INA ZAN GANSHI Part 03
INA ZAN GANSHI Part 03 . Katsina.. K'arfe sha biyu na rana direban Mom yayi horn gaban kataferan gate din gidan Kawu Habibu, bude gate mai gadi yayi da azama kansancewar ubangidansa ya sheda mai zuwa su. Parking yayi ya fito ya bude mata kofar b'angaranta, cikin isa ta fito tanai karewa gidan saman kallo sannan ta taka zuwa tangameman palon. Ajiyar zuciya kawu Habibu ya sauke, tun shigowarsu yake tsaye bakin window benan yanai kallonta, hali da bazai canza ba abunda kadai ya furta sannan ya juyo saukowa. Hajiya Suwaiba matar sa ta fito daga kitchen, kicibis tayi da ita tanai ma palon mugun kallo, "hajiya Fati harkin karaso ashe, sannu da zuwa" Hajiya Suwaiba ta fada cik'e da fara'a. Ayatsine tace "sauri nake kice wa Kawu na iso" Gyaran murya kawu Habibu yayi yana saukowa. Kunya ne ya kamata batayi tunanin zai jita ba, mazewa tayi tace "Kawu ashe kana kusa, ina wuni". "Lapia lau Fatima",ya amsa hade da zama kan kujera, itama zaman tayi, hajiya Suwaiba ta koma kitchen nema mata abun sha. Gaisuwa sukayi mai tsawo kafin Mom ta gabatar da abun da ya kawo ta, Jinjina kai kawu yayi, yasan tabbas rana irin tayau zataxo, matar da bata daukesu abakin komai ba shine yau ta tako taxo dan danta xaiyi aure, ashe dai komai nada ranarsa. Nisawa yayi yace "naji dadi matika, Abdulrasheed zaiyi aure, naso ace na hadashi da diyata Hafsat saidai hakan bai yuyu ba". "Gaskia ne" Mom ta fadi tana murmushi dabai kai zuci ba, yaushe ma zata yadda Hafsat ta auri Rasheed, mai kawu yake dashi ma, mutumin da rabin dunkiyar sama Ubanta ne basa, dan lecturing da yakeyi nawa yasamu, shima dai xance kawai yage, bazata yuyuba, Mardiyya ce daidai da Boy dinta. Tattaunawa sukayi da kawu, sannan ta gayamai sun riga sun tsayar da rana sati daya kacal, farin ciki sosai Kawu yayi, yanaji da Rasheed tamkar dansa, halin uwarsa kadai yasa yake maintaining distance. Sun dade suna magana daga bisani Mom ta masu sallama ta kamo hanyar Kd. Gidan Hajia Safara ta nufa, nanma sun dade suna tattauna yadda buki zata kasance, daga bisani ta mike zata wuce suka hadu da Abban Mardiyya ya shigo, gaisawa sukayi da Mom yana zolayarta ya shirye shirye, dariyar kawai tayi bata amsa baima ta wuce waje Hajiya safara ta rakata bakin motar ta. Murmushi Abban Mardiya ya saki aransa yana fadin "ku gama shirin bukin ku kafin nima nawa buki yaxo" darawa yayi ya karasa wuce warsa ciki. *** Bikin ya kusanto gadan gadan, kwana biyu kadai ya rage, pre-wedding picture kusan ashirin suka dauka da differnt photographers, sunyi matukar kyau, matured style sukayi wanda bai sabawa addinin musulunci ba, Duk inda ka shiga xancen kadai ke ruruwa, Iv din bukin da picx sai yawo suke a social media, daga masu murna sai masu ihu ganinsa, wasu dan shishigi ma har watapp name dinsu Rmd suka maida. . Tun bayan datayi sallar azahar Batul take jin jikinta amace, gabadaya ta rasa make mata dadi, shi matsiyacin can kusan sati bata gansa ba, hajjo da Baba da yan kannanta ne suka fado mata arai tahau lalubar wayarta da tunga aka kawota bata bi takan shiba, dauka tayi taga yaki kunnuwa, tsaki taja sanin cewa rashin caji yahana ta kunnu, gashi kuma gidan ko wuta babu balle soket. Fitowa tayi tadau bokiti tace, "Inna na fita dibo ruwa" "Kar dai ki dade"Inna tafada daga cikin daki. Dire bokitin tayi ahankali bakin karga sannan ta fito tsakayir unguwar dubawa tayi ko zata samu masu cajin haya, wayam babu ko alamun su, wani gidan siminti tagani can gaba dasu da wutar lantarki awaje, da azama ta taka ta shiga gida, Kwakwasawa tayi, yarinya mai suna Hafsat Rano ta bude, "ina wuni, dan Allah caji nakeso asamin, ga gidan mu can" Batul ta fada tana mata nuni da gidansu. Shigo, amma maman mu ta fita" acewar Hafsat. Godiya Batul tayi ta shiga ciki, yammata biyu zaune tagani kusa da socket suna cajin wayoyinsu suna chating, kaman munafuka ta gaidasu sanna ta sakala nata cajin, gefe guda taja ta zauna hade da tagumi. Dariya daya cikin yammatan mai suna Baby nurse tayi tana fadin "nashige su mistakely na tura pre wedding picx din Rmd da matarsa group, yaukam nasan dole xarah ta cireni". Dayar mai suna Dija Waziri tace "maiya kaiki kinsan dai Xarah bata bari aturo abunda bai shafi littafi ba, turomin hoton Iv dinsu, zakije Dinner din ?. Ihu murna Baby Nurse tayi tace "invited or no invited we must be there,". shewa sukayi hade da tafawa, . Sauraran su Batul take amma tarasa inda xancen su ya dosa, kalmar Rmd kadai hankalinta yafi karkata akai, kasa daurewa tayi ta kunna wayarta, gashi kuma bata watsapp balle su turo mata hoton, karfin hali tayi tace "sis dan Allah turonin picx din Rmd ta Bluetooth". Kallon banza Baby nurse takai mata, abun mamaki wai ta bluetooth, har yanxu ana yayin sane ta fadi aranta. Cikin rawar jiki Dija waziri ta kunna Bluetooth tahau tura mata, godiya sosai Batul tayi bata tsaya jiran wayar ta cika ba ta cire ta koma gida, dakinta ta shige da gudu batare data tsaya sauraran Inna dake magana ba. Addua takeyi wayar na bisa kirjinta, so take ta kalli pic din amma tana tsoro karya zamana Rmd da take muradin samu bai hadu ba, dakyar dai tasamu courage ta kalli pic din, kur tayi tana kallon kyakyawan fuskar sa mai dauke da murmushi, saidai kuma kaman taso tasan fuskar wani guri, a iya tunanin ta bata gano ba, sanin ya mata nisa inama zata ganshi, wani irin sonshi da begansa ne ya mamaye zuciya ta, ware idanu tayi adaidai lokacin da suka sauka a fuska Mardiyya, tsaf tagane ta kwanaki sun hadu a ostrich bakery, last tym da taganta ba karamin burgeta tayi ba amma yau duk sai taji wani irin haushi da kishinta....dafe kai tayi tana fadin innalilahi wa inna'ilaihi rajun, Mamuda ka cuceni,, adalilinka wata ta maye gurbin wanda nake muradi arayuwata, Allah ya isa tsakanin dakai, na tsane ka, banza matsiyaci dan tasha" kuka sosai ne ya kufce mata, su baba da hajjo da tayi niyan kira fasawa tayi, wurga wayan tayi gefe cike dajin haushin su, koma miya faru sune suka caza mata. ****** Buki Budiri ya kankama, duk wata shagali na bukin hausa, turawa dana India gabadaya an kwatanta, duk fadin duniya zancen su ake, BBc, cnn, aljazeera, channels, nta tashoshi da dama ka kune hirar auran Rmd Da Mardiyyah ke wanzuwa, manyan mutane ,yayan sarakuna da gwamnoni duk sun hallara ranar daurin auren su. Karfe 3 na rana aka mika amaryan gidansu Rmd nan inda suke zama da Mom, Hajiya safara baki yaki ruhuwa sai murna take yarta tayi goshi, guraran 8pm aka fara shirin tafiya haddaddiyar Dinner da xaa ayi a fountain Mansion...ni xarah nace bara na leka Batula nasan za ayi african time kafin afara. ** "Yaunxu Batula baza ki bar kukan nan ba, abu yakici yaki cinye wa tun shekaranjiya kina abu daya" Inna ta fada tana tsaye bakin kofar dakin. cikin shesheka tace "Inna dan Allah kice wa Mamudu ya dawo ya sakeni, bana sonshi, ki taimaka ya sakeni na auri wanda naso" karasa maganar tayi cikin kuka mai tsuma zuciya. Ba karamin tausayin ta Inna taji ba, karasa shiga dakin tayi ta zauna gefen ta tana fadin "karki damu very soon xai sakeki, "Dagaske Inna" ta fada in cool voice. . Kai kadai Inna ta taga mata alamu eh, hankalinta na kan fuskar wayar Batul, hoton Rmd din ke kan screen saver ta wanda tuni tayi croping ta cire fuskar Mardiyya, "kaico yarinya kishe ke dawainiya dake," inna tace aranta Lallashi sosai Inna tahau yi mata amma kamar zugata take kara sautin kukan ta take. Tamkar an tsigare ta mikewa tayi tana zara idanu sannan ta janyo ghana must go din ta, budewa tayi tadau yar dubu daya rak data mallaka arayuwarta sannan tadau jan gyale ta yafa bisa kodaddiyar goriyar atamfa dake jikinta, "Ina xaki adaran nan" Inna ta fadi tana kallonta. Cikin saurin tace "bazan dade ba" ficewa tayi da azama ba tare da ta jira cewarta ba. Sauke numfashi Inna tayi ta mike tsaye tana kai komo adakin, yazamata dole tama Rasheed magana, lokaci yayi dazai fito ya nuna mata shine wanda takeso tun kafin ciwon zuciya ya kamata, yadda taga Batul na kuka ta yadda cewa lailai tayi sanyi kuma ta saduda, dakinta ta nufa tahau lalubar wayarta dan kiran Rasheed. . Babban titin unguwar ta tako tanai sak'a da warwara a zuciyan ta, Iv data gani ya nuna mata a fountain Mansion xaai Dinner saidai kuma batasan gurin ba, amma kuma idan taje ya xatayi, nuna kanta garesa xatati ko miye ?, gigiza kai tayi hakan bazai yuyyba, zataje ne kawai taganshi ido da ido. Napep data tsada ba wanda ya dauke ta acewarsu gurin district area ne da napep ko achaba basa zuwa, dakyar dai tasamu taxi sukayi ciniki ya kaitaa naira dari shida dan ba karamin nisa ne da inda ya dauke taba, can farkon hanya ya sauketa ta tafara takowa toward the gate, Kasa karasawa tayi bakin gate din, sojijin kusan 20 ke tsaye bakin gate din, sai manyan motoci da suke artawa ciki a guje, daga gurin da take tana jiyo sautin wak'a dake dashi. Tsuru tsuru tayi, bugun gabanta na tsananta, shahada tayi ta nufa gate din, daya daga cikin soja ya dakatar da ita yana tamvayar ta Iv, ba'a bata ba tace dashi, tuni ya kuma daure fuska, dan kuwa babu mai shiga sai da Iv, dinner din is strictly on invitation. "Oga dan Allah ka barni na shiga " ta fada amarairace. bai tanka taba saima kallon gefe sa da yake, Mom ke takowa cikin takun kasaita, sanye take cikin tsadaddiyar leshe kanta daure da gele wanda Oshewa beauty suka mata tieing, kallonta Batul tayi aranta tana adduaa Allah sa matar ta barta ta shiga. Karasowa tayi. "Julius make sure ku tsaya postion dinku, gasu nan isowa" ta fada tana kallon julius bata ma lura da Batul dake tsaye ba, juyawa tayi zata tafi sai kuma ta juyowa kallon Batul, dauke kai tayi da sauri ta kalli julius tace "miya kawo almajirai gurin nan ? "Hajiya ayi hajuri, yanxu zata tafi" Harara takaimai taja tsaki ta wuce. "Yarinyar kibar gurin nan, kafin nasa a wulla ki titi" "Dan Allah ka barni na shiga, it very urgent" kuka ta sanya tana magana. D'ayan soja dake tsaye yace "yunwa take ji, bara atura kodan snack ne abata ta tafi" Gefe Batul tayi ta tsaya tana sharar kwalla. Covony na mayan motoci guda ashirin sukayi, motar amarya da ango ne a tsakiya, suka karaso gaban gate din basu shiga ba, duk motocin suka tsaya, Zaune suke a motar babu mai magana tsakanin, jifa jifa ne Mardiyya ke kallonsa ta saki murmushi, shima murmushi yake sakar, gabadaya hankalin sa baya jikin sa, maganar su da Inna a waya kadai ke yawan mai a kai, ita so take ya nunawa Batul kansa, saidai bazai iyaba dan kuwa ba sonta yake kuma bai yadda ta saduda ba, nan gaba tana samu wani oppurtunity halin karyar ta xai dawo, asalima he is planing of sakinta idan Baba ya dawo daga tafiyar kauye da sukayi. . Numfasawa yayi ya jingine kansa cikin seat hade da kawar da kansa gefe yana duban waje da hasken lantarki ya gwauraye, gabansa ne ya fadi ganinta can nesa tsaye tana zubda hawaye, idanuwan na kallon motarsa tasu da tasha decoration, motar kadai take gani banda mutane dake ciki kansancewar tinted glass dinta. Kallon ta kawai yake yana mamakin abunda ya kawota gurin nan, Inna tacemai ta fita amma baiyi tsammanin nan tazo ba, gashi yanxu sha daya na dare yayi baisan ma yadda zata koma gida ba dan babu abun haya gurin. Hannu yasa da niyya bude bangaransa xai fito tayi sauri daura hannunta daya sha lalle bisa nasa, kallonta yayi ta sakar mai murmushi, tace 'it time" murmushin dabai kai zuci ba yayi yace "okay' Fara tafiya motocin sukayi suka shiga ciki. Bangaran Batul kuwa kuka kawai take ba kagauta, snacks da soja ya kawo mata fir taki karbar, dakyar da sudin koshi tabar gurin bayan Julius ya sama mata lift a motar wata da zata koma gida. Karshe haduwa Hall din ya hadu, Fadin haduwar Hall din kauyanci ne, jama'a masu hannu da shuni ke zaune gurin, daka ga couple din kasan suna cikin farin cikin, dukda cikin damuwa yadda xata koma gida yake bai hanashi sakin fuska ba. Budirin kadai ake ana ciye ciye cikin jin dadi da annashuwa, can na hango members na *xarah Bukar novel 1, 2, & 3, Home of novel, Pherty novel, Musha karatu, Qurratul-Ayn Novel, Mom fatu Novel*, mamakin ina suka samo Iv nake, ban gama mamaki ba sai ganin su *Miss xoxo Ummee Agoss, Sadiya Jegal, Mom fatu, Queen Miemee, Rookie kazxx, Ramalurv, Hafsat Rano, Dija Waziri, Waliyyah* hakince nagansu suna kwasar loma, nima baa barni baya ba, ledar dake boye cikin jakata na fiddo na kwashi varieties of abincin dake gurin dan kaiwa kawayena su *Mrx Ay, Naja wali, Faty so, fati Imam, Aysha Gajo, Aisha Magasa Kusan 3am taro ya watse, kowa ya tattara yayi gida, couple ma suka koma gidansu. ***** Bayan kwana uku. Mom ta wuce Abuja huta da gajiya, Zaman Rasheed da mardiyyah ba yabo ba fallasa, sosai Mardiyya ke kokarin faran tamai, ba laifi shima yakan kokarin faranta mata dukda bata gabansa, sunyi waya da Innaa ya yanke shawara zuwa dauko Batul ya dawo da ita gidansa, dukda haushinta yakeji zai yi kokarin sanyata farin ciki dan ya lura her case is critical. Bayan Sallah Isha Mardiyyah ta taimaka mai yayi shurin sa tsaf cikin kananun kaya daya kara fiddo da azahirin kyau sa, har bakin mota ta rakasa ya fice daga gidan sannan ta koma cikin gida cike da shaukin sanshi. Kwalliyarta tayi cikin dogowar bakar abaya. Tsakar gidan ta fito rike da empty Ghanar ta tana kakkabewa, Inna dake zaune tayi dariya ganin tabar kukan da takeyi tun safe, jira take Rasheed ya iso taga reaction dinta, gashi kuwa tayi kwalliya abunta tayi kyau, komawa daki Batul tayi tana maida kayanta cikin ghanar sannan ta zuge ta fito rike dashi, Cike da tsiwa ta tsaya kan Inna "tsohuwa Allah kaddara saduwa, idan jikanki ya dawo ki tabbata ya sakeni, idan ms bai sakeni ba xan dawo dakaina na amshi takarda ta". Mikewa Inna tayi da azama, tace "Batul ina zaki adaran nan ? Yake da yafi kuka cuwo tayi, tace "Babu ruwanki, na riga na yake shawarar fita duniya dan cinma burin rayuwata, babu wanda ya isa ya hanani" Kwantar da murya Inna tayi tace "tabbas ba wanda ya isa ya hanaki, amma dan Allah kiyi hakuri ki tsaya kona minti 20 ne, i promise you won't regret it". "Sai kiyi ai" Batul ta fada tana hararar Inna, juyawa tayi zata fita, Inna tayi saurin rike Ghanar tanai rokonta karta fita, fir Batul taki hakura ganin Inna zata bata mata lokaci yasa ta saka mata Ghanar ta fice waje tanai tsinewa matsiyacin gidan. Da gudu Inna tabita waje amma ina Batul ta riga ta tsare, gudu kadai take batare data waiwayo ba, Hannu Inna ta aza akanta tana fadin "Batul kinwa kanki, opportunity daya rage maki kikai shuri dashi", haushin kanta sosai Inna tayi, da tasan mai hali bazai canxa ba da bata tsaya lallaba Rasheed ya bata chance ba. Komawa tayi gida ttadau waya ta kira Rasheed, driving yake kan titi, kadan ya rage ya karaso unguwar, daukar wayar yayi Inna ta shaida mai abunda ke faruwa cike da damuwa, kwantar mata da hankali yayi yace zasuyi magana idan ya karaso. Gudu take harta karaso titi, batama ankara da kokarin tsallaka titin da take ba, sai ganin hasken mota tayi ya kusan to da gudu, cike da kidema tayi baya dan kauce mata amma tuni tayi latti motar sa dage dayan lane dince ta faso aguje, wani mugun burki yaja adaidai lokacin da ta kwalla ihu ta fadi kasa sumammiya. . Hankali tashe yayi parking ya fiso, Addua kadai yake Allah yasa bata ji ciwo wa, karasawa yayi gareta yana haska fuskatar, wazai ganni inba Batula ba, wani mugun tsaki yaja cike da tsanarta, ji yake kaman ya barta gurin yayi tafiyarsa saidai bazai iya ba kodan darajan mahaifin ta. Daukata yayi yasata bayan mota sannan yaja komawa Gidansa da ita, yana parking farfajiyan Mardiyya ta fito da fara'arta, bude motar yaya ya fito da ita kwance bisa hannunsa, da azama Mardiyyah ta nufesa hankali tashe, magana take bai saurare taba banda saurin da yake yaje ya direta, babbab daki mai shegen kyau ya nufa da ita sannan ya kwantar da ita bisa lausassan gado. "Sweetie wace wanan" Mardiyya ta fadi arude, dan kuwa ta fisa tsorota, atunanin ta macacciya ce. "Accident tayi, ki kula da ita" ya fadi ya fice daga dakin, dakinsa ya nufa ya zauna cike da taikici sannan kuma ya kunna karamin Tv dake manna a bangon dakin, Tv ne mai dauke da connection footage na gidan gabadaya, part kusan goma na gidan ya nuna, yasa remote yayi zooming part din dakin da ya kwantar da Batul, jira yake kadai ta farka yaga reaction dinta. Toilet Mardiyya ta shiga ta dibo ruwa a bowl hade da hand towel sannan ta dawo kusa gareta tahau goge mata fuska inda ya kwarzane, bayan ta gama mikewa tayi ta sauka kasa kiran altine ta hada ruwan zafi a flask. . Bayan mintuna biyu Batul ta farka a gigice, tsorata tayi ganin ta a wagegen daki, zaburewa tayi ta mike tana karewa dakin kallo, ina ne nan kadai take tambaya aranta, tasan dai moto ya kusa bige ta ta fadi daganan kuma sai gata anan, "kodai wanda suka kusa kade tane suka kawo ta" ta fadi aranta. Tsoro da mamaki ne ya kamata, da sauri ta fice daga dakin, bin tangameme stairs din tayi da kallo tana adduaa neman tsari, atunaninta gidan yankan kai aka kawo ta, dago da idanuwanta tayi taga hadaddudun frames mai dauke da picx din Rmd da Matarsa kusan shida anyi decor dasu ajikin bagon, rike baki tayi kam tamkar wace tayi niyyan ihu, jin motsin zaa hawo yasata rugawa dakin da gudu, kwanciyar tayi tana neman mafita, dan kuwa indai gidan Rmd Allah ya kawota bazata fita ba, mafita kawai take nema, can kuma dabara ta fado mata ta saki murmushi hade da runtse idanunta. Kallonta Rmd yake ta Tv, saidai baisan dalilin komawar ta cikin dakin da gudu ba. Murmushin gefen baki yasaki, yasan definitely she is up to somtin, kashewa yayi ya fice zuwa dakin. Ahankali Mardiyya ta shigo dakin ta karasa kan gadon ta zauna, bude idanu Batul tayi tana lumshe su kaman wace yanxu ta farfado, mikewa tayi zaune tana kallon mardiyya da itama kallonta take. "Wace ce ke ? Batul ta tambaya tanai mata kallon rashin sani. Murnushi mardiyya tayi ta matso da ita tana fadin "ya jikin naki ". Kallon rashin fahimta Batul tayi mata, "banda lafiya ne ? "sweetie ya kawo ki dazu, wai kin samu accident" Tsurewa Batul tayi tahau kuka karya, "accident when n how, i cnt remember anything". Mardiyya sarkin tsoro, tashin hankaline ya bayyana karara a fuskarta, atunanin ko Batul tayi loosing memories dinta. Rikota tayi tace "baiwar Allah ya sunanki "Na manta" batul ta fada cikin muryan kuka. Cike da tausayi Mardiya tace "plz try to remember wace ce ke, koda ma garin da kika fito ne, kiyi kokari ki tuna" Shuru batul tayi kaman mai tunani can kuma tace "abu daya na iya tunawa Mardiyya tace "Gayamin " "Nasan dai ni yar sarki ce, it seems someone is plotting to kill me" karashe maganar tayi tana juya kanta as if she is trying to recall wasu abubuwan. "Kill you " mardiyya ta fada in shock. Yes" abunda na sani kenan, kuka sosai Batul ta fashe dashi hade da fadawa kafadar mardiya, lallashin ta Mardiyya tahau yi. Duk drama da Batul take akan idonsa, basu lura daya shigo ba, gyarar murya yayi duk suka dago suna kallon sa, mikewa Mardiyya tayi ta karasa garesa, tana fadin "mutune abun tsoro, i wonder mai beautiful princess tayi suke son kasheta" cike da tausayi tayi maganar. Kasa magana yayi tsananin tsanar Batul da yakeji aransa, kallonta yake, aransa yana fadin "she will never change...... . Amarairece Mardiyya ke kallonsa, ko alamun tankawa bai yi ba, banda kallo Batul da yake fuska murtuke, murya kasa kasa tace "Sweetie bakace komai ba" Ficewa yayi daga dakin batare dako kanzir ba, Batul dake kallonsa duk taji ba dadi, mugun kallo dayake mata yasa ta kasa sukuni, tsoronta daya kar ya gano karya ta shirga masu. . Daga inda Mardiyya ke tsaya tace "kar ki damo da looks dinsa, he is nyc magana kuma ba kasafai yake ba" Girgiza kai tayi kaman zata tayi kuka, Mardiyya tacigaba, "ki kwantar da hankali, you're welcome to stay har ranar da xaki tuna masarautar ku" Nagode",Batul ta fadi cike da tausayin kanta, deep down aranta murna take abun nema yasamo. Mardiyya bata bar dakin ba saidai ta kira Altine ta kawo mata komai na bukata sannan tai mata sai da safe ta fice. Dadi sosai Batul taji mikewa tayi tsaye tana tikar rawar murna. Toilet ya shiga ya sakan wa kansan shawa, mafita kadai yake nema ya rasa, duk hanyar da yabi Batul ce zataci riba, idan ya fito ya bayyana mata kansa gaba takai ta, idan kuma ya sake ta still taci rabi wani guri zata je tacigaba a inda ta tsaya, shawara daya ya yake danci galabarta at her own game. . Karfe takwas na safiya Batul ta farka daga bacci, agurguje ta shiga bayi ta dauro alwawa tayi Sallar asuba, aranta tana jinjina lausassan gado da Sanyi Ac dakin, da wayota bata taba missing sallah asuba sai yau, istigifari tayi ta koma gadon taci gaba da baccin ta, sai kusan goma ta tashi. Shigowa dakin Altine tayi da nikiniki kayan ta ajiye cikin wardrode sannan ta gaidata tace mata kayan sawane Aunty ta aiko akawo mata. "Okay" kadai Batul tace cikin nuna rashin damuwa akansu, bayan Altine ta fita mikewa tayi ta ciro kayan tana kallo, kayane yan kanti masu matukar kyau da tsada, tsalle tayi tana taka rawar "if" na mawaki Davido. . Wanka ta shiga da axama ta fito ta shirya cikin riga da skirt na kanti daya amshi jikinta sannan tayi zaman tsantsara kwaliya, bayan ta gama, fitowa tayi sukayi kicibis da Mardiyya zata shigowa, murmushi tayi tace Princess kin tashi" "Eh" Batul ta fada tana kallon yadda mardiyya tasha kyau, kamar mai zuwa buki, duk saita rena nata. Hannunta Mardy ta riko tace muje muyi breakfast, tsum tsum tabita tanai karewa gidan kallon in a Stylish way gudun kar su gano bata saba ganin hadaddn gida haka ba. Dinning suka nufa taja mata kujera ta zauna sanna tace "minti daya barin dauko Sweetie" da sauri ta haura sama. Haushi ne ya kama Batul ganin yadda Mardiyya ke wani rawan kai da Rmd, banda feleki miye saikin dauko sa" ta fadi aranta, shataf ta manta da wani mijinta Mamuda sai yanxu ta tuna shi, tsaki taja tanai kallon abinci dake jire gurin, karaf idonta yakai kan roasted chiken dake gurin, wani mugun yawu ta hadiya, Jira kadai take suzo afara. . Tsaye ta iske sa yana button din shirt dinsa, temaka masa tayi sanna suka fito tare saukowa, kallo daya Batul tayi masu ta dauke kai, wani irin xafi zuciyar ta ke mata, bata rai tayi ta daura kafa daya kan daya, karasowa sukayi Dinning din ya janyewo Mardiyya kujera ta zaunna sannan ya zauna gefenta, kallon batul yayi bata da niyyan gaidasa saima daure fuska da tayi, murumshi ya saki dan bakaramin kyau tamai ba, yace "Good morning Princess" Kaman jira take, princess daya kirata dashi yay mata dadi, wato shima ya yadda kenan, murmushi ta saki tace "morning My prince" Atare Marfldiyya dashi suka ware idanu suna kallanta,. Murmushi ta saki irin ta yan duniyan nan tayi tace "kuna yana yi dashi, dou i cnt recall his face, shi yaka mata na aure, datx y am trying so hard na tuna shi, i love him alot am sure shima yana can yana nemana". Ran mardiyya yadan sosu, kasa boye kishinta tayi, haushi taji yadda Batul tace prince dinta na kama da mijinta, hannunta Rasheed ya riko, cikim murya kasa kasa yace "we have to support her idan har munaso tayi regaining memories dinta, plz be strong and trust me" Kai ta girgiza alamar ta yadda da xancen sa, tana son Rasheed shiyasa kome ya fada mata take naam dashi, farin cikinsa shine nata. Basu tanka Batul ba, suka fara cin abuncin bayan Mardiyya ta zubawa kowa a filet, sultan chips ne da roasted chicken sai tea hade a kowane cup, Satar kallom su Batul take tana ganin yadda sukecin abunci cike da yauki, jifa jifa kuma Rasheed ya saki Murmushi, ko tari babu maiyi cikin su tsananin yadda suke bawa table manners dinsa, . kasacin kazar Batul tayi saboda fork da table knife da taga suna ci dashi, gashi ba daman tasa hannu class dinta ya zube, daurewa tayi ta rike fork da wukan ahannu daya, kazar tayita cacakawa ta kasa dauka, mazewa kawai tayi ta ajiye fork din tadau tea din tana sha. Duk a idon Rasheed, dariya ne kadai baiba ya dake, kadan kadai yaci a abinci ya mike tsaya ya karasa gurinta, "Princess har kin koshi ? Ya fadi yana murmushi Yatsine fuska tayi tace "i dont eat much" Fork din ya dauka yace "plz kici, baa zaman yunwa agidana" hannuta ya rike yasa mata fork din. Wani irin yir Batul taji da hanusu suka game guri daya wani irin yanayi ta shiga da ita kanta bata gane ba, "tnx my Prince" ta fadi hade da kirkiro murmushin dole, gabanta sai faduwa yake, zuciyar na tuna mata tana da miji. Barin Palon Rasheed yayi yahaura sama, Mardiyya ta mike ta maramai baya. Tsulum Butal ta mike tahau kwashe duka kazar dake cikin filet dinsu tana fadin "waya ki dadi, ai dole ma naci kodan huce haushi kosai da bredi da Mamuda ya kawo min daran farko na" hadesu tayi cikin filet dinta tahau ci da hannu cikin sauri tana duban stairs kar su sauko su kamata. . Dire mazauninta tayi kan dayan daga cikin d'ima d'iman kujeru dake parlour, Altine ta k'wallawa k'ira, daga can kitchen ta amsa ta karaso dagudu. "Barka da rana Aunty Princess" Altine ta fadi hade da risinawa. Murya ciki ciki ta amsa mata da "barka dai, akwai fruit ? "Ranki shi dade akwai su"Altine ta fadi cikin rawar jiki, aganinta ba karamin matsayi tayi ba yar sarki na mata magana. Yatsine fuska Batul tayi tace "kawo min, kafin ki wuce ki kunna min Tv" Altine tace "angama" Tv din ta kunna sanna ta koma kitchen dauko mata fruit. . Murmushi Batul tayi ta k'urawa tangameman Tv idanu da kusan mintuna 10 da suka shude tayi tana kokarin kunnawa takasa, shiyasa ta kira Altine ta fake da fruit dan kawai ta kunna mata. Atsaftace Altine ta kawo ta ajiye mata a side table din kujerar da take zaune kanan ta wuce tsabgogin gabanta. Ahankali yake saukowa daga stairs, kunnesa nanuke da wayarsa yana answering call, sai ipad dinsa rike a hannu ,hada ido sukayi tayi saurin kawar da kanta adalilin wani yanayi data shiga, baiko bi takan taba ya karasa ficewa waje. Ajiyar zuciya ta sauke, tanai hamdallah da ya fice daga gidan. Mikewa tayi ta leka window waje babu alamunsa sannan ta kira Altine ta dauko mata talkalmi heel dake cikin kayan da Mardiyya ta bata, sanya su tayi akafarta sannan ta fice haraban gidan dan karewa ko ina kallo. Tafiya take dakyar cikin heel kasancewar bata saba ba, kallon ko ina take cike da sha'awa colourful folawowin dake shuke ta ko ina na gidan, can ta hango karamin stone waterfall na zubda ruwa da azama ta kara sauri takunta, ba karamin burge ta yayi ba, abunda bata taba gani ba. Ba ta ankar ba tayi missing steps, tim ta fadi kasa hade da sakin yar kara, kokarin mike tayi, taji muryar sa akanta. "Fatan dai Princess bataji ciwo ba" ya fadi yanai mika mata hannu dan agaza mata. Kallon hannusa tayi kaman zata mika mai nata sai kuma ta fasa, mikewa tayi tana kakkabe jikinta sannan dubesa, "Banji ciwo ba My prince, mi kakeyi nan ? Ta fadi tanai smiling. . Gurin zaman mutum ya nuna mata, yace "zaune nake ina tunaninki" Kallon rashin fahimta tamai, hannuta ya rike yajata gurin suka zauna sannan yace "Tun farkon haduwan miyasa kika boyemin ke princess ce ? Ware idanu Batul tayi, bata fahimci inda xancensa ya dosa ba. Hannuta biyu ya rike gam yana fuskantar ta. "kalleni dakyau, i want you to remember my face, nasan kinyi loosing memory naki, but plz try hard to remember" Shuru Batul tayi tana kallonsa, hannuta ya saki ya kunna ipad din yana fadin "let me show you sumtun, am sure zaki tuna" Photo gallery ya shiga yahau nuna mata picx da sukayi tare, sanye suke da english outfit, ko wanne su sanye da handwarmer bisa kansu ga snow ta ko ina a background din hoton, iya tsurewa Batul takai, mamaki da tsoro ne suka kamata, yarinyar kan hoton itace ba kowa ba amma tasan dai ba ita bace din, murya sarke tace yaushe mukayi snaping picx dinnan kuma a ina ne" Numfasa yayi yace "two year back a London, can muka hadu muka fara soyayya, unfortunately you left without saying goodbye sai dana kawoki gidan nan nagene ki, am sure ganina da kikai yasa kikace nayi kama da prince dinki, bakiyi karya ba dan kuwa am your prince" Hauka ya rage Batul ba tayi ba, dan kuwa ya gama daureta ta, look alike dinta yake nufi badai itaba, tunda uwarta ta haifeta ko bakin border bata taba zuwa ba balle london. Ajiyar zuciya ta sauke. "Na manta gaskia, saidai zuciyata batai karya ba ina ganinka nasan akwai connection tsakanin mu, ashe dai dagaske you are my prince". "Yes my princess" ya fadi hade da janyo ta jikinsa. "Jikina yasha gayamin zamu hadu smday, am so happy to meet you" Ihu kadai yarage Batul tayi, tsam ya rungumeta ta kasa kwance kanta, igiyoyin auranta uku kadai ke yawan mata akai, Sakinta yayi tayi azaman mikewa tsaye tana fadin "kaina na ciwo, i need some space" bata jira cewarsa ba ta bar gurin da saurinta. Murmushi yayi yanai bin bayanta da kallo harta shige cikin gidan. Cike da fargaba ta shiga parlour, sauri kadai take ta ganta dakinta, hannu data ji bisa kafarta yasata korma uban ihu, a tsorace ta waigo "Lapia kuwa "Mardiyya ta fadi tana kallonta, tun shigowar ta take mata magana amma hankalinta baya jikinta. Cikin rawar Murya kaman zatayi kuka tace "bana jin dadi ne" rugawa sama tayi da gudu ba tare data jira cewar Mardiyya ba. Tausayinta Marfiyya taji, aganinta ko rashin memories dinta yasa ta zama traumatise. Yunin ranar zuwa dare adaki Batul ta zauna, gabadaya jikinta yayi sanyi tsoro ma take su hadu da Rasheed kar yaxo mata da batun da ita kanta bata gane ba, saidai har yanxu mamakin picx din data gani take, babu tantama look alike dinta ce, amma toh ina take, ya sunanta, why did she left him without saying goodbye, duk tambayoyin nan a zuciyar ta take fadi, tunanin kadai take yadda zata gayamai ba ita bace, idan kuwa tace mai ba ita bace lailai kuwa zai gano memories dinta ya dawo daga nan kuma asirinta ya tono. Jin motsi an taba kofar dakin yasata azamam mikewa tsaye cike da fargaba, Altine ce ta shigo rike da Dinner ta ahannu, gaidata tayi ta ajiye bisa center table dake gurin sannan ta fice. Kadan ta iya tsakura taci, daga bisani kuma ta shiga toilet freshen up. . Kwance take bisa kirjinsa tanai zubamai shagwaba, daure wa kawai yake yana biye mata, azahirin gaskia hankalinsa baya jikinsa, numfasawa yayi yanai shafan gashin kanta, "Diyyah" ya kira sunanta da salon da bata taba ji garesa. "Miyasa banga princess during dinner ba" ya fadi. Lumshe idanu tayi ta dago dubansa, tace "I dont know, kaman bataji dadi datx y na bata space, why do you care? Ta karasa maganar amarairace. Matse ta yayi tsam jikinsa yace "am the cause, kinga dole nadamu" You are right" ta fada tanai shafar sajansa. Janye jikinsa yayi kadan. "Ina zuwa" ya fadi tare da kokarin matsar da ita daga jikinsa. Riko hannusa tayi. "Sweetie ina zakaje ? "Am thirsty, i need some water" Zaune tayi da azama "Let me get it" kokarin mikewa tayi. Ya zaunar da ita, "dont worry, yi baccin ki, yanxu xan dawo". Ba yadda ta iya ta koma ta kwanta, dan bazata iyamai musu ba, slight peck yakaimai ta a cheek sannan ya fice yabar dakin. Ajiyar uciyar ta sauke, tana bukatar Man dinta ta rasa ya zatayi, ba mamaki ma office dinsa na cikin gidan ya nufa ya fake da ruwa zai sha, gyara kwanciya tayi tanai lumshe idanu cike da so da shawa'arsa. Ahankalin ya turo kofar dakin ya shigo, shuru babu kowa banda sanyin Ac daya ratsa ko ina na dakin, motsi ruwan daya jiyo a toilet ya tabbatar mata tana wanka. Sofa dake dakin ya nufa ya zauna jirar fitowar ta. Fitowa tayi daure da karamin pink towel, karasawa tayi gaban dressing mirror tanai karewa kanta kallo, duk da jikin ta asanyaye yake bai hanata iyayi da kwarkwasa a gurin ba, tsadadun mayukan dake gurin duk saida ta bude ko wanne ta shafa sabanin da Vaseline blueseal ne manta, turaruka kusan goma duk saida ta bude ta fefesa sannan ta sanyawa lips dinta red lipstick dake gurin, tayi kyau matika dukda ba wata kyale kyale tama fuskar ba, kallon Madubin take tana admiring kanta. . Akan idonsa duk abunda take, gabadaya ya gama shagala da kamshinta dake shigar mai hanci, lumshe ido yayi ya mike ya karasa bayanta, yatsun sa yakai bisA wuyanta yanai yawo dasu. Batul kam tayi nisa, dream nation dinta ta lula, fuskar kadai ke kallon mirror amma ruhin baya tattare da ita. Motsin Hannu dataji kan boobs dinta yasata dawo wa hayyacinta, idu hudu sukayi ta mirror, ihu taso kwalla wa yayi caraf ya rufe mata baki da Hannusa, kokarin guduwa tayi ta kasa kasancewar matse ta gam dayayi jikinsa. Cigaba yayi da mata yawan tsutsa da hanusa at the same time kuma yana fadin "Kin tuna da wannan " ya fadi saitun kunna ta, numfashinsa gabadaya ya gaba firgita ta, kai ta girgiza alamu bata tuna ba. Hannusa yakai kan towel din yanai kokarin cirewa yace"you used to enjoy it, idan ina miki hakan, how cms kin kasa recalling happy moment or your life" Iya tsurewa Batul takai, wana irin iskanci ne wanna, ta fada azuciyar ta, daurewa kawai take, wani irin yanayin marar mistallatu ta shiga, sama sama Take ji numfashin ta. Wani mugun karfi ne yazo mata tayi sauri warce jikinta daka nasa, cikin zafin nama ya janyo ta ta faso bisa jikinsa, kafin takai ga ihu yama tsukeken bakinta cafka, cikin salon mugunta yahau tsotsan lebbenta, tuni tara fita hayyacinta, saida yaga ta tsumu sannan ya turewa iya karfin sa yanai kai mata mugun kallo, jajir fuskan ta yayi tsabar azaba, kuka ta fashe dashi dan ba karamin tsorata tayi dashi ba. Cikin wata kasalalliyar murya yace "did you enjoy it?. Harara takai mai, banxa dan iskaa" bata karasa ba ya wanke fuskar ta da lafiyayyar mari da saida taga wuta ya wulka, Dan kara tasaki ahankali hade da dafe kunci ta da tunda uwarta ta haihefa babu namiji daya taba mata haka, kallonsa kawai take afirgice, da gudu ta fada toilet tana tsuga kuka, ko amarfiki batayi tunanin Rmd dinta xai iya mugunta haka ba, asalima batazo gidan dan yana harassing dinta ba tazo ne kawai yasota amma shi yanai bata kallon yar iskan budurwar shi, kuka kawai take tana sumbatu sai yau taga ranar Mamuda da komin rashin Mutunci da takemai bai taba tanka taba, shine yau kalma biyu kacal sun caza mata mari. Baibi bayanta ba banda Murmushi daya keyi, duk da a mugunta yayi kissing dinta he really enjoys it, ficewa yayi daga dakin ya koma dakinsa, tsaye yaga Mardiyya tanai kai komo a tsakiyan dakin, tana ganinsa ta karaso garesa, "Sweetie ka dade.." Ta fadi, bai amsa taba yakai bakinsa cikin nata, suka fara kissing juna passionately. . *** Bayan kwana Uku Tun randa hakan ta faru Batul tahau wasan boya dashi, Duk wata hanya da zata tsada ta dashi bata bi, koda wasa bata zaman dakinta gudun karya shigo ya farmata, ako yaushe gurin Mardiyya take makalewa danta lura ko kallonta bayayi idan suna tare, shi dinma yayi busy, aiyuka sosai ke gabansa, wuni yake a office dinsa na gidan yana danne danne computers sa, ganin haka yasa Batul sakin jikinta da kare zagewa akan ita princess ce. Da yamma likis, zaune take dakin Mardiyya tanai karambani gyarawa kayan shafanta dake kan dressin mirror zama, Mardiyya na kan gado kwance tana latsar wayarta, jifa jifa kuma suma juna magana. Roban ban kitso Batul ta daga tana fadin "Sister Mardy kinga wannan ya kare" Dagowa Mardiyya tayi tace "tun jiya nace Altine ta wulla trash, ashe bata dauka ba" Gefe Batul ta ajiye robon tace "ni gobe saloon nake son zuwa" "Ba matsala, Allah ya kaimu goben sai muje" Dadi sosai Batul taji, turowar kofar dakin ya katse mata hanzari, shigowa yayi rike da wasu takardu a hannusa, nan take jiki Batul yahau bari, matsawa jikin bango tayi ta lafe, ko kallonta bai ba ya karasa gurin Mardiyya da tuni ta mike zaune. "Diyyah, ga wannnan kije office kimin compiling dinsu cikin data base na marketing department" ya fadi yana mika mata papers din Karba tayi tana fadin "right away" mikewa tsaye tayi da azama tana cewa batul "princess ina zuwa, duty calls" sannan ta fice ya mara mata baya. . Ajiyar zuciya na relief ta sauke, gadon ta karasa da niyya zama taji ya banko kofar ya shigo, atsorace ta daskarewa agurin, karasowa gabanta yayi yanai mata shuumin kallon sanna yakai hannusa bisa fuskarta, "princess baki iya gaisuwa ba ? Daburcewa tayi, tahau fadin "ina kwana my Prince" baki na rawa ta karashe maganar. "Ina kwana by this time" ya fadi hade da janyota jikinsa, kame jikinta tayi tsam dan bataso irin kallon dayake mata. "Princess" ya kira sunanta cikin wata kasalalliyar murya daya kashe mata jiki, kallonsa tayi tanai kokarin jan baya, yayi saurin tarota, boobs dinta dake neman fasowa daga cikin yar karamar riganta yake kalla, da sauri tayi azaman sa hannu ta tokare, cire hannun yayi yace "bakya so na kalli abuna". Gutun tsaki taja cikin kaguwa da kallon dayake mata, "Ni kike ma tsaki ? Ya tambayeta Banza tayi dashi hade da dauke kai, matse ta gam yayi yahau kissing ko ina na fuska ta, kokarin karkato da kanta yayi dan kissing lips dinta, fir taki yadda dan ba karamin haushi yake bata ba, murmushi mugunta ya saki yakaima boobs dinta wani irin raruma data saki karamar ihu, bata ankara ba sai ganin tayi yana latsar boobs din hade da kokarin cire mata riga. Hannusa tayi saurin rikewa, "Dan Allah kayi hakuri, banaso" Bai kulata ba saima kara cigaba da abunda yake, kuka ta fashe, "Dn Allah kabari, akwai aure akaina" Sakin ta yayi yanai mata mugun kallo, sanna ya shako wuyanta, "yaushe kikai aure, wa kika aura? Cike da karaji da zare idanuwan sa da suka sauya launi zuwa ja yake maganar. Akideme Batul ke kallonsa ba tare da kwakwaran motsi ba, ita kanta batasan ya ankai tace akwai aure akanta ba. Baki na rawa tace "bansani ba, nadai san ina da aure, dan Allah kabari" Fuska daure yace "Ni zaki rainawa wayo, gayamin wa kika aure, waye mijin" Shuru tayi banda matsar kwalla da take, shakar da yayi ma wuyarta ma ya isheta. "Yau zaki san baa raina min wayo" fizgo ta yayi suka fada toilet dake dakin,, duk ta furgici tarasa uwar mai xai mata, bowl mai fadin dake cikin jacuzzi ya kunna ruwan sanyi ciki sannan ya kashe bayan ya cika. Kallonta yayi yace "yau dolene ki gayamin waye mijinki" wuyarta ya damko gashin kanta ya zubo dan tuni hular kanta ya fice, kallo yalwan gashi yayi ya dauke kai, tuni Batul ta rikice atunaninta wanka xai mata sai kuma taga ya tsugunar da ita hade da tura kanta cikin ruwar, ihu ta saki bayan ya ciro kanta daka cikin ruwan "Waye mijinki" ya fadi fuska ba annuri. . Iya galabaita Batul takai, ga ruwan bai dan banxa sanyi, tsabar mugunta sai kanta yayi sakanni yake fidda ta. "Nakasa numfashi, dan Allah karka kashe ni" ta fada, numfashi sama sama, ido jajir. Tambayar ta ya kuma yi, tayi shuru ba amsa kara danna kanta yayi cikin ruwan sannan ya fiddo ta. Kuka sosai ta fashe dashi "kayi hakuri, nakasa tuna waye mijin" Murmushin mugunta ya saki, ya kuma danna fuska ta ciki, kusan sai hudu yayi bata da niyya gayamai waye mijinta, cikin fusata ya ture ta, tsantsin ruwan dake gurin ya kwasheta ta fadi kasa, atake bakinta ya fashe, jini yahau zulala, ko kallonta bai yiba yayi hanyar ficewa sai kuma ya dawo ya damki wiyanta, "na baki nan da 24 hours idan baki gayamin waye mijinki ba, abunda yafi wannan zan miki" take yatsu kafarta yayi ya fice afusace. "Innalilahi wa inna'laihi rajun" kadai Batul ke ambata, cike muryar kuka mai tsuma zuciya, agabadaya jikin ta radadi yake mata, kanta wani irin azababban ciwo yake mata, kuka kadai take tana dana sanin kawo kanta gidan Rmd dayake barazanar kasheta, da yanxu tana gidan Mamuda bawan Allah hankalinta kwace ba tare da yayi gigin taba lafiyar jikinta ba, sai yanxu ta tabbarta kauyanta shine birninta, talaucinta shine kwaciyar hankalin ta, ina amfanin an wadata ta da komai amma ba kwashiyar hankali. 24 hours daya bata kadai ya kara firgita ta, mikewa tayi tsaye dakyar tana fadin "gidannan ba gidan zamana bane, mundin na kara kwana daya saidai afita da gawata" fitowa tayi daga dakin tayi hanyar stairs ba tare data leka ko dakinta ba, gudu gudu sauri sauri ta fice waje ba tare da kowa ya ganta ba, tsakanin cikin gidan da gate ba karamin nisa ne dashi ba haka ta taka ta karasa, securities hudu sanye da uniform tagani, harda mata biyu cikin su, ko kallonsu batai ba tahau kokarin bude gate din, kallota sukayi sukace "Baa fita saida izinin Oga "Ni ba yar gidan nan bace, ku bani guri" tafadi tana harara su. Damko hannuta mata biyun sukayi suna fadin "oga yace karmu bari ki fita" Hankali batul atashe tahau masu magiyan su barta, ko kallonta basui ba suka cicibeta zuwa cikin gidan, direct inda suka hango Rmd tsaye suka kaita, wani wawam mari ya tsakar mata afuska, yace "My princess baa fita a gidan nan sai da izinina" . "Ba fita xanyi" ta fadi, fuska jajir ko ganin haske batayi sosai tsabar azaba. Cema security din yayi su kaita up stairs inda dakinta yake, sannan ya kalleta yace "23 hours 30 minute remaining...."
0 comments:
Post a Comment