.
Hurewa Iman ido Yasmeen tayi wanda hakanne yadawo da ita daga tunanin data shiga. "Yasmeen kinsan bama irin wannan wasan dake don Allah kifad'amin gaskiya". Yasmeen wayarta ta ciro ta nunawa Iman hotunan bikinsu da Hydar sannan tace. "To yanzu kin yarda ba wasa nake mikiba ko?". Rage murya Iman tayi alamar rad'a tace. "Yasmeen keda Aunty ba Y'an'uwa bane?". "Y'an'uwane mana". "To meyasa kika auri daddy bayan kinsan mijin tane?". "Saboda Daddyn ki yanuna ze iya mutuwa idan ban yarda na aureshi ba, koko laifine danna ceci rayuwar Daddyn ki?". Da sauri Imam ta girgiza kai sannan tace. "But Yasmeen" "shshshsh, keep your mouth shut,just answer me, are you happy for having me as your new Mum or not? just tell me".inji Yasmeen. "I really happy for having you as my sweet Mum,Allah yabaku zaman Lfy, dukanku".ta fad'i tana dariya. Rungume juna sukayi. Ranar Yasmeen da Iman guri guda suka kwana yayinda Hydar yake tare da Khairat dan tuni suka shirya dama ance tsakanin mata da miji se Allah. Al-amura sunci gaba da tafiya yadda yakamata, Yasmeen kissa take zubawa bata wasaba yayinda Khairat itama ba'a barta a baya ba, tabi sawun Yasmeen d'in Amman dayake ita Khairat tana da saurin fushi Yasmeen tafi cin galaba akanta dan ita Yasmeen koda taji haushin bata bari kowa yagane.
.
Yau Yasmeen ce da girki,dan haka tun safe take aykace aykace a gidan,hydar yafita gurin ayki tun da sassafe. D'akin Hydar taje ta gyara ta feshe shi da turaruka masu k'amshi,sannan tajawo k'ofar ta rufe,tanufi nata d'akin tana cikin gyaran d'akin taji amai yana taso mata da gudu ta nufi toilet tafara kwara aman kamar zata amayar da kayan cikinta, da kyar tasamu ta gyara inda ta b'ata ta dawo d'aki, kwanciya tayi a k'asa tana hutawa bata tashiba seda taji ta dawo normal, sannan ta nufi kitchen ta fara hada-hadar d'ora girki. Bayan tagama d'ora komai ne tanufi d'akin Hydar domin ta manta bata kwaso kayan wankin shiba akan kujera ta barsu danhaka taje kwasowa,sede me tana zuwa seta tarar ankulle k'ofar d'akin ancire key kuma tayi imani Khairat ce zata rufe,alhalin ranar girkinka kai kake da iko da d'akin dan haka falon Khairat d'in tanufa. A zaune tasameta ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana karkad'awa hannunta rik'e da mukullin d'akin tana jefashi tana cafewa. "Aunty dama key nazo kibani na d'akin Daddy dan inaso zan kwaso kayan wanki nabada a wanke". Cike da masifa da bala'i Khairat tasoma magana,dan dama cike take da Yasmeen d'in. "D'akin na Ubanki ne da zaki zo kitasani a gaba akan in baki key?". Ran Yasmeen ba k'aramin b'aci yayiba, kuma dama ba wannanne Karo na farko da Khairat ta zagi Ubanta ba tasha yimata bata kulata, Amman yau de kam se abinda hali yayiwu takaita bango,dan haka tabata amsa azafafe. "D'akin bana Ubana bane, kamar yadda yake kema bana Ubanki bane, dan haka yazamarmiki dole kibani key d'in d'akin Mijina". Jikake Tass Tass Khairat ta wanke Yasmeen da Mari sannan ta hankad'ata ta fad'i tabita tafara dukanta iya k'arfinta,Yasmeen har ta d'aga hannu zata rama sekawai ta fasa ,dan koba komai taci darajar mijinsu. Khairat ko zagin Yasmeen take Ta Uwa ta uba tana dukanta fad'i take. "Yau senaci kan ubanki a gidannan, duk wata rashin kunya da rashin mutunci dakike tak'ama dashi yau zan sauke miki su, shegiya tsinanniya me mance halacci". Yasmeen ta daku a hannun Khairat,tayi tayi ta kwaci kanta a hannunta Amman ta Kasa, sabida Khairat tafita k'arfi nesa ba kusaba,hakan yasa Yasmeen tagaji ta saduda tabarta tana ta dukanta, wani naushi da Khairat takaimata k'asan mararta shiyasata kwalla wata razananniyar k'ara sannan ta fad'i k'asa sharab, hakan yay dai-dai da shigowar Hydar falon, jini ya hango yana zubowa daga k'asan k'afafuwan Yasmeen yayinda Khairat ke zaune akanta tana duka. Muje zuwa readers.
.
Da gudu Hydar yak'arasa gurinsu wani wurgi yayi da Khairat gefe guda ya sunkuya ya d'auki Yasmeen wacce zuwa lokacin ko numfashi batayi. Da gudu yanufi mota da ita ya kwantar da ita yaja motar zuwa Asibiti,da isarsa Asibitin Ma'aikatan Asibitin suka fito suka amsheta. Emergency room aka kaita,likitoci suka rufu akanta,Hydar ko se safa da marwa yakeyi hankalinshi atashe yama rasa wanne hukunci zewa Khairat fatanshi Allah yatashi Yasmeen lafiya. Likitane yafito yace Hydar yabiyoshi office,marawa likitan baya yayi har suka isa office d'in suka zauna,hannu likitan yamik'a masa suka gaisa sannan yafara yimasa bayani kamar haka. "Ranka yadad'e a binciken damuka yi mungano madam tana d'auke da ciki na tsawon wata biyu,amman sanadin duka ko fad'uwa da tayi ko akamata akan cikin yasa cikin ya zube,yanzu Muna buk'atar jinin da zamu k'ara mata dan tayi asarar jini da yawa". "Inna lillahi wainna ilaihirrajuun", itace kalmar dake yawo akan bakin Hydar,lokaci guda ya rikid'e yazama Aliyun ko likitan seda ya tsorata da ganin yanayinsa.
.
Jininsa aka gwada yayi dede da nata dan haka nashi aka d'iba aka samata,ana gama d'ibar jinin afusace yanufi motarsa yajata zuwa gida. Khairat ko ba k'aramin tashin hankali tashigaba ganin jini nabin Yasmeen lokacin da Hydar ya d'auketa,gaba d'aya tagama firgicewa tama rasa abinyi se safa da marwa take yi a falo shigowar Hydar ce ta dawo da ita seti,tun kamin tayi wani yunk'uri ya rufeta da duka,be kyaletaba sedan kanshi dayaji ya gamsu. Kuka Khairat take ba na wasa ba tana rok'on shi yayi hak'uri,mari ya kifa mata lafiyayye wanda har tuntsurawa tayi sannan yace. "Tur da kishi irin naki Khairat,yanzu ko nagama yarda hundred percent cewa zaki iya kasheni ma ba Yasmeen ba, tunda har zaki iya yimata dukan da ciki ze fita ajikinta sabida tsabagen son kai irin naki, Khairat baki da imani kwata kwata dan da kina dashi da bazaki haikewa yarinyar da kikasan ba k'arfinku d'aya ba, Da kina da imani da tuni kinjima da yarda da k'addarar kasancewar Yasmeen abokiyar zamanki, nagaji Khairat dan haka ki tattara ina ki inaki kibarmin gida *na sakeki saki d'aya*,yanzu ba se anjimaba kificemin a gida"ya k'arasa zancan hawaye na zuba daga idanuwanshi. Ihu Khairat ta saki ta ruga ta Kama k'afar Hydar tana fad'in. "Wayyo Allah na shiga uku!!!Hydar karufamin asiri kayimin kowanne kalar hukunci Amman banda na rabuwa dakai, wlh bazan iya rayuwa ba babu Kai, kuma wlh bansan Yasmeen nada cikiba kayarda dani da bazan daketaba,Hydar wlh in Abba yaji wannan batu kasheni zeyi karufamin asiri kamaidani d'akina don Allah",ta fad'i cikin matsanancin kuka tana rik'e da k'afarshi.
.
K'wace k'afarshi yayi sannan yace mata. "Wlh da Abba ze kasheki senafi kowa murna, dan Allah yace "annafsi bin nafsi",kinga kema kisan kan kikayi,dan haka nagama magana idan kika bari nadawo nasameki wlh sekin raina kanki"yana gama magana yajuya yafice a gidan yanufi Asibiti zuciyarshi na tafasa. Kuka Khairat take kamar mahaukaciya gabad'aya ta kid'ime ta gigice tana neman agajin ubangiji, ganin tarasa mafitane yasa ta d'auki abinda zata iya d'auka ta zuba a mota gamida y'ay'anta Arfat da Meema ta kama hanyar kaduna tana kuka kamar zata mutu, Allah ne kawai yakaisu lfy. Gidan Fatima ta nufa dan nanne kawai take tunanin samun sassauci dangane da hukuncin dazata fuskanta daga sauran dangi. Ko a fuska bataga chanji ba daga Fatima hannu bibbiyu Ta amsheta,itako se kunyarta takeji k'arshema de rushe mata da kuka tayi,tashiga zayyana mata abinda yafaru ta k'arashe zancen dacewa. "Wlh Fatima ke kad'aice zaki yarda dani Wlh bansan Yasmeen tana da cikiba wlh bansaniba". Hankalin Fatima in yayi dubu yatashi jin Hydar ya saki Khairat akan Yasmeen.,sannan ga Yasmeen can a asibiti rai a hannun Allah kuka Fatima itama tasa tana fad'in. "Why Khairat? why always you?me yasa kika lashi takobin dole se kin haifar da tashin hankali tsakanin Iyayenmu?me zumuncinsu yay miki kikeson ruguzashi?, duk abinda Yasmeen tamiki kece kika siya da kud'inki bawai kuma ina fad'amiki hakan bane dan ina bayan Yasmeen, gaskiyace dole nafad'amiki Khairat bakyawa kanki da Iyayenmu da Mijinki adalci"ta k'arasa zancan tana kuka.
.
"Wlh Fatima base kin maimaitaba nasani nice banida da gaskiya,duk abinda mijinka yanuna yana so nuna masa zakayi kai kafishi so da na ja Yasmeen ajikina wlh nasan haka bazata faru akainaba,Fatima nashiga uku don Allah kitaimakamin ki rufamin asiri insu Abba sukaji zancannan kasheni zasuyi kitausayamin don Allah". True love gaskiyace. Fatima rungume Khairat tayi tana kuka tana mata alk'awarin insha Allahu babu mejin wannan maganar ta kwantar da hankalinta. .D'aki Fatima taba Khairat ita da yaranta sannan tashiga tunanin ta ina zata fara shawo kan wannan matsalar? Amman Bari taji daga Hydar d'in inde yakira waya ya sanar da Yasmeen tayi B'ari to ko tabbas dole asiri ya tonu amman idan be kiraba shine abin zezo da sauk'i. Hydar yana isa asibitin yatarar Yasmeen ta farka se kuka take mararta na ciwo,da sauri ya isa gurinta ya rungumeta yana rarrashinta gami da kwantar mata da hankali har ciwon ya lafa. Kwananta uku a Asibitin aka sallameta ta warke sarai kamar ba itaba sede d'an abun da ba'a rasa ba, koda suka isa gida tayi mamakin ganin Iman ce kawai a gidan,bayan tayi wanka Ta hutane taci abinci Hydar yashigo d'akin yabata maganinta sannan yatambayeta abinda ya had'ata da Khairat ba musu ta fad'amishi komai iya gaskiyarta. Tausayinta yaji yakamashi ashe akan tanason faranta mishine akamata asarar ciki wanda har yanzu Batasan da batun zubewar cikin ba hasalima batasan tana da cikin ba dan Hydar be fad'amata ba dan baya so ta tsani Khairat a ranta kodan zumuncinsu. Fatima jin shuru Hydar be fad'i Yasmeen bata da Lafiya bane ya kwantar mata da hankali,uwa uba wayar da sukayi da Yasmeen d'in itama batace mata Khairat ta doketa ba,shi yabata kwarin guiwar son dedeta tsakanin Khairat da Hydar batare da sanin Iyayensu ba, Fatanta Allah yasa ta dace da hakan. To Fatima muma muna miki fatan kidace. .
.
Fatima number Hydar ta kira. Bayan sungaisane ta soma da cewa. "Hydar naji duk abinda ke faruwa tsakaninka da matanka,kuma a gaskiya hukuncin da kayiwa Khairat bedaceba ze jawo mana tashin hankali sosai adanginmu don Allah kayi hakuri kamaida ita dakinta batare da iyayenmu sunji ba dan tunda ta taho a gidana tasauka gudun bacin zumunci". "hmm Fatima kenan,yanzu duk laifin da Khairat ta aykata min kikeso namanta naci gaba da zama da ita to wlh dasake inda kin tilastani yin abinda bansoba to yanzu ni ba yaro bane dazaki tilastani,ko wancan lokacin ma yarintace tasa naamince, dan haka inzaki iya sa ido kiyi kallo kisa kicire kanki acikin wannan maganar",yana gama fadamata haka ya kashe wayar gaba daya. Hankalin Fatima tashi yayi dajin kalam Hydar hakan na nufin dole se zancan yakai ga iyayensu kenan. Yasmeen kwananta biyu da dawowa gida Amman bataga Khairat da yarantaba, koda ta tambayi Hydar cemata yayi taje Kaduna ne,be sanar da ita komai,fatan Allah yadawo dasu lafiya tayi. Yasmeen ce zaune gaban computer tana latse latsenta,a dakin Hydar,kamar ance taba kawai seta shiga inda mutum zega abinda ke faruwa a gidan wato CT camera old videos tashiga. Hydar tagani yana dukan Khairat,har zuwa lokacin dayace yasaketa,har batun zubewar cikinta duk seda taji. Tashin hankali baa samishi Rana. Ita bata cikin takeyiba sakin da akayiwa Khairat a dalilinta shi yafi daga mata hankali,da sauri taciro wayarta takira Fatima tana bata labari gami da tambayar ina Khairat din take.
.
Kwashe duk abinda yafaru Fatima tayi tabata labari har yadda sukayi da Hydar,Yasmeen bataji dadin abunba sam,kamin suyi sallama seda Fatima ta roki Yasmeen akan ta roki Hydar yadawo da Khairat dakinta. Hydar yana dawowa daga gurin ayki yaga Yasmeen atsaye tana kallonshi babu alamar walwala a fuskarta, karasawa yayi inda take ze rukota da sauri ta bige mishi hannu sannan tasa mishi kuka tana fadin. "wanne kalan suna kakeso duniya takirani dashi,sokake zumuncin gidanmu ya rushe a tsakanin iyayenmu,mene naka na sakin Khairat dan munyi fada,kana tunanin wai dan na aureka bana son tane,cikina da ya zube daga Allah ne ba ruwan Khairat wacce nayi imani da tasan inada ciki bazata dakeniba,".tacigaba da kukanta. Hydar ya rasa abinyi wato yanzu Yasmeen tasan abinda yafaru kenan waya fada mata,rasa amsane yasa yawuce dakinshi, da shigarshi dakin ya fahimci inda Yasmeen taji zancan ta hanyar ganin computer dinshi a bude. Dakinta ya nufa domin ya rarrasheta, Duk magiyar dayake mata taki sauraronshi karshema cewa tayi itama Kaduna zata tafi. Hydar yaga daru gurin Yasmeen dan bata kyaleshi ba har seda ya furta yamaida Khairat Amman darajarta taci. .Waya tasashi yayiwa Fatima dan ta sanar da Khairat Hydar yamaida auransu ba musu yakira Fatima ya sanar mata. Wani dadine yakama Fatima da Khairat dan har kuka sukayi name farinciki. Fatimace ta maida Khairat gidanta sannan tamusu waazi sosai akan illar tarwatsa zumunci suyi hakuri su zauna Lafiya. Bata kwanaba a ranar ta koma kaduna ranta da zuciyarta sunyimata sanyi. Yasmeen har kasa ta tsugunna tanemi gafarar Khairat,cikin kuka itama Khairat ta tsuguna tana neman Yasmeen ta gafarta mata abinda taimata, dukansu kuka sukeyi suka rungume juna. Hydar yaji dadin ganinsu a haka zuwa yayi ya rungumesu duka yana sa musu albarka da fatan zaman lafiya a tsakaninsu. Bayan wata goma. Yasmeen naga Hydar ya dauko da tsohon ciki tana kuka Khairat na binshi da wani akwati suka shiga mota basu zame ko ina ba se asibiti,ananne naji ashe nakuda take. Labor room aka shigar da ita abin gwanin tausayi bata jimaba ta haihu tasamu yan biyu duka maza kamarsu daya da Hydar. Murna da farincikin dasukayi baya misaltuwa barinma Khairat har kuka tayi na farin ciki. Ranar suna yara suka amsa sunan Abban Khairat da Abban Yasmeen.suna kiransu da Fadeel da Nabeel. Fadin bidirin da akayi baze yiwuba Amman fa taro yakai taro. Khairat da Yasmeen yanzu ba wani fada a tsakaninsu dan yanzu Khairat tagama gane albarkacin Yasmeen taci Hydar yadawo da ita,Yasmeen tana mutunta Khairat sosai itama haka. Taron family Hydar ya kaisu Kaduna ananne Hydar yabada labarin abinda yafaru tsakaninshi da Khairat da kuma tsakanin Khairat da Yasmeen, fada dekam sun shashi bana wasaba daga karshe fatan zaman lafiya akayimusu taro yawatse kowa yatafi. Yasmeen ta koma makaranta inda take karanta bangaran likitanci,Iman tayi aure itama inda ta auri wani dan majalisa itama abin gwanin Shaawa. Bayan shekara ashirin da biyar. Abubuwa sun faru da yawa a tsawon wannan lokaci aciki harda rasuwar Granny da Abban Khairat, da iyayen Hydar gaba daya sunyi jimami daga baya suka fauwallawa Allah. Taron jamaa na hango a cikin masallacin sultan Bello dake anguwar sarki Kaduna,ko baa fadamaba taron na daurin aurene,kunne nasa dan inji auran wa akeyi ayko najidin domin ji nayi ana fadin. An daura auran *Hydar Kamal mukhtar, Da Amaryarsa Fatima Hydar Jibreen,*ikon Allah Ashe da rabon Hydar da Fatima suyi aure.
.
Zumuncinsu se kara karfi yakeyi ta kowacce siga. Yasmeen yanzu yaranta biyar hudu maza mace daya me sunan Khairat,itama Khairat ta haifi yara uku mata aciki da mesunan Yasmeen suna kiranta princess. So da kauna tsakanin Yasmeen da Hydar sede hamdala har zuwa yanzu bashida wani farinciki se nata,kuma yana yin adalci atsakaninsu dan koda wasa baya bari yafifita wata a gaban wata, duka daya take daukarsu. Arzikinshi se karuwa yakeyi ba dan kadanba, haka shima kamal mijin Fatima yasamu babban matsayi a gurin aykinsu dan haka tuni ya tamfatsa gini a garin Abuja yamaida Fatima can. Yasmeen da Hydar one love with Khairat. *Alhamdulillahi ala kulli hali.* *Godiya ga Allah Subuhanahu wata ala,daya nunamin wannan rana dana gama littafin cin Amana ko fansa.*
tnx u
ReplyDelete