INA ZAN GANSHI Part 05
INA ZAN GANSHI Part 05 . Tsananin ranar daya k'walla garin bai hana ta ganin duhu da jin sanyi ba, Tafe take tana lailayi sakamakon jirin dake neman d'ibar ta tsabar yunwa da radad'in da zuciyan ta yake, kuka take ba k'agauta, horn din motar dataji bayanta yasa ta daskarewa tsaye batare data waigo ba. Tuk'owa gaban ta yayi hade da wining glass kasa, hada idanu sukayi yanai kallon yadda idanuwanta sukaisauya launi zuwa ja, kawar da kai yayi ya ciro d'ari biyar daga wallet dinsa, cikin rashin damuwa da yanayinta ya cilla mata kudin afuska yabai wa motar wuta yayi gaba. Yak'en da yafi kuka ciwo tayi hade da sa hannu tadau kudin da tuni ya fad'i k'asa, jinjina kai tayi, tana xancen zuci, ko mi yay mata bataga laifin sa ba ita ta jama kanta, asalima sonshi ba raguwa yayi a xuciyan taba idan ma ya dawo gareta hannu bibbiyu xata amshe sa, saidai ayadda taga fuskar sa she doesn't tink xai k'ara waiwayanta, kuka sosai take tana consoling kanta, tasan Mamuda nada kirki da kyakyawan zuciya baxai share taba, he will definitely come for her. Hope sosai tayi ta bawa kanta, taxi ta samu ya dawo da ita gidan sanna ta biyasa da dari biyar din. Marwa tagani tsaye gaban gidan, yana zuba yan tarkace a gidan baya, da azama ta shige gidan sanin cewan tarkacan Inna ne. Tsaye taga Inna bakin kofa tana kokarin datsewa da k'wado, dan ihu mai tattare da tashin hankali tayi tana fadin "Inna karki tafi ki barni" Sai sannan Inna ta ankara da ita, sosai Batul ta bata tausayin sakamakon fita hayayyacinta da taga tayi. "Batula kin dawo ashe" Inna ta fadi hade da zare mukillin k'wadon. Karasawa gabanta Batul tayi ta tsugunna, cikin kuka tace "inna dan Allah ki zauna dani, bansan ina xan nufa ba, Mamuda ya sakeni ko kuma ince RMd ya sakeni dan nasan kinsan komai" Dagota Inna tayi tanai kallonta. "Batula laifin kini ai, kwanaki ba yadda ban rokeki karki tafi ba kikayi kunnan uwar shegu kika kara gaba, inda ace kin tsaya da Rasheed bai sake kiba, aranar yaso bayyana maki kansan amma ke kika tafi nuna mai kanki" Sosai take kukan tace, "nasan na tafka babban kuskure, amma Inna ai bai kamata ya sakeni ba kodan son dana kemai" Goge mata hawayan Inna tayi. "Kidaina kuka, Allah yasa sakin yafi alheri, yanxu Ki dau kayanki ki koma gidan ku" Kai ta girgiza, "Inna tsoro nakeji bazan iya komawa gida ba, ki temaka ki zauna dani kafin wasu kwanaki saina koma gida inyaso muje tare ki tayani bawa Baba da Hajjo hakuri" Ajiyar zuciya Inna ta sauke tace "kinga ni baa garin nan nake ba, Jikana ne abokin rasheed shiya kawoni nazauna dake na dan wasu lokuta, yanxu kuwa gida xan koma Zaria na cigaba da sana'ata shiyasa kika ga na dawo daukan sauran tarkace na" Kyankyame Inna tayi tana rokonta, "dan Allah kije dani Zaria, ko talla ce xan miki, Inna ki temaka.." Karashe maganar tayi cikin matsananci kuka. Ba karamin tausayinta Inna taji ba, tace mata ta dauko kayanta su tafi, cikin rawar jiki Batul ta fada daki ta warb'o ghanar ta fito sukayi waje, Marwan suka shiga yajasu zuwa tashar kawo suka shiga motar Zaria. . *Kauyen Marke* Jigawa state. . Zaune Hajjo take a tsakar gidan su mai zagaye da kara masu kauri, Rike take da rariya tana tankadar garin masara. Shigowa baba yayi yanai wa su Hassan nuni da inda zasu ajiye buhun albasar dake lafce bisa bayansu, ajiyewa sukai hade da sauke numfashi. Zama Baba yayi bisa tabarma dake shimfud'e, Hajjo tamai sannu hade da mikewa bakin randa dibo mai ruwa. "Noma akwai dadi, kaman karmu koma Kaduna" Hussaini ya fadi yana zama kan tabarmar. Hassan dake tsaye yace "nikam na matsu mu koma naga Batula" Guntun tsaki Hussaini yayi. "Batula ta manta mu, tunda tayi aure bata kira kosau daya ba, gashi ita layinta baa samu, na tabbata arziki tayi ta yashe mu" Kwafa baba yayi yace "banason gulma, ku tashi ku bani waje". Tsum suka mike suka fice, takaici ne yakama Hussaini, ya dade da lura duk cikinsu Baba yafi son Batul, sau da dama tayi laifi baya hukuntata saiko Hajjo ta mata duka amma su abu kadan yahau masu fada, shiyasa sam Jinin su bai hadu da itaba dan kuwa bayason raini dukda ita din yayar shice. Ruwan Hajjo ta mikamai ta zauna tanai kara mai sannu. "Ka sanar da Mamuda batun fasa tafiyar ? Acewar Hajjo. Wayar aljihunsa ya ciro yana fadin "zuwa gobe dai xan kirasa yanxu wayar ba caji". Numfasawa Hajjo tayi tace, "na yaba da hankalin yaron sosai, saidai halin Batul nake tsoro, Allah yasa tana kyautatamai" "Karki damu, Insha Allahu lafiya suke". "Allah yasa" ta fadi, Hira su cigaba dayi cikin kwanciyar hankali. **** Kaduna. Aiki sosai yayi a office, bayan yayi sallah isha ya nufi hanyar gida. Cikin shirin atampa riga da skirt tayi, fitowa tayi daga dakinta da niyya sauka kasa taji tashin zuciya, da azama ta ruga toilet, wani mugun amai yaxo mata tahau kwararawa, dogon numfashi ta sauke bayan tagama ta wanke baki ta fito, bakin mirror ta nufa ta kara shafa powder sannan ta sauko kasa. Mom ta iske zaune parlour tana shan fruit, Kallon ta tayi sannan ta zauna tace "Mom yaushe kika dawo " ta fadi in state of confusion tana kura mata idanu. Guntun tsaki Mom taja bata tanka taba, zama Mardiyya tayi tana tunanin tambayar danai mata can kuma tace "Mom har yanxu fa princess bata dawo ba Takaici ne yakama ta, magana xatayi ya shigo palon hade da sallama, jacket suit dinsa rike a hannu. Mardiyya ce ta amsa fuska dauke da fara'ara tanai mai sannu da zuwa, mikewa tayi zuwa kitchen dauko mai abun sha. Zama yayi kan doguwar kujerar da mom ke zaune, gaidata ta yayi ta amsa ciki ciki. "Ina fatan bakaje bibiyar matsiyaciyar yarinyan nan ba" ta fada tana kallonsa. Amsar ruwan da mardiyya ta mike mai yayi ta koma ta zauna. Kai ya girgiza yana kallon Mom yace "nasan bakya kaunar ta, pls Mom kibar kiranta da matsiyaciya, she was once your daughter inlaw but not any more" Tashin hankali ne ya durar mata, cike da kidima tace "Bangane ba, inlaw as how. Maida da dubansa yayi bisa Tv dake kunne yace "ex wife ditace" Zabure wa Mom tay tsaye, cikin rawar jiki ta kwashe sa da gigitancen mari da saida Mardiyya ta kwalla ihu tsabar firgita. "Abdulrasheed ni zaka rainawa hankali, da izimin ubanwa ka aureta.." Cikin huci mom tayi magana. Ransa ya bacci matika, saidai bazai tsaya yi mata bayanin sanadin auran ba, dukda ba son Batul yake ba bazai fadi masu halinta da dalilin zuwanta gidan nan ba. murya mai dauke da bacin rai yace "it doesnt matter tunda nariga na saketa" mikewa yayi yahaura sama ba tare daya tsaya jiran abunda zata ceba. Rai bace Mom ta zauna tana huci, yaushen hakan ta faru bata da matsaniya, lailai kuwa Rasheed yayi betraying soyayyar da takemai, kallon Mardiyya tayi dako ajikinta saima remote dake hannuta tana canxa channel. "Waike wace irin dabbace, kinaji ya maki kishiya bada saninki ba amma ko ajikin ki" Mom tafadi cikin tsananin baccin rai. Ajiye remote din tayi ta dubeta sanan tace "Mom mi kikeso nayi, ihu da hauka dan kawai ya auri princess, d first time dana gansu tare nagane he truly loves her, shiyasa ban taba interfering da duk care da yake nuna mata ba" Harara Mom takai mata tace "sai yau nagane bakya son d'ana kin aureshi ne dan kudin sa" Murmushi Mardiyya tayi. "Ko daya wlh, as far a good wife kuma maison mijinta dole nayi supporting abunda yakeso, koda ace zai dawo da princess i"ll support him. Haushi da takaici ne suka cikata, miketa tayi hade da wurga mata pilo dake gurin tabar palon afusace. Cikin rashin damuwa Mardiyya ta mike ta nufi kitchen, fridge ta bude ta dauko ice dake leda ta fito ta haura sama. Ahankali ta tura kofar dakin ta shiga, zaune yake kan gado kansa dafe bisa hannusa, zama tayi kusa garesa hade da janye hannusa, dagowa yayi duban ta da idanuwan sa da suka sauya launi. "Sweetie kayi hakuri" ta fadi tanai dumama mai gurin marin da ice, shuru kadai yayi ya kwanto da kansa bisa kafadarta haunta daya na shafar mai baya. www.itzays.tk *** Washe gari daya tashi hankalinsa gabadaya yayi gurin Batul, ko breakfast bai ba ya wuce gidan, wayam yagani bata gidan kuma babu jakar kayanta. Hankali tashe ya fito yana tunanin ko su Baba sun iso ne ta koma can gidan da sassafe, da axama ya fada motan ya nufi gidan Baba nan ba basu dawo ba. Wayarsa ya fiddo yayi dailing no din Baba, buga daya ya dauko. Aladabce ya gaidasa. Baba ya amsa da fara'a Shuru yayi yama rasa mai xaice, katse shuru Baba yayi da cewa "Mamuda kaji mu shuru ko, dawowar bata yuyuba sai nan da sati uku saboda aikin noma daya rikeni" "Allah ya kaimu Baba" ya fadi cikin kokarin boye damuwarsa. "Ya matar taka ? Baba ya tambaya. "Kalau take" ya amsa agajarce. Sun jima suna waya da Baba daga bisani sukayi sallama. Iya kidima Rasheed yakai, tsoransa daya kar ace ta gudu wani gidan, number Daddy malam yahau trying, kusan sau biyu bizy, ana ukun ne yadauka. Rasheed yace "wai dawa kake wayane kusan rabin awa" Dariya yayi yace "inna ce fah, kasan jiya ta koma Zaria" Guntun tsaki yaja. "Miyasa Inna ta koma da kanta, naso ace nina maida ta Zaria dakai na". "Kunfi kusa, saika kirata kamata ya hanya" "Tukun nadai, nazo gidan banga Batul ba Dariya daddy malam yayi yace , "why do you care, ta tafi gidan su kenan". Bata rai Rasheed yayi yace "bata gidansu, so nake ka bincika min unguwan masu kudi ko Allah zaisa aganta sannan har kad poly ka je ka bincika min" Dariya sosai Dady yake babbakawa, "toh kadai yace mai" Rasheed ya katse wayan, can gidan da take ya koma ya zauna na kusan awanni biyar babu alamun ta. . Bayan kwana Uku *Zaria* . Abinci dake gabanta ta matsar gefe tana sharar kwalla, rashin nemanta ba karamin ci mata zuciya yake ba, all her tot xai dawo gareta, amma shuru ko inuwarsa bata gani ba, kuka sosai ta fashe dashi, rashin zuwan sa kadai ya nuna mata both Rmd da Mamudan basu da good heart kuma ba santa suke ba, itace kadai take wahalar da kanta, share kwalla tayi ta mike tana alwashin yakace sonshi aranta, tunda har baixo ba he is dead to her, gwara kawai ta cireshi aranta dan samun nutsuwa. Dakin Inna ta shiga ta sanyo Hijan ta fito gaban gidan inda Inna ke tuyar wainar, ga mutane da dama zagaye da ita suna jiran abasu. "Inna kawo" ta fadi tana amshen ludayin hannuta, Murmushi Inna ta sakar mata ganin yadda tayi maganar ba tare da kuka ba, tunda suka iso zaria bata da aiki saina kuka, asalima yauce rana ta farko data fito temakawa Inna, sabanin da saidai ta zauna gidin pampo tana kuka. Sakar mata Inna tayi ta mike zuwa cikin gidan dauko miyar wainar, zuciya daya Batula ta dage da juya waina a tanda, tuni masu miko kudi suka fara tana zuba masu, wani matashi ne ya karaso gurin yana fadin "jikar mai waina sako min na dari" ba masu ta amsa mai hade da zuba mai. Murmushi Inna tayi, tana daga gefe tana zuba miyar, mamaki sosai tayi da Batula bataji haushin sunan da yaron ya kirata dashi ba, sabanin ada saidai ta bisa da ashariyar an zubar mata da aji. Babu inda Rasheed da Daddy Malam basu nufa ba babu labarinta, sosai hankalinsa ya tashi, duk wayar da sukayi da Inna bata taba cemai Batul na tare da ita ba, shima bai mata xancen ba yasan ba yadda xaai Batul taje gidilanta. Sosai ya wahala ya gangara komawa gida. Handbag dinta dake ajiye kan gado Mardiyya ta dauka, sanye take cikin doguwar abaya ta yane kanta da babban mayafi, gurin takalma ta nufa da niyya sanya heel sai kuma ta fasa sakamakon dan kumbura da kafafunta sukayi, flat tadau tasa, ta sauko ahankali tayi waje gurin motarta, shiga tayi taja ta fice daga gidan, motar Abbanta taga yayo kwanar unguwar, mamaki sosai tayi saida bazata iya komawa gidan ba sakamakon appointment da take dashi da Doctor a asibiti. Jiki ba lak'a motarsa ta danno cikin gidan, parking yayi ya fito ya iske Motar Abba parke daga gefe, baiyi mamaki ba atunaninsa Mardiyya yazo gani. Cusa kai yayi cikin palon, harxai haura sama ya jiyo muryar Mom da Abban Mardiyya daga can Guess Parlour. Kaman xai wuce ya fasa, mamaki ne yakamasa, yasan Hajiya safara da Mom basu rabuwa da kuskus, yau kuma miya kawo mijinta gidan, karasawa yayi bakin kofar ya tsaya sauraran su. "Alhaji nasha gayama ka rabu dani danba auranka xanyi ba, yama zaai ace na aurin mijin aminiyata bazai yuyuba" acewar Mom. Nisawa yayi yace " amintakar ku ba hujja bace, gidanta daban naki daban" Murmushin dabai kai xuci ba ta saki, ta lura dai yana son ballo mata ruwa. "Bafa xan aure kaba" tafadi. Magiya da rokonta yahau yi, Mom kuwa ta k'ule dashi, dan kuwa bai kai matsayin da zata aure saba, tafi karfin sa. "Kai Alhaji ka bar batun auran nan, akwai igiyoyin aure akaina, kasa kuma baa aure kan aure". Kallon rashin fahimta yayi mata yace "kina da aurene, yaushe kika sake aure, bayan mutuwan Baba Rasheed" atare ya jero mata tambayan. Guntun tsaki taja cikin kagara da batun sa tace, "akwai Auran Baban rasheed a akaina Ware idanu yayi "Bangane ba, a aljanna ko a duniya, nasan mamaci baya dawo wa" Afusace Mom ta mike tsaye "Waikai baka da fahimta ne, nace ma auran Babban rasheed na rataye wiyana kuma yana nan da ransa bai mutu ba" cikin karaji ta karashe maganar. "What" Abban Mardiyya da Rasheed suka fadi atare cikin zare idanu. Karasa shigowa parlour Rasheed yayi yana kallon Mom da tuni tasha jinin jikinta. . www.itzays.tk . Daskarewa Rasheed yayi, tashin hankali da firgici shimfid'e bisa fuskar sa. Shi kansa Alhaji Bello ware idanu yayi yana sauraran karin bayani, kallan wulakanci tamai sannan tace "Alhaji ka fita idanu na, kaga adalilin nacin ka na furta abunda ba hakan bane, tunda kaki ganewa gwada nama b'aro b'aro, bana sonka dan Allah ka shafamin lapia". Hular kansa yahau gyarawa yana fadin "Allah ya baki hakuri, kinga tafiya ta" ficewa yayi daga palon batare daya jira cewarta ba. Ajiyar zuciya ta sauke ta maida dubanta ga Rasheed da itama kallonta yake "My boy dont mind my words, haushi yaban yasa na furta hakan, babu wani aure akaina" Cikin rashin gamsuwa da maganar yace "kince my Dad is alive" Kwantar da Murya tayi tace "bakaji nace kawai fada nayi ba, believe me your Dad is dead". Baice uffan ba ya fice parlour ba tare daya gamsu da abunda tace ba. Tunda har ta furtan hakan akwai kamshin gaskia ciki, idan ma koran Abba mardiyya take sonyi ai akwai oda strategies da zatayi using ba wannan ba. Main palon ya k'arasa ya zauna yana tunanin wazai tuntuba da batun yadda mutuwar Babansa ta kasance, kawu Habibu ne ya fadomai arai, tabbas shi d'aya zai iya fayyace mai ko Babansa nada rai koya mutu, duk azuci yake xancan, dafe kai yayi, gabadaya duniyar tamai zafi, bai gama nutsuwa da b'atan Batul ba ga wata gagaruma Mom ta janyo mai. Mikewa yayi da zama ya haura sama zuwa dakinsa. Freshen up ya shiga toilet yayi ya fito, ya shirya cikin kananun kaya, ya sauko kasa ya fice haraban gidan, motarsa yafada yaja zuwa home of hospitality (katsina). Cikin sa'a ya iske kawu habibu gida bai fita ba, gaisawa sosai sukayi daganan ya zayyano mai xancen dayaji Mom ta fada. Jinjina kai kawu Habibu yayi yace. "Tabbas abunda ta fadi ta fade sane kawai dan wata manufarta, amma kam Baban ka ya dade da rasuwa, tunshi kuma bata sake aure ba" D'aurewa kan Rasheed yayi da kalaman kawu, yakasa aminta da abunda suke fadi, shidai yasan akwai wata boyayyen al"amari dan jikinsa na fadi mai babansa na raye tunda Mom ta furta. Nisawa yayi yace "kawu miye sanadin mutuwar sa, kunyi mai jana'iza ? Girgiza kai yayi, yace "Bana nan sanda ya rasu, ina Ghana karatu lokacin, bayan na dawo Maman ka kece min ya jima da rasuwa, nayi kuka rashin sa ba kadan ba, tsohonka akwai halin kirki da daddako" "Allah yaji kanshi" Rasheed ya fadi asanyaye, saidai ayyada ya lura da xancen Kawu bai da matsaniya akan mutuwar Baba, same story da Mom tabasa shine wanda yasani, ba yadda ya iya dole ya nunawa kawu ya yadda da xancensa dan bazai iya mai masu ba. Sun dade suna hira daga bisani yamai sallama ya kamo hanyar dawo wa Kaduna. . *Zaria* 8.26pm . Iya karfinta ta sanya tana wanke shinkafa wainar gobe, daga can gefe Inna ke zaune tana yankar alaiyaho. "Ilimi akwai dadi, Inna nima dai xan shiga islamiyyar daran nan" Batul ta fada tana sauraran karatu dalibai dake tashin daga can islamiyar dake gaba dasu. Inna tace "Islamiyar akwai karantarwa, babu wasa sam, yaro kadai xan tura ya karbo maki form ki ciki gobe ki fara zuwa' Cikin jin dadi tace "nagode sosai Inna". Yaro ya shigo hade da sallama, amsawa sukayi yace "Nafi'u mai shayi ke sallama da jikar mai waina, yana waje" "Kai yaro koma kace bata fitowa" Inna ta fadi tanai zarowa yaro ido, tasan xaa rina sunga yar kyakyawa zasu fara damunta da k'wado sallama. Dakatar da Yaro Batul tayi tace "kace mai gani nan" Toh" yaro ya amsa ya fice. Kallon Inna tayi tashe, "inna kiyi hakuri naje, kinsan shi dan adam komin yadda yake ba abun wulakantawa bane, wannan abu ya faru akaina, banaso tarihi ya kuma maimaita kansa. Dariya Inna tayi, tace "gaskia ne, kije amma karki dade". Hijabin ta dake lankaye kan igiyar shanya tadau tasa ta fice wajan gidan. Tsaye ta iske shi, hannusa rike da bakar leda, jkinsa sanye da kodaddiyar tshirt da wando daga ganin wankan kure adaka yayi. "Ina wuni" ta fadi hade da sunne kai kasa, tasan dama saiya biyota, dazu dataje teburansa siyan biredi sai wani kirki yake mata. "Lapia kalau yammata" ya amsa. "Sunana fatima" tace Yace kiyi hakuri nakira ki da yammata, gaki da babban suna" Murmushi tayi tace "ba komai, ya kasuwa ? "Alhamdulilah" ya amsa mata. Shuru ne ya biyo baya, sai can kuma yace "fatima tunda naganki naji sonki araina, dan Allah ki bani dama na nuna maki tawa salon soyyayar. Murmushin dayafi kuka ciwo tayi, tuni ta cire so aranta, shi kuma gashi yaxo da kokan baransa, dago dakai tayi ta dubesa, Nafiu ba laifii dukda ba sonshi take ba tana iya aurensa, yana da kirki hankalinta zaifi kwanciya dashi. Nisawa tayi tace "nagode sosai da Soyayyar ka, Allah yasa hakan yafi alheri". Dadi sosai yaji ya mika mata ledar hannusa, kin amsa tayi, yace "ki karba, biredi ce na taho maki dashi" "A'a wlh ka barshi, so kake na cinye ma jarinka" Dariya yayi, ba yadda baiba ta karba taki amsa, hira kadan suka dan tab'a, tamai sallama ta koma gida, tuni Inna ta shige daki, zama tayi tsakar gidan tanai tunanin Baba da hajjon ta, kiransu take sonyi saidai wayar ma batasan a wace duniya ta yarba tsabar rawan jikin zuwa nema Rmd, ba mamaki ranar datai gudun nan Inna ta biyota wayar tafadi daga hannuta. www.itzays.tk ***** Washe gari cikin mayuwaci Hali Rasheed ya kasance, duk ya susuce, bini bini ya koma gidan can ko zaiga Batul amma wayam, ta bangaran Mom kuwa bai kuma tunkararta da zancen ba. Agajiye likis ya dawo gidan, dakinsa ya nufa ya iske Mardiyya na kokarin shimfuda bedsheet, saurin rikonsa tayi ganin yana kokarin faduwa. "Sweetie are you alright" ta fadi tana kokarin zaunar dashi kam sofa, "Am not" ya fadi cikin murya kaman xai kuka. Zama sukayi atare tace "plz ka gayamin matsalar ka na taimake ka, i hate seeing you like this" Ajiyar zuciya ya sauke yanai lumshe ido, murya kasa kasa yace "Diyya ki gayamin gaskia meke tsakanin Abbanki da Mom". Gabanta ne ya fadi, jin tambayar bambarakwai, "babu komai" ta fadi. Gyara zama yayi ya xayyane mata komai dayaji suna fadi. Mamaki sosai ya kamata wai abbanta da Mom so disgusting ma, yaushe ma Ummanta zata yadda hakan ta faru. "Amm sweetie kana ganin akwai kamshin gaskia babanka is alive" Yace "Am sure he is alive, babu dai wanda xai gayamin gaskia" Ajiyar zuciya ta sauke tace "i have an idea". Kallonta yayi. Gabanta na faduwa, tana tsoron fadi mai easy way dazai gano gaskia, saidai ayyanda yake bazata iya jure ganin sa cikin bakin ciki ba dole ta fadi dabarar dake ranta, amma tasan hakan na iya barazanar da auranta. Tace "sweetie kaje ka samu Umma, ita kadai ce tasan duk wata sirrin Mom, am sure zata gayama gaskia, idan har tace ma your Dad is dead you have to believe her, itace kadai hope dinmu yanxu" Murmshi yayi hade da riko hannuta yace "Diyyah you are smart saidai Hajiya Safara is smarter than you, kema kinsan ko sama da kasa zata hade she wont say a word" "I know she wont say a word, shiyasa zan fadima weak point dinta" Mikewa yayi kadan daga shigidan da yayi yana kallon ta. tace "hajiya safara nada matukar kishi marar mitsaltuwa, abu daya zaka gayamata she will blow out all abunda kakeson sani" Bakinta takai kunnan sa tamai rada danima banji ba. Yace "are you sure it will work ? Tace "trust me" Mikewa yayi tsaye yana fadin "i'll be back" ficewa yayi da axama. Numfasawa tayi, tana fadin "Allah yasa ban ballo wa kaina ruwa ba". , Bai zarce ko ina ba sai gidan Hajiya Safara dake unguwar Rimi, horn yayi mai gate ya bude, karasawa ciki yayi yay parking motar. Tunda daga window palon Hajiya Safara ta kyallarosa, Biebee dee mai aikinta ta kwallawa kira, da azama Biebee ta karaso hade da risina, "sirikina ya iso, maza dauko kayan sha da motsa baki ki kawo". "Toh Hajiya" Biebee ta fadi hade da juyawa zuwa kitchen, sosai take tsoron Hajiya shiyasa komai take kaffakaffa. Knocking yayi ta karasa ta bude mai kofar, fuskar ta dauke da fara'a "Auta momy yau kaine da kanka" ta fadi tanai washe baki. Gaida ta yayi fuska ba yabo ba fallasa sannan suka karasa kujera hade da zama. "Ya mardiyya, hope dai tana lapia" Kalau take, urgent magana ya kawoni" ya fadi atakaice. Cikin hankalta da nutsuwa ta kasa kunne saura ransa. "Umma ki gayamin gaskiA nasan kinsan komai, dagaske Babana na raye ?.. Dariya sosai ta fashe dashi tace "waya gayama shirman nan, toh idan ma mafarki kake ka farka, ubanka na karkashin kasa. Murmushi yayi ya kalleta yace "rumour naji agari, nima ban yadda ba". "Karma ka yadda, karya ce babban". Acewar Umma. Hira kadan suka taba cike da wasa da dariya daga bisani ya mike xai wuce, taka mai tayi zuwa bakin kofar ya juyo yana fadin "Umma Allah ya sanya alheri fah". Kallon rashin fahimta tamai Yacigaba "Abban yaje can gidanmu sun dade suna hira da Mom, ashe soyyaya suke, kwanannan ma zasuyi aure" cike da farin ciki ya karasa xancen, bai jira cewar taba yayi gurin motar sa. Daskakera Hajiya Safara tayi kaman kankara tsabar kidima da tashin hankali, jikinta har wani rawa ya dauka, hango Mom kadai take amatsayin kishiya, dafe kai tayi tsananin yadda kanta ke tsarawa, ita Fatima zatama zamba cikin aminci, sai yanxu tagane kallon da mijinta ke mata idan taxo gidan, bazai yuyuba, fatima kinyi kadan baki isa ba, duk azuciya take maganar. Cikin zafin nama ta karasa da sauri inda Rasheed ke tsaya yana kokarin bude motar. "Yana nan da ransa bai mutu ba" ta fadi cikin huci. Fasa bude motar yayi yana kallonta, hannuta ya riko yace "Umma yana ina, plz ki gayamin" Cike da baccin rai take magana. "yana garin Kaduna, saidai bansan a ina yake ba, kaine kasan inda yake"... Kallon rashin fahimta yayi mata. Tace "yarinyar da Mom ta tarar a gida she is your sister, babanta shine mahaifinka"... Rasheed kam ya gama rudewa, wace yarinyar take nufi badai Altine mai aikin suba. Tacigaba "ranar daka fadi mata fatima ex wife dinka ce she was very devastated, fatan ta daya Allah yasa auratayya bai shiga tsakanin kuba".. Iya gigita Rasheed yakai yama kasa gane wace Fatima take nufi, Haunnsa ta rike gam tana fadin "yarinyar nan princess kanwar kace ta jini" Wani mugun kara ya kwalla wanda gabadaya gidan saida ya amsa, cikin rawar jiki ya saki hannuta ya fada motar yaja ta afusace. Dogon tsaki Hajiya Safara taja aranta tace "no i messes with my husband" afusace ta juya tayi cikin parlour, garara raf sukayi da Biebee dake rike da jug da ruwa, wani wawan mari Hajiya safara ta kai mata sannan ta wuce daki. Jikin rawar jiki biebee ta durkusa tsince glass daya fashe. . Gudu yake shararawa harya karaso gidan, ko parking motar bai iyayi dakyau ba, ya fito cike da kidema ya shiga gidan, Mardiyya ya iske zaune Palo, ko kallanta baiba ya fada dakin Mom agigice, kwance take kan gado ganin yadda ya faddo cikin dakin yasata razana hade da mike tsaye. Durkusowa yayi gabanta, cikin muryar kuka da tuni ya sarke sa yace "Mom y, miyasa kika min karya babana ya mutu, wosrt part of it princess kanwatace, kinsani baki gayamin" Wani mugun mari ta kwashe shi dashi, tace "ni nake maka karya, a gidan ubanwa ka jiyo labarin nan". Bai damu da mari ba, yace "hajiya safara ta gayamin, kuma nasan datx the truth". Gabanta ne yafadi jin ya ambaci Safara, lailai kuwa itace babu wanda yasan da hakan sai ita, amma kinci amanata safara, mu zuba nidake, duk azuci take magana. Karyarta ta kare dole ta fadi mai gaskia ayita ta kare, dagosa tayi kan gadon sannan ta zauna gefen sa suna fuskanta juna. "My boy kayi hakuri, i did all that to protect you, your father was cruel, he never appreciate us" Kuka ta fashe dashi, hannuta ya riko "mom cigaba sai miya faru ? Tsayar da kukan tayi tace "rabuwa yayi damu adalilin matar daya auro, Mahaifiyar so called princess, My boy d first day dana ganta yasa nayi kokarin tabar gidan cox banason past dinmu yazo yana hunting dinmu, plz stay away from her" Kuka sosai ya fashe dashi yan hango fuskar Baba wai shine mahaifinsa, saidai halinsa da Mom ta fadi he isnt buying it a bit, babban tashin hankalinsa bai wuce na cewa Batul kanwar shice ba, bai taba jin sonta ba sai yanxu da yaji wai kanwar shice, wani irin sister love game da ita ke ratsa mai gangar jiki da zuciya. Yace "Mom ki temake ni, Princess is missing, duk fadin kaduna na bincika ban ganta ba" ya fadi yana kuka, ido jajir. Lallashi sa tahau yi tanai kara basa hakuri. Karasa shigowa Mardiyya tayi da tuni tana tsaye bakin kofar, kuka take ta nufosa, Mugun tsawa Mom ta daga mata hade da mikewa tsaye "You have overstayed your welcome, pack your tinx ki barmin gidana" Ko kallanta mardiyya batai ba tacigaba da takowa gurinsa, kafin ta kara taku daya tuni Mom tayi taku biyu uku takai mata gigitaccen marin da yayi baraxanar sanya jinin gabobin jikinta daskarewa. Ihu ta saki tsabar raradi, kallon Rasheed tayi da bai san abunda ke faruwa ba, kuka kawai yake yana kiran sunan princess..... . www.itzays.tk . Gabad'aya baya cikin hayyacinsa, jin ihu mardiyya akaro na biyu yasa shi dawo wa hayyacin sa, bakin kofa ya ganta Mom na kokarin turata waje. "Sai kin bar gidan nan tunda bana ubanki bane" Mom ke fadi cikin daga murya. Mikewa yayi ya karasa gurin. "Mom plz calm down, xata bar gidan yanxu nan" Kallon mardiyya yayi da har yanxu bata bar kuka ba, yace "bakiji abunda tace ba, wuce ki hada kayanki" Kasa cewa uffan Mardiyya tayi saima kara sautin kuka da tayi ta bar gurin da azama, mara mata baya yayi ya fice daga dakin. Dogon Ajiyar zuciya Mom ta sauke ta koma gado ta zaune hade da dafe kanta tsabar takaici, Hajiya Safara idan kinsan wata baki san wata ba, nayi danasani gaya miki sirri na, saidai akwai certain things da baki sani ba. K'wafa tayi, yazama dole tadau mataki akan Batul, dan bazata yadda danta ya kara auro bata, just jini daya da tace suke duk yabi ya rikici, she wonders ya zayi idan yagano ba kanwarsa ta jini bace, duk azuci take magana. Tunanin ranar data fara ganin Batul ta shiga yii... . Tuna Baya (Flashback) Shekaru Shida da suka wuce. . Daidai round about ta kasuwar checheniya ta cikin jahar Kaduna ta hango sa daga can gefen titi suna loda kwandan kayan miyan cikin keken Napep, Gabanta na ya fadi, madubin fuskata dake nane bisa idanuwan ta cire cike da mamakin kara ganin sa, kusan shekaru ashirin da bakwai rabon ta da sashi a idanu sai yau tun bayan rubuwa da tayi dashi a katsina. Saidai ganin data mai ya tsofe ba kamar da ba, keken taga ya shiga matuk'in yaja su suka tafi. Saurin tada motar ta tayi zuciyar ta na azalzalarta ta bishi taga ina zai nufa, can cikin unguwar kawo taga keke ya nufa, tsayawa yayi daidai wani gidan bulo da babu sementi, daga cen nesa tayi parking tana kyallarosa. Kyakyawan Yarinyar yar kimanin shekaru sha biyu taga ta fito gidan, jikin sanye da kayan makaranta na islamiya, gaida sa tayi ya fiddo naira ashirin ya bata sannan ta wuce, sai kuma maza biyu masu kama taga sun fito, suma sanye da kayan makarantar, gaidasa sukayi suka wuce. . Duk akan idonta, karaso wa Satin Motar ta yarinyar tayi natai karewa motar kallo, baa ganin wanda ke ciki kasancewar ta tinted, nan Mom ta samu daman kare mata kallo sakamakon hannu datasa tana taba motar cike da sha'awar ta, "Batula munyi latti fah" Hassan ya fadi yana juyowa baya dan tuni sun yi gaba" Guntun tsaki taja tace "oh ni fatima, yaron nan bazai daina kirana batula ba" ruguwa tayi tanai ihu su jirata. Maida dubanta Mom tayi zuwa gurinsa saidai tuni ya shige gida, mai keken ma baya gurin, dogon tsaki taja hade da buga steering, taso ace ta samu details akanshi, reverse tayi kokarin yi taga wani dattijo ya shiga gidan ya fito cikin sakanni kalilan rike da kwandan albasa, ganinsa tayi ya karasa wani teburi hade da ajiye albasan akai Saurin jan motar tayi garesa, sannan tayi wining glass. "Sannu" ta fadi Washe baki abokin Baba mai suna Lamido yayi, tambayarsa tayi nawa kwando albarsa, yace da ita dubu da dariya biyar, dubu biyu ta fiddo tabasa hade da barmai cancin, godiya sosai yayi. Tace "naga wani da kayan miya ya shiga can gidan, waye shi ? Dariya lamido yayi "muhammadu ne shine mai teburin ai, nazo ne kafin ya karaso" Murmushi dabai kai zuci ba Mom tayi tace, "ayyo, naga yaran sun fito daga gidan yanxu, halan yayan sane" Lamido yace "su yan biyu ba, hassan da hussaini yaran sane" K'wafa Mom tayi, aranta tana fadin wato shi aure yayi ita tana can igiyoyin akanta, afili tace "naga wata yarinya tare dasu, wace ita. "Yar'sa ce ta fari" Gabanta ne ya fadi. Yacigaba "bayan mutuwar danuwan sa ya auri uwar yarinyar wato ikilima, kinga kuwa shine ubanta kuma amatsayin yarsa ta fari". Bata cira cewar saba taja motar afusace tabar gurin, wani mugun tsanar sa da yaran taji azuciyar ta, ba mamaki Ikilima matar kaninsa Ahmadu ya aura, sunyi zaman gida daya dasu a kauyan kafin hausa, kuma zaman baiyi dadi ba, dan alokacin basa shiri da Ahmadu ko kadan dan baya daukan raini daga baya ne ma tafara girmama shi Amma toh yaushe rasu, ta tambayi kanta... Rai bace ta koma gida ba tare data fadiwo kowa xancen ba. Saidai abunda bata sani ba bayan Baba yaxo lamido bai boye mai komai ba ya fadi mai yadda sukayi hade da kwatanta mai Mom, tsaf baba ya gane itace, cikin rashin damuwa ya cigaba da tsafgogin sa. Dogon Tsaki Mom taja bayan ta dawo daga doguwar tunanin data lulA, mikewa tsaye tayi tana kai komo a tsakiya dakin, zacen zuci take. "Dole na nemo Batul duk inda ta shiga a fadin duniyar nan kafin My boy ya ganta, i have to deal with her kafin nakai ga ubanta, amma ta ina zan samu phone number dinta balle nasa a binciko min ita" Tunanin mafita tahau yi, can dabara nemo wayar Rasheed ya fado mata tasan bazai rasa nambar taba, cikin azama ta fice palon da niyan hawa sama ta hango wayoyinza jefe kan kujera, dauka tayi da zama, babu lock ko code tayi azaman shiga contact bincike, tsaf ta duba babu contact mai suna Batul, fatima ko princess, tsaki taja dabarar shiga maajiyar hotuna ta fado mata, cikin saa kuwa tana shiga taga pic dinta kwance kan kujerar parlour tana bacci da alamun ma batasan ya dauka ba, daukar wayar tayi ta shiga daki ta tura hoton wayarta sannan ta dawo parlour ta ajiye mai tasa wayar. Dakin ta koma cike da muguyan manufa aranta. . Gabadaya kayanta Mardiyya ta kwashe tasanya akwati, kuka kawai take ta caza ma kanta saidai still bata blaming mijinta, atleast she is happy tunda ya gano baban sa is alive da kuma sister daya jima yana fatan ace yana dashi. Bude kofar dakin tayi sukayi kicibis zai shigo. "Muje yace da ita, hade da karban dayan daka cikin trolley da take rike dashi. Kallonsa take kamar zatayi kuka ganin dayan hannusa ruke da nasa akwati. "Sweetie ka bari kawai na tafi, kayi hakuri ka zauna da mom she really needs you". Kai ya girgiza, "Diyyah muje kawai, it high time mubar mata gidanta, for 33 year nake tsugunne da ita, this time kuma i need some space" ya fadi hade da sauko wa, binsa tayi a abaya har suka sauko, wayoyinsa dake parlour yadauka, suka fice daga Parlour. Ma'ajiyar mota suka nufa, ya bude butt ya sanya kayan suka shiga mota yabar gidan. Tuki yake yana trying numban Baba da dayan hannusa, saidai not reachable kadai yakeji, kusan sau wajan goma abun daya suke maimaita mai, tsaki yayi hade da wulla wayarvbaya, yasan Mom bazata mai Karya ba sai dai yadda tace Baba ne ya rabu dasu bai yadda koda k'wayan zarra ba, definitely saiko itace ta rabu dashi dan yana talaka, ayadda yaji labarin Mom tana karama yar gata ce sosai kuma babanta mai bala'in kudin ne, it doesn't make sense ace shi yayi abandoning dinsu, for wat reason, buga steering yayi cikin tsanin bacin rai, rashin sanin inda Batul take ba karamin konamai zuciya yake ba, ita kadai yakeson gani koya ji sanyin a zuciyar sa, yasan itama bazata rasa sanin wani abu game da auran baba da Mom ba. Haka dai suka karaso maidaidecin gidansa mai dauke da daki biyu da palo, parking sukayi ya sauko cero masu kayansu, dakyar Mardiyya ta samu ta fito daga motar, taku daya biyu tayi, taji tana neman faduwa, sauri taro ta yayi dan kuwa kiris ya rage bata je kasa. "Are u alright" ya fadin yanai kallonta, itama kallonsa take saida ta kasa furta koda kalma daya. "Muje ciki" yace da ita, kasa takawa tayi yayi saurin cicibarta suka shiga ciki, dakin ya shiga ya direta kan gado yanai mata sannu. "Diyyah kodai muje asibiti" Kai ta girgiza kafin yayi wata maganar tuni ta rufe idanu, bacci yayi gaba da ita Shafe gefen fuskarta yayi yana jiyo numfashin ta dake fita ahankali, cike da tausayinta ya janyo comforta dake gurin ya lullube ta, yasan kukan data yi yasa tazama exhausted. . Shuru dataji yasa Mom fitowa parlon, haurawa sama tayi ta leka Dakin Mardiyya, babu ita balle kayanta, murmushin jin dadi tayi ta karasa dakin Rasheed, wayam ta gani babu kayansa sai wata takarta data gani da rubutu, an ijeye kan gado. Dauka tayi ta bude, tahau karanta abunda ke ciki. "Am sorry Mom, banda zabi daya wuce nabi matata mubar miki gidanki, burina daya na nemo duk inda princess take although she is my sister i won't stop loving her, dukda da diyar kishiyar ki ce, i hope wataran zaki sanyawa zuciyar ki so da kaunar ta. Love you Mom" Squeezing takardar tayi hade da wurgi dashi tana huci, wayarta dake hannuta ta duba hade da dialling wata number, bugu daya aka dauka Tace "Roze kaga picture dana ma sending ? Cikin muryarsa ta yan daba yace "Nagani, na miye ne ? "Roze yarinyar nake so ku nemo ku kawo min ita dead or alive" Dariya yayi yace "angama hajiya, yanxu xan tura yara parade duk inda take zasu ganta. "Make sure duk wata kauye da birni na kaduna ku bincika, Yarona is desperately searching for her, make sure ku kawo min ita kafin ya ganta". "Ba matsala Hajiya, muna da branch ko wana gari, duk inda take zamu ganta. Katse wayan Mom tayi tana huci, afili tace "saura ke Safara, i have unfinished business dake" afusace tabar dakin. Mayafi kadai da car key ta dauka ta fice waje, motarta ta shiga taja zuwa gidan Hajiya safara cikin fusata. As usual, daga window Hajiya safara taga dirar motar Mom, fito tayi da azama zuwa farfajiyan gidan sukayi kicibis. "Munafuka maciya amana, kwadayayya, duk hallacin danai miki haka zaki sakamin " mom ke fadi cikin daga murya. Harara hajiya safara takai mata, tace "karuwan banza kin dauka bansan bibiyar mijina kike ba, idan ni mai kwadayi ce ke kuma karuwa ce" Hannu Mom tasa ta wanke ta da mari, "Kika mareni" Hajiya safara ta fadi kin shock. Kokuwa ce ta barke tsakanin su, da gudu Biebee dee dake labe bakin kofa ta fito tanai rabasu, dakyar tasamu ta janye Hajiya safara da tuni tafara jigata. Cikin huci mom tace "zaki ci ubanki, saina nuna miki ni ba tsarar ki bace" juyawa tayi ta koma motarta. Zagi sosai Hajiya safara take lailayo mata, dakyar Biebee taja ta suka koma parlour cike da mamaki aminan juna yau sune da zage zage da bankadawa juna asiri, jinjina kai tayi, azuci tace "aminantaka akwai dadi, saidai duk yadda kake da mutum ba ko wana sirrin ka zaka fadi mai ba, koba jima koba dade akwai shaidan yana iya shiga tsakanin ku, daganan kuwa fallasan asirin ya biyo baya, love all but trust no one" (ni xarah nace maganarki dutse.) . Fitowa Mom tayi tare da parking gefen titi, tunanin kadai take yadda zata rama betrayal da aminiyarta tai mata, sai yanxu takejin haushi fadi mata komai nata alhalin ita bata taba gayamata komai game da ita ba, dogon tsaki taja tana karason tuno wani abu da zatai using against her, abu daya ta dade tana son sani game da Hajiya Safara shine "source of her income (asalin dukiyar ta)" asali Alhaji Bello talakane, Mardiyya nada shekaru biyar aduniya hajiya safara ta koma Ghana gaisuwar rasuwar Babanta, bayan wata shida ta dawo amatsyin mai kudi, abu daya tace masu wai gadon Ubanta ne, kadarorin daya bari ta siyar ta dawo Nigeria. K'wafa Mom tayi tana kara fadin "babanki talakane, asalima talauci ya kawo ki nigeria har muka hadu a skull din da kika shigo amatsayin yan alfarma, i know you're hiding something, amma miye ne ? Ajiyar zuciyar ta sauke ta kunna motar ta karasa gida. **** Bayan kwana biu. Rasheed da Daddy Malam basu bar neman Batul ba, sune har Abuja zuwa nemanta, aganinsu can garin Manya ne kila can ta nufa, ba hope haka suka dawo kaduna. Ta bangaran Mutanan Mom su Roze suma basu fasa baza idanu ba, akullum saita ninka masu kudi da zata masu idan har suka gano ta, sosai suka fantama yin aikin su. . *Zaria* . Juya wainar take cikin hankali da kwarewa, masu siya sai siya suke, wani yaro ne ya miko kudi. "Gashi inji Nafiu wai kisamai ta hamsin" Toh" Batul ta fadi hade da amsan kudi tana murmushi. "Shiga cikin gida ka dauko min kwano" tace da yaron. Kwanon ya dauko ya bata, ta zubamai harda miya tare da karamai da nama. "Gashi ka kai, kace ina gaida sai, karya manta da dare idan na dawo islamiyya zamu hadu" ta fadi tare da mikama yaron kwano, amsa yayi da toh sannan ya wuce. "Mu kenan bazaa a samana a kwano ba sai leda" wata yarinya dage gurin ke magana. Dariya kawai Batul tayi tasan zolayar ta take. "Ke jikan mai waina sako min ta dari" wani matashi dan Tasha ke fadin haka cikin daga murya. Daure fuska tayi, koda wasa taga iri irin su b'ata rai take, "kawo kudi" ta fadi. Hannu yasa aljihu yana kokarin ciro kudin tare da kare mata kallo, fasa ciro kudin yayi, ya ciro wayarsa kirar Techno yana kallon hoton ta dage cikin wayar, kusan minti biyu yayi yana compare and contrast din fuskar ta dana hoton, babu tantama yagano ita dince, fasa siya yayi yabar gurin, lungun ya samu ya kira ogansu na gurin ya shaida mai yaganta, nan take suka ajiye plan din cafketa da dare. . Kaduna . Cikin sauri ya fito daga dakin, kitchen ya nufa inda yaji motsi Mardiyya. "Diyyah na fita" yace da ita. "Sweetie ina kuma, dazu kawai fa kadawo" "Kin manta we are still searching for princess" Kallon rashin fahimta tamai "Wace princess? Gira sa ya daga yanai kallonta, yace "Sister inlaw dinki" Still bata gane ba, ganin zata b'ata mai lokaci yasa yabar gurin. Dafe kai tayi tace "Allah ya bayyanaki Princess" Rasheed dake labe bakin kofa yana jinta, recently haka take behaving so confused anjima kuma ta koma normal, bai kawo komai aransa ba ya fice ya shiga mota yabar gida. . Daddy malam ya kira awaya suka hadu a hanya ya daukesa suka bazama da shiga unguwanni neman ta, daddy malam kam ya fara gajiya da abu daya babu hope, shawarar zuwan gidan redio da talabijan y kawo, ba masu Rasheed ya yadda dan shima ya dade da tunanin haka. Juya kan motar yayi zuwa hanyar da zata sadasu da gidan labarai. Wayar Daddy ce tayi rurri, dubawa yayi yaga Inna, cike da fara'a ya dauka suka gaisa, Tace "wato ka manta ni ko? "Haba kakus zanxo kwanan nan, aiki ne yamin yawa" ya fadi. "Wana aiki ni xaisa kaki xuwa" Inna ta fadi atakaice. Yace "Batula ce ta b'ata, shine fa muke yawon nemanta haryau babu labarinta" Salati Inna ta saki, tace "Batula ai muna tare, ta jima a Zaria" Cike da mamaki yace "batula na gidan ki" Wani mugun burki Rasheed yaja tamkar yaji maganar da suke, karbe wayar yayi yace "Inna gani nan zuwa" katsewa yayi hade da saurin yin reverse. "Nidai sauki ne na koma gida, nabar Maman Aryan ita daya" Daddy malam ya fada yana dariya. Tsayar da motan yayi ba tare daya kallesa ba. Daddy yace "ka bari gobe sai muje, yanxu fa Magrib tayi" Harara ya kai ma "kaidai sauka kawai". Sauka yayi yana Dariya. Rasheed yaja motar, massallacin hanya ya tsaya yayi Sallah sannan ya buga motar to zaria, cikin mintina ashirin da biyar har ya iso, a gurguce ya fito ya shiga gidan. Inna na zaune tsakar gida tana jan jarbi ya shigo, zama yayi jiran ta sallame sannan ya gaida ta, cike da faraa ta amsa mai. "Inna ina Batul take ? Dariya tayi. Daure fuska yayi atunaninsa wasa take mai "Bata nan, taje islamiya, sai tara zasu tashi". Ware idanu yayi, wai batula a islamiya, mikewa yayi yanai tambayarta ina islamiyar take, nan ta kwatantamai na bisa bakin titi. Da azama ya fice, bakin gate din islamiyar ya tsaya cike da farin cikin xai ganta, agogon hannusa ya duba just 20 minti ya rage su tashi. karamar kofa dake bayan Islamiyar suke tsaye daga can nesa. "Ka tabbata tanan take biyowa idan suka tashi" "Eh, ta nan ne, yafi kusa da gida da take azama" Matsawa gefe su hudun sukayi jiran ta fito su chapke ta. Cikin sa'a Batul ta fito daga karamar kofar, tafe take hankalin kwance tanai kara tilawar karatun da Malama Sophie ta koyar su, takun data ji abayanta yasata waiwayawa da sauri, wayam tagani babu kowa, gabanta ne yahau dukan uku uku, cikin sauri takara daga kafafunta tanai waiwayan bayan, kamar daga sama taga gardi biyu tsaye a gabanta, kafin ta juya tuni biyu su tsaya daga baya sun zagaye ta. Murmushi Rasheed yake baki yaki rufuwa, yan mata da samari sai fitiwa suke daga gate din, ware ido kadai yake yana jiran fitowar little Sister dinshi.....
0 comments:
Post a Comment