INA ZAN GANSHI Part 04
INA ZAN GANSHI Paru 04 . Zazzab'i mai zafin gaske ta kwana dashi ba tare da runtsawar kirki ba, har kusan 11 tana lullub'e cikin bargo bata sauko breakfast ba. Turo kofar dakin Mardiyya tayi hade da sallamA, can ta hango ta dunk'ule karshen gado tana freezing, karasawa bakin gado tayi da axama ta yane bargon. "Princess baki da lafiya". Hannu takai bisa jikinta, zafi rau taji tayi azaman cire hannun. kuka Batul ta fashe dashi ta riko hannuta, "Sister Mardy dan Allah ki temakeni nabar gidan" "Haba princes keda bakya cikin hankalinki taya zaki ce haka, kiyi haukari har memories dinki ya dawo nayi alkawarin maida ki masarautar ki dakaina" Kuka sosai Ta kuma fashewa dashii, tayi dana sanin ce masu tayi loosing memories gashi tana son barin gidan sunki yadda, lallashi da ban baki Mardiyya tahau bata, dakyar tabar kuka bayan Mardiyya ta ce mata zata kaita asibiti, dadi taji aranta tafara tunanin yadda zata tsere daga can. Zaune yake parlour yana sipping coffe dake rike hannusa cikin mug, Tv dake kunne yake kallan labaran duniya. Cikin takun sauri mai dauke da tashin hankali ta sauko, dayan daga cikin kujerar ta nufa lalubar mukullin motar ta data cilla gurin. "sweetie princess bata jin dadi, zan kaita asibiti" ta fadi tanai cigaba da laluban ta, ganin mukulli tayi ta juyo tana fadin, "barin dauko ta" taku daya biyu tayi da niyyan haurawa saman taji ya kira sunan ta, tsayawa tayi tanai kallonsa, bai kalleta taba, fuskar sa na bisa Tv yace "babu asibitin da zakuje" "Sweetie dan Allah ka bari muje, she needs a Doctor" "Diyyah" ya kira sunanta a tsawace, kallonta yayi fuska daure. "naje baza kuba, koma ki zauna" Tuni Mardiyya ta tsorata, ya rikide mata ainihin Mr Rasheed din data sani, "Adalilin Mene (Ummi Jay) zai mata tsawa" ta fadi axuciyanta, jiki ba laka ta taka kujerar dayake zaune ta zauna gefe dashi adan rukube. Wayarsa ya fiddo ya kira Doctor Ramalurv sukayi magana sannan ya katse. Shuru ne ya ratsa sakanin su, kowa da abunda yake sakawa a zuciyarsa, bayan minti sha biyar Doctor Ramalurv ta karaso gidan, gaisawa sukayi ya mike rakata dakin Batul. Kwance take tanai jiran shigowar Mardiyya, ganinsa ya banko kofar dakin yasa ta razane "Shigo Dr" yace da Ramalurv da take biye dashi abaya. Saurin rufe idanu tayi kaman mai bAcci amma tuni yasan ba baccin take ba, taba jikinta da aune aune Doctor tayi sannan tA rubuta mata magungunan bukata ta mika mai takarda, tana fadin "Mura ya haddasa mata zazzabi, for now dole ta kiyaye amfani da ruwan sanyi" "Okay" ya fadi hade da godiya, bai karbi takarda ba yace ta baiya mardiyya dake kasa taje ta siyo, sallama sukayi ta sauka kasa. . Mardiyya bata kawo komai aranta ba ta amshi takardar ta fice zuwa pharmacy da azama. Jin alamun shuru yasa Batul bude idanu, karaf sukayi ido hudu dashi, tsaye yake yana kallon ta hannuwansa biyu bisa kirjinsa yayi folding. Murya can kasa yace "princess ya jikin ki ? Karashe magana yayi hade da zama kan gadon, fuskokin su na fuskantar juna. Janye jikinta tayi gefe tana kara lullubewa, ba karamin shayinsa take yi ba, sai kace bashi yajaza mata zazzabin ba. "Da sauki" ta amsa mai cikin murya kaman zatayi kuka. Hannu yasa ya cire bargon, yarage daka ita sai karamin nitie dake jikinta, saurin takurewa tayi gurin guda hade da kawar dakai gefe, tsoron ta daya karya dawo mata da batun tambayarsa, adiriganta awanni sha hudu suka rage ta bashi amsa, saidai har yanxu batasan abunda zata fadi maiba. "Tashi kiyi wanka" yace ita Raurau tayi da idanu "Sanyi nake ji" Cikin zafin nama ya mike hade da sunkutar ta zuwa toilet, kuka ta fashe dashi tanai rokansa, atunanin ta abunda yay mata jiya zai sake, dire ta yayi, yahada warm toilet cikin jacuzzi. Kallanta yayi yace "Baza ki shiga ba saina turaka ciki" "Zan shiga" ta fadi hade da rabawa ta gabansa, taba ruwan tayi taji da dumi sannan ta kalle sa "dan Allah ka fita" Harara yakai mata "kina gamawa make sure kizo down stairs breakfast" Kai da girgiza alaman eh, ya juya ya fice daga dakin. Yunin ranar yar gata ta zama daga shi har Mardiyya lallbata suke, duk abu da takeso shi sukeyi, kokarin kame kanta kadai take gudu kar gata yayi yawa tafara wuce gona da iri, atleast Rasheed ya kyaleta bai kuma mata batun komai, opportunity kadai take nema ta fice tabar gidan saidai ta lura babu daman hakan saboda tight security na gidan, babban tashin hankali shine idan ta koma gida mai zata ce da Mamuda da Inna, dan kuwa karyarta takare, asalima karya ce ta sanya ta cikin ukubar da take ciki ayanxu. Washe gari, guraran biyu na ranar taga anata dafe dafe da gyaran ko ina na gidan, Mardiyya sai up and down take tana aikace aikace sai kusan 5 taga sun kammala. Mamaki kecin ta, tarasa wanda zata tambaya what the occasion is all about, tana daga parlour ta k'wallawa Altine, da azama tazo hade da dukawa kasa. "Altine yimin tausa" ta fadi. "Toh ranki shi dade" Altine ta fada tana washe baki, tausar tahau yi mata cikin kwarewa da hazaka. Tambayar ta takeso yi amma ta kasa, dakyar dai tasamu courage din tambayar ta ko bakine zasu zo. Kara washe Baki Altine tayi tace "Momy ce xata dawo, mahaifiyar mai gidan" Ware idanu Batul tayi, gabanta na dukan Uku uku, fatan ta daya Allah yasa matar mai saukin kaice, indai ta biyo danta a mugunta lailai kuwa kashin ta ya bushe. . K'arfe shida motar Mom ta diran agidan, ajiyar zuciya mai dauke da relief ta sauke tana shakar sanyayyiyar iskar dake bazama a farfajiyan gidan. Cikin takun takama ta k'arasa takawa bakin kofar parlour gidan cike da mamakin Altine batazo tarbar taba Turo kofar palon tayi ta kusa ciki kai batare da tayi sallama ba. "Altine" ta kira sunanta ganin ta duk'e tanai ma Batul tausa, duk atunanin Mom mardiyya ke kwance gurin, ganin Mardiyya na sauko wa daga stairs fuska dauke da fara'ar yasa ta karasa shiga cikin palon. "Sannu da zuwa Mom" Mardiyya ta fadi Yauwa" Mom ta amsa cikin k'aguwa da ganin waye hakinci kan kujerar palon gidanta. "Bak'uwa mukayi" Ta fadi tanai kallon Batul dake kokarin mikewa zauna tana sosa idanu, dan tuni bacci ya kwashe ta jin surutu yasata farkawa. Ido hudu sukayi tayi azaman mikewa tsaye adan firgice. "Ina wuni, sannu da zuwa" ta fada murya sarke, gabanta na faduwa sakamakon gane Mom da tayi wace ce ta k'irata da almajira a fountain Mansion. Kallon wulakanci Mom ke mata, aranta tanai fadin "wanne ne karo na uku da take ganin yarinyar nan, amma miya kawo ta gidan nan" Afili tace "wace ke, daga ina, gurin wa kika zo" atare ta jeho mata tambayoyin, fuska ba annuri. Caraf Mardiyya ta amshe dacewa " tayi loosing memories dinta, abu daya mukasani game da ita shine she is a princess" Murmushin dabai kai zuci ba ba Mom tayi, tace "Princess my foot, dayake baku da hankali wannan tayi kaman da princess, she looks more like a Gold digger" Shuru Batul tayi kaman ruwa ya cinyeta, fisgo ta Mom tayi da karfin gaske ta rike ta kam, cikin karaji da zare idanu tace "Nawa kikeso nabaki ki fita daga rayuwar mu, kinsan dai nasanki, duk wani cunning moves dinki bazai yi aiki akai naba" Fashewa da kuka Batul tayi dan ba karamin riko tayi mata ba, ita ba kudi takeso ba asalima idan zaa bude mata gate fecewa zatayi, saidai mamaki take yadda Mom ta ganeta so easily, dan ko ranar dinner ba wani kallon k'urilla tayi mata ba. Matsowa Mardiyya tayi ta cire hannun ta daga mugun riko datai mata, tace "plz Mom kiyi hakuri ki barta, bata da isheshen lapia, ina kika santa ? Nisawa Mom tayi. "bansanta ba, all i know is saita bar gidan nan yanxu" ta fadi hade da kara riko hannuta, janta tayi bakin kofar palon hade da hankada ta waje ta fada jikinsa dayake kokarin shigowa. "Mom"ya kira sunanta cike da baccun rai, yasan zaa rina yasa yaketa sauri danya iso gidan unfortunately traffic jam ya tsayar shi. "For goodness sake Mom mai tayi miki daga zuwanki? Ya fadi yanai rike da ita suka shigo ciki, kuka sosai Batul take, taga samu taga rashin da tuni ta ware. Dogon surutune bazata iya ba, balle akan matsiyaciyar yarinyar nan, abu daya tasani shine bazata bari ta zauna mata gida ba, kallonsu tayi tana girgiza kai, aranta tana fadin bazai yuyuba, almajira da danta over her dead body" batace uffan ba ta wuce dakinta dake nan kasan, hand bag dinta ta dire tadau wayarta ta kira Hajiya Safara, sun jima suna magana sannan ta katse cike da tsananin baci rai. "Hope bata ji miki ciwo ba" ya fadi yana k'arewa jikinta kallo, kai ta daka mai bata bar kukan ba, yace "kiyi shuru banaso kuka, very soon zaki bar gidannan kinji" "Okay" ta fada araunane. Nufasa Mardiyya tayi tace "Sweetie kodai na kaita gidan Umma ta zauna".. Kallan baki da hankali yayi mata, yadda ya tsani Hajiya Safara ko makiyinsa bazai kai gidan ba, balle ma Batul, dukda ba sonta yake ba taci albarkacin mahaifinta. "babu inda zata" ya fada atakaice, janta yayi suka haura sama, Mardiyya ta bisu da kallo zuciyar ta na zayyano mata abubuwa iri iri. Da dare kowa daban yaci abunci adakinsa, daka ga su hudun kasan basa cikin walwala, kowa da abunda yake sakawa aransa. Da safe Mom ce tafara zama dinning yin breakfast sannan Mardiyya da Rasheed suka sauko, gaida ta sukayi ta amsa da fara'arta tamkar ba abunda ya faru, "My Boy kayi resuming work ? "Not yet" ya fada fuska ba yabo ba fallasa. "Allah kaimu" . "Amin" ya amsa agajarce. Serving dinsa Mardiyya tayi suka fara ci atsanake. Altine ta karaso rike da plate ta dibi abincin xata wuce, Mom ta dakatar da ita da cewa "ke, ina zakije da abincin nan?" Altine tace "Aunty princess xan kaiwa"? Takaici ne ya cikata, kalmar princess da suke ambata yana mugun kona mata rai, "ajiye ki wuce aikinki" ta fadi. Ajiyewa altine tayi tabar gurin. Mikewa yayi hade da daukan abincinsa yabar gurin batare daya kallesu ba yahaura sama. Tsaki Mom taja hade da dangwarar da spoon din hannuta, kallon Mardiyya tayi da itama kallonta take, tace "ban taba ganin shasha kamar kiba, da wayewar ki da komai kalli yadda mijinki ke tashi zaune kam shegia yarinyar can amma ko aji kinki" Galala Mardiya tayi tana kollanta tace "ni banga wani abu acikiba, shi yayi causing accident dinta so kinga dole ya damu da ita" Harara takai mata, "jiya daya ke rungume da ita duk damuwar ce komi ? Shuru Mardiyya tayi tana gasgata xancen. Mom tacigaba, "dole musa hannu tare musan yadda tabar gidan nan" Ware idanu tayi. "Mi yayi zafi haka, plz mom ki bari tayi regaining memories dinta, nidai ba hannuna ciki, dama keda Umma kun saba kulle kullen ku nidai bada niba". Gwab'e mata baki Mom tayi tamike tana cewa "wawiyar yarinya" Turo baki Mardiyya tayi tanai gunguni, itadai bata ga wani abu tattare da princess ba da akeson barin ta gidan, asalima tausayi take bata. . Tsaye take tsakiyar dakin tanai kaiwa da komowa jikinta sanye da yar figiyar rigar bacci, sak'a da warwara na abunda zata fada mai take, shawara daya ta yanke na fadi mai gaskiyar wace ce ita, idan har ta fadi hakan kadai xaisa yabarta tabar gidan asauwake. Turo kofar dakin ne yasata ta dan firgita, shigowa yayi fuska murtuke. Jiki na rawa ta tadau zani ta daura tana fadin "ina kwana". Bai amsa ba ya mika mana plate din hannusa, "bana jin yunwa" ta fadi araunane bata da niyyan amsa, mugun kallo ya kai mata ba shiri ta amsa hade da matsawa lungun gado ta zauna.. Zama yayi kan Sofan dakin hade da shigidewa, fuskarsa na kallon sama. Kasa cin abinci tayi tanai jujjuya spoon din hannuta, so take ta gayamai amma tana tsoro, dakyar tasamu courage ta mike tadau mayafi ta karasa gabansa ta zauna. "Dan Allah kayi hakuri ka barni na tafi " Yana jinta bai tanka ba saima runtse ido da yayi kaman mai bacci. Taci gaba, "niba yar kowa bace agarin nan, asalima karya nayi dana ce ni jinin sarauta ce". Ko motsi Rasheed bai yiba banda kasa kunne dayayi yana sauraranta. Bata boye komai na rayuwarta taba ta kwashe ta fadi mai sannan ta hada da cewa "ina son mijina dan Allah ka barni na tafi na nemin gafarsa" Karasa magana tayi cikin shesheka, shuru ne ya ratsa sakanin su na mintina biyar sannan ya bude ido yanai mata kallon mamaki. "Princess yaushe kika iso nan, kukan mi kike, kiin gama cin abinci ? Ya fadi murya kasa kasa kaman wanda ya farka daga bacci. . Gabanta ne ya fadi, badai baiji abunda tace ba, murya sarkake tace, "ban gama bama" Mugun kallon yakai mata, cikin tsawa yace "zaki tashi anan ko saina mare ki" Tsum ta mike, tanason tambayarsa ko yaji amma tana tsoro ganin yadda ya daure fuska. Mikewa yayi ya fice daga dakin tanai binsan da kallon bakin ciki da takaici, ajiye plate din tayi gefe tana rusa kuka. Office dinsa na cikin gidan ya nufa ya zaune hade dafe kansa, maganar zuci yake. what next, tunda tayi confessing, shidai ba sonta yake ba balle ya cigaba da zama da ita. K'wafa yayi yana yana neman mafita, chance daya zai bata tayi proving kanta, idan har batayi ba he has no choice daya wuce ya rabu da ita for good. Kusan awa hudu ya kwashe gurin yana sake sake, daga can palon kasa yafara jiyo hayaniya kamar ya share sai kuma yafasa sakamakon muryar Mom daya jiyo tana tsine tsine. . Fitowa yayi da azama ya iske yan sanda kusan goma tsaye a Parlour Mom na yi masu bayani cikin daga murya, Mardiyya na tsaye gefe tana sauraran ta. "Make faruwa ne" ya fadi yana kallon Mom, "Sata akamin acikin gidannan" Kallon ta yake ya kasa gasgata xancen, miyasa tunda baai sata ba sai yanxu daga zuwanta. "Miye aka dauka" "Sabon Gold earring dana zo dashi is missing" cikin huci ta karashe maganar, kallon yan sanda tayi tace "kuyi searching ko ina na gidan including the rooms" "Toh hajiya" suka fadi atare hade da fara dube dube. Murya kasa kasa yace "Mom miyasa baki gayamin an miki sata ba zakiyi alerting police" Harara takai mai, "Nayi laifi saika dakeni" Matsawa tayi can gefe batare data tsaya saurarasan ba, Mardiyya ce ta matso garesa tace "cikin mudai ba barawo, i tink ko Mom tayi misplacing earring din wani gurin". Shuru kawai yayi baice komai ba, yasan drama ne kawai Mom take babu wani Gold dinta da aka sace. "Muje sama, kuyi checking duka dakunan" Mum ta fadi tanai masu jagoran hawan saman, da azama yabi bayansu yana fadin "mom dan Allah ki bari, i will get you a new one" Banza tayi dashi suka karasa hawa, direct dakin da Batul take suka fantsama ciki, ran Rasheed ya baci matuka, dadin abun ma bata dakin tana toilet tana wanka, bakin kofar toilet din yaja tsaya gudun karta fito su ganta. . "Lungu lungun da sako ku tabbata kun duba, cox i dont trust her" Mom ke magana ayayinda yan sanda sai biincike da bude bude suke, itadai Mardiyya kallon su take cike da haushi, dan kuwa bazata bari ama dakinta iskancin nan ma. Daga pilo daya daga cikin yan sanda yayi saiga dankareriyar earing na gold shumfide gurin , dauka yayi yana fadin "hajiya wanan ne? Kwarai kuwa shine" ta fada hade da dafe kirjin cike da mamaki" Ta kuma cewa "Dpo tana wanka, ku shiga bandaki ku kamata karta gudu" Mamaki ne yakama Rasheed, wanan wana irin abune Mom dinsa keyi haka, yasan Batul da karya badai sata ba, idan ma sata tayi how com ta sace one earring, wata zuciyar tacemai it can be possible mayb siyawar xatayi tayi kudin data ta jima tana mafarki zama mai kudi. saurin kawar da tunanin yayi yana girgiza kai. "Mom dan Allah kiyi hakuri, nasan bakison zaman princess agidan nan, insha Allah yanxu zatabar miki gida". Mugun kallon ta jefasa dashi. " idan na barta taci bulus kenan, bai xai yuyuba dole hukuma su yanke mata hukuncin daya dace da ita koda ma ace yanke hannuwan ta xa suyi" Dafe kai yayi cike da tashin hankali, yace "xan yanke mata hukunci da kaima, dan Allah Mom ki sallami yan sandan nan" kamar xaiyi kuka ya karashe maganar. Tausayi yabata saidai kuma bazata iya hakuri so called princess ta zauna mata a gida ba, kallon police tayi ta sallamesu hade da ce masu zata bukace if needed. Fita sukayi ta mara masu baya hade da hararar Mardiyya dake tsaye tsuru tsuru. Zuciya daya ta fito tana kakkabe ruwan gashin ganta, jikinta daure da towel, ganinsa datayi bakin kofar yasata azama komawa ciki, da sauri yasa hannu ya riko gashin kanta hade da finciko ta waje, ware idanu tayi tanai kokorin kwace kanta, Mardiyya dake tsaye ta shigemai gaba, "sweetie plz calm down, trust me nasan ba ita ta dauka ba" Ido jajir ya kalleta, turera gefe yayi yana fadin "stay out of this." Jan Batul yayi suka fice daga dakin ayayinda take mai magiyan ya saketa. Ran Mardiyya ya sosu, ina xai kaita ahakan daba kaya jikinta, binsa tayi abaya, kafin takai ga karasa wa dakinsa tuni ya shige da Batul ya banko kofar da karfin gaske. Gabanta na dukan uku uku ta makale jikin kofar hade da dasa kunne tana sauraran abunda zai wakana. Wurgi yayi da ita kan gado har kanta yana buguwa, zaburewa tayi ta mike zaune, atunanin ta ko fade zai mata yasata kara susucewa "Dan Allah kayi hakuri" ta fadi cikin murya kuka. Iya kuluwa yakai, koma miye Mom dinsa tayi mata itace sila, Fuska ba annuri yazaro belt dake cikin closet. Zama yayi bisa kujera dake dakin yan fuskan tar ta. "Zonan" yace da ita. Mikewa tayi tsaya cikin rawar jiki ta nufesa. Kawar dakai gefe yayi yace "On our kneels" Astorace tayi axaman ijiye gwiwowin ta kasa tana kara basa hakuri. Daga belt din sama yayi hade da mikar da ita sannan ya kalleta. "Miyasa kika sacewa Mom Gold earring dinta" Tsuru tayi dan bata fahimci inda xancen sa ya dosa ba. "wana Gold" ta fadi cikin shesheka. Tashin yayi yakai mata bugu daya, tuni ta bankare hade da kwalla uban ihu. Rutse Idanu Mardiyya tayi, bazata jure abunda kunnanta ke saurara ba, bugun dataji yay mata tamkar ajikinta taji sa, barin gurin tayi cike da tsananin tashin hankali ta sauka zuwa dakin Mom. . Zare mata idanu yayi yace "ki gayamin gaskia, nasan ke kika sace ? Kuka sosai take tana fadin bata dau komai ba, rufe idanu yayi ya dinga dukan ta iya son ransa sannan ya kuma tambayanta "ke kika dauko, Yes or no ? Hawaye kadai take iya zubdawa, tuni karfin ihun ta yakare, ta lura idan ba cewa tayi itace ta dauka ba bazai kale taba "Yes nina dauka" ta fadi cikin hopless murya. Cikin rashin damuwa da yanayin yace "Good, abunda nakeson ji kenan" Saida ya kara bugunta sau uku sannan yayi cille da belt ya shiga toilet. Ko kwakwara motsi ta kasa, zubar kwalla kadai take tana kallon farin fatar jikinta daya sha tabon laftar daya yi mata, "duk adalili mene" ta tambayin kanta, bakin halinta na rashin wadatar zuci, biyyayyar iyaye, kwadayi da neman duniya ya janyo mata, Sata da bata taba yiba yau an k'alamata tasha duka abanxa, sai yau ta kara gasgata xance bature dayace All that glitters is not Gold, shedan yakaita ya barota, kaso abu ya zama shairin ka, kuka sosai take tasan ukubar ta bai kare ba idan Baba da Hajjo suka san abunda ta aikatawa kanta. Amma mijinta Mamuda fah mai zatace dashi, abun kunya nema ace da auranta tazo gidan wani namiji da zama, duk a zuci take fadin hakan. Tsaye yayi gaban mirror dake toilet din, idonsa jajir yanai zubda hawaye mai cike da bacin rai, ji yake tamkar ya cire hannusa yayar tsabar yadda yake jin haushin bugun da yay mata akan laifin da bata aikataba. Hannusa yakai ya bugi madubin da karfin gaske ya tarwatse, jini sosai yafara malalowa daga hannusa, dafe hannu yayi jikin bango yana kuka cike da wani yanayin marar fasara, tunanin kadai yake ya zaiyi tabar gidan, dabarace ta fado masa ya dauki karamin hand towel dake gurin ya lullube hanusa dake tsiyaya da jini ya fice daga bandakin, nan tsugunne ya ganta inda ya barta baice kala ba ya fice daga dakin. . Banko kofar dakin Mardiyya tayi ta k'usa kai ciki, Mom na zaune tana karatun Newpapers taganta tsaye fuska ba annuri. "Mom kije tsoron Allah, bakya tunanin ki mutu da alhakin princess akanki, am 100 percent sure ke kikayi plotting komai" Mikewa Mom tayi tsaye ta nufo, "ni kike gayawa magana kamar wata saarki" Mari Mom ta kwashe ta dashi kafin takai ga bata amsa. Kuka ta fashe dashi hade da dafe kuncin ta. "Zaki ci ubanki ne" Mom ta fadi hade da daukan waya ta kira Hajiya Safara, magana sukayi sannan ta mikawa Mardiyya wayan. "Hello, Umma" ta fadi cikin shesheka. Ashariya Hajiya Safara tahau lailayo mata cikin masifa tace "Mardiyya ki shiga taitayinki, am trying to secure your future kina can kina hauka, idan nazo gidan nan zaki ci ubanki ne, yar banxa yarinya marar wayo. "Umma nifa bance komai ba, nidai injustice ne banaso, makirci da kuke plotting da Mom bazai amfane ni da komai ba saidai ya kashe min aure" duk cikin kuka take fadin hakan, bata jira cewar Umma ba ta mikawa Mom wayar, amsa tayi cikin zafin nama ta dasa a kunne suka cigaba da magana sannan ta katse. Mugun kallo tama mardiyya tace "Rasheed da nane, koda kin gayamai nice nayi plotting komai, bazai yadda dake ba cox he loves me alot more than yadda kike tunanin, tun muna mu biyu ki lallaba bakin ki kiyi shuru, yarinyar nan da kike siding she is a big treat to our lives, am warning you stay away from her" Karaf a kunna Rasheed dayake kokarin shigowa dakin, fasa shiga yayi, yabi hanyar fita waje da azama cike da mamaki kalaman Mom, ina tasan Batul da har take ikirarin treat, kawar da xancen yayi dan ba wannan ne ya damesa ba, Batul kadai yakeso tabar gidan tun kafin Mom ta illata ta. Ma'ajiyar motoci ya nufa yashiga mota yaja, bakin gate ya karaso yace da security subarta ta fice idan ta fito sanna yaja yabar gidan, tuki yake yana kara jajjadawa kansa last chance kadai ya rage ma Batul, idan har tayi loosing he has no choice other than to leave her. Kuka sosai Mardiyya takeyi, fitowa tayi daga dakin ta haura sama zuwa dakin. Zama tayi hade da tagumi tana tunanin wana abu mamanta da maman mijinke ke aikatawa, koma miye tasan babu alheri cikinsa. Dakyar ta iya mikewa, dafe bango tayi ta karasa dakin ta, zani da hijabi kadai ta dauka ta sanya jikinta, barin gidan kawai zatayi koda ace ta fence ne, ahankali tasamu ta sauka taci saa ba kowa palon tayi saurin rugawa waje, tun kafin takai ga isa bakin gate din taga an wangale mata, atunanin ta wata motace zata shigo, ba tare da bata lokaci ba tayi sauri ruguwa ta fice daga gidan. . Cab ta gani pake gurin da azama ta fada tanai fadin mai unguwar da zai kaita, bai tsaya ciniki da ita ba, yaja motar, da isar su, fitowa tayi, cikin sheshek'a ta tambayesa nawa kudi, "oga ya biya" ya fada had'e dajan motar yayi gaba. Mamaki da faduwar gaba ne suka diran mata. "kodai Rmd yaga fitar tane" ta fadi a zuciyar ta. Kallon kofar gidan tayi tana tunanin makomarta, wani sabon kuka ne ya kufce mata dakyar ta iya samu courage din tura kofar langalangar ta k'usa kai ciki gidan hade da sallama. Zaune yake a tsakar gida bisa tabarma, kunnen sa nad'e da radio yana sauraro, jikinsa sanye da koriyar yadi da bakar hula bisa kansa, sauraran radio yake cikin nishadi da annashuwa. Ciki ciki ya amsa, ba tare daya dago kansa dake kollan k'asa ba. Arakub'e ta karaso gabansa hade da tsugunna wa, dukar dakai kasa tayi, kasa kallon sa tayi tsabar kunya shi dataji ya diran mata, ko adama ba wani k'are mai kallo take ba tsanin yadda take k'insa, yanxu data fara sonshi kunyar abunda tayi ya hanata ta dagowa. K'ara sautin kukan tayi tace "Sannu da zuwa" Dago dakai yayi ya dube ta sannan yace "Nina dace da miki sannu da zuwa, ya duniyar fatan dai kin samo abunda kikeso ko dayake amsa takardar ki ya dawo dake" Kai ta girgiza hade da riko hannunsa. "Mamuda dan Allah kayi hakuri ka yafemin" Dan k'ara ya saki kadan tsabar azaban yadda ta matse mai tafin hannunsa. . Saurin sakin hannu tayi sakamakon jinin da taga yana diga, cike da kid'ima ta ciro hijab dinta tahau kulle gurin dake yanke. Bruises din jikinta ya kalla yana kara jin haushi kansa, hannu yakai gurin yana fadin "Batula miya same ki haka ? Tsigarr jikinta ne ya tashi, ga wani uban radadi da gurin kemata. "faduwa nayi" ta fadi cikin matsananci kuka, mikewa tayi da axama ta fada cikin dakinta, kuka sosai take tana tunanin yadda xata fadimai gaskia, saidai tsoro take karya rabu da ita. Jinjina kai yayi yasan zaa rina, shi kuma yadau alwashin idan bata fadi mai gaskia halin data shiga ba bazai cigaba da kasancewa tare da ita ba. Mikewa yayi hade da cire hijab din dake kulle hannusa ya fice daga gidan zuwa pharmacy dan samun cikekken treatment. Sallamar Almajiri ce ta katse mata kukan da take, hijab dake ghanarta ta ciro ta sanya sannan ta fito, mika mata ledar kayan miya da danyar shikafa yayi yana cewa maigidan ya aiko sa, amsa tayi sannan ta roki almajirin ya dibo mata ruwa a burtsatse, ba musu ya dauki bokitai dake gurin ya fice waje. Tun shigowarta bata lura da dakin Inna dake datse da k'wad'o ba sai yanxu da hankalinta yakai gurin, jiki mace ta nufi Bakin murhu aza wuta. Har bayan sallah isha bai dawo ba, dan abinci data ajiye mai cikin samira tuni tayi sanyi, kara aza wuta tayi ta dumama sannan ta zauna bakin kofar dakinta jiran dawo warsa cikin tagumi. . Mikewa Mardiyya tayi dakyar ta karasa gaban drawer, janyowa tayi ta ciro magunguna kusan kala hudu sannan ta balle ko wanne tasha ta kora da ruwa dake rike hannuta a glass cup. Jiri sosai takeji, ta jima bata jita jikin yanayin ba, tsabar kuka da tayi ke barazanar janyo mata zazzabi, Shuru har dare bata ji motsin Saba atunaninta ko yana office, dakin Batul tuni ta duba bata cikin, kayanta data gani yasa tayi tsammanin ko ta shiga toilet gasa jiki dan tuni ta leka dakinsa babu kowa. Dakin Batul ta nufa, wayam ba labarinta, toilet ta leka babu ita balle alamun danshin ruwa, cike da tashin hankali ta nufi dakinsa nan ma ba alamun bil'adama ciki, tura kofar toilet tayi ta shuga, saidai jinin da broken mirror data gani yasata girgiza, azaman tsaftace gurin tayi cike da mamaki abunda ya faru, fatan ta daya kar ya zamana Rasheed ya jima princess ciwo agarin bugunta. Fitowa tayi ta leka office baya ciki, daki ta koma tadau wayarta tahau kiran sa no response. Saukowa kasa tayi ta nufi dakin Mom dake kwance kan gado tana kallon tashar Aljazeera a Tv, ganin Mardiyya ta fado dakin yasata daure fuska. "Mom banga princess ba kuma Rasheed baya gida" akideme take maganar. Tsaki Mom taja, tuni taga ficewa Batul da gudu ta window dakinta. "Ta koma gidan Ubanta" ta fadi. Ware idanu Mardiyya tayi tace "mom badai kin kore taba, kinsan dai Rasheed bazai ji dadi ba" K'wafa Mom tayi Tace "Mardiyya ki shiga taitayin ki, kinsa dai auran nan naki nice nayi insisting, Rasheed ba sonki yake ba". Anzo gun, b'ata rai Mardiyya tayi, yau ita Mom kema gori, batace uffan ba ta juyawa zata bar dakin. "Rasheed ba karamin yaro bane, he has the right to sleep duk inda yakeso dan bai dawo ba dat doesnt me ki hana kanki bacci" Mom ta fadi cikin kota kula da yanayin ta. Karasa ficewa Mardiyya tayi cike da kunin rai, dakinta ta nufa ta kwanta cike da tunanin yadda rayuwarta zata kasance gaba. Karfe sha daya Rasheed ya dawo gidan da Batul take, leka dakin yayi yaganta makure can karshen bango tana bacci, tabarmar dake jingine yadau ya warwareta hade da shimfuda ta, kwanciya yayi kai yana tunanin bazai iya kwana agidan ba, asalima ya dawo yaga lafiyar tane. . Motsin dataji yasata farkawa, mikewa tayi ta fito rike da samirar abincin, gidan duhu ko haske babu banda haske farin wata daya gauraye gurin, karasa tayi inda yake kwance, ta durkusa aladabce, cikin sanyin Murya tace "ga abinci" "Na koshi" yafada ataikace. "Dan Allah kaci" Banxa yayi da ita bai tanka ma, idan yayi magana mai tsawo tana iya dago muryar sa. Ajiye abincin tayi gefe, ta kwanta kan tabarmar dan nesa dashi suna fuskantar juna. shuru sukayi na dan sakwanni kowa da abunda yake sakawa aranshi. Ajiyar zuciya ya sauke yace "Batula ina kikaje ranar da kika bar gidan nan ? Gabanta ne ya fadi, tace "Ranar dana fita wani mutum ne ya kadeni da mota yakaini gidan sa da matarsa mai kirki, shine nayi masu karyar ni yar sarki ce na manta komai, barina sukayi na zauna a gidan shine kuma yau na dawo, Nasan nayi kuskure dan Allah ka yafemin" cikin muryar kuka ta karase maganar. "Cigaba" ya fadi. Shuru Batula tayi tana tunanin gayamai abubuwan daya faru tsakaninta da RMD, tsoro takeji sosai, mudin yasani tasan rubuwa xaiyi da ita, bazata fadimai ba amma tayi alkawarin gayamai nan gaba idan ya fara sonta. Cikin shesheka tace "Shikenan abunda ya faru" "Kin tabbata abunda ya faru kenan, babu ragi babu kari ? Kuka sosai ta kufce dashi tace "eh na tabbata". Numfasawa yayi yace "gobe zamu je inda xan yanke maki hukunci" "Dan Allah kaiyi hakuri ka yanke min ko wana hukunci amma karka rabu dani, i cnt leave without you" sosai take kuka. Hannu yakai bisa fukarta yace "ki kwantar da hankalin ki" Tsayar da kukan tayi, tana feelling hannusa dake bisa fuskarta. "Good nyt" ya fadi hade da cire hannusa. Lumshe ido tayi tana mai jin dadin kasan cewa tare dashi. **** Washe gari data farka tuni ya rigata tashi ya fice masallaci sallah asubah, Murmushi tayi data jima bata yiba, kama ruwa tayi sannan tayi alwala ta shige dakin gabatar da Sallah. Karfe bakwai shuru bai dawo ba, tashi tayi ta kyalyale gidan fes sannan ta dubama shinkafar ta sanya asamira ta ajiye jiran dawowarsa. Sai kusan sha daya saura ya dawo, tana daga dakin ta jiyo dirar mota agaban gidan, gabanta ne yafadi atunanita RMD ya biyota, hijab ta dauka ta sanya, fitowan ta tsakar gidan yayi da daidai shigowar sa, bata kallesa ba tasan shine sakamakon kyakyawan kafarsa data kalla, Risina wa tayi tace "ina kwana Bai amsa ba ya riko hannuta zuwa waje, ganin dankareriYAR jeep parke agurin yasata firgita, saurin tirjewa tayi tana fadin "Mamuda ina zaka kaini" Bude bayan motan yayi ya turata ciki ya rufe sannan yashiga gaban mazaunin banxa ya zauna. Gabanta ne ya fadin Ganin wani daban ke tuka motar, tsoronta daya kar ya zamana gidan RmD zasu nufa. "Gidan zamuje ?" Daddy malam ya fadi yana kokarin tayar da motan.. "Eh, hurry up inason zuwa office" Rasheed ya fadi cikin muryar sa na ainihi. Ware idanu Batul tayi jin Mamuda na batun office, bama wannan ba Muryar sa sounds familiar, tsananta bugun gabanta yayi har suka karasa madaidaicin gidan Rmd na ainihi wanda babu mai zama ciki sai shi idan ya tashi b'adda kama. Parking Daddy malam yayi a farfajiyan Gidan, sauka Rasheed yayi ya bude side dinta, ta fito yayi gaba ta mara mai baya cike da tashin hankali da tunani kala kala. Parlour ya bude ya shiga, ta shigo ta rakube gefe, zama yayi bisa kujera yanai kallon yadda tayi tsuru tsuru. "Zonan ki zauna" yace mata yanai mata nuni da kujerar dake fuskantar sa. Karasa tayi ta zauna fuska duke. Yace "Dago ki kalle ni" Ahankali ta tago tana kallan sa, "kin gane ni ? Daga kai tayi alamar eh sannan tace "mamuda ne mai keke Napep" Murmushi yayi dan kuwa ta basa dariya. Mustache din fuskarsa ya cire ya kuma tambayanta kota ganesa, kura mai idanu tayi yaso yayi kama da Rmd amma tasan bashi bane. "Baki gane niba bako princess ?" Jin kalamansa tayi tamkar saukar aradu, mikewa tayi cike da tashin hankali tana kallon sa. Daure fuska yayi yace "to show how stupid you are kin kasa tantance mutum daya with two different identity" Kai ta girgiza, it cant ba possible, tayama xaace mutum daya ne, sai yau takarewa Mamuda kallo bammanci su da Rmd mi haske ne da muryarsa daya canxa. Daddy Malam ne ya shigon Parlour, kallonsa yayi hade da mikewa tsaye yace "Make sure bata gudu ba, she is really good at it" shigewa daki yayi ya nufi toilet. Kuka Batul ta fashe dashi zuciyar ta na azalzalanta da bashi bane, plan ne kawai ake son rena mata wayo, amma Mamudan ta ba Rmd bane. . Bayan 30 min ya fito sanye da Grey suit, kyakyawar fatarsa sai kyalle take, yayi kyau matika, binsa tayi da idanu har ya zauna. Cikin kuka tace "i dont believe you, nasan Mamuda is somewhere around, dan Allah ka fito dashi Cikin ko in kula da yamayinta yace "I dont own you any explanation, na baki chance jiya still baki gayamin gaskia ba, it seems you will never stop been a liar, ajininki yake" Kallonsa take tana gasgata lailai shine, amma miyasa xaiyi playing dinta haka, tasan both mamuda da Rmd tana sonsu miyasa shi ya boye mata kanshi, lailai ramin karya kurarre ne, all this while da mutum guda take zauna tana sharo mai karya akan wanda batama sani ba, duk azuciyan ta take fadin haka. Takadda ya ciro daga aljihunsa yana fadin "burinki Mamadu ya sake ki, gashi yau ya cika maki" mika mata takarda yayi taki amsa saima sautin kuka data kara, cilla mata yayi bisa fuska tasa hannu ta bude. Saki daya taga yayi mata, wani irin ihu ta kurma tanai rokonsa, Mugun kallo yakai mata yace "tashi ki fita na sallameki", rokonsa sosai tayi akan ya janye sakin, tsawa ya daga mata ba shiri ta mike tsaya cike da kidema, hanyar kofar tayi taji yana fadin "kina iya kwana a gidan for today, gobe saiki tattara ki koma gidanku saboda suma iyayenki goben zasu dawo daga kauye, saiki saurarun jiran hukuncin su" Bata iya tanka saba ta cusa kai tayi waje, tashin hankali mai tsananin ke tattare da ita, idan har Baba yayi hakuri ya barta tasan Hajjo ba zata barta da rai ba, kuka sosai take wani irin mugun son Rmd da Mamuda ke fuzgarta lokaci guda, ita kanta ta kasa tantance wata fiso acikin su. Kallonsa Daddy Malam yayi cike da tausayin Batul yace "she loves you alot, kayi hakuri ka maida ta, " Mikewa Rasheed yayi cikin rashin damuwa yace "am late for work" bai jira cewar Daddy ba ya tsuri mukulin mota dake ajiye ya fice daga parlour.
0 comments:
Post a Comment