AGOLA Page 26-30
.
Al,amin yana sauka london suka hadu da abokinshin yana jiranshi a air pot. Direct gidan shi suka wuce, bayan yayi wanka yayi sallah, yaci abinci. Anan suka fara tsara yanda zasu dauko Jidda. Duk da abokin Al,amin ba musulmi bane amma yana da riko da addininsu, kuma yanada gaskiya, sunanshi Daniel, kum makwabcin Joseph ne, sede halinsu kwata kwata badaya bane. Kwanan Al,amin 2 suna lura da duk wani shige da ficen Joseph. Jiran lokaci kawai sukeyi su shiga gidan, ko so daya bega Jidda ba, hakan ya tabbatar mashi baya barinta fita.
Ginin su Sameer har ankusa gamawa, fenti kawai akeyi, Sameer beda lokaci kullum yana plaza ko gurin masu gini. Falak tayi kyau sosai, idan kaganta baza kace Falak din daka sani bace, takara girma, kyawunta yakara fitowa. Yanzu babu abinda kedamunta, se tunanin Dadynsu Jalila, kullum cikin yimashi addu,a take.
Kuma Baba mairo tace kada suje gidan se nan dawani lokaci. Zamansu da Sameer zamane na mutunta juna, suna bala,in son junansu, Sameer bayasan ganin bacin ran Falak, itama haka, kasancewarta mace me hakuri kuma tasamu miji me hakuri. Haryanzu akwai sauran kudinta a account, ko naira Sameer yafitar seyayi mata bayanin abinda akai da ita, har fushi tayi mashi akan abinda yake mata amma yaki bari, yace haka shine gaskiya. Dole tahakura badan taso ba.
.
Ajikin gidansu yasa akayi shaguna guda biyu, yace na Falak ne ze zub mata kaya asamu me tsare mata, musamman da unguwar basuda irin shagon saida kayayyaki haka.
Baba mairo da Umman Sameer hankalinsu kwance suke sana,arsu cike da girmama juna, dan Baba mairo ta girmi Halima sosai, dan ita Halima bawani tsufa tayi ba, kawai de halin rayuwa ne yamaidata babba, amma yanzu da kwanciyar hankali tafara zuwa masu tuni tafara maida jikinta. Duk wata shawara dazasuyi Baba mairo suke kawo ma ita, idan kuma abun yafi karfinsu, Kawun Sameer suke kaima ita.
Zarah ce zaune adakin Asabe, bayan sungama gaisawa, tace waini Inna haryanzu shiru babu Jidda, nifa hankalina yafara tashi, kawai ina cikin kwanciyar hankali yarinyar nan zata sani cikin damuwa, aduniyar nan babu abinda ke damuna se rashin sanin inda Jidda take, tun Alh, yana tambayata ina mashi karya har nafara gajiya.
Jiya yake cemun zezo har nan yatafi da ita, kuma idan har bata fitar da mijin aure ba, duk wanda yasamu zebama ita. Shine nazo dan Allah kirakani gurin boka yaduba mun inda take, kotana raye, kuma arufema Alh, baki yadena maganarta, kota dawo kada yatambayeta inda taje.
Asabe tace gaskiya ni kaina abun yana damuna, kuma kinga idan haryagane bata gidan nan muze zarga, gara muje arufe mashi baki kawai. Ita kuma nasan duk inda take zata dawo. Malam dayake bakin kofa yana jinsu yashigo, ya kalli, Asabe, duk da yanajin tsoronta, amm wannan karon seda yayi magana.
Yanzu ke Asabe kina ganin abinda kikesa yarinyar nan tanayi dede ne? Na dade ina jin duk wani abu da kukeyi akan bawan Allan nan, wai seyaushe zaku tuba kudena abinda kukeyi? Kadafa ku manta akwai wata rayuwa bayan an mutu, kum kowa ze tsaya agaban Allah yafadi abinda yayi, wanda aranar baki baze iya magana ba, saboda shima makaryaci ne. Ke kuma Zarah abinda nakeso dake kiji tsoron Allah, kina ganide tun aduniya yafara nuna maki ishara, akan diyarki, yanzu Allah kadai yasan inda take, kuma duk inda take, ba halin kwarai take aikatawa ba.
Nasha ganinta da manyan mutane suna sauketa kofar gidan nan, amma dayake baku daukeni abakin komai ba, bakwajin maganata, yaude nafada maku iya gaskiyata, idan harkunji to, idan kuma bakuji ba, wlh inaji maku tsoron ranar danasani, ranar da babu lokacin gyara barnar da kukayi.
.
Zarah ta zunburo baki tace wai kai Baba mekaga munyi? Nifa wlh banason takura, dama naga duk sanda nazo gidan nan labe kake mana, kuma kana nufin Inna Asabe ita zata cuceni ne, ko gorin haihuwa zaka mata? Kuma ni nasan babu abinda Jiddata take aikatawa se alheri, kawai de kanamun bakin cikin yanda na auri me kudi, itama tasamu. Kuma mekaji munce zamuyima Alh?
Inna Asabe tace ai gara ke dayake diyarshi ce kifada mashi, wato Malam yanzu duk irin rikon danayima Zarah beyi maka ba? Lallai nayarda da,akace namiji ba dan goyo bane, to ai kadeji da kunnanka, abinda diyar taka tace. Kuma wlh wannan shine karo na karshe da zakaji muna magana kashigo kasa mana baki. Wuce kabani guri, namiji da akai kana halin mata. Allah yabaki hakuri ammade Zarah kiji tsoron duniya, kuma ni kike fadama magana. Kije duniyace ta isheki komai, wanda bezo bama jiranshi takeyi.
Dallan can kawuce kabamu guri, fita yayi yana matsar kwalla, wai yau diyar daya haiface take fadamashi magana. Asabe tace aikinyi mun dede, maza zuma ne, dole seda wuta. Shiyasa nace kada ki saurarama mijinki, kina ganinde duk irin biyayyar danakema Babanki amma yau yayimun gori. Kukan munafurci tasa, anan Zarah tashiga bata hakuri. Asabe tace tashi muje inrakaki dan Dije bata nan tayi tafiya. Tashi sukayi suka wuce gurin boka.
Tundaga ranar da Zarah tasama Alh, magani a abinci bekara maganar Jidda ba, shiyasa hankalin Zarah yadan kwanta, duk itama bata bacci sosai, dan tanason Jidda, tamafi sonta akan Jalila, dan halinsu daya da Jidda. Saukinta daya boka yace mata Jidda tana raye kuma yakusa dawowa gida.
Yau Jalila tagama final exam dinta, kuma ayau tagama shirya kayanta domin tafiya gida, driver take jira. Yana zuwa yadauketa, seda tafara biyawa cikin kasuwa inda kakansu yake. Dan ita bata zuwa gidansu, kwata kwata jininta be hadu dana Asabe ba, shiyasa tunda tafara karatu so 1 taje gidan.
Abakin shagon dayake zama tasameshi, tasowa yayi yana fara,a ganin Jalila, dan yana sonta sosai, tana temaka mashi, da yan kudi duk sadda tazo gurinshi, har bakin motar yakaraso, bayan motar yashig, bayan sungaisa da driver, Jalila tace ma driver yadan jirasu awaje. Gaisawa sukayi take fada mashi batun tafiyarta yau, dan tagama karatu, sosai yayi mata murna, sede beji dadin tafiyar taba zedena ganinta, dan itace abokiyar shawararshi. Jalila tace ai kaka kona tafi zanrika zuwa, kuma baga waya nan nabaka ba, zamu rika gaisawa, idan akwai wani abu seka fadamun tanan, idan yakama inzo senazo, ai babu nisa daga Kaduna zuwa Zariya.
Goge kwallan data zubo mashi yayi, Jalila tace kaka akwai abunda ke damunka, bantaba ganinka cikin damuwa haka ba. Murmushi yayi yace Jalila akwai abunda kedamuna sosai ma, kuma akan mahaifinki ne, da kuma Zarah,,,,,,,, anan yafada mata duk irin firar dayaji su Asabe sunayi da irin cin mutuncin da Zarah tayi mashi.
.
Seda Jalila tayi kuka, jin irin abinda Umminta keyi, hakuri tayi ta bashi, tace Kaka nima nasan akwai abubuwa da dama wanda Ummi takeyi, kuma bakowa bane yake zugata se su Inna Asabe da Dije. Amma Ummi tayi mani kashedi babba akan idan taji ina shiga maganar da babu ruwana aciki, har cewa tayi zata tsinemun, hakan yasa ma tunda nataho karatu ban koma gida ba, Dady ne kuma yanazuwa muna gaisawa.
Addu,a kawai nake masu, amma Kaka yaya Jidda tayi nisa batajin kira sede addu,a. Yace kikara hakuri insha Allah wata rana gaskiya zata fito, mucigaba dayi masu addu,a, kuma kamar yanda Zarah tafada maki, banason kishiga abinda babu ruwanki. Allah yayi maki albarka, kuma dan Allah Jalila kinga kingama karatu, kada kitsaya ruwan ido, kifitar da miji kiyi aure, banason zamanki agidan nan, kinga Falak tayi aurenta tahuta,kema Allaj yabaki miji nagari. Haka sukayi sallama takawo kudi tabashi, suka tafi.
Ayau Al,amin suka shirya yanda zasu dauko Jidda, Daniel yace kabari zan shiga gidan tunda yau munci sa,a shidaya yadawo, zanje muyi fira, zan bashi wiky nahada mashi da maganin bacci, dayayi zankiraka seka taho. Al,amin yace to amma megadin gidanfa? Daniel yace kabari nasan yanda zanyi dashi, kaide kazama cikin shiri, kadauki visa dinku da kayanka, nayima me taxi magana yanzu zezo yajiraka kuna fitowa kushiga yawuce daku. Godiya sosai Al,amin yayi mashi kuma yayi mashi alkawarin idan yasamu dama zezo surika gaisawa.
Zaune ya iske Joseph afalo yana kallo, bayan sungaisa Daniel yace joseph kaboye yanzu kaja kaya ko. Murmushi Joseph yayi yace haba ogana kaine bana ganinka, ya labari? Daniel yace lafiya lau, wata sabuwar whisky nakawo maka jiya wani abokina yabani ita, amma kasan bana shan irinta, shine nakawo maka. Katabar kwalbar Joseph yayi yace wow amma nagode, budewa yayi yafara sha, Daniel yace yauwa bama gateman dinka yasiyomun, irin whisky danake sha acan bakin titi.
.
Karbar kudin joseph yayi yafita yana tangadi yafita, bayan ya aiki megadi yadawo yacigaba da shan whisky dinshi suna fira, cikin lokaci kadan yafada bisa kujera bacci yadaukeshi.
Cikin sauri Daniel yadaukeshi yakaishi daki, yakira Al,amin. Jidda tana kwance adaki tasha giya da kwaya summata yawa tana bacci, Al,amin be tsaya bata lokaci ba yadauketa daga ita se riga da dogon wondo, kanta babu dankwali yasha tsohon kitson attache, fita sukayi ko tsyawa daukar jakarta beyi ba, ga uban kudin da Jidda ta tara aciki haka yabarsu suka fita, me taxi suka samu dan nan suka shige yadaga ma Daniel hannu suka nufi air pot, shima Daniel yafita. Tun acikin mota Al,amin yaciro jallabiyar daya siyowama Jidda yasa mata, yakama gyalen yadaura mata, sede duk abinda akeyi bacci take.
Suna zuwa ya sallami me mota suka jira aka kira sunansu yakamata suka shiga, ko acikin jirgin kwantar da ita yayi bisa cinyarshi tacigaba da baccinta. Suna isa yayima wani abokinshi waya yazo yadaukesu suka nufi gidanshi.
Ayau su Falak suka tare. Asabon gidansu daya keru, yayi kyau sosai, duk da bawani ginin karya akayi ba, amma yayi kyau, duk wanda yashiga ciki seya burgeshi, anzuba kaya masu kyau, dakin Falak yasha kaya masu kyau, kitchen dinta kamar nawata diyar me kudi.
Kwance Falak take akan cinyar Sameer suna fira, wayarta ce tayi kara, dauka tayi tace habawa Jalila nikam nayi fushi, yau satinki nawa da dawowa, amma kinkasa zuwa kiganni. Jalila tace dan Allah kiyi hakuri wlh banaso Ummi tasan gidanki zanzo, amma yanzu kiran danayi maki ma kwatancen gidan nakeso kimun ganinan ina shiryawa.
Falak tace to Allah yasoki, bara inturo maki da address din yanzu. Jalila tace Allah sa de mijinki baya nan dan wlh tsoran masu shaye shaye nake. Dariya Falak tayi tace ai babu abinda zemaki, kuma bayama nan, Jalila tace Allah Falak dande kinmatsamun inzo banason zuwa inga halin dakike ciki. Falak tace nide banason wani dogon surutu sekinzo. Kashe wayar tayi tana dariya, ta tura mata da address din.
Sameer yace keda Jalila ne hala? Tace emana, kasan metace, yace a,a wai cewa tayi Allah sa baka nan tsoron yan shaye shaye take. Dariya yayi yace ai zanso inga irin mamakin da Jalila zatayi idan tagammu amatsayin ma,aurata.
Au, kinga namanta tundazu inaso infada maki, dana fita shago nahadu dawani babban abokina Saleem, tare mukayi Zariya dashi amma shi yasamu aiki, awani kamfani na babanshi. Dama kuma bussiness yakaranta, nikuma nayi Pharmacy. Yarigani gamawa da shekara 1 danmu shekara 5 ne sukuma 4.
.
Bayan mungaisa yake tambayata menakeyi anan, nace mashi ai shago nane, shine yace meyasa ban bude chemist ba, natsaya bude shago, shine nace mashi kasan bude chemist ba sauki bane dole sekana da hanya shiyasa kawai na bude plaza.
Yace mun bana aiki ne, nace mashi wlh na nema harnagaji bansamuba, shiyasa kawai na hakura. Shine yace anjima da dare zezo yasameni ashago muzo nan gida ze amshi takarduna ya bama babanshi yanemamun aiki, kinsan babanshi babbane dan a Abuja ma yake aiki.
Falak tace kai amma gaskiya naji dadi sosai. Allah yasa asamu, yace Ameen. Tace bara intashi inshiryama Jalila abinci kafin tazo, yace to nide ina daki bacci zanyi idan tazo kitadani.
Jalila tafito cikin shirinta tace ma Zarah Ummi nagama shiryawa, zantafi. Zarah tace kijira driver yazo ya kaiki mana, yanzu zedawo. Jalila tace a,a Ummi kawai kibarshi zantafi sauri nakeyi kuma kawata tana tajirana. Kudi tamika mata tace gashi nan sarkin sauri, kigaisheta, amma kada kiyi dare fa. Tace to Ummi nagode.
Fita tayi tahau taxi tayi mashi kwatancen inda ze kaita, yace yagane gurin. Tafiya suke tana tunanin halin dazata iske Falak aciki. Dede wani hadaddan gida suka tsaya yace mata hajiya mun iso seki kirata kiji wane gidanne aciki. Jalila tace malam anya nanne unguwar kuwa, nifa duk cikin gidajen nan babu wanda yayi kama da irin gidan da,aka cemun Falak tana ciki. Yace tonide sauka kibani kudina ki kirata mana idan bata fitoba seki nemi wani ko. Sauka tayi tabashi kudinshi taciro wayarta takira Falak.
.
Cike datashin hankali Zarah tace Asid yaushe ka koma haka? Dama ba dan iska bane kai? Meyasa Mairo ta munafunceni? Zubewa kasa tayi tana kuka, Murmushin mugunta Asabe tayi, sannan tadauki kayanta tace tofa, Allah ya kyauta, nizan wuce hajiya kada dare yayi mun.
Saurin kamota Zarah tayi tace haba Inna kibari ki kwana mana, ai yanzu yamma tayi. Komawa tayi tazauna tana dariya aciki ciki, Sameer yace Ummi kiyi hakuri Baba mairo bata munafunceki ba, tayi abunda yadace ne, domin kinkasa rike marainiyar Allah shiyasa tayi kokarin kubutar da ita daga sharrinki.
Anan Sameer yafadama Zarah komai, kuka kawai takeyi. Falak tace Ummi dady bayanan ne? Dadyn Ubanki, ke awa dazaki tambayeshi? To wlh tunkafin inkirga 3 kubacemun daga gidan nan, cuta ce kun cuceni, bakomai amma wlh duk ranar da kika bari kafarki takara taka gidan nan sede adau gawarki.
Kuma duk ranar dakika zo neman mijina Allah ya isa, dan idan har ina raye bazan barki ki kara hada ido dashi ba. Kutashi kubarmun gidana, kai kuma nabaka daga yau zuwa gobe kamaidomun kudina dakasan nabaka, idan bahaka ba, wlh kotu zata rabamu.
Murmushi Sameer yayi yace haba Ummi meyayi zafi haka? Ni dama can bantaba kashe ko kwandalarki ba, wata jaka yadauko agefenshi yamika mata yace wannan kudinki ne, tundaga dubu 10 da kika fara bama Baba mairo har kudin sadakin da kika bani, babu kwabonki dayayi ciwo. Hannun Falak yakama wadda take ta kuka, suka fita, abakin kofar falon suka hadu da Jidda wadda tundazu take tsaye tana sauraronsu.
Da kallo tabisu harsuka wuce, mamaki kawai takeyi wai Falak ce da mijinta, harma ga alamar ciki ajikinta. Baki ta tabe takalli Umminsu datake ta kuka ta kalli jakar kudin dake gabanta tayi murmushi tajuya tayi waje.
Asabe tace hajiya kitashi mukoma daki kada Alh yazo ya iske ki haka, muje inada mafita cikin sauki. Jakar kudin tadauka suka wuce daki. Seda Zarah tagama kirga kudin tsaf taga sun cika, sannan tasakasu cikin drawer tadawo tazauna.
Inna kenake saurare, banida sauran wata dabara, dolene muje gurin boka babu bata lokaci kashe Falak zanyi, shi kuma mijinta da Mairo wlh bazan kyalesu ba, tunda suka munafunceni, haba dama biri yayi kama da mutum.
.
Nayi mamakin yanda Mairo tayi saurin canzawa daga son datakema Falak zuwa tsana, duk yanda akayi aranar da mukayi waya dake aranar taji duk wani plan dina, saboda inagama wayar babu dadewa tashigo tana kukan munafurci. Kuma gashi bayan bikin Falak babu dadewa itama tace zataje ganin gida, gashi haryanzu bata dawoba.
Asabe tayi dariya tace aini dama nayi zargin wani abu agame da Mairo, kawaide nayi shirune. Toyanzu duk ki kyale wannan maganar, akwai mafita sede tana da wahala, na manta danazo ban fada maki ba, Boka ya mutu.... zunbur Zarah tayi ta mike taname dafe kirjinta, tace nashiga 3 ni Zarah, boka yazakamun haka seda bukatar nemanka tayi sannan zaka mutu.
.
Asabe tace kwantar da hankalinki wannan badamuwa bace, duka shekaranjiya Dije tadawo daga tafiyar danace maki tayi, dama ban fada maki bane, kasar yarbawa taje wata mata ta aiketa gurin wani babban boka, domin bakaramin hatsabibi bane, yashafe bokan dakika sani, dan aikinshi alokacin dakika fadi bukatarki alokacin take biya, kuma shi aikinshi beda makari.
Sede bakananan mutane yakema aiki ba, daga matan gwabnoni shugaban kasa, sarakuna se manyan yan kasuwa da yan siyasa, sabida aikinshi ba dubunnai yake amsa ba, miliyoyi ne. Ko Dije Matar sarkin Zariya ce ta aiketa.
Zarah tazauna tace yauwa Inna wlh harnaji dadi, yanzu yaushe za,aje? Asabe tace kina ganin zaki iya harka dashi, kinsan fa bawasu kudi gareki ba, kada yayi maki aiki ki kasa biyanshi aiki yadawo kanki.
Zarah tace wlh Inna kozanyi yawo tsirara bazan bari Falak tacigaba da rayuwar jindadi aduniya ba,( wa iyazubillah). Zankashe konawa ne domin ganin burina yacika akanta, kuma aikin ba ita kadai za,ayi mawa ba, hada Alh, inaso ta karbomun maganin mallakar zuciya tayanda beda makari, kuma bazanji shayin suhadu da ita ba.
Asabe tace kinga kudi sunkaru tunda aikin mutum 2 ne, kawai hotonsu zaki bada atafi dashi sekuma kudi, amma bari inkira Dije ince takirashi taji yawan kudin. Amma hajiya inazaki samu kudi masu yawa haka? Uhm kede bari Inna, kinsan Allah yana temakona aduk lokacin danashiga matsala, jiya Alh yabani million 6 na kayan auren Jalila, dama niyata inkashe mata million 3 indau 3, kuma gashi yanzu wani aiki yashigo, inaganin kawai zanyi mata siyayyarta anan kinsan Alhjn atafin hannuna yake bawani abu zece ba.
.
Asabe tace hakama yayi, inaganin kisiya mata na million 2 kirike 4 kinga kome aka bukata bakida sauran damuwa. Zarah tace haka za,ayi Inna shiyasa nake sonki nasan idan har kina raye, Allah yabarmunke.
Bara inje insa Jalila tadora abinci ki kira Dijen kiji konawane nafison ayi komai cikin sauri. Tana fita Asabe takira Dije tafada mata komai, nan take Dije tafada mata yanda zata ce.
Bayan Zarah tashigo Asabe tace uhm, aiki game kareka, kinsan Dije da mutane, muna gama waya takira bokan harsungama magana, tafadi mashi matsalarki, harya yanke mugun hukuncin dazeyima Falak, danshima yanajin haushin masu cin amana. Dariya Zarah tayi tace kai amma naji dadi, gaskiya Dije kawace tagari. Nawa yace kudin aikin?
Uhm aini hajiya abunne naji dayawa, kodayake biyan bukata yafi dogon buri, boka yace maganin dazeyima Alh, zaki mallakeshi, dayanda shine zerika aiki amma kudi suna gurinki, ko naira 1 baze iya kashewa ba, seda izininki, daya samu kudi kece ze kawomawa. Kara washe baki Zarah tayi tace kai, kice nazama babbar Hajiya, kawai fadimun kudin konawa ne, nasan nan da dan lokaci zanmaida mafiyansu.
Uhm na Falak de yace kibada million 2, na Alh kuma 1 da rabi, se kuma kudin da Dije zatayi kudin mota dasu dubu 50 sena abinci dan kwana 2 zatayi. Zarah tace kai kudinma babu yawa tunda acikin million 4 ina da saura, bakomai zan bata dubu 100 gaba daya nasan zasu isheta, gashi ku kuma ba accounta gareku ba bare intura maku.
.
Asabe tace mene account, kai mude munfi gane murike kudi ahannu, barema Dije ai tasaba tafiya da manyan kudi, haka kawai kitura mata kudi a banki taje cirowa ma aikatan suga batayi kama da wadda zata fidda kudi masu yawa ba, su kira mata yansanda. Kawai asamu. Babbar Gana, ashirya mata su aciki, seta dora kayanta asama babu wanda zece kudine aciki.
Zarah tace toshikenan ai tunda aikinta ne, yanzu kibari gobe monday, se inje banki da Ganar su shiryamun su acan idan nazo gida se tasaka kayan asama. Asabe tace nima gobe zankoma dawuri semu dawo tare da ita jibi idan narakata tasha se inwuce, amma bake zaki kaimu ba, kisaka driver saboda idon mutane. Zarah tace toshikenan, kema kinada dubu 20. Asabe tace ah, lallai nagode.
Zaune suke adakin Baba mairo Falak tanata kuka, Baba mairo tace dan Allah kidena wannan kuka, babu abinda ta isa tayi maki wanda Allah neyi maki ba, tabbas dole munemi temakon Kawunka Sameer, kasan ance idan kana da kyau ka kara da wanka. Halima tace ai baza,a bari se gobe ba, kutashi kawai muje, tashi sukayi suka nufi motar Sameer.
.
Azaune suke afalonshi bayan sungama gaisawa Baba mairo tayi mashi bayanin komai. Shiru yayi nawani lokaci sannan yace toku baku fahimci komai ba agame da rashin son Falak ta hadu da Alh? Inaganin koma wane asiri ne akayimashi to makarin yana jikin Falak, kuma dole sesun hadu zamu iya temakonshi, idan har mukayi nasarar karya asirin jikinshi tosemu fara bashi temako, domin idan har babu tsari ajikinshi komun karya asirin zata iya yin wani.
Yanzu a ina yakamata kiganshi? Eto dazude damukaje baya gida sede bansani ba, ko yakoma, amma zan tambayi Jalila idan haryana gida se ince tafada mun. Malam yace hakane, amma banaso kifada mata dalilinki nason ganinshi, kawai kice kinason gaidashi ne, kinsan tsakanin da da Mahaifiya.
Zamu dage da addu,a kuma zanbaku wanda zakurikayi kullum kafin ku kwanta bacci, insha Allah komai zezo dasauki. Godiya sukayi mashi suka tafi.
Jidda ce tashiga dakin Zarah tadebo kudi masu yawa, tazo fida suka hadu da jalila, Jalila tace wai dan Allah meyasa Yaya jidda kika canza hali ne? Kinsan fa duk wasu halaye marasa kyau dakike aikatawa agidan nan nasansu, wai yau kece da sata, kuma kudin Ummi, haba meyayi zafi Haka, ni wlh banga abinso ajikin wannan saurayin naki ba, kum....saukar mari taji afuskarta shiya hanata karasa maganar datakeyi. Inaso intuna maki nice yayarki bakeba, kuma inada ikon yin duk irin rayuwar danaga dama banason sa ido, zanyi mugun saba maki idan kikace zaki rika samun ido. Tunda har Allah ya rufamun asiri babu wanda ya isa yatonamun.
Dan haka kifita a idona idan harkinaso incigaba da kallonki amatsayin yar uwa. Shikenan yaya dan Allah kiyi hkr insha Allah bazan kara shiga harkar kiba, inde hakan zesa bazaki cireni amatsayin yar uwarki ba, kinsan banida kamarki. Juyawa tayi tafita tana kuka. Jidda tafita tanufi dakin viju.
.
Tanazuwa tasameshi yagama shirinshi dama yace mata tafiya zeyi ta kwana 2 shine yace yanason kudi dubu 100 daya dawo zabata, shine tadauko mashi na Zarah. Kallonshi tayi kamar zatayi kuka tace haba Viju yanzu harka shirya ai seka bari mudan huta kona bankwana muyi ko, kasan zanyi missing dinka kwana 2. Haba Baby kada kidamu abakon tafiya ta sun shirya nikadai suke jira kibari idan nadawo ai muna tare ko. Dakyar ya lallabata yafita, yahau mashin aranshi yana fadin nidake har abada, hakawai yarinya kinkoma kamar kwanko, mezanyi dake, ta ko ina kinzurma haka kawai kirika morata nikuma ina wahala, gara inkara gaba, dama kudin hayata sunkare.
Bayan kwana 1 su Asabe sukazo dashirinsu natafiya, kwana 1 sukayi duk wani shiri sungama, anshirya kaya asaman kudin Zarah tabasu hoton Falak da Alh, wanda tunkafin Hajjo ma tarasu suka dauka lokacin graduation din Jidda, dayake Jalila tanada na Falak ita kadai, shine Zarah tadauko. Acikin jakar Dije aka saka hotunan, sukayimata sallama tasa driver yakaisu tasha. Asabe tace to sena kara dawowa ko.
Alhamdulillahi Sameer yasamu aiki A Genaral hospital na kaduna, abangaren pharmacy sosai su Falak da Halima sukaji dadi, suma rayuwa zata canza masu, wani abokinshi malamin islamiyar dasuke koyarwa tare yamikama amanar plaza dinshi, komai yana tafiya dede.
Suna zaune afalo Jalila takira Falak tafada mata Dadynsu yana gari, sosai taji dadi tayimata godiya tace gobe sunanan zuwa..
Kwance tasamu Jidda akasa tana ta faman amai, cikin sauri Jalila takarasa shiga dakin tana fadin dama Yaya jidda nace maki bakida lafiya tun kwanakin baya kikacemun lafiyarki lau, saboda bakison zuwa asibiti, kalli yanda kika koma jikinki kamar baki cin abinci, dan Allah kiyi hakuri muje asibiti, Jidda tace Jalila banason zuwa asibiti kisiyomun magani kawai. Jalila tace wlh a,a yaude tunda Dady yana gida semunje asibiti. Fita tayi domin kiransu Zarah.

Atare suka shigo dakin da Jidda take, kwance suka sameta gaba daya tagama galabaita, Zarah da Jalila duk sun rude, Alh yace su gyarata bari yafiddo mota a kaita asibiti. Cikin lokaci kan kani suka gama shiryata suka wuce asibiti.
Suna zuwa suka nufi gurin likita, anan yafara dubata, duk tambayar dayake mata bata bashi amsa, ganin haka yace masu sudan jirashi awaje. Matsowa yayi yace Jidda inaso ki kwantar da hankalinki kibani amsar tambayar dazan maki, jikinki yayi laushi sosai, idan har baki fadi abinda kike jiba zaki shiga matsala.
.
Kwallan dake idonta ta goge, takalleshi, ahankali tace, Dr. dan Allah kowace irin cuta ka gano ajikina inaso karufamun asiri kada kabari iyayena suji. Murmushi yayi yace Jidda waya fada maki kina dauke da wata cuta? Nide Dr, kawai inaji ajikina dole asamu cuta ajikina.
Shikenan zansa ayi maki test duk abinda result yabada zamu gani, a,a wlh idan har Dady yasan za,a yimani test dole yaga result din dan Allah kada kabari amun test. Kada kidamu. Bazasu san anyi maki ba, zan temakeki. Fita yayi yakirawosu.
Alh, agaskiya jikin Jidda yayi sanyi dole zamu kwantar da ita asa mata ruwa, sbd maleria tayi mata kamu sosai, gashi tayi amai ruwan jikinta yayi kasa, amma insha Allah ko zuwa gobe zata samu sauki, dan bawani babban ciwo bane, kawai aman datayi ne yasa jikinta yayi laushi. Alh, yace babu damuwa Dr, kayi duk abinda yadace bamusan bata da lfy ba, se Jalila ce take fada, kasan Jidda batason magani shiyasa ta hana Jalila tafada. Allah yakara sauki.
Nurse yakira suka kaita daki aka saka mata drip, Alh yace sukoma gida tunda tayi bacci seku shiryo kafin ta tashi, Jalila tace a,a nide zan tsaya anan, Dr, yace kije kada kibar Hjya ita kadai, tunda tayi bacci harzaku dawo bata farka ba, akwai allurar baccin da aka zuba adrip din ai. Sallama sukayi mashi suka tafi. Suna fita tabude ido, Dr, yasa nurse suka turata zuwa dakin daza a dauki jininta.
.
Mamaki ne, yakama Dr, ganin result din da wata nurse takawo mashi, duk da dama yayi zargin hakan amma yayi mamakin ganin yadda cutar tayi nisa ajikinta amma ba,a dauki wani mataki ba, duk da yasan laifinta ne bataso asan tana dauke da cutar. Kallon Jidda yayi itama shi take kallo. H,I,V gareni ko Dr? Uhm dama nasan dole hakan zata faru dani, duk da laifina ne, da nazo an aunani dawuri da bankai wannan matakin ba. Dr, yace hakika Jidda kinyi wauta da har kikasan kina dauke da wannan cuta amma kika ki zuwa asibiti kifara karbar magani, gashi yanzu tayi karfi ajikinki. Amma kada kidamu idan har zaki kiyaye dokokin dazan baki zakicigaba da rayuwarki, tunda baki kai last stage ba.
Zaki sha magunguna kuma babu tsallake, kuma zaki dage da cin duk wani abu megina jiki insha Allahu zaki samu sauki kuma jikinki bazeyi saurin nuna kina dauke da cuta ba. Zan baki maganin wata 1 idan kika shanye sekidawo ki karbi wasu amma idan kika dawo zan hadaki da wanda zaki rika amsar maganin agurinshi cikin sauki, kuma zanzuba makisu acikin wata roba, babu wanda zegane wane irin maganine sewanda yasanshi, nide fatana ki kiyaye. Godiya sosai Jidda tayi mashi se kuka takeyi, aranta tana fadin wlh tunda aka sakamun cutar nan nima sena saka ma wasu.
.
Asabe yana zuwa gida tasamu mijinta tayi tamashi bala,i adole seya saketa, takaji dazama dashi garin zata bari, dayake dama umarninta yake bi, nan take yasaketa, yana sakinta yaji kanshi ya sara, yaji kamar yadauke mashi wani abu me nauyi, dan danan ya kwanta saboda jiyake kamar ze fadi, ganin haka yasa Asabe shigewa daki tahada duka kayanta tafita domin samun dillaliyar dazata siya, malam Garba yafi minti 30 akwance, yana tunanin abubuwa da dama, dayaji kanshi ya lafa yayi hamdala yatashi yadauro alwala yafara nafila, dan jinshi yake kamar kamar duk wata damuwarshi ta kau, saboda yarabu da Asabe.
Gidan Dije taje suka kara tattaunawa, sbd gobe zasu tafi, Asabe tace kinsan daga gidan Tabawa nake dillaliya, anjima zatazo tasayi kayana, dan babu abinda zanyi dasu muda zamu bar gari. Dije tace nima de sayar danawa zanyi, dama bawani yawa garesu ba, ni har na kosa gobe tayi wlh mubar garin nan nahangomu a Lagos cikin daula. Dariya sukayi suka kashe.
.
Bayan sunkoma asibitin dayake dare yayi suka dan zauna dan jikin Jiddan yayi sauki tasha drip, Zarah tace Alh, kutafi kaida Jalila nizan kwana da ita, Jalila tace a,a Ummi kibari inkwana. Alh, yace aike yarinya ce Jalila jinya kuwa ai se babba. Kibarta takwana tunda kwana daya ne gobe zasu dawo gida ai. Sallama suka yimasu suka tafi, ganin suntafi Zarah tafita takirawo Asabe, tafada mata abinda yafaru, tace amma goben zanciro kudin bana son Alh, yagane, nasan dawuri zasuzo duba Jidda zansa likita yabar sallamar se da rana, suna zuwa sena barsu nadawo gida amma fa kutaho dawuri.
Washe gari dasafe Dr, yashigo anan Zarah tafada mashi bukatar ta, yace toshikenan babu damuwa dama akwai saura drip 2 daza,a samata zuwa azahar nasan sun kare seku tafi.
Gurin karfe 8 Alh da Jalila suka shigo, hamdala Zarah tayi, bayan sungaisa, suka tambayi jikin Jidda, Zarah tace dasauki sosai ma, dan tadena aman kuma taci abinci sosai jiya. Alh, yace Allah yakara sauki, bara inje gurin Dr, inji yaushe za,a sallameta. Zarah tace ai yashigo dazu, yace seda rana sbd akwai drip 2 da za,a samata. Amma kuzauna bara inje gida inyo wanka bazan iya yin wanka anan ba, idan nadan huta se indawo. Alh yace hakane gsky nasan bakiyi bacci sosai ba, jiya, bakomai kitafi nima zuwa 9 zan wuce office akwai abinda zanyi tunda ga Jalila nan seta zauna agurinta, Jidda tashi kici abinci kinji. Sallama Zarah tayi masu ta amshi makullin motar Alh, tace idan taje seta bama driver yakawo mashi.
Tana zuwa gida ta iske su Asabe har sunzo, farinciki ne, yakamata tabude gidan suka shiga tabama driver key din motar tace yakaima Alh, wanka kawai tayi tace sukirata taje takarbo kudin, tace suduba kitchen idan akwai abinci suci idan kuma babu sesu dora kafin tadawo.
Tana zuwa banki babu bata lokaci dayake akwai wanda tasani dan danan aka shirya mata kudin acikin jaka, tadawo gida, duk da tadan dade, tana zuwa gida tasau driver yadawo, tasashi yadauko mata kudin. Kaya aka dora asaman kudin babu wanda zece kudine aciki, takirawo driver tace yadauka zekaisu tasha, yana fita ta dauko hoton Alh, dana Falak wanda tasamo adakin Jalila tabasu, Dije takarba tasa ajakarta, Zarah takawo dubu 30 takara ma Dije tace tarike ahannunta. Asabe tace nima ai tare zamu tafi senaga tashinta daga can nima inwuce dan nace ma Babanki bazan dade ba, Zarah tace toshikenan Allah ya tsare nima asibiti zankoma. Sallama sukayi mata suka fita, itama tashiga motarta tawuce asibiti.
.
Suna zuwa sukaci sa,a mota takusa cika, seda driver yatafi sannan suka se su 2 ne zasu tafi, Dije tace wannan jakar asata abayan mota kayane aciki amma dan Allah aturata ciki sosai kayan sana,ata ne, drivern mota yace karkiji komai madam kawai shiga mota muware, seda suka biya kudin motar sannan suka shiga, Wata inyamura suka samu akusa da ita Asabe tazauna Dije dazauna kusa da Asabe, suna jiran mutum 1, Asabe baki yakasa rufuwa sun sami duniya. Dije tace gsky Kawata nayi farin cikin haduwarmu gashi ta sanadiyarki zanzama babbar hajiya. Asabe tace kede bari wlh idan muka isa Lagos dole muyi kara,in yanmatancin mu baruwana da harka da tsofaffi, yara zansamu masu jini ajiki tunda inada kudi inkashe masu surika biyamun bukatata. Dije tayi dariya tace ashede kema kina irin tunani na. Kinsan hanyar Lagos batada kyau shiyasa nace asaka mana kudinmu abayan mota nace masu kaya ne, sbd kada wani yasan akwai kudi masu yawa acikin jakar, kinga baruwanmu da tunanin yan fashi. Asabe tace gsky kina da dabara. Dahaka mota tacika suka daga zuwa Lagos.
.
Sameer ne da Saleem da Falak, amota suna hanyar zuwa asibiti dan Falak tayi waya da Jalila take fada mata suna asibiti Jidda ba lfy shine suka wuce dubata dan tadafa mata Dady yana asibiti shima.
Waya takira Jalila tafito tayi masu jagora, Saleem se kallonta yakeyi yana murmushi, Sameer yace kun tsaya sewani sunne sunne kukeyi sekace bakin fulani, mude bamuson kilibibi. Saleem yace ina ruwanka sa ido, kasan kowa datashi kalar soyayyar. Falak tace Allah baka hkr kada kacinyemun miji, dariya suka saka baki daya.
Da sallama suka shiga dakin, Alh, yana zaune abisa kujera ya amsa sallamarsu, har kasa suka duka suka gaishe shi, ya amsa da fara,a suka tambayi jikin Jidda yace dasauki. Falak tace Dady ina kwana, mikewa yayi yana kallonta cike da mamaki, dede lokacin Zarah tashigo da sallama, cak ta tsaya ganin abinda yake faruwa, kowa hankalinshi yana kansu, babu wanda ma yasan da shigowarta. Ganin babu wanda yakula da ita yasa tayi saurin juyawa tafita, mota tanufa tayi gida dasauri hankalinta tashe.
Alh, yace Falak, tace na,am Dady, komawa yayi yazauna yadafe kanshi dan jiyayi yana juya mashi, Sameer ya matso kusa dashi yana fadin Alh, lfy de? Yace kiramun Dr, dasauri. Fita yayi shida Jalila suka kirawo Dr, yana zuwa Alh, yace bayajin dadi kanshi yana juya mashi, nan Dr, yace ya kwanta bisa dayan kadon yafita yakawo mashi magani yabashi yasha sannan ya aunashi, yace Alh, babu abinda yake damunka kila de rashin bacci ne yasama ciwon kai, amma ka kwanta kadan huta zaka samu sauki, godiya yayi mashi sannan yafita.
Ruwa Sameer yadauka yayi mashi adduo,i sbd dama kawunshi yafada mashi akwai asiri ajikin Alh, hakan yasa ya tofa mashi addu,a dan yasan ganin Falak ne yasa mashi ciwon kan. Cikin ikon Allah yana shan addu,ar yasamu sauki.
.
Zarah tana zuwa gida tashiga daki kamar zatayi ihu sbd tashin hankali, durowarta tabude tafara binciken sauran maganin mallakar da boka yabata tasama Alh, a abinci dayake tarage kadan. Ajiyar zuciya tayi dataganshi.
Kitchen tanufa domin doramashi abinci farinciki duk ya rufeta tana fadin wlh karyarki tasha karya kitonamun asiri, kai kuma Alh, zanga bakin dazaka samu damar yimani maganar Falak, dakaci abincin nan zaka dawo hannu, Dadi nama dayane, tana gidan mijinta bazasu samu damar zama su dade tare ba, kafin sukara sabawa nasan Dije ta isa gurin boka daga ranar kungama yawo. Kwance maganin tayi tajuyeshi acikin plate tayarda ledar ta ajeshi tadauko tukunya takunna famfo zata daurayeta. Maganin tazuba acikin tukunyar tazuba ruwa, tana fadin gara kutafasa tare nasan zefi jikuwa kuma zefi aiki, dauko tukunyar tayi zata dora bisa gas, juyawar dazatayi silbi yajata tafadi tukunyar tafadi ruwan yazube.
Wani irin ihu tasaka tana fadin nashiga ukku, shikenan tawa tasameni, tashi tayi takashe gas din tafita tana kuka, daki takoma tazauna tabuga tagumi tarasa meke mata dadi, wayarta ta dauko takira Asabe, amma akashe, wurgi tayi da wayar tasa kuka. Ganin kuka baze mata ba, yasa ta tashi tashiga wanka tana fadin ai nasan yarinyar tanada Imani bazata iya fadama Alh, abinda namata ba, kawai zan gwada mashi komai lafiya kafin wani lokaci aikin boka yafara, da wannan tunanin tasamu kwarin guiwa tashiga wanka.
Alh, yakalli Falak abin mamaki yaga hada ciki ajikinta, wasu hawaye yaji suna zubomashi yagoge yace Falak se kuma yayi shiru, tashi yayi yace haryanzu Zarah bata dawoba, kila bacci yadauketa, nara inje office inbada sako, daga can zanwuce gida banajin dadin jikina, tunda ruwan yakusa karewa zancema Dr, kutaho gida idan yakare kusameni agida.
.
Zaune suke afalo Alh, yace ma Jalila kirawo Umminku najita shiru, Cike da karfin guiwa Zarah tashigo tace a,a Alh, harkun dawo kunganni shiru wlh, kaina naji yana ciwo ina gama wanka nasha magani nakwanta kawai ina farkawa naga lokaci yatafi, sannunku.
A,a yau kuma amare ne agidan namu, ai dama nasan da kunji Jidda ba lfy zaku taho, hala Jalila ce tafada maku, zama tayi kusa da Alh, wanda yaketa kallonta cike da mamaki, danshi yaji ana fadin Falak amarya, kuma gata da ciki towai yaushe ma tayi aure? To tama gama karatunta? Shi yadade beji ankira sunanta agidan ba, bare kuma yasata a ido. Zarah takatse mashi tunaninshi tace Alh, munkusa samun jika agidan nan fa. Sameer, Saleem, Falak, Jalila harma da Jidda kallon mamaki sukema Zarah.
Alh, yace dan Allah kufitar dani duhu, naji kuna wasu maganganu wanda bansan dasuba. Zarah tayi murmushi tace Alh, kana nufin baka gane Falak ba? Yace a,a ammade nasan Ameer yarasu, Falak da Jalila sungama makaranta, nayi masu alkawarin wucewa wata, kuma gashi Jalila ce kadai tayi karatu ya akayi Falak batayi ba, hartayi aure nibansaniba? Zarah tace lallai Alh, da badan nasanka ba da se ince kasamu tabin hankali, kabada auren Falak da hannunka, kuma kazama waliyinta kabani kudi nayi mata siyayya sannan kace kamanta, haba Alh, kode ciwon mantuwa yafara samunka? Falak fa da bakinta tazo tace tasamu mijin aure bazatayi karatu ba, har na hana kace bakomai tunda mijinta yanada hankali setayi agidanshi.
.
Dafe kai Alh yayi sbd rudun daya shiga, ganin Zarah tana iya sakama shi ciwon kai yasa Sameer yamatso kusa dashi yace Alh, kada kasama kanka dogon tunani ba,a son irin wannan yana iya yawo maka matsala, addu,a yakama kayi hakane Ummi batayi karya ba, nine mijin Falak kuma kaine kabani ita kazama waliyinta idan katambayi mutanen unguwar nan zasu fada maka anyi haka. Alh, yagoge kwallan idonshi yace shikenan nagode Sameer, tabbas nasan akwai abinda yasameni, sede bansan komenene ba, amma naji dadi sosai tunda Falak tasamu miji nagari, Allah yabaku zaman lfy.
Falak inaso kiyafemun kada ace nakasa rike amanar da Hajjo da barmun, idan har akwai wani abu dana yimaki kiyafemun bansan awane yanayi nake ciki ba, sede zanyi yanda kace bazan tsananta bincike ba, sema ingodema Allah daya yayemun abinda nakeji. Nagode. Sosai. Gashi ankusa bikin Jalila kema Jidda naso ace kinsamu miji dase ayi tare, amma bakomai Allah yakawo maki mafi alkahiri.
Zarah tayi murmushi tace ameen, Alhn yace wai ina Baba mairo ne, haryanzu bata dawo bane? Zarah tace e kasan ai tadade bataje gidaba, dama tace zata kwana 2. Anan suka cigaba da fira sosai Falak taji dadi yau tana fira da Dadynsu wanda rabonta da haka tadade, tashi su Sameer sukayi suka masu sallama yace zedawo anjima yadauketa. Jalila tace tashi muje daki, Alh, yace a,a kuzauna anan munyi fira kinga anjima zata tafi. Zarah ta maka mata harara, tace Jidda tashi muje kiyi wanka kici abinci ki kwanta nasan kingaji. Haka suka zauna suna tafira cike da jindadi.
.
Tafiya sukeyi duk sungaji sunyi bacci harsuntashi, gashi magriba hartayi basu isa ba, Asabe tace kai, gsky Lagos akwai nisa, aini tunda nake bantaba tafiya menisa haka ba. Dije tace kede bari, sede dana tuna rayuwar jindadin dazamuyi idan muka isa se inji banajin gajiya. Asabe tace.........Innalillahi wa inna ilaihir raji,un shine abinda sukaji driver yana fadi, hakan yasa Asabe tahadiye maganarta suka maida hankalinsu ga driver. Meyafaru mukaji ana salati? Driver yace to jama,a Allah yahadamu da yan fashi kowa yafara addu,a. Tunkafin yagama maganarshi yataka burki ganin ansetasu da bindiga, parking yayi gefen hanya. Dije tace ma Asabe anshi wannan dubu 15 ne idan akace mubada kudi kibasu nima. Zan basu na hannuna, kada kifada masu akwai kudi ajaka, nasan dasun duba zasuga kaya tunda sauri sukeyi dare beyiba bazasu tsaya dubawa ba.
Kowa yafito, sukaji ana fadi, haka kowa yafito suka fara karbar kudi suna binciken motar, inyamura ana bude jakarta aka samu dubu 50, suka anshe nan tasaka kuka tana fadin nabani kuyi hakuri Oo, yarona beda lafiya zankai masi kudin magani, daya daga cikinsu yace kimana shiru ko in fasa kanki, aka zo kan Asabe ana buda jakarta aka samu 15k, suka dauke, ana zuwa kan Dije aka samu 20k itama suka kwashe, ganin sunsamu kudi agurin kowa yasa wani yace ya isa haka kuzo muware kunsan oga yana jiranmu gashi dare biyi sosai ba, kutashi ku bace mana anan, suka fara shiga mota, Inyamura ce tafara shiga se kuka,takeyi, sannan Asabe tashiga
.
Asabe ta kalleta ganin yadda take kuka yabata dariya tace inbanda abunki darashin dabara inrin taku yaushe zakitaho Lagos da kudi ajaka har dubu 50. Kinga sunyi maki hankali gobema seki kara tafi baki boye kudiba. Muyanzu wazece muna da miliyoyi acikin boot? Kuma gashi an anshi kadan zamu wuce abunmu. Driver yace wai mekuke jira ke ki matsa masu su shiga muwuce mana. Dije tace ai bansan wane irin surutu Asabe takeyima wannan matarba duk kintare hanyar.
Dasauri Inyamura ta ture Dije tayi waje tana fadi wallasi akwai kudi a boot. Cak kowa yatsaya yana kallonta. Dan fashi ya ce wane boot, tace amota. Dariya yayi yace kowa yafito, nan take jikin Asabe da Dije yafara rawa, Asabe tace nashiga 3 bakina yajamana. Anan aka fiddo kaya, aka ciro jakarsu, yace suwaye keda wannan jakar, su Dije suka ce mune, yace tokuzo nan, kai driver daga ina kuke, yace Kaduna, to kusauran kowa yashiga mota, suna bude jakar suka cire kayan sama anan suka ga makudan kudi, nan take suka maida ma kowa kudin shi suka ce sutafi subar su Dije anan,
Haka suka tafi suka barsu suna ta kuka, haka suka tasa keyarsu suka nufi gurin Ogansu, suna zuwa suka zazzage duka kudin, Ogan yace shegu, ina kuka samo wadan nan kudin haka? Wlh Oga wata inyamura ta temakemu muka samesu agurin wadannan, Yace sake dubamun jakar hannunsu, ana duba jakar Dije, aka ciro hotuna, yace Oga babu komai se hoto, yace mugani. Cike da mamaki yamike tsaye yana kara murza idonshi yace Hajjo, dama kina Raye??????
0 comments:
Post a Comment