.
Ta iso Kaduna lafiya,tunkamin tagama parking ta tabbatar da zancan Faeexa sabida motar Hydar da tagani a k'ofar gidansu. Da gudu tashige cikin gidansu har ta wuce sit room sekuma ta dawo sabida jin muryar Hydar da tayi aciki shida Abban ta,da sauri ta fad'a cikin d'akin tana kuka jikin mahaifinta ta nufa ta rungumeshi.
.
Gaba d'ayansu sunyi mamaki da zuwanta,babu ma kamar Hydar, cikin kuka Khairat take magana da mahaifinta. "Abba wlh Yasmeen da Hydar so suke su kasheni,Hydar bashida adalci ko kad'an rabona dana sashi a idona,ko naji muryarsa tun ranar da yataho da Yasmeen sekuma yanzu dana ganshi tare da kai, Abba kataimakeni kar na mutu don Allah". Maganganun Khairat tabbas sunshigi mahaifinta dan ko a ido ka kalleta kasan bata da kwanciyar hankali,duba da ganin yadda tarame tayi bak'i tafita hayyacinta. Hydar ko ji yayi kamar k'asa ta tsage yashige don kunyar da yaji,gaba d'aya rasa yadda zeyi yayi,se yanzu ya gane beyi mata adalci ba,natafiya da yayi batare da ko kud'in cefane ya bata ba,kunyar idon Abba gabad'aya ta dabaibayeshi,so yake yay magana Amman yakasa. Abban ranshine ya b'aci game da abinda Hydar yama Khairat,ko wanne irin laifi tamasa,be dace ya kwashe sama da kwanaki saba'in batare da yaje inda take ba, sosai abun ya b'ata masa rai dan har akan fuskarsa se da fushin shi ya nuna. Hydar zeyi magana Abban ya dakatar dashi da cewa. "Kar kacemin komai Hydar, nagama fahimtar komai, nide abu d'aya zance maka shine kayi hak'uri idan kuma kagaza hak'urin dasu to duk wacce ta b'ata maka rai ka sallameta kawai ta dawo gida dan zama da ita bashi da amfani a gurinka". Wayyo Allah. Hydar gabad'aya rikicewa yayi tabbas yasan yau yakai Abba k'arshe shiyasa ya masa wannan maganar. muryar Abba ce ta dawo dashi daidai. "Khairat kije kici gaba da hak'uri kinji ko,sanin kankine matar shige bata daraja a idon mijinta,mijinku bakece zabinsa ba Yasmeen ce zab'insa, kinga ko matsayinku baze tab'a zuwa d'aya ba a gurinshi, dan haka kicire idonki akan komai,kuma karki ce zaki had'a kanki da ita dan ke wuya zakisha, kamar yadda kikasha a yanzu,duk sanda ya sallameki kizo gida,mu kina da muhimmanci a gurinmu,kitashi ki wuce gidan mijinki yanzu batare da kowa yagankiba".
.
Cikin kuka Khairat takewa Abba godiya Ta Mik'e ta fice daga sit room d'in tanufi motar ta ta tayar takama hanya tana kuka gwanin ban tausayi. Shiko Hydar har zufa seda tashiga Karyo masa, Dan tabbas ya amince d'ari bisa d'ari be kyautawa Khairat ba sabida ko Abba seda ya cemishi se yayi hak'uri da shirmen daze gani daga gareta,muryar Abba ce ta katseshi dacewa. "To Malam Hydar munji dad'in wannan ziyara da kuka kawo mana kaida Amarya, Allah yasanya alkha'iri aci gaba da hak'uri,kugaida gida nabarka lafiya" yana gama fad'amasa haka yafice daga sit room d'in yashige cikin gida. Hydar kamar tsohon me basir kasa zama yayi, tabbas be kyautaba dole ya wanke kansa agurin Khairat hakanne kawai ze faranta ran mahaifinta. Fita shima yayi zuwa k'ofar gida gurin motarshi yanufa , waya ya d'aga yakira Yasmeen sabida ta je gidan Fatima dan acan takeso ta kwana,d'agawa tayi Ta gaisheshi ko amsawa beyiba yace. "Baby kitaho yanzu zamu wuce Abuja yanzu inkuma ba yau zaki tafiba nide yanzu ma zan wuce". Dariya Yasmeen takeyi harda hawaye dan gaba d'aya bata d'auki zancan nashi serious ba shiyasa cikin dariya tace. "Tabd'ijan! inzo Kadunar yau kuma sannan inkoma yau to wlh ba inda zanje, amman kai Tunda kashirya tafiya to Allah ya tsare hanya yakaika lafiya"ta fad'i tana kyalkyala dariya dan duk zatonta wasa yake mata dan yaji bakinta. Shiko amsawa yayi. "Ameen Babyna next week sena turo driver yad'aukoki". ba musu tace masa "to" Suna gama wayar ya fad'a mota ya tada ita shima yakama hanya gudu yake bana wasaba har yazo ya wuce Khairat akan hanya duk da itama gudun take Amman seda ya wuce ta. Be wuce gidaba, kai tsaye masu decorations ya biya yadauko suka zo sukayi decorations d'in gidan gaba d'aya kamar a India ko ina ka kalla haske ne ke tashi an rubuta FORGIVENESS IS THE SWEETEST REVENGE MY WIFE,PLS FORGIVE ME. Ko ina haka aka Rubuta, akan gadonta kuwa flowers aka zuba pink color akayi designing d'in heart daga tsakiya aka rubuta i miss you my princess,now am ready to be with you, please forgive me.kai in tak'aice muku gidannan ba inda ba'asa ba daga k'arshe wani had'ad'd'an cake ya ayka aka siyo mishi an rubuta am sorry my love akan cake d'in, d'akinta yakaishi aka masa decorating d'in inda ze ajiyeshi na musamman,wanka yayi ya shirya sude yaran se mamakin abinda ke faruwa suke, d'akinsu yaturasu yace karsu fito,shima guri yasamu ya Adana kansa dan yasan Ta kusa shigowa,ilai kuwa k'arar bud'e get yaji alamun ta dawo kenan. .
.
Khairat tana parking da gudu ta shige cikin gida dan har yanzu kuka takeyi,abinda taganine ya tilasta mata tsayawa fuskarta d'auke da mamaki. Bin rubutun take d'aya bayan d'aya tana karantawa da gudu ta haura sama inda d'akinta yake nanma ba k'aramin mamaki abun yabataba tunani take akan wayayi mata wannan abun? kode su Iman ne?bari de taje ta tambayesu, juyawar da zatayi tajita kawai ak'irjin mutum bud'e baki tayi zatayi ihu da sauri ya had'a bakinshi da nata hakanne yasa tagane waye. Be saketaba seda ya tabbatar da ta natsu sannan ya cire bakinshi anata,tun kamin tayi magana ya zube k'asa akan gwuiwowinshi ya had'a hannayenshi guri guda alamar neman yafiya. Hankalin Khairat ba k'aramin tashi yayi ba yau kamarta Hydar yake durk'usawa yana neman Afuwa?,da sauri ta durk'usa itama tana kuka tana neman gafararsa,rungume juna sukayi yana share mata hawaye yace. "Nasan banyi miki adalciba duk da de ke kika jawo amma pls kiyi hak'uri kinji hakan baze k'ara faruwaba insha Allahu"yasake rungumota jikinshi. Wani sanyi ne yake ratsa zuciyar Khairat tabbas ta yarda Hydar adalin sarkine sede ajizanci irin na d'an Adam. Cake d'in daya semata suka yanka kowa yaba d'an uwansa abaki dagananfa sallah sukayi sukaci abinci, koya Khairat ta Kalli decorating d'in da akayi dominta ranta sanyi yakeyi, Amman da zaran ta tuno Yasmeen se taji duk bata cikin natsuwa. Adaran sun martaba soyayya tamkar darensu na amarci sosai Hydar ya wanke laifinsa agurinta wanda ko shakka babu yasan Abba ma zeji dad'in hakan.
.
Yasmeen washe gari da wuri ta baro gidan Fatima zuwa gidansu,dan tanaso suje gidansu Hydar ta wuni acan,shuru shuru Hydar be kirata ba kuma bezoba shiyasa ta d'aga waya ta kirashi sede wayar akashe take,tsorone yafara kamata duk numbobinshi seda takira amman akashe hankalinta ba k'aramin tashi yayiba. Ummanta taje tafad'awa hak'uri ta bata tace, Hala" wani abunne ya tsareshi Amman ki kwantar da hankalinki zezone". Har zuwa azahar number shi bata shiga kuma bezoba dan haka gurin Abban Khairat taje ta sanar dashi,kwantar mata da hankali yayi yace Bari yakira Khairat ko tana da wata number tashi danshi sam be kawo aransa Hydar yatafi Abuja ba. Yana kiran Khairat bugu d'aya ta d'auka bayan sungaisane yace mata. "Kinada wata number Hydar ne kibani? Wanda nake dasu duk nakira akashe suke kuma gashi najishi shuru bezoba". "Abba ay Hydar gashinan yana bacci Tun jiya ya baro kaduna yama rigani isowa gida Amman bari ince mishi ya kunna wayoyinshi kana nemanshi". Da sauri Abba ya katseta da cewa,"kisashi ya kunna wayoyin Amman karkice na kiraki zannemeshi zuwa anjima".Yana gama fad'amata haka yakashe wayar,in yace Hydar be k'ara kima a idonshiba yayi k'arya,tabbas Hydar d'an mutuncine dayasan mutuncin manya, kuma ya yarda Hydar bayason b'acin ranshi dan yayi imani b'acin ran da ya nuna masane yasa yatafi Abuja a jiya Amman bawai Dan Khairat ba. Dubansa yakai gurin da Yasmeen take gabad'aya ta zuba mishi ido tana jiran k'arin bayani dan bata fahinci komai ba. "Yasmeen wai Hydar d'in ya tafi Abuja jiya a gida ma yakwana Amman zuwa anjima ze kunna wayoyinshi yanzu wai yana baccine,dan haka ki kwantar da hankalinki yana cikin k'oshin lafiya". K'irjin Yasmeen ne yamata nauyi sabida azababen kishi,sallama tayiwa Abban ta wuce gidansu d'aki tashige ta fad'a kan gado tana kuka,wato ashe jiya da gaske yake mata akan tazo su tafi Amman tak'i binshi,shine kuma dan wulak'anci ya rufe wayoyinshi sabida yana tare da matarsa,ranta ne yaci gaba da b'aci zuciyarta na ayyana mata abubuwa daga k'arshe wata shawarar ta d'auka da zuciyarta ta bata.
.
Mikewa tayi tashiga wanka bayan tafito tayi kwalliya Ta shirya cikin doguwar riga bak'a irin na saudiyyarnan da ake cewa umbrella,nad'e kanta tayi acikin gyalen rigar tasa farin takalmi da farar jaka tafito ta leka d'akin Ummanta tamata sallama akan zataje gidansu Hydar ne,adawo Lafiya Umman tamata sannan tasa kai tafice a gidan. Kai tsaye Abuja junction taje ta d'auki drop d'in mota ita kad'ai zuwa Abuja, da la'asar ta isa k'ofar gidan ta sallami driver ita kuma tashige gidan,kai tsaye falon gidan ta nufa tako yi sa'a a bud'e yake, murd'a k'ofar tayi ta shige,ba kowa a falon dan haka da sauri ta haura sama inda d'akinta yake,hamdala tayi ganin key ajikin k'ofar dan haka bud'ewa tayi a hankali tashige d'akin tamaida k'ofar ta rufe. Alokacin Hydar da Khairat sun shiga wanka shiyasa basuji shigowarta ba,yara kuma suna makaranta Iman kuma taje gidansu friend d'inta tana birthday. Yasmeen tana shiga toilet ta shige tayi wanka sannan ta dawo ta bud'e akwatin lefenta ta zab'o wasu riga da wando tasaka,rigar hannu d'aya gareta yayinda ko cibiyarta bata rufeba, shikuma wandon irin jeans d'innanne dake tsayawa Dede k'asan mazaune,wandon ash color rigar bak'a, tana gama saka kayan gaban mirror taje ta tsara kwalliya tasaki gashinta yasauka har gadon bayanta,k'arewa kanta kallo tayi tasaki wani killer smile sabida ganin yadda hips d'inta suke awaje abun gwanin burgewa,wani takalmi tasaka bak'i me tsini wow abun se wanda yagani turaruka kalakala tagama feshe jikinta dasu. Sannan tasamu gefen kujera ta zauna waya taciro takira Fatima bayan sungaisa ne take sanar mata abinda ke faruwa. Dariya Fatima tayi sannan tace, "Yasmeen baki da dama wlh yanzu shine kika gudu gidan mijinki ba sallama dan kishi nacinki? nide ba ruwana wlh kyayiwa Umma bayanin da kanki". Magiya Yasmeen taringa mata akan tacewa Umma Hydar ne yad'auko ta dakyar Fatima Ta amince sukayi sallama. Tananan zaune taji motsin fitowar su Hydar, ta window ta leka ilai kuwa sune rungume da juna sunnufi k'asa,sakin labulen tayi k'irjinta na bugawa da k'arfi. Hydar da Khairat kuwa abinci sukaci suka dawo falo suna wasanninsu,khairat k'in sanarwa Hydar sak'on Abba tayi dan tagama gano Yasmeen ce take nemannasa, hasalima itace ta kulle masa wayoyin dan kar Yasmeen ta kirashi. Suna tsaka da y'ar jefawa junansu fulo suka fara jiyo sautin takalmanta tana sakkowa,tsorone ya kamasu dan sunsan Bakowa a gidan sesu kad'ai,cigaba da sakkowa take tana tafe tana kad'a k'ugu hips d'inta se rawa suke tana taunar cingum a bakinta har tagama sakkowa. wohoho duniya. Khairat sanda tayi arba da Yasmeen kusan fad'uwa tayi, dan tsananin firgitar da tayi da irin had'uwar da Yasmeen tayi,cije baki tayi ta ce aranta"why always am looser?,why?". .
.
* Yasmeen cigaba da tahowa take cikin takunta me d'aukar hankali,shiko Hydar suman tsaye yayi don tunda yake da Yasmeen bata tab'a yin dressing irin wannan ba, ba ma hakaba tunani yake ta yadda akayi tazo nan bayan yasan tana Kaduna. Yasmeen ko Hydar ta nufa tana tafiya tana kashe shi da murmushi,tana zuwa rungumeshi tayi ta manna masa kiss a kumatu,sannan tasak'ala hannayenta akan kafad'arshi bayan ta kamo nashi hannayen ta d'ora akan k'ugunta, cikin shagwab'a ta fara magana. "Haba my love shine tunda muka dawo baka nemeniba? tun jiya bangankaba se yanzu to yakake?".ta fad'i gami da k'ara rungumeshi tana kukan shagwab'a. Hydar tsintar bakinshi yayi da cewa, "am sorry princess baccine yad'aukeni kinsan nagaji". Khairat da gudu ta haura sama tana kukan takaici wato dama ashe tare ma suka taho amman dan munafunci irin na namiji be sanar da ita ba,wannan wacce irin masiface Hydar ya had'ata kishi da ita?. Yasmeen ko tana ganin Khairat ta bar gurin tasaki murmushi alamar nasara,kwace jikinta tayi ajikin Hydar d'in takoma d'akinta, da sauri Hydar yabita abaya kamar wani bindi. Tana shiga d'akinta tasamishi kuka,gabad'aya rud'ewa yayi yarasa yadda zeyi kamota yake tana kwacewa,tana cigaba da kukannata. "Haba my baby meyasa kikeson d'agamin hankaline?kinsanfa banason kukanki, Amman seyi kikeyi pls ya isa haka kiyi shuru". Nanfa yashiga rarrashinta dakyar tayi shuru sannan tace. "Shine kataho kabarni ko?". "Ay nace kitaho mutafi kika k'i to yazanyi dake Baby?". "Ni nad'auka da wasa kakemin ashe da gaskene, se yau naita kiran wayarka akashe har Abba naje na fad'awa yakira Khairat shine tace wai kana bacci ka kulle wayane,niko danaji haka shine nace to bari inzo In tayaka baccin". Ta k'arasa zancan tana dariya. Shima dariyar yayi sabida abunnasu Khairat da Yasmeen dariya yabashi wato Khairat ta rufe waya dan kar Yasmeen takirashi sega Yasmeen tazo da kanta itama Ta rama lalle shi d'an gatane. "To baby yanzu komai ya wuce kinjiko? Anjima inada magana daku after dinner".
.
"To my love but yanzu yunwa nakeji,kuma ni ice cream nakeson sha so kazo muje ka kaini nasha".ta fad'i cike da kissa tana wani jujjuya mazaunai. "OK to yi sauri kishirya kifito muje bari naje nama Khairat magana ko zata je". Ranta besoba Amman seta share tace "To". Fita yayi yanufi d'akin Khairat kuka yasameta tanayi da sauri yakamota yana tambayarta meyasameta, cikin masifa tafara magana bayan ta kwace jikinta daga nashi. "Wlh kayi asara Hydar,menene ribar munafuntata dakayi?ashe tare da Yasmeen kuka taho Amman ka b'oyemin? wlh kaci gaba, Allah na kallonka nasan kuma baze barkaba". Shareta yayi dukda maganganun sunyimasa zafi amman yadaure yace mata. "Kizo muje musha ice cream inzakije kitashi kishirya yanzu". "Babu inda zanje tsohon munafuki kawai kaficemin a d'aki". Ba musu yajuya yafice lokacin Yasmeen tuni ta shirya Danhaka hannunta yakama suka fice a gidan se huci yake alamar ranshi ab'ace yake. Yasmeen cikin kissa, takwantar da murya tace. "Yanzu dannace ka kaini shan ice cream shine kake wannan fushin? Tunda ranka bayaso mukoma gida nafasa zuwa".ta fad'i hakane dan tanason gano meyasashi b'acin rai. "Badake bane baby,nida Khairat ne, dan kawai kinyi wannan maganar ta d'azu shine yanzu danaje akan tazo mutafi karkiji zagin datamin".mitssu yayi tsaki. Killer smile ta saki alamar buk'ata tabiya, dama dantaji ne yasa tayi hakan kuma gashi tajin. Amman afili ruk'o hannunshi tayi tana dariya tace. "Kayi hak'uri my love komai lokacine inya wuce shikenan, pls amata Afuwa",har wani fari take da ido Wanda ya tilastawa Hydar cewa. "Bakomai baby yawuce". Sun isa gurin shan ice cream d'in suka siya, Amman Yasmeen cewa tayi sede su zauna acan susha ayko hakan akayi dan basu shigo gidaba se magrib. Khairat suka samu a falo ita da Iman, tana ganinsu tare wani takaicinne yasake kamata,itako Iman da gudu taje ta rungume Yasmeen tana murnar ganinta, d'aki Yasmeen taja Iman. Iman naganin sun nufi d'akin Amaryar Daddynta taja burki tace. "Ke baki da kai ne? nanfa d'akin Amaryar Daddyne". murmushi Yasmeen tayi sannan takamo Iman suka k'arasa shigewa d'akin. Seda suka shiga Yasmeen ta juyo tabata amsa da cewa. "To ay nice Amaryar Daddyn,wacce ya Aura". Ba idoba hatta hanci da baki seda Iman ta zarosu. muje zuwa.
0 comments:
Post a Comment