da cewa yaci gaba da addu'a Allah yatabbatar da alkha'iri. Part d'inshi yawuce a falo yazauna yakira Khairat a waya,bugu d'aya ta d'auka tace. "Sanyin idaniyata yanzu nake zancan ka araina ashe kana kusane shiyasa".
.
"Kai ammafa naji dad'in hakan,to ya kuke I hope komai normal?". "Lafiyarmu k'alau sede kewarka da take damunmu". "Sorry zamu kasance tare har abada,dama ashe kunada family meeting gobe amman shine baki sanar daniba,?se d'azu da muka gaisa da Abba yake sanar dani,kuma yanemi alfarmar keda Yasmeen ku halarci taron a goben,so dan haka na turo driver yadawo tun d'azu seku shirya da wuri gobe kutaho da sassafe kinjiko? keda Yasmeen zakuzo Iman kubarta dasu meema tunda akwai masu gadi". Dad'ine yakashe Khairat yau gashi akaron bati zata kaduna cike da murna tace. "Ayya kayi hak'uri ban sanar dakai bane sabida nasan ba lalle ne kabarmu mujeba, amman kayi hak'uri kuma insha Allahu gobe zamu iso akan Kari". Sallama sukayi zuciyarshi cike da tausayinta da'ace ze iya hak'ura da Yasmeen dayayi kodan farincikin Khairat to baze iyabane amman harga Allah yana tausayinta. Washe gari da sassafe suka shirya dan Yasmeen Khairat nasanar da ita zancan Hydar murmushi kawai tayi,dan tasan bomb ne ke shirin tashi da d'aya daga cikinsu. Kayanta data had'a su tayi saurin kaiwa boot batare da Khairat taganiba driver yasaka mata sannan takoma ta d'auko na Khairat d'in shima akasa. Har mota Iman tarakosu suka shiga driver yajasu zuwa kaduna. Sun iso kaduna lokacin danginsu sungama taruwa kwansu da kwarkwatarsu, kowa se murnar ganinsu akeyi nan aka shiga hirar yaushe gamo kamin a zauna taron. Ita ko Yasmeen gidan su Khairat takai jakarta d'akin Maman Khairat d'in ta b'oye,basu jima da zuwa ba su Abba suka kirasu aka had'u a tsakar gidan su Khairat dan yafi fad'i. Bayan bud'e taro da addu'a se gaishe gaishe dasuka biyo baya, daganan kowa yashiga kawo matsalarsa ana warware masa,wa'inda sukayi fad'a da junansu aka shiryasu, kowa fuskarsa inbanda annuri ba abinda take fitarwa,Abban Khairat ne yace a saurara yanada magana me muhimmanci.
.
Gabad'aya natsuwa sukayi suna sauraron abinda zece,gyaran murya yayi sannan yafara da cewa. "Munada wata magana me matuk'ar muhimmanci dazamu tattauna akanta, wacce kowa cikinku nakeso yamata duba na tsanaki dan inba hakanba abin ze haifar da gaba me tsanani acikinmu, dan haka kowa yabani hankalinsa" . K'ara natsuwa sukayi sosai suna sauraronsa. "Ba wata magana bace illah Hydar mijin Khairat yana son yak'ara aure, kuma bakowa yakesoba illah Yasmeen k'anwarta". A gigice Khairat ta mik'e tsaye jikinta inbanda rawa ba abinda yake da kyar tace. "K'aryane wlh,wannan zancan k'aryane, taya Yasmeen zata iya auran mijina wannan hirace". Tsawa Abba yadakamata yace takoma tazauna, yayinda gaba d'aya falon yakaure da hayaniya kowa nafad'in albarkacin bakinshi. Seda kowa yayi shuru sannan ya d'ora da cewa. "Jiya Hydar yazo har gida yasanar dani buk'atarsa nason Auran Yasmeen,wanda kunsani nasani wannan al-amari ba haramun bane shiyasa nace yabari zamu shawarta akan zancan". Abban Yasmeen ne yamik'e ranshi ab'ace ya damk'o Yasmeen d'in yafara duka,da kyar aka kwaceta a hannunshi cikin fushi ya fara magana. "Kaiconki Yasmeen wlh kinyi asara,mijin y'ar uwarki zaki aura to wlh matuk'ar nina haifeki baki isa kisani jin kunyaba". "Kai har Kana da iko da Yasmeen sama dani? da zakace in kaine mahaifinta? to inso Kake ka tabbatarmin da yanzu ka haihu bisimillah Nasiru nunamin iyakata".Abban Khairat yafad'i cikin tsananin b'acin rai dan maganar Abban Yasmeen d'in ta b'atamasa rai. Kubiyoni taku har kullum.
.
Hak'uri Abban Yasmeen ya durk'usa yana ba yayannasa,sauran family ma suka sa baki sannan ya hak'ura aka ci gaba. Yasmeen se kuka takeyi sabida ta daku a zuciyarta ko fad'i take,"wlh ko kasheni za'ayi sena aureshi". Khairat gaba d'aya komawa tayi kamar wata mahaukaciya se zare ido kawai take tana soshe soshe, abin gwanin ban tausayi, duk da bata gama yarda da abinda ake fad'inba. Abba ne yaci gaba da magana. "Yasmeen inaso kitashi kiyimana bayani kinason Hydar ko bakya sonshi? domin shi ya tabbatarmin inbake baze iya rayuwaba shin ko kema hakan take a gurinki?". Mik'ewa Yasmeen tayi without fear tace. "Tabbas Abba inason Hydar kuma nima a shirye nake narasa rayuwata matuk'ar ban sameshi a matsayin mijinaba". Wani kukan kura Khairat tayi ta shak'e Yasmeen kamar wata me aljanu idonta sunfito waje sosai bakinta har kumfa yake tace.
.
"K'arya kike Yasmeen wlh baki isa kihau shimfid'ata ba,bakiji kunyataba kike furta kinason mijina agabana da kuma iyayanmu?menayimiki haka dakika rasa me zaki sakamin dashi se cin amanata? me nayi miki?Yasmeen me nayimiki?".kuka take sosai tana jijjiga Yasmeen d'in, itako Yasmeen ko ajikinta illah ma kwace jikinta a hannunta datayi sannan tace. "Ina kiranki da babbar murya dakiyi gaggawar cire kalmarki tacewa naci amanarki,ni banci amanarkiba hasalima abinda nayi ay bakaina farauba,nide abu d'aya nasani shine ni bazan hana zuciyata abinda takesoba akan farincikin wani,kamar yadda Aunty Fatima tayi a k'arshe ta b'ige da ciwon zuciya, niba haka nakeba Hydar mijinki yayimin kuma inasonshi". jikake tass Fatima ta d'auke Yasmeen da mari tasake k'ara mata cikin kuka ta fara magana. "How dare you Yasmeen?i said how dare you?!!,karki k'ara jingina wannan maganar da abunda yariga ya wuce,inma Danni zakiyi ni najima da yafewa,ke bama hakaba waye ya baki labarinnan da kike rik'e dashi tsawon wannan lokacin? Tell me who told you our secret"Fatima rik'e take da Yasmeen tana hawayen tausayin Khairat. Yanke jiki Khairat tayi ta fad'i k'asa sumammiya,dagudu akayo kanta ana mata fifita kan kace me gida yakaure da hayaniya masu kuka nayi, dan basu tab'a fuskantar tashin hankali irin wannan ba, ruwa aka yayyafawa Khairat ta farfad'o ay kamar jira Yasmeen take ta farfad'on tace.
.
"Wlh Aunty Khairat ba suma ba ko mutuwa zakiyi sena auri mijinki,tunda kema baki tausayawa Aunty Fatima ba kika iya rabata dashi bayan kinsan shine buri da fatanta kamar yadda shima Yaya Hydar d'in Aunty Fatiman ce burin ransa kika rabasu, a sanadin hakan har ciwon zuciya ta kamu dashi kamar zata mutu Amman baki tausaya mata ba, to wlh nima kam banajin zan tausayamiki matuk'ar Yaya Hydar yana Raye kuma nima ina raye sena Aureshi dan tun shekaru bakwai dasuka wuce nake da burin karantar dake illar *cin amana*shiyasa natashi da burin *fansa*banajin akwai wani yanayi dazaki shiga dazesa na janye k'udirina,dan haka ki shirya zama dani a matsayin kishiyarki nanda wasu kwanaki". Faskaren itace Umman Yasmeen ta d'auko ta jefeta dashi Allah yasota ta kauce,mik'ewa tayi zata bita Umman Khairat ta dakamata tsawa da cewa. "Ya isheki haka nace,wlh kika sake kika kuma dukanta wlh sena shayar dake mamaki, meye naku na ganin laifinta bayan ga babbar algungumar can da yadace ku daka,ay dama Khairat na fad'amiki akwai ranar k'in dillanci kuma gata Allah yakawomu,wlh inde inada iko akan Yasmeen seta auri Hydar koda kuwa babu wanda ya amince acikinku". Gaba d'aya kansune ya kulle sunrasa gane inda maganganunsu suka dosa, kamar hakan na nufin akwai sa hannun Khairat game da ciwon zuciyar Fatima kenan. Abban Khairat ne yadakawa kowa tsawa suka natsu sannan yakai dubansa kan Fatima yace. "Fatima ki dubi girman Allah ni mahaifinkine kidaure kisanar dani dalilin kamuwarki da ciwon zuciya kiji tsaron Allah ki sanar dani gaskiya". Cikin kuka Fatima tafara magana dan bata da ikon b'oye mishi tunda ya d'aureta da jiniyoyin jikinta dan Allah ba abin wasa bane. "Tabbas Abba Hydar ni yake so kuma nima haka, akwai soyayya da shak'uwa me tsanani tsakaninmu har zuwa ranar daka kiramu akan mu fitar da mijin aure,se jinayi Khairat tace ita Hydar yakeso hankalina yatashi shine ma abinda ya hanani magana har muka baro gurinka, bayan mundawo d'aki ne tasameni tacemin yazama dole nabarmata Hydar sabida a matsayinta na kyakkyawa da ita yadace baniba, sabida ikrarinta nacewa ita matar manyace, tajamin kunne akan idan har ban barmata shiba zata kashe kanta kokuma taje tayo cikin shege tace shi yayi mata, Ta yadda dukanmu zamu rasa tunda tasan inde tayi hakan bazaku yarda ku Aura minshiba, haka dole nabar mata shi badan banasoba sedan samamata farinciki"ta k'arasa zancan cikin matsanancin kuka. Umman Khairat ce ta amshi zancan. "Kuma nima shaidace dan Fatima ce Ta matsawa Hydar har ya yarda ya auri Khairat dande kawai ya faranta ran fatiman"daganan ta kwashe duk abinda tasani ta shaida musu. "Kuma kamin na amince da auran Khairat seda mukayi yarjejeniya da Fatima akan duk sanda nasamu zab'ina ko a inane zan aureta, kuma ita kanta Khairat d'in tasan da zancan kuma tayi na'am da hakan,sede ta amincene aganinta da zaran munyi aure zata d'auki hankalina"inji Hydar wanda ke k'ok'arin k'arasa shigowa cikin tsakar gidan, dan tunda aka fara cece kucen Yasmeen tayimishi text a b'oye akan yazo kar akasheta a banza shiyasa yazo yanzu. Dukansu sunyi mamakin ganinsa har yasamu guri kusa da kamal ya zauna basu dena kallonshiba.
.
Kowa hankali atashe suke kallon Hydar. Abban Khairat ne yasoma magana cikin fushi wanda basu tab'a zaton yana dashiba. "Khairat kinyi asara wlh duniya da lahira yanzu duk yadda kuke da Fatima seda kika ci amanarta, to ke wacece da baza'a d'au fansa akankiba wlh kinyi kad'an kece silar komai kinso zumunci yab'aci to da yardar Allah zumuncinmu daga Allah yake ku baku isa ku tarwatsamana shiba". Zasuyi magana yadakatar dasu da cewa. "Bana buk'atar jin komai daga gurinku, Hydar inaso kamik'e ka shaidawa kowa abinda ke ranka buri da kuma fatanka". Mik'ewa Hydar yayi cike da kwarin guiwa Khairat binshi kawai take da ido kamar mujiya fatanta Allah yasa yafasa Auran Yasmeen. "Salamu Alaikum jama'a ni Hydar inason Yasmeen da aure kuma banida wani buri daya wuce inga faruwar hakan shine fatana zanrik'esu duka bisa gaskiya da rik'on amana inde har kun amince kun bani". Gaba d'aya gurin kaurewa yayi da hayaniya wasu nacewa Sun yarda wasu nacewa basu yarda ba. Abban Khairat ne ya tsawatar musu ta hanyar cewa. "Ba shawararku muke soba abu d'aya nasani ko duka duniya gatan Khairat ne sena aurawa Hydar Yasmeen yanzu batare da bata lokaciba, ko kunaso ko bakwaso tunda nidasu munaso ya wadatar"yana gama fad'in haka yasa hannunshi a aljihu yaciro bunch d'in d'ari biyar dubu hamsin kenan ya d'aga sama yace. "Ni Alhaji Mukhtar Abubakar uba ga Hydar ina nemarwa d'ana Hydar auran y'arku Yasmeen abisa sadaki naira dubu hamsin,idan kun amince waliyyin Yasmeen yafito ya bani auranta". Ihu Khairat tasa ta je ta kama k'afar Abban nata tana kuka tana fad'in. "Abba karka tarwatsa farincikina wlh bazan iya kishi da Yasmeen ba tafini komai, Abba kishi da ita azaba kawai zansha mace irin Yasmeen aka had'ata da kishiya wlh seta kashe kishiyar da bak'in ciki don Allah karka yimin haka natuba kagafarceni don Allah".wani kyakkawan mari Abba yasakarmata wanda yatilastamata ganin wucewar wutar nefa a waya, agigice tasaki k'afarshi takama ta Abban Yasmeen tana rok'onshi,rasa yazeyi da ita yayi kawai rungumeta yayi yana rarrashinta dan zuciyarshi tafi tata k'una kawai de anfi k'arfinsane.
.
Abban Khairat ne yasake nanata buk'atarsa tanemawa Hydar auran Yasmeen inda yabuk'aci waliyyin Yasmeen ya fito Amman gaba d'ayansu ba wanda ya motsa hakanne yasa yace. "Hydar da Yasmeen kuzo muje masallaci a d'aura muku aure nan banida wata darajar daza tasa su bani auran kutaso muje" ya mik'e yana shirin ficewa. Da gudu Abban Yasmeen yaje ya kama k'afarsa yana fad'in. "Yaya don Allah karka tonamana asiri kayi hak'uri karkayi fushi damu inde waliyyine gani zanmata walicci don farin cikinka kawai badan suba kayafemana don Allah". Dakyar Abban ya hak'ura yakoma yazauna nandanan aka fara karanto sharudd'an aure yana amsawa daga k'arshe yamika sadaki aka d'aura auran Hydar da Yasmeen cikin k'ank'anin lokaci. Khairat tana ganin angama d'aura auran ta yanke jiki ta fad'i k'asa sumammiya da gudu sukayo kanta Zasu Kawo mata agaji Abba yadaka musu tsawa yace. "Duk Wanda yasake ya tab'ata wlh senayi Shari'a dashi,dukanku ku watse a gurinnan na sallami kowa kubarta ta mutu ma intaso, mugun iri zamu rage" ya fad'i cikin tsananin fushi wanda ke nuni da abinda yafad'a ze iya aykatawa. Jiki a sanyaye d'aya bayan d'aya suka dunga ficewa a gidan har kowa yafice amman Hydar na tsugunne a gabanshi kallonshi yayi yace. "kai me kake jira dabaka fitaba?". Kukane ya kubcewa Hydar sabida yayi imani duk abinda Abba yakeyi dauriyace kawai dason k'arfafa zumunci amman ba wanda za'awa y'arsa haka komai laifin da tayi beji zafiba,cikin kuka Hydar yace. "Abba kayimin dukkan hallacci kuma nagode kuma zan kasance me maka biyayya akowanne al-amari sede yanzu Abba zuciyata tagaza yimaka biyayya kayi hak'uri wlh bazan iya ganin Khairat cikin wannan yanayin natafi nakyaleta ba" yana gama fad'in hakan ya nufeta d'aukarta yayi kamar gawa yafice agidan motarshi yanufa da ita ya kwantar da ita abaya yashiga yatada motar yanufi asibiti da ita. Abba ko zuciyarsa da tayi bak'ik'k'irin abisa abun da yafaru tabbas dauriyace kawai yakeyi Amman kulawar da Hydar yanuna ga Khairat a gabansa yasa duk wani b'acin Ransa yanemeshi ya rasa tabbas ya yarda Hydar k'addarace ta fad'a masa nason auran Yasmeen amman bawai dan ya shirya wulak'anta Khairat ba, wani farinciki yaji yana shigarsa tabbas yayi abinda yadace Allah yabasu zaman lfy.
.
Yasmeen ko duk inda tashiga se gulmarta akeyi ana kyararta,wasu suyi agaban idonta wasu kuma suyi abayan idonta. To kunsan halin mutuniyar taku ba tsaron kowa takejiba dan haka Bud'ar bakinta se cewa tayi. "Ayyiriririy ni Amarya a Gidan Hydar tunda bak'inciki yasa kun Kasa yimin y'ar gud'ar da akewa Amarya yayinda aka d'aura mata aure toni nayiwa kaina,kuma wlh komai zakuce daga bayane tunda nariga nazama mallakinsa Wanda ku baku isa ku rababa dan haka kun dade baku zageniba"ta fad'i cikin isa ita duk zatonta iyayenta basa cikin gidan shiyasa tazage ta karkad'awa masu gulmar tata rashin kunya. Wuf taji an damk'ota ta baya Umman tace kan tayi wani yunk'urin guduwa tariga ta rik'eta nanfa tashiga dukanta kamar zata kasheta dangin suna kallo bawanda yazo ya ceceta ita kuma takasa gudu Umman ko cigaba take da dukanta iya k'arfinta Yasmeen tun tana kuka har muryar ta dusashe da sauri Fatima tazo ta kama Umman Da kyar takaita d'akin da ba kowa tace cikin kuka. "Haba Umma meyasa kike hakane?dukan dakike matane ze warware auran da aka riga aka d'aura? koko shine ze shafe abinda yafaru,?kidubafa kiga ko kara cikinsu bawanda yamiki kina dukanta amman bawanda ya ceceta wanda aka'ida hakan ba dede bane,Umma duk abinda kayi se anmaka, meyasa baki dauki hakan a matsayin sakayyace Allah yayimin ta wannan hanyarba? nide gaskiya kidena dukanta haka shi kanshi mijinta inyaji kindaketa wlh girmanki ze zube a idonshi tunda son da yake mata banawasa bane Amman kiyi hak'uri inna batamiki rai". Ajiyar zuciya umman tayi sannan tace. "Fatima rainane yab'aci badan komaiba sedan ruk'on da Khairat tayimata na tsakani da Allah amman bawai ina Jada hukuncin Allah bane, bakomai bazan kuma dukantaba,matuk'ar batazo inda nakeba". Kamal ne yace Fatima ta fito su tafi gida Abba yace su wuce gida shiyasa da zasu wuce ta kama hannun Yasmeen suka tafi tare dan bazata barta ummansu ta Illa tata ba itama lokaci yayi dazatawa Y'ar uwarta rana, tunda tasan komai Yasmeen tayi Dan ita tayishi. wannan kenan
0 comments:
Post a Comment