INA ZAN GANSHI Part 02
INA ZAN GANSHI Part 02 . Daidai inda rumfar Baba ya tsaya duk suka sauko yahau agazamai sauk'e kwandon. Batul kuwa bata jira komai ba tayi gaba da azama. "ke yazaki gudu baki bani kudi ba ? Mamuda ya fadi ayayinda yake kokarin dire kwando hannunsa, bata juyowa ba balle ta tanka banda saurin da takeyi, nisawa Baba yayi yace "ya'ta ce, zan biya gabadaya" Sunne kai yayi, kunya Baba yaji ya lulub'esa, inda ya biyemata yaukam da girma ya fad'i, taimakon Baba yayi da wanke tumatir sannan ya tayasa kaso, albarka sosai baba ya shimai, dukda ba wata doguwar hira sukayi ba amma tsohon ya kwanta mai arai, yana shirin tafiya Husaini ya k'araso gurin ya gaida sa aladabce, ciro dari takwas Baba yayi ya mikamai, fir yaki karba, ba yadda baba baiyi ba, ganin yaki karban halal dinsa yasa baba yace Husaini ya kaisa gida yaci abinci kanan ya wuce, dukda Mamuda baiso hakan ba amma wata xuciyar ta tursasa mai son xuwa gidan. Hassan tsaye gindin rijiyawa yana wanki, sai yusuf dake zaune daga gefe yana homework, Hajjo ta fita mak'ota barkan haihuwa, Sallama sukayi Hassan ya amsa suka karaso ciki ya gaida shi, "Batula fito ki sawa bak'on Baba abinci" Husaini ya fada daidai tsetin dakin, kayan jikinta take ragewa tasanya wani kod'adda tshirt da zani, tana jinsa tayi banza banda kokarin bude ostrich ledan ta da take, sake maimatawa yayi sannan ta amsa mai, "Batula yafita daga bakinka kafin na fito na wanke ka da mari" "Tofah, Manya na magana" Hassan ya fada yana dariya, harara Husaini yakaima, ya kalli Mamuda yace kayi hakuri bara na zubo ma" tabarma ya shimfada mai sanan ya zubomai dambun hatsi da Hajjo tayi, murmushi Mamuda yayi hade damai godiya yahau cin abinci da tunda uwarsa ta haifesa bai taba gamo dashi ba, haka dai ya daure yana cusawa. Fitowa tayi daga dakin rike da ledar tana shewa, batama lura dashi ba tadau kujerar tsugunno ta zauna tsakaiyar gidan, "yehoo ku fito yau party zamu.." Ido hudu sukayi ta kasa ida maganar, sai kuma ta dauke kai kaman bata sanshi ba gudun kar yayi mata magana su Hassan su dauka ko saurayinta na. "Party nami" Hassan ya tambaya. Ta gefe ido ta kalli Mamuda sanna tace "kayan dadi sabon saurayi na ya tsiya min, idan kunaso na baku zakamin wanki, shi kuma husaini yamin guga, auta kuma ya gogemin takalmi" ta karashe maganar tana kallo yusuf da tuni yawu ya tsinke mai, atake Hassan ya yadda ta mika mai burger ya karba yana santi, yusuf kuma ice cream aka bashi banda husaini daya hada rai bayaso. Hassan yace "wai waye saurayin nan naki, yana zuwa nan ? Fari tayi da ido, "mai kudi ne ba lailai ne kasan shiba, kana jin labari wani Rmd, most influential family a garin nan" Yace "gaskia bansan shiba, halan shi ne saurayin naki ? "Eh fah shine, very soon xai turo gaiswa". Wage baki Hassan yayi yana kallonta, yasanta sarai da karya amma wanan kam ya wuce tunaninsa, kwashewa yayi da dariya yace " uwaka karya, ubanka karya, Batula kinayi ina jin dadi kina bari ina jin haushi, ina mai kudi ina talaka irinki, dan Allah ki rage ta gobe" Kowa gurin saida ya kwashe da dariyar abunda Hassan yace, Mamuda kam harda rike ciki yana darawa, yarinya ga kyau amma ba kyau halin, saidai yadda take karya in a classy way ke kara bashi dariya. Akule ta mike tsaye, "banxaye sai kuyi tayi dai, yan bakin ciki" fuu ta wuce daki da kunin rai, tana jiyosu suna kara darawa. Mikewa mamuda yayi yamasu sallama ya fice dan kuwa idan ya xauna yana iya amayo kayan cikinsa, gurin baba ya nufa yamai godiya samlnna ya wuce. **** A firgice ta farka tana karewa dankareran palon kallo, hamdala tayi da Allah yasa mafarki tayi ba dagaske bane da yau hankalin ta tashi xaiyi idan My boy ya gano akwai boyayyan al'amari da take boye mai sama da shekaru talatin. Altine ta kwalla wa kira ta kawo mata fresh milk tasha ta shingide cikin kujerar tana kokarin kawar da rayuwar past dinta dake neman dawo mata sabon fill ababin rayuwarta na yanxu. . Sallama sa ce ta katse mata tunani, ta amsa cikin boye damuwar ta, karaso wa yayi kusa gareta, "Mom are you alright, naga your face is pale" Murmushin dabai kai zuci ba ta sakar mai, "am, good, ya yau din ? "Lapia kalau, i really enjoy it" ya fadi yana murmushi, itama murmusawa tayi cike dajin dadin ganinsa cikin farin ciki, bisa cinyarta ya ajiye kansa tasa hannu tana kwantar mai da lausasan gashin kansa, tace "Abdulrasheed yau kasani farin ciki, alway b happy kaji? "I'll Mom" ya fadi yana kara fadada fara'arshi. Wayarsa ya laluba aljihu ya ciro yayi daillng no din Mardiyya, zaune take tsakiyar gadonta Tana tofa addu'ar bacci taga call dinsa, tsoro da mamakine ya kamata by diz tym ace ya kirata, jiki sanyaye ta dauka, tayi shuru. Murya kasa kasa Yace "Mardiyya hope dai ban tashe kiba ? Dadi taji yadda ya kwantar da murya tace, "banyi bacci ba, ya daran ? "Cool' Shuru tayi tana juyo heart beat dinsa, nisawa yayi yace "mi kika dauka a office dina ? Gabanta ne ya fadi itakam bata dau komai ba banda daya daga cikim hanky dinsa data zara amma kuma bata san inda ta ajiye ba, tace "ban dauki komai ba" "Are you sure ? Tsoron Allah ne ya shigeta, karya itace abunda bata iyaba, "am sorry Mr rasheed na dauki hanky dinka without ur consent" Ajiya zuciya ya sauke, "ina hanky din yake" Cikin rawar murya kaman zatayi kuka tace "i lost it" Abinda yake sonji kenan, katse call din yayi, aransa yana tunatin where on earth ita kuma wacan tasamu hanky dinsa, Mom ce ta katse mai tunani da cewa "my boy nasan kana santa, ka aureta i promise you won't regret it" Kallon rashin fahimta ya daga kai yay mata, tace "dont be silly, who else idan ba Mardiyya ba" Yake kawai yayi ya maida kansa, zuciyar na bijiromai abubuwa da dama. **** Yau da wuri taje lec ta dawo kasancewar ruwa da akayi ta makawa yasanya yawanci lecturers basu zoba, tana ganinsa tare da Baba akaramin zauren gidan ta bata fuska, shishigin yafara isarta tun ranar daya sauke su akullum sai yaje teburin Baba hira, yanxu kam tamkar yaron baba haka ya zama duk wani aike da dauko kayan miya gurin tsari shi Baba ke aika, takai ma yanxu sun saba da Hajjo, har wani kwanan abincin daban take ajiye mai. Baba sannu" ta fadi cikin hade rai, dama akulle ta dawo da haushi Billy yau data tsitsaye ta akan deceiving dinsu take, fada sosai sukayi saida Minal tasa bakin akan lailai gobe saita kaisu gidan su cousin dinta Rmd, karfin hali kawai tayi ta amsa masu da naam, ranta duk ajagule ta rasa mafita. . Kallon ta Baba yayi, yanayinta ya nuna ba lapia ba, yace "fatima mike damunki ? Kuka ta fashe dashi "Baba nikam na gaji da talaunci nan, wai yaushe zakayi kudine, miyasa ma na fado cikin zuria ka" sosai tafashe da mugun kuka, kollanta Baba kadai yayi yana murmushi bayau mace tasaba cin zarafin saba, saidai kalaman fatima ba karamin fama mai ciwo daya dade da samun waraka azuciyar saba. Ran mamuda kam ya gama bacci hannu ya daga da niyyan sharara mata mari, baba yarike hannusa "dukan mace bai kamace kama, karka kuskura" Acewar Baba. Harara Batul ta kaimai ta ruga gida aguje, baba ya rike hannusa suka fice zuciyarsa na tafarfasa. Gam Hajjo ta capke ta data shigo, dan kuwa duk abunda tace taji ta, kaman an aikota tahau Batul da dukam tsiya, banda ihu da kuka ba abunda take, "Kafin ki kashe ubanki ni xam kashe ki" hajjo ke fadi cikin kunin rai tana mai kara kai mata naushi, saida tayi mata lillis sanan ta barta tana fadin "yar banxa yarinya, kasheki xanyi na huta da bakin cikin ki, nagode wa Allah daya azurtani da kannanki dayau kin kasheni abanza" Kuka sosai Batul take, tana jawa bawan Allah mamuda Allah ya isa, aganinta tunda yaxo hajjo ke kirbanta, dan kuwa rannan abinci taki zubamai hajjo ta mata lilis yauma ba, wani mugun tsanan shi take ji aranta, ayyada zuciyarta ke tafasa inda zataga Rmd binshi kawai zatayi tabar masu gidan, dan kuwa shine kadai gatan ta yanxu. "Oh ni fatima ina Xan Ganshi,.." Ta karasa magana cikin matsananci kuka, atunanin ta a zuciya ta fadi not knowing afili tafada, jim muryar Hajjo tayi akanta rike da ludayin miya, tana cewa , idan na fasa maki baki zaki ganshi da kyau" Ba shiri ta mike da azama tayi cikin bayi da gudu tana kuka. . K'ashe gari bataje makaranta ba, fuskarta gabad'aya kumbure tsabar kuka, tana jiyo Hajjo da k'annan ta a tsakar gida suna hira taki fitowa, ga uban yunwa da takeji tun abinci jiya bata latsawa bakinta komai ba har ila yau da sakaliya tayi. Wayarta dake kashe ta kunna ta kira wani saurayinta shehu da tuni ta dade da jefasa a k'wandon shara, matashi ne irin masu son aci duniya, Baban sa mai kudi ne sosai, yana son Batul saidai son jiki irin nasa yasa Batul bata son basa fuska, bugu daya ya dauka tamkar jira yake, kirarin daya saba mata yafara tuni ta dagatar dashi, tacemai lailai yaxo bayan magrib akwai muhimmaciyar magana da takeson yi dashi, sannan kuma wen coming yaxo mata kayan dadi, naam yayi da bukatun ta cike da jin dadin kota sauya shawara game dashi. Kaste wayan tayi taja jiki zuwa bangon dakin ta shingid'e. Baba ke zaune daga gefen teburin kayan miyansa yana alwala, Mamuda ya karaso da Marwan sa ya faka gefe ya fito suka kara gaisawa da Baba, bai jima da bari gurin ba. dayar butar dake cike da ruwa ya janyo yayi alwara sannan suka mike zuwa masallaci dake gaba dasu kadan. . Sadaf ta fito daga dakin rike da siliwas dinta a hannu, Hajjo ke sallah tsarkar gidan, ta tako ahankali ta bayanta tayi waje da azama, ajiyar zuciya ta sauke ganin babu kowa rumfar Baba, waigawa tayi ba alamun motar Shehu sai ganinsa tayi da kafarsa yana tunkaro ta hannusa rike da bakar leda. "Miye haka zaka zomin da kafa, ina motar" ta fadi tana karasawa garesa. Dariya yayi. "Popcy na yanani daukan mota saboda reckless driving danakeyi, mashin ma naso zuwa dashi" Harara takai mai, "Allah kiyaye kazo gurina da mashin, ai aji down kenan, yanzu dai miye a ledar ? Daf da ita ya matso, yanai kai mata wani shu'umin kallo, yace "Tukun nadai, , nifa duk kin hargitsa min kwakwalla, wace magana zaki gayamin ? Ja da baya tayi kadan tanai mai kallon bansan haka sannan tace "Shehu temako zakamin, gobe xan kawo frnds dina gidanku su kanga amatsayin wani cousin dina" Kallon rashin fahimta yayi mata, waye cousin dinki, ya sunan shi "I dont know, nasan dai Rmd ake cemai, i want you to act like him idan mukazo" Galala yake kallon ta, baiyi mamaki abunda takeso yayi ba, dan kuwa yasan halinta sarai, farkon haduwan su ba yadda bata jifan shi da karya, daya gano gidansu ne yasata saduda ta koma real Batulan ta, yanxu kuma ba mamaki wata bomb take shirin ajiyewa. "Okay ba matsala, saikun zo din, amma nikuma mai zan samu in return, kinsan dai gwamnati ta hana aikin banza" cikin zolaya ya fadi yana kai hannu zai rikota, batare da ya kai hannusa ba ta warce ledar zatayi gaba, saurin shawon gabanta yayi yana fadin "Batula babu kodan kiss" kiris yarage yakai mata kiss tayi saurin kawar da kanta gefe sukayi ido hudu da Baba da Mamuda dake tsaye suna kallonsu. Rai bace Baba nufeta yana cewa "mia kikeyi da yaron nan, ban hanaki haduwa dashi ba" Jiki na rawa tace "dama assignment zaimin" "karya kike" Baba yafadi yana kallon shehu da tuni yasha jinin jikinsa, "uban mi ya kawo nan ? Shehu kam be boye komai ba ya zayyane wa Baba abunda ya kawo shi, salati baba ya saki, wana wace irin yarinyace, shi Rmb yake kowa, wayene, ina kika sanshi ? Tsuru tayi tana kokarin boye ledar abayanta, warcewa baba yayi ya bude yaga bankararriya kazar yahuza, innalilahi kadai yake ambata ya mikawa shehu leda hade da korarsa, fashewa da kuka tayi ta ruga cikin gida, Mamuda kam kasa magana yayi, kila idan aka duba ransa yafi na Baba bacci, tir kawai yake da hali irin na Batula, wani irin tsanar ta ke sokanshi a zuciya. Kwafa Baba yayi yace "yarinyan nan ga karya da kwadayi, tsoro na daya karta fara sata da bin maza" Nisawa Mamuda yayi yace, "ayi hakuri Baba, kuruciya ce zata gyara nan gaba" "A'a dai mamuda, i dont tink fatima zata gyaru, aurar da ita xanyi gobe goban nan kafin tajaza min abun kunya, Yekuwa xa'ayi a masallaci maiso na aura masa" "Baba ayi haka kuwa, kasan fah Batula mai kudi tasa ran aura kar talaka irina ya ansan tayin" Kur Baba yayi yana kallonsa sannan yace "Mamuda na baka ita, dan Allah karka ce a'a kaine daidai da ita ba wasu can maisu kudi datasa agaba ba" Gaban Mamuda ne ya fadi, shikam mai xaiyi da yarinyar nan, shuru yayi baice uffan ba banda nauyin da kimar tsohon da yake gani. . "Nasan baka sonta, dan Allah ka amsheta amatsayin Sadaqa na baka ita" baba ya fadi cikin murya kaman xaiyi kuka. Kasa cewa Uffan Mamuda yayi har suka taka zuwa inda rumfar baba, Marwan sa yanufa ya zauna zaija ya kalli baba da shima kallonsa yake, jiki sanyaye yace "sai da safe" Baba yace "indai ka karbi sadaqa ta gobe xan ganka karfe biyu agurin nan da shirin daurin aure, bai iya amsawa ba banda jan marwan da yayi ya wuce, jan marwan yake amma gabadaya hakalinsa ba ya jikinsa, xancesu da baba kemai yawo akai, jin awani wawa horn abayansa yasa shi dawowa hayyacinsa, parking yayi gefen hanya hade da fiddo wayarsa, dannawa yayi ya kira Daddy Malam, magana daya biyu sukayi sannan ya katse. Bayan mituna goma da parking dinsa wata arniyar Jeep ta karaso gurin, da azama Daddy malam da wani suka fito daga ciki, gaida Mamuda sukayi, bai amsaba ya fito ya shiga cikin jeep din, dayan da suke tare yaja Marwan yayi gaba, Daddy Malam na gefe shike driving suka isa wani karamin gida mai shegen kyau. Parking yayi suka fito atare, Daddy malam yace "Mamuda ne ko Rasheed" ya karasa maganar cikin zolaya. Fuskar daure yace "Rasheed ne" Dariya Dddy malam yayi, "daga gani nagane wanan Rasheed ne, irin daure fuska haka, watx wrong ? Ajiya zuciya Rasheed ya sauke, baice komai ba suka karasa cikin palon, zama yayi kan kujera, Daddy malam ya shiga toilet ya dauko spirit da detol ya zauna gefensa, yace "tym to get back to real Rasheed Mohammad Deeni" ya fadi yana mika mai cotton wool. Amsa yayi, ya cire kodaddiyar rigar dake jikinsa yahau goge ko ina na jikinsa dake shafe da bakin mai, har kafafusa saida ya kalkale, artificial mustache dake fuskar sa duk saida ya cire sannan ya shiga toilet yayi wanka ya fito fas ainihun Mr Rasheed dinsa, red tshirt da blue jean ya sanya ya fito palon. Bai boyewa Daddy malam komai game da Batul da sadaqan ta da baba ya bashi. Sosai Daddy malam ya bushe da dariya, yace "ka yadda kawai tunda tana sonka, kuma kai take burin aure" Nisa wa Rasheed yayi,yacd "Rmd mai kudin takeso ba Mamuda talaka ba, nifah na mugun tsanar ta ba kadan, i cnt tolerate her, nayi disguise din kaina ne just to find true love ba wata gold digger can ba" "Ni kuma i tink you should marry her, just to teach her a lesson, irin su they have to experience defeats kafin su shiga taitayin su" Acewar daddy Malam. Rasheed yace "Hakane kuma, ka kawo point, i will personally deal with her to the extend idan taji mai sunan Rmd bazata tayi gigin cewa tasan shiba, matsala ta Mom ce, i dont tink she will accept" "Karka damu, i have an idea," Daddy malam ya fada, matsawa kusa garesa yayi ya gayamani wasu magana dani kaina banji ba. kai Rasheed ya kada yace "are you sure zata yadda? Daddy Malam yace"Bata da matsala, i'll talk to her" Sun jima suna tattauna nawa daga bisani kuma Rasheed ya mike ya wuce gida. Kuka Batul tayita tsugawa a tsakar gida har Baba ya shigo gidan, takalmin kafarsa ya cira yana fadin kina tashi ana ko saina mauje ki" huf ta mike ta shige daki. Hajjo da saura yaran dake zauna suna cin abincin a faratin daya ko ajikin su, yi sukai ma tamkar bata wajan. "Mallam sannu da zuwa" Hajjo ta fadi hade da mikewa tsaye, yauwa Baba ya amsa mata ya kirata suka shiga daki, xayyane mata komai yayi da hukuncin daya yanke, sosai taji dadi danta jima tana neman yadda zata raba hanya da Batula sai gashi yau an badata sadaqa asauwake, fatan ta daya kar Mamuda yaki amsa, kodama yaki amsa saidai anemo ko waye alaka mai ita. **** Yau friday tun Karfe goma na safe Batul ta fito da shirin fita makaranta, dakin Hajjo ta leka "na tafi" ta fadi fuska daure ko gaisuwa babu. Kallon banza Hajjo takai mata, tace "babu inda zaki, ki koma daki ki hada kayanyi, yau zaki barmin gida" "Ina da test ne, kuma ai nan gidan mune" Harara hajjo takai mata "Ayyo ashe dai matsiyacin gidan nan nakune bansani ba, toh baki da gado a gidan nan tuni Babanku yayi sadaqa dake, anjima kadan mijin daya temaka ya kwashe ki zai dauke ki ku tafi" Ware idanu batul tayi tanai mata kallon rashin fahimta, " kina bace min daga nan ko saina sharareki da mari" Hajjo ta fada cikin karaji da zare ido. Tsum tsum Batul tayi ta koma daki ta cire kayan jikinta, tujajjiyar tshirt na tun lokacin siyasar Baba buhari ta APC ta sanya jikinta da tsohon zani ta fito gindin rijiya ta zauna hade da tagumi, ba xancen da Hajjo tayi ke damun taba, asalima bata gane inda maganar ta dosa ba dan kuwa babu yadda xaai ace an mata aure bada sanin taba. yunwa sosai takeji baa mata tayin abinci ba, gashi Hassan da Husaini basa nan, yusuf dake daki tare da hajjo ba bari zatai ta aike saba, ganin yunwa xai halakata yasa tahau hada wutan gwarwashi dan dama koko. . Fitowar su lecture suka shiga mota zasu wuce gida, Minal tace "Allah yasa dai Fatima lapia, tun jiya batazo skull ba, ga wayarta kashe" Kwafa billy tayi tace, "bana gayamiki ba, fatima makaryaciya ce, na tabbata ramin tane ya kure shiya hana ta zuwa". "Billy kar kice haka, ki mata uxuri, am sure zuwa monday zatazo ta kaimu gidan Rmd" Tsaki billy taja, "wlh ta raina miki yawo, nikam muje gurin Baba mai kayan miya na siyi Salad. Haka dai kika ce" Minal ta fadi hade dajan motar suka nufi rumfar baba, baya gurin sai Hassan dake zaune yana jiremai, ganin su Minal sun tsaya yasa shi mikewa hade da gaidasu, amsawa sukayi, Billy ta siya salad na 300 masu kyau, harza su wuce Minal tace "kyakyawan yaro, billy baki ga kaman su da Fatima ba" karaf a kunna Hassan, kallosu yayi ya kara fadada fara'arsa. Billy tace "aikuwa suna kama, amma bazaki hada ba, Fatima masu kudi ina ita ina hada iri da masu saida kayan miya". Dariya sosai Hassan ya kece dashi, jikinsa kawai ya gayamai fatima yayarsa suke nufi, yace "aikuwa inada yaya Fatima, kamar mu daya da ita" "Haba" suka fadi atare, ina take "Ga gidan mu can, kuje tana ciki" nuna masu gidan yayi da yatsa. Billy tace "bana gayamaki ba, yarinyar nan makaryaciya ce, muje mu gani" "Kidaina saurin concluding muje dai" Minal ta fadi hade daja motan zuwa gaban gidan, sauka sukayi suka karasa gaban kofar gidan mai langalanga, babu ko sallama Billy tayi gaba ta afka cikin gidan. Fatima na zaune gidin rijiya tana kurban koko a kwanan silba, tana ganinsu ta firgita, atsorace take kallon yadda suke mata kallon mamaki. Sabule dankwalin kanta tayi tace "Minal sannu ku, kuma kunzo yin kitson ne ? Kai kawai suka girgiza alaman a'a, tacigaba "gidan mu nacan baya, kitso nazoyi agidan nan" Hajjo dake kokarin kama ruwa abayi kasawa tayi jin karyar da yarta take k'wandarawa, fitowa tayi bayan tayi adduaa fita bayi, kallon su Minal tayi da suma kallan ta suke, sannan ta kalli Batul datai tsuro tsuro da ido, tace "Ba shakka gidan kitso kike zo, saidai bansani ba ko uwarkice makitsiyar.... . Shuru Batul tayi tana sosa gashin k'eyarta cike da kunya, ji take tamkar ta mike ta fad'a rijiyar dake fuskantar ta, kayan jikinta ma ya isa susan karya take ba gidan kitso tazo ba. Murmushin dabai kai zuci ba Hajjo ta sakar masu sannan tace "yammata mungode da ziyara, saidai bamu dafa komai ba balle mu baku gashi yaune daurin auran kawar taku" Cike da mamaki su ukun suka zaro idanu suna kallon Hajjo, hardai Batul da firgici ya bayyana fuskarta, atare Minal da Billy sukace "Auran gaske ? Kallon baku da hankali Hajjo takai masu, ina aka tab'ayin auran karya koda yake sunan Batul na biyu karya dole su watso mata tambayar, bata amsa suba ta juya ta shige daki. . kallon tir da hali Billy ta watsa mata, "amma dai kinji kunya fatima, haihuwar irinki asara ce, banza, makaryaciya". Haushi ne ya turnuk'e Batul, cikin borin kunya ta mike suka hau cece kuce, kasa cewa Uffan Minal tayi banda mamakin hali irin na batul da take, sau da dama ana bada labarin masu halinta bata taba yadda ba yau sai gashi ya faru akanta. Dakyar Minal taja Billy suka fice daga gidan, Hajjo dake jinsu bata lek'o ba, saidai asarar haihuwa da Billy ta fadi yay mugun mata ciwo, ita haihuwa k'yautar Allah ce komin ya yaro yake bai kamata ka dangan tashi da asara ko tsiya ba saidai ka bishi da fatan shiriya idan ya kauce hanya, tanaji da Batula har ranta halinta kadai yasa batason tsakan mata fuska. Saida Batul ta tabbatar sunja mota sanna ta fad'a dakin hajjo, ba tambayar duniya daba tai mata akan gaskiar auren, banxa kadai Hajjo tai da ita tana mai cigaba da hajun gabanta. Farar yadi wace ake kira da mamar ya sanya da hula buluwa, fuskar sa fayyus daka ganshi kasan baya cikin farin ciki, daure wa kawai yake, nan suka hadu da Baba a bakin massallaci, gaidasa yayi alabadce, Baba ya amsa, ganin yanayin sa baba yace "Mamuda karka damu, idan baka da kudin sadakin nizan biya maka" Yaken dole ya saki yace "Baba ba matsla, akwai kudin". "Madalla, Allah yayi ma Albarka" Amin",ya amsa suka karasa ciki, bayan sun gabatar da Sallah aka dauran auran AbdulRasheed Muhammad Deeni da Fatima Muhammad Yero akan sadaki duba goma kacal. Bayan sun fito wani mugun sanyi jikin sa yayi, wani abun mamaki shine yadda Baba bai tambaye sa akasari suna daya bambamta ba, sai mai cema dayayi "Mamuda aure zaman hakuri ne, dan Allah banda niba kayi hakuri da yarinyan nan" "Insha Allah" kadai ya iya furta mai, Babu wanda yace uffan cikinsu har suka karasa gida, ta bangaran Baba bai kawo komai aransa ba game da sunan, aganinsa Mamuda da ake kiransa dashi lakabine na gidansu. Tsaye yayi waje Baba ya shigo gidan, turus yayi ganin Batula tsaye bakin kofar dakin hajjo da kodadan kayan jikinta, atunanin sa batayi wanka ba. "dauko kayanki muje" Baba ya fadi. . Turo baki tayi "babu inda zani.." bata rufe baki ba taji saukar wayan rediyon bayanta, "wuce dan ubanki ki dauko kayanki" Hajjo tace tana shirin kara lafta mata. Kaman zatayi kuka tace "banyi wanki ba, duk sunyi datti" "Haka kuwa zaki kwashe su, idan kinje can kya wanke abunki" K'in motsawa Batul tayi, saida taga Hajjo dagaske take sannan ta ruga daki tana kuka, kayanta dake cikin tsohuwar ghana must go ta daukA ta fito, hannu Baba yasa ya karbe suka fice waje Hajjo na mata fatan zaman lafiya. Kuka sosai Batul take bata gama girgiza ba saida taga Baba ya jefa ganar cikin Napep ga kuma Mamuda agaba yana shirin ja, harara ta watsa ma cike da tsana, cikin muryar kuka tace "Baba babu mota ne ? "Kedai shiga muje" baba ya fadi. Rai bace ta shiga, sannan ya shiga ya zauna kusa da d Ita. Kuka take ba k'agauta, ba auran miji ne ke b'ata mata rai ba sai cikin keke da za'a kaita, wato ma mijin matsiyaci ne, uwa uba yadda tayi planing ma kanta big wedding shine Baba da Hajjo suka k'askantar da ita, irin su Dinner, mother's eve, fulani day event dayawa datasa buri sun wuce ta, honeymoon da ake fita waje duk bazata samu ba, Allah ya isa kawai take ma dan iskan daya amshi Sadaqan ta kuma tadau alwashin ko waye sai yayi dana sanin amsarta. Tudun wada layin yan kosai ne unguwar da Rasheed yayi parking Marwan, nan take ta kara fashewa da kuka da ganin gidan, tasan su talakawa ne, gidansu da take rainawa yafi wanan fasali nesa ba kusa ba, karamin gidane wanda rabinsa da salansa mai tsatsa aka kewaye shi, unguwar ma gabadaya ba fasali irin ghetto area ne da gwamnati batasan da zamansa ba. Nasiha sosai Baba yayi mata sannan suka fito ya taka mata zuwa bakin kofa, yace "ki shiga kakarsa na ciki" acewar Baba. Jiki sanyaye ta cusa kai ciki tana waigowa kallon Baba, ran Rasheed adakule yake amma saida ya dara, nikaina xarah saida na dara (hhhh), Marwan Baba ya koma rasheed yaja maida sa gida. . Tsohuwar tagani zaune tana carafke adan karamin tsakar gida dako mutum 5 ya masu kadan su tsaya cikin sa, dukuna biyu ne kananu da bayi dake lungu tsakar gidan an kewaye shi da kwano, hannu Batul ta aza akai tana ihun ta shiga uku ta lalace, sai sannan tsohuwa mai Suna Inna kulu ta lura da ita, mikewa tsaye tayi tana guda "amarya ta iso yiririiii" karasawa kusa Batul tayi zata rikota, da azam Batul tayi baya tanai mata wani mugun kallo, "karki kuskura ki tabani" Galala Inna kulu tayi tana kallonta, "kaji ja'ira miye aciki danta tabaki, jikana fa kike aure" Harara takai mata, "jikanki ko matsiyaci, jifa gidan da kuke kaman akurkin kaji" Bata ankara ba sai gab taji abakinta, Inna kulu ta buga mata dutse, hannu takai gurin taga jinin, kafin tayi magana Inna ta cafke kunnata, "bamu da tsiya agidan nan, bamu ganta ba bamu santa ba kina jina ? Kara damke kunnan tayi. "Eh naji" Batul ta fadi cikin kagara, sakin kunna tayi, bata jira komai ba ta fada dayan daga cikin dakunan tana kuka, wayam dakin yake ko yar katifa babu sai tabarma a shumfud'e, ajiye Ghanar tayi bisa tabarmar ta kwanta tayi filo dashi, kuka kadai take daga bisani Bacci yayi awan gaba da ita, bayan Magrib ta walka kasancewa hutun Sallah take, jiki mace ta mike ta leko tsakar gidan, Inna tagani zaune tana can carbi, tsaki taja tace "tsohuwa yunwa nake ji" Banxa da ita Inna tayi saida ta kare hade da shafa addua sannan ta kalle tace, "ba abinci agidan, saidai kici kanki". Gyara tsayuwa Batul tayi, "Aikuwa saidai ku nemo, dan ban iya xaman yunwa ba, Hakkina ne jikanki ya ciyar ni" cike da tsiwa take magana. Murmushin dabai kai zuci ba Inna kulu ta saki sannan tace "lailai kin tabbata matar Sadak'a, daga zuwa yau sai nema hakki, anya kina barinsa ya runtsa yau ? Salamar sace ta hana Batul kai mata amsa, amsawa Inna tayi ya karaso ciki rike da bakar leda da kullin kaya. kallon sa Batul tayi tace "nagodewa Allah, nasan Baba bazai barni agidan nan ba, bara nadauko kayana" ta fada hade da komawa cikin dakin da saurinta. . Kallon juna sukayi da Inna alamun ina xancen ta ya daso. Ghanar ta dauko ta fito tana fadin "akurkin nan ba gidan zamana bane" Kallonta kawai yake bashi da niyya motsawa, tace "Mamuda muje mana kar dare yayi," Zama yayi jikin wata rashe dake guri, yace "Muje ina ? "Gida mana" ta fadi tanai mai kallon banza, duk atunanin ta Baba ya aiko a maida ta gida. Cikin ko in kula da yanayinta yace, "kin taba ganin inda amarya ta koma gidansu bayan an kaita ? Takaici ne ya cika, so take kadai subar gidan kafin jikin Inna ya dawo. Inna kam ta gama kulewa da ita, tace "miye kake boye mata, kaine Mijin nata ba kowa ba, idan bata shima albarka ba ai bata zage kaba, in banda kai ma waxai amshi Sadawar ta" Ware idanu Batula tayi jin kalaman Inna, saidai ta kasa gasgata shin mafarki take ko gaske, yama zaai ta auri Mamuda, mai yake dashi, waye ubansan, murya Inna data ciyo tana fadin mijinki ne yasa ta zabura hade da wurgi da Ghanar, ihu take tana nema agashi dan kuwa mutuwar tace kadai xai fiye mata akan taga mumunar rana irin tayau, kuka take tana fadin "Allah ya sauwake na zauna dakai, banza matsiyaci, talaka, bakauye, kashe kaina xanyi akan na zauna dakai" sambatun take kaman sabuwar mahaukaciya, kallonta kawai suke, zuciya Rasheed kaman ta fito dan haushi, kalamanta ba karamin zafi sukai ma, inda da gaske zata kashe kanta dayafi kowa farin ciki. Iya k'ulewa Inna takai, gaftareran wuka dake bisa tagar dakinta ta dauko, ta cilla daidai inda kafar Batul, atsorace taja baya dan kiris ya rage bata kwaye mata fata ba. "dan uwarki dau wukar ki kashe kanki, shegiyar yarinya, kin dauka muma sonki muke, kina mutuwa bamu da asara, keko uwarki da ubanki basu da asara, yar banxa tantiriya, gwara ki mutu mu huta" Inna ta fada cikin daga murya da tsananin bacin rai. Cikin karaji Batul tadau wukar kamar zata cakawa kanta, ganin ko ajikinsu yasata cefar da wukar, tabbas basu da asara idan ta kashe kanta balle ma wana hauka yakai ta kashe kanta tun burinta bai cika ba, danne zuciya kadai zatayi ta zauna kafin kwana biyu ta san inda dare yayi mata. Tsaki taja tadau ghanar ta koma daki, mikewa yayi yama Inna ido sannan yabita zuwa dakin, jikin bango ta rakube tana sauke ajiyar xuciya, ko fitila babu dakin sai hasken farin wata daya gauraye ta waje, ganinsa da tayi yasa ta mike tsaya hade da kaimai kallon banxa, ledar ya mika mata "ga abinci kici" Ba kunya ta amsa, ya fice. zama tayi bata lura da kullin kayansa daya ajiye ba, bude ledar tayi taga Kosai biyar da guntun biredi, tsaki taja, aranta tanai karajin tsanar Mamuda, in banda tsiya ko yar kazar amarye bai iya siya ba (ni xarah nace idan ya baki kaza, ke kuma ki bashi miye ). yunwar da takeji yasata cusawa dan dole. Hira da dariyar Inna da Rasheed keyi, tana jiyo dariyar su amma bata tantance mai suke fada ba, tashi tayi ta sakawa kofar sakata sanna ta koma tayi kwanciyar ta. Mikewa yayi ya kwakwaso yace ta bude, tayi banxa tayi dashi, saida yace ta miko mai hula cikin kayansa sannan ta lura dasu, dauka tayi ta bude kofar bata mika mai ba tayi cille dasu waje hade da rufo dakin da sakata. Bai damu ba, dan kuwa da gangan ya ijiyesu, tsince su yayi yakai dayan Dakin da Inna take ya ajiye sannan yay mata sai da safe yabar gidan. . K'ashe gari da k'arfinta ta tashi, fuskar ta dauke da murmushi dan kuwa tayi alwashin daina zubda tsad'addan hawayen ta kan matsiyacin nan, ranar kin dillanci kadai take jira. Kayan jinkinta ta cire ta dauro zanin wanka ta fito tsakar gidan, bayin ta leka taga babu ruwan balle famfo sai bukitin k"arfe marar hannu dake ajiye, tsaki taja aranta tanai tir da talauci, kofar Inna kulu ta nufa ta tsaya, babu ko gaisuwa tace "Tsohuwa xanyi wanka". Daka cikin k'uryar dakin Inna tace. . "nazo na mike ne ? Mikewa tayi hade da sunkutan redionta ta fito tana kara maimaita abunda ta fadi. Cike da tsiwa Batul ke kollanta, "ruwa zaki ban nayi wanka" Yar tsugunno dake gurin Inna ta dasa mazaunin ta akai sannan tace "ayyo ainan babu ruwa, waje zaki je akwai burtsatsan unguwa saiki dibo" Kallon rainin Batul takai mata, tayama xata fita waje diban ruwan kamar wata buduwar k'auye, agidama Hassan ke jamata ruwa a rijiya balle kuma nan daba zama taxo ba. "Ba girma na bane, saidai jikanki ya fita ya debo min" "Toh saiki jirasa yaxo" Inna ta fadi cikin ko ta kula da kallon da take mana. "Ina ya fita da safan nan" Batul ta tambaya . Banxa da ita Inna tayi, saima redio data kunna jin labaran karfe takwas. Tsayuwar mintinu ashiri Bayul tayi, Inna bata tanka taba, wanka kadai takeson yi danji dadin jikinta, ganin tsayuwar ba amfani yasan ta komai daki tasanya hijb ta fito, bokitin dake bayin ta dauka ta fice waje. Sai yanxu ta karewa unguwar kallo, jama'an cikin ta ba abun kallo akara bane, gaba da gidansu kadan butsatsan yake, mutane kusan ashirin data ganin bisa layi yasata jan mugun tsaki, itakam bada ita zaai haukar nan ba, dole nema subarta ta diba dan ita ba kalar subace. Karasawa tayi tanai ma kowa kallon wulakanci, su dinma ita suke kallo, dire bokitinta kusa da wanda tagani yana diba, jira kaidai take ya cire tasanata, yana cirewa kuwa ta sanya, murmushi tayi ya kusa cika babu wanda ya tanka ta, saima kallon ta da kadai suke, kadan ya rage ya cika, wata yarinya dake can baya ta karaso tasa hannu tayi wurgi da bokitin ruwan ya kelaye gurin. "Ke kin isa, wa kika fi gashin tsuliya anan dahar zaki raina mana wayo kizo ki ganmu alayi dan iskanci shine zakiyi babakere" yarinya mai suna Dija ke magana cikin karaji da zare idanu. Murtukewa Batul tayi, ta nunata da yatsa, "ke bakauyiya, ki kiyaye ne, kinsa dawa kike magana kuwa " "Nasani mana, da mutum nake bada dabba ba, layi kuwa sai kinbi tunda ba ubanki ya kafa famfam ba" kallon sama da kasa Dija ke mata ayayinda take maganar. Dariya yan gurin su kwashe dashi, daya dake gurin tace "kalle tafa damu da ita banga bammaci ba, sai felekan tsiya harda wani ansan dawa take magana, kaji ja'iri, mukam nan saidai kici na jaki" Ruwan ne ya cinye Batul tayi tsit, tayi underestimating dinsu, batayi expecting zasuyi magana ba yadda tayi masu kallon yan primitive society, cike da kunya tadau bokitin ta koma baya ta tsaya, dariya kuwa basu fasa ba, ignoring kadai Batul tayi har layi yaxo kanta, bisa kai ta aza ta koma gida cike da tausayin kanta. Wanka ta shiga sharp shrp ta fito, sauri take tana da lecture by 10. . Kwalliya sosai tayi cikin atamfa riga da skirt ta fito ta riske Inna hartai wanka tana zauna bisa tabarma tana shan shayi da buredi da fried kwai, mamaki karara tayi yaushe Inna ta debo ruwan waima yaushe ta kunna murhu aza ruwan zafi da soya kwai, gadai murhu babu alamun an taba, tsaye tayi kan Inna, "kudin mota, xan wuce makaranta" Cikin fara'ar Inna ta kalleta tace "mijinki zaki tambaya bani ba, kuma ai kyaci abinci kafin ki fiti ko". Kaman jiran take tace toh xan ci" wazai ga kwai da biredi ya kyale, dama yunwa takeji ba kadan. "Gashi" inna ta fadi hade da mika mata bakar leda Budewa tayi da azama, saidai abunda tagani yasata yamutse fuska, taliyar hausa ce danya da manja da kulli gishiri da yaji, "Tsohuwa miye wannan" "Abincin ki mana, dare da rana, ga murhu can ki dafa asawake, ga langar samira xan ara miki tunda baki kawo tukunya daga gidan kuba" Kuka ne ya rage Batul batai ba, daurewa kadai tayi ta ajiye ledar ba tare datace uffan ba, tunanin kawai take ta tashi ta gudu ne ko yaya, toh idan ta gudu taje ina, shi wanda take muradin so baima san da zaman taba, fuskar sama ba sani tayi ba, ance he is rich & simple, amm toh ina zata ganshi, burinta daya taga tazama matar mai kudi ba matar matsiyaci ba. Zaman kusan awa biyu tayi gurin Mamuda bai zoba, yunwa na nema illata ta, mikewa tayi tahau aza murhu, abunda bata taba yiba saidai Hajjo tayi, ba karamin wahala tasha ba sannan wutan ya kama, karamar bokiti datagani tadau ta debo ruwa ciki tahau kikirkiri din daura taliyar. Bayan ta sauke, ko tayi batama Inna ba tahau ci. Sai bayan Sallah azahar Rasheed ya shigo gidan, tana ganin sa tahau surfa masifan yaja mata bataje makaranta ba, gaisawa da Inna yayi kafin ya zaune yace mata "banda halin ciyar dake da biya miki na makaranta, hakuri xakiyi idan Allah ya hore nan gaba kyaje, rayuwa saida manaji, ina abinci na ? Ya gama soka mata kibiya azuciya, daskerwa tayi tana sauraran sa sannan tace "duk inda kudi suke dole ka nemo su, uwarka ma tayi kadan ta hanani zuwa balle kai karan kadan miya, abinci kuma ban dafa dakai ba" Kallonta kawai yake bai ce uffan ba, aransa fadi yake bakisan uwata ba dole kice haka, duk randa kika shigo hannuta zaki gane ruwan ba sa'a kwando bane. Masifa sosai da fitsara tayi tamai, wata zuciyar nace mata toh idan kinje makarata kicewa su Billy mene, ai da kunya ma, kila ma sun gama yada ta aduniya, hakura kadai zatayi tayi da batun makaratta kafin tasan abunyi nan gaba. **** Sati biyu zani bata canxa ba, halin Batul sai wanda ya karu, akullum Rasheed xaije gidan amma maganar arziki bata hadasu, iya kaci susha hira da Inna da dare ya koma gida, dadi sosai Batul takeji aganinta a kekensa yake kwana waje ita ta kame a daki, wanka da cin abinci duk bayayi agidan, atunaninta tsoronta ya hanasa sakat. Ta bangaran Inna kuwa ta rasa daga ina ake kawo mata abinci mai rai da lafiya, saida taga tanaci amma ita an barta da manja da yaji, ba abunda ya shafe ta, opportunity kadai take jira ta fece. Yau ya jima a gidan suna hira da Inna, sai kusan tara yamata sallama, rai bace yabar gida, yafara gajiya da cin mutunci Batula, sakinta zaiyi ya shafawa kansa lapia tunda ba sonta yake ba. Inyaso taje can ta karata da karyar ta, shidai Rmd ya mata nisa saidai ta nemi wani can daban. . Agajiye likis ya dawo gida bayan ya tsaftace jikinsa, Mom ya tarar tsaye tsakiyar palon tana kai komo, kafin yakai ga isa gareta ta tunkaro sa, cike damuwa tace "my boy daga ina kake by this tym Agogon hannusa ya kalla, goma dayan mintinu amma ji yadda take interrogating dinsa kaman karamin yaro ,rabawa gefenta yayi ya zauna kan kujera, "Ancemin kwanan biyu bakaje office ba, idan kasa wasa asset dinmu xai iya dropping" ta fada tana kai mazaunin ta dayan kujerar dake gefensa. Takaici ne ya cikasa, matan biyun duk sun dauramai zafi, ya dawo gida bai tsira ba, Mom dinsa mai kudi amma sai shegen son kudi alway seeking for more, dayar can kuma talaka but desperate to be rich by all mean, kodayake baima san inda ta dosa ba, karyata kadai ya isheshi bugun zuciya. Nisawa yayi yace " Mom gayamin make tsakanin ki da Hajiya safara" Gabanta ne ya fadi, wace irin tambaye ce wannan, ta fadi aranta, afili tace "babu komai, kawata ce tun muna yammata, miyasa ka tambaya ?. Kawar da tambayar yayi dacewa, "na yadda xan aure Mardiyya" Dariya mai dauke da farin ciki tayi, "ka fara sonta kenan ? Kai y girgiza, "a'a, xan bata chance ne, you once said kwarya tabi kwarya, shiyaaa nayi deciding auranta" Dadin sosai Mom taji, atleast xata huta da threat din Hajiya safara, saidai wani hanzari ba gudu ba, zusa katsina ya kamata, amma da wana ido zata dubi kawu Habibu, kusan shekarau sama da ashiri ta yayesu a ababin rayuwar ta, saukin abun ma My boy yakan kai masu ziyara. Mikewa Rasheed yanai mata Sai da safe, bai jira cewarta ba yayi gaba, tuni ya gano ta lula duniyar tunanin dabai san ta miye ba. . Bayan kwana biyu ba inda yake zuwa sai office, da wuri yau ya shirya ya fice office, aiki sosai ya wuni yana yi, charles ne ya shigo yace Mardiyya keson ganinsa it urgent, izini ya mai data shigo, sanna ya fice. Da sallama ta shigo, hannun ta rike da files, amsawa yayi yanai sakar mata murmushi, karfin gwiwa ta samu ta karasa ta hade da mika mai, bai karba ba ya mata nuni da ta ajiye, "Ki zauna mana" ya fada ganin tana shirin fita. Akunyace ta zauna, yace "Momcy bata gaya maki good news ba ?. Sunne kai tayi danta gane inda xancen ya dosa, "Ya preparation" Nisawa tayi, dakyar tace "babu wani shiri, am sure kaima you aint interested da wani grand Preparations". Murmushi yayi yana cigaba da kallonta, duk lokacin nan yarasa miyasa bai gano good side of her ba sai yanxu, koda yake Batula ta sanya shi gano hakan, sau da dama akance yaran masu kudi basu da tarbiyya ashe ba duka aka taru aka zama daya ba, guntun tsaki yaja aranshi, bai taba cin karo da bad girl irin Batula ba, wani mugun tsanar ta yakeji aranshi. "Marfiyya inason auran nan yaxama grand weedding, wanda kowa a duniya saiya san ni Rmd nayi aure". Tsuru tayi tana kallonsa, ita mamaki ma yabata all of a sudden ya yadda da auranta kuma big wedding yakeso, kodayake itama hakan takeso, halinsa yasa ta kama kanta. Hira sosai sukayi kaman masoyan asali, tun tana kame kanta harta saki jiki tana dariya.
0 comments:
Post a Comment